Shiga Office dinshi Xaiyi ganin yawan patients din dake Xaune yasashi Shiga Office din dake kusa da nashi. Xaune yaganshi ya Xubama files din dake gabanshi ido, da Alama tunanin wani Abun yake. Xama yayi kan daya daga kujerun dake gefe yana kallan shi. Yazeed! Yazeed! Yazeed! Saida yakira Sunanshi Sau3 Kafin ya dago ya kalleshi. Yusuf yaushe kazo? murmushi Yusuf yayi inafa Xakasan Nazo. Yazeed wai har Akwai wani Abu dazai dameka ka kasa Sanar dani? menene Amfanin friendship dinmu na tun yarinta? 2days Har Wani rama Kayi habaaa Ai koda'ace baka Sanniba Naxo na tambayeka meke damunka Xaka fadamun yaxeed bare ni dakaina. dan tsaki yazeed yaja Nifa na fadamaka babu Abinda ke damuna,Wlh kafiye Naci yusuf. Shikenan kaje ka kashe kanka yazeed Sabida tsabar Xurfin Ciki da miskilanci. Eh Naji Ciwon Hauka kakeson Na dauka Nasakama kaina bayan Ni bawani Abu dake damuna. Ok. Naji. patients din daka Tara waje faaa? Pls Yusuf kaduba Su mana. Wlh baka isaba dan Rainin wayo Saidai natura maka Nursing1 da zatai helping dinka. Tabe baki yazeed yayi Ai Abin bana tada jijiyoyin wuya bane Naji turomun. Eh din Yusuf yafada yafita waje, karo yaci da Dr Zainab dake kokarin Shigowa. Maman Haneef barka. yawwa Dr Yusuf Angon Kausar. Kedai Kincika tsokana Dr Zainab. Babu Wani ai Angon Kausar dinne. dariya yusuf yayi. Naga kinyi Shirin tafiya time be karasa ba. Eh wlh Hanif ne Sunyi Hutu A Skul yau.Xanje na dauko Shi. Ashe daukan excuse kikazo. dariya Dr Zainab tayi Aikuwa dai. Yana Ciki dai ko? Yana Ciki yusuf yabata Amsa. Ok ta fada yayin data bude kofan. Shiga tayi Ciki yusuf yanufa inda su kausar Suke Zaune. barka Dr yazeed! yawwa Maman hanif. Pls inason Xantafi gida yanxu Anyima Su Hanif Hutu ne yau. Amma lokacin tashi beyiba Kiyima babanshi Waya ya daukoshi. Abban Shi baya gari. Nifa da Sonake kiduba patients din dake waje. Ayya Amun uzuri. ba damuwa kije. Thanks Ser. tashi tayi Xata fita Ammm Pls Dr Zainab! dawowa tayi ta Xauna Any problem?? last time dana kiraki Xuwa gidan yazeed Naji kinyi wata Magana Namance me kikace yanxu. Murmushi Dr Zainab tayi Natuna ni. Cewa nayi Naga Amaryar mu Allah yakaimu musha biki. "Exactly" Amma time din wace kika gani ne??? feenah mana Dr! kara juyowa yayi gaba daya Maman Haneef feenah ai bata dace dani ba. Ido Dr Zainab ta fiddo waje Lallai Dr yazeed baka lura d Kyau ba, Ai Wlh duk sanda kuka jera kuka fita babu wanda Xayi tunanin Kai ba mijinta bane. ba karamin dacewa Kukai ba Ga yarinya mai Hankali Wlh. Murmushi yazeed yayi Amma batasona Ai Dr. Murmushi itama tayi Amma kai kanasonta ne??? Sosa Kai yazeed yayi Ni bana Sonta kawai Naga Ina yawan tunaninta yanxu I don't know why. O.k. Nazata ma kana Sonta ne dana San yanda Nayi nahadaku kuka Sha Soyayya. Cije lebe yazeed yayi yanason yima Dr Zainab magana Anma besan mai Xaice mata ba. Shikenan yazeed bari natafi Amma kadaina yawan tunaninta kada Kaje kaji kanasonta Alhalin bahaka Ranka yaso ba. fita tayi bata jira amsarshi ba. Cikin Ranta kuwa dariya Abunma yabata. Mutum yafito yafada Abun dake damunshi Miskilanci bazai barshi ba, Ai nima kuwa baxan Nuna maka Nasan kanayi ba. Yazeed tana fita yabuga table din dake gabanshi Nifa naso ta turota Dan nadade banganta ba. Anma gara nacire Tunaninta kamar yarda Dr Zainab tace tunda ba Sonta nake ba. Rufe bakinshi kenan Aka turo Kofar. Be dagoba bare yasan waye yashigo. Zama tayi a daya daga kujerun face adaure kuma batada niyar magana. Shakar kamshin turaren yake Har Cikin Ranshi yake jin dadinshi. dagowa yayi dan ganin waye ido biyu yayi da feenah. Ido ya fiddo waje lokaci daya ya maida y lumshe yana murmushi. Bansan maiya tuna Cikin Ranshi ba ya maida fuska ya daure Sak yazeed din da yakoma. ke baki iya Sallama bane?? Cikin Ranta tace Shiyasa 2days banason haduwa dashi wlh. Ba dake Nake ba. Saida tadan bata lokaci Kafin ta dago kanta tana kallonshi. Atare Sukaji wata irin faduwar gaba atare kuma Suka maida kansu kasa. aini nayi baka Amsa ba feenah ta fada. miye yasa baki tsaya har Sainajiba? Nifa Wlh Abinda na tsana kenan tambaya da nuna isa feenah ta fada Cikin Ranta. Afili cewa tayi Nifa bansan mai Zan gaya maka ba, bro yusuf ya turoni Nan if not Kasan babu Abinda Zai kawoni wajenka,pls kacemun ga Abinda kake so Natashi natafi. tunda tacigaba da magana yake kallon bakinta yanda take motsashi idan b kallonta kake ba saika Rantse kace ba ita take maganar ba. dawo d Hankalinshi yayi kekoh! Koda yake nadade dasanin bakida kunya tun farko. Amma Xan koya miki Hankali Soon.yanxu wannan file's din Xaki iba kirinka turamun patient din dake waje One by One. Zumburo baki tayi ta'iba file's din tayi waje....kallonta yayi yasaki Murmushi komai kyau yake mata Cutie.
