INdo kuwa tunda ta koma gida take wanke hakorinta ko abinci k'in ci tayi sabida kar yayi daud'a malam Sadeeq ya hanata kyauta. kwanciya tayi male-male a tsakar gida kan tabarma tamkar me yin azumi, takaici da haushi suka cika inna ta kalleta tana daga tsaye Innan tace.
"Ke! 'Yar nan ki rufawa kanki asiri kizo kici abinci kin ganin min sakarya, banda malamin naku mugune taya zai hanaku cin abinci sabida wani an goge baki, toh bari ki kashe kanki ai kinyi wa kanki..."
INdo tayi shiru tana ci gaba da rik'e ciki tana birgima, baban su ne ya shigo ganin yadda INdo keyi ne yasa shi tambayar inna nan ta sanar mishi aikuwa ya fara fad'a tare da cewa ta tashi taci abincinta amma ko motsi INdo tayi shiru sai hawaye da take fitarwa a hankali. Juyawa baban nasu yayi direct ya wuce gidan da Sadeeq yake ciki, kwankwasawa yayi yazo ya bud'e sam be san shiba dan haka ya fara mai kallon rashin fahimta baban INdo yace.
"Sunana malam Hamza uban INdo d'alibarku ta makarantar tsefawa, ga 'yata can zata mutu tak'ici tak'i sha sabilida kunsa musu dokar yin buruhi. Toh bazai yiwuba, tun wuri kaje kasa taci abinci dan idan ta mutu akan wata kyautar ku ba yafewa zanyi ba kur'anikuwa.."
"Subahanallahi malam ai ni ba haka nake nufi ba itada ma ba..." Sadeeq be k'arasa magana ba malam Hamza ya cafe zancen ta hanyar d'aga masa hannu yace.
"Karkayi min wani batukaji ko, tanacan tana malan geruwa dagani har uwarta munyi-munyi taci abunci tak'iya wai kar bakinta yayi daud'a. Ita Uwata ai batada jimirin yinwa ko azumi goma bata iyawa dan haka kokaje kasa taci abinci konaje har gidan protocol (principal) d'in nayi mai bayani zaka kashe mana 'ya'ya."
Tsaki Sadeeq yaja a k'asan zuciyarsa sannan ya rufe gidan ya kalli baban INdo yace "Muje toh amma ni ba haka nake nufin suyi ba."
Kwance suka tarar da ita tayi shame-shame tamkar wadda zata mutu gaban malam Sadeeq ya buga mamaki da tsoro suka dirar mai cikin sanyin jiki ya kalli INdo bakin sa yayi mai nauyi ya daure dai yayi mata magana cikin dakiya.
"Aisha tashi zaune please."
Da kyar INdo ta samu ta iya d'ago kwayar idonta tana kallon malam sadeeq d'in yayi mata alama da ka nan ta mik'e zaune da kyar jikinta duk yayi fututu da k'asar gurin da ta kwanta rigar jikinta daga wajan hammatar ta yage sikert d'in ma duk yasha faci tana son mik'ewa amma ta kasa, hankalinsa ya kuma tashi lokacin wayarsa na ta faman ringing amma ya kasa d'agawa bare yasan ko waye. Daurewa yayi ya kuma matsawa kusa da ita yana kallonta yace.
"Aisha tashi kici abinci ai ni ba haka nake nufi ba, kinga idan kin gama cin abincin ma zaki iya yin brush d'in amma ba'a zama da yinwa idan ba haka ba mutuwa ake yi tashi kinji."
Kasa mik'ewa tayi saida baban ta yace da innar ta mik'ar da ita sannan aka zaunar da ita ta jingina da jikin bango jikin duk babu kwari tayi zuru-zuru da ita kai daka ganta kasan tana cikin wani hali. Kallon Inna malam Sadeeq yayi gabaki d'aya tausaya musu yake sabida ganin halin da suke ciki na rashi, ya karyar da baki yace.
"Mama a kawo mata abincin taci."
Sai Inna taji wani banbarakwai daya kirata da Mama yayin da INdo ta ke numfashi da kyar dan da kyar take iya bud'e ido. Inna ta kawo dambun mazara ta turawa INdo gabanta Sadeeq ya kalli kwanon sam babu alamar akwai mai a ciki ya kuma kallon INdo wadda ta luma daddaud'an hannunta wanda duk k'asa ta 6atashi yaga ta fara watsa danbun cikin bakinta, mamaki yasa shi yin shiru ba tare da yayi magana ba har ta cinyee besani ba yana tsugunne yana tunani.
Sai da ta gama cinyewa sannan Malam Sadeeq ya mik'e, ya yiwa Inna sallama sannan ya fita. A k'ofar gida ya tarar da baban INdo nan ya kuma bashi hak’uri da kuma k'ara yi mai bayanin abinda yake nufi akan su, mahaifin INdo naji ya dinga 6oye hakoransa wad'anda suke jawur sabida tsabar cin goro da rashin kula dasu.
Yana shiga gida ya zaro wayarsa missed call ya tarar na Abubakar, sai da ya zauna a bakin katifarsa sannan ya kira layin har sai da ta kusan yankewa sannan yaji an d'aga.
"Sadeeq ina ka shiga ne inata kira baka d'aga ba..?!"
Cewar Abubakar cikin sanyin muryarsa da jan aji, Sadeeq ya shafa kai yana kuma sauke ajiyar zuciya yace.
"Twinnie ina jin sai na d'auki shawararka, wannan kauyan yafi karfina wallahi haukan su yayi yawa sosai."
Yayi shiru yana sauke numfashin takaici kafin Abubakar d'in yace.
"Da kyau gara tun yanzu ka fara gane cewar kafi k'arfin secondary teaching ka dawo nan gara ko FCE kano ne kaje kayi lecturing."
Shiru suka yi na d'an lokaci kafin Sadeeq yace.
"Toh zan kuma yin shawara amma nima abun kauyan nan ya fara isata, abun nasu yayi yawa ga gidadanci."
"Twinnie kullum haka kake cewa yanzu kawai aiwatarwa zaka yi mudai muna nan muna yi maka fatan alkairi."
"Ok insha Allahu sai munyi waya anjima a gaida min da qibdiyyah."
"Zataji dakyau gata nan ma muna tare."
Beyadda sun gaisa da itaba ya kashe wayar dan yaji ta fiye shiru da yawa kuma shima ba surutu garesa ba.
***
Tun ranar laraba Rukayya ta wanke mata kai bayan tasa mata fiya-fiya kwarkwatar sun mutu sannan tayi mata zanan Hausa shuku, kai idan kaga kan bazakayi tunani na jiya bane sabida ya kitsu sai dai jan gashi gareta ba bak'i ba. Uniform d'inta kuma ranar alhamis tasa zare da allura ta d'inke so gabaki d'aya inda ya yage ta kuma wanke su duk da sun riga sun kod'e kuma bata da wasu ba kud'in yin sabo ta goge fason k'afarta k'afar tayi kyau duk kuwa da be fitaba gaba d'aya.
Gidan innatuwa me kunshi taje tasiyo lallen goma da talatin din da rukayya tabata,da kanta rukayyan ta yarfa mata jan lallen ta rufe mata fason kafarnan,a ranar da yamma indo tatafi kasuwar dakali wajen idi shoe shiner hannuwanta rike da wasu jemammun takalma kambos duksun fatattake,
“Idi xaka iya gyara wannan takalman”
“Mugansu”cewar idi
“Gasu kambas(kambos) ne idi kaga insipehen(inspection)malamin mu xeyi ranar juma’ar nan kuma bakaga kyautar dayake be nikuma so nake naci shadda ma yasin”
“Bari na gwada nagani xasu gyaru mana sede xaki biya kudi dayawa”
“Kai idi nawa?!”
“Nera hansin”
Rantsuwa Indo ta dinga kwasowa tana kalallame idi da kalamai tana faman xabga masa roko ta karkare da,
“Dan manzon salati idi kayi hak’uri ka temakamin nice fa indo..Indo Malam hamxa ta makarantar tsefawa nan nan kusa dakai.”
Cikeda isar nacin da take masa idi ya wafci takalman yashiga gyara su,yadau lokaci yana dinkecan nane can da gum sannan yai polish d’insa se kyalli yake Kai kace bashi bane sannan ya mikawa Indo ,cikin murna ta karba harda lashe kasan takalmin
“Ta kwarankwatsa ya fita kuma,lalle aiki seme hi,Sannu idi yasin kaci abaka hinkafa da miyar ja me nama”
“Allah ko Indo?”
“Yasin idi”
Cikin sake gyara kananun kayan da sukai yawa ajikinsa Wai shi gaye yace,
“Toh Indo nikuwa ina lami?(kawar Indo)”
“Oh lami tana nan,oho de bansan mata bama kasan makarantar gangare take tunda mijin kanwar babar su ixama chayamen(chairman)”
Kada Kai idi yai yana murmushi,cikin tsokana Indo tace,
“Wai haryanxu kana ciki ne?!”
“Eh mana Inason lami wallahi kawaide bata sona ne tafison shehulle”
Cikin karkad'a kugu had'e da rausaya idanuwa INdo tace,
“To ai kaine idi,dole lami tafison shehulle kullum fa tanada daurin tsire da leman roba na yangayu Kai kwa se mammakon bala'i”
“Ba haka bane Indo amma xan gyara..”
Da haka sukai sallama da ita tana tafe tana jujjuya takalmanta ranar kuwa barkakkiyar safar da tayi shekaru batako kallansu hasalima kama tukunya ake dasu ta dinga durxa tana wankesu ruwa uku tai musu ,Kai kowa mamakin Indo yake har inna tafara sanyata a sujjada idan tai sallah don gani take aljanun tsafta ne suka shafeta kwanan nan..
***
Rana bata Karya sedai uwar d'iya taji kunya yau take juma’a tashin Indo uku kafin asubah inna tana korata waita xata safiya tai,asubar fari kuwa ta mike tai bandaki ranar de atakaice baccin kirki Indo batai ba.
Sega Indo tai wanka abinda yabawa kowa mamaki agidan nasu sede basu da man shafawa sai dai manshanu ko na girki shi kuma bashi garesu ba dan haka tana saka kayan makaranta ta fita zuwa gidan Rukayya lokacin mijinta na nan INdo ta kwankwasa musu k'ofar d'aki tare DA cewa,
"Rukayya kina ciki kuwa? Zuwa nayi ki aramin kayan kwalliyarki inyi zani makaranta.." Ta k'arasa fad'a tana me shiga cikin d'akin sukayi kicib'is da ita, "Au ashe kinji ni."
"Eh INdo bari na d'akko miki su nan tsakar gida."
Cikin d'akin ta koma ta d'ebu mata su lokacin mijin ta shima yazo zai fita INdo ta ganshi ta dashare baki tace
"Au kaima d'anlami ashe kana ciki yanzu ka tashi a bacci ne?" Ya tsaya kusa da ita yana kallonta yace "Eh INdo yau kuma za'a makarantar kenan."
Tace "Eh gahima kuwa." Rukayya ce ta fito ta mik'awa INdo kayan kwalliyar shi kuma d'anlami yasa kai ya fita. Tana zaune tana yi Rukayya na kwarzanta ta wai tayi kyau ai yau sai dai in bak'in cikin ne zai hana malam sadeeq ya bata kyauta. Zuciyar INdo ta kuma shiga cikin wani irin yanayi najin dad'i, ita dakanta tanajin sauyi a cikin jikinta sabida iskar da take shigarta ta k'ofofin gashin jikinta. Da sauri ta kammala kwalliyar
Tashi Rukayya tayi bayan ta kwashi kayan kwalliyar ta shiga cikin d'aki ta mayar dasu ta mik'awa INdo turare sai faman dariya take sabida yadda takejin ta wani daban yau. Tafeshe rigarta Rukayya tayi saurin cewa.
"Haba INdo ya kike kuma 6ata kayan makaranta salan yaga jirwaye ya hanaki...? A jikin hammatarki zaki fesa.!" INdo tayi yadda ta gaya mata sannan tace.
"Sai nazo kawo miki kayan da zan samo Rukayya..."
Tayi dariya itama cikin jin dad'i da fatan alheri tace "Toh INdo Allah ya baki sa'a sai kun dawo."
Gida ta shiga yau ko karin kumallo bata tsaya yi ba sabida kar bakin yayi daud'a tayiwa Inna sallama tabar gidan yau harda littattafanta da suka yayyage tazuba a leda ta tafi burinta yau ta samu atamfar ko ya bata wani abun da zata dinga alfahari dashi, yau sai da ta riga kowa a makarantar zuwa principal ne kawai da masu kula da makarantar bata riga ba taje ta zauna kusa da farkon aji da niyar ko masu gurin sunje bazata tashi ba tafi son a fara ta kanta yau.
***
Lokacin 8:15am yana gaf da shiga ajin aka yo mai waya hakan yasa shi tsayawa dan ya amsa. Dubawa yayi sai yaga ansa my twinnie yayi murmushi sannan ya d'anyi baya da ajin sabida hayaniyar da suke yi ya d'aga tare da karawa a kunnansa.
"Twinnie me ya how far..?!"
Sadeeq ya fad'a yana d'an sosa k'eyarsa da k'asan biro, daga can 6angaran Abubakar yace.
"Surprise..!"
Sadeeq najin haka yayi murmushi tare da cewa.
"Kana gate ko..?!"
Abubakar yayi dariya yace "yah kana ina yanzu.?”Sadeeq ya kalli ajin sannan yace "twinnie me kashigo ciki ina aji uku jss 3c nima yanzu zan k'arasa shiga ciki."
"Okay..."
Suka kashe wayar Sadeeq ya shiga hannunsa d'auke da ledar viva yana shiga 'yan aji suka tashi ana gaida shi da k'arfin tsiya dan yanzu ba k'aramin so suke mishi ba, ya ajiye akan teburin sa ba tare daya kallesu ba yace su zauna nan ma suka ce "thank you Sir..." Shima da k'arfin su kamar kuma had'in baki.
Waje ya lek'a ya gani ko ya k'araso yana hangosa ya d'aga mai hannu suka yiwa juna murmushi tundaga nesa har Abubakar ya k'araso suka yi musabuha sannan suka shiga cikin ajin, nan ma yaran suka sake tashi suka gaida d'ayan daya shigo amma kotakan su bebiba ya tsaya suna magana sai Sadeeq d'inne yayi musu alamar su zauna da hannu tunda shi ba yadda zaiyi d'alibansa ne dole ya kulasu.
