Mahaifin Mabaruka ya mutu tana
da shekaru ashirin da hudu a
duniya, sakamakon wani
mummunan hadarin jirgin kasa
da ya ritsa da shi a kasar Indiya.
Mahaifin nata Faruk ya bar
duniya da bakin cikin har Allah ya
karbi ransa bai ga mijin yar sa
abar kaunarsa Mabaruka ba. Sau
da yawa ya kan so ya tambaye ta
shin ko ta sami saurayi To amma
idan ya tuna da yadda take ita ba
kyau ba a fuska hakan nan ga ta
gurguwa sai ya yi shiru domin ko
kadan bai san ya yi abin da zai
sosa mata rai Duk da haka nan
sau da yawa ya kan yi alfahari da ita domin ta yi matukar kama
dashi musamman ma tababben
hancinsa mai kamar begila.
Sa'ar da mahaifinta ya rasu, sai
duk kusan kamfanunnukansa da
makudan kudinsa gami da
sauran muhimman kadarorinsa
suka koma karkashinta. Cikin
kankanin lokaci ta zamo tabani
ka ga sarki, ga ta dai gurguwa
kuma mummuna, amma fuskarta
ta fi komai kyau ga duk wanda
ya santa a zahiri da badini ba
don komai ba kuwa sai don
dimbin arzikinta.
Lokacin da mahaifin Mabaruka ya
cika shekaru hudu da rasuwa, sai
mahaifiyarta Aliya ta yi kiranta
wata rana da yamma ta ce da ita.
"Mabaruka kina tunanin aure
kuwa?" Mabaruka ta sunkuyar da
kai cikin taraddadi, domin ta san
tun da take wani saurayi bai taba
dubanta a matsayin ta burgeshi
ba, sai dai ya dubeta a matsayinta na macen da ta fi
kowa arziki a cikin matan Afirka.
"Ina yi." Ta ce da mahaifiyarta
kanta a sunkuye. Aliya ta dubeta
cikin tausayi, domin ta san ko ita
da ta sha miya a duniya ta fi
Mabaruka kyan gani a fuska.
"In dai kin sami wanda ki ke so
sai ki sanar dani, kin ga ke kadai
nake da ita a duniya, shi yasa
nake matukar son na ga jikokina
a duniya tun ina da sauran
numfashina."
Mabaruka ta yi shiru tana
sauraren mahaifiyarta, yanayin
fuskarta a birkice. Ita kanta ta
san mummuna ce, sau da yawa
in ta kalli madubi sau daya ba ta
son ta kuma kallo a karo na biyu,
amma ta kan gode Allah da ya yi
mata dimbin dukiya. Aliya ta yi
nazarin fuskar yar ta na tsawon
lokacin sai ta ga duk hankalinta
ya tashi. Ta san abin da ke
damunta dan haka sai ta dubeta
da murmushin karfafa gwiwa ta
ce.
"Kada ki damu da yadda Allah ya
yi ki Mabaruka, abin da nake so
ki kula shine kina da dukiya, kin
san kuwa a wannan zamanin ba
ta da na biyu." Ta dan yi shiru
tana nazarin fuskar Mabaruka.
"Ina fatan kuna fahimta ta?"
Aliya ta ce da ita tana dubanta
ido da ido.
Mabaruka ta girgiza kai a
sanyaye. Akwai alamun kwalla a
idanunta. To amma bata bari
mahaifiyarta ta gane ba domin ta
san hakan na iya tayar mata da
hankali.
"Abin da nake so da ke Mabaruka
shi ne ki duba ki waiga, ki hanga
da idanunki, duk fadin garin nan,
idan kin hango namijin da ki ke
so, ki ka ga ya kwanta miki a rai
ko wane ne shi ki yi kokarin ki
shawo kansa ya zo nan gida
gurina!" Mabaruka ta dubi
mahaifiyarta cikin kaduwa ta ce.
