*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀1⃣
NOTE:-
_WANNAN LITTAFIN HAKKIN MALLAKATA NE,,XANCENA D'AYANE BANYI SHI DAN CIN ZARAFI GA KOWA BA SAI DAN KYAUTATA ALAQA。WANNAN LITTAFI TUKUICI NE GA D'UMBIN MASOYA WANDA SUKA NUNA DAMUWARSU AKAN TAWA QADDARA。NA SHAIDA WANDA KEDA DUBUN MASOYA DUNIYA SHIKEFA MAGANIN QUNCI MUTANEN MEDIA ASMEENAT TA GODE_
*BISMILLAHIR RAHAMANI RAHIM*
⬅
zafin rana ake kod'awa mai wuyar fassara da misali!!! wanda har takai ta kawo mutane basa iya gudanar da harkokin su na yau da kullum,,, har sai sanyin la'asar ya keto. hakan ma ranar yau ta kasance,,,sanyin la'asar yaketo laqwasss! bishiyoyi sunfara kad'awa, mutane sunfara sakewa, masu zama qasan bishiyoyi sun baje suna firar duniya,,kuma labarin su na yau yaraja'a ne akan yaushe rabo da zafi irrin wannan,? wasu nafad'a anyi kwatankwacin zafin a saudiya wanda yayi sanadiyar mutuwar biliyoyin rayyukka, haqiqa ko anan nigeria da ana lissafawa da tabbas rayukan zasuyi muni, duk da ma anayabawa qoqarin gwamnatin tarayya! da najaha, da qungiyar,likitoci ta duniya! da masu haqqi Akan harkokin lafiya akan yadda suke wayar da kai da temakon gaggawa idan buqatar hakan tataso,,,, amma a gefen munauwar ba haka abun yakeba, baida tabbacin wane yanayine ake ciki,,,domin mahaifin sa yayomasa gayyar baqin ciki alokacin da yake,tsaka da farinciki arayuwarsa,,,,lokacin da yakamata ace ya mori quruciyasa lokacin akayi ginin baqinciki azuciyarsa, bayajin komai sai d'aci,,,,,, yau RANACE MAFI BAQI DA MUNI GARESA lokacin dayaxo isar dasaqon xuciyarsa, alokacin qaddararsa tasashi kuka, abunda bayazato bare tsammani,,,,,yau duk miskilanci da gaye da rashin yadda sun qaura aduniyar sa. ba abunda yake xariya da birgima a duniyar zuciyar sa se kalaman Abbah...qasan tyels yake reto ya kulle d'akin baya motsin kirki domin rikicin dake rayuwarsa yagirmi tunaninsa...a wanan yanayin Ahamad yashigo yafirgita ganin munauwar akan tyels yana birgima, cikin sanyi da rawar murya yace Munnauwar Meke faruwa? idanunsa dake lumshe yabud'e jin muryar Ahamad,,, sunyi kad'uwa mai fixgar hankali, domin zaka iya rantsuwa idan qwalla tabaro idanuwansa to tabbas jinine''' hannu ya miqowa Ahamad alamar yad'agoshi" haka kuwa akayi'' Cikin murya maifeshin xafi yace ahamad Abba nason zalintar rayuwata, yanason cutar dani Ahamad,hum, hum,,, Amma wata kila besan aibuna bane, shiyasa yake gani idan yabani umurni ya cimma burinsa!! rabani da khairat ahamad tamakar zare rainane alhalin akwai rayuwa tare dani''' munauwar kayimun bayani yadda zanfahimta bangane rabaka da khairat ba? bazaka ganeba Ahamad! bazakagane ba! domin wannan abun kunyane gareni ace na Auri y'ar cikina!!! kuma ko y'ar cikinnawa y'ar qauye! kuma ko y'ar qauye bagidajiya',,,kuma ko bagidjiya y'ar matsiyata, hum!Ahamad wlh koda mafarkine yaxiyarci qwaqwalwata zan auri y'ar qauye xan ajiyeshi "A" gefen ibliz ,,,,d'ifffff fahimtar ahamad ta d'auke tunanisa ya jagule, yakasa me zaice da munauwar dan kwantar masa hankali,cox sarai yagano yarinyar da ake neman laqabawa munauwar,,,,,, kuma muddin itace tunanin sa kebashi,,, zab'in da abbah yayiwa munauwar azahirin gaskiya ya cuceshi,,duk wannan thinking yayi shine adaqiqun da bazasu gaza biyar ba,, yasaki gwaron numfashi tare da lasa baki yace munauwar bakada jah domin hukuncin iyay......NO Ahamad, hum NO...Wlh koda ba itace abba ke nufiba zanyi jayyayya dashi a wannan karon domin sauran matan dukkkk na d'auke su tarkace,, khairat kawai nake gani na amunce ma raina cewa maccece!!!!baxan dakatar dakai yanxu ba munauwar saidai take my advice... kabi abun asannu because I Know abba bayacewa iyi,, yasake cewa a'a!!!! wani malalacin kallo munauwar ya aikoma Ahamad tare da cewa a wannan karon zaice iyi yace a'a Ahamad domin baxanyi biyayya ga auren bagidajiya ba....koda kuwa zan qarar da y'ay'ana atiti, daqarfi Ahamad yad'aga hannu tare da cewa listen...munauwar idan kaya yab'ata be kamata hankali ya b'ata ba...! murmushi yayi wanda yafi kuka ciwoo tareda tsare Ahamad da ido na wasu secound sannan wata zazzafar qwallah ta malalo Agefen idaniyar sa ta hagu,,,cikin muryar kuka da tausayi yace you are right Ahamad!!! Kafad'i Abunda ranka yaso... fad'a domin dafin ciwon na zaunene azuciyar munauwar bata ahamad ba!! you misunderstand,,,munauwar sam ba son zuciyata nafad'a ba! kawai Inaso kabi "Ahankali duk son dazakayiwa wani baikai darajar iyaye ba, sune zasu soka koyaya kazamo""" bazasu tab'a juyama baya ba,,, zasu kyautatama koda kai ba mai godewa bane,,, shiyasa nace kabi assanu kasa Allah shi zai jib'anci Al'amarinka ni ko kai bamu isa goge abunda allah yazanaba...bai jira me zaifito harshen munauwar ba yafice karaf sukayi karo da Amma arikice tace ahamad yayi magana ko har yanxu?...... muryarsa ba dad'in magana yace amma kisa baki abba yajanye ra'ayinsa wannan hukuncin yayi tsauri dayawa.....cikin kaushi tace Ahamad ku kwantar da hankalinku,,,but wlh idan har zuciyata na harba jini dai dai bazan amunce da wannan gurguwar shawara tashi ba domin zancen banxane yakeyi.......
