Dedicated to hassana Dan larabawa end khadeey pinky
Sadaukarwa gareku khadeey da hassana ina kaunarku har kulum
🍉page1/2🍉
🍓🍓🍓🍓🍓
Xaune take tana nazarin rayuwa wato maimounatou kenan doguwa ce fara mai idanu gata da sura mai kyau wato kirar kalangu coca cola batada wani jiki anma akoy kira gata da kyau yar asalin kasar niger ce acikin baban gari mai suna maradi mahaifinta buzu ne alhaji sani mahaifiyar ta kuma bafulatana shiyasa ta dau kyau gaba da baya dan kap yan gidan su tafisu kyau
Su hudu ne ga iyayensu fatima itace ta farko sanan ismael,mai bimasa kuma maimounatou sai auta idrissa
Maihaifin maimounatou Sunansa alhaji sani Dan asalin kauyen zinder ne dake cikin kasar niger dan boko ne tsantsa ma aikacin banki kuma sanan baban Dan kasuwa sunyi auren soyaya ne da mahaifiyar maimouna mai sunan Aichatou itama yar kauyen zinder kince itama doctor ce tana aiki a baban asibitin kudi dake nan kasar maradi
Dan haka sunan zaman lafiya da son juna
Fati ta gama karatunta na jarida yanzu haka tana aiki ne dan haka tayi aure da ya guda ,ismael ko yana kasar france yana karatu, maimounatou yanzu haka ta gama secondry tana jiran sakamako na jami'a tun tana karama take da ilimi ga saurin doka a islamiya kuma tayi sauka tanada wata kawa wada suka tashi tare mai suna hafsa sun shaku sosai iyayen su har suna mamakin irin shakuwar su haka KO a makaranta suna tare shawarar su daya
Wanan kenan
Yau sun dawo daga islamiya duk da sunyi sauka hakan baisa sun daina zuwa islamiya ba mimi tana shiga gida ta tarar da wata bakuwar mota baka jif range rover aa dady ya kara siyo wata mota ne ko kuwa baki akayi ta girgiza kai tashiga falon da salamarta tayi cak sakamakon bakuwar fuska da tagani ta gaida su shida dadyn nata Dan ta gane bakon wato wanan abokin dadyn ne da yake Nigeria wato alhaji souleymane ya juya yace alhaji kar dai Ace mimi ce ta girma kworaikuwa itace kaga ta girma ko wly kuwa cewar alhaji souleyman nan sukaci gaba da firar su
Momy nadawo kina ina ganinan Baby cikin kicin ta jiyo muryar momynta ta shigo da salama ta rungume momyn daga Baya momy kina aiki ke kadai ina masu aikin bari ni nace su bari kinsan bana barin yan aiki suma dadynki abinci to momy bara in kama miki a a keda kika dawo daga islamiya a a momy ay ba wani gajiya nayi ba na suka kama suka kamala nan suka jere a table momy ta kali maimouna tace mimi maza je kicema dadynki su fito abinci ya kai haka sukecemata saboda tanada sunan mahaifiyar dadyn ta wato kakarta shiyasa suke cemata mimi nan dai taje ta fadama su dadyn nata ta fito toilette taje tayi tukon tafito aka jera bisa diner aka fara cin abinci duka family dan al'adarsu ce ko baki sukayi tare suke cin abinci Dan haka an jera ana cin abinci sai raha akeyi alhaji suleyman yace niko alhaji wata magana ke cikin bakina tun dazu to inajinka cewar dadyn maimounatou nace mai zai hana a hada auren maimouna da dan wajena abdalah ya ka gani shima yana nan ya dawo daga karatu munyi munyi ya fido matar aure anma shiru har yanzu cikin washe baki alhaji sani yayi kai agaskiya naji dadi alhaji souleyman ai kai me aurar da mimi ce ba sai ka tambayi izini na ba tunda aka fara magana gaban mimi ke wata irin faduwa haka ta tashi dan KO abincin bata samu ta karasa Ci ba mahaifiyar ta na ankare da ita Dan itama ta bata tausayi haka mimi ta fada kan gado kukan ma yaki zuwarmata dan da ta samu kukan wata kila zataji salama daga zuciyarta acikin wanan halin mahaifiyarta ta isketa
