Kafin ta bata amsa sai ta ji karima tana cewa don tsabar bakin jini irin na o'o sadaka ma an rasa mai so, duk yanda maza ke son mata amma an rasa mai sonta.Sakina tace,aikin banza sa'idawa.Salame ta mike ke mara kunya waye mai saka idon? Bilki tace ke sakina kin hauka ne? Su karima suka soma masifa amma sakina bata yi shiru ba,fadi take toni da ku nake? Kuna maganarku,nima tawa nake yi. Bilki tace wuce daki bana son rashin kunya.Ladiyo tace yi min shiru munafuka ke kike sata bata son hayaniya don haka sai ta mike ta nufi dakinsu.Cikin haka har suka shiga ss3. Lokacin 'yammatan duk sun kawo,hatta Asma'u auta an soma girma, ga malam mamman kullun cikin fada yake kan cewa ya gaji da ganinsu sannan duk cikin dangin su ya cigita koda wanda yake so amma sun ce sam saboda tsana, cikin haka suka soma jarabawar sauka mansura da bilkisu sunfito daga gidan su mansura zasu zo gidansu Bilkisu a kofar ghda suka ga Sakina tare da wane dan yaro suna hira....
Mansura tace Bily gaskiya ki masu sakina magana su daina kula kananan yarannan ba fa aure za su yi ba, sai dai bata yara. Bilkisu tace kin san sakina da shegen musu in na musu magana sai suce wallahi ba samarin su bane 'yan makarantar sune bari zanyi maganin su yau sun samu mama tana cin abinci suka zauna mansura tace mamanmu zan ci tuwon nima, ta turo mata kular gashi nan ki saka gamiyar can cikin tukunya wata nayi kin san yau ladiyo ce ta yi girkin mansu tace. A'a mamanmu ba an raba girkin ba? Bilkisu tace kin san matan gidan sai dai shirin Allah sun kuma cewa sai dai a hada,Mansura ta ture kular tare da cewa ba zan ci tuwon wannan kazamar ladiyon ba. Bilkisu tace yauwa. Mamanmu, gaskiya kima su sakina magana su daina kula kananan yaran nan, ga masu sonsu 'yan mutunci, ai gara ma su fitar da mazan saboda fadan baba ko yaya ki ka gani tunda suna j.s.s3 ne sun ci gaba can dan fadan baba yana daga min hankali ta soma hawaye duk dana tsani maza da ace na samu mai sona ko yaya yake Allah zan yi aure ne..
Ko dan ke ma ki huta da gorin'yan gidan nan, mansura tace haka ne tunda suna da manema, cikin tausayi mamanmu tace maigado kena ke tunani bana son su riga ki aure,gashi naso suma suyi karatu mai dan zurfi.Bilki tace kada ki damu aure da mutuwa duka na Allah ne,kema zaki samu saukin fadan baba in kin rage biyun,suna cikin tattaunawa ne maryam ta shigo mama tace mamina daga ina?Tace banace miki Ibrahim ya iko kirana ba?Tace yauwa dama ina son in ji shin da gaske ne auran ki zai yi?Maryam ta sunkuyar da kai kasa tace tun tuni fa yake cewa zai turo na ce mishi a'a saboda ga antinmu nan bata yi ba. Bilkisu tace kin ji shirme,to dama in yazo kice mishi ya turo tunda ba boyayye ba ne,kowa yasan gidansu akwai mutunci,mansura ta duki kafadar bilki tace kai su Bily akwai shegen manyace,suka sa dariya bily tace Allah kuwa na sakina ne wannan Abdul din nake ganin sai an dan yi bincke kanshi,saboda don kano ne Mansura tace shin kece za ki bincika?Bilkisu tace,to hakkin baba ne kema kuma kin san ba zai yi ba amma a san yanda za'ayi ko Mamanmu? Ta ce dole kam.
Bayan binciken da Mamanmu ta saka aka mata kan mai son sakina ta hanyar mijin hajara suka gamsu da maneman sannan ta basu dama suka fito aka sa rana. Walimar saukar su Bilkisu tazo inda aka yi a cikin harabar makarantar tasu. Bilkisu ta amshi kyaututtuka, kamar su'ya mai ladabi ta daya, tsafta tare da taimakon malamai, wato in ba malami sai a sata ta koyar da yaran. Mamanmu sai da tayi kukan murna, yayi da labari ya karade unguwar, Umma ta shirya musu walima ta musamman tare da buga musu kalanda da sauran abubuwa, wai! Nan Abu ya ba su Ladiyo haushi in da suke ta yar da habaici.
Washe garin walimar, wai a banza tunda ba walimar aure bace, shi kan shi baban su kanshi kato yake duk Wanda ya mishi murna, sai ya yi ta fadi 'yarshi tayi sauka amma bai taba basu koda biyar din fensir ba.
A gida kuma cika ya shiga yi yana cewa bata da ladan komai dan ta sauka tundaba aure tayi ba, ga Bilkisu duk ba wannan ne a gabanta ba, mafarkin Yarima da ya zame matan masifa shi ne matsalarta, ko gyangyadi ta yi sai ta ganshi, ga rashin mashinshini ta rasa me ke faruwa da ita.
Duk abin da aka sama rana ai yazo, sai ga Bilkisu Sakina yazo, 'yan Bauchi sun zo tun sauran kwana uku biki, ranar ce kuma aka kawo a kwatunanan da ket suka kawo, kaya masu tsada da kyau Ibrahim yana aiki ne a zonal office Kaduna, don haka ma can za'a kai ta, yayin da Sakina zata yi kano Abdul dan kasuwa ne in ji ' yan magana suna cewa, Dan kasuwa mai kamar wani sarki.
Su Ladiyo sai zunburar baki da jin haushin maigidan ga zaton su duk abin da ake facaka dashi tun kafin ranar daurin aure shi yayi, basu San ma daga in ake da shi ba, ya kawo kudin sadakin da ya amsa naira dubu ishirin- ishirin ayi amfani da kudin ba, da kyar ya ba da dubu ishirin yace ya dauki dubu goma-goma cikin sadakin kowaccensu, cewarshi zai ci da su ne a banza? Mamar tace sadakin hakkin yara ne amma tunda ka ce haka shi kenan yaje ya dauki ladan tuwon ko kuma kudin hatsin da ya ba su.
Hajiya Kilishi uwar dakinta, hakika ta taimaka sosai, domin ita ce ta yiwa yaran kayan kicin, baban Mansura shi ne ya yi musu gara, yan Bauchi kawunan amare tare da sauran dangi kudi suka kawo, akwai da shin da tayi gidan hajara nan ta hada aka je kasuwa aka hado musu kaya na gani da fada, Umma ita ce ta sai musu zannuwan gado da labulaye, sadkain su kuma a hannunsu mama tace aba su, amma su kace sun bata.
Biki yayi kyau komai cikin tsari dangin uba kam ba wata gudunmawa sai dai su cika gida sunata Jan girki tare da yiwa Bilkisu shaguben tayi abin kunya kannanta sunyi aure sun barta, abokan wasanta kam sun fake da wasa sun cacaccaba mata magana . har da cewa kyau bai ji rana ba. Tun da ba mshinshni kyan Dan maciji batun ya bata ran Bilkisu amma Mansu tace kada ki damu Bily wani jinkirin alkairi ne, amma ba mutane duka ba ne suka San haka ba. Bilkisu ta ce don tani ban damu ba surutun ne bana so kawai, amma nima basa gabana.