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀2⃣
_gaisuwa mai tarin yawa nake aikowa ga masoyana aduk inda suke afad'in duniya sannan ina maku barkar sabuwar shekara ta gilgorial kalanda hijirar annabi isa alahi salam!iiii,,,, ina roqon allah yabamu tarin alkhaira da nasarorin rayuwa yatsare,muda hassada da hangen nasama damu yasake sanyawa munadaga cikin sallihan bayi_
⬅
idan har zuciyata na harba jini dai,dai bazan amunce da wannan gurguwar shawara tashiba !domin zancen banxa yakeyi……cikin taushi da ladabi Ahamad yace ni zankoma Ammah,,,,,, allah ka daidaita mana komai cikin nasara yatafi,,,haka wunin yau yakasance baqiqirin kamar dagaske mutuwa akayi..... har sale sulin dare yakama, saidai abba ba abunda yadameshi,, yad'auki fushinsu amatsayin shirme..bayan wayewar gari ammah batashiga sashensa ba shikuma bai nemetaba! tasalima harkar takardunsa ke gabansa,,,cike da cin magani ammah tashigo d'akin,,,kallo d'aya zaka mata kasan tana buqatar bacci abunka da wanda yasaba da hutu,,har taxo ta zauna gafen gadon dayake zaune,,saboda jarumta irrin ta mazan jiya bai masan tana zaune gurinba,,,ammah qiris take jira tafashe ruwan maganganun da suka dameta, da takamasa birki akan qudurinsa na aurawa d'anta mitsitsiyar yarinya, kuma wadda tabautu da aikin qauye,,,,tare da d'aukar alwashin sai bayan ranta zata had'a zuri'a da yarinyar dataxo "A" baqin littafi,,,,,, wannan tunanin a zuciyarta kawai suke reto,,batare da arzikin fita sarariba,,,jin yayi banxa da itah tace Abban munauwar!! ataqaice,, kallonta yayi tare dacewa yaya dai,,,? cike da,jin kai, da hauka irrin ta mata tace A gaskiya bana goyon bayan shawararka, domin maganar gaskiya kana neman zalintar yaron nan.... cikin tsawa yace kitsaya matsayinki,,kar kishigo hurumin da banakiba, kuma zaqewar kina nema tayi yawa bugu daqari ina mai maki Albishiri abunda zaitada auren munauwar da jaleelah gawata ko ta munauwar,,, but muddin muna samun ni'imar numfashi, muna fitarwa kisanya aure sai inqaddara ta rusa auren..murmushi tayi tare da cewa idan kuwa hakane kayi kuskure,,, domin wlh bazanbari a cutar dashi ba, koda kuwa shine silar Ajalina Abban munauwar!! amma qiri qiri zakabi san xuciyarka ga wadda yaro keso ace a'a,,,kuma saboda rashin adalci,, ga matanan da suka mallaki Asalin kyau, y'an boko, y'ay'an masu dashi karasa matar aura masa se wadda taxo Abaqin littafi, kai ko kunya bakaji ganin duk maitashen kud'i da martaba biro auren qwarya tabi qwarya yake ma y'ay'an sa amma,,,,??? tass! tass! tass Abbah ya tsaida kalmar da taso fita sarari tare da cewa ni bazanyi auren qwarya tabi qwaryar ba,,auren qwarya tagari shine zab'ina ga d'ana kuma,kisani maganar tada auren nan tamkar da tsewar igiyoyin aurenki ne........ki kiyayeni fuuuu yajah riga, yafita…… cike da jin haushi da takaicin Abban munauwar, tace muxuba mugani? amma wlh se bayan raina...tare da baro d'akin itama,,,, kai tsaye tayi d'akin munauwar dirsha yake zaune kansa cikin qafafunsa wanda tasha jinin jikinta haka ya kwana,,,cikin kad'uwa da jimami tadafa kafad'arsa tare da kiran sunasa munauwar A silale!! d'agowa,,,yayi idonsa cike da qishin bacci,, cikin rawar murya da sarqewa yace amma be kamata narayu ba,,,be kamata nakai yau ina numfashiba hum amma,,,bai kamata qaddarata tabiyo min wannan hanyar ba,,, yaqarashe maganar cikin rishin kuka…… kallonsa tayi na daqiqu tare da cewa munauwar bazan tab'a bari ka auri wadda yake iqirariba,, zab'inka shine nawa, kasanya aranka ina tare dakai..... hannun ta yariqo duka biyu tare da cewa amma ki kai kukan ki ga Allah ya mallaka min khairat domin itace zab'in ruhina, baxan iya rayuwa babu khairat ba amma, itace bugun numfashina,,,hannu takai tare da shafa sumar kansa kamar qaramin yaro tace auren ka da khairat bagudu ba, jah da baya, sannan ta jawo hannun sa tamkar yaron da aka raba da nono jiya, batazame,ko,ina dashiba se wani qasaitaccen band'aki dayagama tsaruwa da kyau,,,sannan tace kayi wanka ka futo ina jiranka kaji yarona tana masa lallausan murmushi,,,,,, haka kuwa akayi befi mintuna goma ba yafito da jalabiya fuskarsa har tasoma zurmawa! sannan ta dubeshi tare da sakar masa murmushi mai sirri,,tace zo kasha ruwa kaje ka gana da khairat d'inka,,, domin nasani tana da buqatar jin labarinka,,,,,bai musaba yazooo gaf da ita yaxauna tare da murd'a wuyansa ixuwa kafad'arta yajawo hannunta yace amma kinji abunda zuciyata kecewa? lumshe idonta tayi domin rad'ad'in zafin so sha'aninsa yafi gaban ananata' sannan tace nasani munauwar bugun numfashin ka khairat yake fad'a.... afili yace amma dayawa nake son khairat fah,,,,,,hum nasani kuma zaka mallaka tare da kafa pure milk abakinsa,, ba laifi yasha dukda bawani d'and'ano saidan hana kukan hanji...bayan shud'war mintuna biyar da sukayi shiru ya miqe tare da cewa amma xanje naga dharkan kiyimin fatan nasara,,,,cike da sakin fuska tace je kanatare da addu'a ta munauwar...haka yatafi cike da jin qarfin jikinsa se yake gani kamar ma anbashi khairat d'od'ar ya miqe titin da zaisadaka da Junaidu Road.....wani katafaren hotel yanufa mai d'auke da kalomi manya manya da zaisaka gano sunan da wuri tare da qyallah haske A Inda maxaunin kalmomin yabayyana GIGINYA HOTEL....Hotel ne na Alfarma da morar rayuwa d'iyan manya masu fad'a aji ke da ikon shigar sa,,,,bai wani b'ata lokaciba ya tura hancin motarsa ciki, qirar B/W! bayan parking da yayi seda ya b'ata mintuna 5-6 sannan yafito..... kallonsa yakai ga inda yake muradin kallo kuma Abunda yake tsammani hangowa shi ya hango... cikin z
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀3⃣
_Ina qara gaisuwar ta'axiya ga iyalan gidan alh.tumaki mahaifin d'ai daga y'ar u'wa abokiyar aiki haleematu sadeeya rasuwa,, tare da roqon allah mad'aukain sarki yasanya can tafiye masa nanan AMEEN._
⬅
Abunda yake tsammanin hangowa shi yahango……cikin zaquwa yanufi hall d'in da idonsa sukayi tozali da abunda yake muradin gani.macce d'ayace jal zaune akatafaren hall d'in,, cikin shiga kalar ta mutanen turai, rigace fara soul wadda ba'abuqatar sama brexiya kasancewar dirin nonuwan da shape sunfi amsar rigar bada brexiya ba,,takalmen qafarta fari se kanta da yasha gyra gwanin kyau da tsari,,,, barasa mai kyau da tsada ce da wanke qoda "A" gabnta. bata zuba a dugon cup d'in dake gabanta ba, Also yanayin zaman darashin sakin fuskarta zai tabbatar ma tana da damuwa...!! ahankali yadinga takawa bai zame ko inah ba se inda matshiyar budurwar ke zaune cikin wata d'arsashiyar murya yace Dharkan!firgigit ta juyo idonta cike da qwallah! cikin muryar shagwab'a da sigar kissa tace my really what is wrong? jiya dayau layukan ka off……qwafa yayi da ido tare da jawota jikinsa sannan yasama musu gurin zama yana shafa sumar kanta yace Dharkan',,,,,,,, d'agowa tayi idonta kamar ba bud'e ba tace my really meyasa kayi nesa dani? bayan kasani saboda kai kawai nake zama nigeria,,,,shiru yayi nawasu lokuta baice komai ba,,,,,tashi