A wani katon gida suka tsaya, mai gadin da sauri ya bud'e motar tare da mika gaisuwa, sunyi parking sannan Habib ya kalli Seemah yace muje ko? Kallansa tai idanunta sunyi raurau kai ya d'aga mata alamar it's okay.
A hankali ta zuro kafarta ta fito, nan suka jero tare da nufar gidan.
Bayan sunyi knocking aka zo aka bud'e wata yarinya ce wanda a haife batafi Seemah ba, tana ganin Habib ta saki fara'a tace " Yaya Habib yau kaine a gida?"
" Tafi shan ni ba ruwana dake ai." Ya fad'a tare da shiga, Seemah na biye dashi.
Matsawa tai d'aya gefen tace " Haba yayana na kaina ai nasan bazaka iya fishi da ni ba."
Kunnenta ya kama tasa kara tare da cewa yaya Habib da zafi fa? Seemah ce ta kalleshi ta saki fuska tace " kai yaya Habib daga isowa sai a fara da cin zali? Amata hakuri."
Sakinta yai yace " kinci darajar kanwata mai daraja."
Kallan Seemah tai tace " badai mai darajar nan wannan sakaliyar kanwar taka ba.....?"
Hararar da Habib ya maka mata ne yasa tai shiru kallam Seemah yai yace " kyaleta kanwata wannan da kika ganta batajin magana."
Jisukai ance lale maraba da Habibullah, juyawa sukai inda maganar ke fitowa, wata babbar macece wanda kana ganinta kasan takai misalin shekara 50, sai dai tasha kayanta ta kuma d'aura d'ankwali abinta dagwas, fara'a ce sosai a fuskarta Habib ma fuska ya saki sosai ya ja hannun Seemah suka karasa gunta, zama tai suma suka karasa suka zauna a kusa da ita a kasa, Habib ne ya gaida ita sannan Seemah, ta amsa tare da cewa " Zara na neman hanaka hutawa ko?"
Kallan wacce aka kira da Zara yai yace ai Ummy wannan yarinyar tana bukatar bulala a gurina.
Dariya suka saki dukansu, Ummy tace tashi ki kira Abbanku, nan ta mike tana cewa yaya habib zanzo Allah, amma sai yaya Ammar yazo kasar.
Da mamaki Seemah ta kalleta Ammar? Habib ne yace " Gwara ma kizo d'an Allab ba wai saboda Ammar ba kinfi kowa sannan yace bayayi dake."
Da sauri ta karasa b'angaren Abba fuska a had'e, tana dawowa, Abba na shigowa, Abba shima ya taho yana farinciki, Ummy yaji tace " Habib wannan fa? D'an ban tab'a ganinta ba?"
Murmushi Habib yai yace " Kanwa tace Seemah." Ummy ta maimaita Seemah? Seemah?
Abba dake tsaye idanunsa suka tashi daga farin ciki, su ka kad'a sukai jaa, sunan yake maimaitawa a ransa da kuma abinda ya faru a baya, abinda ya ruguzama kaninsa rayuwa ya kuma tada hankali duk zuri'arsu suka zama abin nuni ga duniya, yana tsaye Zara tace "Abba yaka tsaya anan?"
Juyowa sukai dukansu suka kalleshi Habib ya saki Murmushi ya mik'e tare da tahowa gunsa, Ummy kam tunda taji sunan itama jikinta yai sanyi, shiru tai kawai tana kallan Seemah.
Habib na zuwa kusa da Abba ya kama hannunsa tare da cewa " Abba na dade banzo gaisuwa ba ko?"
Kallansa Abba yai idanunnan jawur, zaiyi magana sukaji ance " Hello My Ummy Ur Son is back." Gaba d'aya kowa ya juya ya kalli kofa, saurayine da baifi su Ammar ba sai dai yasha kayan nigogi kana ganinshi kaga saurayin dake ji da kansa, idanunsa nakaikan Habib ya karaso da sauri yace "Hello Bros long time no see"
Baki Habib ya saki sannan ya kalleshi daga sama har kasa yace " Zaid kanannan a yanda kake, nikam yaushe zaka girma?"
Baki yad'an karkata irin salon ' yan gayo maza d'in nan zaiyi magana idanunaa suka kai kan Seemah da sauri yakarasa kusa da ita ya matsa daf da ita yana kare mata kallo, itama kallansa tai tare da kokarin matsawa, mikewa yai yace Wow ummy she is just my type.
Idanu Seemah ta zaro tare da kallansa, Zaid ya kanne mata ido d'aya dasauri tai kasa da kanta, gun Abba ya koma yace " Abba kumin aure please, nan da 1 week inasan auran yarinyarcan."
Cikin tsawa Abba yace " Ashe haryanzu zaid bazakai hankali ba? Daga ganin yarinya kawai kafara min zancen banza? Kasanta ne? Ko kasan tsatson ta?"
Kowa sai daya tsarata a falon.
Cikin rashin fahimta da raahin jin dad'i Habib yace " Abba baka tambayeni ba ai, Kanwatace fa, Seemah."
Abba ya kalleshi cikin bacin rai sai kuma ya juya ya koma ciki da sauri, Habib ya bishi da kallo, Seemah kam tumda take yauce rama ta farko da tsawa ta girgizata, jitai idanunta sun ciciko, Zara ta kalleta tace " Yaya Habib Gimbiyarku na neman yin kuka da alama bata sabajin tsawa ba."
Da sauri Habib ya taho, Zaid yasa gudu ya rigashi zuwa, kusa da ita yakara zama shima kamar me shirin kuka yace " Babyna kiyi hakuri, haka sirikinki yake sai dai nima na dade banga b'acin ransa haka ba, but karki damu tunda ni inasanki zan kareki daga komai."
Matsawa Seemah tai baya kad'an tana mai kallan mekakeyi hakan? Ummy ce tace " Zaid ka bari mana." Tafad'a tare da mikewa tace Habib inasan ganinka.
Nan suka juya, Zara ta girgiza kai tace Seemah ina tausaya mikk kin had'u da cingam d'an manne, itama ta mik'e ta bar falon.
Zaid ya kara matsowa gun Seemah yace " Babyna nasha wahala gurin nemanki,meyasa kika wahalar dani sai yau kika bayyanamin kanki?"
Seemah ta kalleshi da mamaki tace " ni kuma? A ina ka tab'a ganina?"
Jitai ya damko hannunta yakai saitin zuciyarsa yace " anan baby na."
Da sauri ta fizge hannunta tare da nik'ewa tace " Banasan haka."
Shima mikewa yai yace me kikeso to? Fad'amim in miki cikin gaggawa.
Harara ta makamai tace " Zaid kake ko? To bari kaji nifa ba ka ra gareni ba, sannan ba tsoro gareni ba, wannan abin da kakemin bakomai bane illa sallon yaudara ta samari masu ji dakansu, saidai me? Am sorry d'an na riga na gano lagwanka, bakuma na tunanin hakan zaiyi tasiri a guna."
Kallanta yakeyi kawai tana gama magana ya fad'i zaune rugub ya sa hannu a kirjinsa yace " wow! Kaiiii!!! I really like ur boldness, Baby na."
Harararsa takara yi sannan taj hanyar waje.
Habib nezaune a falon ummy, ta kalleshi tace " Habib kad'au yarinyar nan kubar gidan nan tun kafin Abbans Zara ya kara fitowa, dan banaji abin zaizo da sauki, kallanta yai yace " dab Zaid yace yanasanta ko me?"
Ido ta runtse tace " kaidai kai abinda nacemaka please Habin banasan abinda aka birneshi da kyar a kara hakoshi."
Kallan mamakin kalamanta yake sai dai ya daure ya mike yace shikenan bari mu wuce.
Zaid bin Seemah yai a tsaye a jikin mota ya ganta, karasawa yai tareda mika mata wayarsa yace ur number is needed here!
Juyawa tai tace" bazan iya bada wa ba."
Zaid yace "Kefa kanwatace, d'an haka dole ne ki samin number dana bukata."
Murmushin mugunta ta saki sannan ta amshi wayar tasa number tai dialing ringing 2 ta katse tace gashi nasa in naje gida zan gani dan ban fito da wayata ba."
Murmushi ya saki yace " Amma Ammar yaci amana ta dabai tab'a nunan hotonki ba."
Kallansa tai tace " ko kuma mutuncin dake tsakaninku bai kai ya kawoba ba, tunda dai ko abokanansa sunsan hotonane akan screen d'insa."
Matsowa yai kusa da ita yace " Wow I really like ur Style dear. "
Mota tai saurin bud'ewa ta shiga tare da kulle kofar, Murmushi zaid ya saki sannan ya juya.
Habib ne ya fito fuskarsa d'auke da tambayoyi kala kala waya ya d'aga ya kira Dad tare da cewa " Dad munzo gidan Abba amma......"
Jiyai Dad ya katseshi yace " Habib meyasa kukaje? Meyasa baka tambayeni ba? Ina Seemah ba abinda ya faru da itadai ko?"
Habib da mamaki yace " Dad menene kake kokarin boyemin? Yaza'ai kace meyasa mukazo gun Abba?"
Dad kam duk ya rud'e yace " Habib, Seemah fa? Is she alright? "
Habib yace eh tare da kashe wayar, meke faruwa?
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
*Bang🔫*
*Bang🔫*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 2⃣3⃣
Nan ya fara nuna mata yanda ake tuki, tafara ja sunayi suna kallan juna wani so ne ke kara ratsa dukansu, bayan sun gama suka fito waje, Seemah ta hau saman bayan mota Jalal ya tsaya a gabanta ta kalleshi tace " wani irin farin cike ne ke ratsani Deen."
Kallanta yai cikin so sai dai kafin yai magana wayarsa tai kara yacirota, yana dubawa yaga Abbansa hakan yasa yad'an matsa kad'an da Seemah, bayan sun gaisa ne Abba yace " Zaka shigo wannan weekend d'in?" Kallan Seemah yai sannan yace " Wlh Abba bansanj ba tukun na ya jikin Zaheeda?"
Abba yace " Da sauki dama zancen kai kudin ka ne, a cikin kud'in da kake turowa akwai ragowa ina ganin ya kamata mukai karshen satin nan." Jalal jiyai kamar an d'au bokitin ruwan sanyi an shekamai a jiki, dakyar ya daure yace kud'i kuma Abba? Da wuri haka? Yad'an kara matsawa hakan yasa Seemah hankalinta ya gaza kwanciya, saukowa tai tare da zuwa ta bayanshi kad'an.
Abba yace " Jalal me za'a jira to? Munada d'akuna dayawa kasani Zainab ba irin yan matan zamani bace da zatace sai kaza take so,to me zamu jira?"
Idan Jalal ya kad'a yace " Amma Abba ita Zainab d'in ta fad'a tana so nane? Karfa ayi abinda bazaiyi dad'i ba, d'an Allah Abba a d'an tsagaita maganar kai kud'in ka ga........"
Abba ya katseshi yace "Jalal anya zaman Abujan nan bai fara lalatamaka dab'iun ka ba? Ka tab'amin musu akan al'amuran dana yanke a kanka? Yau kai ne da kanka?"