"Mama...ya ya za a yi na iya kawo
shi har gida? Sai dai in shi ne ya
ganni ya zo ya ce yana sona."
Aliya ta dubeta gami da dariya.
"Mabaruka kenan. Na fahimci har
yanzu ba ki san irin yadda
mutane suka dauke ki bane. To
bari in fada miki duk kasar nan
ke ake labari saboda tsabar
kudin da ki ka gada. Duk da
yadda ki ke ganin ki din nan ki ke
raina kanki kin fi karfin raini,
domin kudinki ya wanke duk
wani nakasu naki. Saboda haka
ina son ki sani cewa babu wani
da namiji da za ki kirawo a girin
nan ya ki zuwa gare ki ko shi
wane ne, domin kina da babban
makamin da ya fi nukiliya tasiri,
dan in ba kudi babu zancen
nukiliya balle aikinsa." Aliya ta
dan yi shiru tana duban fuskar
Mabaruka sannan sai ta daga
hannu ta nuna fuskarta ta ce.
"Na baki daga nan zuwa sati
guda duk namijin da ki ka gani
ya yi miki ki yi kokarin ki kawo
min shi nan..
Nan da rana ya ta yau kenan....
Ranar da ta yi daidai da cikarta
shekaru ashirin da takwas a
duniya! Mabaruka ta ji wani
zazzafan gumi ya fara lullubeta.
Tambayar da ta fi damun
zuciyarta shi ne, shin a cikin
mako guda ya ya za a yi ta sami
saurayin da ta ke so, ta kuma iya
jawoshi har gida!
Sidi Mai jaka ya yi shiru anan,
sannan ya dubeni da murmushi
ya ce.
"Nas, ka ga abin da nake fada ma
ko? Ai daman sai da na ce da kai
kayi hakuri da sannu zan hade
ma bakin zaren labarin biyu na
daure. Gashi kuwa na daure ma
su kamar yadda na yi maka
alkawari." Na dago kaina gami da
ajiyar zuciya
"Haka ne." Na ce dashi
"To ya ya kuma bayanin can inda
muka baro, inda Mabaruka ta ce
da Anas ya shiga mota su tafi."
Sidi mai jaka ya dubeni ya yi
murmushi ya ce.
"Nas kenan, na dai fuskanci ka fi
son can daya bangaren labarin
ban yi mamaki ba a matsayin ka
na saurayi dole ne labarin
soyayya da kudi ya burge ka."
Sidi Mai jaka ya yi shiru kana ya
tsikari tubani guda ya jefa a baki
ya dubeni idanunsa na zubar da
ruwa kamar kuturu saboda
masifaffen yajin dake cikin
tubanin
"Nas, ina son ka kaddara a cikin
zuciyarka cewa ga Mabaruka da
Anas nan zaune a cikin
tangamemen falon gidansu
Mabaruka suna fuskantar
mahaifiyarta Aliya
"Na kaddara." Na ce dashi cikin
sauri domin na gama kaguwa na
ji yadda za ta kasance. Sidi mai
Jaka ya goge hawayen dake zuba
daga idanunsa sannan ya ci
gaba.
