Mummy tana zaune rannan da yamma sai ga hjy munnira sam mummy bata kawo komai ba, suka zauna suka gaisa sai hjy munnira tace
"hjy takakkiya nayi, wallahi iyayen asmau sunce a dawo da ita lkcn aure yayi"
Mummy ji tayi kamar hjy munnira ta soke ta ita sam bata taɓa kawo wa cewar wai asmau zatai aure ba, ta gama sakankan cewa kaji san kai
Gyara zaman ta tayi don wannan magana ce da a za yi ta sosai asmau zata tafi bayan sun gama sakin jiki da girkin ta ai da sake
"hjy munnira ya baki taɓa min wannan maganar ba sai yau" inji mummy
"yo hjy sai na gaya miki ai kema kinsan mace ce kuma wataran dole ne tayi aure ko ba haka ba" shiru mummy tayi don kuwa zancen hjy munnira gaskiya ne
Tattaunawa suka shiga yi inda daga ƙarshe aka yanke hukunci mummy zata neman mata miji a cikin ma'aikatan gidan tunda ko taje can ma sai Allah ya haɗa ta mijin
A haka sukai sallama akan idan mummy ta samo mata mijin zata kira hjy munnira
Mummy ta tara ma'aikatan ta maza sannan ta musu albishirin akwai yarinyar da take son aurar wa cikin su ko akwai me so
"kar ku damu sadaki da kayan aure duk ni zanyi"
Kusan mutane biyar suka amsa suna so amma tunda mummy ta ambaci sunan asmau sai kowa ya janye
Mummy ba yadda batai da ma'aikatan ba amma kowa sai ya ƙi, kowa sai ya dinga kawo uzurinsa
"wa zai auri wata asmau ga baƙi ga rashin fara'a" inji driver, babu yadda mummy batai ba amma fafur suka ƙi haka ta sallame su suka watse
Duk wannan abun da ake yi asmau bata san wainar da ake toyawa ba, hankalin mummy ne ya kuma tashi don duk yadda ta ɗauki abun ba haka yake ba
Shawara ce ta faɗo mata sai ta tara ƴaƴan ta ko akwai wanda zai auri asmaun in yaso sai ta zauna amatsayin cook ɗin daga baya idan ta girma ta mallaki hankalin ta a san yadda za a yi
Bayan duK sun taru amma banda sabit wanda yake ƙasa me tsarki shida matar sa, mummy ta gabatar musu da maganar da kuma hukuncin da ta yanke na ɗaya daga cikin su ya aure ta in yaso daga baya a san abin yi amma yanzu wannan shine kawai shawara
Shiru sukai kowannen su na jimamiba wanda yake son auren asmau, da babban ɗanta tafa ra
"isma'il me kake tunani"
"gaskiya mummy bazan aure ta ba saboda kwananan zan sake aure ƴar meduguri ce magabata kawai zan gabatar a fara shirye shirye"
Ako koma kan na biyu sulaiman shima ya kawo uzurinsa, mummy tana kallon muktar ɗan ta na uku yace
"gaskiya bazan iya ba matana sun iya girki"
Tooooo faaaa abu ya taru ya haɗar wa mummy
"yanzu duk cikin ku babu wanda zai auri yarinyar nan na wani ɗan lkc haka kune son yarinyar nan ta tafi, a banza a wofi" ta faɗa ranta a ɓace
Kowannen su ɗauke kansa yayi mummy ta dinga faɗa kamar ta ari baki dukkan su suka tsuke baki can sai sulaiman yace
"mummy ai mu mun matan mu sun iya girki, ɗan autan ki ne matar sa bata iya girki ba kuma yarinyar nan kamar saboda su take zaune me zai hana ki aura masa ita"
Dukkan su suka amsa da haka ne kam shi kaɗai ne ma mata ɗaya
mummy shiru tayi tasan halin sabit da rigimar sa zata iya lanƙwas kowanne su amma banda shi,
"kun san halin sabit zan iya lanƙwasa ku amma banda sabit taurin kansa yafi komai"
"mummy ba sai ayi auren ba kafin ya dawo sai dai kawai ya dawo ya tarar da amarya" muktar ya faɗa yana d ariyar mugunta don ba ƙaramin rigima za a sha da sabit ba idan ya dawo ya tarar da ya angwance 💑
Babu yadda mummy ta iya haka ta ɗauki shawarar ƴaƴan ta dole ne ta aurawa sabit asmau kafin ya dawo in yaso idan ya dawo ayi duk waccd ayi da shi ita dai ta riga ta gama
Bata ɓata lkc ba taje ta faɗawa mijinta batun auren sabit ɗin da asmau amma bata faɗa masa dalilin auren ba
Dady sai yace
" to shikenan dama gobe zani kano ɗaurin aure sai kawai mu ƙarasa can garin su yarinyar sai a ɗaura mata tunda kince ya dawo kike son ayi"
Mummy sai taji daɗin yadda sam dadyn be yi tambayoyi akan auren ba
Aka gama shirye shiryen auren duk mutanen gidan suka dunguma sai kano auren sabit da asmau har da asmaun wacce sai a mota sannan mummy tai mata bayanin auren
Da yake da ƙuruciya a tattatare da ita sai ta yadda, lfy suka isa kano suka sauka a hotel ɗin tahir guest palace suka kwana
Kashegari suka kama hanyar azore, kasancewar ba a san da zuwan su ba don haka suna isa suka sauka a gidan me garin na fulanin
Suka gabatar da abinda ya abinda ya kawo su sam me garin be gane asmau ba sai da tayi bayani sannan ya gano ta
Nan da nan yasa aka kira kawun na tan ya zo shima aka gabatar masa da maganar auren
Mummg tayi mamaki da taji cewar basu suka tura hjy munnira ba da maganar auren suka ce musu su rabon da hjy munnira ma ta bada kuɗin aikin yarinyar har sun manta
Ko kaɗan dady be ji daɗin wannan abun ba yarinya tana aiki amma sam iyayen ta basa samun ladan aikin ta, sai da ya biya su kuɗi a madadin na aikatau ɗin ta sannan suka kuma gabatar da aurawa ɗan su asmau
Babu wani ja'inja wan mahaifin asmau ya yadda inda atake a ka ɗaura auren sabit da asmau akan sadaki mafi ƙanƙanta
Baffa wan mahaifin asmau shi aka ba sadaki amatsayin sa na uban ta, daga nan daddy ya shiga rabon kuɗi
Mutanen gari sai turuwa suke suna ƙara ƙaruwa kamar sallah ana cewa ai asamau ta je binni ta haɗu da me kuɗi
Baffan ya so su kwana amma sai suka kawo masa uzurin zasu koma ne kasancewar kashegari ake sa ran tasowar ango sabit 😂
Amma sai da suka ƙarasa gidan baffan suka ga gidan sannan suka kama hanyar kano inda suka sauke daddy a kano sannan suka kama hanyar abuja
Mummy kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ganin ta mallaki asmau yanzu asmau ta zama mallakin ta, kuma babu abinda zai raba ta da ita
```ni kuwa mmn walid nace anya kuwa sabit zai yadda ya zauna da baƙar mace amatsayin matar sa mutumin da baya son baƙi```
******************
Cikin hukuncin Allah sabit da badia suka dawo gida lfy sai da mummy ta kwaɓi dukkan ƴaƴan ta akan kar wanda ya faɗa masa maganar auren
Don haka ko daya sauka sam be sani ba hidimar sa kawai ya ci gaba tare da kwasar girkin wacce a yanzu take a matsayin matar sa
Itama mummyn ko da suka dawo bata ce asmaun ta bar inda take ba tunda auren ai kamar suna ne, don kawai asmaun ta zauna a nan wajen su
Sai da suka huta suka nutsu sannan mummy ta kira shi da matar sa badia da kuma asmau dukkan su ta tara su a falo
Sabit da badia da mummy suna zaune a kan kujera inda asmau take zaune a ƙasan carpet fuskan nan tata sam ba annuri don kuwa tasan kiran menene
Sai bayan da kowa ya nutsa sannan mummy tace
"sabit bayan ka tafi matsala ta taso ta yadda dole ne a aurar da asmau don haka sai nai mata aure"
Kallon mummy yayi
"yo mummy ina ruwana da auren ta ai aiki aka ɗauke ta kuma ake biyan ta idan zata iya aikin da auren to idan kuma baza ta iya ba ta ƙara gaba ai ba ita kaɗai ce ta iya girki ba sai mu nemi wata"
"ai kai ne mijin" tsab sabit yaji abinda mummy tace amma sai yake jin kamar kunne sa ne yake masa kuwwa
"mummy me kinace" bata maimaita ba face idƙ da ta zuba masa
"kamar naji kince nine mijin wannan abun koo" ya faɗa yana nuna asmau
"ashe kaji kuma wallahi da wasa ka sake ka furta mata kalmar saki wallahi sai nayi mugun ɓata maka wallahi sai kaga ɓacin raina tunda auren ka da asmau babu wanda zai taimaka sai kai
Tunda de duk ƴan uwanka kowannen su yana da mace biyu kuma acikin biyun akwai wacce ta iya girki amma kai kana zaune da ɗaya ɗayar ma wacce bata san darajar aure ba balle wani miji"
Faɗa mummy ta dinga yi ta inda take shiga ba tanan take fita ba tsab ta san halin sabit in tak masa lako lako sai ya watsa mata ƙasa a ido gwanda tai masa ta ruwan zafi in yaso duk a dafe a tare
Sabit shiru kawai yayi yana saureran mummy wannan shine wai a dake ka a hana ka kuka, ita kuwa badia tana zaune a gefe ta cika tayi fam kamar zata fashe wannan shine ga mari ga tsinka jaka
Ga kishiya ga kuma kushen ta da mummy take yi wai bata iya girki ba
"amma mummy duk a gidan nan a rasa wanda za a haɗa da wannan halittar sai ni" ya faɗa ran shi a ɓace kalmar nan ta daki asmau sosai wai halitta
Ɗagowa tayi ta maka masa harara sai kace ita cewa tayi tana son sa ai ko maza sun ƙare a duniya ya rage daga ita sai sabit baza ta so shi don ta fahimci ɗan renin hankali ne
"mummy kin san tsari na na mace ɗaya sannan kinsan ni ba me son mu'amala ne da baƙin abu ba balle wai ace matata ce baƙa" ya faɗi kalmar ```matata``` kamar wanda yake da kashi a baki
