Da sallama suka shiga falon Sarki Hasheem, yana zaune
abisa kekenshi yana sana,ar tashi wato tunanin
Fulaninshi, matsawa kusa dashi Sarki Qaseem yayi.
Kafadarshi ya dafa ahankali yadago yana kallonshi, wasu
siraran hawaye suka fito daga idanunsu su duka biyun,
alamu Sarki Hasheem yayi mashi da lafiya? Murmushi
yayi mashi yakama kekenshi yafara turawa.
Seda yakawoshi kusa da su Waziri sannan ya sake shi,
shide kallonsu kawai yakeyi, Jakadiya Safeeya takamo
hannun Fulani wadda take boye abayanta, tafito, adede
lokacin dasuka hada ido da Sarki Hasheem Fulani taji
kanta yayi wani irin sarawa.
Shi kam Sarki Hasheem besan lokacin daya mike tsaye
ba bakinshi yana motsi yana nuna Fulani da hannu ba,
itakam nan take ta kwala wani irin ihu tafadi kasa, shima
jikinshi ne, yafara rawa yazube kasa idanunshi suna fitar
da kwallah.
Dasauri suka isa gurinshi, Jakadiya Safeeya kam gurin
Fulani ta nufa, sede tana tabata taji babu alamun
numfashi atare da ita, Waziri yakama Sarki Hasheem
yadora kan cinyarshi jikin sarki se rawa yakeyi yana kara
nuna Fulani da yatsa, da karfi yace Fulani.
Jakadiya Safeeya takalli su Waziri tana kuka tace bata
numfashi fa. Sarki Qaseem wanda duk yagama rudewa,
yama rasa ina zeje, ya kalli Waziri yace yazamuyi ne?
Waziri yace kawai muwuce dasu duka asibiti ina ganin
zefi sauki.
Sarki Qaseem yace ma Jakadiya taje takira Suhailat tazo
sutafi tare, anan Waziri yakira wasu fadawa suka kama
Sarki aka kaishi mota, Sarki Qaseem kuwa da kanshi
yadauki Fulani ya kaita mota. Waziri yatara manyan
fadawa kusan guda 20 yace nabaku umarnin bayan
fitarmu kada wani ko wata yakara fita koya shigo
masarautar nan, harse mundawo idan nabada umarni.
Jakadiya Safeeya kam tana zuwa part din Gimbiya
Suhailat, jikinta yafara rawa, dan batasan dawane ido
zata kalleta ba, ganin zata bata masu lokaci yasa kawai
tashiga, alokacin Gimbiya tana zaune falo tabuga
tagumi. Saurin tashi tayi tana kallon Jakadiya cike da
fargaba tace.
Dan Allah kada kicemun narasa Yarima dan Allah,
sunkuyar da kai tayi tace baki rasa shiba, sede
memartaba ne yace infada maki kifito mutafi asibiti. Ai
dasauri taje tadauko hijabinta tafito suka nufi mota, tana
zuwa suka shiga wata mota ita da Jakadiya, su kuma suka
shiga dayar Wazirri jasu zuwa asibiti.
Azaune, Areef yake bisa gadon beauty ya rike hannunta
idanunshi suna fitar da hawaye, kara kallonta yayi yace
dan Allah beauty kitashi haka nan, wlh zan iya samun
matsala idan har baki farka ba. Haisam ne ya matso kusa
dashi yadafa shi, yace kayi hakuri abokina zata samu
lafiya, bagashi kana kallo numfashinta yna tafiya dede
ba. Addu,a zaka yimata zata tashi.
Suna zuwa aka nufi emergency dasu, sede shi Sarki wani
daki aka kaishi tunda dama likitan yasan cesa dinshi,
akan Fulani likitoci suka taru suna bata temakon
gaggawa.
Gimbiya Suhailat da tambayoyi suka cika cikinta, gashi
tana son ta tambayi Jakadiya Safeeya amma kunya ta
hanata, ganin haka yasa Jakadiya tace Gimbiya muje kiga
jikin Yariman mana, kamar jira takeyi ta tashi cike da
kunya tace muje de infara ganin jikin surikar tawa ko?.
Bakaramin dadi Jakadiya taji ba, dajin furucin Gimbiya,
tace to muje, Gimbiya tace dan Allah kiyi hakuri da
abinda namaki, wlh idona ne yarufe, har na furta maki
wadan nan maganganun, amma kiyafe mun, kuma
Hubby yayi mun bayanin komai nagane.
Tabbas soyayya baruwanta dawani mulki ko sarauta,
kudi ko talauci, wlh nayarda da zabin Yarima dari bisa
dari, ada kam nayi kuskuren cewa dole dan sarauta seya
auri jinin sarauta, segashi tun ba aje ko inaba Allah ya
nunamun ishara, kuma nayarda da abinda nagani.
Murmushi Jakadiya tayi tace haba ai babu komai, nice
yakamata innemi yafiyarki, dan na rufe maki abubuwa
da yawa wanda ba laifina bane, amma muje kiga jikin
nasu, daga baya zakiji komai.
Hannun beauty dake cikin na Areef ne yafara motsi,
saurin kallonta yayi yana fadin Haisam wlh beauty motsi
takeyi, kara matsawa kusa da ita sukayi, Ayman tace aiko
Yaya ga idonta nan yana juyawa, Areef yace beauty bude
idonki nine akusa dake, babu wanda ze rabamu, dan
Allah kitashi Abba ma yana dubaki kuma shima ya
amince. Kallon Ayman yayi hawaye suna zuba a idonshi
yace dan Allah kuce ta tashi.
Adede lokacin da su Gimbiya suka turo dakin babu
wanda ya kula dasu dan hankalinsu yana gurin beauty,
tsaye Gimbiya tayi tana kallonsu, gaba daya tausayinsu
yakamata, gani takeyi duk itace tasasu awannan halin,
matsawa Jakadiya tayi kusa dasu.
Adede lokacin beauty tabude idonta, bata sauke su akan
kowa ba se akan Gimbiya Suhailat, ai kawai gani saukai ta
tashi cikin tsorata ta kwala kara daga karshe tace
Mama............ gaba daya dakin seda suka firgita dajin
abinda beauty tayi, saurin shigewa jikin Areef tayi jikinta
yana rawa, kara rungumeta yayi yana shafa bayanta.
Se alokacin ya juya yaga Momynshi ce ashe beauty
tagani, saurin daure fuska yayi yace Momy dan Allah
kifita, kina ganin yanda beauty ta tsorata daga ganinki,
tunda beauty take bata taba magana ba, amma ayau ta
dalilin tsoranki datakeyi gashi magana tafito abakinta.
Dan Allah kifita tunkafin takara ganinki tarasa ranta, wlh
nima mutuwa zanyi. Cike da tashin hankali Gimbiya
tajuya tayi hanyar waje tana kuka, Jakadiya tayi saurin
kamota tana fadin kada kifita kidawo zanyi mata
magana, kai kuma Yarima ka nutsu kasan dawa kake
magana.
Jawota tayi suka matso kusa da gadon beauty wadda
take kwance ajikin Areef, ahnkl Jakadiya ta dafa
kafadarta tace tashi kiji wani abu Yar Baba kinsan de
bazan cutar dake ba ko? To idan har kinyarda da hakan
inaso kitashi kuma kada kiji tsoron komai, Gimbiya tazo
dan tadubaki kuma tafada maku tayarda zakuyi aure
keda Yarima.
Ai dajin haka beauty ta tashi sede bata rabu da jikin
Areef ba, shikam murmushi kawai yakeyi, yana kallon
Momynshi. Kusa da beauty Gimbiya ta matso takama
hannunta, tace diyata kiyi hakuri kinji wasa nakeyi maku,
babu wanda ze rabaku, nima inasonki, jawota tayi ai
kamar jira takeyi tashige jikin Gimbiya, ai gabavdaya
dakin aka sa dariya.
Da wani irin ihu Fulani ta farka tana fadin wayyo nashiga
3 zasu kasheni, haka tayi ta ihu, ganin taki natsuwa
likitocin suka leka suka kirawo su waziri, addu,a Waziri
yayi ta tofa mata shida Sarki Qaseem, cikin lokaci
kankani ta nutsu, sede gaba daya afirgice take.
Wani likita yace da alama tunaninta yadawo, sede
agskiya atsorace take, kila mutanen dasukayi mata
sanadiyar shigarta wannan halin sun tsoratata sosai, dan
haka shawarar dazan baku idan har akwai malami, to ku
kaita yayi mata addu,a insha Allahu zata dawo dede.
Waziri yace mun gode sosai, amma kana ganin za,a iya
sallamarta ayau? Likita yace kwarai ma kuwa, ai babu
sauran wani abu dayake damunta, dan ta dade tana shan
magani, duk da ba mune muka bata ba, amma mungane
ana bata magunguna masu kyau. Sarki yace mungode
bari muduba jikin Yaya.
Shima Sarki Hasheem jikinshi yayi sauki, dan soyake
abarshi yaje yadubo Fulaninshi, amma likitan yahana,
turo kofar dakin sukayi tare da sallama, aibyana ganinsu
Sarki yace ina Fulani ya jikinta? Gaba daya seda sukayi
mamakin maganar data fito daga bakin Sarki, dan yau
shekaru 18 da watanni beyi magana ba. Da sauri Srki
Qaseem yaje gurinshi yana murmushi ya rungumeshi
yana fadin Yaya wlh itama ta warke ayau ma zamu koma
gida.
Cike da fara,a Sarki Hasheem yace da gaske? Waziri yace
sosai ma, runtse ido yayi wasu hawaye suka zubo mashi
yace Allah nagode maka daka dawomun da Fulanita, ya
Allah katona asirin duk wanda yayi ma Fulani hakan ni
kuma nayi alkawarin wlh bazan barshi ba.
