Ƙiri² Asma'u ta kasa tashi , kusa da bakinta Amisty ta matsa da nata bakin sannan tace sweetheart miye ? Kallonta Asma'u tayi sannan tace na gaji , murmushi Amisty tayi da gefen bakinta sannan tace kin gaji tun yanzu ? Idan na fara suma zakiyi kenan saboda daɗi ko ? Shiru Asma'u tayi batayi magana ba ,
Uhum Amisty tayi tare da laso bakin Asma'u taɗan taɓo ƙirjinta ta waje , ƙara lasar saman luɓunanta tayi saita ɗago sannan ta ƙara tare da haɗa bakinsu wuri ɗaya tana mata wani irin sumbata wadda Asma'u ta danganashi da ko mijinta bai iya irinshi ba !
Tun a palo suka fara lalacewar su hankalin Asma'u yakai ƙololuwar tashi cikin sarƙayƙiyar murya tace muje ɗaki don Allah......
Amisty ta taimaka mata ta tayar da ita suka nufi bedroom , jikin Asma'u yana kyarma ta cire kayanta kaf sannan ta haye saman gado Amisty ta rufa mata baya suka ci gaba da halakewarsu !
Har ƙarfe 10:30pm babu Amisty babu labarinta , na kira wayarta yafi a irga bata ɗauka ba dan bata saba fita bata faɗamin taje wani wuri ba , duk wadda na tambaya ina Amisty sai yacemin baisan ina taje ba saboda suma kansu bata faɗa musu zata fita ba ,
Gajiya nayi da kiranta na haƙura nayi kwanciyata dan na huta , ina kwanciya Amisty tazo ta tsayamin a rai , tun lokacin da tamin abun nan a ƙofar gida duk lokacin dana raɓe ni ɗaya sai abun yazo ya tsayamin a rai ,
Tsoki nayi tare da gyara kwanciyata na rufe idona danyin bacci , murmushin Amisty nake gani sai kuma kallon da tamin , innalillahi wa'inna ilaihir raji'un nayi tare da miƙewa na ɗauki buta nayi waje ....
Hafsa na gani ita da A ` i rumgume da juna , a'uziyya naja tare da cewa wai ku wane irin "yan iska ne da Allah ? Na rantse da girman Allah idan baku daina min wannan muguwar ɗabi'ar ba duk sai na tashe ku a gidan nan ,
Dariya A ` i tayi tare da sakin Hafsa tace Allah ya baki haƙuri uwar ɗakinmu , ban sake magana ba nayi gaba , bayi na shiga ban wani daɗe ba na fito ina fitowa nayi alwallah na shige ɗaki na , wannan rana kusan kwana nayi ina sallah dan banajin daɗin ganin Amisty a zuciyata ko kwalwata !
A ɓangaren su Amisty kuwa kwana sukayi suna baɗalancinsu Asma'u taji dadin wannan harka domin Amisty bata da ƙyanƙyamin taba Asma'u gamsuwar da ko a wurin mijinta bata taɓa samu irinta ba , ga Amisty ta iya soyayya domin ta daɗe a harkar lesbian gwanace kisan farko , koda safe itace ta wanke Asma'u a toilet kuma itace ta shafa mata mai da powder ta taimaka mata ta saka kaya sannan tace zata tafi gida.
Asma'u tace da Allah karki tafi ? Murmushi Amisty tayi tare da jawota jikinta ta lumshe idanuwanta sannan tace karki damu ina dawowa anjima bana so mijinki yazo ya sameni a safiyar nan za'a samu matsala kinji ko ? Jinjina kai Asma'u tayi saida Amisty ta sumbace duk wasu muhimman wurare a jikin Asma'u tare da cewa ki kula ,
Asma'u tace to, sakinta tayi ta fito da sauri daga ɗakin dan har 9:00am tayi bata so mijin Asma'u ya ritsesu dan shima zata mishi horon da Sultana ta bata zata haɗasu dukansu taji dasu zata huta da Asma'u mijin kuma zatayi harka dashi dan ta samu kuɗi , dan da tana da wata sana'a ko hanyar samun kuɗi da baza ta bi maza ba , amma dole sai ta nemi maza sun bata sannan itama zata samu nayiwa karuwan matanta hidima...
Tunda Amisty ta fito Asma'u ta koma gefen gado ta zauna , tunanin Amisty takeyi gaskiya ta yaba da jarumtar ta kuma Allah yasa yau ta dawo su kwana tare ,
Ina tsaye ina saka caji Amisty ta shigo ɗakin kamar an jefota , rumgumeni tayi tare da cewa oyoyo my Sultinah na dawo jiya inata kewarki sweetynah fatan dai kinyi bacci mai daɗi ?
Kwantar da kanta tayi a saman ƙirjina , murmushi nayi tare da cewa tou sakarni mana , ƙara ƙanƙameni tayi tare da cewa uumm umm cikin sagwaɓa , har a raina abin yamin daɗi dan haka ban sake cewa Amisty tashi ba , jin nayi shiru yasa Amisty taɗan jijjigani sannan ta ɗago ta kalleni da kallo mai ɗaukar hankali tace me kika dafa mana ?
Saida na zauna sannan nace ni ban wani dafa komai ba , idanuwa Amisty ta zaro tare da cewa tou me zanci kenan yunwa nakeji wallahi , sai kici haƙuri na faɗa , Amisty tace saida mai bada haƙurin kinsan ina ƙoshi da komai amma bana ƙoshi da mata...
Tsoki nayi tare da kallon Amisty nace aike "yar iska ce wallahi , dariya tayi tare da ɗagamin gira ta kwanta sannan tace ai iskanci abun so ne wallahi danma baki san daɗin da akeji ba idan anayinshi....
Shiru nayi ban sake mata magana naci gaba da sabgar gabana , ita kuma wayarta ta fiddo bayan tayi latse latsenta ta kara a kunne , bayan an ɗauka tace ranka ya daɗe kana gari kuwa ? Banji abinda yace ba tace yawwa da Allah yunwa nakeyi aɗan kawomin abin ci yanzu ina jira , magana na cikin wayar yayi , wata irin dariya Amisty tayi tare da cewa tou babu damuwa idanma akwai wani mai ɗan ƙwari a tahomin dashi , tou babu komai ina jiranka , tana faɗin haka ta kashe waya...
Kallona tayi sannan tace mother da Allah a fitar da lido waje yau banajin daɗin zama ɗakin nan , miya sa ? Na tambayeta ! Ba tare data kalleni ba tace idan ina ganinki a hakan nan komai zai iya faruwa ji nake kamar in haɗiyeki , ban kalleta ba nace Amisty ramin gafiya ba irin na maciji bane , wuta bata kamuwa haka kuma iska bata riƙuwa, domin fito da maciji daga rami dole saida hayaƙi , kamun maciji badai yaro ba saboda silɓinshi ,ki sani kama Sultana ba abune mai sauƙi ba dan kamun kifi dole saida fatsa....
Murmushi Amisty tayi tare da cewa aike sai kiyi ta magana da yaren da bana ganewa , nima murmushin nayi tare da cewa kamar yadda bakya gane yaren haka baza ki taɓa gane gaban Sultana ko bayanta ba domin shan ruwa da haɗiya lokaci ɗaya ba dai bakin mage ba , a fitar da lido ina nan fitowa idan nayi wanka...
Fita nayi tare da ɗaukar ruwana na wanka na nufi bayi , Amisty kuma murmushi tayi tare da cewa zan kamaki yarinya zaki basu labarin fito da maciji dole saida hayaƙi ban taɓa neman mace ban samu ba zanyi waya da malam zulyadain na gaji da ganin abinci yunwa na damuna , lido ta ɗauka tayi ƙofar gida ita da sauran "yan tashar ,
Lokacin dana fito daga wanka babu kowa a tsakar gidan sai mijin Nana yana wanki , ban kalli inda yake ba nayi ɗaki abuna , ina shiga na fara shiryawa riga da sikat na saka na atamfa bayan na gama shafa , kayan kuwa sunyi matuƙar karɓar jikina ƙuguna ya fito sosai sai kace na wata uwar mata , turaruka na fesa tare da ɗaura kallabi wayana na ɗauka nima nayo waje bayan na gama ,
A ƙofar gida na samesu zaune saman dakali kuma da alama magana na sukeyi saboda naga sunyi shiru a lokacin da nake tahowa wurinsu , banma kowa magana ba na samu wuri na zauna naci gaba da latsa wayata ,
Amisty tace ga abinci nan idan zaki ci ! Ban kalleta ba kuma banyi magana ba , Amisty tace mother ina magana kinyi shiru , tsoki nayi tare da cewa na ƙoshi , cikin yanayin damuwa Amisty tace haba ya kuma kin ƙoshi ? Ban sake magana ba naci gaba da sha'anin gabana...
Lido insu sukaci gaba dayi amma kaf hankalin Amisty da tunaninta yana wurina , ni kuma ina tunanin yadda zan fara kore mazan dake zuwa gidanmu dan na gaji da zama dasu Amisty idan babu mazan bariki tou kowa zai fita ya kama gabanshi...
Ina wannan tunanin naji Amisty tace tou idan bazaki ci abinci ba kisha ko lemin mana , banyi magana ba na miƙe na matsa can wurin filin gidajen da aka rosa na zauna ,
Halbar da robar lemun Amisty tayi tare da cewa wallahi malam zulyadain bazai min ƙarya ba duk bala'en yarinyar can saina maida ita abun tausayi ta bana haɗiye miyau akan mace bansha ba wallahi , duk wacce tamin taurin kai asiri zaiyi tasiri akanta , tabbas itama Sultana zata yaba aya zaƙinta ,
Ban san gaibu ba amma tunda na lura da yanayinta bazan sake yadda da ita ba , ko yunwa zai kasheni na daina cin duk wani abu daya fito daga hannun Amisty kuma zan huro ma mazan bariki masifa duk wani kwarto saiya daina zuwa gidan nan , dama nina buɗe ƙungiyar kuma zan rufeta da kowarar kowa ,
Saida aka kira azahar na koma gida danyin sallah , har yanzu mijin Nana bai gama wanki ba tana can balbaɗɗiyar saman dakali sunayin lido , bayan na shiga gida ne Amisty take ba su Nana labari cewa malaminta yace duk daren daɗewa sai ta mallaki Sultana a hannunta kuma zata juyani san ranta ta kwantar da hankalinta lokaci ya kusa , amma a labarin malamin yace akwai wani yana nan shi zaizo ya tafi dani mutane dasu daɗe basuji labari na ba kuma yana nan ya kusa zuwa shima bada jimawa ba ,
Shine tace idan ta sameni zata maidani kaduna kafin wannan mutumin da yake magana yazo , dan malam yace babu makawa mutumin zai tafi dani kuma idan har yazo komai na rayuwata zai canza dan ko iyayena bazan sake gani ba gida ne zai kaini ya ɓoye ina ne ? Shine Allah bai nuna ba , idan ta kaini kaduna zatayi ta badani haya wa manyan hajijoyi tasan idan har tayi kasuwa dani ba kuɗi ba kuɗiɗina sai tayi...
Hafsa tace tou waye wannan mutumin ne ? Amisty tace malam yace matashi ne kuma duniya ta tsaya akanshi , yace mai mulki ne kuma cikakken attajiri ne , shin mai mulki ne ko basarake wannan shine ban sani ba , jinjina kai Hafsa tayi sannan tace karki zubar da abincin nan kiyi mata wayau sai taci shi , murmushi Amisty tayi sannan tace kwantar da hankalinki wata ma jiya a ice cream na zuba mata da zan tafi saida tayi kuka , dariya sukayi dukansu tare da tabawa sukace Allah ya nuna mana Sultana tana kuka akanmu zamusha shagali domin yarinyar gaskiya Allah ya hore kayan marmari a tattare da ita , haka dai sukaci gaba da labartawa akaina da kuma yadda zasu mayar dani inyi ta binsu kamar wata karya...
Suna ƙofar gida har bayan magrib suna hauka , da daddare bayan ƙofar gidanmu ya ɗauki harami kamar yadda ya saba a ko wane dare , bayan na fito nakejin labari cewa Dikko ya samu kujerar da yake nema yayin da mutane ke cewa yaron yana da sa'ar rayuwa gashi kamilin namiji ,
Magana ta karaɗe gari Allah ya bawa ɗan gwamna kujerar abokin babanshi daya mutu , duk inda ka nufa a gari maganar Dikko akeyi yayin da wasu keji idan sune a irin wannan damar ba ƙaramin farin ciki zasuyi ba , gashi Dikko ko auren farko baiyi ba amma ya shiga sahun manyan mutane da duniya zatayi alfahari dasu , wasu kuma cewa sukeyi tauraruwar ɗaukakarshi ne ya tsaya shi yasa na saman kujarar ya mutu dan Dikko ya hau ,
Har ga Allah naji baƙin ciki , yayin da naji dama baici ba shege munafikin Allah ɗayan mazinaci ya ɓoye ya saɓawa Allah amma a idon al'ummar gari suna masa kallon mutumin arziƙi bayan ni nasan mazinacin ne kuma shima yasan yayi zinar , hawaye ya cika min ido nace Allah ka kwace kujerar mulki a hannun Dikko babu mulki ma a hannunshi ya wulaƙanta al'umma inaga ya samu,
Wani naji yana cewa yo ai wallahi yaron nan tsaron da zai samu ko gwamna baya samun irinshi kai kana wasa da kujerar kaza , mutumin ya faɗi sunan kujerar da Dikko ya samu nidai bansan ko miye yace ba kuma wallahi bana iya maimaitawa ,
Wani daban naji yace ai naji ance har gwamnan jigawa ya bashi ɗiyarshi , Eh ai mutane basu abu dan Allah Dikkon ne wallahi dole sai ka bashi ɗiyarka ga ilimi gashi ya fito tsatson mutanen kirki ga kyau ga ilimin addini ga ilimin boko Dikko ga kuɗi ga mulki Allah dai yasa muna da rabo duniya da lahira , wani yace kai saidai mu tara lahirar amma a duniya su Dikko duk sun tare komai...
Tsoki nayi tare da juyawa na koma cikin gida ina tsinewa Dikko albarka wallahi idan dai ina da rayuwa ba tsaro ba ko tsoro yake tsare Dikko saina ci mutuncishi kamar yadda na ɗau alƙawari ,
Tunda na shigo ɗaki damuwa ta dameni na rasa inda zan saka raina naji sanyi wuri na samu na zauna a ƙasa na jingina da bango tunanin ta inda zan hudowa lamarin Dikko na farayi nasan ba lallai bane ya sake shigowa anguwarmu ba saidai ya bada umarni a duba dokuna kila ma yanzu babu wani ruwanshi da labarin doki Sultana kuma yasha banza kenan...
Murmushi Dikko yayi a dai² wannaan lokaci sannan ya kalli Al ' Ameen yace bansha ba , ruwa ne aka ajiye shine Al ' Ameen yayi tunanin ya gama zai ɗauke Dikko yace baisha ba , fita Al ' Ameen in yayi Dikko ya kalli hoton Sultana a wayarshi sannan yace ki daina tunani kona manta dake daren daɗewa Dikko baza taɓa mantawa dake ba , kina da matsayi na daban a rayuwata dalilin abu ɗaya yasa nake ɗaga miki kuma bazan daina ganin mutunci ba har abadan duniya zanzo bada daɗewa ba ki ƙara haƙuri kuma ki zama mai yafiya banda yadda zanyi dake haka kema baki da yadda zakiyi da Dikko , ina cikin farin ciki a yau dan haka kema kiyi farin ciki a daren nan An mata....
Wallahi bazanyi ba , ni kuma Amisty ke tambayana abinda ke damuna nace mata babu dan ba wadda yasan abinda ke tsakani na da Dikko ban taɓa bawa kowa labari ba zuciyata da rayuwata kaɗai suka san wannan sirri , Amisty tace tou kiyi shiru kallon Amisty nayi tare da cewa yanzu na fara kuka kuma bansan ranar da zan daina ba , inaji a jikina baƙin ciki da ƙunci na rayuwa banma saka hannu ba zan haɗu da wani gagarumin tashin hankali da bansan ranar zuwanshi ba , zan rasa wani abu mai mahimmaci a rayuwata zan zama abin tausayi da kwantacci wata rana na ƙarasa maganar ina murmushi....
Simi ² Amisty ta miƙe dan a tunaninta na samu warwarewar tunani , a wurin na kwanta naci gaba da kuka har bacci ya ɗaukeni ,
Yauma Amisty saida ta shirya sihirinta ta tunkari gidan Asma'u , cikin farin ciki Asma'u ta tari Amisty tana maijin daɗin zuwanta , yauma ice cream aka bata ta lashe kamar wata mayya , idan babu kwaɗayi ba wahala,
Babana zaune a gaban malamin shi , yace a zana masa ƙasa a duba masa halin da uwar masu gida take ciki ? Waya ɓata min waya faranta min ? Ina cikin farin ciki ko ina cikin damuwa ? Akwai wani dake harina kuwa ? ......
05/09/2019
*MEELAT MUSA CE...* 🧚🏻♀
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 27
Gyatsa malam yayi sannan ya ɗauko wuri ya feshe da turare irin nasu na matsubbata , a saman farin ƙyalle ya watsa wuri in suka watse ko wanne bai haɗu da ɗan uwansa ba sai guda biyu suka haɗe a wuri ɗaya...
Kallon Babana malam yayi sannan yace waye wannan yake tare da ita ? Baba yace Allah ya gyara aikin malam aikai zaka warware mana komai wannan ɗin shine yake tare da ita uwar masu gida kenan ko ?
Girgiza kai malam yayi tare da cewa bana tunanin wani namiji zai sake shiga rayuwar Maryam saidai mu bincika muga waye wannan ! Cikin damuwa Babana yace aiko idan bai fita harkar uwar masu gida ta salama ba zai fita da ƙarfin bala'e ko waye ,
Iyakar bincike malam yayi amma ya kasa gano ko waye yake tare da Sultana , an buga ƙasar an zana an goge an sake rubutawa amma abinda binciken ya nuna wai a kulle yake , wai prvt istihara jama'a kun taɓa ji ?
Hankalin Babana ya tashi yace malam babu abinda ya gagareka ,{ kai jama'a saboda an taɓo ɗiyarshi harya manta da Allah yana iƙirari wai babu abinda ya gagari malam } duba min miye kuɗirinshi akanta malam !
Bincike malam yayi sannan ya ɗago ya kalli Babana yace kaga ka fita harkar rabata da ko waye wannan domin duk wanda akazo istihara aka kasa kamashi shirin duniyarshi ba ƙarami bane gaskiya , wannan yayi zarra kuma yasha gaban duk wani mai tada mishi ƙura abinda yasa nace haka idan har kace zakayi wani sihiri akanshi wallahi zaka lalace...
Babana yace lalacewa kuma na nawa ? Aiko asiri zaka ma mutum idan kaga yana caca kawai ka barshi , tou Binna ba'a caca kaɗai ya tsaya ba ga caca ga neman mata idan akwai lalacewa wacce tafi wannan akan uwar masu gida na yadda zanyi wallahi !
Ƙara duƙufa malam yayi zuwa wani lokaci ya fara magana ba tare daya ɗago ba yace Aliyu wannan mutumin da muke magana yana gaf da Maryam kuma yana zuwa wurinta babu jimawa zaizo da farin ciki amma zai koma da ita yana mai baƙin ciki , abinda zai kawoshi da abinda zaisa ya tafi da ita duk ban gani ba amma tabbas zai tafi da ita kuma zata ɗauki tsawon shekaru babu wanda zaiji labarinta ,
Cikin tashin hankali Babana yace ina zai kaimin ɗiyata ? Malam yace ina zai kaita nima ban sani ba amma tafiya babu makawa , waye shi ? Malam yace sanin ko waye shi da ƙudirinshi duk sai mu jira zuwanshi , cikin ɗimaucewa Babana yace kafin yazo ina tare da "ya ta ina nan ina jiran zuwanka a gabana ka taɓa uwar masu gida saina gana maka azaba mafi girman azaba a duniya , ka fara lissafi daga yanzu kwanakin mutuwarka na tunkaro ka muddin ka tunkaro rayuwar ɗiyata kazo ina jiranka....... Ya ƙarasa maganar jikinshi yana wata irin kyarma idanuwanshi jajir kamar an watsa mishi yaji sai zufa yakeyi kamar wadda maciji ya sara....
Malam ya tausayawa Babana dan haka yaci gaba da bincike amma Allah ya ɓoye mutumin da zai shigo rayuwata , cikin tausayawa yace Aliyu kayi haƙuri tunda nake dakai baka taɓa nema baka samu ba sai wannan , kai kanka kasan iskancin da Maryam ta taro ba ƙarami bane banda muka dage akanta da yanzu bata taruwa a garin nan sanin kanka ne ,
Da sauri Babana ya rufe idonshi dan duk duniya ya tsani a danganani da kalmar iskanci , laya malam ya miƙowa Babana yace gata nan kaje ka samu jaririyar mage sabuwar haihuwa wacce dai bata buɗe ido ba , tou a yage bakinta a saka wannan layar sannan a kashe magen a jefar da ita a tsohuwar rijiya , bazan maka bayanin komai ba zaka zo ka bani labari yadda Maryam zata watsar da kowa da komai ta dawo gareka...
Hahaha Babana yayi dariya irin ta basawa tare da cewa godiya nake malam uwar masu gida zata dawo gareni , zata manta da duk wani abun daya faru a baya ta dawo nutsatsitsiyar ta kamar baya , godiya Babana yayi sannan ya tashi ya tafi....
Baccin dai babu daɗi dan ko da nayi bacci ɗaya farkawa nayi daga nan na shiga tunanin rayuwa da tunanin mutuwana wacce zata iya riska na kai tsaye ba tare dana shirya ba , ina ƙoƙarin koyawa zuciya tsoron Allah na canja halayya amma sam sai zuciyata ta karɓi huɗubar sheɗan cewa yarinya dake ? Duka shekarunki nawa a duniya ? 17 zuwa 18 ne ai mutuwa ma baza ta wani zo wurinki ba ki dage kawai ki more talatarki kafin larabarki ta riske ki....
Karki kuskura ki bar bariki ba tare da kin kafa tarihi ba , ki zuge rayuwarki kaf wata rana zata tofo domin rayuwa ita da zogala basu da wani banbanci kinga dai zogala kullum cikin zugeshi akeyi amma kafin wani lokaci ya sake fitowa , mafita ɗaya ce su Amisty kawai zaki kora sai ki shiga cikin ahalin Baba ki sake haɗo wata daba , yess 🤷🏻♀ dama Baba ƙarami yacemin karuwa zan koyawa "yar sa karuwancin idan an tashi kwatance a cikin ahalimu za'ace karuwai biyu idan har na bari na zama karuwa ni ɗaya gori bai ƙare ba har ɗiyan ɗiyana amma idan na taɓo wasu a ciki shiru zakuji ustaz ya samu mace...
Da safe bayan na gama duk abinda nakeyi wanka nayi na shirya cikin riga da zani na atamfa nayi ƙofar gida , dukansu a saman dakali na samesu zaune hada Amisty sallama nayi musu sannan na samu wuri na zauna , a cikinsu babu wadda yaimin magana kuma babu wadda ya ansa min sallama , sukaci gaba da labarinsu ,
Ban damu ba domin dama su ba ma'abota ansa sallama bane ba , cikin girmamawa Amisty ta taso tazo gabana ta durƙusa da wainar filawa an daka mata tashshi mai shegen daɗin ga tumatur da albasa tasha kallo ɗaya nayi ma wainar yawu na ya tsinke , Amisty tace ga abinda kike so nayo miki mother ,
Cikin farin ciki na ansa tare da fara kwararawa Amisty godiya sannan nabi kowa nace yaci , murmushi Amisty tayi tare da cewa ai kowa yaci taki ce ke ɗaya uwar gidan kwarata , jinjina kai nayi tare da miƙawa Amisty nace tou kici kema , no nikam bana ci kinsan waina bai wani dameni haka ba , miƙewa nayi tare da cewa ai wannan shagalin sai an rufe ƙofa ,
Dariya sukayi gaba ɗayansu tare da cewa sai kace dai kin samu mijin zalifa ? Nima dariyar nayi ba tare da shigewa ciki , umm waini za'a cuta da gwangwanin fulawa ɗaya tashshi naira talatin da manjan naira hamsin , Amisty kenan idan har bakisan halina ba har yanzu lallai babu ranar da zaki gane wace ce Sultana...
Ina shiga cikin gida ɗakina na shiga na kwashe wainar na zuba a leda bayan na gama na fito na zubar a bola , ɗaki na koma naci gaba da danƙarar tashshina saida na haɗa zufa na tabbatar bakina ya kama tashshi sosai sannan na fito ƙofar gida da tissue ina goge majina ,
A gaban Amisty na ajiye flet in tare da ƙara fyace majina idona yayi jajir sannan na zauna kusa da Amisty , murmushin mugunta tayi tare da lasar bakinta kamar mayyar da ta daɗe batayi kamu ba , nima murmushin nayi tare da kallon Amisty nace ɗan matsa daga gefe kar ayi abun kunya bisa titi !
Kallon su Hafsa tayi tare da ɗaga musu gira alamar tayi nasara, ɗan cije leɓona na ƙasa nayi tare da ƙanƙance idona na dama , kallona Amisty tayi sannan tace wane irin abun kunya za'ayi ne ? Murmushi nayi tare da cewa ji nake kamar in lashe ki , na nuna lashewar da harshena sannan na haɗe haƙorana na gaba sukayi ƙara ƙass.
Uhum kwarata kenan gaba ɗayansu sukayo kaina kamar an watso mutane a doka daji , yadda namun daji ke kawo hari kowa ya ɗauka karya rasa , murmushi nayi tare da ajiye hannuwana ta baya na jigina dasu ina kallonsu , Hafsa tace uwar room ya kikeji ne ? Rufe idanuwana nayi tare da girgiza kaina sannan nace ai bama zan iya musultawa ba ,
Nana ta riƙo ƙuguna tana kallona bayan wani lokaci tace ɗan daure ki misilta mana yadda kikeji ! Har yanzu idanuwana a rufe yake nace misali kece aka rufe a ɗaki kwana biyu babu ci babu sha idan aka fito dake kika ga abinci wane irin ci zaki masa ?
Amisty tace ai ƙalu bale ga duk abincin dana damƙa , buɗe idona nayi sannan nace tou idan aka ajiye miki farfesun kaji sai aka kawo miki kwaɗon ganzo ko garin kwaki a ciki wane zaki ci ? Hafsa tace ai kowama kazar zaici , dariya nayi tare da cewa me yasa zaki ci kaza kibar ƙanzo ? Amisty tace saboda itace tafi daɗi da amfani a rayuwata ,
Gyara zama na nayi nace to idan kika samu namiji kika samu mace a ciki wannen zaki ɗauka wane zaki bari ne ? Amisty tace ai mace ba'a haɗata da kowa domin ita tafi kaza daɗi ke wane zaki ɗauka wane zaki bari ? Ta ƙarasa maganar da tambayana....
Gyara bakina nayi tare da cewa gaskiya dani namiji amma yanzu mace nake so nima , age agegege..... Kunji wani sabon taken iskanci wai agege , gaba ɗayansu suka faɗi age agege ,
Saida na gama kallesu tsaf sannan nace amma ina da sharaɗi fa ! Amisty tace faɗi sharaɗinki mother , yawwa idan dai zan faɗa harkar lesbian gaskiya sai kun bani haɗin kai na tsaya saman ƙafafuwana mun kora duk wani namijin bariki ta hanyar tambayarshi abinda yake bashi sha'awa a bariki , ta haka zamu gano inda matsalar take zamuyi gyara domin ceto matan auren da suka rasa mazajensu , domin gaskiya bana iya haɗa bariki da harkar mata ,
Shiru sukayi suna kallon junansu , nima ban sake magana ba ina saurarensu abinda zasu ce , Hafsa tace meya shafi harkarki da rashin kula namiji kuma ? Salon nawa ne a haka gaskiya dan idan baku manta ba yanzu maza nake bana mata , amma tunda zan ajiye maza na ɗauki mata dole saina fitar da maza a rayuwata ....
Da ido sukayi magana sannan sukace har zuwa yaushe zamuyi aikin ne ? Na sati ɗaya ne , na basu amsa , tou munji mun yadda suka amsa gaba ɗayansu , jinjina kai nayi alamar na gamsu , Hafsa tayo ta kusa da fuskata da wani banza bakinta zata sunbaceni , murmushi nayi tare da tare bakin ta da ɗan yatsa na nace yi haƙuri hajiyata lokacin naku bai fara ba ,
A hankali taja baya , murmushi nayi a zuciyata tare da cewa Mother ta ibi ruwa ta jefa guga duk wanda yai wannan yazo da zamba , ko akan wannan zasu ɗau misalai , domin Sultana tayi naɗi da lauje , "yar birni tayi nitso da ƙoƙo gani naci banza zan zare adda , kowa yayi ƙuri sai yayi muzu a ƙarshe mu zuba dani daku...