Ajiyar zuciya Jalal yai zuciyarshi tai ba dadi yace " Abba ba haka bane kayi hakuri d'an Allah." Katse wayar Abba yai Jalal yanata Hello hello jin shiru yasa ya duba wayar, gaba d'aya jiyai jikinsa ba dad'i juyowa yai da niyyar ganin Seemah sai dai a bayanshi ya ganta idanunta taf da kwalla da sauri ta juya zata wuce, hannu yasa da sauri ya riko hannunta, tana tsaye batare da ta juya ba sai dai hawaye a hankali suka fara sauka daga idanunta, Jalal ne ya matso ta gabanta tare da kallan fuskarta, da sauri tai kasa da ido tana hawaye jikimshi ya karayin sanyi, dakyar ya daure tare da jan hannunta suka fara tafiya, gun zamanta ya bud'e mata ta shiga shikuma ya tsugunna daga setin kafafunta hanayensu na rik'e, yadaure yace " Meemah kinji komai?"
Kallansa tai da raunanan idanunta hawaye suka zubo ta luntse ido tare da had'iyar wani abu tace " Deen aure za'a maka?"
Shiru yai baice komai ba tace " dama a can England ana yawan cewa First love bai fiya kai mutum ga aure ba, Deen ban tab'a soyayya ba sai akanka, na d'ade da fara sanka amma sai yau Allah yai zamu fad'ama juna sirrin zuciyoyin mu ashe yau ne kuma rana ta karshe da......." da sauri yakai yatsarsa bakinta yace shiiiiiii Meemah don't say something like that. "
Kallansa tai hawaye nakara bin kuncinta hannu yasa yana share mata yana cewa " Meemah iyayen na ke san auramin ita, kuma bansan yanda zanyi in hana ba, d'an haka na taso ban iya musu ga mahaifina ba."
Hannunsa dake kan kuncinta yana goge mata hawaye ta rik'e kallanta yai da mamaki tace " Deen please don't live me."
D'ayan hannunsa yasa ya kara damke hannun nasu yace " I won't live you Meemah, but ke kina tunanin za'a barki ki aureni?" Kallansa tai tace "menene da kai? Ni komai yamin naka."
Dariya yai yace "ba wannan ba, kinsan dai duniyar da nake ciki da wacce kuke ciki va d'aya bace."
Tace" Duk abinda nace inaso ahi akemin a gidan mu so karka damu da wannan, kai nake so ba wani abu naka ba."
Murmushi ya saki sai kuma ta fizge hannunta tare da hard'e su, ya kalleta yace " lafiya?" Tace " ba dai auran waccen zakai ba sai kuma kai tunani kara aure na ba?" Kallanta kawai yake yana mamakin kalamanta tacigaba" Jal nifa a tarihin rayuwata babu raba miji."
Kallanta yai ya guntse dariyar dake neman fitowa ya mik'e tsaye tare da cewa " Shikena da na d'auka ko mata uku gareni tunda muna san juna ba wani abun bane amma yanzu na gane." Yai maganar fuska a had'e.
Seemah ta kalleshi tace uku? Da sauri ta fara waige waige Jalal ya kalleta da mamaki wani shago taganu daga nesa da sauri ta fara tafiya, Jalal yasha gabanta yace ina kuma zaki? Bata mai magana ba kawai nunamai shagon tai, yace me kikeso? Alama tamai da ruwa, yace koma bari in siyo, nan ya karasa yace abashi robar ruwa, nan mai shagon yace naira 100, Jalal ya zaro ido yace ya pure water naira 5 shikuma wannan har 100? Mai shagon ya kalleshi da mamaki, wallet d'insa ya d'auko 200 ne a ciki ya mika tare da ansar ruwan, ya juya yana zuwa ya mika kata, ansa tai tasha sannan ta mikamai tace kuskure bakinka, yace bangane ba? Cikin shagwab'a tace nidai ka kuskure bakinka banasan tuna kalamanka dakai na mata uku.
Dariya ce ta kamashi yace " haka kike da kishi? Tace ba kishi bane ba amma ai......... Dariya yasa tare da girgiza kai, komawa yai mazaunin driver yace " Yamma ta farayi kar a nemiki a gida."
Juya kai tai tana kallan window, Jalal yai murmushi ya tada mota, sun fara tafiya ya sa hannu ya anshi ruwab hannunta ya sha, kallobta bishi dashi tace "cewa fanai ka kuskure baki ba fa ka shanye maganarka ba." Kallan bakin jarkar yai saitin inda shatin jambakinta yake nan ya kara kafa rubar yasha tare da sakin wani murmushi shikanshi mamakin kansa yakeyi.
Fizge robar tai tace " bazaka amsamin ba?" Kallanta yai kad'an sannan ya maida kallansa zuwa titi baice komai ba.
Tafiya suka cigaba ba tare da kowa yayi magana ba haushi ya gama kama Seemah kara ta saka da sauri Jalal ya kalleta yace " Seemah menene? Da sauri ya gangara gefen titi tare da maida hankalinshi gaba d'aya kanta hannayenta ta sa ta rufe fuskarta, ciki damuwa ta sa hannu ya zare hannun data rufe fuskarta yace " Meemah menene?"
Idanunta a rufe suke yace " wani gurin ne ke miki ciwo?" A hankali ta bud'e idanunta tace" banasab ina maka magana kana k'in bani amsa, it hurt me."
Kallanta yai batare dayace komai ba ya gyara zamanshi tare da fara tuki, kallansa take rai a b'ace jitai yace " Wani sa'in ne bana sanin me zan ce miki, ban tab'a shiga ciki hali irin wannan ba inji wai bansan me zance ba sai a kanki."
Juyowa yai yad'an kalleta sannan yacigaba " Ban tab'ajin irin haka ba a tsawon rayuwata."
Kallansa takeyi jikinta yai sanyi, kalamansa sun tab'ata idanu ta lumshe tare da jingina kai tace " I will take ur word as ni ka fara so a duniya."
Kallan hanya kawai yake yana murmushi itama lumshe ido tai tana murmushi, wani irin so takema Jalal da ko suna tarr jitake tana missing d'insa, zuciyarta na bugawa a duk lokacin dayake kusa da ita, kalamansa kesa zuciyarta da ganganjikinta su yi lum cikin wani shauki, ya zatai in wani abu ya bemi shiga tsakanin............wayar Ammar ce ta katseta, basai ta duba ba d'an ringing d'insa daban ne a wayarta, d'auka kawai tai tare da gyara kwanciyar kanta zuwa kallan Jalal, tace " Yayana ya? Ammar yace " Seemah yanzu Zaid ya kirani wai a lalai shi ya d'auka number kice, murmushi tai tana kallan Jalal tace " Shareshi yaya shi wai a dole sai na bashi number ta shine na bashi ta ka."
Ammar yai Dariya yace " Kai Seemah, me yasa? Bai miki ba?"
Tana kallan Jalal tace " inafa zaimin bayan na riga na kulle zuciyata?bana kuma tunanin wani zai samu damar shiga." Kallanta Jalal yai wani farin ciki ma ratsashi bai tab'a ganin yarinya kamar Seemah wacce bata kunyar kalamanta ba, ko d'an ba anan ta taso ba? Sam bata kunyar fad'ar abinda ke ranta.
Da mamaki Ammar yace kamar ya? Tace " there is something like that. "
Tana kainan tace yaya bye zan k'ira anjima.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
*FIGHTING*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 2⃣4⃣
Sun isa gidan Jalal yai parking a waje sannan ya kalleta yace " zan wuce." Kallansa tai tare da d'aga kai alamar eh, Jalal na fita itama ta fito tare da Kallansa ta baya, sannan tai ajiyar zuciya ta shiga gida, a tsatsaye taga su Farida da Aisha, suna ganinta Farida ta hau cewa Seemah ina kika shiga? Ko kallanta batai ba ta karasa gun Bala ta mik'amai key tace ka shigo min da mota, sannan ta karasa inda suke, tace " sannunku da gida yaya fa?"
Wani kululun takaicine ya kamasu duka, Aisha ta zuciya tace " bakiji tambayarki ake ina kika je ba? Kinsan neman da muka miki ne?"
Wani irin kallo ta watsa mata tare da cewa " ke in kin fita nemanki ake? Me kuka d'aukeni? Jaririya? Ko me? Ko kuwa ban isa in fita ba?" Tana kainan ta kallesu tai ciki, Aisha tai kwafa tace " wlh Auntu na tsani yarinyar nan."
Farida ta bi Seemah da kallo tace " in muka duba kalamanta bata fad'i karya ba, in kika fita ba nemanki akeyi ba, meyasa ita bata isa ta fitaba sai muhau nemanta."
Aisha tai shiru, Farida tace " Aisha na kula Seemah ba yarinyar banza bace kawai yanda zatai responding magana ne bata iya ba, ita kawai abinda ke ranta take fad'a bata damuwa ko kalaman zasu b'atawa wanda aka fad'awa rai."
Aisha ta jinjina kai, nan sukai ciki gani za'a bud'e gate a shigo da mota.
Seemah kam tama shiga a bakin gado ta zauna ranta a b'ace, dasauri tai dialing number Jalal yana d'agawa yai sallama, ajiyar zuciya tai jin muryarsa sai taji duk bakin cikin ya tafi murmushi tai sannan ta katse layin tare da kwanciya ta rungume pillow, wani shaukin so ne ke ratsata, Aisha ce ta shigo tare da kallanta tace "Seemah me kikeyi hakan?" Bud'e idanu tai tace " Bazaki gane ba ko na fad'a miki." Aisha kam ta sani batasan Seemah sai dai wannan hali nata ma birgeta ko anyi fad'a da ita yanzu in har ka mata magana to komai ya wuce.
Zama tai a bakin gadon tace " nakula dai soyayya ke ratsaki." Seemah najin haka ta mik'e tare da cewa kun shirya da saurayin ki? Tagumi tai tace " inafa haryau bansan a ya muke ba." Seemah tai ajiyar zuciya tace a ganinki yana sanki? Aisha tace I can't tell d'an shekara 1 da suka wuce ne ya ganni a hanya yace ya sona, to ni tun daganan muka fara waya, sai dai bai tab'a zuwa inda nake ba sannan ba nemana yake ba.
Seemah ta kalleta tace " Just 4get him, d'an banaji yana sanki ko kuma mayb akwai wacce ya gani yanaso daga baya." Aisha ta kalleta tace " ni kaina inasan in manta dashi sai dai na kasa, amma ke kamar naga kwanan nan kina cikin wani yanayi.
Seemah tai murmushi tare da cewa " wani nake masifar so sai dai ni kaina nasan nafi sanshi." Aisha tace ya akai kika sani?
Seemah ta rufe ido tace " ni bai dameni ba d'an nafi sanshi abinda na damu da sani shine shima yana sona," tai ajiyar zuciya tace "that's all I need. "
Aisha ta kalleta gaskiya wannan boldness na Seemah da kuma halin ko in kula yana birgeta.
Jalal kam ya kwanta bacci sai dai sam ya kasa bacci sai juyi yakeyi shi kad'ai why is he feeling uneasy? ganun abun bazai kare ba yasa ya mik'e ya d'auro alwala tare da fara salolin nafila.
Da safe wajen karfe 10 Seemah dake kwance ta bud'e ido a hankali, sai dai abinda ta gani ne yasa ta kara lumshe ido, DAD ta gani ya na shafa kanta, bayan ta kara bud'e idon tau murmushi tace " Dad I miss u alot." Ita duk ta d'auka mafarki take jitai yace " kin tashi Sweetheart? "
Mik'ewa tai da sauri ta zauna ta zaro ido tace Dad? Dad ya kalleta yace " dafatan Princess d'ina tana lafiya."
