*_BURI 'DAYA_*
_MAMUHGEE_
_HASKE WRITERS ASSO💡_
*_1_*
Bismillahir-rahmanir Raheem.
Sauri yake faman zubawa Amma yanda saurin nasa yake tamkar Yana gudune sbd yanda ko gani bayayi sosai ga babbar rigarsa sai cika takeyi da iska tana qarawa,
Da safe kafin yafita jin zuciyarsa yakeyi fes sbd tunanin yau ranar sa'arsace tunda zasuje maula gidan mai arzikin da yafi kowane mai kudin jahar kudi harma dana wasu jahohin saigashi masifar datafi ha'darin mashin bala'i ta afko masa Dan gwara yasan sama mashin yayi dashi ya zubar akan abinda rashin hakurinsa yaja masa ayau din,
Yana shanyo kwanar layin gidansa wani mugun zufa ya yanko masa ya tattaro kuzari da qarfin hali yacigaba da tafiya Yana kallon tarin kalolin 'yan ta'addar dake cike da qofar gidansa sun baje sunashan iskar makeken bishiyar durumin dake qofar gidan kusan su goma Sha biyar kowanne da kalar mugun makamin dake soke cikin qugunsa ko wani sashe na jikinsa Wanda duk qaddara takaisa shiga huruminsu yanxune zasu yiwa rayuwarsa illa Kuma ba Wanda ya isa ya tanka sbd hukumar ma da ikonta suke aiki sbd zakinsu shine amintaccen yaron DIKKO DILLA.
Wasu daga cikinsu fuskokinsu cike sukeda zanen Sara ko Suka haka jikinsu kusanma Babu Wanda fuskarsa bazata saka mai qaramin qarfin jini zawoba sbd Sam babu alamar wasa atareda fuskokinsu ga wani irin warin daga da wiwi dake tashi tun daga farkon layin unguwar shiyasa yawanci duk Wanda yake Dan asalin gari yasan anguwar ba wurin ganganci bace anguwar sarki ZAKI NEYO ce Sam ba'a mata garaje.
Da gudu gudu sauri sauri yaqarasa shigowa gidan tsohuwar babbar rigarsa kalar ruwan madara data koma kalar brown tana sake dibar iska sbd sauri dayake diba kamar zai tashi sama musamman yanzu daya qara ganin bataliyar 'yan daban dake qofar gidansa kamar qofar gidan wani qaura.
Yana shiga tsakar gidan sbd tsantsar rudewar dayake ciki ya kwashi wani mugun tuntunbe saura qiris ya kife cikin garinda iya talatu ta shanya na kayan mata datake siyarwa duk da duk rabi garin kukane take zubawa sbd yayi mata afkin siyarwa.
Zaune take tana lissafin jarkar tsimin data Saida wadda duk rabi jollyjus ne ta zuba aciki shima sbd afki.
Kallonsa tayi amatuqar sheqe cikin takaicin yanda ya tashi goga mata asara ta hanyar barar mata da gari a 'dan hasale tace"
Wai meye hakane kaketa muzurai kana rawar jiki kamar 6arawon daya ha'diyi kunama?,
Yanzu wannan garin dakake Shirin bararmin kasan hasarar nawane zaka jazamin Wanda nasan ko shekara zakayi kana sana'ar taka ta mutuwar zuciya bazaka Tara kudin biyana ba inyi magana jarabben sarkin gidannan yace bayason hayaniya kokuma yakamamin dabbobi yasa ayanke masa inaji Ina gani qatti suci banza.
To wlh banshirya hasaraba kusa Dan haka kafita idona inrufe.
Takalmin hannunsa ya fitar daga cikin babbar rigarsa data gama jiqewa da zufa,
zufa na qara tsatsafo masa Yana zare qananun idanuwansa dasukafi kama Dana Chinese din hauren qasa yace"
Qaddara takaini daukar aron takalmin ZAKI NEYO wainda kikaji dahiru yace dubu biyar suke nafita dasu wlh sun katse fata fata duka qafar biyu gurin gudun mahaukatan Karnukan da alhaji dikko dillah yasa aka sakarmasa ga yan maula da mabaratan dasuka tarar masa qofar gidansa duk da tarin yan sandan dake gadin gidan.
Wani irin sabon qululun baqin ciki da takaicine ya quleta tana watsa masa wani mugun kallon takaici baqin ciki yahanata ce masa qala sbd duk iya quluwa da baci ranta yayi sbd sanin masifar da hakan zai jawo
ta miqe ta tahau tattara kan akuyoyinta da kajinta dake walwalarsu filin tsakiyar gidan Dan tasan yau akwai saukar aradu a gidan Dan yau ko butar gidan saita ci uwarta idanba Allah ya tsareba baresu
Akuyoyinta da kajinta kuwa tasan tsaf zai take mata kawunansu su mace abanza,
Tana zaman zamanta rukayya taje Lagos ko wata shegiyar qasar ta hado jini da kafirai kokuma qila wata qabilar anxo anhaife mata masifar daba ita kadai ta addababa har yan gari da anguwa Dan kuwa neyo ba ubanda baya tsoro da shakkarsa ga wani irin kwarjini dayake qarawa mutane tsoronsa.
Wani Dan dakin kaji ta gargadasu gabaki daya ta rufe da kwado ta zare mukullin ta dawo tafara tattara garinta tana kwashewa cikin takaici da baqin cikin dake tafasa zuciyarta ta bude murya tace"
NADIA uwar uban me kikeyi a bakin murhun haryanzu dabazaki taso kitayani tattara duk wani tattalin arzikina dake tsakiyar gidan nanba kinaji mara danganar ubanki ya ballo Mana balain dayafi 1990 masifa.
Aje plate din robar dake hannunta tana fifita wutar murhu dashi tayi ta taso gabanta na matuqar faduwa sbd jikinta dayayi sanyi dajin abinda babansu yayi Dan tanajinsa duk abinda yake fadawa iya talatun koba komai tasan idanba Allah ne ya fiddataba akantane zaifi sauke haushinsa tunda itace mara galihu agidan Dan idan yafara kowa shigewa daki yake ranar bamai fitowa saiyagama fushinsa ya sauka ita kuwa dole take fitowa sbd balain iya talatu shiyasa idan tafito yake sauke Rabin haushinsa akanta ga wani irin mugun tsoronsa da shakkarsa da Allah ya halitta a dukkanin zuciyoyin 'yan gidan harma Dana waje saidai zata iya cewa itakam tsoronta yafi nakowa duk da dai duk balai da msifar iya talatu da duk anguwar ake tsoro itama shakkarsa takeyi.
Jikinta na Dan rawa tafara tattarawa iya talatu kayanta..
Da 'yar waqar sani sabulu wata 'yar budurwa tashigo gidan taci ado cikin Riga da skirt na atampar sheraton 'yar dubu uku da dari biyar fuskarta a kimtse tsaf da kwalliyar dataji hoda da foundation datai mata kyau ba laifi da Jan jambaki 24 hours hannunta riqeda Jakarta da 'yar wayarta vivo mai Dan dama dama sai qamshin bokhour takeyi daga gani cikin nishadi tadawo.
Cak ta tsaya tsakiyar gidan tareda kallonsu cikin mamaki da 'yar fargaba ganin sai tattara kayan tsakiyar gidan sukeyi fuskar iya talatu ba alamar rahama ko kadan ta maida kallonta kan babansu dake tsaye gefe sai zufa yakeyi kamar Wanda yaci wuta takalli iya talatu tace,
Iya lafiya kuke kakkamta kaya rana tsaka?