Likita yayi gayran murya yace Alhmdull, dama nace
maku yawancin irin wannan matsalar idan har mutum
yahadu da ita ta dalilin rasa wani abunda yakeso, to aduk
lokacin daya ga wannan abun alokacin da beyi
tsammanin ganinshi ba, to inhar Allah yaso ze iya samun
sauki.
To hakane yafaru da memartaba, jikinshi yasamu lfiya,
nan da wani lokaci zefara tafiya kamar kowa, amma
kada yayi garaje, gurin fara tafiya, yanzu haka zamu
bashi sanda wadda zata temaka mashi gurin tafiya.
Kuma zaku iya tafiya ayau, sede dole seyasha
magungunan dazamu bashi, suna zasu temaka mashi
jikinshi yayai kwari.
Sarki Qaseem yace yanzu kam tunda farin cikinshi
tadawo ai ba magani ba, komai zesha. Dariya suka sa
gaba daya, Sarki Hasheem yace yanzu de ku kaini inga
Matata ko kuma intafi da rarrafe, dariya sukayi likita
yace a,a ga kujera nan kuturashi yaga farin cikinshi.
Kwance take idanunta akulle, amma ba bacci takeyi ba,
tanaso tayi tunanin,sede data fara setaji kanta yana
sarawa, da sallama suka shigo, lokaci guda ta bude
idonta, bata sauke su ako ina ba, se akan mijinta, jan jiki
tayi ta tashi zaune, fuskarta dauke da murmushi, turashi
sukayi har kusa da gadonta, sannan Waziri yakamo
hannun Sarki Qaseem sukayi waje.
Hannunshi yasa yakamo nata, fuskarshi dauke da
murmushi, saukowa tayi daga bisa gadon ta durkusa
kusa dashi ta shige jikinshi tana kuka, kara rungumeta
yayi yana shafa bayanta.
Dakin beauty suka nufa, azaune suka samesu se fira
sukeyi, suna dariya, beauty kuwa tana jiin Gimbiya, se
dariya takeyi, sede haryanzu tun maganar datayi tafarko
bata kara cewa komai ba, Areef ma kasa matsawa yayi
yana manne da ita, wani irin farin cike ne yaratsa zuciyar
Sarki Qaseem ganin yanda yasamesu.
Sarki yace waini ina Areef marar lafiya ne, munje
dakinshi mabu ganshi ba? Dariya suka saka, Areef yace
Abba ai nawarke, Gimbiya tace ba dole ya warke ba,
tunda yasamu abinda yakeso, dariya sukayi. Waziri yace
ai seku tashi mufara shirin tafiya gida tunda kun warke
dare yayi sosai. Sarki yace gaskiya kam, yaude asibitin
tazama ta masoya.
Haka likita yabasu sallama tare da magungunan Sarki
Hasheem dana Fulani, suka kama hanya zuwa gida, sede
haryanzu Sarki Hasheem bega beauty ba, dan seda suka
fara shiga mota sannan suma suka fito. Lokacin dasuka
isa gida kuma dare yayi sosai, hakan yasa Gimbiya taja
Ayman da beauty tace ma Jakadiya kema kitaho
mukwana anan kisan de Yaya baze baki Matarshi ku
kwana tare ba. Dariya tayi tace hakane, muje kawai.
Kallon su Areef tayi tace Haisam kaima kafada ma su
hajiya anan zaka kwana gurin budurwarka kada suji
shiru.
Rufe fuska yayi yana dariya yace ai nafada masu, tace
yauwa maganata tayi dede kenan? Adede lokacin da
motar su Waziri da su Sarki tashigo harabar gidan, suna
haskawa jikin wata bishiya suka haske fuskar Medaki, ai
dasauri takara labewa, domin ta dade agurin jiran dama
kawai takeyi tasamu tagudu, hannunta rike da dan
kullinta, sede babu wanda yaganta daga Sarki Qaseem ,
se Waziri wanda dama shine yake jan motar, Sarki da
Fulani suna baya, wani murmushi Waziri yayi , yawuce.
Bayan yayi parking motar yayi saurin fita yakirawo masu
gadin gidan, ai Medaki tana ganin haka tayi surin
komawa part dinta, kara jaddadamasu yayi akan su kula
da tsaron gidan, kuma akulle kofa babu wanda ze kara
shigowa bare fita.
Haka suka raka Sarki da Fulani har falo, Fulani ta kalli
Waziri tarike kanta kamar me tunanin Sarki yace lafiya
Fulani ko kanki yake ciwo? Kai ta girgiza, can kuma tayi
saurin bude ido tace ina yarinyata? Sarki yace kina nufin
kin haifi cikin jikinki kuma yana raye? Kai ta girgiza tace
dan Allah kubani diyata wlh nasan na haihu, kada
kucemun ta mutu.
Waziri yace ki kwantar da hankalinki, diyarki tana nan,
araye asalima babu abinda yake rabaku, atare kuka
zauna, babu abinda yasameta, sede yanzu tana gurin
Gimbiya Suhailat, kuma nasan sun kwanta kinga dare
yayi kibari seda safe zaki ganta.
Murmushin jin dadi tayi ta daga mashi kai, sallama
sukayi masu suka fita. Sarki yace turani muje daki muyi
wanka, murmushi tayi tafara turashi, atare sukayi wanka
tana temaka mashi, bayan sunfito sukayi sallah sannan
suka kwanta suna me cike da farin cikin ganin junansu,
sun rungume juna kamar za,a rabasu.
Suna fita Waziri yakalli Sarki yace kaga abinda nagani
kuwa? Sarki yace nagani, kabari kawai Allah yakaimu
gobe nasan zamu gano sauran munafukan gidan nan.
Sallama yayi mashi kowa yanufi part shi.
Washe gari da misalin karfe 10 Malam na darazo ya iso,
aka saukeshi amasauki, bayan yagama cin abinci aka
kawoshi fada, alokacin su Sarki Hasheem da fulani sun
iso gurin tasha kyau sosai, tana zaune agefen Sarki,
bayan sungama gaisawa da Malam, ya tambayi jikinshi
yace Alhamdulillahi ai jiki yaya sauki, dama akwai dalilin
dayasa kuma yanzu nasamu maganin akusa dani.
Dariya malam yayi yace to mungodema Allah, amma
abinda nakeso da akai, sekayi hakuri da duk abinda
zakaji ko zaka gani, ayanzu, nasan zaka shiga cikin
damuwa, amma munaso mukawo karshen muna fukan
gidan nan, kuma kaima nasan zaka so kasan wadan da
sukayi ma Fulani haka.
Sarki yace hakane, babu komai, Allah yasa inji alkhairi.
Malam yace amin, adede lokacin su Gimbiya Suhailat
dasu beauty, Ayman, Jakadiya , Areef da Haisam suka
shigo, ai beauty tana ganin Mamanta da gudu taruga
tafada kanta tana dariya.
Itma tana ganinta tayi saurin rungumeta tna fadin
yarinyata, Sarki da mamaki ya kamashi dasauri ya kalli
fulani yace wannan ce diyata? Kai tacdaga mashi, besan
lokacin da kwalla tacika mashi ido ba.
Waziri yabada umarnin afito dasu Jakadiya Karima,
sannan yasa Jakadiya Safeeya takirawo su Gimbiya
Zakiyyah da Medaki, wani bafade yasa yakirawo Baban
Fulani da Baban Darazo, kowa yasamu guri yazauna yana
kiran abinda za,ayi.
Nima nace bara in anje alkalamina injira shigowar su
Sarkin Fada.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 100⚜105Cikin isa da mulki Gimbiya Zakiyyah tashigo, ko sallama
ma da kyar tayi, guri tasamu gefen Sarki tazauna, dan
batasan yasamu lfy ba. Kallonshi tayi fuskarta dauke da
murmushi tace barka da asuba memartaba yajikinka?.
Sanin ko anyi mashi magana baya amsawa yasa tadauke
kanta bata kula da motsa bakin dayayi ba. Kallon malam
tayi tace malam barka da asuba, yace yauwa kintashi lfy.
Medaki ce tashigo jikinta duk yayi sanyi kamar
antsamota daga ruwan zafi.
Akusa da bakin kofa tazauna duk tagama rudewa, cikin
rashin jindadin abinda tayi Sarki Hasheem yace medaki
dawo nan mana. Ai Gimbiya Zakiyyah batasan lokacin
datace yaushe kafara magana memartaba?.
Murmushi yayi kawai yayi shiru, haryanzu babu wanda
ya kula dasu Fulani, bayan medaki tazauna kusa da
Gimbiya Zakiyyah, kallonta tayi tadan duko kusa da
kunnanta tana murmushin mugunta tace ina fatan kinyi
kwanciyar karshe agidan sarauta? Seki shirya karbar
hukunci.
Sallamar su Sarkin fada da Jakadiya ne tasa Medaki tayi
saurin tashi tana hawaye. Wani murmushin jindadi Sarki
Hasheem yayi, ganin Jakadiyarshi, dama yana so ya
tambayeta domin ita yakeso yayima albishir na samun
diya da yayi, domin yasan tana daya daga cikin masu son
yasamu karuwa.
Da fara,a yace Jakadiya matsonan infara baki albishir
medadi, ai jitayi kamar yan hanjin cikinta zasu fito,
kamar ance Fulani tadago kai, ai tana dagowa sukayi ido
4 da Sarkin fada. Wani irin ihu tasaka ta ture beauty,
tashi tayi kamar zata ruga tana fadin gashi nan yazo zasu
kasheni.
Waziri da Sarki Qaseem bakaramin mamakin abinda
take fada sukayi ba, duk da dama suna zarginshi.
Jakadiya Safeeya da Gimbiya Suhailat ne suka rike Fulani,
Sarki Hasheem kuwa jiyayi kamar yatashi, gaba daya
jikinshi rawa yakeyi, ganin haka Sarki Qaseem ya matsa
kusa dashi yadafashi yana bashi baki.