"Twinnie ga abin zama ka zauna."
Avubakar ya kalli kujerar sannan ya juya yana kallon 'yan ajin sai ya gansu fes-fes dasu hakan ya bashi mamaki ya kuma rasa wadda zai kira ta goge mai kujerar dan bazai zauna a haka ba. Shi duk a tunaninsa ba wad'anda ya sani bane ya kalli Sadeeq yana shafa sajen fuskarsa yace.
"Twinnie congrats an sake ma class."
Sadeeq yayi murmushi tare da juyawa ya kalli 'yan ajin sannan ya kalli Abubakar yace, "twinnie sune dai wad'anda ka sani kawai canjin yanayi aka samu."
"Woww good of you."
"Thanks twinnie."
Abubakar ya kalli 'yan matan ajin kawai ya nunu Maryam Ali ya yafitota, jikinta na rawa ta mik'e ta k'arasa inda yake tace.
"Malam gani."
Mtwww “wai ban hanaku ce min malam vane? Ko kunga nayi kama da teacher?"
"Allah baka hakuri."
Maryam ta fad'a bakinta na rawa, yayi banza da ita sannan yace "daga yau kar wanda ya kuma ce min malam ko sir suna na doctor Abubakar Salman Harun, karna kuma zuwa ajin nan wata tace min malam ko wani sir ku kirani da doctor Abbakar or doctor ASH."
Ajin yayi tsit babu meyin motsi yaja tsaki tare da kallonta yace "Oya tashi ki goge min kujerar da zan zauna."
Da sauri Maryam ta zaro ido jin abinda yace sabida ta tuno sanda yasa INdo ta goge mai da hijjab d'inta, ya zata yi gashi ba'a duba taba yau ta shiga uku zai ja mata.
"Ko baza kiyi vane.?!"
Ya tambayeta ganin bataje tayi abinda ya sanyata ba, hawaye suka zobu mata shi kuma Sadeeq yak'i yin magana jiki a sanyaye tana kuka taje tasa hijabinta ta goge mai tasss sannan ta koma gurin zamanta sai kuka takeyi shi kuma yaje ya zauna tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana d'an kad'asu. Sadeeq ya kalli Abubakar yace.
"Bari sai na fara yi musu inspection."
Abubakar ya kallesa yace "na ina kuma..?!" Sadeeq ya d'auki rular yana cewa "na jikinsu har kyauta nake basu that's why kazo ka gansu neat." Abubakar ya ta6e baki sannan Sadeeq ya tafi farawa wanda har lokacin bemasan INdo na ajin ba, Abubakar yace "okey twinnie duk wani wanda beyi maka wani abunba ka turosa nan gurin." Ya fad'a yana d'aukar wayarsa dan kiran Qibd'iyya yace mata ya sauka lafiya kuma yaji sassanyar muryarta mai sanyi.
'Yan aji najin abinda ya fad'a kowa ya fara duba abinda beyi ba dai-dai lokacin da Sadeeq ya k'arasa gurin bencin da yake farawa kuma INdo ce a farko dan haka kafin ta gama duba abinda bata yiba har ya k'arasa.
"Ohh my God..! Wacece wannan kamar Aisha?"
INdo ta dashare baki kamar gonar auduga yayin da 'yan aji suka bita da kallo shi kuma malam Sadeeq ya saki wani tattausan murmushi ganinta yau tsab-tsab da ita sai dai makeup d'in da tayi ne duk ya cuceta dan duk ta cika fuskar da d'ige-d'igen baki da janbaki sai dai yaji dad'i dayaga tayi wanki yace.
"Toh muga bakin." Ta bud'e mai hak'oran nata ya gani ya d'aga kai sun d'an fi na baya ya kuma cewa "muga kanki." Nan ma ta bud'e da saurinta ya kalla gashin nan yayi d'as da kitso ya kuma kad'a kai domin tayi k'ok'ari sosai lallai hakan yana nuna masa cewar ba k'aramin son a bata kyauta takeyi ba yayi murmushi yana wani sak'e-sak'e cikin ransa kafin yace.
"Toh kinyi komai Aisha muga farcanki."
Sai a lokacin ta tuna sam bata yanke ba sai ta 6ata rai idanunta yayi rau-rau zata yi kuka dan tasan rashin yanke farcen ba k'aramin asara zai janyo mata ba Sadeeq ya kuma cewa "muga farcan ki Aisha."
A hankali ta mik'a mai hakan yasa shi saurin kallanta domin beso ta fad'i tausayinta ya kamashi ba yadda zaiyi dole yace.
"Aisha baki yanke farce ba, tashi kije wajan doctor Abbakar..."
Tana hawaye tace “Amma malam hikadai nefa banyi ba kuma wabillahillaxi mancewa nayi dan Allah kayi hakuri kabani atamfar.."
"Tashi ki fito Aisha."
Tashi tayi tana kuka domin ba k'aramin haushi takeji ba ta k'arasa wajan Abubakar wanda waya take kare a kunnansa shi kuma Sadeeq ya cigaba dayi idan yaga wanda beyi wani abunba sai ya turasa wajan Abubakar, shi kuma ganin yara sun taru a gabansa yasa shi cewa Qibd'iyya.
"M love bari na barki zan..." Ya kasa k'arasawa sabida ido hud'u da sukayi da INdo zuciyarsa tayi wani rass gashi idanta yayi jah sabida kuka sai kawai yaji zuciyar sa nayi mai wani irin zillo ya kashe wayar bema sani ba sannan ya mik'a hannunsa ya janyo na INdo ita kuma ta fara dak'irewa a tunaninta dukanta zaiyi ta fara ihu tana bashi hakuri shi kuma ya damk'e hannun nata sabida yadda yaji shi cikin wani irin mood akanta....
Love u m Fan's👍
*HAJJA CE*👈
[7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥
♥♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.
_Shafin yau naki ne tawan daughter'n My Nana Hafsatu Xoxo da Nana Hafsatu Rano wato *BILLY S FARI* wannan mata Allah yayi miki abinda kikeso duniya da lahira, ya azurtaki da 'ya'ya na gari masu albarka. Hajja ce tana sonki kamar yadda take son H², Allah yabar k'auna da soyayya.😍_
Page *7*
Da gudu suke bin ta suna cewa ta basu bokitan su na talla amma tamkar iska gudu kawai take har se da ta shige cikin gida sannan ta dire bokitan ta zauna tana maida numfashin wahala. Inna ta kalleta tana jimamin hali irin na 'yarta ta ganin babu ranar da zata fito ta fad'i INdo bata yi wani abun na zagi ba, wannan dalilin ne yasa tayi niyar zuwa gidan me salati ko zata samu wani temakon da za'ayi mata akan fitinar ta amma baban su ya hana yace shi 'yarsa lafiyar ta sumul.
Kad'a kai kawai Inna tayi ta cigaba da mark'ad'an ta akan irin dutsen nan, INdo na gefe su kuma su Idi sai faman kumbura suke ta bud'i bokitan Ubale me d'auke da awara ta d'ibi guda biyu sannan ta tura mai bokitin nasa, ta janyo na idi shima ta d'ibi wainar rogo ta mik'a mai sauran tana cemusu.
"Naci lada kuma wabillahillazi kuka sake ganina kuka fad'i wata kalmar sai na jamuku asara kuce ba suna na A’isha ba." Suka d'auki bukitan su sukayi waje kowanne da irin kalar wulak'ancin da zai mata a zuciyarsa, Nafeesa k'anwarta ta shigo gidan tana ganinta tayi saurin 6oye kwanon awarar dan karta d'aukar mata.
"INdo rowar jaraba." Cewar Nafeesa tare da k'arasawa wajan INdon ta zauna harda su tankwasa k'afafuwa ta mik'a mata hannu alamar ta sammata.
Mtww "idan ni marowa ciya ce dalla malama kekuma mecece? Ungoni ki matsa ki bani guri." Ta juya tana kallon Inna tace "Inna ga awara idan zaki ci."
Inna ta k'araso gurin tana cewa "Ni wallahi 'yar nan bana son wannan fitinar taki, inda Allah ya temaka ma kun koma makaranta zaku shiga ajin gaba ni banaci na k'oshi da abin fitina." INdo ta fara sosa kai tana kanne ido d'aya sabida jin zafin yajin bakinta tace "Inna wallahi bazan koma makarantar nan ba wata zaku sakemin, wai d'azu harni malam Sadeeq zai cewa tinkiya! Wallahi toh bazan koma ba yaje yacinye makaranta."
"Yanzu kin dena zuwa 'yar nan? Toh wacce kike son a mayar dake ke ba tsayayyan saurayi ba bare ayi miki aure yau na shigesu ni Maryama."
"Inna wallahi bazan koma tsefawa ba na fasa zama likitar dama temako zan dinga yi toh yanzu kuma nafasa suje sunemi wata." Inna ta kad'a kai babu abinda zata iya cewa akai koda baban su ya shigo ma bata gaya maiba bare su d'auki wani mataki haka suka barta kullum bata nan unguwar bata waccen har aka d'iba sati biyu ko hanyar makarantar bata bibare asakaran zata shiga, tsab Sadeeq ya manta da ita domin ya toshe duk wata hanya daya san suna had'uwa.
**
A 6angaran Abubakar kuwa yana matuk'ar son Mareeya har hakan ya fito fili ragowar nurses suka fuskanta, wasu suka hakura dashi yayinda wasu kuma suka d'auki tsana da takura suka d'orasa akan ita Mareeyan suna ganin itace tayi wani kulla-kullan har ya karkata wajanta ya barsu. Sosai suka shaku Abubakar har ya had'a su da Sadeeq awaya suna gaisawa hakan ya sake narkar da sonta a cikin zuciyar Abubakar d'in.
**
Wata ranar juma'a ne Sadeeq dayaje makaranta dama duk juma'a yakewa 'yan ajinsa duban tsabta, yana duba farcensu, hak'oransu, mata ya duba kitso maza kuma aski da kuma uniform duk wanda yafi kowa tsafta zai bashi kyauta. Ashe INdo ta samu labari yau yana cikin dudduba su sai gata ta shigo askwane cikin ajin malam Sadeeq ya kalleta cikin tsananin mamaki kamar aljana uniform d'in nata sharkaf da ruwa a haka tasa su gashi tayi wata mahaukaciyar kwalliya kamar wata ifirituwa ta fara tafiya zuwa bencin su Uwani halilu suka matsa mata har ta kusa kai duwawunta k'asa yayi saurin dakatar da ita ta hanyar yi mata wata razananniyar tsawa ya had'a da cewa.
"Ke meya kawoki wannan ajin? Wacece ke haka? Daga wane sahun aka zakuloki..?!"
INdo ta kalli kan teburinsa taga kayan kyaututtukan da zai bayar sai ta dashare mai jawur d'in hak'oranta domin tunda ta siyi brush da makilin d'in nan bata ta6a yi ba zuwa tayi ta zubesu a gida toh dama ba'a sababa ta k'arasa zama tukunna tace masa.
"Haba malam Sadeeq nicefa INdo malam Hamza."
"Will you shut up...Nonsence, zoki fitar min daga aji wawuya waya kawoki jss 3? Keda har yanzu kina jss 1 shine yau zaki wani shigo min zoki fita kafin na lahira ya fikijin dad'i." Yayi maganar yana nuna mata k'ofar data shigo ransa a matuk'ar had'e, sai ta fara kallon 'yan ajin d'aya bayan d'aya tare da mutsittsike idanuwa taga dai still sune dai 'yan ajin nasu na da amma ya za'ayi yace wai nan ba ajinta bane dan shi munafukine, tokuwa babu inda zata dan nan gwamnati ta tsaga mata dan haka tayi kicin-kicin da fuska wai taga ko zai kuma cewa tafita.
"Ke Aisha ba magana nake yi miki ba?"
Ya fad'a yana k'arasowa bencin da take, INdo tayi saurin mik'ewa tana kallonsa tace "Yo toh malam duk fa k'awayena ne kuma 'yan ajinmu ne ya zakace na fita ina zanje ni."
Yace "Tallah, koba ita kika fiso ba? And bakin ce bazaki sake suwa tsefawa fa yau kuma wane munafuncin ne ya shigo dake da wasu jik'akk'un kayanki kila ma fitsarin kwance kika yi, oya zoki out kina 6ata mana lokaci."
Duk cikin maganarsa babu wacce take k'ona mata rai irin yace tazo ta fita, kuma kallon kayan kyautar tayi kawai sai ta rushe da kuka tana fad'in "Kai malam.. Kai malam, sai da kaga nazo na kusa cinye kyautar nan shine zaka ce natafi ba ajina bane. Toh malam wane ajin zan koma kuma?."
Tsananin mamaki ya cika Sadeeq ganin tana kuka, tunda yake be ta6a ganin hawayenta ba sai yanzu haka kurum kuma sai yaji duk ya tsani kansa domin yasan ita d'in mahaukaciya ce ya kamata ya dinga bata kulawa ta wani 6angaran ko Allah zaisa ta gyara wani abun hakan yasa shi juyawa yanaci gaba da duba 'yan ajin har ya zabo mutum shidan da zai bawa kyautar . Yana zuwa kan INdo tundaga kan uniform ya fara rankwashin ta domin haka yake yiwa duk wanda yake da gyara, INdo tayi saurin dafe gurin tana furta.
"Kai...kakai...kakai..! Malam da zafifa." Yace "ha..bakin muga teeth naki." INdo da taji yace ha bakin yasa ta bud'e mai tamkar zata cinyeshi yayi saurin matsawa sabida wani hamami dayake tasowa daga ciki yana toshe hanci yace.
"Such a stupid hak'oranki zaki nuna min bawai cewa nayi ki hangame min ba."
Hannu tasa ta toshe bakin tunawa da tayi lokacin da sukace bakinta yayi yalo ya kalleta yace.
"Bazaki bud'e ba saina mareki..?!"
