🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣6⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
**************
*Federal University dutsinma*
.......Ta shako wuyanta ta buga da table, gyalen ta ya fadi hular gashin da ke kanta itama tayo kasa, wani chukuikuyon kitso ya bayyana ba 'a ko ganin tsagar ga kegen can manne a wuya.....kaiii Bilkisu kina hauka...mAnwar ya fada a firgice..... Ta nuna Shi da hannu daya korar mun wadannan kattin ta kallesu tana zare ido.... *What the hell are you doing here*?????.... Wata Kara mufeeda ta saki ta dago ta da karfi goshinta ya Kara tsawo kamar wani bread da ake Kira danbisije na funtua...
Ya yunkura zai riketa ta Kara buga kanta a table....Zan nakasa ta Anwar wallahi...... Ya daga hannuwa sama okay ..okay... Ya kallesu kuje waje... Kofar class din da bakin tagogi students ne makil ...... Idanun ta sun kada sunyi jawur tana magana tana zare mishi ido...... Kai bazaka iya maganin ta ba ko? Zan ci ubanta yau saboda duk makarantar nan yarinyar nan ta tsone man ido..... Zan yi..wallahi zanyi maganin ta please kada ki janyo mun bala'i kada kiyi kisan Kai Bilkisu.... wannan cin fuskane ki barshi ta mayar da gyalenta please....Ta ingizata da karfi tayi baya ta fada cikin sit bayanta ya daki kujera da karfi ta saki wata Kara.... Yayi wurinta da gudu a firgice...... Tayi tsalle ta dira gabansa kana tabata Ina karairayata....... Chief security suka gani da wasu securities subhanallah meke faruwa anan.... Yana ganin Anwar yace ranka ya dade da kanka???
Dan Allah ku fita da mufeeda kuje da ita.... Magana yakeyi a harmutse duk ya rikice, Bilkisu kuwa ya dake ta Sha mur Kai baka taba cewa ita ce tayi wannan tashin hankalin ba....... Ya kalli security daya je da ita clinic.... Yallabai kuyi hakuri muje office... Ita ce tayi gaba...... Zuciyar ki tayi yawa Bilkisu wannan yarinyar ta wahala me yasa Zaki.... Ta dalla mishi harara , ka Sanya a daureni na daki sahibar ka kasa a kaini prison..... Ohh my God,
Da gudu sadeeq ya dawo cikin makaranta jin wannan mummunan labari,
Abin mamaki Bilkisu ta Sami shaidar lallai mufeeda ce ta Fara tsokanar ta..... Anwar ya shiga ya fita case ya mutu. Suka fito duk ta chukuikuye fuska... Sadeeq yarinyar kaga zata yi kisan Kai ko?
Bilkisu me...... Na rantse da Allah idan ka Kara mun maganar waccen Yar iskar Zan sameta har dakinta na Mata tsinannen duka Wai Anwar kasan Hali na kuwa?
Na sani a yau, na sani wallahi Dan Allah kada ki Kara kula ta zan kawo karshen matsalar..... Kada ma ka kawo zata ci ubanta.... Ya kalli sadeeq duk sukayi murmushi.
Kawo key din na dauko Miki motar sadeeq ku jira anan..... Ya wuce da sauri, sadeeq ya danyi dariya, duk kin hargitsa mun Anwar kin San Shi baya son tashin hankali..... Tunda takai fagen mufeeda ko? Ai Dole ya hargitse, wace irin masifa ce Suleiman ke bai gani ba?
Kasan Allah ka gaya mishi idan bai nesa da mufeeda ba sai na halaka ta...... Itama daga yau Dole ta shiga taitayinta kuma Zan fada mishi.
Ya iso, ganin baida niyyar fitowa yasa ta fada baya ta zauna Dole sadeeq ya shiga gaba.... Suna fita yayi hanyar gidan sa Yana fadin Bari ki Fara ajiye mu tukun ta mishi banza kawai.
Har ciki ya shiga da motar suna tsayawa ta fito ya dan koma gefe ta shiga wani mugun ribos da tayi sai da ta birge duk Wanda ke shiyyar.... Ya bita da murmushi kaiii sadeeq yarinyar can karshe ce..... Suka kyalkyace da dariya Ina so na ce ta dafan abinci amma duk na tsorata da ita.... Sadeeq ya kwashe da dariya Bilkisun kake tsoro????
.... wallahi tsoronta nake sadeeq, ya fada Yana dariya.
Kaga tsawar da ta daka mun Wai na ce su mustapha su fita???
Duk suka Kara kyalkyace da dariya.... sadeeq ya ce ko baba da babansa.
Mufeeda kuka kawai takeyi, ba dukan ya Mata zafi ba, irin yanda ta cire Mata hular gashi ta tozarta ta gaban jama'a..... Ta kasa daina kuka, kunya ta hanata fitowa daga clinic din ta tafi daki.
Hakuri kawai kawayenta ke bata, Asma'u ta ce Ina ga mufeeda ki shafawa kanki lafiya ki kyale Anwar... Wallahi ko Zan rasa rayuwata bazan hakura dashi ba..... Duk suka zaro ido.
Amina ta ce wallahi matar sa da gaske sunyi Aure mufeeda ki fita batun Anwar ki tsira da mutuncin ki nifa nake gane Miki Yanzu irin wannan cin mutuncin keda dadi?
Ta goge kwallan da suka zubo ko Zan kyale Anwar sai na Rama wulakancin da ta mun wallahi bata Sha lale ba..... Ai kuwa next ba ita ce zata nada Miki duka ba wadannan kattin da ke gadin ta..... Ku duk baku San abinda naji ba, wallahi Anwar fa shine *Hamza bushara* ...... Duk suka kwalalo idanu suna kallonta. Da gaske Asma'u?
Tayi murmushi wallahi kuwa, aini tuni na Fara sensing Anwar wani shege ne ko Kuma baban sa ne wani don gadarar gayen tayi yawa ko lecturers Kuna ganin shakkar sa sukeyi..... Mufeeda ta saki wani irin kuka irin shikenan ta shiga uku kawai..... Amina ta dafa kafadarta kiyi hakuri ba class din ki bane Anwar maganar gaskiya sai irin su Bilkisun saboda Kinga babanta wani me itama tsaye take.... Ba wani babanta wallahi ko Yar gidan malam shehu ce tunda Anwar na sonta shikenan.....Kuma idan Kun tuna zuwanta ance sun Sha fada sosai da ita dashi tun farko ta nuna Bata tsoronsa, ke kuwa mufeeda ke ce Kika bayar da kanki yaushe Zaki ringa bin namiji Kuma guy kamar Anwar kema ai kinsan kin siya ma kanki buhun wulaknci.
Tana kokarin parking Aisha sauko daga napep ta shigo da gudu...... Wai kin daki mufeeda?
Ta fada tana shessheka , ta fito motar, ta bi su mustapha ( body guard ) da harara tayi ciki tana fadin Aisha yarinyar nan Bata da tarbiyya Kuma duk laifin Anwar ne...Anwar Kuma? Shi meye nasa aciki?
Ta hayayyako Mata tafi karfinsa ne da bazai ce ta kyalesa ba? Me yasa sauran Yan matansa ke tsoronsa ita kadai ce zakakka????
Amma Yanzu kinji yanda ake Mata Allah ya Kara a school? Wallahi mufeeda ta shiga uku ko kunya ta isheta kinji labarin da ake yi kuwa?... Maryam ta kallesu ya akayi ne? Tana kwance falo suka shigo
Ta cire hijab ta fada bedroom dinta.... Aisha ta zauna...wallahi Bilkisu ta nakada ma mufeeda tsinannen duka har tana cire Mata hular gashi..ta karasa maganar tana kyalkyatar dariya.. Maryam ta tashi zaune bani in Sha.....
Hmm yarinyar nan ta debo ruwan dafa kanta Wai inba ita jakka ba waye zai shiga shirgin Anwar da Bilkisu soyayyar da kowa ji yake da kansa, soyayyar da sukeyi ma juna ta gadara wa ita ta shiga tsakani????
....ta danyi kasa da murya Wai kinsan an daura musu Aure Ashe?
Maryam ta zaro ido.... Tayi saurin Dora yatsa a lebe alamar tayi shiru....
Haba nidai wallahi nayi mamaki abun fa akwai alamar tambaya.... Kuma kin San waye Anwar?
Ta zaro ido tana girgiza Kai alamar a'a.... *Hamza bushara*..... Ta kwalalo ido ta dafe kirji..kice wallahi.
Tayi Yar dariya wallahi kuwa ta budo Mata waya duba ki gani... A nuna Mata. Ta Kara zaro ido... Bilkisu ta sani?
Tayi dariya wallahi ta sani yarinyar can hmmm kibar ta kawai..... *Bushara* Maryam ta maimaita... Yanzu Bushara takeyi ma wannan iskancin Aisha..... Aisha ta kama dariya fitowarta yasa duk sukayi shiru....
Ta zauna bisa kujera Maryam kinyi break?
Eh, ta fada a darare....
Aisha tace naji ana Kiran wayar ki kuwa.... Ta janyo jakar sai kawai tayi tsoki ta wurgar.... Bazaki dauka ba?
Kyaleshi Anwar ne..... Maryam ta zaro ido..
Aisha tace me yasa bazaki dauka ba?
Me zance mishi?
Duk wannan hatsaniyar waye ya janyota?...... Meye laifin sa Bilkisu?
Ta Sha mur, Aisha har Yanzu Ina mamakin me yasa yarinyar nan ta kasa rabuwa dashi?
Kina ganin ba laifinsa bane??
Ba laifin sa bane..... Ta Mike tare da buga tsoki tayi kitchen......yunwa nakeji Maryam Ina masu aikin?
Maryam ta kalli Aisha itama ta kalleta Aisha ta kyalkyace da dariya Maryam kuwa kasa darawa tayi. Ta rike Baki *Bushara*..... Kut!
Ya kalli sadeeq nifa wannan fitinar yasa naso na mayar da ita Abuja kaga Yanzu da alama ni ne nayi laifi.... Sadeeq yayi murmushi ai dole taji haushin ka mufeeda ta kasa kyaleka itama tana nuna bata tsoronka kaga kuwa Bilkisu Dole ta tuhumeka....
... sadeeq ya zanyi da yarinyar Nan? Wulakancin duniya wane ke ban Mata ba?.... Duk da Haka ya kamata kayi wani Abu da zata kyaleka... Kamar ya? Dukanta zanyi?
Zagi na gidan duniya na Mata amma Bata da zuciya domin Allah meye laifina?
Ka barta zuwa anjima kilan ta dauka..... Bilkisun? Tabbb, yarinyar nan wuyar lallashi gareta Yanzu kaga Ni ta janyo mun jidali shegiya.... Sadeeq ya kwashe da dariya....
Soyayyar ku na birgeni nawan.... Ya Kai mishi duka wane birgewa Dan ubanka ana ba juna wahala....Au Ashe Kai ma ka San Haka... Sadeeq ko zaka je ka bata hakuri ?
Eh, Amma Bari ayi sallah tukun.... Wai mu Dan ubanka baka kawo Mana masu girki ba?
... ....... Ba wani Mai girki da Zan kawo, Ni nafi son ta dafa mun.... To ka kirata a waya ko ka Mata text.... Bari dai ta huce.
Ya harareshi to ai kaga irin wannan ranar da aka kafsa fada mune Masha wuya ko?....
Ya Mike Bari na dafa indomie.... Please zanci.... Baka cinta Dan ubanka..ya wuce Yana banka mishi harara.
Sadeeq yasha tsayuwar Shi taki fitowa, inda Allah ya taimakeshi suna da lecture four.......
Tana fitowa ta Kira mustapha.. kuyi wa Allah basai Kun bini ba Allah Yana tare Dani, bana bukatar tsaronku don kuwa bana wasa da addu'a...
Ya danyi murmushi toh Hajiya,....tana fita suka rufa Mata baya.....
Yana tsaye bakin kofa, ko kallonsa batayi ba ta wuce tana Zama shima ya zauna.... Ajin yayi tsit kowa ya maida hankalin sa wurin su don kuwa basa gajiya da dramar su. ....
Wai fushin na menene Bilkisu?
Ta harareshi kawai.
Yayi murmushi ke me yasa kin na son dauran laifi babu gaira?...... Au Ashe ma baka da laifi ko?
Me yasa har yau mufeeda ta kasa kyaleka, saboda me baka son ta daina kulaka????
Ya daga hannuwa sama na rantse da Allah Ina so ta kyaleni Bilkisu baki ganin irin wulakancin da nake ma yarinyar can Amma taki zuwa???..... Kuma shine ke nuna tafi karfinka?
..... Zaiyi magana malamin ya shigo.....
Ya dauko wayarsa ya rubuta Mata text a WhatsApp...
```kiyi hakuri please```
Ya Dan zunguro ta galla mishi harara ya Mata nuni da baki cewar ta duba Wayarta......
Ta tura mishi da harara....
Ya rubuta ``` please sorry I don't want to see you pissed off```
Taki magana.
Ya Kara rubuta Mata..
```You snubbed your husband?``` tare da imoji na zare ido.
Ta Kara tura mishi harara
``` sai ya tura Mata kuka```
Ta Dan kalleshi ya langwabar da Kai ya rubuta... ``` wallahi Zan yi maganin ta please am sorry```
Ta danyi shiru sai ta rubuta mishi ``` it's okay```
Yayi saurin tura Mata ``` Oya smile na```
Ta Dan kalleshi ya sakar Mata murmushi... Sai kawai ta duke tana Yar dariya.
Malamin na fita ya hawo table ya zauna gabanta Yana Yar dariya *Mun shirya ko?*
Ta danyi murmushi.
Sai ki koyan abinda akayi tunda kin Hana ni naji komai... Ta harare Shi Nima halan naji?
Ya kyalkyace da dariya gaskiya wannan semester din akwai damuwa Anya Zaki Bari na ringa ganewa?
Ta Kara mishi harara...
Kun shirya ko? Ni an kyaleni cikin Rana daga Biko ya kalli Anwar Dan ubanka ka Kara Sanya ni cikin shirginku sai naci ubanka..... Tayi kasa da Kai tana murmushi Shi Kuma ya Kama dariya.
Suleiman yazo zai wuce Anwar yayi saurin rikoshi ranka ya dade idan ba hello ai akwai daga hannu ko?
Ya danyi murmushi ya Mika mishi hannu ya kalli Bilkisu, Hajia Allah yasa Allkhairi... Amin Suleiman Dan Allah ara mana abinda akayi Yanzu idan ka rubuta..... Anwar yayi fit ya fizge littafin ni zaka ba Alhaji ba ita ba.
Yabar masu book din ya wuce Yana Yar dariya....