Rungumeshi tai tare da cewa Dad yaushe kazo? Ya shafa bayanta yace " nayi missing daughter ta dayawa shiyasa nazo in ganta mukuma tafi tare."
Dagowa tai cikin mamaki tace " Dad satina fa d'aya?"
Dad yace tashi kiyi wanka kiyi breakfast ni zan d'an fita im ma dawo sai muje yawo, murmushi ta saki tare da dunkule hannunta ta bar babbar d'an yatsa tace " Dad u are the best."
Dad ya mik'e tare da cewa sai na dawo tace " ok" shima yace ok.
Farida ya tadda a kasa yace bari in wuce, tace Dad bakai breakfast ba? Yace naci abinci a jirgi zani Suleja ne.
Bayan Dad ya isa Suleja ya fito ya shiga gidansu, Hajiya na zaune a tsakar gida ta baza tagumi yai sallama, tare da shiga amsawa tai tana kallan hanyar kofar.
Dad ya shiga yana cewa " Hajiya meyasa ake barin kofar nan a bud'e." Kallansa tai cikin wani farincikin ganin d'anta shikanshi jira yake yaga ta mike sai dai abinda ya bashi mamaki gani yai ta koma ta had'e fuskarta, shiyasan laifin amma gani yake yanzu ai yaci ace an daina.
Karasawa yai ya zauna a kusa da ita tare da gaisheta, ta amsa fuskarnan a had'e, kofar band'aki aka bud'e mahaifinsa ne ya fito Dad cikin farinciki yace kawo ka fito.
Kawo ya karaso ya zauna Dad ya gaida shi, sai dai kawo bai amsa ba sai fad'a daya biyo baya, Isma'il ni zaka cima mutumci? Har kaine zaka turomin yarinyar nan gidana? Dad ya kalleshi tare da cewa " Kawo naga wai ai yanz....."
Katse shi kawo yai yace " Yanzu me? Ka d'auka zamu manta? Ko kuwa d'an ka raina mu? To wlh bari kaji ko mutuwa nai bana bukatar yarinyar nan ta min zaman makoki."
Dad idanunsa suka kad'a yace " Haba Kawo in muka duba abin nan yarinyar nam ba itace mai laifi ba me ta sani?"
Hajiya ta katseshi" haka zaka ce? Yarinyar da dalilinta ya ruguzamana farinciki, ya sa mukai hijjira daga garin mu, kacemin me? Ba ruwanta?"
Jikin Dad yai mugun sanyi yace " Dan Allah kubar maganar nan."
Kawo ya mik'e cikin fad'a yace " kai wai wani irin mara zuciya ne? Ko kuwa san Fatima ne ya maka yawa? To wlh bari kaji na fad'ama, magana ma sai tazo aure, kai kana tunanin zaka iya boye maganar ne har karshen rayuwar ka?"
Dad ya runtse idanu da karfi, meyasa kowa bazai fahimceshi ba? Suna tunanin abinda ya faru shi bai ji zafin abin bane ko me?
Hajiya tace " sannan kayima yaranka waya su dawo Nigeria na hana zaman kasar wajen, dama d'an kar muga fuskar yarinyar yasa muka ce kabar kasar amma yanzu tunda kai dakanka ka aikota har cikin gidan mu sai ka shirya shirin dawowa, karkuma ka kuskura kamin musu akan maganar nan."
Dad yace " naji zan dawo amma maganar karatun Seemah fa?" Kawo yace " kai wannan ya dama ba mu ba."
Sunyi shiru kafin dad yace
" Dama abinda ya kawoni shine ina tsoron kar Seemah ta iso lokacin aurene zancen da aka burne ya taso, sannan banaso yarinyar ta fuskanci wannan gaskiyar mai wahalar gaske, shiyasa nake tunanin aura mata Ammar."
Hajiya ta watsa mai wani kallo tace " me? Ammar? Kanada hankali kuwa?" Dad yace " dan Allah Hajiya ku yanda da shawarar nan, in yaso sai ince Ammar ne ba d'ana ba."
Kawo ya ce lalai na yadda Isma'il ka fara zarewa, tashi kabar mana gida sannan kamasu Junaid waya su tattaro su dawo, in ka kuskura ka koma kasar nan zakaga maizai biyo baya.
Dad kamar wanda akama duka ya mik'e abin mamaki Hajiya ganitai hawaye yana kwaranya daga gefen idanunsa, ita kanta jikinta sai yai sanyi.
Hmm Turkashi. ......
Seemah kam tana fitowa daga wanka ta k'ira wayar Jalal shima yana zaune a office, ganin kiranta yasa ya mik'e ya fita yana sallama ta lumshe ido wani sanyi na tsata itama ta amsa, Jalal ya saki wani murmushin dad'i yace " Meemah kamar na dad'e ban gankiba nakejina."
Wani dad'i ne ya kamata tace " kasan me? Yace a'a tace "jinake kamar nayi shekara 1 da fara sanka, ji nake kamar bazan iya rayuwa ba in wani abun ya rabani........"
Jalal ne ya katseta yace"Karki karayin wannan furucin, ba abinda zai rabamu in sha Allah, in kuma kina bukatar b'acin raina kisake fad'ar haka."
Kan gado ta fad'a tare da lumshe idanunta tace " Deen ina masifar sanka, ni na sani nafi sanka akan yanda kake sona."
Karfe dayake gun ya dafa yad'an kwanto yace " haka dai kike tunani amma ni anawa sanin nafi sanki, yau zamu had'u amma ko?"
Tace " Dad yazo yau zamu fita dashi sai dai komin dare inajin in ban gankaba za'a iya samun matsala." A tare sukai murmushi yace bari inkoma aiko tace to Deen.
Yana katse wayar ta rungume wayar a kirjin ta idanunta a lumshe hango Jalal takeyi kawai a idanun nata.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 2⃣5⃣
Dad ya fito jiki a sanyaye, mota ya shiga tare da dafa kansa da sitiyarin motar, zuciyarshi a ciki take fall da damuwa, yanzu ba wanda zaibi bayanshi a birne maganarnan da Ammar? Yasan halin yayansa sarai bazai bi bayan shawarar nan ba sai dai bashi da wani zab'in daya wuce yayan nashi.
Nan ya tada mota yafara tuki, yana gaf da shiga layin Seemah ta k'irashi tace Dad yaushe zakazo kad'auken? Dad yace " Seemah ina d'an wani abin ne bansan how long abin zai kai ba , ko zamu bari sai gobe muje?"
Seemah ta turo baki tace " shikenan Dad, Allah yakaimu." Yace Amin.
Suna Sallama ta kalli kanta a madubi da sauri ta rufe fuskarta da hannu biyu sannan ta bud'e ta kanne ido d'aya tace "See you My Deen." Tana fad'ar haka tasa dariya tare da kara rufe fuska tana murmushi.
Wayarta ce tai kara ta jawota ganin no name yasa tai sauri zata d'auka sai kuma ta ce haba Seemah d'an tsaya mana,Cool down, kinfiya azarb'abi, nan ta tsaya sai da ta kusa katsewa ta d'aga tare da cewa " ya akai?"
Kallamanta sun bashi mamaki yace " ban gane ya akai ba? Bakiso na k'iraki ba ko me?"
Seemah tai shiru tanajin wani sanyi a zuciyarta, Jalal yace shikenan sai anjima, zai katse tai saurin cewa Deen?
Jalal ya maida wayar, Seemah tace " irin jan ajin nan na mata fa zan maka kaikuma ba hakuri."
Dariya ce tazoma Jalal yace" to ni nasan ba wannan tsakanina dake, in fact ma ba haka kike ba."
Cikin masifa Seemah tace " Me kake nufi da ba haka nake ba? Lalai ma Deen wato kana so kace bani da aji ko me?"
Jalal yace" kema kinsan ba haka nake nufiba, nufina sanda kikemin nasan bazai barki kimin haka ba, kuma nima........"
Ha what? Deen mai kake nufi? Wato harkasan sanda nake maka? Ni bansan wanda kake min ba."
Jalal yace "oh my God! Seemah meke damunki yau? Ko kin tsaya kinji karshen maganata?"
Dariya Seemah tasa tace" just teasing you! Kasan me? Inaso inga ima tsokanarka."
Iska Jalal ya furzar sannan yace " zan rama ne." Tace guess what? Dad ya fasa zuwa muje d'an haka zamu iya had'uwa.
Wani sansanyan murmushi Jalal ya saki yace inzo gidanku mu tafi? Tace a'a zan zo wajen Company d'in sai kazo mu tafi, yace alright nan sukai sallama tabi wayar da kallo tarr da manna mata kiss.
Dad yana shiga yai parking har ya nufi ciki yaji ance " Mazan England ne a kasar tamu?" Juyowa yai jin muryar d'an uwa rabin jikinsa, a zaune ya ganshi daga gefen garden d'insa yana rik'e da jarida, nan dad ya juya zuwa inda yake, suna haduwa suka rungume juna Dad yace Yaya ashe kana waje? Abba ya kallesa yace baka fad'amin zakazo ba?
Dad yai ajiyar zuciya tare da zama a d'aya kujerar yace " Yaya su Seemah sunzo ko?" Wani mugun kallo Abba ya sakar mai ya had'e fuska kamar zaki dama shi bashida fara'a, yace" Isma'il da hankalinka ka turo yarinyar nan kasar nan?"
Dad yace " Yaya ya zanyi? Yarinyar nan takai shekara 20 'yan uwanta da ita kanta sun damu akan tazo nikuma sai naga kamar lokaci yaja yaci ace magana yanzu ta wuce."
Abba yace " kai kana tunanin magana irin wannan tana wucewa ne? Ko ni dana ganta jinai komai ma neman dawomin sabo."
Dad ya runtse ido yace " Yaya ka taimakeni yanda ka taimaken a baya, mu binne maganar nan da auranta da Ammar, in nace Ammar ba d'ana bane ba wani abu, nasan Ammar sarai bazai damu ba."
Abba idanunsa suka kad'a yace " wai Isma'il kanada hankali kuwa? Bakasan tsatsonta ba amma me? Ka aura mata Ammar? Wai kai wani irin mutum ne da bashi da zuciya, banda bala'in da mahaifiyarta ta ja maka yanzu kuma me? Ammar?"
Dad idannunsa suka ciciko yace " Yaya karka tunamin da abinda ya faru d'an Allah yaya, yanzu ni yaya matsalata d'aya banasan abinda zaisa Seemah cikin bakin ciki bare har tasan wannan mumunan al'amarin."
Abba ya mik'e cikin zafin rai yace " Bazan goyi bayanka akan lalatamana zuri'a ba, sannan bazan yanda kasama Ammar bakin ciki akan wata banza da ba'a............"
Da karfi Dad ya rufe ido yace " Yaya Please stop saying anything, please. "
Abba ya kalleshi yana tausayin Kanin nasa sai dai bazai yadda da hukuncinsa ba, nan yace " Isma'il inka warware mayi maganar ka gama tunanin ka shigo ciki."yana kainan yai ciki, Dad ya fara saukar da numfashi sama sama, kansa na sarawa, hannu yasa ya rik'e kansa jiyai hawaye na zubomai.
Seemah tana gama shiryawa ta fito a falo taga farida tace "Aunty zan danje ganin gari." Tace Seemah kinsan halin yaya......
Seemah ta katseta da cewa" ai shima bai hanani ganin gari ba." Tana kainan tai waje, sun fito ita da bala sai dai motarsu na fita Zaid ma kokarin shigowa sai dai ganinta a baya yasa ya saki murmushi tare da juya kan motar ya bita, sam ita batasan yana binta ba.
