Kin bari su hada ido tayi tana girgixa kai tace "Doctor plss ka sake ni..." Yace "Noo..." Kwankwasa kofa aka yi suka kalli kofar a tare, ta xaro ido tace "Wayyo ka sake ni..." Saketa yyi ya mike yana kallon kofar, ta tashi da sauri tayi hanyar bedroom, karasawa gun kofar yayi yace "Waye?" Muryar Ramla ya ji tace "Ni ce!" Yace "What?" Tace "Abba yana kiran ka wai..." Yace "Alryt ga ni nan xuwa" tace "Toh baxa ka bude ba yaya?" Yace "Yess" tabe baki tayi ta juya ta wuce, juyawa yayi ya shiga bedroom din ya ganta tsaye bakin kofa, tana ganinsa ta juya, ya rungume hannayensa yace "Ashe kina sa Hijab?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ina wayar da na baki?" A hankali tace "Yana gida!" Ya juyo da ita yana kallon fuskarta yace "ki ajiye shi kusa da ke yau, i will cal you" ta sunkuyar da kanta tace "Toh" yayi murmushi yace "Mu je in raka ki" hanya ya bata ta fita sannan ya fita shi ma, har kusa da gidansu ya rakata yana kallonta yace "Kar kiyi bacci fa, i will call you..." Daga haka ya juya ya wuce ta bi sa da kallo, snn ta nufi gate kamar mara laka ta shiga. Abuturrab na isa gida ya wuce parlor din Abbansa, Abba dake waya tun shigowarsa ya ajiye bayan ya gama yace "Aliyu!" Abuturrab yace "Na'am..." "Kadai san in ka raina ni to yakumbo ta wuce raini a gun ka koh?" Cewar Abba kenan yana kallonsa, Abuturrab ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, Abba yace "Tashi ka je...." Ba musu ya mike murya can kasa yace "Kayi hakuri Abba dama..." Kofa Abba ya nuna masa, hakan yasa ya fita kawai, sha biyu saura ya gama abinda xai yi ya rufe laptop snn ya dau wayarsa yayi dialing layinsa dake wayar da ya ba Samantha, tana kwance hannunta rike da hymn book tana dubawa kiran ya shigo wayar dake gefenta, langwabar da kai tayi ta dauka ta yi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Hope baki yi hacci ba?" Tace "Yanxu xan yi..." Yace "Tafi ki wanke idon..." Murmushi tayi ta make kafada kamar yana ganinta, yace "Ina son in maki wani tambaya samha..." Tace "Samantha not samha..." Yace "Noo samha not Samantha.." Tace "Uhm to ina jin ka..." Shirun kusan second ashirin yayi kafin yace "Za ki iya aurena?" Kasa cewa komai tayi sbda mamaki da ya cika ta, yace "I know you re there!" A hankali tace "Aure kuma?" Yace "Yeah.." Ta girgixa kai tace "But ae bbu aure tsakaninmu da kai, our religion differs, am a Christian, you re a muslim..." Yace "Akwai aure tsakaninmu...." Da mamaki tace "How?" Ya shafa kai yace "Sai kiyi addinin ki in yi nawa!" Wani shirun ta kuma yi words dinsa na mata yawo a kai, murya can ciki yace "Samha!" Kasa amsawa tayi, cikin sanyin murya yace "Baki so na kenan..." Jikinta yayi sanyi still ta rasa abun cewa, kiranta ya kuma yi kamar xata yi kuka tace "Ni ban san me xan ce ba..." Yace "Ki ce za ki aure ni" tace "you know that's very impossible, taya hakan xai yiwu bayan addininmu daban daban...." Lumshe ido yayi yace "Nace maki kowa addininsa xai yi, i see nothing wrong with that...." Rasa ma wani tunani xata yi a lkcn tayi, xata iya auren Abuturrab kuwa? Did she even love him? She know she so care about him.. Tunanin hakan sai da yasa gabanta faduwa sosai, to in ta yarda xata aure sa Mumy da Abba fa? Ya relative dinsu xa su dau xancen... Muryarsa taji yace "Samha!" Hawaye ne ya cika idonta ta kasa amsawa, da dadewa tasan she had alwayz like him, amma bata taba tunanin har xae shigo da xancen aure tsakaninsu ba, a hankali taji yace "Shikenan sai da safe" lkci daya hawayen idonta ya xubo cikin rawar murya tace "Doctor kasan baxai yiwu ba, My parent... My relatives, my...." Kuka ta fara masa, duk ya rikice yace "Kuka kuma... Pls stop it now" kasa daina kukan tayi, yace "OMG don nace xan aure ki shi yasa ki kuka, ok am sorry baxan sake ba..." Daga haka ya katse wayar, ya jefar gefensa ya kashe wuta yayi kwanciyarsa, hade kai tayi da gwiwa ta fara kuka, daga karshe ta gaji ta kwanta, kasa bacci tayi daren ranan, maganganun Abuturrab kadai ke mata yawo a ka, sae kusan karfe uku ta samu bacci ya dauketa, Mumy ce ta tasheta karfe takwas da minti sha biyar, ta mike xaune, Mumy tace "Baki tashi kinyi morning devotion din ki ba wnn wani irin bacci kika yi" Kallon idonta Mumy tayi tace "Me ya samu idon ki, kuka kika yi ne?" Samantha ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "kai na ke min ciwo..." Mumy tace "Kai kuma? Toh tashi ki shirya sai kiyi breakfast ki sha magani," daga haka ta fita, da kyar Samantha ta mike tsaye don ji tayi gaba daya kanta ya mata nauyi, bathroom ta shiga ta wanke baki tayi wanka sannan ta fito, tana goge jiki Abuturrab ya fado mata wanda hakan sai da yasa gabanta ya fadi sosai, hawaye ya cika idonta, jiki a mace ta karasa shiryawa, Blessing ta shigo da tray dake dauke da breakfast ta ajiye mata ta gaisheta snn ta fita, da kyar ta iya shan tea xata kwanta sai ga Mumy ta shigo da magunguna ta bata ta sha, mumy tace "Thank God sai da ku ka gama jarabawa ciwon kan ya same ki, ki kwanta xuwa anjima mu ga" daga haka ta fita, Samantha ta kwanta hade da lumshe ido, ta kasa daina tunanin Abuturrab ta kuma rasa dalili, a da tasan yana yawan fado mata barin idan suka dade basu hadu ba, amma tun daga jiya da daddare xuwa yau sae ta ga ya fi na ko da yaushe, to fushi yayi ne yasa ya kashe wayarsa amma ai gaskiya take fada, runtse ido tayi ko bacci xae dauketa amma shiru, sae a lkcn tasan ashe fa ta damu da shi haka. Har washegari Abuturrab bai sake kiranta ba, ita dai tasan bbu wani ciwon kai but da Mumy ta tambayeta me ke damunta sai tace ciwon kai, tun da take abu bai taba tsaya mata a rai kamar yanda wannan ya tsaya mata ba, ta kasa dauke tunanin a ranta, Mumy ta kira Abba dake Lagos ta fadi masa bata da lafiya xa su je asibiti, Abba yace ba sai anje ba xae turo likita, Abuturrab na xaune office yana aikin gabansa, baka taba cewa abu na damunsa sai dai da xaka shiga xuciyarsa ka ga tulin damuwar dake tattare da gun sae ka tausaya masa, babban damuwarsa bai san yanda xae yi da Yakumbo ba don yasan shi ake ta jira, gashi ya kasa daina tunanin Samantha, yasan ba fault dinta bane that's just the fact but kawai ya shareta ya kuma dau ma kansa alkawarin ko ba yanxu ba sai ya aureta ko da kuwa threatening din kisa xa ayi masa, Tun a daren yake raya ma kansa to ko ya koma ga saudat, yana jin kuma xuciyarsa ta aminta da hakan coz he gat no option. Daren ranan ya shirya ya tafi gidansu Saudat, tun da yayi parking a kofar gidansu yake kallon motar dake parke gaba da nasa ganin kamar akwai mutane a ciki, ae ko sai ga shi an bude motar saudat ta fito, tabe baki yayi ya tada motarsa kawai yayi reverse ya bar gun, bai bar layin ba kiranta ya shigo wayarsa, ya ci gaba da tukinsa ba tare da ya sake kallon wayar ba. Washegari Wednesday yana xaune office ya hade kai da table Mujaheed ya shigo, har ya karasa gun table din Abuturrab bai dago ba, mujaheed ya bugi table din yace "Bacci kake a bakin aiki doctor?" Dagowa Abuturrab yayi yana kallonsa yace "Daga ina haka?" Mujaheed yace "Asibiti na xo bani da lafiya mana" murmushi Abuturrab yayi yace "Ohh i see" mujaheed yace "Ya na ganka haka kamar kana tare da damuwa" Abuturrab yayi yake yace "Damuwa kuma, am just tired ne, ya aiki?" Mujaheed yace "Alhmdllh"
*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫
22......
