Kai Gimbiya Binta ta girgiza, tana mai fad’in ‘’Ba ki san
makircin wanga d’iya ba ne Didi, bari dai na baki labarin kad’an daga cikin
halin ta.’’ Nan fa ta saka Bintu a faifai, k’arya da gaskiya haka ta had’a ta
shedawa Gimbiya K’amariyya, ba don komai ba ko don ta samu mai taya ta saka
baki a hana Bintu komawa makaranta.
Jiki na kyarma Bintu ta fito, Allah ya sa shigowar Inna
kenan su ka had’u a rariya. Inna na ganin Bintu ta san akwai abin da ke
damunta, tambayar duniyar nan Inna ta yi mata, amma ta k’i fad’a mata, sai
k’arya ba ta jin dad’i ta yi mata. Ta na mai mata Allah ya sauwake ta ja ta
gefe ta bata fatan dusan da ta taho mata da shi dan karin kumallo kafin ta yi
na ta wajan, tabar Bintu ta na zabga loma.
*** *** ***
Da yammaci, sati guda kenan da dawowa su Bintu.
Bintu kwance tare da Inna da Habibu zaune bisa tabarma a
tsakar gida su na shan iska dan kuwa zafi ake na gaske ma kuwa. Inna da ya
Habibu ke hirar halin da ake ciki na fari a yanki, su na muhawarar yanda za a
sami mafita, in da Bintu ta yi kwance can gefe, gaba d’aya tunanin Aisar ne ya
addabi rayuwar ta, dan ko yanzu ma tunanin na shi ta ke yayinda ta ke murza
zobensa da ke sanye cikin yatsunta.
Baba ne ya shigo kamar an jefoshi, fad’i ya ke ‘’An dai
wad’i(fad’i) ba nauyi!'’ Tashi su ka yi tsaye a tare, Inna na mai tambayar ‘’Malam
lafiya kuwa?’’
Baba ya ce ‘’Yo to tunda aka fara fari ina mu ka ga lafiya?
Yau fa kur’ia aka doka a fada, kuma sakamakon shi ne za mu nemi sulhu da kuma
taimako daga wajan mak’iya abokan gaba, eh masarautar Fabarusa!’’
Babu wanda bai girgiza ba jin kalamin na Baba. Habibu ne ya
ce "Gide a rasa in da za a k’ask’antar da kai sai wajan abokan gaba?’’
Baba na mai d’aga kafad’a ya ce "Ta dai faru ta k’are an yiwa mai damo
d’aya sata, don kuwa magatakarda ya tura wasik’a zuwa Fabarusa, idan an amsa
gobe da sassahe za a d’auki hanya tare da Uban Gabasawa(Sarki) da kansa
zuwa wajan abokan gaba nema sulhu’’
Ya na gama fad’in haka ya shige ciki Inna na mai bin
bayansa. Shi kuwa Habibu silifa d’insa ya ja ya saka sannan ya fice, wato ya
fita yad’a zancen kenan. Bintu kuwa komawa ta yi zaune abin ta, duk da dai
itama ta yi tunanin neman taimako daga Fabarusa, jin za a je d’in da gaske sai
ta tsinci kanta tana mai fad’uwar gaba.
********
Washegari da sassafe Mai Martaba da tawagarsa su ka d’auki
hanyar Faburusa. Babban gida sam babu armashi kowa cikin fargaba ya ke. Gimbiya
K’amariyya tafi kowa shiga tashin hankali, gashi tun jiya ta ke kiran wayar
Yerima Barde amma wayar ba ta shiga. Gani ta ke kamar alakarsu ce ta zo
k’arshe. Ita kuwa Gimbiya Binta damuwarta daban ne, tun dawowar su ta ke ta
sak’e-sak’e akan abinda za ta ce da Takawa(sarki) ya canza mata baiwa, dan ita
aradu ba za ta koma makaranta da Bintu ba.
Ranar Allah ya taimaki Bintu ta yi aiki da hidimarta cikin
Babban gida ba tare da ta sami matsala daga wajan Gimbiya Binta ba. Da yammacin
ranar ta raka Yerima Nadir Lambu, nan su ka ta tad’in su kamar ta sami babban
mutum. Labarin makarantar su ya ce ta bashi, nan fa Bintu tai ta bashi, har da
labarin Aisar. Bata san ta na kewan sa sosai ba sai da take maganar sa a zahiri
ba a zuci ba, wata k’ila ma ya manta da wata Bintu, abun da take fad’awa kan ta
kenan. Shi kuwa Yerima Nadir kallon ta kawai ya ke ba tare da ya fahimci in da
ta dosa ba, ballantana ya gane halin da ta ke ciki.
******
Bayan magrib ta koma gida, shiru har lokacin sarki be dawo
ba. Bayan sun ci abinci suna kwance a falo ita da Inna, sun ci sa’a akwai wutar
lantakarki, fanka ke kad’awa ta na mai fitar da k’ara alamar ta fara
gazawa.Akwatin radiyon Inna su ke sauraro in da ake labaran duniya.
Jin mai karanto labarai ya ce ‘’Jikin shugaban k’asa Gaddafi
Nur ya tashi, za'a fitar da shi zuwa k’asar waje domin ba shi taimako’’ Ya sa
Bintu tashi zaune da sauri ta na mai tambayar ‘’Inna daman shugaban K’asa be da
lafiya?’’
‘’Eh Allah sarki ai be da lafiya, yo to da k’alau ya ke ai
da tuni ya magance wanga fari da mu ke ciki, dan ba kya sauraran labarai ne shi
ya sa ba ki ji ba’’ Inna ta amsa mata.