Ta dafata mimi kiyi hakuri da hukuncin da mahaifinki ya yanke Dan nasan bazai baki abinda zai cutar dake ba yanzu momy auren dole dady yakeson min karkice haka mimi auren biyaya zakiyi kuma insha allah zaki ga ribar biyaya na sawwama
Sai alokacin mimi tasamu kuka yazo mata nan dai mahaifiyar tata tayita rarashinta bangaren dadyn ta kuwa sai tautaunawa bisa kan auren suke Dan sun Sa rana nan da wata guda
Aci gaba da gashi 🍇🍇
Maimou love😘😘
[4/12, 14:29] +227 80 22 99 15: 👩⚕Labarin👩⚕
Maimounatou 🇳🇪
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
Na✍
Maimouna Matar abdoulaye AM💋
Dedicated to hassana dan larabawa end khadeey pinky
🍉page3/4🍉
🍓🍓🍓🍓🍓
Bayan magariba dadyn mimi ya tura idrissa domin ya kirawomasa mimi a kwonce ya isketa duk da yaro ne bazai huce shekaru goma sha uku ba anma ya tausayama yar uwarsa kwonce ya isketa duk jikinta yayi sanyi dan tunda wanan abu ya faru sallah kaway tayi ta kwonta anty mimi way kije daddy yana nemanki to shine abinda ta iya cewa hijabin ta ta dauka tayi bangaren mahaifin nasu shi kadai ta tarar domin abokin nasa baya nan salama tayi ta zauna kasa kusan kafafafun mahaifin nata kai a duke tace daddy gani
Yawa yar albarka wato mamata dama magana da mukayi dazu ne zamuyi mamana inaso kiyi hakuri bisa ga hukunci da na yanke ba tare da naji ra'ayinki ba abinda nakeso kisani shine alhaji Souleymane abokina ne tun muna samari abotakar mu ta huce abotaka tazama yan uwantaka duk abinda kikaga nazama a yanzu ta dalilinsa ne mutunan kirki ne shida zuri'a sa ga baki daya dan haka bazan kaiki inda za à cutar dake ba ina fata kin fahimceni ko naji daddy bana fatan ranar da zaka umarceni akan inyi maka abu inyi musu a kansa matsawar bai sabawa adinin musulumci ba dan haka na yarda da zabinka yawa yata allah miki albarka Ameen daddy tashi jeki ki turo min mahaifiyarki to tace ta fita bangaren mahaifiyarta tayi tayi mata salama momy way kije daddy na kiranki to ganinan zuwa ina fatan kinci abinci ko ea môm daga nan ta fice dakin ta
Da salamarta ta shigo alhaji barka da hutawa yawa hajiyata dama magana Ce nakeso muyi yakikaga shawarar da muka yanke akan mamana alhaji ay nasan bazaka zaba mata abinda zai cutar da ita ba kuma inka duba ay abdalah yaron kirki ne dan haka allah ya tabatar mana da alherin sa ameen madame dina nasan bazan samu matsala dake ba allah ya miki albarka ameen
Haka mimi ta kwona cikin kuka da gari ya waye zazabi mai tsanani ya kama mimi momyn ta ko wurin aiki bata jeba tana nan tana dawey niya da ita haka hafsa ta shigo mimi ta gayamata komai ita tausarta tayi tayi tare da kalamai masu dadi fati ma tazo itama ta rarashi yar kanwar tata wanan kenan
Waye abdalah
Asalin sunan sa shine abdoulaye souleymane SS