A ƙofar gida muka yini dukanmu amma ni ina tashi naje nayi sallah idan lokaci yayi kuma dana gama nake dawowa domin duk iskanci su Amisty a saman tafin hannuna yake , duk wani barbaɗe² ankare nake dasu domin suna sakin layi cikin magarnarsu , ni banci ɗiyar kowa ba uwata batayi ba babu wanda ya isa yayi akaina kallon biri sukemin ina musu kallon ayaba zasusha mamaki ranar da film in ya ƙare....
Da daddare , kamar yadda ƙofar gidan ya saba a ko wane dare haka ya fara ɗaukar harami motoci suka fara layi ƙamin yadda suka saba , kamar yadda muka saba muma a ko wane dare haka muka fito ina gaba su Amisty suna biye dani a baya , dan yau a gida zata kwana tunda mijin Asma'u gidanta yake yau...
Wani zafaffen Alaji ne yace Allah ya taimaki uwar gidanmu , harna wuce nayo baya dan haka aka ajiye min kujera na zauna suka koma bayana dukansu suka tsaya kamar yadda suka saba , gaisawa mukayi na tambayeshi iyali ? Lafiya qalau yace tare da ɗan maida idonshi ga waya , murmushi nayi tare da cewa Alhaji wai matanka nawa ne ?
Shiru yayi baiyi magana ba yaci gaba da kallon wayarshi , Alaji na sake kiran sunanshi , miƙomin wayar yayi tare da cewa ko kema zaki kalla ne ? A face buk sai maganarshi akeyi Allah dai yasa kar bakin duniya ya kashe shi mutane suke tayin posting hotunanshi suna tayashi murna...
Ya faɗi maganar tare da miƙomin wayar , ƙin ansa nayi Hafsa itace ta ansa bayan wani lokaci tace Alhaji ya naga ana haɗashi da wata mai siffar maguna , dariya sukayi gaba ɗayansu Amisty tace ke kuma mai siffar kisau , duk kallo sukayi dukansu A ` i tace aiko wannan mai kyau ce gaskiya kedai kawai kice kinajin kishi ,
Alhaji yace ai itace zai aure ɗiyan gwamnan jigawa ce , sai yanzu na gane ko hoton waye ake kallo , Amisty tace yaushe za'ayi bikin ne ? Alhaji yace ƙarshen watan nan shi gwamnan keta sauri dan yaga Dikkon so yake ya zuƙe dandai suna da zuminci amma da bana tunanin za'ayi auren nan gaskiya...
Miƙomin wayar Amisty tayi tare da cewa kalli mutuminki zaiyi aure , tsoki nayi tare da cewa ta ina ya zama mutumi na kuma ? Hafsa tace wanda kukayi faɗa asibiti wai mother mema ya haɗaku dan a lokacin naga kuna abu cikin gayya² dadai gani akwai azazza a tsakaniku.
Murmushin ƙarfin hali nayi tare da ansar wayar amma banba Hafsa amsa ba , kallon hoton nayi yayin da wani hadarin baƙin ciki ya taso min , tsoki nayi tare da cewa Hafsa siffar me gareta kika ce ? Hafsa da baƙin ciki ke gurgurawar zuciya tace shegiya tsinanniya mai siffar karnuka ai in Allah ya yadda wannan auren babu ubanda zaiyi shi ,
Kawai dai haka nan nakejin babu daɗi a raina , zuciyata kuma tana kwaɗayin ƙara kallon hoton Dikko , amma na hanata tare da cewa kwantar da hankali keda zakici mutuncishi saurin me kike bayan lokaci ya kusa....
Maida hankali na nayi wurin Alhaji tare da cewa Alhaji matarka nawa ne wai ? Mata ta ɗaya mene ne wai ? Ba komai na bashi amsa tare da cewa tou me yaja ra'ayinka na faɗowa matan bariki haka rana kwatsam ? Kallona yayi cikin ɓacin rai yace me yasa kikemin irin wannan maganar da Allah ? Nima kallonshi nayi ido cikin ido sannan nace haka tsarinmu ya koma dole duk wani namijin dake cikin barikin nan saiya faɗa mana abinda ya kawoshi bariki , idan ya faɗa mu kuma sai mu bashi tsula²n mata ya more daga garesu saboda munyi oder manyan mata daga jahohi da dama , haka tantancewa mukeyi mu gano namijin da ya kamata muje dashi a cikin wannan tafiya tamu mai taken bariki ta giga.....
07/09/2019
Taku a kullum ... 👇🏻
*JAMEELA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 28
Kallo Alhaji ya bini dashi mai nuni da yama rasa abinda zaicemin , murmushi nayi tare da cewa da Allah kar kaga kamar cin fuska ne ko wani abu ko zaka taimakamin naga hoton matar ka ?
Me yasa kike son ganin hoton matana ko zakije ki haɗamu da ita ne ? Ya ƙarasa maganar cikin sigar barkwanci , murmusawa nayi tare da cewa haba Alaji yadda da arne shi yake sa aci yankashi , kuma daɗin aure kesa mata tace miji Baba... Ganin hoton iyalinka bashi ne yake nuni zan faɗa ba , nasan gidanka komai da komai naka na sani hoto kawai zan gani sai nayi gaba abuna...
Amma kafin na tafi don Allah me yaja ra'ayinka ka afkowa matan bariki bayan ka baro naka matar gida ? Ɗaure fuska yayi tare da cewa me yasa kike so kimin haka wai ? Dani dake da ku dukanku taimakekeniyar juna mukeyi manta da lamarin matana da kuma abinda yasa na faɗo barikinku mu fuskanci abinda ke gabanmu !
Miƙomin wayar yayi da hoton zuƙeƙiyar matarshi wacce ta gaji da haɗuwa duk inda ake neman mace takai kuma duk inda ya nuna matanshi abun kallawa ce , gaba ɗaya tafi su Amisty komai na morewa amma bata kai diddigen Sultana ba , danni a tara mace dubu baza'a iya samo ɗaya kamarni ba ,
Caf na faɗa tare da kallon Alhaji sannan nace wannan kyakkyawa ya akayi ka baro kyau siga da nagarta ka faɗowa kwarin mata ? Me matan bariki suka fi matar ka ? Me yasa ka kashe sunna kake ƙoƙorin ɗabbaƙa zunubi ? Me yasa kabaro inuwa ka dawo rana ? Ya akayi kabar rahama ka dawo azaba ? Me matan bariki sukafi matar ka don Allah ? Me ya ɗaukar maka hankali da macen bariki har ka baro taka kazo wurinmu....... ?
Kallo Alhaji ya bini dashi na kece abun tausayi mai ƙaramar shekaru dake kina ɗaukar kayan daya fi ƙarfinki , kamar nasan abinda ke zuciyarshi nace manta dani ka fuskanci taka rayuwar , nasan matsayin zina , illolinta matsalolinta wahalhalunta tashin hankalin dake cikinta da kuma bala'en dake tare da ita , san zuciya da ɗaukar huɗubar shaiɗan ya mantar dani , domin yawan kusantar saɓo yana hana ganin girman zunubi , kasan surar da Allah ya sauke akanmu mu mazinata , ina matsalar take tsakanin kai da matar ka ne ?
Gyara zama Alhaji yayi sannan yace :• me yasa matan bariki suka fi iya jan hankalin namiji ? Ba tare dana kalleshi ba nace shaiɗan ne yake ƙawata maka su domin yasan zina hanyace da take kai mutum ga halaka , zina tana zubar da mutinci tana rage ma mutum daraja a wurin ubangiji sannan mutuncin shi zai ragu a wurin al'umma kuma zina tana rage ƙwarjini fuska ,
Har yanzu baka bani amsar tambaya na ba , miya ja ra'ayinka shiga harkar bariki wai ? Alaji yace matan bariki kullum a shirye suke basa taɓa gajiyawa da ansar buƙatarka duk lokacin daka zo musu zasu anshe ka cikin farin ciki ba tare da gajiyawa ba , zaka kwanta da mace babu wari a jikinta babu ƙarni ko zarni bare kuma hayaniyar "ya "ya , yayin da zaka kwanta da matarka lokacin zata fara cewa batayi ma yara shimfiɗa ba , kana mata magana tana wani fiffizge kai tun kana sha'awar abun har yazo ya fita akanka ,
Kallon Alaji nayi sosai sannan nace , filawar bisa hanya tasha banban data cikin gida , mace kamar filawa take idan ta samu wuri mai kyau kuma akayi mata ban ruwa yanda ya kamata idan dai tasha ruwa ta ƙoshi duk wanda ya gani sai ta bashi sha'awa , lokacin da filawa ta rasa ruwa zata bushe ta soye duk wadda ya kalleta baya sha'awar ƙara kallonta , to haka mace take , matan bariki wayau suke muku kuna basu kuɗi suna gyara jikinsu a cikin kuɗin da kuka basu a ciki suke siyan abunda zasu ja muku hankali dashi , matarku ta sunna tana can viseline in da zata shafa wahala yake mata , taya zata gyara bare har ta baka sha'awa ? Idan baza ka damu ba zanyi magana da matarka idan Allah ya kaimu idan har tabi shawarata tabbas zaku samu rabauta , kai kuma zan koya maka yadda akewa mace ban ruwa ....
Shiru Alaji yayi zuwa wani lokaci yace babu damuwa kije na yaddar miki , godiya nayi masa sannan na miƙe ɗauko kujerar sukayi suka biyoni da ita yayin dana tsaya wurin wata motar...
Ajiye min kujera akayi na zauna , motar a buɗe take dan haka na ɗora ƙafata ta haggu a saitin mazauni driver tare da cewa malam barka da dare ! Allah ya taimaki uwar ɗakinmu ya haƙuri damu ? Alhamdulillah na faɗa tare da cewa ya iyali ? Kamar jira yake yace tana can shegiyar saida nayi mata jakin duka na fito , kallon agogon hannuna nayi ba tare dana kalleshi ba nace me tayi maka ne ? Ta rainani idan na shigo da leda takemin sannu da zuwa idan banzo da itaba ko daga ɗaki bata fitowa , yau na yanka rago dake duk sati nake yankawa , mahaifiyata tazo nace a ibar mata shine tayi mata rashin kunya ni banji daɗin abunba shi yasa nayi mata duka na baro gida ,
Kallonshi nayi sannan nace to me kazo kayi nan ? Dariya yayi irin ta sakarkari sannan yace nazo a ban natsuwa , jinjina kai nayi sannan nace tou yau babu maganar bariki kaje gida ka lallashi matarka muna zuwa gidan idan Allah ya kaimu , ina faɗin haka na miƙe nayi gaba , ɗauko kujerar sukayi suka biyoni domin cikin gida na nufa...
Hayani mazan suka farayi tare da cewa ya zanyi musu haka ne ? Ai haka ma babu adalci , a zuciyata nace wannan matsalarku ne ba nawa ba ,
Ina shiga gida na shige ɗakina , Amisty ta rufomin baya , itace ta kulle ɗakin domin dare yayi kowa a gajiye yake babu abinda yake buƙata sai bacci , kayan jikina na cire na ɗaura zanin bacci , Amisty kuwa da kayanta tayi kwanciyarta ,
Tunda na kwanta fuskar Dikko kezomin a idanuwana , ya ƙara kyau abu ga farar fata ga hutu ga gayu gemunshi yasha gyara sai kyalli yakeyi , an gyara ƙasimbar ta kwanta sosai dake farine sai abun ya bada wani irin sirrintaccen burgewa , shi ba wani tsoho ba amma dole sai ya zama tsoho me yasa yakeyin haka ne ? Dan yaga gemun yana mishi kyau gaskiya fa yayi mishi kyau shi yasa yake ɗaukar hankalin mata , gemu da ƙasimba make up in maza kenan...
Ajiyar zuciya na sauke tare da gyara kwanciyata , damuwa nakeji sosai ina ta ƙoƙarin molaƙe rayuwata ashe shi Dikko yana can yana ƙoƙarin gyara tashi , zaiyi aure ya barni ina cikin karuwanci , ina ganin zan masa rata ashe shine zaimin rata , ya zama shugaban al'umma ta wani gefen ni kuma na zama shugabar rusa rayuwar farin cikin wasu da tawa rayuwar ? Hawaye ya cikamin ido bayan sun gangaro na maida numfashi dakel sannan naci gaba da zancen zuci ! Me yasa na zaɓi na zama karuwa ? Me yasa banyi ƙoƙarin zama ta gari ba ? Mai makon na zama waraka ga al'umma sai na zama cuta a garesu...
Kukan zuci naci gaba dayi irin mai kartar zuciyar nan wanda kesa mutum yaji kamar zai mutu shi naci gaba da yi numfashi na naji yana ƙoƙarin fita daga jikina dolena na tashi zaune da sauri naci gaba da fita dan ceto tawa rayuwar....
Zaune yake ya hakince irin zaman nan da yakeyi na ya raina mutane , ɗage yake kallon kowa yayin da bakinshi ke motsawa a hankali cikin kwarewa da goguwar iya cin cingom , Al ' Ameen ya kalla sannan ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi yace wai mema zance mata idan tazo ? Murmushi Al ' Ameen yayi tare da shafa kanshi yace tuba nake ranka ya daɗe , dan tunda akayiwa Dikko kyautar Sadiyya bai taɓa zuwa ba sai yau , baya ko waya da ita yauma Dadynshi ne ya matsa mishi shi yasa yazo !
Dan ko hotunansu dake yawo a social media haɗawa akayi bashine da ita suka jera suka ɗauka ba , Dikko baiyi magana wa Al ' Ameen ba Sadiyya ta shigo cikin palon , gaisheta Al ' Ameen yayi sannan ya fita...
Cikin karairaya da kwarewa da bariki tayo inda Dikko yake zaune , ɗan taɓe baki yayi a zuciyarshi yace bari inga rashin kunyarki , bai gama tunani ba ta zauna tare da ɗora kanta a saman kafaɗarshi tana mai sauki ajiyar zuciya cikin yanayin mai nuni da tana cikin shauƙi, daga waje har ciki Dikko baiji wani shock ba , dan haka yace sauke kanki mace bata hawana , na miki uziri nayau idan kika sake zaki samu matsala....
A shagwaɓe tace haba diye { dear } ... Yanayinka sch ne amma ya kake abu kamar class ? Banza Dikko yayi baice komai ba , jinyayi shiru yasa tace ya hanya da mutane ne ko ? Nan ma bai bata ansa ba , zagba surutu taci gaba dayi tare da cewa idan sukayi aure zata mishi soyayya , ba komai kake ta wani jan allo dana fara rubutuna zaka sauke , hauka dai tayi ta zuba mishi tare da son ƙara kwanciya jikin Dikko amma abun ya mata girma ,
Bayan ta gaji da surutun tayi shiru , can kuma taci gaba , kasha drinks mana , ta ci gaba da lissafo duk abinda aka kawoma mashi , har ta gaji ta sake ɗaukewa , ganin Dikko bazaiyi magana ba yasa ta fashe da kuka cikin kuka take cewa haba Yaya wai me yasa baka so na ne ? Ina ta magana amma kamin shiru ka mayar dani kamar wata mahaukaciya ! Nifa "yar uwarkace ka soni dan Allah kodan zumunchin dake tsakaninmu....
Kallonta yayi sannan yace ya isa , kije ki kwanta a gajiye nake muyi magana anjima , goge hawayenta tayi tare da cewa ai ko na kiraka ma baka ɗauka , karki damu zan ɗauka insha Allah , murmushi tayi tare da miƙewa cikin farin ciki , shima murmushin yayi zuciyarshi tace dama An matane a wannan yanayi , wata "yar jakace a gefenshi ya nuna mata yace ɗauka...
Ɗauka tayi babu ko godiya ta fice a palon , wayarshi ya ɗauka ya nuno hoton Sultana , ya ɗauki tsawon lokaci yana kallonshi bayan wani lokaci yayi magana a bayyane cewa kuka kikayi , ina gane yanayin farin ciki da damuwa idan na kalli hotonki , duk yanayin da naji na shiga tou kin shiga yanayin meke damunki ne ....?
Banda ajiyar zuciya babu abinda nake saukewa har yanzu zaune nake ban kwanta , ɗan ɓata rai Dikko yayi a daidai wannan lokacin ya kalli hoton Sultana sannan yace ki daina damuwa ki zama mai farin ciki a ko wane lokaci , taɓa screen in wayarshi yayi tare da cewa kiyi bacci cikin aminci da salama ....
Ajiyar zuciya na sauke tare da komawa na kwanta , ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni , .....
Koda Dikko ya koma masauki wanka ya farayi duk saida ya gama abinda yakeyi sannan ya cire wayarshi daga airplane mode , kamar wani munafiki wai ba'a kunna waya sai dare sosai zai duba saƙon da aka turo masa , a lokacin zai shiga yanar gizo , a lokacin zai ansa waya idan aka korashi itama sai wacce yakeji zai iya ɗauka , da zaran kuma ya gama abinda yake zai sake rufewa sai kuma wani daren , wayarshi ɗaya kuma da ake samunshi ba kowa yake da number ba , daga gidansu saida wanda shine yaga dama ya bashi , dan dayaji an kirashi da wayar to yasan kirane mai mahimfaci ,
Wani vidio ya buɗe da abokinshi ya turo mishi , kafin vidion ya buɗe ya fara karanta rubutun ƙasan vidio da akayi ,
_Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , Allah yayiwa Fatima rasuwa sakamakon fyaɗe da akayi mata , abun babu kyan gani kuma ko su waye da gayya sukayi mata sun wulaƙanta yarinya bataji bata gani ba , sannan suka ɗauki vidio a waya suka bada wayar a cikin envilop aka kaiwa Babana har Office dan lokacin kwananta ɗaya da yini ba'a ganta ba , gawar kuma suka zo suka jefar a ƙofar gida..._
La'ilaha illa anta sub'hanaka inne kuntu minaz zalimeen Dikko ya furta a lokacin daya gama karanta saƙon ya fara kallon vidion , ƙattin maza ne sunkai su biyar amma duk sun rufe fuskarsu da maX , ihu Fatin keyi amma babu abinda ya damesu kowa burinshi ya biya tashi buƙatar , wani irin motsi Dikko yaji kwalwarshi tayi kanshi ya yamitsa da sauri ya ajiye wayar tare da dafe kanshi da dukan hannuwanshi biyu abinda yakeji da game da Sultana ya dawo mishi sabo....
Lahaula wala kquwwata illa billahil ' aliyyil azeem , Dikko yake ta maimaitawa ya ƙurawa kafet ido kamar Sultana ce a wurin , saida natsuwa tazo mishi yaci gaba da zancen zuci lallai ya cuci rayuwar Sultana shima bashi da banbanci da mutane biyar ɗin nan domin magungunan daya sha sun bashi wani irin ƙarfi wanda ko allura hauka akayi ma doki iyakar abinda zaiyi kenan dan nuna shi mai ƙarfi ne , hawaye ya cikawa Dikko ido tausayin Sultana ya ƙara kamashi lallai ya cuci yarinyar nan !
Yau wane irin baƙin ciki iyayen Fatima suka shiga ? Wane irin ɗaci sukeji idan sukaga wannan hoto ? Ya Abbakar zaiji yayin daya ga wannan hoton akan ƙanwarshi ? Da nine ya zanji idan haka ta kasance akan ahalina ? Kwantar da kanshi yayi a saman hannun kujara ya rufe idanuwanshi duk yanda akayi akwai abinda Baban Abbakar yayi suka ɗauka fansa dan yanayinsu ya nuna a lokacin da suke aikatawa kamar biyan bashi ne sukeyi , Allah na tuba ka gafartamin ka sakawa An mata soyayya ta mai girma a zuciyarta , sona ya hanata bacci da tunanin kowa a duniya saini , ta daina jin maganar kowa sai tawa , ka saka mata san kasancewa dani inuwa ɗaya kasa mata firgici idan ta yini ko ta kwana bata ganni ba , ka ɓadda mata tunanin kowa da komai na duniya saini , ka saka mata san jin muryata ka goge mata kuɗirin fansa akaina , nayi alƙawari zan zamar mata natsuwa zan zama uwa da uba data rasa masu kishinta bazan barta tayi kuka ba haka kuma zanyi ƙoƙarin sakata farin ciki , duk wanda ya ɓata mata ko yasa taji damuwa nine zan tsaya harsai naga tayi farin ciki , Allah ka gafar tamin ka goge damuwata a zuciyar an mata ta zama soyayya mai ban al'ajabi ga kowa ,
Buɗe idanuwanshi yayi tare da goge hawayenshi , sannan ya ɗauki wayar ya goge vidio ba tare daya gama gani ba , wayar Abbakar ya fara kira dan jajanta mishi kafin yaje mishi ta'aziyya , Sadiyya koda ta kira Dikko text ya tura mata idan ya gama zai kira , koda ya gama abinda yake ba wulaƙanci ba da gaske ya manta da labarin kiran Sadiyya , da tunanin An mata yayi bacci....
Da safe wanka nayi na shirya cikin riga da zani na atamfa , hijabi na saka sannan nacewa Amisty zanje in dawo ! Ina zakije tunda safe haka ? Ta tambayeni ! Takalmi na saka tare da ce mata zanga wani a bakin hanya , addu'ar a dawo lafiya tamin ni kuma na fice daga ɗakin...
A ƙofar gida na anshi makullin mota na dana sa aka ɗaukomin , ɗan daba ɗaya na dawo dan ya rakani gidan Alaji koda an samu ɓacin rana , abinda yasa ban tafi dasu Amisty ba saboda kar ya zama naje gyara kuma gyaran ya zama ɓarna.....
Tafiya mai nisa mukayi zuwa gidan Alaji , a ƙofar gida nayi parking sannan na fara kiran wayarshi dan dama banzo ba saida izininshi.........
09/09/2019
*JAMILA MUSA.....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 29
Bai ɗauka wayar ba ya fito daga cikin gidan , ina cikin mota zaune nima ban fito ba , shine yazo har wurin mota ya buɗe gidan baya ya zauna amma bai rufe ƙofar ba , juyawa nayi ina kallonshi tare da cewa dana kira naji baka ɗauka ba nayi tunani ko baku tashi bacci ba !
Gyara maɓallin rigarshi yayi tare da cewa ai ina ganin kiranki nasan kina ƙofar gida shi yasa nace kawai bara na fito basai na wani tsaya ɗaukan waya ba , murmushi nayi na juyowa ina kallon gabana wato na juya daga kallon Alaji nace muje ciki to...
Tou muje amma bata nan ta shiga maƙota , ɗan zaro ido nayi amma banyi magana ba , a zuciyata nace maƙota tun wannan safiyar ? Lallai akwai ƙatuwar matsala , sauka nayi daga cikin motar tare da cewa muje *Wane Yaro* ɗan daban da nazo dashi ,
Rufe mota ta nayi muka nufi cikin gidan dukanmu , a ƙaton palon matarshi ya saukemu gafa kujeru har kujeru amma datti yasa sun tashi aiki , bakajin wani ƙamshi ko na tsitsiyar ƙamshi bare kayi tunanin zaka samu turaren wuta banda zarnin fitsari palon kaca ² a firgice babu abinda ke tashi sai wani ƙanni² a palon....
Saman hannun kujera Alaji ya zauna ni kuma kallabin kaina na ciro na shimfiɗa a matakalar da zata gangaro dakai cikin palon dan wannan kujerun idan har na hau su yau babu abinda zai hana ƙurajen ƙyama su fito jikina....
Fira muka farayi da Alaji ya ɗan fara karanto min matsalolin da yake fuskata , yace ga ƙazanta ga rashin ragowa ga fita babu gaira babu dalili , ga rashin godiya ko zai kashe kanshi ya bata bata taɓa masa godiya ba , wallahi idan har zai kwanta da ita sai ankai ruwa rana sannan kuma babu wanka bare yayi tunanin zai ji wani ƙamshi da zaisa mishi yaji wani shauƙi yayin da yake kwanciya da ita...
Uhum har ga Allah ba sasanci ya kawoni gidan Alaji ba a wannan lokaci , ina da wani ƙudiri nawa na daban , ina so inga yanayin yadda yake hidima da gidanshi , surutar da matarshi take amfani da ita kuma har store insu yau sai naje dan inga idan naci gaba da tarayya da Alaji zai iya ɗaukemin duk wasu buƙatu na ? Dan nima in samu wanda zai tayani kula da tawa rayuwar , zan kuma bigi cikin matarshi ta faɗamin komai nasu da wasu sirrika na Alaji daga nan ni kuma zan ɗaukeshi sai tayi da gaske ma zata sake ganinshi...
Babu ko sallama ta faɗo cikin ɗakin daga ita sai ɗaurin gaba hijabinta riƙe a hannunta , Abbu Afsar ka tashi kenan ? Bai kalleta ba yace na tashi daga ina kike ne ? Kallona tayi sannan tace wallahi gidan Naja naje tace zata shigo bata samu damar shigowa ba kusan kwana biyu mijinta ya hanata fita shine nace ta bari ni nazo , kallonta Alaji yayi tare da cewa ita da bata raina mijinta ba ! Ya hanata ta hanu ke kuma da kika raina naki sai kika fita babu izini na.
Tsoki tayi tare da zama saman kujera tana cewa baka gajiya da tsegumi haba da Allah dan naje tou miye ? Murmushi nayi ina mai kallonta , gaskiya kyakkyawa ce sosai , ga kyawu har kyawu amma an kashe kyawun da ƙazanta , yarinyar mace kamar wannan tana zama da ɗaurin gaba , gashin hamatar ta kanshi idan kika kamashi zaki iya kitsashi saboda yawanshi , tana da haƙora masu kyau amma ta kashesu da rashin wankewa , kanta kuwa ƙaramar ƙarya kila yayi shekara rabonshi da a kwance , kitsone saman kan amma baka isa ka gane ta ina aka ɗauko tsagar kitson ba ,
Tou bamu dai gama maganarmu ba da Abbu Afsar Ummu Afsar ta shigo gidan , tsokin da tayi masa yasashi tashi ya fita daga ɗakin , ina kwana na gaisheta , ansawa tayi tare da fyace majina da gefen zaninta , sannan tace ban gane ki ba ,
Uhum ai baki sanni ba na faɗa ina sadda kai ƙasa cikin nuna mata ni ta gaskiya ce tunda nasha hijabi daga sama har ƙasa , kallona tayi sannan tace Allah sarki sannu da zuwa , ki dawo saman kujera mana !
Nan ma yayi na bata amsa , bara na kawo miki ruwa , tou na faɗa yayin data miƙe tabar palon , babu wani ɓata lokaci ta dawo da wasu irin haɗaɗɗin kulololi masu matuƙar kyau da tsada , ta wuce taje ta ajiyesu a saman tebirin cin abinci ,
Saida ta ajiye sannan tace bisimillah mana , ta faɗi maganar cikin sakin fuska , banyi magana ba na tashi na nufi tebirin cin abinci yayin da Wane Yaro ya zauna a wurin dana tashi ,
Kujera taja itama ta zauna kusa dani sannan muka sake gaisawa, ɗora hannuna nayi saman kular da take ƙoƙarin buɗewa nace suna na *Sultana* ɗiya ga Aliyu Muhammad Binna , Babana sananne ne kuma ya shahara a harkar caca , dani da Babana da kowa nawa muna zama a gidanmu cikin kwanciyar hankali , nazo wurinke dan gyara miki wani kuskure Allah dai yasa banyi shishshigi da yawa ba.....
"Yar gajeriyar dariya tayi sannan tace ke kuma me yace miki nayi masa ne ? Kallonta nayi sosai dan na fahimci yanayin rayuwar tata , bata da babbar ciwon dake damunta wanda ya wuce rashin ɗaukar shawara , tana da taurin kai sannan kuma abinda taga dama shi takeyi babu wanda ya isa ya sa tayi ko ta bari sai ciwon rashin wayau dake ɗawainiya da rayuwarta...
Kauda kaina nayi daga kallonta sannan nace ni bai faɗamin komai ba , gyara zama tayi tare da cewa baya da aiki sai kai ƙarata bana san wanka bana shara bana goge ɗaki ban iya girki ba , ban iya kwanciyar aure ba , cikin hayani tace yaje ya nemo wacce ta iya duk wannan abun dana lissafo ban iyaba ta ƙarasa maganar da dukan tebirin data ajiye kulolin da ƙarfi...