[4/21, 01:44] A~PROF: 40. Biki ya tashi lafiya, kowa na sambarka, gudunmawar da ta samu na kudi daga abokan arziki tace da Umman su mansura ta aje mata saboda komai gada,Allah zai fito mata da nata,Bilkisu sun gama zana jarabawarsu cikin sa'a sun riga su mansu da kwana biyu suma suka gama mamanmu ta ce maigado ki shirya kije ki ma ummata kwana biyu mana,tunda baki shiga sana wayyar ba mana? Cikin murna tace kamar kin shiga raina mamanma,Asma'u auta tace zan je Aunty maigado.Bilkisu ta harare ta auta zan fa duke ki in har ki ka kuma ce min maigadon nan, tace na daina to zanje Aunty Bilki?Tace a'a ke kam ki na da islamiyya. Mansura ta dube ta,Bily ba zaki bari sai week end in Abbanmu yazo mu tafi tare ba?Saboda nima zan je gombe ne. Bilki tace,nan da kwana hudu zan fi kowa son muje tare,amma zaman nan da zan yi na kwana hudu zan sha gori da habaicin 'yan gidanmu, kan cewa na rasa mai sona."ta dafa kafadarta, kada ki damu mansu, zan tafi goben in yaso in zaku je gombe sai na baki adireshin kizo nima ba sai naje na gaida yan gombe ba
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 13馃彽
Mansura tace to shikenan muje ki rubuta min adires din, kuma zan zo da safen na raka ki tasha Bily tace to Mansu.suna tafiya a hanyar sun rike jakar su biyu kowa ya rike hannu daya,Bilkisu tana zayyane ma mansu abin da ya faru yanzu, waton abin da mahaifinta tare da kishiyoyin mama suka mata,mansura tana tsananin son bilkisu, don haka itama taji haushi tare da takaici amma sai ta ce kiyi hakuri, ba komai ke damunsu ba sai hassada,bilki ta dube ta kin sani ne mansu? Taci gaba. Wallahi duk da tsanar dana ma maza saboda wannan abin da ake min yasa nima yanzun nake jin na kosa in yi aurannan, tsaki mansu tayi tare da cewa, duk ma nawaki ke?Don Allah kada ki saka kanki cikin damuwa. Haka taci gaba da lallasinta tare da bata hakuri har suka kai gurin mashin, tace ki koma sai na ganki tace a'a sai naga tashin motarki, haka kuma har gareji ta raka. Bilkisu sai da motar ta tashi sannan mansu ta koma cike da kewar aminiyarta kamar yarda ta bar Bilkisun cikin tunaninta, suna son juna fiye da zaton mai karatu,
Ba ma kmar mansu, tana tsananin son Bily, sukan su iyayanta sun san haka, don tun suna yara ko dinki ne aka mata in ba ama Bily ba sam bazata saka ba komai sai dai ai musu tare,shi yasa ko mamanmu ma in ta dauki albashinta in har zata sai ma Bilkisu wani abu tare take saye. Umman mama taji dadin zuwan Bilkisu don duk cikin jikokinta tafi son ta domin tana da hankali, sannan tana koya mata karatu tare da addu'o'i. Bata manta wani hutu da tazo ta koya mata zikirorin sallah,gasu nan har yau tana yinsu. Adda wata yar dattijuwa ce da su kawu Aminu suka daukarwa umma suna biyanta tana tayata yan aikace-aikace,don ma umma akwai ta da juriya tare da kazar-kazar.Bilkisu tana son bauchi tana jin dadin zama da umma tun jumma'a ta damu yan gidan da labrin zuwan mansu,umma ma ta damu tana son taga mansura nan dai,ga tsarabar mansu da tasha,sai dai har lahadi ba mansu duk ta damu. Monday gidan kawu Aminu ta kwana,ta tatara ta wuce gidan kawu Abubakar ko'ina taje sonta suke su da ya'yansu.
Ran Jumma'a tana kwance kan gado umma ta tafi masallacin jumma'a adda tana wanke-wanke sai kawai taji sallama muryar mansunta ce da gudu ta fito tana fadin oyoyo mansuna.nan ta yar da jaka suka rungume juna,sai yau ki kazo? mansu na shiga damuwa,tace bari ke dai Bily,Abbanmu ne ya kwafsa min,tare da shi ma muke yana waje,da sauri Bilki ta dauko hijabi ta debi ruwa suka fita,suna cikin gaisuwa sai ga umma ta dawo,nan tace ya shigo ciki,ya shhiga suka gaisa nan kuma yayi mata sha tara ta arziki yace shi zai wuce kaduna ne,shima satin shi daya a gombe suka mishi rakiya ya tafi. Da dare suna kwance kan gado barci yaki zuwa sai hirarsu suke yi, mansura tana ba bilki lbrin tun wancan satin suna gombe,tace har kuka na yiwa Abba akan ya kawo ni nan amma ya ce sai ya tashi tafiya. Bilki tace nima haka nan duk na damu,mansu tace albishirinki?Bilki tace goro kwarya goma sukayi dariya,tace.Abba yace kafin mu dawo zai saya mana form na jamb,murna bilkisu ta somayi domin da har ta debe tsammani da karatu tunda abin na kudine
Suna tafe a kan hanya suka ji anata horn bayan su amma duk suka share
Ganin basu da niyyar tsayawa ya saka shi fitowa ya biyosu, assalamu alaikum yace musu,suka tsaya mansura ta jujo yayin da Bilkisu ta sha mur tare da kin juyowa,don Allah zan iya magana daku ko da na yan mintina ne? Mansu tace muna jin ka, yace nagode gaskiya ni dai na ganki ne nake sonki,mansu tace wa ni?Yace kwarai,tace gaskiya an min miji,sai dai wannan Bily ta dube su cikin daure fuska tace,ni matar aure ce, ita ce budurwa,dan kyakkyawan saurayi yace,ai ke kam nasan kin fi karfina shi yasa ma banzo nan ba jama'a na kaini inda Allah bai kai ni ba,kalmar nan ta kinfi karfina tana ba su Bilkisu mamaki,shin dama mace tana fin karfin namiji?Bilkisu ta daure tace,na gode da ka gane haka,yanzu dai na baka kawata,domin na ganka da alamu na masu hankali,yace nagode sosai,ni sunana Umar Faruk Sulaiman ni mutumin gombe ne,nazo gaida kanwar mamana ne a nan bauchi,sannan ina aiki a kaduna ne, tare da bankin PHB, ku fa?Bilkisu tace mu yan zaria ne,
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 14馃彽
Amma batun dogon bayani sai mun sake haduwa,yace a ina? Kuma yaya sunan kawar taki?Tace sunanta Mansura,ta nuno mishi gidan su umma daga nesa ga gidan kakarmu can in ka samu lokaci a nan zaka ji sauran batu, taja mansura dake tsaye tamkar wawiya tana jin su,yace nagode ko zan rage muku hanya?A'a mungode,cewar Bily Gidan uncle suka kwana,kani ne gurin umman mansu,adaran farooq yazo nemansu basa nan,sai da yamma suka soma shirin dawowa,anty salma matar uncle itama tana ta yaba kyan Bily,haka sanda suka taho kowa sai ya tsaya yana ta kallonta,ta saba ko zaria haka take fama da kallon nan,kullum mutane suna ganinta amma tana fitowa sun dinga kallon ta kenan. Sun idar da sallar isha'i umma tana basu lbrin zuwan bakonsu,sai ga dan aiken mansu tace,Bily ba ki kyauta min ba,meyasa ne zaki jona ni da mutum?Ko sauraran mansu bata yi ba,tace da yaron kace tana zuwa.Wasa wasa saida mansu taga bacin ran Bily sannan ta fita gurin farook,sunyi hira kuma yaji komai dangane da mansu sun yarda dajuna da suka ji yangari daya ne
Mansu tana son farooq sai dai tana tunanin Bily bata son tayi aure,ta barta don haka tayi mata shawara su aure shi tare mana? Hkan ya kusan kawo musu rigima sai dai umma ta tsawata sannan mansurta hakura.Satin mansu biyu ita kuma Bilkisu hudu Abba yazo yace zai wuce gombe ne,jibi zai zo su tafi saboda monday zasu soma zana jarabawa,don haka su shirya ran jajibarin tafiyarsu.Sun yi sallama da kowa kawunan Bilkisu sun musu dinke-dinke tare da tsarabobi, umma tace gaskiya ya kamata kuje gomben ne don haka kawu Abubakar ya saka su cikin mota yayi gombe da su sun ji dadin ganinsu Abba ma yace shi kenan ya huta tsayawa.Daren ranar ne Bilkisu cikin mafarkintan nan na fama,Yarima ke ce mata,kiyi kokarin sanin wanene Yarima kafin ki bar bauchi da safe kam suka dauko hnyar zuwa gida, zuciyarta cike da tunanin wanene Yarima?Meke faruwa tsakaninsu? Umma da mamanmu sunyi farin ciki da ganin yayansu Bilkisu har wani kyau ta kara tare da yar kiba duk da cewa ba wani jiki ne da su ba.
Sun zana jarabawa cikin sa'a duk su haye,Abba ne tsaye kan komai har suka samu shigewa Bilkisu ta samu fannin da take so na yayinda Mansura ta hakura da gefen lissafin don bashi ta nema ba,baba ya tambayi mamanmu shin wani sabon karatun ta kama?Mama tace to Allah bai kawo miji ba,ai sai aci gaba da karatun ana cikin yi in mijin yazo ai dole ne ayi auren, yace ba wani,na lura Fatima akwai burin daki kaci akan yarinyar nan, amma nasan maganin abin ya fita yana zage-zagenshi,mama ko cewa tayi Allah ya kyauta. Haka rayuwa taci gaba abubuwa na faruwa yau sauki gobe tsanane shekararsu ta farko, lokacin ne farooq ya matsa kan batun auran su da mansu.Tun dama ita ce mai jan lokaci wai ko Bilkisu itama zata samu ko da cikin school din su ne amma duk son mata irin na yan jami'a babu wanda ya taya Bilkisu,sai dai kallo wasu har tuntube suke yi in suna tafe suna kallonta,bisa ga wannan dalilin ne yasa mansura ta jira yi zuwan farooq wannan satin da yake kaduna yake aiki shi yasa duk sati yake zuwa shima yazo..
