Kusan kwanaki su zeenah sukayi suna jinyar jikin su yayinda suka qudiri niyyar sae sun rama abinda aka musu fiye da wnn.
6angaren bintu kuwa abinda sukayiwa su zeenah yasa ta d'anji sauqin abinda take ji a ranta amma kullum cikin tunani da nadamar abinda ta aikata take ga kewar waheed da takeji sosai a ranta wanda duk ta tuna aure zaiyi sae ta zubar da qwallah.
Rnr da taji an d'aura auren sa da husna kuwa kuka tayi tmkr wacce akayiwa mutuwa sae anti Hafsa ce ta zauna tayi ta rarrashin ta tana bata magana.
Ranar wata asabar
Anti Hafsa ce zaune ita da mijinta suna fira inda a cikin firar ne yace"ni kuwa Hafsa me zae hana bintu ta ci gaba da zuwa aiki da zaman nn da takeyi kullum cikin damuwa.
Anti Hafsa tace"wlh kuwa kmr ka sani kullum cikin damuwa take musamman da taji waheed yayi auren nn bata da sukuni kwata kwata ko d'aki ma bata cika fitowa ba sae idan na kirata tazo muci abinci snn take fitowa da zarar kuma mun gama sae ta koma.
Mijin anti Hafsa ya numfasa yace"to Allah sauwaqe amma yana da kyau ki bata shawara ta rage damuwar nn a ranta kar ta janyowa kanta wani ciwon.
Anti Hafsa tace"Abban ilham wlh ba yanda bnyi ba kan ta rage damuwar nn a ranta amma ina,inaga sae na had'a ta da Abdallah gobe yace zae shigo daga nn ma sae in gaya masa zancen komawar ta aiki dmn nasan in shi ya mata magana zata koma.
Yace"hakane nama manta ban gaya miki ba gobe jabir zae zo cewa da qanin shi"
Anti Hafsa tace"ae ya kirani ya gaya min sae murna yake anyi posting d'insa a nn zae yi service.
Mijin anti Hafsa yace"hm jabir abinda yake so knn ya kuma samu ae dole yayi murna.
Yana kaiwa nn kawai sukaji sallamar sa ya shigo janye da akwati dukkan su saeda sukayi mamaki mijin Anti Hafsa yace"Aa jabir kaeda kace sae gobe zaka shigo kuma shine yau ka mana bazata"
Jabir yace"kayi haquri yaya wlh ina cikin kewar ganin ku sosai gashi kuma nasan gobe zaka koma abuja shine nace bari inxo yau mu gana musha fira daren yau nawa ne ba na anti ba.
Dariya mijin anti Hafsa yayi itama Anti Hafsa tayi dariya had'e da fad'in bari inje in kawo ma ruwa kasha,kasha hanya.
Bayan ta kawo mishi ruwa da lemu da abinci yaci yasha sukayi zaune sae firar bayan rabuwa suke har yana tambayar bintu Anti Hafsa tace"ae tana ma gidan nn bari in kira ma ita ku gaisa"
Yace"Allah sarki mutuniya ta tana gidan nn knn kira min ita mu gaisa mun jima bamu had'u ba.
Anti Hafsa ta kira mishi bintu wacce suna gama gaisawa ta koma.
Jabir yace"amma dae anti bintu bata da lafiya koh dmn gabad'aya naga yanayin ta ya sauwa kominta a sanyaye kuma bata yi murna irin wacce idan mun had'u muke yi ba.
Nan Anti Hafsa ta gaya masa duk abinda yake faruwa yayi shiru kana ya cire hular kansa cikin jimamin abun yace"bintu tayi babban kuskure Anti wanda ko kad'an banji dad'in sa ba wlh, yanzu ya za'ayi a shawo kan wnn al'amarin.
Yako za'ayi jabir Allah dae ya sauwaqa kawai.
Mijin Anti hafsa yace"amin" had'e da fad'in"tashi muje ka sauke kayanka a BQ"
Jabir da
duk jikin sa yayi sanyi ya miqe janye da akwatin sa suka tafi.
Washe gari guraren 12 na rana Abdallah yazo.
Bintu na d'aki taji shigowar shi ta fito ta same shi zaune kan doguwar kujera ta gaida shi wanda cikin sakin fuska ya amsa mata had'e da kama hannun ta ya zaunar da ita kusa dashi yana kallonta da kulawa yace"bintu ki rage damuwar nn kinji jibi duk yanda kika rame.
Bintu ta kalle sa qwallah tap a idonta kmr zasu zubo tace"ta ya zan iya cire damuwa a raina yaya bayan har yanzu umma da Abba fushi sukeyi dani ba wanda ke d'aukar wayata a cikin su.
Da saurin sa yasa hannu ya share mata hawayen da suka gangaro kan kumatun ta yace"is ok bana son kukan nn kin sani kuma da sannu su umma zasu daina fushi dake kinji"
Gyad'a masa kae tayi tare da qara share hawayen fuskarta
Abdallah yace"da akwai wani abinda kike so?
Tace "um um ba komai"
Anti Hafsa dake jera masa kayan motsa baki tace"ni dae ke son ta koma aiki dan wnn zaman in banda damuwa ba abinda yake qara mata.
Abdallah ya kalli bintu yace"kinji abinda anti Hafsa tace"
Bintu tace"naji zan koma"
Yace"gud sauko muci abinci toh"
Girgiza kanta tayi alamar a'a snn ta tashi ta nufi d'aki sae kallon ta yake har ta shige.
Anti Hafsa tace"shike nn kuma ita da fitowa sae idan na kirata muci abinci ko abincin ma kad'an take ci ta koma.
D'auke da damuwa Abdallah ya girgiza kansa snn yace"jabir fa jiya ya kirani a waya yace min ya shigo koh"
eh amma ya fita kasan yanada frnds sosai a garin nn.
Hakane shifa yaya yusuf ko ya koma Abuja?
Eh tunda sassafe ya koma yama bada saqon wasu hadaddin kaya da ya siyo maka a abuja yace a baka.
Allah sarki shidai baya gajiya nagode sosai Allah ya saka masa da alkairi sae na kirasa in masa godiya.
Tace"Bare gaskiya kayan sunada kyau iri d'aya ya siyo maka kaida jabir dan yaga Hassan da usaini ne ku bakwa son rabuwa idan kun had'u".
Murmushi Abdallah yayi yace" bari ma in kira jabir d'in yazo muga juna dan ganin nake bazan kwana a nn garin ba yau zan koma"
Hm kai ma dae ka fad'a dan kasan jabir kam bazai barka ba kuma nima bazan barka ba sae ka mana ko kwana d'aya ne.
Yace"Anti kisan dis week zan koma school kuma da na koma exam zamu fara,karatu nakeyi ba dare ba rana har bana son in tsallake ko rana d'aya"
Hm kaji iyayen karatu sae kace kanku aka fara.
Abdallah yayi murmushi yace"anti kinsan karatun namu dole sae da haka ba irin wanda zaka sako wasa a ciki bane.
Hkne amma dae kasani nn zaka kwana se gobe da yamma ko zaka koma.
Ba komai anti naji snn ya d'aura da cewa"anti wae ina su ilham ban gansu ba?
Su ilham suna islamiyya duk weekend 8am suke zuwa su dawo 8pm
Yace "gud tsarin ya min inace suna maida hankli kuma suna fahimta?
Tace"wlh sosai kuwa suke maida hankli kuma suna fahimta musamman ilham"
Yace"mashaa Allah,Allah ya taimaka yasa sufi haka "
Amin cewar Anti Hafsa.
Bayan Abdallah ya gama cin abinci ne ya kira jabir yazo suka tafi can BQ sae firar bayan rabuwa suke dan sun jima sosai basu had'u ba.
A nn jabir ke jajanta masa abinda ya faru game da bintu har yana nuna masa rashin jin dad'in faruwar hakan.
Abdallah yace"hm bari kawai jabir abun ba dad'i gaskiya bansan me ya d'ebe ta ba har taji bata ra'ayin haifuwa a lokacin da ta sami ciki wae ita bata tashi ba se ta had'u da su zeenah suka qara kaita suka baro"
Jabir yace"wlh ni tun lokacin da na fara ganin su naji yaran basu min ba kwata kwata ashe mugun haline dasu har wnn zeenah d'in tana wani liqe min wae ita sona take jaka kawai d'an chakwai dani ita kuma jibgegiya ina zan tafi da ita.
Dariya Abdallah yayi had'e da fad'in"kae baka da dama jabir ae zeenah ba wani jiki ne da ita ba kai dai kawai baka sonta"
Jabir yace"wlh Allah ni ta min qatuwa nafi son er chakwai dae dai ni wacce zamu jima muna damawa bata zamar min uwa ba.
Allah ya baka to
Jabir yace"Amin kafin yake cewa ni kuwa Abdallah har saki nawa ne waheed yayiwa bintu da baza a sake zuwa a basu haquri ba ko Allah zae sa wnn karon ta saurare mu dmn nidai bana son ganin bintu cikin damuwar nn nafi son ta koma d'akin mijinta wlh.
Abdallah ya numfasa snn yace"wato jabir bintu taqi ta snr da kowa ko saki nawa ne kuma har ga Allah naso in sake komawa gun mami in bata haquri amma yaya Abbas yace wlh duk yaji na sake zuwa nida shi ne.
Haba shikuwa yaya Abbas kan me zae ce haka.
Hm yaji haushi ne sosai akan abinda yaji bintu ta aikata dmn kasan a dalilin sa ne muka san waheed sbd amintar da ke tsakanin su,kuma kasancewar waheed mutum ne da baya da wani girman kai akai akai in ya sami lokaci yake kawo masa ziyara har ya zamo tamkar d'an gida haka muma muka d'auke sa kmr wani d'an uwan mu har soyayya tazo ta shiga tsakanin sa da bintu wacce tun bata kulashi sbd shirin da basa yi da yaya Abbas har tazo tana kulashi.
To ganin haka ne yasa na kira yaya Abbas na gaya masa abinda ake ciki da niyyar yazo muje gun mami ko ganin sa zae sa ta saurare mu amma yace kar ma in sake masa mgnr bintu ya kuma rantse kan kar in kuskura in koma gidan, inna tafi yaji nida shine,na san halin sa mutum ne mai baqar zuciya wlh komai zae iya faruwa idan naje sbd gabad'aya halin Abba ne dashi ya kuma zo shima ya zama soja like father like son shiyasa dole se na bishi a sannu har in samu ya yarda muje ba tare da mun sami wata matsala nida shi ba.
Jabir ya numfasa yace"hkne kam dmn a d'an sanin da na masa na fahimci mutum ne da kwata kwata baya son raini dole sae an bi yanda yake so ko za'a zauna lafiya.
Ae kam
cewar Abdallah wanda da haka sukayi shiru ba wanda ya sake cewa komai sae tunanin da kowa keyi a cikin ranshi.
Bayan sati biyu da faruwar haka,tuni bintu taci gaba da zuwa gurin aikin ta wacce har yanzu ta kasa cire damuwa a ranta ko zuwa aiki a kan dole take yin shi.
Haka 6angaren waheed yana rayuwa ne kawai dmn farin cikin mahaifiyar sa ba dan yana jin dad'in rayuwar ba,
wanda ba dan yana bin umarnin ta ba da ba wata mace da zaiyi rayuwar aure da ita bayan bintu da har yanzu yana cikin qunci da takaicin abinda ta aikata a gareshi ba wae don ya yarda cewa ta aure sa ne dan dukiyar sa ba sae dan kanme ta aikata haka a gareshi na zubar mae 'ya'ya da tayi da kullum cikin tunani yake ya kasa bawa kansa amsa hakan yasa Amaryar sa Husna sam bata jin dad'in rayuwar auren nasu sbd kwata kwata bata samun wata kulawa a gurin waheed.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 29_*
Sannu sannu lokaci keta tafiya kwanaki da watanni sunja amma still bintu na nn kullum cikin damuwa da tunani,in ta zauna d'aki bata da aiki sae dai ta shiga video a wayar ta tayi ta kallon video records d'in da sukayiwa juna ita da waheed na rayuwar su mae cike da zallar so da ban sha'awa wanda hakan kesa ta qara jin tsanar kanta suna rayuwar su mae dad'in gaske amma ta zamo silar wargaza duk wani farin cikin su da kullum in ta kwanta bacci sae tayi mafarkin waheed yazo cike da murmushi ya rungume ta yana fad'in ya yafe mata duk abinda ta mishi tazo su shinfid'a sabuwar rayuwar da tafi ta baya ma.
Ko yanzu ma kwance take tana bacci cikin mafarkin ta da yafi na kullum dad'i,dan ganin kanta tayi ta koma gidan waheed suna rayuwar su mai cike da dad'i tamkar ba wani abinda ya faru har ma tana d'auke da ciki d'an wata shida waheed sae ririta ta yake tamkar zae had'iye ta ga mami akae akai sae tazo ganin lafiyar ta snn hankalinta ke kwanci.