"gaskiya mummy da sake ya za ayi in shigo in kalli wannan baƙin abun a ɓangare na ai wannan ma sai ta saka ni in ta firgita cikin dare, in matsala bata sa zuciya ta bugawa ba wannan halittar zai sakani" ya faɗa yana ƙara nuna asmau cikin tsana
Asmau iya ƙulewa ta ƙule ƙarshe ita tunda take ba a taɓa ci mata mutunci ba kamar yadda sabit yai mata *shin wai baƙi muni ne* ta tambayi kanta
shiyasa fa ita tunda taji da wannan ɗan rainin hankalin za a haɗa ta dashi shi taji sam bata san abun amma kasanceqar bata da mafita yasa ta yadda da lamarin
Sabit ya cigaba da kushe asmau kamar ba gobe inda mummy ta tsaya ta barshi ya gama faɗin abinda yake son faɗa sai daya zage ta tas sannan yai shiru yana huci
"to in banda abin auta ai na faɗa maka dalilin auren ko ba haka ba, kuma ba wani da zai haɗa ka da asmau tana can boys quaters tana aikin ta kai kuma kana ɓangaren ta me zai haɗa ka da ita, da matar ka ta iya girki shi kenan sai in raba auren itama taje ta auri wani"
Jin cewar akwai lkcn da auren zai yi expire ne kuma ga yadda tsarin auren yake na asmaun baza ta dinga zuwa ɓangaren sabit ɗin ba ya sa shi kwantar da hankalin sa
Ya kakkafa asmaun doka na in ta ganshi ta canza hanya don baya son yana cin karo da mummunar fuskar ta sannan kar ya sake ya ga ƙafarta a ɓangaren sa duk aka gama maganar kowa ga san matsayin sa sannan mummy ta sallami kowa
Sam badia ba haka ta so ba taso ace sabit ya bijirewa mummy amma sai taga saɓanin hakan
Ko da suka koma ɓangaren su sai faɗa, wai dama ƙila ya so auren ne shi yasa ana faɗa masa ya hau borin ƙarya in da da gaskene ai da sai ya saki asmau
Yai mata bayani yai mata rantsuwa amma ina sam ta ki yarda kawai sai ya share ta yayi wucewar sa ɗakin sa shima yaje yaji da abinda ya dame shi
[4/17, 4:50 PM] 🥦: 👩🏽🍳 *menu of d day*👩🏽🍳
*brown rice served with liver and egg sauce, Apple milkshake*
*brown rice*
*ingredients*
-shinkafa
-man gyaɗa
-maggi
-curry
-green beans
-carrot
-peas
-attaruhu
-albasa
-tafarnuwa
*method*
1) ki wanke shinkafar ki tas sai ki shanya ta don ta bushe, idan ta bushe sai ki ɗauko tukunya ki zuba mai sosai sai ki saka tafarnuwa da albasa amma kaɗan
2) idan suka ɗan ɗauko soyuwa sai ki zuba shinkafar ki ki ci gaba da soyawa, kina yi kina juyawa har sai tayi brown sosai sai ki sauke ki tsane man
3) ki yanka attaruhu da albasa yankan cubes, sai ki zuba a tukunya da ɗan mai, sai ki cigaba da soyawa, idan sun dauko soyuwa sai ki zuba ruwan da zai dafa miki shinkafar ki
4) ki zuba maggi, curry thyme da duk wani seasoning da kike so, idan ya tafasa sai ki zuba shinkafar ki tafasa ɗaya sai ki zuba carrot, peas, green beans ki rage wuta, idan ya dahu sai a sauke
*liver and egg sauce*
*ingredients*
-tomatoes
-attaruhu
-albasa
-hanta
-kwai
-curry
-thyme
*method*
1) ki wanke sai yanka hanta ƙanana sannan ki tafasa ta da maggi, thyme, tafarnuwa, albasa
2) idan ta dahu sai ki sauke, ki jajjaga attaruhu, tomatoes albasa da tafarnuwa
3) ki zuba mai a kasko sai ki ɗan saka masa albasa ko tafarnuwa don yayi zafi, idan yai zafi sai ki juye jajjagen nan a ci gaba da suya, a zuba maggi a cigaba
4) minti ɗaya biyu sai ki zuba hanta a ci gaba da miya, idan miyar ta ɗauko soyuwa sai ki matsar da miyar gefe ki zuba kaɗaɗɗan kwai a gefen da ba komai ki barshi sai ya ɗauko soyuwa sai ki fara dagar gaza shi
5) idan ƙwan ya soyu sai ki haɗe shi da miya ki ɗan ƙara bata tsoro sai ki sauke sai a ci da brown rice
*Apple milk shake*
*ingredients*
1)apple
2)dabino
3)cardamon powder
4)sugar
*method*
1) ki yanka apple ɗinki ƙanana, ki cire ƙwallon dabinon ki, idan dabinon bushash she ne ki jiƙa shi
2) ki haɗa apple, dabino, cardamon powder amma kaɗan, madara da sugar sai ki markaɗa
3) ki saka ƙanƙara a jug ko cup ɗin da za ayi serving ki juye milk shake ɗin ki
👩🏽🍳 *Bon appetit*👩🏽🍳
*ASMA'UN SABIT*
[10:29PM, 5/2/2018] +234 806 399 9164: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
P⃗a⃗g⃗e⃗ 9🌹
Har garin Allah ya waye sabit da badia basu daina fushi da junan su ba, haka kowa ya shirya ya kama hanyar office cike da jin haushin ɗan uwan sa
Sai da suka dawo badia taga sam sabit bashi da niyyar lallashin ta kamar yadda yake mata ada idan sun yi faɗa yasa ta zuwa ta tsara wanka da kwalliya irin wacce sabit ɗin yake so
Sai da akai sallah magariba ya dawo daga masallaci ya zauna a falo yana kallon news sannan ta fito tana karairaya
Ɗago ido yayi yakalle ta sai ya kasa ɗauke kanta, badia ta gama karantar sa tsab wani, dai da taje har kusa da shi sannan ya ruƙo hannun ta ya zaunar da ita akan cinyar sa
"ya dai my only wannan wankan yayi da me zan biya ne" ya tambayeta yana kashe mata ido
Fari tayi da idon ta wanda ya sha lashes na kanti
"haba *SD* sai kace baka san matsalar da muke ciki yanzu bane na auren ka da wannan yarinyar" ta faɗa fuskar ta kamar me shirin kuka
Sabit jinta kawai yake yi amma gabaɗaya ta gama da shi
"yanzu don Allah *SD* na dace zama da kishiya kalle ni fa"
Ta faɗa tana miƙewa tare da jujjuya jikin ta gaban sa ta yadda zata ƙara rikiɗa shi,
"only wannan salon naki yana ƙara rikita ni, zo nan in ji ɗimin jikin ki da nai missing jiya" ya faɗa yana kai hannun sa don ya jawo ta, sulalewa tayi ta ƙara nesa da shi inda shi kuma ya koma kan kujerar ya zauna yana kallon ikon Allah
" *SD* kalle ni fa so kake friends ɗina da ƴan uwana suyi min dariya kayi min kishiya ni me kurin baza ka ƙara aure ba" ta faɗa tana jujjuga jikin ta ya yadda zai ƙara ƙare mata kallon, sabit dai yana zaune kamar mutum mutumi sai kallon ikon Allah
"only ki zo nan muyi maganar mana zan fi ganewa" ya faɗa yana me niyyar kamo hannun ta wanda ta miƙa masa sannan ta taho da cat walking sai girgiza take yi inda gaba ɗaya duk wani lissafin sabit ya gama kwance wa
Sunkutar ta tayi sai bedroom ɗin su,
Tana kwance akan gadon su inda ta rufe jikin ta da bed cover, a haka sabit ya fito daga toilet ya same ta,
"only dia na ɗauka zakiyi joining ɗina a toilet ne" ya faɗa yana goge kansa, ɗan ƙaramin tsaki taja sannan tace
" *SD* naga alamar kamar wannan auren da akai maka da sanin ka kana so shiyasa sam baka son mu samu mafita"
Ajiye towel ɗin yayi ya ƙaraso inda take zaunawa yayi a kusa da ita inda ya riƙe mata hannun ta sannan yace mata
"haba only ya zaki dinga abu kamar baki sanni ba, dia kin sam taste ɗina kin san koman da nake kin san yarinyar nan gabaɗayan ta ba taste ɗina bace
Mace me kamada namiji namijin ma kamar ɗan prison, me zanyi da ita sam bata da girly personality, kuma kin san nafi son mace me koman ta na mata ne, amma wannan kamar wani namiji fa haka nake ganin ta"
Badia taji daɗin yadda ya kushe asmau sai ta ƙara narkewa sannan tace
" yanzu *SD* yaushe zaka sake ta"
"dia kin dau ji abinda mummy tace sai kin iya girki don haka sai ki dage ki koya"
A firgice ta ƙwace hannun ta daga cikin nasa wanda hakan ya barshi da sakin baki
" *SD* kana nufin kana goyon bayan in koyi girki kenan, kuma kasan ni am not a kitchen person" riƙe ta ya ƙara yi
"na sani only dia amma kinga abinda mummy tace idan kin koyk girki mun huta nima sai ki koya min in yaso sai mu dinga sharing duty yau in kikai girki gobe sai inyi kinga mun huta da cin abincin da bamusan tsabtar wanda yayi ba ko"
Ya dinga kamale ta yana rarrashin ta har ta yadda zata fara koyon girki, suka gama haɗa plan cewar a waje zata je koyon girki ta yadda sai dak kawai mummy taga ta iya girki haba ai da ta ƙware da wannan ƴar iskar yarinyar tayi waje va sakinta kawai sabit zaiyi ba sai ta saka shi ya kore ta ma
*******************
Hjy badia ta je ta sai form a wani cooking class zata ta fara koyon girki, ranar da ta fara zuwa ta ga yadda ake abinci kamar tayi amai
Babu abinda yake tayar mata da hankali kamar nama ɗanye, tunda ta bar cooking tace bazata ƙara komawa ba saboda basu da tsabta
Sabit sam be damu ba don haka sai ya kuma samo mata wani cooking class ɗin shima duk sammakar ce wai basa wanke nama ya fita tas suke ɗaura wa
Cikin wata ɗaya sun zageye kusan dukkan cooking class ɗin da suka sani amma duk cikin su babu wanda ya iya girkin irin wanda badia take son yi babu yadda ta iya haka ta haƙura da koyon girkin
Sabit ne ma ya dinga matsa mata akan ta kuma dubawa, ko da faɗa masa matsalar ta na ƙyanƙyamin naman da basa wankewa sai yace mata