Daga lokacin da katuwar (Jeep)
din ta ajiye su Anas da Mabaruka
a farfajiyar gidan zuwa lokacin
da suka ratsa akalla Falo Bakwai
ANAS YA GAMA FITA DAGA HAYYACINSA domin a iya tunaninsa bai taba imani da
cewa akwai gidan da ya kai na
su Mabaruka tsaruwa ba a duk
fadin garin. Gashi dai Anas
ma'aikacin otal ne, haka nan otal
din ita ce uwa ga duk wata otal
dake fadin garin wajen
kayatuwa, amma sa'ar da ya ga
irin tsari da ni'imar da aka shirya
a gidansu Mabaruka sai ya ga
duk darajar otal din ta zube a
gurinsa, ta koma tamkar kango a
zuciyarsa. A tunanin Anas ya
dauka irin kayatattun gidajen
nan da ya kan gani a finafinan
Turawa, ba za a iya taba
samunsu anan ba sai a kasashen
turawan, domin abu ne mai
wuya ace irin yadda almajirai ke
cika tituna taf da barace-barace
da kuma tarkacen marasa aikin yi
da talakawan dake ta sintirin
neman abinci sau daya a rana a
titunan Najeriya, wai za a sami
mai arzikin da har zai iya gina
irin wannan! Hakika Anas ya yi
masifar kaduwa sa'ar da ya shiga
gidansu Mabaruka domin bashi
da maraba da irin wadanda yake
gani a finafinan turawa. Anas ya
yi imani da cewa da ace za a
dauke shi a cikin barci bai sani
ba a jefashi a gidan, idan ya farka
ya ganshi ciki babu abin da zai
hana ya ce aljannu ne suka
dauko shi suka kawo shi London.
Lokacin da suka isa babban falon
gidan karfe takwas da yan
mintuna. Sa'ar da Aliya ta shigo
dakin tuni har Anas ya zabi
bangare guda na daga tarin
kujerun dake dakin ya lume a
ciki, to sai dai kuma duk wanda
ya ganshi ya san a bala'in tsorace
yake, domin a rabe yake a gefe
guda ya yi fakare baya ko
kwakkwaran numfashi kamar
jikakken zakara.
Aliya ta matso zuwa tsakiyar
falon, ta dubi Anas da tattusan
murmushi.
"Ina son ka saki jikinka Anas ka
dauka a zuciyarka cewa nan
gidan ku ne." Anas ya ji gabansa
ya fadi ras! Rabon da da wani ya
ce dashi nan gidansu ne, tun
ziyarar sa gidan wata
budurwarsa Safiya wadda
iyayenta suka so su makala masa
ita, da kyar Anas ya samu ya
tsere, domin a duk fadin duniya
abokan gabarsa guda biyu ne,
talauci da aure!
Aliya ta nemi kujera ta zauna.
Daga inda take zaune tana
fuskantar su Anas, hakan nan ta
lura da cewa Anas duk a rude
yake tuni har ya faera zubar da
gumi duk kuwa da ni'imar rabar
dake kwararowa dakin. A
zuciyarta, Aliya na cewa lallai abin
ma zai zo da sauki tunda ma ya
gama tsorata dani, don haka sai
ta kalli Anas kai tsaye ta ce.
"Ina fatan ta fada ma dalilin da ya
sa ta kawo ka gidan nan?"
Anas ya dubi Mabaruka a rude,
Mabaruka ta yi masa murmushin
yake, sannan ta sunkuyar da kai
a kunyace a zuciyarta tana cewa,
oh! Yau na shiga uku za a
tursasa mutum ya aure ni ba tare
da yana kaunata ba.
Ganin Anas ya yi shiru sai Aliya ta
dube shi ta ce.
"Bawan Allah mene ne sunanka?"
"Sunana Anas...." Ya ce bakinsa na
rawa.
Aliya ta sake duban kyakkyawar
fuskarsa ta ce, "Ina son ka dubi
yarinyar nan da kyau ya ta ce."
Anas ya dago kai cikin kaduwa
ya dubi mummunar fuskar
Mabaruka na dakika uku sannan
ya sunkuyar da kansa.
"Na...kalleta.. ." Aliya ta yi
murmushi "Anas, abin da ya sa
na ce ka dube ta shi ne, domin ka
ajiye hotonta a cikin zuciyar ka,
domin ita ce matar da za ka
aura."
Anas ya dago kai cikin tsananin
kaduwa, "Hajiya...ban fahimce ki
ba?"
Aliya ta dubeshi da murmushi.
"Sannu a hankali za ka fahimce ni
ka kuma fahimci dalilin da ya sa
na ce da kai ita za ka aura."
Ta dan yi shiru tana mayar da
numfashi.
