20-Mai unguwa yace,to nima hakimi ne yayo min aike naje,shine yace lallai muzo tare da kai.Idanun Malam Mamman ya shiga zarewa tare da cewa mai girma hakimi kuma ranka ya dade?Mai unguwa yace ,shi don haka yanzu sai kaje ka shirya mu tafi.Jikin Malam Mamman yayi sanyi,yace cikin in-ina,badai wani abu nayi ba ko?Ranka ya dade nifa ko hakimi ma ban sansa ba.Mai unguwa yace,to ina zaton dai kan 鈥榶ar wajenka ce ko Bilkisu ne sunanta?Sai dai munje kaji saboda shima hakimi ina zaton sakon daga samane,can gurin mai martaba sarki,don haka kaje ka canza tufafi.Jiki yana rawa ya nufo gida,yana tafe yana surutai ni wannan yarinya ta zame min bala鈥榠,ni in za鈥榓 kasheni banace ga kamannin dagaci ba,amma yau sanadin wannan 鈥榶ar iskar yarinyar gani wai har gaban sarki zanje,ko wane bala鈥榠n ta jono min?Oho!,yanzu haka labarin karuwancin nata ne yaje kunnansu.Daidai nan ya shiga gida yana tsaki,matan suna gindin murhu suka dubesa har suna hada baki,lafiya malam?Yace ina fa lafiya,waccan 鈥榶ar iskar taja min wai yanzun gidan sarki ake nemana.Suka ce,wace?Yace,Bilkisu mana.Mamanmu dake daki ta jiyo,don haka da sauri tayo waje don jin me Bily taja masa?Ta fito daidai sanda yake cewa kurum zataja min fitina,yanzu haka ma sunji labarin gantalin da takeyi ne shine aka kirani ahukunta ni.Ladiyo tace,a鈥榓 karka yarda malam,ai ba kaine ke karuwancin ba itace ko kaje karka yarda acutar dakai.Salame tace,ko ko sunji har yau ba a mata aure ba ba.Karima ko cewa tayi,nidai da zakaji tawa,da ka ki zuwa saboda ina tsoron kadasu daure ka ba da hakkinka ba,in haka ta faru mu aka cuta masu kananan yara.Ladiyo tace hakane,ya shiga dakin Salame yanasa kaya,yana cewa, wa zaiki zuwa kiran sarakai?Ai sai azo da dogarawa akamaka.Daya fito ya kalli gurin da Mamanmu take,ki shirya kayanki,domin inna dawo da wani cin zarafin kema zaki samu naki rabon.Ya fita nan Salame ta yafa mayafi ta shiga sashen Gwoggo tana hawayen gulma,wai anzo daga gidan sarki an tafi da malam saboda Bily,yawon banzan da take yi yaje kunnansu.Budar bakin Gwaggo sai tace,babu kaico,na mayi murna ga bokon nan,ni nasan dama haka za鈥榓yi.Ta soma masifa da cewa,ni dai abar min dana suzo su kama uwarta don itace ta tsaya mata.Kafin kice haka,labari duk ya kaima sauran sassan,nan da nan gidan ya cika,sassansu Mamanmu suka dungumo inda take zaune bakin gado cikin daki,ta hada kai da gwiwa.Hankalinta atashe,tasan wani sabon sharrinne za鈥榓 kagawa Bily.Masifar Gwaggo ce ta sakata kuka,tana dai ciki bata fito ba,kowa yana ta fadin albarkacin bakinsa,sai tsinuwa tareda zagi suke yiwa Bily wadda bata san hawa ba bata kuma san sauka ba.Suna isa gidan hakimi,babu bata lokaci suka tafi gidan sarki cikin motar hakimin,anyi musu iso suka shiga duk jikin Mamman yayi sanyi,yana dai binsu ne.A zuciyarsa yana Allah ya isa tsakaninsa da Bily.Suka zube sukayi gaisuwa cikin magana irinta manya sarki ya soma bayani,da farko yace ina mahaifin yarinyar?Hakimi ya nuna shi tare da cewa,gashi nan ranka ya dade.Mamman kamar yace bashi bane,sai dai yasan ba鈥榓 katsalandan afada,don haka yayi shiru,sarki ya gabatar da maneman auren Bily,daga masarautar Bauchi.Idanu ya zaro yana kallonsu,nan suka gabatarda bukatarsu,jiki yana rawa Mamman yace,a-an baku.To hakane ai ba komai,hakimi yace,ka nutsu Mamman.Suka bukaci afadi sadaki,Mamman yace,ni dai na bar komai gurinka hakimi,duk yanda kukayi ni me biyayyane,ko sadaka ne ai zan bada ita kunfi karfin wannan ranka shi dade.Nan dai hakimi yace su bada dubu dari,Allah ya sakama abin albarka.Sarki ne ya bada sadakin,yace tasa gudunmuwar.Sun gabatarda kayan na gani ina so,akwati biyar,ga na uwa dana uba,uku-uku ga kuma wani seti can guda hudu,suka soma bayani kansu,wannan sune kayan da zata koma sawa yayin tsareta ga al鈥榓dar gidan sarauta in dan sarki zai auri yarda bata shafi sarauta ba.Ana boye ta na tsawon wata biyu,babu wanda zai ganta sai Yarima,sai ko shakikanta.Sannan zata daina amfani da duk kayanta sai wannan,wayar hannunta za鈥榓 karba abata wannan Yarima ne kawai zai dinga kiranta,sannan tunda an bada sadakinta,ynzu mune ci da shanta.
yanzun mune ci da shanta har ayi auren. Don haka a kiyaye, kuna da gurin boyeta ne ko mu bada gida! Mai martba yace, ni zan bada guri tare da masu mata hidima har zuwa auren. Hakimi ya matso kusa da mallam mamman yace,to sai zancan tukuici, ana fa badawa. Mlm mamman yace. To.To!Ni me zan ba su? Sai dai sadakin. Hakimi yace Aa,sadaki hakkin yarinya ne.kawai sai suka ji sarkin mai adalci yana cewa a rubuta musu check na dubu dari biyu a buga sterm suje su amsa. in takaita,nan dai suka shirga kaya cike da mota sannan aka kwaso da sharadin cewa gobe za azo a tafi da Bilkisu, ko in ce anuna musu gidan Bilki. Kuji wani lamari.suna isa gidan har yanzu cike yake da yan jaje,don bayan yan sassa har makota sun shigo.
sai dai suka ji tsayiwar motoci, sannan sai ga Dogarawa suna shiga da akwatuna, jiki yana bari yasa aka shimfida katuwar tabarma aka soma Jere kaya seti- seti, nan mutane suka shiga kallon- kallo kowa yana son jin Karin bayani. Mlm mamman babu baka sai yake yi. Ya Ciro kudi ya ba Dogarai yana godiya suka tafi suna mishi murna, lallai ya iya haihuwa, sun so suga wannan yar tashi suga ya ya take?
Shi ko nan jama'a suka yo kanshi, uwarshi ta soma da cewa mamman me ka je yi gidan sarki, wannan kayan fa? Cike da doki yace, Goggo ai arziki ne ya kira ni. Ya shiga raba idon ina zai gano Mamanmu cikin matan dake gurin amma bai ganta ba, sai yace INA Fatima ne? Fatima ki zo ga ikon Allah. Tana tsaye daga kofar dakinta amma bata ko kalle shi ba. Ya ce Goggo daga Masarautar Bauchi ake son Bilkisu. Yasa hannu cikin aljihu,ga sadakinta dubu Dari cif haka ya dinga nuna komai yana washe baki jiki yana rawa sai kace a wasan kwaikwayo,
Makota suna ta sambarka yayinda matan gidan suka shiga zare idanu.gwaggo kuwa ko kunya, murna ta shiga yi tana cewa lallai mun haye, sai godiya. Karima tace, ka ko ji da kyau? Salame tace shi ne dai anya ma kuwa zancan nan gaskiya ne? Ladiyo kam kasa magana tayi.
[8:48AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 35馃彽
Mamanmu cewa tayi.
Mlm gaskiya ban yarda da wannan zancan ba,in dai ka saida ita ne ka sanar dani, don nasan dama neman yanda zaka rabu da ita ka ke yi, don haka ni bana neman kai da ita,haka kawai bata ga mutum ba bai ganta ba ace an biya sadakin ta naira dubu dari? To ban yarda ba ka ji na ma gaya maka tun wuri ka maida musu kudinsu.