Hira suka ta yi a asibitin har bayan la'asar suna fitowa daga masallaci ko wannensu ya dau hanyar gida, yau kam Abuturrab a main house dinsu ya sauka, Mami dake parlor ta bi sa da kallo bayan ya gaisheta har ya haura sama, wanka yayi ya fiddo jallabiyarsa a daki ya sa yayi kwanciyarsa. Ringing din wayarsa ne ya tashesa kusan magrib, dai dai shigowar mami dakin tace "Lafiyan ka Aliyu, baccin yamma ana xaune kalau?" Mikewa xaune yayi ya dau wayarsa yayi picking call din, daga daya bangaren aka ce "Hello!" Abuturrab yace "Good evening" "Evening, kana gida ne doctor" cewar mutumin kenan, sae a snn Abuturrab ya dau murya yace "Yeah ina gida sir, ya aiki?" Mr David yace "We Thank God, daughter na ne bata da lafiya, i want you to check on her if it's ohk by you and you re less busy pls" Abuturrab da hankalinsa ya tashi lkci daya yace "Ohk sir, i will do that right away!" Daga haka ya katse wayar ya kalli Mami dake tsaye har lkcn tana kallonsa yace "Mami na gaji da yawa ne yau" tace "ko abincin fa baka ci ba" mikewa yayi tsaye yace "Bari in dawo daga masallaci Mami" daga haka ya fita, ana idar da magrib ya tafi gidansu Samantha, bayan sun gaisa da mai gadin ya shiga, mai aiki ce ta bude masa kofa bayan ya danna bell, ya amsa gaisuwarta ya tambayeta inda Samantha take tace tana bedroom, ita ta raka sa har sama, ya bude kofar dakin suka yi ido hudu da mahaifiyarta dake xaune dakin alamar dai likita take jira, tana ganinsa ta hade rai sosai, ya sunkuyar da kansa ya karasa dakin ya gaisheta da ladabi, da hanci ta amsa masa ta mike ta fice, Abuturrab ya durkusa kusa da gadon yana kallonta ganin yanda lips dinta yayi ja, hannu ya daura forehead dinta ya ji dumi, a hankali yace "Samha..." Bude ido tayi da sauri ta mike xaune, ya kamo hannunta yace "Ina ke maki ciwo?" Hawaye ya cika idonta ta ki cewa komai, cire bargon jikinta yayi yace "Talk plss" ta sauke idonta kasa, ya tsura ma wuyarta dake dauke da farin cross ido, a hankali ya kai hannu kai xae tsinka ta rike hannun da sauri tace "Mumy ce ta sa min" bai kulata ba ya tsinka shi ya jefar gefe daya, ta sauke hannunta tana kallonsa, kallon kwayar idonta yake shi ma, hawayen da ke makale idonta ya gangaro ta daura kanta a shoulder dinsa cikin sanyin murya tace "Ni fa ban ce komai ba doctor, and you re angry, kayi hakuri pls..." Ya harde hannunsa da nata ya lumshe ido yace "Noo, kin fa ce baxa ki iya aurena ba" ta fashe da kuka tace "Nooo ni bnce haka ba fa..." Shiru yayi yana jin saukar hawayenta a shoulder dinsa, ya shafa kanta a hankali yace "But nace kiyi addinin ki inyi nawa fa, still kika ce it's impossible" girgixa kai tayi tace "Bayan kana rabani da duk wani abu na addini na shine xaka ce min haka, yanxu fa ka tsinka min rosary dina...." Buda ido yayi jin abinda tace, ya dago kanta yace "Ohh you gat me wrong samha..." Da sauri tace "Noo i am right" yace "You re sick kuma rosary din nan is a burden....." Hade rai tayi tace "A tunanin ka ba, kayan jikina bai xame min burden ba sai rosary" yace "Alryt am sorry baxan sake ba..." Bude kofa aka yi ya koma baya da sauri blessing ta shigo da gani kasan mumy ce tace ta taho, Ya kalleta yace "Taimaka mana da cup of tea pls.." Tace "Toh" snn ta fita, ya kamo hannunta yace "Toh yanxu ina ke maki ciwo" kanta ta nuna masa, yayi shiru yana kallonta, can yace ohk yanxun nan xae daina, lumshe ido yayi ya manna bakinsa kan goshinta, turasa ta fara yi tace "Doctorrrr" ya rike kanta gam ya sauko da ba lips din har kan hancinta sannan bakinta, yayi mata light French kiss, turasa tayi ta hade rai, ya wara mata ido ya koma baya yace "Alryt am sorry wife...." Blessing ce ta shigo da cup din tea ya karba ya mika ma Samantha, ta6awa tayi tace "Akwai zafi ai" ya ajiye sa kan bedside drawer yace "Toh bari inje in dawo yanxu" da ido ta bi sa har ya fita, gida ya koma ya dauko mata drugs ba a dau lkci ba ya dawo, har lkcn blessing na dakin, yayi mata kallo daya ya karasa gun Samantha ya dau tea din da ya ajiye ya kai baki yayi sip dinsa snn ya mika mata yace "Toh ya huce" hannu tasa ta karba, aka bude kofa Mumy ta shigo, mikewa yayi ya bude ledan maganin ya gwada mata yanda xata sha ya ajiye ya d'an saci kallon mumy ya ganta tsaye fuskar nan a murtuke, dukawa yayi kamar xae dauki abu murya can ciki yace "I will call you ltr..." Daga haka ya juya, bai bari sun hada ido da Mumy ba yayi mata sallama ya fita. Kamar jiya yau ma sha biyu da wani abu ya kirata, tana kwance ta dau wayar tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "How you feeling now?" Tace "Da sauki..." Yace "Sai kice Alhmdllh..." Ta buda ido tace "Alhmdllh kuma?" Yace "Yess" tace "Tohm Alhmdllh" yayi murmushi yace "Good, a ina muka tsaya jiya a maganar mu?" Bata ce komai ba yace "Samha..." Cikin sanyin murya tace "Na'am" yace "Baki son maganan ne?" Girgixa kai tayi kamar yana ganinta tace "A'a fah" yace "Say something now" da kyar tace "Duk yanda kace doctor" murmushi yayi yace "Ohk we'll talk about that face to face...." Cikin sanyin murya tace "Toh" "Me xa ki bani for my birthday?" Wara ido tayi tace "Woaw, it's also my birthday month, wani date ne naka?" Yace "Da gaske kema month dinki ne?" Tace "Eh mana, my birthday is on 10th june...." Da mamaki yace "Are you for real?" Tace "Yes mana" yace "Woaww what a concurrent! It's same with mine" tace "heey doctor ba wani nan..." Yace "Am serious samha, i was also born on 10th june" tace "Wow so we re birthday mates?" Yace "Yeahh and we gonna celebrate it together.... No wonder shi yasa kike da kyau kema kamar ni... Haka kuma xa mu haifi yara duk june 10" Ta xaro ido tace "Uhm?" Yace "Yess am serious baby, today is 3rd, 7 dayz to our birthday!"