"me zai hana ki nemi wannan yarinyar ta koya miki kinga ita ta ƙware kuma daga gani tana kula da tsabtar abincin ta"
Sam badia bata yadda da wannan shawarar ba ai bada kaine ma yarinyar da aka aura mata mijinta itace zata ce ta koya mata girki ai ta faɗi ƙasa ba nauyi
Ƙiri ƙiri tace bata yadda ba inda daga karshe har ta kai su da faɗa wai sabit yanzu ya fara son asmau, shi kuma ya dinga rantse mata ba abinda yake haɗa shi da ita, faɗa sukai da gaske
Ganin sabit bashi da niyyar sakkowa ne ya sa badia shiryawa domin zuwa wajen asmau koyon giki ```tirƙashi koyon girki wajen kishiya amma an faɗi ba nauyi```
Asmai tana zaune ta gama lunch kenan duk an rarraba kowane ɓangare tana shirin hutawa kenan sai taji wata yarinya asabe da ke aiki a kitchen ɗin gidan ta shigo
"anty asamau wai inji wannan farar matar me iyayi tace kije" tsayawa nayi ina tunanin wace farar mata ce ko dai mummy ai asabe ta san mummy
Tashi nayi na ɗauko hijabi na na fito, ina fitowa naci karo da badia sai wani yatsine fuskar tar take yi kamar wacce taga kashi
"ke da a wannan ƙazamin wurin kike mana girki kina aiko mana da shi, meye amfanin ɗauko ki aiki ko ba biyanki ake yi ba, don me yasa baza ki dinga sakawa ana gyara wajen ba" ta faɗa
Ƙarewa wajen kallo nayi babu abinda ya same shi yanzu yanzu nan suka gama share wa amma ƴar rainin hankalin nan zata wani ce wai datti
Samun gefe tayi ta kyafe sannan tace
"ki dauko tsintsinya ki ƙara share wajen don nazo ne zanyi wa sabit girki bazan iya ciyar da mijina abincin da aka dafa a wannan ƙazamin wurin ba"
Ban ce mata komai ba kawai nai shigewata ciki nai kwanciya ta har yanzu bata san wace asmau ba bata san ko wannan koɗaɗɗan mijin natan bai isa ya sani ba balle ita
Ganin na daɗe ban fito ba ya sata shigowa ɗakin ganina a kwance ya sata fara masifa
"lallak ma yarinyar nan kinci kin ƙoshi shiyasa har na saki aiki amma kika ƙi yi"
Iskar data kwaso ta ma ban shaƙa ba balle ita, masifa ta dinga yi tana gaya min magana wai ƴar ƙauye ta zo birni, ganin bazan iya shiru ba yasa nace mata
"to wai in girki zakiyi na ɗauka part ɗin ki ma akwai kitchen meyasa ba zakiyi a can ba" na faɗa kaina tsaye
Masifar dai ta ci gaba da yi kamar ba gobe sai da ta gama sannan ta ɗauko wayar ta ta fara dailing
Ana ɗauka na ga tafara magana
" *SD* ai ma faɗa maka yarinyar nan ƴar rainin hankali ce kagan ni a kitchen ɗin amma tana kwance sam ban san me take nufi ba" ban san me yace mata ba sai kawak ganinai ta miƙo min wayar
Daga ita har wayar na doka wa wata harara sannan na kuma mai da kaina na gyara kwanciyata ta,
Wani zagi na ji ta ɗura wanda sai da na toshe kunne na saboda tsabar girman sa
" ikon Allah *SD* wallahi ta ƙi karɓa," ban san me ya faɗa mata ba sao dai naji ta kashe,
Intercom ɗin da ke kitchen ɗin aka kira ban da niyyar tashi sai dana ga dama har ta kusan tsinkewa sannan naje na ɗauka, ashe mummy ya kira shima mummy's boy 😁
Ana take gaya min wai in koya wa badia girki ban musa mata ba kawai dai na dawo nace wa gwanar ta zo muje kitchen ɗin
Dagewa tayi wai bazai tai girkin ba har sai na saka yara sun ƙara gyara kitchen hmmm lallai baki san wace asmau ba na faɗa, neman wuri nayi na kuma kwanciyata
sabit ta kuma kira ta kuma faɗa masa ai na kuma kwantawa shi kuma ya kuma ƙara kiran mummy ko da mummy ta kira tsab nai mata bayanin abin da ke faruwa bata ce ko mai ba kawai ta kashe wayar
Allah ne kaɗai yasan me tace aa sabit ɗin sai gashi ya kira ta wai muyi girkin a haka wannan abun ya bala'in ɓatawa badia rai
shigewa tayi kitchen ɗin inda na bita a baya don fara girkin fatana dai Allah yasa har mu
gama bamu ƙona kitchen ɗin ba don na fahimci ƴar rainin wayo ce to nima duk all d same ne ai
*Parpesun naman kaza zatai masa da jollof rice sai cole slow da kima fruit salad* ```recipe yana ƙarshen page ɗin in shaa Allah```
Ita me koyon girkin tana zaune akan wani stool na kitchen ɗin nice nake komai, naman kazar nan an wanke shi ya fi so goma
Ni dama tunda na wanke tace be mata ba sai na dangwarar mata da shi,
"kiyi irin wanke war da kike so idan kin gama na ɗaura" na faɗa mata na cigaba da haɗa ragowar abincin
Asabe ta kira ta sata ta wanke hannun ta yafi a ƙirga sannan ta saka ta wanke naman
Idan ta wanke sai ta kawo mata da ta kalle shi sai tace
"je ki ƙara wanke wa har yanzu be dena ƙarni ba" lallai manya na girki nace a raina
Girkina kawai nake tayi amma ita uwar iyayin tana can a kan kaza har na gama jollof ɗina da taji kayan lambu ba a gama wanke kaza ba 🤔
Komawa gefe nayi ina kallon ikon Allah duka an gama wanke zaƙin kazar ma ko wane zaki zatayi oho, sai da ta gaji don kan ta sannan tace a bani in tafasa ta, duk wannan fa acikin koyon girki ne lallai mata nada aiki a gaban su
Tafasa ɗaya kazar tayi duk na gama haɗa mata kayan ƙamshi sai tashi suke yi amma baiwar Allah nan abinda zai fito daga bakin ta shine
" ki kashe gas ɗinnan ki sauke kazar na ki ƙara wanke ta sai ki mayar da ita don wannan ƙarnin natan in ba an kuma wanke ta ba bazai rabu da ita ba"
Matsawa nayi na bata wuri sannan nace mata
"zo ki sauke ni bana taɓa abu idan yana tafasa aljanuna basa so" tsorata tayi sai kuma tai gum da bakin ta
Sai can ta kira asabe wai asabe ta sauke, ganin yarinyar zata cutu ya sani na sauke da kaina a guje ta fice daga kitchen ɗin wai kar aljanuna su tashi da ita
Tukunya kawai na canza na ƙara kayan haɗin na ƙarasa kazar sai da aka gama tas sannan ta shigo ta saka yaran wajen binta da abincin part ɗin ta ina jinta tana kiran mijin wai ta gama amma fa ta wahala ashe girki da wuya
Ban san me yace mata ba naji dai tana dariya sannan tai masa fatan dawowa lfy sukai sallama ni dai asmau nace to ayi dai mu gani in man kitso zai soya ƙosai
👩🏽🍳 *menu of d day*👩🏽🍳
*chicken pepper soup, jollof rice served with cole slaw, fruit salad*
*chicken pepper soup*
*ingredients*
-chicken
-attaruhu
-albasa
-thyme
-curry leaves
-lawashin albasa
-green pepper
-maggi
-tafarnuwa
-egg
*method*
1) a wanke kaza sai a saka ta a tukunya a saka curry leaves, thyme, maggi albasa da tafarnuwa sai a rufe a barshi ya ta tafasa, a sakar mata ruwa
2) ki jajjaga attaruhu da da albasa, idan kazar ta ɗauko dahuwa sai ki zuba attaruhu ki ɗan ƙara maggi sai ki rage wuta ki rufe
3) ki yanka lawashin ki da koren tattasai sai ki kaɗa kwai ki ajiye
4) idan kazar ki ta dahu sai ki buɗe ki zuba ruwan ƙwan amma ki taɓɓatar da ruwan yana tasafa, kar ki juya
5) idan kwan ya dahu sai ki zuba lawashin da kika yanka ƙanana da koren tattasai ki rage wutar gabaɗaya ki rufe, idan ya dahu ki sauke ya kasance yana da ruwa ruwa
*JOLLOF RICE SERVED WITH COLE SLAW*
*ingredients*
-rice
-tomatoes
-attaruhu
-albasa
-tin tomatoes
-stock fish
-nama
-maggi
-curry
*method*
1) ki gyara stock fish a cire duk dattin da kashin sannan a jiƙa shi a ruwan zafi
2) ki tasafa shinkafar idan ta tafasa (per boil) sai ki sauke ki wanke ta
3) ki wanke naman da stock fish ɗin ki sai ki zuba a tukunya ki zuba maggi tafarnuwa da albasa ki rufe
4) idan ya tafasa sai ki markada, sai ki sauke ki juye, ki zuba mai a tukunya da albasa da ƴar tafarnuwa don ya ɗan soyu,
5) ki markaɗa tomatoes da attaruhu da albasa sai ki zuba akan man nan, idan ya tafasa sai ki juye naman nan da stock fish ki barshi ya tafasa
3) idan sun tafasa sai ki ɗan ƙara ruwa kaɗan ki zuba tin tomatoes, curry ki ƙara maggi in be ji ba sai ki zuba shinkafar
4) idan shinkafar ta ɗauko tsotsewa sai ki yayyaɗa mata yankakken green pepper da kuma lawashin albasa sai ki rage wuta ki rufe ya dahu sai ki sauke
*coleslaw*
*ingredients*
-cabbage
-carrot
-peas
-green beans
-kidney beans
-egg
-mayonnaise
1) ki haɗa kayan veges ki wanke ki gyara duk ki yanka na yanka wa ki haɗe su waje ɗaya, ki yanka da daffaffan ki ki haɗa ki zuba mayo ki juya ki serving
*PS* ki tabbatar da veges ɗin sun tsane in so samu ne ma su bushe kafin a zuba mayo ɗin
*fruit salad*
Ingredients
-kankana
-gwanda
-abarba
-ayaba
-sugar syrup ( ki tafasa ruwa da sugar idan sugan ya narke sai ki sauke ya huce)
-foster clark (pine apple and ginger flavour)
*method*
1) ki gyara fruit ɗinki ki yanka su ƙanana amma banda ayaba