Haba Seemah kina ganin tun Ranar bekara nemana ba, Anya da'ace da gaske yakamu da Sona Ai da yanxu yakara nemana ko? tsaki Seemah taja Cikin Ranta Afili dariyan dole tayi Khady kincika Xumudi. Kinsanfa miskilin mutum irin yazeed komai Sai anbi Ahankali kanshi. yanxu Samu Xaki kikara Xiyartarshi daga Sanda kikaga yafara Sonki kamar ya mutu Saiki daina Xuwa wajenshi da kanshi Xakiga yadawo yana bibiyarki. haba dai Aunty Seemah? Ke wai khady Kamar ba mace ba koda yake yarinta Yasa, keni banma Ga dalilin dayasa kikeson Aurenshi ba Naga duk Abinda Ake Samu Cikin Auren kema yanzu kina Samun Shi. Hakane Seemah ni kawai Sonshi nake d Aure idan ban Aure shi ba inaganin Xan iya Samun matsala. Ashe kuwa Zaki mutu! Kallonta Khady tayi kamar ya??? da Sauri Seemah tace ina nufin Zaki mutu dan dadi dan kuwa Kamar kin aureshi kin gama. dariya khady tayi Har kinsa gabana ya fadi daxun. ai Saiki dauko Abinki ki maida dan munkusa musha biki. dariya khady tayi Shiyasa Nakesonki Seemah. Allah ko? Eh dagaske Mana. magana Seemah Zatai Mufeeda tashigo dakin. Xama tayi fuska adaure. Toh lfy kuma Mufeeda? Haba nagaji. Wlh nagaji Seemah Saikace wata bilonia ce nidin Haba ina dalili. Wai miye yafaru Mufeeda? Seemah kina ganin yawan kudin Dana kashe kan yazeed bokaye daga maicemun Aurenmu Zai kasance bayan Sati2 Sai Mai cemun yaxeed Zaizo ya Sameni da kanshi.kina ganin bokan Chan danaje wajenshi cemun yayi Aranar yazeed Zaizomun d maganar Aure yau nakoma yana gayamun wasu banxayen maganganu Haba. Lallai dole kidamu kawata, Ammafa tawani bangaren Sainaga kamar ba Abun damuwa Aciki Sabida kinriga kinsanar da yazeed Halin wacce Akace Xai Aura,kinga yanxu ba lallai ya aureta ba, Hakan Wata dama ce dazakibi kikara Zagewa dan ganin kinci Nasara. Keni Seemah Nama tambaya Ance Shida yarinyar basa wani Soyayya.Sai yanxu Nayi danasanin fada mishi Halinta tunda Abanza Nayi,gashi Ranar bakaken maganganu Nayita fada mishi Son Raina, kinga Idan bada bokaye ba ban isa nakara tunkarar Yazeed kai tsaye ba. Kallon Khady Seemah tayi ta kashemata Ido daya. Amma mufeeda Sainaga Kamar kidaina Asaran kudinki haka,kefa mace ce Yanzu kinemo kissa kirinka jefa mishi Kawai. Hmm Seemah bakigama Sanin Halin Yazeed ba Wlh,ba irin kissa da ban mishiba duk Abanza. Amma Bokan danaje wajenshi yau yace mun rushemun Al'amurana Ake, duk yanda Akai feenah din nan ce Kuma Amma Xanyi maganinta ne Ahankali. Lallai kam kidau mataki iska dai na wahalar damai kayan Kara Wlh. Kaman ya fa?? Ita feenah din Nake Nufi mana inaganin son maso wani fa takema yazeed din. Kinga kuwa ai Awahalce Zata kare. dariya Mufeeda tayi Kedai Bari Wlh Nasanma Son masu Wani din take mai Adaiyi mugani. dariya Abun yaba Seemah Sosai cikin Ranta take fadin "Wannan batasan me take ba" Afili Cewa tayi Adaiyi mugani kam. Kallon Khady Mufeeda tayi waike yaushe Xaki tafi ne?? Yatsina face khady tayi Saina Samu biyan bukatata. Tashi Seemah tayi tana dariya Zaku mutu kan Wanda besanma kuna haukar Sonshi ba. Amma idan bukata ce ai kingama biya Saidai Ko dan kedin jarabatuce.kiyi Aure Kawai Shi yafi. Aunty mufeeda bazaki gane ba mijin danakeso Ake neman Asircewa Nikuma na hana,burina kawai nakeson yacika Na Aurenshi kafin nabar garin nan. tabe baki mufeeda tayi ta tashi tabar Wajen.
Xuwa yanzu yaxeed yagama tabbatar ma kanshi Son feenah yake, matsala daya dole yacire Sonta Aranshi domin ba Sonshi take ba. Leemah tun tana tunanin mai yasa yazeed yakeson taita mishi firan Feenah har ta daina tunani. dan yanzu da xaran sun koma gida Xai xaunar da ita yace tamishi firan dasukai. ganin haka Yasa take mishi firan Feenah Hakan Kuwa yakeso Xama yake tana bashi lbr yana dariya Kamar ba yazeed mai Halin Shariya ba. Miskilancin dai yana nan domin haryanxu yaki Sanar da kowa Abinda ke Ranshi. fadanshi da feenah Sai Abinda yakaru ma. Sam ita haushi yaxeed yake bata, kusan huni Suke fada Cikin hospital din nan. Yusuf Shidai yanzu yazubama yazeed ido danyaga gudun ruwanshi,dan haka be nuna mishi cewa ya gane komai game dashi ba. Haka rayuwan take ta Cigaban musu. Leemah da Nazeer yanzu Anxama daya daurin Aure kawai Ake jira,domin yanxu basa iya Rayuwa batare da daya yaga daya ba. Mufeeda da Khady Soyayyar yazeed ba karamin Azabatar dasu take Ayanxu ba. gashi duk inda Mufeeda ta bullah Sai Taga ba chanji dan haka yanxu tadan lafaaaa Acewarta Sai bayan kwana biyu tacigaba da neman mafita. Khady Har yau takasa kara komawa wajen yazeed Acewarta kada yagane ita ba mutuniyar kirki bace gara Shi ya nemeta. Haka Seemah ke kara dulmiyar dasu kan cewa Xasu Samu Nasara, Abayan idonsu taci dariyanta ita daya. Abba da daddy Sun yanke Shawaran Saka Ranar bikin Nazir da Leemah,inda inno takafa kanbu kan sai Anhada Dana yazeed. Yanzu Abba da daddy tunanin dasuke Yi kenan yanda Xasu Shirya Abun. dan haka Suka yanke Shawaran haduwa gaba dayansu gobe a gidan Mamy you
💖💋💋💋💖💋💋💖
YAR LESBIAN CE
💖💋💋💖💋💋💋💖
By
Nadeeya mohd Ahmad
(💖Nadseer💋)
dedicated to
Xaynab Ummu mahbub
Page....60
Washe gari gaba dayansu gidan Abba Suka yada Zango,inda Suka hallara babban parlon dake Kasa. Shigowar Abba da daddy kawai Suke jira. mintuna kadan tsakani Saigasu Sunshigo. gaisawa Sukayiyyi daga bisani Abba yafara Magana. Yazeed ina yusuf ne?? Abba yace Suna Hanya Shida Kausar. Madallah kafin karasowarsu Bari Naji ta bakinka. Matar danace kasamo kasamu kuwa?? durkusar dakai yazeed yayi kasa Abb.....inno dake kusa dashi tayi Saurin Kai bakinta Saitin kunnan Shi,tsaka Wannan karan kada ka Cuci kanka Xuwa yanxu Kai kanka Kasan Nafisatu kake So, Toh kafadi Gaskiya idan ba hakaba Amadi Zai Aura maka koma wacece. Maganar inno ta dake kunnan Shi, Gaskiya ta fadamun Inno. Amma yarinyar bata Sona Ai kuma! ni yanzu nace inasonta gaban mutane girmana Ai yafadi,kuma Xata kara Rainamun wayo tunda dama bata da kunya. Sannan ma....Mamy dake dayan bangarenshi Xaune ta katseshi my Son kafadi Abinda ke Ranka kada kabari Abbanka yayi fishi yamaka auren dole. Auren dole kuma?? Tambayar da yazeed yayi ma Zuciyarshi kenan! Abba Zai iya Amma gaskiya ni bazan Jama kaina Raini wajen yarinya karama ba.magana Zaima Abba yaji Sallamar yusuf da Kausar. Saida Suka gaisa gaba daya yusuf yadawo kusa da yazeed y Xauna. Abba ne yacigaba dama kai muke jira yusuf Kasancewar yakamata Ayi Komai kana Nan. Abokinka nake tambaya ko yasamo Matar danace