"Da farko dai ina son ka sani
cewa ni ce na sa Mabaruka na ce
da ita duk namijin da ta gani ta ji
ya kwanta mata a rai ta kawo
min shi.....Abu na biyu kuma shi ne tun da
aka haifi Mabaruka bata taba
neman wani abu ta rasa ba, shi
yasa to na ce da kai ita za ka
aura, domin kaunarka ce ta sa ta
kawo min kai."
Anas ya ji kamar an dora masa
buhun alhaki a tsakiyar kansa,
domin ko mosti baya iya yi
zaune yake ya yi mutuwar
tsohuwa sai idanunsa ne ke ta
kifkiftawa kamar idanun
barawon akuya, to amma
zuciyarsa na kai kawo. Cab! Na
auri gurguwa mummuna! Ai da
na auri wannan ma gara na auri
uwar domin ta fita komai da
komai.Anas ya share gumi sa'ar
da zuciyarsa ta tuno masa da
cewa wannan mummunar
gurguwar fa da ake kokarin cusa
masa, sunanta KUDI!
"Anas." Aliya ta katse tunanin sa.
Anas ya dago kai ya dubeta.
"Ina son ka bani hankalin ka
nan." Anas ya dube ta ido da ido
ya ce.
"Ina jin ki."
"Idan ba ka san wannan yarinyar
dake gabana ba bari in fada ma.
Ka ga duk fadin kasar nan babu
wata mace da ta mallaki kashi
daya bisa hudun dukiyar da ta
mallaka haka nan ita ce mace ta
biyu a kudi a cikin duk matan
Afirka Da mun biya ta mutane da
tuni an aure ta ko dan a amfani
kudin da take dashi, to amma
kuma ni na fi son ta zabi wanda
take so da kanta." Aliya ta dan yi
shiru tana mayar da numfashi.
"A yanzu kai ta gani ta ke so shi
ya sa ta kirawo ka gare ni. Anas
ina so ka auri Mabaruka domin
auren ta alheri ne a gare ka." Ta
sake yin shiru a karo na biyu
sannan sai ta dubeshi ta ce.
"Nawa ake biyanka a wannan
busasshiyar otal din da kake
aiki?" Anas ya hadiyi yawu da
kyar kwakwalwarsa sai juyawa
take yi cikin kokon kansa.
"Du...dubu takwas!" Aliya ta
dubeshi ta fashe da dariya ta ce.
"Dubu takwas! Kyakkyawan
saurayi kamarka a dubu takwas?
Ko kuwa kullum ne ake biyanka
dubu takwas din? Anas ya
girgiza kai.
"Wata-wata ake biyana."
Idanun Aliya suka zazzaro waje
cikin tsananin kaduwa.
"Wata guda a dubu takwas." Cab!
Allah rufa asiri." Ta yi shiru na
dan lokaci sannan ta sake duban
Anas.
"Idan yanzu na baka manajan
daya daga cikin
kamfanunnukanta albashin
naira dubu dari biyu ya yi ma...a
wata guda nake nufi."
Anas ya ji zuciyarsa ta harbo da
karfi kamar kibiya tana kokarin
fasa masa kirji, dubu dari biyu!
Tun da yake bai taba tsammanin
zai sami dubu hamsin ma ba a
duniya lokaci guda.
"Ya...yi min." Ya ce da kyar domin
makogwaronsa ya bushe. Aliya ta
yi murmushi sannan ta ci gaba
da cewa.
"Ka je gida ka turo iyayenka
domin nan da sati guda za a
daura muku aure. Ina son kuma
ka sani cewa daga yanzu duk
inda kake so a duniya za ka iya
sa kafar ka, haka nan ban da
albashinka, duk karshen wata na
yi maka alkawarin naira dubu
dari daga cikin ribar da nake
samu karshen wata a kamfanina
na atamfa, sannan a matsayin
kyauta ta musamman da zan yi
ma a matsayin ka na angon yata
zan saya ma wannan busasshiyar
otal din da kake aiki a ciki, in sa a
rugujeta a sake gina ma ita, in ya
so sai ka zabi sunan da ka ga ya
dace ka sa mata." Aliya ta yi shiru
tana numfasawa, sannan sai ta
mike tsaye ta dubi Anas ta ce.