Ta d'aga maikai bakinta a toshe da hannunta tace "Malam gara ka marenin da na bud'e ma ballahillazi." Mtwww yaja tsaki dan yasan babu abinda za'a za6a a gurinta, ya kuma matsawa ta baje hancinta tana shak'ar k'amshin turaren jikinsa yace "muga farcenki." Tana jin haka tayi saurin zame hannunta daga baki ta cukwaikuye hannuwan acikin hijjabi tana zaro mai ido ya kuma kuluwa yace "muga kanki..?!"
A hankali ta bud'e shi ya kalla tare da ta6e baki ya bar gurin, akwai kitso saidai ya tsofa sosai dan ko tsagar ba'a gani gashi gashin nata jah ne kamar gashin akuya sai dai da ka ganshi kasan zaiyi laushi domin irin me yalai-yalai d'in nan ne, ta kalli Uwani halilu tana sosa hanci tace.
"Uwani kin ta6a cin gasar kuwa?!" Uwani ta harareta tare da k'in bata amsa ganin haka yasa tayi mata kallon sama da k'asa tana fad'in "ji banza kina jima ina tambayarki." Malam Sadeeq ya d'akko wani yadi na maza ya mik'awa D'ahiru Miko ya durkusa har k'asa ya kar6a sannan yayi godiya malam Sadeeq yace.
"Ku tafawa D'ahiru miko ya samu wannan kyautar ne saka makon d'inkin uniform d'insa sabo ne, yayi aski sannan baya barin farce zak'o-zak'o gashi yana k'amshi babu wari a jikinsa hak'oransa ma sun fara haske.." Aka fara tafawa raf-raf-raf INdo sai k'arayi take da k'arfi har aka gama yi sau biyar yadda ya koya musu INdo bata denayi ba sai da yace "ke inji..!, ya isa haka baki ji yadda suka had'u suka yi nasu ba ne a tare?" Sai a lokacin ta dena amma fa bakin nan a wangale tamkar ita aka bawa yadin.
Mace kuma Murja Ashiru ce ta samu ya bata fallen atamfa biyu itama aka tafa mata still INdo sai da ta zarce har wani dak'irewa tayi sai da Atika bawa ta bige mata hannun sannan ta denayi yace musu "Yau Atika bawa tafi ko wace mace tayi kitso harda kunshi, kayan makarantar ta harda guga babu farce ta yanke itama tayi brush." Aka sake tafawa sam INdo bata iya ba da kowa zai denayi amma ita sai ta k'ara. har ya kammala bama ragowar suka koma suka zauna yayi musu nasiha akan tsabta sannan ya kwashi littattafansa zai fita INdo tayi saurin cewa.
"Malam...!" Ya tsaya cak ba tare daya juya ba tace, "nima wata juma'ar zanyi duka amma ni hadda (shadda) nakeso ruwan bula kaji ko...?!"
Juyawa yayi ya kalleta sannan yace "Toh kiyo amma bake zaki gaya min abinda kike so ba sai abinda nayi niyar bayarwa kinjiko..?!" Tayi shiru bata amsa mai ba yayi tafiyarsa ta zauna tana cewa "kajishi fa, salan kawai a baka abinda bakaso mtww." Babu wanda ya kulata ta mik'e ta koma wajan Atika ta k'arbi atamfar tana gani ji take inama ta tace har ta hango irin d'inkin da zatayi dan taga wani style a jikin Rukayya amarya. Duk wanda aka bawa kyauta sai da taje ta ansa ta gani har ta fara Allah-Allah wata juma'ar tazo itama taci za6e....
*HAJJA CE*👈
[7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥
♥♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.
Page *9*
Still hannunsa na rik'e da nata ya rik'e sai kallon fuskarta yake dan ba k'aramin kyau kwalliyarta tata tayi mai ba, INdo kuma sai k'ok'arin ture mai hannunsa take tana hawaye murya k'asa-k'asa kamar munafiki yake mata magana yace.
“What's your name make up artist..?!”
INdo tayi shiru sai tasa ka hijjab d'inta ta sharo hawayen fuskarta duk bak'in kwallin da tayi kwalliya ya wanke hijjabin daga gaba Abubakar ya kalleta sosai shi har lokacin begano taba domin be ta6a ganinta tsab-tsab kamar yau ba ya kuma cewa.
"Baby ya sunanki ne.?!"
Sai a lokacin INdo ta fahimta ya kalleta ya kuma cewa,
"kinga kin goge kwalliyan naki da kuka ki dena kinji ko? Ya sunanki??"
Ta share majina da bayan hannunta wanda be rik'e ba ai yana gani yayi saurin sakar mata d'ayan hannun ita kuma ta matsa baya tare da cewa cikin kuka.
"INdo malam Hamza." Abubakar ya d'an zaro ido waje kad'an kafin yace.
"Zonan gurin." Ya nuna mata inda yake son ta tsaya da k'afarsa, a hankali taje gurin ta tsaya sai dai idanunta nakan tebur din da malam Sadeeq ya ajiye kayan kyautar da zai bada. Tsaye tayi mai k'ik'am sam hankalinta baya kansa shi kuma ya kalleta yana murmushi yace.
"Woww sunan Mama na gareki, toh amma ba zaki tsugunna ba kika min k'erere..?!" Da sauri ta tsuguna still fuskarta na wajan kayan, ganin bashi take kallo ba yasa shi maida kujerar sa saitin da idanta yake gurin tayi saurin kallansa ya tsuke fuska yace. "Menene baki yi ba aka fito dake?!" Ta cukwai-kuye hannunta tun kafin ta bashi ansa dan tasan mugune a hankali tana turo baki daya sha bakin kwalli a le6an tace.
"Wallahi nayi komai, kawai farce na manta ban cire ba shine malam Sadeeq yace na fito kuma wallahi malam..." Ya zabga mata harara tayi saurin toshe bakinta da hijjab kafin taga ya dena tace. "Kayi hakuri dakta Habubakar mantawa na keyi kace ba sunanka malam ba, amma wallahi nayi niyyar yankewa niko dan naciyo atamfa amma duk saina manta hef (shaf).."
"Ohh muga farcan naki.." Ta fito dashi yasha lalle a yatsun ta nuna mai, hannu yasa ya janyo nata yana kallah murya sanyaye INdo tace mai. "Dan Allah Dacta Habubakar kace ya bani ni yanzu ma zan iya cire farcen, dan iyayanka kace ya bani dan Allah kaji..?!"
Sadeeq ne yazo gurin ya kalli d'an uwan nasa rik'e da hannun INdo hakan ya bashi matuk'ar mamaki da al’ajabi cikin sauri Sadeeq ya zare hannun INdon daga na Abubakar cikin harshen turanci Sadeeq yake mai magana cewa.
"Twinnie why na?am i day dreaming or are you really the one holding a village girl hands,and if you have forgotten about it then I haven’t ,this villagers are cruel,I don’t want them to think something else in their mind ..This is so not you”
Cikin ko’a jikinsa abubkhr ya daga kafada sannan yafara magana,
"Habba twinnie sunan Momcy gareta fa shi yasa, gashi kuma tayi kwalliya irin wadda nake so that's y kaga ina iya rik'e hand's na ta."
Mtwww "inajin baka ganeta bane shi yasa kake sakar mata fuska, toh bari na tuna maka kowa cece INdo malam Hamza, wannan me satar amsar ce me cizon maza nasan yanzu ka harbo ta."
"Really my twinnie? Abubakar ya fad'a yana sake maida kallonsa fuskar INdo, kwakwalwarsa kuma tana sake hasaso mai lakacin daya kamata ta duk'ufa tana kwafar note dan sam koda ta kwafo ma bagurin da aka tambaya bane, ya kuma kallon Sadeeq cikin mamaki yace
"Gaskiya m twinnie kayi k'ok'ari indai haka ne. Ashe k'azan tace duk ta maidasu mahaukata Gaskia I'm sure nan gaba za'a sha mamaki indai suka d'ore da haka za'aji dad'i sosai."
K'afarsa yaji ana jijijigawa hakan yasa shi saurin kallon k'afar kawai yaga INdo ce take mai alamar magiya tana nuna mai ya samo mata kyauta kota meye Sadeeq dake fito da kayan zai bawa wad'anda suka ci ya kalli Abubakar dake kallon INdo kawai yaja tsaki sabida takaici. INdo kam sai nunawa Abubakar malam Sadeeq takeyi alamar be zabo mataba zasu k'are yayi dariya cikin zuciyar sa ya kalli sauran masu kuskuran yace.
"Kuzo nan muyi photo daku." Suna jin haka suka ruga bayansa suka jeru amma sam INdo batayi gigin zuwa ba hankalin ta yana wajan malam Saseeq dayake ta rabo zuciyar ta tamkar ta fito tsabar fargaban karsu k'are.
"Humaira zo mana ayi dake." Abubakar ya fad'a yana kallon Indo , ita kuwa bata masan da ita yake ba tana ji tana gani har malam Sadeeq ya kammala bada kyautukan taji wata muguwar tsanarsa tundaga k'asan zuciyar ta ya game da ilahirin jinin jikinta tayi ta zagba mai harara bemasan tanayi ba yana can yana sake yiwa wad'anda sukaci kyautar nasiha da kuma muhimmancin tsabta da Ilimi.
“Kuje kuma ku zauna kowa yaje gida yayi karatu ranar Monday zanyi muku test duk wanda ya fad'i ni nasan irin hukuncin dazan d'auka akansa kunajina ko?!"
Malam Sadeeq ya fad'a bayan yaga yau twinnie d'in nasa da mutunci ya shigo, duk 'yan ajin suka ce "OK uncle." Dayake yana k'ara d'an wayar dasu, amma INdo data tashi sai da ta d'auki ledar littafinta ta faki idonsu duk da cewar Abubakar nason yayi mata photo da kwalliyar ta yana can yana tambayar Sadeeq mezai iya bata koda ba babba bane ba sukaji tana cewa.
"Baza'ayo karatun tess (test) d'in ba, kai idanma kun sake ganina a makarantar nan dan Allah ku soya ni. Wallahi malam Sadeeq yayi karya kuma ance babba me karya d'an wuta ne gobe k'iyama yana kusa da fir'auna, Allah ya sakamin sabida na kashe kud'ina garin yin kunhi da gyara kambas d'ina sai Allah ya saka min. Yo dan baka bani atamfar ba seme, nima Inna ta zata sai min ai sallah ta kusa."
Tana gama fad'a ta murgud'a baki ta juya da gudu zata arce taji an rik'eta gam cikin tsananin tsoro da tashin hankali tayi k'ok'arin juyawa taga waye sai taga malama Murja ce ta cafketa tare da tura ta cikin ajin, tana zuwa ne da yake period d'inta ya shiga sai taji irin rashin kunyar da takewa malamin hakan yasa tayi shiru sai data kai k'arshe zata gudu tayi saurin kamata.
Tsananin mamakinta suka kama Abubakar, sai yanzu ya kuma tabbatar da cewa itace ya tashi a fusace yayi kanta jin yadda take gayawa twinnie d'in nasa magana. Sadeeq ne yayi saurin taresa yana kad'a mai kai alamar karya doketa, yana wani irin numfashi ya ture hannun Sadeeq d'in daga kafad'arsa yana cewa.
"Ka rabu dani Sadeeq bakaji yadda take had'aka zama da fir'auna ba, barni naci uban shegiyar yarinyar nan da har ina tausaya mata ashe batada mutunci har yanzu."
"A'a twinnie barni da ita, kayi hakuri ka kwantar da ranka. Malama na gode da gudun mawarki, ke kuma zonan..." Sadeeq ya fad'a yana damk'o hannunta Abubakar kuwa jiyake tamkar ya ham6areta sabida 6acin rai. Fita yayi da ita sai ihu take musu har suka k'arasa cikin staff room ya kalleta yace.
"Kama kunnanki."
"Dan Allah malam kuyi hakuri."
Babu wanda ya kulata sai dai duk malam cikin staff room d'in saida suka bada shedar rashin kunyar INdo, ganin babu mebada hakuri ne yasa ta sunkuya ta zura hannunta tana nishi tana cewa "malam wallahi hannuna baya kaiwa abakacin sa kace nayi nibdom (kneel down) kaji."
Jiyosu ma tayi suna hira babu wanda ya kulata dan yau takaisu bango, tun tana magiya har tayi shiru. Ta dad'e tana kamun kunnen kawai suka ganta ta fad'i k'asa Abubakar dake kusa da gefenta besan lokacin daya kai hannu zai tarota ba amma saida tayi k'asan, ashe baccine ya kamata, kuma duk da fad'uwar da tayi hakan besa ta tashi ba saima zarcewa da tayi tafara sauke munshari.
"Twinnie mu wuce tunda ka gama."
Beh jira cewar sa baya k'arasa inda INdo take kwance sai uban munshari takeyi tamkar wata babbar mata a hankali ya dinga k'iran sunanta amma inah ko motsawa batayi ba, hannu yasa dai-dai kafad'arta yana jijjigata nan ma still bata motsaba. Ganin yadda yake bin ta a hankaline yasa Sadeeq mik'ewa ya d'auki dorina yana zuwa ya tsula mata a baya. A razane ta mik'e ta rarumi Abubakar dake tsaye kusa da ita tana cewa.
"Wayo Allah atamfata ce."
Sak'e tsula mata yayi tayi saurin sakin Abubakar tayi k'ark'ashin tebur d'in malam yahaya tana kuka tana sosa gurin cikin kuka take bashi hakuri yayin da shi kuma Abubakar ya fita daga cikin staff room d'in. Sai da wasu malam suka bawa malam Sadeeq hakuri sannan aka ce taje ta tsugunna ta bashi hakuri tayi sannan ya hakuri yace kuma duk sanda ta kuma yin fashin zuwa makaranta sai yasa ankamota yayi mata duka tace toh.
Fitowa yayi amma bega Abubakar d'inba har ya fita gate babu bare alamun motarsa, sosai Sadeeq yayi mamaki sai ya nufi gidan shima amma abin mamaki bako motarsa a gurin hakan yasa shi kiran wayarsa aka sanar mai cewar a rufe take, mamaki ya kuma sark'e Sadeeq. Yana tsaye a gurin har su INdo suka wuce suna gulmarsa be kulasu ba.
Shi kuwa Abubakar yana fita motarsa ya hau yakama hanyar gida, haka kawai yau yaji baya son jin kukan INdo zuciyarsa har zafi take mai duk kuwa da cewar yasan itace batada kunya amma ya rasa dalili, tunda ya taho tunaninta yakeyi yayi-yayi ya halasto qibd'iya ya kasa sai dai INdo da kamanninta ya buga sitiyarin motarsa yafi sau ashirin harya k'arasa gida. Yana shiga yaji Maman su na cewa.