Harara iya talatu tafara watsawa dattiya dake tsaye har lokacin kafin tace,
Rashin hakurinsa yakaisa ga daukar takalmin ZAKI NEYO yasa yaje yawon maula aka hadosu da miyagun karnuka sukaiwa takalmin fatafata.....
Kallon babansu tayi cikeda takaicin Rashin danganarsa da ako yaushe baya jawo musu alkhairi sbd fargaba da tsoron masifar daya jawo musu basujiba basu ganiba ta turo baki tace,
Nikam baba meyasa bakason ko yaushe a zauna lafiya agidannan gashi yanzu mutum saiya kwana biyu bai wani dogon motsiba sbd tashin hankalin yaya neyo
Yanzu wlh ko mai neman aurena yazo qofar gidannan saiya gwammaci karo da mahaukacin matashin kare akan fushin wannan abin daka yi baba.
Kallon iya talatu tayi cikin takaici tace,
Ni wlh nakoma gidansu anty saratu sai dare ko gobe zandawo Dan wlh bazan yarda a mari wannan kyakkyawar fuskar tawa abanzaba tunda babu Wanda yake siyamun mai.
Juyawa tayi rai abace cikin haushi da takaici ta fice tabar gidan tana guna guni sbd tasan tsaf da marin neyo gwara mashin yayi sama dakai.
Nadia kuwa cikin sanyin jiki duk takai ma iya kayanta daki tadawo ta gaban baban nasu dake tsaye Yana muzuran ido cikin mirsisi yace,
Ke ungo nan yi musu dubara da allura da zare ki dinkesu kikai dakinsa ki ajiye masa Kuma wlh duk rintsi Kar shegen dayace nine nasakasu.
'dagowa tayi da sauri takallesa da manyan fararen idanuwanta cikin tashin hankali.
Harara ya watsa mata yace,
Bazakiyi bane kike kallona kamar nace ki kashe mutum.
Sunkuyar da kanta tayi tareda girgizawa idanuwanta na cikowa da hawaye ta karba da hannu biyu ta wuce.
baza babbar rigarsa yayi tareda kada mata iska ya fada dakin iya talatu Yana sharce zufan daya kasa daina jiqasa.
Nadia kuwa bakin akurkin dakinta ta zauna bayan tadauko allura da zare tahau yiwa takalman kwaskwarima jikinta na matuqar rawa sbd sanin yau kwanan wahala zatayi idan yadawo yaga wannan dinkin a jikin takalmansa bayan antsinka.
'Daga takalmin tayi ta qura masa ido tsawon mintuna hudu kafin ta sake sakin ajiyar zuciya akaro na Babu adadi bayan zamanta na Shirin dinkin takalmin.
Iya talatu dake zaune ha'deda rai zuciyarta na qara cika da takaicinsa ta harari qafafunsa cikin quluwa tace"
Kaga nidai yi daga can gefe karka takani da wannan qafafun naka dasukafi kama da kofato,
Kuma wlh kasani matuqar Zaki yayi mummunan sauke mana balainsa aka gogamin asara wlh saikaji a aljihunka da cikinka Dan wlh sainayi sati banbaka tuwonaba tunda zuciyarka tagama mutuwa Sam ko kunya bakaji kullum Kaine daga ha'darin mashin sai karo da keke kokuma gudun fanfalaqin ceton rai duk gurin yawon maular mutuwar zuciya.
Bai kulataba yahau cire babbar tsohuwar rigarsa dake sharkaf da zufa duk saita qara canxa kala.
Ficewa yayi ya dauki buta ya nufi bayin dake tsakiyar gidan ya fito ya zauna ya wanke qafafunsa da ako yaushe talatu ke shammata sbd shegen yawonsu dashima yasan yanadashi sbd idan ya bazama cikin gari yafara yawo sai Rana ta fadi yake dawowa gida wanda wani lokacin wahalar banzace yakeyi sbd haryagamo gantalinsa yadawo bayasamo ko nera biyar.
Yana cikin wankin qafar yajiyo qarar fito Yana dosowa cikin gidan qafa daya dama ya wanke zaifara ta biyun yaji fiton Yana sake dosowa cikin gidan atake ya aje butar ya miqe sukai ido hudu da Nadia dake zaune tana kallonsa cikeda tausayin kanta na aikin daya data.
Cikeda borin kunya ya dauke Kai daga kallonta ya nufi dakinsa da iya talatu yashige bai tsaya wanke dayar qafarba tunanin qila Zaki ne yadawo duk da yasan Zaki Sam baya fito sbd tsabar mulkin dayake murzawa a dabanci Dan ko wani hakimin bai kaisa baza mulkiba atasa duniyar ta 'yandaba Wanda shiyasa ake kiransa da sarki Zaki.
Itadai iya talatu Bata sake kallonsa ba sbd tana lureda duk hankalinsa duk ba kwance yakeba sbd abinda yayi din Saidai bazatayi masa mgn ba qyalesa zatayi ai zakin shine daidan kowane dan banza na gidan Dana waje.
Cigaba tayida hada garin kayan matanta tana daurawa a leda batareda ta kalli ko inda take zaune Yana qoqarin shafawa qafafuwan nasa Vaseline kamar Wanda zaije wani gurin.
Lalah ne yashigo gidan Yana fito daukeda wata baqar leda ta kayan neyo daya daya karbo masa guga sbd akwaisu da babbar hidima sbd AMBY DIKKO DILLA na gari Kuma zakinsu shine babban yaronsa dayafi yarda dashi da boyayyun ayyukansa.
Dakin zakin dake farkon shigowa ta zauren gidan ya shiga ya ajiye masa kayan kan katifa yafito ya jawo qyauren dakin.
Harzai fice ya dakata tareda juyowa da sauri ya kalli Nadia dake riqeda takalmin Zaki da aka siyo masa daga kaduna....
Baki ya sake cikeda mamaki da tantama ya dawo gabanta ya tsaya Yana kallon hannunta dake riqedasu Yana rawa alamar amatuqar tsorace take.
Cikin tsananin mamaki da muryarsa irinta riqaqqun yan ta'adda yace"
Wannan meyene a hannunki?? Yana nunawa da hannunsa sbd sanin ba magana takeyiba.
Jikinta har wani irin rawa yakeyi sbd tsananin halinda zuciyarta da gangar jikinta suke ciki
hannu na rawa ta daga zata nuna qofar dakin babansu saita tuno da gargadinsa tayi saurin sauke hannu tana sake qanqame takalman.
Amasife yace"
Ke ubanwane yace ki shiga dakin sarki harki dauko wannan takalmin Dan......zaro manyan jajayen idanuwansa yayi sbd sai alokacin ya lurada yanda suke ya hadiye wani yawu cikin jinjina mata yace"
Wlh idan ko sunana yafito acikin Wainda suka gani saina qarasa mayarda maraji bayan Rashin magnar dakike fama dashi.
Ficewa yayi Yana jinjina mata Dan kuwa ba qaramin jarumtar tabama takalmin tayiba.
Yana fita qofar gidan atake ya tseguntawa Nanu Yana cewa"
Babahh yaufa akwai saukar aradu a cikin gida da anguwarnan mubi ahankali Dan kuwa yau antabo sarki inda ba'a tabowa.