"Ka yarda zaka aure ta?" Anas ya
ji kamar katanga ta fado masa a
tsakiyar baya. Abu daya da ya
tabbatarwa kansa shi ne in duk
za a bashi duniyar nan domin ya
kaunaci wannan mummunar
gurguwa ba zai taba iyawa ba, to
amma da albashin naiura dubu
dari biyu a wata, da naira dubu
dari a sama da kuma kyautar
otal din da za a bashi, ya tabbatar
ko da Mabaruka kuturwa ce sai
ya aureta. Cak! Yau na zama
miloniya cikin sa'a guda... Ya ce
cikin zuciyarsa, koda ya tuna da
cewa lagwada otal za ta zama
tasa sai ya ji wani zazzafar gumi
na farin ciki ya zubo masa
tuntuni ya dade yana addu'ar
Allah ya bashi damar da zai rama
wulakancin da manajan otal din
ke yi musu, sai gashi a banza
yanzu dama ta samu a bagas.
Wani busasshen murmushin
mugunta ya subucewa Anas nan
da nan ya dauki alkawarin cewa
duk ranar da ya mallaki ota din
sai ya tikawa dan dukurkushin
manajan dundu a tsakiyar baya.
"Anas!" Aliya ta katse masa
tunani "Tunanin me kake... Baka
amince bane?" Anas ya girgiza
kai cikin sauri sannan ya ce.
"Kin ce cikin sati za a daura
auren ni ko yanzu naira dubu
takwas ce daidai a aljihuna ita
ma ta albashin da aka biyani ce
dazu da yamma."
Aliya ta yi murmushi sannan ta ce
"Tun da ka amince ina kai ina
fargabar kudi, nan gidansu ka
zo." Ta dan yi shiru sannan sai ta
ce.
"Kana jin naira miliyan goma zata
isheka fara shirye-shirye kafin
zuwa jibi". Anas ya ji yawun
bakinsa ya kafe ya dube ta a
rude.
"Miliyan goma kika ce ko kuwa
dubu goma."
Aliya ta fashe da dariya sannan
ta dubi yarta Mabaruka wacce ke
gefe ta yi tagumi tana
sauraronsu ta ce
"Miliyan goma na ce ko sun yi ma
kadan a kara ma?"****
Sidi mai jaka ya yi ajiyar zuciya
sannan ya dubi kwanon tubanin
dake gabansa cikin takaici duk
yawan tubanin nan ya hadiyesu
baki daya saura kwaya uku kacal
cikin kwanon.
"Nas ga labari ya dauko dadi
gashi kuma tubanina ya zo Gangara. Irin wannan abin shi yakansa wani lokacin na ji duk na
tsani bada labari domin tubanin
nan tamkar mota ce da man fetur
idan babu shi ka san ban cika
abin kirki ba".
Sidi mai jaka ya yi shiru yana
kallon cikin kwanon tubanin
sannan ya dubeni fuskarsa a
murtuke.
"Kamata ya yi ka karasa min
zuwa sallar Azuhur, idan na
koma gida sai na sa kakata ta
sake yi ma wani tubanin." Nan da
nan fuskar Sidi mai kaja ta
washe.
"shi yasa nake son ka NAS. Domin
daga na yi motsi sai ka gane abin
da nake nufi." ya dan yi shiru,
sannan sai ya ce, bari a gurguje
na kulla maka wani sabon zaren
labarin da wannan, domin naga
kamar lokacin sallah ya kusa."
Sidi Mai Jaka ya tsikari tubani na
ukun karshe ya jefa a baki
sannan ya dubeni.
Nas, ina son ka dauka cewa tuni
har an daura auren Anas da
Mabaruka gurguwa."