Tun daga lkcn wayarsu ya xama constant don xaman gida kawai take, duk bayan awa biyu sai ya kirata, hakan kuma yasa bai damu da rashin ganinta ba tunda suna waya, a haka har ya rage kwana daya birthday din nasu, da daddare yana daki ya kirata yace "Baby plss ki daure ki fito yau mana, i want to see you" ta kalli agogo taga har tara da rabi tace "But baka kalli agogo ba koh doctor" yace "Na kalla mana ai ba dadewa xa kiyi ba" xata yi magana yace "Plssss" kamar xata yi kuka tace "Doctor....." Yace "Plss" turo baki tayi tace "Na ji" daga haka ta katse wayar, tayi tagumi, can ta mike ta dau hijab ta sa ta kashe wutan dakinta ta fita, ko blessing dake daki bata sani ba, tana isa gidan bata gansa parlor ba, ta bata fuska tana kallon kofar daki, a bayanta taji sa a tsaye ta juyo da sauri ya wara mata ido yace "Welcome..." Tace "Toh kiran meye" kama hannunta yayi ya shiga da ita kitchen yace "Am hungry kuma potato and egg nake son ci, hope Mumy baxa ta neme ki ba" shiru tayi bata ce komai ba, can a hankali tace "Ohk... Mumy ta tafi church" Yace "Good, cire hijab din" tace "No xan yi a haka" gun da potatoes suke ta nufa ta debi wanda tasan xai yi masa ta fara ferewa da peeler, cikin kankanin lkci ta gama, duk yana tsaye yana kallonta, kafin minti goma har ta gama, ta daura ruwan Lipton ta juya tana kallonsa tace "Ko baxa ka sha ba" yana rungume da hannunsa yace "Xan sha mana" kayan kamshi ta xuba ta rufe snn ta dau dankali da kwan ta fita ta kai parlor ya bi ta da kallo, tana dawowa kitchen din tace "Toh kaje ka ci kafin ruwan shayin yayi" ya girgixa kai yace "No xan taya ki jira a nn" murmushi tayi bata ce komai ba, haka suka ta tsayuwa har ruwan ya tafasa ta juye flask snn suka fito, sai da ya tilasta ta suka ci abincin a tare, nan ya sa masu film a system tun tana cewa ita gida xata wuce har ta hakura tana kallon, kamar ance ta kalli agogo taga sha biyu saura 'yan mintuna, xaro ido tayi tace "Na shiga uku, doctor kalli agogo" mikewa take son yi ya riketa yace "But it's late Samha...." Turasa tayi tace "Let me plss, ni bana son kana min irin haka, you are just letting me betray my parent, ni ka sake ni" a fusace tayi maganar ta mike ya bi ta da kallo har ta isa kofa ta dawo don daukar takalmanta dake bakin kitchen, lkci daya aka bude kofar parlon, still tayi a gun tana kallon kofar, Ramla, Khaleesat, da Ilham ne suka shigo a tare, juyawa yayi shi ma yana kallonsu sannan ya kalli agogo da mamaki, ko kadan bai lura da abinda ke hannunsu ba da mamaki yace "Lafiya?" A tare duk suka bude murfin ruwan gora me sanyi dake hannunsu suka tuttula masa gaba daya a jiki lkci daya suka ce "Happy birthday....." Bai gama recover ba duk suka fice da gudu suna dariya, me Samantha xata yi banda dariya, ya kalli system dinsa da aka yi masu wankan tare ya mike da gani kasan ransa ya gama baci ya shige bedroom, Samantha ta langwabar da kai ta karasa parlon ta dau system din ta kashe ta ajiye kan kujera a bude, snn ta dauke lallausan rug din da ya jike ta fita da shi waje ta shanya, ta koma kitchen ta dauko mop da bucket ta share ruwan da ya malala a parlon bbu bata lkci ta gama ta wanke mop din, ta dawo parlor tayi jim, can ta kalli agogo sai kuma ta nufi bedroom din, xaune ta gansa gefen gado ya rike kai, ta xaro ido tace "Baka cire kayan ba?" Bai tanka ta ba haka yasa ta karasa ta durkusa gabansa tace "Doctor...." Ganin bai dago ba tayi shiru tana kallonsa, a hankali ta dago kan nasa suka hada ido, kamar xata yi kuka tace "Toh ka cire kayan kar sanyi ya kama ka mana" unbutton din shirt din ya fara yi, ta mike tsaye ta taimaka masa ta cire, tana kallon singlet din jikinsa tace "Toh ka cire doctor" mikewa yayi ya bude closet ya fiddo wasu inners ya shiga bayi, ba a dau lkci ba ya fito, a hankali ta juya masa baya, ya fiddo pyjamas dinsa ya saka, ita dai tana tsaye tana fidgeting din fingers dinta, kamar ance ta juyo ta ga belt hannunsa ya nufi kofa, da sauri ta bi sa ta rikosa tace "No doctor daga suna maka wasa, they just wished you happy birthday, kalli fa hana idonsu bacci suka yi har sae da sha biyu yayi, kai baka san wasa ba?" Ya wani hade rai yace "Ina wasa da su ne xasu xuba min ruwan sanyi a jiki" bata fuska tayi tace "Toh meye don sun xuba ma ruwan sanyi, after all they wished you a happy birthday" karamin fridge din dake dakin ya nufa ta bisa da kallo ya bude ya ciro ruwa me sanyi ita dai kallonsa take taga ya nufota yana bude ruwan, wani k'ara tayi xata gudu ya cafkota, ta kwala wani k'aran jin ruwan sanyi, k'adan ya xuba mata ya ajiye, ta fashe da kuka ya wara mata ido yace "Happy birthday...." Kwace kanta tayi xata fita ya rungumota yana dariya yace "Ashe ba dadi" dage hijab dinta xai yi ta rike da sauri tace "Bana so...." Da karfi ya cire hijab din ya ga yar fingil rigar bacci ne jikinta, ya ja ta xuwa kan gado ya kwantar da ita ya rufa mata bargo murya can ciki yace "Go to sleep it's late" daga haka ya fita ya rufe kofar parlor ya dawo, a rufe ya ga idonta ya dau blanket ya xaga inda take ya durkusa cikin sanyin murya yace "Happy birthday wife!" K'in bude ido tayi duk da tana jinsa, xae mike yaji murya can kasa tace "Happy birthday also dear...." Murmushi yayi ya mike ya kashe wutan dakin ya fita parlor yayi kwanciyarsa.