tayi zaune tare da jan hannusa sukayi ciki,,,bayan sun shiga mazauni tayiwa kanta a qirjinsa,,,sannna ta lulbo yatsansa ta kafe shi da idonta masu narka da zuciyar munauwar ya manta da komai,,cikin sigar murya mai cike da karaya tace my really waya tab'a mun kai jikina nabani ba lafiya... gwaron numfashi yasaki tare da cewa qaddara Dharkan,,,,,qaddara my really? eh ita! wannan wace irrin qaddara ce haka da harza tayi sanadiyar zubda qwallar muradin raina?,,,,,tana tura harshenta akan qwayar idaniyarsa dan ganin ta tsaida malalar Ruwan dake mararin fitowa duk da cewa ana riritasu dan ganin basu baro lacirimal gland ba,,,,sannan tace can qasa maqoshinta my really stop cry pls!! bazan juraba ta qarashe cikin kuka. shafa idanuwanta yayi tareda magana cikin rishin kuka,,,,, jiya takasance *BAQAR RANA* da tajiyar da kunnuwana mummunan labarin da beyemun hallaciba,, kasancewar numfashina bai daina bugawa alokacin da saqon ke isa ga qwaqwalwata,,ranace da duk tazagayo wajibina ne nazubda hawaye!! domin zunubanta sunyi muni a tarihin rayuwata...! itace ranar da komai girman alkhairi yashigo mun baxan wunin mai farinciki ba....,,,, da kyar tace wannnan wane irrin labarine haka ,,,,da yajera tarin tsana da neman tarwatsewar tunaninka my really? kallonta yayi tare da cewa wai Aure xa'amun kuma ba dake ba khairat!!! dass! dass! dass!! xuciyar khairat ta buga ajere haqoran ta har had'uwa sukeyi dakyar tace my really dai,dai jijiyoyin dake aiko saqo suka aiko min?. cikin rashin kuzari yace nafiki jin maganar Dharkan. saidai batada mazauni agurbin zuciyata, domin nariga da namutu daniyar bautawa khairat,,,kallon sa tayi idonta jagaffff da qwallah tace my really kaine rayuwta, but bansan meyasa Qaddara zata bijiro da wannan maganar ba, kai naga baqaramin yarobane ka san meyadace dakai, domin ba namiji ba, ko macce ganganci ne ace annema mata miji.....Dharkan kiyi shiru jikina nabani kece u'war y'ay'na, kuma baxanyi dogon jikiri ba watannan mai shigewa shagalin auren mu zaifara. Duk da yanayi da take baihanata murmushi ba,,, martani yamaida tare da cewa yajikin naki? rikicin dake rayuwata ne yahana naji lafiyar jikin naki BAQAR RANAR Jiya,,,,,, cike da jan aji da shasheqar kuka tace naji sauqi,,, lumsa ido yayi tare da jawota jikinsa yarad'a akuunenta meye labari?? saida tawani marmara ido tace kaine labarina"" amma kuma,,,,,,,menene fad'a mun kinji... yau zuciyata cike take da tsoro! tsare ta yayi da ido tareda cewa don't worry Dharkan ba'abunda zai rabani dake domin kece duniyata ke kad'ai zuciyata tabawa soyyayar gaskiya,,,,murmushi tasaki mai sauti tace I LOVE YOU. kiss yabama gefen nonota da yawani murjewa cikin riga kamar danshi aka bugata. a fili taski wata y'ar tsuwa mai nuna Alamar jin dad'i,,, tare da cewa Ashagwab'e d'auke hannunka bana so? meyasa? yarad'a mata,, marata ke alamar ciwo! oh, kekam kamar mai sabon ciki kullum ciwoooo!! xumb'uro baki tayi tace hum sai inkai kamun cikin!! lah la, lah rufa mun asiri yaushe ma nadawo nigeria? to wakeda penis d'in yimun ciki bayankai,,,cike da so yace babu,,,,haka suka kasance cike da farantawa juna rai....har lokacin fitarsu hotel d'in yayi,,kowa yanufi gida cike da zaquwa da muradin zamansu tare...kan su isa bari muji wacece khairat ataqaice!!!? khairat Y'ace ga Alh. Sanusi d'an boko! mutum ne dayasan darajar biro da girmamashi, rayuwar turai da boko ita yazab'awa kansa,, shiyasa yayiwa kansa tsarin haihuwa d'aya jal,,,,,tunda aka haifi khairat yaje yayi vasectomy wanda atarihi ba afiye samun Namiji biyar da yayita from 1961 to yanxu ba,, but shi saboda son duniya da rashin yadda da tsufa yayi,,,,,shiyasa yabama khairat y'ancinta abunda taso mai kyau ne ko akasinsa shi zatayi, sam batasan wahalar duniya ba,, batasan kwab'a ko hantara ba, Abud'aya tasani shine duk abunda tagadama shine takeyi,,,,khairat kenan ataqaice...bayan isar mumauwar gida qwaqwalwarsa ta hargitse da fitina sakamakon toxali da idonsa sukayi........
COMMENT'S💯
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀4⃣
_Zainab Idree(makawa)ina qara baki haquri akan abunda yafaru jiya duk dacewa naso tsaida zance but allah beso ba kiyi haquri kuma naji dad'in hangen nesanki da yadda ki ka fahimce ni kaitsaye ngd_🌹
⬅
qwaqwalwarsa ta hargitse da fitina sakamakon tozali da idonsa sukay...! da kayan Abunci kala kala· wanda bako shakka tafiyar Abba ta zuwa ASAKO baijanye ba! cikin daqiqu yaji komai yadawo sabo sumul~ tamkar ma yanxu kalaman abbah ke amo akunnensa· A daddafe yashiga d'akinsa, ya zube kan katifa tare da sakin rishin kuka,,, jin kuka baimatar dashi baqinciki ko rage zugin da ke tafasa A zuciyarsa,, yasa shi bud'a powder cocain yana shaqawa tare da shan barasa A haukace,,,dan ganin ya rage quncin da keneman rabashi da Allah...haka dare mai mugun tsayi yafara shigewa,, wanda yakasance tsakanin bacci da farkawa ga munauwar,,, tun asubbah yafarka saidai kashhh! baya mai murna kasancewar sa me shaqar numfashi……kuma tabbas yau da besan muhimmacin sallah ba da ba abunda zaisa yasallaci Assubah,, but duk da haka baifita wajen massalaci ba ad'akin yagabatar da ita gaggauce,,,,Abba beyi mamakin rashin ganin munauwar masallaci ba dan yasan rikicin da akeyk, amma yana da yaqinin yasallaci assubah cox mutum ne mai son Addini, bai bari gumakan zamani sukayi tasiri akanshi ba,,,,dan yau dayawa masu kud'i sun manta Allah,,, bazaka tabbatar da hakanba se kaziyarci masallacin Assuba..kaxiyarci inda ake hada hadar kud'i kagane cewa da gaske kud'i ana bauta masu! ba mazan ba bamatan ba,,,yau aure yakoma na naira,,,kud'i sunfi mutunci girma ga rayuwar d'an adam awanan zamanin in kanadasu ko u'warka batada'ga ma yatsa,,,,da wannan qaramin tunanin yafitooo yashiga gidansa tsittt! da yake mutum ne dayasan haqqin d'an adam da sanin darajar aure,, bai bin kan qyalar da matarsa ke masa ba,,,kansa tsaye yatosa kansa d'akin tare da cewa amman munauwar ni zantafi,,,,wani kallo ta watsa mai tare da cewa ALLAH ya wargaza mummunan nufinka akan d'anah.... baibi kanta ba yaqara jaddada ma kansa wannan itace ranar haqurin da kowanne ango da amarya Ake jaddada masu suyi da juna,,,,a fili kuma yace sai nadawoooo! sam bahaka taso yafito bakinsa ba, but duk da haka tabishi da fad'ar ta Allah bataka ba· cike da saqar Abubuwa aransa yafito kabiru da hanxari yace ranka shi dad'e bissimillah tare da bud'a murfin mota. bayan yayi Addu'a yashiga,, kabiru yarufe suka tafi。 