Suna zuwa wajen company d'in tace Bala yai parking ta mik'amai kud'i tace ka koma gida, yace madam yau dai d'an Allah......, ta katseshi da cewa " so kake in koreka daga aikin ko me?" Da sauri ya amsa tare da bata hakuri, yana fita tama Jalal waya ta iso, jitai anbud'e d'ayan gefen datake zaune ta baya da mamaki ta kalli kofar kafin tai magana Zaid ya shigo, ta kalleshi da mamaki tace " malam ya dai?"
Zaid ne ya juyo da fuskarsa tare da cewa " Wow I really miss u a lot. "
Ta kalleshi tare da nunashi da yatsa tace " You?" Yatsar ya rik'e tare da ajiyar zuciya yace " yeah Baby is me, wow har naji wani sanyi."
Hannunta ta fizge sannan ta kara nuna shi da yatsa tace " Ya Zaid don't you dare try to touch me again."
kai ya kwantar ajikin kijera yace woooo kai baby u are killing me with your charm.
Leb'e ta ciza sannan ta fito daga motar cikin takaici ta jingina da motar.
Zaid ma ya fito yazo daf da ita tare da cewa ina zamu ne Baby? Harara ta nakamai tace matsa min ko bakaga a yanda kake bane? Tafad'a tana kallan yanda ya babbaketa, murmushi ya saki sannan yace " Baby I........" Naushin da aka mai a fuska ne yasa bai karasa ba, jikake tim ya fad'i a kasa, Jalal cikin hucci yake kallan shigarsa kana gani kasan ta samarin zamani ne da sukejin kansu a sama, Seemah ganin naushin nan yasa ta kalli Jalal zatai magana taga ya kara d'agoshi zai makamai wani, da sauri ta rik'e hannun Jalal tace " Deen?"
Idanunsa sun kad'a sunyi jaa, ya kalli Zaid sannan ya kalleta yace waye? Zaid kam zafin dakemai zugi a baki ne yasa yakai hannu gefen bakinsa mezai gani? Jini? Wani kara ya saki yace jini? Jalal ya makamai harara yace kamin shiru kosai na karama wani? Zaid ya kalli Seemah yace " Babyna waye wannan da......." Jalal ya dunkule hannu saura kiris ya bugamai, sai kuma ya tsaya tare da kallan Seemah, sannan ya kalli Zaid yace baby?
Seemah ta kalli Jalal tace " My Deen sakeshi d'an uwana ne he is just joking, baka ga yanda yake magana ba? Kana gani kasan na mayaudara ne ai."
Jalal ya maimaita sunan a ansa My Deen? Tamasan ta fad'a kuwa? Kallanta yake cikin wanj shauki sannan ya tura Zaid gefe yace " Meemah me kika ce?" Ta kalleshi tace name fa? Yace " Abinda kikace yanzu da zakimin magana."
Kai ta juya tana murmushi tace muje ko? Jalal ya d'an canza fuska.
Zaid ya kalli Jalal yace " wai d'an tacema My Deen? Ahh amma kai gara ne, kamar bakasan mata da yaudara ba? Sai suce ma mutum My Heart sai ka duba wayarsu kaga ansa maka Jerk.
Jalal ya kalleshi da mamaki sannan ya kalli Seemah tare da cewa muga wayarki? Kasa tai da ido tace " So kake kabar Ya Zaid ya had'amu dakai?"
Zaid yace " Ahaf da alama ma bakada sunan mutunci a wayar." Yana kai nan yad'agama Jalal hannu yace " Boxing Man nayi nan.
Jalal ya d'auke idansa daga kan Zaid ya kalli Seemah tare da cewa muga wayarki? Miyau ta had'iya ta tina No name tasa, da sauri ta zagaya ta shiga mota sannan ta danna horn, Jalal ya bud'e motar ya shiga fuska a had'e gani yake kamar jerk d'in ma aka samai.
Seemah ta kalleshi ganin yanda yakejan mota da karfi, sai da sukaje can wanj guri sannan ya gangara yai parking tare da mik'a mata hannu alamar ta bashi, d'an yaga ta d'auko wayar da alama so take ta canza, ganin bata da niyya yasa ya fizge wayar tare da fitowa daga motar, wayarsa yadaga ya kirata, me zai gani No name ne ya bayyana akan wayar kurama sunan ido yai No name? Da rashin suna ai gwara jerk d'in ma, Seemah ce ta fito tazo kusa dashi jiki a sanyaye tace " My Deen amma......" wanj kallo daya buga mata yasa ta kasa karasa maganar, tafiya ya farayi itama tana binshi a baya, takalmi mai tsini ne a kafarta sam bata kula ba ashe dutse ne a gun kawai tai tuntube da takalmin Kara ta saka Jalal ya juya da sauri, sai dai ina? Har ta fad'i ta fara gangarawa dama kwari ne a gun, cikin tsananin rud'o ya lekata, ganinta a ya she a gefe yasa yai saurin d'ilikawa, yana sauka ya d'agota duk ya rikice ya shiga jijigata tare da k'iran sunanta, a hankali ta bud'e idanunta ta saukesu a kansa, kallansa takeyi shima kallanta yakeyi jiki a sanyaye yace "Seemah are u alright? "
Murmushi ta saki tare da cewa a hankali" ba wai rashin me zan sa maka bane yasa na saka No name, nasane saboda a time d'in ina sanka gashi fad'a kawai ke had'amu da kai shi yasa......"
Yatsa yasa a leb'anta cikin sanyin murya shima yace " Ya isa haka Meemah it doesn't matter ko me kikasa, abu d'aya na sani ina ganin sona a idanunki kamar yadda nima nake sanki."
Ta lumshe ido tace " then why?"
Kin manta nace miki zan rama? D'azu da mukai waya? Banyi tunanin abin zai jawo har ki fad'i haka ba."
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
*To u My Beely Badaru, Happy Birthday Sis, wish you long life and Prosperity.* ........😍😍😍😍😘 *Have fun it's ur day Beely.*🎂💃🏻💃🏻💃🏻
No. 2⃣6⃣
Mikewa Seemah tai tare da zama a kasan gun shima Jalal ya zauna kusa da ita kallan nesa da gun tai daji ne a gun, sannan tace " Deen Inama zan iya tsayar da lokaci?" Kallanta yau sannan shima ya kalli gun yace in kika tsayar da lokaci muna nan yaushe zamuyi aure kenan?
Murmushi tai sannan ta juyo takurama ido tace " kana ganin za'a amince dani a gidanku?" Kai ya d'aga mata yace " karki damu da wannan ni nasan me zanyi akai."
Ta d'auke idonta daga kanshi sannan tace " Ban tab'a tunanin zanji ina bukatar kasancewa da wani har inji inasan inyi aure ba."
Ajiyar zuciya yai ya kura mata ido ji yake kamar ya d'auketa su gudu, Juyowa Seemah tai itama ta kalleshi idanuwansu ya had'u da juna, jitai ta kasa d'auke ido daga kanshi, wani irin kallo sukema juna mai ciki da ma'anoni daban-daban a hankali Jalal yakai hannu gefen fuskarta yace " Meemah I promise you this, I will always love you."
Idanu ta lumshe sai ga hawaye sun zubo mata, Jalal ya kalleta yace menene? A hankali ta bud'e ido tace " Deen akwai time d'in da hawaye ke bani mamaki, suna zuwa a lokacin bakin ciki, sai dai akwai lokacin da in farin ciki yama yawa sai kaji hawaye."
Sauke hannunsa yai daga fuskarta sannan ya mik'e yace " Okay tunda haka ne mu gudu mubar garin." Mik'e wa itama tai tana dariya tace " what? Mu gudu muje ina?"
Juyowa yai ya d'ana mata hannunsa a goshi ta rik'e gun cikin shagwab'a tace ka sake ko? Yace wasa nake miki so nake insaki dariya ke kuma naga kina neman d'aukan abin serious.
Juyawa tai tana kokarin haurawa sai dai ganin abin da wuya yasa ta juyo ta kalleshi tace na kasa, Murmushi yai sannan ya matso tare da mik'a mata hannu yace " kina da ni shine kike cewa kin kasa?" Hannu ta bashi nan suka fara hawa, suna isa suka shiga mota suka juya zuwa gari, sun tsaya a traffic light sai ga wani ya kawo agoggon hannu, guda 2 ne a kwallin iri d'aya sai dai d'aya na mace ne d'aya kuma na namiji komai na agoggon iri d'aya ne, Seemah ta kalli me agoggon tace bani wannan, nan ta siya yana tafiya Jalal ya kalleta yace dama kina siyan abin kan hanya? Hannunsa ta kalla dake jikim sitiyarin mota bata tankamai ba kawai ta fara sa mai agoggo, kallanta yai da mamaki yace me kikeyi hakan?
Bata tankamai ba sai data gama sannan itama tasa nata ta jira hannunta kusa da nashi kallan agoggunan yai komai nasu iri d'aya murmushi yai yace anko kikeso muyi ko me?
Hannu ta buga a goshinta tace "Oh God ya zanyi da Deen? Baisan komai a harkar soyayya ba."
Jalal ya had'e rai yace " to in ba anko ba menene wannan?" Ta kalleshi tace " Couple watch ne baka sani ba?"
Had'e rai yai ganin an basu hannu yaja motar, Seemah ta kalleshi tace kasan meye ma'anar abindq mukasa? Bai amsa mata ba ta cigaba da cewa " it will always bring us together, haka ake cewa a England magic d'in abin kenan, sannan daga yanzu karka tab'a cirewa daga hannunka in ba haka ba........"
Sai kuma tai shiru kai ya girgiza yace " in ba yarinta ba mezai sa kiyi believing akan wannan shirman in na shire kuma sai me? Sai mu rabu ko........"
Da sauri tace "please kai shiru, kasan me? Mu acan in tsakanin saurayi da budurwa wani ya cire nashi to yana nufin wanda ya cire d'in bayaso a cigaba da relation ship d'in."
Jalal yace " inkuma ya tsage ko wani abun fa?"
" worse scenario kenan, alamar akwai bad abu dazai faru tsakanin masoyan."
Hararta Jalal yai yace " Kuma ke kina fad'amin kin yadda da wannan shirman?"
Tace " ba hadda bane mu acan munyi believing da haka ne."
Kai Jalal ya kara girgizawa yace " na manta ashe 'yar 20 yrs ce."
Harara ta makamai batace komai ba ta juya kai tana kallan titi.
Sunje daidai shiga kwanar gidansu motar Habib na fitowa daga layin, clashing sukai Habib yabi motar da kallo, tabbas motarsa ce, Kallan na ciki yai baidai gane ba saboda suna tafiya yadai ga namiji sannan a kwai mace a gefensa kamar Seemah.
Har sun hau titi hankalinsa ya kasa kwanciya ya kalli Driver d'insa yace mu koma gida, Seemah kam Jalal na ajiyeta a waje yace bari na wuce zan d'an tsaya a company kafin na wuce, ta kalleshi tace dagaske gobe zaka Birnin gwarin? Kai ya d'aga mata yace " dole insan abinda zanyi kafin sukai kud'i." Kai ta d'aga tace " I will miss you." Shima yace mee too.