Cikin tsoro nace saurara kiyi haƙuri ba hayani ta kawoni ba , shin ko kina fama da matsalar rashin abinci ne ? Ko rashin sutura sabun wanka ko na wanki ? Rashin turare ko man wanke baki ? Cikin ɓacin rai tace babu abinda na nema na rasa dalili dai bazai yuwu ba kullum namiji yayi ta sussukata ni ba gero ba ,
Dariyar mugunta nayi mata tare dayi mata kallon wawiya , data riƙe mijinta ram a hannu da bai kallo matan waje ba , wannan ba matsalar Alaji bace itace ta kai mijinta ga halaka , na rasa abinda yake damun matan ƙarshen zamani , babu biyayyar aure ba ladabi mace ta mayar da mijinta kamar almajirin gidanta baida wani mutunci ko daraja a idonta....
Yake "yar uwata ki sani aure yana da babbar matsayi haka kuma namiji yake da babbar daraja , mijinki shine sirrinki suturarki aljannarki sai kin gyara rayuwar aurenki sannan zaki samu rayuwa mai daɗi a gidan duniya da ƙiyama dan miji ba abin wasa bane , mijinki ba abin wulaƙantawa ba ne sannan kuma mijinki ba abokin gabarki bane , abin ƙauna ne abun tausayawa ne a gareki , ki kwantar masa da hankalinsa sai Allah ya kwantar miki da naki , ki bashi natsuwa sai Allah yasa kema ki samu natsuwa , kisa mishi farin ciki sai Allah yasa kiyi farin ciki a gidan duniya da lahira....
Matan bariki suna da illa kuma suna tattare da masifun dasu ma kansu basu san suna dasu ba , bariki wuta ce mai azabar raɗaɗi da wahala , zina halakace kuma babbar cutace , me matan barike suke dashi wanda baku dashi ne ? Komai iri ɗaya ne abu ɗaya suke dashi wanda matan aure suka rasa , kuma suma matan auren suna da abu ɗaya wanda matan bariki basu da irinshi !
Wannan abu ba komai bane sai sakaci , shine abinda matan aure garesu , matan bariki kuma basu dashi , matan bariki basu da sakaci abinda matan aure suka rasa kenan...
Ummu Afsar ta saki baki ga wacce bata sani ba taci gaba da buɗemin sirrin mijinta wanda haka ba daidai bane ga duk macen data san abinda takeyi , ɗakinta da tsore inta babu inda bata kaini ba dan in gani da idona tana da komai na rayuwa tsaftarce da haƙƙin Alaji bazata bayar ba , tunzura ta nayi tare da cewa Eyy ki barshi gaskiya gaki ma yadda kike kyakkyawarki ko kun rabu sai kin samu wanda yafi shi , murmushin jin daɗi tayi tare da cewa ai cewa ma akeyi nafi ƙarfin shi , kallonta nayi tare da cewa gaskiya keɗin duniya ce da matsayin gidan sarauta...
Sallama mukayi da ita tayomin rakiya har ƙofar gida inda nayi parking in motana , saida na fara tafiya sannan nasa Wane Yaro ya kiramin wayar Alaji , bayan ya ɗauka nace masa ina san ganinshi amma ya faɗamin sirrintaccen wurin da zamu haɗu , bayani yamin sannan nace masa na gode tare da kashe wayata...
Kai tsaye gida muka nufa a bakin hanya na ajiye Wane Yaro ni kuma na wuce gida , a ƙofar gida nayi parking in mota ta na shige ciki , sallama nayi kamar yadda na saba na wuce ɗakina , ruwa na zubo a boket naje na watsa sannan na dawo ɗaki nayi kwanciyata dan hutama rayuwata....
Bayan sati biyu , abubuwa da dama sun faru , ga lamarin iskanci na kuma yanzu na zuƙa hannu na , Babana kuma ya samu mage kamar yadda malam yace kuma ya aiwatar da aikin kamar yadda akace yayi ,
Na samu Alaji munyi magana dashi kuma ya faɗamin cewa yana san wayayyar mace "yar gayu wacce zata biya masa buƙatarshi a duk lokacin daya so , ba laifi yana da wanka kuma yana gayu kuɗinshi a sake yake ga mata , dan haka na ɗaura dashi cewa ya saurareni ina san na haɗa gidanmu sannan naci gaba da harkar bariki na,
Da alkairi na nake shiga cikin ahalinmu , nakan basu kwance kaya , in siya musu kayan kwalliya idan na samu kuɗi , ina aika musu da kayan abinci kuma ina zuwa lokaci ² ina basu sha'awa kuma cikin hikima na fara musu tallar bariki ,
Duk wata hidimata yanzu Alaji shike ɗauke da ita , babu abinda na nema na rasa fanni abinci kuɗin kashewa da kuma suturu ya kwacemin duk wani abinda zaizo ya dameni , yauma ƙaton rago ya kawomin dan haka na sakashi a napep na tura Wane Yaro yakai gidan Baba ƙarani da 100k nace ya sayi icce...
Babana kenan , ɗan duniya abin alfahirin uwar ɗakin kwarata , cikakken namiji mai dogon zamani , namijin duniya gatan mata , ka gansu ka ƙyasa ko ba sisinka su bika , baka gada ba haye kayi Sultana tai gado ɗan gado kuma saiya zarta.....
Uhum Baba kenan , Amisty ce kwance a saman Baban Sultana suna ɓalgacewa bayan sun gama ɓalɓalewa yake tambayarta ya Uwar masu gida ? Tace tana nan cikin ƙoshin lafiya , Amisty itace take kaiwa Baban Sultana labarin halin da Sultana take ciki , kuma shine ya tirsasawa Amisty ta kwashe kayanta ta dawo zamani dan kawai ya riƙa jin halin da nake ciki , abin kunya Baba ka rasa macen da zaka huta da ita sai abokiyar "yar ka , dakai da Amisty duk ranar da Sultana ta gano ku zaku fuskanci babbar matsala....
Lokacin da Baba ƙarami yaga rago abun ba ƙaramin burgeshi yayi ba dan babu biki ba suna kuma ba sallah kawai an bashi kyautar rago , yaji daɗi sosai a lokacin da Wane Yaro yaje kai rago ya samu Zainab da Farida a gidan dan haka daya tashi zai dawo suka biyoshi zuwa wurina...
Nayi farin ciki da ganin "yan uwana , muka rungume juna cikin soyayya irin ta "yan uwan da suka daɗe basu haɗu ba , sannan muka shiga jajantawa juna yaushe rabo ? Bayan an gama suka tambayeni ko na fara kasuwanci ne ? Dariya nayi tare da ce musu sosai ma , me kike siyarwa ne ? Suka tambayeni kai tsaye nace *Karuwanci* shine sana'ar da nakeyi...
Zasu fara wani mamaki nace karku wani damu kuma kar kuyi mamaki nayi amfani da huɗubar da Baba yake baku ku tashi ku nemi kuɗi domin ku kare mutunci kanku , huɗubar ce na ɗauka kuma da ita zanyi amfani kuma ma babu laifi an samu nasara tunda na siya gida ga mota kuma ina da "yan canjina , ku kun samu gida da mota ne ? Na tambayesu , shiru sukayi , murmushi nayi tare da cewa karku damu ƙanwarku ta kasa kuma ta samu masu siya nayi ciniki sosai dan haka kawai ku dawo nan muci gaba da zama dan tunda na siyi gidan na fitar da ɗakunan matan Baba shima Baban zan dawo dashi dan kasuwa bata yuwuwa babu shugaban ƙungiya....
Gaba ɗaya wutarsu ta ɗauke musu basu da zaɓin daya wuce su dawo zama tare dani tunda inda suke a raɓe suke , koda suka tashi tafiya na basu kuɗi na basu kayan sakawa , sunyi godiya sosai tare dacemin insha Allah zuwa jibi zasu dawo , rakiya nayi musu suka tafi...
Baba ƙarami da jama'ar dake da sauran mutunci a idon Babana sune suka sameshi suka bashi magana cewa ƙauracemin bashi ne zaisa nayi halayen kirki ba , ya dawo kusa dani wani abun ma a gaban idonshi bazanyi ba , Baba yace shi ba wani abu yakeji ba kawai kunyata yakeji ya zama sokon uban daya kasa ceton "yarshi daga shiga wata baƙuwar rayuwa !
Magana suka ba Baba harya amince zai dawo gidana , kuma yaje wurin Maman Fa'iza suka ce zasu dawo suma jibi idan Allah ya kaimu dan haka gida zai dawo kamar yanda yake da , su Nana Karima da suke zaune a gidan kuma bazan tada su ba saidai idan sune suka tashi da kansu...
Da marece ina kwance Amisty ta shigo ɗaki babu sallama , jakarta ta ajiye ta ɗauki buta ta nufi bayan gida , tana fita na tashi da sauri naje na ɗauko jakarta na buɗe , kuɗine masu yawan gaske a ciki dan haka na tattarasu gaba ɗaya na kwashe su na ɓoye sannan na koma saman katifa nayi kwanciyata kamar yanda nake daga farko...
Ban daɗe da kwanciya ba ta shigo tare da cewa tashi gidansu Hafsa zamuje bata da lafiya , subahanallah na faɗa tare da tashi zaune nace meya sameta haka ?
Ƙonewa tayi ta faɗi maganar tare da ɗaukar jakarta , nima tashi nayi banko ɗauki gyale ba makullin mota kawai na ɗauka tare da cewa muje , tunda nake ban taɓa zuwa gidansu Hafsa ba sai yau zan fara , a tsakar gida nayiwa su Nana saina dawo sannan mukayi waje dani da Amisty...
Daga ni sai Amisty muka tafi ni naja motar har muka isa gidansu Hafsa , har zanyi parking a waje Amisty tace inyi horn za'a buɗe , banyi musu ba na dannan horn mai gadi ya kwashe mana get muka shige , kusa da motar Hafsa anan nayi parking in mota ta sannan muka shige ciki...
Har muka isa ɗakin Hafsa bamu haɗu da kowa ba , palon ɗakinta ma ba kowa dan haka bedroom muka shiga kai tsaye , Hafsa tana kwance a saman gado an naɗe ƙafarta da farin bandeji , idonta a rufe kila tanayin bacci ne , zanyi mata magana Amisty tace karki tasheta bacci takeyi , banyi magana ba na samu gefen gado na zauna , palo Amisty ta koma babu jimawa ta dawo ɗauke da wata ƙatuwar roba bansan ko miye a ciki ba , wurin ƙoƙarin ta hawo saman gado ta ɓareminshi kaf a jikina , tsakiyar idonta kaɗai na kalla na gane wannan abun shiri ne ,
Kallon kokon data makomin a jiki nayi sannan na sake kallonta , kiyi haƙuri Amisty ta faɗa , ba koma nace cikin sanyi jiki dan Amisty tsoro take bani , cikin sigar lallashi tace ki shiga toilet saiki wanke , banyi magana ba na miƙe na nufi inda Amisty ta nunamin da ɗan yatsanta , kokon gaskiya baya wankuwa gefe² dole sai na cire kayan nayi wanka gaba ɗaya dan babu inda bai kai ba ,
Cire kayana nayi nai wanka , bayan na gama na wanke kayana na ɗauro towel na fito da kayan a hannuna da niyar ince a ina zan shanya ? Ina fitowa naga Hafsa tana rufe ƙofa da makulli bayan ta gama ta tillashi can saman waldrop , bayan ta tilla ta warware bandejin sannan tace hausawa sunce mai haƙuri mawadaci nasha haƙuri kuma na daɗe ina dakon yunwa da ƙishirwa , yau zanci insha zan kore duk wata tsohuwar yunwar dake cikin hanjina... Dariya sukayi tare da tafawa ita da Amisty....
Amisty ta ansa da cewa lallai zamuga wasan kura ga uwar kwarata gata lesbian , Hafsa tace tabbas yau zan koya mata irin namu salon tunda muma ta koya mana irin nata , a'uziyya naja tare da ƙara riƙe towel in jikina gam , murmushi Hafsa tayi tare da cire rigar jikinta tace kinga sheɗan baya tafiya gashi ma ya fara cire rigar jikina , kin gani ta faɗa yayin da ta ɓalle bireziyarta , ja baya na farayi da niyar komawa toilet ina ihu a kawo min ɗauki *kwarata* sun rufeni a ɗaki ,
Dariya Hafsa tayi tare da shan gabana tace ina zakije ne ? Kuma babu mai cetonki dan gidan ma babu kowa , shi yasa nace Amisty ta kawomin ke kwana biyu zakiyi kawai kafin nan nasan kema kin zama "yar hannu...
A saman bedsite naga kwalbar mai mai gurguwa dan haka da sauri na yada kayana na ɗauka na kwaɗawa Hafsa a kai harsai da jini ya fita , ajiyar zuciya ta sauke tare da fizgoni tace nagode ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin haɗa bakina da nata , da ƙarfi na tureta naci gaba daba da ihu ina kai mata duka , kwata ² bataji dan haka ta janye towel in jikina , ita da Amisty suka kamani mukaci gaba da kokowa da ƙarfin bala'e suka ɗorani saman gado.....
11/09/2019
💅🏻 *MEELAT MUSA NE....*
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 30
*_Ina miƙa saƙon ta'aziyya ga "yar uwar aikinmu Halima Yahya 20 Allah ya bada haƙurin rashi ubangiji yasa ta huta Allah ya kyautata namu ƙarshen idan ajaliyyarmu tazo...._*
Amisty ta danneni da ƙarfin tsiya Hafsa ta sauka dan ɗauko igiyar da zasu ɗaureni da ita , murmushi nayi tare da kallon Amisty sannan na nunata da yatsa na juya na kalli Hafsa itama na nunata da yatsa sannan na gaggaɓe da wata irin dariyar dani kaina bansan na iyata ba ,
Lokaci guda kuma na ɗaure fuska kamar bani nayi dariyar ba , da sauri Amisty ta kalli Hafsa suka kalloni a lokaci ɗaya , hawo saman gadon Hafsa tayi tana ƙoƙarin riƙe hannuna ta ɗaure , kallonta nayi kamar wata sakara sannan nace dake da Amina ku tabbata idan har kuka min wani abu kasheni shine kawai mafita a rayuwarku , amma na rantse da girman Allah wanda ya halicceni ya halicceku dani daku dukanmu shi muke bautama , mutuwa ta ko taku zata iya zuwa ko wane lokaci yanzu ko anjima , ko kuyi ko ku bari yanda kuka buɗemin sirri saina buɗe sirrin uban kowa a cikinki ,
Bayan buɗewa saina tona musu asirin da ku kanku sai kunsha fiya² kun mutu saboda baƙin ciki , kar wacce ta ɗauremin hannu ko ƙafa kuyi duk iyakar iskanci da kuka iya , bashi ne kuma bazaiyi kyau ba a lokacin da zan biyashi akan iyayenku ,
Muni , baƙin ciki , firgici , tashin hankali gaba ɗayanku zaku fuskance su yayin dana shigo rayuwarku , ina da illa kuma ina da bala'en haɗari haka nake dasa baƙin cikin da baya mantuwa a zuciyar duk wanda ya nemi ya dasa baƙin ciki a rayuwata , ciwo gareni haka nake da ɗaci kuka akemin kamar mutuwa yayin da na shigo gida dan ruguza farin ciki zuri'a ɗaya , ku lasa ku maida miyanku tunda kun buɗa ni kuma nayi alƙawari daga yanzu rayuwar farin ciki ta ƙare gareku ,
Kallan kallo suka tsaya yi kowa da abinda take saƙawa a zuciyarta , tsoki nayi tare da cewa kuna ɓatamin lokaci domin ni ruwan ƙorama ce zuwa nake da ƙarfi na tafi idan kuma na tashi tafiya nakan tafi da abu mafi soyuwa ga al'ummar gari za'ayi ta tunani na har shekara ta zagayo ba'a gama wani kukan ba zan sake caɓar wani abun inyi gaba dashi haka mutane zasuyi ta kuka dani har ranar da mutuwarsu zata riskesu , dake da dake duk wanda na bari a cikinku ya huta ban yafewa kaina ba...
Dukan ƙofa akayi da ƙarfi tare da cewa Hafsa me kukeyi kuma ? A shagwaɓa tace Mom ya akayi kuka dawo ne ? Ƙara dukan ƙofar tayi tare da cewa ni banje ba tunda na shigo nakeji ana ihu *kwarata* wai me ke faruwa ne ...?
Dukansu shiru sukayi , ci gaba tayi da dukan ƙofar tana cewa wallahi idan kika bari na buɗe ƙofar nan da kaina zaki ci ubanki.... Cikin yanayin ɗacin rai Hafsa ta kalleni sannan ta sauka ta fara ƙoƙarin saka rigarta a lokacin har Mom inta ta zuro makulli ta waje ta fara buɗe ƙofa...
Murmushi nayi da gefen bakina nima na sauka daga saman gadon na ɗauka towel in na ɗaura , ban gama ɗaurawa ba ta shigo ɗakin , kayana na ɗauka da makullin motar na raɓa ta gefenta zan fita , riƙoni tayi tare da cewa ke daga gidan ubanwa kika zo nan ke kuma....?
Ko kallonta banyi ba da nace mata daga gidan ubanta nake , bakiji ina miki magana ? Kema nan dako haihuwarki ba'a gama ba har kin iya iskanci haka ? Kallonta nayi sannan na faɗa mata kaf abinda ya faru na ɗaura da cewa kuma na rantse da girman Allah saina rama ,
Haƙuri ta fara bani , niko nace dama kin adana kalmomin haƙurinki kila zasuyi tasiri a lokacin da "yarki ta fara halbe²n mutuwa , ina faɗin haka nayi gaba , a palo naga wata ƙatuwar hijabi dan haka na ɗauketa nayi gaba , a ƙofar palo na saka sannan na wuce inda na ajiye mota ta , ina zuwa na shiga naja cikin gudun tashin hankali nabar gidan kamar babu rai a cikin motar...
Tuƙi nake bansan inda nake bi ba , domin idona cike yake da hawaye yayin da hankalina da zuciyata suka tafi tunanin hanyar da zan samo iyayensu Amisty dan babu hanya mafi muni da zan saka musu inba inyi iskanci da iyayensu ba kuma in ɗauka vidio in tura musu...
Wani irin wawan burki na taka dan ban lura ba traffic ta riƙeni , tsayawa nayi tare da sauke gilashin mota ta ina kallon wata mace data bugawa wata mota itama dai masiffiyace itace take da laifi amma sai rashin kunya takeyi ,
Kyawawan motoci ne masu tsada kuma ta kashe musu fitilar baya kuma sai zagi takeyi tana cewa idan sunajin su wasu shegune itace maganin "yan iska sai an biyata motar ta data goge , tunda sune sukayo baya , duk wanda ya bata haƙuri sai tace batayin haƙuri uban waye ma ake tuƙawa a motar ?
Daga ciki aka sauke gilashin motar ya sauka a hankali , Dikko na faɗa tare da ƙarasa sauƙe gilashin mota ta dukanshi , matsawa matar tayi taci gaba da zazzagawa Dikko rashin mutunci , kuma ya hana kowa yayi mata magana , murmushi nayi tare da ɗaga kaina na kalli danja har yanzu ba'a sakemu ba , amma waccan wawiya ce da tasan Dikko da bata shiga rayuwarshi ba Allah dai yasa ba a gidan haya suke zama ba suma...
Ina tunani naga ta juyo tana kuka kome Dikko yace mata Oho su kuma an sakesu sun wuce , ɗaga gilashin motar nayi nima ana sakinmu nabi bayan motar matar da gudu dan ina so inji abinda Dikko yace mata take kuka ,
Itama gudu takeyi sosai nima na take tawa sosai , muna samun sarari na shiga gabanta , dole ta tsaya har yanzu tana cikin ɓacin rai , fitowa nayi daga cikin mota ta ko takalmi ban tsaya sakawa ba , na nufo motar matar har yanzu kuka takeyi , gidan gaba na buɗe na zauna , kallona tayi tare da cewa lafiya ?
Cikin yanayin damuwa nace abinda aka miki ne baimin daɗi ba shi yasa na biyoki in baki haƙuri me ya haɗaki dashi ne ? Cikin ɓacin rai tace ɗan iskan yaro ne gashi da siffar mutanen kirki amma baida mutunci , kuma baida kunya ko kaɗan , driver inshi ne yayo baya ya gogi motana ni kuma na kasa haƙuri na fita nayi musu magana shine duk sukamin shiru , ni kuma nace uban waye ma ake tuƙawa a motar ashe yana ji yana sauke gilashi ni kuma naje wurinshi da niyar ce masa bai kyauta ba shine yace min...
Wai kar inmi mishi rashin kunya bayan yasan komai , cukwui da nonon raƙumi nasha aka bani kyautar motar na taho kan titi ina ma mutane ganganci ko an faɗa min titi ɗakin mijina ne ? Ban tsaya naji sauran bayanin shi ba na taho saboda yaci min mutunci da yawa...
Lallai Dikko cikakken ɗan iska ne , haƙuri na bata tare da fita daga cikin motarta na nufi mota ta , wato ya yazo gari kuma hali na nan bai canja ba , mota na koma na shiga naja nayi gida ,
Tun kafin inyi parking naga Nana zaune a saman dakali sai kuka takeyi , ko inda take ban kalla ba na wuce cikin gida , dan har Nana haushinta nakeji saboda abinda su Amisty sukamin....
Wanka nayi tare da sake wanke kayana na bazasu a saman igiya , ɗaki na koma na shirya bayan na gama abinda nake na ɗauko kuɗin Amisty dana sace na fara irgawa , ban gama irgawa ba naji A ` i tana kwalamin kiran cewa kizo ana kiranki a ƙofar gida ,
Abinda raina ya bani Babana ne dan haka na ajiye kuɗin na fito , a tsakar gida Karima ke ƙyanƙyasa min cewa an saki Nana , idanuwa na zaro tare da cewa innalillahi garin ya ? Nayi maganar a sirrance tare da natsawa kusa da Karima ! Karima tace ai labarin sai kin dawo kije kiji kiran da ake miki , har ga Allah banji daɗin mutuwar auren Nana ba kuma na lashi takobin gyara aurenta da gaskiya ,
A ` i ta ƙara cewa jiranki akeyi , cema Karima nayi ki jirani ina dawowa , bayan na fito ƙofar gida nacewa A ` i waye yake nema na ? Filin da aka rushe gidaje ta nunamin kallon motar da akayi parking nayi sannan na kalli A ` i nace waye ? A ` i tace wani dattijo ne , wane kala ne ? Fari ne ! Ya yanayinshi yake ? A ` i tace wallahi ban lura dashi sosai ba yaro dai ya turo yace Sultana taje...
Kai tsaye na nufi wurin , tunda mu "yan kasuwa ne ina zuwa na buɗe mota na shige naja na rufe garam , shi kuma ya sanyawa motar lock , ko faɗuwa gabana baiyi ba domin dama raina ya bani za'ayi haka ,
Waye kai ? Na tambayashi domin duhu ya shiga , ni ne , ya bani amsa , kaine wa ? Na sake tambayarshi , *Shekara biyu...* ne ya bani amsa , dama ana ganin shekaru ? Umm idan bakya ganinsu zaki wuce su ? Ɗan gajeran tsoki yayi tare da cewa yanzu ba wannan ba me yasa kike san yawan yin kuka ? Ni banda isashiyar lafiya sai kiyi ta kuka kina taramin damuwa ! Me akayi miki ɗazu ne ?
Tou sai yanzu na gane ko waye , murya nabi na ganoshi , me kuma ya sake dawo dakai cikin rayuwata ? Na tambayeshi , bai bani amsa ba ya fara gangarawa da motar yana saukowa , riƙe sitiyarin nayi nace ina zaka kaini ne kuma ? Janye hannuna yayi daga saman sitiyarin baiyi magana ba a daidai lokacin daya sauko ya juya kan mota ta kalli titi...
Haba wai ina zakaje dani ne haka ? Ba tare daya kalleni ba yace yi haƙuri An mata yanzu zan dawo dake bazan daɗe ba , shiru nayi , kinyi haƙurin ko ? Ya tambayeni cikin sigar lallashi murya mai kwantar da hankali dasa natsuwa , shiru nayi ban sake magana ba , a hankali yayi tuƙi har muka fita bakin hanya , yana hawa titi kuma ya fara falfala gudu kamar yanda ya saba.
Tafiya mai nisa mukayi , sannan Dikko ya sauka daga saman titi yaci gaba da gurzar burji , ganin ɓoyayyar hanya yasa na fara kuka , kallona yayi tare da cewa wai miye ne ? Kina tunanin zanyi miki wani abu ? Ɗan soɓaro baki yayi sannan yace wannan hanyar tafi sauri ne bara mu koma titi tunda kinajin tsoro..
Nidai bana so ka mayar dani gida, kwaikwayo na yayi tare da cewa idan naƙi mayar dake kuma fa ? Sai in barka da Allah.... , murmushi yace An mata kenan waike bakijin kunyar min rashin kunya ? Banaji kai har abunda za'aji ma kunya ne , murmushi yayi bai sake magana ba ,
Wayarshi ya fiddo yayi latse² sannan ya kara a kunne , bayan an ɗauka yace fito na iso , kashe wayar yayi ya faka motarshi gefen wani gida ,
Duk dani dashi babu wanda ya sake magana har mutumin ya fito daga gidanshi , saitin Dikko ya tsaya ya gaisheshi cikin girmamawa nima ya gaisheni cikin mutuntawa , ko kallonshi banyi ba ban kuma ansa ba , gyara zama Dikko yayi sannan ya kalleni fuska a ɗaure yace bakiji ana gaisheki , gabana ya faɗi yanayin kallon da yayi min nace ai nace lafiya lau bakaji ba , kauda kanshi yayi sannan yace ya kukayi dashi ne ? Yake tambayar mutumin , Eh babu damuwa amma sai an koma hutu ,
Dikko yace har yaushe ne hutun zai ƙare ? Mutumin yace saura sati biyar , tsoki Dikko yayi yace ko na barta yanzu ? Cikin girmamawa yace ai matan gidan dukansu basa nan idan dai sun dawo zan kiraka insha Allah ,
Ba komai sai ka kira ɗin , inji Dikko godiya mutumin yayi sosai cewa yaga saƙo yafa gode sannan ya matsa , Dikko yaja mota muka dawo gida ,
A ƙofar gida yayi parking sannan yace ki kiyayi dawowa ta iskanci da rashin kunya cike da kai amma babu ilimi ni bana san zama wuri ɗaya da jahili kina ɗawainiya da fankon kai a haka kike tunanin zaki hareni shakaru biyu masu zuwa ? Dan dai zan fita katsina a daren nan amma wallahi dana zaune dake har tsawon sati biyar saina koya miki hankali bakauya dake kina fitowa ko hijabi babu ke ba ɗiyar kafirawa ba , zama saman dakali yawon banza fira da maza rashin kunya da tara "yan daba duk ranar dana waiwayoki jikinki zai baki labari fice ki ban wuri kafin in fara miki rashin mutunci , ya ƙarasa maganar tare da buɗemin motar na fice...
Fita nayi daga cikin motar jiki a sanyaye dan duk duniya babu abinda na tsana irin inji an danganta ni da kalmar jahila , kuma ba ƙarya bane jahilarce ni , fita katsina kuma da zaiyi yanzu zaije jigawa saboda an fara shagalin bikinshi ne naji ana ta faɗa ,
Banda tsoki babu abinda Dikko keyi da ana canja hali daya canjawa Sultana hali , duk duniya babu abinda baya so irin mutumin da baya ganewa , wallahi idan har Allah yasa ya dawo lafiya sai an nemi An mata an rasa idan zata shekara dubu saita ta wadata da ilimi , baida inda zai ajiyeta daya tafi da ita , kuma yana so kusanci mai girma da shaƙuwa ta shiga tsakaninshi da ita ,
Rayuwarshi da ita ya fara kuma yana so ya kulle da ita , farin ciki da duk wani jin daɗin shi yana hannun Sultana bai taɓa tunani zaiji soyayyarta ko kaɗan ba a zuciyarshi , daya san wannan ranar zata zo da baiyi mata abinda yayi mata a baya ba ,
Bai ɗauki mace komai ba amma ƙaramar yarinya ta hana mishi sukuni , da girmanshi waishi soyayya zata zo ta dama , kamarshi soyayya zata hana bacci abubuwa suyi ta masa yawo a zuciya , idan An mata tayi fushi ko kuka duk yanaji wannan bala'e kamar asiri.....
A ƙofar gida na samu Nana har yanzu bata daina kuka ba da takardar sakinta a hannu , wurinta na nufa dan jajanta ma......
Dikko kuwa yana komawa gida ya ɗauki abinda zai ɗauka suka kama hanyar jigawa......
12/09/2019
Jamila Musa....