Cikin gidan kuwa jiki a salube ta tashi ta sidada dakinsa ta ajiye daga ciki bakin qofa tadawo cikin gida taci gaba da aikin tuwon iya talatu na siyarwa da dare jikinta amatuqar sanyaye Dan har wani zazzabi takeji.
##Mamuh..
*_Mamuhgee2_*
Iya talatu na gama daurin garinta na mata ta tattara ta zuba cikin jakar datake yawon sana'ar kayan matan ta miqe batace masa qalaba musamman ganin magriba ta gabato tana saneda idan ba Allah ne ya rufa asiriba bazai fita sallar ba Saidai yayi agida.
Daga baqin qofar dakin ta tsaya itama zuciyarta na qara tafarfasa takalli Nadia tace"
Ke Kinga bar tuwon nan Dan kuwa ko anyisa kwantansa zanyi sbd Babu mai gigin zuwa yau gidan nan idan sarki yadawo yafara sakin boma boman balainsa.
Babu 6ata lokaci ta sauke qatuwar tukunyar tuwon miyar kuwa tunda sunyi sai ayi tuwon siyarwar gobe da ita Dan dama iya talatu na hakan acewarta miyarma tafi zaqi sbd magi da kayan miyar sun qara tsuma.
Ana Kiran magriba tagama tsare tsakiyar gidan da bayinsu Wanda wannan Kuma qaidar zaki ce dole ake share gidan da yamma awanke masa bayi sbd wankan maraice duk da bayin Babu siminti haka take kelaya masa ruwa ta wanke.
Gama alwalarta keda wuya ta hangi JJ yashiga dakin ya Zaki da wata irin qatuwar sharbebiyar wuqa Mara kyawon gani atake hankalinta yatashi ta miqe sbd dazarar kaga JJ to sarki nanan sbd shine amintaccensa shikuma Babu abinda yakeyi Saida jj sbd JJ yakasance tamkar wani sashe na jikinsa da rayuwarsa,
JJ shine mutum na farko dayake gani tamkar amatsayin 'dan uwansa na jini wanda yasani kowane balai JJ zai iya runguma akansa,
Sunsha fafatawa da manyan 'yan taaddar wani yankin JJ ke kare masa kowace irin Sara da sukane shiyasa jikinsa da fuskarsa kusan koina dinkine na sare sare.
A sulale tashige dakinta daya zamto na mamarta tun tana raye ta shimfida tabarmar sallarta ta kabbarta da sauri sbd tasan daga yanzu komai na iya faruwa.
Iya talatu na fitowa alwala ta hango fitowar JJ daga dakinsa ta sake hade Rai takaicin dattiya nadawo mata sabo ta zauna Babu Bata lokaci tayi alwala ta miqe tanaji yaro na sallamar abashi gishiri da daddawa na saba'in tayi kamar batajiba ta fada daki tana mitar"
Yanxu ga ciniki na bibiyar mutum Amma ba hali sbd ni nafi kowa asarar rayuwa ta auren Dan maula,acikin masu maularma Mara dangana.
Shidai dattiya najinta baice qalaba yatayarda sallarsa yafara sbd yasan talatu idan tafara mitarta saita Hana duk wani jindadinsa walwala.
Babban durom 'dinta dake gefen randar tsakar gidan cikeda tsiminta data zubawa jollyjus harda qarin tiara sacet 'daya taji yayi wata irin qara alamar ball akayi dashi atake ta tayarda sallah tana hararar bayan dattiya dayaqi sallame sallah bayan tasan yagama.
Wata irin kakkausa,budaddiyar murya dake natse da iko tareda tsatsauran Rashin arziki yace"
Duk ubandake gidan nan yafito kafin wlh yanzu nasa bulldozer tazo tabi takan gidan gaba daya...
Wani yawu dattiya ya hadiye Yana fici fici da ido cikin qarfin hali irin na yanuna sallah yakeyi yayi gyaran murya alamun sallah sukeyi.
Sake daga murya yayi yace"
JJ kiramin anny awaje yazo duk ubunda ke cikin gidan nan idan bai fitoba ya sakar musu bingo yaci uwar kowa da kowa yafitomin dasu.
Assalamualaikum assalamualaikum""iya talatu da dattiya Suka sallame sallar atare tana takallesa tace"
Wlh katashi kafita kafada masa gaskia tun kafin asako mana shegen bingo dinnan yazo yayimin banna kana gani wancan karon inaji Ina gani aka sakosa yayimin kaca kaca da katifa tayi kamar injin aka sata aka 6arza.
Kallonta yayi Adan hasale yace"
Wai talatu meyasa bakida Imani ne Sam bakya girmamani amatsayin mijinki kullum sai Rashin da'a.
Wani sheqeqe takallesa tace"
Yanzune kake maganar miji da mata kanaji 'dan ta'addar 'dan qanwarka yanamin fatali da kayan tattalin arzikina.
NADIYA data gama sallah a sadade tafito tanabin bango hannuwanta a fuskarta sbd tasan itace zata fara Shan mari.
Fitowa dattiya yayi Yana zaku'do kafada fuska da alamar tambaya yace"
Kai zaki banason Rashin arziki meya faru kake mana barazana da bulldozer da mangaribar nan iyeee?
Wani kallo zakin yayi masa da manyan idanuwansa masu rikita mutane da kwarjininsu atake yagama laranto yanayin baban Kuma yasan duk duniya Babu ubanda keda jarumtar dazaiyi qalula yadauki abinsa bada izininsaba sai baban kallonsa yagama na mintuna kafin ya juyo gurin Nadiya data rabe a bango kamar munafuka atake 'dinkin zare da allurar dake jikin takalminsa Suka dawo masa yasan ba aikin kowane Dan iska bane sai ita atake ya fizgota ya kifa mata wani lafiyayyan mari tayi saurin zubewa qasa tana girgiza masa Kai alamar yayi hakuri hawaye na cikowa idanuwanta.
Cikin muryar bada umarni yace"
Wlh kika sake shiga huruminda banakiba saina karya wuyanki nabawa bingo namanki dagake har ubandake dake saki.
JJ yayiwa wani kallo yace"
Kasan mezakayi akan hakan.
Juyawa yayi yafice Yana murda zaren layar maganin qarfe dake daureda murdaddiyar qwandar hannunsa kasancewar Babu riga ajikinsa sai baqar singlet sa dogon wando baqi Wanda kusan kullum sune kayansa shiyasa murdadden jikinsa ke sake sakawa mutane shakkarsa.
Kallon baba JJ yayi tareda sake wani lalataccen murmushi kafin ya juya yabi bayan Zaki Yana 'dan kallon gefen Nadiya sbd jin sheshekar kukanta data fara bayan barin Zaki gurin.
Ba kunya baban ya kalleta cikeda qarfin hali yace"
Ke banason shashanci me akayi na kuka?maza maza tashi kibar nan.
Miqewa tayi ta nufi dakinta ta zauna inda tagama sallah tanajiyosa lokacinda ya sauke wani irin numfashi mai qarfi Yana cewa"
Waiiiii fitar kutso.
Baza rigarsa yayi ya wuce waje hankalinsa kwance ya nufi qofar gidan mal idi maqwafcinsa dasuke firar dare tare harma dacin tuwon dare tare hakama sana'arsu guda wato yawon maula.