"Na dauka." Na ce da shi. Sidi mai
jaka ya dubeni, sannan ya ci
gaba.
Wato Nas, watanni biyun da suka
biyo bayan bikin Anas sun yi
matukar jefa Anas a cikin sabon
yanayi.
Lokacin da Anas ya bar gidan su
Mabaruka bai tsaya ko ina ba sai
wurin iyayensa, jikinsa na rawa
ya ce da su aure zai yi. Lokacin da
labarin auren nasa ya watsu a
cikin dangi sai aka yi ta zuwa ana
taya mahaifansa murna, domin
duk garin babu wanda bai san
ko wacece Mabaruka ba. Da yawa
daga cikin mahassada suka yi ta
zunde, tsegungumi da gulma,
suna cewa wai in ba lalacewa ba
ina kyakkyawa kamar Anas ina
auren gurguwa mummuna.
Wasu daga cikin masoyansa sun
taya shi murna, domin sun san
duk da dai bai yi dacen mata ba,
to amma ya yi bankwana da
talauci har abada, wannan a
gurinsu ya isa abin farin ciki,
domin a tunaninsu Anas ya gama
samin kwanciyar hankali da
nutsuwa.
To kamar yadda suke tunani NAS
hakanan ta kasance a cikin
watanni biyun da suka biyo
bayan bikinsu, domin Anas ya
sami hutun da bai taba tsammani
ba a iya tsawon rayuwarsa.
Da farko dai da yake daman shi
ba damuwa ya yi ba da wani
addini ba kullum kwanan duniya
Anas baya tashi daga barci sai
karfe goma sha daya na safe,
sannan ne zai tashi ya yi wanka,
sannan ya nufi wurin aiki.
Zamantakewarsa da Mabaruka ta
bashi mamaki, domin ya sami
Mabaruka macece mai iya dadin
magana, da tarairaya, duk kuwa
da cewa gurguwa ce, wani sa'in
sai su tafi bakin (Swimming pool)
su yi ta wasa da katuwar bal
marar nauyi, Mabaruka na zaune
akan kujerarta a bakin ramin
ruwan, shi ko yana ciki, idan ya
jefo mata, sai ta cafe ta jefa masa.
Wani sa'in kuwa sai Anas ya
dauketa a mota su yi ta yawo a
cikin gari suna bin guraren
shakatawa abinsu da yake Anas
gwanin ban dariya ne, sai ya yi ta
yi Mabaruka tana dariya. Wannan
ita tasa sau biyu ko uku kawai
Anas ke zuwa gurin aiki a sati.
"Kada ka dami kanka Anas da
yawan zuwa wurin aikin nan
kudi ne, muna dashi albashinka
kuma ko kaje ko baka je ba dole
ne a baka." Mabaruka ce ke cewa
Anas haka a wata safiya suna
karin kumallo.
"Anas, zamanka kusa dani ya fi
min zuwanka aiki, domin ni har
kullum idan na dubeka sai na ji
zuciyata ta yi fari tas, dan haka
ne bana son rabuwa da kai koda
dai dai da kankani...domin ..." Ta
dan yi shiru tana duban Anas.
Anas ya dube ta sa'ar da ya ji tayi
shiru.
"Domin muma me...?" Mabaruka
ta dube shi.
"Domin bana son wata mace ta
mallaki zuciyarka a duniya idan
bani ba, shi yasa ka ga na ce ma
sau biyu kawai za ka ke zuwa
aiki a sati."
Anas ya ji zuciyarsa ta harba, ko a
lokacin da yake yawon banzan
sa, babu abin da ya tsana a
rayuwarsa irin mace mai naci,
wacce zata makale masa kamar
cingam ta hanashi shan iska.