yasamo, Kasan 6months kenan danace mishi, banda Shekara1 Dana taba bashi last time. Eh Hakane Abba Ai yanxu inaganin yasamo wacce yake So. Madallah Shine Nakesonji daga bakinshi Ai. K'asa kasa Yusuf yayi da murya kaji Abinda Abba kesonji daga bakinka, idan kaga dama kaki fadan Gaskiya Sabida miskilanci irin Naka. Kana batamana lokaci yazeed Mamynshi ta fada. Amm Abba ni bansamu wacce nakeso ba Har yanxu. kallonshi Leemah,Kausar,yusuf da Nazeer Sukayi da Alamar tambaya. Lallai Wannan bro din bazai taba Chanza hali ba Leemah ta fada Cikin Ranta. Mtsww Kaje ka kashe kanka yazeed Yusuf ya fada Cikin kufula. Yazeed kenan Soyayya ba'a mata yanga Kausar ta fada Aranta Tana murmushi. Nazir murmushi kawai yake yana kara jinjina Son girma irin Na yazeed. Inno data Cika da takaicin yazeed Afili tace dan iska kawai, kafison Abarka da kafura tana Shigomana gida Alabe tana fita a labe, toh Wlh baka isaba! Amadi kabashi balaraba yar gidan ladoo dama tun sanda yana Zuwa wajena take Sonshi. Mamy Na dariya tace Aikuwa mamah Nasan yarinyar tana Zuwa gaidani idan naje! Ita kuwa Fatima Kinga idanma yarinyace baya So Ga balaraba. Shikenan hakan Za'Ayi Abba ya fada lokacin daya maida hankalinshi kan Nazir. Captain kaidai munsan komai kuma munyi Shawaran Saka Ranar bikinku kaida Leemah Ayau. dan haka Nan da wata2 Za'ayi Aurenku insha Allah. Murmushi Nazir yayi mungode Abba, Leemah dake gefe jitake kamar ta tashi ta taka Rawa dan farin Ciki. Hada ido Sukai da Nazir Atare Suka kashema juna ido. Minstilinta Kausar tayi mazari Kawai ai kyabari Sai Ranar Auren kiyi Rawar kai haka. dariya Leemah tayi Kai Kausar kemafa haka kikai. Cigaba Abba yayi ALHJ Umar Faruk ko kanada magana dasu? gyada Kai dad yayi Aa babu Amma wacece balaraba da Za'a ba my Son? Kuma yace yana Sonta ne?? da Sauri Inno tace Ai A Katsina take Umar,ta dade tana Sonshi ba lallai Saiyace yana Sonta ba tunda beda Matar Aure,mukuma mungaji da ganinshi haka b Aure. Murmushi kawai dad yayi Allah yasa Alkairi Toh. Amin inno tace da Sauri. Kallon feenah Abba yayi My daughter kema ina Alkawarinmu dake yake?? Saida tadan bata lokaci daga bisani tafara magana, Abba Ni duk masu nemana babu Wanda Nake so, Saidai ko nan gaba. babu Wani Nan gaba Munafukan banxa, Ai Wlh Umar Akwai Wanda tun lokacin damukaje Auren Kabeer yola yanuna yana Son Nafisat, kaga tunda batada Zabi itama Amata Aure dashi Kawai. Inno ke zayyno Zancen nan. dariya dad yayi Shikenan mamah inno indai yamiki Ahadasu Kawai ba wata damuwa. Kallon dad feenah tayi tajuyar da kanta Xuwa wajen inno harara ta Wurga mata hade da kara daure fuska. Juyawa inno tayi ta nuna batamasan feenah nayi ba. Alhmdllh Abba ya fada. Tunda yazeed da feenah Sukadai Suka rage marasa jin magana ta, ni Xanyake hukunci da kaina. Wata biyu dasuka Rage Na bikin Nazir da Leemah, Aciki yazeed Shima Zaiyi Aure, dan Zuwa gobe Zani Katsina dan nema mishi Auren balaraba din. itama Feenah Alhaji Umar kashirya muje yola munemi yaron da inno tayi magana Ayi komai dan duk tare Zan Aurar dasu Arana daya. Hakan yayi daidai dad yafada Allah yakaimu da Rai da lafiya. Amin duk wajen Suka Amsa banda feenah da yazeed dasuke jin Kamar Sushake inno. kutashi kutafi ko. tashi Sukai gaba daya wajen ya Rage Abba, dad,Mamy,mumy Sai inno. Bansan mai Suke Shirin tattaunawa ba Na tashi Nabi bayan su yazeed.
Fadawa kan bed yayi lokaci daya ya Rike kanshi ya Rasa miye kemai dadi, gashi gaba daya ya Rasa Wani irin tunanima yadace yayi Ayanzu. tura dakin yusuf da Nazeer Sukai, Ciki Suka Shiga Suka Xauna. Ko kallon yazeed dake kwance basuyi ba, yusuf yafara ma Nazir magana. Gaskiya Captain ina tayaka Murna, Nan da wata2 kaima kaxama Ango tare da masoyiyarka wacce kakeso take Sonka. Murmushi Nazeer yayi kaidai Bari Dr yusuf yau dinnan jina Nake Kamar A Aljannah. Wai yau nine Akasama Ranar Aure da Leemah wacce nadade inasonta Kai Alhmdllh Wlh. Kaban dariya Captain kaidai Allah yasoka baka yaudari Xuciyarka ba, da yanxu Abba yayi maganinka irin Na feenah. Lallai yusuf aini son girmana bekai na feenah ba, duk Abinda nakeso bana Shakkar fadanshi ko A'ina ne, Sabida ni Xata kwabemawa gaba idan ma ban fada ba. Gaskiya Captain ka hadu Shiyasa Nima lokacin banyi Sanya wajen fadama Kausar inasonta ba, Alokacin har Zugani Ake wai mai Xanyi da karamar yarinya, gashi yanxu banda farin Ciki babu Abinda ke tsakaninmu. Nagani ai Dr Allah muma ya nuna mana lokacin mu. Amin Captain Amm....Wani tsaki yazeed yaja wanda yasa yusuf yin Shiru. Juyawa Sukai lfy yazeed? yusuf ya tambayeshi. ya Zaka tambayeni ko lfy bayan komai Agabanka Akayishi. Ohhh wai wannan Abun kakejama tsaki haka?? Aini banga Abun damuwa Anan ba bakada Wacce kakeso, Menene Na damuwa kuma dan Inno ta Zaba maka? Haba Yusuf wai wata balaraba fa take Cewa, Ni Wlh bana Sonta Koma mai Xa'a Mun bazan Aureta ba. Nanfa daya yazeed Kasan Abba baxai Janye magar Shiba tunda babu Wanda yace kaki Samo mata. Inada wacce Nakeso yusuf ita dince bata Sona. Hmmm yazeed tunda Agaban Abba baka iya fadin haka ba, muma ka Rabu damu tunda be Shafemu ba. Yusuf kasan banida Abokin daya wuce Kai ko? tayaya Kana ganin Xa'amun Abinda banaso kuma Kayi Shiru? Yanzune kasan baka da wanda yawuceni Yazeed? Najima tunda ka gane hakan yanxu me kakeson Nayi bayan ni bansan Sirrin Zuciyarka ba, kokuma Dan nine Sarkin Rashin kunya Sainacema Abba be kyauta ba bayan ni banida wacce Xan baka, kawai kayi hakuri Kama Abba biyayya ka Aure wacce Suke So maybe....haba yusuf inno cefa kadai Tasan yarinyar ita kadai kuma take bakin cikin Zamana Agidan nan Saikace kanta Nake Xaune. Tabe baki yusuf yayi duk Abinda babba ya hango yaro baya hangoshi koda yahau tsani. Kaga inno ta hango Wani Abun Atare da balaraba dan haka kayi hakuri Kawai. Yusuf... katseshi Yusuf yayi tunkan yace komai, Nidai ka kyaleni yazeed yanda ban isa Naji damuwarka ba, haka ban isa Nayi jayayya da Abba ba. tashi yazeed yayi yabar dakin Rai Abace. dariya yusuf da Nazeer Sukai. dan Rainin wayo Ai gara da inno ta Samo balaraban Wlh yaje yayi Auren kauye tunda girman Kai baxai Bari yafadi wacce yake soba. Murmushi Nazir yayi Shidai yazeed yanayinshi daban. Ai haka Sister dinka itama take Nazeer. Shikenan yusuf itama ai dan kauye Zasu aura mata kaga Sunja mawa kansu. dariya Sukayi Atare yayinda Suka Cigaba da firarsu kan yanda bikin Xai kasance.