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 31
*_Gaisuwa ta musamman gareki "yar uwa ta gari fatan alkairi da addu'ar Allah ya ƙara zaman lafiya da ƙauna mai girma tsakaninki da mai gidan ki , RABI MUSA ..._*
A damuwance na zauna kusa da Nana dan ina tattare da ɓacin rai da damuwa , ansar takaddar nayi da cewa saki nawa akayi miki ne ? Cikin kuka Nana tace saki ɗaya , tou ina shi mijin naki yake ? Cikin shashshekar kuka tace yanzu ya shiga cikin gida...
Tsoki nayi nace tou me yayi zafi haka har ya sakeki ? Ƙara fashewa da kuka Nana tayi saida tasha kukanta har ta godewa Allah nidai ban bata haƙuri ba kuma bance tayi shiru ba saida ta gaji ta rufe bakinta da kanta na kuma sake tambayarta abinda ya haɗa har akayi mata saki !
Aure zaiyi ! Ba tare dana kalli Nana ba nace tou ke ina ruwanki da auren banzarshi da zaiyi ? Saida Nana ta ƙara goge hawaye sannan tace ba auren ya dameni ba matar da zai aura itace ciwona , wace alaƙace tsakaninki da ita da har bakyaso ta zama abokiyar zamanki ne ?
Rumtse ido Nana tayi tare da ƙara rurewa da kuka tace *A ` I* zai aura fa , ɗan gajeren tsoki nayi tare da miƙewa nace A ` in banza A ` in wofi ! Da saboda A ` i har kika kashe aurenki ? Kiyi haƙuri Nana gaskiya baki da wayau kuma lokacin dana so na farkar dake daga baccin asarar da kikayi dake dasu A ` i kuka haɗu kuka riƙa cimin mutunci , kin watsa mutuncin aurenki kin lalata rayuwarki kika biye musu suka koya miki maɗigo ,{ Lesbian } ta koya miki kika koya kuma kika iya , gashi yanzu zata aure miki mijin kinga zaki tashi a tutar babu , ba abokiyar iskanci babu mijin aure..
Idan kuma zawarcin kika fuskanta ga "yan mata tsalala sabbin zubi suna yawo a gari suma basu samu sun shige ba , idan maza suna kallon lutsa²n zawarawa wankakki "yan gayu masu ƙamshi da gogewar zaman takewar aure , Nana gaki muguwar ƙaza babu sallah babu salati babu biyayyar aure ki faɗamin wane sakaran namiji zai kalleki bare yayi tunanin jajibar ki ya kaiki gidanshi ,
Ke kanki baki wanke kanki ba bare namiji yayi tunanin idan ya aureki zaki wanke mishi gidanshi , mazan yanzu sunfi san kwankwashshin mata , masu gogewa wanda zasu gyara masu gida ba su kashe musu gidaje ba , dan mazan yanzu suna kashe kuɗaɗe su gina gida na fita idon duniya , tou yau dake da A ` i wa gari ya waya Nana ...? Kin san zawarci kuwa ? Kai lallai kin tafka babban kuskure aradu...
Juyawa nayi zan shige gida Nana ta riƙoni cikin kuka tace ki taimaki rayuwata wallahi ko naje gidanmu korata zasuyi Baba baya san *Zawarci* shi yasa ban tafi ba , tou idan kuma na bashi haƙuri ya mayar dake kika sake jawo matsala fa ? Bazan jawo ba Mother kuma zan ɗauki duk shawarar da kika bani bazan sake tsallakewa ba ,
Tou zan baki shawara idan har kika ɗauka ba A ` i ba ko uwar A ` i mijinki bazai sake kallo ba bare ya sha'awar aure tunda sun zama maciya amana , Nana tace ngode sosai....,
Muje cikin gidan , lokacin da muka shiga har mijin Nana ya gama tattara kayanshi ya fito zai bar gidan ,
Gabanshi nasha tare da cewa Audu ina so zamuyi magana dakai don Allah , kallona yayi ƙasa da sama yace idan har maganar Nana zaki min bana so , ko Nana autar matace duniya na haƙura da ita , cikin sigar lallashi nace don girman Allah kayi haƙuri ka saurareni , ka bani dama nayi magana dakai na minti biyar kaɗai dan Allah badan halina ba ,
Tsoki yayi ya koma da baya ya jingina da bango sai haɗe rai yakeyi shi mai gida , murmushi nayi sannan na matsa kusa dashi nace Audu meya haɗaka da Nana ka saketa ne ? Banza yayi ya ƙaleni , ban damu da shirunshi ba naci gaba da cewa tou nidai don girman Allah ina neman alfarma kuma wannan alfarmar ba kowa zaka ma ita ba saini , na roƙeka da girman Allahn daya halicceka ya baka aron numfashi da lafiya , ya baka ji ya baka gani yayi maka hankali , idan har kaji daɗin wannan ni'imomi da ubangiji yai maka kayi haƙuri ka mayar da Nana ...
Cikin damuwa Audu yace Sultana Nana bata da mutunci kwata² ina ce duk abinda Nana kemin a gaban idonki , Nana ta rainani itace dakamin tsawa fita ba izini na magana da mazan waje duk wanda nace bana so tanayin tarayya dashi sai ta kafe tayi , rabon da inyi kwanciyar aure da Nana tun muna tsohon gida , na rabata da A ` i taƙi ta rabu da ita , A ` i tana so na kuma tana tausayamin sai in aurota dan ta kwantarmin da hankali na , kuma nace zan auri A ` i sai tacemin bata yadda ba ? Bayan tana san A ` i ta kasa rabuwa da ita tou idan na auro ta ta zama abokiyar zamanta ai duk wata ƙauna ya kare ko ?
Duk cikin ɓacin rai yakeyin maganar har wata maganar ma bata fita , haƙuri na bashi saida na tabbatar ya sauka sannan nace tou aurenka da A ` i fa babu fashi kayi aurenka bama hanaka , amma kayi haƙuri ka mayar da Nana dan soyayyar da kake ma manzan rahma S. A. W ,
Jinjina kai yayi yace in zauna da ita da baƙin halin nata da ƙazantar da duk iskancin da takemin a haka ? Karka damu mayar da ita sauran gyaran duk nawa ne idan bata gyara ba ni da kaina zan ƙaro maka mata sadaki da lefe duk ni zan bayar kuma zan baka jari , tou shikenan na mayar da ita...
Godiya nayi mishi sannan nasa Nana ta anshi kayanshi ta mayar cikin ɗaki , nayi musu saida safe , na wuce ɗakina , ina shiga Karima ta shigo tana cewa wallahi banso kika sa aka maida ita ba , banza nayi bance da ita komai ba , ta ƙari kilbibinta naji babu ansa ta fice....
A ɓangaren su Amisty kuwa ina fita Momyn Hafsa ta cire wayar wuta taci gaba da dukansu babu ji babu gani , tana dukansu tana cewa wato na hanaki wannan iskancin bakya bari ko ? Tou wallahi yau saina kashe ki , dama tunda nabar gidan nan na kasa samun natsuwa zuciyata tana saƙamin tunda bana nan nan zaki kawo "yan iska su tarar min a gida , Amisty ganin hankalin Mom ya fita jikinta tana dukan Hafsa har ta daina motsi yasa ta biyo ta bayanta ta fice da gudun tashin hankali ,
A bakin get ta faɗawa mai gadi Momy ta kashe Hafsa , da gudu ya nufi ɗakin Hafsa , ita kuma ta fice daga gidan , saman Hafsa ya samu Momy tana dukanta tana yaginta duk tayi mata kaca² jini saibin jikinta yakeyi , da sauri ya ciro wayarshi ya kira Yayan Hafsa ya faɗa mishi duk abinda ake ciki dan babu yanda za,ayi ya ɗauke Momy , babu ɓata lokaci ya iso , dakel ya ɓanɓare Momy sannan mai gadi ya kama mishi Hafsa suka tafi asibiti da ita....
A asibiti kuwa likitoci sun tabbatar cewa Hafsa bata mutu ba , dan haka suka shiga bata taimakon gaggawa dan ceto rayuwarta....
Amisty kuwa a gidan Asma'u ta yada zango , tana zuwa wanka tayi Asma'u ta kawo mata abinci taci sannan suka ɗora iskancinsu daga inda suka tsaya !
Tunda safe almajirai suka fara kawo kayan "yan gidanmu a cikin baro , sahu ɗaya yaran sukayi nace idan sun koma suce a samu mota a zubo kayan zan bada kuɗin ,
Nana na kira ɗakina nayi mata nasiha , cewa ki rufawa kanki asiri ki gyara halayenki , ki zama mai tsabta ki fita daga harkar zaman majalisa kija mijinki jikinki , ki zama mai biyayya da haƙuri a rayuwarki , karki kuskura mijinki ya sake neman haƙƙinshi a wurinki ki hanashi , ko inuwar Audu kika gani ki bashi natsuwa ,
Tsafta a rayuwar aure itace jigo , kamar yanda baki shiga makaranta dole saida uniform , bazai fa yuwu ba ki gama duk wata fangila taki kisha yawo cikin rana ga kaurin zufa ga warin rana gana haƙi , zaninki na zarnin fitsarin yara ga ƙarnin tunbiɗi babu wanka babu wanke jiki ba sake kaya a haka zakije kice namiji ya kwanta dake ? Wace natsuwa zai samu ? Taya zai samun natsuwar da zai biya buƙatarshi....?
To idan zaki gyara ki gyara , ki nemi ruwa da turare sabulun wanka da man shafawa ki fara wanka , ki zama mai biyayyar aure kima mijinki sannu da zuwa idan ya dawo ki masa rakiya idan zai fita tare da addu'ar Allah ya bashi halal inshi , ki gode masa akan abinda ya kawo miki ki kuma yi haƙuri idan bai kawo miki ba , ba kullum ake nema a samu ba , dole wata rana a samu wata rana kuma a rasa , kin dai ga yanda rayuwar take tafiya dan haka ki tashi ki miƙe da gaske ki janye tunanin mijinki daga kan A ` i idan kuwa ba haka ba ta shigo to aradu sai tayi waje dake...
Jiki a sanyaye Nana tayi godiya tare da cewa bara in tashi nace da dai kin kyauta ki kuma zuƙe jikinki daga sabgar matan banza , insha Allah Mother ngode sosai , yayi kyau na faɗa tare da cewa zan fita saina dawo , addu'ar a dawo lafiya tamin , ni kuma na irga kuɗi 20K na bata idan an kawo kaya ta sallami masu motar , in an rage canji ta ajiyemin , insha Allah ta amsa min sannan ta fita , nima na shirya na fice !
Anguwar su Amisty na nufa , kafin inkai ƙofar gidansu nayi parking jikin wani shago , amma ina hangen gidansu Amisty , wayata na kallo da take kuka , lambar Amisty ce keta tsalle saman screen in wayata , kamar bazan ɗauka ba na ɗauka dan inje me zatace ! Ina ɗauka ta fara ,
Tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkairi ba , ciwon tsakar dare mai hana bacci , ance kinje anguwarmu bayan kin sacemin kuɗi me kuma kikaje yini ? Murmushi nayi tare da gyara zamana sannan nace tsauni da ƙaya da tsawon zango maibi da ƙafa sai ya daure , yaro bai ɗaukar yaro dan kansu matsa sai sun faɗi , guguwar tsakar dare ga tsoro ga ban al'ajabi , kura bata cin damisa saidai taci zaki , ki saurari kaidina zuwa gobe kamar yanzu , kashe wayata nayi dan ganin mahaifin Amisty ya fito ,
Yana wucewa da motarshi nima nabi bayanshi da tawa motar , a hankali yake tuƙi nima a hankali nake binsa saf da ƙafa har ya isa wurin aikinshi , inda yayi parking nima a wurin nayi yana fitowa nima na fita murmushi ɗauke da fuska na nufi wurinshi ,
Da sallama na isa wurinshi tare da cewa sannu , yawwa ya ansa yana kallona , murmushi nayi tare da cewa naga kamar baka ganeni ba ma ko ? Cikin muryar dattijantaka yace Eh ban gane ba gaskiya , ajiyar zuciya na sauke tare da cewa me yasa baka gane mutane haka ? Murmushi yayi sannan yace to bani sani mana , nace tou sakamin numberka mayi waya dai zuwa dare , babu musu ya ansa ya gwagwaɗamin lambar shi nayi ajiyeta da Lamba shidda , bayan na gama ajiyewa na kirashi yaga tawa sannan nayi masa sallama na wuce ,
Daga nan ban zame ko ina ba sai Office in Babansu Hafsa , suna da dokoki masu tsaurin gaske dan haka aka hanani shiga , nayi ² aka hanani , lambarshi na tambaya itama dai ban samu ba , dan haka na haƙura na nufi gidansu Hafsa ,
A wurin mai gadi na samu number bayan na bashi cin hancin 5K , ina ansa na nufi gida , cikin farin ciki nayi sallama dan har "yan gidanmu sun dawo dukansu , amma Inna bata dawo ba , Babana kuma saida dare zaizo ,
Cikin kulawa nake gaishesu amma kowa sai ya ansa min a wani dusasar , haka nan dai na haƙura na wuce ɗaki na , saida nayo wanka na fito Nana ta shigo ta bani cikon kuɗina tace ta bayar da kuɗin ta sallamesu , godiya nayi mata sannan tace bara ta sharemin ɗakina , nace babu damuwa ta share...
Satin "yan gidanmu ɗaya da dawowa amma Babana baizo ba kuma Inna bata dawo ba itama , Baban Amisty da Baban Hafsa munayin waya dasu , kowa ya damu yaushe zamu haɗu dan wayar babu abinda ke cikinta banda zallar sakin layi , har yanzu badai mu haɗu ba kuma sati biyar ya ragemin a lissafin satikan da Dikko yake lissafi....
Mijin Zalifa ma ya matso lamba mu haɗu amma yanzu bashi ne gabana ba , Alaji wato Abbu Afsar shi kuma yana min hidima sosai wacce ta wuce hankali ma , maganar wani abu har yanzu babu wani abu daya shiga tsakaninmu yadai cemin yana so muyi aure na zama abokiyar rayuwarshi niko ba auren ne gabana ba ,
Zalifa kuma tazo min da labarin mutuwar ƙawar Amisty wacce muka haɗu da ita a station Fadeela wacce tayi cikin shege da aurenta kuma itace ta kawomin Zalifa gidana , ta mutu sanadiyar rataye kanta da tayi bayan tasha gwagwar maya wurin zubar da ciki bai zubu ba , kuma sunje wurin bokaye anyi asiri anyi tsafin amma cikin bai fita ba , kuma anyi ƙoƙarin ɓatar da hankalin mijin dan ya yadda cikinsa ne shima ba'a samu nasara ba , dan haka ta kashe kanta , ...
A ɓangaren ango D K yau akayi walima amarya ta tare a gidan angonta Dikko dake G R A { karkara road } , an gina gida na faɗi a faɗin birnin garin katsina , an kashe kuɗi kuma anyi hidima ta kece raini , gida ya tsaru iyakar tsaruwa , iyayen amarya suma sun kashe kuɗi wurin ƙayata ɗakunan amarya da palukanta tunda kuɗi da kuɗi ne suka haɗu abindai sai wanda ya gani , duk inda ka nufa a gari maganar auren Dikko akeyi da gidanshi , gaskiya Dikko mai sa'a ne...
Cikin farin ciki ango ya shiga ɗakinshi danshi babu wani abokin daya rakoshi cewa yayi baya so , bayan yayi wanka ya saka jallabi ya nufi ɗakin amarya , itama tayi wanka ta shirya cikin shiga mai kyau da burgewa , a ɗakin amarya yayi alwalla suka gabatar da nafila raka'a biyu dan miƙa godiya ga mai duka ,
Bayan sun gama sukayi addu'o'in neman zaman lafiya da wanzuwar arziƙi mai ɗorewa tare da addu'ar Allah ya basu zuri'a masu albarka ya kuma kauda sharri da fitina a zaman aurensu , bayan sun gama ya dafa kanta yayi mata addu'a ,
Bayan ya gama ya koma palo dan ɗaukoma amarya ɗan abinda ya shigo mata dashi kamar dai yanda kowa ya sani anayi , sama ² Sadiyya taɗan lallasa tace ta ƙoshi , shine ya tattara sauran yaje ya zubarwa da karnuka , bayan ya dawo ya wanke hannunshi da bakinshi ɗakinshi ya koma ya sake ciwo ɗama dan shima ya nuna tashi jarumtar a daren farkonshi da matarshi...
Itama amarya fitar ango ta ƙara gyarawa ta cuscusa na cusawa ta shafa na shafawa ta kukƙurɓa na ƙurɓawa ta ɗaga katifa ta jera layunta , ango na dawowa itace ta taroshi dan a halin yanzu sha'awar Dikko ta rufe soyayyar da take mishi ,
Cike da bariki taja Dikko suka sauka saman gado , daga nan labari ya fara canja salo , kowa dai gwanine wurin ganin ya nuna shi wani shege ne , Dikko kuwa a zuciyarshi yake mamakin Sadiyya dan yasan duk macen da bata goge ba a harkar maza tana tsoron namiji bare kuma a daren farkon ta ,
Yayin da Sadiya kejin daɗin salon Dikko ta yaba mishi ko a haka aka tsaya tasan Dikko namijin duniya ne gaskiya Dikko ya karanci mace yasan duk wasu salo na burge da saka nishaɗi , ya iya sirrika masu tsayawa a zuciya , duk mazan da tayi mu'amula dasu tasan Dikko zakara ne a cikinsu ,
Soyayya tai nisa ango ya tunkari gidan sarauta , amma me zai samu ? Labari yasha banban domin dai wani ya rigashi hayewa saman kujerar mulki , la'ilaha illa anta sub'hanaka innee kuntu minazzalimeena , lahaula wala kquwwata illa billahi aliyyil azeem , Dikko ya faɗa tare ci gaba da cewa Allah na tuba , Allah ka yafemin , kukan makirci Sadiyya ta fara wani irin kallon tsana Dikko yabita dashi yayin da yake kallonta kamar an mata a daren daya kacaccala mata rayuwa ,
Yaya DK don Allah ka rufamin asiri yanda Allah ya rufa maka , ka rufe wannan sirrin don girman Allah karka tona min asiri.... Wani irin tashin hankali yazo a zuciyar Dikko ya tsaya yayi ² yayi control in zuciyarshi ya kasa yana ƙoƙarin sauka daga saman Sadiyya matsalarshi tazo , wani iri ihu yayi ya tafi gaba ɗayanshi kafin kace mi ? Tuni lumfashin shi ya tsaya cak..... Wannan itace babbar matsalar dake damunshi da ranshi ya ɓaci sai kawai numfashin shi ya ɗauke....
Cikin ruɗewa ta ɗauki wayarta ta fara kiran Momyn Dikko , babu ɓata lokaci ta ɗauka Sadiyya ta karanta mata halin da Dikko yake ciki , jikin Momy na ƙyarma ta miƙe "ya "yanta suka riƙeta saboda karta faɗi ta samu matsala , kuka ta farayi tana Allah ka tausawa rayuwata idan har Dikko ya samu matsala mijina ya shiga tashin hankali ubangiji ka dafamin a dukkan lamurarra na , meya faɗawa Dikko rai a wannan dare ....?
Kai ku sakeni ta faɗi maganar tare da kwacewa ta shiga ɗakinta ta nemo wani magani da ake mishi amfani dashi idan lalurarshi tazo , ko Dadyn bata faɗamawa ba driver ya ɗaukota tayo gidan Dikko dan tasan idan har Dady yaji to idan dai Dikkon bai mutu ba kilashi yana iya mutuwa...
Sadiya kuwa tana gama waya da Momy ta sakama Dikko gajeren wando dakel , sannan ta lulluɓeshi da bargo ,
Babu ɓata lokaci Momy ta iso , Sadiyya ta buɗe mata ƙofa kuma itace tayi mata jagora har zuwa ciki , a ɗakin Sadiyya ta samu ɗanta kwance cikin tausayawa tace meya haɗaku ne ? Sadiyya cikin daburcewa tace ba komai wallahi , Momy tace bazai yuwuwu ba me kikai masa ne ? Fashewa da kuka Sadiyya tayi tana cewa wallahi ba komai Momy , Hmm shine abinda Momy ta faɗa tare da matsawa kusa da Dikko ta buɗe bakinshi ta zuba mishi magani , kamar mai ciwon aljannu haka ya tashi kamar babu abinda ya taɓa faruwa dashi , kallon Momy yayi tare da cewa lafiya kika zo ? Ya ƙarasa maganar yana ma Sadiyya kallon tuhuma ,
Cikin so da ƙauna Momy tace ba komai yanzu ma zan tafi , zaiyi magana Momy tace ba komai , tana faɗin haka ta fice daga ɗakin da maganinta bata barshi ba , Sadiyya kuma gefe ta koma ta zauna ta rasa inda zata saka ranta dan Dikko ya tsareta da ido....
Tsoki yayi bayan wani lokaci sannan ya gyara kwanciyarshi , idonshi na kallon sama ya rasa abinda ke mishi daɗi , amma yayi alƙawari kamar yanda Sadiya ta nemi ya rufa mata asiri wannan maganar duk duniya babu wanda zaiji kuma babu wanda zai sani , kuma ya zamarshi dole ya zauna da Sadiyya abin family a saketa zuminci zai samu damuwa.....
Saukowa yayi daga saman gadon ya nufi ɗakinshi , Sadiyya kuma abun duniya duk ya dameta , sai yanzu take nadamar da bata da rana.....
13/09/2019
Meelat Musa....💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 32
Dikko kuwa yana komawa ɗakinshi wanka yayi , a gaggauce ya shirya bayan ya fito cikin ƙananan kaya , blue in riga da upwhite in wando shima takalmin irin wando ne amma rufaffi ne takalmin , ya naɗe hannun rigar daidai guiwar hannu , turare ya fesa sannan ya ɗauki makullin motarshi ya nufo ɗakin Sadiyya , a bakin ƙofa ya tsaya har yanzu tana nan zaune inda ya barta kamar asara ,
Kamar ba abinda ya faru dashi ɗazu kuma babu wata damuwa a tattare dashi yace zanje in dawo yanzu ! Cikin jin kunya da kama kai tace ina zakaje yanzu ? Naga har 11:05pm shima kallon agogon yayi sannan yace Ey ai na sani juyawa yayi tare cewa saina dawo bai jira yaji abinda zata ce ba...
A wannan dare kai tsaye gidanmu Dikko ya taho ni kuma a lokacin ina zaune saman dakali dani da Alaji muna fira , tun kafin ya fito nasan shine dan tuƙishin yasha banban dana kowa , cikin filinshi yayi parking sannan ya juyo motar ya haskemu da hasken fitila , Alaji dake da matsalar ido ya fara kauce² yana burza idanuwanshi dan gani ke barazanar ƙare mishi...
Fitowa Dikko yayi ya zauna saman mota , Alaji kuma miƙewa yayi ya fara laluben hanya dan gaucewa haske , cikin damuwa na kalli Alaji ina gilashin ka ne ? Ba tare da yayi magana ba ya miƙomin makullin mota , da sauri na ansa na nufi motar dan ɗauko masa gilashi ,
Da sauri na dawo da gilashin a hannuna nace tou saka , bawan Allah hannunshi yana kyarma ya ansa ya saka , ajiyar zuciya ya sauke cewa waye ne ya haska ? Baiga mutane zaune a wurin ba ? Banji daɗi ba gaskiya , haƙuri naba Alaji tare da cewa idan akace kayi hukunci wa mutumin daya haska maka ido me zaka mishi ? Alaji yace wallahi da fitulun motar zan kashe...
Shiru nayi ina nazari dan nasan idan har na faso fitulun motar Dikko na sake tarowa kaina fitina , tou amma ai ba gidan haye muke zaune ba , zuciyata ta ingizani in koma cikin gida kawai in ɗauko taɓarya na rusa fitulun kamar yanda Alaji yake sha'awar gani...
Kallo Dikko nayi dake zaune a saman mota yana kallonmu tas , gaskiya bana iyawa idan ya riƙeni a wurin can jakin duka zaimin babu wanda yaji kuma babu wanda ya gani , ya dakeni ya daki banza , kallon Alaji nayi tare da cewa barshi ya samu daidai dashi muje ka tafi gida ,
Rakiya nayi ma Alaji har wurin mota ya shiga , addu'a nayi masa Allah ya tsare hanya Allah ya fisheshi dare , ina tsaye a wurin harya tafi , buzum² na nufi gida dan anguwar ta ɗinke da duhu sosai gashi babu wasu "yan gayu da zasu kunna gen bare su bamu sadakar fitila ɗaya a cikin anguwa muga haske , yanda baki baya ɓace maka a cikin duhu haka ƙofar gidanmu bata ɓacemin dan haka na tunkari gidanmu cikin sauri...
Ina ƙoƙarin shiga Dikko ya fizgoni tare da cewa yawwa kwanakin baya kince zaki gauraya dani nine abokin wasar ki yarinya ? Ya faɗi maganar cikin neman fitina idan yaji haushi mi yasa tun a lokacin baiyi magana ba ? Sai yanzu ?
Da nayi tunanin babbaka mishi ashariya amma sai zuciyata tace karki biye mishi so yake ya jagula miki lissafi , idan har kika zageshi ko kika faɗa masa baƙar magan akwai wani abu a zuciyarshi , kawai kice masa yayi haƙuri , kinga idan baiba kinsan masifa yakeji...
Cike da rashin kunya nace kayi haƙuri amma hakan baya na nuna inajin tsoronka bane a , a , dan ɗan dambe yaja baya ba yana nuni ya tsorata bane gyaran tako ne , a haka zaki gyara takon kina tarayya da makafi ? Baki ba kwalwarki natsuwa ba zance har 11:49pm a haka kike tunanin zaki gyara tako ? Duk macen da tasan abinda take tana cikin gidansu kamar yanzu amma ke kina nan kina balbaɗewa a santa , kindai ji kunya !
Cikin jin haushi nace kaine kaji kunya ƙato dakai kana faɗa da mace , murmushi yayi tare da cewa kindai gane baki iya gauraya da Dikko kenan ? Tunda dai kinji tsorona kin fanshi kanki a daren nan amma dasai na hanaki baccin dare...
Jana yayi tare da cewa nima muje kimin rakiya , tirjewa na farayi bazan je ba , kallona yayi sannan yace kifa wuce muje idan ba haka ba kinsan Allah ɗaukarki zanyi , tashi nayi na daina tirje² cikin murya mai saukar da kasala yace muje ya faɗi maganar tare da sakin hannuna , gaba nayi yana bina a baya har wurin mota , buɗewa yayi ya shiga ni kuma na juyo da sauri , shima cin taya yayi ya biyoni da sauri tare da cewa An mata zo zo zo banza nayi na shige gida , saida safe ya faɗa , ko inda yake ban sake kallo ba na shige abu na...
12:20am Dikko ya isa gidanshi zuciyarshi na ƙara azabtuwa da soyayyar Sultana , addu'arshi a daren yau itace yanda yakejin kishin Sultana ubangiji ya sanya mata kishinshi a zuciyarta , yanda yakeji soyayyar ta itama Allah ya saka mata soyayyarshi , yasan dama babu ranar da zata ga girman shi tunda ya gama ɓareshi a wurinta , amma yasan idan dai tana mishi soyayya zatasan girmanshi dan darajar wannan son nashi dake zuciyarta....
Da sallama ya shiga ɗakin Sadiyya har yanzu tana nan inda ya barta tasha kuka har ta godewa Allah , cikin tausayawa ya kalleta yace har yanzu baki kwanta ba ? Dakel ta sauke ajiyar zuciya cikin kuka tace ina kaje ? Kusa da ita ya duƙa ya ɗagota cikin sigar lallashi yace meye ? Ki daina kuka kinji ya ƙarasa maganar tare da rumgumeta , cikin shashshekar kuka tace ina kaje ? Shine ka tafi ka barni ,
Shiru Dikko yayi , Sadiyya taci gaba da cewa nasan da ciwo a rayuwarka yau kaji babu daɗi kuma nasan duk lokacin daka kalleni zakaji baka ƙauna na , murmushin ƙarfin hali yayi cewa haba keko waye yace miki haka ? Sadiya tace ka daina ɓoyewa Yaya DK nasan babu daɗi kuma akwai ɗaci kayi haƙuri ka rufemin wannan sirri ko bayan babu ni...
Lallashin ta Dikko yayi saida ya tabbatar ta samu natsuwa har tayi wanka sannan suka kwanta , har Dikko yayi bacci Sadiyya ta kasa bacci baƙin ciki yazo ta taru a zuciyarta sai kukan zuci takeyi tare da nadamar biyewa soyayyar zuciya...