titi suka hau d'od'ar da zummar barin birnin shehu zuwa Zamfara· bayan wani dogon Zama da suka shafe suna tafiya batare da tsayawa ko inaba sun Iso ASAKO lafiya! se dai fuskar shi ta canxa ganin har yanxu bawani sauyi, a fili ya furta ko yaushe ne talakka zaiji dad'i aqasar nan? kana yayi shiru,,,yana zurawa garin idonsa, ya firgita da suka shiga tsagwaron qauyen, da yaga yanda mata suka kewaye rijiya suna d'ebo ruwa, wasu sun d'ebo suna kantafiya! ko waccen su takalmen leda ne a qafarta,,,wasu kuma dandazo na gefe suna surfe da manyan tab'are· da Abubuwan Al'ajabi tab aransa har ya isa garkar mlm sale...anan kuma yaqara shayar da kansa mamaki ganin yadda al'ummah sukayi dandazo suna kallon mota, yab'ata mintuna daga bisani yafito cike da jimamin Rayuwa,, ganin cewa ba wanda yafi wani gurin Allah se wanda yafi tsoron sa,,amma cikin adalcinsa kowa da yadda aka tsara zai zauna A gidan duniya,,,yana fitowa sowar mutane ta kaure ana kirari shiko yana baxamusu naira!kuma domin Allah yake bayarwa badan kirari ba. mlm sale da hanxari yafito da yaga Amininsa DIKKO har qwallar farinciki yasako,,,Abban munauwar bai dubi shigar sale da irrin wata shu'umar daud'a da wani tattarewa da kayan sukayiba hannu ya ware suka rungume juna irrin na yaushe rabo. sannan sukayi ciki annan suka fara fira kamar yadda suka saba in sunhad'e……sale yarasa me zebawa abban munauwar domin ba komai gidan se fura da har tafara y'ay'an tsami,,can kuma yace bansan zakazo ba da nasa jalee tamuku daka mai tsamice kad'ai a gidan,,,,murmushi yayi tare da cewa bakomai d'auko mun nasha ai gidanmu nazoooo!! haka ya miqe tangal tangal kamar iska zata ture shi yafad'i saboda tsabar taulauci da wahalar qauye! yayi cikin wata bukka da aka zagaye da kara……tunda ya miqe abban munauwar ke jajantawa zuciyarsa dubi sale kamar wanda ya shekara sittin inda yaqara tirr da neman tsari ga talauci,,yana haka sega sale yafito da qwaryar fura a hannunsa, zuciyarsa cike da d'ar akan wannnan walaqanci yabama mutum mai daraja wannan furar, sai dai ga mamakin sale tas Abban munauwar yashanye,,sannan suka gaisa yaqara yiwa sale ta'aziyar matartsa da tambayar ina jaleelah? karb'a gaisuwar yayi tare da cewa jalee na daji amma da anyi sallar azahar zata dawo...gwaron numfashi yasaki tare da cewa kardai bata zuwa makaranata sale,,,,? ah, tana zuwa kasan mu se andawo daji ake shiga boko da dare ayi arbi! dariya yayi tare da cewa madallah,,,haka suka kasance daga bisani yamiqa qoqon bararsa ga mlm sale akan ya aura ma d'ansa munauwar jalee...mlm sale seda ya soke kai cikin zuciyar sa yace tab ana dara ga dare yayi....domin yazo da Abunda baisan zaifaru ba! dan da yasan hakan bazaice da dauda yaturo magabata ba....... A fili kuma yace jibi ne zanbada auren jalee amma ko gaba da gabanta inshine alkhairi allah yasanya ayi damu,,cikin zaquwa yace Ameen nagode da karamci sale, ina roqon Allah yabar zumuncin mu...suna haka sega jalee kara masu tarin yawa bisa kanta se famar haki take, ba takalme a qafarta zani daban, riga daban, an sha Adon kwalli da janbaki ba ko Alamar kwantawar nono a qirjinta...salllama tayi cikin muryar su ta y'an 14 sannan ta Ajiye karan tare da gaishe su cikin d'aa da kamun kai.....sannan ta miqe kud'i yazaro yabata amma fafur taqi amsa dole yabawa mlm· sale yace abata。 haka dai har abban munauwar yakoma‘’ bayan magarib sale yakirata dan shaida mata,, gaban se rasss yake ganin yadda jalee ta shaqu da dauda·…… ko yazata d'au zancen?
💯
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀5⃣
yadda jalee ta shaqu da dauda yazata d'au zancen? saida yayi gyaran murya wanda haryasa jalee cewa sannu papa!! ya karb'a da yauwa jalee,,,, dama ina son kiyimun Alfarma ki auri d'ana d'an Aminina da banida tamkarshi Aduniya,wanda nayi imani in yabuqaci raina zanciro nabashi kafun qyaftawar ido da rufewarsu,,,, nadad'e da son Dikko yanemi Alfarmata, amma beyiba! se a wannan karon! duk kunya da kawar da kai irrin ta ba fullacen qauye, be hana jalee cewa papa dauda fah? shiru yayi mai cike da nazari· sannan yace karkidamu zanmasa bayani da kaina, A firgice tace A'ah papa!! kayi haquri ni baxan iya rayuwa ba dauda ba, shine na sallamama rayuwata ga baki d'aya,,,,,wasu zaratan hawaye suka kub'uce ma sale,, cikin muryar kuka yace shikenan jalee ki auri wanda kikeso! amma bantab'a tsammanin zab'inki yafinawa ba?, sam namanta da zakibani kunya,, da banyanke hukuncin cewa nabaki munauwar ba! jalee ki auri dauda sai dai Alfarma d'aya kibari har bayan raina... rasss! rasss! rassss gaban jalee ke bugawa jikinta har b'ari yake ta durqusa tana sharar masa hawaye,,,, Akunnuwanta kalaman hajjo mahaifiyarta ne ke kurma ihuuuu tamkar yanxu take yinsu,,,jalee bakida kowa se papanki, karkiyi abunda zaisashi kuka, dukkk rintsin rayuwa kikasance mai kyautawa gareshi, yanxu da biyayyata da tashi duk shi xakiyiwa,,,,A fili kuma cikin rishin kuka take cewa papa kayi shiru,, baxan so nakasance mai sab'a ma umurninka ba, zan Auri wanda kakeso na Aura papa!!! murmushi yayi tare da cewa ngd jalee da biyayyar ki gareni allah ka amunce Rayuwa tazamo kuyangar farinciki agareki yana neman share ruwan hawayen dake wanke fuskarta……ganin basuda niyar tsayawa ne yace jalee ki tsaida kukanki mana,, da kyar ta d'ago tace dan Allah papa, karka tsaida zubar hawayena yanxu, dama wasu darairai masu zuwa nan gaba,,zaiyi magana ta katseshi da cewa ka amunce da buqatata banaso narayu ina mai tsallake umurnin ka papana!! tausayin jalee ya kamashi sosai ya sadda kai qasa tare da cewa shikenan jalee je Allah kayimiki Albarka. tunda tasamu shiga d'akin tasaki wani axababben kuka tare da sa tsummah ta toshe bakinta dan kar papa yajiyo sautin kukan ta,,,,haka har magriba ta doso jalee batada labari gashi yau ta kasance ranar farinciki ga mutanen qauyen,, coxxx ko wacce ranar lahadi bayan anci kasuwa antashi sukan had'a dandalin masoya kowa yayi kirari da watsin kud'i ga A bun begentashi,,,,dandali yacika da y'anmata ansha Ado kalar na mutan karkara,,sai dai dauda gani yake kamar ba wanda yaxooo saboda tauraruwar shi bata riga ta faso ba,,,,hakan yake fita yana zagaya filin tare da sakin habaicin haryanxu ba macce adandalin har aka kusa tashi ba jalee, da azamarsa yafice baizame ko inaba se garkar su jalee!habun gidan mlm shehu yasama tare da damqa masa naira biyar yakira masa jalee...ba b'ata lokaci yafito tare da cewa ga tanan xuwa...idanunta duk da darene zaka tabbatar Apolo yakamata saboda jah da kumbur,,i while bashibane Azabar kukan da yakasa tsayuwa ne "A" idonta Adaddafe ta qaraso gurin da suke fira da hasken ranta,,,,yau ba sallamah ta isa gareshi tare da sadda kai qasa,,,,cike da nuna damuwa yace jalee bakida lafiya ne? kai ta girgiza Alamar a'a! jalee to me kefaruwa ne haka? cikin disassar murya tace da farko zanso kayi imani da qaddara dauda...qaddara nayi imani da itah jalee mai kyau da kuma akasinta. duk wadda taxo mun godiyar Allah nakeyi domin idan nayi kuka akan qaddarata na tabbatar itama kuka zatayi dani jalee!! Idonta ta d'ago ta had'a dana dauda A Firgici yace Innalillahi wa innah ilahim rajiu'n me yasamu idonki jalee? maidasu tayi qasa tace Anrabani dakai dauda, hum anyanke alaqata dakai, an haramta min mallakarka dauda,,,,cikin tsawa da kaurin murya tare da gangarowar qwallah mai ratar tsayi yace ya isa haka jalee,,, domin inada yaqinin ko qaddara bazata yimun wannan gangancin ba bare d'an Adam..........