Da ga alhaji souleyman SS mai gold baban sa wato alhaji souleymane mai kudin gaske ne yanada manyan shaguna na gwolagwolai kasa daban daban yanada mata guda mai suna hajiya rabi fulanin adamawa ne duka sunada kyau irin na fulanin asali sunada yaya uku babansu shine nuradine mai bi masa shine abdalah sai autarsu safiya yar kimanin shekaru sha takwos 18years abdalah ya gama karatunsa a kasar waje yanzu haka yana aiki a baban kanpanin Mahaifin sa ne dake nan kano yayansa nura yayi aure da yaya biyu shi dan jarida ne
Abdalah yaro fari kyakyawa yanada sufar kakarfa yanada hanci dogo ga idanu masu dokar hankalin yan mata ga saje siriri da yasha gaira akan fuskar sa bakikirin dogo ne anma ba can ba in takaice muku abdalah kyakyawa ne na gidan gaba abdalah yanada wata dabi'a na in har bashi ya zabi abu ba tofa ko kalonsa bayayi yanada wani buri akan mace guda uku na daya ta zamo mai Son adini 'na biyu kyakyawa kuma mai ilimi, na uku kuma tazamo mai sura mai kyau,yanada wata yarinya mai sunan rukaya budurwar Sa Ce yar gidan wani hamshaki ne mai kudi ita kadai iyayenta suka malaka tanada kyau har ya kusa yin yawa tanada ilimi na boko kadai saide sam batada sura Dan a shafe take duka kulum tana ciko da wanan wando na yanzu da ake yayi na Baya da kuma rigar mama mai ciko wanan ne yasa abdalah yake tunanin macen da yake burin samu Ce sunyi makaranta a kasar waje tare dan yanzu sun fara zancan aure saide yana jiran dadyn Sa ya dawo daga tafiyarsa ya shaida masa wanan kenan
Aci gaba da gashi 🍇
Maimou love😘
[4/12, 14:29] +227 80 22 99 15: 👩⚕Labarin👩⚕
Maimounatou🇳🇪
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
Na✍
Maimouna Matar abdoulaye AM💋
Dedicated to hassana dan larabawa and khadeey pinky
🍉page5/6🍉
🍓🍓🍓🍓🍓
Bayan kwona biyu mahaifin abdalah ya tafi wato alhaji suleymane yau asabar mimi gari yayi mata zafi komi bata jin dadin sa ga hafsa ma da suke basket ball din ma tayi tafiya can kauyen mahaifiyar ta mimi tana matukar Son basket-ball a cikin wasan motsa jiki dan har gasar ta suke yawan zuwa a garuruwa domin ta kworai sosai wurin wasan to shine yau kasancewar bata jin dadin zaman dakin ta shirya cikin kayan sport din ta jajaye sunyi matukar yi mata kyau jajaye gashin kanta ta gaira ta kule tamauw kasancewarta mai gashi sosai ga tsawo kuma ga yawa dan dakyar take iya kule sa to ba dole tayi gashi ba uwa bafulata uba buzu ay gadon sa tayi ta doki takalman ta manya suma na sport tasa ta fito momy zan tafi wancan bangaren momy tayi dariya tace my daugther basket ball din ne ko ae wly momy kwona biyu banyi ba kuma ga jikin nawa ba dadi shiyasa ok ma fille bye
Ta fito tayi wani bangaren dake cikin gidan su wata runfa mai kyau irin ta turawa anan naga ta duka ta doko ball din sai kuma tayi wani bangaren tana shan wata kwona wani baban filli nagani mai shegen kyau na basket Ball din ne kasancewar gidan baban gida ne mahaifin mimi yasan mimi nason basket-ball tun tana yarinya shima kuma wasan sa kenan dan haka da zai gina gidan sa yasa aka ware mata baban filli bangare guda aka gaira mata shi da komai na basket-ball dan haka daddyn ta yacema daddy Abdallah cewar dan allah amasa alfarma cewa gidan da mimi zata zauna dan allah a dan ware wani bangare a gaira mata filin basket-ball daddyn abdallah yace kar ka damu ay shima Abdullah wasan da yafi so kenan dan haka gidan da nasa aka gina saida aka ware masa baban filli na basket-ball dan haka karka damu to kunji