Anwar kenan, yau kuma Suleiman kakeyi wa magana????
Ya Dan Sosa Kai gayen Yana bani tausayi wallahi duk wulakancin da na mishi a masallaci idan muka fito wallahi sai ya bani hannu.... Ta ce hmmm.
Ya dan harareta ba hakan Yana nufin fa Zaki ringa kulashi ba fa..... Amma ai ma gaisa ko?
Eh, Amma idan kin saka nikaf, Wai yau me ya hana ki Sanya? Ya zaro ido......
Ta langabe Kai kamar zata mishi kuka Anwar Dan Allah ka saukaka mun da nikaf...... Wallahi sai kin saka ya dire Yana masifa...kammm idan Kika Kara fitowa babu nikaf wallahi sai kin koma Koda kuwa za ayi test ko exam..... Shikenan naji ta fada tana zumburo Baki.
Muje ki ajiyeni gida...
Wai Kai duk motocin da na gani gidanku fa.... Yayi murmushi kawai.
Ta haraeshi Wai Kai an fada ma har Yanzu ba'asan waye Kai ba?
Ya watsa hannuwa tare da daga kafada.... Ta danyi dariya tana son wannan move din....
Ungo kaja mu toh,
Yayi gaba abinsa bai ko kalleta ba.......
Ta bude suka shiga ta bata wuta.... Duk aka bisu da ido..... Ba karamin tafiya sukeyi da zukatan dalibai da malamai ba, ya kalleta Yana dariya waya koya Miki mota haka?
Ta mishi banza, ya kwantar da sit ya Dora kafa bisa dash board yayi filo da hannuwansa kinji kunya ta Hana mufeeda shigowa school?
Ta galla mishi harara sai kaje ka shigo da ita ai..... Ya runtse ido Yana dariya.
Taci gaba da hararar sa tana magana watau Kai hankalin ka na gunta kana bin kwaf kwaf.... Ke rufan asiri ya tashi da sauri wallahi da wasa nakeyi zolayace..... Hey nawaoooo....
Ta kawar da Kai kawai .
Ya canza maganar da cewa, me Zaki dafa mun yau?
Ta yi shiru.
Kinji?
Har abinci Zan maka?
Eh Mana, kiyi mun tuwo please kinzo da manshanu?
Ta ce um.
Amma anan zanzo inci kinji ko?
Ta kalleshi da sauri yayi Yar dariya ko ke Zaki kawon gidana na jiraki?......... Taci wani uban birki ji kake kuuuuuuu....😄✍🏼
*Zainab wowo mamar Abdallah*💖💖
*YOU ARE THE BEST AMONG BESTEST, ALAWIYYA NASIR*💞
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣7⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
👉🏼💗💕 *Mz na nufin moza ( mother) watau ( Salamatu Dahiru ) wannan page din duka naki ne Allah ya bar mun me MZ ana mugun tare*🤝🏼 ```Aminatu na godiya kina qalbinta```
**************
*Federal University dutsinma*
Ya wuntsula ya Mike da sauri keeee kina hauka ne Zaki kifar damu, ki rufa mun asiri Ina son ganin Yan dagwai dagwai.... Ta galla mishi harara sauka munzo... Ya duba da sauri yaga an wangame get, zuwan keda wannan burkin ko kuwa kawon abincin?
Kinji?
Kazo kaci gidana..... Zaki zo ki daukeni?
In daukeka fa kace, Wai meye amfanin motocin can? Ta nuna da yatsa yayi murmushi kunyar hawan su nake Allah... Ta danyi dariya kunya?
Eh wallahi sai nake ga kamar kowa zai ringa kallona...
Sai Ni rasa kunya ka sa nake hawan Wagga?
Ya kyalkyace da dariya to ai ku Daman Mata da kyale kyale aka sanku duk neman da mukeyi suwa muke kaiwa kudin? Ko bakiji ance Mana *Bayin Mata muke?*
..... Nidai naji sauka ...kina korata?
A'a Ina dai son naje nayi tuwon ko?
Zaki zo ki daukon please?
Dan Allah Anwar kazo da kanka.... Ya bude motar fine... Zanzo bye take care ya shige .
Tayi Yar dariya kawai ta tafi.
Karfe takwas yazo shida sadeeq gidan falo biyu ne na farko da na can ciki, bai tsaya komai ba ya wuce ciki abinsa... Sadeeq Kuma ya zauna na farkon shida su Aisha.
Riga da skirt ne jikinta sun kamata, ta zumbula hijab ta wuce da abincin a tray.
Sai kace muna a gida, ji yanda ka dararrashe... Yayi murmushi kawai.
Ta zuba mishi komai ta mike.... Ina zakije?
Ke wace irin bagidajiya ce Yar kauye? Haka are serving Mai gida???
Ta galla mishi harara, ya ce, naji dai Amma zauna ki cire wannan hijab din..... Ta zaro ido to Bari na dauko kallabi ko gyale..... Ya ajiye chokali ya kalleta fuska daure.... Ina son ba daddy mamaki Amma da alama wannan gardamar taki zata janyo Miki.... Tayi saurin cire hijab din gashin ta ya warwaro bisa bayanta warrrrrr ya sauka....yabi gashin da kallon ya hadiye tuwo ba shiri Amma duk da Haka bai saki fuska ba....
Ta yi tsumu kunya ta baibayeta, musamman da ta lura Yana yawan kallon kirjinta. Kayan sun matseta duk ta takura.
Ba tare da ya kalleta ba ya ce ```Kinsan kina da kyau Bilkisu?```
Gabanta ya bada ras!
Jin tayi shiru yasa Shi kallon ta yace kinji??
Ta Kara yin shiru....wannan kalmar ta kinji idan ya fada tana Jin kamar ta gantsara mishi cizo....
Bazaki amsa ni ba?
Ya kafa Mata ido, ta danyi murmushi tana Kara sunne kanta sai murza hannu takeyi kamar Mai yin alwala....
Yayi murmushi,kina da kyau Bilkisu Ina son structure dinki ... Tsikar jikinta ta bada wani Yarrrr.....
Ya ajiye chokali tuwon yamun dadi akwai Wanda zakiyi mun dumame da safe?
Um, ta ce a hankali.
Amma kamar generator dinku bashi da karfi ko? Naji AC din Bata tafiya da kyau ko kuwa fault din nata ne?
Huh?? Ya ce Yana kallonta...
Kila, ta fada ahankali... Wai kin takura ne?
A'a ta fada tana sunne Kai.
Bana son wannan ruwan daukon wasu marassa sanyi a can...ya nuna karamin fridge... Ta Mike ya bita da kallo, Koda ta juyo yayi saurin kawar da Kai kamar Yana latsa waya..... Ta mika mishi ya hada da hannun da ruwan ya fizgota , ta fada jikin sa zata kurma ihu ya toshe Mata Baki..... Kina ihu su sadeeq zasuce ga Bilkisu can ana harka...ya fada Yana Yar dariya.
Ta runtse ido jikinta ya Fara kyarma.... Dan Allah kayi hakuri..... Wayyo na shiga uku...
Wannan kunyar taki ke tunzurani kinki sakin jiki dani..... Dan Allah Zan saki sakeni ka gani.... Ya zagayo da hannayen sa ta gaba ya harde su daidai kirjinta ya soko kansa ta wuyanta Yana Mata Rada..... Ke nifa ba dutse bane ko katako.... Ta runtse ido wayyo na shiga uku Dan girman Allah ka sakeni.
Zan sakeki Amma wallahi Kika motsa kinji na rantse yau ba me kwatarki.... Naji Zan tsaya please na tuba. .... Ya cire hannuwansa ... Ta saki ajiyar zuciya kanta kasa sai kyarma takeyi duk ta tsorata....
Kyarmar ta mecece ya riko hannunta..... Dan Allah kayi hakuri..ta fada kamar zatayi kuka.... Ya Kara rungumota Dan Allah ki jira....Anwar kace zaka ba daddy mamaki fa.... Eh na sani. Ya fada kasa kasa .
Dan Allah ka sakeni.... Ke wallahi bazan iya ba, Dole na ringa taba ki don ki Saba kunyar Nan tayi yawa....ke Yanzu na say Miki ido kawai ba Dan romance ai Kya ce bani lafiya...... Wayyo ni Bilkisu na shiga uku...ta fada a hargitse .
Ya shafa gashinta.... Ina son gashinki .... Jikin ta ya bada tsammmmm....ta runtse ido.
Dan Allah kizo muje gidana ki kwana.... Sai kawai ta rushe da kuka.... Ke wasa nakeyi yi shiru.... Ya saketa Yana dariya... Jikinta sai kyarma yakeyi.... Ta goge hawayen ya bita da ido.... Haka kike da tsoro?
Ta hada Kai da guywa kawai....
Ya Mike shikenan tashi ki saka hijab muje ki rakani ...ya dauko hijab din a hannunsa.
Ta Mike .... Wallahi ko kiyi shiru ko na tafi da ke ... Tayi saurin goge kwallan, yayi murmushi matso na Sanya Miki hijab din... Ta matsa ya rungumota..... Dan Allah ki Dan ban minti biyu .... Ta sunne jikinsa ta Kara sakin kuka.... Ya buga tsoki... Kedai wallahi akwai ruwa ruwa...
Aure Dadi gareshi ki kwantar da hankalin ki mu.... Ta Kara sunne Kai ..ya kyalkyace da dariya to sakeni shikenan ba abinda zamuyi.
Ya saketa a hankali, Ya koma ya zauna bisa kujera ya zuki iska ya fesar tare da fadin ohhh my God.
Tayi tsaye har lokacin Bata daina kyarma ba ya fizgota ta fada jikinsa Yana fadin idan Baki saki jiki ba Allah yau sai dai mu kwana anan.... Ta sunne jikinsa, kokarin dagota yakeyi taki yarda.... Yayi dariya to ki daga ni na tashi ko?
Ta kasa dagowa.....wallahi Zan birkitar dake... Ta Mike da sauri ya riko hannunta tare da mikewa ya janyo bayanta ya kwanto samanta kansa bisa kafadar ta Yana magana cikin Rada Rada.... Bilkisu Ina Jin tsoro fa Anya Zan iya ba daddy mamaki wallahi duk kin rikitani.... Nidai Dan Allah kayi hakuri Anwar na tuba..... To ki jiyo in Baki kiss...... Ta zame ta zukunna tare da kankame jikinta tana fadin wayyo.... Ya Dan zukunna shima.... Wallahi kiss kawai zanyi please....nidai Dan Allah ka rufa man asiri....
Yayi Yar dariya okay naji tashi na tambayeki... Ta Mike da sauri ya matso ta matsa baya... Ya kalleta ya da matsawa?
Ta zumburo baki kayi tambayar inaji.... Ya nufota ta ringa baya baya... Bata Ankara ba taji ta daki bango ta kankame jikinta.... Ya tsaya gabanta ya harde hannuwa ya goya su a kirji tare da kura Mata ido duk sun kankance.....
An taba kissing dinki?
Jikinta ya bata tsammm..... Kinji? Ya fada.
Bazakiyi magana ba?
Wallahi ban taba ba..... Hada wallahi?
Wallahi tallahi ta fada kamar zatayi kuka...
Kina so kiji yanda akeyi?
A'a Dan Allah kayi hakuri.. .... Me yasa bakya so?
Tsikar jikinta ta Kara bada Yarrrr.....kinji?
Hakanan...
Ya sunkuyo daidai fuskarta tare da dafe bangon da hannu yace ki shirya anytime from now Zaki ji yanda akeyi.
Ya tallabota yasa Mata hijab ya figi hannunta suka fito....
Sadeeq shida Aisha kadai a Falon Maryam tayi ciki abinta..... Ta kalleshi idan ka Gama muna waje.....
Kanta a kasa ta kasa dagowa ta sanyata jikin mota ya matso kusa da ita sosai kamar zasu hada jiki ya Fara Mata magana a hankali.... Ina so ki sani ni ba katako bane,in shaa Allah bazan kasa ba daddy mamaki ba Amma da sharadin sai kin daina wannan kunyar kin sakemun jikinki..... Ta runtse ido ya sunkuya Yana lekenta..... Wannan kunyar taki wallahi tana Sanya mun sha'awar ki Bilkisu tabbas idan Baki saki jiki Dani ba to I have no choice but to sleep with you..... Ta juya ta kife Kai ga mota *na shiga uku ni Bilkisu*..... Ya juyo da ita, matsalar bani da kunya ko a gaban waye Zan iya taba ki don haka kina da aiki ja don duk ranar da na bukaci taba ki Kika Hana kamar yau to ki sani Zan...... Anwar please.... Ta fada tare da runtse ido. Ya kyalkyace da dariya... Sadeeq ne ya fito Shi kadai ba Aisha .... Ya kallesu to pigeon muje ko?
..... Sadeeq yarinyar nan ta fiye kunya fa tana takurani da yawa...
Tayi sukutiiiii, Sade yayi murmushi Bilkisu ya da kunyar miji Kuma?
Ya zagaya ya shige mota.....Yana fadin kasan baka Gama ba ka fiddoni..?
Ya kalleta sadeeq bai gaji ba ko mu koma?.... A'a kuje Dan Allah...ya Kyalkyace da dariya matsoraciya kizo mun da dumamen school gobe zanci a mota kinji ko?
Ta Dan saki ajiyar zuciya ta ce toh.
Ya langwabar da Kai Bilkisu bana son tafiya wallahi.... Ta ce ya Salam! Amma a zuci...
Zan say kawo Miki irin pad din kamfanina kiyi amfani da ita ance tana da kyau sosai idan Bata Miki ba Kinga Dole a canza sabuwa..
Ta mishi banza.
Yayi murmushi kinji?
Um, ta ce.
Ko Zaki bini..
Ta ingijeshi ta kwala. da gudu ya tuntsure da dariya ya fada mota...... Sadeeq anya Zan iya zuba ma yarinyar can ido?
Ka rufa Mata asiri Dan Allah... Ya fada Yana Yar dariya.
Amma fa tana da tarbiyya sosai could you imagine ta tsorata simply don na yi hugging dinta?
.....wallahi Anwar Bilkisu na bani mamaki ta fita daban daga cikin Mata maganar gaskiya wannan lokacin kafin ka sami yarinya Mai kamun Kai irin ta Yana da wahala kasan abinda ke bani mamaki?
Ya girgiza Kai..
Yanda she's fully hijabite wallahi kaga fa tun zuwan ta school din nan Bata taba Sanya gyale ba Bata shigar banza ga addini sallah Bata wuce ta cikin jam'i naji ana rade radin ita za a ba Amira....
Ya danyi murmushi, wallahi har tausayi ta bani Yanzu duk jikinta ya tsinke da rawa sadeeq ta tsorata da nace zanyi kissing din ta wallahi hada kuka....