Tunda safe na farajin hayaniyar "yan gidanmu masu abun kuɗi suna ɓoyewa , masu wayoyi na kashewa suna adana abunsu , muryar Naja yayata naji tana cewa wallahi gashi nan yayi parking fa , zai fito , zai fito ya fito , gashi nan zai shigo zai shigo.... Sai kuma naji gidan ya natsu yayi shiru kamar babu masu rayuwa a cikin gidan , tashi nayi na leƙo ta jikin window dan ganin wanda yake shigowa , Babana duniya kenan , kai ina san Babana wallahi dan nafi sanshi fiye da Inna ,
Da sauri na buɗe ƙofa na nufi wurinshi da gudu ina mai farin ciki da ganinshi , cikin soyayyar da ya saba nunamin ya riƙeni tare da cewa bi sannu Uwar masu gida karki faɗi , yayi maganar cikin jin kunyata ya kasa haɗa ido dani tsaɓanin yadda yakemin a baya , rumgume Babana nayi tare da fashewa da kuka nace me yasa ka tafi ka barni Babana ? Kasan ina sanka banajin daɗin rashinka a kusa dani ? Me nayi maka kayi nisa da rayuwata ?
Shiru yayi baice komai ba , naci gaba da cewa idan har akwai sauran wata soyayya bayan wacce nake maka Babana itama na baka ita dan jaddada soyayya da ƙauna a gareka , ina alfahari dakai daka zama uba a gareni , kuma ina addu'a na kasance dakai har numfashin ƙarshena a duniya , kuma ina roƙon Allah yasa kar na wayi gari babu kai a duniyar nan , ɗagowa nayi cikin kuka na kalli cikin idon Babana nace karka sake tafiya ka barni ka kasance dani dan nima na samu duk irin soyayyar da ko wane mai Baba yake samu a duniya Babana...
Baiyi magana ba yaja hannuna muka fita ƙofar gida , motarshi ya buɗe muka shiga muka zauna , cike da soyayya Babana ya kalleni yace Uwar masu gida duk wata soyayya ta duniya wacce Allah ya halitta ta bayan soyayyar shi da manzansa da nake a duniya soyayyarki ke ɗaya tak ta goge soyayyar kowa a faɗin duniyar nan , idanuwana basa kallon kowa haka kuma zuciyata bata nunanin wani a duniyar nan idan bake ba ,tun daga ranar dana sameki ubangiji ya ɗoramin jarabtar soyayyarki a zuciyata , ni Allah bai ɗoramin ciwon son "ya "ya ba , wallahi bansan yanda akejin soyayya ɗiya ba saida Allah ya kawo zamaninki...
Nayi kukan baƙin ciki nayi nadama da har na kasa samar miki farin ciki , tunda nake a duniya ban taɓa nema na rasa ba , haka kuma babu wani abu na rayuwa daya taɓa kubcemin matsawar inajin soyayyarsa a zuciyata , an cuceni an kuma yaudareni da har aka samu nasarar rusamin farin cikin rayuwata , nayi tir da Allah wadai dana zama sokon uban da ya kasa ceto rayuwar "yar sa....
Mamana ki yafemin ni ban cancanci na zama uba a gareki ba , banso kika zo cikin rayuwar wahala ba , banso ba kuma banji daɗin haka ba , da ana canja uba dana zaɓar miki mafi girma da matsayi a duniya ya zama shine mahaifinki domin kiyi rayuwa mai inganci ba rayuwar dana sani ba ,
Uba ɗan caca bashi ne ya dace da rayuwarki ba , ba nine ya dace na zama uba a gareki ba bayan ni na kasance bana cikin mutanen kirki , idona ya rufe da duniya bansan duniya bata da daɗi ba saida na kasa magance duk wata damuwa taki , saboda haka ki daina alfahari dani nasan ke da kanki zaki gogeni daga lissafin rayuwarki matsawar kika gane wane irin mahaifi gareki a duniya...
Girgiza kaina nayi tare da cewa duk rayuwa sunanta rayuwa , jin daɗi ko rayuwar baƙin ciki baya sa a gane mai rabo a duniya , girman zunubi da saɓo baya sa kakai mutun jahanma domin rabon rahama wannan daga Allah ne , ɗan caca da ɓarawo duk matsayin su iri ɗaya ne a idon al'umma amma a wurin ubangiji azabarsu ta rabauta , manta da abinda ya faru baya kawai mu fuskanci rayuwa , amma waye Bello ? Meye tsakaninka dashi ? Me ka mishi wanda har ya zaɓi nice zaka saka a wasan caca.....?
Hawaye ya gangaro daga idanuwan Babana , murmushi nayi tare da riƙe hannunshi ina masa kallo mai tattare da soyayya.....
Cikin soyayya shima ya kalleni sannan yace ki jirani ina dawowa yanzu zan mayar da mutane motarsu , idan na dawo zan faɗa miki asalin waye Aliyu Binna , haɗuwata da Bello abinda ke tsakaninmu saka ki a wasan caca duk zakiji , sakin hannunsa nayi ba tare da nayi magana ba na fice daga motar , shi kuma yaci sitiyari yabar anguwar , cikin gida na koma ban damu da hararar da akemin ba naci gaba da sabgogin gabana....
Har yanzu Sadiyya bata daina kuka ba , kuma Dikko yayi lallashin duniya taƙi ta daina kuka kuma taƙi taci abinci , daga jiya zuwa yau ta rame idanuwanta sun kumbura , Dikko ya gaji yace mata kode shine bata so ? Sadiyya tace duniya da tasan zata zama matarshi kwata² da bata ɓata rayuwarta ba , gajiya yai ya fita sabgarta yaci gaba da huɗɗoɗin gabanshi zai bar gari ana rantsar dashi idan Allah ya kaimu gobe...
Cikin ƙananan kaya ya fito yayi kyau sosai a cikin coppie brown in riga, da wando ash mai haske , rufaffin takalma brown mai haske yayi stocking yafa ɗauku iyakar ɗaukuwa yayi kyau sosai , ɗakin Sadiyya ya nufa yana ɗaura baƙar agogo a tsintsiyar hannunshi yana cin cigom cikin salo mai ɗaukar hankali...
Da sallama ya shiga tana kwance saman gado cikin bargo ƙasa² kakejin sautin kukanta , yaye bargon yayi fuska a haɗe yace waike baza ki daina kukan banzar nan ba ,? Nifa bana san iskanci bana so inyi ta magana abu ɗaya , zan tafi idan kinga dama kiyi shiru idan kinga haggu kiyi ta kuka har masu kuka suzo su sameki....
Murmushi Sadiyya tayi tare da cewa Allah yasa ka sauka lafiya , kuma kayi haƙuri idan har kazo ka samu na mutu to ka yafemin , tsoki Dikko yayi ya fita ba tare daya sake mata magana ba ,
Al ' Ameen shine yaja su , Dikko ne a gaba mutane biyu kuma a bayan mota , su huɗu kenan , kuma saida suka biyo ta anguwarmu amma yau bamu samu haɗuwa da Dikko ba , kuma ya aiko kirana har gidanmu akace masa bana nan , bayan kuma ina nan , amma banji lokacin daya aiko kirana ba.... ,
Dikko yaso ya ganni amma haka ta gagara , dole ya haƙura suka ibi hanyar Abuja.......
14/09/2019
Jamila Musa....💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 33
Tafiyar Dikko babu jimawa Nana ta shigo take faɗamin mai gidan dokuna yazo nema na amma ance bana nan...
Tsoki nayi ban bata ansa ba , tsintsiya ta ɗauka taci gaba da share ɗaki , ni kuma jakata na ɗauko na buɗe ina kallon abinda nake fesawa mutum ya tafi bacci , jijjigashi nayi bayan naji sauran abinda ya rage na mayar a jaka ina mai addu'ar haɗuwa na da iyayen su Hafsa...
Maganar Babana naji a tsakar gida yana cewa duk iya ƙwarewa munafircinku na gano ku baƙaƙen munafikai , wato duk lokacin da kukaji motsina sai ku kashe wayoyi ku ɓoye kar nace ku bani kuɗi kuce babu , idan naji babu zansa wayoyi suci kasuwa , dan ku bani kuɗaɗen , lissafo duk yayuna yayi masu waya cewa kowa ta kawomin wayarta dukanku ancemin har face buk kukeyi , kuma na gani da idona dan babu wacce banga hotonta a cikinku ba...
Cike da damuwa suka fara fitowa Babana yana zaune a saman kujera kowa sai ta bashi ta koma ɗaki cike da ɓacin rai , bayan ya gama tattare wayoyin kaf ya kira babban yayanmu yace maza kasuwar tsaitsaye ka siyar min dasu , da guda² yake bashi wayoyin tare da faɗa masa adadin farashin da yake so a siyar da ko wace waya...
Shima Yayanmu cikin fargaba yace Baba ai duk kuɗin daka faɗa baza'a siya a haka ba , wata irin harara ya zabgaga mishi tare da cewa wannan kuma damuwarka ne , kai tunani ya rage ma yadda zaka siyar danni duk kuɗin dana faɗa su zaka kawomin a ko wace waya na faɗa maka , yana faɗin haka ya miƙe ya nufo ɗakina...
Da sauri Nana ta ajiye tsintsiya saida tayi masa sannu da zuwa ta fice daga ɗakin , bayanta yabi da kallo zuciyarshi tana ƙisima mishi wasu abubuwa , amma bai ansa sannu da ta masa ba...
Gefen katifa ya zauna kusa dani cike da soyayya irinta mahaifa yabini da kallona mai tattare da tsantsayar soyayya , murmushi nayi nima ina kallonshi nace Babana baka da kuɗine ? Murmushi yayi bai bani amsa ba , nima murmushin na sakeyi kamar yanda yayi sannan na jawo jakata ina cewa ni ina da kuɗi bara na baka...
Ansar jakar yayi tare da rufeta yana mai cewa nifa ina da kuɗi Mamana kinsan mage kota ƙoshi sai ta hari ƙwari , ajiye kuɗinki anjima zan ƙaro miki wasu , ajiye jakar yayi a gefena sannan yace Mamana tun kuna ku hamsin da bakwai har yau an wayi gari kun zama ku sittin ciff,
Tsoki yayi tare da kauda kanshi gefe yace tirr , wallahi da za'a tambayeni abinda nake so a musanya min da tulin "ya "yan nan ke kaɗai zan cire a cikinsu sauran a mayar min dasu daga motocin hawa sai ƙayataccin gidaje , ita kuma matar malam bahaushe ita dai burin ta kawai ta tara taron "ya "ya ita dai a mutu kawai taci gado , tou ban ajiye ba kuma bazan ajiye ba duk wacce ta haifi "ya "yanta taji da abunta ni babu ruwana...
Uhum Babana kenan mugunta kamar mai tsaron gidan yari , wato karya nema ya ajiye idan baya duniya a ci gado , hmm halin Babana saishi kallo nabi shi dashi ga wayyen mutum kisan boko ɗan gayu mai buɗewar ido yana da ilimin boko mai zurfi amma saboda tsabar baƙin ciki ko aikin gwamnati bayayi , tunda yaga ana ruguwar haifar mishi "ya "ya ya daina aiki ya koma caca...
Kallona yayi yace ki ɓoye sirrin mahaifinki koda bana faɗin duniyar nan , ki zama maimin addu'a bayan mutuwa ta ɗaukeni daga kusa dake , ki nunamin soyayya irin wacce nake nuna miki Mamana , ina miki soyayyar da duk duniya bana ma kowa irinta , banajin kunyar kowa idan nayi abinda ban kyauta ba amma Allah ya sani inajin kunyarki Mamana , babu wanda ya isa yasa nayi ko na bari amma idan har kika hanani na hanu , labarin waye Binna kuwa zan faɗa miki ne saboda abinda ya faru dake wanda ba'a san raina hakan ta faru ba , kuma ki yafemin na roƙeki ya haɗa hannayensa biyu tare da ci gaba da cewa kuma bazan sake tafiya na barki ba , ya ƙarasa maganar yana mai min kyakyawan murmushi ....
Riƙe hannunshi nayi tare da cewa kayi alƙawari ? Jinjina kai yayi yana murmushi yace nayi miki alƙawari , nima murmushin nayi tare da cewa nima nayi maka alƙawari Babana bazan taɓa tafiya na barka ba , yayi Allah ya albarkaci rayuwarki Uwar masu gida , da amin na ansa tare da gyara zamana , shima gyara zamanshi yayi sannan ya fara....
*ALIYU MUHAMMAD BINNA...*
Shine cikakken sunan da kowa ya sanni dashi , *BINNA* laƙani ne dana sakawa kaina shi bayan na shiga harkar wasan caca , dalilin binna kuwa saboda tsabagen neman asiri irin nawa , *BINNA* a binne kenan , dan da anyi magana kaza bazai yuwu ba , zance a binne shi kawai , tou idan nace a binne sai mutane suka fara ankara da abinda nakeyi dan haka sai nayi waiwayen damisa na zama Binna kawai dan ɓatar da mutane lissafinsu , sunan yana firgita kowa haka kuma yake bawa kowa tsoro duk wanda yaji ance *BINNA....* tou binna abin tsoro ne abun firgici tashin hankali ne ga duk wanda yasan Binna da irin rayuwar da nakeyi...!
Malam Muhammad shine mahaifina , Maryam wacce ƙauye yasa ake kiranta da mero itace mahaifiyata , matan malam 2 mero da sahura , mahaiyarmu itace ƙarama kuma dake ta daɗe bata samu aihuwa ba , ita kuma Sahura dama tuni ta kwankwatso ɗiyanta goma sha shidda , hmmm Babana yayi tare da cije haƙorashin na gefen dama ya karkace leɓunansa sukayi sama , jinjina kai yayi sannan yaci gaba da cewa "ya "ya sha shidda saboda haɗama sai kace wata kaza , dan tun kafin a auro Mero tuni Sahura tayi haihuwarta ta gama...
Mu talakawa ne na abin musali , kaf zuri'armu ba'a taɓa samun mutumin daya mallaki kaza biyar ba , kaf kauyen Ƙarara babu mutane masu talaucinmu , bamu gaji arziƙi ba kuma babu wanda yayi shi , kowa dai yanashan azabar talauci yadda ya kamata ,
Malam kuwa wutar talauci data isheshi ya rasa inda zai saka ransa saiya fara aikin tsubbanci , kuma sai Allah ya tallafa mishi domin idan yayi aiki kamar yankan wuƙa wuyar dai kafin yayi ne kawai , cikin ƙanƙanin lokaci sunansa ya fara ketawa yana zagawa kunnen jama'an duniya , yayin da mutane suka fara kiransa mai gobe da nisa...
Nanfa harka ta buɗe dan Allahn yace masa zama , tun abun bai fita ba har mutane suka fara shigowa daga cikin birni suna zuwa wurinshi , a tsabibincin nasa fa yakai maƙura kuma shekarar arziƙin nasa ya tsaya kalmar zama da Allah ya yaddar masa taci gaba da tabbata akanshi....
Malam fa ya fara tara abun duniya , liƙafa taci uban ta da , dan malam ba mutum bane mai rowa dan haka jama'a suka fara saɗaɗowa zuwa gidanmu cin arziƙi , cin nan 3 a yini tou fa idan mutum yazo zaici ya ɗinke har yayi guziri , shi yasa gidan namu kullum ya koma kamar wani gidan biki ko suna...
A lokacin da Mero ta samu cikin farko Sahura kuwa tace ina wuta ta jefata , nan ballin asiri ya fara tashi jefe² tahana mahaifiyarmu zaman lafiya , da ta samu ciki sai ya ɓare , ciwon yau daban na gobe daban , abun dai babu daɗi ,
Su kuwa malam ba abinda ya damesu da harkar da iyalinsu ke ciki burinsu kawai sudai a kawo musu , kullum matan malam basu da aiki sai wanke alluna , ana haka dai har Allah yasa Mero ta samu cikina , tunda Sahura ta lura Mero tana da ciki taci gaba da wurgago subbancinta , haba ina harta isa ? Allah yace saina zo asiri baya tasiri a wannan lokaci sai hukuncin Allah...
Har Mero ta haifeni cikin wahala take da musibar rayuwa , tunda na sako ƙafa duniya dama azababbena aka haifoni , da rana zansha baccina har in gode Allah , amma da zaran an kira sallah magrib na fara kwarara ihu har garin Allah ya waye babu wanda ya isa ya runtsa idonshi kona second a gidan nan saboda kuka na , a haka akayi suna Allah ya cidani da Aliyu , ina wannan masifafen kuka da an kira asubahi kuma zanyi bacci , malam kuwa saida ya rubuce yace abani insha maganin kuka duk ranar da aka bani rubutu kukana sai yafi na jiya , har malam ya haƙura ya daina rubutu ana bani...
Haka Mero ta haƙura taci gaba da rainona duk wanda ya ganta yasan tana tattare da damuwa , tabi ta soye tayi baƙiƙƙirin saboda tsabar rashin kwanciyar hankali , dana fara zama kuwa idan ta zaunar dani zan fashe da wani irin ihu mai firgici wanda dole saita ɗaukeni ta goyani , nadai zama fitinanne ta ko wane sashi ,
Dana fara rai rafe kuma ɓarna harta ƙeta , duk abinda yake na Mero bana ɓatawa amma daga ba ita ba duk abinda na gani saina tadashi aiki , Sahura tace iskanci kesa nakeyi ɓarnar tunda nasan abun uwata bana ɓatawa , da nayi mata ɓarna sai tayita dukana maimakon inyi kuka sai inyi ta dariya...
Abun fa ya fara tayar da kowa hankali , har aka yayeni a nono , iskancina kuma sai abinda yayi gaba , tun ina ɗan firiri na , na iya tsakalo fitina saidai idan ban fita ba , masu kawo ƙara kuwa haka zasu jero layi , wasu a biyasu wasu kuma a basu haƙuri...
Shekarata 3 Mero ta sake samun ciki , amma har ta haifeshi Allah bai sanar da Sahura ba , tashin hankali wanda tayi ba kaɗan ba , amma bata da yanda zatayi dan duk wanda yazo baya komawa sai idan Allah yaso...
Ranar suna data zagayo aka sakawa jariri suna Muhammad , wanda ake kiranshi da ƙarami , ku kuma kuna ce masa Baba ƙarami , haka dai akaci gaba da cakwakiyar rayuwa , har Allah ya kawo wata mace matar wani attajiri malam yayi mata aiki , bayan buƙata ta biya shine ta siyawa malam gida anan cikin garin birnin katsina , a anguwar ƙofan marusa , daga nan muka tattaro mukayo birni !
Shekarar mu biyu da dawowa birni Mero ta ansa kiran mahaliccinta babu jinya haka kuma babu ciwon kai bare na hannu , nasha kuka kamar zan mutu na rashin mahaifiyata , wanda Sahura ko a kwalar rigarta ,
Bayan anyi kwana 3 da rasuwar Mero Sahura ta samu malam ta kitsifa masa ita bata iya zama dani ga iskanci ga rashin kunya ta taɓani ace dan uwata bata raye take azabatar dani , saidai ya raba mana wurin zama ,
Ba tare da nazarin komai ko tunani ba , yace in bar mishi gidanshi dani da ƙarami , haƙuri na bawa malam akan ya bari saiya kamani da laifi , amma fur ya ƙeƙashe idanuwanshi saina bar mishi gida , ina ƙoƙarin barin ɗakin malam Sahura tace sai inzo in tafi da ɗan uwana dan so take gaba ɗaya fitina ta fitar masu daga gida , a lokacin shakarar ƙaramin 2 da wattanni , ni kuma ina da shekara biyar da "yan watanni , haka malam yayi mana korar karnuka , ina kuka na ɗauki ƙarami muka fita daga gidan ,
Ina ɗauke da ƙarami na shiga cikin gari , duk wanda ya ganni ɗauke dashi zaice na mayar da yaron nan bana iya ɗaukarshi , ko sauraron mutane banayi bare na basu ansa , tafiya nakeyi har aka kira magrib , ni kuma a lokacin na isa wata anguwa ita Gambarawa....
Bakin wani shago na zauna na sauke ƙarami dake ta zabgaga kukan gajiya da yunwa , bayan na zaunar dashi naje na ɗauko buta da wani ya gama alwallah ya ajiye na bashi sauran ruwan daya rage yasha , bayan yasha na matsa wurin mai shagon da yake ƙoƙarin buɗewa ya dawo daga sallah nace Baba da Allah ka taimakamin da sadaƙa zan siyawa yaro abinci yaci ,
Cikin hargowa yace ai sai ka buɗe ka ɗauka mishi ɗan barauniya , dama irinku ne masu sacewa mutane abu idan basa nan , wata irin kwanya yaimin tsakiyar kaina harsai da nayi tunanin kaina ya huje , dariya nayi tare ce masa ka nunamin inda zan ɗauka , kuɗi ya fiddo daga cikin aljihunshi kwaci ² shege ɓarawon banza , kallonshi nayi sannan na duma ma kuɗin wawa , kaf kuɗin na kwace na ruga na cicciɓi karami nabi lunguna ba tare da nasan gari ba ,
Biyoni yayi da gudu yana a tara ɓarowa , ƙarami kuma sai kuka yakeyi saboda ya wahala , ganin jama'a na ketowa daga hanyoyi da dama yasa na samu wani zauren gida na sake na rufe bakin ƙarami sautin kukanshi ya daina fita...
Dube ²n su sukayi basu sameni ba saboda haka suka hakura kowa ya kama gabanshi , saida na tabbatar babu kowa sannan na fito naje na samawa ƙarami abinci yaci muka bar anguwar Gambarawa a daren na dawo Qerau da zama....
Haka rayuwa taci gaba da tafiya , ni na saka kaina makarantar allo kuma na samu gidan aiki , gidan aikin suka sakani makarantar boko , haka dai na haɗa abu goma da ishirin , ga karatun allo ga boko ga gidan aiki ga rainon ƙarami ,
A daddafe dai nayi ta dafa rayuwar kuma ban sake zuwa wurin malam ba kuma daga Qerau zuwa Ƙofar marusa babu wani nisa ,
Shima ƙarami daya isa sakawa makaranta boko gidan aiki na suka sakashi , kuma tare dashi mukaci gaba da aikin gidan , daga baya ma suka bamu wurin zama a cikin gidan ,
Na gama secondry sch Bello ya shigo cikin rayuwata , gidan ƙawar matar da muke zaune gidanta itace take aikena gidan ƙawarta gidan kuma a maƙotan gidansu Bello ina zuwa idan aka aikeni nan ya ganni ya liƙemin , yana zuwa gidan da muke zaune yana yini wani lokaci ma har kwana yakeyi , ya shigeni sosai abota mai girma ,
Makarantar gaba da secondry tare da Bello muka fara nidai nayi karatu kuma na fito da sakamo mai kyau yayin da Bello ya faɗa harkar mata , a lokacin kuma ƙarami yana secondry sch aji biyar , bayan na gama degree aka fara neman min aiki , yayin da ni kuma nake neman ƙara faɗaɗa ilimin nawa...
Har wannan lokaci banje wurin malam ba , kuma malam bai nemeni ba ni kuma naƙi nemansa dan dama ni nasan inda yake , saida naci gaba da karatu na , na faɗa harkar wasan caca daga nan duk lissafi ya jagulemin , dan duk wannan kangarar da nayi a baya tana da dalilinta kuma a gaba zaki ji ta , dan bayan na baro gida naɗan samu natsuwa , amma shigowar Bello rayuwata yasa na ida ƙwacewa......
16/09/2019
Jamila Musa.....💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 34
*_Fatan na samu kowa lafiya ? Kuyi haƙuri na jina shiru kwana biyu banajin daɗi ne amma na samu sauƙi alhamdulillah ngode da addu'o'in ku a gareni masoyana , gaskiya naga soyayya kuma ngode sosai , na warware zamu ɗaura daga inda muka tsaya , fatan alkairi a gareku masoyana kuyi farin ciki..._*
Shiru Babana yayi ya zubamin idanuwa yana min kallo mai tattare da bayaso ya faɗamin , nima ƙureshi nayi da idanuwa amma bance masa komai ba , shiru yayi yana nazari zuwa can ya ɗago ya kalleni , nima kallonshi nake har yanzu zuciyata dai ta bani kila zai ɓoyemin wani abu ne...
Gyara zama yayi yaci gaba da cewa , zuwan Bello rayuwata yazo min da al'ajabi mai girma , wanda ya kasance bana iya ƙetare maganarsa , idan yacemin inyi zanyi idan yace na bari zan bari ya rabani da ko wane aboki shi ɗaya ne abokina ,
Bello shi ɗayane iyayenshi suka aifa , kuma attajirai ne na gaske , soyayyar duniya sun ɗorawa Bello sun sangartashi yadda ya kamata , saidai ya kashe waccan mota ya ɗauka waccan , ba mazaunin gida bane ba , domin duk kayanshi na sakawa yana cikin motarshi , tafiya yake jira kawai yayi gaba , gashi cikakken ɓarawo domin duk ƙarfin arziƙi mahaifinshi saida ya duƙar dashi ƙasa.
Tun wancan lokacin Bello ya mallaki bantan baƙin biri , daya ɗaurashi duk inda ya shiga idan dai akwai kuɗi hayaƙi ne zai riƙa tashi , da yaga yahaƙi yasan kuɗi ne a wurin zai buɗe kawai ya kwashe yayi gaba ,
Bello mashayi ne , ɓarawo ne , ɗan caca ne sannan tantirin mazinaci ne , idan har ya zuƙawa mace masifa tou duk irin kamun kanta da natsuwarta sai Bello ya keta mata mutunci , baya neman zawara baya neman matar aure sai "yan yara ƙasa da shekarunki , shekaruna kenan ni Sultana , kuma daya biya buƙatarsa ya gama da ita wata zai nema...
Da nayima Bello magana sai yacemin sa'ar caca malaminshi ya bashi , gabana Bello ke zuƙewa kuma gabana yake kwalbewa , ma'ana a gabana yake shawuwa yasha sigarinshi yasha giya da sauran kayan shaye ²n shi...
Ni kuma a lokacin na koma makaranta naci gaba da karatu na , dan zurfafa ilimina dan na fahimci rayuwar idan baka da ilimin zamani mai zurfi tou ka zamo an maido wuta an ɗauke...
Banda isashshen lokaci bansan abinda gida yake ciki ba idan na tafi makaranta , gidan da ake riƙemu akwai ɗiyar mai gidan itama yarinya ce ƙarama lokacin tana js3 ashe itama Bello ya ɗora mata alƙalamin kudirinshi akanta wanda ya fake da soyayya ne ni kuma duk ban sani ba ,
Wallahi babu abinda na sani tunda bana nan , ƙarami ma baya zama gida shima makaranta , Bello idan yazo bama nan zai buɗe ɗaki kawai ya shiga babu mai hanashi tunda abokina ne ,
Wata rana kwatsam ina makaranta "yan sanda suka zo suka tafi dani , tambayarsu na farayi lafiya ? Babu mai lokacina , haka suka sarkafeni da sarƙa suka tafi dani ofishinsu...
Suna zuwa office sukaci gaba da dukana babu ji babu gani , sunma hanani nayi magana bare naji laifina ? Saida suka min lullusar fitar hayacci sannan aka wurgani cikin cell aka rufeni ,
Saida na dawo hayyacina naga Bello gefena yana kyalkyalamin dariya , ƙarami na gefe sai kuka yakeyi , goge hawaye nayi tare da cewa me mukayi haka abu babu mutunci ? Dariya Bello yaci gaba dayi yana shan lolypop inshi...
Ƙarami na kalla nace meye wai ? Cikin kuka yace wai rafe naji dai suna cewa , cikin ɓacin rai nace rafe me ? Miye rafe kuma ? Ƙarami yace nima ban sani ba kawai dai haka naji suna cewa , tsoki nayi zuwa can nace waye yayi rafe ɗin ? Cikin kuka yace mu duka naji suna cewa , har yanzu Bello dariya yakeyi yana shan lolypop , raina naji ya ɓaci na tashi nayi kan Bello naci gaba da dukanshi babu ji babu gani ina cewa me mukayi ne ...?
Dariya Bello yakeyi yana cewa wallahi hauka yasa suka kawoku , ni kaɗai nayi kuma yarinyar da kanta tacemin tana so in rantsar da ita , itama ta zama cikakkiyar mace kamar kowa , tou dan nayi abinda takeso sai azo a rufemu , ai godemin ma ya kamata suyi , shaƙe Bello nayi sosai tare da cewa itama ka zuƙe.......?