Fitowa yai ya fara tafiya yana kallan motar ta wuce sai dai Habib bai ga fuskarsa ba sai bayansa daya gani, Suna zuwa kofar gida Seemah na fitowa, tana ganin motar Habib ta karasa kusa da motar, Habin ya zuge glass yace" Kanwata daga ina kike?" Ta kalleshi tace guri mai dad'i yaya.
Gaban Habib ne ya fad'i guri mai dad'i? Ya fad'a yana kallanta, tace " yaya kaje ka dawo yau da daddare sai muje gun Dad inada abinda zan fad'a muku, tafad'a tana kallan agoggon hannunta.
Habin ya gyad'a kai yace shikenan ba dad'ewa zanyu ba, amma wanda ya kawoki kamar ba Bala bane? Murmushi tai tace Some One Special ne yaya, ka bari zancen dazamuyi dakai kenan da daddare.
"Okay bari inje, Amma Some.........."
Katseshi tai tare da cewa bye yaya, tafad'a tare da shiga ciki, key kawai ta ba Bala ta shiga gidan fuskarta d'auke da tsantsar farin ciki.
Dad sai jeka ka dawo yakeyi a d'aki, yarasa daga inda zai fara tufko zaren sam komai ya cud'e mai, Ammar shine kad'ai solution d'insa, waya ya d'aga ya kira Ammar, yace Ammar ka taho Nigeria gobe, inyaso kabar Junaid akan harkokin aikin shi kad'ai, wani farin ciki ne ya kama Ammar yace amma Dad step mom fa? Shi Dad sam yama manta da harkarta, yace kabarta acan ai ba wani abu bane, kuma za'abar gida ba kowa ne? Ammar yace " Dad na gode kamar kasan hankalina nakan Kanwata wlh, Dad yai murmushi yace kaje kai booking flight, nan sukai Sallama.
Ammar wani sanyin farin ciki ne ya kamashi ashe zai ga kanwarsa kafin 1month? Kaiii shi harya kosa goben tayima.
Hmmmm
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
.
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 2⃣7⃣
Jalal zaune yake akan kujera rik'e da takardu inka ganshi zaka zaci karantawa yake sai dai sam hankalinsa baya kan takardun, Seemarsa kawai yake gani a jikin takardar tana murmushi, ya kurawa takardar ido a hankali shima ya saki murmushi jiyai an kwankwasa masa desk, da sauri ya d'ago ganin manager d'insu ne yasa ya mik'e tare da cewa " Manager yaushe ka shigo."
Kai ya girgiza yace " Jalal kwana biyu meke damunka? Sam baka maida hankali akan aikinka, gashi ka tsiri wani d'aukan excuse inka fita sai ka dad'e baka dawo ba."
Kasa dakai yai baice komai ba, da fa kafad'arsa yai yace " Please Jalal ka koma yanda na sanka, yanzu ka duba maganar project d'in nan namu, sam ka kasa maida hankali akai gashi kasan kaf Team d'in nan namu da kai muka dogara."
A hankali Jalal ya d'ago ido ya kalleshi jikinsa yai sanyi a hankali ya furta" I will work really hard Manager."
Yace " thank you Jalal." Yana kainan ya bud'e office d'insa ya shiga, Jalal kam fita yai ya shiga toilet, ruwa ya zuba a fuskarsa sannan ya sa hannayensa biyu a kuncinsa yace " Wake Up Jalal, Get a Hold of Yourself. " yana kainan ya fito ya koma office ya fara aikinsa, sai dai jefi jefi yana kallan agoggon hannunsa.
Seemah kam tagama yanke hukuncin fad'ama su Dad maganar Jalal saboda sam batasan sud'inga zuwa wanj gun in zasuyi zance, bayan tayi Sallar magrib ta fito falo, anan ta taradda Farida dasu Ra'isa, suna ganinta suka fara murna ta karaso kusa dasu ta zauna tace homework akeyi? Suka d'aga mata kai, tace to azo nizan koya muku, da gudu suka mik'e daga kusa da Farida suka dawo kusa da Seemah, dariya tai tace Aunty na mik'i kwace.
Cikin sakin fuska tace " ni naji dad'in kwacen ma dan dama na gaji."
Seemah ta dukufa tana koya musu homework har ya Habib ya dawo, da sauri ta mik'e taje kusa dashi tace " Yaya ka dawo? Ka fad'ama Dad?"
Kanta ya dafa yace " oh ni kaina nakosa inji me Autarmu zata fad'amana haka, na fad'ama Dad yace muje gidan da yake."
Da mamaki ta kalleshi tace " wani gida yake?"
" ni kaina ban sani ba ashe Dad daga can yasa Abbansu Zaid ya d'inga masa gini, yana turo kud'in sai d'azu ya fad'ama."
Ta jinjina kai tace " ohhhh lalai Dad da alama yayi tanadin bikina, kasan ku maza ne a gidan Abba akai taronka haka ma za'ai nasu ya junaid, duk da banzo bikinka ba amma naji a jikina bayan bikin kane Dad yafara min tanadi."
Dariya sosai Habib yai yace " lalai kanwata kin girma, mene? Tanadin bikinki? Hahhhhh lalai zan sanar ma Dad 'yarsa aure takeso."
Idanu ta rufe sannan tace " yaya mu tafi to ko?" Yace " haba kanwata a barni inga 'ya'yana da matata tukunna mana."
Baki ta turo ta juya baya alamar fushi, Farida data dawo daga kai briefcase d'insa d'aki ta tsaya tana kallam ikon Allah, Habib yace "naji muje to tunda haka kikeso." Juyowa tai ta saki ihu tace " yauwa my bros." Da gudu ta wuce d'akinsu d'auko mayafi, tana kallan Aisha a zaune ko kulata batai ba taja mayafi tai waje, Aisha ta bita da tsaki tace " wani sa'in ta kulani, wani sa'in kuma ta nuna batamasan inagun ba."
Seemah na fita, Habib ya kalli Farida yace " sai na dawo" sannan yabi goshin su Ra'is da kiss suka juya sukai waje, suna shiga mota Ammar ya k'irata, tad'aga wayar ta shiga zubamai shikuma yana biyeta,bai gayamata gobe zaizoba saboda yanasan ya bata suprise.
Habib ya girgiza kai yace " Seemah in baki shawara?" Tace tame fa? Yace " karki kuskura kuyi waya da Ammar a gaban saurayinki ko wanda zaki aura, in fact karma ki bari su had'u.
Da mamaki tace "meyasa? Bayan yayana yafi ji dani nima kuma haka."
Habib yai murmushi yace "shine matsalar ai, yanda kukeji da juna in saurayinki ne ko budurwarsa sukaga yanda kuke zasuyi zargin wani abu."
Dariya sosai tai harda tafa hannu tace " Zargin me zasuyi bayan yayana ne uwa d'aya uba d'aya?"
Habib yace " wannan shikad'ai ne hujjar zai sa suyi shiru."
Takarasa dariya tace " to da wannan hujjar da mezai sa suyi zargin wani abu? Kaidai kawai yaya kanaso ka cina nine."
Haka yai ta tsokanarta har suka isa wani katon gida, bawai kato bane sosai sai dai yana da nasa girma d'an yayi biyun na Ya Habib, Habib ya kalli gidan yace " Lalai Dad har yai gida babban a garin nan ni babban d'ansa ban sani ba? Tace kamanta na fad'a maka? Yace auuuuuu na manta ai ashe fa na bikin Seemah me.
Tai kasa dakai tana murmushi, an bud'e musu gate sun shiga, Habib ya kara kallan gidan fitilon da akai kwalliya dasu a waje sun kara fito da filin gun, Seemah tace wow yaya bazan bika ba, na dawo gidanmu kenan.
Ya d'an ja kunnenta yace " ina kika isa? Ai kafata kafarki, kuma ma kinga ai ba masu girki a gidan, ko kin iya abinci ne? Ta ciji leb'enta tace " yaya fad'ar bakar magana ko? Zan baka mamaki ne."
Tana kai karshen maganar ta bud'e kofar motar ta fito, ta nufi gidan, Habib ma ya fito sunyi knocking sosai har Habib yafara kokarin k'iran Dad sai kuma aka bud'e kofar, Dad ne tsaye sanye da jallabiya, yace " Sorry my Princess na barki a waje ko?"
Ta had'e rai tace " da alama Dad bakai farin cikin ganina ba."
Hannu yasa ya jawota ciki yace " Sorry Swthrt kema kinsan ba haka bane wani tunani nakeyi sam banjin kwankwasa kofar ba."
Ta furzar da wata iska sannan tasa hannu tad'an biki goshinta tace " Oh God! Yazanyi da Dad d'ina? Dad kamanta an hanaka tunani mai zurfi? Ko kake hawanjinin ka ya tashi in shiga uku?"
Shiga ciki yai yana murmushi, Habib ya matso kusa dashi ya kara kallan falon komai ansa na furniture's da kayan kallo, yace " kaiii Dad yaushe akai gidan nan da har komai an saka?"
Dad ya kalleshi yace " kaidai kanada aure karma kai tunani zan baka aran d'aki a gidan nan." Ya juya zai ma Seemah magana sai dai bata gun, ya waige waige yace " Seemah!!!" Tace naam, ya juya da sauri inda maganar ke fitowa, tana kan matattakalar beni, yai murmushi wato d'akinta take nema tunda tasan Dad yasan tafisa Sama, kallanta yai yace muje in nuna miki d'akinki.
Da gudu ta karasa Sama tare da bud'e d'akin datake tunanin shine, baki ta bud'e ta kasa karasawa ciki Habib ya karaso da dariya yace " hala d'akin naki ba komai sai katifa........"
Shikanshi kallan d'akin yake komai na d'akin pink ne sai ratsin milk, ya juyo ya kalli Dad, da sauri Dad ya juya baya yana sosa keya, Seemah da gudu ta juya ta fad'a jikin Dad tace " Dad thank you soo much, Dad duk wani abu danakeso kafin na fad'a kake min, I love you soo much."
Da sauri ta sakeshi ta koma d'akin ta shiga kallan komai, Habib ya kalli Dad yace " Dad amma yaushe ka gyara d'akin nan?" Yai murmushi baice komai ba, ji sukai Seemah tace " Dad ku shigo mana," nan suka shiga suka kalleta ta baje akan gado, suna shigowa ta mik'e ta kamo hannun Dad ta zaunar akan gadon, tace " Dad na fad'a soyayya mai karfi, yazanyi inbanyi shekara 2 a d'akin nan ba?" Tai maganar cikin shagwab'a, da mamaki Dad ya kalleta sannan ya kalli Habib yace " me kikace Seemah? " ta mik'e tace ehem, Dad kasan me? Ya girgiza kai, tace wani guy nake bala'in so, ban tab'ajin abin da nakeji ba sai a kansa.
Gaban Dad ne yai wani irin mugun fad'uwa, cikin tsoro ya kalleta yace " just now what did u say?"
Ba Dad kad'ai ba ko Habib yasha jinin jikinsa, shima yace " Seemah me kikace?" Tace" ahhhhh so nawa zan maimaita, yaya shine wanda ka tambayenk d'azu, ah kama sanshi ai jalal na gun aikinka."
Dad ya runtse ido abinda yake tsoro shikenan yana shirin faruwa, Habib cikin b'acin rai yace " Haba Seemah wannan yaron kike so? Yaron da ko kayan jikinsa kika kalla kinsan abinda zasuci a gidansu ma da alama wahala yake basu, shi kike cemana kina so?"