Ya kyalkyace da dariya ya ce baiwar Allah.
Sai ka lallaba ta ka Kara daurewa kada ka janyo ma kanka jangwam ta rikice maka Kuma...... Naga alama fa akwai rikici .
Kasan Aisha ta nuna tana da interest akaina?
Ya kalleshi haba???
Ya Dan Bata rai, no Bata mun ba, Ina son mace mai Jan aji nafi so na Sami mace wacce Ni ke binta tana ban wahala ba ita ce zata ringa zakewa ba..... Kamar Bilkisu kenan? Ya katseshi Yana dariya... Yayi murmushi Anya Zan Sami kamar ta at least ma ko wacce bata kaita ba.. da tana da kanwa ko Yar shekara biyar ce Allah da Zan jira..
Suka kyalkyace da dariya.
Ya zuki iska ya fesar.... Gaskiya Ina bukatar matata .....ka rufa mata asiri Anwar Dan Allah kaifa da kanka kace zaka bada mamaki...... Kai nifa ba katako bane ko?.
Eh,but at least ka duba yanayin idan ta Sami ciki fa?
Shine me? Ya harareshi, Ina nufin kaga na farko tun a laulayi idan Mai Shan wahala ce an Sami matsala musamman ga karatunta, kaga automatic spill over, na biyu bazata taba fita zargin mahaifan ta ba cewar ita ta sanar da Kai akwai Aure bayan an gargadeta da tayi shiru,na uku karatu da goyo Anwar is not easy akalla.... enough jor.... Ya daga mishi hannu... Amma Zan ringa Dan romancing dinta gaskiya ban iya daurewa..... Romance din zai ringa Sanya maka sha'awa akwai ranar da wallahi zaka kasa controlling kanka tunda kamar yanda ka fada din Kai ba katako bane...... Ya Allah !!! ya fada tare da maida Kai ya kwantar bisa sit, sadeeq meye dabara?
Ina ga mu rage ziyarar su gida , ka ringa tsareta school duk maganar da zakuyi nasan idan kana ganin jama'a bama zaka kawo komai a ranka ba..... Nawaoooo,!!! Ya fada tare da tashi zaune.. gaskiya nidai an kwareni ....
Sadeeq ya kyalkyace da dariya rawar kanka ta janyo maka....... Ya Kai mishi duka, naje nayi.
Yanzu dai ai daga wannan semester din saura daya ko?
Biyu dai....
Ya katseshi ...ya ja dogon tsoki kawai ya kwanta tare da runtse ido. Sadeeq ya bishi da kallo Yana murmushi......
Wai ya mufeeda ta hakura ko?
Ya yatsuna fuska, ance har yau ta kasa shigowa school saboda kunya..... Maganin ta kenan... Ya tashi zaune Yana Yar dariya kasan ni duk wake bani dariya?
Ya ce sai ka fada.
Helen, tunda akayi case din nan Yanzu ko layin da nake zaune Bata bi kasan arna da shegen tsoro....... Suka kyalkyace da dariya.
Bilkisu ta zabga uban tagumi har lokacin jikin ta bai daina rawa ba, kirjinta kuwa sai dakan uku uku yakeyi, *Na shiga uku ni Bilkisu Wai kiss* .... Nikam dama na hakura da Abujan da Yanzu Ina can zamana qalau..
Ta runtse ido lokacin data tuna ya zagayo da hannayen sa bisa kirjinta ya kwanto jikin ta...... Tsikar jikinta tashi Yarrrr lallai akwai damuwa .... Ta bude ido su maza basa da kunya ko kadan....
Haka ta kwanta tana ta juye juye da ta tuno Shi da yanda ya ringa Mata sai ta kudundune jikinta ta boye kanta cikin filo.....
Murjanatu cikin masu aikin gidan ta Kira da sauri ta ce maza ta dumama tuwon jiyan kafin ta fito wanka.....
Yau taga amfanin nikaf, saboda da Babu ita tasan bazata iya kallon Anwar ba.....
Tana shiga ajin anata raba test din da Richard munafuki yayi. Two over ten, three mutum biyu keda 5 su chinayye...... Itama two taci, Anwar ya saka tashi aljihu kawai lokacin da ya buda yaga yaci nine....
Ya kame Baki na shiga uku.... Mutumen nan wallahi mugu ne daman yafi so mu fadi.... Sadeeq na bayanta ya ce nawa Kika ci Bilkisu?
Ta mika mishi 2 ce shegen kaifa? Yayi murmushi three..... Anwar yayi fit ya fizge takardar ya na zagayo ya kalli root dake kusa da ita yace ban wuri.... Ta kwashi takardun ta ta koma sit din da ya taso.... Basai ka fizge ba two ce kai nasan nine kaci don ma baya bada cikon da tabbas ten zaka ci....... Inji waye ya fada Yana murmushi....ta zumburo Baki nidai fiddo naga Ni...... Ya Mika Mata Yana murmushi.... Kamar jira ake taje hannun Bilkisu aka Fara rokonta ta bada ayi snapping.... Ta Mika musu.
Mutumen can na daga mun hankali bana kaunar Dan iska.... Yayi dariya Kuma duk da Haka Baki taba faduwa course dinsa ba ko?
Ta harareshi Amma da yake akwai nikaf bai gani ba tace da hawan jini, da na ruwa ko?,ya kyalkyace da dariya, toh eh Mana,duk sai ya gama tayar Mana da hankali tukun Kuma *E* din nan dai ce ko *D* ..... Ina laifi ai yafi carry over ko?...... Zatayi magana malamin ya shigo..... Ya fiddo waya ya dan Mata magana a hankali..... Shiga WhatsApp...
```kinyi barci jiya?```
Ta maida mishi da ```me zai hana?```
```ni kuwa kasawa nayi saboda tunanin ki```
Ta kasa cewa komai
```kinji```
Ta ce ```Hmmm```
```smiles kin zo mun da tuwon?```
```yana mota```
```ina zamuje naci```?
```ina fa, anan waje ko?```
```Bana son waje is too open let's go to the field or new lecture rooms side I need quite place okay?```
Tayi shiru.
``` kinji ko?```
Ta maida hankali gun lecture.... Ya zunguro ta da hannu ....dole ta rubuta mishi
```naji```
Yayi murmushi.
``` sai Anja mun aji?```
```Ka bar mu muji lecture Anwar```
.....```ke ni ban wani ganewa ki Bari kawai zamuyi tutorial```
```Hmmm```
Malamin na lura dasu,
Yana gamawa ya ce tear a sheet of paper write your number only......
*Mun shiga uku ka ga abinda nake gudu ko?*
Ya sumke Yana Mata dariya.
Kina da black biro?.....
Banda Shi ta fada cikin tsiwa.
To kiyi sauri ki wanka ko na rubuta miki,?
Kawai kayi na kwafa idan Kuma ya tayar Dani shikenan.....
Yayi murmushi....
Ya Fara dictating questions based on what he discussed.
Ta Kara tsure Mata tana magana kasa kasa ... Wallahi kana ja mun wannan semester din..... Yayi shiru Yana murmushi Yana rubutu.
Tana kokarin Jan layi ya turo Mata takarda har ya Gama Daman two questions ne. Ya ci gaba da rubuta nashi Yana layin karshe kawai malamin ya ce hands up...... Amma sai da ya karasa Kai Anwar karshe ne......ta galla mishi harara cewa zakayi kasan abinda ka taka, yayi dariya to meye acikin nan cubweb theory din ke da wahala?
Ta ce hmm, duk ya Gama birgeta, gunguni kawai ke tashi cikin ajin.
Yana zuwa layin ya karba ya dan harari Anwar din ya wuce ....
Yana fita sadeeq ya taso kaga mutumen Nan ko?
Yayi murmushi bana fada ma ba, gaskiya naji dadin bayanin jiya... Ta kalleshi da sauri au Daman kunyi wannan din?
Sadeeq ya ce wallahi jiya kamar wasa ya koyan Kinga da yau naci kaniya ta...... Ta ce hmmm kawai,
Anwar ya kalleta kema yau zamu Fara karatu kiyi hakuri..... Na fito karfe hudu kenan?
A'a ki Bari sai after Isha zanzo gidan....
Gabanta ya Fadi, na marecen nake ga zaifi ko kuwa?
No!, Bana son yawan fita inba lecture akeyi ba, kawai ki jira zanzo kinji ko?
Toh, ta ce a hankali.
Ya Mike muje....
Ka Kira sadeeq muje yaci..... Zan rage mishi ..
Anwar meye Haka? Wasa tare ci banban.... Ya danyi dariya yarinya kawai kice kina son wani kusa kada muje na cinyeki Ni kadai.... Laaaa ni ba Haka nake nufi ba..... Sadeeq!!! Ya kwala mishi Kira....
Ya karaso Yana murmushi ya akayi?
Tuwo aka kawon Wai bazan ci ni kadai ba sai tare da Kai... Yawwa Bilkisu Allah dai ya biya kin San kuwa yunwa nakeji wallahi.... Ya banka mishi harara Kuma Kai baka wuce tayi ko?
Ban wucewa kin ganshi Nan ko ruwan zafi bai iya dafawa .... Duk suka kwashe da dariya.
Ina zamuci tuwon?
Field... Anwar ya bashi amsa.
Okay kuyi gaba Zan biyo ku da mashin.
Ungo nidai kaja motar Dan Allah..... Ya wurga mata harara ya fada gaba ya zauna kawai.
Dole ta shiga ta ja motar a hankali.... Duk inda suka gitta sai an bisu da kallo.. ba karamin kashe zuciyoyi sukeyi ba a school din suna bada *Plus*
Sadeeq na gama ci yabar wurin yace zaije aski.
....me Zaki dafa mun da dare?
Abinda kake so, ta fada..... Ke daga nikaf din nan na ringa ganin idonki.... Ya karasa maganar Yana yakice Shi .... Ta yi kasa da Kai tana murmushi..... Ya shafa gefen fuskar ta Yana fadin ```lemme see this baby face``` ... Ta to dariya ta ce kaiiiiiii.....
Yes, ya fada Yana Kara kallonta,
Me Zaki dafan?
Abinda kake so, ta Kara maimaitawa.
Kiyi mun chips mana.
Toh, ta fada a hankali.
Babban fridge din nan Kinga akwai kaji da naman rago da kawuna ko?
Um, ta ce.
Idan kina bukatar kifi kiyi mun magana a kawo Miki Shi kinsan baya da dadin ajiya saboda karni ko?
Gaskiya fa.
Me yasa baki taba rokona wani Abu ba?
Ta kyalkyace da dariya kaiii Anwar... Yabi fuskar da kallo..... Yana murmushi.
```Bilkisu kin San cewa ke din ta daban ce kuwa?```
Na sani Mana... Ta fada tana murmushi.
Ya akayi kika sani.....
Tayi dariya saboda *Bushara na Sona*..... Ya kyalkyace da dariya for the first time kin kirani *Bushara* Dole na Miki kyauta yau Zan canza Miki motar Nan...... Dan Allah ka barta Ina sonta....... Karki damu ai ba rokona kikai ba, Ina son ki bar tarihi FUDMA a ringa kwatancen mu..
.. Yanzu ma anayi.
In tambayeki???
Ta ce um,
Yaushe Kika Fara Jin kina Sona?
Ta yi kasa da Kai tana dariya.....
Kunya kike ji?
Ta Kara murmusawa..... Okay rubuta mun ta WhatsApp..... Ka Bari Zan fada maka..... Yaushe?.
Tayi shiru tana murmushi.
Kunyar ki tayi yawa Bilkisu....
Muje ki ajiyeni gida .
Ta tayar da mota,
Har ciki ta shiga yau, ya ki fita ya tsareta da ido sai kuma ya ce affff.... Ki jirani Ina zuwa please ya shiga gidan da gudu.....
Ta bishi da kallo tare da sakin ajiyar zuciya a hankali....
Ya dawo dauke da Yar leda Mai kyau a hannunsa, ya leko ta taga, it might be Baki zo da English wears ba ko?
Kisa wannan anjima.... Ta zaro ido...
Ya Kara sunkuyawa ba abinda Zan Miki Allah kuwa kawai Ina son ganinki cikin su matsala daya za a Samu idan kika Fara wannan kunyar taki lallai Zaki janyo ma kanki na taba ki.... Ban Baki a boye ba, just wear it and feel free okay????
Ta daga Kai a hankali.... Yayi murmushi that's my babe...... Tayi baya da motar ta fita a hankali duk jikinta yayi sanyi duk da bata ga kalar kayan ba.....
Yabi motar Yana murmushi... Ya ce tsoron ta yayi yawa gaskiya. Ya zuki iska ya fesar ya wuce ciki.
Ta zabga uban tagumi daki ita kadai ta zuba ma kayan ido, doguwar riga ce Mai kame jiki da hannun vest, daga kasa akwai tsaga har kusan guywa maroon ce Dana da wani katon belt bisa kugu, da jefi jefin flowers jikin rigar red. Aisha ta taimaka Mata sukayi farfesun kaji, sannan suka soya chips din kaskon karshe ta shiga tayo wanka tabar Aisha ta karasa ta feshe jikin ta da turaruka masu kamshi ta gyara gashinta Amma ta mishi gammo ta nade tare da zumbula katuwar hijab.... Tana fitowa taci karo da Aisha bakin kofa zata shigo ....Wai duk meye kikeyi haka ga Anwar can yazo.... Gabanta ya bada ras!.... Shida sadeeq ne?
A'a Shi kadai ne gaskiya... Kin saka ma coconut juice din ice ?
Eh Yana fridge muje na Kama Miki.... Barshi baya son haka, ta katse ta.
Yana zaune kasa ya Mike kafa Yana ta latsa waya sanye da farin boyel Mai laushi kansa ba hula.
Ta ajiye plate din chips din da cooler farfesun ta ce ... Ina wuni?
Ya Dan dago sai Shan kamshi yakeyi ya ce ... Bilkisu ya kike?... Na Sanya ki aiki ko?
Ba komi, ta fada tare da mikewa... Ya bita da kallo duk kamshin turarenta ya kashe Masa jiki.
Ta dawo da sauran kayan ta zuzzuba mishi Yana satar kallonta da wutsiyar ido, da tazo dagowa sai ya basar.
Tana gamawa ya tura Mata Wanda ta zuba mishi ya janyo sauran da ke cooler gaban Shi ya ce wallahi sai kin cinye duka Koda zakiyi amai.... Ta dago Kai da sauri ,.. ya hade girar sama da kasa yasha mur ...
Dole ta dage ta Fara ci sai da tafi Rabi yaga da gaske turawa takeyi sannan ya ce mikon dankalin na Kara bai isheni ba.... Ta tura mishi da sauri ya cinye... Peppé soup din Nan yayi dadi fa.