2) idan kin yanka su sai ki zuba sugar syrup ɗin ki, sannan ki zuba foster clark a cup ki ɗan zuba masa ruwa sai ki juye a salad ɗin ki zuba flavour indan kina so ki saka a fridge
Idan an tashi serving sai a yanka ayaba akai a ci
👩🏽🍳 *BON APPETIT*👩🏽🍳
*ASMA'UN SABIT*
[10:30PM, 5/2/2018] +234 806 399 9164: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
*ina jidda mmn surayya nayi breaking record ɗinki ko 💃🏼💃🏼💃🏼 to ga page nan naki ne u alone, zan ce miki naji daɗin ciran tutar nan taki 🏳 zan maƙala shi a goshina har in gama littafin nan jzk ga page nan naki ne dedicated to u sannan recipe ɗin ƙarshe da fatan za a birge bbn surayya da shi na gode*
*Hishma ya karatu nace kije school kiyo yo karatu kizo mu raba ilimin 🤣 don inji daɗin rattabo wani sabon littafin bayan wannan*
P⃗a⃗g⃗e⃗ 10🌹
Ko da sabit ya dawo da daddare yayi wanka ya shirya badia ta gabatar masa da abinci ci yayi har da santin sa
Girkin badia kamar girkin yarinyar can, inji
"gaskiya only ban taɓa sanin cewar u r gifted ba sai yanzu, girkin ki na farko kamar wacce ta ƙware, kina nufin da kanki ki kai wannan girkin"
Rausayar da kanta tayi tare da yin fari da wannan fake lashes ɗin da ta saka sannan tace
" haba *SD* ya za aiyi ince maka ni na yi amma ka tsaya ka na tambaya ko kana ganin kamar bazan iya bane"
Shiru yayi kawai ya kai lomar rice yana ƙara gyaɗa kansa, matsalar girkin ɗaya taste ɗin abincin yarinyar yake yi, ya riga ya saba da cin girkin asmau don haka duk lkcn da ya ci abinci in ba nata bane ya sani sannan baya wani ƙoshi
Amma wannan kamar ita tayi, ko dan ita ta kowa only ɗin nasan shiya sa girkin na only ɗin yake tasting kamar nata
Kai amma in only ɗin shi ta iya irin wannan girkin me daɗi taste ai ya gama more wa ```ni kuwa mmn walid nace ko ina ra'ayin shi na rashin damuwa da macen da bata girki ba oho```
Tas ya cinye abin sa yana ta santi, ita da yake mara kishin kai ce sai ta dinga yi masa dariya a ɓoye
Haka badia ta cigaba da zuwa wajen asmau koyan girki amma tun lkcn da ta je sau ɗaya taga ana yi bata kuma zama a yi agaban ta ba, sai dai ta ɗauki waya tai ta chatting in an gama ta sa a ɗauko mata a kawo mata part ɗin ta
Ana haka badia ta kuma samun ciki, wannan cikin da tsirfa ya zo ga kwaɗayi, don haka sai aiki ya kuma ƙarar wa asmau
Wani sabon salo ma da suka ɗauko shine wai asmaun ta dinga zuwa part ɗin sabit ɗin tana aiki don yanzu badia baza ta iya ba
Mummy ce da bada wannan umarnin, ƙiri ƙiri asmaun tace gaskiya bazata iya ba ita girki kawai zata yi amma sai mumy tace ko taje tafara aikin ko a sallame ta gaba ɗaya
Ganin cewar bata da tsuntsu bata da tarko ya sa ta haƙura amma da ta tara kuɗin da tasan zasu ishe ta yin rayuwar ta zata bar gidan
Ranar da ta fara zuwa part ɗin taga abu, im banda ƙarnk babu abinda falon yake yi, haka ta tsiri gƴara sai yamma ta gama, ɗakin su falo kitchen, toilets ɗin ma kamar an shekara ba a wanke ba saboda tsabar dauɗa
Kallon gaye take wa sabit ɗin amma tunda ta zo ta ga irin wurin da yake sai ta rena masa ashe ma ƙazami ne ta faɗa a ransa
Sabit sai yamma ya dawo yadda ya ga part ɗin nasa ya canza ya sa yaji daɗi a ransa, kitchen ɗin ya kira ya buƙaci asmau ta zo, ƙin zuwa tayi sai da ya kira mummy ta kira ta sannan ta tashi ta shirya ta je tana shiga falon ya hauta da faɗa
"ke wai don ubanki ba biyanki nake yi ba da zan ce ki zo kiƙi zuwa har sai na kira mummy sannan zaki zo" fuskar nan tata da kullum take a cunkushe ita ta ƙara cusheta kamar wacce bata taɓa fara'a ba wannan abun shine yake ƙara ingiza sabit yake kuma ƙara tsanar ta wai ace mace sam a lamarin ta ba fara'a
sai da ya gama zage ta tas sannan ya saka aiki wai ta haɗa masa dinner, cikin kitchen ɗin ta shiga ta haɗa masa taliya me ruwa sosai ta kawo masa
yana buɗewa yana gani. abinda ta dafa ya antaya mata shi a jikin ta, wani irin ihu ta saki inda ta fara sosa hannun ta da ƙafar ta daya ƙone
"don ubanki ance miki ina cin taliya ne kin taɓa ganina na ci taliya, tashi kije ki kuma dafo min wani abun useless kawai"
duk dakiya irin na asmau sai da ta tsorata da lamarin sabit, ta ɗauke kayan jiki na ɓari tayi hanyar kitchen,
tana shiga ta rushe da kuka, ita sam bata ma san me zata dafa masa ba, ga hannun data ƙone da shi sai raɗaɗi yake mata
Jin takun shi tayi wanda hakan ya firgitar tar da ita ta ɗauki tukunya tare da zuba ruwa tana shirin ɗorawa a kan gas,
"me zaki dafa min" ya faɗa da husky voice ɗin nan nasa
"doya da miya" ta faɗa a firgice, wani ɗan iskan kallo ya watso mata,
"kinga alamar ina cin doya ne, wai me yasa ke daƙiƙiyace, tun ɗazu nake jin yunwa amma ki bani abinci abun ya gagara sai kace ba biyan ki nake yi, shike nan dafa min doyar amma bana son miya ki kawo min ita haka gaya"
Abin yai mutuƙar bata mamaki amma kuma sai ta dafa masa
Tana gamawa ta juye a plate ta fita, yana zaune yana shan furar sa, ta ajiye masa
"je ki ɗauko min abin kwashe sharar can, (parker)" bata kawo komai ba ta tafi ta ɗauko masa
Tai mamakin da taga ya juye doyar akai, sannan ya miƙe ya zare belt ɗin jikin sa, guda ɗaya ya sakar mata tai wani tsalle ta dire sannan yace mata
"oya maza ɗauki doyar nan ki cinye ta a haka in ba haka ba wallahi yau sai dai gawar ki" ya faɗa yana gyara belt ɗin hannun sa
Kallon doyar tayi wacce take a cikin parker idon ta na hawaye ta ɗauka ta dinga cusawa ba miya ba ruwa haka ta dinga cusa doyar tana rawar jiki
Gashi a ƙoshe nake, gani ba masoyiyar doya ba, ga doya ba miya haka azzalimin nan ya dinga saka ni ina ƙasimar ta ina haɗiya da kyar ga belt a hannunsa
Amai ne naji yana taho min inda na fara yunƙurin yinsa, saukar belt kawai naji a bayana wanda ya kuma saka ni tsalle tare da haɗiye wata ƙatuwar doya wacce ban tauna ba
"idan kika sake kika min amai sai na karya ki, daga yanzu idan na kuma buƙatar abinci daga gare ki kika kuma kawo min abinda bana ci zaki ga abinda zan miki, da wata fuakar ki kamar ta aljanu baƙa ƙirin" ya faɗa
Sai dana cinye doyar nan tas sannan ya saka ni dafa masa tuwon shinkafa miyar kuɓewa ɗanya
Ba ni na gama girkin ba sai ƙarfe 02 :54am na tsakar dare duk na gaji har wani dishi dishi naƙe gani saboda tsabar baccin da nake ji
Ina fitowa baya falon kuma ƙofar falon a kulle take da mukulli, na rasa yadda zanyi, ɗan zama nayi a ƙasan tiles ɗin falon don injira fitowar sa har bacci ya kwashe ni be fito
Ruwan sanyi kawai naji ana zuba min ina cikin bacci na a zaune wanda ya farkar dani
Bayan ruwan zafin nan sai naji an take min hannu na dana ƙone wani zafi daya ziyarce har sai dana kusa yin pitsari
Kukan azaba na saki tare da riƙe masa ƙafar daya take min hannun nawa ina roƙon ya ɗaga min hannu na
"waya baki damar yin bacci ko an gaya miki bayi nayi bacci ne ba tare da izinin iyayan gijin su ba" ya faɗa yana ƙara take mata hannun nata
Kuka na saki sosai tare da yiwa wannan mutumin Allah ya isa, sai da ya gaji don kansa sannan ya ɗaga min hannun wanda naji kamar an min gafara
"kuma ki haɗa min breakfast" ya faɗa yana wucewa, kuka na saki kamar ba gobe, na miƙe na wuce can inda nake da zama BQ kenan
Sallah na farayi sannan na fara haɗa breakfast yanzu tsoron sabit nake ji ban taɓa tunanin akwai mutum daya iya zalinci ba kamar sabit
Sai da na haɗa breakfast aka rabo kowanne part sannan na samu nutsuwar duba ciwo na, ya kunbura, ga raɗaɗi da azaba da yane min
Hawaye ne kawai naji suna zuba daga idona masu zafi, wai sai yaushe zan samu ƴan cin kai ne, yaushe ne nima zan san jin daɗin a duniyar nan
Magani ma samu na saka a hannu na inda na ƙone da ƙafata, sannan na samu na kwanta, ban daɗe da bacci ba naji call ɗin intercom ɗin kitchen
Kasancewar bani kaɗai bace yasa na share kawai, ganin sai ringing take tayi ba a ɗauka ba ya sani miƙewa na je na ɗauko, sabit ne jin muryar shi sai daya sa zuciyata bugawa
"ina asmau" ya tambaya da muryar nan tasa me rikita min ƴaƴan hanji
"nice" na faɗa jiki na a sanyaye
"na fahimci har yanzu baki yi hankali ba, iskancin da ke kanki har yanzu be ragu ba kizo part ɗina ina jiran ki yanzu kika ɓata min lkc zaki san sauran"
Katse wayar yayi kafin in masa complain ɗin hannun nawa, hannun nawa na kuma dubawa yadda yake shirin chaɓewa inban yi hankali ba
Hijabi na kawai na ɗauka nayi part ɗin nasan ina takaicin wannan rayuwa, ina shiga yana ,zaune shida sahibar tasan suna kallo