Dad cikin tsoro da mamaki ya kalli Habib yace " mene?" Seemah ta mik'e taye taje kusa da Habib ta rik'e hannunsa tace " Yaya nifa a hakan nace ina sansa, meyasa bazaka bani goyon baya ba? Yaya bazaka gane irin san danake mai b..........."
Jitai an wanke ta da mari, cikin firgice ta kalli Dad da itadunsa suka kad'a sukai jajjawur, kamar me shirin zubar da kwalla mai zafi, Cike da mamaki Habib ma ya kalleshi, bai tab'a ganin Dad a wannan yanayi ba, cikin fad'a Dad yace kada ki kuskura ki kara min zancen yaron nan, sannan ku wuce ku koma gidan Habib dare yayi, Seemah data kasa tantance meke faruwa, mafarki take ko kuwa gaskiya ne, kamar bata motsi take kallan Dad, Dad ya kalli Habib yace " sannan kada ka kuskura ka kara barin Seemah ta fita, in fitar ta zama dole sai ka sanar dani." Yana kainan yai waje.
Seemah tabi bayansa da kallo, tama kasa kuka kawai hannunta ne a gun, Habib ne ya tako a hankali yazo kusa da ita zai dafa ta, juyawa tai da gudu tana hawaye tai kasa, mota ta bud'e ta zauna ta saki wani irin kuka mai ban tausayi.
Habib ya sauko tare da kallan Dad dake zaune a kan kujera idanunsa a rufe, yasan halin Dad da kuma yanda yake san Seemah, da alama ya mareta ne amma a zahirin gaskiya yafita jin zafin marin, harzai mai magana yaga kamar gwara ya kyaleshi, shima yai waje.
Yana shiga mota yaji kuka da Seemah take ya b'aci cikin damuwa ya kalleta yace " Seemah is okay kema kinsan Dad bawai yaso dukanki bane, ko ya tab'a dukanki?" Ta girgiza kai cikin kuka tace " Yaya menene laifina? D'an inasan Jalal ko d'an bayaso inso talaka?"
Habib yace " ya isa haka, gwara ki bar maganar wani Jalal d'an ko Dad bai hanaki ba ni zan hanaki."
Takara sa kuka, meyasa kowa bai fahimceta ba? Ita tad'aurawa kanta soyayyar nan? Basa ganin inta rabu da Jalal ta rabu da farin cikin ta ne?
Jalal kam jin d'akin ya isheshi ga sai hira suke da shewa yasa ya fito waje, yana tsaye a kan hanyar layin banda tunanin Seemah ba abinda yakeyi, gobe zaije gida ya sanar dasu...........wani me keke ne yayo kansa gadan gadan da sauri Jalal ya tsalle daga gun zuwa jikin bishiyar dake gun, hannunsa ne ya bugi bishiyar yai ajiyar zuciya tare da kokarin mekewa, mai keken ne ya taho da sauri ya taimaka mai yace " kaji ciwo ne? Jalal ya kalleshi yace a'a, amma wani irin tuki kake haka?"
Yace " Yahkuri wlh fitilar kekence ta mutu sam ban kula ba." Jalal ya kalleshi yace to Allab ya kiyaye, mutumin ya juya, hannunsa Jalal yaje kad'ewa mezai gani? Agogonsa ne ya fashen, cikin takaici ya kalli agogon kamar yasa ihu, kalaman Seemah ne suka dawomai, na in agogon ya tsage akwai Bad abu dazai faru da su.
Dariya ya saki yace " Jalal meke damunka? How can you believe that?"
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
*_This page is dedicated to you My Intimate Friend Aisha Muhd Umar, May almighty Allah grant all your good wishes_* ........
No. 2⃣9⃣
Jalal haka ya zauna yaci abincin nan bayan ya gama ne ya kalli Zainab dake gogema Zahee jiki yace " Umma fa?" Tace tana d'akina, ya mik'e tare da cewa bari in ganta tace to, har yakai bakin kofa a hankali yaji tace " Yaya?" Jalal ya tsaya ba tare da ya juyo ba, tace " nasan akan me ranka ya b'aci saboda Abba yaje aiki ne, sai dai kayi hakuri yaya amma Abba saboda harkar auranmu yake tara kud'i" da sauri Jalal ya juyo ya kalleta tai saurin yin kasa dakai tace " tun bayan ankai kud'i Abba kullum sai ya fita yin aiki, duk dabansan wasu aiyukan yakeyi ba amma naji dakansa ya fad'i dalilin aikin da Umma ta tambayeshi."
Jalal jiyai kamar an kwaramai ruwan sanyi, cikin sanyin jiki ya zuge labulan ya fita, ya na fita ya tsaya a jikin bango ya zaiyi? Shidai gaskiya magana d'aya ba yazan Zainab, a matsayin kanwa ya d'auketa ba wai a soyayyar aure ba, yai shiru can ya taka zuwa d'akin Zainab, bayan yayi Sallama Umma ta amsa daga ciki ya zuge labulan d'akin a bakin kofa ya tsaya, ko ba komai yasan Zainab akwai tsafta da san gyara, kallan Umma yai cikin sanyin jiki yace " Umma inada magana." Ta d'ago ta kalleshi, sannan tace ka zauna sai muyi maganar, a kasan ledar d'akin ya zauna sannan yace " Naso sai Abba ya dawo in fad'a muku gaba d'aya amma yanzu sai nai tunanin gwara ma fara sanar dake."
Ta kalleshi cikin damuwa tace " menene Jalal? Wani abun ne ya faru?"
Kai ya jijiga mata yace "ko d'aya kawai dai inasan insanar daku abinda ke rainane."
Umma batai maganaba amma ta tattara hankalinta gaba d'aya kansa, Jalal yai kasa dakai yace " a gaskiya Umma inada wacce nakeso, ina santa sosai kamar raina, sannan banaji zan iya auran wata ba ita ba.."
Gaban Umma ne ya yanke ya fad'i cikin tsananin firgice da tsoron kalaman Jalal tace " Jalal me kake nufi da kalamanka?"
D'agowa yai ya kalleta yace " Umma kinsani sosai tunda ke kika haifeni, kinfi kowa sanin Zainab a matsayin kanwa ma d'auketa kamar yanda Zahee take a guna."
Umma ta mik'e taye ta matso kusa dashi ta rik'e hannayensa cikin rud'ani tace " Jalal dan Allah karkabar mahaifinka yaji wannan zancen, d'an inyaji daga ni har kai bansan abinda zai mana ba."
Jalal ya runtse idanunsa yace " Umma please ku barni ko sau d'aya nai abinda nakeso, tun dana taso bam tab'a yima Abba musu ba arayuwata, hatta abinda zan karanta a jami'a shiya zab'amin da kansa ba wai san raina bane, d'an Allah Umma wannan karan ya shafi rayuwata gaba d'aya ki taimakamin......"
Idanunta suka ciciko ita kad'ai tasan wahalar da d'anta ya sha, to amma ya zasuyi? Ko ita tanasan Zainab.
Zatai magana aka yaye labulan da karfi akace me kace Jalal? Juyawa Umma tai da sauri ta kalli Abba da idanunsa suka kad'a sukai jaa na b'acin rai, Jalal yai kasa dakai yace " Abba ina kwana?" Ran Abba yakara b'aci yace nace me kace? Ya fad'a tare da shigowa ciki, Jalal ya d'ago a hankali yace " Abba inada wacce......."
Cikin tsawa Abba yace " kada ka kuskura ka kara maimaita kalaman nan, kafi kowa sanin Zainab itace matarka ko kaki koka so."
Jalal ya d'ago ido ya kalli Abba, shikansa yasan yauce rana ta farko daya tab'a musanta maganar mahaifin nasa yace " Abba dan Allah ka barni na auri wacce nake so, wlh yarinyar nan itama ba ruwanta."
Abba ya fusata yace " yau ni Jalal zaka kalla ido cikin ido kacemim wai in barka ka auri wacce kake so? Anya kuwa kaine Jalal?"
Kasa kawai Jalal yai da ido jiyake zuciyarsa na tafasa, Abba cikin takaici ya bar d'akin yai waje da sauri, Umma ta kalli Jalal cikin tausayi sai dai batasan me zatace ba itama ta fito, Zainab data fito daga d'akin Zahee jin hayaniya ta kalli Umma tace " Umma lafiya?" Umma takasa amsa mata kawai d'aki ta wuce.
Jalal kam jin zuciyarsa na zafi kawai yai saurin kiran Seemah, tana zaune kusa da Ammar tana ganin kiransa ta kalli Ammar tace "yaya saurayina ya kirani." Da mamaki ya kalleta sai dai kafin yai magana ta gudu d'aki, tana shiga ta d'aga tare da sakin ajiyar zuciya, jin shiru yasa tace Deen? Kanaji na?
Wani abu ya had'iya sannan yace " Meemah ya kika tashi?"
Ta kwanta akan gado tare da jan bargo tace " na tashi lafiya sai missing d'inka dake neman yimin yawa."
Bai san sanda ya saki murmushi ba yace " Na isa fa?"
Da sauri ta yaye bargon tace " da wuri haka? Hmm kunyi maganar? Sun yarda? Ya kukai?"
Dariya yasa sosai yace " duk ni kad'ai? Wanne akeso in amsa?"
Dasauri tace" ya kukai please? Fad'amin kaji?"
Murmushi yai yace bamuyi maganarba tukun yanzu na iso, tai ajiyar zuciya tace " ahhh jinai kamar zuciyata zata fito dan tsoro."
Ya kara sakin murmushi yace" da ina kusa dana ba ki......" da sauri ta sa hannu a goshinta tace " wayyo zafi" tai maganar cikin shagwab'a, dariya ya saki tace " Deen me na maka ka d'ana min?"
Dariya sosai ya d'ingayi yace " Ahhhh that's My Meemah you always make me laugh."
Tai murmushi tace " In mukai aure sau 10 zan saka dariya a rana."
Dariya ya sakeyi zai magana yaga Zainab a tsaye a bakin kofa idanunta sai zubar da hawaye sukeyi, kallanta yai sai yace ma Seemah" zan kiraki anjima." Tace okay miss u...... katse layin yai ya kalli Zainab, ya mik'e zai zo gunta da sauri ta juya da gudu tai waje , kai ya dafa yace " Ya Allah gani gareka."
Seemah kam kwanciya tai ta rungume pillow a kirjinta tace I miss you Deen Muah......sai kuma tai saurin liliba da bargo wai ita a dole kunya jitake in aka rabata da Jalal to lalai karshen rayuwarta yazo.
Mikewa tai ta sauka kasa ta zauna kusa da Ammar, kallanta yai yace " kingama waya da saurayin?"
Ta rufe idanta da hannu biyu sannan ta bud'e ido ta kama hannunsa tace " Ya Ammar ina tsananin san Deen, jinake in aka rabani dashi kamar........"
Had'a rai Ammar yai yace " bana ce karki kuskura kiyi irin wannan soyayyar ba?"
Ta kalleshi tace " ni kaina Yaya bansan ya akai nazama haka ba."
Ya mik'e tsaye yace da alama ma kinfi sanshi akaina, dariya ta saki tace kai yaya ka manta kai Special Oppa ne?
Ya harareta baice komai ba, ta taso ta rike hannunsa tace " yaya bansan meyasa Dad bayasan Jalal ba."
Da mamaki Ammar ya kalleta yace " ya ganshi ne?" Tace " a'a kawai daga fad'amai inada wanda nakeso naga ransa ya b'aci."
Ammar yai murmushi yace" that means ba saurayin naki bane baiso, bayasan kiso wani ne."