Wani tsakin takaici iya talatu tasaki data fito taga yanda tsakar gidan yayi jajir da kalar tsiminta dayayi fatali dashi tana tattara robobin durum din daya fashe tace"
Wlh dai ruqayya kin cuci rayuwata nidai ko bayan mutuwarki banhutaba Dan gwara ace kinanan da wannan masifar dakika barwa jama'a,,
Kai wlh Allah yatsinewa yawon duniya.
Itadai Nadiya najinta ta lafe sbd kullum idan aka tabo iya saita tsinewa yawon duniya dayayi sanadin samuwar yah Zaki wani zubin kuwa tata uwar ake zagi.
Dakinsa yakoma zuciyarsa ba wata doguwar damuwa sbd yau babbar ranace agaresu sunyi nasarar qwace mulkin shiga da fice na duk wani baqin mai ta hanyar ruwa Wanda yasa gobe sukeda babbar hidimar bikin murna Wanda alh dikko yasaki wasu mahaukatan kudi aka tsara shiyasa kawai yau baiyi wani daukar matakiba duk dai za'a Dan koyawa baban hnkali badan haka ba wlh da yau kowa saiyaji ajikinsa ko dukiyarsa.
Qarfe goma da arbain baba yataso daga gurin fira yayo gida Yana shigowa Kai tsaye ya nufi butar dake bakin gurin wanke wanke Yana juyowa yayi ido hudu da bingo Yana wani irin shesheka Yana zaro harshensa dake dalalar yawun dake nuna tsantsar ha'darinsa.
Butar saki cikin tsananin tashin hankalin dabai saniba yace"
Ya salamu,,,ya azzizu....Wai menake gani haka..ke talatu...ke talatu..Nadiya.. Nadiya Zaki fito kosainaci gidanku idan nasameki.
Wani irin tsalle bingo yayi
Bai direba baba yayi wurgi da buta ya nufi dakin Yana isa qofar yajita gam alamar iya talatu ta rufe Dan dama tasan wlh Zaki bazai bar babanba.
Ganin bingo yayo gurinsa aguje ya nufi qofar fita yatararda an qargameta Yana juyowa bingo na yowar tsalle zan afko masa shima tsallen ya daga yayi gefe yakama katanga zai hau Amma kasancewar dattijanci yasa yakasa Amma Kuma bai fasaba Yana kama katangar yanaji hannunsa ya gwafce Amma bai tsayaba ba wata wata ya dire waje sai cikin kwatar gidan mal idi atake ya miqe Yana dingisawa ya fada gidan mal idi Yana rafka gigitacciyar sallama.
Kallonsa mal idi yayi Yana haskasa da fitila yace"
Lfy mal dattiya?
'dingisawa yayi Yana gyara tsayuwarsa sbd qugunsa daya riqe yace"
Haba mal idi yaza'ayi kabar kwata qofar gida haka ba'a ragewa gashi yanxu naje wucewa na fada
Yanxu Dan Allah idan banibane wani yaji ciwofa?""ya qarasa zancen Yana matse ido cikin duhu sbd tsananin zugi da qafarsa da hannunsa suke masa.
Cikin jimami mal idi yace"
Naji zan gyara kwatar kaje kajida kanka dai yanxu.
Cikin masifa yace"
Au hakama zakace??
To mal datti yanxu kakeson nagyara da daddaren kokuwa?nace zan gyara da safe.
Waiwayen qofa yayi Yana hararar idin cikin duhu Dan so yayi yace zai gyara yanxu saiya tayasa har bingo yabar gidan ga qafarsa da hannunsa sai shegen zugi suke masa,,,kaiii Allah ya tsinewa ubanda yayiwa ruqayya cikin Zaki dandai shikam Zaki yazame masa masifa da balai yanzu dabai guduba yanaji Yana gani bingo zai yayyage masa Kaya da mazaunansa ta yanda saiyafi wata baije yawon maularsaba..
MAMUH.
*_Mamuhgee3_*
Jan qafarsa data riqe yayi Yana 'dingisawa a duduqe ya nufi qofar gidan nasa Yana tura qyauren yaji yabude yasaki wata irin qwafa yana cewa"
Nibansan menayiwa ruqayya ba zataimin wannan sakayyar ta ha'do zuri'a da dangin marasa Imani gashinan 'danta zai kasheni kwanana Basu qareba.
Tunda yaji qofar abude yasan sunkama bingo dinsu shiyasa yashigo Kai tsaye
Itama iya talatu tsabar Rashin 'da'a ga miji sai yanxu daya gama hasarewa zata bude qofar dakinta.
Tsuke fuska yayi ya kwadawa Nadiya Kira tafito tana sunkuyar dakai sbd sanin dazu Bata fitoba daya kirata.
Ciki ciki yayi da qananun idanuwansa yafara zuba mata fadan Rashin arziki kafin yasata ta debo masa ruwa ya wanke jikinsa da duk yabaci da kwata ya dudduqa ya qarasa 'daki Yana sakarwa talatu nata fadan a kaikaice itadai Bata kulasaba sbd gabaki daya ranta har lokacin abace yake.
Haka Suka kwana kowa na hararar Dan uwansa.
Qarfe 6 na safe ta Dora ruwan kunu a babbar tukunya tahau aikin sharar gidan kafin ta bude dakin kaji da akuyoyin iya talatu Suka fito Suka hau walwalarsu a tsakar gidan tana cikin wanke wanke yashigo gidan wuyansa rataye da towel milk da brush tareda Colgate toothpaste.
Kallo daya tayi masa taci gaba da aikinta sbd batada muryar ko gaisuwa shiyasa iyakacinta da kowa ido.
Ruwa yadiba a qaramin plastic bucket yakoma dakinsa ya zura heater ya kunna ya fito qofar gidan inda yake cikeda yaransa wasu na karyawa wasu na wasa makamansu sbd taron yau.
Wata kujerar busashen katakoce dake kafe acikin qasar gurin alamar tariga tashiga qasa bazata taba daukuwaba ga sulbi sbd alamar dadewarta da qarkonta
JJ yayi saurin dauke wuqar daya Dora gurin Zaki ya zauna ya karbar wuqar Yana bin bakin kaifinta da ido yace"
JJ wannan qwamar taka yau cikin takalmina zan sata akwai Wanda dikko keson nayiwa zanen yorbawa agurin taron.
Dariya JJ yayi shida Nanu..
Nanu yace"
Sarki kowaye wannan za'ayiwa na yorbawa tasa taqare tunda sarkine dakansa zai masa aiki.
Wani irin murmushin gayya yayi Wanda ya lotsarda kumatunsa ya 'daga wuqar Yana kallo yace"
Yau uwarsa bacci zatayi tana sauke ajiyar zuciyar kukan dazata yini tanayi.
Dukkaninsu dariya Suka sheqe da ita suna"""Allah ya tarwatsa maqiyanka sarki.
Ruwa Nanu yakawo masa yafara brush dinsa daganan zaune sukuwa nan wasu Suka cigaba da gyara makamansu.
Kallon JJ daya qura masa ido yayi yasaki wani slow murmushi Yana jingina da bayan kujerar yace"
Yaya akayine magajin Zaki.
Cikeda jin dadi jj yashafo tarin sumar kansa da akayiwa kitson cuku bayan anyi dying dinta zuwa baqi da brown yace"
Neyo yau kwarjinin naka bazai Barima ko alh dikko yafika cikawa mutane idoba.