Bintu na mai dafe kai ta ce "innalillahi wa
innailaihirrajiun, Allah sarki Monsieur Aisar, suna cikin tashin
hankali’’
Inna ta dubeta, ‘’Waye shi kuma Bintu?’’
Nan Bintu ta kwashe labarin Aisar ta fad’awa Innar ta.
Fuskarta na nuna rashin jin dad’in labarin, Inna ta had’e fuska. ‘’Ai da
walakin goro a miya, shi ya sa mana na ga kin dawo wata wuri wuri da ke, d’an
shugaban k’asa Bintu?’’
Bintu na mai tura baki ta ce ‘’Yo to Inna minene ciki? Ba fa
wani abu ba ne taimako gareshi kawai........’’
‘’Wani taimako? Chiim zanne la nya bangin! (rufa min baki ko
na buge ki)’’ Inna ta katse ta, ta k’ara da ‘’Taimako ne har da siya miki
turare ma su tsada haka Bintu? Binta sudan? Kafin kafin? Danduala? Turaren da
sai Saraki kad’ai ke sawa? Kuma ki na dai ganin yanda Gimbiya ta yi mi ki
saboda shi? ngoy awo gulgin d3! (ai ga abinda nake fada), yanzu ba za ta bari
ko koma maranta (makaranta) da ke ba!"
Komawa Bintu ta yi ta kwanta, ta na mai lumshe idanu. Kana
ta ce ‘’Allah ya ba shi lafiya’’
"Wa fa?’’ Inna ta tambaya. Bintu na mai bud’e idanunta
ta ce ‘’Mahaifin Monsieur’’
Tsaki Inna ta ja, kafin ta amsa da ‘’Yo to amin, amma kanki
ya kamata ki yiwa addu’a fero (yarinya) a halin da ki ke ciki, ki ma cire
wannan mutumin daga ranki, can ga su gada zomo ya ji kid’an farau ta’’
‘’Inna Allah na sa a raina." Cewar Bintu. Kamar daga
sama su ka jiyo Habibu daga tsakar gida ya ce
"Kin gama komai kauna(kanwa) ta?''
Ashe duk maganar da su ke ya na can zaune tsakar gida ya na
jiyo su ba su sani ba. Murmushi Bintu ta saka, ita kuwa Inna cewa ta yi ‘’Ala
sakaa (Allah ya kare)"
Washegari da asubar fari Bintu na tashi daga barci Baba ne
ya fad’o ranta, don kuwa har su ka yi bacci be dawo ba. A tsakar gida ta tadda
Inna ta na alwala, ka na ta ce ‘’Inna barka da asuba’’
‘’Barka dai Bintu, kin tashi k’alau?’’ Inna ta amsa mata.
"Lafiya lumi, shin Baba kuwa an dawo?’’ Bintu ta sake
tambayarta, inda Inna ta amsa mata da sun dawo lafiya lumi kan ta shige d’akin
ta bayan ta gama alwala, ita ma Bintun buta ta d’auka ta shige band’aki.
Babban gida kuwa a yau rashin armashin sa ya fi na kullum,
babban abin da ya bawa Bintu tsoro da ta shiga gidan da rana shi ne ganin
Gimbiya K’amariyya cikin tashin hankali. An hana kowa shiga d’akin ta, Bintu ma
dan ita ta takawa Gimbiya Binta baya zuwa wajan Gimbiya K’amariyya ya sa ta
d’au haske, duk da dai ita ma iyakacin ta bakin kofa ne. Duk yanda Bintu za ta
yi domin binciko abinda ke faruwa ta yi, amma abun ya ci tara, babu wanda ya
iya bud’ar baki ya ce komai, dan kuwa kowa tsoran ace shi ya fad’a ya ke.
Haka dai Bintu ta koma gida jiki a sanyaye. Ta tadda Inna
zaune tsakar gida, kusa da ita ta zauna a gajiye ta na mai fad’in ‘’Inna barka
da yammaci, ashe kin taho’’
Bud’ar bakin Inna sai cewa ta yi "Barka dai d’iyarnan,
ba dole na taho gida ba, Babban gida yau ba dad’i, fada babu kwanciyar
hankali.......’’
‘’Yo to ina fada ina kwanciyar hankali!’’ Baba ne ya
katseta, wanda ya fito daga b’and’aki hannun sa ruk'e da buta, sanye cikin
shigar bayin Sa’ayrasa. Kujerar tsakar gida ya ja ya zauna kafin ya k’ara da
"ai da ni mai fad’a aji ne a wanga masarauta, da aradu ba a je Fabarusa
ba, yo to ina bawa d’an bayi, ina ni ina bada shawara?’’
Cikin k’aguwa ta ji abinda ke faruwa Inna ta ce ‘’Shin ya ta
kasance ne Malam? K’ak’a an ka yi ne?’’
Murmushin takaici Baba ya saki kan ya fara ba su labarin
yanda ta kasance a masarautar Fabarusa. Wato ba k’aramin fad'uwar gaba
Bintu ta ji ba jin Baba ya ce ‘’Da bud'ar bakin Sarki Abdulrahman sai
cewa yayi za mu kawar da gaba, za kuma mu ba ku bashin damun hatsai da dabino
yanda aka buk’ata daga gare mu dan ceto rayuwar alumma, amma fa da sharad’i.."
"Sharad’in me?’’ Inna da Bintu su ka tambaya a tare.
Baba na mai girgiza kai ya ce ‘’Ku dai tsaya ku ji furucin
tsohon banza, sharad’in shi ne, Uban Gabasawa(sarki) ya amra(d’aura) masa d’aya
daga cikin d’iyoyinsa mata....’’