Ya zaburo ke Fatima ahir dinki, 'yarki CE ko ko 'yata? Dama ina neman wanda zan ba na rasa sai kuma gashi an zo nema har gida? Daina wannan zance, to ni ina ruwana da wani suga juna? In anyi auren sun ga junan. Gwaggo tace, kai barta me kashin tsiya,in bata yarda ba fasawa za'ayi? Kwaso kayan ina yara kai Ku kira almajirai,. Sukai can sassan gwaggo amarya, ita kuwa gwaggon sasa cewa tayi, haba Amarya komai fa yana son bincike, Ku bari a bincika a ga wanene duniya fa ta lalace, da masifa gwaggo Amarya tace, ke rufe min baki bana son bakin ciki, idan jikarki ce ai ba za ki ce ayi bincike ba, binciken banza? Allah ma ya hana bincike. Gwaggo sasa tace Allah sarki, ni na San in dai mutumin kirki ne ni na ma fiki murna, kema ganin kudi ne ya gama zagin yar da uwarta? Tasa kai ta fita a sasan,
Mamanmu tace, lallai yanzu ne kasan yarka ko?Ni dai naga yanda za ayi wannan aure.Yace,Oho kya ja da sarakai,danni na riga na amshi sadaki,gara ma kiyi mata waya tazo don gobe zasu zo su tafi da ita.Salame tace,to ko dai har an daura auren ne?Ya fita yana cewa,ke kuma ina ruwanki? Sarakan bakin ciki! Salame tace,ai yau kuma mune yan bakin ciki.?Yace,eh ku ne mana.tamkar wani zautacce ya fita yana cewa,bari in kira yara su kwashe kayan sukai sasanki gwaggo,kada cikin dare a kunna musu wuta.mutane duk suka tafi suna cewa,ko dai mutumin nan ya saida yarsa ne,tunda dama ba sonta yake yi ba?Wasu kuma suna cewa,Aa gaske ne zai aurar da ita ne ga sarakuna don yaga kudi,kilan dai tsoho ne mijin su ko su gwaggo karima da salame da ladiyo dakin ladiyo suka shige suna jajanta ma juna tare da neman mafita. Ladiyo tace,ni duk ji nake yi ma duk zazzabi ya rufe ni, wato mlman nan kudinmu suka yi taci basa komai?Karima tace A'a dan yifa aiki yayi, tunda ai babu saurayin da ke kula tan kamar yanda muka bukata Amma sai dai muce yanzu dai aikin ya baci an samu akasi,ai bamu makaraba,sai muje a wargaza al'amarin.Salame tace. To ko cikon kudin nan ne da bamu bashi ba yaki mana aikin?Nan take suka yarda cewa haka ne,kuma suka yanke shawarar cewa zasu je goben nan. Dan ma kada su fita yau nd a gane dama gashi lokaci daya mlm ya canza har dayi musu habaici.ta ajiye hijabin sannan ta koma ta zauna tunani yasha kanta.Ta rasa wa zata tunkara.Zaraf ta mike tace bari naje gidan Umman mansura. Mamanmu tayi sallama a gidan,ta shigo daidai sanda umman mansura ta ajiye hijabinta tare da amsawa.ta fito taga mamanmu,tace,Aa dama ke ce?Shigo nima yanzun nan nake cewa kwana biyu ba mu gaisa ba,da safe in zan je aiki zan biya.Mamanmu tace,uhum!Ke dai bari, nima yanzun zuwa nayi ki kira min maigado,kira min lambarta.Umman mansura tace,lafiya? Mama tace,ina fa lfy, babansu ne da rikicinshi kin dai san halinshi, wannan karon kuma dazun fa ina zaune da rana ya same ni cikin daki,wai shi ya gaji da ganin maigado tana yawon karuwanci Yarinya ta zama annoba,menene wanene?Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.Can aka yi sallama dashi yana dawowa kuma sai cewa yayi in hada kayana,gashi nan an aiko nemanshi daga gidan sarki,wai suma sun ji labarin gantalin da maigado take yi. Yana dawowa zanga cin zarafi.to in dai takaita miki umman mansura, yana dawowa sai gashi da kaya niki-niki da kudin masu yawa wai sadakin maigado ne, akwatuna kashi-kashi, wlh ni sai ma tsoro ya kama ni,na soma tunanin ko dai ya saida ta ne tunda nasan baya kaunarta?Umman mansura tace,ikon Allah to a ina ya samo mata mijin?Mamanmu tace. Oho,ni ko sauraron shi ma ban yi ba,kila ma sun daura auren ne don naji yana cewa wai gobe zasu zo su tafi da ita. Umma tace,Ikon Allah. Ina zuwa bari in kira Abban su mansura muje mu same shi a ji kan zancen.amma ai ba akira Bilkisu yanzun ba a ruda ta,gashi kin san ta bata iya rudewa ba.yana gida ko?Mamanmu tace, yana nan kofar gida ya tara makota da yan uwansa mazan sai lbrin yake basu,sai ka ce wani zararre.. Umma tace,kije gida in anyi sallar isha'i zamu zo yanzun insha Allah. Mlm Mamman ko ana idar da sallar isha'i ya shigo dakin mamanmu tana zaune kan abin sallah,tayi tagumi ya zauna yana 'yar dariya. Abin al'ajabi wai yau malam ne yake min fara'a cikin zuciyar mama kenan take sakawa.yace fatima cire tagumi ai kin daina tagumi,ki kwantar da hankalinki muyi magana,sallamar umman mansura ne ya tsaida shi ya amsa tare da cewa,ku shigo.Tace yauwa kana ciki ba? Nima ni da maigidan ne dama gurinka muka zo, yace bismillah ku shigo, shimfida tabarma fatima. Umma tace bari in kira shi to. Sun zauna bayan gaishe-gaishe,sannan Abbansu mansura ya soma da cewa,mlm mamman,mai dakinka ce tazo mana da wani batu na game da yarinyar nan Bilkisu,shin me yake faruwa ne?Mlm mamman ya gyara zama,ya shiga rattafo musu yanda abin ya faru,daki-daki.cikin jin dadin shi gashi lbrin baya gundirar shi,hakan baya gajiya daba lbrn. Babu wanda ya katse shi sai da ya kai aya. Abban su mansura yayi gyaran murya sannan yace Maman Bilkisu in dai abin da ya fada haka ne, to wannan abin farin ciki ne da murna, ki kwantar da hankalinki, zan yi waya gidan su mansura yanzu, kuma zan sa a darennan shi mijin mansuran ya bincika min ta hanyar buga waya mu ji gaskiya lamarin, tunda ai Yariman da ake magana kani ne a gurinsa, dole zai San komai, mlm mamman yace, ita dai ta sani ni fa na riga na bada 'ya, ke ko dan wa'yancan sakarkarun matan masu nuna bakin ciki ba kya ware asha daula ba. Mamanmu ta ce, kai dai ka sani kun fi kusa da su. A yau ne kasan sakarkaru ne? Umman mansura dariya ma ya bata,a ranta tace, namiji kenan.
Lalubawar farko Abba ya samu farooq, lokacin yana kwance ya dora 'yar bebynsu sa'adatu a kirji, Mansura ta saka kanta a cinyoyinshi, ya dauki wayar ya duba.yace, kai Abba ne ya tashi zaune tare da dora babyn akan katifa, yace salamu alaikum, Abba ina yini? Suka gaisa. Abba yace, kana da lbrin Yarima dan uwanka zai yi aure? Farooq yace Aa ai baya nan ma.Abba yace, to yi waya ka min bincike yanzu-yanzu, farooq yace, to Mansura da ta tsura mishi idanu tace, meyace? Ya daga mata hannu, inda zuwa, layin magajin Malam ya nema yasan shi ne zai San komai, bayan sun gaisa ya ce magaji shin gaske ne Yarima zai yi aure? Magajin Malam yace, haka ne, har ma an bashi matar a Zaria, kawar matar ka ko? Cike da mamaki yace, Oh dama Bilkisu CE? Magajin Malam yace ita CE mana, yanzu haka an biya sadaki farooq yace, Yarima ya sani? Aa in ji magaji, bai ma san za ai masa aure ba, kuma mai martaba yace kada a sanar dashi. Farooq yace shi kenan, mun gode. Ya kira Abban Mansura yace eh Abba zai yi aure wai Bilkisu ce ma, Abba yace, to shikenan, ina so tunda gobe Sunday kana gida ka zo min da Bilkisun, amma kada kace mata komai ko ta sani? Farooq yace Aa yace kar ka sanar da ita sai kun zo. Ya kashe wayar.....
[8:48AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 36馃彽
Cike da mamaki farooq ya zuba ma waya idanu, Mansura a tsorace ta zaro idanu itama, tana kallon shi tare da cewa, wai menene Baban dady? Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce wai Yarima ne zai yi aure. Ta dan ja tsaki, to in Yarima zai yi aure me ya kawo Abba ciki? Ni wlh har na tsorata, zatona babu lfy ne,.Yace. Aa to kin San wadda Yariman zai aura ne? Ta sake zaro idanu tace wa? Yace Bilkisunki ta nan gidan.. Mansura ta mike Bil..... Wa? Yace, Bilkisu. Ta kuma dafa kirji in ji wa? Yace, gashi yanzun na kira magajin Malam ya tabbatar min har an biya sadaki! Sai dai wata tsiyar, shima Yariman bai sani ba, yanzun haka bai ma San za ai masa aure ba, itama nan gashi bata sani ba. Amma Abbanku yace gobe muje kada ki nuna mata kin San komai. Mansura taja tsaki, gaskiya ban so mata Auren Yariman nan mai zafin kai ba, farooq yace, ni ko na mata murna, domin Yarima yana da halin girma irin na gadon gidan su abin da ya faru tsakaninsu wannan shedanne . da zaran sun zauna zama na Auren sunna za su sasanta Kansu, kuma za ya kula da ita. Mansu tace, Allah yasa.
Su ko a nan zariya, Abba ya tabbatar ma da Mamanmu cewa batun aure gaskiya ne haka ne. Ya kara kwantar mata da hankali su da Umman mansura. Sun tafi kan cewa sai gobe in Bilkisu tazo zai zo a fito da kaya a duba.