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 15馃彽
Da tashi damuwar tason ya turo magabatanshi zaman gaurantaka ya ishe shi, yana bukatar mace a kusa dashi. Don kada yaki yarda da batun yasa tasha kunu kafin ta bude motar ta shiga ganin yanayin tane ya fadar mishi da gaba saboda nan duniya ya tsani yaga mansura cikin damuwa,yace meya tasani yaga mansura cikin damuwa,yace meyafaru.Sweetyna?ta sake daure fuska gaskiya ni ina ganin zai yi wuya muyi aure. Cikin tsoro yace,saboda mene?Tace saboda Bily,gaskiya farooq ba zan iya aure in bar Bily ba,sai dai ka zaba cikin biyu,ko dai ka aure mu tare,ko kuma mu hakura da juna zan jira ta in ta samu sai muyi tare,baki ya saki tare da bin ta da ido,dariya ma ta bashi yana dariya yace kuruciya kenan,kowa da irin tasa,haushi ya kama ta,tace dariya kake min? Kuma nice kuruciya shekara ashirin shine kuruciya ko?Ta juya zata fita,ya riko ta haba mansura,me yasa kike irin wannan magana? Yaya ma zaki ce in auri Bily?Gaskiya bazai yiwu ba.Bily tafi karfina, bani da halin da kera gidan da zan sakata. Cike da mamaki ta kalle shi kana nufin sai me hali ne zai aure ta, ka kalli gidan su mana. yace ke baza ki gane bane,kuma nima ban san yanda zan miki bayanin yanda nake ganhnta bane,so mu bar maganar.tace to shikenan,Allah ya hada kowa da rabon shi,zata fita yace ban fa gane nufinki ba?Tace ai zabi na baka,kuma kace mu bar zancan cewa zaka aureta,wanda haka yana nufin ni da kai sai bankwana.Ta fice ta bar shi zaune.Mamakinta yake yi yasan takan komai in ta kafe sai dai ya hakura ko kuma ya hada tada Bily,don haka sai ya tashi motarshi sai gidan su Bily,dai dai wannan lokacin tana kwance cikin daki bisa gado jikinta rinkif da zazzabi.Asma'u auta taje ta siyo mata magani,mama tana kofar dakinta yayin da su ladiyo suke zaune a gindin murhu, suna cin tuwo hira suke yi kasa-kasa ba a jin me suke fadi sai dai ajiyo dariyarsu,yaro ya shigo yace wai an ce ana kiran Bilkisu,nan take suka katse dariyarsu,kuma suka shiga kallon-kallo, mama ma taji daban don ba a taba hakan ba,tace in ji wa?
Yar yace in ji wai farooq,mama tace kace tana zuwa,ta shiga daki tace ke maigado ki zo saurayin mansura yana kira, ta sauko tana tunanin anya lfy?Don ko yaushe yazo tare da mansu suke zuwa, sai ta shigo su fita tare tana fita ladiyo ta kwala ma yarta Basira kira,tace zo nan Basira,suka yi mata rada ta fita da gudu,jim kadan ta dawo da gudu tana tsugumawa a gabansu tace wani ne a mota na ganta,a gidan gaba ta zauna,karime tace kin ji ko?Gaskiya gobe zamu koma kusfan na kada mlm yayi mana haka?Salame tace na ma kasa mgana,saboda ko kwanan nan nawa muka bashi? Ladiyo tace niga bashi ma da ake bina ban biya ba,na kuma ciyo wani muka hada muka bashi haka nan suka ci gaba da tattaunawa tare da shirya yanda zasu yi.A cikin mota farooq ya rattafo ma Bilkisu yanda suka yi da mansura, amma sai yace mata shi ne nazo in ji naki ra'ayin. Ran Bilki ya baci tace muje gidan,a fusace ta shiga dakin mansura, bakin gado ta same ta ta zuba tagumi cike da takaici ta dube ta,nagode mansu tallat ma ki ke yi,.
ki sani koda Farooq ya amince ni ba zan yarda ba,kuma in har kina son mu shirya dake gara ma ki fito ku sasanta,in kuma kika ki ni dake zamu hakura da zumuncin haka nan,wanda muka yi baya Allah ya bamu lada,tafita da gudu mansu ta biyo tazo kiji Bily,daf da kofar fita ghdan ta rike ta wallahi Bily ba wai ina tallarki bane,ya matsa min da zancan zai turo ni kuma gaskiya bazan iya aure na barki ba,Bilkisu ta girgiza kai tare da rike hannun mansura,kada ki manta mansu kannaina da muke ciki daya sunyi aure,yanzun haka duk suna da tsohon ciki ne,ki sani aure yana gaba da komai a gurin mace, Allah bai ce wani ya jira wani ba,kin sani ko ni bana daga cikin matan da zasu yi aure a duniya?Ta numfasa muje gurin shi,da kyar suka shawo kanta ta yarda ya turo daran ranar,Bilkisu bata yi bacci ba yau ce rana ta farko da ta soma zubar da hawaye,saboda rashin masoyi,wani kunci ta samu kanta ciki. Gurin binciken wanene farooq su Abba suka gano ashe mahaifin shi abokin Abbane, zamanin suna secondary wannan yasa suka tsaida
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 16馃彽
Tsaida bikin watan may,wata biyu kenan, shirin bikin suka kama saboda babu lokaci ishasshe,Mansu dai rigima suke tasha da farooq,duk da irin lallashin da yake mata. Ana sauran sati biyu bikin yace za'a kawo akwatuna,nan tasa mishi rigimar in dai bai yi ma Bilkisu komai da yayi mata na akwatin ba,wallahi ba zata taba saka kayan ba,kallonta ya tsaya yi yana tunanin kanta daya kuwa?Yace kin san nawa na kashe mansura?Tace ni ina ruwana ko gida bana saka kaya in har bata da irinshi in ma kasan baka da halin yi mata tun kan a kawo kaje ka raba mana wanda ba iri daya ba ne ka canzo ta fitittike taki sauraronshi kan dole yaje ya sayo zannuwan da ta kalman zuwa gyalulluka,kayan shafa da akwatuna ne bai sa yaba da 'yan kunne,yaje ya aje,randa aka kawo akwatuna suna makaranta amma sun san da zuwan 'yan kawo kayan,tunda yan gombe ne zasu amsa daganan sai suka hadu da danginAbba da na farooq su kawo zaria, kawayen,umma ne suka tari yan kawo kayan kaya ne na ban mamaki, da suka dawo daga mkrnta gidansu Bilkisu suka zame
Mamanmu tana basu labarin kaya,Bilki duk ta matsu suje su gani, masha Allah in ji bilkis time da ta gama duba kayan,umma farooq yayi kokari,mansu kam kosawa tayi yazo ran sati don ta ji ina na sahibarta? Ya kam iso da kayan cikin katuwar akwati guda daya ko rufuwa bata yi, amma sai mansu tace ita kam sai ya sayi set din akwatin,yace haba mansu wlh account dina yanzun ba ko naira,yakike son in yi? Tace to gaskiya zan je in ciro 2 ka hada mata da wannan ni sai na dauki biyu da ket,yana mamakin wane irin so ne wannan mansu take ma Bily?Suna cikin haka sai ga bilkisun, da fara'arta ta kwankwasa glass din motar a tare suka fito tace brother kasha kamshi fa,yace kanwata ya gari da shirye-shirye? Tace mungode Allah,ya naku? Bata jira amsar shi ba, ta dubi mansura dake cika tana batsewa,tace yaya ne mansu any problem?Mansura ta dan daga kafadunta alamar babu dan bata son tasan maganar. Farooq yace akwai ya koro mata komai, kasa magana bily tayi kallon mansu kurum take yi...
Kafin daga baya tace laifin kane farooq daka ki sanar dani harka biye mata kasiyo kayan yanzun kuma zaka juya da sune ka mai da bana so kuma na lura mansu bata son mu rabu lfyne, ni da ita,shawarar da zan baka kai namiji ne,kuma sai yanda tace zaka sha wahala don bata da hankali kasa ni kai ne mai bada umarni da hani suna gurinka,so be carefull,kaya kuma nagode bana so ko ka kara mata ko kuma ka maida ka amshi kudinka.ta juya ta koma gida tana mamakin son da mansura take mata, nan ta kara shiga damuwa dama tana tare da tunanin yanda zata kasance in mansu tayi aure tunda yanzun ma gidan take kwana,amma taji mamanmu tana cewa zata sa atoshe uwar dakinta abude ma Bilkisun kofa ita da Asma'u,mkrnt tare ko ina tare,Umma suka kaima kayan itama sai da tayima farooq fadan biyewa mansuran sannan tayi godiya ta kira mamanmu ta bata, mama ma kin karba tayi sai da Abba yasa baki yace kayan mansura na Bilkisu ne,haka nan kayan Bilkisu na mansura ne shi ko daya baiga laifin mansura don tace mijinta yayi ma Bilki kayaba Bilkisu taki ayi wasu bidi'o'i a bikin tace walima kurum zasu yi in da zasu gayyato mlmai dan su yi wa'azi haka ko akayi,dama daurin auren can gomben aka yi sun soma walimar bayan sallar la'asar,inda malama sa'adiya tayi wa'azi akan hakkin aure wato miji akan matarsa Bilkisu wace suke zaune kusa da juna ita da mansu tace kin dai ji ko?Mansu kam jikinta ne yayi sanyi,dayake gombe za akaita can ma akayi jeren in hutun shi ya kare sai ya samar mata gida nanzaria saboda karatu shi kuma zai na zuwa mata hutun karshen mako.washe gari suka dauki hanyar gombe kuka mansu keyi tun daga zariya har gombe haka nan bilkisu sai ma washe gari randa zasu dawo a wannan rana mansu da bily sun sha kuka,da kyar suka rabu har ma wasu sun taya su kukan, aure kenan, tun a mota bilkisu ta soma kewar mansu, dashi ke su mamanmu ne suka je jere gomben basu je kai amarya ba,mama ma a talauce dubu biyar taba umma da kyar ma ta amsa.