*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫
23.....
Da asuba ya rakata har gate dinsu don tace karfe bakwai Mumy xata dawo, ya rungume hannayensa yana kallonta yace "dont forget karfe shidda plss love..." Ta kallesa tace "Nace maka ni ban san yanda xanyi ba fa, Mumy xata tambaye ni inda xan je, idan nace mata church nasan ita ma xata je idan bata ganni ba kuma sai in ce me" yayi shiru yana kallonta, can yace "Toh kice mata gidan kawar ki xa ki je mana" turo baki tayi tace "Allah yasa ta bar ni" daga haka ta d'aga masa hannu ta shiga gida. Har bayan la'asar Samantha tunanin me xata ce ma Mumy da xata bar ta ta fita take, can dai ta dau shawarar sa na cewa tace gidan kawarta xata je, ae ko biyar da kusan rabi ta shiga dakinta ta sameta ta xauna gefenta a hankali tace "Mumy xan je gidansu Victoria kinga ta daina xuwa nan don bana xuwa gidansu...." Tsit tayi tana mamakin kanta don ita dai tasan bata karya gashi yau Abuturrab yasa tayi, duk jikinta yayi sanyi ta fara wasa da fingers dinta, Mumy dake mata wani kallo don taga alamar karya take wanda hakan ya daure mata kai wai yau samantha ce ke kkrin hada karya, bata dai nuna ta gano ta ba tace "Tun safe kina gida baki ce xa ki ba sae da yamma tayi?" Shiru tayi bata ce komai ba, Mumy tace "Toh tafi kar ki dade amma" Samantha ta kasa cewa komai kuma ta kasa kallonta, can dai tace "Toh Mumy driver ya kai ni" Mumy ta xuba mata ido sai kuma tace "Toh kije kiyi masa magana" mikewa tayi ta fita ta koma dakinta, hawaye ya cika idonta ta rasa dalili, wayarsa dake gunta ta dauka ta kirasa, yayi mamakin ganin kiranta ya dauka yace "Wife!" Hade rai tayi tace "You made me lie to my mum, ni bana karya kasa nayi karya" sai kuma ta fashe da kuka, yace "Alryt, shknn yi xaman ki a gida kawai, it's nothing and i don't want you to lie because of me" daga haka ya katse wayar, jikinta yayi sanyi ta sake kiransa ya ki d'agawa, ta fashe da wani kukan ta xauna gefen gado, can kuma ta mike kamar mara laka ta shiga bathroom, wanka tayi ta fito ta shirya cikin abayarta tayi rolling, sosai tayi kyau duk da bata yi wani kwalliya ba, ta boye wayarta a jaka ta fito tana rike da jakar, Mumy dake shirin fita church tayi ma sallama ta fita driver ya ja ta xuwa inda tace wato gidansu Victoria, mintin ta sha biyar a gidansu Victoria ta sake kiran Abuturrab, wnn karan sai da ya kusa katsewa ya dauka, kasa cewa komai tayi amma kiris ya rage ta fashe masa da kuka, shi ma dai kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "ya aka yi samha?" Ta fashe da kukan da ke cin ta tace "Bayan kasa na fito gida shine ka ki daga kirana koh?" Da mamaki yace "kin fito da gaske? Kina ina" cikin rawar murya ta gaya masa, ya lumshe ido yace "Alryt, gani nan xuwa am sorry plss" daga haka ya katse wayar, shidda da 'yan mintuna ya iso anguwar, tun da ta fito gate yake kallonta har ta karaso ta bude gaban motar ta shigo, ya lumshe ido yace "Am sorry samha" bata ko kallesa ba ya tada motar suka bar gun, wani babban gun make up taga yayi parking, ta kallesa tace "Me xa mu yi a nan?" Ya fito daga motar ya zaga ya bude mata ta fito tace "Me xa mu yi a nan mana" Yace "Follow me ko kuma in kama hannun ki" daga haka yayi gaba ta bi bayansa kamar xata yi kuka, babba ne gun kwalliyan sosai, har kunshi ana yi da gyaran gashi, matar dake gun da alamar ita ce me gun tayi masu sannu da xuwa da fara'a ya nemi kujera ya xauna, Samantha ma ta xauna sai dai duk gabanta faduwa yake, Abuturrab yace "Madam light make up nake son ayi mata...." Samantha ta hade rai tace "Make up kuma!" Bai kalleta ba yace "Xan je in dauko kayanta yanxu...." Matar tace "Muna gyaran gashi da kunshi na amare, bari in kawo maka list ka ga bbu abinda bama yi a nan" Abuturrab yace "No ba sai an kawo ba, a gyara mata gashi kawai sai make up" daga haka ya mike yana ma Samantha wani kallo da manyan sexy eyes dinsa har ya fita, ji tayi kamar ta rusa kuka, nan matar da yaran gun suka taho don yi mata abinda yace. Sai bayan magrib ya dawo rike da leda ya mika ma matar yace "A dan yi sauri madam lkci ya wuce" babu yanda samantha ta iya haka ta bi matar. Gown ce me d'an karen kyau ja with long sleeves, mai ratsin silver daga saman wuyar kawai, dama gata fara gown din ya wani haska ta sai ka rantse amarya ce, gashi kamar an auna ta, ya fito mata da shapes dinta tun daga sama, tayi kyau iyakar kyau, ga gashinta da aka gyara mata bakikirin da shi ya xubo har kasan wuyarta, matar sai maa sha Allah take cewa tana kallonta, necklace ta sa mata da earrings suma silver sai bracelet da wristwatch, ta fiddo takalmi me ratsin ja da silver ta bata ta saka, matar da samantha ta gama tafiya da imaninta tace "Ya sunan ki 'yan mata?" Samantha ta sunkuyar da kai a karo na farko da taji wani iri tace mata sunanta Samantha, murya can kasa tace "Samha!" Matar tace "Ki gode ma Allah Samha kina da kyau, wanda ya xo da ke shine angon naki koh?" Samantha ta sunkuyar da kai kawai, matar tace "Allah sarki, Allah