Da sallamata na shiga sallamar da ba wanda ya amsa min kamar ba musulmai ba
"shiga kitchen kiyi mana abinci" ya faɗa ba tare da ya kalli inda nake ba
"hannuna ciwo yake, ƙonewa nayi in ban kula da shi ba sai ya fara ruwa"
"Muga hannun" ya faɗa kamar gaske, nuna masa nayi sai ya miƙe ya shiga kitchen sai gashi da wata baƙar leda
"nannaɗe hannun ki da wannan ledar sai kiyi mana girkin bana son cin ƙazantar ki" ya faɗa saboda tsabar mugunta
Hawaye ne ya fara zubar min na karɓi ledar zan fara ƙullawa a hannuna sai naji badia tace
" gaskiya *SD* bazan iya cin abincin da yarinyar nan tayi ba yama nake cin abincin ta balle kuma da wannan jagwalon a hannun ta" ta faɗa fuska a yatsune, sallamat sukai inda nai ta wa Allah godiya don ina da tabbacin idan na cigaba da girki akai akai ciwon zai iya kuma chaɓewa
Ina fita daga nan part ɗin mummy na nufa na gaya duk abinda ya haɗa mu da shi, kallo na tayi sannan tace
"to in banda abin asmau ai *AURE BAUTA* ne, duk abinda kika ga ya faru a cikin aure ki tabbatar yana daga cikin ƙaddarar ki sannan bauta kike yi kije kiyi ta haƙuri har Allah ya kaimu lkcn da badia zata gama koyon girkin ta sai a raba ku amma yanzu biyayya shine naki"
Wani baƙin ciki ne ya zo ya maƙale min a ƙirjina wato *AUREN BAUTA* ke nan nake yi, na zama baiwa kenan, na yadda duk *AURE BAUTA* ne amma ba irin wannan bautar ba
Ganin bani da wata mafita yasani tafiya ɗakina na kwanta ina me roƙon Allah ya saka min da gaggawa
******************
Bikin isma'il ne ya taso inda zai yi aure a maiduguri ta uku ce, sai shirye shiryen tafiya suke yi harda mummy balle kuma ƴan uwan sa
Buri na da fatana ace sabit ya bar gidan don yanzu wata baiwar ba tafi ni ƴanci indai aka ce sabit yana gidan, mugunta kala kala yake gwada min kamar wani mara imani
Banda wahalar gyaran part ɗinsa da ya zame min tilas kullum don matar sa tana da ciki mtssss
Ranar friday da yamma suka shirya domin zuwa maiduguri biki inda shi angon ya rigasu tafiya tin da safe, wannan uban rigimar ina kitchen yasa aka kira ni sai dana bushi iska sannan nazo
Abinda ke haɗa mu da sabit kenan ya fi san daya kira ni in zo ni kuma gani da shegen taurin kai, kusan kullum da muguntar da zai gwadamin amma gobe bazan daddara ba
Ina shiga sai da sha ruwan takalmin sa ya doddoke ni da takalmin sa ni kuma na bishi da Allah ya isa a zuciyata
sannan ya sani gyaran kayansa sai kace wata matar sa ooops na manta ashe da aure tsakanin mu ko, sai da na gama haɗa masa kayan sa sannan ya sani fitar masa da akwatin
Kinkimar akwatin nayi na fita ina ja da ƙyar, a ƙofar get ɗin gidan naci karo da daddy har ƙasa na durƙusa
"daddy ina kwana" sai daya kalle ni ya gama ƙare min kallo sannan yace
"kar dai matar sabit ce wannan" ya faɗa yana nuna ni, mummy da ke gefe ta murmusa sannan tace
"itace asmau kenan ƴar baiwa" murmushi yayi yana gyaɗa kansa irin nasu na manya, a wannan lkcn sabit ya ƙaraso
"sabit kasa matar ka ta haɗa kayanta sai muyi tafiyar da ita tunda a hotel zamu sauka kaga itama taga gari" sam ban kawo da ni ake ba shima sabit ɗin sam be kawo ni ba ya ɗauka badia don haka sai yace
"daddy ai bata jin daɗi kuma dr. yace ta daina nisa da gida" kallona daddyn yayi sannan yace
"asmau me ya same ki" ɗagowa nayi na kuma kallon sa sannan na girgiza kai alamar ba komai, kallon sabit yayi sannan yace
"kace bata da lfy" sai a lkcn na gane wai dani da yake shima sabit ɗin sai a lkcn ya gane
"a a daddy ba sai naje ba anty badia bata da lfy ni nake kula da ita" na ƙarashe zancen
"zancen banza kenan kishiyar ki zaki kula da ita ko mijinki, maza kije ki haɗo kayanki muna jiran ki"
Kallon sabit nayi wanda ya haɗe ransa kamar an aiko masa da mala'ikan mutuwa sannan na duƙar da kaina mummy ce naji tace
"muje in taya ki haɗa kayan nakin" ƙafafu wana a sage na ja su sannan na bi bayan mummy a zuciyata bace dady ka ba sabit license ɗin cin ƙwal ubana
👩🏽🍳 *menu of d day*👩🏽🍳
*yam balls, potato pancake, fish cake*
*yam balls*
*ingredients*
-yam (doya me gari tafi daɗi akan me danƙo)
-eggs (dafaffe da ɗanye)
-attaruhu
-danbun nama ko kifi
-albasa
-curry
-maggi
-garin bushash shen burodi
*method*
1) ki fere doyar ki sai ki ɗora ta a wuta ki bi ta da sugar da gishi, sugan ya ninka gishirin yawa
2) bayan doya ta dahu sai ki sauke ta ta huce, ki ɗauko wankekken turmin ki ki zuba albasa da attaruhu ki jajjaga sai ki kwashe a roba
3) ki zuba doyar itama ki daka ta ba kirɓawa ba ki farfasa tasai ki sauke ki haɗe da kayan attaruhun
4) ki zuba maggi da curry danbun ki sai yanka ƙwai ƙanana a ciki ki ƙara sai ki duddun ƙula kamar ball 😁 Kamar fuskar na
5) ki zuba mai a kasko ki dan saka albasa sannan ki barshi ya huce, ki fasa ƙwai a roba ki zuba maggi da albasa isashshe sannan ki kaɗa
6) ki dinga ɗaukar ƙwallon doyar kina sakawa a garin burodin kina tsomawa a ruwan ƙwai sannan ki soya har sai yayi brown sai a kwashe a barshi ya tsane
*potato pancake*
*ingredient*
-dankali
-albasa
-attaruhu
-maggi
- mai
*method*
1) ki fere dankalin turawan ki sannan ki gurza shi, itama albasar ki gurzata
2) ki jajjaga attaruhunki sannan sai ki haɗe da dankalin da albasa sai ki saka maggi, idan yayi ruwa dayawa sai ki ɗan ɗaure da flour, (ni dai nafi amfani da potato flour)
3) ki zuba mai a kasko idan yayi zafi sai ki zuba kullin dankalin ki ki soya idan ɓangare ɗaya yayi brown sai ki juga ɗayan idan ya soyu sai ki sauke
*fish cake*
*ingredients*
-kifi (kowane iri ne)
-shrimps
-squid
-attaruhu
-albasa
-maggi
-mai
-flour da corn flour
*method*
1) ki gyara kifinki ki cire ƙaya in me ƙayar ne, ki gyara shrimps da squid sannan ki saka su a food precessor ɗin ki, ki haɗa da albasa, attaruhu, corn flour da flour sai ɗan mai kaɗan sai ki rufe ki kunna
2) idan baki da food processor, sai kiyi blending kifin da shrimps da squid, albasa attaruhu ɗin sai ki juye a roba sannan ki haɗa kayan flouɗ ɗin da maggi da ɗan mai
3) in babu blender sai ki tafasa su sannan ki daka su kafin ki haɗe da kayan flour ɗin
4) kaɗan zaki saka flouɗ ɗin yadda dai kwaɓin zai ɗinga danƙo a hannu bi ma'ana ya dinga kama hannu ba da tauri ba
6) bayan kin gama haɗa komai sai ki zuba mai a kasko sannan ki dinga ɗiba kina sakawa a cikin man kina soyawa har ya soyu sai ki kwashe
👩🏽🍳 *BON APPETIT*👩🏽🍳
*ASMA'UN SABIT*
[10:29PM, 5/2/2018] +234 806 399 9164: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
*ina masu cikin mu 🤰🏻🤰🏻da mmn .....reeda da real me ........... Ban kama suna ba 🤣🤣🤣 duk ina muku fatan sauka lfy*
Page 11🌹
Part ɗin mummy muka je itace ta bani ƴar ƙaramar jaka, sannan na wuce ɗakina, kayana na haɗa sannan na fito zuciya ta sai dukan uku uku take na san akwai rikici tsakanin mu da sabit
Motar da mummy take ciki nan na shiga kusa da mummy na zauna na tsuke fuska don kar ace in fita in koma motar da sabit yake, ilai kuwa sai sulaiman wansa yace
"asmau ki fito ki zauna kusa da mijinki don daddy ne ze zauna" kau da fuska ta nayi kamar banji ba har daddyn y ƙarasa sai yace
"ke me kike yi anan ga mijinki can ya shiga waccen motar maza wuce kije wajen mijinki ni ma ki barni da matata" kunya ce ta kamani na tashi na fita daga motar na wuce motar da sabit yake zaune
Shi kaɗai ne a bayan motar, rasa ina zan shiga yayi, gaban motar zan shiga ko bayan motar,
"bazaki shigo bane ko so kike a zauna ai ta jiranki gimbiya" sabit ya faɗa cike da takaici, kusa da shi na shiga na zauna inda ya matsa can ƙarshen sai kace wacce zan goga masa cuta
Muka fara tafiya, har muka je airport ba wanda ya tanka wani, muna sauka na gudu wajen mummy ni wallahi yanzu sabit tsoro yake bani
Private jet ɗin daddy zamu shiga don haka babu wani ɓata lkc ko duba passport, muka hau, ina shiga na fara dibi dibin gurin zama, muryar daddy naji yace
"sabit kama hannun matar ka ka zaunar da ita kusa da kai naga kamar first flight ɗin ta ne"
Jinayi cikina yai ƙululu ban ankara ba naji ta damƙi hannu na, tare da matse min shi yacca har ƴar ƙara na saki
Sakin ƙarar ne ya shi take min ƙafa wanda zafin takalmin nan nashi kamar na ƙarfe ya shige ni kamar an ɗaura min dutse a kafar
Toshe baki na nayi inda wasu hawayen azaba suka fara sauka daga cikin idona, jaa na yayi ya zaunar dani a kan kujera sannan ya fara kiciniyar saka set belt ɗin sa