Gimbiya Zakiyyah kuwa batasan lokacin data mike tsaye
ba tana nuna Fulani, Medaki kuwa kukanta har yafito fili,
duk da sanyi da falon yakedashi be hana zufa keto mata
ba. Gaba daya sauran mutanen Falon sun shiga rudani,
Areef kuwa matsawa yayi kusa da beautynshi yari keta
sosai, yadora kanta saman kafadarshi, dan yasan
batason hayaniya, ita kam kuka tasaka tunda Fulani ta
tureta.
Malam da kanshi ya matsa kusa da Fulani datake kwance
akan cinyar Jakadiya tana ta kuka, addu,a yafara yimata
yana tofa mata. Sarkin fada kuwa da Jakadiya zaman yan
bori sukayi suna rarraba idanu.
Sarki Qaseem ne yayi gyran murya sannan yace ya isa,
kowa yasamu nutsuwa kuma azauna domin muyi abinda
yakawomu. Malam yadade yanama Fulani addu,a kafin
tasamu tadawo cikin nutsuwarta. Sarki Hasheem kam
gaba daya kanshi yagama daurewa shiru kawai yayi yana
karanta addu'oi, hakan yasa yafara samun nutsuwa, sede
haryanzu idanunshi suna kan Jakadiyarshi data kasa
kallonshi.
Bayan kowa ya nutsu Waziri yatashi yace ma malam
yabude masu taro da addu,a. Bayan angama Waziri
yafara magana. Alhamdulillahi da farko zanfara dayima
Allah godiya daya kawomu wannan rana mecike da farin
ciki da kuma bakinciki.
Da farko zanfara gabatar da matar Sarki, kuma amarya
agurinshi wadda akafi sani da Fulani. Bayan shekaru 18
da wasu watanni bata gidan nan, inda aka samu wasu
marassa imani suka shigo har cikin dakinta suka
dauketa........ Sallamar Su Baban Fulani ce ta tsaida Waziri
daga jawabin dayakeyi.
Fulani tana ganin Babanta ta tashi tanufi gurinshi, ai
shima yana ganinta yabude hannuwa tashige jikinshi
tana kuka. Shima kukan yakeyi seda suka bama kowa
tausayi. Bayan sun natsu suka zauna, Baban beauty kuwa
gaba daya mamaki yagama cikashi ganin abin al,ajabi.
Waziri yaci gaba da magana. Kamar yanda nace ba,asan
wadan da sukazo suka dauke Fulani ba, amma tunda
Allah yasa gata tadawo kuma tana cikin hankalinta.
Kuma zata iya nuna wadanda suka aikata haka akanta to
duk wanda yakasance cikin masu laifi, tabbas ze fuskanci
hukunci me tsanani, kuma kowane irin matsayi gareshi a
masarautar nan.
Ai kamar daga sama sukaji Medaki ta tashi tana fadin
shikenan munshiga 3 wlh, ba laifina bane, duk kutsaya
wlh zanfadi iyakar gaskiyar dana sani. Gimbiya Zakiyyah
tayi wani murmushi aranta tace lallai zaki sha
mamakina,ni nasan babu wanda zeyarda idan kikace
hadani.
Waziri yayi murmushi yace rankiyadade munajinki.
Tashi tayi tana kuka tafada masu duk abinda sukayi
itadasu Gimbiya Zakiyyah, akan batan Fulani, sede bata
fada masu abinda suke aikatawa da Sarkin fada ba.
Gaba daya falon aka dau salati, Sarki Hasheem kuwa
zama yayi kamar dutse, kallon Jakadiya Karima kawai
yake idanunshi na zubar da ruwa. Waziri yace da kyau,
tashi Gimbiya Zakiyyah tayi tafara magana cike da mulki.
Inada ja agame da maganar Medaki, wannan maganar
datayi kawai tafa deta ne sbd wani dalilinata, amma
kowa yasan bana shiga harkar talakawa taya za,ayi
inhada baki dasu mu aikata irin wannan shirmen.
wanda kowa yasan duk wanda yafito daga gidan sarauta
bazeyi haka ba. Idan kuma har tace dani, ni nayarda
sukawo sheda, idan har aka sameni da hannu aciki
nayarda da duk wani hukunci daza,amun.
Waziri ya jinjina kai, alamar gamsuwa, ya kalli Medaki
yace kina da wata shedar dazata nuna mana tana da
hannu acikin abinda kika fada? Wata zufa ce takara keto
mata, hawaye suna zuba a idonta tafara girgiza kai, tace
a,a amma wlh dama tace zan gani....... kamar daga sama
Sarkin fada yace nine shedar akwai ta acikin wannan aiki.
Kusan ma itace shugabarmu domin ita tasamu yin
wannan aiki, kuma ni inada shedar dazata nunama kowa
abinda ma bakusani ba, dama na ajeta sbd irin wannan
rana. Ai Gimbiya Zakiyyah batasan lokacin data sauko
kasa daga kan kujerar datake ba.
Anan Sarkin Fada yatashi yace tabbas ni nasan ayau
asirina yagama tonuwa, dan haka banga dalilin bata
maku lokaci ba, nasan Allah ya dade yana aramun rana,
sede inaso kuyi hakuri da duk abinda zakuji, bakomai
bane yasani aikata haka se SON ZUCIYA.
Wadda azamanin nayanzu shine abinda yake dawainiya
da mutane da dama, wanda kuma bakowa bane yake
saka mana son zuciya se shedan, da kuma mu kammu
idan muka kasa tsarkake zuciyarmu.
Ban kasance mutum nagari ba a masarautar nan, na
dade ina aikata abubuwa da dama, sede babu wanda
yasani, harzuwa yanzu. Alokacin da aka haifi Yarima
Areef, babban dalilin dayasa najawoshi jikina shine dan
insalwantar da rayuwarshi, yazamana beda amfani
arayuwa gaba daya.
Ada nayi niyar kasheshi sede shakuwar damukayi tahana
ni, duk da Jakadiya Karima taso akasheshi, nine na hana.
Babu irin maganin da ban bashi ba dan kawai inga
yazamo dolo agidan nan amma hakan beyuwu ba, abu
daya nasan yayi tasiri ajikinshi shine yanda bedamu da
sarauta ba.
Alokacin daya girma se abun yadawo kaina, tunda
yadawo daga karatu na lura bayason ganina, hakan yasa
naja baya dashi. Amma sanin naci ribar cire mashi
sarauta aranshi hankali na ya kwanta.
Wannan kenan.
Bayan Jakadiya Karima tazo tasameni akan Gimbiya
Zakiyyah tana nemana, bayan naje ita da Medaki suna
zaune tafadamun abinda takeso inyi, sunaso insan yanda
zanyi inhallaka Fulani da abinda ke cikinta. Aranar da
dare itace agurin Sarki, hakan yabamu damar shiga
dakin Fulani mu biyu, nina fesa mata abinda yake sa
mutum bacci, sede ban fesa mata ba sebayan
muntasheta, alokacin taganni seta fara kokarin yimana
ihu, hartaji mani ciwo afuska, ganin za,a jimu ne yasani
fesa mata maganin, nan take tayi bacci.
Kamata mukayi muka fita da ita, muka sata mota, dama
munhada baki da masu gadin gate su 2, wato Lado da
Mati, hakan yasa suka bude mana kofa muka fita. Munyi
tafiya menisa dan seda mukaje wani daji dayake bayan
garin Darazo kusa da wata Mabarta, anan muka wurgata
cikin wani rami.
Sede wanda muka aikata laifin dashi banganshi anan ba,
amma inaso ashigomun da amintaccen bawan Sarki
Hasheem me kula da komai nashi nacikin gida, shine
wanda yatemaka mun mukayi wannan abun.
Sarki Hasheem runtse idonshi kawai yayi yana karanto
addu,a dan zuciyarshi zafi takeyi, jiyake kamar zata fito.
Ganin haka Malam yasa aka miko mashi ruwa yayi
addu,a aciki yabama Sarki Qaseem wanda shima kukan
yakeyi, yace yabashi.
Dakin yayi shiru sautin kukan mutane kawai akeji,
jisukeyi kamar almara ce ake fada masu. Bayan anshigo
da bawan, anan yaxube yana kuka, yace dan Allah
kumun rai wlh Son Zuciya ne da kwadayin abun duniya
suka kaini da aikata wannan abu. Waziri yace haka kowa
yake fada Son Zuciya, Ai kowa yasan son Zuciya bacinta.
Sarkin fada yafiddo wata karamar waya daga aljihunshi
yamika ma Waziri yace wannan shine shedar dazata
nuna maku akwai sa hannun Zakiyyah acikin duk wani
munafunci da akayi, bazan kirata Gimbiya ba sbd tazama
tamkar mata agurina. Saurin dafe kai Sarki Hasheem yayi
dajin abinda Sarkin fada yafada.
Wata waya waxiri yaciro yajona ajikin wayar yahada da
T. V ya kunna kowa yamaida hankalinshi akan t,v. Tun
daga lokacin dasuke zaune afalon Gimbiya Zakiyyah tana
fada masu yanda za,a kawar da Fulani, da duk wani
munafunci dasukayi, harzuwa lokacin daya fara neman
Medaki, tunda Sarki yaga sunfara aikata masha,a yarufe
idonshi, aranshi yana fadin wato dama karya medaki
tamashi babu wani fyaden da akayi mata, dama can yar
iska ce. Areef kuwa yahana beauty ma ta kalli abinda
akeyi, ya kwantar da ita akan cinyarshi yana shafa mata
kai, daga haka tayi bacci.