Haba feenah kiyi hakuri komai idan kikaga yafaru dama Chan haka Allah yasa. Mai yuwuwa kiga Dan yola din Shine Zai Zame miki farin Ciki Agaba. Nasani Kausar Amma Ni bance inaso Asamamin mijin Aure ba, lokacin danake matukar Son nayi Auren ai basu yanke Shawaran haka ba, Sai yanxu da wannan inno din tazo komai tace Suce toh basusan lokacin wannan ya huce ba. Sorry besty inaganin wasa Suke muku babu wani Auren kauye dazasu muku. Lallai feenah kinfini Sanin Halin Abba Saikiyi tunani yana chanxa magana ko idan yayi ta Xauna. Kumafa Hakane Wlh, Amma kema feenah kin tabbatar bakida Wanda kike So? Ni Wlh Leemah banida Wani Zabi. Kingani kibari kawai ki Aurenki Kinga Rana daya Zamuyi ma kamar yanda muka tsarama Rayuwarmu. Hakane Aike da wanda kikeso Za'a miki Auren. Sorry Kema zakiso Nakin ne Soon. Tabe baki feenah tayi wai Saikace angaji dani Wai Wani dan yola, Ai wlh barima Naje Nasamu inno din Nan. Tana fita Kausar da Leemah Sukai dariya. Kinga inno ta iya jan fada daman. Aini banga laifinta ba Leemah Gara tayi maganinsu. Amma Kausar nagane da gaske feenah bata Son bro Yazeed fa, Saidai Shi gaba daya yamutu Akanta yanzu. Dama bana dade inagaya miki hakan ba, Shima yaxeed din Cikin lokacin Nan yafara Sonta, Amma dama Chan nasan yusuf ne yashirya Hakan. toh ai Kausar hadin yayi ne Sosai. gaskiya kam koni zanso ace feenah ta Auri yazeed Amma Kinga da'ace yazeed din besaka Son girma ba yafada yana Sonta da komai yazo da Sauki. Amma yanxu lokaci ya kure musu tunda ansama musu Masoya. Allah yasa Hakan Shine Alkairi toh. Amin dai Leemah. dakin inno feenah ta wuce tashiga. Yazeed tagani tsaye inno nakan bed. Kallo daya tamai ta kauda kai tana jiran inno tagama mgn. Kadaiji Abinda nace maka Wlh idan baka Amince da balaraba ba Saina fada, Ai da idona naga tokafurar tafito takalmi A hannu. Kacigaba da Rainamun wayo tsaka wannan lokacina ne na Ramawa. Rasa Abinda zaicema inno yayi. ga feenah data Shigo yanzu gaba daya hankalinshi ya kasu biyu. bangare guda na Xuciyarshi yana tunanin. ya Akayi inno taga Mufeeda ta fita daga part dinshi? Lallai daman tarani takeyi tabbas idan tafadama Abba Cewa mufeeda naxuwa wajena babu Abinda Zai hana ya yarda tunda wai har Inno ta iya daukan mufeeda pic a yar Nokia dinta. bangare guda gaba daya feenah ce tarikitar mishi da tunani ganinta kadai yasashi jin Wani yanayi. Wani irin SO nakema yarinyar Nan? Nifa banma gama yarda Cewa Sonta nakeba, ina ganin tausayinta ne Yamun yawa haka...... Feenah ce ta katseshi. Inno this is d last time dazan miki honing Kan kidaina Shiga harkata, Shi wanda yazo yacemiki yana Sona gaya miki nayi Ni inason Shi? Kawai kinaji da tsufa duk kibi Ki damu mutane. kuma Kije kisan yanda Xaki kisa Ajanye maganar aurena da Wanda bansanshiba. Kinji Nafada Miki karashe maganar feenah tayi Tana karkadama inno hannu. Tana gamawa tayi hanyar fita. Yazeed da tunda feenah tafara magana yazubamata ido gaba daya ta tafi da tunaninshi. tabe baki Inno tayi babu Wanda zesani Chanza maganata. Auren kauyene dole kiyi tunda Ummaru daga kauye yazo ya Auri Hafsat. kaikuma tsaka dallah fita kagaban Waje. Jin shiru beyi Magana ba yasa ta dago kai. ..Sakin baki tayi ganin inda yazeed yake kallo. Tohfa dama Wannan Shi ake kira suman tsaye? Hannu takai saitin idonshi tana kadawa. Firgit yazeed yayi miye haka inno? tsaka kai Zantambaya miye haka, tun dazun tafita baka saniba kayi Suman tsaye, Al'Quran kaban tsoro chanake mutuwar tsaye ma Kayi. Mtsww cemiki nayi Dan Ita Nake kallon kofa Toh? danwa kake kallo Toh? ai duk da baka juyaba Sai yanxu. Akwai Abinda nagani ne yazeed yafada lokacin dayabi Hanyar Fita. dariya inno tayi Xaka gane bakada wayo Ai go
💖💋💋💋💖💋💋💖
YAR LESBIAN CE
💖💋💋💖💋💋💋💖
By
Nadeeya mohd Ahmad
(💖NADSEER💋)
dedicated to
Xaynab Ummu mahbub
Page...61
Wata daya da Abba yasaka Bikin Leemah da Nazir. Masoyan jinsu suke kaman Sukara jawo lokacin. bayan wata Shakuwa data kara Shega tsakaninsu harda kulawa ta musamman dasuke Samu wajen iyayensu. Matsala daya ke damun Leemah yanda feenah gaba daya Ta daga Hankalinta Kan Auren kauyen daza'a mata. tun Leemah nabata hakuri har tagaji tayi Shiru. yazeed yanzu bashida Aikinyi wanda ya wuce tunani. Dan kusan yanzu Adaki yake huni, wajen Aiki baya kula kowa dukdan Sabida Auren da Abba yace Zai Mai. tun Mamy namai fada Kan yanda yadamu har tadawo tana tausaya mishi. Ganin yanda Dan nata yadawo lokaci guda. Ibadar dayakeyi ada yanxu duk yabari. Sallahr farila daker yake kawota bare Aje Ga Nafila. gaba daya Rayuwarshi ta Chanza game da Auren daza'ai mishi, bangare guda Ga wani irin Son feenah dake kara dawainiya da Zuciyarshi. Saidai bayanda Zaiyi tunda yanaji yana gani Xa'a Rabashi da Masoyiyarshi. tunanin dayake huniyi Kenan dan haka gaba daya ya hana kanshi Sukuni. feenah bangarenta hakan ne kusan huni take Adaki tana kuka, Acewarta Anya Sonta Ake Xa'a Aurar da'ita A kauye! tunda data nuna tanason Auren ba'a mata ba sai yanxu ne Zasu Auramata wanda batama Sanshi ba. Me yasa bazasu jira har Zuwa lokacin da Xata Samu wanda take So ba? Sake sakenta kenan, kullum mum Cikin lallashi take Amma kamar kara Xugata take. Ko'ina ta daina fita duk dan Ace Anfasa Auren Amma kamar kara zugasu take. dan Shirye shiryensu kawai Suke, inda Mamy tasamo musu mai gyaran jiki, duk dacewa bikin da Saura. bangaren Kausar da Yusuf Soyayya sai abinda yaci gaba dan gaba daya kulawa ta musamman Sukeba junansu. Yauma Kausar ce kwance ta daura kanta a Cinyar yusuf tana Zuba mishi Shagwaba, yusuf Sai faman lallashinta yake Kasancewar 1week kenan tana