Bilkisu kam itama mamanmuce ta bata dubu bakwai tayi ma mansu yar sayayya ba dan sun ishe ta ba,sai don bata dashi amma tasha alwashin in ta gama karatu tana kama aiki zata kula da mansu fiye da kanta,ba don mansu bata da shi ba,sai donta kwanta,hakanan Bilkisu taci gaba da zuwa makaranta ita daya, amma kullum sai tasha kukan rashin mansu. Can ma gombe ango yakasa gano kan amaryarshi,duk da lallashi gami da ban bakin da yake mata,har dan hutun nashi na sati hudu ya kare,kafin nan yasamu dan madaidaicin gida,suka dawo sunyi murna da ganin juna ita da mansura suka ci gaba da zuwa mkarnta. Wannan satin ko nace Friday farooq yazo dawuri lokacin suna makaranta shi ne yaje yazo da su bayan ya kira mansura cikin new phone din ta nokia.cewa gashi nan zuwa nan take ta canza fuska har Bily ta gane, tace bakiso zuwanshi ba ne?Tace a'a nadai gaji ne.Bily taso su sauke ta gida amma sai farooq yace yana son magana da ita,agidansu ne yake cewa na sani be dace in miki zancan nan ba sbda ke ba matar aure bace kuma irin zancan nan..
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 17馃彽
bai dace ya hada mu ba sai dai dole ne in mikishi dan nasan kece zaki iya min mganin abin da yardar Allah mansura dai tun da muka yi aure sam taki yarda dani yau sati biyar kenan sai kace wata yar karamar yariya.na mata wa'azin nayi fadan nagaji tana cutar dani,batun yayi ma Bily nauyi har ma ta kasa kallon farooq,amma duk da haka tace kayi hakuri ka yafe mata tayi kuskure bazata kara ba,taja hannun mansu cikin dakinta,suka zauna gefen gado ta dube ta cikin yanayin damuwa, kin san masifar dakike ciki kuwa?Kin san zunubin da kike diba? Koda yake nasan kin sani tunda tare muka yi karatu nace malami daya ya koyar damu,..nan dai Bily Tai tayi mata fada da nasiha..!Cikin hawaye take ma bilkisu wlh bily,tsoro nake ji,dariya ma ta ba bilkisu, jibe ki wai tsoro ta mike ina son gobe labari ya canza in ba haka ba wlh- wlh kinemi wata bilyn bani ba,ta fita mansu ta biyo ta tana kira,kin tsayawa tayi farooq ya biyota shine ya sauke ta gida lokacin Babansu yana nan zaune awaje tare da wasu yan uwansu,kallo yabita dashi.Baba tsalha wan shine yadube shi.
Yace toga shaida kana gani? Amma zan dauki mataki,gara dai cewar baba tsalha. washi gari tun misalin bakwai saura sai ga farooq yayi sallama da Bilkisu, suka gaisa yace ta taimaka suje gida ta lallasar mashi mansura tana can tana ta kuka ko kula shi taki tayi Bily tayi maza ta shirya ta bishi suna shiga gidan mansu tayi saurin fadawa jikin mansu ta kara fashewa da kuka tana Allah farooq baya sona baya tausayi na mansu tayi saurin rufe mata baki tana lallashin ta nan ta wuni tana kula da ita sai dare ta tafi.
Baba tsalha yakalli mamman sannan yace,ina jinka mamman, kace Inusa ya shirya aure?Mamman yace, haka nace.Baba tsalha yace,ban da kai mamman wanne mahaukacin uba ne zai ba Inusa auren 'yarsa? Yaron da bai san ciwon kansa ba,sai shaye-shaye da bin kwararo yana damke kajin mutane da agwaginsu ba sana'a. Malam mamman yace to nina bashi Bilkisu tunda ita shegen bakin jini yayi mata yawa,Baba tsalha yace to ni fa ba ruwana kuma bani da kudin masa aure, mamman yace dama ai sadaka zan bashi,kuma da zaka ce babu ruwanka ka sani ko sanadin auren ya shiryu?Baba tsalha yace shi kenan zan mishi bayani.Abin ban mamaki,Inusa ma da tsohonshi baba tsalha yakira shi yayi mishi zancan Bilkisu cewa yayi a'a tafi karfinsa.Babansu bilki tare da baba tsalhan ne suka tasa shi suna rokonshi ya yarda,yace zai dai yi tunani. Yayi sallama kofar mamanmu tana ninke kayanta yayin da Bilkisu ke cin tuwo,fuskarshi sam babu annuri gaban bilkisu ya fadi dama duk sanda ta ganshi sai gabanta yayi muguwar faduwa,balle yanzun da ya shigo afusace,ya dube ta ke Bilkisu daga yau naba inusa ke tunda abin naki ya zama iyashege,haba dole mana maza suyi ta gudunki,kowa yana tsoron ciwon kanjamau, ashe maza kike bi, su ladiyo sun sha gaya min amma na kasa yarda sai yanzun da na gane ma idona,dan tsabar iskanci kam har kofar gida ake zuwa daukarki to na kawo kasrhen abin inusa shi ne na bawa ke,ido ta zuba mishi cike da mamaki tana kallonshi, yanzu ne ta kara yarda mahaifinta baya kaunarta,domin duk uban da yake son yarshi bazai taba yarda ya kwatanta ta da auren yaro irin inusa ba yaron da babu arabi balle boko, sai shaye-shaye,kullum cikin datti tamkar mahaukaci,ga satar tsiya ba sana'a tana cikin tunani ya katse ta,kin tsare ni da ido ba neman shawara nake yiba,umarni na bada dama ai nine musulunci ya bawa damar in zaba miki miji,bata san sanda tace amma baba Inusa baya daya daga cikin mazajan da musulunci ya yarda a basu aure, saukar mari taji sannan yace sai ki gaya min Wanda musuluncin ya yarda a bashi ke da kike rainawa yanzun haka ya ki sai lallashin shi ake yi ya rufa miki asiri har kina da ta cewa? Ya dube mama wadda ta tsananin bakin ciki da mamaki ya hanata magana yace kece ke zugata na jima da sanin haka to ki sani kan wannan Auren kema naki Auren yana siradin karshe, in kin tafi gidanku kuma in daura Auren ya fice fuu...... Kuka mai karfi Bilkisu ta saki sannan ta juya tana kallon Mamanmu cikin kuka take fadin Allah Mamanmu wannan karon bazan yarda ba ni ba zan aure inusa ba, shi baba baya kaunata Sam ta matsa ta kama kafafun mamanmu tana cewa me yasa baya sona? Me na mishi? Ko dai ni din ba yarsa bace?
Kuka da mama ke makewa shi ne ya kwace cikin kuka take cewa nima wannan karan na gaji ai ba akan shi kike ba. Hakkinki da Allah ya dora mishi matsayinshi na uba bai kula dasu ba, sai yanzun ne zai ce hakkin shi ne ya zaba miki miji?
Zamu ji mugani, yan kwanakin nan rigingimu sun kankama cikin dan lokaci. Mutane kalilan ne suke cewa bai dace a aura ma inusa Bilkisu ba, tunda shi ba nutsattse ba ne, sauran kam sun ce an cuci Inusa, mahaifiyar Inusa ma tsalle ta daka tace sai da yar tayi kwantai sannan za a lika ma danta?
Har sassan su ta shigo cike da masifa ta samu mama tana wanka sai Bilkisu zaune ta tasa abinci ta kasa ci, saratu uwar Inusa ta dubi Bilkisu ta ce, ke ina uwarki gunta nazo, in kuma bata nan bari na baki sako ki gaya mata, ki ce nace hadin bai hadu ba kin gantsare kin rasa mai so za a maka wa dana? Har fa masallatai an kai cigiyar mai sonki an rasa, anyi yawo da hotunanki an gaji, ga bin maza ki je ki saka mishi ciwon zamani.
Mama ta aje bokitin wanka ta dubi saratu tace ke saro ki dube ni da kyau, in kina zaton nima na amince a hada min 'ya Da mahaukaci ne ki ka zo nan ki yi rashin mutunci to ki sake sabon tunani Inusa mutun ne? ina tambayarki? Don kunga ina muku shiru ba yana nufin tsoro bane kuma ba kasawa bane, duka nawa megadon take shekara 20 da yan watanni ne kuke mata wannan surutun, Ku shiga cikin unguwar nan Ku duba in babu wadanda suka girmeta . don haka daina daga jijiyar wuyanki nima ba zan yarda a dauki zukekiyar yarinya kamar maigado a ba Inusan da ko gabas bai sani ba bare yanda ake sallah,. Saratu cikin sanyin jiki tace oho dai na dai gaya miki kar a makalawa yarona, kila da ciwo ehe, mama tace ba gara kowane ciwo ba da ciwon dake jikinshi na jahilci, baki in yasan abin da zai fada bai San Wanda za a maida mishi ba, haka ce ta samu saratu ta tafi cike da kunya yayin da su Ladiyo dake gefe suna kallon suka ji haushin saratu yanda ta tsaya matar nan tayi mata ta tas.