"Kajishi can najiyo tsayuwar motarsa da alama ya dawo. Toh shikenan 'biyu kyautar Allah kaima Allah yayi maka albarka." Sai da ya bari ta kashe dan yasan da Sadeeq takeyin wayar sannan ya shiga cikin gidan nasu bakinsa d'auke da sallama....
_Kuyi hakuri da wannan, kunsan bawa duk yadda yaso yayi abu idan Allah bebashi dama DA iko ba toh babu abinda zai iya yi a rayuwarsa. Nagode luv you all._ Gaisuwa da fatan alkairi zuwa ga aunty Sdy jegal, Ina miki fatan alkairi a duk inda kike, Allah ya raya mana baby boy d'inmu cikin addinin musulinci.😘
*HAJJA CE*👈
[7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥
♥♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.
_Shafin yau na kune 'yan grp d'ina wato *HAJJA CE NOVELS GRP* da *ZAURAN BIEBIE ISAH* tare da *🅿HERTY NOVELS* da *MUSHA KARATU N YBK2* gara nayi muku jam'u domin idan na tsaya lissafoku sai kunji haushina kunce dama typing nayi muku da wannan lissafin. Hak'ik'i ina jin dad'in yadda kuke tare dani, comments d'inku nasani dariya da kuma nishad'i uwa uba kwarin gwaiwa. Nagode sosai #ana tare da INdo malama Hamza._🤝😍
Page *10*
Amsawa Maman tayi tana had'a musu zo6o. k'arasawa yayi ya zauna akan kujera 'yar tsugunno sai faman shafa sajen fuskarsa yakeyi. Umma Dijeh ce ta fito daga parlor kasan cewar muhad'u a parlo ne ta kallesa tana murmushi cikin wasa tace mai.
"Likita bokan turai, daga sallar juma'a kuma sai ina? Ko yauma za'a lek'a mak'ota ne..?!"
Wayarsa ya zaro zai kunna domin tunda ya baro makarantar ya kasheta sabida yasan dole Sadeeq ya nemeshi, shikuwa beshirya abinda zai gaya masa ba. Kallan Umma Dije yayi sannan yayi murmushi yace.
"Haba Umma jiya fa naje, kuma yauma bata nan." Dariya suka yi itada Maman sannan ya tashi ya fito yashiga d'akinsu, kayan jikinsa ya rage ya zauna daga shi sai vest da boxer shorts sannan ya kuma d'aukar wayarsa dai-dai lokacin kuma Sadeeq ya kuma kiransa. Babu yadda zaiyi dole ya d'aga kodan ya kare kansa daga wajan abokin haihuwar tasa, cikin basarwa ya kara a jikin kunnansa tare da fad'in, "My twinnie sai kaga na taho ko?!" Sadeeq dake zaune a k'ofar gida ya ta6e baki sannan yace.
"Ba gani nayi ba nemanka nayi na rasa wanda kuma ni bansan dalilin yin hakan ba, twinnie kasan irin tashin hankalin daka sakani? Da police station zanje nakai report sai kuma muka yi waya da Mother take cemin gakanan ka k'arasa why did you do this to me ah?!"
Duk sai Abubakar d'in yaji babu dad'i ganin yadda duk ya tayarwa da d'an uwan nasa hankali, da kyar ya samu mafitar da zai wanke kansa ya numfasa tare da cewa.
"Kayi hakuri nima saida na taho naga rashin dacewar hakan tunda bamuyi sallama ba, abinda ya faru shine ina fitowa Dr Inuwa yake sanar dani ana nemana a cikin asibitin da gaggawa shi yasa duk na rud'e na kashe wayana dan karsu dunga damuna sorry twinnie kaji kayi min afuwa.."
"Okk bakomai yanzu tunda naji kana gida sai anjima."
Kamar ya tambayesa INdo sai kuma yayi shiru suka ajiye wayar shi kansa besan yadda zai fad'i abinda yakeji ba har mamaki yake yi ya ajiye wayar yashiga toilet. Wanka yayi lokacin har an kawo mai abincinsa an ajiye amma ko kallansa beyi ba sai wayar ya sake d'auka ya shiga gallery, hotunan dayayi mata ba tare da kowa ya sani ba. Yana gani yana duba na e so yake yagano meke damunsa amma inah..ya kasa tantancewa sai faman k'aryata zuciyarsa yake yi da abinda take shaida mai.
INdo kuwa tana zuwa gida ta fara cire kayan jikinta tana killarwa ta sanya wata kod'add'iyar shadda doguwar riga wanda ta d'age mata sannan ta dawo tsakar gida ta zauna tana kallon kunshinta. Wani irin tsanar malam Sadeeq da Abubakar suka sake mamaye cikin zuciyarta ta cewa Inna.
"Inna wanki zanyi gobe na tafi gidan yakumbo Tsahare, wallahi billahillazi bazan sake zuwa makaranta ba saye zan yi tafiya ta naga ta tsiyarsu mugaye."
Cikin dafe k'irji Inna tace "ke 'yarnan saye kuma? Kiyiwa Allah da ma'aiki kiyi shiru da maganar tafiyar nan kinsan dai babanku baya son zuwanku garin nan tun abinda ya faru tsakaninsa da jummala."
"Inna wallahi saina tafi, kina jinfa abinda mugun malamin nan yace, wai idan na dena zuwa makaranta saiya saka an d'akkoni toh wallahi barin garin zanyi hena dad'e sannan zan dawo a'he."
Hankalin Inna ya tashi dan tasan idan baban su yaji toh lashakka sai anyi fitina duk da cewar tsaharan k'anwarsa ce amma tun a haihuwar shehu suka samu sa6ani akan naman suna shikenan sukayi baram baram kuwa yace bashi ba d'an wansa sannan yacewa Inna ya haramtawa 'ya'yansa zuwa garin idan sukaje kuma Allah ya isah. Tashi INdo tayi tabar gidan ta shiga gidan Rukayya, tana ganinta ta fara murna tare da cewa.
"Kai INdo shine ko a kawo min kyautar ingani ko?!"
Saida INdo tasamu guri ta zauna sannan tacewa Rukayyan "Yo ai basu bani ba, wai wani ban yanke farce ba ninasan dama malaman nan ba kaunata sukeyi ba kawai dan dai nafi karfin sune bayadda zasu yi dani shegun."
"Kan uba! Yanzu kina nufin babu abinda malam Sadeeq yayi miki?!"
"Sai duka nama dayayi kuma nace Allah ya isa." Nan suka cigaba da hira har INdo na bata labarin tafiyarta saye gobe Rukayya tace.
"Kai INdo sai kuma yauhe zaki dawo?!" INdo na watsa shinkafa da wake tana cewa "babu lokaci idan na tafi henayi aure zan dawo yasin."
"Kai INdo baxaki dawo ba kenan?!"
Rukayya ta kuma tambaya cikin jimami, ita kuwa INdo ko'ajikinta tace "Eh bazan dawo ba he randa malam yadena zuwa garin nan."
"Kai Allah ya wadaran wannan malamin da yaja zaki tafi, zamuyi rashinki INdo barema Inna."
"Kyale Inna can na barota sai masifa take dan nace zani saye wai bazani ba toh alkur'an saina tafi."
Haka suka dinga hira da Rukayya har bayan la'asar sannan ta koma gida inda ta tarar da Inna ta gayawa babansu yace toh babu inda zata ta kule d'aki bata sake fitowa ba. Tun asubar fari ta farka ta tsinci kayanta tasa a d'ankwali ta d'aure ta d'auk'e fitilar da aka haska d'akin da ita wato shekarau mekwayayen nan k'ananu a jikin katako tayi sad'ab-sad'ab gidan a kulle yake ta jefa kullin kayan ta katanga sannan itama ta kama ta dirga ta kwashe kayan nata ta an taya da gudu sai bakin titi ko tsoro bataji.
Tayi tafiya sosai sannan gari ya fara haske daman babu buk'atar yin sallah dan bawani yi takeyi ba sai taga dama. Mota na zuwa ta tsayar dasu ta shiga dama da d'ari ukunta a hannu data ara wajan Rukayya. Can gida kuma tunda suka farka suke neman Inndo, duk gidan da akasan tana zuwa saida akaje bata nan. Kuka Inna tasanya domin tasan yau INdo tayi mata abinda zai iya 6allamata aure, lokacin da baban yaji cewa yayi k'arya Inna takeyi tasan ta tafi dan haka itama ta shirya tabi bayanta su dawo tare kasan cewar sunsan zata iya zuwa. Ko kud'in mota Inna batada su amma a haka malam Hamza ya takura mata kan cewa sai taje ta dawo da INdo haka ta fito tana hawaye. A bakin titi malam Sadeeq ya ganta harya wuce ya dawo duk da cewar ta rufe fuska da mayafin jikinta tana share hawaye yaje yace.
"Baiwar Allah kiyi hakuri lafiya dai ko..?" Shiru batayi magana ba duk da besan kowace ba ya zaro d'ari biyar ya bata babu yadda zata yi ta k'ar6a tana ta zazzaga mai addu'a shidai ya wuce ita kuma mota na zuwa tashiga tana fatan Allah ya temaketa can din INdo ta tafi, ayau bazasu kwanaba zata dawo da ita.
Wajan k'arfe biyu da rabi INdo ta shiga wata rugar fulani anan cikin sayen bakinta a washe hannunta d'auke da kullin kaya, suna zazzaune k'ark'ashin bishiya suka hangota nan da nan yakumbo tsahare ta had'e rai fuskar nan babu yabo babu fallasa tana dakan fura haka INdo ta k'arasa gurin tana dashare musu hak'ora.
"Wacece wannan kamar mai sunan Gwaggo..?!"
Cewar talatu yayar malam Hamza dake kwance, INdo ta k'arasa tare dayin cilli da d'ankwalin kayan nata tace.
"Nice nan yakumbo talatu ahe duk kuna nan, yau dai gani a garin ku ina kwananku...?!"
Duk suka amsa suna tambayar ta su Sagiru da Nafeesa da Shehu tace lafiya lau amma banda yakumbo tsahare daketa faman dakan fura, ko ajikin INdo ta mik'e tare da zuwa wajanta tana cewa.
"Sannu yakumbo tsahare, ina su lawisa take..?!"
"Ke karki yimin rahin kunya aradun Allah kuwa, idanma Ubanki ne yau ya turoki toh dagake harshi d'in zan iyayi muku rahin mutunci jacan ki bani guri ni."
"Allah baki hakuri daga tambaya.."
INdo ta fad'a tare da komawa wajan su yakumbo talatu aka kawo mata d'umamen tuwo da fura da nono tana ci suna hira har su lawisa suka dawo daga tallar nono, murna da farin ciki ba'a magana duk da cewar Lawisan cikima gareta har tayi aure tsiranta da INdo shekara biyu ne.
Cikin gidan suka wuce suna zazzaga shirmen su. Inna kuwa la'asar sakaliya ta iso saye sabida da kyar ta samu motar da ta kawota a d'ari da talatin. Saida tayi sallah sannan taci kwad'on rama da fura bayan sun shaida mata cewar INdo tazo amma sun tafi tatsar nono, hankalin Inna ya tashi tace ta kalli malam iro mijin yakumbo talatu tace.
"So nake a yau mu koma gida gahi bata kusa kuma ina neman yadda zanyi mu samu kud'in komawa." Malam iro ya kalleta da mamaki sannan yace.
"Haba dai Maryamu, yanzu fisabilillahi har yaushe zaku koma gida, hasalima ita INdon bata kusa kuma da kyar idan zata yadda tabiki dan tasamu yara, kuma na tambayeta randa zata koma tace sai an kori wani malami a garin naku."
Inna ta fashe da kuka malam iro ya kalleta yana jin tausayinta dan yasan tsoran d'an uwar matar tasa takeyi. Hakuri ya dinga bata ita dai hawaye kawai takeyi gashi tana matukar kaunar malam Hamza duk da cewar shima yana matukar santa amma hakan baya hanashi yimata wulak'anci. Har magariba su INdo basu dawo ba sai wajan k'arfe takwas na dare, koda taga Inna batayi wani murna ba kotaji tsoro ita kuma nauyin mutane ya hanata yi mata magana.
Cikin dare Inna tasamu INdo ta gama lalla6ata akan ta yarda gobe su koma amma fir tace wallahi bazata koma ba nan zata zauna sai lawisa ta haihu koda zata koma. Da gari ya waye haka Inna ta kama hanya dama tunda taje yakumbo tsahare bata ko kalli inda Inna takeba har ta kama hanyar komawa sumaila.
Koda Inna ta koma gida malam Hamza baya nan, kafin ya dawo harta sarrafa musu gero tayi musu burabusko yana dawowa yaci yayi hani'in data sanar masa cewar INdon tak'i dawowa sai yace. "Kyaleta Maryamu ni kaina na huta da fitinarta taje can karta dawo d'in."
Bayan sati biyu.
Tunani da damuwa da begen son ganin INdo suka addabi zuciyar Abubakar, duk iya yinsa na ganin ya kawar da hakan daga cikin zuciyarsa hakan ya gagara. Ya rasa meyagani a tattare da ita har yakejin irin abinda yakeji cikin ransa da gangar jikinsa, yasan duk lokacin da asirin zuciyarsa ya fito fili zaisha wulak'anci gurin Sadeeq dama sauran abokansa. Tashi yayi ya tafi Sumaila kauyen na sani direct babu wanda ya sanarwa.
Yana zuwa zuwa ya tarar su Sadeeq sun tashi daga makaranta yarama sai fitowa sukeyi, samun kanshi yayi dayin gaba zuwa unguwar su INdo ko Allah zaisa ya ganta, amma har Sadeeq ya dawo ya tarar dashi besamu yaga ko kyallin kallabinta ba hakan kuma ya hargitsa ilahirin tunaninsa na Ina zai ganta?
"M twinnie..! Ta6 lallai kaida kace min kaida garinnan saidai in wucewa zakayi shine yau na ganka at this time..?!"
K'ak'alo murmushi Abubakar yayi yana kallon hanya dan befidda ran zai hangota ba. Ganin yadda Sadeeq d'in ke kallansa ne yasa shi saurin cewa.