fama da Rashin lafiya. Sorry my Wife kici kadan kawai bada yawa ba! Um"um ni banason ci nakoshi Yusuf. Me yasa kikace namiki Zakici kuma? dazun Naji inaso ne yanzu kuma Na koshi. hancinta Yusuf yaja Nidai kici kadan. Shgawabe fuska tayi dama kace yau Xaka Nuna min result dina. Murmushi Yusuf yayi yes Xan nuna miki Anjuma.pls kanuna Mun yanxu Nidai. dariya ta bashi yanayin yanda tayi maganar. tashi yayi ya dako back dinshi. Wata paper yaciro yana murmushi. Albishirinki! goro Kausar ta fada Cikin kosawa. Wani kalan goro? da Sauri tace fari. dariya Yusuf yayi ya mika mata paper din. budewa tayi ta fara karantawa lokaci guda ta tashi daga kwancen da take tana kallonshi da Alamar tambaya. ido ya kashe mata "you have a 2months pregnant" koh? da Sauri Kausar ta fada Jikinshi da gaske ne Abinda nagani Yusuf?? Shafa bayanta yusuf keyi lokacin daya fara fadin yes d gaske matata takusan tazama Mum. Kara Rungumeshi tayi i Am happy hubby. Kice Alhmdllh my Wife. Alhmdllh kausar tafada. Rungumeta Yusuf yakarayi yayin da yashiga Kwararo mata addu'an Sauka lfy da Samun Zuri'a mai Albarka. Hubby kuma Sam ban san inada Ciki ba har 2months ko Amai banayi. Hancinta yusuf yaja ai Haka Akeso habibti. Amma bazan fadama Su feenah ba! Why? Surprising dinsu Xanyi Saidai kawai Suga na haihu. dariya yusuf yayi Sosai, Ai da kanshi babyn Xai tonaki idan ya girma. bazan bari yafito ba ai. dariya yusuf yayi Cikin Ranshi yace lallai haryanzu Kausar yarinya ce. Zomuje nafada miki yanda Xakiyi kada Su gane. tashi Kausar tayi tabi bayanshi Zuwa bedroom dinshi. Janta yayi kan bed ganin Abinda yake shirinyi yasa ta Shagwabe face Nifa banda lfy kasani. Jawota Yusuf yayi jikinshi Sorry. toh ka fadamun mana. Kawo kunnanki kiji oya. mika face dinta tayi Yusuf yayi Sauri kama lips dinta kissing dinta yafara Ahankali, tun tanason hanashi har Sakon yafara isarmata Dan haka tashiga tayashi.
yau tunda Asuba mufeeda tashiga Shirin fita. Dan haka tana gama Shiri ko kallon Seemh d khady dake bacci batai ba ta fita. Motar Seemah dake Harabar gidan Nasu tashiga tajaaa da gudu. tafiyar mintina30 tayi Zuwa wani kauye dake gaban kd Kafin Akai Zaria. parking motar tayi a bakin titi Inda ta tari Machin domin yakarasa da ita Cikin wani daji. Nan ma ba karamin tafiya Sukai ba. Saida Suka kusa karasawa wanda ya dauketa yafara mata magana. Hajiya Gaskiya tunda kikazo wajen bokan nan bukatarki tagama biya! Allah Ko bawan Allah? Allah kuwa Nake fada miki Hajiya duk matar Dana dauka nakawo Nan da farin Ciki take fitowa. lallai kace yau natako sa'a nima Wata kawata tamun kwatancen Nan din. Ahhh Gaskiya kawarki yar gari ce Ai yau nake fadamiki kishiyarki Zatabar gidan. Uhum bama wannan ya kawoni ba Malan. Sauka tayi, Zaka tsaya Nafito bawani dadewa zanyi ba dan kamaidani titi. Hajiya Ana jirana faaa. Zan Kara maka kudi kan yanda ka daukoni. Ahhh kaji harka jeki kizo Ina Nan. Karasawa Kausar tayi daidai yar wata bukka tana Sallama. tadan juma Awajen kafin katon wani mutum yafito bayanshi da wata mata. Daga ganin matar irin Matan manyan masu kudine marasa tsoron Allah. Wucewa matar tayi tabar wajen. Ke babu ka'idar Sallama Anan wajen. Afuwan boka mai Nasara. Biyomo toh kicire takalmi tafiya da bayaaaa. yanda bokan yace ma mufeeda haka tayi tabishi Xuwa Cikin yar bukkar. Munsan meke tafe dake. Wani saurayi kikeson Aure Wanda ada kikesonshi dan kudinshi, Zuciyarki ta Chanza kinasonshi yanzu b dan kudi ba, baya Sonki ko kadan Shi, dan haka kikazo A Cusa mishi Sonki Kamar yayi hauka, duk dacewa kinje wajen bokaye da dama bukatarki bata biya ba. duk dacewa mufeeda Tasaba jin irin haka wajen bokaye Hakan be hanata mamakin wannan bokan ba. duk yanda kafada Hakane boka. Wata irin dariya yayi ta marasa imani mudin munsan komai daman. Amma boka Ancemun batamun Al'amarina Akeyi Kozan Iya Sanin wake batamun? Leko Nan kiga mai batamiki tanayine domin itama takamu dason yaron. Lekawa mufeeda tayi ganin khady Cikin kokon ba karamin Razana tayi ba. Lallai zatasan koni wacece. Boka yanzu tayaya Zan Samu Shiga Zuciyar yazeed yazama nikadai yakeso kuma ya aureni?? Wannan aikinmune kin Samu, Saidai Aikin Akwai kudi da yawa. Boka kada kadamu konawa kake bukata zan baka indai bukatata Xata biya. dariyar bokaye yayi Ayauma idan kinason Auren yazeed zaki aureshi, Saidai Akwai mace daya dayakeso fiye da kowa babu wanda Zaiso Kafin ita Saidai bayanta. Yanzu Zanmiki Aiki kizama kece Abaya. Amma kada kidamu da wacce yakeso din Aurema Za'ai mata ba daman ya Aureta. Saidai duk dahaka Zakizauna da kishiya domin Ahalin yanzu Mahaifin yaron Aure Zai mishi, Saidai yaron bayason wacce Xa'a aura mishi din. da farko da mufeeda Taji yazeed Aure Xaiyi hankalinta yatashi,Amma dataji cewa bayason yarinyar Saitaji daidai. boka ba damuwa Abarshi yayi Aurenshi Amma Asan yanda Xa'ai dai Na Aureshi. Wannan ita dayace bukatarki? Ita kadaice boka. leko kigani yanxuma Aikinmu Zai fara. Lekawa mufeeda tayi Cikin kokon da boka ya nuna mata yazeed tagani kwance yana bacci tayi mamaki domin tasha ganin Acikin lokacin nan yana Sallah. kingani yanzu natura mishi Aljana, daya tashi zaifara nemanki, barima kigaaa. Yazeed taga yatashi daga kwancen dayake Rike da kanshi, Amaimakon taga yayi salati kaman yanda yasaba Saitaji yana kiran mufeeda. Wani irin Tsallen murna tayi inda taciro kudi masu yawa ta aje gaban bokan. wani kwalli yabata tarinka Shafawa duk sanda xata hadu da yazeed. Gdy tayi ta fita tabar wajen. Lokacin da mufeeda takoma baccin Su seemah Suke dan haka tashiga Shiri danzuwa gidan su yazeed.