Gaban Bintu ne ya yanke ya fad’i. ‘’A amra masa d’aya daga
cikin d’iyoyin Uban Gabasa?’’ Inna ta maimaita.
Kai baba ya gyad’a mata, ya k’ara da ‘’Acewarsa, ba zai ba
da zallar dukiya har haka ga tsohon abokin gaba ba, ba tare da ya sami madogara
ba, kenan amren d’aya daga cikin Gimbiyoyin Sa’ayrasa shi zai sa dole Uban
Gabasawa ba zai yi wasa da dukiyar ta su ba, a fad’ar sarkin Fabarusa fa’’
Hannu bisa ha6a Inna ta ce ‘’Hallo ta nan ya hito? Ba
ya taimako sabida da Allah sai an bashi d’iya? Na ji ance sarkin ga ya bawa
shekara tamanin baya, tsufa dai ta yi gardama’’
Gaba d’aya hankalin Bintu a tashe ya ke, musamman da tasan
alakar Gimbiya K’amriyya da d’an sarkin Fabarusa, wato Yerima Barde, kuma ta
san babu shakka Gimbiya K'amariyya za a za6a ba dai Gimbiya Binta ba.
‘’Shin yanzu ina aka kwan?’’ Muryar Inna ta dawo da Bintu
daga kogin tunanin da ta fad’a. Baba ya amsa mata da ‘’Tununna dai, an dai ce
za a yi shawara, amma gaskiyar lamarin da kyar za mu kiya , jama’a ana cikin
wani hali’’
Ya karkata buta ya fara alwala. Jin haka Bintu ta d’aura kai
bisa gwiwa cike da tausayin Gimbiya K’amariyya, duk da dai ba kukan ta ba,
mutuwar uwar kishiya.
Bangaren Gimbiya Kamariyya kuwa, tunda jakadiya ta sheda
mata halin da ake ciki ta kasa samin nutsuwa, gaba d’aya ta fita daga
hayyacinta. Washegari da safe ta na kwance bisa cinyar Gimbiya Binta ta na ta
kuka kamar k’aramar yarinya, Gimbiya Binta ce mai rarrashinta. Wayarta ta shiga
k’ara, da sauri ta duba, ganin wanda ke kiranta ya sa tayi sauran danna wayar
ta kara bisa kunnenta.
‘’Yerima mun shiga
uku, Yerima ya zan yi?’’
Muryar Barde kad’ai ta isa rikita mai sauraro, murya ce mai
tattare da kwarjini, k’asaita da kuma nutsuwa. Duk da tashin hankalin da take
ciki be hana ta runtse idanunta ba yayin da ta ji ya ambaci sunanta
"K'amariyya.....’’ Sannan ya fara magana cike da k’asaita ‘’Ki kwantar da
hankalinki, babu wanda ya isa ya auri matata, fad’amin shi wannan da ki ke
magana akai wanene shi? Waye ubansa? Dan wani masarauta ne?’’
‘’Fabarusa, amma ba za mu iya jayayya da shi ba Yerima,
sawun giwa ya taka na rak’umi....’’ Ta na magana ne cikin shasshek'ar kuka.
Hankali kwance Yerima Barde ya ce "Fad’amin sunansa, dan wani gida ne
acikin masarautarmu? Shin da me ya ke tak’ama haka ya tsoratar min da
Gimbiya?’’
Ta na mai magana a hankali, dakyar ta iya furta ‘’Yerima Mai
Mar-ta-ba ne.....’’
‘’Wanene Mai Martaba?’’ Ya tambaya a takaice. Jin haka ta
san be gane in da ta dosa taba, ta ce ‘’Mai Martaba sarkin Fabarusa....’’
'Dif ta ji Yareima Barde, shiru kamar wanda ruwa ya shanye
har sai da ta duba wayar dan azatan ta wayar ce ta yanke. Ganin be yanke ba, a
hankali ta furta ‘’Yarima...’’
Dogon numfashi ya ja kafin ya ce "Akwai kuskure, babu
wannan maganar, ki saurari wayata zuwa anjima.’’ Ya na gama fad’in haka ya
katse wayar. Wani sabon kuka Gimbiya K’amariyya ta saka. Cike da tausayi
Gimbiya Binta ta ke dubanta, cikin ranta kuwa ta k’udiri niyyar ceto rayuwar
‘yar uwarta. Ta na mai murmushi ta ce da Gimbya K'amariyya ‘’Didi kar ki damu,
aradu sai na share mi ki hawaye, in har na kasa aratta kashe ni.’’ Sannan ta d'auki hanyar fita bayin ta na biye da
ita.
******** *********
FABARUSA
Yarima Abubakar Abdulrahman wanda aka fi sani da Yarima
Barde na Fabarusa, shi ake nufi da wannan kalmar kyau, dan buzu jikan buzu, shi
ba sarki ba ya fi sarki iko da mulki. Fari ne sol, dogo mai k’irar nan ada ake
danganta su da k’irar zaki. Ya na da faffad’ar kafad’a maji k’arfi da kumari.
Sam babu alamar muni a tattare da shi, ya na da dogon hanci da ya zo daf da
bakinshi, da manyan idanu mai rikita duk mai kallo. Bak’in gashin da ya sauko
tun daga sajenshi ya zagaye fuskarsa, har zuwa saman bakinsa. Abun ku da buzu
ya na da suma kamar balarabe, baki wanda yayi lub-lub kwance bisa kansa. Yawan
sumar ya sa ba ya damuwa da aski, sai dai ya rage, hakan yasa idan aka gan shi
akan yi zaton balarabe ne.