Bushewa yayi da dariya to me ake jira da abun kwaɗayi.... ? Yau taji abinda uwarta keji , da sauri na rumtse idanuwana dan naji kaushin maganar Bello a raina , murmushi yayi tare da cewa kaji babu daɗi ko ? Tou ai itama uwar ta tuni na bata alƙalamin daraja kuma yanzu nan zata zo ta fitar damu dan nace idan har ta bari muka kwana sirrinta a buɗe yake dan ina da babbar sheda ,
Kallon Bello nayi idona cike da hawaye nace hajiya ma .....? Murmushi Bello yayi yace harda tukwuici take bani ma , kuka naci gaba dayi dan banji daɗin abun ba , daga haka nayi shiru na samu wuri na natsu muna jiran tsammani...
Hajiya itace tayi cuku² dan Alhaji shine yasa aka kamo Bello kuma Bellon yace tare mukayi kowa saida ya zagaya sau biyu domin ya buɗe mutuntakar a yarinyar yadda ya kamata !
Saida Hajiya ta saki kuɗi sosai tare da ƙaryata zance mijinta cewa ba Bello ne yayi wannan aika ² ba wasu daban ne sukayi kuma suka gudu haka nan aka ɗaura alhakin tuhuma akansu yara marayu basuji suka gani ba sai Allah ya saka musu...
Saida aka kai ruwa rana sannan muka fito , Bello yace mena faɗa muku nace muku zamu fito babu ɓata lokaci , haushin sa kawai nakeji domin naji ciwon wulaƙantawar da yayiwa yarinyar da nake ma kallon ƙanwata , kuma naji ciwon keta mutunci mahaifiyata Hajiya da ta ɗaukeni matsayin ɗa , kuma nima daga wannan lokaci na ɗaura ɗamarar saina masa yaji idan da daɗi !
Alhaji kuwa korar kare yayi mana daga gidanshi bayan yayi maganganu masu zafi da ɓatanci akanmu , kayanmu muka kwashe daga gidan Bello ya bamu mazauni a gidansu...
Duk lokacin dana kalli Bello sai naji kamar in haɗiye zuciya in mutu saboda tsabar baƙin cikin abinda yayiwa mutane masu mutunci , koda zai fita da daddare binsa nayi domin na fara harin rayuwarsa ,
Gidan caca muka nufa dashi , shine zuwana na farko dan kallon wasan da Bello zai buga , bayan yayi "yan al'adunshi ya binne ya ɗaura , hankalina ya tashi ganin tulin kuɗi da aka zuba , cikin ƙanƙanin lokaci aka fara gabatar da wasa , an ɗauki lokaci mai tsayi ana gwabzawa bayan wasan yayi zafi Bello ya lashe wannan makudan kuɗaɗe ,
Bayan ya kwashe kuɗinshi aka fara shagali , kwalaben giya suka fara wali da dai duk wani mai ɓatar da hankali , ina cikin ɓacin rai dan haka bansha ba , amma Bello yace idan nasha zan rage damuwa , dan haka na ansa nasha cikin ƙanƙanin lokaci na nemi damuwa na rasa !
Uwar masu gida labarin dai bazai buɗu duka ba , dan wasu labaran bai kamata na faɗa miki ba , mu tsaya haka nan , domin nima na zama atsabibin matsafi dan ko magana nayi bata faɗuwa ƙasa na koma kamar wani mai kambun baka saboda tsabar neman asiri irin nawa !
Daga nan na shiga wasan caca nima , naci gaba da harkar mata , shaye² da duk wani abunda ya zama zunubi , nayi nisa banajin kira , sheɗan yaci gaba da busamin sarewar halaka na shi , ga Bello bashi da ƙanne ,
Bayan ƙarami ya gama secondry sch yacemin bazai ci gaba da karatu ba , nayi juyin duniya yacemin daga haka ya tsaya , to ni na bashi gidan zama wanda a caca na ciwoshi , kuma ni na bashi kuɗi yaci gaba da kasuwanci , kuma duk matan daya aura nine na kashe kuɗi nayi masa hidima ,
Ƙarami bai daɗe da aure ba Malam ya saki wasan , wato ya mutu , bayan yasha doguwar jinya an girbi abinda aka shuka domin aikin tsubbu ɓata ce , ya lalata maka zuri'arka ga dakon zunubi , wasu an ɓatar an raba an haɗa dan dole an talauta wasu an raba aure an raba uba da ɗa anyi an gama dai duk an tafi an iske Allah....
Bayan ƙarami yayi aure aka barni daga ni sai Bello mukaci gaba da gurza rayuwa , har Allah yasa ya samu yarinyar da yake mugun so , kyakkyawar yarinya mai hankali da biyayya Bello ya mutu akan yarinyar nan , sukaci gaba da soyayya , na tambayeshi ko itama dai kamar sauran ? Yacemin a , a wannan ta aurece gaskiya , naji daɗi sukaci gaba da zuba soyayya sun shaƙu sosai tarayyarsu abun burgewa ,
Basu wani daɗe suna soyayya ba sukayi aure , lumshe ido Babana yayi sannan yaci gaba da cewa ango na shirin shiga ya angonce Binna ya anshi budurcin matar Bello , Bello yayi kuka saida yayi jinya gashi kuma yana mata san da baya iya rabuwa da ita , uhum tafasha azaba yarinyar nan , bayan Bello ya samu sauƙi akaci gaba da abota ,
Nima yana nan zai rama ashe , to yanda kasar suri bata cuwuwa ga bakin duk wani bil'adama haka Uwar masu gida tafi ƙarfin Bello dan yasan idan yace akanki zai ɗauki fansa tabbas nima zan rama akan "yar sa , shi yasa ya matsamin na sakaki a caca , hawaye ya cikawa Babana ido ,
Yaci gaba da cewa yasan duk duniya ya cire soyayyar Allah da manzan sa babu wanda nake so a faɗin duniyar nan bayan ke , tabbas yasan zanci caca shine suka juyarmin da hankali ta hanyar bani asiri cikin abunsha , bayan sunyi galaba a kaina suka rasa abunyi , shawarar abokinmu ya nema shine yace yasan wani da yasan Dikko , yace idan aka kaiki a wurin bazan iya ja da hukuma ba , hankalina ya kwanta da naji wurinshi kike nasan babu abinda zai faru ,
Ashe shima sun shirya mishi gadar zare , ɗan masu aikin gidansu shine yayi jagoranci , cikin kuka Babana yace aka ciwa "ya ta mutunci , haka na gudu na ɓuya kamar ƙolo na boye saboda kunyarki , duk da nayi haƙuri ban ɗauki fansa akan abinda Bello yayi ba duk da haka bai faru ba ,
Amma dana biyewa sharrin zuciya gani takaini ta baro ni , murmushi nayi nace ba komai Babana na yafe maka , kuma wannan abun ka ƙaddara babu abinda ya faru , !
Amma me yasa ka bar iyalinka cikin wahala ? Tsoki yayi sannan yace nima haka aka barni a saman titi bansan mai kyau ba bansan mara kyau ba , banda mai nunamin kyakkyawa ko mummuna , babu wanda ya kula dani shi yasa nima na saki kowa yayi rayuwarshi ,
Baba Allah fa yana kallonka , ka karanta kuma kaji ka gani kuma kasan abinda Allah yace akan iyali , girgiza kai yayi tare da cewa kar muyi haka dake Mamana , banasan maganar su , tou Babana amma me yasa baka aiki ne ? Wannan ra'ayina ne , caca na zaɓa kuma zanci gaba bazan daina caca ba sai numfashina ya ƙare , cike da damuwa nace ko kana da dalili ne ? Uwar masu gida mubar maganar nan ,
Tou Babana ina Sahura ? Kuma me yasa kayi kangara kana ƙarami ? Murmushi Baba yayi tare da cewa wannan kangara wani aiki ne malam yayi akan wani yaro dan ya lalace , matar Babanshi tazo ayi mata aiki ne , sai abun ya dawo kaina ,
Matar ta dawo ta faɗawa malam buƙata bata biya ba , can wurin binci kenshi ya gano inda aiki ya sauka kuma ya warware komai , idan dai kayi mugunta tou ka daina saurin rufe ƙofa domin dawowa takeyi , Sahura kuma tana can gidanta bana dai zuwa gaskiya...
Tou ita Inna baza ta dawo ba ? Manta da ita gani nan na isheki taje can tayi ta zuciyarta , kallon agogon hannunshi yayi ya miƙe yana cewa bani makullin motarki , miƙa mishi nayi ya fita yana mita ba'a kawo mishi kuɗin wayoyinshi ba , gaskiya Babana bansan irin halinshi ba , dandai yaƙi yadda ya faɗamin komai duk haka ya bani labari nidai a duƙunƙune....
A ƙofar gida ya anshi kuɗin wayoyinshi yayi gaba , "yan gida kuma cewa sukeyi da wani yake da motar nan sai Baba ya siyar da ita amma da yake ta Sultana ce komai daren daɗewa zai dawo mata da abinta , saboda kar yamin faɗa raina ya baci shi yasa baiji a ina na samu mota ko yamin faɗa ina hawa mota ba ,
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya , Babana yake amfani da mota ta , Bello ya fita harkata nima na fita harkashi , d c o babu ruwana dashi , Hafsa da Amisty banda labarinsu , su A ` i ma bana shiga sabgarsu , mijin Zalifa da Zalifar duk na daina jinsu , Alaji kaɗai yake zuwa fira danshi ya matsa aurena zaiyi...
Haka nan na tsira yin bedday babu gaira babu dalili , nayi i v nasa akaci gaba da rabawa , har a gidan radio nasa Alaji yakai sanarwa , manyan baƙi a wurin Baban Amisty mai yanka cake kuma Baban Hafsa , wurin taron kuma wani zuƙeƙen gidan Baban Hafsa , nayi gayya duk wani lungu da saƙo na zaƙulo manya ² karuwai nakai musu gayyata wanda duk ba ƙawaye na bane nasu Amisty ne ,
Al'amarin wannan taro ya karkato da hankalin jama'ar gari a kaina dan ban ibo abun da wasa ba , kowa da abinda yake faɗa akai na yayin da wasu mutane suka cewa taron iskanci ne ba wani taron birthday ba ,
Hafsa kuwa Amisty tayi mata waya ta faɗa mata cewa zanyi birthday amma taga venue gidan shaƙatawar Dady inta ne , yaushe ne ake taron Hafsa ta tambaya ? Amisty tace mata ranar laraba , Hafsa tace tou Allah ya kaimu zata ga yanda zan wulaƙanta ta ....
Nima da Nana ta bani labari dariya nayi tare da cewa Nana nima zan wulaƙanta ta yayin da taga Dad inta ya yanko cake ya rungumeni yana bani a baki na , itama Nanar dariya tayi tare da cewa Allah ya kaimu zanje idan har Audu ya barni ,
Lokacin da Dikko ya samu labarin wannan taro da zanyi zuciyarshi tayi mishi ɗaci domin yasa ana biyayyar mishi rayuwata duk wani motsina da komai nawa babu wanda Dikko bai sani ba ,
Tsoki yayi tare da kallon agogon hannunshi jinjina kanshi yayi ya cusa "yan yatsun sa ko wane yana gogar ɗan uwansa , laraba , ya faɗa a bayyane tare da sake jinjina kanshi , litinin kuma ya faɗa a bayayyane Allah ya bamu aron rayuwar muje larabar dani dake........
19/09/2019
Jamila Musa 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 35
Har yaci gaba da cin abinci kuma yaji gaba ɗaya moƙoshin nashi abincin baya wucewa , tsananin ɓacin rai da damuwa suke ta kartar masa zuciya , dakel ya haɗiye yawu mai ɗacin gaske , kallon Al ' ameen yayi yace kiramin Umar....
Wayar ya ɗauka da sauri ya fara kiran wayar Umar , saida Umar ya ɗauki wayar ya miƙawa Dikko cikin ladabi , ansa Dikko yayi cike da ɓacin rai yace har yanzu kana anguwar ko ka fita ne ... ?
Magana Umar ɗin yayi , Dikko yace tou kaje ka kaima An mata waya zanyi magana da ita yanzu ² yi sauri karka ɓatamin lokaci , saida ya jira abinda Umar zai faɗa sannan Dikko ya kashe waya ,
Ina zaune ƙofar gida dani da Alajina muna fira Umar ya faka da machine inshi , kallo ɗaya nayi masa na kauda kaina yayin da na ciro wayana na fara ƙoƙarin kiran Wane Yaro ,
Sallama yayi suka gaisa da Alaji nima ya gaisheni , ansawa nayi babu yabo ba fallasa , ɗan gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa dan girman Allah saƙo aka bani wurinki , daina kiran wayar Wane Yaro nayi na tattara hankalina kaf wurin Umar nace waye ya baka saƙon ne ...?
Cike da ladabi ya miƙomin waya bayan ya kira number ya miƙomin yana cewa kiyi magana an ɗauka , cike da wasi² na kara wayar a kunne na tare da cewa Assalamu Alaikum....
Ansa sallamar yayi yana mai ci gaba da cewa An mata kinaso in saka ƙafar wando ɗaya dake ne ? Shiru nayi banyi magana ba , Dikko yaci gaba da cewa na rantse da Allah ki kama kanki wannan iskanci birthday in da kika taro ki warwareshi tun kafin inzo wurinki ina fushi , banda kyau idan na ɓata rai ki roƙi Allah ya rabaki da ganin fushi na amma na rantse da Allah.... Saida yayi rantsuwa mai sa faɗuwar gaba sannan yace idan kunne yaji ....
Sai kuma yayi shiru bai ida faɗar maganar ba , ni kuma na ɗaura da cewa idan ka barni na huta baka ƙaunar Allah , tsoki nayi tare da miƙawa Umar wayarshi naci gaba da magana na da Alaji ,
Cike da masifa Dikko yace Umar ya maidomin wayar , bani yayi nima kuma na ansa , cikin sigar lallashi yace An mata nine bana ƙaunar Allah ? Wai mi yasa kike min magana haka babu ɗa'a , ai kasan gidanmu ba'a koyamin ɗa'a ba shi yasa ma har nayi rashin ɗa'ar a cikin gidan ubana ,
Dikko yace idan kinajin rashin kunya ki fita daga cikin mutane ki zageni idan kin isa , ni nasan baki isa kimin rashin kunya inda babu kowa ba , dama kin tsaya a gaban waɗanda ko naso nayi miki hukunci zanyi haƙuri a haka kike tunanin bakyajin tsoro na ne ? Idan dai bakijin tsoron Dikko maza ki tashi daga inda kike kice Dikko ƙarya kakeyi nafi ƙarfin ka takuramin ki faɗi haka kiga yadda zanyi wasan kura dake wallahi ....
Kamar wata sakara na miƙe na matsa daga inda su Umar suke , ashe shi kuma yayi wayau ne dan kar in riƙa wulaƙantashi ne a gaban yaronshi , saida na matsa sannan nace ƙarya kake ni nafi ƙarfinka kuma nafi ƙarfin ka takurani dan banajin tsoronka kayi duk abinda kakejin zaka iya yi na matsa daga cikin mutanen....
Dikko yace tou babu komai dani dake aga fasashshe , ni zanzo katsina insha Allah gobe talata , ke kuma zakiyi birthday ranar laraba sai nazo , kuma karki sake kiyi mafarkin gemuna na faɗa miki....
Gemun banzar ka gemun wofi , Allah ya sawaƙe min in ganka a barci na , cikin murya mai saukar da kasala yace nifa bana san cika baki bayan nasan komai , kawai yarinyar kirki taga ustaz ta maƙale mishi aidai kina so na ko.... ?
Tsoki nayi ban bashi ansa ba na kashe wayar naje na bawa Umar ko sallama banma Alaji ba na shige gida raina a ɓace ,
Murmushi Dikko yayi bayan na kashe waya tare da cewa An mata rigima , zaki zo kusa dani kuma inaji a jikina wata rana zaki rumgumeni ki kalli cikin idanuwana kice Dikko ina sanka , yana maganar yana nuna yanda Sultana zatayi , cikin farin ciki yaci gaba da cin abinshi bai sake kiran Umar ba , kuma koda Umar ya kira dan ya faɗa masa cewa Sultana ta tafi bai ɗauka ba ,
Shima Alaji kiran wayana yayi tayi naƙi ɗauka , ya gaji ya tashi yayi tafiyarshi , shima Umar tafiyarshi yayi gida ,
Ni kuma ina shiga ɗaki saman katifa na faɗa nayi ruf da ciki bansan dalili ba , maganar Dikko yake dawo min a zuciyana , karki sake kiyi mafarkin gemuna , cike da fargaba zuciyata ke cewa kodai Dikko ya gane ina kallon masa gemu ne .... ? Tsoki nayi na gyara kwanciyata ina tuno kyakkyawar fuska Dikko , tunani dai barka tai a zuciyata har bacci ya ɗaukeni....
Da safe Alaji yazo ya kaini kasuwa dan Babana baya nan kuma motana tana wurinshi , siyayya na bada mamaki nayo domin fa Alaji yana da hidima kuma yana da gabata , ya kashe kuɗi duk yanda tunani baya tunani , ko kayan da zan saka wurin partyn zagayowar shekarar aihuwata wallahi masu masifar kyau da tsada ya siyo min abun dai zabburgewa sai wanda ya gani ,
Bayan mun gama siyayya nace masa ya tafi zanyi kitso idan na gama zan kirashi ya ɗaukeni , Alaji yace to saida ya ƙaramin kuɗi ya tafi ni kuma na shige shagon "yan arna da basa gane yare na , na fara faɗa musu abinda nake so amma dan ubansu wai basu gane ba , saida wata rantsatstsar karuwa maiji da iskanci har iskanci yayi mata sign tayi musu bayani , girar ido za'a sakamin akaifa da kuma atach duk gashina saida nasa aka yimin ƙari saboda tsabagen wawanci irin nawa ,
A ƙofar gidanmu kuwa 5:00pm Dikko suka kafe motocinsu , aikawa yayi a kirani amma sai akace masa na tafi kasuwa , maimakon ya tafi sai yace zai jirani har na dawo ,
Duk lokacin da minti ɗaya ya wuce sai Dikko ya kalli agogo ranshi ya ƙara ɓaci , shiru ² babu ni har aka kira magrif , cikin damuwa yace ma Al ' ameen muje zan dawo anjima ,
Tashin motocinsu sukayi gaba ɗaya suka taho , suna fita anguwar mu kuma muna shigowa hannun riga mukayi dasu wato suna fitowa mu kuma muna shigowa ,
Babu abinda na sauko daga mota nace ma Alaji ya tafi sai Allah ya kaimu , sallama mukayi dashi ya tafi ni kuma na shige gida , ina shiga na shirya a gaggauce domin Baban Amisty zaizo , naje kasuwa har nayo kawalcin mace zan haɗasu , itace karuwar da muka haɗu ta tambayeni sana'ar da nakeyi nace mata karuwanci nakeyi , tace ashe tafiyar ɗaya ce ? Nace mata Eh musayar number mukayi har na bata labarin iyayensu Amisty tace suna da mai ne ? { kuɗi } nace sosai ma , shine tace a cikin daren nan in bata aron kowa a cikinsu ita kuma tamin alƙawarin zata ɗaukomin su dukansu a cikin yanayi mara kyau tou shine zan haɗasu , duk da dai malami da mawaƙi da karuwa basu da amana amma zuciyata ta yadda da ita 100% ,
Har ƙofar gida Baban Amisty ya ɗaukeni kuma yanzu ma muna fita Dikko yana shigowa , akace masa yanzun nan muka fita ko bakin titi bamu kai ba , da sauri ya biyo bayanmu ko zai sameni amma bai iskomu ba , ganin baisan ta ina zai samoni ba yasa ya haƙura ya koma ƙofar gidanmu a ranshi yayi alƙawari ko zankai yaushe ban dawo ba zai jirani ,
Daga gidanmu ƙofar soro muka nufa gidansu Mamy ƙarfe 8:18pm mukayi parking a ƙofar gidansu kamar yanda tayimin kwantance , bayan mun tsaya na kirata a waya , babu jimawa ta fito cikin shiga mai ɓatar da hankali , tana isowa ta kama mota ta buɗe ta kashe a gidan baya , shi kuma yaja mota muka tafi , shegen tsoho kenan yace ina muka nufa ne ? Yayi maganar yana kallona ,
Murmushi nayi tare da cewa nifa guzirin dare nayo maka itace zaka tambaya bani ba , kaga ni kullum muna saka rana amma abun bai yuwu ba shine dana ga mai buƙatar ruwa a tsakar rana nace tazo ina da ƙatuwar randa { tukunya } a gidana har yoyo takeyi { ɗiga } kaga kuwa idan har ta riƙe babban kofi a tausayawa ruwan nan domin saita ƙare shi kaf hankalinta zai kwanta , juyawa nayi na kalli Mamy sannan nace a ina zakisha ruwan ne .... ?
Cike da bariki tace aishi ruwa ko a tsakiyar hanya shanshi akeyi saidai idan ba ƙishirwar ke damunka ba , amma tunda ni mace ce dole zan matse ƙishirwa har mu isa gida , amma ka daure kar kayi tafiya mai tazara dan lumfashina gaf yake da ɗaukewa , !
Karkata mota yayi ya ibi hanya , muka nufi kwaɗo , har muka isa babu wanda ya sake magana , a ƙofar gida yayi parking shida ita suka shiga aka barni a cikin mota , shigarsu babu jimawa na fara kiran Baban Hafsa inda zamu sameshi ya faɗa mana nace muna zuwa babu ɓata lokaci , Mamy kuma da Baban Amisty bansan abinda ya faru ba , sundai share awa da rabi sannan suka fito...
Bayan sun fito ta buɗe inda nake zaune tace fito mana haka nan , nace kidai shigo muje , Mamy tace nan zamu sauka , fitowa nayi mukayi sallama dashi tare da ƙara tuna mishi sai mun haɗu wurin party yace in Allah ya yadda , yana tafiya muka samu wuri muka zauna , wayata ta ansa ta tura min vidion data ɗauko nashi abundai babu kyan gani ko ya akayi tayi masa dibara ta ɗaukoshi tasa shi sai iskanci yakeyi , a wayana ta tura bayan ta tura ta shiga whatsapp ta turawa Amisty abinda zata faɗa nake faɗa tana rubutawa...
_Salam aminiyata Amisty , Sultana ce ban sani ba ko kin goge lambana shi yasa na baki sani dan kar ki shiga dogon nazari da tunani , kinsan mage bata cin bushiya , idan kuma maciji ya raɓi bushiya noƙe kanta takeyi yana tahowa da ƙarfinshi dan niyar mugunta sai ta noƙe kanta ya soki ƙayoyinta , maciji baya san tabo daga nan sai ya sari kanshi ya mutu , bushiya sai ta fito taci gaba walinta a duniya , tou haka tsaka take mage kaɗai ke cinta ta rayu amma ke in kakaci ta sai sheƙawa lahira , ganin aljanni a siffarshi akwai tsoro da firgitarwa masana ɓoyayyan sirri suna cewa idan kaga aljani a siffarshi kwanakin mutuwar ka ne yazo , nidai naga aljani ban mutu ba kuma naci tsaka ban mutu ba shi yasa na turo miki kema ki gani shin kina da yawancin kwana ko daga yau kwananki ya ƙare ne....?_
Turawa tayi ni kuma na ɗora da voice note cewa kiyi haƙuri kuma kibi sannu ki warware maganganuna kinsan tsarƙesu nakeyi idan kin gani kiba Hafsa ta tayaki gani....
Bayan na tura muka hau napep muka doshi barhim estate acan Baban Hafsa ke jiranmu , shima dai sun shana yadda ya kamata kuma Allah ya bata nasarar ɗauko min mugu , itama Hafsa tura mata nayi da voice note cewa...
Duk gudun kare idan yaga kura ɓoyewa yake domin tsira da rayuwarshi , haka mutum idan yaga abun tsoro kuka yakeyi ya rumtse idanuwanshi , irin haka kikaji a lokacin da kika cire towul in dake jikina..... ?
Ina gama faɗa na sakeshi ya tafi.... , Napep muka hau muka nufo gidanmu , saida aka fara saukeni aka wuce da ita bayan ta shedamin zasu zo wurin shagalin ita da zugar tata ƙawayen , godiya nayi ina ɗaga mata hannu har suka tafi ,
Kallon agogon hannunshi yayi yaga 11:35pm , daga ina nake a wannan daren shine tambayar daya fara ma kanshi kuma bashi da mai bashi ansar tambayar , ni kuma cike da farin ciki na tunkari ƙofar gidanmu sai tsalle² nakeyi na jin ɗaɗi na shige gida abu na ,
Jiki a sanyaye DK yaja motarshi ya nufi gida zuciyarshi tana mishi babu daɗi , amma yayi addu'a gobe tazo mishi lafiya ,
Yau laraba kuma itace ranar da nake wannan gagarumin taro wanda na samu damar gayyato mutane daga sasoshi da dama , tunda safe ake shiga da fice a gidanmu duk inda ka buɗe idonka zunzurutun karuwai ne kawai suke kai koma , wane yaji ga wane waccen taji ga wance , taron motoci ne burjik a ƙofar gidanmu duk wanda ya wuce sai yayi tir da irin matan da dake ƙofar gidanmu !
Shi kuma Dikko a safiyar nan tayi mishi babu daɗi dan matarshi aka kai asibiti bata da lafiya sosai , kuma taƙi cin abinci ta rame tayi duhu saboda ciwo da damuwa , hankalin Dikko idan yayi dubu ya tashi da guda ² kallo ɗaya zaka mishi ka gane yana cikin damuwa , ga damuwata ga ciwon matarshi ....
Taruwa akaci gaba dayi duk yaran Baba Ƙarami sunzo gida ya cika taf kuma na duba har yanzu daga Amisty har Hafsa babu wanda ya hau online dan suma suna can suna shirya tasu gadar zaren ,
Komai fa anyi kowa ka gani a wurin shima yakai wani babban shege , sai 6:00 aka fara tafiya wurin partyn , Nana dai bata samu zuwa ba mijinta ya hanata kuma ta hanu , Karima itama bataje ba amma A ` i da Saude tare dasu aka tafi duk yayuna maza da mata sunje ,
Dikko yana duƙe gaban gadon Sadiya riƙe hannunta yayi cike da damuwa yace Sadiya karki kashe kanki don Allah idan baki so na ki faɗamin sai in sahale miki auren nan ki huta , ni ina da damuwa idan naga kina cikin damuwa ko nayi miki wani abu bai miki daɗi ba ne ?
Karkata kanta tayi gefe hawaye suna ci gaba da gangaro mata , zama Dikko yayi gefen gado ya tattaro natsuwarshi fuskar Sadiya ya tallafo da duka hannayenshi yace mene ne ? Ki faɗamin wai meke damunki ne ? Dakel ta ɗaga bakinta zatayi magana a daidai lokacin da wayarshi ta fara ringing , cirowa yayi ya duba , Umar ne dan haka ya ɗauka tare da cewa ina ne..... ?
Bayani Umar ɗin yayi masa , bayan ya gama Dikko ya kashe wayarshi , shafa gefen fuskar Sadiya yayi ina zuwa , yana faɗin haka ya miƙe ya fito daga ɗakin , ita kuma taci gaba da kuka , bayan ya fito yacewa Mom insha zaije ya dawo yanzu , Allah ya tsare tayi masa Al ' Ameen da sauran tawagarshi suka rufa mishi baya.... !
A bakin get suka ɗauki Umar suka nufo inda muke taro , a lokacin anci rabin shagali itama Hafsa ta taho dan ta wulaƙantani tunda gidan Babanta ne , amma tana zuwa labari yasha banban duk wannan taron jama'ar bai hana uban Hafsa rungumeni ba ya yanko cake yana bani a baki , gaba ɗaya wurin aka ɗauki sowa da ihu shi dama Alaji tunda ya ajiye kayan party nace kawai yaje tunda taron mata ne babu maza , kuma yayi tafiyarshi...
Lallaɓawa tayi ta koma da baya ba tare data bari wani yaji koya ganta ba , ihu akaci gaba dayi sakin sauti akayi yadda ya kamata mata sukaci gaba da farantawa sheɗan ,
Hafsa tana fita taci karo da Dikko ya fito daga mota , da gudu ta nufi wurinshi tana kuka cikin kuka ta fara faɗa mishi abinda Sultana tayi mata niko nace danma baki ga vidio ba , number wayar Sultana Dikko ya ansa a hannun Hafsa ya fara kiranta ,
Muna ta cashewa wayata ta fara zurzur dan ba ƙara takeyi ba murzawa takeyi sai kaji sautinta yana shiga maka hannu burbur , ɗauka nayi naci gaba da kwantace ba tare dana jira naji ko waye ba ,
Cikin wata irin murya yace fito gani nan na kasa gane gidan , wallahi banyi tunanin Dikko bane nayo waje , ina fitowa naga Hafsa tsaye da wanda bansan ko waye ba domin ya juya bana ganin fuskarshi sai bayanshi , cike da mugunta nayo wurinta dan a tunani na taga vidio zamu cashe rashin mutunci ,
Saida nazo gabansu na gane Dikko buɗe baki nayi da zumar nayi magana ya wanka min wani irin gigitaccen mari harsai dana juya kamar ranfa saboda karfin mari kafin in dawo hayyacina ya sake wankamin wani firgitacce wanda saida nayi ɗimuwar tunani na dan wallahi a daidai lokacin da zaka tambayeni suna na bansan abinda zan faɗa maka ba ,
Ƙara ɗaga hannunshi yayi zai kaimin wani marin a gigice na riƙe hannun cikin kuka nace yi haƙuri don Allah , a tsawace yace tou shiga mota , har yanzu dafe nake da inda ya mareni na nufi wurin motar da kanshi ya buɗemin na shiga sannan shima ya shigo dani dashi ne a baya , rufe murfin motar yayi Al' Ameen yaja sauran motocin suka biyo bayanmu...
