“Ja chan gefe waze sai miki wannan k’aton mota?” Baban dake jinsu ko k’ala bece ba.
“Baba kaji Yashmeen wai ba nawa bane.”
“Seta hanashi zama nakin ai muga.”
“Baba wai dagaske motan Zeezee ne wannan?” Asked Omar.
Zeezee fa ba wasa se tuk’i take ta shiga d’akin Mama ta fito tayi d’akinsu Mariam tayi parlour, ba inda bata shiga da motar tata har bathroom, Yasmeen da takeson tad’an d’ana itama taje ta samu Zeezee kafin ta baro parlour. “Zeezee ta d’an ara min motarki na nad’a kinji?”
“O’o manya bashuwa chiga.”
“Manya erinsu Adda Mariam da Ya Ibraheem ba? Yi hak’uri.”
“Ni o’o banasho.” Da k’yar Yasmeen ta iya shawo kanta ta yarda ta bata dan d’anawa, dududu da shigan Yasmeen befi minti d’ai ba Zeezee ta soma k’iriniya ita a bata motan ta Yasmeen da mota ya mata dad’i kuwa tak’i. D’an karen banzan ihu ta saki tare Baba ya shigo yana tambayan ko lafiya “ya haka? Me kikeyi k’atuwa dake cikin motan Zeezee?”,Yayi tambayar wa Yasmeen dake ta raba ido bayan ta fito daga motar. Nan Zeezee tamai bayanin komi, “yi hak’uri K’anwata kekuma ki sake shiga mata mota kiga k’atuwar banza kawai.”
“Wayyayi shena fad’a” nan ta juya
“Tsaya kiji, zan had’a miki naki kema a leda seki sha da akwai dad’i sosai.”
“K’alya kina shon kimin wayo.”
“Wallahi ba k’arya ba” wasu ledan ta sake cirowa tasawa Zeezee madara da milo ciki sannan itama tayi haka anata sede nata yafi na Zeezee yawa aikuwa uwar rigima ta hau ihu “wayyayi naki yafi nawa yawa ki k’aya min.”
“Toh kiyi shiru mana sekin fallashemu ne.”
“Ni sekin k’ala min” tasake sa kuka ai kafin su hankara Mama ta diro d’akin tare da kamasu red-handed. Take Yasmeen ta b’oye ledarta a baya Zeezee kuwa se fitina take “ni ki k’ala min”
“Me za’a k’ara mikin?” Ido Yasmeen tama Zeezee nufin tayi shiru ta b’oye nata itama amman ina ita bata nan take ba, “Yasmeen ne tasha min madala kad’an nata da yawa.”
“Madara!” Exclaimed Mama, “Yasmeen ban hanaki d’iban madara kina sha ba?” Kame-kame Yasmeen ta shiga tana b’arin baki.
“Ni ki k’ala min” Zeezee tayi breaking silence d’in.
“Oya kawo madaran nan dukan ku” ba musu Yasmeen ta kai nata “kema Zeezee bani naki” kaman dagske ta nufa wajen Mama kamar kyaftawan ido tabi gefenta tasa gudu taje ta samu Baba tasha madaranta tayi nak!
“Kuma wayyayi balin shake baki shweet d’ina ba tunda kin fad’awa Mama.” Zeezee tayi maganan wa Yasmeen tana barin gun, koda tazo shigewa ciki bata ce wa Mama dake ta faman kiran sunanta ko uffan ba. D’akin Mama ta nufa ta tara teddy bears nata sannan ta bud’e turaren Mama ta zazzage kan teddies d’in k’amshi har waje malam!
“Tsaya wannan ba k’amshin turare na bane?” Mama tayi maganan tare da miqewa ta nufi d’akinta. “Ai ba turare d’aya bama” cewar Mariam. Mama na tabbatar da hakan ta kama Zeezee ta mammaketa bada jimawa ba Baba ya dawo sarkin d’aure wa k’arya gindi, balbale Mama ya shiga yi bayan na ya lallashi Zeezee.
“Kalli fah! Remote d’i TV’n ta cinye kap! Abin naki lafiya kuwa Zeezee?”
“Ahap! Ai kad’an ka gani wallahi wataran tab’arya zata d’au ta fasa TV’n nan naka dashi ba wai kai komi tayi dai-dai neba, this is just the begining Zeezee kinyi dai-dai.”
“Da take kira na da suna na kota zagen kota min b’arna me kake cewa? Yarinya ace abarta koba haka ba? kaima seka barta yanzu yarinya ce, Auta ta taho muje kici abinci” da gudu Zeezee tayi gun Mama ta d’aga ta.
“Wallahi kin kyauta ke kuma wai bakinki razor ba ki sake cimin remote kigani mschww!”
“Ramin mugunta tauna shi gajere!” Mama tayi stating tare da baro parlourn.
Monday morning as always and usual Zeezee tayi ta daru da k’yar aka samu aka shiryata school seda taga Lubiee hankalinta ya kwanta.
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa Zeezee, rikicin yau daban na gobe daban ga wani masifaffen rashin kunyan da take tashi dashi kuwa ba wanda ya isa ya tab’ata a gidan, ka tab’ata ma jikin ka ze ma bayani. Ba yadda Mama batai da Baba asa Zeezee a islamiya ba sam yak’i wai seta k’ara girma. Ana cikin haka bikin ‘yar Aunty SDY ya iso duk events da akayi Mama tasamu hallara, sauran kai amarya Kano da za’ayi da kuma yin dinner da ya rage, cikin sauk’in kai ta tambayi Baba izini ya kuma bata.
Kayakin Mama ne baje kan gado se had’a akwatin ta take tana cikin yin hakan Zeezee ta shigo d’akin delibrately matching Mama’s ironed clothes da motan ta.
“Sabon iskanci nekuma haka Zeezee kina ji kina taka min kaya matsa min!”
“Toh ba na miki honk ba” ta murgud’a baki.
“Dake da honk d’in uwaku.”
“Kema-”
“Wallahi kika kuskura kika zageni dukan ki zanyi a d’akin nan” Mama tayi saurin katse ta. “Ni thank god ma gobe zanyi tafiya in huta wallahi.”
“Nima shena biki.”
“Ai da inyi tafiya dake gwara na fasa tafiyan” ba tare da Zeezee ta tanka Mama ba taja motan ta tayi d’akin Baba kukan munafirci ta soma tana mishi bayanin abinda ya faru ba tare da b’ata lokaci ba ya mik’e suka dawo d’akin Mama aiko tana ganinsa jikinta ya bata Zeezee ce takai k’ararta. “Wallahi Ahj inma batun inbawa Zeezee hak’uri kazo yi is better ka koma dan ba bata zanba yau abin nata is getting out of hand.”
“Kinsan kinyi laifi kenan, anyways ba abinda ya kawoni ba kenan ki had’awa Zeezee kayakin ta itama da ita zakiyi tafiyan.” Zumbur Mama ta mik’e tsaye tana zaro ido, “da wa zanyi tafiyan? Wallahi baran je ko ina da wannan maras kunyan ba.”
“Kin de jini” ya fad’a authoritatively.
“Wallahi bazan yi tafiya da yarainyan da bata jin magana naba, kalan taje tabani kunya a idanun jama’a, ace yarinya sede bata ga abu gun yara ba tace itama se an siya mata kuma da kake wani cewa zata bini makarantar ta kuma fa? Kai zaka je mata?”
“Wallahi ba haka ba, ba inda zanje da wannan yarinyan ehe!”
“Ni shena biki Hafsah!” Zeezee tayi maganar cike da tsiwa da fitsara.
“Nifa na gaya miki Hafsah.”
“Wallahi da inje da ita gwara na fasa tafiyan ai dama anyi me yawan, dinner ne daman kawai ya rage se in fasa zuwa.”
“Eh sede ki fasan amman muddin zaki sekinje da Zeezee.”
“Eh nafasan...” Bayan ficewar Baba, Mama ta d’au wayarta takira Aunty SDY tayi making up excuses kan bazata samu zuwa ba dan ta gwammaci missing bikin da tai tafiya da Zeezee.
Haka Allah ya cigaba da raya Zeezee har takai matakin primary 2 a karatu tanada actual 6 years kenan, tana girma se dad’a kyau take sede wani hanzari ba gudu ba, hak’waran gabanta duk sun zube se gib’i kake gani in ta washe bakin hakan yasa siblings nata suke making jess of her suyi ta mata dariya itako tayita kuka tana jan Allah ya isa in Baba ya dawo ta gaya mai ya d’au mataki. Zeezee de kam ta gagari kowa a gidan rikicin yau daban na gobe daban, bata jin maganan kowa se na Baba.
Mama ce zaune tsakar gida tana gyaran farce Zeezee ta shigo sanye take cikin wani ‘yar kanti iya gwiwarta, kitson shuku biyu ne akanta wanda ya sha beads. “Mama!” Banza da ita Mama tayi “Mama!” Ta kira for the second time.
“Meh? Meh? Meh kuma kikeso yau?” Tayi maganar tare da d’ago kai tana k’ura wa Zeezee ido.
“Kibani d’ari cikin kud’in da Ya Zannah yabani ranan.”
“Wai shin an gaya miki kud’in naki haifafa yake ne? Dubu biyu ne kacal kuma a tambayan k’ananun canji duk kin k’arar da dubu biyun, d’arin dana baki jiya shine k’arshen kud’in naki.”
“Wallahi k’arya ne kina son ki kashe min kud’ina ne kuma wallahi bazan yarda ba” tayi maganan tana bubbuga k’afa. Dirty look Mama ta watsa mata sannan ta cigaba da yankan farcenta ganin haka Zeezee ta wuceta takai dab da shiga d’akin Mama kenan Mama ta sa mata kira “Zeezee! Wallahi kika kuskura kika tab’amin kud’i kinji na rantse dukan ki zanyi na gaya miki kud’inki ya k’are.”
“Wallahi zaki gani” cewar Zeezee in a very low voice hawayenta ta share sannan ta d’au hanyan barin gidan “kuma ki dawo ki sa hula kafin ki fitan.”
“Barin sa ba” ta murgud’a baki sannan ta fice. Gidan Ummu Mufeeda ta nufa bayan tayi sallama ta gaishe ta “yauwa sannu Zeezee yawo ba d’an kwali ko? Bakisan bakin mutane kad’ai ya isa ya karya miki wannan sumar taki ba?” Shiru Zeezee tayi batace komi ba as tana nazarin wani k’aryan zata mata chan tace, “yauwa Mama na ne ta turoni wai in kinada N500 ki bata in ta samu zata miyar miki, batada cenji ne kuma tana son ta sallami wani.”
“Toh nagode” ta amsa tare da ficewa, kantin Ya Wakeel ta nufa ta kashe d’ari biyar d’in tas cikin sayayyan shirmen banza sannan tadawo gida Mama na ganinta bata ce mata komi ba ta wuce da ledar parlour. Bajewa tayi kan rug ta tab’a wannan ta tab’a wancan tana cikin haka Mama ta shigo, ko d’ago kai ta kalleta batai ba se shan chocolates nata take “ke ina kika samu kud’i kikayo wannan siyaya?” Shiru... “Dake fa nake magana! Am very sure babu kalan wad’annan chocolates cikin na school naki.”