"Malam Sadeeq nasu INdo, wai kuwa har yanzu kana basu kyautar?!"
"Meza'a fasa twinnie? Itace dai tun ranar bata sake zuwa ba, dana tambayi babanta rannan danaje gidan yace wai ta gudu kauyen su sai randa aka koreni zata dawo kaga kuwa ba rana kenan.."
Daram..! K'irjin Abubakar ya buga besan lokacin da ya furta "what...?!"
*HAJJA CE*👈
[7/1, 5:02 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥
♥♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.
_Shafin yau naki ne tawan *HALEEMATU G KHALEEL* (Aneesa didi), Allah yayi miki albarka ya k'ara nisan kwana Allah ya tayaki rik'on Namcy na khadijatu (shareefat) Allah ya azurtaki da miki Nagari ina sonki fisabilillah like H³_💋
Page *11*
Sadeeq ya bishi da kallon mamaki ganin yadda ya furta kalmar tamkar yace masa shine yabar garin ko Mama. Kallansa ya kumayi kafin ya juya yayi hanyar shiga gida yana cewa.
"Kai twinnie bafa Qibd'iyya nace maka ba naga har kana ihu."
Harya bud'e gidan ya shiga Abubakar betaso ba, hanyar gidan su INdo yabi da kallo ji yake tamkar zai ganta amma bako kurarta haka ya k'araci zamansa kafin ya tashi yabi Sadeeq cikin gidan. Lokacin daya shiga tararwa yayi Sadeeq harya shiga wanka hakan yasa shi zama tare da dafe goshinsa sabida tsananin saramai dayaji yana yi. Fitowa Sadeeq yayi zama yayi kusa dashi yana kallansa soyake ya gano wani abu a tattare da d'an uwannasa, Abubakar ya d'ago ya kalli Sadeeq ganin yana mai kallon tuhuma yasa shi wayan cewa ta hanyar cewa.
"Twinnie wai yaushe zakuyi hutu ne?!"
Sadeeq ya mik'e tare da janyo singlet zai sanya yace "kasan ba'a fiyeyin hutun maulud ba so kawai sai term ya k'are ni yanzu mafa na farajin dad'in makarantar sabida suna bani had'in kai yanzu shi yasa na dena neman transfer."
"Oh idan na fahimta kana nufin kace dama Humaira ce ke baka matsala duk fad'in makarantar ko?!"
Abubakar ya tambaya yana zaro ido, Sadeeq yafara shafa mai yana cewa, "eh toh idan nace maka a'a nayi kamar kuskure idan kuma nace maka eh toh shima banyi karya ba domin tun sanda ta dena zuwa nake ganin students d'in suna k'ara maida hankali, haka nima ban sake zagin wata ko wani ba, kai banma sake rik'e bulala ba kaga kuwa idanma nace itace matsalata banyi k'arya ba.."
Abubakar ya dafe kai jin Sadeeq yace INdo ce matsalarsa yaji haushin Sadeeq sosai saidai ya danne dan yanzu so yake INdon ta dawo gida bayajin zai iya hakura har ranar da tayanke hukuncin zata dawo yayi yace.
"Amma twinnie a ganina a matsayinka na malami kamata yayi ace kaine ka fara k'arfafawa yarinyar nan gwiwa wajan ganin tasamu wani kyakyawan abun dazai taimaka mata a rayuwarta kuma a matsayinta na mace."
"Kai twinnie kasan kuwa yarinyar nan? Ka manta abinda tace min da addu'ar datayi min, wai ko'a lahira ina kusa da fir'auna. Wallahi a yadda naji zuciya ta a lokacin ko naso in targad'ata Allah yayi malamai suka saka baki na kyaleta."
Ganin yadda Sadeeq yad'auki zafine yak'arawa Abubakar damuwa, babu ta yadda zai iya samun ganin INdo sai ta hanyarsa yau gashi ta kaishi bango yace bazai temaka mata ba. Cikin nuna halin damuwa Abubakar yace.
"Okey naji ni nayadda zan tallafa mata koda dawani abunne nasan wata rana al'umma zasu amfana da ita. Yanzu inason kasanya kaya kaxo muje gidan su muji inda ta tafi."
"Twinnie wai yaushe kadawo me sauk'in kaine? Kodai-kodai so kake ka kiwata ta tun yanzu kafara banruwa?!"
Mtwww Abubakar yaja tsaki dan shi kansa jinsa yake a wani bai-bai, yau ko kiran Qibd'iyya beyi ba sabida zumud'in son ganin INdo.
"Kai meye haka twinnie? Ni kamar ni zan tsaya jiran wannan kurkurar yarinyar, har yaushe ma zata waye tayi kamar yadda nakeson Qibd'iss? Kawai dai ina son mu sami ladane ta hanyar gina mata wata rayuwar sabuwa wannan shine kawai manufata..."
"Ohh toh ai akwai irinta da suke buk'atar hakan m twinnie bawai dole sai itaba, ni wallahi na tsani yarinyar nan garama data bar garin wawuya kawai sai idanuwa kamar na mayu.."
"Shhhhiii m twinnie duk meyayi zafi hakan? Kayi hakuri nitunda nayi niya zan temaka mata insha Allahu tunda kai kayi fushi..."
"Hakan dai yafi.."
Cewar Sadeeq. Sun dad'e suna hira har akayi la'asar zasu tafi masallaci Abubakar yake cewa "M twinnie idan mundawo ina son karakani muje gurin baban ta ko Maman ta dan Allah."
"Ohh wai daman baka manta da zancen ba?"
Sadeeq ya tambayesa yana dariya, Abubakar ya kalli katangar gidan ya tuno lokacin da ta watso mai hijjab da takallmi yayin da Sadeeq ya tuna sanda ta watso mai ruwan k'anzo suka wuce Abubakar na murmushi yayinda Sadeeq ke faman jan tsaki.
Suna dawowa Sadeeq ya d'auka ko mutumin nasa ya manta dan haka yak'i kallon koda gidan su yarinyar, suna zuwa zasu yi kwana Abubkhr yayi saurin dakatar dashi ta hanyar rik'e masa hannunsa yana cewa.
"Ya haka ne twinnie? Ina kuma zakaje?!"
"Oh wai dama baka manta ba?"
"Eh ai kasan ba'a manta yin alheri musamman idan mutum yayi niya."
Sadeeq yace "naji toh karka gayan magana,ke shiga kice ana sallama da malam Hamza."
Yayi maganar yana kallon Nafeesah dake zaune a k'ofar gida, ta kallesu ganin su iri d'aya sak bakinta bud'e haushi ya Kama Abubakar cikin takaicin kallon da take yi masa yasa shi cewa "Ke bazaki kibane kika saka mana na mujiya?!" Da sauri tayi firgit tana susa tace "Ai baya nan yana can wajan aikinsa a bakin hanya."
Kallon Abubakar Sadeeq yayi dan yaga yazai yi amma sai yaga ya wani ta6e baki irin sunyiwa kansun nan amma cikin zuciyarsa kwata-kwata ba haka bane suka juya suna tafiya Sadeeq yace.
"M twinnie muje na kaika inda zaka temaki masu neman temako domin bawai rayuwar INdo ce kad'ai take buk'atar hakan ba, indai kayi niyar temakawan to kazo muje wani gidan."
Mtwwwww Abubakar yaja tsaki ganin yadda Saseeq d'in ke takura masa da zancen wani gidan, shi duk gaba d'aya mafa yafi buk'atar yaga INdon ko zaiji wani 6arin na gangari jikinsa da ruhinsa sun samu sassauci amma Sadeeq ya kasa ganewa ya kuma had'e rai cikin basarwa yace, "okey bari next week zan dawo sai musan abinyi yanzu bari na koma sabida aikin yamma gareni." Yafad'a yasan duk bala'i nan da ranar asabar INdo ta dawo, shi dai Sadeeq be damuba dan dama be d'aukarwa wani aiki ko takura ba bare yasa kansa cikin damuwa, yana yin alheri a duk lokacin da yake da kud'i. Sallama suka yi a bakin k'ofa Abubakar ya tafi yayin da Sadeeq ya shiga cikin gida cike da kewar abokin haihuwar tasa.
Abubakar kuwa tsakanin sa da Qibd'iyya sai hange daga nesa, sam yanzu ya dena ganin kyawunta bare yaji kwarin guiwar zuwa wajanta. Ita kuma ta rigada ta kamu da kaunarsa domin ya riga yayi mata dashen zazzafar soyayyarsa gashi ta dena kula kowa sabida shi, yau kimanin sati uku kenan ta kasa ganokanshi ya rage nemanta ko kiranta a waya bare ya taka yaje gidansu tad'i sam ya dena har abun ya fara damunta.
Kwanaki na tafiya Abubkhr na kuma shiga cikin damuwa da tunani. Ana ya gobe zai koma sumaila kauyen na sani k'aninsa Khaleefa ya shigo d'akin nasu, kwance ya tarar dashi yayi rub da ciki ko shirin tafiya asibiti beyi ba khaleefan ya k'arasa ciki tare da cewa.
"Yaya Habu Abba na k'iranka yana d'aki."
Beko juyo ba ya d'aga mai hannu sannan khaleefa ya fita shi kuma ya mik'e dakyar ya sanya zilaika sannan ya fita yana wani 6acin rai. Kwankwasa k'ofar yayi Abba yace ya shiga, yana shiga ya gaidashi sannan yasamu guri ya zauna abban yace.
"Yauwa Abbakar dama zance Mariya ne, mahaifinta yayi min magana an tambayeta wanda ta tsayar tace kai shine nace toh ya bari nazo naji ta bakinka ya ake ciki."
Gabaki d'aya ya daburce besan lokacin da yace.
"Abba aure kenan fa..?"
Yafad'a cike da tashin hankali dashiga cikin d'imuwa, Abba ya kallesa tare da cewa.
"Eh Abbakar aure tunda ai kaine kaje gidan nasu."
"Amman Abba da an d'an k'aramin lokaci kafin ayi maganar auran nawa zuwa nan da wani d'an lokaci."
"Amman kai Abbakar kasan dai bazan zuba ido kaida d'an uwanka kuzauna har yanzu babu Aure ba? Kuma gashi kai har gidan su yarinyar sunsan da zamanka."
"Eh Abba ai bayi ne baza muyi ba, lokaci kawai nakeso ka k'aramin dan inason tabbatar da wani abu dan Allah..."
"Tom naji zan k'ara maka lokaci aman da sharad'in wanan maganar tamu ta karo karatunka zuwa k'asar Spain dan nariga na samu duk abinda ake buk'ata. Yanzu gobe nakeson kaje abuja zakayi wani signing na tabbatar da tafiyar taka, sai kuma na koma kan Saddiqu shima a sake mai wajan aiki."
A rud'e yace "Abba har yanzu dama kananan da burinka na k'aro karatun mu? Innalillahi."
Ya furta cikin sanyin murya, Abba yace "Eh Ina nan da wanan burin Abbakar Ina matukar kaunar naga kun cigaba a duniya, don Allah kucika min wanan burin nawa dan wata ran kune iyayen k'annanku, sannan nima naji dad'i a tattare daku."
Nan da nan jikin Abbakar yayi sanyi, babu yadda zai yi dole yacikawa Abban su burinsa ya mik'e da kyar yana had'a bango harya koma cikin d'aki.
Kwanciya yayi ruf da ciki ya fara tunanin taya zai iya samu yaga INdo har ya tallafi rayuwarta sannan ya bawa zuciyarta abinci dan yana son ganinta ra'ayul Ayn. Ina zaije yasake ganinta kafin ya tafi, yanzu ya yarda ba shida wani buri sai son ganishi tare da INdo...
*HAJJA CE*👈
[7/1, 5:03 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥
♥♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.
_*HASKE WRITER'S ASSO..* wannan shafin na kune yau na bakushi kyauta. Allah ya k'ara had'e kanmu ya kuma k'ara fasaha mai amfani #ana tare all_🤝😍
Page *12*
Washe gari Abubakar ya tafi abuja danyin abinda Abba yasa shi. Tunda kuma ya dawo daga abuja kullum akwai inda zashi sam baya samun zama gashi yayi-yayi Sadeeq ya d'aukar masa amana da alk'awarin nemo INdo ya kula da ita amma Sadeeq yak'i shi adole idan zai tayashi toh saidai ya canza wata amma ba INdo ba, da haka sukayi bankwana baram-baram kowa najin haushin d'an uwansa.
INdo kuwa wayyo Allah tazo saye kauyanci da k'arin abubuwa duk sun dad'a k'aruwa ta zama tamkar 'yar garin duk inda kaje sai kaji labarinta kaf kauyan sun-santa dan akwai shiga jama'a. Da mutum d'aya ne basa shiri wato yakumbo tsahare, sam basa jituwa da juna ko a layin band'aki.
Ranar da lawisa ta haihu kuwa su INdo sune masu jigo, anyi ruwa anyi tsaki tazama tamkar itace me jegon dan ta kanainaye komai lawisa kuwa sai kawaici take bata magana. Ranar suna aka sanyawa yarinyar Raihanatu suna kiranta da Ladi kasan cewar ranar lahadi aka haifeta.
Watan INdo biyar a garin saye ta kuma irin wayewar nan ta karkarar fulani. Jin dad'inta kawai takeyi samari kuwa su tara ne kowa sonta yakeyi suna yi mata kyaututtuka sosai dan da haka take tattara kaya sawa tana kuma siyan kayan kwalliya abin sai wanda ya gani duk bak'in cikin yakumbo tsahare sai dai ta kawar dakai.
Ta manta dasu Inna tama manta dasuwaye malam Sadeeq sam yanzu rayuwarta takeyi babu takurawa...
*BAYAN SHEKARU UKU*
K'arfe hud'u da rabi da minti shida, Sadeeq Salman Haruna ne cikin mota 403 ash color yana bin bayan wata kyakyawar budurwa. Tafiya take cikin nutsuwa da iya bawa k'asar da take takawa hakk'inta, duk da cewar taga ana binbayanta hakan besanya ta waiga ko tayi alamum tsayawa ba har ta shiga kwanar gidansu.
Shima beyi mata magana ba yana ganin gidan data shiga yayi murmushi sannan ya juya kan motarsa yabar layin yana sak'awa da kwancewa ta yadda zai fara tunkarata da kalma mafi tsada da daraja a gurin wata d’iya mace.