Bilkisu ta ji dadin yanda mama ta gaggaya wa saratu magana, domin sun raina musu hankali a gidan rigima ta kasa karewa babansu Bilkisu da baba tsalha sun matsa ma Inusa randa ya amsa musu da dare cewa ya yarda washe gari da asubahi ya tattara yanashi- yanashi ya gudu don ba zai iya Auren Bilkisu ba, kuma shi kanshi ya rasa dalilin gudun Inusa yasa rigima ta tsananta uwarshi tace ba zata yarda ba kila asiri ne mama suka ma danta ya bar gari, su Ladiyo ma haka suka ce ma maigidan kuma ya hau kai ya zuna ya samu Mamanmu yana ta masifa fadi yake gara ma taje ta karya asirin tun kafin abu yayi nisa banza tai musu suka yi ta surutun su suka gaji suka yi shiru dama ance watan kwaram daya ne da ya wuce shi kenan. Sai dai ita kuma bilkisu tana mamakin akan kinta ne Inusa ya bar gari?In ko haka ne,da mamaki meke faruwa kenan?Lallai bakin jininta ya bunkasa, cikin dan tsakanin sakina ta haihu 'yarta mace, anyi suna da sati uku maryam ma ta haihu danta faisal yayin da yar sakina taci sunnan maman Abdul,Amina. suna kiranta da mimi, mansu ma anyi ciki shagwaba ta karu ga laulayi dole Bilkisu ta koma gidan saboda farooq kaduna yake in yazo Friday sai ta dawo gida.Haka rayuwar ta ci gaba da juyawa,Bilkisu tana zuwa makaranta har mansu ta haihu, dan yaronta mai kyau yaci sunnan baban farooq, suna kiran shi dady. Bilkisu tayi juyi yau shekara duka nawa ta sani ba wai tayi girman da za'a ce gashi gashi ba ne amma surutun mutane ya isheta,ita kanta tana so tayi aure yanzun.. Sai kuma gobe.
Yarima kwance kan wata kujera jikinshi sanye cikin gajeran fari tas din wando da yan singilet din ta, gefenshi Vicky ce sanye da da brezzier da pant wasannin su na yau da kullum suke tana da kusan rabi na abin da yake so a gurin mace, sun yi nisa cikin shagala Sam bai ji sallamar ba bare ya amsa,sai da mai sallamar ya shigo kai tsaye kuma ya rufe kofar da karfi da sauri ya zare bakin shi daga na Vicky wace ta soma fita daga hayyacinta, magajin Malam ne ya ce maza ka tashi tare da mai martaba....... Sallamar mai martaba ce ta katse magajin Malam daga maganar da yake, tsoro da faragaba tare da kunya ne suka rufe Yarima, Vicky kuwa tsawa magajin Malam ya mata, ta mike ta fita, Yarima yana zaune akan kafet ya dukar da Kan shi bai ji dadin wannan ziyara ta ba zata da da mahaifinshi ya kawo mishi ba, wannan shi ne karo na biyu da ya kamasa da mace wancan zuwan ya samu ya kare kanshi da cewa abokiyar karatunshi ce, duk da mai Martaban ya gansu ne suna kissing din juna, kuma bai ce ma Yariman kala ba shi ne dai yake ta borin kunyan shi to yau fa?
Da me zai kare kanshi? Dubi kayan jikinshi dubi nata, gara ma wancan karon duk da kaya a jinkinsu.
Magajin Malam ne ya soma magana afuwa Yarima yake nema Allah ya taya maka a yafe mishi. Mai martaba ya daga ma magajin Malam hannu alamar yayi shiru, sannan cikin magana irin ta manya yace, Modibbo dama saudiya zan shige na ratso domin in ganka, kuma na same ka lafiya duk muna waya kullum, yaya karatun naka? Cikin in-ina yace Alhamdulillah ranka ya dade, yaya su Umma? Ummar ka lafiya shin ko kana da matsalar kudi? Ya dan shafa kai I to ba dai sosai ba, mai martaba yace in da matsala ka fada, yace eh akwai bayan wannan fa? ya ce babu ranka shi dade, ita kenan, ya mike ya nufi kitchen yazo da ruwa da lemunkan sha, ya dire ma magajin Malam don yasan mai martaba ba zai sha ba, ya shiga daki ya saka kaya har lokacin jikinshi a sanyaye yake , yasan halin mahaifinshi sarai shirun da ya mishi ba yana nufin ya bar shi bane ya sani zai hukunta shi ta in da baya zato, don shi baya fada bare zagi, yanzun shi dai zai saurari hukuncin daza a yi masa Allah yasa kada ya maida shi gida nigeria da karatun shi dan ba ya son karatu can kuma matan can basa burge shi duk kyan ya mace .
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 18馃彽
kwanan mai martaba biyu a malaysia kafin ya wuce Saudi yayi kwanakin ne a wani shahararren masaukin baki dake cikin birnin na malaysia. Yarima sam bai yi mamakin shirun da mahaifin nashi yayi mishi ba. Domin yasan zai yi maganin abin, wani Abu da yaba magajin Malam mamaki, gidan Yarima yake kwana kuma ganin da mai martaba ya mishi bai sa Yarima ya daina kwana da mata guda biyu a shimfidarshi ba, don haka magajin Malam yake kwanciya a falo ko dayan dakin Yarima, magajin malam dai shine babban abokin Yarima kuma shi da ne ga waziri, mai martaba yana son shi tamkar Yarima. Shi yana karatun injiniya, yayin da Yarima ke karatun likita mai martaba yazo da shi don yaga abokinshi ya juya gida shi kuma ya wuce Saudi, bayan sun ga tashin mai martaba suka dawo gida, kai tsaye fridge magajin Malam ya nufa a kitchen ya dauko robar ruwa, kusa da Yarima ya zauna da yake kokarin kiran Ummarshi,
Layin ya ki shiga, ya dubi Yarima yana son yin magana amma yasan halin yan kayan shi, don haka sai yayi nufin share zancan amma kasancewar Yarima mai matukar saurin fahimta sai yace um'hum ina jin ka, magajin Malam yace ban yi magana ba.
Yarima ya dube shi cike da kasaita irin ta yayan sarakuna, sannan yace kana so yin maganar ne ai, magajin Malam yace nasan halinka ne zaka iya cewa yanzun ba time din amsa ba ne, Yarima yace tambaya zaka yi kenan?
Magajin Malam yace tun shekaran jiya nake son yin tambayar, Yarima yace bata dame ka ba ne da kayi ta koda ba zaka samu amsa ba.
Magajin Malam yace zan iya tambayar yanzun ko? Yarima ya tabe baki tare da fadin in kaso ba, magajin Malam ya gyara zama, dama ina son jin me yasa kaci ka son mata? Kuma me yasa ka canza daga silent din ka zuwa mara jin magana? Yarima ya ajiye wayar a gefenshi sannan ya ce na kasa samun Umma din ma ya kalli magajin Malam wacce zan amsa maka? Duka in har zan samu, ya ce to mata abin so ne don su ne nishadi na karshe, duk cikakken namiji mai lafiya yana son mata, sai dai kowa da nashi salon son, sannan ban canza ba har yau ina nan a silent dina, magajin Malam yace ka canza domin a da in har mai martaba ya hane ka da yin wani Abu ka bar shi har abada, amma yanzu ba ka damuwa da hakan. Yarima yace me ka gani? Ya ce in daina ban daina ba? watannin baya mun zonan dashi mun sameka da mace. Sai kuma gashi wannan zuwan ma gara wancan cikin sutura kuke wannan karon ba Ku da maraba da tsurara, sannan kuna cikin halin sumbatar Juna, kilama damun jima ba mu shigo ba mu same Ku cikin wani halin. Yarima ya zuba mishi ido babu wani hali da zaku same mu da ya wuce wannan domin ni kamar yanda ka sani komai da lokacin shi, wannan lokacin ne na wasanni kuma duk nacin mace ba zan wuce mata haka ba ka fahimta?
Sannan kai ma zan tambaye ka wancan zuwan da Ku ka yi ka ji mai martaba yace kar na kara? Hasalima bai ce min kala ba. Haka nan wannan zuwan kaji ya yi min magana ? Magajin Malam yace amma kasan hausawa sun ce shiru ma magana CE, ta ishi mai hankali ko? Sannan kana ganin shirun da ya yi maka yana nufin ya ji dadin abin da ka aikata ne? Yarima gairgiza kai ko kusa nasan ba haka ba ne, INA cike da sanin zai dauki mataki kaina, sai dai ina tsoron irin hukuncin da zai yanke min, magajin Malam yayi dariya tare da fadin, ai na san ka shirya daukar kowane hukunci ne tunda ka kasa daina hulda da matan duk da yana garin ka ci gaba da kwana da mata har biyu kasan ko matanka ne na sunna addininka bai amince maka ka kwana da su, su biyu ba ko?