ya bada xaman lafiya da xuri'a dayyaba...." silver head tie mara nauyi matar ta daura mata, sannan ta fesheta da turare kala hudu da ya saka cikin kayan, matar takara mata da nata, snn ta kama hannunta suka fito, tun da suka fito Abuturrab ke kallon Samantha ko kiftawa babu, ita kam kasa dago kanta tayi, duk occupant din wajen kallonta suke ko wanne na fadin maa sha Allah, Har gabansa matar ta kai ta, sai a snn ya mike da kyar ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu talatin din dake ciki ba tare da yace komai ba ya mika mata, farin ciki ya lullube matar ganin tulin kudin, karfin halin kama hannunta yayi suka fita tana binsa duk jiki a sanyaye, suna shiga mota ya kamo hannunta cikin raunin murya yace "promise to be with me no matter the situation we re going to find our self samha..." Kasa cewa komai tayi hawaye ya cika idonta, harde hannayensu yyi cikin sanyin murya yace "Talk plss Samha," rungumesa tayi cikin rawan murya tace "I promise!" Kiss ya shiga yi mata a wuyarta, duk ta rikice tana turasa, da kyar ta samu ya saketa, ta hade kanta da gwiwa, jiki a mace ya tada motar ya ja suka bar wajen, sai da ya je gidan wani abokinsa don shiryawa shi ma, sai dai bai bari ta fito ba ya shiga gidan, ba a dau lkci ba ya fito sanye da suit dinsa na royal blue. Bata bari sun hada ido ba har ya ja motar. Wani lafiyayyen hall taga sun yi parking, tun daga waje kana iya ganin uban motocin dake Parke ga abokansa na hannun dama na jiran isowarsa, yana fitowa ya xaga ya bude mata ya kama hannunta ta fito, wani kallo suka dinga mata gaba dayansu shi dai yana rike da hannunta har ya iso gabansu, sai a snn suka ankare, kusan dukkansu suka sa hannu aljihu suka fiddo sabbin dari biyar biyar suka watsa masa shi da ita, lkci daya suka ce "Happy birthday Aliyu" dariyar yake yayi ya na rike da ita ya nufi hall din suka rufa masu baya. Sai ka rantse d'an sarki ko d'an shugaban kasa ke birthday tsabar cika da haduwar wajen don Aliyu akwai son life, manyan 'yan mata da samari masu ji da kai ne kuma a gun, Gaba daya kallo ya koma kan Samantha, wanda hakan yasa Abuturrab ya ji wani kishi ya rufesa, komai da aka yi design a gun red and silver ne, manyan cake har uku ne a gun, nan aka fara shagalulluka, ita dai Samantha taki sakin jiki, shi ma kuma bai takurata ba, Saudat na daya daga matan da suke gun, sai dai tun da ta kyallara ido taga Samantha hankalinta ya tashi barin da taji wai birthday mate dinsa ce kuma da dukkan alama budurwarsa ce, bbu wanda ya dauko Samantha Christian ce, Abutuurab dai na ta kallon agogo don bai son su wuce tara gun, ko da xa su wuce hakan ma yafi son ya maida Samantha gida, tunda Samantha ta xauna bata tashi ba sai da aka fara hotuna shi ma kuma tilasta ta yayi, ae ko kowa so yake suyi hoto tare, har dai aka gama sai yanka cake, Yayi ma abokinsa magana cewar ya ba ma Dj umarnin kashe wakar da ke tashi coz he wants silent, cikin kankanin lokaci gun yayi tsit, wanda hakan yasa kallo ya dawo kan Abuturrab dake facing din Samantha, kasa kallon cikin idonsa tayi, da mamakinta da kowa na gun sai gani suka yi ya durkusa a hankali on his kneel ya sa hannu a aljihu ya ciro wani box me bala'in kyau ya bude, sai ga kyallin diamond, abokansa na ganin haka suka dauko Mp xuwa inda suke ko wannensu na cewa waowww, Abuturrab ya ciro ring din ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Will you marry me plss?" Tafi hade da ihu ya kauraye ko ina, tuni aka fara video da waya, bbu wanda abun bai burge ba a wajen sai saudat da taji kamar xuciyarta xai fashe, samantha kam hawaye ne ya cika idonta, ta kasa ce masa komai ga ido da ya tsare ta da, da kyar ta gyada kai hawayen idonta ya xubo, cikin sanyin murya tace "Yyess i will!" Dai dai lkcn da ya gama xura mata xoben ya mike ya rungume abarsa, aka dinga tafi da shewa ana daukarsu photo, juyawa saudat tayi ta fice daga hall din da gudu, gift ba na wasa ba Samantha ta samu a gun don har ta fi uban gayyar samun kyauta, karfe tara kuwa ya fita da ita daga gun, duk taki yarda su hada ido, sai da ya kai ta part dinsa ta canza kaya snn ya rakata har kofar gidansu, bata yi wata wata ba ta shige ta bar sa a tsaye, yayi murmushi ya juya ya bar wajen. Xaune taga Mumy a parlor fuskar nan nata bbu alamar rahama, jikinta yayi sanyi ta karasa ta gaisheta kanta a kasa, cikin kakkausar murya Mumy tace "Daga ina kike Rebecca?" Gabanta yayi mugun faduwa tana kallon uwartata a hankali tace "Birthday Mum" Mumy ta mike tace "Birthday din wa" sunkuyar da kai tayi xuciyarta na bugawa tace "A frnd" fincikota Mumy tayi tace "ki gaya min meye hadin ki da likitan dake xuwa gidan nan?" Sosai samantha ta tsorota kafin tace komai uwar ta sauke mata mari cikin tsawa tace "Baxa ki bani amsa ba??? Uban meye tsakanin ku, a ina kika san shi? Har ya sauke ki a mota" Samantha ta fashe da kuka jikinta na rawa tace "Mumy kiyi hakuri don Allah, he's a frnd!"
*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫
24.....