Tana shiga filin ta fara bugawa cikin kworewa tanayi har wani juyawa take na kworewa tayi wani tsale mai ban sha'awa ta tila kwolo cikin raga tapi taji rap rap an mata daga baya tana juyowa taga momyn ta da daddyn ta cikin kayan sports hada dan kanan ta idrissa kasancewar gidansu kamar turawa suke sunada ilimi da tarbiya saide akoy su da son harkar turawa
La momy daddy kune mama na ina kawar taki kike basket ke kadai daddy hafsa tayi tafiya shi yasa dan haka zamuyi équipe ke da ni idrissa kuma da momyn ki la la allah daddy mimi ban yarda ba cewar mahaifiyar mimi dan ku kun iya shine zakumin wayo naki saide mimi dani shi kuma idrissa da kai ok ba matsala cewar dadyn mimi nan suka fara gwonin sha'awa sai kusan magariba suka bari su mimi suka ci sunata dariya haka kowa yayi wurinsa domin yin wanka kuma su gabatar da sallah
Wajen daddyn Abdullah yau kwona biyu kenan da dawowar sa daga niger dan haka daddyn sa ya nemi ya gana dashi my Son dama wata magana nakeson muyi mai mahin manci inaso ka bani hankalin ka dakyau kaji ba yau ba munyi munyi ka fido matar aure ka ki ka fido la daddy dama dakata cewar daddyn sa ban gama ba bayan naje Niger naga har abokin nan nawa dan haka muka yanke hukuncin cewa zamu hadaku aure da yar wajen sa zumbur abdallah yayi ya tashi idanunsa duk sunyi ja haba daddy kace in fido matar aure ina jira ka dawo kuma yanzu kace za a hadani da wata watan ma yar niger a gaskiya daddy ni ba amin adalci ba gidan ku nace gidan ku da kanada wada kake so kaki kawota tun wuri dan haka yanzu bakin alkalami ya bushe sai ka fara shiri nan da wata daya ne auren
Haba alhaji yanzu anma yaron nan adalci kuwa cewar hajiya ya isa haka cewar daddy hukunci dai na riga na yanke dan haka bana Son kananan magan ganu ya tashi ya shigewar sa daki abdallah ya zube kasa wasu hawaye suka zubo masa momyn sa tazo ta tarbosa my Son me yayi zafi haka kayi hakuri kabi umarnin ka ni kuma na maka alkawari sai ka auri wada kake so ay ni farin cikin ka shine nawa allah momy allah kuwa ka amshi umarnin mahaifinka ya zumburo baki to anma momy yar Niger fa ni nasan ba wayayu bane kuma sam munanu ne daki kai ni gaskiya momy kar kayi musu yaro na to momy indai an Aura min masoyiya ta ni banida matsala cikin ransa ko cewa yake duk rada akayi gigin hadani aure da wanan yar kauyen ta niger din wly sai ta gane kuren ta Hum tab
Aci gaba da gashi 🍇
Maimou love😘
[4/12, 14:30] +227 80 22 99 15: 👩⚕Labarin👩⚕
Maimounatou🇳🇪
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
Na✍
Maimouna Matar abdoulaye AM💋
Dedicated to hassana dan larabawa end khadeey pinky
🍉page7/8🍉
🍓🍓🍓🍓🍓