Magajin Malam yace wane hukunci ka ke ganin mai martaba zai yanke maka? Yarima yace sai Allah shi ne ya sani sai kuma shi. da na zace zai CE zai mai da ni Nigeria in yi karatu a ga ban shi yanzun kam na bari wannan tunanin tunda a gabanka ya kara min kudi, magajin Malam yace ni ko sai INA tunanin kila ya yi maka aure........ Da sauri Yarima ya tashi zaune au! What? Yayi yar dariya kada ka manta am 22 fa yaushe aka haife ni, da har zan yi aure? Please bar wannan zancan ban isa aure ba, magajin Malam yace kai ko ka isa har ko ka zarta tunda da mata biyu kake kwana. Yarima yace tab da ko ya yanke min hukunci mafi muni, ni fa aure nayi da wuri in yi shi nan fa shekara goma masu zuwa, kana da garantin kaiwa wannan lokacin! Cewar magajin Malam Yarima ya mike tare da fadin, in na biye maka sai in shiga time din wanka na, ya nufi dakin shi magajin Malam ya bi shi da kallo yana kuma mamakin Yarima, yaro mai shiru shiru da kamun kai, yana da natsuwa ta karshe shi yasa yake samun girmamawa gurin al'lummar Bauchi, shi kanshi ban da ya gane ma idon shi abin da Yarima yake yi zai musa, yana da girmama lokacin shi yasa yake da cika alkawari in har ya dauka.
kwankwasa kofa aka yi tare da neman izinin shigowa, magajin Malam da ke zaune yaba su izinin suka shigo, turawa ne mace da namiji, sun gaisa sannan suka tambayi prince ya gaya musu cewa yana wanka, suka dubi a gogon da ke manne a bangon falon sannan suka jira shi yayi musu izinin zama, jefi-jefi suke hira suna kallon fim din da suka samu magajin Malam yana kallo, Yarima ya fito cikin bakin jeans tare da shirt mai dogon hannu tare da layi-layin baki da fari takalminshi mai shegen kyau tare da tsada shima baki ne, sumar kanshi irin ta asalin fillo tasha gyar tana ta sheki, kamshin turaren matador yana tashi a jikinshi, Dora ta kalli M, tace He's handsome guy, ta mike ta isa gurin shi cikin kasaita ya kalle ta tare da fadin ya take?
Gefen kunnashi ta sumbata sannan ta rike mishi hannu ya dubi magajin Malam wanda haushi ya hana shi magana, yace abokina bari mu shiga school da kai magajin Malam ya amsa suka fita yaja tsaki Allah yasa mai martaba ya yiwa Yarima hukuncin barin wannan kasa da lalcewa tayi mata yawa.
Mai martaba Alhaji Isma'il Abdullah ya kammala umrarshi lfy, kuma ya matsu ya dawo gida saboda matsalar dan shi Yarima, Al'amin yayi addu'o' masu yawa kan Allah ya shirya mishi nutsattsen yaron nashi sai dai wasu lokutan yafi ganin laifin shi da ya dauko shi ya kawo shi wata kasa masu wata irin tarbiya babu mai saka ido babu mai tsawatar wa ya kama mishi gida mai tsadar gaske sannan ya cika mishi account da kudi lallai yace mishi je kayi yanda kake so, duk da cewa ya halasta mutum yaje ko ina ne dan neman ilmi shi yasa duk abin da Muslim ya tsara mana in munce zamu bar shi sai mun gaba dai dai ba, wannan shi ne dalilin da yasa aka ce in danka ya balaga kai mishi aure, mai martaba ma yace wannan ne ya dace da Yarima wato aure, kuma yasaha alwashin da ya sauka gida zai yi shawara da mutum daya, ya san tsohon zai taimaka mishi.
Cikin bacci taji ana girgizata, Aunty in ji Mamanmu, ta yi mika tare da hamma sannan ta sakko jikinta a mace zuciyarta cike da tunanin mafarkinta Yarima ne a mafarkin yake matsa mata da son ta nemo labarin shi, har ma suka yi rigima don tace me sanin labarin shi zai kareta da shi? Yayi fushi ya tafi yace mata ba ya kara zuwa sai randa ta samo labarin shi, ta mike tana tunanin dama ta huta don itama ta gaji da mafarkin shi....
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 19馃彽
Bilkisu ta dubi Mansu, kizo muje tare, ta saba dady a kafada maimakon nonon da take bashi, tayi gaba zo muje, gurin shirya abincin. Shagala abokan farooq suka yi da kallon wannan baiwar Allah, tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya kagi wannan yar tahalika, basu kara tsinkewa ba sai da ta soma gaida su da wannan zazzakar muryar tata, cikin in ina suka amsa mata har ma taji nauyin hakan ta koma falo in da su Sakina suka shagala da kallon wani Nigerian film, a tashar African magic, Mansur ne ya soma magana, abokina ina ka samo wannan zukekiyar yarinyar kaman tasha hatimin Aninabi Yusufa don kyau?
Sani ya amshe iya gane ganena ban taba ganin mace mai kyaun ta ba, farooq yace wanene zai shiga a cikin Ku? Sani yace tab ni wannan tasha gabana, sai dai ko su mansur ko Aminu, Aminu ya ce ni ba Ku ji ban tan ka ba? Dan nasan wannan daga gidan sarauta, sai ko gidan wani shugaba ko na jiha ko na kasa, duk tadin da suke yi Mansu tana jin su wannan Abu yana daure mata kai, farooq yace yaya za Ku ce mata, yarinya ce mai hankali, ko ilimi, da saukin kai, mansur ya ce barni dai wannan ka kalle ta da kyau kuwa? Firgita ni take yi da kwarjininta mai ban al'ajabi, in har na aure wannan tuni zan zama zauna nan, duk suka sa dariya, Mansu ta damu tana son sanin MEKE faruwa ne kowanne namiji ke fadin tafi karfinshi...?
Sai yamma suka baro gidan Mansu, ta cika yaran su Sakina da Maryam da kudi tare da kayan shafa. Bily ko kaya ne kala hudu na salla da farooq yayi mata, kanta amsa sai da suka hau sama da Mansura, don tace sun yi yawa ba zata karba, kuma sun yi wahala da ita da yawa, yaushe ne itama zata samu ta kwatana musu? Mansu tace wannan kuma na Allah ne shi ne mai yanda yaso ke dai ki dauka, Allah ya bar mana zumunci.
************************
magajin Malam ya dubi Yarima, prince don Allah ka sake hali ni zan tafi kaga har mutane sun soma shiga jirgi, please Yarima be a Muslim, Yarima ya kalle shi yanzo ni ba Muslim ba ne? To ka zama cikakke. I will do my best, magajin Malam yace ni fa har mamaki na ke ji, gaba daya ka canza Yarima ya dafa shi na sani kana tsoro ne kada nazo Niger in yi abin da zai zubar da mutuncin gidanmu ne I'll never do it kada ka damu zan kula, Yarima yana kallon magajin Malam har ya shige jirgin don zuwa gida.
Mai martaba ya sauka lfy jerin gwanon motoci ne suka zo filin jirgin don daukar yallabai, ya kashingida bisa kafet ya dafa tuf-tuf dan hutawa, gefenshi kuma uwargida ce sarautar mata ta jera mishi kayan shaye- shaye da ciye- ciye. Hajiya salma kenan mace mai mutunci da sanin ya kamata, gata da son addini tare da tausayin na kasa, gefenshi ta zauna tana tare da cewa yako lbrin autana?
Cike da sakin fuska ya ce autanki, lfy lau, ya kara girma tare da zama namiji sosai, Hakika kasar ta amshe shi tamkar balaraben kasar misra suka yi dariya, tace shekara biyu kawai da ban ganshi ba shi ne ya zama duk wannan? Yace zaki ganshi zan shirya miki zuwa tace shifa ba zai zo Hutu ba ne? Ya dube ta zai ci gaba da zuwa hutunshi a Saudi ne, duk da cewa ina tunanin nan gaba kadan wani sanadi zai kawo shi nan gida, hira suke yi yana cin abincinshi, taso ya sanar da ita ko menene zai yi sanadin zuwan Yarima, amma sai yace ta bari in lokaci ya yi zata sani.
kamar ko yaushe in har zai je gurin dattijon sirikin nashi yafi son ya fita shi daya kuma yaja motar da kanshi kamar yanzu kenan, karfe tara na dare ne yaja motar dan zuwa gun surukin nashi ne shiga dakin Modibbon ya sanar mishi da cewa ga mai martaba.
Bayan ya zauna suka gaisa da tsohon mai tarin shekaru masani ne na Qur'an and hadisai, Allah ya yi mishi baiwar sanin abubuwa da dama, shi ba mishiriki ba ne, baya duba ko bugun kasa, tsoho ne mai bautar Allah tare da takawa, shekarunshi dari babu uku amma in ka ganshi zaka zata bai fi saba'in ba, wasu suna gani tamkar waliyi ne Allah dai ya bar ma kansa sani cike da girmamawa mai martaba ya gaida Modibbo tsohon mai daraja ya amsa cikin sakin fuska da kulawa ya tambaye hanyar da kuma abokinshi wato takwaranshi Yarima Modibbo mai martaba yace yana lfy yace a gaishe ka,
Ya gyara zama, yanzu ma matsalarshi ce ta kawo ni, tsohon ya tattaro hankalinshi gurin mai martaba sannan yace gaba, zuwa na biyu ina samunshi da mace hankalina ya yi matuka gurin tashi, yanzu da na yanke shawarar in yi mishi aure, sai a tura mishi matar can, ko yaya ka gani? Tsohon yayi shiru tamkar mai nazari, sannan yace haka ne yafi dacewa domin saboda gudun wannan matsalar shi yasa musulunci ya yi horo da ya'yanku sun balaga to Ku musu aure,
Mai martaba ya ce haka ne, kwarai na yi mamakin canzawar yaron lokaci guda, tsohon yace babu wanda zai gagara daga shaidan, don shi ba rago ba ne, yanzu kaje gida akwai istihara da zan yi game da al'amarin shi idan Ubangiji yaso sai musan ta in da za'a bullo, mai martaba ya shiga godiya tare da yin sallama da tsohon wanda ya yunkura ya tashi ya yo ma sirikin nashi rakiya zuwa gurin mota.