Jeki Kai kayan kizo da books din da zamuyi ba dadewa zanyi ba.....
Ta mike da sauri ya bita da kallo sai kawai yayi dariya.... Tana dawowa ya Kara hade fuska.... Kina jira na ce ki cire hijab din????
A hankali tayi sama da ita.... Tsikar jikinsa ta bada Yarrrr, ya hadiye wani tsinkakken miyau sai kawai yayi kasa da Kai ya Fara budo littafin da ta Miko....
Tunda ya Fara bayani bai dago ba ..... Tun tana Jin kunya da tsoro har ta fahimci Sam ba ta ita yake ba gashi sai wani Shan mur yakeyi.....
Tana ganewa sama sama har sukayi course biyu.
Duk ta makure... Ya dago Kai kina ganewa kuwa?
Um, ta ce da sauri, saura kadan yayi dariya.
Yau barci nayi da Rana sosai...
Wai kin San cewa an gano nine Bushara school din Nan?
Ta danyi murmushi, nasan za a gane Kam...
Saboda me Kika ce haka?
To Anwar ko wadannan kattin da ke Bina da wadanda ke gidanka yaci asan Kai waye.... Ya danyi dariya inji waye kawai tsabar sa ido ne.
Naji class din mu za a yi jacket da shirt na graduation Ina ga ni Zan dauki dawainiya ko?
Ya dai kamata. Ta fada kanta kasa.
Yayi murmushi, Nima Ina son yiwa yaran Nan alheri me kike ga Zan raba musu?
Kudi, ta fada.
Kudi Kuma?
Eh, Mana kudi zaifi saboda kowa yasan meye damuwan sa Kuma kudi ke maganin komai ko kuwa?
Kuma fa, Shi yasa nake sonki wallahi saboda kina da hankali...kamar nawa Zan basu?
Yanda kayi niyya Kuma ai kafi kowa sanin iya karfin ka.
Ya kura Mata ido, ki fada mun Mana ai Yanzu shawara mukeyi nida ke ko?
Ka dai kiyasta Ni ban San nawa zance ba ko kayi shawara da sadeeq..... Da ke zanyi. Nawa kike ga ya Dace na raba masu?.
Tayi shiru... Ka Bari zanyi tunani toh.
Okay, sai na jiki tashi ki karon ruwan in Sha... Ta Mike ya bita da ido, kafin tazo kawai ya Mike kamar Mai neman wani abu,
Tana kokarin Miko mishi ya mameta ya kamo sai kawai taji ya hada bakin sa da nata, ta saki ruwan kasa..........✍🏼😄🙈
*Zainab wowo mamar Abdallah*💖
*Mz , mz, mz Ina nufin ( salamatu Dahiru ) Allah ya Kara zumunci mother kina Raina koda yaushe.*
*ALLAH YABARKI DA ALHAJI NURA NA'IMA AMADU SPEAKER YAN ADAWA BAKU IYAWA MUNE AMARYA KUMA UWARGIDA MUTU KA RABA IN SHAA ALLAH*💞💞💞
*Yauma page daya za'a samu Ina busy*
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣8⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano mam in huhan Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
```Bazan taba mantawa da ke ba Maryam Aliyu Yar adu'a ( M. Ali ) uwar Noor my in-law kina Raina Koda yaushe```
👉🏼💕 *Mz ( salamatu Dahiru ) Ina Kara godiya Allah ya Kara dalili my mother*
*****************
*Federal University dutsinma*
....... Tun tana iya motsawa har jikinta ya mutu murus, duk illahirin kafafuwanta rawa sukeyi suna neman gagara daukarta, Jin tayi lakwas yasa Shi juyawa da ita ya zauna bisa kujera ita Kuma tana bisa kafafun sa..... Yayi iya gumin sa ya taba inda yake so, karkarwa jikinta kawai keyi duk ta firgita..... Ya saki ajiyar zuciya ya janye bakin sa a hankali..... Sai kawai ta tusa kanta cikin kirjinsa ta saki kuka... Yayi shiruuuu...
Zuciyar sa na mishi sake sake, shin ya biya bukatar sa ko ya ba dady mamaki?
Da ya motsa sai ta rikeshi gamm ta Kara sakin kuka.... A hankali yake fitar da numfashi.... Sai kawai ta bashi tausayi lallai ya Kara tabbatar wa kansa da Bilkisu yarinya ce karama.... Tunda har ta kasa supporting kiss kuma hakan ya bashi tabbacin this is her first kiss.....
Tayi Mai isarta, har lokacin jikin ta rawa yakeyi..... Da ya motsa sai ta Kara rikeshi.... Ya danyi dariya.. ``` To ki sakeni na tashi ko?```
Tayi shiru,
```Bilkisu```
Ya Kira sunan ta a hankali,
.... Ta Kara fashewa da kuka ``` Dan Allah kayi hakuri```
..... Ya Kara dariya naji sakeni Dan Allah ai ba Kya so ko?
Ta daga Kai cikin jikin sa...
Okay Zan tashi na tafi sakeni....
Ta Dan sakeshi.... Yana motsawa ta koma da sauri .... Ya kyalkyace da dariya da ya gane ba tsoro kadai ke addabar ta ba hada kunya..... Ni Kuma yau tawa ta sameni ni *Hamza*...... Bazaki sakeni ba? To gyara mu yi kwanciyar mu anan.... Ta sakeshi da sauri tare da soke kai cikin kujera..... Ya Kara dariya.... Ba rakiya kenan?
Tayi shiru..... Ya kawo hannu ya taba ta, saki kuka tare da kankame jiki..... Ya Kara dariya ya ce tohm na siyo ma kaina rigima da kudina..... Ya zukunna gaban ta, Shikenan daina kukan Zan tafi Amma Dan Allah ki dauki waya idan na Kira matukar bakya son na maimaita kinji ko?...... Saura kadan ta wawuro fuskarsa ta cije don takaicin kalmar ```kinji ko```.
Ya saki ajiyar zuciya ya mike sai da safe I will miss you honestly..... Ya fita da sauri.
Tafi mintuna ashirin a wurin kafin ta tashi zaune.... Ta Dora hannu a Kai *Na shiga uku ni Bilkisu idan Haka ne halin Anwar na gama banuwa* Shi baya da kunya?
Ashe abinda nake karantawa da abinda malaman islamiya ke fada gaskiya ne?
Ta Mike jiri ya kwasheta, ta koma ta zauna.... Ikon Allah, ta kalli hannuwanta sai kakkarwa sukeyi, tsikar jikinta tashi Yarrrr tana tuno abubuwan da suka faru... Namiji???? Shi har wata dariya yakeyi... Ta zumburo baki tare da zabga uban tagumi.
Yana shiga sadeeq yaji kamshin turarensa ya canja gashi cikin wani yanayi na nishadi .... Ya bishi da kallo kawai Shi Kuma ya fada toilet ya sakar ma kansa shawa.......
Duk su Aisha sun shige sun kwanta, ta shige dakin itama Kai tsaye kewayen ta fada......
Ta na rungume da qur'ani kiransa ya shigo..... Taji wani dammmmm a kirji.
Ta dauka Amma samm ta kasa magana....
Kinyi wanka?
Tambayar ta bata haushi ta mishi banza.... Kinji?
Um, ta ce a hankali.
Kin kwanta ne Yanzu?
Tayi shiru......
Ya ce kinji?
Ta ce um,
Yayi murmushi, Baki ya mutu ne?
Tayi shiru.......
Ya ce huh?
Da kyar ta ce hmmm.
Ya danyi dariya.
Thank you so much Bilkisu, wallahi naji dadi sosai Zaki Sami Lada Mai tarin yawa kin San Haka?
Tayi shiru...kanta sunkuye kamar Yana kallonta wayar ma kunya take Bata.
Ya Kara dariya Wai Baki magana?... Ko muyi video call........ Nidai a'a..... Ya tuntsure da dariya to kiyi magana inji, kiss kawai ya rikitaki haka Ina ga..... Zan kwanta Dan Allah..... Ta fada kamar zatayi kuka ya kyalkyace da dariya..... Shikenan sleep tight sweetie.... Ta latse wayar da sauri kirjinta na bugawa ..... Ai shikenan Ni Kuma tawa ta sameni ta fada a hankali.
Ta Dade barci bai dauketa ba har kusan karfe uku da Rabi..... Shi yasa ta rasa lecture karfe bakwai don Bata tashi ba sai Tara saura.
....... Sadeeq ya kalleshi ya Bilkisu bata zo lecture ba?..... Ya danyi dariya kawai...
Ya bishi da kallon tuhuma.... Me ka Mata?.... Ya daga hannuwa yana dariya wallahi ban Mata komai ba kawai kiss ne ....... Ai nasan baka iya ba daddy mamaki Anwar Kuma yasan abinda ka je ya dawo Kan yarsa akanka yasa ya yanke wannan hukuncin...... Allah Ina iyawa.... Me yasa ka taba ta toh?
Ya galla mishi harara halan ni katako ne da Zan tsaya da Aure Ina kallon matata haka zikau ai ko Dan romance din a daga mun kafa ko?
.... Sanya ma Rai koshi ke kawo yunwa Anwar a haka, ahaka zaka je inda baka son zuwa Dan Allah Ina baka shawara ka tausaya ma yarinyar nan ka Bari akai maka ita...... Kuma duk ta tsorata jiya kaga yanda jikinta ke Bari?
Ai dole ta tsorata, bacin islamiya da sai ince anya tasan me ake ce ma Aure saboda yanayin yarinyar na bani mamaki...... Wallahi yarinya ce sadeeq nayi mamaki jiya ta kasa daukar kiss...... Mtseww ai ka yi sauri...
Shin Zan kiyaye ai dai na Dana.... Ya mishi gwalo... Ai Kuma ka Dano ma kanka ko? don na tabbatar Yanzu ka siyo rigima da kudin ka..... Wallahi
kuwa, ko agabanta na fada jiya..... Amma fa na kashe bakin rigima Zan Sami sauki saboda ta tsorata da Ni...... Ya ce hmm.
Yaki zuwa gidan ranar ta kashe wayar ta...
Ta ce ma su Aisha zatayi karatu ne daki Koda sun jita shiru.
Kwana daya , biyu har uku Bata shiga school ba. Taki kunna waya kuma.
Hankalin sa ya Fara tashi, ya Sami sadeeq ya fada mishi suna tare da Anas ya Dan kebe shi.
... Yarinyar nan fa taki kunna waya kaga kuma Bata zuwa class.. nasan za a rina Anwar ai ka Mata shigar kutse da ka bari da Yan dabaru da hikima sai ka shawo kanta amma Haka zikau ai Dole ta firgita..... Ya kamata ka fahimceni ya zaka biye Mata ka dauki taking side.... Ya fada a hasale... Na sani amma Ina kwatanta maka ne...... Naji nidai kaje ka lallasar mun ita don Allah Kuma in shaa Allah bazan Kuma ba tell her this please.
Shikenan....amma Zan Fara magana da ita ta waya tukun..... Kana da wani layin nata bayan Wanda ta rufe?
Through Aisha...... Okkkay.
Yayi sa'a kuwa suna tare zasu ci abinci...... Ungo sadeeq na magana ta Mika Mata wayar ......bayan sun gama gaisawa ya danyi kasa da murya Anwar din na tsaye sun Sanya handsfree..... Idan babu damuwa ki Dan ware muyi magana....
Batayi gardama ba .... Tana shiga daki ta zauna sai tace ...Ina ji.
Bilkisu nasan kina da hankali, nasan kina da ilimin addini, Ina so Dan Allah kiyi hakuri duk da abinda mijin ki yayi ba laifi bane wata kila hakan ya Sanya ki shiga wani Hali.... Sadeeq gaskiya Anwar na mun abinda bana so, da bakin sa ya ce zai ba daddy mamaki abinda ke tayar mun da hankali shine duk ranar da daddy yaji Ina Haka da Shi wallahi bazai taba yarda cewar ba ni na sanar dashi akwai Aure ba.
Ya kasa gane hakan..... Na sani Bilkisu, ya kalli Anwar kallon da ke nuna ```kaga abinda nake Gaya maka ko```...... Yaci gaba da cewa, kiyi hakuri ya mun alkawarin bazai Kuma ba..... Baya iyawa, na Fara planning kawai Zan koma gida ne sai ya mun transfer kamar yarda ya..... Ya fizge wayar.... Billahil azim bazan Kara ba kiyi hakuri Bilkisu.
Tayi shiru Jin shine ya karbi wayar.... Yaci gaba da magana.... Wallahi nayi hakan don ki saki jiki dani ba Wai..... Shikenan ya wuce.
Yayi murmushi, na gode Dan Allah kizo lecture two kinji ko?
Shikenan. Ta fada.
Thank you...... Ta ajiye wayar kawai ba tare da ta karasa ji ba.
Ya kalli sadeeq Yana dariya yace, ta kasa Yi mun fada .... Murmushi kawai yayi ya barshi wurin ya koma gun Anas.......
Gaban ya Fadi ganin dalleliyar mota ajiye kirar Toyoto 2019 Fara.
Ita da Maryam suka fita, kamshi kawai ke tashi a motar .... Me yasa baku fadan ya kawo motar ba?...... Sadeeq yace muyi shiru Kar mu fada.
Ta ce hmmm kawai.
....... An kafsa fadan ne ko?
Murmushi kawai tayi cikin nikaf Mai sauti..... Daga nesa ya hango motar ya saki ajiyar zuciya ya shiga class Yana jiran isowarta.
Har ta zauna bata lura dashi ba wurin taga tsaye sai bayan da tagan Shi tsaye kusa da ita..... Matsa na zauna. Ya fada a dake!
Ta matsa Yana Zama ta ce.... Ina wuni.
........ Keni ba lafiya ba. Ya hau masifa, idan na Miki laifi I prefer ki mun duk tsiwar da Kika iya da fada amma bazan iya daukar this type of your punishment ba...haba. kwana uku? You switched off your phone, you skipped class, I believe ko zuwa nayi Zaki gudu daki ki kulle Haka akeyi ma miji horo?.... Nidai shikenan.... Ta fada a hankali..... Ba shikenan ba, wallahi idan Kika Kuma kashe wayar ki idan na Miki laifi zakiji ni baibai.... Sai kawai ya bata dariya ta duke tanayi...... Au dariya ma na baki ya balle bottle din rigarsa na sama ji kasusuwa kamar ba hakki na nabi ba?