ADO DA KWALLIYA GODIYA TA MUSAMMAN DA COMMENTS INKU DUK DA CEWA YANAXU LABARIN ZAI FARA🖊
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀6⃣
_uhum uhum eham SAMARIN SHAHO tun yau na had'a kayana dan Abun yaxo da qafiya, musamman azamanin nan samarin shaho kawai kema mata reto azuciya ina tare da ke besty🥂_
GODIYA MAI QIMA GA
MAMAN NANA
UMMU HAYDAR
KUNA DABAN NE AZUCIYATA INA TARE DAKU💯🌹
⬅
tare da gangarowar qwallah mai ratar tsayi yace ya isa haka jalee,,,ya isah!! domin inada yaqinin ko qaddara baza tyimun wannan gangancin ba, bare d'an Adam........d'agowa tayi tare da cewa kar ka zauce kashiga hurumin Allah sbd,,,imin shiru jalee!, rabani dake yafi rabani da duniya zafi,,,bazan tab'a bawa wani d'a NAMIJI dama yashigo gonata ba, muddin Ina shaqar iskar ubangijina,, abu d'aya nakeson ji wanene kika ba lasisin da har zaizo yace yana son ki,,,,,?cikin kuka tace nima bansan shi ba dauda! qaraya kikeyi jalee! idan bakisan shiba tayaya kikasan za'a aura makishi? jalee kar kimaidani bagidaje dan kinga na haukace cikin qaunarki,,,,,cikin kuka ta durqusa tare da cewa dauda baxan ma qaryaba,,gaskiya nake gayamaka,,bansan waye shi ba? nadai san waye mahaifin shi! to waye shi? cikin sarqewar muraya tace baba Dikko,,,,,durqusuwa yayi yana makahon kuka numfashin su najiyo na juna yace kuma kin amunce jalee? sai dai ta d'an zura idon shi anata tace bani da zab'i da yawuce amuncewa amma kuma nasani zuciyata na tare da dauda, bagaskiya bane jalee? to meyasa kake qoqarin qaryatani dauda,,,,? ko dan kaga zuciyata ta wahaltu da sonka? a'a jalee sai dai dan na yaudarin kaina da koyawa zuciyata sonki wanda nakeji u'wa ko u'ba bazanji kiransuba,, alokacin da bakunan su ke kuskuren rabani dake!! dauda hakan yana nufin bakayarda da son da nakema ba? tayaya zan yarda? idan har sona kike ba kya iya rayuwa sedani ga shawara? asanyaye tace inajinka dauda...kan zancen yagirma mu tsere can wata duniyar muyi aure da bawa soyayyar mu y'anci...kuka da idonta da bakinta atare suka bud'e tace kasan kuwa me kakecewa dauda? eh! nasani,,,,bashawara bace dauda,,,! saboda burin rayuwar mu musadukar da iyayenmu? mu manta hallacin su? tabbas wannan zancen ya tabbatar mun kin yaudareni jalee tunda harkinaji zaki iya rayuwa ba dauda kin maidani kifi rijiya wanda besan komai ba sai dai zafi miki kyau kece dani kud'i su kamantar da ke soyayyata!!! komai yafito bakinka fad'a dauda kanada gaskiya kuma zan ma u'zuri kasancewarta BAQAR RANA Agaremu,,,sai dai duk dahaka bazantab'a binkaba,, domin kafun na had'u da soyayyarka ta iyayena nafara samu hum !sune tun banxoba suke d'aukin zuwana. bayan nazo duniya ina girma soyayyata na girma Azukatansu,, amma saboda na rayu zan manta soyayyar su dauda,,,,,?? baki abud'e yake kallonta da kyar yace da gaskene mata hallayyar ku d'aya kun qware wurin kuka da yaudara tare da tabbatar ma NAMIJI bazaku rayuba in har kuka rasashi,,,, ko yanxu baxan baxan rayu ba dauda,,, zaki rayu jalee,,, tabbas zaki rayu amma ni zamutu,, domin kece duniyata。 da ke natsara zaman aurena,,,a gaggauce tace muyi haquri qaddara ta riga fatanmu,,,, tare da zura qafarta cikin gida,,,cikin jigataccen kuka yace jalee kin tafi kenan? a'a dauda zuciyata na harbawane saboda kai bazan tafi nabarka ba,,,gangar jikinace da biyayya zasu barka,,,,wayyo uhm hmm humm uhmm to meyasa ruhina yajira wannan *BAQAR RANA*? abunda nake tambayar nawa ruhin kenan! ta shige da gudu tana kuka yayinda dauda ke ganin duniya tamasa fili fayau,, ji yake tamkar yaqoneta kowa ya huta da jiran mutuwarsa! wadda inkajirata tabbas zaka had'u da munanan ranaku masu Azababben duhu da BAQI,,,,haka dai rayuwar qunci da ciwon so sukazauna Azukatan masoyan! A gefen abban munauwar kuma yakoma gidansa cikin qoshin lafiya sai dai hankalinsa yad'an soma tashi ganin ga baki d'aya munauwar ya burkice kamar sabuwar hauka,,,kuka yake mai tsuma rai da jajintawa Al'amarin zuci,,,cikin murya me sanyi yace munauwar dan na nuna ikonane akan ka kake wannan hauka? d'agowa yayi tare da cewa Abba qwaqwalwata ce ke neman hautsinewa da jini muddin karabani da khairat,,,,bazan iya rayuwar Aure da jaleelah ba,, ina roqo kajanye Abbah,,, cikin fushi da quna rai yace na janye munauwar! amma kasani banda wanda zai maye gurbinka ya Auri jaleelah!!! sai dai inada hurumin ajiye macce hud'u kasancewata d'a NAMIJI,,,,Ammah da ke kwance tana kallon su seda takai tsaye……
comments🖊
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀7⃣
_sadaukarwa ga tawa har gaban abada mrs jameela musa (meelat)🌹_
⬅