Yarima zaune kan wani dan dakali karkashin wata bishiya mai sanyi cikin makaranta, yana nazarin littafan biology, dago kan shin da zai ya sai ko ya sauke idanunshi kan wata yarinya 'yar mutanan China tana sanye da gajeran siket wanda iyakarshi tsakiyar cinyarta, rigar jikinta kuwa singileti ce mai dan siririn hannu,
Ta cikin gilashin idonshi yake kare mata kallo nan zuciyar shi ta kwadaitu da lafiyayyar fatar ta, da takusa in da yake sai ya yi tamkar bai ganta ba, a nata gefen yau ne gani na uku da ta mishi gayen ya tsaya mata a rai, tayi niyya yau zata kula shi ta tsaya gefenshi cikin harshen turanci take CE mishi sannu da hutawa kasaitar tashi ta motsa, yi yayi tamkar bai ji ta ba, sai da ta sake maimaitawa sannan ya amsa ba tare da ya dube ta ba, tace zata iya zama kusa dashi?
Yace in taso haka zata iya, ta zauna tana satar kallon shi, ta dan yi gyaran murya, sannan tace shin zata iya tambayarshi? Hannu ya daga mata kafin yace yanzu ba time din tambaya ba ne, shiru tayi na dan lokaci sannan ta ce to zai iya taimakon ta? Ko yanzun ba lokacin taimako ba ne? Ya bata amsa dace wa in taimakon ya shafi kar2 ne zai iya in ko wani Abu ne daban to ba a yin shi cikin makaranta ya tambaye ta shin ta fahimta? Tace eh ta gane, nan ta soma mishi tambayoyi akan abubuwan da suka yi mata duhu shi ko ya shiga bata amsa yanda zata fahimta har zuwa lokacin sallar la'asar ya mike ta ce ina zai je ne? Yace ya fita lokacin kar2 ya shiga na sallah don haka yanzu sallah zai je.
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 20馃彽
Mamanmu ta dubi Bilkisu ta ce maigado ki daure kiyi amfani da maganin nan ga na turaren nan wannan kuma wanka zaki yi da shi, Bilkisu ta dube ta Mamanmu kada ki shiga cikin mata masu shiga gurin malamai saboda gudun shirka, aure lokaci ne. Mama tace maigado ba zan kauce hanya ba, wannan da ki ka gani Ummana ta ai ko dashi wannan na iskokai ne, abin nan yana bani tsoro, na rasa gane me ke faruwa? Bilkisu cikin sanyin murya tace kada ki damu Mamanmu, In'sha Allah, Allah zai kawo min mafi alkairi, wata rana sai labari,
yanzun su Bilkisu sun shiga shekara ta uku a jami'a { A.B.U} mass comm. Take karanta wa, tana sha'awar zama yar jarida duk da kasancewarta ba mai yawan surutu ba amman tana so ta zama cikin yan media, karatunta ta saka a gaba in da Mamanmu ta hana kanta ci da sha ta dage dan ganin burin maigado ya cika, duk da Abban Mansura yana taimaka mata sosai to karatun jami'a ya wuce wasa wasa, dan gane da mahaifinta sai abin da ya karu na tsana, da kuma tsangwama.
***************************
Jumma'ar yau kam Modibbo tsohon nan daga masallacin jumma'a ya nufi fada dan ganawa da mai martaba, cikin wani daki na musamman suka kebe duk suna zaune ne kan dar duma bayan gaisawa da suka yi Dattijon ya soma magana. Abu na farko da na fara gani cikin al'amarin Yarima na ganshi mai yawan fitsari ne in na ce mai yawan fitsari ina nufin yana da matsananciyar sha'awa, game da batun aure kuma ba da gaggawa kamar yadda ka ke nufi ba, amma zai yi aure ba da jimawa sosai ba, saboda matar tashi ba yar yankin nan jihar ba ce, sannan tana da matsala, haduwarsu da Yarima zai kawo abubuwa da dama, a cikin binciken nawa na ga al'amura da yawa, amma Allah shi ne mafi sani haka nan yafi mu sanin komai game da abin da zai faru, anan gaba. Sai dai za a iya nema mishi Auren daga wasu jihohi yazo yaga wadda zasu sasanta ko Allah zai sa tana ciki, haka ne in ji mai martaba, za a nemo mishi hotuna nan su sai in sa a kai mishi ya zaba in yaso sai ayi bikin a tura mishi can, dattijon yace to madalla haka din ma ya yi zamu bisu da addu'a, bayan tattaunawa suka yi sallama.
Yarima yana cikin bahon wankan mai cike da kanshin sabulai kaloli masu sa santsin jiki da laushin fata, kwance yake ciki ya yi lamo zuciyarshi dam da sha'awar yarinyar yar mutanen China, yau sati daya da haduwarsu kullum sai ta neme shi da yawa tana son shiga harkarshi musamman da ta San in yana makaranta to karatu yazo abin da bata sani ba makaranta tana cike ne da yammatanshi sai dai sun san baza ya kula su a school ba in kin matsu isko shi gidan shi sau biyu suna rigima da Vicky.
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 21馃彽
Bilkisu sun shiga shekara ta karshe a makaranta , da kyar da sidin goshin da taimakon su Abban Mansura ta gama Degree na farko, ta samu damar zama yar jarida, suna gida sai jiran bautar kasa, cikin yardar Ubangiji da sa'a Kaduna aka tura ta, farooq kam yace ba wata bautar kasa da Mansu zata yi saboda tsohon cikin dake gare ta tuni ma ya tafi da ita Kaduna gidanshi na can, don haka gidan su Mansu take son zama kamar yanda suka yi da Mansu, ta waya,
Dama cikin shekara hudun nan Mansu a shiririta take karatun, course din da aka bata ba shi ta nema ba, gidan farooq ya kama a malali na sani same road, ya yi kusa da sakatariyarsu, Bilkisu duk da cewa sai ka hau mashin, ranar da ta soma saka kayan NYSC zaku ganin tamkar tafi kowace mace sa'a Mansura ta ce kin yi kyau wlh Bily, ta dubi Mansu, ina tunanin yaya zanyi na fita da wando? Zan dinga saka after dress idan zan fita in naje zan cire.
zaune kofar gidan Yarima, magajin Malam ne tunda ya sauka ya iso gidan a kulle,ya sani kamar wannan lokacin Yarima yana makaranta, zaman kusan awa uku sai ga Yarima shi da yar mutanan China, hannuwansu rike cikin na juna, magajin Malam yace toh! Abu ya kara gaba, tunda yanzu har cikin gari yana yawo rike da mace, abin damuwa ba ne, ya tsaya cike da matukar mamaki ganin magajin Malam ya iso yana cewa, abokina tun yaushe ka ke a nan? Magajin Malam ya mike Yana dan karkade rigarshi, nafi awa biyu ina jiranka fa, suka yi musabiha rike da hannun juna suka nufi cikin gida, tana biye da su Yarima, ya ce jiki na fa ya yi sanyi da ganinka, Allah yasa ba hukuncin mai martaba ba ne zan fuskanta, magajin Malam yace barin na huta nayi sallah, to yi bari na amso mana take away suka fita shi da chelen don yanzu ta zamar mishi jaka, ko ina tana manne dashi ga tsinannan kishi, dama tana yawan gaya mishi su a dokar kasarsu mutum ba zai yi mata biyu ba.
Yarima kam ya ce mata shi sai dai tayi hakuri da shi, soyayyah zai yi da mata da yawa, amma macen aurenshi daya ce, ta kan ce ita ce? Sai yace mata ba zai iya sani ba, zaune suke tsakiyar falon Yarima da magajin Malam, yan ciye ciye suke yi tare da yan hirarraki ya matsu yasan Dalilin zuwan magajin Malam shi ko magajin Malam sai ja mishi rai yake yi, tare da tsokanarshi, Yarima don Allah magajin Malam yi min bayani mana, mikewa ya yi ya shiga bedroom din Yarima Ya dauko jakarshi irin wacce ake ratayawa , yazo ya zauna ya zage ta ya ciro envelop ya mika ma Yarima gashi in ji mai martaba sakon kenan yace lallai ka duba in je mishi da amsa, ya mike rike da jakarashi duba ina zuwa bari na maida jakar.
Daya bayan daya yake bin hotunan da kallo, ya'ya ne na sarakuna da na manyan attajirai, kuma yan juhohi daban- daban, domin ya gani a bayan hoton magajin Malam ya dawo ya zauna kusa dashi cike da tashin hankali mai tsanani Yarima ya dubi magajin Malam, wai martaba yana nufin in zabi mata? Ina zaton haka ne in ji magajin Malam, Yarima Ya ce gaskiya ba amin a dalci ba, 24 years shi ne zan yi aure? Gaskiya ba zan iya ba, kwana kadan mutum ya tsufa, ya tara yara magajin Malam yace to yanzu ya zaka yi?