Yarima Barde bai da wata sutura da ya wuce farin tufafi,
kullum tufafinsa fari ne k'al, haka zalika rawanin ko hularshi. Mutum ne mai
tsafta, isa da k’asaita, wanda hakan kan
janyo wasu da dama danganta halinsa da mai shegen girman kai. Shi ne na ishirin
wajan mahaifinsa, inda ya ke da yayye goma sha tara, goma sha takwas mata duka
suna gidajen mazajensu, da namiji d’aya Abdulkarim wanda ake kira Sadauki,
tsirar watanni biyar ne tsakaninsu, shekararsu Talatin da biyu da haihuwa.
K’annensa goma, mata biyar da maza biyar.
Kasancewar hali da ya bambanta tsakanin Barde da Sadauki,
inda Barde ya ke da nutsuwa hankali da sanin yakamata, Saudauki shi ne shaye
shaye, rashin tarbiya da bin mata. Hakan ya sa Barde ya zama mafi soyuwa wajen
mahafinnasu Mai Martaba Sarkin Fabarusa, duk da kuwa da yawa ana lak’anta
soyayyar d’an da mahaifin akan soyayyar da Sarki ya ke yiwa mahafiyar Barde ne
ya shafi d’an na ta, duk da dai ba ta cikin fada, ko ince k’asar Nijar baki
d’aya.
Cikin lambu ya ke zaune bisa katuwar darduma, tare da
dogarawa uku wanda ke tsaye daga gefe guda. Yanayin da iska ke kad’awa da kuma
yanda gayayyaki da furanni su ka yi koreshe shi zai tabbatar maka da daminar
bana ta yi kyau a masarautar Fabarusa.
Sanye ya ke cikin farar shadda dinkin yar shara, ga farar
hular shi da ta sha kari karkace bisa kan sa. Tunda ya aje wayar Gimbiya
K’amariyya ya kasa motsawa daga in da ya ke. Dogon numfashi ya saka, ya na mai
k'in gasgata abun da ya ji daga Gimbiya K’amariyya, kasancewar ba ya nan sa’in
da Sarkin Sa’ayra da tawagarsa su ka ziyarci Fabarusa.
Ganin ya yunk’ura da niyar tashi, Dogarai su ka yo kansa da
sauri, yayin da d’aya daga cikin su ya matso gaban Yarima ya aje farin takalmi
gaban sa, su na mai fad’in "Hattara dai magajin Sarki, hattara salamun
Yarima’’
Cikin k’asaita ya zura k’afafunsa cikin takalmin, Dogarai su
ka rufa ma sa baya, ba su fasa fad’in
"Lafiya salamun Yarima, lafiyarka dama da hauni, dama
da hauni lafiya, salamun salamun’’
Isar su bakin kofar lambu, da ke kufar ba ta da tsayi sosai,
ga Barde da tsayi mashaAllah. Dogarawa su ka ce "Shafi bisa Yarima,
sunkuye salamun’’(ma’ana Badde ya dan sunkuya kada ya bugi hular sa).
Da fad’ar haka Barde ya d’an sunkuya, sai gasu sun fito daga
cikin lambun. Duk in da su ka gifta sai ka ji ana mik’a gaisuwa. Shi kuwa ko
kallo ba su ishe shi ba, Allah Allah ya ke ya isa ga turakar Sarki, sai
dogarawan ke amsa masa gaisuwar, haka kuma ba su basa fasu nusar da shi ba ta
hanyar kiran lafiya, duk san da su ka yi arba d abin da zai iya tuntu6e da shi,
ko wanda zai iya 6ata shi kamar danshi, ko gidan tururuwa ko rami, sai ka ji su
na ambaton
‘’Hattara salamun Yerima’’
Haka har su ka kai ga turakar sarki, in da su ka tadda
Jakadiya daga bakin kofa. Ganinta Yerima ya tambaya Sarki shi kad’ai ne zai iya
ganinsa? Da ke Yerima Barde dan gaban goshin Jakadiya ne nan da nan ta masa
iso. Kai tsaye ya shige yayinda sauran dogarawan su ka yi tsaye su na jiran sa
daga waje.
Da shigarsa ya tadda Mai martaba hakimce, k’ishingid’e bisa
wata k'atuwar dadduma da aka yi da fatar rak’umi, yayiwa hannun sa na hagu
majingini bisa wani k’aton tintin mai zanen tambarin masarautar fabarusa,
hannunsa na dama rik’e da k’aton jarbi ya na ja.
Kyakkyawan tsoho ne mai kimanin shekara tamanin a duniya,
shi kanshi Barde be k’ara ganin tsufar mahaifin na sa ba sai yanzu da ya gansa
sanye cikin farar jallabiya, furfura fal bisa kansa, amma ace ya nemi auren
yarinya yar shekara ishirin, wanda ya yi jika da ita, kai har tattaba kunne ma!
Gaskiya dai maganar nan da kuskure.
Zancen zucin da Barde ke yi kenan yayin da ya zube gaban
Mahaifin na sa ya na mai mik’a gaisuwar sa. Amsawa Sarki yayi, tare da fad’in
"Barde da wani abu ne?’’
"Barde ya dukar da kai kasa, kana ya ce
‘’Allah ya ja zamanin ka, shin za a taimakawa masarautar
S’ayrasa ne?’’
Sarki na mai murmushi ya bashi amsa da
‘’Tabbas za mu taimaka musu, amma fa sai sun ba mu dama’’
Barde bai gushe ba ya k’ara tambayar Sarki
‘’Allah ya taimake ka, tunda su ka zo gare mu, ai sun bada
damar kenan, Allah ya taimaki Sabkawa.’’