Har lkcn ban dawo daga duniyar zafin takanin da yayi ba don haka sam ban ma san ana saka wani belt ba
Sai da mummy tace "sabit asmau kuwa ta saka set belt" sannan na lura da cewar ana sakawa
Yunƙurowa yayi jikina domin ɗauko set belt ɗin inda ya saka gwiwar hannun sa a kan cinya ta tare da danna na gwiwar sa
Cinyar tawa kamar zata tsage don azaba haka naji wani irin kuka na saki wanda hakan ya janyo da hankalin duk wani wanda yakd cikin jirgin
Daddy ne ya fara tambayar lfy, kafin in bude baki ba tuni sabit ya yi magana
"daddy wai tsoron flying take ji" sakin baki nayi ina kallon babban mutum da ƙarya
"karki damu asmau ga mijinki a kusa da ke ba abinda zai same ki, kai kuma ka lallashe ta" daddy ya faɗa cike da kulawa sannan ya juya
Kukana na cigaba tare da yi masa Allah ya isa, mintsini na kuma ji ya mannara min cizo sosa wurin na kuma yi tare da ƙara furta kalmar Allah ya isa da ƙarfi Ƙwafa yayi sannan yace
"zaki gane kuren ki idan mun sauka zaki san baki wayo"
A haka flight ɗin ya tashi, don tsoro gaskiya na tsorata amma sai na dake don bana son wannan ɗan rainin sence ɗin ya samu damar ta
Lfy ƙalau muka sauka a maid. daga nan motoci suka kuma zuwa ɗaukar mu wannan karan da sauri na shiga kusa da mummy sannan na kyafe, ko da daddy ya zo sai be ce infita ba sai kawai ya shige gaban motar har yana tsokana ta wai yaga nafi sabawa da mummy akan sabit, murmushi kawai nayi na jin kunya
A wani hotel muka sauka inda bayan an kai mu ɗakunan da muka kama, nayi mamaki ko ince nai takaicin da aka ce wai ɗaki ɗaya zamu ɗauka da sabit 🙆🏼♀
Ai nasan cewar na kaɗe daga ni har ganye na, Muka shiga ɗakin yana ɗan girma sosai, muna shiga ya faɗa banɗaki, ni kuma na samu wuri na ajiye jaka ta sannan na ɗan rakuɓe na zauna, bai daɗe ba ya fito da towel a jikin sa daga gani wanka yayi
"oya maza tashi ki shiga toilet ɗin nan ki zauna a ciki ko kina tunanin tare zamu zauna a nan ɗaki da ke, ai rayuwar banɗaki zakiyi"
Sam ban fahimci abinda yake nufi ba sai dana ga ya hankaɗa ni cikin toilet ni da jakar tawa sannan na fahimci ashe a toilet yake nufin zan zauna yau naga ta kaina Kan toilet sit ɗin na koma na zauna na zuba uban tagumi ina kallon ikon Allah, rasa yadda zanyi nayi, ƙarewa toilet ɗin kallo nayi yana da ɗan girma ba laifi,
Bath ne babba sai sink sai toilet sit, sai ɗan space haka
Zama nayi na zuba tagumi da na gaji da zaman sai na ɗauro alwala, na fito duk dai jarabarsa ai baze ce in sallah a toilet ba ko Yana yana gaban laptop ɗin sa yana ta danne
Ƙarasowa nayi ɗakin sannan na tsaya ina tunanin ina ne gabas, ɗago kai yayi yana kallo na inda ni kuma nayi kamar ban ma san yana yi ba
"uban me ya fito da ke bana ce ki zauna a toilet ba" ya faɗa fuskar nan tasa a murtuke
"naga alamar kina son zama kusa da namiji Allah dai yasa ba kin saba bin su bane shiya duk inda nayi kina biye da ni, inda wata macen ce me kunya yadda ta ganni daga ni sai gajeren wando ai kunya zata ji amma ke ko a jikin ki"
Kallon shi kawai nayi wani takaici ya rufe ni
"sallah zanyi ko itama sallah inyi ta a banɗaki ne" na faɗa kaina tsaye
"ni na isa ince kiyi sallah a toilet kije can kiyi amma kina idar wa ki koma toilet don bazan iya zaman ɗaki ɗaya da ke ba, naga ke kina son mood ɗin na ganin mu tare amma ni ko a ƙafa aka ɗaura min sai na yanke na gudu" ya faɗa yana maida kai tare da ci gaba da abinda yake yi
Zuwa nayi inda ya shinfida sallaya na tada sallah, sai da na idar sannan na miƙe na koma toilet, yunwa ce kawai take cina ina zaune akan toilet sit ɗin sai naji an buɗe ƙofar
Wata leda ya wullo min ɗaukar ledar nayi na buɗe, kaza ce a ciki da yoghurt, kasancewar toilet ɗin ba wani ƙazanta a ciki ga kuma yunwa ya sani buɗewa na fara ci
Sai da naci na ƙoshi sannan nai brush zani na na ɗauko na shiga bath ɗin na shimfiɗa da niyyar kwanciya sai naji ya hankaɗo kofar
Maza fice min da gani zanyi fitsari inyi alwala in kwanta, shiru nayi kamar bacci nake yi, shima sai ya ɗauka da gasken baccin nake yi don haka sai ya saki jiki ya fara fitsarin sa
Sai da naji ya fara yi sannan na tashi zinbir zanyi waje, a guje ya nemi ƴar kaciyar tasa ya mayar wando be gama fitsarin ba ni kuma nai waje da gudu
Sai daya gama sannan ya fito
"meye na fitowa da gudu bayan kin saba gani, nawa ne dai sai dai kiyi fata amma yafi ƙarfin ki"
Ni dai ban kula shi na raɓe shi na shige naje na shiga cikin bath ɗin na kwanta, wayyo Allah kamar ina kwance akan ƙashi juyi nake amma bacci yaƙi zuwa
Can na kasa bacci sai na tashi na fito daga toilet ɗin, ɗakin ya ɗau sanyi sannan an kashe fitilar lallaɓawa nayi naje kan gadon na kwanta sannan na rakuɓe ƙarshen gadon don kar in tada shi
Ban daɗe da kwanciyi ba bacci ya kwashe ni,
Kiran sallah naji sai na ƙara juyi tare da ƙara duƙunƙune wa saboda sanyin da ake yi, sannan na kuma komawa bacci na me daɗi na sakankance ina bacci kawai naji an haɗaka ni na faɗo ƙasa tim
A guje na tashi inda shima ya biyo ni ze dake ni, toilet na faɗa na saka key na kulle, dukan ƙofar a ya shiga yi yana cewa in buɗe
Kin buɗewa nayi, har ya gaji ya dena nasan duk wanda ɗakinsa yake kusa da namu yaji don yadda yake bugun, a zuciyata nace mugu ai na waye na daina barin ka kayi min mugunta
Can aka fara kiran assalatu, nan ma yazo ya fara bugun in buɗe masa zai yi alwala a zuciyata nace sai dai karkayi sallah, sai daya gaji da bugun sannan ta tafi
Jin buɗe ƙofar ɗakin ya sani ni ma na buɗe toilet, sai da na gama fitowa sannan mukai ido huɗu da shi ashe be fita, na juya zan koma ya damƙo ni,
Tsalle na dinga yi ina ihu ai na waye yanzu wallahi sabit bazan kuma bari ka kuma duka na ba, tsaya wa yayi yana kallo na yadda na daddage sai tsalle nake yi
Belt naga ya ɗakko wanda hakan ne ya sani na ƙara ƙwala ihu wanda ban daɗe da kwalawa ba sai ga knocking a ƙofar mu, shi yaje ya buɗe
Mummy ce ina jin tana tambayar lfy da yake bashi da kunya sai yace
"mummy ba komai kawai faɗa tsakanin mata da miji, daɗi ne yake sata wannan ihun amma in shaa Allah baza ta kuma ba"
Sam be bari ta shigo ba balle in gaya mata Itama mummy da yake ta iya ɗaurewa ƙarya .......🤭 sai ta juya ta tafi, dawowa yayi na ɗauka wajena zai yo har ina shirin wage baki 😱 sai gana yayi hanyar toilet
Alwala yaje yayo sannan ya fito yai sallah asuba lkcn gari har ya fara wayewa a zuciyata nace ba lada, yana idar wa ya tasa ƙeyata na koma toilet sannan yaja ƙofar wai ni a toilet zan dauwama ne
Ina zaune bacci ya fara ɗauka ta, sai na fara gyangyaɗi a kam toilet sit ɗin, ƙarar buɗe ƙofar naji wanda hakan ya tabbatar min da shi don haka sai na tashi
Harara ya doka min sannan yace
"maza tashi ki fice wanka zanyi" sim sim sim na fice na bar masa toilet ɗin, ina fitowa naci karo da breakfast an kawo, daga dukkan alamu ya ci
Kallo ɗaya nayi wa abincin na ɗauke kai ba a bani ba duk da dai nasan hadda ni aka siyo amma ba a bani ba bazan ci ba,
Yana fitowa ya kora ni toilet, inda shikuma ya hau shiri, har cikin toilet ɗin ina jiyo ƙamshin turaren sa daya ke fesawa sai bayan daya gama sannan ya leƙo
"ki fito ki karya kuma da kingama ki koma toilet, kar inzo in same ki a ɗakin nan" yana gama faɗar haka ya fice
Sai da na tabbatar da ya daɗe sa tafiya sannan na fito nai break fast inda na samu chips da kwai sai pepper soup na hanta wanda yaji curry
Sai da na ƙoshi sannan na tashi na koma toilet don bana son abinda zai kuma haɗa mu da sabit,
Zama nayi a toilet na rasa abinda yake min daɗi ga bacci ina ji amma babu comfortable guri na kwanciya, duk inda na juya ba daɗi, miƙewa kawai nayi na fito ɗakin na saka key sannan na kwanta akan gadon ai ko ya dawo sai yayi knocking kafin in buɗe
bacci na nasha sosai sai la'asar sannan na tashi kuma har lkcn be dawo ba alwala nayi na zo na tada sallah ina cikin sallah sai gashi ya shigo
Ganin yadda gadon yake a hargitse ne ya tabbatar masa da ankwanta
"wato ke bakya jin magana ko, nace miki kar ki kwanta sai da kika kwanta ko" kasancewar sallah yake yi ya sa shi saurara min
Ni kuwa ganin yana jiran in idar yaci zalina ya sani na sake sabon kabbara tare da tada wata sabuwar sallah
tun yana jirana a tsaye har ya gaji ya zaune, ko dana fuskanci hankalin sa yayi wajen tuni na zura a guje sai toilet na rufe, nai mamakin da be biyo ni ba