Firgigit taga ta tashi daga mafarkin wacce cikin rashin kuzari ta tashi zaune tare da had'e kanta da guiwa hawaye masu zafi suka shiga silalowa a hnkli kan kumatun ta dmn ko kad'an bata son tana irin wnn mafarkin ta farka amma ta rasa meyasa kullum sae tana cikin yin mafarkin ta mae dad'i ta ganta kawai ta farka ba tare da wani ya tashe ta ba,kaddai haka na nufin mafarkin ta bazai zama gaskiya ba.
Nan ta saki kuka a hankli sae ga anti Hafsa ta shigo d'akin kae tsaye ta had'iye kukan ta kuma sa tafin hannunta a 6oye tana share hawayen fuskarta.
Anti Hafsa ta qarasa gurinta ta zauna a hnkli kusa da ita tare da d'aura tafin hannun ta kan gadon bayan bintu tace"bintu sau nawa zan roqe ki kan ki rage yawan kukan nn da damuwar nn basune mafita ba addu'a ce mafita amma kinqi ki daina shin ni ban isa insa kiyi abu bane ko in baki shawara?
Bintu ta d'ago kanta a hankli tana kallon anti Hafsa snn ta girgiza kanta tace"ba haka bane anti Hafsa kiyi haquri ina cikin yanayinda bansan ta yaya zan iya fidda damuwa a raina ba ko da naso hakan kuwa dmn na kasance wacce iyayena ke fushi dani ta yaya zanga wani haske har damuwa ta cire a raina ba tare da sun daina fushi dani sun yafe min ba.
Ta qarashe mgnr ne cikin kuka, cike da tausayi Anti Hafsa ta rungume ta sae rarrashinta take tana fad'in"shiyasa nake son ki dage da yin addu'a ko Allah zae sassauto zukatan su umma su daina fushi dake"
Tace"Aunty ni kam wace irin addu'a ce banyi ba ba dare ba rana amma kmr banayi sbd na riga na aikata abinda dole sae Allah ya hukuntani.
Allah mae yafiya ne bintu dan haka kici gaba da yin addu'a ki kuma ci gaba da yawaita karatun qur'ani fiye da yanda naga kinayi da sannu zakiji qunci da damuwar dake ranki suna tafiya kinji"
Bintu ta gyad'a kanta anti Hafsa tace"to tashi muje jabir ne yake neman ki"
Ba musu ta tashi suka fito falo jabir dake zaune kan doguwar kujera sae faman danne danne yake da wayar sa har bintu taje ta zauna kusa da kujerar da ke facing d'inshi snn ta gaishe shi.
Sae a snn jabir ya d'ago ya kalle ta had'e da fad'in "iyayen bacci kin tashi duk lokacinda na shigo se ace min kina bacci ni kam wae ba kya gajiya?
Ya qarashe mgnr ne sae kallon ta yake da kulawa ita kuwa kanta qasa tayi shiru ba tare da tace mishi komai ba sbd mostly ba dan tana jin bacci take yin sa ba sae dan kawai ta ganta tanayin mafarkin sun shirya ita da waheed da sam bata son taga ta farka.
Jabir dake kallonta bae sake ce mata komai ba kasancewar sa mutum ne da baya son takura kowa wanda ko kad'an baya son ganin mutum cikin damuwa koda bai san shi ba kuwa.
Anti Hafsa wacce ta fito daga kitchen d'auke da fruits a plate an yanyankasu so cute ta kai gaban jabir ta ajiye snn ta zauna a kusa da kujerar da yake zaune tana kallon bintu tace"wae bintu ba magana naji jabir na miki ba amma kin masa shiru kmr bada ke yake magana ba"
Jabir da ya kai slice d'in kankana a bakin sa yayi murmushi yace"anti bata son damuwa ki barta kawai"
Anti Hafsa tace"hm bintu duk gabad'aya ta sauya sae kace ba kaine abokin wasan ta ba da har guje guje kukeyi a tsakanin ku"
Jabir yace"anti kinsan wancan lokacin bata cikin wata damuwa yanzu kuma akan mata uzuri"
Hakane
Cewar Anti Hafsa wacce still idonta na kan bintu tace"tashi to ki tafi dama ganin ki da ba yaya ne yace ina kike"
Bintu bata ce komai ba ta tashi ta bar gurin jabir ya bita da ido har ta shige d'aki kana ya maida duban sa gun anti Hafsa yace"anti meyasa kika ce ta tafi?
Tace"to jabir
ganin nayi ta zamar maka kmr wani foto kana mata magana ba amsa.
Duk da haka anti ae da kin barta sbd yawan zaman d'akin nn ita kad'ai na qara mata damuwa amma ko bata cewa komai in ta zauna cikin mutane yafi.
Anti Hafsa tace"wato jabir damuwa nake ji in na ganta shiru bata cewa komai shiyasa nace ta tafi d'aki amma ni kaina bana son zaman d'akin da take yi wlh.
Jabir ya numfasa yace"to me zae hana kuyi mata aure anti"
Aure kuma jabir meyasa kace haka?
Anti kinsan ni mutum ne da bana son ganin kowa a cikin damuwa tunda daidaita tsakanin su da waheed bai yiyu ba har gashi tuni ta gama idda y not idan da akwai wanda ke zowa gurinta ace kawai ya fito.
Hmm! jabir wa kake tunanin bintu zata kula a halinda take ciki snn waye zai ji dalilin rabuwar ta da mijinta da kuma matsalar mahaifar da take d'auke dashi ya aure ta.
Anti duk wani mae sonta da gaske wa en nn hujjojin ba wata matsala bace burin sa kawai ya aureta.
Hm Jabir knn da kmr wuya samun irin wnn masoyi dmn ftr kowa yayi aure ya hayayyafa dan haka kama bar wnn zancen.
Anti kuskure d'aya ne bintu ta aikata shine zubar da cikin farko da tayi sauran duk makirci ne aka shirya mata, matsalar mahaifar ta kuwa inshaa Allah matsala ce da za'a iya magance ta.
Anti Hafsa tace"akwai abinda baka sani ba jabir shine kwanakin baya na d'auki bintu mukaje asibiti dmn a bamu maganin da zae magance mata matsalar mahaifarta a nn likita ya bamu tabbacin cewa matsalar mahaifar ta babbar matsala ce da sae an fita da ita waje an mata aiki sbd wnn maganin da su zeenah sukayi sa mata ya illata mahaifar sosai ta yanda ko ta sami ciki bazai kai koina ba zae zube.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!amma anti shine ba'a sa yaran qara ba a biwa bintu haqqinta wnn cin amanar ae yayi yawa.
Wlh jabir bintu ce ta roqe ni kan kar inyi haka dmn bata son umma taji ta qara shiga wata damuwa,amma ba dan haka ba naso na sasu qara a hukunta su ta yanda ko maqiyin su suka ga zae cutar da bintu wlh baza su barshi ba.
Shiru jabir yayi can yace"Anti idan dan wnn matsalar ne ni naji na gani idan har bintu tana sona wlh zan aure ta.
Da mamaki anti Hafsa ta kalle sa tace"jabir kasan me kake fad'a kuwa kaifa saurayi ne da baka ta6a yin aure ba"
Yace"Anti nasan zakiyi mamakin abinda zae fito daga bakina shine,haqiqa na jima ina son bintu tun ba yau ba wato tun lokacin auren ku da muka fara had'uwa naji ba wata 'ya mace da nake so kmr ta, amma na kasa snr da kowa har ita kanta ba dan komai ba sae dan ganin cewa a lokacin yarinya ce sosai kuma nima ba wasu shekaru ne dani ba se na barshi akan sae ta girma dai dai nima na samu na kammala karatu na fara aiki snn ko zan bayyana sirrin da ke raina, kwatsam tana kammala secondry school naji za'a mata aure,ba yanda na iya dole na haqura dmn na riga na makara amma na shiga cikin tsananin tashin hankli da baqin cikin rashin samunta wanda dalilin haka ne ya janyo min matsaloli da dama a school har mutane suka d'auka ko rasuwar Abban mu ne ya ta6ani da yawa.
Anti Hafsa dake sauraren shi tayi shiru dmn haqiqa ta tuna lokacin da yake ta samun matsala a shchool da kowa yayi tunanin ko mutuwar mahaifin su ce ta ta6a shi da yawa dmn lokacin auren bintu yayi dai dai da mutuwar mahaifin su wanda ba dan matsalolin da yayi ta samu ba da yanzu ya kammala school har ma ya fara aiki.
Tace"haqiqa jabir na tausaya maka amma ina mai baka haquri auren ka da bintu ba zae yiyu ba"
Cikin tashin hankali jabir yace"dan Allah meyasa kika ce haka Anti?
Sbd sanin kanka ne bazai yiyu ba, da dai ace tun a wancan lokacin ne da kaji kana sonta ka fad'a da zaka same ta amma yanzu bazai yiyu ba gaskiya kayi haquri.
Yace"naji nayi kuskure da ban fad'a a wancan lokacin ba amma dan Allah tunda yanzu na fad'a kiyi haquri ki taimaka min tun kafin in rasa damata wlh still ina sonta anti ko kad'an ban ta6a jin sonta ya ragu a zuciya ta ba sae ma qaruwa da yake.
Tace"baka fahimce ni ba jabir ni matsalar da bintu take d'auke dashi yasa nace aurenku bazai yiyu ba snn kuma a matsayin ka na saurayi bai kamata ace ka auri wacce ta ta6a yin aure ba,byn kuma irin matsalar da take dashi a mahaifar ta
u have to think kayi tunani kowa ka gaya ma mgnr nn bazae barka ba.
Yace"anti koma mene ne ni nace naji na gani ina sonta a haka nidai kawai kice min kin amince"
Tace"Aa bazan ce na amince ba jabir kuma ina roqon ka dan Allah kar ka bari yayanka yaji wnn mgnr kaji"
Shiru jabir yayi yana kallon ta cikin marairaice fuska yace"anti ki gaya min dan Allah ko dai wani mugun hali nake dashi da ba kya son bintu ta aure ni"
Anti Hafsa ta girgiza kanta dan ko ta ina jabir baya da wata makusa hadadden saurayi ne mae kyaun gaske gashi fari tas tamkar zuciyar sa sam bayada wani mugun hali.
Tace"ko d'aya jabir babu wani mugun hali da kake d'auke dashi dmn duk maccen da ta same ka ta gama yin sa'a a rayuwa kawai dai auren ka da bintu ne bazae yiyu ba,ba dan naqi ba sae dan yafi dacewa da kai ka sami yarinya buduwar mae cikakkiyar lafiya.
Jabir zae yi magana knn tace"dan Allah jabir kar kace komai kaji bana son mgnr nn tayi tsawo.
Take idanuwan jabir sukayi jajur suka ciko tap da qwallah ya tashi da sauri ya bar falon.
Anti Hafsa da ta bishi da kallo ta girgiza kanta dmn ya bata tausayi amma sam ba aikin hankali bane tace ta amince son kan zae yi yawa gwara kawai ya sami budurwar yarinya dai dai shi ya aura.
Nan ta bar falon wacce bata zarce koina ba sae d'akin su ilham gun bintu ta same ta zaune kan bed ta jingina bayanta da pillow waya a hannunta ta kafe idonta akan screen d'in wayar ko kyaftawa bata yi,
anti hafsa tayi tsaye tana kallon ta had'e da girgiza kanta snn taje kusa da ita ta zauna kan bedside drawer tare da kar6ar wayar bintu ta duba abinda take tunani kuwa shine wato pics d'insu ne take ta kallo ita da waheed da gabad'aya folder d'in ba wani foto sae nasu.
Kafin anti Hafsa tace komai bintu ta kama hannuwan anti hafsa cikin yanayin begging qwalla cike a idonta tace"Anti hafsa ina son yaya waheed bazan iya ci gaba da rashin sa a kusa dani ba,dan Allah ki taimaka min in koma gareshi wlh rayuwata bazata ta6a dad'i ba sae tare dashi"
Nan kawai ta fashe da kuka anti Hafsa ta jata jikinta sae rarrashin ta take.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 30_*
Bayan wasu en kwanaki da faruwar haka ne.
Da dare guraren qarfe tara Anti Hafsa ce ta fito daga wanka tana zaune kan dressing mirror tana shafa mai sae ga mijinta ya shigo d'akin cikin shirin sa na bacci yayi tsaye hannuwan sa cikin aljihun wandon sa sae kallon ta yake ta jikin mirror.
Murmushi ta sakar masa tare da juyowa tace"Abban ilham ya akayi wani abu kake buqata ne?