‘’Ba su ba mu dama ba, kila dai za su bayar, amsar ta su mu
ke jira’’
Sarki ya amsa a tak’aice. Jin haka Barde ya rusunar da kai,
kana ya ce "Allah ya d’aukake ka ranka shi dad'e shin wata dama ce
wannan?’’
Sai da wasu d’an dak’ikai su ka wuce, kafin Sarki ya bud’i
baki ya ce
‘’Ba wata dama ba ce, illa kulla aminci ta hanyar kawar da
gaba har abada. Mu na son tabbatar da amincin Sa’ayrasa, kafin mu fidda
tsagwaran dukiya wajan taimaka musu, don haka mu ka yanke hukuncin auratayya
tsakanin masarautarmu da ta su’’
Gaban Barde ne ya fad’i, cikin ransa ya na mai nanata
"Dagaske ne kenan, innalillahi wa innailaihi rajiun!’’ Sarki na mai
dubanshi, ganin yanayin da ya shiga ya ce
‘’Mu na sauraran Barde, akwai abun da ya kamata mu sani
ne?’’
Nan da nan Barde ya nutsu, ya na mai 6oye halin da ya ke
ciki ta hanyar yin nauyin baki ya ce
"Babu Allah ya ja da ran Mai martaba, Allah ya tabbatar
mana da alkairinsa’’
Cikin nuna jin dad’i Sarki ya ce
‘’D'an mu ya gama magana, mun san a koda yaushe kai mai
amincewa da hukuncin mu ne ba tare da ka tsananta bincike ba, shi ya sa ba mu
da haufi akanka. Wannan lamari alkhairi ne ga masarautar mu’’
Jikin Barde kamar wanda aka d’aure, zuciya sark’ak’e ya yiwa
sarki sallama. Kai tsaye na shi sashen ya nufa, in da ya ji zazza6i na neman
rufe shi tsabagen 6acin rai.
******* ********
Sa’ayrasa kuwa, Gimbiya Binta na fita turakar Sarki ta nufa,
in da take da tabbacin za ta sami Jakadiya. Ta ko yi sa’a ta same ta ta gama
shirya Sarki kenan, ya fita ran gadi. Zaune ta ke farfajiyar turakar sarki, ta
na cin goro. Ganin Gimbiya Binta gabanta, ta shiga mata kirarin da ta saba mata
‘’Ture a ga tsiya, a kalla ruwan ido ya tsiyaye, tanka ka
lalace, shiga d’aki bakin ciki ya kashe ka, ta Amale(Sarki) kin fi darbejiya
d'aci, mai san zama da ke ya tambayi hali.’’
Gimbiya Binta na mai murmushi ta d'agawa bayin da su ka taka
mata baya hannu, ma’ana su ba ta waje, nan da nan su ka koma da baya, yayin da
Jakadiya ta mata tayin ko za su shiga daga ciki ne? Gimbiya ta ce rariyar ma ba
laifi. Sabuwar shifid'a Jakadiya ta mata, In da Gimbiya ta ke tambayar shin ya
lafiyar Takawa?
Jakadiya na mai girgiza kai ta ce "Bijimin Duniya ana
wani hali, damuwarshi ta kai matuk’a, abinci ma ba sosai ya ke iya ci ba, fari
da batun tsohon banza na Fabarusa shi ya sako shi gaba Gimbiya’’
Gimbiya Binta na mai duban Jakadiya ta ce ‘’Jakadiya, halin
da mai martaba ya ke ciki zai iya illata
shi da ma iyalan sa baki d’aya, kuma watsi da lamarin Fabarusa barazanar
rasa rayukan talakawa ne, domin za su ga Takawa ya fi san iyalan sa akan
talakawan sa, wanda hakan ka iya kawo rabuwar kai a wannan masarauta ta mu,
kuma ko shakka babu k’udirin abokan gaba Masarautar Fabarusa kenan’’
Jakadiya na mai jinjina kai ta ce
"Sadak’ata Gimbiya, wannan batu na ki na yarda da shi’’
Gimbiya Binta ba ta gushe ba, ta nisa sannan ta k’ara da
‘’Masarautarnan kaf, babu wanda ya kai Jakadiya kusanci da
sarki, yanda ya yarda da ke babu na biyunki, ke ki kasan Takawa, ke ki kasan
cikin Takawa, shi ya sa ake kama k’afa da ke kan lamarin Takawa, gani na zo da
shawara da kuma neman taimako daga gare ki, ban sani ba ko Jakadiya za ta
amince da ni’’
Jin haka Jakadiya ta jefa kan ta baya, ta saki wani irin
dariya mai k’ara kafin ta fara yiwa kan ta kirari kamar haka
‘’Sai ni Hindu Maryamu, jikar Baba Kilishi, jikar Nana, ban
fito ba sai da na shirya ko a lahira rago ake duka dan bantan uba, lokacin iska
akan ci 'ya'yan tsuntsu, kuci bayan gaban da k’aya’’
Ko da Jakadiya ta kai ga aya a kirarin ta, ta na mai duban
Gimbiya Binta ta ce fad’i in ji, in dai cigaban Babban biji ne sha yanzu magani
yanzu. Jin haka Gimbiya Binta ta waiga kudu da arewa, gabas da yamma sannan ta
dubi Jakadiya ta ce
‘’bangon gidan ga kunnuwa gare shi Jakadiya’’
Jin haka Jakadiya ta matsawo kusa da Gimbiya Binta, ta amsa