***************************
Wayarsa ta soma ruri,Chelen ta mike ta dauko masa wayar,yana ganin number Magaji yace,Allah dai yasa lafiya?Ya daga sun gaisa sannan Magaji yace,mai martaba ne yace a tambayeka yaushe zaku samu hutu?Yayi shiru,sannan yace,sai nan da sati kila bakwai,yace ok,zan gaya masa.Yarima yace,lafiya Magaji?I think so.Yarima yace,naso ma nayi hutuna anan.Magaji yace,ok,ka iya yin waya ka gaya masa.Kai fa,bazaka fada ba?Inji Yarima.Magaji yace,No.Ya kashe wayar tare da cewa kada ka fada din,ni zan masa waya.Chelen ta matso kusa tana lasar kirjinsa da yayi laf da suma,tace tana son ya koya mata Hausa tana son yaren,yace bashi da time,kuma shima ba iyata yayi sosai ba,don shima Hausa fulani ne.Idanu ta tsura masa tana gaya masa cewa bazata gaji da gaya masa cewa yana da kyau ba tace shiyasa take kara son sa harma takan kirasa da One in town.Shi ko ce mata yayi yana sonta ne kawai irin na sha鈥榓wa,yace shi fa bai ma gama yarda cewa akwai wata soyayya ta No one but you ba.Shiru tayi don tasan yana nufin abinda ya gaya mata ne,kuma ya jima yana gaya mata haka,tasan bazata taba tursasa zuciyarsa ta so taba,kuma tasha yin fushi dashi,sai ya share ta sai dai ta dawo da kanta don shi bai iya lallashin mace duk da yanda takai da ji da kanta.Shiyasa kawai ta hakura da yin fushi dashi. Sun iso zaria misalin sha biyu,kai tsaye gidansu Mansu suka nufa,sun iske Umma tana shirin fita.Abba kuma ya dan fita shima,tace su zauna tana zuwa,Bily tace bari ta leka gida Umma tace a鈥榓 su dai jira gidansu Maman ta nufa,ta samu Mamman a dakin yace,yauwa Hajiya,shigo kinji fama nake da baiwar Allah nan za鈥榓 kawo kayan nan dakin tayi wa 鈥榶an uwanta waya suzo saboda mutanan nan zasu zo ne su kaita gidan ajiya,an jima kamar yanda nayi muku bayani jiya,duk taki ta bani hadin kai. Umma tace yanzu dai gata nan sun iso suna gidanmu,bari inyiwa Mansu waya ince suzo nan din ko dan tasan halin da ake ciki?Mama tace nima damuwata kenan,gaskiya in maigado bata son abin nan nima bazan so sa ba,dan fari ba mahaukaci bane,koda nake kauda kai kanta ba don bana sonta bane,ina dai kara ne,wulakancin dakayi ta mata cikin gidannan,ko tsinto ta akayi ba鈥榓 mata haka ba,shikenan haka rayuwarta zata zama cikin bakin ciki.Nan bata huta ba kuma tayi auren kudi can ma taje taci gaba da fuskantar wulakanci?Sam bazan lamunta ba,yaja tsaki ai kinji ki da wani zance,ba鈥榓 tuna abinda ya riga ya wuce,batun aji ra鈥榓yinta wannan ba dole bane tunda ko ashari鈥榓 mune masu zaba mata miji.Mamanmu ta kalli Umman Mansu tace,kirasu dai muji zabinta shine nawa nina san wahalar da nasha kan 鈥榶ayana.Bily ta rasa dalilin dayasa suna nufowa gidansu taji gabanta yana ta faduwa,ta dubi Mansu tace,ko dai wani abu ne ya samu Mamanmu?Mansu tace,me kika gani?Ta kama hannu Mansu ta saka akirjinta tace kinji fa kirjina.Faruk yace,ba komai insha Allah.Suna shiga da sauri ta nufi dakinsu,ganin Mama zaune yasa tayi ajiyar zuciya har duk 鈥榶an dakin suka dubeta,ganin Mama hankalinta ya kwanta,sai dai tasan da magana don banza Baba ba zaizo ya rashe haka ba.Ta shiga ta zauna kusa da Maman,tace Mamanmu har naji dadi dana ganki lafiya domin na zata wani abu ne ya sameki.Umma tayi 鈥榶ar dariya tace,鈥榶ar Mama kenan Mama kuwa cewa tayi lafiya lau maigado.Su Mansu suka shigo,Bily ta kara shimfida wata tabarmar,sannan aka shiga gaisawa,ta gaida Baba wanda zuciyarsa ta tafi ga tunanin yanda 鈥榶artasa ta nuna halin ko in kula dashi yau ne kurum abin ya fara masa ciwo,don da baya ma so ta nuna ta damu dashi Bayan gaishe-gaishe,Umman Mansu ta dubi Bily tace,kin san Yarima?Gaban Bily ya fadi,ko dai yasa anci ma iyayanta zarafi ne?Ta tambayi kanta,Umma ta katseta kin sansa nace?Bily ta girgixa kai alamun a鈥榓,tare da cewa ni sam bansansa ba.Yace nayi masa wani abu ne?Umma tace,a鈥榓 sannan ta dubi Malam Mamman tace,malam bani kudin nan.Jiki yana rawa ya ciro ya miko mata,ta amsa sannan ta aje agabanta.Wannan sadakinki ne,Bily ta zaro idanu tare da dafa kirji,Umma taci gaba ga kaya can yanzun za鈥榓 shigo dasu na zance,bikin bazai fi wata biyu da sati daya ba,me kika ce? A rude Bily ta juya ta kalli Mamanmu,sannan ta fada kan Maman tare da fashewa da kuka,tana cewa Mamanmu menene zabinki?Ki fada min zabinki shine nawa.Amma ina so ku sani Yarima zai aure ni ne ba domin yana sona ba,sai domin ya idar da wani nufi nasa na cin zarafina.Malam yace,ke dai kawai kice kinfi son kici gaba da zama agari babu aure,mutane suna zagina,amma ina kika san Yariman da har zaki wani ce yayi ne don yaci zarafinki mutumin da aka ce yana kasashen Turawa?Mama tace,tashi ki share hawayenki,in har ba kya son sa babu matsi,don ba akan kowa kike ba.Malam ya fita fuu yana cewa,ni dai ya rage naku.Uba ke bada aure kuma na bada ta.Sadaki kuma gashi nan a hannunku,in zaku ja da sarakuna ne bismillah.Ya sake lekowa,kada ku manta yau zasu zo su kaita su adana,sai ku shirya abin ce musu in sunzo ni kunga tafiyata,ya shuri takalmansa yayi waje.Umma ta dubi Bily dake kuka Mama nayi,ta waiga gurinsu Mansu inda sukayi shiru tamkar ruwa ya cinyesu,sai Mansu dake kuka,tace ku tashi kuje can gidanmu,ke Mansu har kai Faruk ku bata shawarar data dace,sai mu saurari hukuncin Ubangiji.Mansu ta kama Bily suka fita suna kuka,Faruk yana cewa suyi shiru kada su shiga cikin jama鈥榓 da kuka waton awaje in sun fita.
[4:01AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 42馃彽
Hakika mai martaba yayi murna da zuwan Yarima, fannin Umma kuwa sawa tayi aka shiga shirya ma autan nata gara kala-kala.Dan hutun sai da yayi wanka ya gama kyale-kyalen sannan ya fito gaban Umma yasa aka zube masa komai ya zauna tare da dararrashewa cike da shagwaba yake cin abincin suna shan hira,yace Umma taya naga duk zuwan da nake yi yau ne kuka fi murna da ganina?Ko dannayi zuwan bazata?Yace da haka kuma kazo ne akan gaba,wato kazo sanda ake son zuwan naka ma鈥榓na dama muna bukatar kazo din,ya dubeta saboda me?Tace saboda komai ma babana,kai dai gama zakaji komai gurin mai martaba.Gabansa ya fadi,amma sai ya daure ya jawo wata hirar.Umma kinyi kyau fa,kamar bake kika haifi su anty Salma ba.Umma tace,kai babana ko yaushe kazo zancanka kenan,wane kyau mun tsufa?Ai ba kyau ga tsoho,fatanmu dai mu ga jikokin kowa muga na auta,kasan 鈥榶ayanka sune asalin jikokin gidannan, kuma sune zasuyi gadon sarauta.Yayi murmushi insha Allah nima har nawa jikokin sai kin gani.Umma tace,a鈥榓 babana bana fatan ganin wannan lokacin yace to mu sake labari bana so kina tunanin cewa wata rana zamu rabu,tace ai wannan ya zama dole,yau ina tawa uwar? Yace,shikenan dai Ummata,ina su anty Fulera? Ta dawo daga jiddan kuwa?Tayi murmushi tasan ya kauce wa zancanne.Tace,sun dawo tuni Abban ya samu sauki sosai,haka suka ci gaba da hirarsu cikin nishadi irin na da da uwa. Masu matukar son junansu,sannan Magaji ya shigo inda yayi masa rakiya zuwa sauran sassan don gaida kishiyoyin Maman tasa,daga nan suka isa fada don yiwa sarki gaisuwa.Bayan ya rusuna yayi gaisuwa,sannan ya karasa gefen mahaifin nasa ya dora kai kan kafar mai martaba,wannan abin tun yana yaro haka yakeyi, mai martaba kamar ko yaushe ya shafa kan Yarima tare da furta Allah yayi maka albarka.Sannan Yarima ya zauna yana kallon yanda fada ke tafiya har zuwa lokacin