“Haaa’ah! Nikam ba kud’in ki na d’auka ba ina ruwanki?”
“Kinsan Allah zan mauje ki, ina kika samu kud’i nace?”
“Nima ban sani ba.” Ganin Mama tayo kanta da nufin bugin ta tasa ihu “zan fad’a zan fad’a.”
Oyya speak up!”
“Gidan Ummu Mufeeda naje nace kince ta ara miki d’ari biyar-”
“Ni?!” Mama ta dafe k’irji.
“Amman karki damu tace ta baki a kyauta kinga ba sekin biya taba.” Bata hankara ba Mama ta fisgota ta hau nad’a mata na jaki bayan ta mata lik’is ta tattara chocolates d’in tayi sadaka dasu wa almajirai. Kuka kenan! Kuka Zeezee tayi tayi tana jan Allah ya isa har bacci ya isketa a garriage koda yaran suka dawo daga islamiyya suka ganta kwance gun basuyi ta kanta ba dan sun san halinta sarai daga tambayarta meya faru seta hauka da rashin kunya kokuwa in Baba ya dawo tace kai ka tab’a ta.
“Maamaa!” Ta fad’a a shagwabance.
“Me ta miki yau kuma?”
“Duka na tayi haka kawai” d’aga ta yayi ya share mata hawayen sannan sukayi ciki “Hafsah! Hafsah! Wallahi muguntan naki ya soma yawa kullum sede ba’a barki da ‘yar nan ba se kiyi ta dukanta sekace ganga? Ina kike fito nace!” Da confidence nata ta fito “ai bakaji me tayi yau ba...” nan ta kwashe labarin komi ta bawa Baba hoping he’ll back her today, to her suprise bayan ya gama sauraronta yace, “toh laifin waye? Da kin bata kud’in da ta tambayekin da duk hakan ya faru ne?”
“Lallai ma Alhj!” Mama ta fad’a short of words, “kana nufin tayi dai-dai kenan?”
“Bance tayi dai-dai ba amman you are partially to blame kuma karki sake tab’a ta dan wallahi zan soma jan Allah ya isa.”
“Wallahi sede kaja amman muddin ta sake tafka rashin hankali kaman na yau banga me hana ni dukanta ba abin kunya yarinya is 6 years old almost getting to 7 amma banda fatiha da nas, falaq and ikhlas ba abinda ta sani” tana kaiwa nan tayi ciki.
“Kar ki jita kinji K’anwa ta zan nemo miki malami yana miki karatu a gida islamiyya nede bara kije ba.”
“Toh Baba.”
Alwalan Sallan Maghrib suka shiga yi kasancewar yau Baba ne ze jasu a gida kowa na alwala banda Zeezee datayi cross leg kan kujera tana game a ipad, fitowan Mama daga bayi ta galla mata harara “ke bazaki tashi kiyi alwalan bane?”
“Barinyin ba!” daidai nan shigowan Baba d’akin kenan “ina yaran suke? Ku fito muyi sallah.”
“Zeezeen fah? Baza tayi sallan bane?”
“Ke ina ruwanki yarinyan nan is just 6 kuma ko a muslince ma cewa akayi se yaro yakai 7 a soma sasa.”
“Meh laifi idan an fara sata yanzu?”
“Kanki akeji Ibraheem ku fito.” Nan suka fiffito Baba yahau jansu bayan sun idar Baba yasa Zeezee ta d’auko school bag nata dan yin homework nata.
“Ni shi nakeso.”
“Yi hak’uri k’anwata gobe shi ze miki amman yau ki zab’i daya cikin sauran kinji? Maza jeki su miki kizo mu kwanta” ba tare da tace komi ba ta fice k’aramin parlour, su Mariam ta tarar ba Ibraheem. “Ya Omar kamin homework d’ina.”
Omar dake jin dad’in chatting dayake ya d’ago kai tare da galla mata harara “bazanyi ba bakiga ina amfani da waya na bane.”
“Kana chatting da budurwa de kuma sena fad’awa Baba kema Adda Mariam naji ranan keda Ya Ibraheem kuna magana wai wani friend d’inshi na sonki duk sena fad’a.”
“Banza yanzu ma kije ki fad’a” cewar Mariam tare da watsa mata harara.
“Zaka min ne ko sena je na gayawa Baba?” tayi maganan tana hararsa da manya-manyan idanunta.
“Kawo in miki” yayi maganan full of sarcasm, wurga mai jakar nata tayi “Verbal Reasoning ne da Quantitative inka gama ka kaimin jaka na d’aki” ta k’are maganan tana harararsa.
“Kutcee! Ya Omar kana jinta take ma wannan rashin kunyan?” Cewar Yasmeen.
“A’a’hah! Barta kekam” yadawo da kallonsa kan Zeezee, “in nagama zan kai miki suke nan homwork d’in?”
“An bamu a handwriting ma shima kamin page 17.”
“Lallai! yanzu handwriting d’inma bazakiyi ba?” Yaseen ta fad’a.
“Ina ruwanki?” ta murgud’a mata baki “dan bance kimin ba kike da bakin magana koh?”
“Ahh ahh! Kekam Yasmeen barta mana, jeki kwanta ‘YAR GATAN BABA.” Dad’i sosai taji taje tayi ta game nata a d’aki koda Baba ya tambayeta assignment infa? K’arya ta mai tace sun gama.
“Omar I don’t trust you what are you planning on doing? Yau kai ne Zeezee ke ma rashin kunya haka baka ce komi ba” states Mariam.
“Bar ni da ita Adda Mariam ita ba hegiya ba, kwab’a mata homework d’in zan ta kama zero yadda gobe za’ayi punishing nata da kyau.”
“Pwhahhah!” Suka kwashe da dariya “wallahi amman ka burgeni da haka zamuna getting back at her fitsararriyar yarinya haka” Yasmin tayi maganan tana jin dad’i.
www.beeenovels.blogspot.com
_Heres a page in honour of you sweetheart divas *Maryam (Abmar), Deeylerhh* and *MeenoUr,* my boo thang thang, ILY'all!_
“Ji yadda kike magana kaman kinyi mata d’aki tak’i kwana ciki, bansani ba ko a parlour kikeson tana kwana.”
“Kamar ya a parlour? Baga d’akin su Yasmeen ba.”
“Wai kina nufin Zeezee ta soma kwana da su Mariam? Mugayen can!”
“Eh mana!” ta basa amsa take. “Ba yayyun ta bane?”
“A dalilin meh zan tura K’anwata kwana da wad’ancan mugayen? Ba abinda ze kai Zeezee d’akinsu Mariam kiji ki sani.”
“Lallai kuwa!” Tayi maganan tare da miqewa ta nufa gun wardrobe nata searching for her night gown “shikenan kullum damu zata na kwana?”
“Eh har sena mata d’akinta itama.”
“D’aki?! Ta zaro ido waje a ina zakayi mata d’akin?”
“Wannan kuma is for me to know and you to find out kin gama feshe-feshenki ki kashe mana wuta, Allah bamu alkhairi” yana kaiwa nan yaja musu comforter da Zeezee sukayi baccinsu comfortably as always.
~* ~* ~*
_Monday morning, 6:10AM_
“Ke! Zeezee wallahi ki tashi kona zuba miki ruwan sanyi iskancin banza shekaranki nawa da shiga makaranta amman ace kullum sekin bawa mutum headache kafin ki tashi a wani gidan ma ke za kina yin wanka da kanki, tashi!” Yasmeen ta k’are maganan cikin sautin tsawa ganin ko kad’an Zeezeen dake baccinta tana tsotsan thumb finger’nta bata motsa ba, hakan ya sake k’uludda ita “wallahi zan mareki tunda Baba bayi gida.”
“Mareta wallahi” cewar Mama ai tana jinki. Tas! Yasmeen ta wanke d’uwawun Zeezee da mari da force ta miqe zaune tare da sa ihu.
“Wallahi barin je makarantan ba muguwa kawai.”
“Huummm!” Yasmeen ta toshe hanci “ji warin baki sekace latrine, k’azama kawai tashi da Allah!” haka da k’yar Yasmeen ta samu tasa Zeezee toilet nan ma zama tayi kan toilet sit tak’iyin brushing da ya kamata tayin, bayan 2 mins Yasmeen ta dawo ready to bath her taga ko brushing Zeezee batai ba hasali ma bacci take comfortably kan toilet sit d’in, ruwan sanyi ta tsiyaya daga famfo ta fesa mata a fuska firgit har tana neman fad’i daga kan sit d’in ta farka “meh haka? Muguwa kawai, Allah ya isa” tasa ihu “Allah ya isa mumuna kawai.”
“Toh kin min tsarki ne da zan sauk’on?” Ta watsa mata harara.
“Yanzu fitsarin ma se an miki tsarki?”
“Pupu nayi.”
“Mschww dirty girl kawai”
“Niba ke ce zakimin ba Ya Omar nakeso.”
“In zaki tsaya ki tsaya” aiko Zeezee ta bijire mata itafa se Omar ze wanke mata pupu. Mama ce tasa baki a k’arshe ta tura Yasmeen kirawo Omar.
Bayan ta samesa a d’akinsu ta isar masa da sak‘on.
“Wallahi bazan jeba kashin ya bushe a jikinta inde ni zan wanke mata.”
“Kaine kashi ze bushe a d’uwawunka ba ita ba d’an banzan yaro kawai maza tashi!” Scolded Baba “bazaka tashin bane sena gaggaura maka mari?”
“Allah sarki Baba yarinyan nan fa yaci ace ta soma tsarki da kanta she is almost getting to seven (7) years”
“Eh bazata wanken ba seta cika seven (7) d’in wuce nace mana!” Haka yana kumbure-kumbure yaje ya wanke mata pupun Yasmeen ta mata wanka. 6:40AM Yasmeen ta kawo wa Zeezee breakfast nata na chips and eggs aiko tana gani ta soma rigima “ni bance chips nake so ba ni indomie zan ci.”
“Kinga ba time yanzu K’anwata yi hak’uri kici wannan d’in.”
“O’o tahau shure k’afafu ni indomie nakeso.”
“Oya Yasmeen kiyi sauri ki dafa mata kiyi amfani da ruwan kettle seya dahu da wuri.” Kamar wacce zatayi kuka Yasmeen tace, “wallahi Baba ba ci zatayi ba yanzu da indomien aka dafa cewa zatayi chips takeso neman sa mutum aiki ne kawai.”
“Banason suratan banza kije ki dafa mata nace!” In 18 mins indomie’n Zeezee ya iso kad’an taci ta jagwal-gwala saura as expected, Mama ta zab’a wai ta sama ta uniform, bayan an sa mata ta d’ago socks nata ta samata anzo sa takalmi aikuwa Zeezee tace ba wannan zata sa ba yau bayan taga shi Omar ya mata polishing, haka yana ji yana gani Baba yasa sa sake mata polishing wani sam be damu ba saboda yasan meya shirya mata a school yau.