Sae da ya lumshe idanun sa a hnkli ya koma ware su a kanta snn yace"eh magana nake son zamuyi"
D'auke da murmushin da ke fuskarta ta taso suka je kan bed suka zauna tana kallon sa tace"ina jinka Abban ilham"
A hnkli ya d'an numfasa had'e da fad'in"me yake faruwa ne tsakanin ki da jabir da naga kwata kwata ya daina zowa cin abinci a nn sae dai inga kin aika masa?
Tace"ba komai nima haka kawai naga ya daina shigowa shiyasa nake aika masa qila yanzu yafi ra'ayin cin abinci shi kad'ai"
Yace"Aa akwai abinda aka masa yake fushi dmn jabir yafi ra'ayin cin abinci cikin mutane idan kuma kika ga ya d'auke qafar sa yaje yana ci shi kad'ai to lallai laifi aka masa yake yin fushi.
Anti Hafsa dake kallon sa tace"ce maka yayi na masa wani abu ne?
Aa ae bazai fad'a ba kin sani amma tabbas yana cikin damuwa duk da yace min ba abinda aka masa.
Anti Hafsa ta numfasa snn tace"hm Abban ilham jabir rigima kawae yake ji"
Wace irin rigima sae kace qaramin yaro ko wani iya shegen ne ya d'auko na son ya rainaki.
Ko d'aya ae kasan jabir baya da wnn asalima ni na masa laifi amma inshaa Allah zan same shi in bashi haquri.
Yace"wane irin laifi ne wnn da har ya iya yin fushi dake?
Tace"um um ba ruwanka nida d'an qanina ne?
Murmushi yayi tare da fad'in"au hakane ae idan tayi tsami ma ji"
Tashi tayi d'auke da murmushi a fuskarta tana fad'in"ae baza ma tayi tsamin ba bare kuji"
Murmushi kawai Abban ilham yayi ba tare da ya sake cewa komai ba ya tashi ya fita acewar idan ta kammala shirin bacci ta same shi d'aki.
Washe gari bintu ce a d'aki zaune kan darduma tana karatun qur'ani,Anti Hafsa ta shigo d'akin d'auke da sallama a bakin ta.
Sae da bintu ta kai aya snn ta amsa mata sallama had'e da gaida ta, Anti Hafsa tace"lokacin breakfast yayi fa kuma sae karatu kike tayi"
Tace"eh anti aya biyu suka rage min in qarasa surar nn in taso"
Tace"eyyah sorry na katse ki amma ina son dan Allah idan kin kammala kije BQ ki kiramin jabir acewar nace yayi haquri yazo muyi breakfast kinji.
Bintu tace"to"
snn Anti Hafsa ta fita daga d'akin.
Tana ida karatun ta rufe qur'ani ta kai shi inda ya dace snn ta fito bata zarce koina ba sae BQ sanye da qaton hijabinta har qasa.
Jabir na kwance idanuwan sa a lumshe kmr mai yin bacci ya soma jin knocking ya tashi cikin rashin kuzari kmr wani mara lafiya yazo ya bud'e qofa,ganin bintu yasa ya d'an saki fuskar sa cikin sauke ajiyar zuciya yace"bintu kece?
Tace"eh anti ce tace kayi haquri kazo muyi breakfast "
Shiru jabir yayi can yace"am sorry sauri nake in fita banida time d'inda zanyi breakfast amma kice mata koda kika zo ma baki sameni ba na fita kinji"
Bintu ta kalle sa kmr zata ce wani abu sae kuma ta gyad'a masa kae alamar taji kana ta juya ta tafi sae kallonta yake har ta 6ace ma ganin sa snn ya koma daga ciki.
Bintu ta sami Anti Hafsa da Abban ilham zaune kan dinning table suna jiran su ita da jabir.
A nn ta snr da Anti Hafsa cewa bata sami jabir ba ya fita.
Kafin anti Hafsa tace komai Abban ilham yace"ya fita? yanzun nn fa da na dawo daga kae su ilham school naga mashin d'insa a ajiye bai isa ace ya fita ba bare yau lahadi ina zai je da sassafen nn haka may be dai yana bacci bai ji lokacinda kike masa knocking ba bari inje in duba shi.
Koda yaje knocking d'aya biyu ya masa sae gashi ya bud'e qofa yace"ya akayi jabir ba kaji lokacin da bintu tazo tana maka knocking bane?
Naji har ma na fito mukayi magana.
Amma shine tace mana baka nn?
Eh nine nace tace bana nn.
Ko meyasa?
Yaya sauri nake ina so zan fita bana da time d'inda zan tsaya yin breakfast that's y nace tace haka bcos bana son kace sae na tsaya yin breakfast d'in.
Cikin rashin yarda da zancen jabir Abban ilham yace"ina zaka je da sassafen nn da har baka da lokacin tsayawa yin breakfast?
Shiru jabir yayi dan ba wani guri da zai je ya fad'a ne kawai.
Abban ilham yace"da kai nake magana ka min shiru"
Yace"yaya kayi haquri bana jin cin abinci ne"
Yaushe ka fara yin qarya jabir to ka sauya dan wlh qarya bata maka kyau,gaya min me ya had'a ka da Hafsa da har kake yin fushi da ita kuma kar ka kuskura kace min ba koma wlh"
Jabir yayi shiru dmn baya son ya fad'a kmr yanda anti Hafsa ta buqata yace"kayi haquri yaya i cnt tell u amma ka tambayi anti Hafsa zata gaya ma"
Guntun tsaki Abban ilham yayi dan ya soma kaishi maqura ya bar gurin ba tare da ya sake ce masa komai ba.
Ya dawo komai bai ce dasu Anti Hafsa ba bae kuma nuna wani 6acin rai a fuskar sa ba har suka kammala breakfast.
Bintu ce ta fara barin gurin nn itama Anti Hafsa ta tashi zata tafi sbd sauri take zata je ta kammala shirya ma Abban ilham kayan sa na tafiya.
Abban ilham yace"yi haquri hafsa zauna zamuyi magana"
Ba musu ta koma ta zauna idon sa akanta yace"mene ne wae yake faruwa tsakanin ki da jabir"
Murmushi tayi tace"wae Abban ilham meyasa kake son sae kaji, i have told u zanje in same shi in bashi haquri mu sasanta kanmu ba sae kunji ba.
D'an guntun murmushi yayi snn yace"wlh bafa zaku min yawo da hnkli ba ni sae naji me yake faruwa"
Anti Hafsa dake kallon sa a d'an shagwa6e tace"plz Abban ilham zancen nn bai shafe ka ba ka barni inje in qarasa had'a ma kayanka lokaci na tafiya.
Yace"Kar ki damu ni nama fasa tafiyar sae gobe inbi jirgin safe gaya min ina jinki me ya had'a ku".
Dariya anti Hafsa tayi had'e da jan karan hancin sa tace"ba wani nn kae dai so kawai kake in fad'a ba kuma zan fad'a ba d'in sirri ne nida d'an qanina"
Tana qarashe mgnr ta tashi da sauri zata bar gurin ya riqo hannunta ta fizge ta tafi da gudu zuwa d'akin shi tana masa dariya ya bita da kallo d'auke da murmushi kana ya tashi ya bita.
Koda ya tafi ya samu har ta d'auko jakar sa tana qarasa shirya masa kayan sa.
Ta bayanta ya rungume ta yasa hannu ya kar6e jakar ya ture ta gefe.
Cikin yanayin shagwa6a ta juyo tana kallon shi ya zauna tare da zaunar da ita kusa dashi yana kallonta yace"Allah dagaske nake miki na fasa tafiya sae gobe"
Dad'i taji har ranta ta kama hannuwan sa d'auke da murmushi tana kallon sa tace"dagaske Abban ilham meyasa?
Sbd na fahimci damuwar da ke fuskar jabir ba qaramin abu bane ya had'a ki da shi shiyasa nake son sae na sasanta tsakanin ku snn ko zan tafi dan na fahimci kmr shine mai laifin shiyasa kk 6oye min ba kya so in sani kar in masa fad'a koh?
Lumshe idanun ta tayi a hnkli had'e da koma ware su akanshi ta qara kama hannayen sa sosai a cikin nata snn tace"ba yada laifi Abban ilham kawai dai abinda yake so ne bazai yiyu ba"
Mene ne yake so?
Hm wae bintu yake son zae aura nn ta gaya masa duk yanda sukayi ba abinda ta rage.
Murmushi Abban ilham yayi had'e da girgiza kansa yace"hm in banda abinki hafsa muda ku ae mun zama d'aya kan me zaki hanashi dan yace yana son bintu bashi yace yana sonta a haka ba"
Haba Abban ilham kaddai kaima biye masa zakayi kayi tunani mana bae kamata ba wlh.
Yace"kinsan Allah Hafsa wlh tun farko ba jabir kad'ai yaso bintu ta kasance matar sa ba har dani dmn tun lokacinda na fara zuwa zance gidan ku naga bintu sak ke naji ba wanda nake son ya aureta kmr jabir amma sae na bar mgnr a raina acewar sae ta kai munzalin aure in kwad'aita masa zancen ashe shi da ya ganta yaji yana sonta ya bar abun a ransa bae ta6a gaya min ba sae yanzu da naji labari a bakin ki wanda zurfin cikin mu dani har shi yasa muna ji muna gani muka rasata, yanzu kuma da yake ganin ya sami dama kice masa a'a ae dole yayi fushi dake.
Anti Hafsa ta numfasa snn tace"Abban ilham kar ka manta matsalar bintu matsala ce da sae an fita waje da ita, fita waje kuwa ba qananun kud'i bane"
Wnn ba matsala bane hafsa kawai amincewar ki muke so idan kuma kince a'a knn kin raina da kamar mu kina ganin baza mu iya ba"
Ba haka bane Abban ilham koda ni na amince nasan bintu bazata amince ba sbd a kullum bata da burin da ya wuce ta koma gidan waheed kaga kuwa bai kamata ace naje mata da wnn zancen ba.
Shiru yayi na d'an lokaci kafin yake cewa"to ke Hafsa yanzu a ganin ki akwai yanda za'ayi bintu ta koma ga waheed?
Eh hanya d'aya ce wato yaya Abbas shine kad'ai muke tunanin idan yaje mami zata iya ta saurare shi amma shi kuma ko mgnr bintu baya son a masa ya kuma rantse kan kar Abdallah ya kuskura ya koma zuwa gun mami,to shine fa har yanzu Abdallah sae fmn lalla6ashi yake kan yayi haquri yazo suje su sami mami amma fafau yaqi yarda acewar ita bintu da ta jawa kanta taje tayiwa kanta magani ae ba uban da ya ake ta.
Abban ilham ya numfasa snn yace"hm Abbas knn soja sarkin zuciya gobe idan na koma Abuja zanje har office d'insa in same shi muyi magana inshaa Allah bazan dawo weekend d'in nn ba sae tare dashi muje a sami mami a sasanta dmn ba abinda yafi dacewa irin bintu ta koma d'akin mijinta shi kuma jabir se yayi ya haquri ya nemi wata"
Cikin nuna jin dad'i Anti Hafsa tace"nagode Abban ilham"
Yace"haba Hafsa ai kin wuce haka a gurina bari inje inga jabir in lalla6a shi ya haqura"
Tace"Aa jabir d'in ba ya fita ba"
Inafa duk fushin da yakeyi da ke ne yace ace baya nn.
Allah sarki jabir yayi haquri kar yaga laifina ba yanda zanyi ne wlh.
Yace"ae dolen shi ma ya haqura"
Ya qarashe mgnr ne kafin yake fita.
Ranar Monday kmr yanda ya fad'a da yaje Abuja har office yaje ya sami Abbas cikin fara'a sosai suka gaisa da juna snn Abban ilham ya snr dashi abinda ke tafi dashi.
Abbas ya gyara zaman sa snn a natse ya saki d'an guntun murmushi yace"Alhj yusuf kaima zaka sako kanka akan mgnr wnn er rainin hankali da tabi duk ta zubar mana da mutunci a idon duniya tasa anayiwa iyayen mu kallon kwad'ayayyu masu kwad'ayin abun duniya.
Abban ilham yace"ae wnn ba laifin ta bane ka sani duk makirci ne irin nasu zeenah "
To ae ita ta janyo komai dan haka ku fita harakarta kawai ae ba uban da ya aike ta.
Kayi haquri dai Abbas kasan bintu yarinya ce kuma tayi matuqar nadama fiye da yanda kake tunani wacce tun lokacinda abin ya faru take cikin damuwa har yau ta kasa cire damuwa a ranta ka tausaya mata dan Allah.
To Alhji yusuf naji me kuke so nayi?
Gud so nake dis weekend kazo muje sokoto mu sami mami mu sassanta al'amarin nn tare da yi mata bayanin komai ta yanda bintu zata fita daga zargi.