Saida aka d'ibi kwanaki hud'u yana bibiyar rayuwar budurwar ba tare da tasani ba sannan. Ranar asabar da misalin k'arfe hud'u da rabi ya dira a k'ofar gidan, yaro yajira yazo yace yashiga ya k'ira masa Fatima Kabir ya'u. Ba jimawa sai ga yaron da wani matashin saurayi wanda zaiyi sa'an Sadeeq d'in sun fito tare, yana zuwa suka kalli juna cikin tsananin mamaki matashin yace.
"Kardai ace twin's d'in dana sani ne? Abbakar ne ko kuma Sadeeq?!"
Dariya Sadeeq yayi tare da bawa saurayin hannu suka tafa yana cewa "cinka da kanka Shamsu kabeer Ya'u dama kananan.?!"
"Hahaha ina nan mana, dallah ka tabbatar min waye a ckinku kasan kud'inne sai a hankali."
Sukayi dariya dukansu sannan yace.
"Sadeeq ne Shamsu ya rayuwa."
Shamsu yace "Alhamdulillahi, gaskiya na dad'e ban sake sanya ku cikin idona ba tun sanda mukayi candy a GSS kwankwaso, ya wai kaine kenan ka biyu sisi na gida."
Shafa kai Sadeeq yayi bayan ya zame hular zannar shi sannan yayi murmushi yana cewa.
"Wallahi kuwa ashe ma k'anwata ce. Anywaya nidai nagani kuma ina so ya za'ayi kenan?”
"Toh ya zanyi tunda kazo kawai zaka jamin raini, k'anwata ce Fateema kuma kayi sa'a this year tayi graduation but gaskiya munan gidan ba'ayi wa mace aure sai tana da ilimin NCE ko Diploma, gashi ita kofarawa batayi ba yakenan?!"
Murmushi Sadeeq yayi cikin jin dad'i domin hakan yayi dai-dai da lokacin dawowarsa daga k'wara state. Cikin rashin nuna damuwa yace.
"Shamsu babu damuwa ni dai burina gidan ku susan dani, kuma a bani dama mufara fahimtar juna tun yanzu."
"Karka damu tunda kana dani babban yaya, wai yanzu wane aiki kake yi..?!"
Sadeeq yayi murmushi tare da cewa "Toh kasan rayuwa babu yadda bata zuwar mawa d'an Adam, da ina teaching ne a wata secondary school amma yanzu ina nan BUK shekarata d'aya da dawowa nan ina lecturing, sai dai akwai wani business danakeyi acan k'wara state hope babu wanda ya rigani Fateema..?!"
Dariya Shamsu yayi tare da sake bawa Sadeeq hannu suka tafa yace.
"Karka damu abokina insha Allahu zaku dai-daita bari ma naje nafito maka da ita."
"Toh godiya nake dad'in aboki a gidan su budurwa🤪." suka kuma tafawa sannan Shamsu ya koma gida. Yana shiga falo ya kalli Fatima dake kwance tana karatun wani novel akan kujera, had'e rai yayi shi a dole babban yaya yace.
"Ke Fatima tashi ki shirya kije waje abokina yana jiranki."
Da mamaki ta d'ago tana kallasan yace "eh ko bazaki jeba ne?!"
Fatima tace "Haba Yaya Shamsu amma kasan dai baba yace karna kula kowa ko..." Ya sake had'e rai sannan yace, "ke! Toh waye baban yanzu a gabanki? Zaki tashi kosai na bugeki, sakarai kawai."
Tashi tayi tana zumburar baki ta kalli Umman su ganin harkar gabanta kawai takeyi yasa Fateema shiga d'aki tana gunguni. Hijabi ta zurma ta fito Shamsu ya kalleta tare da cewa.
"Ke koma ki shafa hosa da janbaki, kinsan ko waye yazo gurinki kuwa.?"
"Gaskiya ni Yaya..." Yayi saurin katseta ta hanyar daka mata tsawa yana cewa, "Baxaki je Kiyi abinda nasaki bane?!" Sake komawa tayi harda hawaye sannan ta shafa hoda tasa coffee d'in janbaki sannan ta kuma fitowa, Shamsu ya kalleta sannan yace "Good girl sauran kuma kije kiyi mai fitsara ko ki gayamai babu dad'i ranki saiya 6aci wallahi domin 6atamana suna zakiyi wuce."
Fita tayi tana kunkuni, a zaure tagan shi suka had'a ido Sadeeq ya sakar mata Murmushi tayi saurin kawar dakai tare da tsayawa ta jingina jikin bango. Jitayi yayi mata sallama ta amsa yayi dariya kad'an ta kuma d'agowa ta kallesa karaf suka had'a ido. Samun kanta tayi dayin murmushi sannan ta gaidasa ya amsa tare da gabatar mata da kansa tana jidai amma batace komai ba sai daya ce mata.
"Ina fatan zaki yarje min nashiga cikin rayuwarki har muyi aure, nayi miki alkawarin kare duk wani hakkinki da kare miki duk wani mutuncin ki burina kawai ki yarda dani."
Samun kanta tayi da cewa "Shikenan na gode tunda har Yaya nane ya baka damar da banta6a tsayawa da wani ba kamar haka."
"Toh godiya nake yiwa Yaya Shamsu, sai kuma yaushe zan kuma dawowa Zarah..?!"
Ya tambaya yana kasheta da salon shi tayi murmushi cikin sanyi, ita kanta batasan lokacin da take maida reply ba. Ya had'u iya had'uwa dan k'irjinta banda bugawa babu abinda yakeyi.
"Nima ban sani ba."
Ta bashi amsa yace "Toh sai wani satin insha Allahu a gaida Umma." Da sauri ta shiga gida yayi dariya yana zuwa mota sai ga Shamsu ya fito yace.
"Kai abokina irin wannan shaf-shaf d'infa wai har kagama siye tane?!"
Sadeeq yayi dariya tare da cewa, "ban fad'a ba nidai, kawai dai dama zuwa nayi na gabatar mata da kaina."
"Hakan ma yayi kyau mutumina, toh Ina Shi Abubakar d'in."
"Yana Spain sun rik'esa amma nan da one month zai shigo k'asar insha Allahu."
"Ahh lallai kaji manya toh Allah ya dawo dashi lafiya muna murna."
"Toh Shamsu godiya yake bari na gudu nima ka kular min da mata."
"hmmm harta zama makenan, Allah ya kiyaye hanya a gaida mutanan gidan."
Suka yi sallama Sadeeq ya tafi, tun daga lokacin indai yana kano toh zaije gidan su Fateema idan baya nan suna mak'ale da waya ta hanyar shamsu domin babanta yaki yadda ta rik'e waya sai ta fara karatu. Sun shaku sosai fateema na sanshi shima yana sonta alkairi kuwa duk zuwa da abinda zai kaimata.
Doctor Abubakar Salman Harun, matashin saurayi mai tak'ama da kyau da ilimi nagarta da wayewa ya zama babban likita wanda duniya ta sanshi take kuma tak'ama dashi. Tun bayan gama karatun sa da shekara biyu a, k'asar Spain suka rik'esa domin suma ya ceto al-ummar su ta hanyar kwarewarsa, yana gudanar da aikin cikin walwala da jin dad'i duk da cewa tunda yabar k'asar tunanin INdo be ta6a gushewa daga cikin al'amransa ba, ya sakawa ransa cewar Allah ne zai bashi INdo bawai wani abun nasaba hakan yasa ya kwantar da hankalinsa yacigaba da karatunsa cikin nutsuwa da sadaukarwa rayuwarsa akan Al-ummah.
Ganin yak'i dawowa ne hakan yasa mahaifinsa ya umarce sa da yadawo gida domin taimakawa 'yan uwansa 'yan Nigeria, bai k'i tayin mahaifin nasa ba saboda shima bak'aramin missing d'in gidan yayi ba. Ga wasu mafarkai dayake yi game da INdo da yake kusan kullum yana son ya ganta yana kaunar sake had'uwa da ita. Hakan yasa yayi niyar komawa gida bayan yayi wa asibitin *CANTABRIA HOSPITAL* bankwana. ba suji dad'in barinsa aiki ba aman sun bashi damar duk lokacin da yake da buk'atar dawowa suna maraba a kowane lokaci..
Wednesday morning at 8:30am cikin airport d'in malam Aminu kano matashin saurayin mai shekaru 32 ya sakko daga cikin jirgin Nigerian airlines. Sanye yake cikin wasu dakakkun suit coffee color sai ta cikin white da cover shoe gashin kansa a saisaye bakikk'irn ya gyara kyakyawan sajansa sai wanda ya ganshi zai iya tantacce d'an wace k'asar ne.
Sadeeq ne ya fara ganinsa dan haka shi yafara k'arasawa wajan cikin fara'a suka rungume junansu. Abba ma ya karasa Abubakar yayi saurin tsugunnawa yana mik'a gaisuwa mutanen gurin sai kallonsu ake, zuciyar Abba tayi fari ganin yadda 'ya'yan nasa suke bashi respect aduk inda suka had'u.
"Welcome twinnie am glad to see you sai daifa yanzu bama kama kazama bature."
Cewar Sadeeq suna tafiya ajere, Abubakar yayi dariya har suka k'arasa cikin mota suna tsokanar junansu. Kwanansa d'aya da dawowa batare da kowa ya sani ba yatafi Sumaila kauyen sani, ba laifi anyiwa kauyan sauye-sauye ya nufi gidan malam Hamza direct cikin ikon Allah kuma ya sameshi a k'ofar gida bayan ya tambaya annuna masa shi.
Bayan sun gaisa ne shi duk a tunaninsa malam Sadeeq ne shi kuma Abubakar be nuna bashi bane ya kalli malam Hamza yace.
"Malam INdo kuwa ta dawo?!"
Malam Hamza ya kad'a kai cikin takaici yace "Ai malam Saddiqu uwata dai k'arfi da yaji ta gujemu, k'iri-k'iri tak'i dawowa, harma gidan su yaron dazata aura acan sayen sun aiko mun kuma bashi dan idan ba haka bama uwata ba dawowa zatayi ba. Wallahi har zuwa nayi da kaina nace mata kabar garin amma tak'i yadda mudawo."
K'irjin Abubakar ya buga jin cewar an aiko, cikin d'imuwa yace.
"Malam wane kauye ta tafi ne? Nidai wallahi inason ganin yarinyar nan tasamu Ilimi koyaya ne, idan babu damuwa kuma ka yadda dani kagaya min kauyan da INdo taje na dawo da ita zan samar mata da rayuwa mai inganci da ikon Allah nidai burina ka yadda dani."
"Toh malam Saddiqu na yadda amma dasharad'in sai munje mun sanarwa dame unguwa, shima yasani da kuma aminina malam 'Dalha.."
"Hakan ma dai-dai ne Malam na gode." Hannu yasa ya ciro kud'i duba ashirin ya mik'awa malam Hamza ya kar6a yana ta godiya tamkar zai mai ruku'u sannan yace suje gidan me unguwar. Suna zuwa aka yi komai sannan suka koma gida Abubakar suka gaida Inna bayan sun kwatanta mai kauyan sayen ya koma gida cike da murna.
Da dare suna zaune a d'aki Abubakar ya kalli Sadeeq yace.
"M twinnie zaka min rakiya gobe dan Allah."
"Zuwa Ina kuma daga dawowarka?!"
Cewar Sadeeq Abubakar yayi dariya tare da cewa.
"Wani guri zamuje wajan k'arfe 12:00pm."
"Allah ya kaimu tunda gurin bashi da nisa, kasan dai Qibd'iyya tayi aure ka yaudare ta."
"A'ah twinnie Allah ne beyi ba." Suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha'wa.
Washe gari suka d'auki hanyar zuwa saye cikin suit d'insu iri d'aya da Abubakar ya taho musu dashi. Tafiya suke tun Sadeeq yana kawaici harya fara magana.
"M twinnie wai ko katsina zamu je ne naga mun wuce dawanau..?!"
Abubakar yayi murmushi sannan yace "A'a kaidai zuba ido kayi kallo."
Cigaba sukayi da tafiya har suka d'auki hanyar saye Sadeeq dai yayi shiru idan ya gaji sai ya kira Fateema har yaga sun fara shiga daji da kewaye mugayen ramuka ya kuma yin magana.
"M twinnine ko kafara sana'ar yankan kai shine zaka fara takaina?!"
Abubakar ya kyalkyale da dariya tare da cewa.
"A'a ban faraba zuciyata nazo d'auka a garin."
"Tofa.. Waye zuciyar take twinnie??"
Abubakar yace "Aishat Hamza,what I mean is INdo malam Hamza."
"What.........???!"
_Kuyi hakuri da wannan wallahi unguwa naje amma duk da haka saida nayi muku. Ina godiya a gareku masoya._
*HAJJA CE*👈
[7/1, 7:39 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥
♥♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
_page 13 na kune 'yan candidate d'in government girl secondary school Kwah, hope zakuji dad'in shi sannan kuma ina muku fatan alkairi a cikin rayuwarku kamar yadda kuke bin labarin nan_💍
Page *13*
"Amman dai baka min adalci ba kasani ko m twinnie? A k'a'ida yau zanje gidan su fatma sabida gobe nakeson wucewa amma kayi min haka, wallahi danasan gurin wannan wayuwayar zamuzo bazan rakoka ba”mtww
"Sanin idan na gaya maka bazaka yadda ba yasani k'in gaya maka sabida ina son muzo tare dakai."
Sadeeq yayi mai banza har suka shiga cikin rugar fulanin, suna zuwa suka ga 'yan mata yara da manya sunzo zasu wuce. Ra6awa Abubakar yayi da motar gefe kasan cewar bazata wuce canciki ba sannan suka fito Sadeeq sai faman cin uban magani yake yi idonsa sanye cikin dark shade shi kuma Abubakar d'an siriri ne nashi fari kal kamar k'ank'ara.
Suna fitowa INdo dake tsakiyar 'yan matan zasu tafi kasuwar badume tana ganinsu ta ganesu cikin karad'i tace.
"Jakar uban nan,sun biyo ni masifaffun malamn nan." Kallon sauran abokan tafiyarta ta tayi tana gyara mayafinta tace.