To bayan kwona biyu komai ya lafa momyn abdallah dakanta dreba ya tuka ta sai gidan kawu bala kawo bala kanan mahaifin alhaji souleymane ne wato daddyn abdallah tana zuwa tayi sa'a kuwa yana nan salama tayi ta shiga yana zaune shi kadai yana karatun kur'ani nan ta zauna har saida ya gama yana juyowa ta duka ta gaida sa yace à a kune a gidan namu yau ae wly ya kwona biyu lafiya lau da fatan dai kowa na lafiya ko ea wly dama nazo ne akoy matsala subahanililah meya faru kawu dama baban abdallah ne yace zaima abdallah aure to yaro ya yarda saide yace shima abarsa ya auri wada yakeso shine mahaifin nasa yace bai yarda ba to yanzu ga yana cikin wani hali ya salam cewar kawo bala wanan wani irin abu ne karki damu gobe insha allah zanje gidan wanan ay sakarci ne to kawu mungode allah ya saka da alheri ba komai ki kara kwontar ma da yaro na hankali to kawu ni zantafi sai kazo a gaida gida yaji cewar momyn abdallah haka ta juyo ta tafi gida
Washe gari saiga kawo bala daidai kowa ya halara falo daddy da momy da abdallah hadama nura da yazo ganin iyayen nasa bayan anyi gaishe gaishe sai kawo yayi gairan murya am dama wata mahinmiyar magana Ce ta kawo ni shine kai souleymane naji wata magana cewar zaka aura ma abdallah wata diyar abokinka bayan kuma yace maka ga wada yakeso to abinda zance maka shine ina umartarka da kabar yaro shima ya auri wada yakeso tunda ya yarda da zabinka kaima ka barsa ya auri wada yakeso mana to anma kawu ya isa haka kawu ya dakatar dashi yace umarni na baka in na isa dakai to kawu Za'ayi yanda kace anma saï an fara Aura masa wacan tukon wanan duk ba matsala cewar kawo bala
Abdullah kuwa sai washe baki yake yana jinjina ma uwar tasa bayan kawa ya tafi daddy ya juya yana kalon abdallah yace wa ya fadama kawu sukayi tsuru tsuru yayi tsaki ya tashi ya tafi dakinsa momy ta tashi ta bisa tace ina zuwa tana shiga daki ta iske alhaji saman gado sai huci yake ta zauna kusa dashi ta dafa sa haba masoyina karka yi hushi da abin alfaharinka da danka nifa Ce taka ta Dan shafa kumatunsa ta sumbace sai ga alhaji yayi murmushi dan hajiya tasan lagon sa yanzu hajiya nida gidana na yanke hukunci anma ku ki bi to ban isa bane saiga hajiya tana shagwoba tamkar wata yarinya haba alhaji na abdallah fa danka ne in baka masa abinda yakeso ba wazai masa ya yarda da zabin da kamasa to shima ay sai ka barsa ya auri wada yakeso nan dai tayita lalaba sa har ya sabko kunsan tsakanin mata da miji sai allah dandanan ta shawo kansa ya hakura to nan dai bayan kwona biyu aka kai kudin rukaya da na mimi komai iri daya saide mota da dady ya sayama mimi shine bai sayawa rukaya ba ansa wata biyu auren rukaya wato bayan wata daya da auren mimi kenan rukaya tayi matukar bakin ciki da taji hada wata abdallah zai aura anma da taji abdallah baya Son wacan hankalinta ya kwonta saide mahaifin abdallah yasha zagi kwondo kwondo
Tunda akasa ranar auren mimi kulum sai momy ta bata abubuwa tana sha bayan tsumi kuma ga wata mahin ta gairan jiki da momyn ta take sata dama akoy na urar ta gairan jiki a dakin ta ga sabululuka masu kyau da tabshin jiki sosai fatar mimi t'a kara kyau da tabshi dama ita ga tabshin fata wada ita kanta tsoron rabshin fatarta take ga gashin ta kulum an gaira shi an turare shi kunsan fulani akoy lakani bare kuma sun hada da lakanin buzaye