Da dare suna cin abinci cikin wani shahararren falon mai martaba,falo ne na gargajiya,yasha kilisa da tim-tim,in yana nishadi yafi son yaci abinci cikin falon.Yanzu ma Umma ce take zuba musu kalolin abincin suna ci,shi ko Yarima fruit yake sha cike da nishadin gashi zaune gaban iyayansa.Mai martaba ya dubi Yarima cikin sigar wasa irin na iyayan da suka shaku da 鈥榶ayansu,yace Allah gafarta Modibbo dama ka samu labarin auren naka ne shiyasa kayi mana zuwan bazata?Nan take cikin Yarima ya kada, kamaninsa suka sauya yace,ranka ya dade dama da gaske ne za鈥榓 min aure?Mai martaba yayi murmushi,sannan ya dubi Umma kinji wani shirme,dama ana wasa da zancan aure ne Modibbo?Umma tace,babana ai ka kusa angwancewa.Shiru Yarima yayi,sai dai duk kayan dake gurin sun fita ransa,duk da son cin dayake yi.Kofin ruwa ya dauka ya tsiyaya ya kai bakinsa yana sha,jin ruwan yake tamkar madaci,amma ya daure yana dan kurba don kada iyayansa su gane,sai dai ya makaro,domin tuni suka fahimci baiji dadin albishir din da suka masa ba sam.Mai marataba ya aje cokalin hannunsa sannan yace,mun maka laifi ko Al鈥榓min?Yarima ya kakaro murmushi yaya zaku min laifi?Ranka ya dade kunyi min gata dai.Ya sunkuyar da kai,na gode Allah ya rama muku.Ya dubi Ummansa banyi rashin kunya ba ko?Suka yi murmushin jin dadi,duk da sun sanya wayance ne.Yarima kam ya shiga rudu,lallai ya gamu da abinda yake tsoro,gashi bashi da mafita, bai saba musu da mahaifinsa ba,ba tarbiyar gidan sarauta bace,sai dai lallai da safe zai samu mahaifiyarsa yana son ya roke ta kan ta lallashi mahaifinnasa duk da yasan ba lallai bane hakan ya yiwu,bacci dai ranar kasawa yayi har nisan dare.Can ya dauki waya ya soma neman Magaji, magaji yana daga waya Yarima yace dan iska za鈥榓 iya hada baki da kai akashe ni tunda har aka kulla min aure baka ce komai ba.Magaji yace,kai haba wace zaka aura?Amma fa nayi murna. Tsaki Yarima yaja sannan ya kashe wayar,ya kwanta badon yana saran bacci ba,sai don kawai yayi tunani,hakace kuwa ta faru domin sai daya dawo masallaci sallar asubahi. Sannan wani nannauyan bacci ya dauke sa.Tara da minti hamsin ya farka, zuciyarsa cike da damuwa haushin koma wacece amaryar yake ji,don ya tsani abinda zai daga masa hankali har ya fita lokacin wani abu ya shiga na wani.Da rigar bacci ajikinsa ya nufi dakin Umma,yana so ne ya dan lallashe ta kila ta goya masa baya duk da yasan babu tabbas.Tana karin kumallo ya sameta cike da fara鈥榓 take dubansa, babana ka tashi?Ya dan turo baki irin na shagwababbun yara ya zauna ba tare da yace kala ba,Umma tayi dariya tare da cewa,auta yau shagwabar ta tashi kenan. Kafin yayi magana, jakadiya tayi sallama, Umma ta bata izinin ta shigo.Tayi gaisuwa gurin Umma,sannan tace,nazo ne in gaida uban dakina, tun jiya bamu hadu ba, naje yana bacci na koma aka ce kuna cin abinci,to yanzun dana je suka ce min ya shigo gurinki shine nace bari dai inzo na kosa inga uban dakina.Umma tace ga uban dakinki nan yana ta fushi.Jakadiya ta dubesa ran uban dakina ya dade,wa ya taba min kai?Yace dubi Umman shi Umma kinji?Tace naji me?Yace don Allah ki gaya ma mai martaba ajanye min zancan auren nan wallahi am too young shekaruna 24,amin aure,ku dubi karatuna mana yana bukatar natsuwa.Umma ta daure fuska,sannan tace kaga kada ka sake min maganar nan,magana an gama ta lokaci ya matso,sannan kazo da shirme?Yasa hannuwansa ya dafe kansa tare da cewa,Oh my God!Please Umma,I hope zaki iya shawo kan mai martaba,ni nafi son inna kai talatin sai inyi tunda kuna son nayi aure,amma yanzun fa 24 nake kafin talatin din ma ace ina da yaran?Bazan iya ba Umma.Ta mike sannan ta kallesa me yasa tun sanda ya sanar da kai baka musa masa ba,sai ni don ka raina ni zaka zo ka tasa ni agaba?To bari kaji bazai yiwu ba.Ta fita,jakadiya na cewa Allah ya huci zuciyarki ranki ya dade. Umma na fita jakadiya ta matso ta zauna kasa agabansa,ranka ya dade ai hakuri kawai zakayi.Ya dubi jakadiya idanunsa jajir yace,jakadiya na san kina taimaka min tun ina yaro,duk abinda nake so kina min kokari musamman agurin mai martaba.
[4:03AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 43 馃彽
Jakadiya tace,cikin sanyin murya da sigar lallashi ranka ya dade, wannan karon mai martaba bazai yi yanda kake so ba,in kuma mun tursasa shi yayi yanda kake so,to girmansa zai fadi,kimarsa zata ragu,me zai ce da sarkin zazzau wanda shine ma ya biya sadakin tare da kebe amaryar taka,wato ya killace ta?Shi kuma sarkin zazzau me zai ce da iyayan yarinya?Sannan kai kanka bakayi biyayya irinta 鈥榶ayan sarakuna ba,domin tarbiya gurinku ake koyo sai aji karfin iyayanka me jama鈥榓r Bauchi zasu ce?Ko kasan labarin aurenka ya shiga Bauchi da kewaye?Ka dawo tunaninka,ka kwantar da hankalinka tare dana Ummanka,gashi tayi fushi.Yayi ajiyar zuciya,ya sanin yanzun bashi da mafita,sai hakuri, ya dubi jakadiya yace, jakadiya yanzun to yaya zanyi?Tace yauwa uban dakina,ka samu Magaji ku shirya zuwa hira da amaryar taka wannan shine zaisa Ummanka ta sakko mai martaba yaji dadi su kuma yi alfahari da kai cewa zamanka a turai bai sa ka zubar da tarbiyarka ta Hausa fulani da addininka na musulunci ba.Yace shikenan,na hakura amma jakadiya Allah ya sani bana son matanmu na Nigeria,sam kauyawa ne basu ko iya kwalliya ba. Jakadiya tace,kai!Bari uban dakina,ba鈥榓 fi 鈥榶anmatanmu kyau ba da iya daurin dan kwali,asha jan baki da hoda.Yayi dariya,tare da cewa ai kauyancin kenan kullum jiki an rufe shi ruf,jakadiya tace ai wannan kuma haka addini ya tsara,inka aureta nan ne zaka ga kyanta kai kadai,ya taba baki sannan yace,ki sanar da mai martaba ashirya mana zuwa can ina ne ma kika ce?Tace zaria,yace 鈥榶ar masarautar ce?Tace a鈥榓,ba 鈥榶ar sarauta bace, shiyasa aka killaceta don dabi鈥榰n sarauta ya shige ta.Ya fita yana cewa,bari inje in yima Magaji waya.A dakinsa kafin ya kira Magaji,sai daya zurfafa tunanin shi lallai dole ya hakura karya zubar da darajar masarautar mahaifinsa,in yaso ana yin auren sai ya koma makaranta ya barta anan in anyi hutu yaki dawowa yayi zamansa can inta gaji ta nemi su sahale mata, yin wannan tunanin shiyasa Yarima ya saki ransa ya kira Magaji yace ya shirya zuwa Motoci hudu ne cike da dogarawa ata gaban ta bayan 鈥榶an sanda ne ta tsakiya kuwa Yarima ne shida Magaji, sai mai dauke da tsaraba zuwa kayan lashe-lashe wanda ango zai kaiwa amarya.Cikin bacci take jin gabanta ya tsananta da faduwa,ta farka da sauri ta tashi tana salati,ta kalli agogo biyu saura tace, a鈥榰zubillahi mina shaidanir rajim.Har lokaci ya tafi haka?Sai da tayi sallah sannan ta shiga wanka tana zaune cikin bahon wankan tana saba jikinta sabulu tare da kara gode ma Allah yanda ya tsara mata surarta,ga fata mai laushi ita kanta tasan cewa ta keru ne samanta da kasanta,sai dai matsalarta daya ce,rashin dacen miji domin nata ganin me zai ce mata?Allah yasa ma yasan menene auren inma yasani ita kam ai ta masa girma sai dai ya nemi 鈥榶ar sha shida.Haka ta fito daga wankan tana tunane-tunane,ta gama shafa jikinta da mai ta zura doguwar riga mara hannu,tasan yanzu masu kula da kwalliyarta zasu shigo.Sai ko gasu sunyi sallama,ta amsa suka kama aikinsu cikin zuciyarta kuwa haushin wannan kwalliyar takeji,ba don komai ba sai don a iska ake yinta,tunda ba miji gareta da zaizo ya gani ba,ita kuma ba fita zatayi ba bare tace...Atika ta katse ta da cewa ranki ya dade Allah yasa bamu muka bata miki rai ba kike tsaki?Bily tace,ina tsakin wannan kwalliyar ne ta isheni.Suka ce ya kamata ace kin saba da wannan kwalliyar ranki ya dade.Su Yarima kam kai tsaye fadar sarkin zazzau suka zarce,suka kai gaisuwa, sunci sun huta tare da yin sallah sannan suka nufi gidan da amarya take. Yarima da Magaji sai dogarawa guda biyu dake biye dasu cikin wata mota,Magaji ya dubi Yarima cike da tsokana yace,nasan gabanka yana ta faduwa,kana tunanin fara ce? Baka ce?Mai kyau ce bata da kyau?Oho.Yarima ya dubesa kamar bazaiyi magana ba har ma Magaji ya sadakar bazai ce komai ba,sannan Yarima yace,ina ma sonta kenan?Yaja tsaki kada ka raina ma kanka hankali,ka zata sonta nakeyi,ko daya yanzu ma jaje nazo in mata.Da sauri Magaji ya dubesa 鈥渏aje? Yarima ya jingina da kujera tare da share Magaji har sanda suka iso gidan.