Shikenan nidai..... Kiban hakuri Dan wallahi kin sani cikin damuwa fa..... Kayi hakuri ta fada tana murmushi cikin nikaf.... Cire nikaf din ya fizgeshi..... Fuskar ta mishi wani fayau, ta Dan dake saboda bata son a gane tana blushing.......... I missed my baby wallahi. Ya fada..... Zai Kara magana malamin ya shigo....
Yana gamawa ya fita ya koma bisa table ya zauna gabanta..... Kunyar ki tayi yawa Bilkisu.
Zaka Fara ko?
To ki kalleni Mana Wai sumke sumken na menene?
Ta danyi murmushi,
........ Jiya sadeeq ya rabawa Yan class din nan twenty thousand each though sun gane kudin daga wurina yake fa..... Kunyi kokari Allah ya Kara arziki Mai albarka, rigunan fa?
Na bayar ayi a kamfanina da ke Paris zasu fi kyau daga can ko kuwa?..... Karaf suka hada ido ya sakar Mata murmushi, ta danyi dariya ta mike ..... Ina zakije?
Ba tafiya zamuyi ba?
No! Ki jira nayo sallah yau muna nan sai dare...... Nima zanje masallaci....ya Dan kalleta Yana Yar dariya me zakiyo masallaci? Kuma Yanzu nayi magana kice zakiji kunya.....Hajiya ki jirani anan Ina dawowa Zan sallami kattin can ko kuwa?......
Dama ai Kai ka damu dasu..... Eh dole su kula dake ...ke din ce bazaki gane ba ya fita Yana kwance agogo.....
Ta bishi da kallo ta zauna ... Watau yasan bani sallah. Kai Anwar case ne...... Hajiya ke bazaki je sallah ba?
Ta sakar Mata murmushi habawa Helen....ai duk kallon ku nakeyi Yan class din Nan Yanzu kowa sai shareni yakeyi kunyi dai dai wallahi ...... Ba Dole ba, kina son Anwar ya sa a kashe mutum ko?.... Kisa Kuma Helen.... Yes ko mace baya so ya zo gurin ki bakiga guards din da suke binki... Mtsew forget about guards zasu hana abota ne?
Hmmm, Bilkisu you won't understand.
Ehe Bilkisu... Tayi kasa da murya is it true you both got married????
Who told you?.... Abeg .
Tayi murmushi yes is true amma ba'ayi bikin ba kawai an daura Aure ne...... Jesus..ta fada da karfi.
Bilkisu ta kyalkyace da dariya.
You are lucky Bilkisu.... Anwar ya bada mamaki..... And he is that young Nigerian billonaire Bushara... Bilkisu ta Kara kyalkyacewa da dariya Helen Zaki kasheni, Bilkisu you are lucky ooo he gave us 20k and our shirts and jacket will come soon free for everyone....... Hango shi sukayi Yana magana da guards ta mike da sauri please tell him I'm your friend too we will keep talking any time Sha.....ta wuce da sauri tana waigen ko ya taho..... Bilkisu ta duke tana kyalkyatar dariya har ya karaso ...... Ke da waye haka?
....... Ta rike ciki Helen..
Yayi murmushi tana Miki hauka ko? Jiya naso kina class din nan kiga hauka ni Dole na fita nabar sadeeq da shirmen su...
Ya figo Jakarta yamcici nasan ba Kya rabo da Malaki.... Ya Ciro short bread biscuit da bounty.
Ka fiye neman magana ta fizge jakar.
Ya harareta pad kike gudun kada na gani Kuma na ganta dai.
Ta danyi dariya kaiiiiiii Allah ya shirya ka.... Tare da ke da zuri'ar mu baki daya...... Ki ce Amin...
Ta danyi murmushi na ce a zuci..... Ya sauko da hannun rigarsa da ya nade yana sanya links ....kin San jiya da daddare kamar Zan kurma ihu?
Ta dan kalleshi ta gefe... Yaci gaba da magana Yana murmushi.... Dana tuna kin kashe waya Kuma saboda ni sai naji kamar inta ihu ana jina a gari..... Ta danyi dariya .. kina yarda kike so ai.
Kayi hakuri ta fada tana murmushi.
...ai Dole in ma banyi ba nine masha wuya.
...... Anwar bana gane Alfa and bitas din ga na econometrics ... Ya danyi murmushi....Kuma basu da wuya fa.
Wannan drivation din ka ganshi.... Ya karbi littafin ya sauko kusa da ita ya Fara rubutu Kinga yanda yake......
A hankali a hankali yakeyi yanda zata gane.... Anwar marshene komai ya hada.
Duk inda ya shige Mata sai da yayi kokari yaga ta gane duk firar ta koma karatu hakan yasa ta saki jiki sosai shima kuma sai yaji dadi ganin ba wani sumke sumke ta saki jiki.
Ana Kiran magrib ya ce muje ki ajiyeni gida zanyi sallah masallacin unguwar mu. ... Shi yaja motar.
Tun daga ranar ya daina zuwa gidanta, abinci shike aikawa ana karbo mishi ko ta tafi dashi suci school, duk firar su a school sukeyi ya dake ya cije baya nuna zalamarsa fili.
Anayin hutu tare suka tafi Abuja Amma bai kwana ba ya koma Kano kwanan sa biyu yabar kasar......
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣8⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano mam in huhan Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
```Bazan taba mantawa da ke ba Maryam Aliyu Yar adu'a ( M. Ali ) uwar Noor my in-law kina Raina Koda yaushe```
👉🏼💕 *Mz ( salamatu Dahiru ) Ina Kara godiya Allah ya Kara dalili my mother*
*****************
*Federal University dutsinma*
....... Tun tana iya motsawa har jikinta ya mutu murus, duk illahirin kafafuwanta rawa sukeyi suna neman gagara daukarta, Jin tayi lakwas yasa Shi juyawa da ita ya zauna bisa kujera ita Kuma tana bisa kafafun sa..... Yayi iya gumin sa ya taba inda yake so, karkarwa jikinta kawai keyi duk ta firgita..... Ya saki ajiyar zuciya ya janye bakin sa a hankali..... Sai kawai ta tusa kanta cikin kirjinsa ta saki kuka... Yayi shiruuuu...
Zuciyar sa na mishi sake sake, shin ya biya bukatar sa ko ya ba dady mamaki?
Da ya motsa sai ta rikeshi gamm ta Kara sakin kuka.... A hankali yake fitar da numfashi.... Sai kawai ta bashi tausayi lallai ya Kara tabbatar wa kansa da Bilkisu yarinya ce karama.... Tunda har ta kasa supporting kiss kuma hakan ya bashi tabbacin this is her first kiss.....
Tayi Mai isarta, har lokacin jikin ta rawa yakeyi..... Da ya motsa sai ta Kara rikeshi.... Ya danyi dariya.. ``` To ki sakeni na tashi ko?```
Tayi shiru,
```Bilkisu```
Ya Kira sunan ta a hankali,
.... Ta Kara fashewa da kuka ``` Dan Allah kayi hakuri```
..... Ya Kara dariya naji sakeni Dan Allah ai ba Kya so ko?
Ta daga Kai cikin jikin sa...
Okay Zan tashi na tafi sakeni....
Ta Dan sakeshi.... Yana motsawa ta koma da sauri .... Ya kyalkyace da dariya da ya gane ba tsoro kadai ke addabar ta ba hada kunya..... Ni Kuma yau tawa ta sameni ni *Hamza*...... Bazaki sakeni ba? To gyara mu yi kwanciyar mu anan.... Ta sakeshi da sauri tare da soke kai cikin kujera..... Ya Kara dariya.... Ba rakiya kenan?
Tayi shiru..... Ya kawo hannu ya taba ta, saki kuka tare da kankame jiki..... Ya Kara dariya ya ce tohm na siyo ma kaina rigima da kudina..... Ya zukunna gaban ta, Shikenan daina kukan Zan tafi Amma Dan Allah ki dauki waya idan na Kira matukar bakya son na maimaita kinji ko?...... Saura kadan ta wawuro fuskarsa ta cije don takaicin kalmar ```kinji ko```.
Ya saki ajiyar zuciya ya mike sai da safe I will miss you honestly..... Ya fita da sauri.
Tafi mintuna ashirin a wurin kafin ta tashi zaune.... Ta Dora hannu a Kai *Na shiga uku ni Bilkisu idan Haka ne halin Anwar na gama banuwa* Shi baya da kunya?
Ashe abinda nake karantawa da abinda malaman islamiya ke fada gaskiya ne?
Ta Mike jiri ya kwasheta, ta koma ta zauna.... Ikon Allah, ta kalli hannuwanta sai kakkarwa sukeyi, tsikar jikinta tashi Yarrrr tana tuno abubuwan da suka faru... Namiji???? Shi har wata dariya yakeyi... Ta zumburo baki tare da zabga uban tagumi.
Yana shiga sadeeq yaji kamshin turarensa ya canja gashi cikin wani yanayi na nishadi .... Ya bishi da kallo kawai Shi Kuma ya fada toilet ya sakar ma kansa shawa.......
Duk su Aisha sun shige sun kwanta, ta shige dakin itama Kai tsaye kewayen ta fada......
Ta na rungume da qur'ani kiransa ya shigo..... Taji wani dammmmm a kirji.
Ta dauka Amma samm ta kasa magana....
Kinyi wanka?
Tambayar ta bata haushi ta mishi banza.... Kinji?
Um, ta ce a hankali.
Kin kwanta ne Yanzu?
Tayi shiru......
Ya ce kinji?
Ta ce um,
Yayi murmushi, Baki ya mutu ne?
Tayi shiru.......
Ya ce huh?
Da kyar ta ce hmmm.
Ya danyi dariya.
Thank you so much Bilkisu, wallahi naji dadi sosai Zaki Sami Lada Mai tarin yawa kin San Haka?
Tayi shiru...kanta sunkuye kamar Yana kallonta wayar ma kunya take Bata.
Ya Kara dariya Wai Baki magana?... Ko muyi video call........ Nidai a'a..... Ya tuntsure da dariya to kiyi magana inji, kiss kawai ya rikitaki haka Ina ga..... Zan kwanta Dan Allah..... Ta fada kamar zatayi kuka ya kyalkyace da dariya..... Shikenan sleep tight sweetie.... Ta latse wayar da sauri kirjinta na bugawa ..... Ai shikenan Ni Kuma tawa ta sameni ta fada a hankali.
Ta Dade barci bai dauketa ba har kusan karfe uku da Rabi..... Shi yasa ta rasa lecture karfe bakwai don Bata tashi ba sai Tara saura.
....... Sadeeq ya kalleshi ya Bilkisu bata zo lecture ba?..... Ya danyi dariya kawai...
Ya bishi da kallon tuhuma.... Me ka Mata?.... Ya daga hannuwa yana dariya wallahi ban Mata komai ba kawai kiss ne ....... Ai nasan baka iya ba daddy mamaki Anwar Kuma yasan abinda ka je ya dawo Kan yarsa akanka yasa ya yanke wannan hukuncin...... Allah Ina iyawa.... Me yasa ka taba ta toh?
Ya galla mishi harara halan ni katako ne da Zan tsaya da Aure Ina kallon matata haka zikau ai ko Dan romance din a daga mun kafa ko?
.... Sanya ma Rai koshi ke kawo yunwa Anwar a haka, ahaka zaka je inda baka son zuwa Dan Allah Ina baka shawara ka tausaya ma yarinyar nan ka Bari akai maka ita...... Kuma duk ta tsorata jiya kaga yanda jikinta ke Bari?
Ai dole ta tsorata, bacin islamiya da sai ince anya tasan me ake ce ma Aure saboda yanayin yarinyar na bani mamaki...... Wallahi yarinya ce sadeeq nayi mamaki jiya ta kasa daukar kiss...... Mtseww ai ka yi sauri...
Shin Zan kiyaye ai dai na Dana.... Ya mishi gwalo... Ai Kuma ka Dano ma kanka ko? don na tabbatar Yanzu ka siyo rigima da kudin ka..... Wallahi
kuwa, ko agabanta na fada jiya..... Amma fa na kashe bakin rigima Zan Sami sauki saboda ta tsorata da Ni...... Ya ce hmm.
Yaki zuwa gidan ranar ta kashe wayar ta...
Ta ce ma su Aisha zatayi karatu ne daki Koda sun jita shiru.
Kwana daya , biyu har uku Bata shiga school ba. Taki kunna waya kuma.
Hankalin sa ya Fara tashi, ya Sami sadeeq ya fada mishi suna tare da Anas ya Dan kebe shi.
... Yarinyar nan fa taki kunna waya kaga kuma Bata zuwa class.. nasan za a rina Anwar ai ka Mata shigar kutse da ka bari da Yan dabaru da hikima sai ka shawo kanta amma Haka zikau ai Dole ta firgita..... Ya kamata ka fahimceni ya zaka biye Mata ka dauki taking side.... Ya fada a hasale... Na sani amma Ina kwatanta maka ne...... Naji nidai kaje ka lallasar mun ita don Allah Kuma in shaa Allah bazan Kuma ba tell her this please.
Shikenan....amma Zan Fara magana da ita ta waya tukun..... Kana da wani layin nata bayan Wanda ta rufe?
Through Aisha...... Okkkay.
Yayi sa'a kuwa suna tare zasu ci abinci...... Ungo sadeeq na magana ta Mika Mata wayar ......bayan sun gama gaisawa ya danyi kasa da murya Anwar din na tsaye sun Sanya handsfree..... Idan babu damuwa ki Dan ware muyi magana....
Batayi gardama ba .... Tana shiga daki ta zauna sai tace ...Ina ji.
Bilkisu nasan kina da hankali, nasan kina da ilimin addini, Ina so Dan Allah kiyi hakuri duk da abinda mijin ki yayi ba laifi bane wata kila hakan ya Sanya ki shiga wani Hali.... Sadeeq gaskiya Anwar na mun abinda bana so, da bakin sa ya ce zai ba daddy mamaki abinda ke tayar mun da hankali shine duk ranar da daddy yaji Ina Haka da Shi wallahi bazai taba yarda cewar ba ni na sanar dashi akwai Aure ba.
Ya kasa gane hakan..... Na sani Bilkisu, ya kalli Anwar kallon da ke nuna ```kaga abinda nake Gaya maka ko```...... Yaci gaba da cewa, kiyi hakuri ya mun alkawarin bazai Kuma ba..... Baya iyawa, na Fara planning kawai Zan koma gida ne sai ya mun transfer kamar yarda ya..... Ya fizge wayar.... Billahil azim bazan Kara ba kiyi hakuri Bilkisu.
Tayi shiru Jin shine ya karbi wayar.... Yaci gaba da magana.... Wallahi nayi hakan don ki saki jiki dani ba Wai..... Shikenan ya wuce.
Yayi murmushi, na gode Dan Allah kizo lecture two kinji ko?
Shikenan. Ta fada.