Murmushi yasakeyi Yana shafo gemunsa na tsantsar ta'addancinsa dayake tarawa ya miqe tsaye tareda nufar qofar gida zai shige yace"
Magajin Zaki Kaine kadai kakewa Zaki kwarjini bayan Kai Babu ubanda bazan ketawa rigar mutunci ba ciki kuwa harda tsohon najadun gidan nan.
Shigewa yayi jj yabi bayansa da kallo Yana girmama girman qauna da matsayinda neyo yakedashi arayuwarsa sbd shine yamaidasa mutum yacirosa daga basifa da balain dayafi ta'addanci,
Yazame masa uwa uba tareda cike duk wani gurbi na Dan uwa dayake buqata aduniya shi
yasa zai iya sadaukarwa da neyo rayuwarsa.
Wanka yayo yafito daga bayin tsakar gidan sanyeda threequater wando da qaramin tawul rataye a wuyansa.
Kallo daya Nadiya tayiwa qaqqarfan jikinsa dake bayyanarda qarfinsa,
Wani dogon tabone da sarar Adda yake zane a qirjinsa har zuwa gefen qugunsa Wanda aka ta6a yimasa lokacin daya fara haduwa da JJ sadai Wanda yayi masa sarar yananan yarasa qafafuwansa har abada Dan kuwa Saran rage yaran neyon sukaiwa qafafuwansa Allah yasa yanada kwana agaba.
Wannan tabo shine tabo 'daya dake jikin neyo sbd tsananin tsaron dake taredashi na yaransa Wainda Suka sadaukarda rayukansu akan sarkinsu.
Cikin wani tsinannan army three quarter da baqar riga Mara hannu data bayyanarda qwandarsa dake bawa baba tsoro yafito fuskarnan sanyeda baqin goggles yafito inda qofar gidan take cike dam da duk wani 'dan daba dake qarqashin ikonsa agarin kowane da kalar mugun makaminda ke soke ajikinsa atake guri yadau ihu da kirarin sai sarki.....
Wuqarda JJ ke miqo masa ya karba Yana sokewa cikin takalminsa Yana qarasawa jikin motocinda alh dikko ya Basu Dan hidima
Yana shiga JJ yashiga nan kowa yasamu Suka shiga atake Suka cike golf guda da bus biyu tareda Hilux 'daya Suka wuce cikin wani matsiyacin gudu dayasa mutane kakkaucewa da gudu suna matsarda kayan sana'arsu.
Baba ma Yana tashi yau din yaji qafarsa taqara tsami radadi take masa sosai ya dingisa ya fito tsakar gidan iya talatu dake zaune suna lissafin kudin kunu da Nadiya ta kallesa a dage tana dakatawa daga lissafin tace"
Wannan Kuma wane irin sabon salone kake mana gurgunta?
Qin tankata yayi yakalli Nadiya data sauke Kai Yana hada 'yan biyar biyar guri 'daya yace"
Ke tashi kaimin ruwa bayi nayi wanka inada gurin zuwa.
Tashi tayi ta nufi bokiti
Iya talatu tasake kallonsa tace"
Magana fa nayi kanaji kayi uwar shegiya Dani.
Tsuke fuska yayi Yana sake dingisawa yace"
Talatu wlh wata Rana Saidai kijiki cikin takaba tsundum matuqar ba rabuwa mukayi da Zaki ba,
Wannan masifa tayi yawa
Gabaki daya tsufa neman damqata yakeyi sbd masifar gidan nan,
Ga naki gana 'yayanki gana wannan sarkin dababu rawani sai neman gigita rayuwata yakeyi.
Kallonsa talatun tayi tana girgiza Kai tace"
Ai wlh kwadayinkane da zalamarka ta abin duniya takaimu ga haka,
Qiri qiri katura ruqayya aikatau qasar inyamurai gashinan takawo Mana abinda yaci uwar uban kwadayinmu ta mutu ta barmu da jidalin qaqa nikayi
Gashi kaikuma Allah bai samaka danganar tsayawa inda kakeba shiyasa muke azabtuwa muda tattalin arzikinmu konace tattalin arzikina tunda Kai bayan matacciyar tsohuwar rigar ba abinda ka aje.
Sake tsuke fuska yayi yace"
Wannan tattalin arzikin naki na hainci gwara na mutu da tsohuwar rigar tawa danayi irinta.
Yanxu dai naji wannan Ina kake cewa zakaje da gurguwar qafar?
'dan sake fuska yayi Yana cewa"
Yau wani gagarumin taro za'ayi daya hada kaf dukkanin qusoshin qasa dasukaci Suka tada wuya musamman sbd taron na alh dikko Dilla ne
Dan haka dole naje Dan kuwa yau 'yan maula ma kasuwarsuce
Bazan zauna acinye duniya badaniba koba komai da 'dingisarnan zan qara lankwashewa nafi kowa samu.
Baka daddara ba kenan""tafada tana hararar gefensa.
Yana kama hanyar bayi yace"
Daka mutu gwara kazama biri.
Bayin yashege Bata sake kulasaba Suka cigaba da lissafi sbd kullum ita arayuwarta a lissafi ta qare.
Cikin wani yadin 'dan Madina kalar baqi da siminti yafito da babbar rigarsa ta kullum ya sanyo hularsa datai mugun masa yawa wadda itama gurin maular yasamota.
Wani irin zaku'do kafada yakeyi Yana gyara babbar rigarsa da hularsa qafafunsa da fuskarsa kuwa tsaf sukaji Vaseline sai maiqo sukeyi ya kalli Nadiya dake gefen talatu tana gyaran shinkafa yace Ina takalmin Zaki na jiya daya zuciya ya wurgo?
Kallonsa sukayi atare itada iya talatu Saidai Kuma basuyi mamakiba saboda sanin waye baban.
Miqewa tayi ta nufi inda ta ajiyesu kusada dakinsa ta dauko takawowa baban ya karba Yana cewa"
Wannan dinkin dakikayi bai tsukuba Amma hakan zaiyi maleji.
Sakawa yayi batareda yakalli talatu ba ya baza rigarsa ya wuce sbd ganin baqin ciki talatun ke yimasa.
#MAMUH
*_Mamuhgee4_*
Yana fita qofar gida yaci karo da mal idi zai kwado sallama shima a shirye cikin tasa babbar rigar shadda kalar blue data wanke takoma kamar sky-blue,
Cikin washe baki yace"
Yawwa mal datti muje Dan Allah Dan nasan yanxu Kam anyi nisa da fara taron.
Cikin 'dingisa Suka kama hanya rigunansu na cika da iska suna qarawa.
Dama ahaka tasu rayuwar take,
Aminaine tun yaranta,
Tare Suka taso,
Kusan atare sukai aure,
Duk wata kalar sana'a tare sukayita har qarshe Suka qare a maula sbd cikinsu baasan wayafi wani son banza da kwadayiba dagasu har matan nasu.