[4:04AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽 MEKE FARUWA 44馃彽
A falon suka zauna,Magaji ya dubi kuyangin dake zube gabansu suna dibar gaisuwa yace,ina Gimbiyar take?Asabe tace,tana ciki ranka ya dade.Yace shaida mata isowarmu,tunda taji shigowar matoci ta kasa sukuni,ta mike tsaye tana ta kaiwa-da-komowa, sanye take da doguwar riga mai hade da hula. Asabe ta shigo ranki ya dade ki bani goron albishir,da sauri Bily tace,Mansu ce tazo ko Mamanmu?Asabe tace,ranki ya dade Yarima ne yazo.Ta dafa kirji cike da fargaba,tare da cewa,Yarima?Asabe tace,eh ranki ya dade.Bily ta soma zufa,koma kice ina bacci don bazan ganshi ba.Saroro Asabe tayi,amma dole taje ta fada,jiki babu kwari ta sanar dasu gimbiya tana bacci.Yarima kam ko juyowa baiyi ba,Magaji ko yace,to bari mu jirata.Ya dan saci kallon Yarima don ya fada ne kawai don yaji me Yariman zai ce,nan take kuwa Yarima ya dakawa Asabe tsawa da cewa,ki taso ta mana,ita wacece da har za鈥榓ce tana bacci? Duk Bily tana ji,nan take ta tuno da maganganun da Yarima ya gaggaya mata,don haka Asabe tana shigowa kafin tayi magana,Bily ta fita.Yarima yana zaune ne saitin dakin nata,don haka tana fitowa tayi arba dashi,yayi kyau cikin kayan da 鈥榶ayan sarakuna suka fi sawa,sai hula mai gashi da kuma takalman sarakai.Sam Yarima bai ko kalli inda take ba,duk da yasan ta shigo yayi shiru yaji da wacce zata fara?Amma sai yaji shiru,sai Magaji ne yace,ranki ya dade karaso mana.Yarima ya juyo da nufin yaga wai shin wannan wacece ita?Zumbur ya mike yana nuna Bily da dan yatsa tare da fadin dama kece?Ya kalli Magaji ka gane ta?Bai jira amsa ba ya soma tafa hannunsa sai da yayi tafi so uku sannan ya taka a hankali ya isa gurinta.Ya dubeta sai yanzun na fahimci dama kina da wata manufa akaina,kuma kinyi Achieving shiyasa kika ce kin sanni tun randa kika fara ganina?So kinyi kokari,yanzun dama nazo miki da abu biyu ne,na farko in tayaki murna sannan in miki jaje,daga karshe kuma in baki shawara,to amma tunda kece ina nufin ba wata can da nake zato ba,wadda bata sanni ba aka tilasta ma aurena bace,to abu uku zan miki ke maimakon biyu zan fara jinjina miki sannan in miki murna in kuma miki jaje,sannan in baki shawara sai dai shawarar da zan baki tasha banban da wadda nazo da ita,taki ta dabance.Ya juya mata baya tare da harde hannuwansa a kirji, jinjinar da zan miki kuwa?Ita ce na yaba da kokarinki yanda kika shiga kika fita tun daga kakana Modibbo zuwa mahaifina kika kuma hado da sarkin zazzau kinyi kokari har zuwacin nasararki na aurena.Sannan ina miki murnar samun miji kamar ni,hakika kinyi sa鈥榓r samun wanda mata ke so,kuma mai burin zama da mace daya rak karin sa鈥榓rki kuwa?Itace gidan sarauta ba鈥榓 saki mutu ka raba matsawar ba kin zo da wata alfasha bayyyananniya ba Sai shawara da farko nazo in ba wadda za鈥榓 aura min shawara ne akan kada ta yarda ta shigo hurumina, wato ta bijire ma aurena kafin zuwan ranar auren. Amma yanzun ke ya juyo ya nunata,bazan baki shawarar karki aureni ba,domin kece kika nema,kuma nima naso hakan don in banbance miki tsakanin aya da tsakuwa,sannan shawara sai kinyi hakuri da zama da karamin yaro kuma bugu da kari yaron jahili da kakkausar murya ya fada.Magaji ya taso yana cewa a鈥榓 Yarima what are you thinking? Yarima ya daga masa hannu don鈥榯 say anything baka san komai ba akan wannan yarinyar.Bily tace,kaini daina ce min yarinya domin ba sa鈥榓rka bace ni,sannan ka daina babatun na shiga nafita don na sameka wallahi kayi kuskure,yanda kake jin an matsa maka haka ma nima har ma gara kai,nida aka tuge ni kan aikina sannan duk zaman da kake bukata na shirya sai ka sani ni ina da ilmi kuma bana fata nabar tafarkin da musulunci ya shinfida min,don haka zan bika in Allah ya sa kai ne mijin nawa(hawaye ya soma zubo mata)sai dai na cutu don ba irin ka naso in aura ba.Ta juya zata tafi Yarima ya fizgota,kinsan zaman da zamuyi?Ya zuba mata manyan idanunsa cikin nata idanun masu tsananin haske da matsakaicin girma,yace ina tambayarki?Tace sai ka fada.Mace mai shekaru da ilimi mijinta karamin yaro jahili,kuma mai tsattsauran ra鈥榓yi sannan miskili in kin shirya you are welcome ya saketa da karfi ya fita. Magaji ya taso kusa da ita yace kiyi hakuri insha Allah komai zaiyi daidai, murmushin bakin ciki tayi ga hawaye yana zuba ita kam yaya zatayi?Daki ta shiga ta hau gado tana kuka zuciyarta kuwa tana tambayarta sai yaushe zatayi farin ciki?A baki ta furto babu rana,don yanzun zaka shiga sabon babin bakin ciki ne gidan Yarima gashi babu saki MEKE FARUWA dani ne? Lokaci baya jira sai dai ajira sa inji 鈥榶an magana,wannan haka ne domin yanzun dai saura sati daya bikin Yarima da Bily,gefensu Mamanmu babu zama,duk da ance ba鈥榓 son azo da komai Mamanmu ta dage lallai abada koda daki daya ne don azuba ma maigado kayanta,Mansu kuwa dubu dari ta zube ma Mama tana bada hakuri babu yawa,ban dana Faruk,su Sakina kowa yayi kokari sai dai su Gwaggo Ladiyo su hana kansu sukuni,sunata faman shige-shige 鈥榶an tsibbu suma sunyi nasu shirin.Gefen ango kuwa sam ba wanda ya zaci baya so,nan ya sake aka shiga shirya yanda biki zai kasance dangi kowa ya kosa.鈥榊an kawo lefe gidan Umman Mansu aka saukesu,suna dauke da akwati doxin biyu tare da key din henesy su anty Salma sun raina ma gidan da aka nemo ma Modibbo aure duk da tsarin gidansu Umma Mansu ina to ace gidansu Bilyn ne kila ko zama bazasuyi ba.Sai dai sun dan yaba da tarbar da aka musu,na kayan lashe-lashe da kuma ciye-ciye, sannan tukuicin dubu dari sun ansa a raine don bai wuce kudin shan sweet din yaransu ba,haka suka tafi suna ta surutu.Koda suka je suka gayama Umma,cewa tayi bata son surutu,in ma ba鈥榓 basu tukuicin ba ai ba addini bane.Ana saura kwana uku biki aka dauko Bily,wadda tasha gyara gurin tsohuwar da jakadiya ta tura,ga kuma Mansun ta tazo mata da tata tsarabar,sannan ga mai lalle tare da dilke.Nan fa Bily tayi kyau kamar aljana.Suna sa kai dakin Mamanmu dangin Mama suka kama fadin tubarkalla masha Allah, Allah yanda mutane suke ta cewa kai Bily kece kuwa?Kinyi kyau kaza- kaza,sai kawai ta boye gidansu Mansu,walima kawai suka shirya inda aka sha wa鈥榓zi da kuma nasihohi,bayan daurin aure kenan.