“All stand!” Ordered Mrs. Audu (form teacher’n su Zeezee) nan da nan su Zeezee da sauran class members nata suka mik’e suna nan har yanzu class da seat nasu d’aya da Lubiee they must be best friends now. “Submit all of your homeworks row-by-row all at once.” Nan da nan d’aliban suka fiddo da homeworks nasu su kayi kamar yadda teacher’n sun ta buk’ata.
“Zainab Isma’il Yusouf!” Called Mrs. Audu angrily, “come here!” Zeezeen da batasan me tayi ba ta mik’e a sanyaye “yes Ma’am.”
“Whats wrong with you? How can you fail all of your homeworks?”
“Me?” Zeezee ta dafe k’irji.
“Yes or do you need some proof?” Mrs. Audu ta d’ago mata zeron da takama a duka homeworks natan “shame on you! class say shame on Zainab” nan ‘yan aji suka hau yima Zeezee shame shame shame illa Lubiee ce bata mata ba. Kuka Zeezee tayi tayi ranan ana fita break ta tarke wata Deborah a lungu tayi mata d’ankaren duka sannan tayi warning nata kan inta kuskura ta kai k’ararta seta mata wanda yafi wannan. Kuma badan komi ta daki yarinyan ba sedan wai ta lura da Aunty tasa su yi mata shame duk Deborah tafi yi da ihu. Baba na zuwa d’aukanta ta nuna mishi homework da Omar ya mata ta fad’i.
“Omar! Omar! Zo nan!” Omar dayasan this was coming ya mik’e yaje “na’am Baba” wulla mai littafin Baba yayi, “explain this, meh haka?” Bayan ya k’are wa makeken zeron dake kan fejin kallo yayi k’ok’ari ya had’iye dariyan sa sannan yace,
“Jiya ina kiranta tazo muyi mata homework d’in tak’i ta gudu nikuma... Nikuma...”
“Kai kuma kayi deciding da kayi failing nata har kasa ayi mata wak’a gaban aji koh? Toh maza ka bata hak’uri.” Ai atapir Omar yace baze bada ba seda Baba yayi dagaske yabata hak’urin aka wuce wajan. Fita Baba yayi kafin nan yace, “kice Mamanku tayi miki homework naki kinji?”
“Toh ba-bye”
“Babu” tabada amsa tana cigaba da tafiya.
“K’arya kike fad’a kikayi ko?”
“Nikam ki barni” daga nan ta wuce ciki, bayan tagama wulli da socks da takalmanta as always tabar vest da panties zallah sannan ta fito da school bag nata zuwa d’akin Mama “wai aji Baba kimin homework d’ina.”
“Yau kuma? Ki jira yayyun naki suka dawo su maki.”
“Ba kina gani ba Ya Omar ya jefar dani da gan-gan naci zero ni kimin.”
“Kawo toh” bayan ta fito da homework d’in Mama ta buk’aceta ta faddo da pencil pack nata sede wayam ba komi ciki.
“Ina pencils nakin suka je?” Shiruu ba amsa, “dake fa nake magana? Ina sabin pencils dana sa maki ciki jiya?”
“Haaa’a! babu sun b’ata ki d’auko min wani” hannu Mama takai bakinta ta bige da k’arfi seda Zeezee tasa ihu, “idan baki bar min magana da rashin kunya ba na riga buge bakin naki kenan.”
“Allah ya isa” ta fad’a tana riqe da bakin nata.
“Ina pencils d’in suke? Ko ki fad’a ko in miki d’ankaren duka.”
“Ni shikenam kullum kiyita duka na Allah ze sak’amin.”
“Ina pencils d’in?!” ta daka mata tsawa, itama a tsawacen ta miyar mata da amsar;
“Sun b’ata babu!”
“Toh wallahi ki bud’e wannan kunnuwan naki da kyau ki jini, zan sa miki wasu biyun kika b’atar da wayan charger na zan chod’e wannan k’afafun naki kinji na rantse” haka da rigima suka samu suka k’are homework d’in.
“Zo ina gunda k’awar taki ta yak’ushe kin?”
“Nifa ba a yak’usheni ba.”
“Maqaryaciya kawo fuskan” ba musu taje Mama ta duba gun tarasa ciwon.
“Ina yake toh? Neman yima yarinya sharri kawai.”
“Wallahi Alhj akwai-” katse ta yayi “seki nuna ai in akwan!”
“Laaa! Bade foundation kika shafa ba?” Mama tayi maganan tana murza hannun ta don gaskata abinda idonta ke fad’i mata. Jin haka Zeezee taja baya da wuri “Baba kaga Mama tana min sharri ba?”
“Karki kulata K’anwata jeki sa hijabi yau malamin ki ze fara zuwa.”
“Eh Zeezee zaki fara karatu.”
“O’o ni bana so suna duka.”
“Wannan bare dake kiba” haka da k’yar ta amince 4:30PM malaminta ya iso tayi karatu tak’i tayita shiririta ita wai bataso. Haka rayuwan Zeezee ya cigaba da kasancewa har ta gama primary one rigimin yau daban na gobe daban ta gagari kowa a gidan.
Washegari da safe Baba yakai Zeezee asibitin ido kasancewar complaining da take, bayan an auna idon nata aka gano tana suffering from short-sightness take gun aka auna idonta aka bata eye glasses aiko Zeezee tace ita bataso ‘yan ajinsu zasu mata dariya kasancewar wani film data kalla UGLY BETTY.
“Su Ya Ibraheem basu cemin glass d’ina yayi kyau ba ni banaso” tasake sa ihu har seda Mama dake ciki tafito.
“Har kun dawo ne? Ya Zeezee da glass haka? Idon bai gani ne?” Ta tambaya, nan Baba yayi mata bayanin komai “ayya auta ta Allah baki lafiya” maimakon Zeezee tace ameen seta kuma rushewa da sabon kuka “toh ni kuma menace?”
“Bakice min yayi kyau ba ni banaso.”
“Haba! Kin ganki kuwa? Dr. kawai, Dr. Zainab.”
“Su Ya Ibraheem basu ce min yayi kyau ba.”
“Barsu, bara ku ce mata yayi kyau bane? Sam baku iya zama da k’annenku ba” Baba yayi scolding nasu, da k’yar Mariam ta iya shanye dariyan ta “yayi kyau” suka fad’a in unison.
“Aikin banza kawai mu shiga ciki K’anwata” haka koda su Omar suka dawo suma basu cemata glass nata yayi kyau ba tayita kukan banza.
The following day as always da k’yar aka samu aka shirya Zeezee, k’iriniyarta ta yau tafi ta kowani rana sabida Baba baya gida, tun fitan sa sallan Asubah be dawo ba da alama wa’azi ya rik’e shi. Bayan an gama shiryata Mama ta feffesheta da turare sannan ta wuce gaban dressing mirror dan d’auko wa Zeezee eye glasses nata wayam! Ta duba gun da ta ajiye jiya babu ta tambayi kowa a gidan duk sukace basu gani ba, nan fa aka shiga neman glass na Zeezee ana cikin haka dai-dai 7:08AM kenan Baba ya dawo gida “hope kun gama shiri, oya kufito mu tafi.”
“Alhj ko kaga eye glasses na Zeezee?” Mama tayi tambayar tana duban cikin wardrobe nata.
“Ba gaban mirror kika ajiye jiya ba?”
“Toh gashi babu ba inda ban duba ba duk babu.”
“Kamar ya babu Hafsah? So kike kicemin glasses d’in yayi k’afa ko meh? Ni wallahi bana son carelessness yanzu ya kikeson taje makarantar?”
“Alhj ji yadda kake magana kaman da gan-gan nayi misplacing ni wallahi am certain agaban mirror na ajiye.”
“Seki d’auka ai in achan d’in kika ajiye.” Bin Zeezeen dake zaune kan gado Mama tayi da kallo tace, “Ke ina kika kai glasses nakin?”
“Aww yanzu kuma sharri zakiyi mata? Kuma ban hanaki ce mata ‘Ke’ ba?”
“Ai tasan me nake nufi ina kika kai glasses d’in?”
“Ni ban d’auka ba, Baba kaga Mama koh?”
“Barta K’anwata zo abinki.”
“Ai tun jiya take cewa batason glass d’in ba tantama ita ta d’auka ta b’oye.”
“Kede kice kinason mata sharri kawai K’anwata ke kika d’auka?”
“A’a” ta kad’a kai.
“Tsakanin ki da wa?” Baba ya tambayeta, Shiruu Zeezee bata ce komai ba “Zeezee ke kika b’oye wai?”
“Dagaske bani bane Baba.”
“Za kiyi wa Baba k’arya?” Kai ta kad’a “to gayamun ina glasses nakin yake?” Baki ta turo “ni banaso.”
“Bakiji me Dr. yace bane Zeezee? Idon ki na ciwo only if kina sawa idon zasu gyaru ko kinaso ki tsufa ba ido?”
“O’o”
“Good then you must wear your glasses temporarily kinji? Yi hak’uri kije ki d’auko min.” Zatayi magana Baba yayi saurin katse ta “shhh! And je ki d’auko min” haka ba yadda ta iya tabi Mama da dirty look sannan ta fice babban parlour inda ta b’oye glasses d’in in between cushion na 3 seater tasa hannu ta zaro ta kaiwa Baba yasa mata da kansa sannan suka fice se kumbure-kumbure take a motan haka har suka isa school.
“Koda me ta miki be kamata ki tuhumeta da dambe ba, kai k’aranta zakiyi wa form teacher’nku.”
“Kai k’ara Baba ai se ‘yan class namu sumin dariya ni ta sake kallo na wallahi dukanta zanyi.”
“Aww bazakiji maganan Baba ba kenan? Inda kuma yanzu kin ji mata babban ciwo ko kin fasa mata kai fah?” Shiru tayi batace komi ba har suka isa gida, isarsu ta fito ita kad’anta Baba na binta da jakanta da lunch pack suna shiga ciki sukayi karo da Mama tana kwashe kayan shanya kan igiya sannu da zuwa ta musu data lura da yadda Zeezee ke cinno k’aramin bakinta tagano da akwai matsala. “Mekuma ya faru yau? Alhj ko kunyi fad’a ne?” Kan wanda bazeyi magana ba yace;
“Ke yanzu da zaran na fad’a miki meya faru seki hau cewa ai dama na gaya maka” Baba na maganan Mama kuwa na bin Zeezee da kallo nan ta hango babban shatin cizon dake hannun damanta.
“Ke da Allah bakin ya isa haka ba sunanta da aka sa a balck list.”
“Me za’a fasa dama mutuwa ko hisabi? Mena gaya maka kwanaki? Ai wallahi kad’an ka gani wataran seta fasa ma wata kai a school a kaiku duka police station anan ne zakuyi hankali.”
“Toh ya isa da Allah muguwa kawai abinda dama kika iya kenan baki wa mutane instead kijata kiyi mata nasiha kina cewa har station se an kaita to tare zakuje kiji in gaya miki.”
“Ai ba nasihar da zan mata kanku akeji tunda cikin sauran ‘ya‘ya na k’waya hud’u ba wanda aka tab’a kawo min k’ararsa yana fad’a a school dan anyi akan Zeezee se meh? Kai ka lalata mata tarbiyyarta saboda haka ba abinda zance mata kai d’in daka b’ata seka gyara” tana kaiwa nan ta gama sauk’e kayakin daga igiya tayi ficewarta.