Ammah dake kwance tana kallon su seda takai tsaye......cikin in ina tace me kake nufi da zamewarka NAMIJI? cikin qunar rai yace rabi ki tsaya matsayinki,,,duk abunda kikeyi ina sane! bawai tsoro ko shakka yake sa ina d'aga maki qafa b!a a'ah saidan sanin darajar aure da yafiya,,,, zatayi magana karo nabiyu ya katseta da cewa shiru!! kuma wlh kika bud'e baki kika mun magana bakin Auren ki sha sha!!,,munauwar ya d'imautu ganin yadda b'acin rai yayi dandanxo Afuskokin iyayensa,, wanda yatabbata duk wanda yafurta wani abu haqiqa ba alhairi bane, cikin muryar mai nauyin kuka yace Abba ka gafarceni, kagafarceni abbana! daga bisqni yakai kallon sa ga ammah tare da fad'ar kuyi haquri banason nazo ajerin y'ay'an dake neman jefa iyayen su cikin nadama! bazan so ba,,, amma dan Allah Abba ka kalli kukana kaji,,,,, yaqara narkewa da kuka mai sauti ,,,,kallon munauwar Abba yayi tare da cewa banida cancanta da zakakira ni Abba munauwar! sam matsayina bai kaiba, tunda har kana iya shaidawa duniya zab'in zuciyarka yafi nawa,,,kana iya kallon idona kace najanye zab'ina munauwar a hakan zanyarda cewa nima ubane? cikin rishin kuka yace dan Allah karkazargeni cikin butltaccin y'ay'a Abba, kazargi qaddarata akan bason zuciyata bane, rubutu ne dabanida ikon gogewa se hakan tafaru ba danni ba se dan ubangijin da bebawa kowa damar zana qaddarar shi ba,,,,, nisa yayi tare da cewa shikenan munauwar! inajin kunya da nauyi ace nayi abu domin Allah na kasa yi duk kuwa girman alfarmar!!! rungume abba yayi tare da cewa na maka alqawari ko zanmutu na amunce da Auren jaleelah dan ganin na kyautama rayuwarka! bazaka mutu ba munauwar! amma kar kayaudari kanka idan ba dan Allah zaka aureta ba, takasance marainiya kuma nazab'o maka itane saboda ka jib'anci Al'amarinta idan cutarta zakayi na dakatar dakai kuma bazan tuhumeka ba,,zansan abunyi!!a daqiqa biyu yagano maganar abbah nakama da harshen damo,,,, hakan yabashi damar dasa magana akan barshen sa,,mai taken idan auren biyayya zai kasance Alkhairi na maka alqawari zanrayu da jaleelah har Abada,,kuka yasub'uce wa Abba tare da cewa nagode munauwar Allah yayima albarka duniya kagama mun komai ngd,,amma kam qiris take jira tafashe bala'i yakai bala'i cikin ranta,, wanda takeji tayi yawoo tsirara ba bakin komai bane dan ganin bata had'a xuri'a da zuri'ar da kakaf A baqin littafi sukazo duniya ba,,,haka tashiga d'akinta tafara zariya kamar sabon kamu se sambatun yin gayyah take ga mijinta Dikko. munauwar Kuwa Abba na haurawa sama yafad'a d'akin mahaifiyarsa,, cikin kaushi tace munauwar kaje da yawuna kace bazaka aureta ba, domin banaji zan cigaba da numfashi idan har jaleelah zatakasance u'war jikokina,,,,murmushin mugunta yayi tare da cewa na Amunce da auren jaleelah ne domin na d'and'ana masa azabar qunci,,amma bazan tab'a tarayya da itah amatsayin mataba, baxan tab'a sassauta mata ba, zata d'and'ani azaba mai rad'ad'i tunda har tayi kuskuren furta kalmar so ga mijin khairat! ,,, da kyau munauwar yanxu na amunce jinina na yawo a sassan jikinka!!! da wannan yafito yasamu Ahamad Kwance yana ta saqa zancen zuciya! bayansa yabi tare da shaida masa zai auri jaleelah!! ras gaban Ahamad yafad'i tare da miqewa zaune yace da gaske ka amunc? hum na amunce sai dai badan komai ba se dan yazama izina ga iyaye,,,,,seda yaqare masa kallo yace munauwar kaji tsoron allah, karkayi tinqaho da kasancewar ka d'a namiji ka cutar da baiwar Allah wadda sam batada laifi, domin bawadda take auren mijin wata, haka ba mai auren matar wani munauwar, ka d'auki auren jaleelah zab'in Allah se kaga komai ya wuce cikin salama!!! tsaki yajah mai sauti tare da cewa naji amma idan har zan sassauta ra'ayina Abu d'ayane zanje na gargad'eta ta gayawa Abbah batasona,,,nisa yayi tare da cewa hanya mafi sauqi kenan muyi hakan,,,,bayan kwana biyu da maganar munauwar ne sanye cikin fararen kaya hannuwan sa sanye cikin aljihu!... gaban wani qaton gida irrin nab'arayin govnatiy yajingina bayansa da motar da yazo da itah,,,khairat ce ketakowa ahankali tana yafqi kamar qiris take jira ta karye Batanbaya wannan gidan sune tafito,, da fara'arsa yace wow! Dharkan kin fahad'u,,murmushi tasaki tare da kawar da zancen dacewa tabbb kafa rame dayawa,, hum ba dole ba wannan tsinanniyar tashigo mun A tsakiyar rana! ai kuwa tsinannah, ya kuka kwashe da mahaifin naka,,? na amunce! what?! eh sosai but dan kawai nagana masa azabar da yagana muna! my really ni miye matsayin aurena? aure ba gudu ba ja dabaya,,,,mahaifina bazai amunce nayi auren sirriba dan kafikowa sanin yatara maqudan kud'in da zanyi shagalin aurena,,,,Abbaiyane xamuyi khairat,, sai dai akwai lokaci,,,,,cikin shagwab'a tace gaskiya bazan iya dogon jiraba yakamata ace nafara jin penis d'inka na yawo a cikin jikina,, humm idan wannan ne bakida matsala zamuyi zaman dadiro kafun lokacin yazoooo,,,,yeeeh shawara mai kyau! haka dai rayuwa tasoma farawa lokaci yad'an tafi wanda yatara abubuwa masu yawa da rikici ga masoya ,takasance lahadi ranar da munauwar yashirya zuwa gidan su jalee Allah ya amunce sun d'au hanya zuwa garin bayan wasu awowi sun sauka garin lafiya! papan jalee ne yakasance mai tarbon baqi,, sai dai ga mamakin Ahamad bawanda yaxo gurin motar tasalima qyamarsu ake,,da qanan maganganu akan cewa ga wanda ya qwacewa dauda mata!!! Bayan yabasu gurin zama yashiga dan kiran jalee,,, s! bata wani tsayawa ba tafito se dai zuciyar jalle kamar ta b'allo tafito waje dan baqin ciki da sallama tashigo cikin murya mai sanyi da tsinka gashin qwaqwalwa,, Ahamad na zaune yayinda munauwar sam bega gurin zama ba,,,ba takalle su bare ta tantance waye angon? cikin fara'a ahamad,yace wa alakis salam jalee barka da yau! alhmdullah ya hanya ta fad'a a taqaice? munauwar ne yajefo magana da cewa ba Abunda yakawo mu ba kenan!!!