Thank you...... Ta ajiye wayar kawai ba tare da ta karasa ji ba.
Ya kalli sadeeq Yana dariya yace, ta kasa Yi mun fada .... Murmushi kawai yayi ya barshi wurin ya koma gun Anas.......
Gaban ya Fadi ganin dalleliyar mota ajiye kirar Toyoto 2019 Fara.
Ita da Maryam suka fita, kamshi kawai ke tashi a motar .... Me yasa baku fadan ya kawo motar ba?...... Sadeeq yace muyi shiru Kar mu fada.
Ta ce hmmm kawai.
....... An kafsa fadan ne ko?
Murmushi kawai tayi cikin nikaf Mai sauti..... Daga nesa ya hango motar ya saki ajiyar zuciya ya shiga class Yana jiran isowarta.
Har ta zauna bata lura dashi ba wurin taga tsaye sai bayan da tagan Shi tsaye kusa da ita..... Matsa na zauna. Ya fada a dake!
Ta matsa Yana Zama ta ce.... Ina wuni.
........ Keni ba lafiya ba. Ya hau masifa, idan na Miki laifi I prefer ki mun duk tsiwar da Kika iya da fada amma bazan iya daukar this type of your punishment ba...haba. kwana uku? You switched off your phone, you skipped class, I believe ko zuwa nayi Zaki gudu daki ki kulle Haka akeyi ma miji horo?.... Nidai shikenan.... Ta fada a hankali..... Ba shikenan ba, wallahi idan Kika Kuma kashe wayar ki idan na Miki laifi zakiji ni baibai.... Sai kawai ya bata dariya ta duke tanayi...... Au dariya ma na baki ya balle bottle din rigarsa na sama ji kasusuwa kamar ba hakki na nabi ba?
Shikenan nidai..... Kiban hakuri Dan wallahi kin sani cikin damuwa fa..... Kayi hakuri ta fada tana murmushi cikin nikaf.... Cire nikaf din ya fizgeshi..... Fuskar ta mishi wani fayau, ta Dan dake saboda bata son a gane tana blushing.......... I missed my baby wallahi. Ya fada..... Zai Kara magana malamin ya shigo....
Yana gamawa ya fita ya koma bisa table ya zauna gabanta..... Kunyar ki tayi yawa Bilkisu.
Zaka Fara ko?
To ki kalleni Mana Wai sumke sumken na menene?
Ta danyi murmushi,
........ Jiya sadeeq ya rabawa Yan class din nan twenty thousand each though sun gane kudin daga wurina yake fa..... Kunyi kokari Allah ya Kara arziki Mai albarka, rigunan fa?
Na bayar ayi a kamfanina da ke Paris zasu fi kyau daga can ko kuwa?..... Karaf suka hada ido ya sakar Mata murmushi, ta danyi dariya ta mike ..... Ina zakije?
Ba tafiya zamuyi ba?
No! Ki jira nayo sallah yau muna nan sai dare...... Nima zanje masallaci....ya Dan kalleta Yana Yar dariya me zakiyo masallaci? Kuma Yanzu nayi magana kice zakiji kunya.....Hajiya ki jirani anan Ina dawowa Zan sallami kattin can ko kuwa?......
Dama ai Kai ka damu dasu..... Eh dole su kula dake ...ke din ce bazaki gane ba ya fita Yana kwance agogo.....
Ta bishi da kallo ta zauna ... Watau yasan bani sallah. Kai Anwar case ne...... Hajiya ke bazaki je sallah ba?
Ta sakar Mata murmushi habawa Helen....ai duk kallon ku nakeyi Yan class din Nan Yanzu kowa sai shareni yakeyi kunyi dai dai wallahi ...... Ba Dole ba, kina son Anwar ya sa a kashe mutum ko?.... Kisa Kuma Helen.... Yes ko mace baya so ya zo gurin ki bakiga guards din da suke binki... Mtsew forget about guards zasu hana abota ne?
Hmmm, Bilkisu you won't understand.
Ehe Bilkisu... Tayi kasa da murya is it true you both got married????
Who told you?.... Abeg .
Tayi murmushi yes is true amma ba'ayi bikin ba kawai an daura Aure ne...... Jesus..ta fada da karfi.
Bilkisu ta kyalkyace da dariya.
You are lucky Bilkisu.... Anwar ya bada mamaki..... And he is that young Nigerian billonaire Bushara... Bilkisu ta Kara kyalkyacewa da dariya Helen Zaki kasheni, Bilkisu you are lucky ooo he gave us 20k and our shirts and jacket will come soon free for everyone....... Hango shi sukayi Yana magana da guards ta mike da sauri please tell him I'm your friend too we will keep talking any time Sha.....ta wuce da sauri tana waigen ko ya taho..... Bilkisu ta duke tana kyalkyatar dariya har ya karaso ...... Ke da waye haka?
....... Ta rike ciki Helen..
Yayi murmushi tana Miki hauka ko? Jiya naso kina class din nan kiga hauka ni Dole na fita nabar sadeeq da shirmen su...
Ya figo Jakarta yamcici nasan ba Kya rabo da Malaki.... Ya Ciro short bread biscuit da bounty.
Ka fiye neman magana ta fizge jakar.
Ya harareta pad kike gudun kada na gani Kuma na ganta dai.
Ta danyi dariya kaiiiiiii Allah ya shirya ka.... Tare da ke da zuri'ar mu baki daya...... Ki ce Amin...
Ta danyi murmushi na ce a zuci..... Ya sauko da hannun rigarsa da ya nade yana sanya links ....kin San jiya da daddare kamar Zan kurma ihu?
Ta dan kalleshi ta gefe... Yaci gaba da magana Yana murmushi.... Dana tuna kin kashe waya Kuma saboda ni sai naji kamar inta ihu ana jina a gari..... Ta danyi dariya .. kina yarda kike so ai.
Kayi hakuri ta fada tana murmushi.
...ai Dole in ma banyi ba nine masha wuya.
...... Anwar bana gane Alfa and bitas din ga na econometrics ... Ya danyi murmushi....Kuma basu da wuya fa.
Wannan drivation din ka ganshi.... Ya karbi littafin ya sauko kusa da ita ya Fara rubutu Kinga yanda yake......
A hankali a hankali yakeyi yanda zata gane.... Anwar marshene komai ya hada.
Duk inda ya shige Mata sai da yayi kokari yaga ta gane duk firar ta koma karatu hakan yasa ta saki jiki sosai shima kuma sai yaji dadi ganin ba wani sumke sumke ta saki jiki.
Ana Kiran magrib ya ce muje ki ajiyeni gida zanyi sallah masallacin unguwar mu. ... Shi yaja motar.
Tun daga ranar ya daina zuwa gidanta, abinci shike aikawa ana karbo mishi ko ta tafi dashi suci school, duk firar su a school sukeyi ya dake ya cije baya nuna zalamarsa fili.
Anayin hutu tare suka tafi Abuja Amma bai kwana ba ya koma Kano kwanan sa biyu yabar kasar......Koda aka koma school bai samu ya dawo ba, topic din sa na project ta email suka ringa communication da supervisor din sa, Bilkisu itama da akayi accepting nata ya ce ta tura mishi Shi ya ringa yo wa Yana turo Mata, ita Kuma da sadeeq suna tura mishi lecture da akayi. Wuni sukeyi video call, ko meeting yakeyi wani lokacin sai ya latsota,
Duk CA din da akayi Shi sai da yazo exam aka mishi,satin sa daya akayi hutu suka tafi da yake course shidda ne...... Abun ya Kara rikicewa saboda hutun sati daya ne, gashi final semester ga daddy yasanya bikin su bayan sun Gama da sati.
Anwar baya zama Nigeria ko kadan, ya Kuma hana su dady fita ko Ina Wai kada ayiwa Bilkisu soyayyar komai.... Shirye shirye ya kankama, sadeeq ma baya zaune.... Koda suka koma makaranta ita kadai ce, lectures sun ragu, course hudu sukeyi kacal, project kuwa Shi ke turo Mata,
Wannan da wuri ya dawo exams saura sati uku, yazo da jackets din su day shirts ko wane da size dinsa, jacket din dark blue da ratsin harsh anyi tambarin fudma ( logo ), kowa da sunan sa bayan rigar, sai white shirt ta yin signing da wando dark blue.
A bayan rigarsa an rubuta *Bushara* Bilkisu Kuma *Mrs Bushara* ya siyo Mata Tommy skirt dark blue Mai wasu irin flowers rose dark blue a jiki kana iya taba ko wace flower ya hadu iyakar haduwa..... Bai Bata ba sai ranar last paper yace ta saka da gyale ya yafe ..... Ga takalmi hills tayi kyau matuka..... Yazo da ledoji na i.v din su ko wace Leda da ticket da gate pass na tafiya bikin.... A ka dauko kattin speakers suna gamawa aka Fara ihu da kidi..... Bilkisu na fitowa Yana tsaye ya ware hannu ta rugo da gudu ta fada aka dau ihu...... Sun birge kowa, ya bude Mata gaban rigarsa ta rubuta *Mrs Bushara* shima ya rubuta Mata *Anwar* a tata sannan ya duka aka yi ta mishi rubutu.... Ita kuwa Mata kawai yace su rubuta kada shegen da ya taba mishi Mata .... Akayi ta dariya...
Nan aka Fara watsin lemuka, ana hotuna..... Anwar na makale da Bilkisu ya Fara watsin dollars.... Makaranta ta rude aka Fara wawaso..... Kawai ya hango mufeeda can ana niyyar danneta wurin kwasar kudi ya zunguri Bilkisu ya nuna Mata Yana murmushi.....ta karbi sauran dake hannun sa ta karasa kawai sai dai mufeeda taga an sunno Mata dumshin kudi...ta dago da sauri tana ganin Bilkisu sai kawai ta riketa tare da sakin kuka...... Duk ta ji tausayin ta. Mufeeda daina kuka Mana... Ta Mika Mata kudin kawai ta juya....
Bata ga Anwar ba, sai ta hangoshi can shida Suleiman Yana sunna mishi wani abu da alama kudi ne baya son kowa ya gani.... Tayi murmushi Bata karasa inda yake ba...... Yana murmushi yayi godiya. Amma ban fadawa mutuniyar ka tare zamu tafi ba .... Au haba.
Allah kuwa. Na ce Mata kawai zamu tafi da wasu Abuja yau saboda Shirin biki sauran tunda akwai ticket sa taho..... Ai kunyi kokari Allah yasa albarka da zuri'a dayyiba..... Amin Suleiman. Sai ku shiga mota idan sun karaso bana son muyi dare kasan rigimar Bilkisu..... Duk sukayi dariya. Jaka ta na daki ta Kaya...... Kayiwa murtala magana ya tafin maka da ita kawai can akwai kayanku..... Ya wuce yabarshi gurin ya nufi inda Bilkisu take.
Motocin sa suka shigo a guje school din... Bushara 1, Bushara 2........ Bushara 10.
Nan wuri ya Kara rikicewa....... Shi da Bilkisu mota daya, sadeeq da Anas mota daya, Suleiman da Ahmad motar su guda......... Suka fice garin duk sun bar mutane da magana a Baki........ Abuja tayi dauka Kuma za a Fara Shirin biki........ though daurin Aure a sokoto za a dauro Shi Amma duk programs din Abuja za'ayi .............😄✍🏼
*ZAINAB WOWO MAMAN ABDALLAH*💖💖💖.
*ALLAHUMMA LAA SAHLAN ILLA MAA JA'ALTAHU SAHLAN WA'ANTA TAJ'ALUL HAXNA IZAAHHH SHI'ITA SAHLAN...."* MU ringa karantawa saboda wannan annoba
Ayi hakuri jiya nayi laifi ban turo ba. Nace ayi addu'a😀
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣9⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
******************
*ABUJA NIGERIA*
Suna Isa daddy ya ce maza Anwar yazo Yana son ganin sa.....
Su biyu a falo daddy bisa kujera Shi Yana zaune a kasa, yayi yayi ya hau kujera amma ya ce hakan yayi..... Ba karamin dadi yakeji ba irin Respect da kunyar Anwar din duk rawar kansa idan Yana gaban daddy bai iya ko kwakkwaran motsi..
... Abinda yasa na kiraka anan Ina son mu tattauna wasu maganganu, na farko akan kayan dakin bilkiyne, Anwar bisa ga Al'ada irin tamu ta hausawa kasan cewa duk diya da Kuma iyayenta suna son suga abinda suka saka ma yarta a gidan auren ta Amma Kai kace sammm baka da bukata, shine muka yi shawara zamu tura maka kudi a madadin kayan...
Na biyu, ta fada mun ka ce lefenta sai taje gidan ka, wannan tsari ya Mana dadi matuka....
Na karshe kuwa da zance shine, programs din da zakuyi tayi yawa ka mayar dashi party daya kwal! Kuyi Shi a jibi don in shaa Allah Ranar juma'a Zan dauketa da kaina in kaita daki bana son duk wadannan bidi'o'in.... Ya dago Kai da sauri ya kalli dadyn suna hada ido ya sunkuyar da sauri.... Yayi Yar dariya Kano zaka ajiyeta ko nan sannan ka hadani da mutum daya Wanda zai mun jagora don juma'ar bacin Kai da na fadawa mahaifiyar ta kadai tasan wannan tsarin nawa.
Ya Kara kasa da Kai yace toh.... A Kano zamu Fara Zama in shaa Allah.
.......madallah. Ina ga shikenan kana iya tafiya.
Ya Dan sosai keya Yana son magana Yana Jin nauyi...... Yaya akwai wata magana ne Anwar?
Ya danyi murmushi.... Ranar juma'a din da karfe nawa?....... Ka turon Wanda zai mun jagora gobe don in shaa Allah anan zanyi sallar juma'a bayan na dawo kaita....... Ya dankara kasa da Kai tare da zaro ido..
Ya rusuna Allah ya Kara girma mun gode....ya Mike.
Ya kalleshi account number zaka bayar kenan?
Ya danyi murmushi ya koma ya zukunna, ayi mun aikin gafara daddy bazan karbi kudi ba, amma idan ko hankali bazai Sami natsuwa Kan hakan ba, to a turawa Bilkisu tunda daman ko kayan akayi mallakin ta ne fatana a Sanya Mana albarka a ciki addu'ar kadai ce zata fi duk wani kayan masarufi ko kudin quality...... Daddy ya kura mishi ido Yana jinjina tunani da hankali irin na Anwar.
Yana tafiya suka Fara shirye shiryen hada party don cewar Anwar sai fa anyi.
Abokan sa na kasashen waje duk sun iso masu kudin Nigeria kuwa abokan huldar sa wurin kasuwa kawai ake jonewa Amma duk wani sha'ani na yarinta da 'ya'yan su Anwar keyi sune abokan.....Amma wannan bikin sun Alkawarin halartar partyn da za ayi a national conference Hall dake presidency a cikin Villa.