Sidi mai jaka ya dago kai ya
dubeni da murmushi sannan ya
ce "Nas, wata uku su Mabaruka
suka yi cikin farin ciki, daga
wannan kuma basu kara samun
koda dai dai da sa'a daya ba ta
farin ciki, domin a safiyar wata
rana ne Mabaruka ita da kanta ta
yi sanadiyar kawo karshen duk
wani farin ciki nasu!
Wata rana da safe aka yi sa'a
Anas ya farka tun da asussuba,
koda yake ba farkawar Allah da
Annabi bace. Anas na kwance
kawai sai ya ji idanunsa sun
bude. Abin ya ba shi mamaki dan
haka sai ya dubi agogo. Karfe
hudu na asuba agogon ya nuna.
Anas ya tashi zaune cikin
mamaki, ya dubi Mabaruka
gurguwa kwance a kusa da shi a
takure kamar kunkuru tana ta
barci abinta, mummunar fuskarta
a yatsune. Anas ya dauke kai
zuciyarsa na wasi-wasin dalilin
da ya sashi farkawa a wannan
lokaci. Tsawon lokaci yan zaune
akan gadon, sannan ne to
maganar Mabaruka ta fado masa.
"...bana son wata mace ta
mallakeka a duniya idan bani
ba..." Wani zazzafan gumi ya
barkowa Anas, sa'ar da ya tuno
da wannan kalami nan da nan ya
sake duban mummunar fuskar
Mabaruka. A zuciyarsa ya ce cab!
Ba zata yiwu ba duk kyawawan
matan dake duniyar nan na rasa
wacce zan kare rayuwata da ita
sai wannan! Anas ya share gumi
sannan ya dada kallon Mabaruka
tsigar jikinsa ta dauki rawa.Sannan ya dada kallon Mabaruka,
tsigar jikinsa ta dauki rawa. Dole
ne na sami hanyar da zan rika
zagayawa gari ni kadai, ya ce
cikin zuciyarsa, wani abu da ya fi
baiwa Anas tsoro da al'amarin
Mabaruka shi ne ya fahimci tana
da bala'in Kishi.
Sau da yawa idan suna tafiya a
mota da taga ya dauke idanunsa
gefe guda ya kalli inda mata suke
sai ta kalleshi ta ce.
"Me kake kallo?" Anas ya kan ji
zuciyarsa kamar za ta fashe
saboda haushi.
Me take nufi ne da zata hana shi
kallon kyawawa bayan duk da
tarin miliyoyin kudin nan nata yar
karamar yarinyar dake talla a
gefen tituna ta fita fasali
Bayan da wannan kuma akwai
wata rana da yamma wata kawar
Mabaruka wai ita Amal ta ziyarci
Mabaruka Lokacin da ta samesu
zaune suke cikin tangamemen
lambun shakatawar gidan Anas
yana karantawa Mabaruka wani
littafi na hausa wai shi SIRRINSU.
Tun kafin Mabaruka ta gama
gaisawa da Amal ta kura masa
idanu. Anas ya lura da irin kallon
da take yi masa, dan haka sai ya
yi sauri ya sunkuyar da kansa
kamar yana kallon littafin da yake
karantawa duk kuwa da cewa a
fakaice kallon kyawawan
kafafunta yake yi ta kasan littafin.
"Tashi ka koma daga ciki kadan
bamu guri zamu gana, idan mun
gama zan sa a kirawoka."
Mabaruka ta ce dashi, Anas ya
mike tsaye simi-simi kamar
tunkiya ya wuce cikin gidan
zuciyarsa na kuna. Kalmar ta yi
matukar kona masa rai, to amma
tunda dai an saye shi ya yarda ya
amince babu abinda zai iya
domin kowa ya sayi rariya ai ya
san ta zub da ruwa. Idan har
akwai abu daya da Anas ya
tabbatarwa da zuciyarsa shi ne
ba zai taba yarda ya batawa
Mabaruka rai ba, domin ya san
hakan na nufin rabuwa da ita,
shi ko ya san a yanzu ya gama
sabo da jin dadi kum...