Babban abinda ya dagama kowa hankali lokacin da aka
nuno sanda suka fara aikata masha,a da Gimbiyyah
Zakiyyah. Salati kowa yafarayi, hakan yasa Sarki yabude
idonshi, sede yayi dana sanin ganin abinda matarshi da
bafadenshi suke aikatawa. Waziri yasa hannu yakashe
wayar.
Shiru kowa yayi se kukan Gimbiya Zakiyyah dana medaki
kawai akeji. Jakadiya Karima ta tashi tace wlh shima
akwai abinda befada maku ba, idan bazaku manta ba,
alokacin da za,a nada Sarkin fada bashi bane aka zaba
ko? Waziri yadaga kai. Nan Jakadiya tashiga basu labarin
da Sarkin fada yabata.
Mamaki yakama kowa jin irin abinda sarkin fada ya
aikata. Hayanice tacika falon. Bayan kowa yanutsu,
Waziri yace lallai babu abinda zamuce sede muyi godiya
ga Allah wanda shine yake tsaremu aduk inda muke.
Tabbas akace dazama da makiyi gara zama da barawo,
kuma dama ance makusan cinka shine makashinka.
Tabbas kunso kashe abinda Allah yaso yafito duniya,
sede babu wanda ya isa ya aikata wani abu seda izinin
Allah. Matar da kukaso kashewa da diyarta gasunan
araye. Kallon Areef yayi yace daga matar taka kowa
yaganta.
Murmushi yayi dan seyanzu yafara fita daga duhun
dayake ciki, tashin beauty zeyi Malam yace abarta, zata
tashi da kanta. Kowa mamakin ganin beauty yakeyi wai
itace diyar Fulani, Sarki kam wani irin sanyi yaji yana
ratsashi duk da damuwar datake ranshi.
Waziri yace akwai bayanin da Malam zeyi mana kafin
afadi irin hukuncin daza,ayi ma kowa. Amma zamuje
hutu daga nan zuwa bayan azahar dan sallah tagabato,
wasu fadawa yasa suka tasa keyar su Gimbiya Zakiyyah,
Medaki dasu Jakadiya yace atsaresu. Kuma yasa suhada
da mati da Lado.
Kuka kawai sukeyi. Sarkin fada kuwa murmushi kawai
yakeyi.
Matsawa yayi kusa da Gimbiya Zakiyyah yace kinsan
akullum tunanin yan sarauta akullum iya karshi harshe,
dan basa amfani da tunaninsu sede na bayinsu. Kinga
koyanzu ya isa kigane banbanci tsakanin Bawa da me
mulki. Kuka tasaka, aka turasu zuwa kurkutu.
Nima yakamata inhuta haka kafin sudawo.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady).
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 105⚜110
Zaune suke gaba daya harda masu laifi, zuwa wannan
lokacin idanunsu haryagaji da zubar hawaye. Sarki
Hasheem ya kalli Gimbiya Zakiyya, duk tafita hayyacinta,
har seda tabashi tausayi dan yasan halin mahaifiyarta
idan hartaji abinda tayi tabbas zata saba mata.
Kawar da kanshi yayi ya kalli beauty wadda take
haryanzu ajikin Areef, tunda Fulani ta tureta haryanzu
taki kara kallonta kuma koda aka dawo sallah agurin
Areef ta tsaya, shikam dama haka yakeso, yariketa kamar
ance za,a kwaceta. Dan bemanta da halin data shiga ba
lokacin da Momynshi tayi mashi fada.
Malam yayi gyaran murya yace Alhamdulillahi Allah
yakawomu abinda na dade ina fatar Allah yakawomana
karshen shi, tabbas masarautar nan tashiga tashin
hankali da rudani, wanda zance bacewar Fulani agidan
nan tamkar saukowar wani haske ne wanda yazo ya
haske duk wani duhu dayake gidan nan. Kuma ya haska
duk wasu munafukai dasuke tare da mutanen gidan.
Abin mamaki wai ace wanda kayarda dashi yanzu
aduniya shine yake cutarka. Gaskiya nayi matukar girgiza
dajin wadanda suka aikata wannan ta,asa wai
makusantan Sarki ne, acikinsu kaf babu wani bare.
Dama haka duniya take, duk wanda zakayima hassada
tamkar kana kara kusan tashi da ubangiji ne, domin
tunda annabi yasamu makiya to babu wani dan adam
din daze iya kubuta daga sharrinsu.
Sede abinda nakeso inkara tunatar daku, shine addu,a
domin itace makamin mumini, duk da ake cewa bawa
baya iya kaucema kaddararshi, amma idan muka rike
addu,a babu abinda bazata yimana ba.
Addu,a takan canza sharri yazama khairi, kuma tanasa
tsanani yazama sauki, dan haka koda Allah ya kaddaro
maka wata kaddara marar kyau, idan har karike addu,a
abun ze iya zo maka dasauki. Arayuwa baka taba gane
makiyinka, harse ranar da asirinshi yatonu.
Agskiya Sarkin Fada kabamu mamaki sosai, da irin
abubuwan damukaji ka aikata, ba kowane me imani
bane ze iya aikata abinda ka aikata. Kaci amanar kanka,
addininka, iyayenka, matarka, da kuma Ubangidanka.
Duk irin halaccin dayayi maka arayuwa, seda ka
ha'inceshi, kashiga gonarshi har 2, duk da haka bata
isheka ba seda kayi sanadiyar rugujewar farin cikinshi,
tahanyar kauda abinda yake matukar so, kaso ka halakar
dasu amma Allah be baka iko ba.
Ko kasan ta dalilinka irin ukubar da Fulani da diyarta
suka shiga? Mezaka cema Allah aranar gobe kiyama idan
yatambayeka akan amana? Ko kasan kalar abincin
dasukaci atsawon shekaru 18 acikin MAKABARTA?
Ta dalilinka matar da babu ruwanta, bata yima kowa
komai ba, amma saboda SON ZUCIYA irin taku kaida
mabiyanka kunsa baiwar Allah tahaihu a MAKABARTA.
Yarinya ta tashi a MAKABARTA. Bata san kowa ba se
Mamanta da kaburbura, da bishiyoyi.
Wancen bawan Allah da kuke ganinshi agidan nan badan
kowa yake zaune ba sedan farin cikin yarinyar da kukaso
ku hanata zuwa duniya. Shine mutum na 2 daya
temakeso, wanda badanshi ba haka Yarinya zata girma
har shekaru 18 amma batasan komai ba, kuma ita ba
hauka ba, barashin lafiya ba.
Kawai saboda tsabar SON ZUCIYA irin taku, bara infada
maku abinda bakusani ba, kuma zakusan cewar duk
zakaran da Allah yanufa da tsara to ko ana muzuru ana
shaho se yayi.
Idan bakusani ba aranar da kuka wurgar da Fulani acikin
dare kuka wurgata cikin rami, to aranar ta haihu, kunsan
suwa Allah yaturo mata kawai dan yanason yanuna
maku baya bacci? Wasu bayinsa ne, kuma yan uwa
musulmai, wadan da suka fito daga jinsin aljanu.
Akusa da fadarsu kuka wurgata, kuma cikin ikon Allah
alokacin suka temaka mata harta haifi diyarta acikin
koshin lafiya. Zakusha mamaki idan nabaku labarin da
daya daga cikin aljanun, wanda yakasance shugaba
agurinsu, shine yabani labarin abinda yafaru. Bara kuji....
Kaf duk abinda Malam yasani seda yafada masu, gaba
daya falon babu wanda beyi kuka ba saboda tausayin
Fulani da beauty, kowa ya tausaya masu yanda sukayi
rayuwarsu acikin MAKABARTA. Fulani da Beauty sunfi
kowa kuka, dan ita beauty tade taso taganta a
MAKABARTA.
Atunaninta nanne muhallinsu, kuma Fulani ita kadaice
wadda tasani, mace, se kuma Baba wanda shima
shikadai tasani namiji. Kuka takeyi sosai ayau dataji
labarinta, ashe inda take tunanin muhallinsu ne, take
cewa acan aka haifeta, ashe muhallin matattune, segashi
yanzu ana fadin AMAKABARTA AKA HAIFETA.
Malam yace ga Baba nan, shine megadin MAKABARTAR
da suke zaune, kuma shine mutumin daya zauna dasu
bisa gaskiya da amana, kuma ko matarshi betaba fada
mawa ba, harseda yaga lokaci yayi daya kamata yafada
mawani, alokacinne yazo yasameni yafadamun.........
Duk abinda Baba yafada mashi seda yafada masu, da irin
dawainiyar da yayi dasu. Hakanne yasa alokacin da
yagama bani labari, mukaje muka daukosu duk da seda
wannan aljanu suka rokemu akan mukula dasu idan har
wani yakara yunkurin cutar dasu bazasu kyaleshi ba.
Tundaga ranar damuka daukosu, nafara tunanin tabbas
abinda nagani acikin istaharata yana shige da wadannan
bayin Allah, idan baku manta ba Waziri, azuwan da
kukayi nafada maku naga Fulani akusa dani, kuma tana
raye, sede bansan awane waje take ba.
Hakan yasa nafara zargin wannan mata da diyarta zasu
iya kasancewa matar Sarki da diyarshi. Amma gudun
kada inyi saurin fadar abinda zuciyata take fada mun
hakan yasa lokacin da Safeeya tazo mani da alfarmar
abata wannan yarinya ta taho da ita nan gidan yasa nayi
tunanin barinsu suzo, sena cemata dole sutaho su duka.
Hakan yasa naroki alfarma gurin Baba nayabar aikinshi
yataho tare dasu. Adaren dazasu tafi nakira Safeeya daki
nake cemata ina zargin wani abu akan mutanen nan,
itama tace mun zuciyarta tafara saka mata irin abinda
nake zargi, dan ita tasan Fulani sosai, amma tacemun
bazata iya cewa ita bace dan alokacin ko Sarki yaganta
baze iya ganeta ba, tsawon shekaru 18, gashi bacikin
hankalinta take ba, kuma bagurin jin dadi ba, babu
wankan kirki, babu sallah, ba lallai bane a iya ganeta.