da ‘’oh toh toh, bari na matso kusa kar iska ta kwasa ta kai d’akin o o da o o
yan bantan uba’’ kunnan ta tafitar daga
lullub’in ta, nan Gimbiya Binta ta shiga zayyana mata buk’atun ta, ko da
Gimbiya ta gama, Jadiya ta ja da baya ta na mai fad’in
‘’Timirin katauje ba sai da kwandala ba, da kwandalar ne da
yafi dama dama, haihuwa babu ciwo sai ka ce fitsari? Gwara ma fitsarin kayi yau
da gobe, haihuwar da babu ciwo sai kace ruwan famfo? Gwara ma ruwan famfo ka yi
murd’e murd’e’’
Gimbiya da ta gano in da Jakadiya ta dosa, ta na mai kallan
gefe da gefe, kusurwa kusurwa gudun kar a jiyo Jakadiya, ta ce ‘’ kar ki ji
komai Jakadiya, ina mai tabbatar mi ki idan har ki ka fad’awa Takawa wannan
shawara sai ya mi ki babban kyauta, dadin dad’awa kuma ni ma mai mi ki kyautan
zannuwa shirin ce, kuma hajjin bana har da ke, aradu ma kuwa’’
Jin haka Jadiya ta ce ‘’yo to menene, dan dai d’an wannan
lamarin da be taka kara ya karya ba? An gama ran ki shi dad’e, yau d’in nan ma
kuwa’’
Gimbiya na mai jin dad’i, babu shakka tarkon ta ya kama
tsuntsuwa ta yiwa Jakadiya sallama, ta bar Jakadiya ta na Allah Allah ta ga
dawowar sarki, dan kuwa dai bana kakar ta ta yanke sak’a in dai batun Gimbiya
Binta mai yiyuwa ne, ga zannuwa da zuwa hajja, wannan shekara dai ta zo mata da
kyau.
******
Bayan an idar da sallar Ishai, kamar kullum Bintu tare da su
Innar ta zaune tsakar gida bisa tabarma su na shan iska. Tun da su ka zauna
Bintu ta tsurawa zoben hannun ta ido, gaba d’aya ta rasa kwanciyar hankali.
Inna ce ta ta6o ta tana fad’in ‘’ba da ke ake magana ba
Bintu?’’ Bintu ta yi firgita ta dawo cikin hayyacin ta "eyee? Na’am?’’
cewar Bintu ta na mai duban Inna da Habibu da su ka kafe ta da ido suna kallan
ikon Allah. Inna na buga hannu a iska ta ce ‘’yo to ba na fad’a ma ba, ba ta
san ka na yi ba Habibu’’
Habibu na duban Bintu da ta sunkuyar da kai, har lokacin
hannun ta be bar kan zuben ba, ya ce ‘’Inna kin sa halin ta, akwai damuwa da
damuwar wasu, yanzu haka babu mamaki lamarin Babban gida ke damun ta, ko ta ce
rashin lafiyar shugaban k’asa.
‘’mtsw wahalar da rai fushi da makwafci’’ cewar Inna ta na
mai nuna Bintu da yatsa ‘’ki je ki d'aurawa kan ki ciwo akan wanda ba su san da
ke ba bare su san ki na yi’’
Bintu ta dai ba ta ce komai ba, ita kad'ai ta san irin
fad’uwar gaban da ta ke fama da shi. Ita dai adduar ta Allah ya sa alkahiri ne
yanayin da ta ke ji.
***** ****
Babban gida kuwa, Jakadiya ba ta yi k’asa a gwiwa ba, bayan
ta gama shirya sarki cikin shirin bacci, Sarki na daga shingid’e, kafin ta raka
shi wajan matar da ta za6a ma sarki kwana gurin ta ne ta ke bawa Sarki shawara
akan lamarin da Gimbiya Binta ta sheda mata, ta k’are maganar na ta da
‘’watsi da al’amarin Sarki Abdulrahman barazanar rasa
rayukan talakawa ne, sake dabara a nemi taimako wata masarautar talakawa za su
ga kamar an fi san iyalan sarki akan lamarin rayuwar su, hakan ka iya kawo
rabuwar kai cikin wanga masarauta wanda dama k'udirin Masarautar kenan. Tun da
Sarki Abdulrahman be ji kunyar yada girman sa ba, da saka rayuwar mu cikin
kunci, mu kuwa ba za mu kasa masa bita da kulle ba, dukan kabarin kishiya’’
shiru ta yi dan shan nufashi kafin ta k’ara da
‘’wannan dalili ya sa na yi bincike ta hannnun Gimbiya
Binta, ta kuma amince da wannan batu, Allah ya ja da ran sa, idan na yi kuskure
a yi min rai, ina tuba’’
Shiru ka je, Sarki na mai juya maganar cikin ran sa, in
akwai abun da ya dame shi duk fad’in duniyar nan baya ya ke da farin da alumar
shi ke ciki, idan kuma akwai abun da ya fi soyiwa a rayuwar sa, to ya bi bayan
iyalin sa, musammam ma yaran sa mata guda biyu, hakan ya sa duk duniya babu
wanda ya tsana, ya ke matsayin babban abokin gama kamar Sarki Abdulrahman na
Fabarusa. Duk da batun Jakadiya lamari ne mai girma, ya tsinci kan sa ya na mai
san yin tuntuntini akai.