Dattiya da ruqayya marayune dasuke uwa daya uba daya suka taso Babu uwa Babu uba sakamakon gudun hijira dasukayo daga wani yankin Cameroon,
Tare Suka kubuto da idi da qaninsa shima Wanda yake kusan tsara da ruqayya,
Alokacin dattiya nada shekara ashirinda uku ruqayya nada shekara goma Sha hudu,
Bayan dogon gararin rayuwa dasuka shiga qarshe Suka miqa ruqayya aikatau gidan wata mai abinci dake kusada Tasha inda sukuma Suka famjama nema,
Da sana'ar Saida rake Suka fara Saidai kullum sune suke shanye fiyeda rabi ahakadai harsuka saketa Suka kama ta shoe shiner itama Babu wani abin garawa daga Suka koma Saida kifi shima dai sune suke karyawa kansu jari
Ahaka Saida sukayi sana'a tafi kala ashirin kafin Suka fara gwada maula aikuwa saigashi sunga harka tafara budewa nan Suka maida himma Dan kuwa maula har wani gari zuwa sukeyi,
Alokacinda Sukai shekaru biyu suka Tara kudin maularsu Suka hada da kudin albashin ruqayya data rigada tazama 'yan mata sbd shekaru zunja yanxu tanada shekaru goma Sha Tara Kuma ba laifi tanajin dadin rayuwarta agidan ladee mai abinci,
Fili Suka siya na dubu dari biyu harda hamsin acikin wata yamutsatiyar anguwa
Ban sabuwar maula ta tashi sbd anfara gini duk da ginin irin nasune na masu qaramin qarfi.
Biyu aka raba filin kowa aka Gina masa gidansa mai tsakar gidan da Babu siminti sai dakuna uku uku da bayi sai daki 'daya a soro.
Dama sunada 'yan matansu atake Suka fara Shirin aure
Dattiya ya auri talatu 'yar ladee mai abinci wadda ta girmi ruqayya sosai.
Idi ma qawar talatun ya aura shafa'atu.
Bayan aurensu da wata daya ruqayya tadawo gidan Wanda yakasance itama tanada gado dashi tunda da kudin aikinta na shekaru Suka hada akayi aikin gidan shiyasa gidan dattiya yafi na idi dakuna da fadi.
Dawowarta gidan bai hanata cigaba da zuwa aiki gurin gwaggo ladee ba sbd rayuwar gidan kowa tasa ta fishesa ce,
Shidai dattiya tunda aka gama amarci ya daina kawo kayan abinci sai Randa yasamo
Ita talatu dama tasan wa ta aura tahau sana'arta ta Saida mayuka da Hoda da jambakin 24hrs da Rani dasu 'yan kunne.
Itama ruqayya yanxu albashinta a hannunta yake zuwa dashi take ciyarda kanta harda gidanba wani lokaci.
Yau kusan sati biyu kenan da zuwan wani inyamurin baqo gurin baban Solomon mai shagon Saida qafaruna dake gefen gidan abincinsu.,
NOAH Wanda ake kirasa NEYO farin inyamurin jahar anambra Wanda yake amatsayin qanin baban Solomon uwa daya uba 'daya,
Farine sosai da Kuma qaqqarfan jikinsa dake nuna Yana motsa jikinsa sosai.,
Kallo daya zakayi masa kasan ko acan garin nasu shi Yana cikin marasa ji sbd dukkanin alamun troway ya bayyana a taredashi,
Tunda yazo yayi aboki 'dan troway irinsa mai suna DIKKO shima asalinsa 'dan haure ne daga qasar Ethiopia acikin jahar Dilla.
Dikko yabaro qasarsane sakamakon kawunsa daya kashe tareda matarsa da 'yayansa ya sato dukiyarsu yayo nesa da qasar shida matarsa dasuka aikata aikin atare.
Tunda yadiro Nigeria yafara sana'ar baqin mai da miyagun qwayoyi tareda safarar gurbataccen magani.
Abota sukeyi sosai da neyo inda Suka hada hannu gadan gadan ga sana'ar Wanda take kawo musu samu sosai,
Banbanci tsakanin neyo da dikko shine,
Neyo baya kashewa Saidai duk inda tantiri yakai yakai harya wuce.,
Dikko kuwa kisa agurinsa ba komai bace matuqar zakai masa shamaki da abinda yakeso to tabbas zai kawardakai Babu gargada,
Dukkaninsu basa shaye shaye basa neman mata sbd tsabar qwarewa da sanin Rashin Imani yasa Sam dikko ko shaawar giya da neman mata bayayi sbd dasune za'a iya Kai mutum qasa.
A boye suke mu'amalarsu Sam Basu so ma asan Wai sunsan juna sbd ha'darin sana'ar tasu shiyasa basa haduwa sai dare.
Tunda neyo yaga ruqayya yaji Babu macen dayakeso idan ba itaba,
Yayi bibiyar harya gaji Sam Bata kulasa sbd tsananin kamun kanta da kama mituncinta.
Nacinsa da yanda yafara zama wani Wawa akanta yasa tafara kulasa duk da tasan alaqar bamai dorewa bace tunda addininsu ba 'dayaba.
Ahankali qaunarsa tafara shigarta
Shikuwa tuni yafadawa bban solo musulunta zaiyi ya auri ruqayya Babu musu bbn Solomon ya amince sbd shima ya matarsa musulmace wanda dama sanadin auren yabaro gida yadawo nan arewa.
Bayan musuluntarsa shida bbn Solomon Suka samu dattiya da maganar ba kunya ya rufe ido yace bazai Bari ruqayya ta auri tubabbe kuma 'dan daba ba.
Da farko kamar wasa saikuwa sukaga da gaske yakeyi Dan tuni ya Hana ruqayyar ko fita.
Daga ruqayya har neyo dayaci sunan aliyu hankalinsu yatashi
Kullum Yana qofar gidan gurin dattiya Amma kullum da sabon Rashin arzikinda dattiya ke musu.
Ahaka dai Abu yayi tsanani sbd kusan so biyu shedan nasasu kusan aikata 6anna ganin haka yasa neyo yanke shawarar tafiya ya nemi sana'ar halal mai kyau ko dattiya zai canxa yabasa aurenta.
Bayan tafiyarsa ruqayya tashiga mummunan hali na rashinsa gashi ko aikin ta daina zuwa take talauci ya rufto musu abubuwa sukai tsanani ita kanta talatu yanzu sana'ar sai ahankali.
Ana cikin haka mamar shafa'atu matar idi tadawo daga Lagos su dattiya dasukaga irin tarin arzikin data samo nan take dattiya ya yanke shawarar bada ruqayya aje da ita itama tayi aikata tasamo musu abun duniya.
Ruqayya naji tana gani aka tafi da ita Lagos inda ta tararda wani babin rayuwar daya firgitata.
Gidane acike taf da 'yan haya dakuna sunfi guda ashirin kowanne da kalar mutanen dake cikinsa.
Azumi mamar shafa'atu itama daki gudane da ita sai 'yan matanda ake kawo mata Wainda take rarrabawa aikatau gidajen manya.
Kwanansu biyu dazuwa ta miqata wani babban gidan abinci aiki.
Ahankali tafara sabawa da rayuwarsu tafara 'dan koyon pidgin sbd saidashi kusan kowa ke mgn a garin.
Ranarda tacika wata hudu da zuwa garin ta taso aiki da daddare tana hanyar zuwa gida wasu matsaya Suka biyota
Tun tana tafiya harta fara sauri daganan Kuma sai gudu sbd kusan su biyar ne.
Gudun fanfalaqi takeyi suna binta gashi anguwar Babu mutane sosai gashi dare yayi.
Tana Shan wata kwana taji an fizgota sun fada wani gida
Arikice ta bude baki zatai ihu ya toshe mata baki ahankali ya furta sunanta Yana cewa"
Keep quiet.