Mamy ce da Abba Zaune A katon parlon nasu sai inno da Leemah dake gefe guda da Alama fira Inno Kema leemah. Yazeed ne yafito Sanye Cikin wata Shadda Orange Colour Sai kamshi yake kwadawa,face dinshi dauke da Murmushi yakarasa wajen iyayen Shi yana gaidasu. Cikin kulawa da nuna farin Cikin yanayin yanda sukaga dansu Ayau Suka Amsa gaisuwan. Shafa kanshi Abba yayi my Son kokaifa yau Har Kyau ka kara Sabida kasaki Ranka. Murmushi yazeed yayi nagode Abba. Allah yamaka Albarka. Amin Abba. Kallonshi Mamy tayi Sai ina haka kanata kamshi? da Sauri inno dake gefe tace Su tsaka bako gaisuwa dan Zakaje wajen balaraba? kallonta yazeed yayi ya yatsina fuska wacece balaraba kuma? matarka mana ta katsina Ai Wlh bagaka yanda kayi Kyau ba har Naji kishi ma. Mtsww ke kikasan balaraba ni kidaina batama Masoyiyata Suna. Wajenta Zaka kenan? Eh inno ko Kada naje? Aa wace ni! Ai soma nake kayi kabar gidan nan,Xanma baka sako Wajen mahaifinta. mtsww Inno kinada matsala. Kamar ubanka ko? Dariya Leemah tayi bro kabar inno zata bata maka rai kafin kaje kanuna kwalliyar. Murmushi yazeed yama Leemah Hakane sister bari naje. Waima ina Zakaje bro? Wajen mufeeda Masoyiya. ba leemah kadai ba hatta inno da Mamy Saida Suka Zaro ido. Abba dabesan wace mufeeda ba shine yayi Murmushi, my son watoh bakason zabina shine kasamo Wata koh. Abba bahaka bane daman mancewa nayi ban fada Maka Mufeeda ba. Ba damuwa son mufeeda yar gidan waye? Kafin inno tabude bakin magana Sukaji Sallama. Abba ne ya Amsa. Mufeeda ce tashigo Cikin Shigar yan bariki, tana tafiya tana karairaya. kallonta kawai Suke da mamaki. Lallai wannan da Sauran miskilancin nashi, maimakon yazo yamun wlcm ma, ga Wannan tshowuwar itama bata tafi ba Ashe!duk sainayi maganinku. Karasawa tayi ta Xauna Sannu Abba Sannu Mamy. Hy kaka, Leemah yan mata kinkara girma. babu Wanda yakulata dan duk sunyi mutuwar Xaune. Abba ne yayi karfin halin Cewa daga yarinya, wa kike nema? Sirikarkace ni Abba! Sirikata kuma?? gira ta daga mishi Alamar eh. da Sauri inno tasaki Ajiyar Zuciya Amadi ina kafurar da nake fada Maka kwanaki wadda yazeed yakawo zai Aura? Itace wannan! Nayi Zaton koya Rabu da ita Ashe kaga Yana bibiyarta. Shagwabe fuska Mufeeda tayi Honey Kaji mai kakarka take fada koh? Tasowa yazeed yayi yadawo kusa da Ita Sorry kinsan tsowuwa ce. Leemah data kufula matuka da hanzari ta taso Tayo kan mufeeda, tashi kifita Agidan Nan tunda bagidan Ubanki bane, bandama ke karyace bantaba jin inda budurwa ke bibiyar Saurayi b.Murmushi mufeeda tayi menene Aciki dan nazo gidan Uban mijina? Mayya yaushe yazeed din yafada miki cewa zai Aureki.kitashi kifita kafin jikinki yafa miki. Honey kanajin kanwarka faa? tashi yazeed yayi yana kallon Leemah. fita a parlon nan Leemah! Babu inda zani bro har sai Wannan tafita. Tsawa yazeed yabuga ma leemah fita nace kafin nakaryaki. Nifa bro babu inda Zani. daga hannu yayi Zai mareta mamy dake kallonshi tace, Wlh yazeed katabamun yarinya Saina saba maka. Mamy bakiji matar dazan aura takema Rashin kunya ba! tashi Mamy tayi taja hannun Leemah dake kuka Sukai Sama. tasowa Abba yayi yazeed Wannan daga gani ba yar gidan mutumci bace,idan Auren dazanmaka ne bakaso ka kawo wadda kakeso kamila ba wannan ba. Abba Ni ita nakeson Aure dan Allah ka Auramun ita. kallon mufeeda Abba yayi kifita kikoma gidanku Sam bakidace da Rayuwar yarona ba. Honey...da Sauri yazeed yace Nidai Abba kafadamata yaushe Xakuje nemamun Aurenta. girgiza kai Abba yayi da mamaki yau yazeed ke jayayya dashi. Juyawa yayi yahau Sama ganin haka yasa yazeed ya Rike hannun mufeeda Suka fita. Tabe baki inno tayi tana tunani Cikin Ranta, kwafa tayi daga bisani ta tashi tabar wajen
💖💋💋💋💖💋💋💖
YAR LESBIAN CE
💖💋💋💖💋💋💋💖
By
Nadeeya mohd Ahmad
(💖Nadseer💋)
dedicated to
Xaynab Ummu mahbub
*I thank God for everything*👏👏
Page...62/65