Tai shiru can tace kuma fa hakane to meyasa? Ya ce inazan sani? K'ila bayasan ki raba hankalinki ne, kina karatu ga soyayya.
Ta jinjina kai Ooooops Nagane maganar.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 2⃣8⃣
Suna isa gida ta wuce da gudu d'akinsu tana zuwa ta fad'a gado ta cigaba da kukanta, Jalal kam sai kiranta yake a waya bata d'agaba, sam hankalinsa ya gaza kwanciya, Habib ma d'aki ya wuce ya zauna a bakin gado, ya rasa meke faruwa, da sauri ya d'au waya ya k'ira Sagir bayan sun gaisa ya tambayeshi ya labarin abokin ka kuwa? Sagir yace wa fa?
" Jalal mana, ni a wani gari yake ne?"
Sagir yai shiru yana mamakin tambayoyi sai can yace " a birnin gwari yake, yaron nan yallabai abin tausayi ne."
Habib yace " ayya iyayensa acan suke kenan?"
Sagir yace " eh nidai ban tab'a zuwa ba amma nasan talakawane sannan yana da kanwa da take kwance ba lafiya, yallabai yaron nan tare mukai makarantar jami'a ma tausaya mai kwarai, ga karatu ga sana'oi dayake saboda harkar makarantarsa dakuma iyayensa."
Habib yai ajiyar zuciya lalai Seemah batada hankali, amma a fili yace " na tausaya mai, iyayensa basa wani aiki kenan."
Sagir yace " gaskiya banaji, d'an inaji kamar mahaifinsa harkar ko gona yakeyi ne, bandai san takamaimai me yakeyi ba."
Habib yace " okay Allah ya rufa asiri, sai da safe." Yana kainan ya katse layin tareda rik'e kai, lalai Seemah yarinta na damunta, ai ko Dad bai hanaba shi bazai bari ta aure wani Jalal ba.
Seemah kam ganin kukan ya isheta yasa ta mik'e zaune tare da d'auko waya d'an ta fad'ama ya Ammar, ganin missed calls d'in Jalal ne yasa ta saki wani murmushi sannan ta mai text, tana gun ya Habib ne suna hira.
Jalal na ganin text d'in yai ajiyar zuciya tare da kwanciya.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Duk yanda Dad yaso hankalimsa ya kwanta yai bacci abin ya gaggara sai juyi yakeyi, tunaninsa d'aya yazaiyi ya warware wannan al'amarin ba tare da Seemah tasha wahala ba? D'an bazai yadda da auranta da wani bare ba, kar azo maganar aure abinda yake a b'oye ya fito fili.
*Washegari*
Da wuri Jalal ya shirya ya nufi tasha, yai sa'a yana zuwa ya samu motar dazata birnin/gwari, nan ya shiga suka d'au hanya........
Seemah kam ta tashi da ciwon kai sakamakon kukan data sha jiya, zama tai a kan gado, tana tunanin matakin daya kamata ta d'auka, Ammar da Junaid su kad'ai suka rage mata, da gudu Ra'isa ta shigo d'akin tace mata "Aunty kizo Uncle Ammar yazo." Cikin mamaki had'i da farinciki ta kalli Ra'isa, tace " Ra'isa dagaske kike? Ya Ammar d'inna ne yazo?" Kai ta d'aga mata, sam ta manta rigar bacci ce a jikinta da gudu ta diro daga kan gado tai falo tana zuwa ta kalli Ammar dake tsaye, ai da gudu ta fad'a kansa duk yanda yaso ya d'aure amma ina sai da suka fad'i kasa, Farida ta girgiza kai, wannan dab'iar fa? Seemah kam d'agowa tai ta kalli Ammar tace " Yaya sorry na yadda kai, amma yaya ya akai haka?"
Ammar yai murmushi sannan ya kalleta sai yanzu yaga kayan baccin dake jikinta, shara shara ne ana hango half-vest d'in data sa, yace " d'aga ni to, d'an naga alama neman karya wannan yayan naki kike."
Tai dariya tare da d'agashi tace " yaya tsaya d'an mintsineni a fuskata kad'an, so nake inji ko mafarki nake."
Dariya sosai tai sannan ya matso ya kama kumatunta da karfi sai datai kara, yace " ya? Yanzu kin gane?" Kara shigewa jikinsa tai sannan tace "yaya kamar kasan ina tsananin nemanka." Yai ajiyar zuciya tare da kallan gefe yace " yazanyi da kanwata? Ai in tana nemana dole jikina ya bani."
Ta zaro ido tace " dagaske kake yaya? Saboda haka kazo?"
Dariya yai har da zama akan kujera yace " lalai kanwata bata girma ba haryanzu zolayar ki nake."
Turo baki tai tare da harararsa sannan tace yaya bari nai sauri nai wanka zamuyi magana.
Ya d'aga kai, ta juya da sauri, Ammar ya bita da kallo fuskarsa d'auke da murmushi, wani sanyi ke ratsashi dayaga Seemah.
Jalal an isa gida lafiya a waje ya tadda Zainab tana wanke-wanke, kallanta yai cike da tausayi tana ganinsa ta mik'e da sauri tare da gyara hijab d'in dake jikinta, yana mamaki shidai ko a d'akinta take tanaji da hijab take zama, bai tab'a ganinta ba hijab ba, katseshi tai cikin murna tace " yaya? Kaine? Sannu da zuwa."
Murmushi yai yace " aiki kike?" Tai kasa da kai ya kalleta yace " sannu zainab, ana sanyi kina wanke-wanke a wajen nan?"
Ta kasa kawai dakai tana wasa da 'yan yatsun hannunta, umma ce ta fito tace " kaima dai ka mata fad'a Jalal, duk yanda nai da yarinyarnan tabarni nai amma bata yarda sam hanani komai takeyi."
Tausayinta ya kara kamashi, jiyai tace " Umma ina zan bari kiyi aiki? Bayan kema hutu kike bukata? Kullum kina gun Zaheeda kina kula da ita."
Umma tai dariya tace Jalal kajita ko? Jalal kam kallanta yake cike da tausayi, Zainab ta d'ago ta kalleshi ganin yana kallanta yasa tai saurin yin kasa da ido, tace " yaya ka shiga ciki sanyi akeyi." Kallanta yai ko rigar sanyi babu a jikinta sai hijab amma wai shida yake sanye da jacket tama cemai ana sanyi, matsowa yai kusa da ita yazare Jacket d'in ya mik'e mata yace " kisa" ta amsa tana kallansa, Umma ta saki murmushin farin ciki ya sani ko Jalal baisan Zainab bazai wulakantata ba, Jala kam yama gani ta amsa ya matsu kusa da Umma yace Umma mushiga, nan sukai ciki.
Kusa da Zaheeda ya zauna idannunsa sunyi jaa, itama idanunta na kansa, sai dai kana ganin alamun fuskarta kasan tana farincikin ganinsa, murmushi ya k'akaro tare da shafa kanta yace My Zahee kinyi missing d'ina ko? Idannu ta lumshe alamar eh, ya had'iye wani abu sannan ya juyo ya kalli Umma yace Umma ina kwana? Tace lafiya lau Jalaludeen, ya aikin?
Yace Alhamdulila, Umma ya jikin Zahee? Takalli Zaheeda tace gatannan dai jiya iyau, sai dai kwanan nan jikin baya wannan tashin.
Jalal ya kalle Zahee yace " Abba fa?"
Tace " yafita wai akwai wani mutumi dake neman masu mai lambu, shine sukaje shida Sani, Jalal ya gyad'a kai, yace " amma Umma kema ya kamata kid'inga hanashi wannan sana'ar da ba amfani take mai ba."
Umma tai shiru tace " kaima kasani bayasan zama guri d'ayan nan."
Jalal ya runtse ido yace " amma Umma kima ganin yanda kafarsa d'aya take? A dalilin me zai d'inga zuwa yanama wasu aiki bayan shi kanshi yana neman hutu? Sannan inya gama kwata kwata nawa suke bashi? Ya wuce dubu 1 ko 2?"
Umma tai shiru, Jalal yacigaba " Umma please ki taimaken ki hana Abba wannan yawon, in kuma lalai sai yayi sana'a ne, to ina ganin in na d'au albashi wannan watan mufara gina karamin shago a wajen gida inyaso in muka gama sai muji me yakesan ya zuba."
Umma ta kalleshi tace ka manta yace " bayasan kasuwanci?"
Cikin zafin rai da takaici Jalal yace " Umma wai menene dalilin dazaisa yak'i kasuwanci? Bayan muna halin rashi ne?"
Umma ya share kwallar data zubo mata tace " Jalal wani babban al'amari ya faru a shagon mahaifinka ne a shekaru masu yawa da suka wuce, 'yan garin nan suka sama shagon wuta, basu san me ya faruba bakuma su duba halin da maishagon yake ciki na bakin cikin abinda ya faru a shagonsa ba."
Jalal ya mik'e cikin b'acin rai yace" nasan wannan Umma, duk dabansan abinda ya faruba amma nasan wannan nasan kuma akan abunda ya farune kafarsa d'aya ta zama haka, sai dai tunda kinki sanar dani abinda ya faru bansan me zance ba"
Yai ajiyar zuciya yace" amma kome ya faru bakya ganin shekaru masu yawa sun wuce da za'a ajiye wannan al'amari?"
Umma ta kara share hawayenta tace " Jalal d'an Allah karkama mahaifinka zancen kasuwanci, ba'abinda ya tsana irinshi."
Jalal ya kalli Zaheeda da yaga hawaye na zuba ta gefen idanunta, sama ya kalla d'an boye hawayesa, ya tsugunna kusa da ita ya saki dariya" ha ha ha Zahee karki damu hira kawai muke da Umma ba wani abu bane kinji."
Umma ta kalleshi cikin tsananin tausayi, ganin yanda yake neman faranta ran kanwarsa yasa taji zaman yana neman ya gagareta, da sauri ta mik'e tai waje, Zainab da ta taho kawomai kunu da kosai, duk taji abinda sukai, ita kanta hawaye take sosai, ajiye kwanon tai ganin Umma ta fito, har zata bita taga kamar be dace ba, nata hawayen ta goge sannan ta shiga d'akin da fara'a, tace " Yaya kanaba Zahee labari ne?"
Ya juyo ya kalleta yace " sannu zainab. " ta zauna a d'aya gefen Zahee itama tana bata labari.
■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■
Seemah da sauri ta wanka ta zura kaya ta fito, akan dinning ta sami Ammar da ya Habib, taje kusa da Ammar ta zauna ta gaida Habib, Habib yace " baxan amsa ba tunda dai baki zauna kusa dani ba."
Ta kalli Ammar tace " Sorry Ya Habib naga tsohuwar zuma, kasan tafi zaki."
Ammar yasa dariya yace " Yaya sai dai kai hakuri kasan ni special ne."
Habib ya girgiza kai yace " lalai Seemah ni zaki ma haka ko? Shikenan nima zan rama."
Ta kalli Ammar tace " ya Ammar I miss you alot."
Ya shafa gefen fuskarta yace " ban yarda ba, bayan banga kin rame ba sai kiba danaga kinyi?"
Zaro ido tai ta kalli Habib tace " Ya Habib da gaske ban rame ba?"
Habib ya harareta yace " sai kiba dakikai kamar me...."