Kwonci tashi yau ake daura auren maimounatou sani tare d'à abdoulahi soleymane bisa sadaki dubu hamsin kuma a yau za a huce da amarya to mimi tasha nasiha kuma ta sha kuka haka tanaji tana gani aka tafi da ita su hafsa sune yan kai amarya kano tare d'à anty ta fati da kuma kanan mahaifiyar ta guda da kuma kanwar mahaifinta ita ma guda haka mimi tanaji tana gani aka tafi da ita kasar da bata san kowa ba kasar da ba nata aciki rayuwa kenan shigar magariba suka ma kano ta dabo tunbin giwa yaro ko dame kazo an fika gidan iyayen abdallah aka fara tafiya da ita tukon momyn Abdullah ga dukan alamu ta yaba da halin sarakuwar tata itama ta mata nasiha sosai sanan dadyn abdallah shima ya mata nasiha daga nan aka huce da ita gidan abdallah sosai suka yaba da gidan nata domin ya hadu iya haduwa saide ace fatan alheri bare da suka shiga falon abin ba Acewa komai dasuka huce dakin da akace na mimi ne way aljannar duniya kenan domin wasu irin kaya ne zance tunda uwata ta haifeni ban taba ganinsu ba ina kalon su oo saida aka suma tsabar rudewa domin mahaifin abdallah shi yayi mata komai ya hana mahaifin mimi yayi dan haka shima mahaifin mimi yasa a masa odar mota range rover daga kasar waje direct aka huce da ita kano domin acewar sa kyauta Ce zuwa ga dansa abdallah
,aci gaba da gashi 🍇
Maimou love😘
[4/12, 14:30] +227 80 22 99 15: 👩⚕Labarin👩⚕
Maimounatou🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 🇳🇪 🇳🇪 🇳🇪🇳🇪
Na✍
Maimouna Matar abdoulaye AM💋
Dedicated to hassana dan larabawa end khadeey pinky
🍉page9/10🍉
🍓🍓🍓🍓🍓
To masha allah ankai mimi gidan ta tangameme mai kyau da tsaruwa abun ba a cewa komai dan in na zauna na fada muku irin tsaruwar gidan to sai mu kwona mu tashi ban gama zayane muku ba iyayen amarya dai sunga ango bisa ga jajircewar mahaifin sa yazo ya gansu har sun gaisa saide amarya sam bata sashi ba a idonta kwona biyu kenan da kawota kuma yan uwanta duk sunyi shirin tafiya dan haka ta jirgi suka tafi mimi tayi kuka sosai kafin su tafi ba kamar ita da hafsa dan sun shaku sosai bayan tafiyar su gidan ya mata shiru dan haka ta fito falo sanye da riga da wando ta zunbulmo katon hijabi
Ta fito harabar gidan ma'aikata na ta gaisheta ta ko ina nan ta fara yawace gidan sosai ya birgeta ba kamar gurin basket-ball da wurin picine wato wurin wanka da t'a gani abokan ta kenan sosai wurin da tsarin ya birgeta ko ba komai zata ringa motsa jiki
Nan ta xauna ta fido kafafunta tasa cikin ruwan tana wasa da kafafunta ta jima sai marece ta koma cikin gidan tana shiga ta shige kurya dakinta wani dan roba naga ta dauka da wani abu baki baki ta debo ta shafa a fuskarta domin tasha alwashin cewa mai gidan nan ba zai taba ganin fuskarta ba ta asali gwonma yaga muninta ko ya sake ta ta koma kasar ta ta cika burin ta na zama cikakiyar likita nan ta shafa wanan bakin abun take fuskarta ta koma wata kala tayi muni wata irin kala ta koma gatanan dai abdallah ne ya shigo yana waya da rukaya nan ya zauna falo yana waya mimi ce ta fito da katon hijabi da fuska da muni dukawa tayi gap dashi ta gaida shi domin ta lura shine mijin nata wani zabura yayi ke wacece ke dan rainin wayo kina mai aiki zaki zo har inda nake ta dago ta kalesa saida gaban ta ya fadi ashe haka yakeda kyau saurin ankarar da ita da yawunsa ya tofa mata ke aljana Ce ko mi tace aljana kuma nice matar ka mana saurin tashi yayi tsaye saman salon ya gwolo ido waje kece mi nice matar ka ta kara maimaitawa wani wawan mari ya sakar mata ni kaina saida na rikice da jin wanan marin kece jakar da aka Aura min kece kazamar yar kauyen da aka Aura min ya allah daddy ka cuceni hada yar kwolar sa a idanu ki bace min da gani kuma daga yau kar na kara ganinki ko inda nake wly badan daddy yace zai tsine min matsawar na sake ki ba to da na sake ki a yau din nan maza Je ki bani guri nan ta tafi anma sai taji ba dadi a cikin ranta