Hannun Mufeeda yazeed yakama Suka fita. Ganin yana kokarin fita daga gidan yasa Mufeeda Shagwabe fuska Honey Muje part dinka mana. Akwai Abinda kikeso ne? Nooo inason Kawai Abba ya Amince Suzo gidanmu Dan muyi Aure da wuri. Wannan ba damuwa bane Mufeeda kizo nakaiki gida dare Xaiyi. Shafa Sajenshi Mufeeda tayi karka damu Xan iya Kwana Awajenka yazeed kawai kazo muje Akwai Abinda Zan fada maka. Haka kawai yazeed yaji baya iya mata gaddama dan haka yabita Xuwa part dinshi. Zama tayi kan bed dinshi tana Shakar kamshin da dakin keyi. Honey Ina matukar Sonka komai naka burgeni yake. Murmushi kawai yazeed yamata yashiga Rage kayan jikinshi. Cikin Ranta take magana inaga bawani bokan dazai iya maganin Miskilancin yazeed, kwafa tayi tunda dai yanzu kashigo hannu ai bawata matsala. Honey Mai Xakayi haka? Aiki Zanyi yafada Ataikaice. Hand back dinta ta Ajeye gefe ta dawo kusa dashi, let me help you. be bata Amsa ba ganin haka yasa takara matsawa gafff dashi hanunta takai Saman bayanshi tana Shafawa, Aikinshi kawai yake Cikin laptop betanka mata ba. Honey Anya parents dinka Zasu bari Na Aureka? Kallonta yazeed yayi nima bansani ba! Amma kanasona ko? Inasonki mana. Kasan yaya Xa'ayi kuwa? Ayi Maine? Ka Aureni ta hanya mafi Sauki! No I don't know. Ok mainene Ra'ayinka Akan kasamu dad din Feenah kasanar dashi komai inaganin he's can help you. Kallonta yazeed yayi ya lumshe ido jin ta'ambaci Sunan feenah. Yeah Hakan Zanyi dan Nima nakosa Na Aureki. Wani irin Murmushi mufeeda ta Saki wanda Ita kadai Tasan ma'anarshi. Honey kanada Kyau Sosai, Sajen nan yakara maka Kyau. Murmushi yayi mata ganin haka tafara Shafa Sajen Nashi. Wani irin Abu yakeji yana Ratsa Shi lokacin da mufeeda ta kai Hannuta tana Shafa kirjinshi. lumshe ido kawai yazeed yake lokaci daya ya jata jikinshi ya Rungume. Honey Sonka fa khady takeyi! Cikin wata irin murya ya Amsa mata wace khady?? Kawar Kausar Matar yusuf. Uhum kigaya mata Ni mijin mace daya ne. Kana nufin Matar da Abba Zai Aura maka baka Sonta? Yeah bansonta. Murmushi mufeeda Tayi Honey kayi Hakuri da Abinda nayi maka last time. Aike bakya laifi Mufeeda kedin ta daban ce. Zokaga mufeeda yanda tayi Wani tsalle jitake kamaar ta taka Rawa. Yanda tayi hungging dinshi yasa lokaci daya yaji wani irin feelings ya tashin mishi. kayan nan Sunmiki Kyau mufeeda! Oh Wow mufeeda ta fada yayin data kara bude Rigar jikinta take bra dinta ta bayyana. Ganin da yazeed yayi kusan Rabin Brest dinta waje yasa ya kama lips dinta kissing dinta yafara da wani irin Salo na daban. Zagewa Mufeeda tayi tana mayar mishi da martani da nata Salon. Knocking din door din da'ake yadawo dasu daga Duniyar da Suka lula. yazeed ne yayi karfin halin fadin Waye? dallah Malan budemun kofaaa. Jin muryan Yusuf yasa yazeed jama mufeeda blanket ya Rufeta.tashi yayi yanufi kofa. yana budewa yusuf yafara masifa tun dazun kanajin mutane kayi wani Banza ka kyale dama Nasani banzo ba ai. Sorry kawai yazeed ya'iya cema yusuf. Bani Hanya toh. Oh Shigowa Xakai? Kada nashiga kake Nufi? No! Toh miye kana Abu kamar mara gaskiya. Ware hannuwa yazeed yayi ya kauce yaba Yusuf Hanya. Shiga yusuf yayi Ciki yazeed yabi bayanshi. ganin mufeeda kan bed din yazeed ba karamin Razana yusuf yayi ba, juyawa yayi yanama yazeed kallon tambaya. bafa Abinda namata malan Kawai....katseshi Yusuf yayi kawai Romancing kayi da'ita. da Kyau.! Ina Alkawarin dakayi nacewa bazaka kara Aikata makamancin Wannan ba??? Tabe baki yazeed yayi wannan bawata matsala bace tunda Aurenta Xanyi. Ido yusuf ya fiddo waje Auren mufeeda fa Kace Zakayi? yeah Soon insha Allah. yazeed mufeeda cefa wadda duk Wata majilisar yan iska Saika Samu Sunanta Awajen. ✋ya'isa malan idan kanason Xaman lfy kadaina kushemun mata dan Wlh Zan'iya komai Akanta. Murmushi yusuf yayi nasan dai baka shan giya yazeed pls katashi daga baccin da kake Nacewa wannan karuwarce matarka. yusuf Wlh Xanmaka Rashin mutumci idan ka kara kiran matata karuwa. Sakin baki Yusuf yayi yana kallon yazeed da mamaki. Tashi mufeeda Tayi daga kwancen yayin data jawo blanket din ta tashi harararta Yusuf Yayi ta nuna batama San yanayi b, karasawa tayi wajen Yazeed ta rike hand dinshi bakin bed din ta zaunar dashi Sorry Honey barshi yace duk Abinda Zai fada Tunda kaidai bazaka fasa aurena ba. Haushi yabani Mufeeda. Sorry karka damu da Abinda yake fada. Murmushi yazeed yayi Ok dear.juyawa tayi takashema Yusuf dake daskare ido...Afusace yusuf ya fita yabar gidansu yazeed yayin da Zuciyarshi ke Saka mishi Abubuwa da dama. honey kabani gajiya da yawa fa. Sorry dear bansan Zan miki haka ba. Uhum kawai mufeeda ta fada tashiga Saka kayanta.Tashi ka maidani Toh. Bawani musu yazeed yasa rigarshi yadauki key Suka fita. Ko kallon Yusuf dake gefen wata bishiya Sunkuye da Kai basuyi ba Yaja motar Suka bar wajen.wata iska yusuf ya furzar daga bakinshi yashiga ya tada motarshi yabar wajen.