Ya na duban Jakadiya ya gyara murya ya ce ‘’Jakadiya mun ji
wannan batu na ki, duk dai ba mu gamsu ba, za mu yi tunani akai’’
Jin haka Jakadiya ta duk’a ta na mai d’unkule tafin hannun
ta na dama yayinda ta d’aga sama ta na mai jinjina ga Sarki, fad’i ta ke
‘’Sukukun bakaka Jatau, mashin da wuta Jatau, idan mai sa6o
bai daina ba mai horon ma ba zai fasa ba!lafiya Barden mahadi! Lagiya Sukukun
bakaka! Lafiya Darzaza amalen sarakuna’’
********
Washagari kan Sarki ya zauna fadanci, yayi kiran Waziri da
Hadiman sa guda hud’u, dan kuwa tun zantawar sa da Jakadiya, har ta kai shi ga
d’akin Inna Salti Sarki be runtsa ba, shawarar Jakadiya ke masa yawo aka. Ai
kuwa dai Waziri ma na’am yayi da shawara, a fad’ar sa ‘’karan ban shi an
maganin zoman bana’’
Biyu daga cikin Mahadin Sarki su ne su ka banbanta batu, ana
su zai fi ga kyau Sarki ya tsaya tsayin daka kan lamarin sa na gaskiya, dan ko
da ba su ji ba, wanga magana hallo maganar mata ce. A wannan sanadin ne Sarki
ya ce in su na biye da shi za su iya zama fada, in kuwa ba haka ba ya na mai
d’aure su har sai hakin masarauta ya cimma ruwa, dan babu damar korar su daga
fada su na amintattun Hadiman sarki, surrin fada babu wanda ba su sani. Da
wannan su ka ja bakin su su ka yi shiru, su na mai Allah wadar da wanda ya bawa
Sarki wanga shawara, dan kuwa Sarki idanu ya rufe madafa kawai ya ke nima, ya
kuma sami bahaguwar madafa mai wuyar 6ullewa sai dai fa Allah shi kyauta da
aikin dana sani.
Bintu na gyaran gadon Gimbiya Binta, ita kuma Gimbiyar na
daga kishingid’e bisa tin tin ana mata danna. Sai ga Jakadiya ta shigo jiki na
rawa daga gani kasan da magana a bakin ta. Bayi na ta gaishe ta, haka ma Bintu
wacce tun shigowar Jakadiya ta ga ta kafe ta ido. Jakadiya na mai duban Bintu
ta ce "ko da ban sani ba ke an Bintu’’
Gaban Bintu ne ya fad’i yayinda ta zube k’asa ta na mai
fad’in ‘’Allah ya huci zuciyar Jadiya, Bintu na ke ba ki 6ata ba’’
Kallan ta ta ke cikin nazari, kafin ta juya ta dubi Gimbiya
Binta, gudun kar sauran bayi su gane sakon da za ta fad'wa Gimbiya, sai cewa ta
yi
‘’ta kan kwaba, ta kan kan ta, ta kan akwati mai taya, sai
sid’if ta fad’a, sai sid’if na d’auka’’
Jin haka Gimbiya Binta ta saki k'awataccen murmushi, dama
abun da ta ke jira kenan, kana ta ce
"zannuwa ishirin sun yi kad’an, aradu na k’ara mi ki
goma har da kallabi goma’’
Jin haka Jakadiya ta rangwad’a gud'a ta na mai fad’in ‘’yaro
wake tab'a mai uwa? Ba zai ci ba kayan kasuwa, sai ni Hindu jikar Baba Kilishi
Jikar Nana, godiya na ke Gimbiya’’
Kana ta kai kallan ta ga Bintu ta ce "biyo ni yarinya’’
Gaba Bintu na fad’uwa duk dai ba ta fahimci zancen na
Gimbiya da Jakadiya ba, ta bi bayan Jakadiya. Ganin haka wata Baiwa mai kaiwa
Yerima Nuhu duk wani labari na game da lamarin Bintu ita ma ta ja kafar ta zuwa
neman Yarima Nuhu, dan kuwa dai ita ma ba ta gamsu da wannan lamari ba.
Bintu na tafe bayan Jakadiya, ganin in da su ka dosa gaban
ta sai faduwa ya ke, musammam da ta ga sun doshi turakar Sarki gadan gadan. Nan
su ka tadda Sarki tare da Waziri da Hadimai, bayan su babu wani mahalik’i da ke
wajan face amintaccen bawan sarki wanda ake kira Nahana. A bakin kofar turaka
Bintu ta kasa d’aga k’afa ta shiga dan tsoro da kwarjini, tun da aka haife ta
ko harabar wajan ba ta tab’a shiga ba, bare ace turakar sarki, ga ta ga sarki.
Sai da Jakadiya ta d’an jawo ta, na mai mai mata shune da baki ta shiga.
Ganin ta gaban Sarki tuni ta zube k'asa ta na mai kwasar
gaisuwa. Yau ga Bintu ga Sarki da waziri har da Hadimai, ko shakka babu dole
k'awarta Cangwai ta ji wannan labarin.
Sarki zaune ya hakimce cikin rawani, ya dubi Jakadiya ya ce
‘’ba mu tarihin wanga d’iya’’
Zama Jakadiya ta gyara, kafin ta ce ‘’Allah ya ja daran
Babban bijimi, wanga d’iya sunan marigayiya Baba Kilishi ta ci, hakan tsirar
haihuwar ta da Gimbiya k’arama kwana d’ai ta, tare su ka tasa da Gimbiya k’ara,
dad'in dad’awa makarantar su d’aya, bambacin su d’aya, wanga dai baiwa ce, kuma
d’yar bayi, diya ce gun uwar bayi da kuma wannan bawa da ake kira Bala, eh
Mahuta ba ,aradu ma kuwa’’
Waziri ya dubi Jakadiya ce ‘’ai fad'uwa ya zo daidai da
zama, uban ta shi an babban bawa nai, ya ta ke da suna?’’