Baki uwar ta bude da mamaki tace "Rebecca yaushe kika fara karya?" Durkusawa samantha tayi cikin kuka tace "Plss Mumy kiyi hakuri am not lying frnd dina ne" Mumy tace "A ina kika san shi?" Rasa abinda zata ce tayi hawaye na sakko mata tace "Kiyi hakuri Mumy" hankada ta tayi cikin tsananin fushi tace "Baxa ki bude baki ki min magana ba?" Jikinta na rawa tace "Watarana ne naje birthday din Suzan shine muka hadu, he helped me" tafe hannu uwar ta shiga yi cikin tashin hankali tace "Nashiga uku, Samantha dama abinda kike yi knn yanzu ban sani ba, when did you change, meye hadin ki da musulmi daga fara bin sa har ya koya maki karya," a fusace uwar ta kuma kai mata mari ta fixgota tace "Maza wuce ki hada kayan ki yanxun nan, dole ki bar gidan nan gobe gobe, baxan bari ki ja mana abun kunya ba, tunda har ya koya maki karya ban san nan gaba me xae faru ba kuma" daga haka ta ja ta xuwa daki, tana tsaye tasa ta gama hada kaya ta tabbata bbu wani abu da tasa a jakar banda kayanta don har wayarta da bata fiye amfani da ba ta karbe, wayar Abuturrab ne dae bata san da shi ba, bedroom dinta ta kai ta ta kulle ta sauko kasa tana huci tana tunanin ghana kawai xata turata gobe tunda tana da visa, Samantha ta hade kai da gwiwa ta dinga kuka, duk ta rasa me ke mata dadi, kallon fingers dinta tayi da sauri taga ring din da Abuturrab ya sa mata na nan, cirewa tayi ta wurgar ta kuma fashewa da kuka, tayi mai isarta ta kwanta nan kasa ta lumshe ido, har ta fara bacci kamar warce aka tsikara ta mike da sauri, kalle kallen dakin ta fara yi tana neman xoben, can ta mike ta nufi ta inda ta wurgar bata gani ba, jikinta yayi sanyi wasu sabbin hawayen suka xubo mata, a hankali ta dinga bin ko ina na dakin tana dubawa, har bayan minti talatin bata gani ba, hankalinta ya tashi ta fara dage komai tana dubawa, kan kace me duk ta juya dakin upside down, da kyar ta ga xoben a wani lungu, ta karasa da sauri ta dauka, dai dai nan aka bude kofar dakin, Mumy, da aunties dinta har uku suka shigo dakin, daya kanwar mahaifinta ce, biyu kuma kannin Mumy ne, Mumy da ta hango xoben dake kyalli hannunta ta karaso da sauri tace "Meye wannan hannunki?" Kasa cewa komai samantha tayi tana kallonsu xuciyarta na bugawa, Mumy ta kare ma dakinta kallo tace "Ubanki kike nema kika rikita min daki, xoben meye wnn kamar na diamond a hannunki" sauke idonta kasa tayi hawaye ya silalo idonta, daya daga aunties din nata a fusace tace "Amma Rebecca ba kurma bace ba dai koh!" Ta fashe da kuka cikin rawar murya tace "Mumy shi ya bani" dafe kirji Mumy tayi cikin tashin hankali tace "Amma na shiga uku ni Rachael, na meye?" Ta sulale nan kasa ta kuma fashewa da kuka sosai tace "He said he wants to marry me" wani jiri Mumy ta dinga ji har sai da Anty Vivian ta riketa, Mumy ta fashe da kuka sosai tace "Ae ni nasan na shiga uku, amma Allah ya tsine ma mutumin nn yar tawa xae yi engaging? Wayyo Allahna kila ma asirce min ita yayi, shi yasa jinina bae taba haduwa da musulmai ba, mugaye ne, matsafa ya ma 'ya ta tsafi, ku kira min David yaji abinda yar sa ta koma, tuni Rebecca ta daina xuwa church na lura, ko taje kuwa bata dadewa take dawowa, Rosary da na bata ta saka sai ta cire, ta bar karanta Bible, ta yaye catechism da dadewa, addu'ar safe yanxu bai dameta ba, kai bata ma yi, Samantha da ko kasheta xaka yi baxata maka karya ba ita ce yanxu da masters a karya, snn ace bae asirce min 'ya ba... Babban abinda ya kuma tada min hankali nayi ta leke ina jiran in ga ta inda xata billo shine yau fa birthday dinta amma yar nn daga ni har babanta bbu wanda tace ma komae abinda bai taba faruwa ba tsawon rayuwarmu tare, ashe birthday d'an iskan ya hada mata" Tana kai wa nan ta kuma fashewa da kuka sosai ta daura hannu a ka, Wani wawan mari kanwar Abba ta dauketa da shi cikin tsananin fushi tace "Waye shi? A ina kika sansa, d'an wani anguwa ne? Me garesa da har ya burge ki kike kulasa?" Kasa cewa komai Samantha tayi sbda wani jiri da ta dinga gani tsabar shigarta da marin yayi, Anty vivian ta rike Sarah kanwar Abba ganin wani marin xata kuma kai mata tace "Haba sis sarah mu bi ta a hankali mana..." Sarah tace "Xaman ta ya kare a Nigeria, gobe gobe xata wuce Ghana, har mu xata dauko ma abun kunya, me xa ayi da musulmi? Yesu yayi mana tsari...." Samantha bata san lkcn da cikin kuka tace "Toh su musulman ba mutane bane? Ina ce Grandfather na har ya mutu musulmi ne shi, kuma dama ba Jehovah ne ya halicce mu gaba daya tare da su ba, kowa da nasabarsa gun Allah.... Kuma a Bible ae dama ance addini xai kasu....." Mumy bata jira jin karashen ba tayi kukan kura sai a kanta, tana duka Sarah na duka, ita kanta Vivian wnn karan wani wawan hauri ta kai mata tana cewa "Rebecca mu kike gaya ma haka???" Da kyar Anty Mary Ann ta ja samantha suka bar dakin, ta shiga da ita wani dakin ta rufe da makulli, Samantha ta sulale kasa ta hade kanta da tiles din dakin, Anty Mary da damuwa tace "Rebecca waye wnn mutumin, meye hadin ki da shi?" Kasa cewa komai Samantha tayi idonta a rufe, xama Anty Mary tayi gefen gado tayi tagumi, tana jin su Mumy na bubbuga kofa kamar xasu cire suna kunduma xagi, daga karshe suka gaji suka bar wajen, Samantha ta mike da kyar ta hau gado ta rufe ido, Mary da ta bi ta da ido ta girgixa kai cike da damuwa, har karfe sha daya samantha bata bude ido ba sai dai ba bacci take ba, mikewa Mary tayi ta shiga bayi, samantha ta juya a hankali taga ta rufe kofar, mikewa tayi ta sauka daga kan gadon da sauri ta bude kofa a hankali kamar kiftawan ido sai ga ta downstairs, Blessing na xaune parlon tana ganinta ta mike da damuwa tace "Sister Rebecca ina xa ki kuma, you re in trouble plss kar ki fita" Hawaye cike idonta tace "Plss don't say anything, kawai kice baki gan ni ba" daga haka ta fice da gudu jin budewar kofa a sama, Blessing ma ta shige kitchen da gudu, ko takalmi bbu kafarta ta fice gidan gaba daya, ae ko Mary na jin budewar kofa ta fito da sauri, ganin dakin wayam ta fice waje dai dai lkcn da Mumy ma ta fito da su Sarah, Mary ta fara kalle kalle hankali tashe, Mumy na ganin haka ta daura hannu a ka ta fara sauka stairs tana cewa "Ae ni shknn na shiga uku na lalace, gudu tayi...." Duk suka bi ta hankali tashe, Mumy ta dinga kwala ma Blessing kira ta fito da sauri, A tsawace tace "Ina Rebecca?" Girgixa kai tayi a tsorace tace "Madam ni a kitchen nake ai...." Kamar Mahaukaciya Mumy ta fita parlon ta dinga kwala ma inusa mai gadi kira ya fito cikin tashin hankali tace "Inusa Samantha ta fita ne?" Inusa yace "Ehh yanxun nan ta fita..." Da gudu su Anty sarah suka fice don bin bayanta, a tsawace Mumy tace "Me yasa ka bar ta ta fita?" Mai gadi yace "Madam ae ba yau ta saba fita ba, in dai xaki kwana church yawanci bata kwana a gidan nan sae asuba take dawowa, nayi xaton yau ma kinje kwana a church ne...." Wani kara Mumy tayi ta daura hannu a ka tace "Yesu!! Ae ni nace dama na shiga uku, Rebecca bata kwanan gida, ina take kwana" kuka sosai ta fashe da, daga haka ta bi bayansu Sarah ita ma da gudu, yau kam samantha bata ji tsoron karnukan dake haushi ba, neman tsoron ma tayi ta rasa, gudu kawai take don tasan da wuya idan ba a san ta fita ba yanxu, tunanin hakan yasa jikinta ya dau rawa a xuciyarta kuwa addu'a take Allah sa Abuturrab bai rufe gate ba, don tasan idan ta tsaya bubbugawa xa a iya risketa kuma tata ta sameta knn gun su Mumy.....