Mum dan Allah kubarni da wannan gyare gyaren Wlh ni banaso. Haba feenah bakiga bikin lokaci kadan ya Rage ba. Toh mum Nifa bason Wanda Za'a Auramun nake ba kuma miye amfanin gyaran? Dama badan Wani Amfani bane kawai dankiji dadin jikin ki ne. Turo baki feenah tayi ganin mum bazata saurareta ba. Mum dan Allah meyasa baza'a Bari Nasamu Wanda nakeso ba? Sabida ke kullum bakida Zabi feenah. Amma mum komai lokaci ne dakun bari Sai lokacina yazo. Bakida wayo Har yanzu feenah, wake kawo lokacin? Allah ke kawowa mumy. that is my daughter kisani yanzuma Allah ne yakawo lokacin Aurenki ba iyayenki bane Sukai son ransu. Amma mumy yola fa Za'a kaini ganinku ma Saina dade. Toh bakiji Ance Matar mutum kabarinsa ba, kawai kisama Ranki natsuwa feenah komai Zaizo miki da Sauki. Leemah wanda takeso Za'a Aura mata feenah kuma zabin inno. dariya maganar taba mum Sanin idan tayi Zata kara tunzura feenah yasa ta shanye dariyar. Leemah takawo Wanda takeso kekuwa idan Aka biye miki Haka Zakiyi ta Zama. keda yazeed Sha'aninku da wuya babu mai iyamuku dan haka Gara da inno tasamo mafita. Nidai mumy ba irin halina daya dashi ba ni banason ma Anacewa haka. Hakane yafiki saukin kai Kenan? Uhm mum nafishi. Murmushi kawai mumy tayi. Sallamar inno sukaji mumy ce ta Amsa yayin da feenah tabi inno da harara. Maraba inno Sannu d Xuwa. yawwa Hafsat ya gidan. Alhmdllh inno Bari Akawo miki Ruwa. Zama inno tayi tana kallon feenah. Nafisatu bako gaisuwa. Yatsina fuska feenah tayi mutum yana gidansu ma ba'a kyaleshi ba. dariya inno tayi Aure dai yazama dole Garama kitafi Chan yolan Ko zamu Sarara. kallon inno feenah tayi, tayi kwafa kinsan idan Naki auren Nan babu wanda Zai tilasta mun ko inno? Ke din waye Ai idan ina raye Amadi da Umar basu isa su tsallake maganata ba. tabe Baki feenah tayi tajuyar da kai. fadan Akeyi ko????? mum data fito daga kitchen ta fada. Wai Shakiyiyar yarinyar Nan har Yanzu batason Auren Nan. Inno daina biye mata tunda dai komai yazo karshe. kinsan kuwa Hafsa jiya dayan mara ta idon ya kwaso Wannan kafurar yarinyar wai ita Zai Aura! Toh inno badai mufeeda din nan ba ko? Ita Kuwa Hafsa bakiga irin kayan data Saka ba, kinga Rashin kunyar da takema Amadi Kuwa jiya? Inaganin Auren ne yazeed shima bayaso Shiyasa yakara kawo mufeeda din Ko inno? Wayema yasanin mishi Hafsa dan bakiga yanda jiya yake Nan da nan da yarinyar ba kamar Zai mata Sujadda. tashi feenah tayi fuuuu tabar parlon tana fadin duk tazo tacika mutum da Surutu, ko miye Ruwanta dan yakawo wacce yakeso Oho? Komai Saidai Ama mutum dole Shine daidai. Saiki dawo idan Son yazeed din kike kifada kada takasheki inno ta fada da karfi. Aikuwa kara fusata feenah tayi dawowa tayi parlon ni Allah ya Kyauta naso mai hali irin na yazeed bare Shi dakanshi, Kawai inafada miki ne kincika takurama mutane da Saka musu ido. Ke da Allah gudu Chan "tunkan ai daram Akai kwandi" yamutsa face feenah tayi tabar wajen dan batagane mai Inno ke Nufi ba. Allah ya Shiryamana yaran Nan. Ai duk kune kuka batasu Hafsat. Inno yaran dasuke ganin bamu basu kulawa ba Wai. Yoo yaranku ba'a iya musu musamman feenah da yazeed, kidai Cire Nazeer dan Albarka Mai natsuwa. Murmushi mum tayi kawai.yayin da inno tacigava da bata labarin yazeed da mufeeda.
Shirye Shiryen biki kawai Suke bangare biyun Nan. Ba karamin kudi Suke kashewa kan Bikin ba duk dacewa bawani farin Ciki yaran Nasu Suke Ciki ba. Leemah damuwarta bata wuce yanda Za'a rabata da feenah ba gashi bikinsu Rana daya babu yanda Za'ai ta Raka kawarta yola, bangare guda kenan. Adayan bangaren gaba daya Al'amarin brother dinta tsoro yake bata ganin yanzu bayajin maganar kowa saita mufeeda ga yanda gaba daya ya rame yadawo wani soko dashi. feenah ma damuwarta bata wuce Auren da za'a mata da Wanda bataso ba wanda hasalima batasanshi ba,bama Wannan ba Acewarta yolan daza'a kaita yafi bata mata Rai, Hakanan take Sukuku koda yaushe ba kwanciyar Hankali. Kausar ma Damuwar kawayenta data mijinta kadai ta isheta, dan ba karamin tada hankali yusuf yayi game da Halin da yazeed yashiga kan Mufeeda ba, kusan rabin dukiyarshi ya saudakar kanta,dan ma yusuf yana hana wasu Abubuwan su faru A boye. Kuma Zuwa yanzu yazeed yasanar da yusuf irin son dayakema feenah yakara dacewa dukda Nasan yanzu tamun nisa, tun farko Nayi Zurfin Ciki ban sanar da itaba, kuma nasan Koda nasanar da ita ba lallai tasoni ba. Lokacin da yazeed ke Sanar da yusuf Hakan ya matukar tausayama Abokin nashi dukda yasan miskilancin shi yaja mishi. Kowa mamakin yanda yazeed yakoma farar daya yake, Saidai gaba daya iyayen nasu Sun dau Abun kan cewa dan bayason Amai Aure da yar kauye ne ya koma Wajen mufeeda, dan haka Abba yace Su Rabu dashi Aure ba fashi duk Abinda Zaiyi yayi. Bangaren mufeeda kuwa duniya Sabuwa batada wata matsala A rayuwarta, wandaka kawai take da dukiyar yazeed Son Ranta, kullum tana manne dashi ta hana kowa ya rabe shi,lokaci Zuwa lokaci takan jaaa Ra"ayinshi da irin makircinta Su'aikata Son ransu Saidai duk da haka Yazeed betaba tunani yin Sex da mufeeda ba, Abinda take da muradi Kenan takasa Samu,gashi tana gudun takurama yazeed Asiri ya karye kamar yarda boka ya fada Cewa Aduk Sanda ta takurashi kan yamata Abu dole Asirin Xai iya karyewa,dan haka take kaffa kaffa. Tuni khady ta gano Asirce yazeed mufeeda tayi babu Hanyar da batabi dan karya asirin ba Abu yaki yuwuwa, gashi yanzu Seemah ta daina bata Shawara cewarta tagaji batada matsala da Abinda yashafesu. Lokacin da bikin Su leemah, ya rage Sati3 Alokacin yazeed ya Same dad din Feenah kan maganar Aurenshi da mufeeda Kamar yadda tabashi Shawara. Yanda yazeed yasanar da daddy haka dad ya mayar ma Abba firrrr Abba yace bazai Amince yazeed ya Auri mufeeda ba kuma bazai fasa Aura mishi balaraba ba. da ker dad din Feenah yasha kan Abba kan yabar yazeed ya Auri mufeeda yana ganin Hakan zaisa yazeed din yasamu natsuwa. Saida Abba ya lura Abin yazeed din da gaske ne tukun Aka tsayar da magana Kan Saidai yazeed ya Auri mufeeda tare da balaraba din.lokacin da Aka Sanar da yazeed cewa yayi ya Amince da Hakan. Haka Akacigaba da shirye shiryen biki duk dacewa Amaren basada kwanciyan hankali ba'a fasa yin komai ba. Yusuf ma daker yacire damuwa yashiga Shirye Shirye, inda yake hada musu party tare da Sanar da abokansu na nesa dana kusa. Kausar ma danne damuwarta tayi Suka Shiga hidima ita da Leemah na gayyatar kawaye. Feenah kuwa cewa tayi babu Abinda Zatayi A bikin dan haka batamabi takansu. Yanzu ne Kuma Hankalin Mamy yakara tashi game da Halin da yazeed yashiga. Maganar inno ce ta fado Mata Arai Ranar data ce. "Abu kamar Sihiri yaro farar daya yafita hayyacinshi mace daya yake gani da daraja" girgiza Kai Mamy tayi tabbas Akwai Abun dubawa Cikin maganar mamah dole Nasamu Hafsa Muyi maganar Nan. Shiryawa Mamy tayi tsafff dan Xuwa gidan Mum din Feenah yin Shawara.
0 comments:
Post a Comment