Kallonsa tayi da sauri jin muryarsa tana ganin shi din ne batasan sanda ta rungumesaba tareda sakin kuka sbd harokacin a tsorace take gakuma mamakin ganinsa.
Saida mutanen dasuka biyota Suka wuce kafin ya saketa ya jata zuwa 'dakinsa na mai gadi dake cikin babban gidan daya jawota.
Kallonsa tayi tana cigaba da kuka shima ita yake kallo zuciyarsa na tsananin jin zafi da qunar ganinta amatsayin mai aiki tundaga arewa harnan Lagos inda ya tabbatarda kowane lokaci zata iya lalacewa.
Cikeda damuwa yace"
Ruqayya Dan Allah ki aureni muyi rayuwa cikin amincin Allah kibar maganar dattiya wlh Kai rayuwarki zaiyi yabaro
Yanxu me kike tunani waincan mutanen zasuyi miki dasun kamaki????
Share hawayenta tayi sbd tasan tabbas rayuwar Lagos dinnan idan har bakada mai kulawa dakai to sunan rayuwarka lalatacciya,
Tabbas zata amincewa neyo suyi aure dataje tafada halaka.
Bayan sungama yanke shawara acikin Daren yakaita har qofar gida tashiga kafin yadawo da niyar gobe zasuje adaura musu aure.
Haka kuwa akayi washe gari sukaje wani masallacin yorbawa aka daura musu aure bada sanin azumi ba dagacan suka tattara Suka bar Lagos sukai abekuta.
A abekuta yayi amfani da kudinsa Suka kama hayar daki daya da toilet inda yasiyo musu komai na amfani da daidan gwargwadon abinda suke buqata Suka fara shimfida rayuwarsu inda yasamu aiki awani garage dake kusa.
Bayan aurensu da wata biyar ciki da cutar sanyi ta bayyana ajikin ruqayya nan hankalin neyo yatashi gashi yanxu abincima gagararsu yakeyi saiyayi daqyar yake samowa.
#MAMUH
*_Buri daya_*
*_Mamuhgee5_*
Cikinta na wata bakwai Abu yayi tsanani Dan kuwa kumburi ne tayi tako Ina Wanda ya sauya kamanninta tsaf Dan kuwa ko qafafuwanta daqyar take dagawa.
Lokacinda abin yayi tsamari yahada kudi daqyar yakaita asibitin kudi atake Suka Bata gado sbd ganin mummunan halinda take ciki Suka tabbatar masa lallai dole za'ayi mata aiki acire abinda ke cikinta Dan kuwa za'a iya rasasu su biyun sbd sanyi yakama qashi da bargon jikinta sosai ta yanda yazamo ha'dari ga rayuwarta data abindake cikin,
Kudi naira dubu saba'in Suka masa total tareda basa telar biyan kudin.
Kallon telar yasakeyi tareda rintse idanuwansa dasukai mugun jajir suna neman zubo ruwan tausayin ruqayyarsa.
Fitowa yayi asibitin Yana tafiya da qafa kan hanya Yana tunanin shida ko dubu 'daya baida ina zai samo dubu saba'in?.
Zama yayi bakin wani babban shagon siyarda kayan masarufi ya rafka tagumi baiko damu da ranar dake dukansaba.
Yafi awa biyu zaune agurin har wasu na basa sadaka idan sun fito atunaninsu bara yakeyi.
NEYO"""yaji ankira sunansa ya dago ahankali cikeda sanyin jiki.
Yayi saurin miqewa Yana qoqarin tattaro kuzari yake kallon Wanda yakira sunansa Yana cewa"
Dikko Kaine nake gani haka????
Rungume juna sukayi dikko na sakin wata dariyar jin dadi ya janye Yana kallon neyo daga qasa zuwa sama yadan yamutsa fuska Yana cewa"
Neey what's happening?
You look terrible??
Numfashi neyo yasaki tareda gyara zaman rigarsa data gama yimasa yawa yace"
Dikko matata na asibiti aiki za'ayi mata sbd ceto ranta da abinda ke cikinta Kuma ana neman kudi nera dubu saba'in Wanda wlh banidasu banida inda zan samesu.
Jansa dikko yayi sukaje mota yashiga tareda bude masa shima yashigo ya tayarda motar Suka fara tafiya
Batareda ya juyo daga kallon hanyaba yace"
Neyo kasan ni,
Kasan yanda nake Kuma bazan taba canxawaba,
Bana aikinda nasan banada riba Dan haka bazan iya baka dubu saba'in ba kyauta Saidai zanbaka wani aiki dazakai kasamu dubu 'dari biyar Wanda zaka biya kudin aikin matarka harma kayi lalurar komai na bayan haihuwar.
Kallonsa NEYO yayi batareda mamakiba sbd yasan waye dikko
Yasan akan kudi baida yarda ko ragi ko akan waye,
Duk aikinda zaiwa dikko yabashi dubu dari biyar yasan ba qananan maqudan kudi shi dikkon zaisamuba Saidai yasan aikin dikko Babu Wanda ba gur6atacce neba
Dole wani mugun abun ne zai masa.
Sauke numfashi yayi yakallesa yace"
Wani irin aikine??
Wani sample na maganin chloeziadenes zaka samomin a matatar magunan qasa dake cikin Lagos
Na dauko 6oyayyun ma'aikatan daga qasar China zasumin irinsa a sirrintaccen kamfanin buga maganin bugina zamu sakarwa mutaneshi duk da Sha kawai zasu riqayi basusan bugineba Babu maganin cutar dazai ringa musu.
Kallonsa NEYO yayi tsawon mintuna hudu Yana jinjina Rashin Imani da mugun son abin duniya na dikko sbd kowace gurbatacciyar sana'a ya iya bayako jin shakku da fargabar yanda mutane ke rasa rayukansu akan abubuwan dayakeyi.
Girgiza Kai yayi kawai sbd shi yanxu bayako sha'awar rayuwa da dikkon,
Kai tsaye yace"
Fadamin inda zanje nakaima idan nasamo,
Kuma ka tabbatarda kudina nanan ajiye hannunka ayau zan kawo maka sample din da yardar Allah.
Dariyar jin dadi dikko yayi sbd shiyasa yake mutuwar son mu'amala da neyo ya iya aiki ba tsoro ba shakka ga sa'a dayakeda ita.
Bakin wani qaton factory dikko ya tsaya da motarsa yacewa neyo"
Idan kadauko kasameni bayan gari gidan mai mai suna Dilla filling station,
Best of luck.
Maimakon yaga neyo ya fita saiyaga ya fada wajen motar Yana mulmulawa kamar baida Rai take kansa dake bubbuguwa da dutse yafara fashewa bai damuba sbd ganin masu tsaron gurin suntaso suna qoqarin taimakosa sbd sunga lokacin aka jefosa daga cikin motar data gudu.
Dikko bai tsaya komaiba ya fige motarsa da mugun speed Yana wani shuumin murmushi sbd yasan aikine neyo yafara.
Daqyar Suka taresa suna qoqarin dagosa sbd tuni fuskarsa ta baci da jini kamar Wanda aka Dade ana ganawa azaba,
Sam basuga numfashi atareda shiba nan Suka daukosa sukayo ciki dashi sbd basuda fargaba ko tunanin komai akan factory dinsu tunda sumsan tsaftataccen aiki sukeyi ba gurbatacceba bare suji shakkar shigoda wani.