Chess of drawer’n Mama wanda ake adana mata socks nata ta fito dasu, sanye take da black english wear kanta a tsefe an kamasa sakwa-sakwa. A dai-dai tsakar gida ta ajiye sannan ta d’ago new pair of socks tasa ta tattara teddy bears nata ta jerasu kan table da bulala rik’e hannunta wai tana musu lesson. Mama na gama cin abinci tafito kai plate kitchen ta tarar da Zeezee da socks tana yawo tsakar gida “haba! Zeezee wani irin sabon salon iskanci ne wannan? An tab’a sa farin socks a gida ne? Bana school bane?”
“Ni ki banni ai ba naki bane nawa ne.”
“Oya maza cire socks d’in ki mayar”
“O’o” ta fad’a stubbornly, idanun Mama na sauk’a kan drawern ta da Zeezee tayi wurgi dashi tsakar gidan ta fusata, kanta tanufa ta nad’a mata na jaki ta kuma sata ta miyar da drawer’n ciki, kuka Zeezee tayi tayi har seda Baba yadawo as always ya bata gaskiya ya yita balbale Mama yana ikirarin ze soma jan Allah ya isa next time ta sake tab’a masa Zeezee’nsa.
Days, months and even years passed by Zeezee nada eleven (11) years yanzu tana matakin Jss 1 a LYS still, yarinya a kullum dad’a kyau take ga tsawo masha Allah bata da wani kauri ‘yar slim to fashion take. Yasmeen kuwa nada seventeen (17) years last year ta gama makaranta tana jiran admission a ATBU into physics education. Omar kuwa is twenty and half (20½) years old an zama saurayi se rawan kai yana ATBU shima studying computer engineering. Mariam kam ma preparation na bikinta ake she is twenty-two (22) years old, last year tayi graduating daga ATBU in microbiology, bikin ta bayan babban sallah in Allah ya yarda. Ibraheem yaya babba kuwa is now twenty-four (24) years old, two (2) years back yayi graduating from ATBU in Petrochemical engineering (course d’in manya!) Saurayi son kowa k’in wanda ya rasa yayi service nasa yanzu haka ya fara aiki a NNPC, kud’i yake samu sosai har ya sai motarsa k’irar Honda Anaconda new model.
www.beeenovels.blogspot.com
_Assalamu Alaikum everyone, I usually don’t say a thing on matters like this but I think its high time I do now, ku sani your negative comments will never stop me from continuing with what I’ve started. Na farko dana fara rubutun nan ba wacce na cukume mata kwalar riga ko bakin zani nace dole seta karanta min littafi in kinga bazaki iya karantawa ba fine quit it there are thousand of books out there sekije ki karantasu amman kam BAZAN TAB’A TSARIN RUBUTA NA BA saboda tun farko dana fara bada idea'n wata na fara ba dan haka dan ke ko ita bazan canza tsarin labarina ba wacce taga bata k'aruwa dashi walillahil hamd seta bar karantawa. Duk me hankalin da ya zauna yasan akwai babban darasi cikin wannan littafin saboda dole ILLAN GATA ze biyo baya, ku baku tsaya kunga k'arshen littafi naba kuna judging d’ina, phew!. Masu cewa wai zagin Mama da Zeezee takeyi is too much inku baku tab'a ji ko gani ba toni nagani da idanu na inda 'ya ke zagin uwa infact abinda ke faruwa mostly kenan a rayumar ta yau and dole agyara kokuwa muna tare da babban hatsari. Ni ba anyhow nake rubutu ba duk books d'ina akwai life lessons ciki kamar yadda wannan ma darusan suna nan fitowa one-by-one wanda already wasu masu tunanin har sun fara gano hakan. I just want to tell y'all masu cewa littafi na baida direction su sani cewa reading is not by force kamar yanda ban saki karantawa ba seki bari dan kanki tunda yana b'ata miki rai ba dole a duniya. Fans dina masu sona kuma thanks y'all for the support, I LOVE YOU ALL, INA TARE DA KU!_
Tsaye take a tsakiyan d’akinta tana sanye da blue vest meh crossed arms seda ¾ black leggings, kanta kitson shade biyu ne wanda ta kama k’arshen da ribbon jaa da alama neman abu take bata gani ba danko gabad’aya d’akin nata upside down yake, d’aki ne me kyan gaske komi cikinsa combination na dark and light pink ne ba’a cewa komai sede masha Allah, dogon tsuka taja sannan ta d’au laptop nata ta fice daga d’akin a fusace tana k’walla wa Baaba meh aikinsu kira “Baaba! Baaba! Baaba!”
“Na’am” dattijuwar ta amsa tare da katse sharan da take.
“Ina kika kaimin USB na?”
“Meh kuma USB Zeezee ban tab’a kominki ba, d’akin naki kawai na share.”
“Bawanin nan kullum sede baki shiga min d’aki ba se na rasa abuna ni wallahi bana so kije ki d’au min USB na kawai” ana cikin haka Mama ta shigo parlour’n “ya haka Zeezee mawa kike d’agawa murya haka?”
“Ma Baaba haka kawai kullum tayita canza min position na abubuwa na ni banaso abanza ta b’atar min da USB yanzu.”
“Bakida hankali ne? Baaban kike cewa haka? Batayi jika dake bane?”
“Wannan kuma ku ya dama nide kar a sake tab’a min abu na, ina wayana in kira Baba ya sai min sabo” ta k’are maganan dai-dai ta shiga d’akinta ta musu banging k’ofar. Binta Mama tayi da kallo sannan ta kad’a kai “yi hak’uri Baaba kinsan halin Zeezee addu’a kawai zamuyi mata.”
“Ba komai Maman Zeezee ai yarinya ce.”
“Kuma daga yau karki sake share mata d’akin, tunda da kin share se tace abinta ya b’ata.”
“Maman Zeezee beyi zafi haka ba.”
“A’a Baaba karki sake ni na fad’a miki.”
“Hello Baba?” Tayi maganan a shagwabance.
“K’anwata ya haka? Meya sameki?”
“Baaba ce” tayi stating almost like crying.
“Me tayi miki kuma?”
“Ta b’atar min da USB na.”
“Shine abin damuwan? Bari yanzu zan aika Omar ya siyo miki kinji?”
“Toh yaje yanzu.”
“Angama K’anwata shikenan?”
“Eh shikenan nagode” tayi hanging. Data connection ta bud’e ta hau whatsapp, group nasu na LYS STARS ta shiga tana glimpsing chats d’in data gama taje kan contact na Lubiee tayi mata sending;
_‘Yan mata kinsan yau kika ce zakizo koh? I will be waiting for you_.
Kafin ta sauk’a Lubiee ta hau tayi replying nata back;
_Ina tuni Babe, Ya Salman nake jira by 3 in shaa Allah zan iso akwai gist fah, Ahmed yace yana son Lailan Jss 1B se nazo deh!_ Zeezee na gama karantawa tayi replying nata;
_Sekin iso I can’t wait_ nan ta kashe datan ta had’a wayarta chargy ta baro d’akin.
“Ya haka kana tsaki kai kad’ai?” Ibraheem dake sake da headphone akansa amman ba komi yakeji ba ya jefa wa d’an uwansa Omar tambaya.
“Mschw! Wannan Baba da Zeezee mana wai inbar duk abinda nake inje in siyo mata USB tayi misplacing nata.”
“Shine abin tsakin? Sekace sabon abu, yaci ace ka saba ai yanzu”
“Ai dole kace haka saboda kaga kai babba ne yanzu ana isolating naka a matters haka wallahi yarinyan nan b’ab’b’ala ta zan mschww!”
“Wai ina Ya Omar ne beje ya siyo min USB’n bane? Inafa so inyi amfani dashi” Zeezee tayi maganan tana shiga d’akinsu Omar.
“Ke ban hanaki yawo cikin gidan nan da vest da ¾ leggings ba? Ce miki akayi gidan arna ne? Maza wuce kije kisa kaya” Ibraheem yayi scolding nata.
“Haaa’a! Jimin mutum, nikam ka barni sekace wani Babana ka tsaya kana wani gaya min abinda zanyi bale ma ni ban maka magana ba kowa yayi harkan gabansa, Ya Omar USB na” ta miqa hannu nufin ya sa mata.
“Ni kike gayawa magana?” Ibraheem yayi maganar a fusace tare da mik’ewa, ganin haka tasa gudu amman ina taku d’aya yayi ya cafko hannunta “wayyo Allah Baba na kayi hak’uri, wallahi bada kai nake ba dan Allah karka tab’ani na tuba.” rank’washi me d’ankaren zafi ya danna mata akai “waye sa’anki anan?” Tana kuka tace, “wallahi babu duk kun girmen kayi hak’uri dan Allah.”
“Shegiya me kan kwa-kwa kawai ki sake min rashin kunya kiga abinda zan miki” ya turata seda ta fad’i, harara ta watsa masa ganin bai ganinta “mugu kawai” ta fad’i chan k’asa k’asa yadda ita kad’ai taji me ta fad’an, miqewa tayi a wahalance ta takai bakin k’ofa tace, “mugu kawai da wani farin fuska kaman k’osai Allah ze sak’a min kai kuma Omar kaje ka siyomin USB na” tana kaiwa nan tasa gudu binta Ibraheem yayi a guje se bayan Mama taje ta lab’e, “meh haka? Sakeni nikam! Kije kiyi rashin kunya kizo kina b’uya min a baya, sakeni!”
“Wallahi Mama yarinyan nan ta kiyaye ni.” Ibraheem yayi maganan yana nunata da yatsa.
“Ai kazo ka d’auke ta ka mata duk abinda kaga ya dace shegen rashin kunya ne da ita.” Jin haka Zeezee ta sake dandame jikinta a na Mama tana ihu dan kanta Mama tabawa Ibraheem hak’uri ya fice, “wallahi Zeezee ki sake kibar halin nan naki kin mai da manyan yayyun ki tamkar kece babba bakijin tsoron idonsu?”
“Nikam da Allah! kullum sede kita scolding d’ina su baki ganin laifinsu ai nasani Baba kad’ai ke sona a gidan nan kuma zaki gani” tana kaiwa nan ta shige d’akinta.
“Haka ya faru? Bari ina zuwa, kinci abinci?”
“A’a”
“Jeki d’iba kici ina zuwa” yana sauk’eta ta wuce kitchen su Mariam da Yasmeen ta tarar se aiki suke da Mama tana tayasu.
“Ina abinci na?” tayi tambayan ma dukansu, ba sannu da aiki ba komai.
“Kinba ma waye ajiya kike wannan tambayar?” Yasmeen ta watsa mata harara. Hararan ta miyar mata itama, “ma ke na baiwa, ni ina abinci na? Tun d’azu ku d’aura lunch kunk’i sekun bari yunwa ya gara mutum.”
“Wai waye sa’anki anan? Zan gaggaura miki mari fah!” Mariam ta bud’e mata ido.