*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫
24/25
Tana isa gate din ta turasa taji a rufe, kasa bubbugawa tayi sai haki take, hasken torchlight ta dinga hangowa daga nesa, ae bata san lkcn da ta fara buga gate din ba, Abuturrab dake xaune ya rike kai a parlor don ya rasa me ke damunsa tun bayan dawowarsa gida ya mike da sauri kamar dama jiran buga gate din yake ya fito ya karasa ya bude, yana ganinta kuwa ya jawota ya rufe gate din gam, sulalewa kasa tayi, ya bita da sauri hankali tashe yace "What Happened Samha?" Mikewa tayi da sauri ta shige parlor ya juya ya bi bayanta, xaune tayi parlon ta hade kai da gwiwa ta dinga rusa kuka, wani mugun tashi hankalinsa yayi, ya dagota yace "Don Allah ki min magana...." Bai rufe baki ba yaji ana bubbuga kofa kamar xa a cire, mikewa yayi da sauri ta rikosa cikin rawan murya tace "Plss kar kaje, Mumy ce..." Kallon mamaki ya dinga mata, lkci daya jikinsa yayi sanyi, su kuwa basu fasa buga gate din ba, ga haushin da karensa ke yi duk ya cika gidan, to bai son a ji a cikin gida, ya durkusa cikin kwantar da hankali yace "Look Samha, bari in je, nasan me xan yi, tashi ki shiga daki" cikin kuka tace "Don Allah kar kaje plsss" rike hannunta yayi yace "Noo, yanxu xa ki ga soldiers din cikin gidan nn sun yo nan, i don't want that, nace maki nasan abinda xan yi" kasa cewa komai tayi sae dai duk jikinta rawa yake, ya mike da sauri ya fita, ae ko sae ga soldiers har uku suna tahowa, ya d'an kallesu yace "No, it's nothing, kila emergency ne, kuyi wucewar ku kawai..." Juyawa suka yi gaba daya sae da suka sha corner, snn ya isa cage din karensa ya bude, karen ya fito kamar jira yake ya nufi gate din, Abuturrab ya bi bayansa, lkci daya ya bude gate din amma ya tare yanda karen baxae iya fita ba, yamutse fuska ya dinga yi kamar mai bacci yace "Any problem??" Bai gama rufe baki ba Mumy ta cakumosa tana haki tace "Ka fito kin da 'ya ta kar in cinna ma gidan nn wuta yanxun nn, fito min da 'ya ta nace!!" Wani kallo ya dinga yi mata yace "Ban gane ba" wani ihu tayi tace "Baka gane ba koh, to wllh yau sae na tara maka jama'a bring out my daughter oo" A fusace Sarah ta bankesa xata shiga gidan, ya hankada ta waje, daga haka ya matsa karensa ya fito ya dinga wani irin haushi yana tsalle duk suka koma baya da gudu sai dai fa hakan bae sa Mumy ta rufe baki ba, duk ta xama kamar wata xautatcciya, can ta fashe da matsanancin kuka tace "Yesu what have i done to deserve this, why my daughter, why rebecca..." Vivian ta dinga jan ta tana cewa "Sister Rachael mu je kawai gobe sae mu je station kinga karen nn sae ya iya cizan mu" da kyar suka ja ta tana kuka sosai ganin kare fa ya dage xae yi cixo don ma Abuturrab na kiransa, suna barin wajen karen ya dawo Abuturrab ya jawosa ciki snn ya rufe gate, ya shiga parlor ya sa key, duk jikinsa yayi sanyi ya karasa bedroom, xaune ya ganta a kasa ta hade kai da gwiwa tana rusa kuka, durkusawa yayi gabanta cikin sanyin murya yace "Am sorry samha, forgive me plss, i know i caused everything" k'in dago kanta tayi, yayi shiru ya ma rasa abinda xai ce, can ya mike duk jikinsa a mace ya shiga bathroom, ruwan dumi ya hada mata ya fito da towel ya durkusa gabanta yace "Plss ki tashi kiyi wanka sai ki kwanta, you will feel much more better" ganin ba kulasa xata yi ba ya dagota ta fashe da wani kuka mai ban tausayi, bai san lkcn da ya rungumeta ba yace "Noo plss samha, you re making me feel guilt inside me..." A hankali ta dinga kukan ya dagota ya cire mata dankwalin abayar kanta, snn ya daga Abayar ta sauke da sauri, murya can kasa yace "Toh tafi bayi ki cire..." Kamar iska xai hurata ta mike sae kuma ta bude tafin hannunta har lkcn xoben na nan, bata bari sun hada ido ba ta saka a finger dinta ta nufi bathroom din a sanyaye, bayan minti kusan ashirin ta fito daure da towel, gaba daya ta mance da ganinta kasan she's not her self, suna hada ido ta kalli towel din ta juya da sauri, bin ta yayi yace "Noo, kar ki maida kayan ki, i wil give you another..." Rigar Pyjama dinsa ya dauka ya kai mata snn ya fito, goge jikinta tayi ta saka rigar da ya sauko mata har kasan cinya snn ta fito, taga baya dakin, gashinta ta daura ta kwanta hade da lumshe ido. Rike da cup din tea ya shigo dakin, har ya karaso inda take bata bude ido ba, ya ajiye cup din murya can kasa yace "Samha!" A hankali ta bude rinannun idanuwanta ta kallesa, ya sakar mata lallausan murmushin kwantar da hankali yace "Tashi ki sha tea, it will help" shiru tayi bata ce komai ba kuma bata tashi ba, ya kamo hannunta yace "Kinji?" Mikewa xaune tayi ba tare da ta kallesa ba, ya dau tea din ya mika mata ta karba ta kai baki, da yake shayin bbu wani xafi rabin cup ta sha ta mika masa, yace "No, daure ki shanye don Allah" girgixa kai tayi cikin sarkewar murya tace "Na koshi" karba yayi ya ajiye, ya mike ya nufi gaban mirror ya dauko paracetamol biyu ya dau ruwan goran da ya rage ya dawo ya mika mata, ba musu ta karba ta bude ruwan ta sha maganin ya karbi ruwan ta koma ta kwanta ta lumshe, lullubeta yayi da duvet don Ac'n dakin a kunne yake, ya kusa awa daya xaune kafin ya mike ganin sha biyu ya wuce ya dau pray mata da blanket ya fita parlor. Washegari yana dawowa daga masallaci ya hadu da Mami dake kkrin shiga parlonsa, sosai gabansa ya fadi, ta tsaya ganinsa tace "Sai yanxu ka dawo daga masallacin?" Ya risina yace "Ina kwana Mami" tace "Lafiya lau, su wa ke buga gate jiya Aliyu?" Rasa abinda xai ce mata yayi, duk hankalinsa ya tashi har ta so gano hakan, ganin irin kallon da take masa ya dake yayi ta maza yace "Kiyi hakuri Mami, a nan anguwar suke, emergency ne daya daga