[4:07AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 45馃彽
Amarya hijabi har kasa da nikabi tasa ta rufe fuskarta don tunda ta fito daga inda aka killaceta sai ta ringa ganin haske yana haske mata idanu,don ta jima bata ga rana ba.Motocin daukar amarya sun kai ishirin zuwa gidan sarkin zazzau,sauran dangi sun wuce Bauchi a mota amarya ko jirgi zasu biyo su Ladiyo dasu Karime suma sun taho don su danyi 鈥榶an binne-binne nan da bokayensu suka basu. Haka nan yanda Mansu ta tubure sai da Faruk yayi ma Bily kaya haka Bily itama ta tubure sai an raba musu nata.Lallabata akayi Mansu ta diba,don Umma cewa tayi baza鈥榓 raba ba tunda tsadar kayan ma ba daya bane, tunda babu kasa da aura duk cikin kayan Mamanmu ma cewa tayi sai sun raba Mansu taki.Amarya ta isa gidan iyayan mijinta daf da magariba nan zasu fara zama agefensa tunda Malesia zasu wuce,gefen yasha gyara da kayan alatu,sannan ga dakin da aka basu suma su Mama sunyi kokari,sannan ga kuma gara shake da mota,duk fa hidimar nan malam Mamman ba ko taronsa,sai dai fa diyarsa ta auri dan sarkin Bauchi.Dinner daya da daya aka shirya a kayataccen Hotel kusan mutum shida ne akan amarya suna shiryata.Ni kaina muna hada ido nace subhanallahi,to ina ga ango.Yana zaune cikin shiga ta alfarma,wata alkyabba ce karshen tsada cikin motarsa limousine Ya kashingida yana kallon TV kuyangi da sauran dangi suka rakota har gurin motar suka bude mata ta shiga kamshin turarenta ne wanda tun tsawon zamanta agidan da aka killaceta tsohuwar take turareta dashi ya bugesa ga kuma na musamman domin shi Mansu tayi mata wanka dashi,ta shigo ta zauna tayi sallama,ba tare da ya kalleta ba ya amsa,sai dai yana kallonta da wutsiyar manyan idanunsa kyan da tayi tare da kamshin turarukan jikinta sun rikita sa kuma take sha鈥榓warta daya jima yanayi ta motsa masa,sai dai ya dake ya kuma shareta, amma zuciyarsa tana ta fadin she is beautiful.Ita ko Bily kasa kurum take kallo tare da yin wasa da yatsunta, xuciyarta kuwa tana kambama kyan halitta irinta Yarima. Guri yayi guri,dama ango da amarya ake jira shigowarsu cikin hall din zuka tana jama鈥榓 sun tsumu 鈥榶ayan Gwamnonin da 鈥榶ayan sarakuna sun jinjina ma zaban Yarima.Kai wani dan sarki daya kasa daurewa sai daya iska Yarima har mazauninsa ya bashi hannu,bayan sun gaisa sannan yace Prince Al鈥榓min ka dauki ta karshe acikin mata,Yarima yayi dan yake tare da godiya. Mansu ta dafa Bily sannan ta rusuno bayanta tace aminiyata kunyi kyau da yawa kun dace sosai tsaki Bily tayi tare da cewa ni duk kunya ma ta isheni, don abin kunya ne in auri dan wannan yaron.Mansu tace yanzun dai ya zama miji sai adaina ce masa yaro,Bily ta dan dubesa 鈥榶an jarida suna ta hira dashi tace bazan daina kiransa yaro ba,tunda ba girmata yayi ba.Dinner tayi kyau,gurin ya tara duk wani mai ji da kansa,鈥� yanmata da yawa sun kira Bily da mai tsananin sa鈥榓,domin cewarsu samun Yarima sai an tona.Bily takai kunnanta lokacin da wani dan jarida yake tana bayan Yarima wane irin farin ciki yake ciki yau kasancewar yayi aure da abar sonsa kuma mai tsananin kyau budar bakin Yarima sai cewa yayi shi wannan rana itace rana mafi muni cikin ranakun da yayi aduniya saboda me?Inji dan jarida cikin mamaki nan take Magaji ya katse dan jaridan da cewa tsabar murna ce tasasa baya iya saita maganarsa please ka tafi sannan na roke ka daka goge wannan bayanin da yayi.Bily bata ji komai ba don yace haka, dama tana tsammanin zance abinda yafi haka ma.Magaji da Faruk sunyi kokarin ganin Yarima baiyi wata tabargaza gaban jama'a ba gurin yanka cake nan ne suka danyi fama dashi yace bazai tashi zuwa ko ina ba don haka suka dauko cake din zuwa gabansa tare da baiwa jama鈥榓 uzurin cewa kunsan Yarima namu dan gata ne sannan shaukin mulki yana dibansa don haka bazai iya zuwa gaban cake ba sai dai mu kawo masa,haka an sha fama kafin yayanka sannan yasa mata abaki itama bayan Mansu tasha fama gurin lallashinta dan haka hoton ba da cake din nasu duk ransu bace yake,sai dai haka ni bai hanasu yin kyauba,haka dangi sukayi ta rawa suna zuwa suna zuba ma ango da amarya kudi, kasancewa duk sunki rawa Bily kam abin bai birgeta ba,ta tuna 鈥榶an watannin baya kafin ta gamu da Yarima bata da wani buri daya wuce ta samu miji,burinta shine aure farin cikinta taga wanda zai ce wance ina sonki,amma hakan ya gagara,har zuwa wannan lokacin da take aure.Ta dubi Yarima cikin zuciyarta tace,gadai mijin kuma mijin nunawa tsara,ta kalli dinbin mutanen dake gurin wadanda ada sai dai ta gansu cikin TV ko jarida ta dubi kayan jikinta zuwa gwala-gwalan hannunta duk wadannan abubuwan sun kasa sakata cikin farin ciki saboda rasa wannan kalmar ta so.To wai ita MEKE FARUWA da ita ne maza basa sonta?Sai ko ga hawaye shar daidai sanda wani dan jarida yake cewa,wane irin farin ciki kike ciki yau ranar aurenki?Ta bude baki zata ce tana bakin ciki ne ita aranar yau sai muryarta ta hau rawa,nan da nan Mansu tace da 鈥榶an jaridan bazata iya cewa komai ba farin ciki yayi mata yawa gashi har kuka ma takeyi.Bily tanaji bata tanka ba,ita damuwarta tasha mata kai,haka akayi ta shagali dangi suna ta bada kyautukan zannuwa, agoguna,masu dauke da hotunansu,wani iya shege da Magaji yayi shine,duk maroki ko mawaki daya zo gabansu Yarima yayi roko sai Magaji yace, yarima ya baka kujerar makka,ko mota kamar sau hudu ana haka,Yarima yana jinsa da yaga Magaji watan bai san zuri ba,kuma kyautar gidan sarauta babu karya ta bada,don haka sai yace Magaji ya isheka haka, inko ba haka ba duk wanda ka sake yiwa kyauta kaine zaka basa,don ni ban dauki yau ranar farin ciki bare har nayi wata kyauta,dariya kawai Magaji yayi yasan dai ya kunna Yarima. Bayan tashi daga gurin dinner haka akayi jerin gwano zuwa gidan mai martaba inda su Bily suka shige gefensu,sai da tayi wanka sannan tazo tayi alwala ta samu su Sakina duk sun kwanta da sauran jama鈥榓.Bily ce kawai take sallah,nan itama tayi sallarta sannan suka soma hira gurin dinner.Bily dai korafi takeyi akan yanda Mansu ta ringa bada ita gurin 鈥榶an jarida ita ko Mansu zakewa tayi tana ta fadin yanda sukayi yau cewarta bata taba ganin mata da miji da suka dace kamar ita da Yarima ba.
[4:09AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 46 馃彽
Sannan ta koma yiwa Bily hirar kayan gyaran jiki,Bily tace don Allah ki kyale ni kina yi kamar baki san wanda na aura ba,wannan yaron ne zan tsaya ina damun kaina saboda shi?Ta dan ja tsaki kinsan Allah koda ina son shine wallahi bazan bata kudina ba gurin wani gyara jiki saboda me ma ya sani game da auren?Ballantana ma ni bai min ba,ba sonsa nake ba shima haka. Mansu tayi dariya har da kwanciya, sannan tace,Bily baki san matasan yanzun ba kenan?Bily ta kwanta tana fadin barni da zancan nan kinji in huta,bacci nakeji. Mansu tace gobe ai ba kya yi shi ba,in mun watse, Bily tace sai ki hanani.Mansu ta kwanta tana cewa,in ban hanaki ba ai Yarima ya hanaki. Cike da tsokana tayi maganar,irinta kawaye. Banza Bily tayi mata taci gaba da addu鈥榦鈥榠nta na bacci,ta rumtse idanunta duk da cewa bata da tabbacin cewa baccin zai dauketa ko a鈥榓.Washegari sabon biki ne ya tashi gidan sarki dama su Umman Mansu suna can gefen Umman Yarima tare da su Gwaggo Ladiyo duk dai iyayen suna can matasan ne kurum anan gun amarya.Misalin sha biyu 鈥榶an yiwa amarya kwalliya suka shigo,sai da sukayi mata turare kusan kala goma daga ita sai vest da skirt,hatta gashin kanta yasha turare iri-iri,sannan ta saka wani leshi marar nauyi aka nade ta da laffaya,zobuna sarkar kafa,鈥榶an kunne,abin hannu. Subhanallah,haka mutane suketa fadi aka fito da ita zuwa falo ana jiran Yarima zasu je gurin sarki yasa musu albarka,sannan azo ayi budar kai.Shi ko gogan yana can ana fama dashi, jakadiya da Magaji sun tasasa da lallashi suka koma masifa.Magaji yayi zuciya ya fita,jakadiya cewa tayi bari taje ta sanar da Umman shi har takai bakin kofa yace jakadiya ta juyo yace yanzun me kike son inyi?Ta dawo cike da fara鈥榓 da kirari,sannan tace ranka ya dade da guda tamkar da dubu wanka zaka soma yi kayi shiga ta alfarma,gimbiya fa na jiranka a falo,na gode ranka ya dade sai ka fito.Ya bita da kallo har ta fita,sannan yaja tsaki ya shige toilet kusan awa biyu ya dauka sannan ya fito yana shigowa falo kuyangi suka mike jakadiya ta tasasu lallai ga zara ga wata, Suka ratsa jama鈥榓 har fada inda sarki yake zaune tare da fadawa da kuma manyan baki 鈥榶an taya sarki murna.Sun zube sunyi gaisuwa suna zaune gaban sarki yayi musu addu鈥榓 sannan yasa musu albarka ya umarci waziri da a miko masa alkyabba ta musamman ce ya tanade ta don yau,nan take yasa ma Bily.Wayaga gimbiya Bily,sarki da kansa yasan dan nasa yayi dace,nan malamai sukayi addu鈥榦鈥榠,sannan marokan sarki suka dora busa da kirari,su Bily suka fito mata suka dau guda ga kuyangi cikin ado suna biye dasu,sai gurin da aka gyara don budar kai,wani katon fili ne nan cikin gidan yasha decoration nan akayi budan kai.Ango da amarya sun samu kudi babu ma kamar ango inda matan sarakai kawan Ummansa da matan Gwamnoni zuwa masu fada aji,banda kyautar kuyangi daya samu daga sakkwato.Ana gamawa dama kamar yana kan kaya ne,suka nufi masallaci da suka dawo wanka yayi sannan ya saci jiki ya fita,wani guest house ya nufa ya kama daki yayi kwanciyarsa da nufin hutu.Su ko can gidan anci gaba da 鈥榶an bukukuwa,yayinda wasu bakin suka soma nade kayansu don tafiya gida.Ciki har da dangin Bily wadda hakan yayi mugun daga hankalita, musamman da taga Mansu ma tana hada kaya,ta zuba ma Mansu idanu tace,Mansu me kike nufi ne? Tace Gombe zanbi mijina,Bily tace ki daina min wannan magana,gaskiya bazaki tafi ba,kuna nufin ni kadai za鈥榓 bari bansan kowa anan ba?Mansu tana dariya tace,ba auren kenan ba?Bily tace amma ke ai na zauna miki. Mansu tace a ina? Tuna dai haka kuka kai ni Gombe kuka baroni,nan take Bily ta soma kuka tun Mansu tana tsokanarta har tazo tana bata magana,itama tana hawaye yanda Bily take kuka duk su Umma Mansu babu wanda baiyi hawaye ba,amma suka ki su kara kwana.Amma Faruk yace kafin su koma Kaduna zasu biyo su Sakina da Maryam suna kuka suka tafi,amma an bar mata auta kafin hutunta na makaranta ya kare,duk daba azo mata da kaya ba tunda ba鈥榓 shirya za鈥榓 barta tun daga gida ba,Umman Mansu ce tace abarta kafin Magariba duk an gama tafiya sai Bily kwance kan gadonta tana ta kuka,auta ko tana falo tana ta kallonta.