Abbas ya numfasa snn yace"a gaskiya Alhj Yusuf bana jin da akwai wani sauran mutuncin da zamu iya tunkarar mami kaf bintu ta 6arar mana dashi kawai dai idan ta sami wani mijin se tayi aure idan auren take buqata,
amma nikam bazan iya wnn abin kunyar ba, inaji ina gani fa yanzu se waheed yayi ta kirana a waya bana iya d'agawa.
Abban ilham ya numfasa yace"Abbas meye abin kunya kuma ea gwanda muje muyi mata bayanin komai tasan duk makirci ne ba da gaske ba akan tayi ta kallon mu da abun.
Hakane banqi mgnr ka ba but zanyi tunani akae duk shawarar da na yanke akai zan kiraka a waya in snr da kae.
Aa fa halinka na sani Abbas ba makawa ka fad'i hakane dan kawai ka huta dani dan haka ba zan fita daga office d'in nn ba har sae mun tsaida gaskiyar magana d'aya.
Murmushi Abbas yayi dan ba qaramin aikin sa bane yace"ae kasan bazan maka haka ba dmn mutuncin mu ne zae gyaru idan munje kaga kuwa bazan yi watsi da mgnr nn ba kawai dai bintu ce bazan sa bakina akan komawar ta ba idan sunyi ra'ayin komawar ta fine idan kuma basu buqata ba shikenan ita ta sani.
Dariya Abban ilham yayi yace"to ae kai Abbas mgnr komawar ta ne jigon zuwan mu dmn sanin kanka ne ba abinda yafi dacewa irin bintu ta koma d'akin mijinta yayinda ni kuma hankalina zae fi kwanciya idan ta koma kona samu jabir ya fidda ran samunta gabad'aya.
Abbas dake kallon sa yace"kana nufin jabir sonta yakeyi knn?
Eh kaji kaji nn ya gaya masa komai bae rage masa ba har zurfin cikin da sukayi.
kana ya d'aura da cewa shiyasa nake son ta koma in samu ya fidda ta a ransa dan jiya na fahimci har kuka sae da yayi dana gaya masa cewa ya haqura da bintu dmn komawa zatayi d'akin mijinta wanda nasan idan ba ganin yayi ta koma d'in ba bazai fidda ta a ransa ba zaiyi ta sa damuwa a ransa ne kullum yaga kmr an hana masa ita ne.
Abbas yace"olryt Allah ya kaimu weekend d'in sae muje mu sami mami shi kuma jabir Allah ya bashi ikon haquri ya kuma bashi wacce ma tafi bintun.
Abban ilham yace"amin"
Snn sukayi sallama ya fita daga office d'in.
Dama rnr juma'a da yamma ne Abban ilham ke dawowa an shirya musu duk wata liyafar tarba shida Abbas.
Bintu sae dad'i take taji a ranta matsalarta ta kusa zowa qarshe sbd Anti Hafsa ta gaya mata komai abinda ake ciki na dalilin zuwan Abbas kan in sun zo zasu je gun mami ne a mata bayanin komai a kuma sasanta tsakanin su ta koma.
Bayan sunzo har sun kammala cin abinci Abbas ya nemi ya ganta jikinta har rawa yake ta nemi hijabi da sauri ta saka taje ta same shi falo shi kad'ai yana zaune kan doguwar kujera ta zauna qasa a gaban sa kanta qasa sae tunani take a ranta tasan zae gindaya mata qa'idoji ne kafin yaje su sami mami ita koma wace irin qa'ida ce a shirye take zata bi indai zaije ya sasanta tsakanin su ta koma.
Qafar sa d'aya kan d'aya sae danne danne yake a wayar sa kmr ma bai san da zuwanta ba yana girgiza d'ayar qofar sa a hankali kana ya d'ago daga jinginen da yake ya sauke qafar sa dake kan d'aya idonsa akanta ya kama kunnen sa yace"ki bud'e kunnenki ki saurare ni da kyau kiji abinda zan gaya miki,idan har kinyi banzan tunani ko wata qa'ida ce zan baki akan komawar ki gidan waheed u are totally wrong!ni qa'idar da zan baki itace naji labarin cewa jabir yana matuqar qaunar ki, yaji ya kuma gani zae aure ki a yanda kike to ina gaya miki ki shiryi kar6ar soyayyar sa dmn zaki aure sa ne ko kina so ko ba kya so!
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 31_*
Da sauri Bintu ta kalle shi cikin girgiza kae muryar ta na rawa tace"Aa yaya aure na dashi bazae yiyu ba"
Abbas ya kalle ta da mamaki ransa a 6ace ya nunata tare da fad'in"ke! rainin wayon naki ya fara kawo kaina knn ko!
A hnkli ta girgiza kanta tace"ba haka bane yaya da akwai dalilin da yasa na fad'i haka"
Fuskar sa a murtuqe yace"wane irin dalilin ne da yafi umarni na fad'i ina jinki!
Kanta qasa cikin sanyin murya tace"dalilina shine yaya waheed bae sake ni ba har yanzu da auren sa akaina"
Yace"what!
Tace"Allah da gaske nake gaya maka yaya"
Oya je d'auko min takardar da ya baki in gani.
Ba musu ta tashi taje ta d'auko takarda ta kawo mishi.
Ya kar6a ya fara karantawa kmr haka.
_Fatima duk da ina jin tsanarki a raina ta dalilin abinda kika aikata a gareni bazan iya sakin ki ba,amma ina son ki gaggauta barin gidan nn kmr yanda mahaifiyata ta buqata kuma kar ki kuskura kice zaki nemi ni a waya har sae kin samo qwaqqwarar hujjar ki da yasa kike zubar min da 'ya'ya, idan kuma har dagaske kin aure ni dan dukiyata ne sae ki gaya min in sauwaqe miki dmn ke ba abokiyar zama bace!_
Abbas da yanayin fuskar sa ya nuna sam bai yarda da takardar ba ya baiwa bintu takarda had'e da fad'in"kar6i idan da akwai wata hujjar ki bayan wnn sae ki kawo min dmn ban yarda da wnn ba"
Bintu ta kar6i takadar tana kallon sa jiki sanyaye tace"wnn ce kad'ai hujja ta yaya kuma shi ya bani da hannun sa"
Yace"kar ki nemi ki raina min da wayo nasan halin waheed ba yau ba mutum ne mai yiwa mahaifiyar sa d'a'a ba zai bijirewa umarnin ta ba dole ya sake ki kmr yanda mahaifiyar sa ta buqata dan haka ina ainihin takardar da ya baki"
Qwallah tap a idonta tace"wlh yaya wnn ce takardar da ya bani.....Qarya kike kije ki nemo ainihin takardar da ya baki ki kawo min yanzun nn ina jiranki kuma kar kuskura kice zaki 6ata min lokaci.
A hankali ta saki kuka ta tashi ta tafi d'aki anti Hafsa da duk abinda ke faruwa tana jinsu tazo ta same ta,ta kar6i takadar ta karanta snn taja bintu dake jikinta tana kuka taje da ita kan bed suka zauna cikin muryar rarrashi tace"kinga bintu ki bashi ainihin takardar kinji zan lalla6ashi ya barki ki koma ga waheed ya janye auren jabir da yake son tursasa miki.
Tace"Anti wlh babu wata takarda da yaya waheed ya bani bayan wnn"
Anti Hafsa tace"haba dae bintu ko dai saki uku ne ya miki shiyasa ba kya so a gani"
Haba anti a saki ukun zanyi ta sa ran in koma ni wlh ko saki d'aya bai min.
To idan ba haka bane meyasa tun farko baki snr da kowa ba sakin ki yayi ba?
Sbd ina tsoron kar maganar ta koma ga mami tasa sae ya sake ni dagaske.
Anti Hafsa ta numfasa snn tace"bintu ko na yarda da zancen ki yaya Abbas bazai yarda ba kuma kinsan halinsa idan ransa ya 6aci zae iya ta dukan ki ne har se kin fad'i gaskiya,dan haka tun kafin hakan ta faru ki nemo ainihin takardar ki kaimasa idan kuma ta 6ata ne sae ki snr masa.
Cikin kuka tace"wlh Allah Anti gaskiya na fad'a yaya waheed bai sake ni ba kuma wnn takadar itace ainihin takardar da ya bani wacce na karanta tun lokacinda ya miqa min ita.
Shiru Anti Hafsa tayi na d'an lokaci snn tace"shikenan ya isa haka daina kuka bari inje in same shi"
Nan ta fita taje ta same shi yana zaman jiran fitowar bintu.
Kusa da kujerar da yake zaune taje ta zauna ya kalle ta a natse yace"ta azaki kin hau shine nima kika zo ki azani in hau koh"
Tace"ba haka bane yaya Abbas gaskiyar ta knn ba wata takarda da ya bata bayan wacce ta kawo ma"
Yace"Hafsa "
Tace"Na'am"
Yace"bana son kisa kanki a harakar nn wnn tsakanin nida ita ne ki tafi kawae ki kama aikin dake gabanki"
Marairaice fuska tayi tace"plz yaya Abbas ya kamata ace ka fahimci bintu tun tana yarinya in ta janyo magana mutun ya kawo qarar ta ya fad'i abinda ta mishi in tasan ta aikata zata ce eh ta aikata,tsoron fad'a ko duka bazai hana ta fad'i gaskiyar abinda ta aikata ba,ko ta nn ya kamata ace ka yarda da gaskiyar abinda ta gaya maka yanzu.
Yace"wancan da wannan daban ne Hafsa dan haka ki ma daina had'a su"
Amma yaya idan ka lura rubutun da ke jikin takardar sam ba nata bane na waheed ne.
Kin manta cewa bintu ta iya rubutun kowa inta tashi da kaf cikin ku ba wanda ke iya irin rubutuna da signing d'ina amma rainin hankalinta yasa sae da ta iya,dan haka ni wnn ba hujja mae qarfi bace da zan yarda da ita.
Amma to yaya Abbas meyasa kake son dole sae ta auri jabir bayan tafi ra'ayin ta koma ga waheed wanda shima inada yaqinin har yanzu yana sonta laifin da ta mishi ne kawai, kuma in yaji kuskure d'aya ta aikata sauran duk makirci ne inshaa Allah zai yafe mata.
Abbas yace"Hafsa kinfi kowa sanin irin aminatar da ke tsakanin mu da waheed da ba abinda ya kamata a gareni irin na sasanta tsakanin su da bintu amma tunda har kika ji nace dole sae ta auri jabir to kiyi shiru da bakin ki kawai bana son sake jin wata magana.
Amma yaya.....dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu had'e da fad'in"na gaya miki bana son sake jin wata magana abinda kawai nake so dake shine kije ki snr da ita na bata nn zuwa gobe ta nemo min ainihin takardar da waheed ya bata idan kuma taqi zata had'u da halina.
Yana kaiwa nn ya tashi ya fita ba tare da ya jira me zata ce ba.
Anti Hafsa ta numfasa tayi shiru sae tunani take can ta tashi taje ta sami bintu ta rarrashe ta kan ta kwantar da hankalin ta zata san abinyi, hakan yasa bintu tayi shiru ta daina kuka amma tasan tunda har Abbas ya kafe kan bai yarda da takardar nn ba tana cikin tsakar mai wuya mae fissheta sae Allah.
Da dare Anti Hafsa ce taje d'akin Abban ilham cikin shirinta na bacci yayinda shi kuma ta same shi ya fito daga wanka knn wanda har ya d'au mai zae shafa yaga yanayin damuwar da take ciki ya ajiye man yazo yaja hannun ta suka je kan bed suka zauna.
D'auke da yanayin damuwar da take ciki ta kalle sa tare da fad'in"Abban ilham tun d'azu na nemi kamin bayani shin me yake faruwa ne kaida kace zaka zo da yaya Abbas kuje gun mami dmn a sasanta bintu ta koma amma sae gashi da yazo yana neman tursasawa bintu auren jabir ba tare da kunje gun mami ba.
A hnkli ya numfasa tare da girgiza kansa yace"kiyi haquri Hafsa ni kaina haka naga abun wani iri ban san me Abbas ke nufi da hakan ba amma gobe da safe zanyi magana dashi kinji"
Anti Hafsa dake kallon sa ta gyad'a masa kae tare da kwantar da kanta a hankli kan faffad'an qirjinsa shi kuma yakai hannu sae shafa gadon bayanta yake d'auke da tunani fal a fuskar sa.
Washe gari bayan sun gama breakfast ne dukkan su suna falo ba wanda ya d'aga ko kan dining d'in basu sauka ba nn Abbas ya nemi bintu ta kawo masa ainihin takardar da waheed ya bata.
Bintu wacce kwata kwata ko breakfast d'in ta kasa yi sbd fargaba da tunani ta kalle sa kmr zatayi kuka tace"wlh Allah yaya wnn takardar da na baka itace ba wata na rantse"
Yace"kar ki raina min hankali wlh ina wasa dake ne!