Duƙar da kaina ƙasa nayi ina kuka cikin sauti mara hayani jikina sai kyarma yake dan har yanzu marin shiga jikina yakeyi ,
20/09/2019
Jamila Musa ..... 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 36
Duƙiyar ta isheni na ɗago hannuwana na rumgume kujerar da ake kira da mai zaman banza , ta kusa da Al 'Ameen babu kowa akai dan haka na rumgumeta kawai naci gaba kuka ,
Kallon hannuna Dikko yayi idonshi ya sauka akan wayata kawai ya miƙa hannunshi da zumar cirota daga wurina , da sauri na ƙara riƙe wayar gam tunda bana saka ma waya wasu malatsan sirri wanda saini na buɗe da kaina zata buɗe a buɗe take zaka iya shiga duk inda kake so...
Da ƙarfinshi ya fizgi wayar kafin yayi mata kyakkyawan riƙo na fizgeta a hannunshi dan bai kamata ace anga wannan ɗaukar ba bai kamata ba , miƙo hannunshi yayi tare da kauda kanshi gefe yace bani ,
Girgiza kaina nayi alamar a , a , cikin tausassar murya ya matso da fuskarshi kusa dani yace bani wayarki nace , matsawa nayi tare da ƙara saƙe wayar a bayana , shima matsowa yayi kusa dani yace zaki bani ko sai kinci cingom ne ... ?
Cikin kuka nace dan Allah ka shafamin lafiya , kallona yayi gefe da gefe sannan yace ta ina zan shafa miki inyi sauri dan nafi so kiyi lafiya da nisan kwana ya ƙarasa maganar yanamin kallo mai nuni da rainin hankali , nima kallon raini hankali nayi masa amma banyi magana ba ,
Shima shiru yayi bai sake magana ba kuma ya daina maganar in bashi waya , daga haka dukanmu babu wanda ya sake magana har muka zo inda zamuzo , duk sauran motocin a waje suka tsaya tamu kaɗai ce aka buɗe ma get muka shiga , bayan Al ' Ameen yayi parking ya fita daga cikin motar aka barni daga ni sai Dikko !
Al ' Ameen na fita Dikko ya sake taro hannu in bashi waya , cikin kalar ban tausayi na maida hannuwana baya tare da cewa dan Allah kayi haƙuri , ni nace kinyimin laifi ne ? Wayarki kawai zaki bani nace ya ƙarasa maganar cikin kausasa murya yana zazzaro idanuwa ,
Tsoro naji ya kamani sosai dan haka da sauri na miƙawa Dikko wayar , ansa yayi yana mai min ƙwafa tare tare da latso wayar haske ya bayyana , kafin ya shiga inda yake so kiran Amisty ya shigo cikin wayar , badai serving nake da sunan mutum ba lamba ce kawai , dan haka kiran sunan lambar dana ajiye number Amisty yayi sannan ya shafa wayar ya kara a kunnenshi ,
Dafe kaina kawai nayi lokacin da Amisty ta fara watso kalamai masu zafi da ɓatanci akaina sai ta ciko bakinta da ashariya sannan ta luƙaƙamin tare da furta wallahi idonta idona sai takaini kiyama ta dawo , maganganun dai babu daɗi dan har mahaifina ta saka duka dai abun gwananin ban takaici , tana zurara zagin wayar Hafsa ta shigo , amma bai ɗauka ba saida Amisty ta sauka ta kashe wayar , har ya gama waya da Amisty kiran Hafsa daya tsinke sai ta sake kira....
Itama Hafsa ta tata nata rashin mutunci itama a kalaman nata maganganu tayi masu kyaushi itama dai abun babu daɗin ji , idan tayi magana taji Dikko baice uhum ba , sai tace kina jina ko ? Sai yace Umm itama itace ta gaji ta kashe wayarta...
Cikin takaici Dikko ya kalleni tare da cewa fita , ina zanje ? Rumtse idanuwanshi yayi tare da sake cewa fita bana san ganin ki wallahi komai zai iya faruwa ki fita kafin naji miki ciwo , ƙaruwa hawaye na sukayi nace da Allah wai ina zanje ? Ki fita........ Ya faɗa cikin murya maisa firgici babu shiri na buɗe mota na fito , sai yaita yin abun kamar wani shafar aljannu ,
Ina fita Al ' Ameen yace muje ciki yayi gaba babu musu na bishi muka matsa , makulli yasa ya buɗe ƙofa sannan ya shiga , nima shiga nayi palo ne mai girman gaske sai wasu ƙoƙofofi biyu da bansan ko ina ne ba , makullin ya ajiyemin a saman hannun kujera yamin saida safe....
Banyi magana ba na saki baki kamar lefen wawiya ina kallonsu suka fice daga gidan , dan daga cikin palon zuwa bakin get ba wani nisa kuma daga cikin palon kana hange duk wanda yake bakin get , wuri na samu na zauna ina maijin takaicin rashin kasancewar wayana a kusa dani ,
A ɓangaren masu party kuwa saidai shagali yayi nisa sannan aka gane bani a wurin , nemana aka farayi amma ina mutane basu ankara ba Dikko yayi layar ɓata dani , wasa ² abu ya zama gaske yayin da wasu ke cewa sunga anmin waya na fita , nemana aka shiga yi amma babu ni kuma babu labarina....
Dikko kuwa asibiti suka fara zuwa ya ƙara duba Sadiya da jiki yayi mata nasiha ya lallasheta , saidai tayi murmushi mai tattare da ƙuna da baƙin ciki tabi Dikko da kallo mai ban tausayi , duk da yawan murmushi ba ɗabi'arshi bane idan tayi murmushi shima sai yayi mata dan ta samu natsuwa domin shi kanshi yasan murmushin shi wani sirrintaccen sirri ne da Allah yayi masa baiwa dashi badan halinshi ba , murmushi yana ma Dikko kyau sosai kuma murmushin shi yana da ɗaukar hankali da burge duk wanda ya gani ,
Saida Sadiya ta samu bacci Dikko yayi sallama da wanda zasu kwana da ita ya wuce gida , yana zuwa wanka yayi bayan ya fito ya saka riga da gajeran wando na jersey palo ya dawo ya zauna zuciyar shi na mishi babu daɗi , gaskiya tunda yake a shakarunshi bai taɓa cin karo da yarinya mai taurinka da rashin ji kanta cike da iskanci ba irin Sultana , a shekarunta har tasan taje ta ɗauko vidion tsiraicin uban wani ta tura ma ɗiyarshi ,
Shi kuma Babanta shima dai anyi tsohon banza ka rasa wacce zakayi lalata da ita sai ƙawar ɗiyar daka haifa , kai abu yayi muni gaskiya , jinjina kanshi yayi shi idan shine duk su Sultana ba mata bane a wurinshi , ko iskanci zakayi da sakarci ai ka samu macen da ta cika mace ta ansa sunanta takai mace ta ko ina da ko ina mai cikakkiyar zarra ba wannan jagwalgwalon yaran ba ,
Ya daɗe yana zaune palo yana tsaƙawa yana kuncewa wallahi zai tsaya saman ƙafafuwan shi ya cusa wa An mata soyayyarshi a zuciyarta idan ya riƙo ragamar rayuwata wato zuciya yasha da ita kuma ya gama da ita har abadan duniya , zata ga girmanshi tasan darajarshi saboda wannan kamun da yayiwa rayuwarta ,
Wayarta ya buɗe yayi binciken duk da zaiyi bayan ya gama ya rufe wayar gaba ɗaya tare da zamewa saman kujera yaci gaba da bacci !
A ɓangaren Babana kuma yana can gidan caca baisan wainar da ake toyawa ba a gidan , yana can ya shawu an zinatu kuma akaci gaba da caca , baya tunanin komai na ɓacin rai bare kuma halin da iyalinshi suke ciki , sabgar gabanshi ya saka a gaba kuma ita yakeyi baiji duk faɗin duniyar nan ba akwai mai iya dakatar dashi akan abinda ya saka kanshi ba....
Gajiya nayi da tsayuwa na tunkari ƙoƙofin biyu da na gani a jere , ƙofa ɗaya a rufe take ɗaya kuma a buɗe , turawa nayi na shiga da sallama a baki na , ɗan madaidaicin palo ne da kujeru masu kyan gaske na leda , sai labulaye masu kyau da tsada wanda suka dace da kujerun , a gefe kuma ga ƙatuwar talabijin girke a tebirin ajiyarta kamar zata ɓaro ƙasa saboda girman ta , abundai zabburgewa , ciki na shiga wato ɗakin bacci babu gado sai ƙatuwar katifa da "yar ƙaramar talabijin liƙe a bango , labulayen suma irin na palo ne , toilet na leƙa sannan na fito daga ɗakin duka nayo waje inga ko ni ɗaya ce a gidan !
Wasu irin murɗaɗin ƙattin mutane na gani marasa kyan gani yanayin duk ko wane ɗaya kamar ɗan rastilin amma su wanɗan nan baƙaƙe ne , suna gani suka yo kaina suna wata irin magana mai tada hankali wallahi saboda tsoro saida na saki fitsari a wurin , saboda wallahi siffar su bata da kyan gani abun tsoro ce abun firgici ce idan kuma sukayi magana sai kaji kamar ba duniya kake ba , tsaye nayi wurin saboda tsoro na kasa gaba na kasa baya , ruɗewa tasa na manta da ina da ƙafafuwa ...
Tunzura babbansu yayi yanayin shi ya nuna yana cikin ɓacin rai dan haka yayi wani irin kuka mai motsa tunani ya ƙara takowa dan ya samu damar matsowa kusa dani , nidai bansan ya akayi na ruga ba saidai kawai na ganni saman katifa har na lulluɓe da bargo ina kuka ! Bansan lokacin da bacci ya ɗaukeni ba ,
Da safe Dikko daga masallaci asibiti suka nufa daga shi sai Al ' Ameen , har yaje ya dawo Sadiya bacci takeyi , bayan ya dawo gida ne ya kira danjin ita kuma An mata ko ta kwana lafiya , lafiyanta qalau suka faɗa tare da bashi labarin abinda ya faru , mugu yaji mugunta , dariya Dikko yayi sosai tare da cewa zaizo anjima ai ,
Ba'a mugun sarki sai mugun bafade , Al ' Ameen bayan Dikko ya gama waya yace mai gida dan girman Allah ka kyale yarinyar nan tayi tafiyarta , sai kace dai itace kaɗai mace a duniya ? Yarinya mara kunya mara tarbiyya mara ɗa'a masu gajeren asali wallahi mutuncin gidanku da nasabarku da kai kanka taka mutuntakar ta wuce ace kana sauraren yarinyar nan wallahi , kana da zarrar da duk macen data ganka duniya sai tayi addu'a ta sameka a matsayin abokin rayuwarta.
Kana babban asali ga cikar zati ga kyau ga kwarjini me zakayi da yarinya mara tarbiyar ? A hankali Dikko ya lumshe idanuwanshi dan duk duniya idan akwai kalma mafi muni da ɗaci a wurin shi bata wuce ace An mata bata da tarbiyya ba , Al ' Ameen yaci gaba da cewa uwa uba kuɗi kana da cikar arziƙin da zaka iya auro mace ko wace iri ce kai ko babu kuɗin sai ta so ka dan kyan ka , abin kunya daci baya ne ka auri ɗiyar ɗan caca mashayin giya manemin mat....
Hannu Dikko ya ɗaga alamar dakatar dashi , shiru yayi bayan yayi shiru yayi masa nuni da ya fita kawai , Allah ya baka haƙuri mai gida ya faɗa cikin girmamawa sannan yabar ɗakin ,
Fitar Al ' Ameen Dikko ya fara nazarin maganganun shi tabbas duk abinda ya faɗa ba ƙarya bane ba , ko wane mai asali yana so ya auro mai asali gidan tarbiyar da mutunci amma miye aibun An mata ? Duk dai haɗa jini da mutane banza bashi da wani amfani dan ba'a gane matsalar hakan sai zuri'a sunzo dan iskanci jini yake bi , tou amma mi yasa ita An mata batajin magana ne ? Wani sashe na zuciyarshi yace ba komai wata rana zata daina , idan har mace tana shakkun namiji idan dai ya shata mata doka tou fa tabbas ba zata karyata ba , wani sashe kuma cewa yayi matsalar ba'a nan take ba , tsoki Dikko yayi tare da cewa da Allah ku barni...
A ɓangare na kuma , da asuba ina farkawa kayan jikina na cire na wanke su saboda na ɓatasu da fitsari na goge katifar dake da leda a jikinta kila ma sabuwa ce , labule ɗaya na ciro na ɗaura , bayan na gama wanke kayan a palo na shanya saman kujera na kunna fanka , ɗaki na koma na shiga nayi wanka tare da ɗauro alwalla , bayan na fito na sake ciro wani labilen na rufa dashi naci gaba da sallah.... 🤔
Bayan na gama na koma na kwanta , ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni , dan banda wata damuwa saidai kaiwai ina so in tafi gida ,
Ina bacci Dikko yazo kuma tun a palo na fara jin faɗashi wai waye yace kujera wurin shanya ne ? Da sauri na tashi na ɗauki bargo na ƙara lullube jikina a dai² lokacin da naji Dikko yace maza cire wannan tsumman kaje ka jefar dashi a waje , kutumelesi ? 😭 rigata mai tsada itace za,a yadar ? Amma dai wallahi Dikko ɗan iska ne , kuɗi fa masu yawan gaske Alajina ya siyamin ita shine zaisa a yado ta ,
Ina cikin kuka naji ƙarar takalminshi yana tahowa ɗakin da nake , ci gaba nayi da kuka ko zai tausayamin yasa a dawo min da rigata , kwance nake cikin bargo fuskata kaɗaice a waje ina kuka , ƙamshin turarenshi ya ƙara matsowa kusa dani haka ya tabbatarmin yana gab dani dan haka na buɗe idona ina kallonshi ,
Murmushi yayi cikin natsuwa sannan ya fara magana cikin kamun kai da aji , gaba ɗaya jiya da daddare tunaninki nai tayi , da sauri nace me ? Murmushi ya sakeyi sannan yaci gaba da cewa tunanin da nayi tayi cikin dare shine nayi kuskure , sam bai kamata ace na ɗaga hannu na mari mace ba , kiyi haƙuri don Allah idan ma baki gamsu ba zaki iya rama marikin kamar yadda na mareki , ƙoƙarin tashi na farayi dan rama marina , cikin magana mai kama da raɗa yaɗan fiddo kyawawan idanuwanshi yace a haba keko ba'a nan ba kinsan babu kaya a jikinki koma kawai ki kwanta ,
Babu gardama na haƙura na koma na kwanta , fita yayi bai daɗe ba ya shigo da wani haɗaɗɗen kwando ya ajiye a can gefe cikin magana mai laushi da kalamai masu burgewa yace kiyi kalaci ya faɗi maganar tare da nunamin inda kwandon yake , zai fita nace am da Allah idan babu damuwa rigar nan kada a yadar da ita anjima idan zan tafi ita zan saka ,
Ba tare daya kalleni ba yace bama buƙatar ita rigar kayanki yanzu zansa a shigo miki dasu palo , wai ance jibi hutun ku zai ƙare idan zan wuce zan ajiyeki makaranta , kallo ni yayi tare daci gaba da cewa kyakkyawar fuska da kyawawan idanuwa irin naki gararin gari ba nasu bane da ilimi suka dace bada taron murnar zagayowar shekarar aihuwarki ba , yana faɗin haka yayi gaba abinshi , ni kuma nace wallahi aiko babu sakaran da ya isa yakaini makaranta tunda ba cewa nayi ina so ba , dawowa yayi tare da cewa kina magana ne ? Banza nayi dashi naci gaba da hararar ƙasa ,
Murmushi yayi da gefen bakinshi ya fita , yana fita na ƙara cewa kuma ko ka kaini saina dawo dan kaga na kwana nan gidan nan ko an faɗa maka ni ina tsoron waɗanda ka ajiye ne ? Sake dawowa yayi yace kina so ki madani kamar wani sa'ar wasanki ko ? Tou idan kinje makarantar ki gudo mu gani , Dikko ya kaiki saboda haka Dikko zaici gaba da ɗauko ki , ke ɗaya na bayar kuma ke ɗaya za'a bani a ko wane hutu , kuma ko hutu akayi idan ba nine naje ba ko waye wallahi yarinya bazaki dawo gida ba gara ma ki fara kamun ƙafa tun yanzu ko zan riƙa ziyartarki lokaci ² idan kuma kika nunamin yarinta sai ina barki kisha baƙar wahala babu abinci babu kuɗin kashewa , yana faɗin haka ya fice abunshi ,
Ni kuma ƙasa² nace sai inyi ta iskanci da malam su sa fiddoni , in dawo gida , kuɗinkan banza kuɗinkan wofi ko an faɗa maka ni matsiyaciya ce ? Hahaha niko nace da kanki ma zaki riƙa cewa ya baki bari dai kisha azaba yarinya ....
A palon ɗaki na Dikko yasa aka ajiyemin kayana saman kujera , shi kuma yayi tafiyarshi , saida naji fitar motarshi na tashi naje na ɗauko kayan na saka ina sakawa ina mita ni za'a bawa kwance kila ma kayan matarshi ne ya ɗibomin , kona ƙannenshi , niko nace kedai kika sani...
Ɗaki na dawo ina cewa shikenan an yado rigar Alajina daya ji kuɗin rigar shi kanshi nasan sai gabanshi ya faɗi , Allah yasa ya dawo yanzu yace in rama marina saina ci abinci na ƙoshi zan zabgaga mishi mari sai yayi fitsari saboda azaba ,
Gaban kwandon na durƙusa ina ci gaba da surutu babu kai babu misali , kwalin makilin da burosh a gefe da sauri na fara buɗewa dan inga abinda aka kawomin inyi kalacin safe dashi .....
21/09/2019
*JAMILA MUSA...*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 37
Gayu mutanen Allah shine abinda na furta a lokacin da naga shagalin dake cikin food flarks , murmushin jin daɗi nayi wai duk ni ɗaya zanji daɗi na , miƙewa nayi tare da komawa da baya cikin farin ciki na faɗa saman katifa zanci daɗi yau zanyi kalaci da farfesu , ga doya ga farfesun "yan ciki , wannan daɗi da hawa tsaunin rayuwa har haka ? Ɗaga ƙafafuwana nayi sama ina musu shangululu tare da rumgume duka hannaye na a ƙirjina cikin farin ciki nace wallahi madarar ma duka zan juyeta...
Wani irin ihun farin ciki na kurma wanda har na waje saida sukaji ni , da sauri na sauko daga saman katifata naci gaba da aiki dan gani nake idan na tsaya wanke baki a iya shigowa aga kamar na gama a fita dasu ,
ina ci ina kaɗai kai tare da addu'ar rayuwa ta ɗauremin da irin wannan daddaɗan kalaci , naci komai kuma komai nasha nayi hamdala ga ubangiji da ya bani aron lumfashi ya bani baki da ciki da lafiya kuma ya ruboto min wannan babban rabo da alƙamin kudarar shi...
Ina gamawa na tattara komai na fitar palo , labulayen dana ciro na ɗaura na mayar dasu mazauninsu na gyara , saman katifa na dawo tunda dama nayi wanka cike da farin ciki na lumshe idona na tafi duniyar bacci.........!
Tashin hankali a gidan su Sultana , cike da farin ciki Baba ya shigo gida ya dawo da kuɗin shi cike da aljihu domin a daren jiya shi ya lashe maƙudan kukaɗaɗen da aka zuwa a wasan caca , ƙofar ɗakin Sultana ya nufa kai tsaye yana cewa Mamana kin ganni sai yanzu ?
Kowa yayi cirko² domin "yan gidansu Sultana tun jiya suka dawo da labarin ɓatanta , kowa dai yana cikin jimami da tashin hankali , Baba kuwa bayan ya shiga ɗaki shiru² bai fito ba dan a tunaninshi Uwar masu gida tana bayi ne...
Zama yayi har ya gode Allah , komi Uwar masu gida takeyi ai ta isa ta gama ta fito gajiya yayi da zama ya fito tsakar gida yana cewa ina Mamana taje ne ? Shiru kowa yayi ya kasa magana , bin kowa yayi da kallo yanayin fuskar su ta nuna akwai wani abu daya faru , bayan ya gama kallon kowa yayi magana cikin karyewar zuciya cewa ina Mamana...... Take ? Ya ƙarasa maganar yana mai bin bango ya sulale ya zauna ƙasa a hankali ,
Maman Fa'iza ce tace mu saka Sultana a addu'a domin yanzu ba abinda take buƙata sai addu'armu mu dage da roƙon Allah har ubangiji ya bayyana mana ita domin Sultana dai ta ɓata , lokaci guda zufa ta ɓarkewa Baba ya tsurama wuri guda ido kamar mage ta ɗana tarko , bayan wani lokaci kuma yace haka zakimin Mamana ? Haka mukayi dake ? Wannan shine sakamakon alƙawarin ? Ina kika tafi ne ? Inajin babu jimawa mukayi magana dake baza ki taɓa tafiya ki barni ba , shine kika tafi kika barni..... ? 😭 hawaye ya gangaro mishi daga cikin idonshi , daga nan yayi na wani mawaƙi da yace ayye mata a ƙame ƙam , tou Baba shima ya ƙame kamar wayar da tayi hucking....
Tunda na kwanta bacci babu abinda ya dameni kuma bana wani tunanin komai haka kuma banga komai ba a cikin mafarki na , bacci na nakeyi cikin natsuwa da kwanciyar hankali , sai da aka kira azahar na farka nayi sallah bayan na gama na watsa ruwa na koma nayi kwanciyata amma ba bacci nake ba !
Gidan shiru kamar babu kowa ciki sai ƙarar iska irin mai tahowa da ƙasa , a hankali sanyi ya fara saukowa irin mai shiga ƙashin nan , zuwa bayan la'asar sanyi ya sauko sosai wanda yasa mutane suka fara saka rigunan sanyi,
Ni kuma da banda rigar sanyi ina cikin bargo na duƙunƙune , ga azabar yunwa da nakeji na rasa inda zan saka rayuwata , har akayi magrif babu wani labarin abincin rana bare in saka ran na dare zaizo , nasha ruwa har nayi fitsari bansan adadi ba , tun ina daurewa har na fara Allah ya isa a zuciyata...
Tunda nayi magrif ban tashi daga inda nayi sallah ba ina zaune na zabga tagumi kuma ni ba addu'a nakeyi ba , ina cikin wannan tunani naji ƙarar buɗe get murmushin jin daɗi nayi nasan Dikko ne kuma yazo da abinci , tabbas abinci yazo ya kawomin , cike da murna na leƙa ta window kuma wallahi shiɗin ne , sanye da tsadajjiyar baƙar rigar sanyi mai kyan gaske da burgewa tana da farin zif daga gaba , an zageye wuyan rigar da farin ado amma ba irin na mata ba ina ganin dibara ce dan kar rigar ta lalace daga saman wuya , sanye da shuɗin wando da takalmi baƙi amma ba rufaffu bane maɗauri gare su kamar sandals , hannun rigar ya ɗan naɗeshi zuwa guiwar hannu , kanshi babu hula kuma fa gaskiya yayi kyau dake baida ƙiba ko kaɗan amma yana da tsayi daidai burgewa bana zarce misali ba...
Al ' Ameen ke ɗauke da kulolin abinci shi kuma waya yakeyi , ina ganin sun tun karo ƙofar shigowa palon nayi sauri na kowa saman abin sallah na kalli gabas ,
Suna shigowa shi Al ' Ameen ya kunna musu kallo , maimakon ya kawomin abinci sai kawai suka zauna sukaci gaba da kallon kwallo , har akayi isha'e suna zaune kamar asara suna kallon kwallo , inajin maganar Dikko lokacin daya shiga ɗaki mai kallon wanda nake ciki yana cewa bari inyi sallah dai , tsoki nayi tare da cewa andai ji kunya sallah a gida , nima tashi nayi nai sallah dan ina da alwallah ...
Har na gama sallah banji Dikko ya fito ba , kuma naji palon ya fara cika da maza ga dukkan alamu kila gidan dai matattara ce ta maza , tunani na farayi karfa su cinye abinci ban samu ba , tashi nayi na fita ɗan madaidaicin palon na zauna ina jiran fitowar Dikko idan ya manta da ina nan tou ya ganni ya gane ina nan ,
Tunda na zauna ƙarar motoci ke shigowa , hayaniyar sai ƙara sama takeyi maza surutu ga magana babu natsuwa , nafa daɗe ina zaman jiran Dikko bai fito ba , kuma bana so na leƙa babban palon bansan ko su waye a wurin ba , na haƙura da niyar komawa ɗakin da aka ajiyeni naji dai bazan iya kwana banci komai ba yunwa nakeji kamar zan mutu wallahi , dawowa nayi kai tsaye na shiga ɗakin ,
Da sauri ya kallo ƙofar dan yaga waye yake shigowa yana zaune saman abin sallah , murmushi yayi ganina tare da cewa An mata miye ? Ɗan suɓaro baki nayi ina wasa da yatsun hannuna nace dama , sai kuma nayi shiru , ɗauke kallonshi yayi daga gareni yace dama me ? Shiru nayi na kasa magana , shima bai sake magana ba yaci gaba da latsa counter , naci uwar mintuna sha biyar Dikko bai sake kallona ba kuma bai sake magana ba ,
Saida ya gama abinda yake ya ɗauke abin sallar daga inda yayi sallah ya ɗora gefen gado , zuwa yayi zai wuce ya fita dan yayi kamar ma babu ni a wurin ,
Ya kusa fita nace yunwa nakeji , yi yayi kamar baiji abinda nace ba ya fice abunshi , biyoshi nayi a lokacin har ya kusa fita daga palon ya shiga babban palon , nace da Allah nace maka yunwa nakeji nayi maganar a tsiwace , naji ya faɗa tare dayin gaba abunshi ,
Tsoki nayi cikin ɓacin rai na koma ɗaki ina gunguni , shi kuma daya koma kallonshi yaci gaba dayi , sai ihu sukeyi "yan iska kamar mahaukata , amma bana tunanin Dikko yana wurin dan har yanzu ban jiyo maganarshi ba , duk wanda aka ci su sai kuji hayani ta ƙara sama , sai gaddama da magana cikin faɗa² ,
Sai yanzu naji dariyar Dikko yana shigowa cewa ko gobe da fansar kura saidai garin da babu awaki , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya nace ashe kaima ka iya karin magana ? A dai² lokacin daya shigo yana dariya ,
Ɗaure fuska nayi kamar ina cikin yanayi damuwa , ko kallonshi banyi ba ya ɓatamin rai ni zai zubowa abinci a gaban bainannasi hmm , ga abinci ya faɗi maganar a daidai lokacin da yake ajiyewa a gabana , kauda kaina nayi na tura abincin na ƙoshi ...