[4:12AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 47馃彽
Can dai taga bata da nayi sai hakuri,don haka ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala tazo ta tada sallah,Asma鈥榰 itama tazo ta tada tana zaune har isha鈥榠 tayi,tana idar da sallah kuyangi suka shigo suna shaida mata batun cin abinci,tace ita kam alhamdulillah,sai dai ga kanwarta nan su bata. Yinin ranar ma ita banda ruwa babu abinda tasha, balle abinci,haka nan suna kwance ita da Asma鈥榰 bacci ma yayi gaba da ita ko kayan jikinta bata cire ba,duk ta gaji take jin jikinta tana cikin baccin taji muryar jakadiya tana cewa,ranki ya dade har kin soma bacci ne?Bily ta tashi zaune,jakadiya tace wanka zakiyi yanzun.Bily kamar tace ki barni inyi baccina,amma sai ta daure tace to ta mike taje tayo wanka sannan tazo zata sa kayan bacci kenan sai ga jakadiya,tare da wasu kuyangin suna dauke da wasu kaya cikin kwalaye,nan take suka shiga yi mata kwalliya, shafa wannan goga wancan fesa wannan gashi kai ma yasha turare yafi kala goma.Jakadiya tana gefe sai data bada izinin su bari sannan ta mika mata wani kwali,kisa wannan ina dawowa.Ba musu ta amsa,jakadiya ta tasa su suka fita,Bily ta bude kwalin nan ko ta dago wata shegiyar rigar bacci bata taba ganin irinsu ba,koda yake yaushe ma ta shigo garin?Cewarta nan take ta saka har da takalmi,jim kadan jakadiya tayi sallama tare da neman izini.Bily tace shigo bayan ta shigo tace ranki ya dade kinyi kyau yanzun sai ki zo muje gurin Yarima.Ita kuma 鈥榶ar uwar taki zanje da ita can gurin Umma mai babban daki.Kamar ta gaddame amma sai ta tuna da maganarsu Umman Mansu,inda suke cewa,ki zama mai biyayya musamman kasancewarki acikin gidan sarauta su ba鈥榓 gaddama don gidan ilmi ne da tarbiya,don haka sai ta mike tabi jakadiya.Suka fita ta cikin falonta suka shiga wata kofa nan ma wani dan madaidaicin falone sannan suka kara shiga kofa,nan ma karamin gurin hutawane ko yin karatu,sai kuma ga kafar bene tayi sama.Bily dai tana biye da jakadiya suka hau sama nan ko wani hamshakin tafkeken falo ne mai tsari.Jakadiya tayi sallama shiru ta nufi wata kofa daga cikin kofofi ukun dake falon ta kwankwasa. jim kadan aka bude,Yarima yana sanye da jallabiya,ya dubi jakadiya kafin yayi magana tace,ran Yarima ya dade,amarya na kawo maka.Ta juyo ta yafito Bily da hannu,Bily tazo ta tsaya kusa da jakadiya. Jakadiya ta nuna mata dakin tare da cewa,mu kwana lafiya.Yarima dake bakin kofar ya hana hanya tare da cewa,haba jakadiya, kuna tirsasani da yawa,shin bata da daki ne?Tana dashi ranka ya dade,amma addini yana tafiya daidai da al鈥榓dar gidan nan,ga al鈥榓dar wannan masarautar gimbiya Bily bata da gurin kwana sai dakinka,kuma saba ma hakan laifine babba.Jakadiya ta dubesa in kaji zafi Allah ya huci zuciyarka,mu kwana lafiya,ta fita.Yarima kam falo ya fito,Bily ta shige ciki.Subhanallahi!!Ta furta afili tare da hangame baki tana kallon dakin,afili tace jama鈥榓 kamar baza鈥榓 mutu ba? Gado ne gashi nan kamar na zinare,in ma ba gold bane to kalar ce asaman gadon.Akwai wasu fitilu kusan guda sha biyu kaloli daban-daban,gadon kawai suke haskawa sannan ga wani net mai ruwan madara ya rufe gadon ruf.Ta tsakiyar net din fitilun suke,ta kai duba kan gadon yana liliye da shimfidu na alfarma ga fuloli da yawa kanana da kuma manya.Kujera daya ce adakin katuwa,sai madubi suk seti suke da gadon,kafet zuwa labule masu kalar madara ne kila ma tare suka zo har da net din.Tana ciki tana wannan juyayin shi ko Yarima yana falo shaidan na tuno masa da sa鈥榠n鈥榮ar su shi da Bily,kalmar jahilci data tofa masa da kuma kiransa yaro sune suka dinga yawo cikin kansa nan take zuciyarsa ta shaida masa cewa ka nuna mata aikin jahilci dana yarinta zunbur ya mike ya nufi fridge din sa ya ciro wani jus na kwalba ire-iren wadanda yafi sha,ya dau kofi ya nufi dakin.Bily tana tsaye ta jingina bayanta da bango,bai ko kalleta ba ya nufi kujera ya zauna, sannan ya jawo dan tebur din gabansa ya jawo wata durowa ya ciro fakitin magani,ire-iren magungunan da suke sha da su Chelen in zasu aikata masha鈥榓rsu,ya balle hancin kwalbar ya tsiyaya jus din cikin kofi ya afa kwayoyin ya bi da sassanyan jus din
[4:14AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 48馃彽
Kan Bily yana kasa zuciyarta ta zurfafa da tunanin makomarta acikin wannan auren sam bata san bikin da Yarima yakeyi ba sai da wayarsa ta soma ringing ta dago idanu ta dubesa gabanta ya fadi kar dai giya ce wannan?Ta tambayi kanta zuciyarta ta yanke cewa lallai giya ce take taji ta kara tsanarsa gami da kyamarsa shi kam cike da isa ya soma hira da Chelen ba tare da shakkar ga amaryar tasa kusa ba,kuma abin takaicin hirar batsa ce tsagwaronta, da turanci suke maganar inda yake nuna mata damuwarsa game da kewarta da yayi acikin hirar tasu yana kara jaddada mata yana bukatarta sai dai inya tuna daren ranar da zaya dawo hutu yana jin saukin kewar a cewarsa tayi masa tanadi inya koma zata gurzu. A karshe ya kira sunan albarkatun kirjinta yace tasa masa wayarta akai shi kuma yayi kissing.Innalillahi wa鈥榠nna ilaihir raji鈥榰n,duk da Bily ba son Yarima takeyi ba hankalinta ya kai matuka atashi,ji tayi tamkar tayi waje da gudu.Da ace ba jakadiya ta kawo ta ba itace ta kawo kanta hakika data zunduma da gudu,sai dai bata san in ta fita ba me hakan yake nufi da sauri ta sulale kasa ta zauna domin sai taji jikinta ya kasa daukarta, kafafunta sunyi sanyi. Hawaye suka soma yi mata zarya kan kumatunta,shi ko Yarima ai suna sallama da Chelen sai ya kira Vicky itama hirar batsar ce dai,kai tir inji Bily cikin zuciya.Bayan Yarima yayi sallama da 鈥榶an matan nasa sai ya mike da kofi ahannunsa ya fita falo jim kadan ya dawo ya aje kofin tare da cewa,in har kina bukata zaki iya sha.Da sauri ta dubesa tare da cewa,Allah ya tsare ni ya dubeta tare da daga kafadunsa gami kuma da taba baki alamun ko ajikina.Bayinsa ma ya shige ya watsa ruwa ya dubeta menene shirinki game da kwananki dakin yaro?Ta mike tare da yi masa wani kallo kafin tayi magana ya kuma cewa,amma ki rike acikin zuciyarki bana sonki kuma baki min ba sa鈥榓rki daya kina da kyau kila in dinga kula ki don kyanki,amma ba don so ba,haka nan kema bana so ki so ni,ya zauna kan kujera yanzun ina son ki cire duk kayan jikinki ki kwanta kasa kan kafet kila inji sha鈥榓warki.Tayi masa wani kallo sannan tace,ai kai abin kyama ne,domin ka kusanta kanka da zina,ka sani baka kai matsayin dani Bily zan cire maka kaya ba,don bana bukatar kayi sha鈥榓wata yanda kuma kake ikrarin baka sona to ka sani nima haka.Yace ashe ilimin da kike ikrarin kina dashi karya ne,don mace mai ilimi iyakacin sanina(koda dai kince ni jahili ne)bata gudun mijinta,matsawar yana matsayin mijinta dolenta ne tayi biyayya ba maganar so agurin,don haka kiyi yanda nace,in kinki zamu gwada kashi duk da kince(yaushe kashina yayi kwari?)domin dole ne na banbance miki tsakanin babba da yaro,ni dake yau dinnan ba sai gobe ba,duk da faduwar da gabanta keyi bata fasa cewa baza鈥榓 cire kayan ba kaji ko,salon kaje ka goga min cuta,fasiki kawai ban cire kayan ba kuma bazan cire ba ban dama rashin kunya har ma ka dubeni kace in cire ka....saukar marin data ji babu zato tana ta masifa shine ya katseta,lokaci daya ya saka kafa ya kwashe ta,ta yunkura zata taso ya sake sa kafa ya maida ta tare da fincike hijabin jikinta.Sun sha kokawa amma ga mamakin Bily Yarima kyaleta yayi take kici-kicinta,don daya tashi lokaci guda ya murdeta sannan ya yaga rigarta haka nan bada soyayya ko lalama yake son maida ta mace ba irin yanda take karantawa cikin littattafai ba,a鈥榓 fyade yake nufi don haka sai ta bar mutsu-mutsu domin ta samawa kanta sauki ta sadakar sai kukan zuci da kiran Allah.Shi ko Yarima duk da ya fahimci budurwace matar tasa sam cikin zuciyarsa babu nufin rangwame,haka nan gyaran da aka mata zuwa kamshinta sun kara taimako gurin fidda shi daga cikin hayyacinsa,har ma ya kasa tuna dawa yake tare illa sunayan 鈥榶anmatansa da yake kira hakan ya kara ma Bily bakin ciki,ta shiga rera kuka.