'yan lokitocin dake cikin factory din Suka dubasa sukai masa dressing shidai yanajinsu yaqi motsawa Saidai numfashinsa dake fita ahankali alamar dawowar numfashin.
Bayan futar dukkaninsu daga 'dan dakinda Suka taimaka masa ya miqe da sauri tareda fara bincike cikin dakin cikin sa'a yasamu uniform din ma'aikatan gurin yadauki daya yasa da sauri tareda Jan hular uniform din yarufe fuskarsa yafito Yana sunkuyar dakai sbd kar aganesa atake ya saje da 'dinbin ma'aikatan dake gurin.
Kai tsaye computer room dinsu ya nema ya sidada yabude qofa ya leqa yaga numbern room dinda samples suke yafito ta nufi room 17 inda yaci babbar sa'ar security din qofar abude yake wani doctor Yana ciki da sauri yafada dakin
Doctorn na juyowa yakai masa wani mugun duka a hanci atake likitan ya yanke jiki ya some
Nan yafara dudduba sample dinda dikko yace
Yanayi Yana kallon qofa.
Takun tahowa yaji daidai lokacinda yagansa yayi saurin dauka daga cikin wani box mai kamar fridge yasaka cikin wandonsa yayi saurin ficewa.
Daqyar ya mayarda kansa dakinda aka barsa yayi saurin cire uniform din ya mayarda kayansa yakoma Yana kwantawa aka bude qofar.
Yanaji an buga alarm na danger ya miqe ya fito da satar jiki ya iso gate sukuwa security Suka bude masa ya fice.
Gudu yakeyi sosai sbd wajen garine sosai
Kusan kilometers tara ne tsakaninsu da cikin gari.
Daqyar ya kawo titi Yana hango mota tafe yayi sauri daga hannu Saidai bai gama aje hannunba motar tayi sama dashi yafado gefen titi jini na fita jikinsa sosai.
Atake mai motar ya gudu yabarsa nan
Rai hannun Allah.
Jini yake fitarwa sosai gashi ko motsi baya iyayi atake yasan mutuwa zaiyi Saidai yayi baqin cikin mutuwa cikin wannan yanayin gashi ruqayya da cikinta baisan wane hali zasu shigaba..
Dishi dishi yake gani idanuwansa na neman rufewa yaga dikko yazo kansa ya tsaya tareda wasu yaransu biyu.
Cikin Rashin tausayi dikko ya girgiza Kai yace"
I'm really sorry best friend Amma Kona daukeka yanxu lalura zaka zamarmin gskia sbd dai mutuwa zakayi Dan haka bazanyi hasarar kudina gurin kaika asibiti muyita wahalar banxaba koba komai kaga Allah nasona da yawa shiyasa hakan tafara sbd kar kudina dazan baka suzama west...
Kai ku cajesa kuciromin sample Dina.
Yanaji Yana gani Suka ciro sample din daga jikinsa Suka wuce Suka barsa hawaye na gangarowa daga idanuwansa harsuka rufe.
Asibiti sunyi jiran dawowarsa har kwana biyu ba labarinsa tuni Suka sallameta nan hankalinta yayi mummunan tashi tafara nemansa lungu da saqo cikin abeokuta
Ga ciwo ga nauyin ciki Amma haka take yawon nemansa Takoma kamar mahaukaciya tun ana Bata sadaka tana qin karba harta fara karba.
Bayan wata daya wani abokin aikinsa daya gaji da zaryar datakeyi gashi yace Takoma gida taqi ita saitaga neyo
Kawai sai yazo yasanar mata anga gawarsa hanyan Lagos sunje sunmasa sallah sun rufesa
Ban yabata kudin mota yace Takoma gida arewa.
Tanajin haka tayi tawakkali Bata tsaya Bata lokaciba bayan kwana biyar tadawo arewa.
Ranar data isa agalabaice ta isa sbd kwana biyu ahanya suna tafiya kodata iso tafara ficewa hayyacinta.
Talatu na zaune tsakiyar gida da tsohon cikinta tana Shan radio taganta tashigo tana daddafa bango.
Gyara zama tayi tareda kallonta dakyau ta tabbatarda ita dince ruqayya.
Batayi mamakiba ta kalli qofar dakinta tace"
Dattiya saika fito kaga baqin magribar dasuka sauka
Dama nafada komai Daren dadewa saita dawo
Gashinan harda 'dan kawu aka samo maka.
Fitowa yayi Yana saka hula akai Yana ganin ruqayya ya zaro qananun idanuwansa akan cikinta hankali tashe yace"
Ruqayya mezan gani ajikinki?
Nida nasaki jiki duk Randa Zaki dawo da 'dibbin dukiya Zaki dawomin shine kika kwaso min wannan iskancin Lagos 'din???to wlh ko zama bazakiyiba dashi acikin gidannan maza wuce tun kafin nayiwa shegen jikinki duka...
Wato tunda na hanaki auren tubabbe shine kika 'daukomin abinda yafi auren tubabben kunya da takaici.
Wata dariya talatu tasaki tana cewa"
Dan Allah da gaske dattiya kasan kunya dahar kake gudun abin kunya?
Rufe ido yayi yafara zazzaga mata Rashin mutunci sbd shi cikin bai wani damesaba kamar yanda tadawo hannu rabbana kamarma wata mabaraciya...
Cikin tsananin azaba ta durkushe gurin sbd naqudar data dirar mata lokaci 'daya.
Beda yanda zaiyi Dole yaje yakirawo shafa'atu matar idi da innaje sukazo dole akai cikin dakinta tun na budurcinta Suka fara qoqarin karbar haihuwarta.
Cikin ikon Allah ana Kiran magriba ta haifi yaronta Wanda yake fari tas jinin Igbo tamkar mahaifinsa.
Cikin qanqanin lokaci aka shiryata
Dattiya da fada dakomai yasiyo kala biyu da sabulun jarirai guda daya da man jarirai yakawo aka sawa yaron.
Dattiya kuwa Duk yanda yake fada da kukan baida dole yake yimata wasu abubuwan itada jaririnda da kanta tayiwa yaronta huduba da sunan mahaifinsa wato *_ALEEYU HAYDAR NEYO_*.
Yanaji yana gani ya yanka mata 'dan ragonsa Yana sake jaddada mata aro yabata zata biyasa kudinsa tace taji idan ta warke zata biyasa.
Ahaka suka fara Gina wata sabuwar rayuwar mai cikeda qalubale gashi bayan haihuwarta da wata biyu talatu ta haifi namiji itama aka saka masa suna dahiru.
Dole ta mayarda hankali tafara sana'a sbd lalurarta data Zaki Dan kuwa tun Yana yaro take kiransa Zaki tunda sunan babansa yaci,
Babu Wanda yataba tambayarta ya akayi tasamu cikin Zaki sai itama Bata bi takan zancenba tafara sanointa Dan tallafawa rayuwar 'danta daya girma harta sakashi makarantar primary.
Zaki ya taso a cikakken marajin yaro sbd ganin irin rayuwarda akeyi acikin gidansu ta Rashin taimako da tausayi kowa tasa ta fishesa akeyi a gidan,
Idan kanada kaci idan bakada ka kwana da yunwa,
Ga shegen son kudi da abun duniya tsakanin talatu da dattiya baasan Wanda yafi waniba.
#MAMUH