“Mschww!” Zeezee taja tsaki, ganin Mariam ta miqe Mama tayi saurin dakatar da ita “yi hak’uri Mariam barta tana yima kanta ne” nan da nan suka sauk’e girkin Zeezee ta matso da plate nata “asamin.”
“Baza’a san ba kinyi sallah neh?” Mama ta tambayeta, shiruu Zeezee batace komi ba dan kuwa batayi sallan ba, “tambaya nake kinyi sallan Azahar?”
“Ni meh had’in abinci da Sallah kisa min kona fad’awa Baba.”
“Jeki gayan maras kunya kawai” dai-dai nan Baba yashigo kitchen d’in “yauwa Baba kaga Mama tasamin abinci wai o’o.”
“O’o kamar ya? Sa mata abinci mana Hafsah.”
“Kasan kuwa yarinyan nan batayi sallah ba infact bata ma sallah kullum ko an sata se baza tayi ba.”
“Bata sallah?” Baba yayi maganan unbelievably.
“Wallahi k’arya ne” cewar Zeezee.
“Toh kinayi neh?”
“Wallahi batayi Mama” cewar Yasmeen.
“Rufa min baki abinda kika iya kenan” Baba ya tsawata wa Yasmeen. “Zeezee wai baki sallah?”
“Baba inayi wallahi kawai yanzu ne ban yiba saboda ina jin yunwa amman ina gama ci zanyi.”
“Yauwa K’anwata I trust you ai” k’wace serving spoon na hannun Mama yayi ya zuba wa Zeezee potatoe porridge d’in da nama biyar akai.
“Haba Alhj ya da haka? Mukuma sauran me zamu samu?”
“Ke ko kunya bakiji ba me zakiyi da nama tsohuwa dake?”
“Nide ba tsohuwa bace kuma naga wanda suka fini shekaru ma sunaci, kuma Mariam ku d’ibi biyar-biyar d’in, yarinya ko aikin d’aga tsinke batayi sede taci tayi kashi tayi rashin kunya kuma aka tashi ita za’a na bata duka naman miya.”
“Kanki akeji” plate ya ja ya d’iba nasa suka fice da K’anwarsa.
Baba ya tara iyalan sa a parlour dan raba musu kayan babban sallan su wanda will take place in 3 weeks time. “Ina Omar?”
“Yaje siyo wa Zeezee USB.” Ibraheem ya amsa.
“Okay” yayi maganan yana zaro had’ad’d’un zannuwan dake cikin wani babban leda, guda goman duka ya baza a kan carpet “ina K’anwata?”
“Na’am Baba” ta matso kusa dashi ta zauna.
“Zab’i guda hud’un da suka miki anan-”
“Haba! Haba! Alhj kayi adalci mana, Mariam Babban su ai ita ya kamata ta fara zab’a” Mama ta fad’a.
“Zani ba zani bane kam? D’auka Zeezee da Allah kar kiji ta.” Gwalo Zeezee tayi ma Mama sannan ta kwasa hud’u mafi had’uwa cikin goman. “Oya kema Hafsah d’au naki guda biyu.”
“Biyu? Ita hud’u ni biyu kuma seda ta d’auka zan d’au wallahi banaso kabata nawan, na hak’ura.”
“Kanki akeji” ya d’au guda biyu ya wulla mata sauran hud’un kuma ya bawa Mariam ta zab’a biyu ta bawa Yasmeen biyu ana cikin haka Omar ya dawo nan Baba ya basu shaddojinsu shida Ibraheem guda uku-uku had’d’d’u masu kyau, bayan nan ya sake jawo wani leda ya zazzage laces biyar ciki nanma yace Zeezee ta zab’a biyu bayan ta zab’a ya raba wa Mama da su Yasmeen ragowar haka kaman suyi kuka sukayi godiya suka watse. D’aki Zeezee ta nufa da kayakin sallanta se tsalle take nata guda six (6) na sauran 3-3 ganin ta wargaza wardrobe natan d’azu agarin neman USB kuma gashi tana son sa sabin kayanta ciki yanzu gashi she is not in the mood of preparing her wardrobe taje tasamu Baba tayi ta mai shagwab’a ita akira Yasmeen ta gyara mata wardrobe nata, bayan taje ta kira Yasmeen Baba ya isar mata da abinda yakeson tayi ai atapir tace ita baza tayi ba ai da gan-gan Zeezeen ta wargaza kayakin, ido sosai Baba ya bud’e mata sannan ta amince se kumbure-kumbere take.
Nan da nan ta shiga gyara wa Zeezee wardrobe nata ana cikin haka Lubiee tazo, parlour’n Baba Zeezee ta kaita suka yita hira kaman ba gobe suna game, bayan Yasmeen tagama gyara mata wardrobe d’in suka koma d’akinta taciro wa Lubiee kayakin sallanta seh 5:30PM Lubiee tace zata tafi bayan sallamarta da Baba yayi yasa Ibraheem yayi dropping nata nan Zeezee tace se ta bisu itama. A bayan mota suka zauna su biyu se k’us-k’us suke har suka yi dropping nata.
“Ayyi Ya-”
“K’aniyanki nan waye driver’nki? dawo gaba nace!” Harara me rai da lafiya ta watsa mai batasan ko ya ganta ta mirror ba, bayan ta dawo gidan gaba ya seta kanta ya sake mata rank’washi me zafi, “Allah ya is-”
“Meh kikace?”
“Babu” hannunta yakama da niyar murd’awa aiko tasaki ihu “dan Allah Ya kayi hak’uri wallahi bazan k’ara ba.”
“‘Yar banza kawai ai ko kiyi behaving kanki ko na b’ab’b’ala ki kamin mu isa gida wallahi” daga nan Zeezee bata sake ce mai komi ba dan lafiyarta tayi shiru on their way back home budurwan Ibraheem Fateema ta mai waya kan tana buk’atan ganinsa nan ya sha U-turn Zeezee na ganin haka tace, “ni wallahi ka kaini gida kafin nan kaje gun Fateeman.”
“Magana kike?” Ya mata sending wani dirty look dan kanta tayi tsit ahaka suka isa Ibraheem yasata tabar motan Fateema ta shiga. Se hira sukeyi tun Zeezee na hak’ura taga bazata iya ba ta mik’e taje ta samesu “ni wallahi kashi nakeji hiran ya isa haka.” Kallonta Ibraheem ya tsaya yi totally out of words.
“Zeezee toh muje in kaiki ciki kiyi?” cwar Fateema.
“Ni bana sharing toilet, na gidanmu nakeso” baki wangalau Fateema ta bud’e tana kallon Zeezee dake murgud’a mata baki sama-sama “toh Baby se next time baby sis is in need kuyi ku tafi.” Har a yanzu Ibraheem ya kasa cewa komai haka yana gani har Fateema ta shige gidansu Zeezee ta bud’e motan ta shiga “toh kayi sauri mana Ya, yafa matseni” bece da ita komi ba ya kunna motar suna cikin tafiya sunzo ta old GRA ya yi parking gefen hanya “meh kuma zamuyi anan Ya?” Nanma bece komi ba ficewa yayi kawai ganinsa tayi ya karyo itche d’anye yana nufan motan kafin tace zata bud’e k’ofar ta har ya isketa, fincikota yayi ya hau zabga mata itchen a k’afafunta daman ‘yar guntuwar ‘yar kanti ne a jikin ta tana ihu tana basa hak’uri amman ina se k’ara mata yake kasancewar hanyan shiru ba hayaniya, seda ya nad’a mata na jaki sannan ya barta lokacin har wani sama-sama nishinta ke. “Kad’an kika gani bake fitsara da rashin kunya ba? Muna tare dake ai gyara miki zama zanyi maza miqe ki bud’e motan ki shiga.”toh kayi sauri mana Ya, yafa matseni” bece da ita komi ba ya kunna motar suna cikin tafiya sunzo ta old GRA ya yi parking gefen hanya “meh kuma zamuyi anan Ya?” Nanma bece komi ba ficewa yayi kawai ganinsa tayi ya karyo itche d’anye yana nufan motan kafin tace zata bud’e k’ofar ta har ya isketa, fincikota yayi ya hau zabga mata itchen a k’afafunta daman ‘yar guntuwar ‘yar kanti ne a jikin ta tana ihu tana basa hak’uri amman ina se k’ara mata yake kasancewar hanyan shiru ba hayaniya, seda ya nad’a mata na jaki sannan ya barta lokacin har wani sama-sama nishinta ke. “Kad’an kika gani bake fitsara da rashin kunya ba? Muna tare dake ai gyara miki zama zanyi maza miqe ki bud’e motan ki shiga.”
“Oya!” Yayi commanding nata, motar ta bud’e ta shiga shima haka sede har a yanzu bata bar kukan ba. “Kuma kimin shiru wallahi in bakiyi ba sena k’ara miki wanda yafi wannan” kukan tacigaba dayi “aww! Baza kiyi shirun ba kenan?”
“Zanyi dan Allah kayi hak’uri.”
“Oya yi shirun kuma wallahi kikaje kika fad’awa Baba na dakeki ya kirani yamin suratan banza zakiga abinda zan miki, kinfi kowa sani na” a da tanada niyyar sanar da Baba abinda yayi mata amman jin ya kashe mata warning ta fasa saboda tasan halin Ibraheem sarai mugu ne first class ma kuwa. Haka tana ta sobbing har suka samu suka isa gida aranta tana meh tunanin wani abin zata yimasa ta rama.
Tana fitowa daga motan ta buga murfin wane zata b’alla ko uffan bece mata shide da murfin motansa ya b’alle da seta raina ma kanta wayo. Karo taci da Baaba A’ee gbam! “meh haka mutum na tafiya bai ganin gabansa” tayi maganan ba tare da tasan da wa ma sukaci karon ba.
“Toh Zeezee lafiya dai koh?”
“Aww Baaba kece sannu nasha ma ‘yan iskan almajiran nan ne.”
“Sannu Zeezee ba gaisuwa?”
“Nikam da Allah kullum gaisuwa baki gajiya da amsawa ne?” Bata jira jin meh A’ee zata ce ba ta wuce ciki, baki A’ee ta tab’e tace, “Allah shiryeki Zeezee.”
Tailor’n su ya iso nan kowa ya fito da zannuwansa bayan ya gama a’aunasu suka zab’i styles nasu Baba ya bada advance har tailor yazo tafiya Baba ya tsayar dashi, “yauwa Shaheed d’inkin nace ka tabbata seka gama dana Zeezee kafin ka fara na sauran saboda kaga ita yarinya ce, su ko ba kayan sallah zasu iya yin sallan ka gane ai?”
“Eh Alhj zan fara da nata in nasamu nayi koda biyu ne a natan sena tab’a na ‘yan uwan nata.”
“O’o ni seka gama min duka six d’in” Zeezee tayi chipping in.
“Bakida hankali? Mu kuma fa? Shaheed please kar ka saurareta” cewar Mariam.
“Lallai sannu toh se an gama da natan za’a tab’a naku maras kunya kawai” Baba ya sanar da ita.
“Allah sarki Baba-” inji Yasmeen.
“Allah sarkin K’aniya, sam ku baku san meh kara wa k’anwarku ba? Se an gama nata a fara da naku ka jini ai Shaheed? Se mun jika nan da 2 weeks d’in.”