Qwallah tap a idonta ta girgiza kanta alamar a'a
Yace"oya maza tashi kije ki kawo min real one!
Cikin muryar kuka tace"wlh yaya babu"
A fusace ya doki teburin dake gaban su yace"kije ki kawo min nace kafin raina ya 6aci!
Cike da tsoro bintu tayi saurin miqewa daga kan kujerar da take zaune tare da fashewa da kuka.
A nn Abban ilham da jabir suka miqe da niyyar magana Abbas yayi saurin dakatar dasu ta hanyar cewa"Aa kunfi kowa sanin dalilina dan haka ku qyale ni da ita dan Allah bana son wata magana daga gare ku"
Cikin rashin jin dad'in faruwar abun kowanen su ya koma ya zauna.
Abbas ya nuna bintu yace"wlh kar ki nemi ki raina min hankali kije na baki nn da wani lokaci ki nemo min ainihin takardar da waheed ya baki idan ba haka ba aurenki da jabir ba makawa sae an d'aura shi.
Cikin kuka bintu ta bar gurin da gudu ta tafi d'aki Anti Hafsa taje ta sameta kwance ruf da ciki kan bed tana ci gaba da kuka ko rarrashinta ta kasa yi sae kallonta take tunani fal a ranta ita ya tasan zatayi yanzu gashi har yanzu umma fushi take yi da bintu kuma bata da hujjar cewa tabbas takardar da ke hannun bintu itace ainihin wacce waheed ya bata tunda ba a gabanta abin ya faru ba, Abba kuwa ba abokin tunkarar ta bane koda wasa wanda ko yaji hukuncin da Abbas ya yanke bazae ce komai ba sae dai yace yayi dai dai ae dan ya isa da ita ne.
Kuyi haquri da wnn.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 32_*
Sallamar Abban ilham ce ta dawo da ita tunanin da take,bata iya amsa masa ba sae fitowa tayi ta same shi a nn bakin qofar d'akin ta tafi jikinsa a hankali tare da cusa fuskarta gabad'aya cikin qirjinsa tana son control d'in kukan da ke son fito mata,cike da yanayin rarrashi Abban ilham yakai hannun sa yana shafa gadon bayanta a hnkli wanda cikin natsastsiyar muryar sa yace"No Hafsa ban sanki da saurin kuka ba wnn karon ma kar ki fara kinji idan kinyi kuka to bintu fa wa zai rarrashe ta.
D'agowa tayi tana kallon sa da kyawawan idanuwan ta farare qal kmr na bintu sun ciko tap da qwallah suna son canza kala tace"to Abban ilham kana ganin abinda yaya Abbas ke shirin yi fa"
Yace"kiyi haquri ki bar komai a hannu na kinsan halin Abbas dole sae da lallami,
idan ya kafe kan abu ya kafe knn ba wanda ya isa ya tanqwasashi sae dai idan shi ya ga dama ya janye dan haka abinda nake so dake kije ki rarrashi bintu ni zan tafi in raka Abbas airport yace zae koma.
A hankli ta janye jikinta daga nashi snn tace"Allah kiyaye hanya a dawo lafiya"
Yace"Amin snn ya fice ita kuma ta koma daga ciki ta shiga aikin rarrashin bintu har ta samu tayi shiru"
Bayan wasu en kwanaki da faruwar haka bintu gabad'aya yanayin ta ya qara dawowa abun tausayi kullum tana cikin fargaba da tunani kar Abbas ya sake tuntu6ar ta duk tabi ta qara ramewa.
jabir ma duk yabi ya damu dmn sam baya jin dad'in ganin yanayin da bintu take ciki wanda har ransa baiji dad'in hukuncin da Abbas ke shirin yankewa ba yaso ace ya haqura suje gun mami shida Abban ilham a sasanta bintu ta koma d'akin mijinta tunda dae har tace waheed d'in bai sake ta ba in yaso shi kuma sae ya haqura ya nemi wata.
Jabir! jabir!.....firgigit ya kalli Anti Hafsa dake tsaye a gaban sa riqe da mug a hannunta ta miqa mishi tare da fad'in ga ruwan Lipton d'in nazo sae magana nake bakajina me yake damun ka haka kake ta tunani?
Jabir da ya kar6i mug d'in ya numfasa snn yace" kinsan damuwa ta d'aya ce Anti shine irin yanda yaya Abbas keson takurawa bintu akan dole sae ta aure ni, a gaskiya banso hkn ba dmn a tsarin rayuwata duk irin son da nakeyiwa mace bana son a mata dole,burina in auri mace wacce take sona nake sonta ta kuma yarda d'ari d'ari bisa zata aure ni.
Idan har ma bada gaske bintu keyi akwai auren waheed akanta ba ni na haqura wlh bana son bintu ta tsane ni".
Anti Hafsa tace"jabir bintu fa akan gaskiyar ta take akwai auren waheed akanta bawae qarya tayi ba yaya Abbas ne kawai yaqi ya yarda wanda dama can kwata kwata tun bintu na yarinya ko kad'an jinin su bai had'u ba ko yaushe cikin takurata yake sbd rashin jin ta da baya so.
Amma ae anti wnn yarinta ne fa bai kamata ace ya d'auki abun har girman ta ba yana takurata haka kmr ba qanwar sa ta jini ba.
Tace"uhm bintu kam har girmanta rashin ji takeyi, kawai dae ba kmr tana qarama ba kuma gaskiya tun da tayi aure ya daina takurata duk abinda tayi na rashin ji sae dai ya kauda idon sa kmr bae gani ba,yanzu ma yaji takaici ne sosai akan abinda ta aikata shiyasa yake son horata ta hanyar rabata da waheed dan kar ta koma kuskusre irin wnn amma fa a tawa fahimtar dan halin yaya Abbas ne na sani zae iya fiye ma da haka.
Jabir yace"in hakane da horon yayi tsanani anti dan Allah ku bashi haquri ya barta ta koma ko haka d'in ae ta horu.
Anti Hafsa tace"to yanzu dae Abban ilham yace abar komai a hannun sa"
Jabir yace"shikenan bari in tafi dare nayi ina son in kwanta da wuri sbd gobe zanyi sammakon fita ne"
Nan sukayi sallama ya fita anti Hafsa kuma taje kitchen ta fito riqe da cup of tea ta tafi d'akin su ilham gun bintu.
Ta samu su ilham duk sunyi bacci bintu ce kawai a farke zaune kan bed cikin shirinta na bacci riqe da littafin addu'o'i a hannunta tana karantawa.
Kae tsaye kusa da bintu taje ta zauna tare da ajiye tea kan bedside drawer tace"ga tean da akwai wani abunda kike so byn shi?
A sanyaye bintu tace"ba komai nagode"
Kallon ta anti Hafsa tayi tare da shafo gefen fuskar ta tace"kisha tean kar ya huce kinji"
Bintu ta gyad'a mata kae snn Anti Hafsa ta tashi zata fita har takae bakin qofa bintu da ta bita da ido muryar ta a natse tace"Aunty"
Aunty hafsa ta juyo ta koma ta zauna kusa da ita tana kallon ta tace"ya akayi ne bintu?
A sanyaye tace"dama zanji ne ko kinyi waya da umma yau?
Eh munyi waya d'azun har ma nayi tunanin in gaya mata halinda ake ciki sae kuma na fasa.
Meyasa anti ae da kin gaya mata dan Allah ko zata ce wani abu akae tunda kinsan yaya Abbas yana jin maganar ta.
Anti Hafsa ta numfasa tare da fad'in"idan na gaya mata nida yaya Abbas ne kinsani gwanda kawai in barshi ya gaya mata da kanshi dan kam dole zae snr masu kafin ya gama yanke hukuncin sa"
Tace"hkne anti amma ina tsoro kar itama umma ta yarda cewa ba ainihin takardar da yaya waheed ya bani na nunawa yaya Abbas ba dmn nasan shi Abba bazai ma yarda ba zae ce qarya nakeyi.
Anti Hafsa tace"hakane dmn a bayanin da umma ta gaya min Abba yayi mata waheed bai fad'a masa cewa bae sake ki ba kawae ya masa bayanin abinda ya faru da irin tirsasawar da mami ta masa kan sae ya sake ki,amma kar ki damu ki kwantar da hankalin ki Abban ilham yace mu bar komai a hannun sa kinji.
Bintu ta gyad'a mata kai tare da had'iye hawayen da keson fito mata.
Anti Hafsa ta mata sae da safe snn ta fita.
Ranar wata assabar bintu ce kwance shiru ita kad'ai a cikin d'aki,su ilham duk suna islamiyya school wayarta a hannunta ta shiga gallery da niyar aikinda da ta saba wato kallon fotunan su ita da waheed,sae ganin tayi Anti Hafsa ta kar6e wayar har sae da ta d'anji tsoro dan bata ji shigowar ta ba kwata kwata.
Cikin rashin kuzari ta tashi zaune kanta qasa,
Anti Hafsa dake tsaye ta girgiza kanta tare da fad'in"zaki fara aikin naki da na d'auka ko kin daina ashe baki daina ba ko bintu, plz sau nawa zan gaya miki ki daina kallon fotunan nn suna qara saki a cikin damuwa amma kinqi ki daina,olryt no vex zan kar6e wayar koma na goge fotunan gabad'aya har video records d'in kowa ya huta"
Da sauri bintu ta kalle ta tare da saurin girgiza kanta tace"dan Allah anti kiyi haquri kar ki goge min wlh zan qara shiga damuwa idan kika yi haka"
A hankali Anti Hafsa ta zauna kusa da ita tana kallon ta da kulawa snn tace"to ya kike so nayi dake bintu?
Kiyi haquri Anti zan daina
Yaushe?
Shiru bintu tayi dan idan ba ta koma gidan waheed ba bata jin akwai rnr da zata iya daina kallon fotunan waheed sbd suna d'an cire mata kewar rashin sa a kusa da ita.
Anti Hafsa dake kallonta miqa mata wayarta kawai tayi dan ta fahimci ba zata iya dainawan ba.
Tace"Dama nazo ne in gaya miki cewa anjima da yamma ina son ki rakani muje mu siyo kayan abinci da sauran su dan kinga Abban ilham weekend d'in nn bai sami shigowa ba aiki ya masa yawa gashi munada buqatar abubuwa shine yace in tafi in siyo mana.
Bintu tace"Allah kaimu anjiman"
Anti Hafsa tace"Amin"
Kafin take fita.
Da yamma bayan sun shirya suka fito basu zarce koina ba sae A.G.G mall.
Trolley basket bintu ta d'auka suka tafi anti Hafsa na za6ar duk abunda suke buqata tana sakawa a ciki,cikin rashin kuzari bintu ke tura basket d'in dan haka kawai suna shigowa taji fad'uwar gaba shine duk jikinta yayi sanyi cikin rashin sanin dalilin faruwar hakan.
Bayan sun kusa kammala siyayyar su ne bintu taje 6angaren inner wears sbd tana da buqatar su wacce tana isa gurin ta tsaya cak tana nazarin daddadan qamshin turaren da taji yana shigowa hancinta da mutum d'aya tak ta sani da irin qamshin turaren.
Basarwa tayi takai hannu gun wata hadaddiyar white bra dake cikin kwalinta zata d'auko taji wani irin lallausan hannu ya kama hannunta ta jiyo a hankali dmn ganin waye sae taga waheed wanda ya saki hannun ta a hnkli ya zagaya da hannun nasa a natse ta bayan qugunta ya kama snn ya matso da ita gab zuwa jikinsa,
bintu da gabad'aya hannuwanta biyu na kan faffad'an qirjinsa ta dafa shi sae kallon sa take da kmr mamaki shi kuma yana kallonta ba yabo ba fallasa.
Qawallah ne suka ciko a idon bintu en lips d'inta na rawa cike da son bud'e baki tayi magana sae taji muryar husna tafe tana waya da mami tana fad'in"eh mami na gama za6ar kayan baby gani zanje in sami yaya a 6angaren inner wears mu had'u a gun"
Kmr saukar guduma bintu taji zancen wacce ta kafe idonta akan Husna dake tafe d'auke da tulelen ciki a jikinta nn take hawaye suka sakko aguje kan kumatun ta,hango mami tafe a bayan Husna yasa tayi saurin janye jikinta daga na waheed ta bar gurin ya bita da ido yana jin kmr yaje ya jawota karta tafi.
Husna kuwa lura dasu yasa ta tsaya cak kmr wacce aka dasa a gurin har mami ta qaraso gurinta tana fad'in"lafiya husna me waheed yake kallo kema kika tsaya kina kallon sa?
Husna ta sadda kanta qasa kwallah tap a idonta tace"ba komai mami abu yake dubawa".