Murmushi yayi tare da ɗaukar abinci zai fita , nace kai nifa wasa nakeyi bani nan nayi maganar tare da nuna mishi ya maidoshi gabana , banza yayi ya fice daga ɗakin da sauri na tashi nabi bayanshi amma kafin in fito harya fice ya koma cikin abokanshi yana dariyar mugunta , a ranshi yace daga yau sai kiyi hankali ni ban iya wasa ba kuma ba'amin wasa ,
Wannan rana saidai na kwana da yunwa nasha kukana har bacci ya ɗaukeni bansan lokacin da suka tafi ba ,
Koda safe dakel nayi sallah saboda yunwa duk jikina ciwo yakeyi kamar nayi aikin ƙarfi , bayan na gama sallah na daddafa nayi wanka , na canja kaya sannan na koma bacci ,
Yauma da asibiti ya fara , ya lallashi matarshi kamar yanda ya saba , yau ya samu ya lallaɓata tasha ruwan tea , ya kuma sake tambayarta damuwarta dai tayi masa zurfin ciki har yanzu , dan haka bai wani damu ba ya wuto wurina ,
Yau shi ɗaya yazo babu Al ' Ameen kuma kai tsaye ya shigo ɗakin , bayan ya ajiye kayan da yazo dasu ya kunna fitila yana cewa anya ma kinyi sallah ? Tashi ya faɗi maganar tare da yaye bargon dana lulluɓe , juyawa nayi na kifa kaina saman katifa saboda haushi ya bani jiya sosai ,
Yauma bakijin yunwa bara in tafi , ya faɗi maganar tare da ɗaukar kwandon , cikin fushi nace abinci banza gare ka , ko an faɗa maka yunwarshi nakeyi muma gidanmu sau 3 a rana akeci ka tafi na ƙoshi nasan yunwa baza ta kasheni ba an girma ba'asan an girma ba ,
Dariya yayi tare da zama gefen katifa yace wai nima irin wasan jiya nake miki amma ke naji kalaman naki zafi garesu ai kema da sai kiyi shiru kamar yanda nayi shiru jiya , sai kace dai kina jirana ? Cike da jin haushi na tashi zaune ina cewa jiranka nakeyi kamar yadda ka zanemin rayuwata haka zan zane taka rayuwar babu gudu babu ja da baya ba abinda ke cikin zuciyata face ɗaukar fansa akan ka ,
Murmushi yayi tare da gyara zamanshi sannan ya ɗaure fuskarshi babu wasa a tare da ita ya fiddo siffofinshi masu tayar da tsikar jiki da saka fargaba yace ke har gobe yarinya ce , amma ki sani ya nuna ni tare da ci gaba da cewa wannan tsarin tamkar sautin radio na ne , na ƙarashi na rageshi yadda nake so , kiyi haƙuri burina kaɗan ne amma sanin ya kamata na yana da ƙarfi , ban iya ba kece kika koyamin kinsa na zama kamar wani sakarai sai biye miki nake ina ƙananan maganganu kamar mace , dakamin tsawa yayi tare da zaro idanuwa sannan ya sassauta maganar shi zuwa sauti mai kama da raɗa yace ki kiyayeni kafin na baki hukunci a karo na biyu , azabar yau sai tafi ta jiya zafi , ina nan kuma namijin ne .... 🤫 ya ƙarasa maganar tare da ɗora ɗan yatsanshi a saman bakinshi yace shitt ya rufe maganar da fiddo idanuwanshi da suka ɗanyi ja...
Jiki a sanyaye na koma na kwanta , ba tare daya kalleni ba yace tashi muyi break , da sauri na tashi naje na wanko bakina da fuskata nazo na zauna kusa dashi cikin ladabi , shine da kanshi ya zuba komai amma tea ɗin a kofi ɗaya ya haɗa kuma da kofi ɗayan mukayi amfani yana sha ya bani insha in miƙa mishi , cokali ma ɗaya mukayi amfani dashi ,
Ba wani damuwa a tare dashi ko kunya ko irin yaji babu daɗi haka dai , tsakaninshi da Allah hankalinshi a natse yake , har muka gama da kanshi ya tattara komai ya mayar a kwandon ya ɗauka kwandon ya fita , ya daɗe sannan ya dawo ya kwanta a gefen katifa ,
Wayarshi ya ciro yace zo kiga in nuna miki "yan uwana , matsawa nayi kusa dashi amma ni ba kwanciya nayi ba zama nayi , ɗago kanshi yayi tare da bani wayar na riƙe a hannuna yana wuce hotuna , wannan itace wance wannan kaza ce dad ina ne kinga momy kinga wannan itace nake bi mawa , tana aure a gari kaza , haka dai yayi ta wucewa har yazo kan Sadiya yace wannan kuma matata ce....
Kai kalmar namiji yace matata kalmar tana da girma da matsayi , matata saida na maimaita a zuciyata sannan nace ban ƙaunarta har abadan duniya na faɗa a zuciyata , kallona Dikko yayi tare da cewa tayi kyau ko ? Ban sani ba nace masa , baiyi murmushi ba kuma baiyi dariya ba yace kada Allah yasa ki sani "yar rainin hankali ,
Cike da ɓacin rai nace dakai da matarka duk kune "yan rainin hankali munafikai dukanku , tsareni yayi da ido tare da cewa kishi ko ? Ya ƙarasa maganar yana nunani da san yayi murmushi amma ya haɗeshi , tsoki nayi tare da cewa hmmm Allah ya sawaƙe min niko waye zanji kishin a cikinku kai ne ko ita ?
Miƙewa yayi tare da cewa tunda baki son na tayaki fira zan tafi , bazan dawo anjima ba Al ' Ameen zai kawo miki abinci , idan Allah ya kaimu gobe lafiya ki shirya da wuri dan bana san tafiyar rana , yana faɗin haka yayi gaba abunshi....
Abinci rana da dare duk Al ' Ameen ya kawo min , yau babu wanda yazo kallon kwallo ni ɗaya a gida bayan naci nasha na koma na kwanta tare da addu'ar Allah ya kaimu gobe lafiya !
Da safe tun kafin in tashi bacci Dikko yazo , shi ya tasheni tare da ajiye uniform a gefen kati yace maza jiranki nakeyi , kallon kayan nayi sannan na kalli Dikko da yasha manyan kaya hada babbar riga hular kanshi kuwa sai sheƙi takeyi saboda sabinta ko wanki ne ? Koma dai miye sai ka kalli kanka a ciki kayi sakace , kallon ƙafarshi nayi nan ma komai yaji gemu ma dai yasha gyara yana nan dai da jan hankali da yakeyi , gaskiya Dikko haɗaɗɗen namiji ne mai tafiya daidai da zamani , ga kyau ya gayu uwa uba iya saka sutura , Dikko nada burgewa ...
Katse min tunani yayi da cewa kin tsaya kina kallona ! Kiyi maza jiranki nakeyi , yana faɗi maganar yabar ɗakin , cikin kuka na nufi toilet nayo wanka sannan nayo alwalla nazo na fara gafatar da sallah asuba da banyi ba akan lokaci , bayan na gama na shirya cikin kayan makaranta ina kallon kaina a madubi na fashe da wani irin kuka wanda har sai da gaban Dikko ya faɗi...
Da sauri ya shigo ɗakin fuskarshi ɗauke da damuwa yace a mota zakiyi kalaci , shi a tunaninshi yunwa nakeji , cikin kuka nace ni wallahi bana san makaranta haba Yaya Dikko me yasa zakamin haka abin kunya a ganin a makatanta yanzu ,
Wani irin kallon rainin hankali yayi min daga sama zuwa tsakiya ta yace lallai yarinyar nan kin rainani nine Yayan naki.... ? Baki da hankali ma da Allah ni wuce mu tafi munatane na jirana , hannu na ɗora saman kai ina cewa dan girman Allah ka kyaleni wallahi bazan sake ba , cikin kwantar da murya yace muje tun kafin kiji babu daɗi ,
😭 hijabi na saka nabar kallabin a katifa nayi waje , abun kunya shi ya ɗaukomin kallabin wai hada jakkar makaranta saboda ci baya , waini zan koma makaranta , ina gaba yana bayana har cikin mota , ni kaɗai na shiga baya ya wurgomin jakar da kallabina ya rufe ƙofar ya shiga gaba , Al ' Ameen yaja muka fita daga gidan , kuka naci gaba dayi ina ma katsina kallon ƙauna , tafiya akeyi sosai dan Al ' Ameen yakai mota maleji wurin gudu , kuka na ya ƙaru lokacin da naga an ibi hanya tafiya da gaske babu fashi....... !
22/09/2019
*JAMILA MUSA CE...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 38
Ƙuramin idanuwa yayi yana kallona ta cikin madubin gaban mota , sai kuka nake ina fyace majina da gefen hijabina , tissue ya wurgomin bai juyo ba kuma bai kalleni ba yace zaki ma mutane shiru haka nan ko kuma dai.... ?
Harararshi nayi cikin muryar kuka nace mara zuciya ko mutum baya harkar ka sai ka shiga nashi mutum ba dangin uwa ba na uba kawai ka shigomin rayuwa , kyakyawan murmushi yayi da gefen bakinshi amma baiyi magana ba , kallonshi Al ' Ameen yayi bakinshi ɗauke da magana , murmushi Dikko yayi tare da cewa manta da labarinta ka ƙaddara ma bama nan bare kayi tunanin munji abinda tace , makaranta dai zuwa babu fashi !
Shiru sukayi su dukansu babu wanda ya sake magana , saidai shi Dikko yana kallona ta cikin madubi idan akayi sa'a muka haɗa ido sai yayi murmushi mai tattare da mugunta , matsawa nayi daga saitinshi dan ya daina kallona , ƙara gyara saitin madubin yayi yaci gaba da kallona , kwanciya nayi na lulluɓe da hijabi naci gaba da baccin dole...
Har nayi bacci na farka bamu isa ba , kuma tafiya Al ' Ameen yake bata wasa ba dan shima kusan irin tuƙin Dikko yakeyi kamar basa san rayuwarsu , ganin har yanzu a hanya muke yasa na sake komawa na kwanta ina mai ci gaba da kuka , jin kukana yasa Dikko juyowa tare da cewa ke miƙomin kunun nan tunda baza kisha ba ,
Cikin kuka nace ina sha , Al ' Ameen yasa ya faka a gefen titi da kanshi ya fita ya ɗauko ruwa a but sannan yazo ya buɗe inda nake ya bani ruwan , yana nufi in kuskure baki na , fita nayi na kuskure bakina na wanke fuskata na koma mota na zauna ,
Ɗan ƙaramin flaks ne na sulba mai kyau cike da kunun gyaɗa tun kafin in fara sha Al ' Ameen ya tada mota ya hau titi yadda ta kamata yaci gaba da gudu , cike da baƙin ciki nake shan kunun , yayi min daɗi sosai ɗan kaɗan na rage na miƙawa Dikko flarks in dan ya ajiye , ansa yayi ya shanye sauran dana rage, a raina kuma tunani nake Dikko ko ƙyamata bayayi yanda yake ɗan gayu mai aji har zansha abu in rage yasha saura na ,
Har muka isa bakin get in makaranta babu wanda ya sake magana , a bakin get Al ' Ameen yayi parking , muna zaune a mota ga dukkan alamu akwai wanda ake jira , bamu wane daɗe ba , wata irin shareriyar mota tayi parking kusa da tamu , wani matashi ne ya fito daga motar yayo wurin motarmu , Al ' Ameen ya sauke gilashin kusa da Dikko , yana isowa Dikko ya miƙa mishi hannu suka kashe ,
Sai kuma aka shiga gaisawa bayan sun gaisa yace ina An matan take ne ? Murmushi Dikko yayi yace gata can baya kuka takeyi , dariya matashin yayi tare da cewa tun daga katsina har bakori tana kuka ? Dikko yace ai bata da aikin yi , dariya matashin ya sakeyi tare da cewa sannu dai za'ayi mata ,
Ba tare da Dikko ya juyo ba yace An mata dani dake waye ya kamata ayi ma sannu ? Banza nayi dashi ban bashi amsa ba , dariya yayi tare da cewa muje sauri nakeyi yayi maganar yana kallon agogon hannunshi , komawa matashin yayi cikin motarshi ya tada , mu mukayi gaba shi kuma yana bayanmu har muka isa bakin ofishin principal , a bakin ofishin mukayi fakin sannan muka fita gaba ɗayanmu muka nufi cikin office in...
Bayan gaisuwa akaci gaba da abinda za,ayi duk wani abinda ya kamata ayi anyi , kuma Dikko yace wa principal ko hutu akayi idan bashi yazo ba kar wani ya ɗaukeni , ya ƙara da cewa ko wannan ya nuna Al ' Ameen yace koshi yazo a , a, niɗin dai , tace insha Allah , saboda Dikko ya ɗaukeni ƙarshen kidahuma JS 1 yasa aka ajiyeni , inajin aji ɗaya na ƙara fashe wa da kuka duk da dama kukan nakeyi tun safe har yanzu ,
Bayan an gama aka ciro kayana daga bayan motar Dikko , a bayan motar abokinshi aka fiddomin katifa , bayan an gama sauke kaya Dikko ya bulale Prcp da kuɗi wanda Al ' Ameen ya miƙa mata su , tayi ta zabga godiya Dikko yace tasa min ido sosai a riƙa zaneni idan nayi abinda bai kamata ba , tace insha Allah !
Ina tsugunne a gefe sai kuka nakeyi , bayan sun gama abinda suke Dikko ya kallo inda nake yace taso ki biyoni , jiki a lalace nabi bayan shi har cikin mota , dukanmu a baya muka zauna , da yanayin tausayi a fuskarshi yace idan kina san wani abu ki faɗawa principal zatamin waya kinji ko ? Nace to , karkiyi rashin ji kiyi karatu kuma ki zama mai haƙuri karki sake ki biyewa abokan banza kinji ko ? Saida na goge hawaye sannan nace tou ,
Shiru yayi zuwa wani lokaci yace tou kalloni kiga , ba musu na ɗaga idona na kalleshi , murmushin shi mai burgewa yayi tare da cewa idan kuma kikayi , uhum ? Ya nuna idanuwanshi da hannunshi , bansan abinda hakan da yayi yake nufi ba , banyi magana ba ina kallonshi dai , yace to nan ? Ya nuna , girgiza kaina nayi alamar a , a tou zakiyi tunani na ko ? Da kai na bashi ansa Eh , tou idan dai kin tunoni kar kiyi kuka kinji An mata zan riƙa zuwa da wuri ina ganinki ai zaki ji daɗi idan kika ganni ko ? Nace Eh ,
Bandir in "yan 1k ya bani guda biyu yana cewa karki yi damuwa sosai kiyi farin ciki kullum don Allah kar kiyi kuka da yawa inaji a jikina idan kina cikin damuwa kinji ko ? Jinjina kaina nayi alamar gamsuwa , godiya yayi tare da cewa tou kya iya tafiya , godiya nayi sannan na fita daga motar , ina fita Al ' Ameen ya shiga yaja suka tafi abokinshi yabi bayan su shima cikin motarshi...
Aji Principal tasa aka rakani tare da cemin idan an tashi makaranta inzo da "yan ajinmu su tayani ɗaukar kayana , nace tou , kamar wata geliya haka nake ji na , na koma kamar wata sakara , haka na zauna ina bin "yan ajin da kallo , kowa sabgar gabanshi yakeyi babu wani da ya damu da wani ,
Koda aka tashi ban nemi kowa ya tayani ɗaukar kaya ba na koma ofishin principal , tou Dikko dai ya nemomin mutunci na tunda yayi mata wanka da kuɗi mutane basa abu dan Allah sai dan hatimin nasara , da kanta ta samu yara suka tayani ɗaukar kayana har zuwa ɗakinmu...
Bayan munje mun ajiye kayan na samu wuri na zauna ina kallon yanda kowa yake rayuwarshi domin ina so na fahimci yanda rayuwar makarantar take tafiya !
Tunda Baba ya sulale ƙasa ya tsaya cak ya daina aiki , yana da rai amma dashi da matacce basu da banbanci ɗagowar da cikin shi keyi kawai zaka gani ka tabbatar da ranshi , wannnan abu yayi ƙololuwar ɗagawa kowa hankali dan haka aka kwashe shi akayi asibiti dashi...
A ɓangaren Sadiyya kuma tanajin jiki sosai dan haka iyayenta suka buƙaci ta koma gida suyi jinyarta , amma daga inda Dikko yake ya murje idonshi tas yace idan dai shine yake aurenta a barta kar wanda ya tafar mishi da mata ko yace ya kasa kula da itane ? Dole suka haƙura suka barta ,
Amisty kuwa da Hafsa lingu da saƙo sun nemi Sultana basu samu ba , kuma wayarta ma idan sun kira a kashe take dan tuni Dikko ya ƙarya layin , kuma sunje wurin Alaji sun tambayeshi ko yana da labarin Sultana yace shima kanshi nemanta yakeyi , yaje gidansu ance an saceta wurin partyn birthday inta Babanta ma yana asibiti baida lafiya , bawan Allah Alaji shine ke kula da Baba duk wani aune ² da magunguna shine yake biya...
Sati na ɗaya a makaranta banda damuwar komai kuma banda wani tunani daya dameni sai Babana da nakejin kewarshi kullum rana , bana tunanin Inna kwata² dan na tabbata itama duk inda take bana rayuwarta kuma bata tunani na amma nasan duk inda Babana yake yana can yanajin damuwa na rashina a kusa dashi !
Har yanzu banyi abokiya ko ɗaya ba kuma bana shiga sabgar kowa tunda babu abinda na nema na rasa , ni ɗaya nake rayuwata idan kuma naje aji idan malami ya shigo zan samu natsuwa na tattara hankali na , rubutu ma ni nakeyin abuna da ɗaiɗaya nake ɗauko ko wane harafi , bana surutu a aji dan ba'a magana da hausa idan kuma mutum yayi za,aci shi tara ne ,
Tun ranar da nazo ban sake zuwa wurin principal ba , kuma ta aiko a kirani banje ba , harkar gabana kawai nakeyi dan gaskiya naji ciwo da Dikko yasa aka ajiyeni JS 1 kuma naci ɗamara saina nuna mishi ni ba jahila ba ce ba ,
Dikko kuwa tunda ya ajiye Sultana a makaranta yaci gaba huɗɗoɗin gabanshi , baiyi waya yaji ya Sultana ba kuma baizo makaranta ba da sunan ziyara , duk juma'a yana katsina yana komawa monday tunda safe yana ta zirga² a hanya saboda rashin lafiyar matarshi amma ko so ɗaya bai biyo wurin Sultana ba ,
Haka dai rayuwa ta taci gaba da tafiya a makaranta , mutane suna ta shigowa rayuwata amma banda lokacin kowa ina so in tsula iskancina amma ba yanzu ba saina san abinda nakeyi , saboda ko magana nayi ma mutum sai kawai inji suna wani min turanci banza shi yasa na fita sabgar kowa nake tawa sabgar..
Wallahi kwata² banajin daɗin zaman makarantar nan a daddafe dai muka fara jarabawa dan hutu za'ayi mana kuma har yanzu Dikko bai zo ba bai aiko ba , kuma kuɗin daya bani har yanzu akwai su kayan provision ina ma akwai sosai dan gaskiya ba ƙananan kuɗaɗe ya kashe ba dan dai kawai inyi farin ciki !
Tunda naga hutu ya fara gabatowa nake neman "yan katsina dan in turasu gidanmu su faɗawa Babana ina FGC nasan zaizo idan muka dawo hutu , na samu "yan katsina amma duk wanda na faɗa masa anguwarmu sai yace bai sani ba dan abinda na lura duk "ya "yan masu kuɗi ne irin wanda basa zuwa yawo kamar yanda mu "ya "yan talakawa keyi...
Dole na haƙura gashi ban riƙe number kowa ba dana riƙe tabbas dana samu aron waya na kira nace a faɗawa Babana yazo ya tafi dani , tou ban riƙe ba banda yanda zanyi inba haƙuri ba dan ban samu yanda nake so ba , duk ɗalibai suna farin cikin hutu kowa yana cike dajin daɗi zaije yaga iyayenshi saɓanin ni da bazan samu ganin Babana ba ,
Anyi jarabawa an gama kuma an bada report ga ko wane ɗalibi nima an bani na saka a jakata na adana abuna ,
Ranar hutu kowa yana cikin farin ciki ko wane ɗalibi ya samu "yanci kamar sakakken tsuntsu kowa na wali sakamakon ni da principal ta tsare a ofishinta , motoci kuwa sai ɗaukar dalibai sukeyi suna tafiya abin dai gwanin burgewa ina ta kallon ikon Allah har ɗalibai suka ƙare kaf dan principal tacemin tun satin hutu ta faɗawa Yayana za'ayi hutu , kuma jiya ta kirashi tace mishi yau ake hutu yace zaizo insha Allah ! Saida kowa ya watse babu sauran ɓishi²n ɗaliba ko ɗaya saini ina jiran zuwan shi ,
Dikko baizo ɗaukata ba sai bayan azahar bayan ya iso ya kira principal ya sanar da ita zuwanshi , dan dama lokaci ² tana kiranshi ya kawo ina tana mishi sannu da hanya , tare muka fito da ita har wurin mota muna tare da ita , bayan mun isa suka shiga gaisawa da Dikko tare dajanshi da fira dan kilbibi an fara magana da hausa sai a wani jefo turanci dan munafirci , gajiya nayi da tsayuwa na buɗe mota na shiga na zauna ,
Yauma ya tunbiza mata kuɗi masu yawa , gaskiya Dikko yana da kyauta sosai zaiyi wuya ka ganshi bai baka ba , ya ganka yanzu ya baka anjima ma idan kuka sake haɗuwa saiya ƙara maka , godiya tayi sosai tare da mana addu'ar sauka lafiya ta wuce...,
Saida Al ' Ameen ya fara tafiya Dikko ya juyo dukanshi yana kallona , bayan wani lokaci yace An mata kin rame me ya sameki ne ? Gyara baki na nayi tare da cewa ina yini , na gaishe shi dan kauda waccan maganar , murmushi yayi tare da cewa lafiya qalau , gaishe da Al ' Ameen nayi shima ya ansa ,
Cike da tausayi Dikko yace kodai baki san wannan makarantar ne ? Dama saida nace bazan kawoki boarding ba kowa yace min wai in kaiki makarantar kwana , a raina nace wato saida kayi shawara kenan , kallon Al ' Ameen yayi tare da cewa ji yarinyar nan ta rame ni gaskiya banji daɗin haka ba wallahi ya ƙarasa maganar yana mai dawo da kallonshi wurina yace An mata ko bakicin abinci ? Murmushi nayi nace ina ci , to baki da kuɗi ? Nace ina da , to meke damunki ? Ko baki lafiya ne ? Yayi maganar tare da nunamin in matso kusa dashi ,
Matsawa nayi kamar yanda yake so , ƙasa² yayi da murya yace meke damunki ne ? Ba komai nace , tsoki yayi tare cema Al ' Ameen ya tsaya zai dawo kusa dani , parking Al ' Ameen in yayi Dikko ya fito ya dawo baya kusa dani , ansar jakata yayi bayan ya rufe ƙofa yana cewa matso kusa dani , juyar da kaina nayi ina cewa nidai ka gyaleni a dai² lokacin da motar taci gaba da tafiya ,
Buɗe jakar yayi yana cewa ni wallahi naga duk kin koma "yar ƙarama Allah dai yasa ba masonyo min ke akayi ba , shiru nayi kamar banji ba , kalloni yayi da kallo maisa natsuwa , magana yayi cikin riƙe haruffa yace umm ya nunamin nayi shiru da kanshi , murmushi nayi shima murmushin yayi yace tou kice wani abu mana ,
Sake maimaita maganar yayi , girgiza kai nayi cewa nice , yace ai banji kin fara kuka ba yau naji kinyi shiru , a daidai lokacin daya fara duba littafai na , haka yayi ta cirosu ɗaya baya ɗaya yana dubawa har yazo kan report ina , warwareshi yayi ya duba , gaba ɗaya annurin fuskarshi ya ɗauke ya ƙurawa report in ido , cikin muryar ɓacin rai yace tsaya , tsayawa Al ' Ameen yayi Dikko yace fita ki koma gaba ki zauna , da sauri na fita na koma gaba na zauna , ina ta mazurai kamar nayi wa sarki ƙarya duk yanda akayi a cikin waccan takarda yaga ɓacin rai...
Shiru yayi tun daga nan ba saike magana ba har muka iso katsina , ko waya aka kirashi baya ɗauka , lokacin da muka iso har an fara sallah magrib , Al ' Ameen na tsayawa na fita da sauri zan wuce cike Dikko yace ke zo nan , da sauri na dawo shi kuma Al ' Ameen fita yayi ya ɗauki buta ya zagaya can bayan gida dan yayi alwallah ,
Buɗe murfin motar yayi ya fiddo ƙafar ɗaya ɗayar kuma tana ciki , tsareni yayi da idanuwa dan haka na sauke kaina ƙasa shiru yayi na wasu mintuna sannan ya ɗago report in yace dan kin ɗaukeni sakarai ni zaki kawo ma wannan abun ? Shiru nayi banyi magana ba , tsawa ya daka min yace baki ji ina miki magana ne ? Cikin rawar murya nace yi haƙuri , fitowa yayi daga cikin motar da sauri nayi baya , shima takowa yayi ya matso kusa dani , da sauri na sake ja baya , ya sake biyoni , yana sake matsowa na ƙara ja baya , idan na sake matsowa kika matsa wallahi saina zaneki , tsayawa nayi jikina ya fara kyarma ina kallonshi ,
Cike da ɓacin rai yace wannan iskanci zaki kawomin ? Girgiza kaina nayi ba tare da nayi magana ba , cikin tsawa yace shin kinyi rantsuwar magana ne ina miki magana kina girgizamin kai , da sauri nace a , a , jinjina kai yayi tare da tillomin report in yace ɗaukarshi ki shiga gani nan zuwa zaki faɗamin iskanci da kikeyi makaranta har kika ɗaukomin na 20 , na ƙarshe ke jakar da baki kishin kanki ya ƙarasa maganar tare da nannaɗe hannun rigarshi dan Al ' Ameen ya kawo mishi ruwa zaiyi alwallah...
Duƙawa nayi na ɗauki report in zan shiga ciki yace kije ki fiddo min jakar banzarki daga mota , da sauri naje na ɗauko jakar na wuce ciki a lokacin shi kuma har ya gama alwalla ya biyo bayana yana ci gaba da faɗa ,
Ɗakin da yake shiga ya wuce ni kuma na shige ɗakin da nake zama , yana nan kamar dai da babu wani ci gaba a cikin ɗakin , alwallah nayo nayi sallah ina roƙon Allah ya bani mafita Babana kaɗai nake ciwon san gani ,
Har nayi sallah isha'e Dikko bai fito ba , su kuma uwayen ƙwa² har sun cika gidan sun fara gardamar kwallo , gajiya nayi na kwanta a inda nayi sallah gaskiya rashin ahali masu mutunci bai ba , duk wanda ya rasa iyaye masu daraja ya zama sai a hankali , ita kuma Inna ko wane irin ahalin suka raine ta ? Soyayya tana rufewa mata ido dasan duniya har su kasa gane aibun namiji , irin wannan rayuwar bata dace dani ba , da na fito daga zuri'a masu mutunci da duk haka bata faru dani ba ,
Inayin rayuwa irin ta dabbobi kuma ni ba dabbar ba , mahaifi ya haifi zuri'a wai ya barsu da cida kansu wannan ba komai bane sai rashin tsoron Allah , caca neman mata shaye² shine wanda na samu a matsayin ubana , rayuwata tazo a garari zata ƙare a raɓe² , na ɓarar da mutuncin da yasa har wani namiji yake da damar shigowa rayuwata ya ɗaukoni daga cikin ahalina ya maidoni cikin rayuwarshi , wannan wace irin rayuwace na samu kaina a cikin ta... ?
Dariyar Dikko na jiyo sai kyalkyatawa yakeyi duk yadda akayi waccan dariyar wallahi mugunta yaji , palon yayi shiru sai salati akeyi ƙasa² amma Dikko sai dariya yakeyi yana ƙarawa , maganar Al ' Ameen naji yana cewa mai gida tou ya za,ayi , miƙewa Dikkon yayi yana dariyar mugunta yayo ɗakin da nake kwance ,
Cikin dariya yace ya miƙo hannunshi yana cewa An mata taso mu tafi , da sauri na taso kallona yayi yace wai duk me kikeyi baki cire kaya ba , ba tare dana kalleshi ba nace ba komai , tou zo mu tafi kina zuwa ? Ya tambayeni , girgiza kai nayi alamar a , a dan Dikko baida saiti abinda na fahimta idan dai yana cikin mugunta zaiso yayi ta zalinci yana dariyar cuta ,
Dariya ya sakeyi cikin sigar cuta yace da Allah kizo mu tafi , kyaleshi nayi na koma na kwanta , murmushi yayi sannan yace to tunda baza ki ba karki bacci ki jirani yanzu zan dawo kinji ko ? Nace tou , kallona yayi cikin wani irin yanayi sannan yace kinsan yau zan hanaki baccin dare sai kin faɗamin abinda yasa kika je kikayo na 20 , nace tou , har ya fita kuma ya dawo yace kiyi wanka kafin in dawo ga kayanki nan palo ki kwashe su ki dawo dasu ciki naga ma duk sunyi ƙura , yana faɗin haka yayi gaba abunshi , ina kallonsu ta window kowa ya shiga mota amma ba'a fita da motar Dikko ba kuma ba'a tafi da Al ' Ameen ba , saida suka gama fita na wuce bayi dan inyi wanka.....
0 comments:
Post a Comment