"Kowa ya samu sanda zamu k'arasa wajan wad'an can malaman, kawai danace muku kulle kukuma sai ku jibgesu."
Suka ce toh kowa ya juya ya samu sanda harda ita sannan suka nufi gurin suma su Abubakar lokacin sun k'araso ciki sam basu ganeta ba sabida tayi girma ta zama 'yan mata, lokacin da ta baro sani tana 12years yanzu kuma tana 15years gashi tayi 'yar k'iba ta kuma canza. Abubakar shine ya taresu yana kallansu yace.
"K'annena dan Allah muna neman gidan da INdo malam Hamza take, wadda tazo daga kauyen sani."
Caraf ta cafe bayan ta rik'e kugu tace, "ga wata nan lafiya kuka zo inda nake..?!" Duk suka zuba mata ido Sadeeq dariya da takaici suka kusan kamashi ya kalleta kallo irinna raini sannan ya juya zai koma cikin mota yaji tace.
"Wannene kaid'in dacta Habubakar ko kuma malam Sadeeq? Na ganeku rasai."
Ko waigowa beyi ba sabida haushi ita kuma ta kalli Abubakar dake tsaye yana kallonta, sam bega wani aibu a tattare da ita ba yaji zuciyarsa ta sanyaya yanajin tamkar ya rungumeta amma bahali gashi ya gansu da sandina kuma su ba shanu a taredasu bareyayi tunanin cewar kiwo zasuje. Cikin sanyin murya yace. "Humaira inason muyi magana dake, naje munyi magana da mahaifinki sauran ke."
"Allahu akubar kabiran, malam Sadeeq ni ba'a renamin hankali wallahi nan garin yanzu sai nasa su rakaku da duka wallahi."
Ido ya zaro jin abinda take cewa ya fara bin hannayen yaran tare da tuna wata kalma ta bahaushe da yake cewa sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, ya d'an kalleta cikin ransa yana tunano ko harsai yaushe ne zata yi hankali. Ya rasa ya zaiyi da su sai yayi murmushi tare da zura hannu cikin suit d'insa ya zaro wallet suka bishi da kallo ya ciro 2k ya mik'awa wata yarinya yace ga wannan kusha alawa.
Kallon kud'in suka yi sai kuma sukayi baya-baya suna zaro idanuwa, ganin dalla-dallan kud'i yasa INdo tayi saurin k'arasawa zata fisge Abubakar yayi saurin janye hannunsa tare da kad'a mata kai yace.
"A'a wannan ba naki bane, naki yana gurin Sadeeq sai kin yadda da abinda zan gaya miki sannan zamu baki su suna can dubu ashirin."
INdo ta dafe k'irji tare da jan baya tace, "Dubu ahirin? Toh kaine dacta Habubakar kenan, meyasa kabari aka bawa malam Sadeeq kud'ina kuma alhalin mugune ba bani zai yi ba..?!"
"Zai baki amma sai kin yadda da maganar da zamu gaya miki."
Tana jin haka tace "kaltume ku kar6i kud'inku, kuyi gaba zan taho daga baya idan na kar6i kud'ina."
Kar6a suka yi sannan suka tafi ita kuma ta yarda icen hannunta tare da goge hannun jikin zaninta, shi kuma sai kallanta yake yi, sam ya rasa abinda ya gani a jikinta yaji zuciyarsa na azabtar dashi, yace.
"Toh kinga wani dutse can muje mu zauna in gaya miki abinda muka zo sanar miki."
Ba musu suka tafi sai juyawa take tana kallon Sadeeq a cikin motar, suna zuwa Abubakar ya zauna ita kuma ta tsaya yace.
"Humaira zauna mana."
"Karkafa kuma cemin wani humaira hekace wata yarinya e'heee."
"Sunan Mamana gareki shima humairan na fad'a ne sabida babu yadda zanyi, ki zauna kijini dakyau abinda zan sanar miki, idan baki yadda ba zamu d'auki wata yarinyar anan kauyan mu bata kud'in."
Da sauri ta zauna ya kalleta yama rasa ta Ina zai fara mata bayani yadda zata faminta ta gane manufarsa karta yi mai hayaniya. Zare glass d'insa yayi sannan ya kalli fuskarta sai faman wasa take da k'ananun duwatsu yace.
"Humairah kina son yin karatu?"
Kai tsaye INdo tace mai,
"A'a aradu nida zanyi aure."
Abubakar ya kuma kallanta, ganin tayi maganar har cikin ranta yasa shi mik'ewa tsaye yace.
"Eh ai zakiyi auran amma ki gaya min idan kinason yin karatu kema wata ran ki zama kamar matar gwamna ko shugaban k'asa kuma kema wata ran ki amfanar da bayin Allah da kuma 'ya'yanki wanda zaki haifa idan kinyi aure."
Rufe ido tayi da tafin hannunta wai kunya sannan tace.
"Eh toh bank'i ta bakinka ba amma ni bazan yi wani karatu ba haka kurum naje malamai su dinga jibgata ba a'hh jikina bana banza bane, kuma ma yazan yi da auran saleleh tunda shaura 'yan makwanni.."
Mtwww Abubakar yaja tsaki jin ta kira salele cikin d'an 6acin rai yace.
"Waye shi salelen? Me gareshi? Ana son fito dake daga cikin duhun kai kina wani sake dulmiya kanki? Kinga humaira ki yadda yanzu mu koma sumaila dake akwai kayan da na tanadar miki sababbi tindaga kan, atamfofi, shaddoji, materials, mayafai takalma, jakunkuna da kayan kwalliya, amma sai kin yadda zaki bimu mu koma can gidan ku..."
Shiru INdo tayi ta fad'a cikin tunani, kallonta yayi ganin tayi shiru ya fara addu'ar karta ce mai bazata ba murya a raunane yace mata.
"Please Humaira talk to me mana."
Kallansa tayi jin yayi mata turanci tace "sake gaya min abinda ka fad'a yanzu da hausa ko da fulatanci sune yarena."
"Oh cewa nayi kiyi magana mana, inason jin matsa yarki I told you zaki samu komai idan muka maida ke sani."
"Kai dacta habubakar kun saba cewa zaku yi amma ni bakwa bani bare ma kuma malam Sadeeq”hmmmm.
"Humaira wannan karan nine zan d'auki duk wani nauyin abunda kike so, fatana da burina ki yadda mu koma nayi miki alk'awarin yi miki duk abinda kike so indai befi k'arfina ba."
"Harda kayan d'aki idan mun tashi yin aure da salele?!"
Ta tambayesa duk da yaji haushi amma be nuna mata ba sai ma eh daya ce mata.
"Toh kuwa zan biku amma hemunje mun gayawa baba iro dasu yakumbo talatu."
Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar Abubakar yace mata.
"Toh muje."
Jerawa suka yi INdo sai d'an tsince-tsince takeyi yana hanata da haka har suka k'arasa. Tun a bak'in k'ofa ta fara k'iran yakambo talatu tafito da d'aurin k'irji tana tambayar.
"Lahiya mai sunan uwa.?"
"Anzo tahiya dani gida, ina lawisa da kande suzo muyi bankwana”
A gindin bishiya Abubakar ya tsaya yana kallon inda suke rayuwa ya kuma tuno cikin garin kano kafin ya tunano garin abuja zuciyarsa ta dira a k'asar Spain. Lallai Allah beyi ko ina dai-dai ba, wannan yafika kaima kafi wani sannan ya furta kalmar "Alhamdulillah."
"Ina wanda yazo tahiya dake d'in, karki ce mini wannan ne?"
"Aradu baba iro shine, d'an uwan malamin mune a sani."
Tabarmar kaba aka shimfid'awa Abubakar ya zauna tare da baba iro k'arin bayani da kuma sanar dashi cewar da izinin malam Hamza yazo d'aukarta. Abinciccika aka kawo mai saidai beci ko d'aya ba sannan baba iro yace.
"Toh gaskiya bazan baku yarinyar nan ku tafi da itaba, hedai muje tare har garin, idan kuma ka yankamu kaida Allah domin hine mesakayya."
Babu gaddama Abubakar ya amince, aka sanar da mutanan gari INdo taje ta harhad'a kayanta akayi mata tsaraba da yawa sannan mutane mata da maza suka tafi raka ta gurin mota.
"Yakumbo dan Allah idan salele ya dawo kice mihi na tafi amma ya dinga zuwa sumaila muna gaisawa kafin bikin mu kinji.?!"
INdo ta fad'a Abubakar dake gaba ya dinga jan tsaki yana jin yadda take k'ara jajjada sak'on da za'a gayawa salele suka k'arasa wajan mota dama tundaga nesa Sadeeq ya hangosu ya dinga kwasar dariya ganin yadda sukayo gungo guda sai tada kura sukeyi, suna zuwa ya had'e rai sukuma mutanen suka dinga fad'in ahe 'yan biyu ne.
INdo da baba iro suka shiga gidan baya sannan Abubakar ya zauna a driver seat Sadeeq na kusa dashi ya data motar suka dinga d'aga musu hannu anayiwa baba iro adawo lafiya. Har suka fito daga surkullen babu me magana sai INdo datake lissafo wad'anda zata yi kewa, suna hawa babban titi iska ta fara hurata ta A.C ta mirgina kai sai bacci har rawar sanyi take yi.
*****
Sani...Suna zuwa har k'ofar gidan malam Hamza suka tsaya baba Iro ya tashi INdo duk ta cika su da munshari wanda hakan be damu Abubakar ba amma Sadeeq iya kuluwa ya kulu, ta bud'e k'ofar da sauri tana fitowa 'yan unguwa suka fara cewa.
"Ga INdo... Ga INdo...!"
Ta bud'e ido tare da kuma mistsike shi tana dariya, duk wanda ta gani saita fad'i sunansa kafin ta shige cikin gida da gudu tana k'iran Innar su.
"Kai INdo yaushe kika dawo?!"
Cewar k'aninta shehu yana wankin kayansa, bata kulasa ba Inna ta fito INdo ta d'areta cikin murna tana washe mata baki.
"Oh 'yarnan kina nan da halinki ko??"
"Ta6 Inna kenan Ina zeje, yana nan aradu wai ina Nafeesah da Sagiru duk bangansu ba..?!"
"Suna waje k'ila dai suntai wani gurin ne, ahe yau zaya d'aukoki jiya malam ke gaya min yadda sukayi da malam Saddiqun."
Cewar Inna INdo tayi dariya bata ma bata amsa ba tace,
"Inna ina Rukayya kuwa, oh ni INdo tana nan kuwa?!"
"Tana nan yanzu ma 'ya'yanta uku sai kuma wanda zata kuma haihuwa."
"Kai Inna yanzu cikin wani gareta kama d'ahare ta saye? Bari naje gidan naganta nikam."
"Haba 'yar nan daga dawowar ki?!"
"Eh wallahi Inna ai Rukayya mutuniya tace kinga tunda na tahi ban mance da ita ba."
Tashi tayi ta suri takalma tayi waje, a k'ofar gida taga su malam Sadeeq da baban ta amma ta wuce sai tsayawa take suna gaisawa da mutane. Lokacin da su Abubakar suka gama magana da malam Hamza abubakar kasa tafiya yayi domin yana son suyi sallama, k'ofar gidan Rukayyar ya k'arasa ya tura yaro ya kirata ya kalleta sai faman dashare baki takeyi tana rufe ido yace mata.
"Humaira zan tafi gida, Zan dawo jibi insha Allahu karki dinga tafiya yawo idan ba haka ba bazan baki komai ba."
"Ai bazan yiba dacta, ammafa karkak'i zuwa kaji?!"
Yace "Toh Humaira Zan tafi amma fa kiyi wanka ranar dazan zo."
Tace "Toh dacta Ina jiranka."
Yana tafiya ta koma gidan Rukayya shi kuma ya shiga mota bayan sunyi sallama da malam Hamza da baba iro. Sadeeq yaja mota suka nufi gida. Da daddare suna zaune abin duk ya damu Sadeeq ya kalleshi yana danna laptop yace mai.
"M twinnie can you tell me why cared Nd protect her? I know bawai dan wancen dalilin bane tunda gashi har kana cemin zuciyar kace please tell me."
Ture laptop d'in yayi tare da kwanciya ya sanya hannuwansa ya tallafo kanshi yana kallon fankar sama yace.
"Twinnie bazan 6oye maka ba hakan yasa naje tare dakai muka dawo da ita gida, twinnie I'm in love with her, I can not do anything with out her. Ina son ta zama matata, ina son na mallaka mata ragamar rayuwata koda kuwa bata zama wayayyar da nake da burin aura ba."
Cikin tsananin mamaki da al'ajabi Sadeeq yake kallon Abubakar jin abinda ya fad'a. Ganin Sadeeq na niyar yin magana yasa shi saurin cewa.
"M twinnie kayi min fatan alkairi, ka kuma taya ni yak'in neman yarda da soyayyar Humaira please n please twinnie."
"Allah ya k'ara dankwan soyayya Allah yasa ayi komai muna nan."
Cewar Sadeeq yana kallonsa, Abubakar yayi murmushi tare da cewa.
"Amin m twinnie thank you."
Kowa ya cigaba da abinda yakeyi zuciyar Sadeeq fal mamaki, shi kuma Abubakar tashi kaddarar kenan auran INdo Allah kadiran alaman yasha.
Washe gari Sadeeq ya tafi k'wara state, a day after Abubakar ya shirya tafiya sumaila yayi sallama dasu Mama, sannan ya d'auki k'anwarsu Hawwah ya kaita wani shago yace ta had'a mai kayan kwalliya, tayi-tayi ya gaya mata na meye yak'i tana dariya ta had'a mai komai sannan ya bata kud'i yace tahau napep. Ya wuce a hanya ya tsaya ya shiga wani Boutique ya siyawa INdo wasu tsala-tsalan dogwayan riguna guda biyar da takalma guda uku ya had'asu da kayan kwalliyar sannan ya wuce sani...
*HAJJA CE*👈
[7/2, 6:33 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥
♥♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
_Ina ganinku dearest comments d'inku na k'ayatar danifa_
*K'anwata Stylish, my Xoxo, Faxyfation, phartzarah, Nuceeyluv, khady, Mmn gausiya, UmmuMuhammad, Khady M/kano, Mmn nuceey, sumeey Q, Meela adeel, Mummy, Hafsat A Fulani buchi, Hafsat A shitu, aunty Ag,💞 Ummul Meenal, Habeeba M, aunty baraka, Mmn Nazir👜* gaskiya bazan iya duka ba kuyi hakuri naga nakusa yin rabin wani paragraphs d'in🤪.