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 33,34,&35_*
Kafin mami tace komai wayarta ta shiga qara ta d'aga kiran had'e da barin gurin, husna kuwa janye da shopping cart d'in da take turawa ta qarasa gun waheed wanda sae a lokacin ya daina kallon hanyar da bintu tabi ya juyo ya kalleta.
A hnkli hawayen da suka cika mata ido suka soma sauka kan kumatun ta,ya kauda fuskar sa gefe tare da fad'in"kiyi ki za6i abinda kk so mu tafi ni nagaji da yawon nn"
Sadda kanta qasa tayi tare da share hawayen fuskarta muryar ta a sanyaye tace"to dan Allah ina son ka za6ar min irin inner wears d'inda bintu kesawa"
Kallon ta yayi zae yi magana se ga mami tace"lafiya me yake faruwa kunyi cirko cirko ko kun rasa abun za6a ne?
Husna tace"Aa muna dubawa ne"
Mami ta kalli waheed da baice komai ba sae hannu yakai ya fara xa6ar duk irin inner wears d'inda yasan bintu naso ba tare da yasan dalilin da yasa husna ta nemi yayi hakan ba.
Damuwa fal ta gani a fuskar sa tace"lafiya waheed me yake damunka?
xa6ar kayan yake ba tare da ya kalle ta ba yace"ba komai mami"
Shiru Mami tayi ba tare da ta sake ce masa komai ba sae girgiza kanta tayi cikin damuwa dmn rabon da taga farin cikin waheed tun lokacin da bintu ta bar gidan har yau koda kuskure bata qara ganin ko d'an guntun murmushi a fuskar sa ba.
Bintu kuwa a lokacin da tabar gurin da gudu taje gun Anti Hafsa taja hannunta cikin kuka tana fad'in"Anti dan Allah kizo mu bar gurin nn"
Anti Hafsa wacce tana tsaye duk ta hango abinda ya faru bata musa mata ba ta saki shopping cart d'inda suka cika tap da kaya ta bar shi nn suka fita.
Securities komai basu ce musu ba suka barsu suka fita dan kukan da bintu keyi kad'ai ya basu cewa akwai babbar matsala.
Har suka isa gida kuka bintu keyi wacce anti Hafsa na faka mota ta fito da gudu tayi cikin gida.
Jabir da shima shigowar sa knn gidan a rud'e ya faka mashin d'in sa yazo gun Anti Hafsa da ta fito cikin mota da saurin sa yana fad'in"Anti lafiya me yake faruwa da bintu dan Allah ko yaya Abbas ne?
Jiki sanyaye anti Hafsa ta kalle sa tace"mun had'u da waheed ne shida mamin sa da matar sa suna siyayyar kayan baby haifuwa yau ko gobe"
Shiru Jabir yayi baice komai ba har ta wuce sai hanneyen sa ya zira a sanyaye cikin aljifan wandon sa kansa qasa cike da tausayin Bintu.
Anti Hafsa kuwa da shigarta ciki d'akin su ilham taje ta sami bintu kwance ruf da ciki tana rusar kuka.
Kan gadon taje ta zauna ta kama hannun Bintu tazo zuwa jikinta wacce ta rungume ta sosai sae ci gaba da kuka take,Anti Hafsa bata hana ta kukan ba sae shafar gadon bayanta take a hankali cike da qwalla tap a idonta.
Can ta soma rarrashin ta tana bata magana har ta samu ta sassauta kukan da take.
Bayan sllr isha bintu ta ida sallah tana zaune kan darduma ta had'e kanta da guiwa,sae ga ilham ta shigo d'akin cikin sallama.
Bintu ta d'ago kanta a hnkli
ilham tace"Anti kinyi baquwa"
Bintu da duk idanun ta sun kunbura kan kuka muryar ta can ciki tace"wace ce?
Ilham tace"nima ban santa ba amma gata nn tsaye a bakin qofa"
Bintu tace"je kice ta shigo"
Nan ilham taje ta snr da baquwar sae ga Husna ta shigo d'auke da sallama a bakinta.
Bintu bata iya amsa mata sallamar ba sae kallon Husna take har ta qaraso gurinta d'auke da mamakin me ya kawota.
Husna ta durqusa a hnkli kan guiwoyin ta gab da bintu,tasa hannu a natse ta sharewa bintu hawayen da suka gangaro kan kumatun ta wacce bata ko san hawaye sun fito a idonta ba sae jin tayi Husna ta share mata.
A nn ta kauda fuskarta gefe tare da saurin share wasu hawayen da suka sake zubo mata.
Husna dake kallon ta muryar ta a sanyaye tace"ki yafe min bintu wlh ban auri waheed ba sae dan bin umarnin hajiyata,
dani har shi ba mai son wani muna zama ne kawai sbd bin umarnin iyayen mu, ko cikin nn da na samu duk a dalilin umarnin mami ne ba dan yana so ba haka nima badan ina so ba.
Ta qarashe mgnr ne cike da qwallah a idonta.
Bintu dake kallonta tace"Husna banyi mamaki da jin zancen ki ba dmn nafi kowa sanin irin son da kike yiwa Amar bakida burin da ya wuce ki aure shi dan haka ni ya kamata in roqe ki gafara bake ba dmn duk ni naja komai har hakan ta faru kika auri wanda ba kya so amma kiyi haquri da sannu yaya waheed zae so ki"
Husna ta girgiza kanta yayinda hawaye suka silalo a hnkli kan kumatun ta tace"yaya waheed bazai ta6a sona ba bintu ke yake so kuma har ko yaushe bana jin zai ta6a iya daina sonki"
Cikin muryar kuka bintu tace"Husna a yanda yaya waheed yake son haifuwa na tabbatar idan kika haifu zae soki fiye dani sbd kin masa abinda na kasa masa dmn cikin ba kya son shi gashi kina d'auke da cikin sa zaki haifar masa amma nida ke son shi na zubar mai da cikin da na samu bayan nasan yana matuqar son haifuwa"
Duk da haka bintu yaya waheed bazai ta6a son wata 'ya mace fiye dake ba,ba kad'an ba yake matuqar sonki kmr yanda nake son Amar shiyasa kullum addu'a ta Allah ya sasanta tsakanin ku ki dawo ga waheed ni kuma in samu ya sakeni inje in auri Amar dmn na tabbatar zai aure ni ko bayan na haifu.
Bintu ta girgiza kanta tare da riqo hannayen Husna snn tace"Husna ina baki shawara kici gaba da bin umarnin hajiyar ki da sannu zaki ga ribar hakan kinji"
Shiru Husna tayi wacce tunda akayi auren kusan kullum se tayi kukan rabata da akayi da Amar amma kuma bin umarnin mahaifiya na gaba da komai kuma riba na tare da hkn.
A hnkli ta gyad'a kanta tare da fad'in"naji Bintu amma idan kika dawo gidan zae fimin dad'i"
Kema kinsan dawowa ta da kamar wuya Husna dmn mami ta gama yarda da duk abinda taji byn ba haka bane.
Kiyi haquri bintu sanin mutum sae Allah duk yanda kake dashi zae iya cutar ka,shiyasa mami ta yarda da abinda taji amma ni a d'an had'uwar da mukeyi a school da kuma gidan mami i really trust u,abinda naji akanki nasan ba gaskiya bane da akwai makirci a cikin sa shiyasa a kullum nake roqon Allah ya bayyana gaskiya ki dawo.
Bintu da hawaye ke sauka kan kumatun ta tace"nagode Husna Allah ya kawo qarshen wnn abun"
Husna tace"Amin"
Snn ta janyo wata babbar ledar da ta shigo da ita ta baiwa bintu tare da fad'in"am sorry wnn inner wears d'inda zaki siyane baki samu kin siya ba shine na kawo miki,kuma dan Allah kar kice bazaki kar6a ba,in kika min haka wlh bazan ji dad'i ba zanga kmr kina kishi dani ne"
Bintu tace"shikenan Husna ba komai na gode bari in kawo miki ruwa kisha"
Aa nagode sauri nake in koma gida dmn ce masa kawai nayi zan tafi wani guri in dawo.
Bintu taje zuwa tashi da niyyar rakata Husna tace Allah tayi zaman ta kawai ta gode.
Bayan ta tafi ne sae ga Anti Hafsa ta shigo d'akin,bintu na tsaye ta linke darduma zata saka a wardrobe
Anti Hafsa tace"bintu me Husna tazo yi a gidan nn ne?
Bintu ta gaya mata komai.
Anti Hafsa ta numfasa tare da fad'in"Allah sarki ae inshaa Allah komai ya kusa zowa qarshe kici gaba da Addu'a kawai"
Shiru bintu tayi bata ce komai ba.
A nn Anti Hafsa ta d'auki ledar inner wears d'inda Husna ta kawo tana dubawa tace"Allah sarki kinga komai irin wanda kike so kmr ta sani"
Shiru kawai bintu tayi amma tasan ba makawa waheed ne ya za6i kayan se dae kawai baisan inda zata kawo su ba tunda bai ko san nn tayo ba.
wacce kirki irin na Husna ne yasa ta kar6i kayan da kuma had'a ta da Allahn da tayi.
************
*Kebbi*
_12:30 na dare._
Zeenah da Sarah ne zaune a nn d'akin su na gidan haya suna kwance sae fira suke me cike da batsa abin ba dad'in ji.
Nan kawai sae ga wata ta shigo d'akin su cikin kuka janye da akwati a hannun ta,da saurin su suka tashi suka tarbe ta suna fad'in"beauty lafiya me yake faruwa?
Bata iya ce musu komai ba sae sake akwatin hannun ta tayi taje kan qatuwar katifar su ta zauna tana ci gaba da kuka suka sameta sae rarrashin ta suke kan ta gaya musu me yake faruwa da har ta iya baro sokoto cikin daren nn haka.
Cikin kuka tace"Handsome ya cuceni wae duk irin rayuwar da muke dashi kwatsam sae gashi yau ya min korar wulaqanci na bar masa gida wae shi aure zaiyi bayan a dalilin sa ne na gudo daga gidan mu kan auren dolen da aka tashi min amma baiga abinda zai saka min dashi ba sae wnn, bayan ya gama morata ya 6ata min rayuwa ya kuma bi duk accounts d'ina da yake zuba min kud'i ya kwashe abinsa kaf gashi banida ko sisi a hannu na sae kud'in mota kad'ai da suka kawo ni garin nn"
Tare suka ce"cabd'i lalai handsome ya cika cikakken mayaudari"
Beauty tace"hm ku barni dashi na fisa kafirci wlh sae nayi maganin sa dama dan kud'in sa kawai nake sonsa ko kashe shi zan iya sa ayi har lafira na kuma sa akwaso min duk dukiyar sa.
Zeenah tace"hakan yayi dai dai wlh shine hukuncin da ya kamata ki mishi amma kuma wa zakisa ya miki wannan aikin?
Tace"hm sae kace baki san waye ni ba,en daba zan nema mana"
Sarah tace"ta yaya to keda bakida kud'i?
Ina da tsadaddiyar sarqar gold ko ita ta isa in biyasu ladan aikin su snn ko ba haka ba ae bayan sun kashe min shi duk wata dukiyar sa kwasa min ita zasuyi cikin sauqi dmn duk inda yake wani 6oyon muhimman abubuwan sa na sani haka har ATM cards d'insa duk kwaso min su zasuyi ba wani pin d'insa da bansani ba,fatana kar ya canza abubuwan sa kafin nn da sati dmn a cikin satin nn ne zai yi aure yayinda nake son a daren agwancin sa a masa wnn aikin idan ana cin angwanci a lafira yaci a can nidai na gama dashi.
Dariya sukayi gabad'ayan su tare da tafawa suka sata a gaba sae qara ziga ta suke.
Bayan kwana biyar da faruwar hakane burin beauty ya gama cika an kashe mata handsome ta kuma mallaki dukiyar sa wacce har party sae da ta had'a dan murna.
Su zeenah kuwa sae qara liqe mata suke waenda su kuma burinsu su rabata da wnn dukiyar ta hanyar yaudarar ta.
Ita kad'ai ce a d'aki ta kunna kid'a sae kwasar rawar ta take cikin jin nice.
Sae ga zeenah da sarah sun shigo d'akin zeenah tace"👍🏻yayi Beauty kiyi abinki bakida wata matsala a rayuwa".
Beauty tayi dariya had'e da kashe kid'an tace"da akwai d'ayar matsalar kuma sae na kawadda ita.
Sukace kaddai ana shirin gano ki ne?
Tace "ko d'aya kuzo kuji dan mgnr mai tsayi ce"
Taja hannun su suka zauna.
Sae da ta kalli kowannen su snn tace"zaku iya tuna wata qawata Husna da itace qawar da na fara had'uwa da ita school?
Shiru sukayi suna nazari can zeenah tace"ko wnn farar yarinyar very silent da ita haka?
Yauwa ita zeenah itace next target d'ita yanzu wacce na jima ina son inyi maganin ta dmn tamin abinda bazan ta6a iya barinta ba.