An kayata wurin mawaka duk sun hallara hada yaron nan matashi Dan katsina Mai tashe Yanzu watau *Aliyu nata ( Aure martaba )*
Iyaye da abokan arziki sun hallara wurin, dangi da duk wani Mai alaka da bikin kowa ya kure adaka.....
An tsantsara ma Amarya kwalliya suna saman bene za a shirya ta aka shigo da wata matsiyacitar *Gown* maroon color *Innalillahi* bana iya describing rigar saboda rigace akalla idan zuwa zakayi shago ka siyo zata haura millions, duwatsun jikin rigar kansu diamond ne, musamman aka mishi ita special da wasu laces da materials Wanda ya ware don party kawai Amma Yanzu daya zata saka.....
Kilibabbu magulmata wadanda ba a rasa irin su a kowane dangi Baki yayi gummm, saboda suna ta korafin duk kudin Bushara bikin sa ba lefe...... sunfi awa shida wasu abokansa a waje cikin motoci suna jiran fitowar Amarya bayan shiga da rigar saboda ganin rigar yasa dole aka canza pattern na kwalliyar.
Tunda ta Fara saukowa ake daukarta hoto, gidan ya rikice,Yan sanda da sojoji gewaye da ita sunki yarda ma a rabeta...... Su mommy da kawayenta na babban falo ana fama da ita Kan zuwa wannan party Amma tace sammm baza ta je ba.
Suna hango fitowar su ya fito mota dasauri...... Ya Sha farar shadda ta karshen karshe Yana isa duk aka dare kawai ya rungume ta.....wuri ya dauki ihu kanka yane cikin gyale sai da suka shiga mota ya daga Shi ya leka....... Ya tallabo fuskar...... tsarki ya tabbata ga mahaliccin Bilkisu..... Ya Kai bakin sa ga nata tayi saurin fadawa jikin sa ta na murmushi..... Ya danyi dariya.... Ke wallahi dadi na dake Yar garin mu ce, ya dagota ba da yawa zanyi ba please......ta Kara komawa jikinsa..... Ya kyalkyace da dariya kaiii Ni Kuma tawa ta sameni daga ni kada ki batan Kaya da Jan Baki toh, nasan karamin aikin ki ne...... Yayi juyin duniya taki yarda ta dago don tasan halin sa tunda yace zaiyi kissing dinta sai fa yayi.....
Ya Kama dariya ya rungume a sosai, ga son jiki ga Kuma tsoro sai a daga ni tunda ba'a son tukuici.
Yana shafa bayanta Yana magana a hankali wallahi nasan rigarnan dole ta Miki kyau. Tunda wasu suka ji labarinta an Fara damuna..... Ya dago ta da karfi Kuma sarkar nan ta hau kayan ko?
Sosai, ta fada tana murmushi.... Wuf! Yakai bakin sa ga nata sai kawai ta tafi jikin sit luuuuu tayi baya.......
Tsayuwar motar yasa Shi sakinta a hankali, tayi kasa da Kai ya danyi dariya na shanye Jan baki ya kura Mata ido ta sunne Kai kawai....... Ya shafi gefen fuskar ta Yana murmushi *shy girl*
Wuri ya dauku, Shi kansa bai taba tunanin ganin wasu mutanen ba Amma sun mishi surprise.
Rike yake da hannunta suna tafiya a hankali Kota Ina Yan daukar hoto ne, abokan su na bakin kofa suna jiran isowar su.
Kawayen Bilkisu sun Sha Anko na light pink lace da blue head sun hadu sun Gama haduwa abinda ga fresh and young graduates.
Daga ciki wani sound na kidi ya Fara tashi kawai Anwar yaga Yan matan nan sun Fara rawa iri daya Nan da Nan wuri ya dauki ihu da sowa...... Rawa sukeyi ta birgewa Anwar nata dariya ya tallabo kugun Bilkisu ya Dan duka ya Mata rada hada chorography kuka hada haka?
Tayi murmushi kawai. Rawar sukeyi sosai har suka raka su mazauni Anwar na Zama ya janyo Bilkisu ta fada bisa cinyarsa lokacin da take kokarin Zama wurin ya Kara rikicewa......
Yan matan suka ja layi tare da canza salon rawa hall din yayi tsit kidan kawai ke tashi an masu kuri da ido ba Wanda ke son ko kiftawa yayi kada ayi wani step din ba gani ba.......
Wani juyi da sukayi kawai sai ga maza sun shigo cikin rawar , sadeeq, Suleiman, Anas, mustapha da su Joseph...... Wayyo Allah wuri ya Kara rikicewa da ihu ganin mazan sun dauki sabuwar tsarin rawar da Yan matan keyi suna juyi iri daya......ai sai turawan nan da sauran abokai da mutanen arziki suka Mike ana barin dollars.
Anwar ya Kara kyalkyacewa da dariya ya Mata rada a kunne keda wa kuka tsara haka? It's seems like you people are surprising me ...... Ta danyi dariya tun a school suka fara practice...... Ke me yasa bakiyi ba?
Ta Kara dariya Kai ma ai baka rawa.
Inji waye? Yau Zan yi.
Tayi murmushi Nima zanyi anjima zamu sake wata..... Keda wa?
Nida su Helen....... Irin waccen?
Ta danyi dariya waccen tafi wannan kyau saboda mu shida kawai zamuyi ta.... Banda ni ko?
Ta Dan duke tana dariya ai baka yi rehearsal ba....... Ina menu na program din?
Ka fiye sauri gashi can ga Mc sai ma can wajen karshe zamuyi fa...... Can't wait. Ya fada Yana kallonta yana murmushi......
Amma Suleiman ya birgeni Kuma yaban mamaki duk ustazancin sa yau Yana rawa haka?
Ta Kara murmusawa ko a school anyi ta mamaki.......
Ana gama rawar aka Fara gabatarwa, kaiii wurin an tara basawan Nigeria wani ma sunan sa kawai kakeji, su Aisha ne kirjin biki ko Zama sun kasayi.
Komai order akayi abinci ma musamman akwai masu bayarwa , basket ake ajiyewa mutum bisa table din sa komai a ciki. Duk abinda kake so akwai a basket din....
A ka umurci Ango da Amarya su fito fili..... Masu wakokin kowa nayo gaba gaba..... Anwar ya ce a Bata *Aliyu nata* ya rera musu *Aure martaba*......
Ai ana cewa rangwal..... Anwar ya Fara takawa Bilkisu da mutane aka Fara dariya..... Kafin kace kwabo fili ba masaka tsinke ana masu barin nairori ...... Ya samu ya gewaya ya kamo hannun Bilkisu ya Mata rada ```Ke maza sunyi yawa muje ki zauna``` sai kawai ta Kama dariya.... Kishin Anwar yayi yawa ranar bikin nasu ma?.
Ya kaita har inda suke zaune sannan ya sauko ya dawo filin...... Nan da nan su sadeeq suka far mishi...... Ya Kama dariya suka Kama rawa.....
*Nata* har tsalle yakeyi duk ya rikice ganin irin barin dollars din da akeyi.
Bayan an gama ne aka Fara cin abinci.
Bilkisu taga ice cream a table din su.... Ta kalleshi yayi dariya kowa abinda yake so ake bashi, Suma can duk basket din da Kika gani ba abinda babu ke kuwa ni nace akawo ice cream don nasan Shi kikafi kauna ...... Ta danyi dariya.
Ya dauko katuwar robar ya bude ya Fara Bata a Baki ..... Kai Anwar karshene..
Bayan an gama ciye ciyen, aka ce Amarya da kawayenta zasuyi rawa...... Anwar ya washe baki yau zanga rawar ki...... Ta kalleshi ta danyi murmushi kawai ta sauka....
Ya kishingida bisa kujera ya Dora yatsa a Baki ya bita da kallo....
Ita ce gaba, Aisha da Na'ilatu nasir bayanta, sai Helen, maryam da chinyere a karshen layi duk sun canza Kaya sun kaso jeans dark blue da white t-shirt sai farin kambas da dark blue facing cap.......
A hankali kidan ya Fara tashi Bilkisun ta Fara wani moves suna kallonta kafin Suma su dauka ....... Wuri ya dau tafi da ihu ganin yanayin daukar rawar kanta..... Ga Na'ilatu daman da son rawa kawar Bilkisu ce ta cikin unguwa tun suna Yara. Mowa na son takawa amma Aure ya Mata katanga don tabbas da wurin ya Kara bada kala.
Unex kuwa ai ita akwai kamewa tana can da kawayenta suna kallon kowa dai dai.
Alawiyya kuwa bayan kujeru ta tsaya tana murza kattan duwawukanta ana Mata nata barin dalolin daga gefe.
Dariya kawai Anwar keyi , turawan nan kuwa duk sun rikice an Gama kashesu da salo.
Wani juyi da sukayi cikin wata rawa ta duke Anwar bai San ya sauko ba ya balle rafar kudi. .... Wuri ya dauki ihu...gani Bilkisun ta canza salon rawa sun mayar dashi tsakiya suna wani takun..... So sai mutane suka karasa gigicewa kawai ya canyota da karfi ya rungume aka dauki ihu aka taso ana barin kudi........
Biki yayi biki.... Partyn ya bada kala.......live aka ringa nuna program din a tashoshin television na gida da waje.....
Sai Sha biyun dare aka gama..... Sai da suka tabbatar kowa ya tafi sannan suka shiga mota .
Ya janyo ta jikinsa, waye ya koya Miki rawa haka?
Ta danyi dariya..... Bude Baki kiyi mun magana ko Kuma na yakai hannun bayanta zai zuge Mata zip din Riga...... Ya hakuri jira inyi magana... Ya kyalkyace da dariya kaiii kin fiye tsoro.
Daddy jiya ya aika da motoci na abinci na ce kada ya siyi komai Amma yaki yarda, Ni Ina da kamfanin shinkafa meye za a kai mun?
Ni ke shigowa da Mai Ina da kamfunan man gyada Amma..... Duk da Haka ai al'ada ce..... Al'ada addini ce?
Ni yaban ke tsingirin gatarin ki na tafi abina..... Ta danyi dariya.
Ya Kara matsawa kusa da ita ..... Ina son salo irin na daddy Bilkisu a gaskiya ya iya dattako da daukar ma Kai mutunci.... Ta ce hmmm kawai tare da Dan muskutawa don taja baya.... Ya Kara matsawa ya janyo ta ya Fara lalube...... Ta ce innalillahi na shiga..... Ke! Kin shiga ukun ko?
Ke Wai kin San shiga uku kuwa?
Ta soke kai... Ya Kai Baki wurin kunnen ta ya ce ```please in zuge zip?```.... Ta ja baya da sauri..... Kayi meye?
Nidai don Allah ka rufan asiri. Ta fada kamar zata mishi kuka .
Ta Riga ta Kai karshe bakin kofa ....ya Kara matsowa Yana Yar dariya to Wai ke gobe ya zamuyi anya bazaki bani wahala ba?....... Ta kudundune Kai ta ce *Na bani* ya kyalkyace da dariya yace ikon Allah.... Motar ta tsaya. Ta say hannu zata bude ya kamota jira Mana saurin me kikeyi?
Anwar nidai Zan tafi gida Dan Allah..... Na Fara Baki tsoron ko?
Tayi shiru. Yayi dariya..... Ya tallabo fuskarta ke ko Yar karar Nan ki kawon gudummuwar tsumi Nasha ko?..... Ta zaro ido.
Ya kyalkyace da dariya, amma dai kin San nasan su waye sokotawa ko?..... Kai Ni ban Sha komai ba..... Ya Kai hannu zai kamota ta makale jikin kofa..... Karya kikeyi kinsha Mana Dan Allah an dafa Miki kaza?...... Na shiga uku ni Bilkisu.... Ya kyalkyace da dariya... Nidai Dan Allah ki dauri kici Kisha kinji ko?....... Naji sai da safe.... Ya janyo ta da karfi ta fada jikinsa yace .... Yawwa kin yarda kenan nasan Kuna ci.
Ohh yau ni tawa ta sameni ni Bilkisu.... Ya kyalkyace da dariya kina birgeni wallahi.
Ya Kai Baki a kuncinta Bari ko nan na Dan sumbata...... Ta runtse ido, ya Dan Kara tattabata yana fadin, ai nayi namijin kokari Bilkisu na ba da mamaki shekara daya ban komai ba .....Hana ai wallahi ko ban nema ba ya kamata gobe ki nemeni da kanki ko? ya saketa.... Da sauri tabar motar yabita da dariya.....
Gabanta sai faduwa yakeyi ita kawai tasan ta Gama mutuwa taje gidan sa.
Washe gari ko ita bata San inda zasuje da daddy ba don baya son fada Mata kada ta Tara mishi jama'a da kuka.
A airport ta kura mishi ido Amma yasha mur babu fuskar tambaya.
Koda ta shiga jirgi ta fahimci abinda ke Shirin faruwa sai kawai ta Fara kuka..... Ashe tun kwana biyu da suka wuce an kai duk Wanda zaiga gidanta ya gano.
Tsinken ragin ta ya Kai daki....... Gidan ba kowa sai Mai gadi kadai, Shi kansa Anwar din bai sanar da kowa ba .
Kuka take wiwi....gidan Yana daddy tsoro ya firgita ainun yasan waye Anwar Amma zahiri gidan ya tayar mishi da hankali Shi kansa ya tabbatar diyarsa ta Gama Dace duniya.
Ya Mata nasihohi masu shiga jiki ya janyo Mata ayoyi da hadisai, kannen ta duka biyun suna gefe suna Yan kwalla Yanzu gida ya koma sai su daddy kadai saboda su Daman London suke karatu basa Zama Nigeria sosai.
Da zasu tafi ta rike su, ta na wani irin kuka.
Haka suka lallabata suka barta kwance bisa gado ji takeyi kamar zata mutu.
Anwar kuwa karfe Sha biyu ya Gama sallamar duk wasu Baki. Banda Aisha da Maryam saboda su daga Kano zai Sanya akai su gida.
Ana saukowa masallaci suka wuce Kano din .
Gidan su makil da jama'a ana wani sabon bidirin.
Kano ta Kai ta kawo unguwar ta cika makil....... Isowarshi yasa garin da unguwar Kara rikicewa..... Yayi ma Aunty Salma waya da Hajiya rukayya Bako da su zo su dauki Amarya a tafi da ita can cikin dangi.....
Har lokacin Bata daina kuka ba, bayan ta shirya sun fito kawai ta hango su Aisha Nan ne zuciyar ta, ta Dan saki.