Nasan dai ba zaka yi gangancin fada mishi wadannan magananun ba? Yarima zufa yake yi, ya dubi magajin Malam ni gaskiya ko da aure zan yi ban sha'awar matanmu na nigeria, musamman. 'Yan arewarmu kauyawa ne, ya watso ma magajin Malam hotuna duba fa ka gani, kalle su bana son irin mutanan gaskiya ni kuma bana da sha'awar Auren mata da yawa, mata daya jal zan yi dan bana son a cika min gida da yara yanda mazan hausawa suke yi, kallon shi kawai magajin Malam ke yi cike da mamaki.
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 22馃彽
Yace Modibbo kana bani mamaki in na ce ka canza kana min musu yanzu har da haihuwar ce ba ka so? Yace eh bana so ko ka taba ganina na dauki wani yaro iya tsawon rayuwarka? Shin ko wasa kaga ina ma yara? Magajin Malam yace to tunda ka ce baka son matan nigerian sai yan wace kasar, yan China? Cikin gatse ya tambaye shi. Yarima yaja tsaki ni yanzu kawai ka ce mishi cikin su babu wadda ta min, kallon hotunan magajin Malam ke yi cike da mamakin yarima, yanmata ne kyawawa, ya dube shi matan sauran kasashin farar fata ba su fi namu kyau da cikar halitta ba,farin ne kurum amma matan arewa sune matan da ya dace mu aura sabo..... Yarima ya katse shi, please wannan ra'ayinka ne ni basu min ba, magajin Malam yace ni ko kaga akwai yarinya da nake so amma ina shakkar tunkararta. Yarima ya dube shi, wannan wace yarinya ce har da zata daga maka hankali? Magajin Malam yace sumayya yar gidan Umman gombe, tsaki Yarima yaja, sannan yace kai dai soko ne, yanzu dama wannan yar yarinya ce har kake wani kana shakkar ta? Kada ka bani kunya mana, ni nan shi yasa na ke matukar burge kaina, duk yanda mace ta kai da tsaruwa tayi kadan in tsaya ina wani binta ko in lallabata ba ayi ta ba, kuma ba za'a yi ta ba, in da na gagara kenan, magajin Malam yace ai matan sun fi son irin Ku masu wulakantasu, ni dai zan kai kaina gurin sumayya da naso ne in jira yi zuwan ka sai ka ja min gora muje, da sauri Yarima ya kalle shi muje INA? Gidan su can gomben cewar magajin Malam, god forbid, ba zan iya zuwa gidan su da sunan na raka ka tadi ba, sai dai in gaida Umman gombe naje kai ni fa ko matan nan da suke da daraja a idona sai dai su biyo ni, ba dai ni na biyo su ba, ni suke ya yi ba su nake ya yi ba.magajin Malam yace ba zaka gane ba ne, matanmu na arewa suna da kamun kai natsuwa da kuma kunya ba za su taba binka ba,sai dai in an dace da masu ra'ayinka su daban ne, tsaki Yarima yaja sannan yace ba a wata mace da zan so ta ba, kaf Nigeria, na fada da babbar murya, magajin Malam ya yi dariya sannan yace daina zafafawa shi Allah ba yanda bai iya ba, in yaso sai ya dauko wuyan ka ya mika ma yar nigerian ta yi ta juyi da kai son ranta, Yarima ya mike tare da fadin wannan kam tatsuniya ce irin ta mutanen da, ko cikin mafarki bana zaton zai yiwu bare a gaske, kai dai kai mishi hotuna ka ce basu yi ba, shi kenan magajin Malam yace in kuma shi yaga wadda ta yi ya zaba maka da kan shi fa? Murmushin takaici Yarima ya yi sannan ya shiga bedroom din shi don yin wanka.
***************************
Cikin sa'a Bilkisu ta soma aikin bautawa kasa, an fi turata gidan radio station na Kaduna, fannoni daban daban duk tana tabawa, wani sa'in ma har gefen TV sukan turata, yau kan news zata yi a dauka duk ta kasa sukuni saboda zata yi wani Abu ne da bata taba zaton zai zo kanta ba, duk da tana sha'awar hakan. Mansu ita da farooq dinta suna ta karfafa mata gwiwa tun a gida, sai da aka dora mata kyamara ta yi addu'a samun nutsuwa nan take natsuwa tazo mata, ta shiga karanto cikakkun labarai cikin harshen turancinta din nan dan gaske, Masha Allah haka duk wadanda suka kalli labaran litinin din yau suke cewa, saboda ganin kyau tare da zazzakar muryarta tana dawowa, Mansu ta rungume ta tana cewa kin ganki kuwa? Tamkar dama kin dade kina yi kina karantowa kina dago kai tare da juya kyawawan idanuwanki, Bilkisu ta ce har ma da sharri wane juya ido kuma? Abokan aikinta ma sun sha mamaki tare da al'ajabin kwazonta cewa suke Allah kin yi kokari Bilkisu Muhammad Salis.
A Zaria kuwa babansu haushin mama yake ji nashi ganin ta tura ya karuwancine a Kaduna, in ma ta sake ta debo ciwon zamani ba dai gidan shi ba,su Ladiyo ma haka suke cewa, ta tafi yawon dandi suna zuga shi yana faman fada. Goggo Amarya kuwa cewa ta yi Allah ya isa tsakaninta da Fatima kuma tayi bakin cikin hada zuri'a da ita, auduga Mamanmu ta sa ta toshe kunnenta tana yiwa 'yarta fatan alkairi ne ta tsaya tsayin daka dan yiwa 'yar tata addu'a saboda Allah yana saurin karbar addu'ar iyaye ga ya'ayansu.
***************************
Lokacin rakiyar magajin Malam filin jirgi ne suke tattaunawa a mota, Yarima yana me kara jaddada ma magajin Malam sakonshi gurin mai martaba, fadi yake yi don Allah kace mishi duk cikin su babu wadda ta yi min, yar dariya magajin Malam ya yi kafin yace wlh ba zan iya cewa mai martaba haka ba, jin ka kawai nake yi, dama shiru na maka in na shiga jirgi in duba hotunan wadda ta kwanta min a rai sai na ce mishi ga zabinka, Yarima yace tab ka ce kaso dai ka kulla min tsiya? Magajin Malam yace tabbas domin kuwa ina fada sai a shiga biki, sai dai kaji an gama.Yarima ya yi parking gefen titi yace da ka cuce ni yanzu to yaya zan yi ne ma? Magajin Malam yace oho, ni dai ba zan iya yiwa mai martaba rashin kunya ba, domin wannan rashin kunya ne, kai ka kira wayarshi ka sanar dashi cewa babu wace tayi maka. Yarima yace kasan ko da wasa ba zan iya ba, to shi ne ni ka ke son in je gaban shi in gaya mishi haka, kimarshi ta wuce nan a gurina, ni kawai ka kai ni kada lokaci ya kure, jirgi ya barni a tasha, wayarshi, ya shiga Neman layin mai martaba, a zuciyar shi kuma yana kisima me zai CE mishi? Yarima yayi sallama lokacin da ya ji an dauka, mai martaba ba ya amsa sannan ya soma gaishe da mahaifin nashi cikin girmamawa, mai martaba yace ina fata kuna lafiya? Lfy lau in ji Yarima sannan yace am dama shi kenan dai dama zan gaishe ka ne, mai martaba yace kayi magana Modibbo nasan akwai abin da ka ke son cewa Aa ba komai ranka ya dade, yace shikenan kaga sakon gurin magaji ko? Yace na gani ka zabe ne? Mai martaba ya jeho mishi tambaya, eh am...Aa ban amma dai kawai Ku zabar min don ni banga wadda ta kwanta min ba.
Yarima ka duba sosai kuwa? Cewar mai martaba, na duba amma Ku duba min duk wadda kuka ga ta yi shi kenan, ni nawa bi ne In'sha Allah, to ko dai auran ne ba ka so? Ina nufin ya yi wuri? Aa in ji Yarima, ni duk yanda kuka yi shikenan zan bi, shirun dan lokaci sannan mai martaba yace shi kenan tunda ba su yi ba za a duba maka wasu sai dai ina maka nasiha da cewa kazama na kirki a duk in da ka ke ka guji zina saboda ita babban zunubi ce ka sani in ka yi da yar wani sai anyi da taka in ko da matar wani kayi haka nan za'a yi da taka, ka zama na gari wannan shi ne yace to na gode Allah ya kara maka nasara, magajin Malam yana nan zuwa yanzu zai taso yace Allah ya kawo shi lfy.
Ya dubi magaji cike da fara'a na ci nasara, kai mugu har kana min dariya, suka tafa ya kai shi filin jirgi suka tashi ya juyo gida cike da nishadi prince kenan.
Watanni shida kenan da fara service din Bilkisu, sallah ce ta zo babba, sun samu dan Hutu na kwana uku su Mansura gombe zasu je sallah sun matsa mata da cewa lallai da ita za suje tace bari in munje zariya kila in je, haka ne kuwa, Allah yasa tana da rabon zuwa, Mamanmu ta ce kuje mana ba zai yiwa ba ma in hana ki zuwa, suna zaune a falon Mansura na gidansu a can gomben tsarar rangida ne da a ka ganshi cikin family house din su farooq an sauke su da kalolin abinci masu dadi dangin farooq suna matukar son Mansura,
0 comments:
Post a Comment