Ahhhhh ya zanyi? Ta mik'e ta shiga zirya tace ya Ammar ya zanyi? Kasan fa banasan nai k'iba? Noo bazanyi breakfast ba, ta kalli farida datai sakwalo tana kallanta, taje ta rik'e hannunta tace " Aunty azumi zan fara."
Habib da Ammar kam banda dariya ba abinda sukeyi.........
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 3⃣0⃣
Dad zaune kusa da Abba dayazo ganin gida, Dad ya kalli Abba yace "Yaya haryanzu banji kace komai ba?"
Abba ya kalleshi fuska a had'e yace " Meyasa baka fahimta ne Isma'il? Taya zaka had'a jininka dana....."
Dad ya katseshi dacewa" Haba Yaya meyasa bakwa fahimta ne, Seemah 'yatace akoda yaushe, duk da a baya nima nayi tunanin kaita gidan marayu, amma daga baya na gane haka Allah ya kaddaramin, kuma inaji a jikina Seemah Amanace Allah yabani."
Abba ya kalleshi cike da tausayi yace " Nafahimci abinda kake nufi amma kai kana tunani su Hajiya zasu yadda da wannan fatawar taka?"
Dad yace " nasani yaya shiyasa nake rokon ka daka taimakamin, Yaya banaso wani abu da zai d'aga ha kalin Seemah."
Cikin takaicin hali irin na kaninsa Abba ya m'ike yace " Seemah Seemah Seemah!!! Haba nagaji da yanda ka damu da yarinyar, anya ma kana kaunar 'ya'yanka kamar yanda kake santa? Ko dai akwai wani abu dabaka sanar dani ba? Bana tunanin akwai mutum irinka a duniya, mahaifiyar yarinyar nan tajaza maka masifar da bazaka tab'a iya wanketa ba amma kai kamar mara tunani."
Hawaye ne suka taru a idan Dad ya mik'e shima ya kalli yayan nasa yace " Yaya alokacin kunki fuskarta ne amma ni kad'ai nasan halin datake ciki."
Cikin takaici Abba yace " Nikarka karamin zancen wata mata can da banasan in tunama nasan ta, sannan ni haryau ban yarda ma........"
Cikin zafin Rai Dad yace " haba yaya! D'an Allah karka kara furtamin kalaman nan."
Abba a zuciye ya bar gidan, Dad ya zube a kasa kawaa yasa kuka kamar karamin yaro, gyambun dake birne a zuciyar sa ya famu, kuka yake sosai bai masan sanda Habib ya shigoba, dayake Abba a bud'e yabar kofar, Habib ya tsaya a bakin kofar yana kallan mahaifinsa jiyai kawai jikinsa ya d'ebi rawa baisan sanda shima hawaye suka fara zubomai ba, kallan mahaifinsa yake cikin wani yanayi mai wahalar fahimta, meyasamu dad? Me akamai? D'an da alama kukan daga zuciya yake fitowa bawai ciwo yaji ba ko rashin lafiya bane.
Habib a hankali ya karaso kusa da Dad ya rungumeshi ta baya baice komai ba sai kuka shima da yakeyi, A hankali Dad ya fara kokarin saita kansa, ya juyo da fuskarsa kan Habib, baice mai komai ba Habib ya rungumeshi yace " Dad menene yakecin zuciyarka haka? Menene ke damunka da har zakai irin wannan kukan? Dad ni babban d'ankane kuma Abokinka ko kamanta haka kake cemin in ina cikin damuwa?"
Dad ya kalleshi kawai girgiza mai kai yake, Habib ya kakaro wani murmushi yace shikenan Dad na d'auka munyi shakuwar dazamu d'inga raba matsalolinmu.
Mik'ewa yai ya fita Dad ya bishi da kallo cikin tausayi sai dai yana tsoron furtama Habib maganar.
Jalal kam ganin zaman da yake ya isheshi yasa ya mik'e da sauri yai waje shima, ya fara neman Zainab, yana tunanin ita kad'ai ta rage masa a mafita yasani inya sanar da ita abinda ke ransa zata goyamai baya.
Sai dai duk yanda yaso nemanta bai sameta ba, haka ya gaji ya koma gida, yana shiga ya ganta a tsakar gida tana shara, cike da mamaki ya karasa gunta yace " Zainab inasan magana dake."
Jiyai Umma tace " bazata ba, Jalal yaushe ka zama haka? Nasani sarai abinda kake tunani."
Jalal yace " haba Umma meyasa bazaki fahimceni ba?"
Zainab ta d'ago fuskarta duk ta b'aci da kwalla, ta kalli Jalal shikin bakin ciki tace " Yaya yaushe ka zama haka? A da na d'auka kai mutum ne mai tsananin girmama iyayensa, menene dalilin dayasa ka canza? Nice bakasan aure? Saboda ni kake wannan abun?"
Jalal ya had'e rai wani kallo ya buga mata yace "in ima magana da Umma karki kuskura ki kara katseni." ajiyar zuciya tai idanunta suka kara zubar da kwalla tace " Umma d'an Allah kubar shi ya auri wacce yakeso." Tana kainan tai d'aki da gudu ta rufo kofar, kallo Jalal ya bita dashi, Umma tace " Jalal ka bani mamaki." Itama ta juya ciki.
Iska ya furzar daga bakinsa wayarsa ce tai kara ya cirota daga aljihu, ganin Sagir yasa ya d'aga wayar Sagir yace " Jalal kana ina? Kazo Habib na nemanka."
Jalal yace " bangane yana nemana ba? Yau asabar ban fahimci dalilin dazaisa a nemi ni ba bayan ina hutun weekend. "
Sagir yace " to d'an ka'ida amma please kazo yanasan ganinka wajen 5 yace it's urgent."
Harzai musa sai kuma yai tunanin da alama maganar bata aiki bace mayb tsakaninsa ne da Seemah, da sauri yacema Sagir okay zanzo.
Yana katse wayar ya shiga d'akin Umma, a zaune ya ganta ta baza tagumi, ya karasa kusa da ita ya zauna ya kalleta yace " Umma?" Juyo da fuskarta tai ta kalleshi, yacigaba" Umma ko nace dole sai na auri Seemah baza ki amince dani ba?"
Tace kwarai, yai ajiyar zuciya yace " ko nace Seemah ce jigon rayuwata bazan iya rayuwa ba sai da ita bazaki amince ba?"
Kallansa tai da mamaki tace " Jalal!! "
Yace " ko nace in ba da itaba bana tunanin zan iya zama da wata a matsayin matata bazaki amince ba."
Kallansa take cike da kulawa tace " Jalal yaushe ka fara soyayya haka? Ban tab'a tunanin zaka so mace haka ba? JALAL meya sameka? Baka tunanin sun maka asiri?"
Mik'ewa yai ya juya mata baya yace " nikaina bansan ya akai na zama haka ba Umma, bansan yaushe zuciyata tai rauni akan mace haka ba, in tana dariya sai insamu kaina cikin farinciki, in tana bakin ciki sai inji nafita damuwa, in taji ciwo jinshi nake kamar a jikina, in ina tare da ita jinake kamar kar mu rabu, Umma bansan meke damuna ba."
Idanun Umma ne suka cika da kwalla, ta kalleshi cikin tsananin tausayi, lalai ta fahimci halin da d'anta yake ciki amma ya zatai da Zainab? Mik'ewa tai ta dawo ta gabansa tace " nafahimceka kwarai Jalal sai dai Jalal abinda baka sani ba shine, rayuwar aure ba soyayya ake nema ba kawai.
Kai ya girgiza yace " Umma ban damu da wad'an nan ba."
Shiru tai jikinta duk yai sanyi, Jalal ya kalleta yace zan koma Abuja yanzu ana nemana zanzo wani satin, Umma d'an Allah kitaimaken kishawomin kan Abba.
Takalleshi tace daga zuwa? Yace eh oganmu ke nemana, tace to Allah ya kiyaye.
Direct tasha ya nufa ya shiga mota, tunani yakeyi ta ina zai fara shawo kan lamarin.
A company d'insu ya sauka, office d'in Habib ya wuce, ba kowa saboda yau weekend, knocking d'in kofar yai daga ciki akace ya shigo, shiga yai da Sallama, Habib ya bashi izini zama, shikam yana tunanin harda maganar san Jalal da Seemah take yasa Dad cikin wannan halin dukda baisan takamaimai dalili ba sai dai shikanshi bazai yarda da wannan soyayyar ba.
Zama Jalal yai sannan Habib ya mik'amai hannu, sun gaisa Jalal yace " akace kana nemana?"
Habib ya kalleshi tare da ajiye takardun hannunsa, yace " kasan kanwata?" Kai Jalal ya d'aga, Habib yace " akwai wani abu a tsakaninku ne?"
Cikin rashin fahimta Jalal yace " kamar me fa?" Habib yace " kamar abinda ke tsakanin mace budurwa da namiji."
Jalal yai murmushi sannan yace " eh, we like each other. "
Habib ya tattara hankalinsa kan Jalal sannan ya zaro envelope ya tura masa abansa, Jalal ya kalleshi da rashin fahimta yace na meye? Habib yace ka bud'e, Jalal ya zaro abinda ke ciki check ne na million 3, cikin tsananin mamaki da tambaya ya kalli Habib yace na meye? Yai maganar tare da ajiye envelope d'in.
Habib yace " wannan kud'in ina tunanin ya isheka ka fara business d'an haka inaso kabar garin nan kaje wani gun ka fara kasuwancinka."
Jalal ya kalleshi yace "bangane in fara kasuwanci ba? Kuma kai a matsayin me kake a guna da zaka bani kud'i ka kuma umarceni akan wasu sharad'u dabata shafi aiki ba?"
Habib yaji zafin kalamansa amma ya daure yace " ina nufin ka rabu da Seemah, kai kanka kasan tafi karfinka, ko kana tunanin kanada abinda zaka kula da ita ne?"
Jalal ya saki wani murmushi yace "Ahhhh dalilin kenan? Sai dai yaza'ayi yaya Habib bana tunanin zanyi accepting wannan offer taka."
Yana kai nan ya mik'e cikin tsananin b'acin rai, zai iya jurar komai amma ya tsani amaidace gara wanda za'a iya siya da kud'i.
Habib shima ya mik'e zaiyi magana kawai sukaga an turo kofar, Seemah ce da Ammar suna dariya, dariyar ta tatsaya ne sanda taga Jalal, da mamaki ta kalleshi tace " My Deen me kake a nan? Ba kace kana birnin gwari ba?"
Idanunsa ta kalla ba shakka ransa a b'ace yake matuka, Jalal ya kalleta sannan ya kalli Ammar ya juya ya kalli Habib yace na wuce, ta kusa da su yazo ya wuce bai kula Seemah ba, Ammar ya bishi da kallo haka kawai yaji bayasan guy d'in.
Seemah kam kallan Habib tai tace " yaya lafiya?" Bai amsa mata ba kawai ta juya tai waje da gudu, Ammar na k'iranta amma inaaa, da kyar ta tadda Jalal yana jiran elevator da sauri tasha gabansa tana hakki, tace " Deen menene? Yanaganka haka? Kana ganina baka min magana ba."
Kallanta yai sannan yace " haka kuke dama masu kud'i? Komai bakwa iya solving d'insa sai da kud'i? What do u people think of me? Kije ki sanar dasu halaye na."
Gaba d'aya Seemah takasa fahimtarsa, bai jira amsarta ba yana ganin Elevator ya tsaya ya danna ya shiga ya barta a tsaya tana maimaita kalamansa.
0 comments:
Post a Comment