Bai yarda ko da wasa ta ganshi ba.... Acan aka kaita inda Hajiya... Nan fa ta ringa ganin gata da tarairaya......karfe hudu su Aisha suka tafi ba tare da ta sani ba, ya masu Sha Tara ta arziki Maryam duk ta gigice hada kukanta.
Karfe takwas aka shirya wata kwarya kwaryan dinner wacce har taso tafi ta Abuja danginsa sun yi namijin kokari.
Sai basarwa yakeyi, ita abun ma sai ya ringa Bata mamaki ganin bai waccen zakewar ko me yasa yake ma Yan Kano Isa da takama?.
Sha daya nayi yace a tashi haka dare yayi.
Suna fitowa ya shige mota da Amarya sukayi gida kawai......
Hannunsa da nashi rike maimakon taga sunyi bangarenta Wanda aka kaita dazun sai taga yayi nashi da ita.
Gabanta ya bada ras!
Suna shiga falon farko ya saki hannunta ya garkame kofa ya zare key ya kalleta muje sama ko?............✍🏼😄
Ayi hakuri da kadan jiya biki nayi na babban Abokina, aminina Kuma kanina sannan dan'uwana. Ayi masu fatan Alkhairi please.
*ibrahim and naja'atu*
*Zainab wowo ce kawar rukayya Bako danbatta ( Allah ya raya Miki sauda da Salma ya Sanya masu albarka amin*💖
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
3⃣0⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *MOM SAUDA AND SALMA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
*NA SADAUKAR DA LABARIN WA ZAI FURTA GA DUKKAN FANS DINA MASU SON LABARIN WADANDA KE GROUPS DA WADANDA BASA CIKI AMMA SUNA KARANTAWA*
******************
*KANO NIGERIA*
....... Ya dan yamutsa fuska ya rike hannunta suka Fara tafiya a hankali, yana Jin yanda hannun nata ke karkarwa tana kyarma.
..... Suna hawa step daya , biyu ya runtse ido ya saketa da sauri ya duka tare da dafe ciki .....Bilkisu cikina.
Ta zaro ido da sauri cikin tsoro saboda tun a party taga yanayin sa duk ya canza, ta Dan duka itama tana leken sa cikin ke ciwo?
Ya daga Mata Kai da kyar.... Innalillahi ta fada tare da kamoshi suka Mike...... Tafiya sukeyi da kyar da kyar, ya Dan kalleta Ina Jin yunwa ce Bilkisu rabona da abinci tun jiya da safe...... Subhanallah ta fada a hankali.
........... Katon daki ne yasha kayan alatu, makeken gado da wordrop ga wasu irin kujeru a gefe babu tarkace a dakin amma ya tsaru da kayan kece raini.
Ga mamakin ta an jera kayan ciye cite bisa kafet din.....ya tafi luuuuu ta Kara taro Shi tare da fadin *Na shiga uku* da karfi.
Suka Fadi rikichaaa bisa carpet din saboda Bata da karfi ko kadan...... Ya riketa gammm idanun sa rufe *Bilkisu cikina*.... ..Anwar ko dai a Kira sadeeq muje asibiti.... Kiban abincin sa naci Dan Allah ya nuna wurin da hannu.
Da sauri ta janyo dan table din da suke sama.... Ya Kara dafe ciki Fara bani something liquid please...... Ta dauko robar fresh milk Mai sanyi ta Mika mishi ya kafa Kai ya shanye, ta bude wani glass bowl sai ga dambun naman kaji ta Mika mishi ga dambu kaci....na koshi. Ta zaro ido Dan Allah kaci Anwar tunda har ka gano matsalar ka yunwa ce... Bazan ci ba ya fada da sauri..... Saboda me?
Saboda ke bakici ba .... Zanci kaci tukun...... Bazan ci ba sai kinci.
Zata Kara magana ya ce Miko madarar, ta Miko da sauri tunanin ta sai Kara ne, ya ce okay shanye duka sai ki ban naman.
Tayi shiruuuu, ya Dan kalleta mayar idan bakyaci duk mayar dasu...... A'a Zan sha ta kafa Kai..... Itama kusan abincin rabonta dashi tun jiyan.
Tana ajiyewa ya tura Mata naman ci sannan yasha mur Yana yamutsa fuska...... Tayi shiruuuu...... Kawai ya Mike da gudu yayi toilet ta jiyo Yana kakarin amai.... Hankalin ta ya tashi matuka lallai Anwar baya lafiya ta mike tsaye ta kura ma kofar ido...
Ya fito Yana layi ta karasa da sauri ta rikoshi sannu ko dai za a je hospital Anwar??...... Matsalata yunwa ce Dana ci shikenan kinsan ni bana wasa da abinci.... Na sani ta fada tana kamashi lokacin da zai zauna.... Ta tura mishi naman kaci Dan Allah ....... Wallahi bazan ci ba sai kinci ke meye Kika ci?
Meye acikin can?
Ya nuna cooler ta janyo da sauri ta bude..... Peppé soup ne okay zuban acan, ya nuna plate..ya dafe ciki tare da dukewa Yana matse ido.
Ta dauko duk ta gigice ta zuba tana gamawa har lokacin bai dago ba, ya ce maza shanye ki zuban nawa a ciki...
Ba yarda ta iya saboda tasan Anwar da kafiya, itama yunwar duk ta addabeta ba yanda ta iya ne, Dole ta dage sai gashi ta shanye tas!, Ta zuba mishi ta mika mishi, ya dan kalleta ya ce kafin na gama kici dambun nima Ina son cin sa.... Shima ta janyo ta Fara tsakura........ Haka haka sai ga Bilkisu tayi Nat! Hada uwar gyatsa.
Shi kuwa Wanda ta zuban ya turo ya ce bai iyaci ya kwanta Yana murkususu....... Ta karaso da sauru kamar zatayi kuka .....Anwar ko dai muje asibiti.... Karki damu da nayi barci shikenan.... Ya Dan gyara ya kwanta ruf da ciki ya juya kawai.
Ta zabga tagumi kawai sai Kuma ta Fara kwallah. Yana jinta tana ta sharbe..... A hankali taji Yana saukar numfashi alamar yayi barci, ta Kura mishi ido.... A hankali barci ke neman daukarta itama, ta Fara gyangyandi....... Barawo Bata San ya sace ta ba .... Yana kwance yaji alamar hannunta.... Ya Dan juyo sai kawai yaga ta yi barci....... Ya danyi dariya ya tashi zaune...... Duk plan ne yayi don baisan ta Ina zai tarbo rigimarta ba.
Ya janye kayan ya koma gefe ya zuba ya cika cikin sa ya cire kayan say ya watso ruwa ... Yayi tsaye kanta Yana zullumin Allah yasa idan ya tabata kada ta tashi.
Sai da ya tabbatar ya gama komai ya kashe fitila sannan ya zukunna ya sungumeta a hankali a jiye bisa gado, ta saki ajiyar zuciya tare da gyara kwanciya barcin ya riga ya dauketa.....ya rage sanyin A.C saboda dakin yayi sanyi da yawa ya Kai hannu a hankali ya Fara cire mata jewelries dinta ..... Yaci gaba da zuge zip......... A firgice ta bude ido.....amma Ina is too late to cry... Zata kurma mishi ihu ya yi saurin rufe bakin da nasa..... Ta rasa inda zata sa kanta....ya riga ya cimmata.... Wasu zafafan hawaye kawai ke fita..............
Ya saki ajiyar zuciya a hankali ya Kara rungumeta a kirji ya lumshe ido ya kasa magana baya iya cewa komai..... Tayi tayi ta tureshi ta kasa ya riketa gammm. Ta Kara sakin kuka ta sunne Kai jikinsa, duk jikin ta yayi tsami....... Yaja blanket ya rufe su..... Ajiyar zuciya kawai takeyi Shi kuwa ya rasa abin yi duk ya gama kidimewa ya kasa kwakkwaran motsi..... Zuwa can yaji ta Fara sakin numfashi a hankali alamar tayi barci....ya Kara mannata jikinsa kirjinsa na harbawa a hankali..... Shikam cikin kunnensa aka Kira sallah..... Ya zame a hankali ya fada toilet.
Kasa zuwa masallaci yayi. Ya saka jallabiya Mai karamin hannu ya feffesa turaruka ya shiga wani daki ya fito da doguwar Riga, pant, bra da under skirt ya ajiye Mata bisa abun sallah..... ya koma gadon ya shige bargo ya Kara janyota jikinsa......
Barci Mai nauyi yayi awon gaba dashi.
Tafi mintuna goma da farkawa..... Tayi shiruuuu ta tabbatar da lallai barci yakeyi ta zame jikinta a hankali ta sauka gadon, tayi toilet da sauri..... Tana shiga ta zukunna ta Kara sakin kuka.... Sai da tayi Mai isarta sannan ta fada cikin kwami.
Ba wani extra towel Dole Wanda yayi amfani dashi ta daura.
Ta leko a hankali har lokacin barci yakeyi ta sadado ta dauki kayan da ta hango ta koma da sauri....
A toilet din ta shirya, ta fito. Tana cikin yin sallah ya farka...... Lokacin da ta sallame taji motsinsa sai kawai ta koma tayi sujada Bata Kara dagowa ba....... Ya kyalkyace da dariya ya taso.
Tana Jin Yana yowa inda take sai kawai ta Fara kuka......
Ya sungumeta yayi bisa gado Yana fadin ai na Sami Baki yanzu Zan bada hakuri wannan laifi Dana tabka....... Ta sunne Kai.
Ya dagota Bilkisu Allah yayi Miki albarka ya sa daddy da mommy aljannah firdausi... Hakika sun Baki tarbiyya Mai kyau a rayuwa.
Ya rungumeta kiyi hakuri wannan Shi ake Kira *Aure* Kuma wannan kadai zai tabbatar Miki da *how much I love you* kinji ko?
Ta yi shiru.....
Lafiyata Lau jiya Yar dabara nayi ki Samu kici abinci saboda na tabbatar bana iya kyaleki jiya Kam .....
Zo muje ya figi hannunta...... Tafiya sukeyi bayan gidan suka zagaya can...... Sai gasu sashen Hajiya.... Tayi saurin janye hannunta... Yayi dariya kunya kikeji?
Idan Kika ringa wannan sum sum din Zaki to nawa kanki asiri ace jiya..... Ta Kai mishi duka dai dai hajiyar na fitowa.... Ya buga tsalle Yana dariya... Hajiya ta washe Baki...... Bilkisu mijin ake duka?
Ta kusa Suma don kunya ta zukunna da sauri ta ce *Ina kwana*
Ta yi Yar dariya lafiya Lau kuxo ga break din can......
Sai kusan azahar suka bar sashen ta dan sake kadan....
Suna shiga ya rikota zo ki gani..... Yabi da ita wani corridor suka shiga wani falo ya ce nan ma naki ne fa, ya bude bedroom din sai ga wasu irin set na gado royal masu kyau gefe jakun Kuna ne set talatin da shidda ya ce ga lefen ki Zaki gani Yanzu ko ba Yanzu ba?
Ta sunne Kai jikin sa kawai.... Ya danyi dariya *Bilkisu kunya*...............
Ya kamota ya zauna a kujera ita Kuma tana bisa cinyarsa.
Gaskiya kin saka ni farinciki Bilkisu naji dadi jiya har mutuwa nayi na dawo..... Bata San lokacin da ta kyalkyace da dariya ba .... Shima ya Kama dariyar ya ce Allah kinji nayi magana? Ai kasawa nayi.
... Next week zamu tafi Dubai a can zamu zauna Ina da gida a can, sadeeq zai ringa taking care na business din Nigeria tare da taimakon su Suleiman...... Ni Kuma Zan ci gaba da duba na sauran countries din nida su Alhaji murtala..... Kina son Zama Dubai?
Ta danyi murmushi ta ce um.Daga nan Zaki dauki Yan aiki ko kina son na can?
Duk yanda ka gani.... Yayi murmushi.
Zan baki appointment idan result ya fito kema kina amsar albashi kin San hausawa na cewa *Da namu gwamma da nawa* ya karasa maganar Yana dariya.... Kin San duk wakokin bikin Nan nafi son wakokin da *Aliyu nata* yayi Mana?
Ta danyi dariya gaskiya ya iya Waka, ya ce sosai ga babu zagi, ba habaici babu maganar banza yaron ya zo da basira Mai tsafta Shi yasa ake rububinsa..........
Ya Dan taba cikin ta Allah yasa jiya Yara sun shiga...... Ta soke Kai jikinsa..... Ya kyalkyace da dariya.............✍🏼
*KARSHE*
Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba.
Muna rokon Allah ya karemu daga cututtukan zamani.
Abinda muka karanta Allah yasa mu amfana da lesson din ciki na Shi mutunci Riga ne, ya kamata mu sani kunya na daya daga cikin abinda ke daga darajar mace a duk inda take.
Kwadayi baya Kai mutum ko Ina sai tushen wulakanci da Kuma nadama.
Mai kudi da talaka duk bayin Allah ne, masu kuci da ke nuna Basu iya rayuwa tare da talakawa ku sani rayuwar dasu bazai rage ku da komai ba sai dai na ku Kara samun daukaka, mutuncin ku zai karu, zaku Sami lada a wurin Allah. Akwai fa'idoji da dama masu amfani akan Haka. ..... Abinda na hakake a labari shine Jan labari ba shine ba, matukar sakon da kake son isarwa zai je to a layi biyu ma ya wadatar...... Kadan Mai albarka yafi Mai yawa yuyuyu.
Rubuta batsa, maganganun banza da rashin kunya ga labari ba shine ke kawo wa mutane kwarjini ga labari ba. Ma'anar labarin , tsabtar sa da Kuma kyautata rubutu saboda Allah. Duk abinda muka rubuta zamuyi depending din sa a wurin Allah. Ya Allah kada ka kamamu da laifin da mukayi bisa ga tunanin munyi da kyakkyawar niyya. Allah ka yafe Mana ka shirya Mana zuri'a.
Qalubale ga itaye, ku daina tura yaran ku makaranta ba tare da binciken abinda sukeyi ba, ku ringa Kai masu ziyarar bazata Kuna saka ido ga yaranku musamman mata, mazan ma abin kula ne Yanzu.
Yan Mata ku sani bin namiji ka nuna kana sonshi bance haramun bane Amma ku sani kunya ma cikon Imani ce, duk abinda musulunci yazo dashi muna daukarshi da muhimmanci .
Allah ya sada mu da alkhairi.
Wanda labarin bai mawa ba sai yayi hakuri.
Sai mun hadu a wani sabon labarin bayan sallah idan Allah ya kaimu.
*Zainab wowo*💖
*MAMAN AL'AMYN, AMINATU AND ABDALLAH*