Shiyasa nace ma Safeeya sutafi tare, ta ajesu agurinta
kuma kada tabari kowa yasan dazamansu idan har
tasamu nutsuwa da tsafta zata dawo cikin kamanninta,
idan kuma ba ita bace shikenan nace munyi temako.
Alokacin nakira Waziri mukayi maganar, dan aduk fadin
masarautar nan mutum 3 nafi yarda dasu, kuma yana
daya daga cikinsu, Sarki Qaseem, da Sarki Hasheem.
Babban dalilin dayasa banyi maganar da Sarki Qaseem
ba, nasan yanda halinshi yake, baze taba iya hakura abi
abun asannu ba, kamar yanda nashirya, shiyasa ban fada
mashi ba.
Bayan Safeeya takirani tafadamun tagano wannan
mahaukaciyar bakowa bace se Fulani da diyarta,
alokacinma nace mata taboye abun harse angano
wadanda suka aikata mata haka. Nakira Waziri nafada
mashi, kuma alokacin yake fadamun yafara zargin Sarkin
Fada.
Ni nace mashi yacigaba da bibiyarshi harse ansamu
cikakkiyar shedar dazata bada damar kamashi sannan,
kuma nafada mashi bashi kadai bane dole akwai wata ko
wani makusancin Sarki. Alokacin seyake cemun shifa
yana zargin Jakadiya Karima.
Nima nayarda da abinda yafada, hakan yasa nace mashi
ya zuba masu ido su duka biyun. To Alhamdulillahi yau
gashi damukayi hakuri Allah yanuna mana makiyanmu
afili.
Sede kuma akwai abu daya danakeso intambaya Waziri.
Ina wannan bafaden da Sarkin fada yajama sharrin kisa,
ina fatan ba,a yanke mashi hukuncin kisa alokacin ba?
Gyara zama Waziri yayi yace, alokacin kam Sarki ya
yanke mashi hukuncin kisa.
Sede ni ajikina bansan meyasa banyarda da hukuncin da
Sarki ya yanke ba, kuma zuciyata takasa yarda da cewar
shine yayi kisan, amma alokacin kuma zuciyata bata
zargin Sarkin fada, sede kawai taki yarda da wanda akace
yayi kisan.
Hakan yasa naja Sarki falo tafada mashi da kada ya
yanke hukuncin dazezo yadameshi daga baya, nine
nabashi shawarar daya yanke mashi hukuncin daurin rai
da rai. Kuma haka akayi, haryanzu yana nan akurkutun
gidan nan.
Sede tun lokacin dana fara zargin Sarkin fada da rashin
gaskiya acikin gidan nan, tun daga ranar nafara kaimashi
ziyara, mukan zauna muyi fira,acikin zaman damukayi
ne, nakara yarda dabashine yayi kisan ba, kuma
akwanakin baya ne nasa aka canza mashi gurin aiki,
harda gurin zama.
Kuma tunjiya nasa aka fiddoshi yanzu haka yana
masauki. Malam yace kasa akirashi yazo nan. Waziri ya
aiki daya daga cikin fadawan gurin. Malam yace wannan
shine iyakar abinda nasani agame da rayuwar Fulani da
diyarta. Wadda haryanzu babu wanda yasan sunanta.
Abinda Baba yake kiranta dashi shine Yar Baba, wanda
yacemun ada yaji Fulani tana kiranta da Baby, jin sunan
zeyi mashi wahala ne, yake kiranta da diyarshi. Amma
ayanzu tunda gashi sundawo gida, za,a iya saka mata sun
kuma Waziri se muji daga gareku wane irin hukunci
zaku yankema wadannan maciya amanar.
Sallamar bafaden da aka aika ne tasasu kallon kofa, tare
suke da wanda aka likama kisan da Sarkin Fada yayi,
zama yayi yana kwasar gaisuwa, daka ganshi kasan
yajigata, atsawon zaman dayayi akurkutu shekaru
dayawa.
Kallon Sarki Qaseem da Sarki Hasheem Waziri yayi,
domin jin abinda zasu fada. Sarki Qaseem yayi gyaran
murya yace, ni babu abinda zance, sede kawai inma
Allah godiya daya kawomu karshen wannan matsala
damuke ciki. Tabbas wadan nan mutane, kunsamu cikin
tashin hankali, babu abinda zance maku se Allah ya isa.
Sede abu daya nakeso kusani, hakan da kukayi bashine
ze samurika tsoron mutane ba,ko kuma mudena jawo
su zuwa jikinmu ba, ai ba,a taba taruwa azama daya,
idan wani yazo daniyar cutarka, Allah ze aiko maka dana
gari, wanda ze zauna da kai badan komai naka ba, sedan
son dayake maka domin Allah.
Idan kuka kalli Jakadiya Safeeya da Malam,da Matata da
kuma matar Yaya wato Fulani, daga baya muka kara
samun Baban Darazo da abokin Yarima wato Haisam.
Duka wadan nan dana lissafo babu wanda muka hada
jini dashi, kuma babu wanda muka tashi dashi acikin
gidan nan.
Asalima bamu taba tunanin zasu shigo cikin rayuwarmu
ba, sedaga baya muka sansu, kuma duk da basu kasance
yan uwa agare mu ba, sun zauna damu tsakani da Allah,
babu wanda yakeda niyar cutar damu.
Idan muka kalli Malam da kanwarshi, bawai dan sun rasa
abinda zasuci bane yasa suka shigo jikinmu. Jakadiya
Safeeya tazo gidan nan badan kowa ba sedan bin
umarnin yayanta, kuma duk da haka tarika kaskantar da
kanta agaremu, wanda inda dan kudine zatazo, ninasan
babu abinda ze kawota, dan aduk fadin garin Bauchi,
darazo, Gombe, harma da makotanmu mutane dayawa
sunsan Malam, kuma kowa yasan babban mutum ne.
Idan har kudine, bayada damuwa dasu, asalima yakan
dauko wasu suci akarkashin shi. Amma duk da haka suke
zama tare damu abisa gaskiya da amana. Wannan kadai
ya isa yanuna ma kowa cewa wanda baku hada komai
dashi ba, ze iya yimaka abinda makusancinka baze maka
ba.
Yanzu ku kalli irin cin amanar da akayima Yaya, Gimbiya
Zakiyya kinci amanar sarauta, kuma kinci amanar
iyayenki, amatsayinki na Uwar gidan yaya amma aka
hada baki dake, aka cuceshi, koba komai, mahaifinki da
Abbanmu abokan junane sosai, kuma dama sune suka
hada aurenku, alokacin Yaya bayasonki amma nayi
imani da Allah haryanzu betaba fada maki keba
ra,ayinshi bace.
Haka yakarbi zabin iyayenmu kuma yazauna dake da
gaskiya da amana, segashi daga karshe kinzama butulu,
bayan butulci ma harseda kika hada da cin amanar
aurenku. Wa iyazubillah, kina matar aure amma kika
aikata wannan babban zunubi agidanki. Amma kanki
kikai mawa, kuma wlh. Kowace irin alaka ketsakinmu
bazata hana ayanke maki hukunci dede da laifinki ba.
Kuka tasaka tana fadin natuba, dan Allah kumun rai, wlh
duk abinda kuka fada gaskiya ne, amma niban aikata
abinda kukagani da son rai na ba. Nide nasan babu
abinda na tsana kamar zama guri daya da talaka, kuma
ni tunda nake wlh wannan aikin da Sarkin fada yamun
shikadai ne, yataba hadani dashi harmukayi magana.
Akwai sanda jakadiya Karima tazo tacemun wai Sarkin
Fada yana gaisheni.
Wlh ku tambayeta idan har zata fadi gaskiya zata fada
maku irin cin mutuncin dana mata akan abinda tazo
mun dashi, wlh babu wata alaka datake tsakanina dashi,
ko aranar danasan munfara aikata sabo dashi, yana
shigowa da masifa narufeshi, amma bansan ya akayi
daga baya harna bashi hadin kai ba.
Dan Allah Sarkin fada kafada masu ba laifina bane. Wani
malalacin murmushi Sarkin Fada yayi yadauke idonshi
daga kallonta. Sarki Qaseem yace wannan kuma yarage
naki, kinsan masarautar nan bata yanke hukunci seta
tabbatar da sheda tazahiri, kuma ba mutum daya ba,
kowa gurin nan yaga abinda kuka aikata, dan haka ki
adana kalamanki.
Kallon Medaki yayi, yace kenarasa ma mezance maki,
kinfi kowa zama cikakkiyar butulu, kinfi kowa sanin
dayanda aka aureki da irin halaccin da Yaya yayi maki,
duk da nibanyarda da labarin da mamanki tabada ba,
amma sbd sanin girman alkawarin da yaya yadaukar
mata, haka mukayi hakuri ya aureki.
Amma kirasa da abinda zaki saka mashi se irin wannan
cin amanar, kema zakiga sakamakonki. Kuma abinda
nakeso dake inaso kifada mana wacece ke? Da kuma
asalin garinku.
Cikin sheshshekar kuka Medaki tace wlh nima bansan
inane asalin garinmu ba, nadesan ayawon damukeyi
daga wannan kauyen zuwa wani iyayena suka haifeni.
Kuma sanin dana yima iyayena basu bani tarbiya tagari
ba, babu ilimin addini bare na boko, to sukansu ma basu
damu danasu addininba.
Nikaina nafara sanin Sallah ne alokacin dana ke bin wata
kawata islamiyarsu, anan nafara sanin addini na, harna
fara fahimta sosai, sekawai innata tafara doramun talla,
domin ita macece meson kudi.