Sarah tace"ita wnn yarinyar da ba ruwanta me ta miki?
Hm! kunsan nace muku itace yarinyar da na fara qawa da ita a school da kaf school d'in banida wata qawa sae ita haka itama ni kad'ai ce qawar ta,se ya kasance muna matuqar shiri ganin cewa halin mu yazo d'aya amma a nata tunanin dmn gabad'aya nuna mata nayi ni mai kirki ce.
Ranar na kai mata ziyara gidan su sae Hajiyar ta ta d'an aiketa wani gida ni kuma na d'auki qafa na rakata dan gidan ba nisa da gidan su,bayan munje mun dawo na kasa zama na kasa tsayi sbd wani hadadden gaye da na gani a gidan irin gayen da na dad'e ina mafarkin samu in aura koda bashida ko sisi amma kash se naji bazan iya gaya mata ba sbd tun farkon had'uwar mu nuna mata nayi ni mtr aure ce bata ta6a sanin cewa zaman dadiro nakeyi da Handsome ba duk a tunanin ta mijina ne dagaske dmn har ziyara take kaimana.
Kasancewar ta fahimci halinda nake ciki sae ta tambaye ni me yake faruwa nace mata cikina ne nake jin ba dad'i,tace idan lalurar bayi ce na shiga mana na sauke,nace mata ba ita bace ulcer tace keson taso min zan koma gida da akwai maganin da nake sha,tace to muci abinci mana tunda gashi har ta d'ebo mana,nace a'a sauri nake idan banje na sha maganin ba komai zae iya faruwa dan har suma nake.
Daga haka bata sake musa min ba na kira handsome yazo ya d'auke ni muka koma gida.
Na yini ina tunanin wnn gayen dare yayi na kasa bacci duk na rufe ido kyakkyawar fuskar sa nake gani da qyar naga safiya dmn ji nayi kome ze faru se na gaya mata dmn bazan ta6a iya rufe sonda nake masa ba.
Sakko na daka irin wanda ban ta6a yin irin shi ba naje school bayan tazo na gaya mata halinda nake ciki.
Sosai tayi mamaki ta yaya za'ayi ina matar aure in bar son wani ya shigeni, nn ta fara d'an wa'azinta na katse ta tare da kora mata bayanin gaskiyar ni ba mtr aure bace ga irin zaman da mukeyi da Handsome da kuma dalilin da yasa na gudo daga garin mu nazo sokoto.
Fad'ar irin mamakin da tayi bazai yiyu ba wacce da ace ba'a zaune muke ba zata iya fad'uwa dan haka ta zamar min tamkar wata statue tana kallona hawaye na fita a idonta.
Wacce ba hawayen mamaki ne a idonta ba hawayen baqin cikin kasancewa ta qawa a gareta.
"Zainab kin cuce ni"
Ita ce kalmar da ta fara fitowa a bakinta nayi qasa da murya cikin rarrashi ina bata haquri amma bata saurare ni ba taci mutunci na tas duk idon jama'a yayo kanmu a rnr duk wanda baisan wace ce ni ba to saeda ya sani,ya kasance duk inda nabi sae nuna ni ake ana magana, haka itama ko hanya ta had'a mu yanzu zata kauce tabi wata hanyar tamkar taga wani dodo,
hakan yasa nayi baqin ciki sosai har bana so in shigo school ga kuma son wnn gayen dake damuna kullum da tunanin sa nake bacci nake tashi har handsome yaso ya gano ni wae na fad'a son wani ina 6oye masa gani nn kullum cikin tunani, nace masa tunanin iyayena nakeyi,yace kar in damu in munyi aure zai d'auke ni muje a baiwa iyayena haquri,jinsa kawai nake dan banida burin da ya wuce in auri wnn gayen ko ta halin qaqa koda ace baya sona in ya aureni kullum zaiyi ta dukana banida matsala indai ina ganin kekkyawar fuskar shi.
Haka na garzaya gurin boka ya bani wani kwalli yace in shafa da zarar na had'a ido dashi an gama zai aureni kuma sae yanda nayi dashi,hm farin ciki fal na tafi wnn gidan da na raka Husna a tunani na zan had'u dashi sbd d'an gidan ne amma sae nayi rashin sa'a baya nn se mahaifiyar sa kad'ai na samu wacce nayiwa qaryar cewa Husna nazo nema dmn naje gidan su ban sami kowa ba wanda nace mata hakane sbd na fahimci ta gane nice na ta6a rako Husna,tace ayya ae Husna bata zo ba amma in bari ta kira min wayar hajiyar husna taji ina suka je,nayi saurin cewa A'a ta barshi zan kira Husna d'in,
banko bar naji amsar ta ba na bar gidan da sauri,tun daga lokacin ban sake komawa gidan ba gudun kar liqi na ya 6alle amma kullum cikin tunanin yanda zan had'u da gayen nake inata neman wanda ya sanshi ko numbar sa ya bani,kwatsam rnr sae naji labarin wae Husna ta aure shi,hm bazan iya muku bayanin abinda naji ba amma tun daga lokacin na shiga tunanin yanda zanyi in fitar da ita gidan ni kuma in samu in aure shi yayinda zanci gaba da rayuwa dashi ni kad'ai har abada ba tare da nabar wata mace ta ra6e shi ba.
Zeenah tace"Amma keda kike da boka a hannu shine har sae kin tsaya tunanin yanda za'ayi ki fitar da ita"
Hm zeenah knn ae naje gun boka da niyyar a haukata min ita tabi duniya koda ya duba a qwaryar sa ta tsafi ya girgiza kae yace abinda nake so bazae yiyu ba dmn wnn yrnyr tana da ibada sosai bazai iya haukatar da ita ba.
To shine dalilin da yasa na shiga tunanin yanda zanyi da ita,na kuma samu dmn a cikin kwanakin nn zan aiwatar da nufina akanta,zan tura wa en nn en fashin da suka min aiki akan Handsome suje su sace min ita sukai ta can wata uwa duniya su jefar a ruwa ta yanda bazan sake jin labarin ta ba har abada.
Sarah tace"kinsan gidan gayen naki knn?
Qwarai na samo gidan sa har ma sunan gayen nawa na sani suna mai dad'i waheed.
Tare suka ce "lah! wae waheed ashe Husna ce mami ta aurar masa?
Tace"Au dama kunsan shi knn?
Zeenah tace"Farin sani ma kuwa dmn shine mijin wnn er uwar tamu bintu koda yake baki santa ba.
Ae kam na santa wnn er siririyar farar yarinyar da na ta6a gani tare daku cabd'i knn matan sa biyu?
Zeenah tace inafa ae tuni ya saki bintu tayi gaba kinji kinji nn suka bata labarin komai.
Beauty tace"kae ashe nn da nake ganin ku dai ba baya ba"
Zeenah tace"hm mune wasa ae wlh da munsan kina sonshi da tuni kin dad'e da shiga gidan matsalar kawai bamu wani saba da juna d'in nn ba har se muna gab da kammala school.
Amma ae ko yanzun bata 6aci ba auren waheed kmr kinyi kin gama but ga wata shawara idan kin amince.
Fad'i ina jinki.
Zennah tace"Akan kisa a sace Husna ae gwanda kinsa a kashe ta kawai kmr yanda akayiwa handsome.
Eh to tausayin yarinyar nake ji wlh amma meye dalilin ki na cewa hkn?
Yauwa kinji abinda nake son kice, wato dalilina shine so nake zargin kisa ya fad'a kan bintu.
Ta yaya za'a zarge ta ita da tayi watanni basa tare?
Hm bud'e qwaqwalwar ki da kyau ki fahimci zance na,A yanda waheed ke son bintu wlh zai iya maida ta tunda ko sakinta da yayi umarnin mahaifiyar sa ne bada son ransa ba dan haka dan kin kawadda Husna bakiyi komai ba akwai wani jan aiki a gaban ki,
dan ko bintu ba baya ba qiriniya ce kawai da ita amma akwai ibada sam bata wasa da addininta,wacce addu'ar ta kad'ai ta isa ta hana miki shiga gidan waheed tunda ta hanyar asiri ne kike son shiga gidan bada ra'ayin kansa ba.
Beauty tace"mgnr ki dutse to ya zanyi knn har zargin kisa ya fad'a kanta?
Nan zeenah takai bakinta a kunnen beauty ta gaya mata magana.
Beauty tace"kina ganin en fashin zasu yarda da hakan kuwa?
Aa ae sam bazaki gaya ma en fashi da police a harakan nn ba kawai zakiyi yarjejeniya dasu acewar in case of rana ta 6aci an kama su kina son koda an tuhume su kawai suce tsohuwar matar sa ce bintu ta tura su duk juyin da za'ayi kuwa kar su kuskura su anbaci sunanki idan sukayi haka ke kuma zakiyi qoqarin ganin kin fitar dasu ba tare da an ta6i lafiyar jikinsu ba ko neman yi musu wani hukunci snn kuma ko nawa suke so zaki qara musu akan kud'in aikin su.
Beauty ta numfasa tare da fad'in"of course nasan zasu yarda da hakan dan sun san bana wasa gurin biyan su kud'i amma ina tsoro fa"
Haba tsoron me ae ina gaya miki da zarar sun furta bintu ce ta tura su wlh ba makawa zancen ya zaunu kar kiji wani tsoro, snn in suka ce kece wa zae fidda su to,ai kinga baza ma su fara ba.
Shike nn na amince amma idan koda police suka je gidan sun samu har en fashin sun gama kisan sun tafi fa?
Aa ae bazakiyi qasa a guiwa ba en fashin na isa gidan after some minutes zakiyi shirin kiran police tunda kince aikin en fashin tamkar yankan wuqa ne suna shiga suke aiwatar da abinda aka sa su, kawai dai kiyi musu kashedin cewa kar su ta6a lafiyar waheed.
Ina ae baza ma su fara ba dan kashedin da zan musu dole su kiyaye.
Tana kaiwa nn wayar ta ta shiga ringing ta d'aga wayar had'e da fita d'akin.
A nn sarah ta kalli zeenah tare da fad'in"nifa zeenah ganin nake ko ba'ayi haka ba da kmr wuya bintu ta koma gidan waheed dan mami ta riga ta tsane ta baza ta ta6a barin sa ya maida ta ba"
Hm sarah gudun nake rana ta 6aci mami ta gano gaskiyar komai shiyasa nayi hakan dmn bani da burin da ya wuce inga rayuwar bintu a lalace wacce idan aka d'aura laifin kisan nn a kanta na tabbatar ko ba'a kashe ta ba tofa za'a mata d'aurin rai da rai ta qarasa rayuwar ta can gidan kaso ba ita ba sauran wani farin ciki har abada.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 36_*
Sarah tace"lallai hkn da kikayi yayi dai dai dmn nima burina knn,baqin cikina d'aya yanzu shine rashin auren nn namu da duk wanda ya fito da niyyar auren mu sae ana batun saka date suce sun fasa sbd sun ji labarin mun zubar da mutuncin mu tun a waje,na rasa a ina suke ji bayan duk irin kamilancin da muke nuna musu muna 6oye musu ainihin halin mu dan mu samu muga anyi auren.
Zeenah tace"Matsalar itace binciken da akeyi kafin aure kuma mazan da muke haraka dasu har su d'in basa yarda su aure mu in ma ka musu mgnr aure ya ishi su gaya maka baqar magana daga rnr kuma ka daina ganin su knn.
Sarah tace"shiyasa tun farko zeenah banso mun fara harakan nn ba sbd gudun irin haka gashi muna samun mazajen aure amma da bincike ya nuna halin mu shikenan su fasa sbd duk mutumin kirki ba zae so ya auri irin mu ba kowa fatan sa ya samarwa 'ya'yansa uwa ta gari mai mutunci da bata riga ta zubar da mutuncin ta a waje ba.
Shiru zeenah tayi dmn bata da abinda zata ce ma sarah sbd gaskiya ta fad'a, a yanda suke samun mane man nn yanzu da halin su na kirki ne basu riga sun zubar da mutuncin su a waje ba da yanzu sunyi aure.
Can ta kalli sarah tace"kinga dnt mind ae ko dan kud'in mu za'a aure mu ko kin mata zamuyi wa beauty sakiyar da ba ruwa dukiyar handsome duk ta dawo hannu mu sae abinda muka ga dama muka samma ta.
Sarah tayi dariya tare da bata hannu suka tafa snn tace"Hakane fa na manta har naji d'an sauqi a raina kuma shawara ita ce dukiyar na shigowa hannun mu gidan hayar nn barin sa zamuyi dmn na fahimci yana daga cikin qarin matsalar rashin auren nn namu a matsayin mu na en mata mun kama gidan haya byn kuma da iyayen mu a gari,kinga se mu sayi kantamemen gida tsadadde mu koma can muda iyayen mu.