*© MIEMIEBEE*
www.beeenovels.blogspot.com
Da Asubaah Mama da kanta tazo tada Zeezee daga bacci don yin Sallah ‘cause anytime ta tura sauran bata tashi. Gbam! Gbam! Gbam! “Zeezee bazaki tashi ki bud’e k’ofar bane?” Murya cike da gyangyad’i tace, “waikam ba naji ba? Ai zan tashi.”
“Shine nace ki bud’en k’ofan.”
“Toh wai ki shigo kiyi meh Mama? Ai zan tashi.”
“In baki tashi ba ma keda Allan ki” daga nan ta wuce d’akinta. Jin shiru hakan ya tabbatarwa Zeezee Mama ta tafi, “ai wallahi bazan tashin ba” daga fad’an haka taja comforter ta cigaba da baccinta se 7:00AM ta tashi tayi sallan ta sake komawa bacci, kasancewar yau Sunday ba school. Se 10:30AM ta tashi tayi wanka tasa wani A-shaped gown nata ta fito, a parlour ta tarar da Baba ta gaishesa sannan ta wuce kitchen dan neman abin karin kumallo chan taci karo da duka sauran ‘yan gidan nasu Mama kad’ai ta gaisar, dama on normal basis tana gaishe da Ibraheem ma amman data tuna da dukan daya mata jiya se ta fasa.
“Ina breakfast d’ina?” Banza da ita duka sukayi Mama ce ta mik’a mata flask natan tace, “in bazaki gaisar da sauran ba Ya Ibraheem fah?” Baki ta turo sannan ta watsa mai harara dan ko kallonta baiyi “ina kwana?” Tace chan k’asa-k’asa almost like whispering, ganin yak’i amsawa yayi banza da ita tace, “tafi nono fari karka amsan” dai-dai zata karb’i flask nata Mama ta rik’e “amman fa yau akwai aiki kinga Baaba bata ji dad’in jikinta ba so bata samu daman zuwa ba yau adalilin haka na rabawa kowa aikin da zeyi, naki aikin share site nasu Ya Ibraheem da musu mopping neh” seda tabari flask na abincin nata ya shiga hannunta tace, “chabd’i! Ni ce zan share musu d’aki meh sauran kuma zasuyi? D’akina kawai zan share kowa ya share nasa.”
“Haka kika ce?” Mama ta tambayeta.
“Eh mana ni ba abinda zan share musu, Allah yayi wa kowa hannu” ta kama hanyan fita daga fad’an haka.
“Tsaya ke! Kika gama breakfast d’in kizo zan aike ki shago” Ibraheem yayi maganar in a serious tone. Shiru tayi kamar bata jisa ba, “ko baki jini bane?”
“Naji” ta watsa mai harara ganin bai kallonta nan ta juya ta hau gun-guni “shikenan shi baida aiki se aikan mutum shago wallahi bazan jeba.”
“Wai Mama kinajin yarinyan nan bazaki buge bakinta ba?” Cewar Yasmeen.
“Barta tanayi wa kanta ne ai ba inda rashin kunya ze kai mutum se halaka Omar Baba na kayi hak’uri ka share muku kaji? Yi hak’uri.”
“Mama wallahi haushi kike ban in kince tana yi wa kantan nan duka ne be isheta ba.”
“Barta de ba muna nan tare da ita a gidan nan ba? Zan gyara mata zama” Ibraheem yayi maganan tare da miqewa haka ranan kowa na aiki banda Zeezee dake kallon disney channel, ita gabad’aya ma tama manta Ibraheem yace ze aike ta shiko yana sane time ya bata inhar takai 12noon bata zo ba ita da shi ne!
“Gani” tace alokacin da ta shiga d’akin nasu bata damu da miyar wa Omar shara bayan da tayi ba, gindin tsintsiyan ya seta k’afafunta ya rabga mata “bakiga shara nake bane da zaki shigo kina miyar min da aiki baya?”
“Wayyo Allah! Allah ya isa na ni nasan kana sharan ne” kunnenta ya kama “meh kika ce?”
“Babu dan Allah kayi hak’uri” murd’a kunnen nata ya shiga yi tana ihu Ibraheem dake zaune yana kallonsu ko k’ala bece ba “ni kike jawa Allah ya isa?” Tana hawaye tace, “a’a na tuba dan Allah kayi hak’uri.” Se anan ya saketa ta shiga share hawayenta N2000 Ibraheem ya mik’a mata “siya min Glo na 2k.”
“Ya nima ka bani N500.”
“Da uban rashin kunyan kin zan baki N500? In kinason kici arziki na ki dena yimin rashin kunya now b’ace min daga gani” bata ce dashi komi ba ta zarce d’akin Baba takai k’ara nan ya turata ta kira Ibraheem d’in.
“Uhm Ibraheem Baba na kanada N1,000 kabani?” Baba yayi maganar cike da dabara.
“Eh Baba” nan ya zaro wallet nasa ya mik’a mai “shikenan?”
“Eh shikenan nagode koh?”
“Ba komai Baba kekuma kije ki siyomin ina jiranki.”
“Wai toh ba na jiba haa’a!” Bayan ficewan Ibraheem Baba ya mik’a mata dubu d’ayan, “saura kuma kije kice dubun daya banin na baki ba ruwa na.”
“Barin fad’a ba Baba nagode” nan da nan taje ta sai masa katin itama ta sai nata.****
Kallo ya galla mata da kanta ta gyara zancen nata, “na’am Ya ka kirani.”
“Se kuma dana kiraki baki iya gaisuwa bako?” Kallo tabi friends nasan dashi Allah yaso ba mumuna cikinku da kunga buro-uba tayi maganan a zuci.
“Ina wuninku” tayi murmuring, k’asa-k’asa suka amsa.
“Kije ki kawo musu drinks sannan Yasmeen tayi guiding naki ki dafa mana indomie tunda ba ayi abinci ba tukuna.”
“Ni? In dafa muku indomie? Gaskia a’a Ya, ni ban ma iya dafawa ba kuma koda na iya ma sekace wata boyi-boyi.”
“Magana kike? nace kice Yasmeen tayi guiding naki.”
“Ni wallahi Ya...” ta hau bubbuga k’afa tana tura baki “ni bazan dafa ba ina kallon shake it up kawai kuyi hak’uri zan kawo muku snacks d’ina na school kusha da drinks d’in.” Dariya sosai ta sa friends nasan d’aya daga cikinsu yace, “Mazaa kabar baby sis nakan nan kawai dama ba yunwa muke ji ba, kawo mana ruwan kawai kinji?”
“Yauwa Ya Suleiman” shide Ibraheem bece komi ba tunanin kalan dukan da ze mata kawai yake, haka taje ta d’ibo musu drinks da snacks nata ta jera musu kan tray dai-dai tazo ajiwa kenan Ibraheem ya cafke hannunta tare da sa mata nank’washi meh uban zafi aka, k’ara ta saki tare da jan Alah ya isa nan ya k’ara mata “meh kikace?” Tana kuka tace,
“Nace kayi hak’uri wallahi sabon kitso ne a kaina.”
“No kubar ni da ita me kika gama cewa d’azu?”
“Babu, Ya dan Allah kayi hak’uri wallahi bazan k’ara ba wayyo kaina.” Kunnenta ya kama ya murgud’a da k’arfi.
“Argghh!” Ta saki k’ara “wayyo Baba na dan Allah kayi hak’hri.”
“In sake saki aiki kice min baza kiyi ba kiga abinda zan miki marasa kunya kawai” ya saketa “get out!” Da sauri ta mik’e tana jan Allah ya isa har ta fice.
*****
Da daddare bayan su Baba sun dawo daga sallan Isha ya kirawo Zeezee d’akinsa, “K’anwata bana kema zanyi maki yanka kinji?”
“Dagaske Baba?” Ta fad’a sounding thrilled.
“Sosai ma K’anwata” rungumosa tayi tana meh jin dad’i ana cikin haka Mama ta fad’o d’akin “ya haka meke faruwa?”
“Baba yace zemin yanka wannan Sallan.”
“Yanka? Alhj yanka zakayi mata?”
“Eh in shaa Allah tunda Allah ya hore min.”
“Sauran kuma fah? Ai kamata yayi ka musu duka ka had’asu kan dabba d’aya.”
“Hmmm Allah ya shirya ka toh partiality a filin Allah haka, kullum ina ma wa’azi amman bakka ji.”
“Kanki akeji jeki huta K’anwata gobe kuna da school.”
“Toh Baba seda safe.” The next day Zeezee ta cika wa kowa kunne a gidan da waqan za’ayi mata yanka za’ayi mata yanka. Yayyun nata tun abin na damunsu ma har sun saba yanzu, hak’uri sukayi suka cire damuwan daga ransu in ba haka ba har ciwon zuciya yana iya kamasu.***
~* ~* RANAR SALLAH ~* ~*
Bayan sun dawo daga Idi Baba ya biya ya siyo raguna manya-manya guda uku, ba tare da b’ata lokaci ba yayi layyansa rago d’aya nasa, d’aya na Mama d’aya na Zeezee. Nan da nan suka shiga aikin nama banda Zeezee dake mak’ale a d’aki tana kallo a laptop nata.
“Shikenan Mama ita Zeezee ba aikin da zatayi tana zaune a d’aki sekace wata sarauniya.” Yasmeen tayi maganar.
“Toh ya muka iya Yasmeen? Dama ace Babanku bai gida ne toh amman yanzu da ance Zeezee ta d’aga koda tsinke ne se ya hau kan mutum da bala’i ki barta kawai.”
“Ai wallahi idan ku kun hak’ura ni bazan barta ba Zeezee! Zeezee! fito nan dan k’aniyanki” cewar Mariam. Jin shiru ta nufa d’akin tan da kanta, miqe kan gado ta sameta, “fito muje muyi aiki.”
“Wai aikin meh?”
“Aikin uwaki ‘yar banza kawai fito! Kin maida mutane boyi-boyin ki fito nace!”
“Ni ban iya ba wallahi kika tak’ura min zan had’aki da Baba.” Seda Mariam tayi dagaske ta samu ta fito da Zeezee daga d’akin. Kujera ta nema ta bata ta zauna suka hau gyaran kayan ciki banda toshe hanci ba abinda Zeezee ke chan kashi ya tab’a mata jiki zumbur ta mik’e “ni wallahi na fasa yin aikin k’azantar nan ku bani wani aikin daban.”
“Akwai wanke-wanke sekije ki kama.” Yasmeen tayi informing nata.
“Ni bazan yi wanke-wanke ba sede wani aikin.”
“Maza wuce kije ki kama wanke-wanken kona gaggaura miki mari maras kunya kawai,karki ga dan ina barin ki wallahi kika b’ata min zan illata ki wuce nace!” Mama ta bud’e mata “ba zaki wucen bane?”