[4:23AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 49馃彽
Abin mamaki mintina suka shude bayan wucewar sakwanni har aka shiga awa itama ta shude kai har amarya ta kasa fahimtar shin aduniya take ko ko a lahira?Kuma bacci takeyi koko ta mutu ne?Ma鈥榓na ta sume gogan bai san ma me take ciki ba har zuwa uku da rabi inda ya samu sukuni na kyaleta ba tare daya ko kalleta ba ya shige toilet jikinsa ya gyara sannan yazo ya haye gadonsa ya barta nan yashe bacci mai nauyi ne yayi gaba dashi cike da nishadin da yake ji na daban wanda tunda yake harkarsa da matan banza bai taba jin hakan ba.Sanyin asubahi ne ya farkar da ita,dishi-dishi ta soma gani kafin daga bisani idanunta suka washe,daga inda take yashe tana hango Yarima tsaf cikin gadonsa yana sharar bacci fitilun tsakiyar gado sun haske masa fuska,bakin ciki ya cika zuciyarta tayi ta kokarin yunkurawa ta tashi ta kasa dole ta hakura jim kadan ya farka cikin mika da salati tana kallon bakinsa yana karanta addu鈥榓r tashi daga bacci,sannan ya sakko ya tsallaketa ya shige toilet.Ruwa ya watsa tare da alwala sannan ya fito ya saka fara kar din jallabiya ya fita duk abinda yakeyi yana yinsu ne akan idanunta amma ko kallo bata ishe shi ba.Ta tuna da Mansu kawarta daren Mansu na farko da Faruk,Mansu tace kwana yayi yana lallashina, sannan da sassafe jiki yana bari yazo ya daukar mata Bily yana ta faman tarairayarta haka nan cikin littafai inta karanta mazan kan rasa inda zasu sa kansu,amma ita dubi abinda nata mijin yayi mata,sam bata son tunawa da daren farkonta zuwa shida na safe ta danyi karfin hali ta mike zaune ta jawo rigarta wadda duk ya yaga mata gashi duk rigar ta baci da jini haka nan ta zura ta dafa bango da dafa bango ta fito falo yana zaune yana kallon aljazira ya ganta tana kokarin fita,ya mike da sauri.Ke kina hauka ne zaki fita ahaka?Ko kallonsa bata yi ba taci gaba da laluben hanya,da sauri ya kulle kofar sauka kasan,sannan ya zauna ya dauko waya ya soma kiran layin Umma,bayan sun gaisa yace ta turo masa jakadiya Kamar minti goma jakadiya ta soma kwankwasa kofa,ya bude sannan ya nufi kujera ya zauna tana shigowa taci karo da Bily daf da kofa cike da salati jakadiya tace 鈥榶annan lafiya?Ta riketa tace,zomu koma ciki.Bily ta girgiza kai alamar a鈥榓,jakadiya tace yi hakuri ranki ya dade,ai ba kya fita haka ba.Ta rike ta suka juya tana cewa ikon Allah, a garin yaya akayi haka? Yarima dai volume din TV ya kara suka koma ciki. Haka jakadiya ta gargasawa Bily jiki,cikin katon bahon wankan na Yarima,kafin ta nufi sasan Bily don kawo ma Bily kayan da zata sa.Ita kuma Bily tayi wankan tsarki sannan ta daura tawul,jakadiya ta kawo mata kaya ta fita doguwar riga ce baka ta zura sannan ta fito duk jikinta babu karfi,jiri ma take gani.Jakadiya ta nado rigar baccin ta saka cikin leda sannan ta dan rike Bily suka fita kai tsaye dakin Bily suka nufa take cewa ikon Allah,wai gaddama kika masa ne har haka ta faru ni laraba?Bily dai shiru tayi.Jakadiya taci gaba da cewa,banda abinki yanzun wa ke yayin wannan?Yara kanana ma irin na kauye in an kaisu daki shiru kake ji tsakaninsu da miji bakaji ba ka gani balle ke da girmanki da iliinki kuma kinsan su maza ba kunya ce dasu ba,gashi ma shine ya kira azo a dubaki.Bily dai tana jinta,kala bata ce ba.Ta kwanta akan gadonta,sannan jakadiya ta fita,gurin Umma ta nufa tana zaune kan sallaya hannunta rike da carbi tana lazimi,jakadiya ta zauna gefe sannan tace ranki ya dade na dawo daga kiran na Yarima ta cira rigar baccin cikin leda tare da fadin Ubangidana yayi sa鈥榓r mace 鈥榶ar gidan tarbiya,ranki ya dade amarya ta kawo budurcinta gidan miji.Umma tace,kai to menene kuma Yarima bazai bar ma cikinsa sirrinsa ba?Ai yanzu an daina wannan abin ilimi ya ratsa ko鈥榠na.Jakadiya tace ranki ya dade abinne yazo da matsala,dole ya nemi taimako,yarinya ce tayi gardama ne nake ga shi kuma dan yau babu hakuri,wallahi karki ga yanda yarinyar nan tasha wuya jini kyace an yanka karamar kaza,tana can kwance babu yanda take Umma tace to yanzun bari inyi ma Doctor Aisha waya tazo ta dubata Ke kuma kije ki sanar da masu aiki su shirya mata farfesu na kaji dana kan sa ko ta danji dadin bakinta.Haka ko akayi,doctor Aisha ta samu Bily kudundune cikin bargo kuka kawai takeyi,ta duba ta likitar da kanta ta hada ma Bily tea tace tasha don za鈥榓i mata allura ne.Bily ta dan sha sannan ta mata allura tare da bata magunguna duk na gajiya ne,tare kuma da huce radadi,haka nan ma likitar tayi mata mita kan cewa mai yasa bata ci abinci ba kafin mijin nata ya kusanceta?Shiru Bily tayi,doctor Aisha tace rashin cin abincin ya taimaka gurin galabaitar dake sannan kinyi kokarin hanasa kanki,kin matse jikinki har ya kaiga ji miki rauni.Cikin kuka Bily ta kwanta tama tsani yanda suke cewa ta hanasa kanta,basa ma tunanin koda ace ta hanasa kantanne ya dace ya bita asannu,bacci yayi gaba da ita wanda dama bata same shi ba jiya.Biyu da rabi ta farka kamar acikin mafarki taga Mansu da dady da Asma鈥榰,suna ta shan farfesu,da sauri ta tashi zaune jikinta ya daina ciwon sai dai ta jita fayau babu kwarin jiki,ta sakko tana cewa Mansu yanzun kika zo?Mansu tace tun dazun,munzo kina bacci muka je gurin Umman Yarima,Bily tace zo nan dadyna yazo ta dorasa kan cinya tana cewa,ina Abbanka?Ita ko Mansu dariya take ta kunshewa har dai Bily ta gaji tace wai dariyar mecece haka?Mansu ta dubi Asma鈥榰 tace,auta keda dady kuje falo kuyi kallon cartoon suna fita Mansu ta koma gefen gado kusa da Bily tace aminiyata Umma tace baki da lafiya duk rigimar kin bar Mamanmu ne ko?Bily ta soma hawaye ta kama hannun Mansu tace,wallahi ba kukan rabuwa da Mama nakeyi ba,dama yaushe rabona da Maman da aka kaini aka tsare kamar nai sata,tasa yatsunta ta matse idanunta,sannan taci gaba wannan mutumin ne yayi min wani mugun wulakanci,wallahi nayi dana sani sosai na sanin Yarima bama aurensa ba.Mansu tace wane mutumi?Bily tace Yarima nace miki.Mansu tace hala ya zazzageki ne?Bily tace ba gara ya min duka bama da fyaden daya min,wallahi har suma nayi kwana cur yana aikin abu daya, wallahi ni bazan iya wannan bala鈥榠n ba.
0 comments:
Post a Comment