Zeenah tace"ae kam dama ni yawon dubai ma zan soma yi dan garin nn bai ishen zama ba akin asibitin ma fatali zanyi dashi in shiga harakar sae da gwalagwalai da hajar mata.
Dariya sarah tayi tare da sake bata hannu suka tafa tace"kina wuta ina binki da fetur,ma jame duk inda kikayi can nayi.
*Sokoto*
Anti Hafsa ce ta shigo d'akin su ilham gun bintu wacce ke zaune kan bed ta had'e kai da guiwa sae tunanin mafitar rayuwar ta take.
Sallamar da anti Hafsa tayi ne yasa ta d'ago kanta a hankli tare da amsa mata sallamar.
Jiki sanyaye anti Hafsa ta qarasa kusa da ita ta zauna,fuskarta d'auke da damuwa tace"bintu yaya Abbas ne ya bugo waya wae gobe zae zo yace ki tabbatar kin tanadar masa ainihin takadar da waheed ya baki kafin yazo"
Shine na kira Abban ilham nace ya akayi shida yace mu bar komai a hannun shi amma still yaya Abbas na kan bakar shi,yace wae muyi haquri ya kasa shawo kansa ne,ya kike ganin zamuyi yanzu?
Bintu dake kallonta muryar ta a sanyaye tace"kar ki damu anti ko yazo ba matsala ni na amince zan auri Jabir "
Da mamaki Anti Hafsa tace"kin amince fa kika ce Bintu?
Eh Anti na haqura zan rungumi qaddarar da ta sameni dmn na riga na jawa kaina ba yanda zanyi.
Anti Hafsa dake kallonta tace"No bintu ni bazan so hakan ba kome zai faru sae dai ya faru amma se na snr da umma halin da ake ciki kafin yaya Abbas yazo,shin wae ma tukuna kin manta da auren waheed akanki ne da kike wnn zancen,ko gaskiyar yaya Abbas ne waheed ya sake ki kike 6oyewa?
Ko d'aya Anti bae sake ni ba amma da kaina zan nemi ya sake ni dmn nasan ko na koma bazan sake yin daraja irin ta farko ba, gwanda kawai in barshi da Husnan shi ni kuma in auri jabir.
Jiki sanyaye anti Hafsa ta dafa kafad'ar bintu tare da fad'in"ki daina zancen nn Bintu dmn bana jin waheed zai iya sakin ki tunda har ya kasa sakin ki a lokacin da mamin sa ta umarce shi se basaja da ya mata"
Anti nasan yanda zanyi ya sakeni cikin sauqi shine zan bar mami tasan bai sake ni ba,na tabbatar in taji hakan koshi waye dole ya sakeni koda baya so"
Anti Hafsa tace"kenan kin yarda taci gaba da kallon mu a matsayin mayaudara?
Bintu dake kallonta qwallah cike tap a idonta tace"Aa bayan na auri jabir zata san gaskiyar komai,wnn alqawari ne na d'auka bazan bar taci gaba da kallon mu a matsayin mayaudara ba dole zan dawo da darajar iyayen mu a idonta ko zan samu su daina fushi dani"
Anti Hafsa ta numfasa a hnkli tare da fad'in"amma bintu kina son waheed fa meyasa zakiyiwa kanki haka?
A nn qwallar da suka cika mata ido suka silalo a hankali ta share hawayen tare da fad'in"ba yanda zanyi ne Anti,amma haqiqa rayuwata baza ta6a dad'i ba sae tare dashi dmn ina matuqar sonshi bana jin kuma zan iya daina son shi har abada,amma ya zama dole in haqura dashi.
Tana kaiwa nn ta saki kuka a hnkli, Anti Hafsa da idanun ta suka ciko da qwallah ta jawo bintu zuwa jikinta tare da sa hannu ta share mata hawaye snn tace"yi haquri daina kuka komai mai wucewa ne kinji tashi muje muci abinci jabir yana can yana jiran mu.
Nan taja hannun Bintu suka fito wacce ta kasa cin abincin sae yawo kawai take da spoon tana motsa abincin a hankli cike da tunanin yanda zatayi rayuwa da wani d'a namiji ba waheed ba,abinda ko a mafarki bata ta6a kawo shi ba se gashi yanzu yana shirin faruwa da ita.
Kukane yazo mata ta tashi da sauri ta bar gurin.
Jabir da ya bita da ido ya maida duban sa gun anti Hafsa wacce tayi shiru ta daina cin abinci.
yace"Anti me kuma yake faruwa?
Tace"magana d'aya ce dai da ka sani jabir"
Yace"to Anti da kinje kin rarrashe ta ai ko?
A hankli ta girgiza kanta tace"ka barta kawai jabir ta cancanci tayi kukan ne shiyasa"
Shiru jabir yayi bai sake cewa komai ba har suka kammala cin abinci wanda dashi har Anti Hafsa ba wani abincin kirki ne suka ci ba sunan sunci ne kawai.
Da gamawar su ne jabir ya tashi ya tafi cike da tunani a ransa,Anti Hafsa kuwa fresh milk ta d'ibarwa bintu dan ba kad'an ba tasan tana jin yunwa damuwa ce kawai ta hana ta cin abinci,taje ta sameta a nn d'akin su ilham cikin rarrashi da bata magana ta samu har tasha fresh milk d'in.
Da dare bayan sllr isha sae ga Anti nafee tazo gidan, ilham dasu daddy suka tarbe ta sae oyoyo suke mata.
Hayaniyar su ne yasa Anti Hafsa ta fito wacce tana ganin Anti Nafee fuskarta d'auke da murmushi tace"Au Nafee kece da daren nn ina kika bar su mimi?
Tace"suna can tare da Abban su sunje shopping a fodio mall daga can kuma su harba A.g.g wae duk dan inji haushi ba aje dani ba.
Ta qarashe mgnr ne d'auke da alamar fushi a fuskarta,
a nn Anti Hafsa ta nemi su ilham da su tafi d'aki snn taja hannun nafee suka zauna kan doguwar kujera tana kallonta tace"me ya had'a ku ne dan san haka kawai sadiq bazai fita daga shi se yara bake ba?
Tace"Anti fad'a mukayi shine yake fushi dani yana jiran in bashi haquri ni kuma naqi sae harakar gabana da nake shine yamin haka dan yasan bazan ji dad'i ba.
Anti Hafsa tace"hm lallai kinfi qarfin ki bashi haquri ko,to yanzu da kika zo me kike so in miki?
To Anti ba kya ganin duk ya kwashe su sun fita har isma'il ma da yake shan mamma ya zan zauna ni kad'ai a gida to"
Anti Hafsa tace"naji amma yanzun nn komawa zakiyi kafin ya dawo idan kuma ya dawo ki same shi har d'aki ki bashi haquri,keda ma rashin bada haquri ba halinki bane yaushe kika fara to?
Anti to dan na masa laifi shine zae sameni a gaban su mimi yayi ta min fad'a ni kuma shine a nn gaban su na gaya masa magana mai zafi na tafi na barshi dan inna tsaya na tabbatar komai zai iya faruwa gashi kuma bai kamata ace munayin fad'a a gaban su mimi ba.
Anti Hafsa tace"duk da haka dai ki same shi ki bashi haquri ki kuma nemi yafiyar fitowar da kikayi bada izinin sa ba.
Ta gyad'a kanta snn tace"to anti bari in tashi in koma amma bintu fa ko yau night duty take da?
Aa jeki tana d'aki.
Bayan taje ta dawo Anti Hafsa ta raka ta zata shiga mota tace"ni kuwa Anti kullum damuwar bintu sae qaruwa take dan Allah yaya Abbas yayi haquri mana haka ya barta ta koma d'akin ta ya janye zancen auren nn nata da jabir bana so wlh nafi so ta koma gidan waheed.
A hnkli Anti Hafsa ta numfasa snn tace"ea yanzu ita bintun da kanta tace ta amince zata auri jabir"
Meyasa Anti kuma ta yaya ita da tace da auren waheed a kanta ko qarya take yiwa yaya Abbas ba ainihin takardar da waheed ya bata ta bashi ba kmr yanda shi yaya Abbas yace.
A nn Anti Hafsa dake kallonta tayi mata bayanin duk yanda sukayi da bintu a d'azun.
Nafee tayi shiru can tace"To ke anti kina ganin ba tsoron masifar yaya Abbas ne yasa ta fad'i haka ba kuwa?
Bana jin haka nafee amma dai zan zauna muyi magana da ita gobe da safe kafin su yaya Abbas su zo dan gabad'aya ta kashe min jiki da zancen ta.
Nafee tace"ae ba ke kad'ai ba anti har ni, haka itama ba makawa zancen yana damunta dan duk naga ta qara shiga damuwa Allah dai ya kawo qarshen wnn abun.
Anti Hafsa tace"Amin"
Kana sukayi sallama,Nafee ta shiga mota ta wuce ita kuma ta koma daga ciki.
Qarfe biyun dare Husna na tsakar sllr nafila kwatsam taga qarti zagaye da ita sun shigo d'akin,ta sallame sllr a rud'e tana kallon su d'aya bayan d'aya kafin ta iya cewa komai babban su ya d'aura mata bindiga aka, muryar ta na rawa cikin tsananin tsoro tace"Aa dan Allah ku gaya min duk abinda kuke so zan baku wlh"
Cikin muryar sa kakkausa mai kaurin gaske yace"yarinya rayuwar ki muke so kuma ita zamu kar6a"
Tace"Haba dan Allah me na muku dan Allah kuyi haquri koma mene ne wlh na tuba bazan sake ba na roqe ku,ku tausaya min kodan cikin da ke jikina dan Allah!?
Bai kulata ba sae qara danna mata bindigar yayi aka zae harbe ta ba shiri ta buga wani irin ihu cikin tsananin firgici har waheed dake kwance a d'akin sa yana bacci se da ihun ya tashe sa,nn ya fito da hanzarin sa wanda duk a tunanin sa haifuwa ce tazo mata amma koda yazo d'akin se yaga sa6anin haka a nn hankalin sa yayi mummunan tashi ganin qartin gaske kusan su biyar zagaye da Husna ogan na shirin harbinta aka wanda tsirif ya rage ya sakar mata bullet,ba shiri ya tafi aguje tare da sa qafa ya shure masa hannu harbin ya sami d'aya daga cikinsu ya fad'i kae tsaye a gurin dafe da inda harbin ya saukar masa.
Waheed bae damu ba sae hannun husna ya kama yana son fitar da ita daga d'akin sauran suka yo kansu waheed ya shiga kare Husna dan ya fahimci ita suke son harbi,Husna kuwa se qara la6ewa bayan sa take cikin kuka mai cike da tausayi tana roqon suyi haquri amma ina sae saukar bullet kawai taji a jikinta ogan su ya harbeta, kae tsaye ta saki qara had'e da fad'uwa gurin,a rud'e waheed yayi kanta se jijjigata yake yana kiran sunan ta amma sam ta daina motsi kwata kwata,nn ya tashi cikin kukan kura yayi kan wanda ya harbeta ya had'a sa da bango tare da shaqe masa wuya iya qarfin sa,take idanun sa suka firfito yana neman agaji ya kasa qwatar kansa haka sauran qartin ma duk qarfin su sun kasa qwatar shi nn wani ya sami makami se dukan waheed yake aka ta koina amma waheed yaqi sakin sa ganin da gaske waheed so yake ya kashe musu oga suka d'auki bindiga sae harbinsa suke har sae da waheed ya sake shi suka fad'i tare dashi har ogan ba mai motsi a cikin su.
Firgigit!Bintu ta tashi daga mummunan mafarkin da take hankalin ta a tashe se fad'in innalillahi wa inna ilaihi raji'un! take,ta miqe zaune tare da kunna bedside lamp,qarfe biyun dare da mintina ta gani a agogon bangon d'akin,a hankli ta dafe kanta yayinda take jin zuciyar ta kmr zata faso qirjinta ta fito sbd dukan uku uku da take.
Tofi tayi gefen hagunta sau uku snn ta nemi Allah tsari daga shaid'an da abinda ta gani a cikin mafarkin ta sau uku kmr yanda addini ya tanadar.
Sam bata jin zata iya komawa ta kwanta dmn ba kad'an ba mafarkin ya matuqar razana ta,a nn ta tashi ta shiga bathroom ta d'auro arwala tazo sae sllh take tana roqon Allah ya sauqaqa abinda ta gani a cikin mafarkin ta yasa kar ya zamo gaskiya.
Haka ta kasance har asuba bata koma bacci ba.
K'arfe bakwai Anti Hafsa na kitchen ta soma jin ana qwanqwasa qofa ta ajiye abinda take tazo ta bud'e qofa, police ta gani su biyu maza mace d'aya, fuskarta d'auke da mamaki tace"police......
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
0 comments:
Post a Comment