“Ba naji ba wai kam” baki ta murgud’a sannan ta k’arasa wajen da aka tara wanke-wanken ta hau yi for the first time, se kwab’awa take tanayi kuda suna mata yawo ajiki abinda tafi tsana kenan! “Ha’aah nikam kudena tab’ani mana” tayi maganan da kudajen wai. Dariya Yasmeen ta hau mata “daidanki kenan su cinyeki ma mu huta” ganin kudan basu bar bi mata jiki ba ta je ciki ta d’au insecticide ta feffeshe wajen wanke-wanken se anan tasamu tagama jagwal-gwala wanke-wanken tayi ciki bata sake fitowa ba seda taji an soma gashi “ni ina rago na? Duk wanda ya cimin nama ban yafe ba wallahi.”
“Gashi chan achan ba wanda ya tab’a miki namanki keda kanki zaki soya” Mariam ta fad’a tana hararta.
“Ke wannan Adda Mariam kin kusan tafiya ma amman bazaki d’an canza hali aji dad’inki kafin ki tafi gidan miji ba, kuma kar kowa ya tab’a min ragona.”
“Saidai in baza ayi sadaqa ba, in ba haka ba cinyan gaba da na baya duk sena yi sadaqa dasu” cewar Mama.
“Wallahi kikayi sena gaya wa Baba ai dabba na ne, kiyi da naki mana.”
“Please Mama karki sake ce mata komi in aka zo yin sadaqan seta hana muga, banza kawai” cewar Omar yana cigaba da latsa wayarsa. Harara da murgud’a baki ta mai sannan ta koma d’akinta.
_10 months later..._
Alokacin Zeezee na Jss2 tana neman shiga na 3 saboda sun ma gama exams na 3rd term nasu sakamako yayi kyau sosai. Zeezee fa ba sauk’i an zama ‘yan mata yanzu se palli da rawan kai, hali zanen dutse har yau bata fasa rashin kunyarta ba, infact sede abinda ya k’aru ma. A month back Mariam da mijinta suka dawo Bauchi da zama kasancewar an mai transfer a gun aiki, sosai Mariam tayi nauyi haihuwa nan da watan gobe in Allah ya yarda, tunda Zeezee ta gano haka ta d’aga k’afa daga gidan Mariam saboda sata aikin da take.
Yau Monday Mariam ta kira Mama kan atura mata Zeezee tad’an tayata aiki zatayi bak’i, Zeezee najin haka tayi faking rashin lafiya ita sam bazata jeba seda Mama tayi dagaske sannan ta shirya akwatinta kaya biyu kacal tasa ciki dan batason ta jima, Ibraheem ne yayi dropping nata chan Fadaman mada inda gidan Mariam yake. Bayan isan Zeezee ta wuce guest room ta dire jakanta sannan ta fito ta tarar da Mariam zaune a parlour tana shan farin k’asa.
“Ina wuni? Ya k’arfin jikin?” ta gaishe ta sama sama.
“Alhamdulillah rice and stew zamuyi min Zeezee.”
“Rice and meneh? Kinfa san inba farin shinkafa ba, ba abinda na iya in zaki saki jiki ki tashi kije kiyi stew naki toh in kuma ba haka ba se bak’in naki suci garau-garau (shinkafa da mai da had’i) wai ace Uncle Mahmoud (mijin Mariam) kullum baida aiki se kawo mutane gidansa chin abinci wallahi mijina be isa yamin wannan d’anyen aikin ba.”
“Ni meya kaini? Ke matarsa bakiyi complaining ba seni, ni dama kun cigaba da zaman ku a Kano wallahi.”
“Jeki kwashe tomatoes da sauran kayan miyan dake fridge d’in ki gyara ina zuwa in d’iba miki albasa.”
“Wai Adda Mariam ni zanyi komi ke kawai zaki zauna nan kina ture-ture?”
“Inda da lafiya na ajinki ma zan ce kizo ki tayani ne?”
“Nikam gaskia bazan yanka albasa ba kema kinsan inada ciwon ido.”
“Se akace masu ciwon ido basu yankan albasa?” Haka suka ta drama har aka had’a kan stew d’in Zeezee ta dafa shinkafa.
Kwana biyu Zeezee tayi ma Mariam taji duk rayuwan bayi mata dad’i, ita ke mata wanke-wanke wai harda shara ma. “Ni wallahi yau zan tafi ban iyawa sekace ni nace kiyi cikin.”
“Meh kika ce?” Mariam tayi snarling at her.
“Ni nayi magana neh?” Ta murgud’a mata baki. “Wallahi yau zan tafi, don ni ba jaka bace.”
“Kanki akeji nide ki gama min shara da wanke-wanken kiyi duk abinda kika so yi.” Haka bayan tagama aikin da cuwa-cuwa kamar yadda ta saba ta shirya tsaf ta d’au wanka cikin purple lace, trolley’nta ta ja zuwa parlour inda Mariamke miqe a k’asa “zaki tafin ne?”
“Eh” tayi maganan tana plugging earpiece nata.
“Toh ki gaida su Mama” daga nan ta rufe idonta danyin bacci. Few minutes later ta bud’e idanun nata taga Zeezee tsaye inda take bata ko motsa ba. “Ya haka? Kin fasa tafiyan ne?”
“Shamawai! Da zanzo inta miki bauta da mijinki ne bazaki sallamen ba! Lallai kuwa!”
“Aww jira kike in sallameki?” Mariam tayi maganan a bit suprised tana dariya da k’yar.
“Eh mana bake kad’ai ba har da Uncle Mahmoud ma.”
“Wallahi k’arya ne ni ki sallameni.” Zeezee tayi maganan stubbornly.
“In d’ari biyun mota ne bazan rasa ba.”
“Chab! Wallahi Adda Mariam ba wasa nake ba ki sallamen.”
“Kisani na dole, ke wato baki aiki tsakani da Allah bama wannan ba jinki ban sane da sharan cuwa-cuwan da kike min neh? Duk dottin k’ark’ashin gado da kujera kike tura su koba haka ba?”
“Wancan kuma damuwanki ai in kikayi bak’i ba leqa k’ark’ashin gadon ko kujeran suke ba, nide ki sallameni in tafi.”
“Lallai kuwa you are not ready to leave inhar ni kike jira na sallameki, zama nan ya kamaki” Mariam na kaiwa nan ta juya mata baya da k’yar. Tsaye Zeezee tayi wajen if only tasan ina Mariam ke b’oye kud’inta, tana cikin wannan tunani ta jiyo k’aran motan Uncle Mahmoud robe dake cikin handbag nata tayi sauri ta ciro ta shafa k’ark’ashin idonta take ta soma hawaye dai-dai nan Uncle Mahmoud ke shigowa anan Zeezee ta soma magana cikin kuka, “wallahi baki isa ba sekin biyani 5k na, ai ba haka mukayi da ke ba wallahi kibani kud’i na” ta rushe da kuka. Mariam batasan alokacin da ta mik’e zaune ba tana kallon wonders kafin tayi magana Uncle Mahmoud yayi sallama, “wa’alaikumus-salam” ita da Zeezee suka amsa in unison “sannu da zuwa Uncle” tace tana share hawayenta kaman dagaske.
“Yauwa sannu Zeezee ta, Hajiya Mariamu sannu da jiki.” Da ya lura da Zeezee seya kamar kuka take, “ya da kuka kuma? Wani abu ne?” A rayuwa Uncle Mahmoud nason Zeezee badan komi ba sede dan k’iriniyarta musamman inya tuna days back da inyaje zance gun Mariam itama tafito tace se anyi zancen da ita.
*December, 2016*
“Kaman ya ba komai? Gashi ina gani kina kuka kice babu, Hajiya Mariamu na me kikayi wa K’anwar tamu take kuka?”
“Wallahi Dear ban mata komi ba ni kaina bansan meke damunta ba.”
“Ai dama haka zakice kin kama kin cinye min 5k kikace nazo tafiya zaki bani, baki ban ba dole kice ai baki san meke damu na ba ni zan tafi.”
“Ni?!” Mariam ta dafe k’irji “yaushe na tab’a cin bashi gunki Zeezee?”
“Wait... Wait Zeezee na, Adda Mariam ce ta ranta kud’i gunki bata biya kiba?”
“Eh Uncle” ta fad’a tana gyad’a kai.
“Wallahi Dear karka jita sharri take neman min.”
“Tsaya mana Habibti muji daga bakin K’anwar tamu.”
“Wallahi karka jita sharri take neman min.”
“Wallahi ba k’arya bane Uncle Mahmoud if only Yasmeen was here data gaskata hakan, a idonta Adda Mariam ta ranta kud’in.”
“Chab! Lallai Zeezee bakijin tsoron Allah.”
“Ai nasan baki k’arya Zeezee, nawa ne kud’in nakin?” Dad’i taji sosai tasa hannu ta share hawayen ta “5K ne.”
“Dear Allah karka bata.”
“Ba ruwanki Hajiya Mariamu tsakani na da K’anwata” wallet nasa ya ciro ya irga 10k “gashi wannan duka naki ne” bayan ta amsa ta irga tsalle ta hau yi “duka nawa Uncle?”
“Eh mana, stew na ranan yayi dad’i wannan tukuici ne.”
“Fa ba ita tayi stew d’in ba.” cewar Mariam.
“Wallahi nice ai Uncle ma yasani” pillow Mariam ta wurga mata “mak’aryaciya kawai” gwallo Zeezee ta mata ganin Uncle Mahmoud bai ganinta “toh Uncle ni zan tafi nagode Allah ya k’ara bud’i.”
“Ameen K’anwata bazaki jira in having lunch nayi dropping naki ba?”
“A’a Uncle karka damu zan tafi da kaina”
“Toh ki gaishe da Mama and everyone” bayan ba-bye taja jakarta ta tafi.
“Eh tace tana gaisheki haka Uncle ma kuma yabani 10k.”
“Toh masha Allah zan kira sa na masa godiya ina kud’in yake?”
“Me zakiyi dashi? Bade karb’ewa zakiyi ba!”
“Yo dama ‘yar yarinya dake sena barki da 10k?”
“Ni wallahi shiyasa banson fad’amiki ammin kyauta ni wallahi kibarmin kud’ina.”
“Haka kika ce?”
“Eh” ta amsa tana gyad’a kai “kinyi dai-dai, Allah kawo ranan da zakice na baki kud’i kiga in ban gaggaura miki mari ba.”
“Allah bare kawo ranan bama ni zan fita gidan su Miss Rama sena dawo” bata jira jin meh Mama zata ce ba ta fice.
Cikin sati biyu Zeezee ta gama kashe 10k d’in cikin k’ananun siyayyan da basuda amfani, ayau Monday suka koma school su Zeezee ‘yan matan Jss3. K’arfe 7:10AM ta gama shirinta Ibraheem yayi dropping nata kasancewar Baba yayi tafiya, yana dropping nata ya wuce office shima. Kasancewar yau ne first day at school basuyi wani abin arziki ba se hira suka ta sha ita da Lubiee and others 2:30PM Ibraheem yazo d’aukan Zeezee ko kad’an bata lura da motansa ba as she was busy gisting with her friends, ransa ne ya mugun b’aci ya fito daga motar a fusace ya nufi inda suke tsayen da hijabinta ya jata. Ashar ta hau d’urawa ba tare da tasan waya mata hakan ba, tana juyawa tayi 4 eyes da angry Ibraheem. “Ya yaushe kazo?”