Aduk lokacin dana saida tana siyamun duk abinda
nakeso, nima tundaga ranar son kudi,yashiga raina.
alokacin kuma na hadu da wani saurayi shine yakara
huremun kunne, haryayi nasarar ciremun budurcina,
seda muka zubar da ciki har 2, kuma Innata bata
tabamun fada ba, wannan shine sanadiyar lalacewar
mahaifata.
Mahaifina dan caca ne, bedamu da ya rayuwata takeba,
shiyasa nakasance tamkar dabbar daji, banida wani
takunkumin daze hanani aikata abinda naga dama.
Sanadiyar Caca mahaifina yarasa ranshi, mutanen gari
suka koremu harmuka hadu daku, Innata tafada maku
karya har kuka yarda damu.
Tabbas nasan naci amanar mijina, wanda yarufamun
asiri, duk da yagane banje da budurcina ba, amma be
tsaneni ba, asalima cikin laluma ya tambayani, shima
nafada mashi fyade akamun wanda karyane, amma haka
ya yarda dani, kuma yacemun beyarda infadama
kowaba.
Dan Allah kayafe mani, nasan bankasance mace tagari
ba, naci amanarka dan Allah kuyafemun. Kuka tasaka
wanda seda wasu daga cikin mutanen falon sukaji
tausayinta,,,,, hayaniya sukaji awaje, Wazirine da fadawa
suka leka.
Wani kodaddan mutumi suka gani wanda beda kyan
gani, sunata rigima da masu gadi. Waziri yace ku kyaleshi
yakaraso, haka yataho yanata zare ido. Yana zuwa yace
wani nake nema agidan nan nayi mashi aiki be bani
kudina ba. Kuma nafada mashi idan har bebani kudina
ba zanzo intona mashi asiri.
Murmushi Waziri yayi yace kashigo semuji wa kake
nema. Kowa mamakin ganin mutumin daya shigo
yakeyi, banda Sarkin Fada wanda yaketa muzurai. Waziri
yace munajinka wakake nema?.
Yace sunanshi Sarkin Fada, kuma ya kasance daya daga
cikin mutanen danake yima aiki, duk wani aikinshi nine
nakeyi mashi, anan yarika fadin duk irin asirin dayasashi
yayi, harda wanda yayima Areef, dana Jakadiya Karima
wanda tazubarma Gimbiya Suhailat ciki kuma aka daure
mahaifarta, har yakawo asirin karshe dayayi mashi.
Yace aranar yazomun akan yanason inbashi maganin
mallakar zuciyar Matar Sarki, Zakiyyah, yacemun yadade
yana sha,awarta amma yasan bazata taba bashi kanta ba,
hakan yasa yazo inbashi magani, alokacin yacemun beda
kudi amma yasan idan yasamu sa,ar kusantarta
yamallake zuciyarta zesamu kudi.
Tun ranar dana bashi bankara ganinshi ba, shine yanzu
nazo inkarbi hakkina. Salati kowa yakeyi, sbd wani abin
al,ajabin dasuka karaji yabullo. Murmushi Waziri yayi
yace kaima seka samu guri kazauna kajira naka
hukuncin tunda Allah yakawoka. Zaro ido boka yayi yana
fadin aishikenan kuma wlh nayafe mashi kubarni intafi.
Seda yabama kowa dariya, nan fadawa suka zaunar
dashi. Se alokacin Sarki Hasheem yayi magana, jikinshi
asanyaye yace Malam, kafadi irin hukuncin daya kamata
ayima kowa abisa koyarwa ta addinin musulunci, kamar
yanda yazo a Qur'ani. Dan nagaji da kallon fuskokin
wadannan mutanen.
Dan duk acikinsu nafijin haushin mutum daya, bakowa
bace se Jakadiya Karima. Allah ya isa tsakanina dake, kin
cuceni, wlh zan iya yafema kowa agurin nan amma
banda ke, bazan taba iya yafe maki ba. Mundaukeki Uwa
asheke makiyarmuce nida dan uwana..... kuka yasaka
tamkar karamin yaro.
Alokacin hatta da Malam seda yazubar mashi da kwalla
sbd yanda yakeyin kuka kowa yasan abun yana cimashi
rai sosai. Sarki Qaseem yana kuka yace Malam dan Allah
ayanke masu hukunci kada ciwon Yaya yadawo.
Malam yace Alhamdulillahi, kamar yanda kuka sani duk
wani laifi na duniya babu hukuncin da Alku'ani da hadisi
basu kawo ba, dan haka zamu duba muga irin hukuncin
da Allah yace ayima masu irin laifinku. Zanfara daga kasa
zuwa sama, wato daga masu karamin laifi zuwa babba.
Zan fara da masu gadi, mati da Lado, tabbas kun aikata
babban kuskure, domin da farko kunci amanar
masarauta, sannan kunbada gudummuwa gurin aikata
fasadi, dan haka hukuncinku anan shine zakuyi zaman
kurkutu natsawon shekaru 2, domin aladabtar daku,
sannan baku bakara aiki awata masarauta.
Se amintaccen bawan Sarki Hasheem, kaima kaci
amanar Uban gidanka, sannan kazamo daya daga cikin
wanda yatemaka ma Sarkin fada kuka sace Fulani. Dalili
daya ne bazesa ayanke maka hukuncin kisa ba, saboda
Fulani bata mutu ba, kuma Qur,ani cewa yayi wanda
yakashe akashe shi, sbd haka kaima za,a daureka
akurkutu na tsawon shekaru 5, tare da aiki metsanani.
Gimbiya Zakiyya, kinkasance matar aure, wadda aka
kamaki da laifuka biyu. Nafarko kina da sa hannu abatan
Fulani, wanda dakunsami dama kasheta zakuyi. Nabiyu
kuma laifin aikata zina. To hukuncin zina anan yakasu
kashi 2, akwai na wadda bata tabayin aure ba, wato
budurwa, akwai kuma na wadda ta tabayin aure.
Idan budurwa tayi zina, kuma aka tabbatar dashedu, za,a
yanke mata hukunci bulala 100, idan abokin yinnata
shima saurayine, hukuncinsu daya.
Matar aure. Duk matar datayi zina kuma tanada aure, ko
ta taba yin aure. Hukuncinta kisane, tahanyar jefewa da
duwatsu, wanda yara ne zasu jefeta harta mutu, za,a
rufe duka jikinta cikin rami abar kanta shine za,ayita jifa
harta mutu.
Idan abokin zinarta yataba aure, hukuncinsu daya, idan
kuma shi beda aure, to nata daban nashi daban. Abisa
shedar da muka samu daga gurin wanda yayi maki asirin
da kika fada wannan alfasha.
Kamar yanda yazo a arba'una hadith, mazon Allah yace
INNALLAHA TAJAWAZILI AN UMMATI➡➡ Lallai Allah
yagafarta ma al'ummata, AL,,KADAHA... abinda sukayi
da KUSKURE. WANNISIYANA... abinda sukayi da
MANTUWA. WAMASTUKURUHU ALAIHI... da abinda AKA
TURSASASU AKANSHI. Rawahul bukhari wa muslim.
Abisa duba da wannan hadisi, sarkin Fada yayi amfani da
karfin asiri ta hanayar mallakeki har kika biye mashi
kuka aikata alfasha. Abisa wannan hadisi, anan bakida
laifi agurin aikata wannan zina. Dan haka bazaki dauki
hukuncin zina ba anan.
Sede hukuncin dazaki dauka na aikata laifin cin amana
gurin niyar salwantar da rayuwar Fulani, dan haka zakiyi
zaman kurkutu shekara 5. Saura hukunci kuma yarage
ga mijinki.
Tunkafin yacigaba Sarki Hasheem yace Malam da ita da
Medaki duk nayanke igiyara aurena akansu, dan haka
kacigaba da yanke hukuncinka. Hannu Zakiyyah ta dora
akai tana kuka.
Malam yace Medaki, kema hukuncinki biyu ne. Amma
tunda nakarshen megaba daya ne, to hukunci daya
zamu yanke maki, naki hukuncin kisa ne, tahanyar
jefewa, tunda ke kin amsa kece kika bama sarkin Fada
hadin kai da kanki. Dan haka hukuncin kisa zaki dauka.
Jakadiya Karima kema hukuncin kisa ne akanki, sbd
kin aikata kisan kai domin kinsa anzubar da cikin
Gimbiya Suhailat. Anyanke maki hukuncin kisa daurin rai
da rai akurkutu, tare da horo metsanani.
Boka, kaima hukuncin kisa ne, ta hanyar rataya, tunda ka
amsa laifinka, kuma Allah kadai yasan iyakar ta,asar
dakayi.
Hukuncinmu na karshe akan Sarkin fada, kai kam da ana
mutuwa adawo to da seka karbi duka hukuncinka.
Amma hukuncinka anan shine kisa ta hanyar rataya.
Anan muka kawo karshen wannan hukunci na
MASARAUTAR BUBAYERO. Inafatan hukunci yayi maku,
idan kuma akwai wani abu kuna iya fada, yajuya yana
kallon Sarki. Sarki Qaseem yakalli Yayanshi. Kai yadaga
alamun hukunci yayi, sannan yace kuma agobe za,a
aiwatar da wannan hukunci.
Ihu Gimbiya Zakiyyah tasaka kamar meshirin shiga
hauka, Medaki da Jakadiya ma kuka kawai sukeyi kamar
ransu zefita. Haka aka kara tasasu zuwa kurkutu kafin
gobe.
Nima nace Allah yakaimu goben da rai da lafiya.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 110⚜115
Kusa da Baban Darazo Fulani ta matsa, idanunta
haryanzu basu dena zubar da kwalla ba, dukawa tayi har
kasa tace, Baba hakika banida bakin dazanyi maka
godiya, kayimun abinda bakowa ne dan Adam bane ze
iya yimani shi.