"Anas." Ya juyo firgigit sa'ar da
muryar Mabaruka dake kwance
kusa da shi ta katse tunaninsa.
Mabaruka ta dubi agogo, sannan
ta yi mika ta dubi Anas cikin
mamaki ta ce.
"Lafiya na ganka a zaune haka
tunda asussuba." Ta dan yi shiru
sannan sai ta miko siraran
hannunta ta shafi bayan Anas.
"Ko ba ka da lafiya ne?" Ta
rikoshi ta mike zaune,
nannadaddun kafafun da Anas
ya tsana fiye da komai a jikinta
suka fito fili. Anas ya girgiza kai.
"Kaina ne ya ke dan sara
min...amma na san nan da dan
lokaci zai bari daman lokaci-
lokaci yakan yi min haka."
Mabaruka ta dubeshi cikin
shakka da mamaki ta ce.
"Ina jin rashin yawan motsa jiki
ne..." Ta dan yi shiru, sannan sai
ta ce ya kamata na hada mana
wata hadaddiyar liyafa ta
shakatawa a gidan nan, ina
ganin haka zai sa ka dan
warware, kuma kamata ya yi
bayan liyafar mu tafi kasashen
turai hutu, domin tuntuni ya
kamata ace mun tafi mun yi
(honey moon) dinmu a can,
dadin da bana ji sosai ne ya
hana."
Ta dan yi shiru tana duban
fuskar Anas "Ko kuwa ya ka
gani." Anas ya ji wani dadi ya
lullubeshi domin tabbas ya san
irin liyafar miloniya me take nufi
ko shakka ba ya yi za a tara zuka-
zukan mata kyawawa, abin da
idanunsa suka fi kaunar gani fiye
da komai a duniya. Don haka sai
Anas ya dubeta cikin sauri ya ce.
"Kwarai kuwa haka za a yi liyafa
ba lallai kin zo da dabara." Suka
fashe da dariya, sannan
Mabaruka ta dora kanta bisa
cinyarsa ta rungumoshi fuskarsa
kusa da tata, abin da Anas ya yi
matukar tsana, ta ce.
"Anas wai don Allah me ka fi
kauna fiye da komai a duniya?"
Anas ya dubeta cikin mamaki
domin tambayar ta zo masa a
bazata, kadan ya rage ya ce da ita
kyawawan mata, to amma da
yake tsohon kwararre ne a sanin
tarkon mata ya fahimceta don
haka sai ya dubeta da tattausan
murmushin yaudara ya dada
rungumota a kirjinsa ya ce.
"Abin da na fi kauna a duniya ki
ke son ki sani?" Mabaruka ta
gyada kai cikin murmushi. Anas
ya dubeta a tausashe duk kuwa
da cewa zuciyarsa kamar ta
tsage saboda haushi ya ce.
"Ke na fi kauna fiye da komai a
duniya."
Mabaruka ta lumshe idanu cikin
tsananin farin ciki Tun da take a
duniya bata taba jin kalamin da
ya faranta mata rai kamar
wannan ba. Wani zazzafan
hawaye na farin ciki ya yi sartu
akan fuskarta.
***
Sidi mai jaka ya dauki dunkulallen
tubanin karshe ya jefa a bakinsa,
ya dubi kwanon cikin takaici,
sannan ya dubeni ya ce.
"Nas, ranar liyafa ta zo. Kamar
yadda Anas ya yi tsammanin tun
farko haka ta kasance domin duk
kusan kala-kala ta kyawu na
mata babu wadda ba a hada a
wurin ba. Liyafar ta sami halarta
mata kyawawa ashirin da uku,
maza goma kacal wadanda mafi
yawa ma daga cikinsu duk Anas
ya girmesu.
Aka yi ciye-ciye da shaye-shaye a
tangamemen lambun
shakatawar, aka saki kidan dujal
yan mata da samari masu
karancin kunya suka fara tikar
rawa.
0 comments:
Post a Comment