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀8⃣
_sadaukarwa ga tawa har gaban abada mrs jameela musa (meelat)🌹_
⬅
munauwar ne yajefo magana da fad'ar ba Abunda yakawo muba kenan......!!! d'agowa tayi suka had'a idoooo dakansa ya tabbatar mata saqon dataji ba tantanma shi yafito bakinsa! sannan ya d'ora da cewa kiyiwa kanki hisabi tun wuri kice bakyasona,, domin macce d'aya nake so khairat! kuma koda kakkaf duniya ba mata bazan tab'a tarayya dake amatsayin mata ba,, jin tayi shiru ya d'ora da cewa idan kud'i kikeso ko kuma zaman birni duk zaki samu! amma da sharad'i kije kigayawa manannen ubanki,, da yanace yaziga Abbana akan yabani ke to yayi kuskure yadda yazooo a baqin littafi haka zaikoma,,, wani razanannen d'aci ne ya bugi maqwagoronta amma ta had'iye ba alamar tsoro ta d'ago tace harshen ka ya tabbatar min da kai wanene!!! babu buqatar baka amsa domin yin hakan gidadanci ne,,, sai dai qaramin saqona gareka kakoma makaranta domin sanin miye iyaye? zancen mahaifina yazooo abaqin littafi shishhigi ne kakewa lamarin ubangiji, domin sanin wanda yazooo abaqin littafi se alahira domin kowa jiran tsammani yakeyi anan sannan ba abun mamaki bane kasancewarka sahon farko a cikinsa! batajira mai zaice ba tayi gaba... ran munauwar yakai qololuwar b'aci kasancewar babu mahalukin da yatab'a dasa magana mai kaifin xafi yabarshi da ita se wannan yarinyar,,,hakan yawa Ahamad d'ad'i domin inbaka yankewa allah ragoba ka yanke ma boka sai dai baice komai ba azahiri domin ko shiru magana ce! munauwar huru iskar bakinsa yayi mai gumin zafi, yace shine mafi girman kuskure a gareki! yana haka sega papa sale da azama ya duqa yace papa dan Allah kar kuyiwa jaleelah dole tunda bata sona zan haqura!! banason muzama sanadiyar wargajewar amintarku dan ta tabbatar min da wanda take so! yaqarashe maganar tamkar zaiyi kuka,,mlm sale seda ya kalato yawun bakinsa yace kayi haquri munawaur d'an yaune ka haifeshi amma baka haifi halinsaba insaha Allahu bazan bata dama ta kunyatani ba se dai ni na kunyatata,,a ladabce yace papa kayimata a hankali da sannu zatagano ina kuka dosa,, kasan tanada quruciya kuma ko baquruciyar hankalin macce baya zuwa d'aya da NAMIJI,, Ahamad da ke jin zancen munauwar ji yake kamar yace da mlm sale tarko ne Munauwar ke had'awa,, amma babu wannan damar! haka yazuba ido munauwar na ta tsara zancen qarya da kyautar kud'i ga mlm sale,,,mlm, baiso amsa ba amma munauwar yakafe da cewa komai yaba mlm kansa yabawa da haka yatafi,,,,, mlm sale jira kawai yake sutafi ya shiga gida,,,,koda yaje ta kifa kanta da guiwa tana shigaggen kuka yace jalee wannan Abun zaki saka mun dashi? wannan shine sakamako na gareki? ashe bakida burin da yawuce ki kunyata ni? bakinta har tsuma yake tace papah me nayi maka wanda bakaso? cikin zafin rai da rawar murya yace kinyi dai dai? tunda har kina iya tambayata mekika mun? matsanancin twari yasarqe shi batar da barin zance nagaba fitowa kan harshen saba ,,har jikinta ke b'ari garin tallafa mashi amma yadakatar da ita da cewa karki matso min nan jalee! bana ko san ganinki! bantab'a tsammanin zaki watsan qasa a ido kici mutuncin yaronan ba,,,,twari ya koma qwace masa! cikin razanannen kuka tace papa kuma ka amunce na aikata hakan? bayan nayi imani zaka iya shaidata akan abunda zanyj da wanda banyi ba? immin shiru jalee bana son jin komai daga gareki sai dai gaf nake da barmaki duniyar se ki rayu da wanda kikeson rayuwar! d'inkewa tayi da kuka a rikice tace kar kace haka papa!! hankalina da qwaqwalwata bazasu juri rashinka ba,,kaine u'wata kaine mai kallon kuka da mararin share qwallata a duk sanda ta kwaranyo,,, kuma ina maka rantsuwa ban cimasa mutunciba,,tasalima shine,,,,,kiyimin shiru nasan kina kukane badan komai ba,, se dan rabuwar ki da dauda! kuma kisa a ranki ko baki auri munauwar ba bazaki auri dauda ba,,,in kuma kika nace se shi zan dauwamma ina nadamar haihuwar ki,, kuka mai cike da bud'ewar baki ya d'inke ga ilahirin fuskarta. tana kara hannu abakin tana shashsheka tana cewa papa ka furta alkhairi akaina, karka makance kayanke mun hukuncin da Allah zai tambayeka! kuma bance bazan Auri munauwar ba na maka Alqawari idan har zakayi farinciki ko zai yanka naman jikina zan rayu dashi! yaji tausayin ta amma yadake da cewa Allah yasa har aranki kike zancen jalee! wata qwallah mai zafi da rad'ad'i ta balbalo masa yace karkiga kamar nashigo ina qoqarin miki dole, a'a sai dan Dikko yakai amini agareni, mutum ne da in ana numfashi akabari zantuna shi,,ya taimake ni taimakon da banida A bun saka mashi,,,,jalee bayan hajjo ba wanda nakeso fiye da dikko! mutum ne mai taimakona baya qyamata, shine yabani gona da gidan danake zaune...shine yayimun aure kuma shi yasaya min ragon sunanki jalee! sunan ki dakanshi yasanya,, mutum ne me qarfafa guiwata akan nayi haquri talauci bautane,,,,jaleee basai nagaya maki ba dukkkk abunda na tab'a lalacewa yake shine mutumin da baiyagajiya da bani yana lalacewa! jalee wannan yacancanci neman Abunda nakeda yakasa samu agurina? jalee ko baya numfashi yacancanci nakasa yiwa zuri'arsa alfarma? hannunsa ta riqe qam tace yacancanci kabashi sadakar rayuwa in yana nema bare abunda rayuwar ta mallaka! papa kasa aurena koda gobe ne niko zanzo sahun farko cikin y'ay'a masu biyayya rungumeta yayi yana shafar gashin kanta tare da cewa bazakiyi nadama ba,,jijkina nabani rayuwa zatazamo kuyangar farinciki a gareki,,,ina alfahari dake jalee na yadda kece suturata ta duniya haka suka kasance!!! gefen munauwar kuma har fatar kansa ke motsi,,, gudu yake irrn na Allah kasa mota ta watsar damu duk a mutu kowa ya huta,,yayinda ahamad yagama sadaukarwa tafiyar ajali suka d'auko......
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀9⃣
_inda kikaso yasauka nan zai zauna maman abban K.d domin wannan nakine ke kad'ai kiyi yanda kikeso kuma masoya ba sai nace komai ba sanin kankune ana tare💯🌹_
⬅
Ahamad yagama sadaukarwa tafiyar Ajali suka d'auko... Sai dai tausayin Alllah da amuncewarsa sun sauke su gida lafiya,,,bayan shigarsu ne da mintuna talatin munauwar ya kafa kwalbar barasa a bakinsa, wadda yakeji ita kad'ai zata mantardashi quncin da mutuniyar dajin nan takafa masa! sha yake ba misali yayinda Ahamad yakasa hanashi,, domin duniya yana tsanar mutumin da bayajin kunyar Allah,, ji yake kamar ya furta cewa yana son jaleelah badan komai ba se dan tsiratar da ita ga khaidin munauwar,,! amma inah baya da ikon wannan, daga qarshe ma barin d'akin yayi kasancewar sanbatun da munauwar keyi sunyi muni, ace cikakken muslmi na iya furtawa domin hakan kana jayayya da hukuncin da Allah ya zartar ma ne! haka lokaci ya d'an jah can wuraren la'asar barasa tasake shi ba laifi,,yayi wanka yasa kaya masu sauqin nauyi tare da baje ma jikinsa tulale kala biyu Habana and Revelation. ya kuma d'auki alawar Buttermint yasaka Abikinsa dan yakashe sinadarin tsamin giyar da yasha,, cox ba shakka abbah yadawo wannan lokacin!! cikin canzawar yanayi da sakin fuska yafitooo amma qasan zuciyarsa ba komai sai d'aci,,, kansa tsaye ya ratsa