Tabbas kazamo daya daga cikin mutane masu
muhimmanci arayuwata, kuma daga yau inaso
kadaukeni tamkar diyarka ta cikinka, inaso kadauko
duka iyalanka kudawo nan dazama dan suma sunzama
yan uwana.
Baba yace babu komai Fulani, duk abinda nayi maki nayi
shine dan Allah, banyi dan wani abu naku ba, asalima
bansan wane irin matsayi gareki ba. Hakika naji dadin
yanda kika dauke ni, kuma nagode Allah yasaka da
alkhairi.
Haka kowa yatashi yanufi bangarenshi kafin gobe da
safe. Haisam ya kalli Areef yace abokina nizan tafi gida,
amma dole gobe indawo in kalli wasan daza,ayi agidan
nan. Tabbas nakara daukar darasi agidanku.
Allah yakara mana karfin imani kuma yacire mana SON
ZUCIYA. Areef yace amin, nima kaina abubuwan gidan
nan sun gama daga mun hankali, naji tausayin beauty na
sosai, ta dalilin masu SON ZUCIYA tarasa ingantatacciyar
rayuwa da kowane dan Adam masu galihu suke samu.
Tarasa cikakken Ilimin addini dana Boko, batasan kowa
acikin yan uwanta ba, batasan yaya mutane suke ba, har
seda Allah yakawota cikin gidan nan. Kalli Umminta,
tasamu kanta acikin hauka harna tsawon shekaru 18.
Agaskiya mutane basa kyautawa.
Nayi alkawarin zan jiyama beauty rayuwa medadi,
wadda batayi irinta abaya ba. Zan sama mata makaranta
me kyau wadda zata samu cikakken ilimin addini dana
boko. Fatana Allah yabani tsawon rai in cika wannan
burin dana dauka. Kamar yanda Sarkin fada yake ikirarin
yasa anciremun son sarauta azuciyata, to be cuceni ba.
Kanshi ya cuta, kuma naji dadin hakan, zanyi amfani da
damar dana samu dan insamu lokacin beauty na, nasan
inda inason sarauta bazan iya samun lokacinta ba, bare
incika mata burin dana dauka, dan haka zan rokisu Abba
ayi bikinmu akusa dan bana tunanin zama da beauty
akasar nan.
Zantafi da ita wata kasa harseta samu ilimi me kyau
sannan mudawo. Haisam yace gaskiya ka kyauta, sede
kasan da kyar idan su Abba zasu yarda, yanda beauty
bata taso agidan nan ba zasu so ace sun sami lokacin
zama da ita. Areef yace katayani addu,a insamu shawo
kansu.
Washe gari da misalin karfe 10 na safe tawagar Sarkin
Yobe wato mahaifin Zakiyyah da mahaifiyarta suka iso
masarautar BUBAYERO. Dan tun ajiya Sarki Hasheem
yasa Sarki Qaseem yafada masu halin da ake ciki. Ba
karamin tashin hankali suka shiga dajin wannan labari,
ba kamar mahaifiyarta datasan ta dalilin haka zata zama
abin tsangwama acikin kishiyoyinta.
Zaune suke afalo, sede Familyn gidan ne, kawai aciki,
tare dasu Mahaifan Zakiyyah, se kuma Waziri, malam da
Jakadiya Safeeya. Agefe guda kuma Zakiyyah ce zaune
atakure guri guda se kuka takeyi.
Mahaifinta ne yayi gyaran murya yafara magana. Hakika
Zakiyyah kinbani mamaki da irin abinda kikayi, saboda
kawai kishi irin naku na mata, yanzu inda Allah yabaku
sa,a kunsamu damar kashe Fulani da shikenan kema
kinza me kisan kai ko?.
Ko agidanku dakika taso acikin kishiyoyi kika samu
mahaifiyarki, kintaba ganin ance ta harari wani acikinsu?
Duk da takasance karama acikinsu amma hakan besa ta
rainasu ba. Agaskiya banji dadin abinda kikayima
kishiyarki ba.
Kuma naji dadin hukuncin da aka yanke maki, wannan
shine dede ga duk mutumin da yace Son zuciya zerika bi
arayuwarshi, koyanzu da kikaga munzo bawai munzo
bane dan ke, munzo ne, kawai dan inbada hakuri agurin
mutanen da kika zalunta, babu ruwana da hukuncin da
aka maki, haka zaki zauna tare da sauran masu laifi har
shekaru 5, idan Allah yasa har lokacin ina raye nibazan
hanaki zama gida na ba, amma kisani kina dawowa zan
aurar dake ga duk wanda naga dama.
Dayake Sarki Hasheem yace kada wanda yafada masu
abinda suka aikata da Sarkin Fada hakan yasa basusan
maganar ba. Dan Sarki yace yanajin kunyar mahaifinta
shiyasa yahana afada masu abinda tayi, duk da ba
laifinta bane.
Kuka sosai Zakiyyah takeyi ta matso kusa da Babanta
takama. Kafarshi tace dan girman Allah Baba kayafemun,
wlh nikaina nayi nadamar abinda na aikata, babu irin
shawarar da Umma bata bani ba, amma nabiyema
hudubar shedan na aikata abinda yazubar da kimar
masarautarmu, dan Allah kuyafe mani koda mutuwa
zata riskeni acikin kurkutu.
Seda kwalla tacikama mahaifinta ido, damma bakin glass
ne a idonshi, juyawa tayi kusa da Ummanta takifa kanta
bisa cinyarta tasaka kuka, tarasa bakin magana, itama
Ummar kuka takeyi sosai, seda suka bama mutanen
falon tausayi.
Mahaifin Zakiyyah ya kalli Sarki Hasheem da Fulani, yace
iname neman gafara agurinku, tabbas Zakiyya ta aikata
kuskure dan Allah kuyi hakuri, muzamu koma seku
aiwatar da duk hukuncin da kuka yanke ma kowa, kada
tausayi ko wani kusanci ya hanaku cika umarnin Allah da
Manzonsa.
Tashi yayi yana goge kwallar data zubo mashi, yanufi
kofa yana fadin Zakiyyah nayafe maki duniya da lahira,
Allah yasa wannan abu daya faru yazama kaffara agareki,
idan munkara haduwa zanyi farin ciki da haka idan
kuma ta Allah takasance se ince Allah yasadamu da
alkhairi, haryanzu kinada lokacin tuba, kada kiga
anyanke maki hukunci ki kasa cigaba da neman gafara
agurin Allah.
Yana kai nan kuka yaci karfinshi yayi waje, fadawanshi
dake bakin kofa suka mara mashi baya. Tashi Umman
Zakiyyah tayi itama zata tafi, Zakiyyah tariketa tana kuka,
tace Umma bakice komai ba, dan Allah kimun magana
kada in mutu da fushinki. Jawota tayi ta rungumeta tace.
Nayafe maki Zakiyyah Allah ya yafe maki, insha Allah
zanrika kawo maki ziyara harkifito, idan kuma na mutu,
addu,ar ki nake nema, idan kinrigani mutuwa, addu,a ta
zata sameki har kabarinki. Sakinta tayi tanufi waje
dasauri tana kuka.
Da gudu Zakiyyah tabita, sede kafin ta isa harsun tada
mota sun nufi gate, haka taruga da gudu, tana binsu,
suna fita aka kulle kofar, anan tazube tana kuka, duk
mutanen gidan suna kallonta.
Acikin mota kuwa Umman Zakiyyah se kuka takeyi, haka
Sarki yajawota yana lallashinta. Tace shikenan yanzu
kowa seyasan abinda Zakiyya tayi, shikenan yanzu
banida sauran kima agurin mutane. Sarki yace namaki
alkawarin babu wanda zesan abinda Zakiyyah tayi, sede
idan tadawo gida, zamusan abinda zamu fada. Kwanciya
tayi tana fadin nagode.
Tunda suka fita Sarki Hasheem yake kuka, yakasa
denawa,gaba daya tausayin Zakiyyah da iyayenta
yakamashi, kuka yakeyi kamar karamin yaro, gaba daya
jijiyoyin kanshi sunfito, ganin haka Waziri yayima
Likitansu waya, yazo.
Bayan yagama dubashi yayi mashi wasu allurai kuma aka
bashi magani, ko minti 5 bekara ba yayi bacci. Likita
yace jininshi ya hau sosai, kuma zuciyarshi tana bugawa
dasauri, saboda tashin hankalin daya shiga, zeyi bacci na
tsawon awa 8 kafin ya farka, idan yatashi ayi kokarin
mantar dashi duk wata damuwa dazata kara dawo
mashi. Sallama yayi masu yafita. Anan suka kulle mashi
dakin suka fita.
Sarki Qaseem yace Malam muje agama abinda za,ayi
kozamu dena kallon fuskokin wadancan munafukan.
Waziri ya kalli Areef yace kaja beautyn taka kubar gurin
nan banaso taga komai, idan zaka dawo kayi kallo to ita
de kabarota acan.
Haisam ya kalli Ayman yace kema wuce mutafi banason
kirika mun kuka, murmushi tayi tace aini babbace kuma
nafi Beauty sanin matsalolin rayuwa. Dan haka kabarni
in kalla, hakan ze karamun imani dajin tsoron aikata
kowane irin zunubi. Murmushi yayi dan yaji dadin
kalamanta.
Gaba daya mutanen masarautar harma da mutanen
waje seda suka cika babban filin da ake wasan dokuna
na Masarautar BUBAYERO, dan kowa yanason yaga
yanda za,a aiwatar da wannan hukunci.
Hada manyan malaman masarautar suma sun halacci
gurin, haka aka fito da masu laifi kowa yasaka kayan yari
ajikinshi, gaba daya kunyar mutanen gurin sukeji, gani
sukeyi kamar duka mutanen duniya ne, aka tara agurin
ganin irin yawan da mutanen suke dashi.