Sai magariba sannan na buɗe yana zaune akan sallaya na raɓa ta gefen sa na wuce na gabatar da tawa anan na zauna har akai isha nayi sannan na tashi zan fice daga ɗakin
"ina zaki" naji yace min
"ɗakin su mummy zanje yunwa nake ji"
"ai dama an saba ci ki cika plate da uban abinci ki wuni kina ci ba abinda kika iya sai ci ko kwalliya irin taku ta mata ma baki iya sai gayyar ci, zo ki wuce ki ke can ga abinci can ki ɗauka ki ci kar kije ki tona min asiri"
Wuce wa nayi na ɗau abinci na zauna naci na ƙoshi sannan na kama hanyar toilet, ina shiga naji an rufe ni ta waje, hmmmm komawa kawai nayi na yi shimfiɗa ta a cikin bath na kwanta na daɗe sosai sannan bacci ya kwashe ni
Da asuba ina bacci a cikin bath naji ruwan sanyi a jikina a firgice na tashi ganin sabit ne ya sani yin Allah ya isa a raina
"fita ki bani waje zan yi alwala" fita nayi sai da yayi ya fito sannan nima na shiga don yin alwalar
👩🏽🍳 *menu of d day*👩🏽🍳
*coconut rice, with fried chicken vanillah smoothy*
*coconut rice*
```ingredients```
-rice
-coconut
-tattasai (green & red)
-albasa
-maggi
-mangyada
-carrot
-peas
-tomatoes
*method*
1) ki yi per boiling shinkafa sannan ki sauke ki wanke
2) ki pasa kwakwa sannan ki gurje baƙin bayan, daga nan sai kk yanka ƙanana sai kiyi blending ki tace ruwan
3) ki yanka carrots, da peas ki tafasa su, sai ki yanka tomatoes, tattasai koren da ja, sai ki yanka alabasa ki ajiye
4) ki zuba mai kaɗan a kasko sai kibi man da albasa kadan, idan man ya ɗan yi zafi sai ki zuba yankakkun kayanki duka banda koren tattasai
5) idan sun tafasa sai ki zuba ruwan kwakwa sannan ki zuba maggi saboda taste idan ruwan ya tafasa sai ki zuba shinkafa sannan ki rage wuta ki ƙara albasa
6) idan shikafar ta dahu sai ki zuba yankakKen koren tattasai ki kashe sannan ki sauke
*fried chicken*
```ingredients```
-kaza
-maggi
-garlic
-thyme
-baking soda
-flour
-corn flour
-mai
-egg
Salt
*method*
1) ki wanke kazar ki sannan ki tsane ta sai ki zuba mata maggi, thyme, tafarnuwa da duk wani spice da kike so sai kiyi ajiye ta a frigde kamar awa ɗaya
2) idan yayi awa sai ki ɗauko ki tsane sannan ki zuba flour, corn flour, baking soda da kuma kwai sai ki jujjuya har sai ko ina yaji sannan ki ajiye a gefe
3) ki ɗauko kasko ki zuba mai idan yayi zafi saki dinga saka kaza ɗaya da ɗaya kina soyawa amma karki sakar mata wuta
4) idan ta fara jaa sai ki kwashe ki bar ta ɗan yi minti ɗaya sannan saki sake mayar da ita har ta ƙarasa sai ki sauke
*vanillah smoothy*
```ingredients```
-yoghurt
-dabino
-vanilla extract
-madara
*method*
1) ki jiƙa dabinon ki ya juƙu sai ki cire ƙwallon
2) ki haɗa yoghurt, dabino, vanilla da madarar da sugar sai kiyi blending sai ki saka ƙanƙara a cup ko jug sannan sai a juye smoothy a kai sai a shaa 🍸
👩🏽🍳 *BON APPETIT*👩🏽🍳
*ASMA'UN SABIT*
[10:30PM, 5/2/2018] +234 806 399 9164: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
P⃗a⃗g⃗e⃗ 12 🌹
Yana idar da sallah yace min in kunna masa water heater, yi na yi kamar naji sai na wuce toilet nayi zamana
Can sai gashi nan ya ƙwanƙwasa min toilet buɗewa nayi a zuciyata nace kamar gaske
"tara min ruwan wanka kuma da zafi nake son ruwan"
Sai a lkcn na tuno da kunna heater, ruwan na tara amma na sanyi sannan na fice naje na zauna a ɗakin, ina kallon sa yana ta shirye shiryen kayan da zai saka na ɗaurin aure
Sai daya gama komai sannan ya shiga toilet ɗin, a tsorace nake nasan abinda zai biyo baya, can sai gashi ya leƙo jikin shi duk kunfa
"shine dana ce ki kunna min heater ashe baki kunna ba ko" ya haɗe girar sama da ta ƙasa, tuni ciki na ya bada ƙululululu nai tsuru tsuru
Kwafa yayi sannan yace
"zan kama kine" komawa yayi toilet sannan ya ɗauko bucket ya wullo min
"ɗauki maza kije ɗakin su mummy ki karɓo min ruwan zafi sauran ki bari in ta jiranki"
Ɗaukar bucket ɗin nayi na fice ina shiga ɗakin mummy naga daddy ma har ya shirya yana shirin fita
Gaisheshi nayi sannan na samu wuri na shantake ina sane da sabit kawai dai na share shi ne don Allah kaɗai yasan abinda zai min idan ya fito me ze min
Itama mummy tana kwance akan gado inda ni kuma nake zaune akan kujera ina kallo, can kusan awa ɗaya sai ga sabit ya shigo duk a firgice, jiki sai ya fara rawa na ɗauka dukana zai yi mummy ce ta fara tambayar
" sa auta lfy kuwa"
"mummy ina lfy badia ce ta ƙara yin miscarriage" ya faɗa rai a jagule, a zabure mummy ta miƙe
"me ya kawo ɓarin"
"oho wallahi mummy ban sani ba kinga na riga na gama haɗa kayana ma abuja zan wuce Allah dai yayi bazan samu ɗaurin auren ba kya gayawa daddy ga matsalar da ta sameni"
Har ya fita mummy ta kira shi, sai daya dawo sannan ta kai duban ta gare ni
"shirya kibi mijinki" a zabure na juyo na kalle ta, shi ma sabit ɗin sai yace
"wallahi bazan tafi da wannan ƙazamar ba, duk inda na shiga ana kallo na" takura masa mummy tayi da kyar ya yadda
Miƙewa nayi jikina a sanyaye Allah ya kawo min ɗauki, cikin hukuncin Allah muka kama hanyar abuja a jirgi, duk abinda nake tunanin sabit zai min sam be min ba don ko ta kaina ma be bi ba yana ta matar sa da ta kuma rasa babyn su
Muna isa gida muka raba hanya inda ni nayi BQ shi kuma yayi ɓangaren sa shi ke nan na huta da jarabar sa
********************
Mummy sai da tayi kwana uku sannan ta taho da amarya wacce ta tare a ɓangaren mijin ta, a lkcn na sha hidimar abincin saukar baƙi kamar ba gobe amma cikin hukuncin Allah kowa ya watse ya rage sai ƴan gidan kaɗai
Wai ina batun koyon girkin badia ne oho mata tunda ta samu ciki shike nan ta watsar da shi dama can ba koyo take ba, ya kasance ni nake giirki hankalina a kwance
Rannan ina kitchen ina ta shirye shiryen dinner sai ga wata kyakkawa cikin shiga irin ta ƴan kanuri wato laffaya sai ƙamshi take yi daga ganin ta nasan amarya ce
Da fara'ar ta ta shigo wanda ni kuma hakan yasani ɗan sakar mata fuska
"sannu zuwa nayi inga inda ake mana girki gobe zan fara girki shiyasa nace bari inzo inga abinci wa nake ci ashe ma yarinyace amma gaskiya kin birge ni da ƙanƙantar ki amma kina zuba girki kamar ba gobe wannan in kikai aure mijinki ya huta"
Dai da ta kai aya sannan ta nunfasa ikon Allah ni ban saba da zance ba balle kuma masu surutu don haka sai na rasa amsar da zan bata
"me kike dafawa ne" ta tambaya tana ƙarasa shigowa kitchen ɗin, ban ce mata komai ba sai ma cooker da na nuna mata bi ma'ana ta gani da kanta
Buɗe buɗen tukwane ta fara yi kowanne ta buɗe sai ta tambayen ni meye a ciki kuma ya dafa wa
Ido kawai nake bin wannan baiwar Allahn da shi don ni ban taɓa ganin mutum me surutun ta ba, kamar wasa sai naga ta cire laffayar ta ta saka apron ta ɗau girki
Ban tanka mata ba amma kuma dana ga alamae da gaske girkin take son koya sai na ɗan sakar mata jiki na har ina ɗan nuna mata yadda za ayi next
Cikin ikon Allah muka gama tas ita ta fara tasting, nan ta hau zuba kamar ƴaƴan kanya, kasancewar hausar tata bata gama nuna ba ya sa wani abun inji wani kuma bana gane wa kuma ban damu ba
Sai da taci abincin ta na dare anan sannan ta tafi inda kafin ta tafi ta ke sanar da ni sunan ta *FANNAH*
_(ban sani ba ko fannah ma ta hikima haka take da shegen surutu shiya sa wannan ma take haka, abinka da barebari ba abinda suka sai 🗣 ko fannah)_ 😜
Tun daga lkcn anty fannan ta zama regular costomer a kitchen ɗina, kullum sai ta zo tun ban saba ba har ya kai na fara sabawa da ita har nakan ɗan saki jiki da ita mu sha hira
Duk wannan abun da muke bata san ko ni wacece a gidan ba ta ɗauka kawai cook don haka kullum sai tayi ta kurantani wai idan nayi aure mijina zai more da girki
Wai in na yadda zata haɗa ni da ƙanin ta aure, kau da zancen nayi ban tanka mata ba don nafi son mu tafi a yadda ta ɗauke ni, ni ba mutum ce me son tona asirin rayuwata ga mutane ba
shikenan kullum in dai nayi girki sai ta yaba kuma sai tace ƙanin ta zai more da mace n da ta iya girki Hmmm shine kawai abinda nake binta da shi, sannan kuma sai ta dinga cewa wai ina da kyau *KUT* wannan jin sa nake yi kamar zagi
Domin ta ina za aga kyau na wannan baƙin nawa ya rufe shi, ni dai bana tanka mata sai dai intayi abin dariya in ɗan yi mata murmushi
Takan bani mamaki yadda take iya wuni a ɗakina ko a kitchen muna girki, tace ita bata yadda ba wai ace kullum mijinta abincin cook zai ci
Don haka in aka ce ranar girkin ta ne da kanta take masa varieties daban daban sai dai in taimaka mata tunda bata iya namu sosai ba