Page *14*
Yana zuwa unguwar ya ganta a k'ofar gida a zaune tayi wanka tayi kwalliya irinta zamani lokacin ba'a gama sanin su concealer ba, amma tasa eyeshado red janbaki tayi kuma jagira.Tana ganin mota a k'ofar gidan su ta shek’a da gudu tana gayawa su Inna yazo kafin ta kuma fita kamar wata saban kamu lokacin harya fito yana rik'e da murfin ya kalleta itama ta kallesa.
Sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda getzner light blue anyi mata dinki na dark blue ya d'ora hula fuskarsa har wani kyali-kyali takeyi kawai INdo ta saki baki da hanci tana kallansa kallo na kurrullah tamkar tana son ganin wani abu ya mik'a hannunsa yana zagaya shi a saitin fuskarta tayi firgigita tare da yin dariya tace.
"Dacta Habubakar wallahi kanada kyau ta6 heyau na ta6a ganin haka."
Murmushi yayi tare da rufe k'ofar ga yara sun fara mai dandazo ya ciro 2k yabasu sannan ya shiga zauran gidan su ta bishi ya tsaya yana kallonta ganin tayi mai wankan dayace tayi harda kwalli sai ya ce.
"Humaira babu gaisuwa? Bafa ki gaida niba."
INdo tace "Au hakane fa ina yini ya gida ya iyaye..?!"
"Lafiya lau baki tambaye ni malam Sadeeq ba why..?!"
"Ta6 narasa wanda zan tambaya hewani malam Sadeeq Allah ya tsare ni wallahi."
Kyaleta yayi ganin bilhakk'i bata son Sadeeq tun lokacin daya hanata atamfa, kallonta yayi yace.
"Ina baba yake?”
Tace "Baya nan."
Abubakar yace "Toh Inna fa?"
INdo tace "tana ciki."
"Toh jekiki ce zanzo mu gaisa da ita."
"Kai dacta Habubakar, kawai kashiga meye na tsayawa ai bazata hanaka ba."
"A'a Humaira ba'ayin haka a musulinci dole sai kinje kin gaya mata."
"Toh hikenan tunda baka yadda dani ba."
Tana magana tana shiga gida, yana jiyo sanda take gayawa Inna sak'on duk maganar da sukeyi yana jiyo su.
"Kai Inna toh meye na saka hijjabi dan nace miki dacta habubakar zai shigo. Lallai saban salo."
Rintsa ido yayi jin yadda INdon keyin magana da mahaifiyarta, lallai yarinyar nan indai yana sonta yadda yake so toh akwai jan aiki a gabansa. Dawowarta kawai ya gani beji motsinta ba, tana dariya tare da wasa da gefen mayafinta tace.
"Tace ka higo an hinfid'a maka tabarma a k'ofar d'aki."
Tana gaba yana bayanta har suka k'arasa ya zauna, daga bakin k'ofar d'akin Inna ta tsuguna suka fara gaisawa. Shiru babu wanda ya sake magana sai gasu Nafeesa sun shigo itada k'awarta suka gaidashi, Abubakar yace ma Inna.
"Inna dan Allah idan babu damuwa ina son ki bani aron su Humaira suyi min rakiya nan cikin gari."
Shiru yaji Inna tayi kafin can kuma yaji tace.
"Toh gata nan ai Nafeesah sai tazo kuje tare harda ita."
"Toh Inna na gode."
Tashi yayi yafita su kuma suka bi bayansa. A baya Nafeesa ta zauna yayin daya kwashe ledojin kayan yasa a k'asa wajan dazata saka k'afa tace ta shiga ta zauna sannan shima ya zagaya drive seat ya zauna tare da tayar da motar suka tafi 'yan kauyan sai gulmarsu akeyi.
Cikin garin Sumaila suka shiga INdo badai surutu ba sai labari takeyi musu sanyin A.c yana ratsata ga k'amshi a cikin motar ta kalli Abubakar tace.
"Dacta Habubakar wannan motar taka akwai sanyi karmuyi mura a bud'e gilahin."
Dariya yayi sannan ya mik'a hannu ya rage A.c ya juya yana kallanta itama shi take kallo yace.
"Humaira ya akayi ne?!"
INdo tayi dariya tana tafa hannuwa tace.
"Meye kuwa, wai Ina zaka kaimu ne hefanan tafiya muke..?"
Parking yayi a bakin titi wajan wani shagon saloon ya kalleta yaga sai kallon window take ya juya bayansa Nafeesa sai bacci take a hankali ya mik'a hannu zai ta6a kafad'un INdo sai kuma yayi saurin janyewa tare da bud'e k'ofar yafita. Zagayawa yayi ya bud'e mata ta fito yace su shiga cikin shagon abar Nafeesah tunda tana bacci suka nufi shagon ya tsaya ta glass inyamurar ta hango su ta fito cikin azama.
"Hey!good evening sir how are you.?!"
"Fine madam how is your business."
"Fine..fine oooh."
INdo tabisu da kallo sai faman tabe baki takeyi ta samu sumintin gurin ta zauna tana kallon titi. Saidai Sadeeq ya gama gayawa madam Gloria abinda za'ayiwa INdo sannan ya kalleta yace.
"Yauwa toh Humaira tashi ku shiga ciki."
INdo ta kalli madam gloria cikin mamaki ta maida kallonta gurin Abubakar tace.
"Mezai kaini wajan arniya dacta Habubakar? Arniya cefa kake cewa naje gurinta, me zata min...?!"
Ganin yadda takeyi ne yasa hankalin Abubakar tashi har mutane sun fara taruwa da k’yar ya satayi shiru yace mata.
"Kayanki zata baki amma tunda bakya so zomu tafi gida."
Da sauri ta nufi madam guloriya tana cemai. "Yo toh ai kaine bakayi min bayani ba."Gloria na gaba tana bin bayanta Abubakar ya girgiza kai sannan ya koma wajan mota yana jiran fitowar Gloria .
INdo kuwa suna shiga gurin taga abubuwa birjic ga manyan madubai ta kalli fuskarta sosai sannan ta fara gyara kwallin daya zazzago mata wajan kumatu Tese yarinyar Gloria ta cewa INdo.
"Sister come and seat here."
Sam INdo batasan da ita ake ba Tese ta kuma yi mata magana still INdo bata juyo ba Tese taja tsaki tare da zuwa ta janyo hannun INdo tare da zaunar da ita a wajan wankin kan sai masifa take da turanci ita kuma INdo tana Hausa.
Cige d'ankwalin Tese tayi taja wani uban tsaki ganin ko tsefewa batayi ba, gashi Mommy d'inta tace tabita a hankali dan wanda ya kawota yace zata iya guduwa. Kibiya tad'auka ta tsefe mata gashi akwai laushi da tsayi saidai babu cika gashi kuma jah ne. Mayukan wanke gashi ta d'ebo sannan ta janyo kan INdo ta malala mata sai mita takeyi har aka gama Madam guloriya ta kuma shigowa hannunta d'auke da riga da takalmi wanda Abubakar ya bata yace abata tasa ayi mata kwalliya.
Lokacin da aka saka kan INdo a dryer taji zafi sai ta saki wani uban ihu wai zafi, Madam Gloria tazo tana d'anyi mata wasa tare da takura mata har aka gama kannan yayi kyau gashi an tura mata shi yayi baki Tese ta nuna mata bathroom a shagwan ta nuna mata tace tayi wanka, INdo tayi da sabulai masu k'amshi gashi ruwan d'umi sannan ta fito sanya da kayan data cire babu wanda ya kulata Tese tayi mata kwalliya sannan aka bata doguwar rigar suka ce ta saka. Duk bayanin da sukeyi mata toh da hannun suke nuna mata tamkar wasu bebaye.
Wata irin had'add'iyar abaya ce pink da belt black sai kwalliyan ma black ta jikin rigan, fitowa tayi daga d'akin bayan tasa saidai jikinta babu bra madam Gloria ta tambaye ta bayan ta nuna mata ta jikinta kasan cewar itama INdo akwa breast d'in ta turo baki tana k'unk'una da alamar dai batada ita.
Babu kunya madam Gloria tafita wajan Abubakar yana zaune suna hira da Nafeesa tace k'anwarsa batada bra amma suna siyarwa ya bada kud'in. Abubakar kunya ta lullu6esa yace toh abata zai had'a a cikin kud'in gyara sannan ta koma aka cire dai-dai size d'inta ta saka suka d'aure mata belt d'in sai ta koma tamkar ba wadda ta shigo d'azu ba. Tese ta sa mata veil bayan ta jera mata ribbon INdo tayi d'as da ita tamkar ba INdo malam Hamza ba.
"Wowww nawawoo see this girl ooooh, you look so beautiful my daughter."
Ita kanta INdo data kalleta a cikin madubi saida ta sake ta6a fuskarta dan a tunaninta ba ita bace, Madam Gloria ta fesa mata turaruka sannan ta kamo hannunta suka fito Tese sai dariya takeyi. Abubakar na ganin sun fito ya mik'e yana kallon INdo k'irjinsa na mugun bugawa, ita kuma ta kasa kallonsa domin wata irin kunya ce da nauyinsa suka dirar mata a lokaci d'aya. Da kyar Abubakar ya iya kallon madam Gloria yayi mata godiya tare da zaro 15k ya mik'a mata ta k'ar6a sai k'ara kod'a INdo takeyi shi kuma ya juya tare da bud'e mata k'ofa ta shiga ta zauna ya rufe.
Cikin tsananin mamaki Nafeesa ke zuro kai tana lek'en fuskarta kafin tace.
"INdo..! Koba kebace ne? Nashiga uku, wallahi kece dan ga fashin gohi nan."
Banza da Nafeesa INdo tayi domin ita kanta tunda aka haifeta bata ta6ajin ta a wani irin yanayi na cikar kamala ba irin yanzu. Abubakar ya kalleta yana lek'en fuskarta shima yayi murmushi tare da cewa.
"Humairah kinyi kyau sosai."
K'irjin INdo ya kuma bugawa kanta ya fara sarawa jitakeyi tamkar an sauyata gabaki d'aya, bakinta kuwa ji takeyi tamkar ansa zare da allura an d'inkeshi ta kasa cewa ko uffan ta kuma kasa kallonshi.
Kunna motar yayi suka fara tafiya sai magana suke mata shida Nafeesa amma tayi shiru, farin ciki takeyi yau gata cikin rigar da ko a cikin mafarki bata ta6a zaton zata sanya taba ga takalmi d'an ubansu tayi shigar da duk kauyen Sani babu wanda ya ta6ayin irinta. Shin mezata cewa dacta habubakar akan wannan abun dayayi mata, shida ba yayanta ba, ba wani nata ba a'a d'an uwane a gurin wani malamin su..!
Saida ya tsaya a wani shago ya siyo musu abubuwan kwalan da makulashe sannan ya nufi kauyen Sani. Daga shi sai Nafeesa kawai suke magana amma ita batayi rigar jikinta kawai take kallo tanajin ina ma salele zaizo yau ya ganta ta zama sabuwa.
A k'ofar gida ya tsaya Nafeesa ta fito ya bata ledojin INdo ma tazo zata k'ar6a ya girgiza mata kai sai da Nafeesa ta dawo ya bata harda ragowar kayanta sannan ya kalleta yace.
"Humaira kina son yin karatu..?!"
Shiru tayi tana faman muzurai, a zahirin gaskiya batada wani sha'awar yin karatu domin tun farko dama batasa shi a cikin tsarin rayuwar taba.
Gani takeyi ma yanzu wace makarantar zatayi dan tafi k'arfin tsefawa sabida duk mate d'inta sunyi candy dan haka ma ta kuma cire san makaranta a zuciyarta. Kallonta yayi yaga yanayinta ya canza ya ciro wayarsa yana yi mata photo wannan kuwa harda su style, ya d'an matsa kusa da kujerarta tare da cewa.
"Matso toh muyi photon tare."
INdo ta matsa suka kusan had'e fuska yayi musu selfie kusan sau biyar yana d'aukar su gaba d'aya sunyi kyau musamman Abubakar dayasan shika-shikan iya selfe. Agogon tsintsiyar hannunsa ya kalla biyar sauran minti uku yace mata.
"Humairah zan tafi sai na dawo please take care."
Murmushi kawai tayi mai sabida bata san abinda ya fad'a ba bayaga (zan tafi sai na dawo). Ya zaro 5k ya mik'a mata tana kallonsu ta wutsiyar ido tana son k'ar6a tana jin wani iri ya d'ora mata a kan cinyarta ta d'auka zata bud'e k'ofar yayi saurin rufewa tare da cewa.
"Humairah baki min godiya bafa zaki tafi, haka akeyi daman."
Tayi saurin rufe idanu tare da cewa.
"Kayi hakuri inata son yima na manta, angode Allah ya k'ara bud'i."
Yace "yauwa kokefa harnaji dad'i, duk wanda yayi miki kyauta ki dinga ce mai angode kinji ko?!"
Tace "Toh zanyi sai anjima yaushe xaka dawo garin mu?!"
Da sauri ya kuma kallonta jin tana neman ya dawo, cikin wata irin murya yace.
"Humairah kina son na kuma dawowa?!"
INdo ta d'aga kai alamar eh yayi murmushin jin dad'i sannan yace.
"Toh shikenan wani satin zan dawo amma ki dinga kwalliya gashi can na siyo miki kayan kinji..?!"
"Toh Nagode ka kaida gida."
"Zasuji amma bakice nagaida malamin kuba."
Tace tana yatsina fuska.
"Ai bayida kirki da kaine bakada kirki amma yanzu shine bashida kirki."
"Toh kiyi hakuri ya dena kinga 'dan biyu nane."
"Naji na dena kace ina gaidahi."
"Zaiji a gaiheda Inna da baba."
Yafad'a cikin kwaikwayon maganarsu, ta fita daga motar lokacin su Uwani halilu sunzo gulma, shi kuma yaja motarsa yabar unguwar zuciyarsa na kudurta mai son auranta.
0 comments:
Post a Comment