Kowa neman boyewa yakeyi bayan dan uwanshi,
Zakiyyah duk tafi kowa jin kunyar jama'an gurin, jitake
kamar kasa ta tsage tashige. Duk abinda takeyi Malam
yana kallonta, besan lokacin da kwalla tazubo mashi ba.
Bawai tausayinta yasa shi kuka ba, kawai daya kalli yanda
take boyewa dan kawai taga yan tsirarrun mutane,
wadan da ko rabin garin Gombe basu kai ba, amma
shine take jima kunya. To inda ranar lahira ce Allah ya
tadata agaban biliyoyin mutane yazataji? Wannan
tunanin shine abinda yasaka Malam kuka.
Bayan sun tsaya agurin da aka tanadar masu, kowa
yasamu nutsuwa, sannan Malam yahau kan wani guri
medan tudu shida Sarki Qaseem da limamin masallacin
masarautar, tayanda kowa ze iya ganinsu.
Seda Malam yasa liman yabude masu taron da addu'a
sannan yafara magana. Har yanzu hawaye basu dena
fitowa daga idonshi ba, musamman daya hau sama yaga
mutane sun nutsu gefe guda kuma ga masu laifi suma
sun tsaya suna kuka.
Kyalle yasa ya goge idonshi sannan yafara magana.
Alhamdulillahi, kamar yanda kowa yasan dalilin taruwar
mu agurin nan, kuma naji dadi matuka da Allah yasa
naga Mata da Maza, Yara da Tsofaffi, sun halacci gurin
nan.
Saboda kowa ze kalli yanda kowa ze amshi hukuncinsa.
Nasan yawancin mutanen gurin nan masu hankali,
wannan taron kadai ya isa ya tunatar da kowa tashin
kiyama, da kuma tsayuwar hisabi.
Da farko inaso indanyi amfani da wannan dama inyima
jama'a tunatarwa akan rayuwar duniya data lahira,
hakika wannan abu da mutanen gidan nan suka aikata
yasa mutane dayawa zasu koyi darasi.
Zanyi magana akan abu 2.
AMANA, da ZINA.
Wa iyazubillah. Hakika mutane dayawa sun shagala
azamanin nan gurin Cin AMANA. Basajin kunyar ha'intar
makusantansu. Dama Manzon Allah (s.a.w), yace idan
karshen duniya yazo amana zatayi karanci, bawa ze iya
cin amanar Uban gidanshi, kamar yanda Da ze iya cin
amanar mahaifanshi.
Ayanzu halin damuke ciki kenan mutane basu dauki cin
amana abakin komai ba.
(1) Kamar yanda yazo acikin hadisin Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata agareshi. Inda Abdullahi bn
Abbas (RA) yace. Lallai kyawawan aiyuka suna sanya
mutum hasken fuska da na zuciya da yalwar arziki da
karfin jiki da soyayya daga bayin Allah.
Kamar yanda sabon Allah yake sa fuska da zuciya duhu
da raunin jiki da tawayan arziki da kiyayya daga mutane.
Rawahul Muslim.
(2). Allah ta'ala yana cewa. Kuma wadanda sukayi kokari
ga nemar yardarmu. Lallai muna shiryar dasu ga
hanyoyinmu, kuma lallai tabbas Allah yana tare da masu
kyautatawa.
(Suratul Ankabut, Aya ta 69).
(3) Allah ta'ala yana cewa. Babu wata musiba dazata
sameku, face sai sakamakon abinda hannuwanku suka
aikata.
(Suratul Al shuura Aya ta 30).
Sadakallahul Azim.
Kai jama,a, ina zamu kai wannan girman zunubi damuke
daukar ma kanmu? Hakika Allah baya yafe laifin wani
akan wani. Baka tunanin idan kaci amanar wani Allah
yadauki ranshi ko ranka batare daka nemi yafiyarshi ba?
Jama'a yakamata mutuba zuwa ga Allah, wlh duniyar
nan tafiya takeyi.
Kada muyarda wasu subamu amana mu ci masu, ayanzu
wanda ka yarda dashi shine wanda yake cutarka. Allah
yasa mufi karfin zuciyarmu. Kowa da anyi magana seya
ce Shedan. Kada kumanta shifa Shedan seyasamu kofar
shiga jikin dan Adam yake iya shiga har yasamu damar
yimasa mummunar huduba.
Idan har mukayi riko da gaskiya da Amana, muka koma
ga Allah, tabbas ze cecemu daga sharrin shaidan. Idan
baku manta ba, duk yanda shedan yakai ga hallakar da
bayin Allah baze taba samun nasara agurin wadan da
Allah ya tsare ba. Ba kuma tsayawa zakayi harse kasamu
tabbacin lallai Allah ya tsareka sannan zaka rika addu,a
ba.
Manzon Allah dakanshi yana neman tsari daga sharrin
shaidan, wanda kowa yasani yafi karfin shedan, Allah
yariga da ya haramta ma shedan kusantar manzonsa.
Amma duk da haka Annabi be kwanta ba yace Allah
yatsa reshi baze nemi wani tsari daga gareshi ba.
To kai waye dabazaka nemi tsari daga sharrin shaidan
ba? Yakamata kowa yadage da yaki da zuciyarshi, ita
kadaice hanyar dazata tseratar damu. Allah yasa
mudace.
Magana ta biyu akan ZINA. Innalillahi Wa inna
ilaihirraji'un. Wannan abu itace abinda yake damun
mutane dayawa, babu yara, ba manya, marasa aure, har
masu aure. ZINA wata musiba ce acikin al'umma.
Allah ya haramta zina, shiyasa ma yace kada ku
kusanceta. ZINA tana tarwatsa duk wani mutunci na dan
Adama, tana sa talauci. Shiyasa Allah yakawo hukuncin
ZINA acikin alkur'ani me girma.
Dan haka ayau kowa zega irin hukuncin daya kamata
ayima duk wanda ya aikata ZINA. Allah yashiryar damu
da iyalanmu, baki daya. Kafin afara akwai jawabin da
Sarki zeyi maku.
Komawa baya Malam yayi yana share kwallan idonshi,
Jama,a da dama agurin seda suka zubar da hawaye akan
jawabin da Malam yayi. Sarki Qaseem yafara magana,
shima daka kalli idonshi zaka gane kuka yayi.
Alhamdulillahi, kamar yanda Malam yayi mana jawabi,
nasan mutane dayawa sun kara sanin me ake ciki
arayuwa. Kamar yanda zamu fara aiwatar da wannan
hukunci, ina me fada da babbar murya, daga yau, duk
wanda aka kara kamawa acikin kasata, dumu dumu da
laifin aikata ZINA , kowani laifi, tabbas se hukunci yahau
kanshi.
Ko wanene, kuma ko wacece, kowane irin matsayi
mutum yake dashi, zamu buga tambari wannan doka
zata fara ayau. Kuma naji dadi sosai da dokar zata fara
daga cikin Masarautar mu, acikinta ma hada masu
sarauta aciki. Karewa ma, hada matan Sarki Hasheem
guda 2. Tunda har muka iya aiwatar da hukunci akansu.
Babu wanda za,a kara daga ma kafa idan ya aikata zina,
watakila hakan yakawo mana sauki acikin kasarmu. Daga
karshe ina yima Allah godiya daya nuna mana wannan
rana. Sauka yayi idanunshi suna fitar da kwalla.
Anan Waziri yasa aka cire Zakiyya da Jakadiya Karima,
dasu Mati da Lado gefe guda, kuma aka fadama mutane
irin hukuncin da aka yanke masu. Medaki se Kuka takeyi.
Tanufo gurin su Gimbiya Suhailat da Fulani, wadanda
suma kukan sukeyi.
Har kasa ta duka sede takasa yin magana saboda kukan
datakeyi, hannuwanta biyu kawai tahada alamun neman
yafiya tacigaba da kuka. Kamota sukayi suka rungumeta
suna kuka.
Seda suka saka kowa kuka agurin, wasu mata sukazo
suka kamata, seda tayi addu,a sannan aka sata cikin
ramin aka rufe jikinta akabar fuskarta. Tunda su Fulani
sukaga haka suka bar gurin suna kuka, mata dayawa
seda suka bar gurin, hatta da Sarki Qaseem fada yakoma
yana kuka, kasa tsayawa yayi agurin.
Bayan anyi mata addu,a akasa yara suka fara jifarta,
ahaka harseda ta mutu😭. Wa iyazubillah. Allah ka tsaremu
daga aikata ZINA. Amin.
Zakiyyah agurin tazube asume saboda tsabar kaduwa,
Jakadiya kam kuka kawai takeyi. Haka wasu suka dauketa
aka shiga da ita ciki.
Boka da Sarkin Fada aka kira. Idanun Sarkin Fada sunyi
jajur saboda kuka, haka shima yaje gurin Waziri, da
Sauran mutane, yana kuka yana neman yafiyarsu. Bayan
anyi masu addu'a aka dorasu saman wani table, aka
samasu bakar hula afuskarsu sannan aka ture su daga
kan table din. Haka sukayita lilo har suka mutu😭. Sannan
aka tasa keyar sauran masu laifi zuwa kurkutu, alokacin
Zakiyyah ta farfado itama aka hada da ita.
Gaba daya mutanen dake gurin babu wanda bezubar da
hawaye ba, jikin kowa yayi sanyi, tsoro yashiga
zukatansu. Haka aka taru akayi masu sallah aka wuce
dasu makabarta.
INNALILLAHI WA INNAILAIHIRRAJI'UN😭😭. Allah kasa mufi
karfin zuciyarmu. Bazan iya cigaba. Da typing ba se zuwa
gobe idan Allah ya kaimu. Abinda nafada da kuskure
Allah yayafe mani.
Nagode da kulawarku, sekunjini anext page insha
Allah.
0 comments:
Post a Comment