Ga wani shegen ƙamshi da kullum ta zo tana zuba shi kamar daga kwalbar turare take fito, ni ba mutum ce me son turare ba amma zama da ita ya sani son nima in dinga sakawa
Rannan tazo koyar girki sai nace mata
"anty fannah kullum in zako zo kitchen sai kin fesa turare ne" nai mamakin dana ga tana shinshina kanta sannan ta girgiza shi tare da cewa
"ban sa turare ba kin ji ƙamshi ne" ko da dai bana kusa da ita tsab ina jiyo ƙamshin ta amma wai zata rena ni
Taɓe bakina nayi sannan nace mata
"kema ai kin san kin saka don gashi ƙamshin turaren ki ya cika kitchen ɗin" murmushi tayi sannan tace
"ko kaɗan ban saka ba turare yana da wani abun idan ka juri saka shi ƙamshin yakan kama jikin ka kaji ko baka saka ba kana wannan ƙamshin, kema idan na haɗa ki da ɗan uwana aure zan baki wannan sirrin"
A matsayi zolaya ta min sai taga na ɓata rai tare da cewa
"anty fannah ina fa da aure kawai dai maganar auren nawa ne bana so don *AUREN BAUTA* ne"
"ban gane ba" ta tambaya sharewa nayi sannan na shiga sabgogi na, itama da fahimci bana son zancen sai ta sako min abinda nake so wata labarin girki
Nan na saki jiki muna tayi har Allah ya taimake mu muka kammala da ya ke ita ce da girki sai bata daɗe ba tana gamawa tayi pary ɗin ta wai zata gyara kafin mijinta ya ƙaraso
Ina mamakin wannan gyarawar tata kullum mace cikin ƙamshi amma kuma wai duk da haka bai yi mata ba sai ta ƙara _kya je ki shaƙe mijin naki da ƙamshin da yafi ƙafin sa, don shi be saba da ƙamshin nan daga wajen matan sa ba_ na faɗa a raina
Sai da daddare da isma'il ya dawo fannah ta gabatar masa da kaɓakin da ta haɗa masa sannan ta zauna inda ya fara ci yana zuba santi sai da yayi nisa a cin abincin sa sannan fannah tace
"habibi wai meye tarihin yarinyar nan asmau, wallahi tausayi take bani kuma jiya muna hira da ita naji tace min tana da aure sannan ta haɗe rai kamar bata son zencen"
Sam be mata nauyin baki ba ya sanar da ita komai akan abinda ya sani akan asmaun sakin baki tayi tana mamakin wannan abu wai sabit baya son asmau saboda baƙa ce
Bayan asmaun kana kallon ta zaka gano tsabar kyan ta, sai dai baƙin daya ɓoye mata kyanta, kuma baƙin natan rashin kula ne da ta sami man da zai karɓe ta baƙin nata zai gyaru ya dawo me kyau
Lallai ma sabit ɗin nan shi sam be san
Me ake cewa mace ba, yanzu wa zai ga asmau ya raina ta a matsayin ƴa mace don kawai Allah ya haɗa shi da ƙyal ƙyal banza sai gayu amma sam ba a san yadda za a kula da miji ba
Aikin banza Allah yayi masa kyauta na mace kamar asmau amma sam be ganiba saboda tsabar shi bashi da nazari shine yayi watsi da rahamar ubangiji ya rungumi waccen jaja amalen macen da ba abinda ta iya sai ƙyalƙyali
Wani tunani tayi sai tayi ƙwafa zai gane bashi da wayo ne, har ta gama abinda take yi ta kwanta tana tunanin wai sabit ne da wannan aika aikar lallai ma bashi da wayo
[4/23, 6:55 PM] Oum Haidar: ********************
Kashegari sai ga anty fannah ta shigo kitchen ɗin tare da ita muka gama abincin rana sannan muka shiga ɗakina don muci
Tare muke cin abinci in dai a nan zamu tare, sai da muka zauna muka fara ci sannan tace min
"asmau wai me yasa ba kya son gyara ko don ki jawo hankalin mijin nakin" tsayawa nayi kawai ina kallon ta,
"ya akayi kika san mijin nawa" na tambaye ta don abin ya bani mamaki
"yo abin duniya yana ɓuya ne, ni dai ina tambayar ki me yasa ba kya son kwatar kanki ƴanci Kina matsayin matar aure amma kin mayar da kanki baiwa" tsame hannu na nayi daga plate ɗin sannan na ce mata
"anty fannah ni fa ina da class kuma gaskiya bazan iya abinda zai sani ƙasƙantar da kaina saboda namiji ba"
"ai ba ƙasƙantar da kai bane, kowace mace ai ƴar kwalliya ce, mu samu mu gyara miki wannan baƙin naki ke ma zaki ga canji"
"wallahi anty fannah bazan yi bleaching akan wani namiji ba wanda be ma san darajar mace ba" dariya ta dinga yi, inda ni kuma na tsaya ina kallon ta
"ba bleaching nace kiyi ba, baki ganin fata ta yadda take baƙi amma kuma kowa ya ganni ya san ni macece ko kema abinda na ke son in gani a tattare da ke kenan ki zama ƴar gayu yadda sabit zai rena kansa akan yadda ya mai da ke cook ɗin gidan"
Taɓe baki nayi sannan na gyaɗa ka na kuma cewa
"ni dai wallahi bazan gyara ba indai saboda wani sabit ne in zai soni yadda nake too in kuwa bazai soni ba ai duniya da faɗi in wani ya ƙi ka ai dubu sai su soka"
Tsayawa tayi ta saki baki tana kallo sam bata ɗauka zan mata girman kai ba, don ta ɗauka zata juya ni yadda take so, duk yadda ta juya sai na juyo mata cewar ban yadda ba ni dai bazan gyara ba saboda sabit ba
"to shike nan mu bar wannan zancen ba kince kina son ki dinga ƙamshi kamar ni ba" ƙara shinshina ta nayi sannan nace
"ina sooo"
"to shike nan muje part ɗina sai in baki turaren da zai karɓe ki duk inda kika ratsa kina ƙamshi har kike ki ratsa zuciyar sabit"
"ai kuwa indai don sabit zaki bani bana sooo" dariya ta saka
"wallahi ba dan shi bane ta so muje" miƙewa mukai muka kama hanyar part ɗin su
👩🏽🍳 *menu of d day* 👩🏽🍳
*brown mac, served with short ribs soup and beef pancakes*
```brown macaroni```
_ingredients_
-macaroni
-mai
-carrot
-peas
- albasa
-maggi
-curry
-tomatoes
-attaruhu
_method_
1) a zuba mai a tukunya sai a ɗan saka ƴar albasa har ta ɗan suyo, idan man yai zafi sai a zuba macaroni a rage wuta sai a soya ta sama sama don kar ta ƙone har sai tayi brown sai a sauke a tsane man
2) a zuba mai ɗan kaɗan a wani tukunyar sannan sai ki yanyanka tomatoes ɗinki da attaruhi ki zuba, idan ya soyu sai ki zuba ruwa ba dayawa ba domin ba a son mac ɗin ta tayi romo haka ake yin ta ƙamas
3) bayan an zuba ruwan sai ki wanke carrot da peas ki yanka carrot ɗin yadda kike so ki zuba a ruwan a zuba maggi da curry sannan a rufe a barshi ya har ya tasafa idan ya tafasa sai a zuba soyayyar mac ɗin nan a rufe sannan a rage mata wuta ta dahu a hankali sai a sauke
*short ribs soup*
_ingredients_
-naman haƙarƙarin rago, har da ƙashin
-dankalin turawa
-ƙwai
-albasa
-attaruhu
-maggi
-indomie/spag
*method*
1) ki samu naman haƙarƙari ki yanka su yadda kike so sannan ki dora a wuta sai ki zuba maggi, tafarnuwa albasa sai ki rufe
2) ki fere dankalin ki sannan sai ki yanka irin girman da kike so, idan naman ya dahu sai ki zuba dankalin sannan ki zuba yankakken attaruhun ki sai ki ƙara ruwa yadda dai zai sa shi yin ruwa sosai
3) ki fasa kwai ki soya, amma in kin tashi soyawa idan kika zuba mai a kaskon in yayi zafi sai ki goge man da tissue sannan ki rage wutar sai ki zuba ƙwan ki kar ki bari yayi jaa fari ake so idan bangare ɗaya yayi sai ki juya ɗayan ɓangaren bayan kin gama sai ki sauke ki bar shi ya huce sai ki nannaɗe shi kamar tabarma sannan sai ki yanka shi ƙanana
4)ki ɗauko i domie ɗinki ki dafa ta a ruwa amma karta dahu sai ki sauke ki tace ta ki ajiye ta
5) idan naman ki da dankalin ki sun dahu sai ki sauke, ki tabbatar da akwai ruwa sosai ko kuma yadda kike so amma miyar nan me romo ce sosai
Idan an tashi za a ci sai a zuba soup ɗin a bowl ki zuba taliyar ki a saman sannan ki zuba yankakken kwanki kiyi masa kwalliya sai a gabatar wa da oga
ps: Idan kuma oga baya son indomie za a iya amfani da spaghetti amma a tabbatar sirara ce kuma ɗan kaɗan ba dayawa ba
*beef pancake*
_ingredients_
-naman sa (tsoka zalla)
-maggi
-tafarnuwa
-mai
-flour
-kwai
-albasa
*method*
1) zaki yanka nama yankan slice ko ince kamar yankan kilishi sai ki jera su akan chopping board ɗinki
2) ki barbaɗa musu maggi sannan ki yanka tafarnuwa ƙanana, sai ki gurza albasar ki duk sai kibi ki yaryaɗa akai
3) daga nan sai ki yaryaɗa man gyaɗa akai sai ki ba saka hannun ki ki daddake su, da tafin hanunki yadda haɗin zai shige su sai ki bar su kamar zuwa minti 2
4) sai ki ɗauke su ɗaya bayan ɗaya kina baɗe su da flour, ki samu kaskwan suyar ki sai ki zuba mai ɗan kaɗan kamar zaki soya ƙwai idan yayi zafi, sannan sai ki kaɗa kwai ki saka masa maggi sai ki dinga tsomawa kina sakawa a kan kaskon nan
5) ki rage wuta baya son wuta dayawa, idan ɓangare ɗaya ya soyu sai ki juya ɗayan ma ya soyu bayan sun soyu sai ki sauke
👩🏽🍳 *BON APPETIT* 👩🏽🍳
*ASMA'UN SABIT*
[10:31PM, 5/2/2018] +234 806 399 9164: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

👩🏽🍳 *BON APPETIT* 👩🏽
0 comments:
Post a Comment