parlon, tare da taka matakalar benen da zaisada shi da d'akin Abban,, zaune yake yana karatun jaradiar AMINIYA da tawallafa adaren jiya,,jin takon yaronshi yasanya shi ajewa tare da fad'ad'a murmushin sa , sannan ya d'ora da cewa yanxu nake ayyanaku araina! kun sauka lfy! sadda kai yayi qasa cike da ladabi yace se godiyar Allah,, papan ma yace a gaida ka sosai! thom munauwar ngd da biyayyah! murmushi yayi tare da miqewa,,,kansa tsaye yasake fad'awa d'akin mahaifiyarsa kwance take ta zurawa silin idoo da alama akwai Abunda take saqawa,, zumbur ta miqe tare da cewa yaushe kadawooo? A raunane yace tun d'azuuuu! kamar zaiyi kuka yaqara da cewa yarinyar nan taci muntuncina, taqara sa na tsaneta wlhil azimm ammah ji nake wa'azi ko kalamai bazasuyi tasiri akan sharri na garetaba,, da kyau munauwar tafad'a tana dariya sannan yad'ora dacewa ammah to yaya zanyi da khairat? na rasa ina zansa raina naji sanyi... wani d'an murmushi tayi tare da cewa Aure biyu zakayi rana d'aya nagama yanke hukunci ahalina zasu nema ma auren muradin ranka! to kina gani Abba zai yarda kuwa,,,? son zuciyarsa yayi haka muma son zuciyar mu mukeyi! kuma Adaren zaka bar qasar nan da matarka! inyaso ita mayyar yarinyar taci kanta ko kuma wanda ya auro ta yasauke mata nauyi,,,, murmushin mugunta yasaki tare da cewa in muka mata haka taci bulus kenan ammah!! zan rayu da itah na wata biyu tareda gana mata azabar da ko sunan NAMIJI taji se tafirgita bare har tayi tunanin kwana bayansa se na quntata mata fiye da d'aukar hankali, se nasa duniya ta tsaneta ana mata tofin Alah tsine daga qarshe na sallamama duniya itah,,,yayi kyau munauwar haka nakeso jinina yakasance tunda na tasoo bana son talakah na tsaneshi amma awayi gari wai jinina zai had'u da talakah! miqewa yayi tare da fita wajen gidan yana shan iska..Ahamad na shigowa ya d'auke fuska amma saboda tsabar miskilanci na munauwar bai tambayi daliliba? Ahamad dan kanshi yagaji yace kace kana nemana,,,seda yajah lokaci sannan yace hakane but nafasa! kallon sa yayi ido cikin ido yace munauwar meyasa ka canxa lokaci d'aya? meyasa kake bari shaid'an na kururuwa "A" ruhinka, munauwar yakamata ka nutsu... ni banga me khairat tafi jaleelah dashiba! "A" hargitse yace karka soma Ahamad ,,bana shayin keta haddin kowaye idan ya tab'a mun zuciya amma saboda kaci mutuncina xaka had'a matata! da wadda jaka tafita qima A idona domin wlh gwara nadinga bin jaka da nayi... A haukace Ahamad yace kai kam qaddarar ka ba mai kyau bace munauwar,, inama ana ba wani dama yacanxa qaddarar wani wlh da nacanxa taka munauwar,, qiyayyah ba hauka bace!,, Ahamad' kace haka domin ba kasan komai ba akan sha'anin "SO" ni nasan "SO" domin zan iya kisan wanda yanemi rabani da khairat... amma ita baxan bata mutuwa me sauqi Ba zan wulaqanta ta tunda har tashigo zuciyata! tabbas duniya makaranta munauwar kashirya zuwan nadama maras Amfani kasa aranka *BAQAR RANA* Zata riske ka Alokacin da baka tsammani zai fi kyau ka Ajiye mummunan ra'ayinka da biyewa hud'ubar shaid'an la'ananne yafice Abunsa......
kuyi haquri da yawa zamuji haushin munauwar saqo nake son isarwa ga iyaye da kuma bijararrun yara kowa nada nasa laifin afuwan👍🏻
maman nana💋
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀1⃣0⃣
_tunawa dake wajibi nane ko dakuwa zamanina ya wuce! maman nana godiya mai qima wannan page kyauta ce gareki💋_
⬅
Zaifi kyau ka Ajiye mummunan ra'ayinka da biyeyewa hud'ubar shaid'an la'ananne yafuce Abunsa...qwafa munauwar yayi yana ta huru gumin zafi da ga bakinsa,, Zuciyarsa kuma se Ayyana jaleelah da fasalinta take sam bata da tsarin da yakeso! Afili yace wannan ba qaddara tabace son zuciyane kawai irrin na mahaifina! bashiri qwallah ta sub'uce masa yace wai meyasa na yaudari kaina na Amunce da zance Abba? me yasa wai? menene yaban tsoro na yarda da kunyata cikin jama'a? Anya zanga wannan *BAQAR RANA* mai cike da tarin qunci? me yasa Qaddarar aurena tazo da kiwoon qauye wanda ni ko banyadda matatabace d'umbin jama'a zasu shaida cewa matatace! tamkar mahaukaci haka yake zancen...Ahamad kuwa tafe yake cike da tarin tambayoyi yana tambayar kansa meyasa iyaye basu qyale y'ay'a da zab'insu duba da dayawa maimakon zumunci abun juyawa yake izuwa qiyayya! sannan kashi tamani da tara matan ne masu wahala gaskiya yakamata iyaye su waiwayi zamani da yanayin kafiya irrin ta yaron zamani! a d'aya b'angaren kuma cewa yake gaskiya y'ay'a butlallaline tunda harsuke manta ni'imar iyaye da dandazoon soyayyarsu suji har akwai alfarmar da zasu nema suqi samu Azahiri yayiwa kansa tambayar da ba ansa wane irrin zamanine wannan? wanda shaid'an kawai ke kad'a gangarsa ana taka rawa, wani Abun haushi ba mazan ba ba matanba! amma kuma idan akayi cikakken nazari laifin namazan yafi yawa! duk da ko mata ba'abarsu Abayah ba! irre irren wannan tunani Ahamad keta saqawa inda yarasa gano mafita da nusar da munauwar gaskiya domin Abun yaxama ruwan dare dama duniya kowa Abunda zuciyarza ke so shine dai dai koda kuwa abun yayi hanun riga da shari'a! A gefen qauye kuma Jalee tamiqawa Allah Al'amarinta zancen mutanen gari beyi tasiri ga kunnuwanta ba ta sadaukar da kai tsakaninta da Allah! duk da cewa intasamu duhun dare ta kanyi kukan rabuwa da dauda mutum ne daba zata manta yawan Alkhairansa ba! roqonta ga Allah d'ayane ya munsanya ma dauda da macce wadda tafita komai Arayuwar sa,,tana wannan tunanin ne qawarta hanne tazo ta zauna daffff da itah tace gaskiya jalee baki kyauta ba gari se maganar cutar dakikayiwa dauda akeyi dan kunga kud'i,,,,murmushi tayi sannan tace hanne bazakigane bane kinsan Aure nufine na Allah amma wlh ko amafarki bantab'ayi cewa dauda ba mijin da zan Aura bane! da tsakiyar rana labarin yasameni cewa wani zanyi rayuwar aure dashi, da fari nayi kuka mai girma daga bisani na gane banida wani zab'i da yawuce na rungumi hukuncin Allah wanda in nakafe se son zuciyata wata qila ba Alkhairi bane amma har ga Allah ba cutarsa nayi ba,, to tayaya mutane zasu amunce da maganar ki jalee!!? uhmm hanne basai sun yadda ba watarana Allah zai warware cikin sauqi,,,, hakane allah ya dai daita mana! Ameen tafad'a sannan shiru yaratsasu!... daga bisani hanne tayi tafiyarta cike da tausayin jalee,,,,,,,,, bayan sati d'aya munauwar ne zaune d'akin mahaifinsa ji yake kamar yace ayi mai alfarma ajanye masa Auren jalee! sedai yayi kasake yana jiran me Abban zaice domin shi yakira shi ba son ransa takawo shiba,, gyara murya yayi sannan yace kafara shirinka wata biyu masu zuwa muka tsaida bikin Aurenku!! munauwar seda yayi rashin hankalinsa na daqiqu sannan da kyar yace Allah yakaimu,,abba ya lura amma yadake Azuciyar sa yace wataran se labari saunawa akayi kuma daga qarshe aji dad'i!! azahiri yace kaje kufara shirinku,,,,,,kwanci tashi asarar mai begen duniya yau saura sati d'aya Auren jalee da munauwar Abba yasanya an d'aukota dan wasu gyare gyare kamar yadda aka saba ga kowace amarya tare take da rakiyar qawayen ladidi da hanne.......
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
0 comments:
Post a Comment