‘’Fatima, amma Bintu aka ce mata, kamar yanda ake kiran
Gimbiya k'arama Binta’’ ta bashi amsa a takaice. Ita dai Bintu ta na nan kai
durkushe daga can gefe amma daga tsakiya da ke ba shakka turakar ba dai girma
ba, na gaske ma kuwa. Ko kwakkwaran motsi ba ta iyawa, bare ta d’an d’aga ido
gudun kar ta had’a ido da Sarki, dan karshen kwarjini ya mata a yau da ta ke ga
ta gashi.
‘’Fatima’’ muryar Sarki ta ji ya daki kunnan, tuni ta k’ara
nutsuwa ta na mai rusunar da kai kamar wacce za ta shige k’ark’ashin k’asa. Ba
mafarki ta ke ba, sarki da kan sa ya kira sunan ta, ina ma Cangwai ta na nan ta
gani da idon ta, dan Idan ta ba ta labari sai ta ce k’arya ta yi.....tunanin da
ta ke cikin ran ta kenan, jin Sarki ya ce
‘’a matsayin ki na baiwa a gare mu, shin akwai umarnin da za
mu ba ki ki bi?’’
Bintu ta yi saurin duk’ar da kai ta ce "tir da bawan da
bai bin maganar uban gidan sa, zan bi umarnin Mai martaba, ko da kuwa hakan zai
zama sanadin rasa rai na, kwankwatsi ma kuwa’’
Kwalla na kad’ai Hadiman nan biyu ba su zibdawa Bintu ba,
shi kuwa Waziri kai ya shiga kad’awa cike da gamsuwa, bare Jakadiya da ta ke ji
kamar ta sab’a Bintu a baya tai ta rawa, Allah dai ya kawo mata tsuntsu daga
sama gashesshe. Sarki na mai nazarin Bintu na wani d’an lokaci, daga bisani ya
ce za ta iya tafiya. Ta na mai godiya ba tare da ta san abun da ake kullawaba
ta fita.
Bayan tafiyar ta Sarki ya ce ya gamsu da komai na ta, amma
ya na so Jakadiya ta sa ido kan ta na wani d'an lokaci kafin su gama zartar da
hukunci. Da haka da haka har su ka wuce zaman fada.
Da yammacin ranar gaba d’aya walwalar Gimbiya K’amariyya ya
dawo. Bintu na zaune gaban ta tana yanke mata farce wayar gida da ke aje d’akin
ta ya fara k’ara. Cikin farin ciki ta d’aga, ganin haka Bintu ta tashi da niyar
ba ta waje, amma Gimbiya K’amariyya ta d’aga mata hannu alamar ta yi zaman ta.
Maganar da Gimbiya ke fad’awa Yarima Barde ne ya bawa Bintu
mamaki, ji ta yi ta na fad’in ‘’Takawa dai ya yanke hukumcin aurar da kauna ta
Binta ga Mai Martaba Sarki na Fabarusa...’’
Gaba d’aya jikin Bintu yayi sanyi, cikin ran ta tausayin
Gimbiya Binta ta ne ya kama ta, har fad’i ta ke
"Allah sarki Gimbiya ta ceto rayuwar ‘yar uwar ta,
yanzu na gane dalilin maganar da sarki ya min, wato ina d'aya daga cikin bayin
da za’a tura tare da Gimbiya Binta, kaiconi Bintu karatun mu kuma shikenan’’
Tausayin Gimbiya da ita kan ta shi ya gajiyar da ita ranar,
ta kasa ta6uka komai har dare yayi ta koma gida.
Suna cin abinci da Inna, yau sun sami sauran biski daga
gidan Sarki. Baba ya shigo babu sallama sai surutai ya ke kamar mahaukaci saban
kamu, fad’i ya ke
‘’ta na ina ne wai ma?’’ ganin su a tsakar gida ya ja ya
tsaya ya na mai fad’in
'’yo to ashe ku nan kusa ma’’
Inna ta yi kasake kafin ta ce ‘’Hallo Malam Lifiya? Yau ko
sallamar babu?’’
‘’sallamar kenan ai uwar matar sarkin Fabarusa’’ cewar Baba
ya na mai duban Bintu da sai saka lomar biski ta ke, hannu baka hannu kwarya.
Inna na murmushin jin maganar Baba, ta ce ‘’Malam yau kuma raha a ke ji?’’
Cikin jadadawa Baba ya ce ‘’yo to wani raha bayan yanzu
waziri ke sheda min, nan da d’an kwanaki za a tura a tsaida ranar bikin Gimbiya
Bintu’’ ya k’arasa maganar ya na mai washe baki wanda daga Inna har Bintu sun
kasa gane manufar dariyar ta sa.
Inna ce ta ce ‘’ayyo,
Gimbiya Binta ko? Ai yanzu haka maganar da mu ke kenan, Wallahi yanzu ta
ke sheda min’’
Baba na mai duban Bintu ya kai mata dak’uwa ‘’ungo nan yar
jakar uba!’’ baki cike da biski Bintu ta tsaya ta na duban Baba. Ganin haka
Inna ta ce "Allah sarki, aradu ba munahinci ta yi ba, hira ce ta kawo
maganar....’’
Cikin k’ulewa Baba ya ce ‘’yo to na gaji da wannan rashin
fahimta ta ki Yagana, gide ina nuna mi ki annabi hallo ki na runtse ido,
wannan(ya nuna Bintu da yatsa) ita za a amrar ga Sarki Abdulrahman na Fabarusa
a matsayin d’iyar Sarki....’’ tuni Bintu ta kwarai, ta wanke Inna da biskin
bakin ta tsabagen tari.