“Wa kike zaga?” Ya danna mata rank’washi a presence na friends nata “Allah ya isa ni nasan kazo ne kuma seka kama ka jani da hijabi ka sakeni”
“Kinada bakin magana ko?” Kunnenta ya kama ta hijabin ya murd’a da k’arfi batasan lokacinda ta soma kuka ba amman hakan besa tayi shiru ba se Allah ya isa take ja mai a haka har yajata mota ya bud’e ya turata ciki se ihu take tana kuka a motan ganin ya faka gefe guda tayi kum da bakinta gudun karya karyi reshe ya mata kalan na kwanaki.
“Nayi shiru wallahi nayi dan Allah kayi hak’uri.”
“Marasa kunya kawai bari mu isa gida” yaja mota. Bayan isansu gida ta shiga bayi a guje ta danna lock tana ji yana kiranta tak’i bud’ewa seda ta tabbata ya fita masallaci ta fito ta nufa d’akinsu, wayarsa ta d’au ta shiga whatsapp ta tayi sending had’ad’d’en break up message cike da zagi da cin fuska wa Fateemah girlfriend na Ibraheem ta wuce d’akinta tasa lock tana me praising kanta.
“Barni da ita Babe.”
“No Baby please karka tab’a ta kabarta.”
“Kamar ya na barta! Baki karanta message d’in bane?”
“I did but please let her be for me dan Allah.” Seda ya nisanta yace, “naji I won’t beat her amman she’ll have to serve some punishment.”
“Eh better amman karka tab’a ta please” hira kad’an suka tab’a sukayi sallama d’akin Zeezee ya nufa direct daman gashi Baba bai gida bale ya d’aure mata gindi kamar yadda ya saba.
“Zeezee!” Bata san lokacin da ta saki fitsari a panties nata ba jin kakkausar muryarsa, shiru tayi bata amsa ba.
“Zainab!” Ya kira sunanta more tensed this time around “wallahi before the count of three ki bud’e k’ofan nan ko na b’ab’b’alki wallahi.” Safa da marwa take a d’akin ta rasa nayi chan tace, “Ya ina toilet nefa.”
“I don’t care ki bud’e k’ofan nan nace kar kiyi pushing d’ina kisa na miki duka.”
“Bazaka dake niba idan na bud’e maka?”
“Nace ki bud’e!”
“Ya dan Allah kayi hak’uri” a hankali ta nufi k’ofan ta bud’e take tayi kneeling “dan Allah kayi hak’uri” ko saurarenta beyi ba ya fincikota da hannu se side nasu yayi wurgi da ita a d’akin. Gabad’aya Zeezee ta gama tsurewa se faman hak’uri take basa “rufa min baki!” Ya daka mata tsawa “ce miki akayi dukan ki zanyi? Kuma koda dukankin ma zanyi, you think wannan hak’urin kin could stop me?” Dan sanyi taji a ranta, wajen laundry basket ya nufa ya fara fiddo da laundry’nsa duk anan kallonsa take bata ce komi ba bayan daya gama ya wurga mata sabulu da omo “oya pack them kije ki wanke min su tatas, isolate the white coloured ones from the rest and believe me in har be wanku me kyau ba zaki sake and don’t think wai da washing machine zaki wanke, uh-uh” yayi shaking kanshi “da bare hands naki now off you go.”
“Nace banaso tattara ki bani waje! Now!” Tana b’ari ta tattara kayakin tayi waje da su waje ta nema ta zauna tana sharb’an kukanta tsakani da Allah tana sumbatu tana kiran sunan Baba, ko uffan Mama bata ce mata ba da ta ganta, bayan data gama shan kukan ta tsoma kayakin cikin bucket tana tunanin ya zata fara wankin. Ganin Ibraheem tayi ya fito da belt a hannunsa take ta fara wankin without knowing how. Kujera yaja ya zauna gefenta yana kallonta tare da instructing nata da zaran tayi pausing kuwa ya d’aga mata belt tana kuka tana jan Allah ya isa ta samu ta gama wankin sukaje gun shanya ta shanyasu tas har takama hanyan d’akinta tana tafiya tana kallon yadda omon yaci mata faracu tana gun-guni Ibraheem ya kira ta “ke! Where do you think you are going? Baki fa gama aikin naki ba.”
“Ya kayi hak’uri wallahi na tuba zan kira Aunty Fateemah na bata hak’uri.”
“Aww kinsan dama abinda kikayi ba dai-dai bane?”
“Eh nasani wallahi na sani sharrin shaid’an ne.”
“Kinsan ba kyau mesa kikayi?”
“Wallahi sharrin shaid’an ne na tuba.”
“Zaki k’ara?”
“Wallahi bazan k’ara ba ko wayanka bazan sake tab’awa ba.”
“Kai inaaa tashi kije ki wanke toilet d’in by then kayan da kika wanke sun bushe kihau gogewa ban yarda da tuban da kikayi ba.”
“Ya wallahi na tuba bazan sake ba, na sake kamin duk abinda kaga ya dace.”
“Maza tashi ki bani waje ki sake tab’amin waya kiga” har da cin tuntub’e agarin fita, d’akinta ta nufa straight taje ta mik’e kan gado.
“Bakiji haihuwar Adda Mariam bane? Zanje tayata zaman jego.”
“Chab! Ke asuwa? Wallahi na rigaki ni zanje mata.”
“Se mu gani ai! Keda ko aiki bakison yinne zaki tayata zaman jego?”
“Wannan kuma keya dama wallahi ni zanje dani za’a ci kajin jego ehe!” ganin Yasmeen ta cigaba da shirya kayakin nata ta fice zuwa d’akin Baba kai masa k’orafi ai kuwa ya goye mata baya just as expected, yace sam ita zataje ta taya Mariam zaman jego ba yadda Mama batai dashi ya bari Yasmeen meh son aiki taje ba yak’i, bayan Zeezee ta gama had’a akwatinta Omar yayi dropping nata a motan Baba.
Mariam dake expecting Yasmeen kawai se ganin Zeezee tayi. “Ya haka ina Yasmeen?”
“Tana gida” ta bata amsa a takaice.
“Tana hanya ko tana gida? Ba ita zata tayani 40 days ba?”
“Baba yace ni zan miki.”
“Ke! God help me wallahi aiki zaki zage kiyi kina jina koh?”
“Ai nasani ina baby’n take muga kota kwaso muninki.” Da yamma Mama da Yasmeen suka iso tayi ma baby wanka.
30 days Zeezee tama Mariam ta tattara kayanta tabar gidan saboda gajiya da tayi da wanke panties na kashi, Mariam se aukin barin ‘ya ba pampers dalili wai ana zafi ga Ramlah se aukin pupu any minute. Ganin haka Zeezee tace zata koma gida Uncle Mahmoud da kansa yayi dropping nata ya bata 3k ai kuwa mutumiyar ta raina ta manta d’ari biyu zuwa biyar da yake bata almost after every 3-4 days nasa kati a waya.
D’akinta ta wuce direct tayi whats needs to be done sannan ta fito tayi d’akin Yasmeen, mik’e kan gado tana karatu ta tarar da ita “Yasmeen ina Baba?”
“Har kunyi arba’in d’in ne?”
“Su gama arba’in nasu lafiya wannan Ramlah take ko meh se aukin kashi minti-minti na gaji da wanke pant na gudo.” Dariya sosai Yasmeen ta tsaya yi da k’yar ta samu ta tsaida dariyan tace, “amman bakida mutunci wallahi sam!”
“Niba wannan ba ina Baba ya bani dubu biyu in cika in sai wani porche dana gani a Jumia 5k.”
“Baba yayi tafiya ai yau.”
“Tafiya!” Tayi exclaiming “shine be fad’a min ba wallahi ya kyauta.”
“Ji mata! matarsa ce ke da seya sanar dake in zeyi tafiya, lallai kam.”
“Ni yanzu ki ranta min 2k, na gama sa rai Uncle Mahmoud ze ban 5k yakama yawani ban 3k mschw!”
“Baki gode ba kenan.”
“Iyi kuwa ko bakin kasuwa naje na zauna zan tara dubu ukun, ranta min 2k d’in kinji?”
“Dalili? Ke d’inda baki biyan bashi.”
“A da ba, da dabansan meye bashi ba amman Allah yanzu zan biyaki.”
“Tsakaninki da wa?”
“Da da tsuntsu ne? Da Allah mana.” Kallonta Yasmeen tayi taji kaifa bazata iya rantawa Zeeze kud’i ba. “Kai! Ban yarda ba kije kice Mama ta baki.”
“Tana gida ne? Kai aiko tana gidan ma ba bani zatai ba ‘cause time da Uncle Mahmoud ya ban 10k ban bata ko k’wandala ba.”
“Kinga erin halin naki ai, nide kije ki rok’eta kokuwa kije gun Ya Ibraheem ko Omar nide na koyi lesson ban sake baki bashi.”
“Ya Omar? Wancan marowacin? Ko dubunsa ban tab’a ci ba, dama-dama Ya Ibraheem d’inma de shikuma yanzu da naje ze kama min suratai please ki bani Allah zan mayar miki nan da 2 weeks” da k’yar tasamu tayi convincing Yasmeen ta bata kud’in nan ta biya buk’atar ta.
* ~ *~ _Few days later_...~ *~
_Wednesday night 12:46AM_ Zeezee ce miqe kan gadon d’akinta tayi ruf da ciki se chatting take a wayarta not minding gobe tana da school ga kuma test da suke dashi a Maths. Bacci ne yazo yayi gaba da ita batasan when and how ba. 5:00AM as usual Mama tazo tayi knocking bisa k’ofar d’akintan gbam! Gbam! Gbam! “Zeezee tashi Sallah” shiru ba response “Zeezee!” Se anan ta amsa uhmmm.
“Tashi Sallah ko kin manta da akwai school yau?”
“Ni banayi.”
“Yaushe ne kikace baki Sallah? Yauma kice bakiyi?”
“Toh date d’ina ya rikice ne” tayi stating sleepishly.
“Banson k’arya fa bud’en k’ofa!”
“Mama dan Allah ki tafi naji zanyi.”
“Kar ma kiyi ba yarinya ce ke yanzu ba ai” tana kaiwa nan ta fice Zeezee bata tashi ba se 6:00AM alwala tayi, tayi Sallah ta koma gado ta mik’e a cewarta wai 6:30AM seta tashi tayi wanka ta shirya.
“Nikan dan Allah wa me cika min kunne? Koma waye ne ya koma seda na gama makara zaku wani zo kuna wani min knocking mschw!” Ta k’are maganan tana zipping school bag nata, drawer’nta ta bud’e taga ba uniform ciki duk sunyi dotti, jiyan daya kamata ta wanke batayi ba tana ta chatting. Ihu ta qurma ta zarce d’akin Mama, suprisingly Mama ta d’ago kai tana kallonta “ya haka? Ba school ne yau?”
“Ai dole kice haka” tayi maganan almost crying “Baba kad’ai ya damu da naje school koko a’a wallahi sena kirasa na irga mai komai, tun tafiyansa nike tashi na shirya kaina baku assisting d’ina gashi a banza yau nayi missing Maths test kuma teacher’n bayayin make up test.”