Dan haka kaway taji wani abu a cikin ranta ya mata shigar sauri niko nace anya dai mimi hum da gudu ta shige dakin ta ta haye gadon ta t'a fara kuka nima na gaji da zaman nan inason in koma gida wurin yan uwana momy daddy nayi kewarku sosai nan tayita kuka daga karshe barci ya doke ta daga nan
Abdallah na shiga dakinsa ya fara kuka kamar karamin yaro dady ka cuceni karasa wada zaka auramin sai wanan mai kama da dodo nan dai shima barci ya kwoshe sa daga nan
Bangaren rukaya ko sosai take jin zafin auren abdallah dan tana tsananin kishin sa ta fito tana kuri ita ala dole ga mai kira Coca cola nan kawayen ta suka fara zugata sai ke mai kirar kalangu abin so ga ko wane da namiji sai ke mai gaba da baya uwa uba ga kyau kamar ke kikayi kanki saike matar so a gidan abdallah daga ke babu wata na baki naira dubu hamsin saboda wanan kirarin naki saudat ta waro idanu waje tace duk ni kadai ke kadai man amina ta kaleta tace nifa kefa me kikayi tayi shiru bata Ce komai ba unhum rukaya nace ya kamata muje wurin boka fa asan yanda za ayi da wanan kishiyar taki rukaya ta yabe baki tace saudat ba sai ankai ta ba wurin boka domin jiya tsananin munin ta har kuka yayi da muna waya yake shaidamin kinga ko wanan ba sai an kaita wurin boka ba kaway zata zamar min yar aiki na ta gaira min daki ta mana abinci shine aikin ta yayi sai kinyi ta abdallah kina ganin babu matsala cewar amina babu matsala kar ku manta fa Abdallah yana matukar tsanar munanu dan haka ba wata matsala
Zaman kadaici ya ishi mimi Dan haka saida ta daidaici abdallah baya gidan kuma tasan ba zai dawo ba sai dare dan haka tarshirya cikin kayan baskets ball dinta ta fita sai baya nan ta dauki ball ta fara bugawa haka tayi tayi har saida taga za afara kiran salar magariba tukon ta tsaida duk tayi zufa toilettes ta fara hucewa tayi wanka tukon ta dauro arwala ta fito ta gabatar da salah ta bayan ta gama ta dauki kur'ani tana karantawa bayan ta gama taji wayar ta na ringin nan ta dauka cikin farin ciki hello momy ina wuni momy nayi kewarku shine kun mantani ko ba mai nema na daga can bangaren momy tace to ma mimi wace kikeso in amsa miki kinata surutu kinki tsayawa mu gaisa
Ko kuwa to yi hakuri momy nayi kewarku ne shi yasa
Aci gaba da gashi 🍇
Maimou love😘
[4/12, 14:30] +227 80 22 99 15: 👩⚕Labarin👩⚕
Maimounatou🇳🇪
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
Na✍
Maimouna Matar abdoulaye AM💋
Dedicated to hassana dan larabawa end khadeey pinky
Hakika ina mai tayaki murnar kamala litafin ki yar kasata kuma yar garinmu wato sajida(Marubuciyar yar Mahaukaciya)
Ubangiji allah ya kara daukaka muna jiran sabon litafin ki mai suna daga tafiya dokan sodja 😉😘
0 comments:
Post a Comment