yaran gidan basu da lafiya!" Tabe baki tayi cikin nuna rashin gamsuwa tace "Ae tun ba yau ba dama ka iya karya" shiru yayi bai ce komai ba tace "Naga alamar your staying here is doing you more harm than before, bari dae Abban ka ya dawo...." Daga haka ta juya ta bar wajen, ya bi ta da kallo a sanyaye, cikin rashin kuzari ya shiga parlor, ya karasa bedroom ya ganta durkushe jikin gado ta hade fuskarta da gadon, karasawa yayi kusa da gadon da sauri yace "me ya faru samha?" D'ago kai tayi tana kallonsa da idonta da suka tashi da gani kasan ta ci kuka kenan da daddare, ya durkusa kusa da ita da damuwa yace "Samha!" Sauke idonta tayi kasa tace "Addu'a nake" sae a snn hankalinsa ya d'an kwanta yace "Ohk, tashi kije kiyi wanka, but you have to hurry up before daybreak, xamu fita kafin su mum dinki su dawo...." Tana jin haka kuwa ta mike ta nufi bathroom, duk tausayinta ya cikasa, yanxu duk shi fa ya ja mata everything she's going through, kuma ko k'adan bata nuna tana jin haushinsa ba, cikin kankanin lkci tayi wanka ta wanke baki da mouth wash ta fito, taga bbu shi a dakin, ta rakube gefe daya don tasan gaskiyarsa su Mumy na iya xuwa yanxu, shi kam main house ya nufa yaji alamar Mami na kitchen da mai aiki, ya haura sama da sauri ya shige dakinsu Ilham duk sun koma bacci, a hankali ya bude press dinsu yana kare ma kayayyakinsu kallo, ganin kamar samantha ta fi son Abaya ya dau wani well ironed Abaya baki da veil dinsa ya rufe gun, rasa yanda xai fita da kayan yayi kar yaje ya ci karo da Mami, bathroom ya shiga ya dauko towel dinsu ya nannade kayan a ciki ya bude window a hankali ya jefar da kayan kasa, yana juyowa yayi ido hudu da Ramla da k'aran bude window yasa ta farkawa tunda basu dade da komawa ba bayan sun yi sllh, mikewa xaune tayi tana kallonsa ya hade rai yace "Ku baku da aiki sai na bacci ne a gidan nan? Oya duk ku tashi ku fita daga dakin nn, breakfast din ma sae Mami taje tana muku?" Yanda ya buda murya yasa duk sauran suka farka, yasan Ramla na iya leka window idan ya fita don haka sai da ya tabbatar duk sun fita suna turo baki snn shi ma ya fita, da sauri ya xaga ya dau kayan ya koma part dinsa, har lkcn tana xaune ya sameta, ya sakar mata murmushi ya ajiye mata kayan ya nuna mata gaban mirror yace "Ga lotion, body spray, perfumes, ki shirya kafin in fito" daga haka ya shiga bathroom don yin wankan shi ma, ko kafin ya fito har ta gama shiryawa tana xaune tayi jigum, mikewa tayi ganinsa da towel ta fice daga dakin, bai wani dau lkci ba ya fito sanye da kananun kaya hannunsa rike da makullin mota yana kallonta yace "Tashi mu je, idan mun fita sai kiyi breakfast" bata ce komai ba ta bi bayansa, ya nufi gun da motarsa ya ke ya bude mata snn ya xaga ya bude ya shiga driver seat, ya fara warming din motar, kamar wanda ya tuno abu yace mata yana xuwa ya koma cikin gidan, kayan ta na jiya ya dauka har da dankwalin ya saka a leda snn ya fito, ya bude bayan mota ya ajiye ya rufe motar, gate ya bude ya dawo ya fitar da motar, ya kuma fitowa ya kulle gate din snn ya shiga motar ya ja suka bar layin, sai da suka hau kan main road snn ya kamo hannunta yace "Samha!" Bata iya ta amsa ba hakan yasa ya kuma kiranta, ta juyo ta kallesa, yace "Gaya min me ya faru jiya" ganin ta ki cewa yasa bae takurata ba, har sai da suka yi nisa sannan yaji cikin sanyin murya tace "I told Mumy everything" kallonta yayi da sauri yace "Me kika ce mata" tsaf ta gaya masa yanda aka yi jiya bata boye masa komai ba, duk jikinsa yayi sanyi ba kadan ba ya kasa ce mata komai, kuka take a raunane wanda yake jin hakan har cikin xuciyarsa, kasa daurewa yayi, yayi parking ya kamo hannunta biyu cikin sanyin murya yace "forgive me samha, ni na janyo komai, kuma duk hakan ya faru ne ta dalilin son da nake maki, no matter what kar ki guje ni Samha, ban taba yi ma wata diya mace irin son da nake maki ba, baya ga mahaifiyata bbu wata a xuciya ta sai ke, ina son ki son da baxan iya kwatanta maki ba, ki yarda da ni, na maki alkawarin har abada baxan barki ba komin wuya da tsanani.... Kuma kin san alkawari kaya ne, i am not using a sugar quintet mouth on you, i mean all what am saying, it's coming from the bottom of my heart" hawaye kawae take, wanda hakan yasa yaji kamar shi ma yayi kukan, ya hade hannayensu yace "But kema ki min alkawarin baxa ki bar ni ba" bata iya ta bude baki ba banda kai da take gyada masa kawai, sun kusa minti goma a haka kafin yayi karfin halin ci gaba da driving din. Karfe bakwai da kusan rabi mota guda na 'yan sanda suka yi parking kofar gidansu Abuturrab, kusan 'yan sanda shidda suka diro, bude kofar wata bakar mota da yayi ma motar 'yan sandar jagora aka yi, Mumy da su Anty Sarah suka fito da wasu maza har uku, da ganin idanuwan Mumy kasan ba tayi bacci ba daren jiya, bubbuga gate yan sandan suka dinga yi da karfi, kwata kwata Mumy bata san main gate din na ta daya bangaren ba, irin bugun da yan sandan ke yi ya ja hankalin masu gadi a can gate din, suka karaso su biyu duk da kayan sojoji jikinsu, suka bude gate din, kallon kallo suka shiga yi tsakaninsu, wani d'an sanda cikinsu ya fiddo id card dinsa yana nuna masu yace "Inspector Gbenga..." Tun kan sojojin su ce komai sae ga Mami da Ramla, duk suka bata hanya ta dinga bin 'yan sandan da su Mumy da kallo, duk da yanda gabanta ya fadi hakan bai hanata dakewa ba murmushi dauke fuskarta tace "Sannun ku da safiya, Allah dai yasa lafiya!" Mumy ta tabe baki tana girgixa kafa tace "Ae babu lafiya har sai dan ku ya fito min da 'ya ta yanxun nan wllh" da mugun mamaki Mami ke kallonta, inspector Gbenga yace "Muna son Hajiya a bamu dama xa mu shiga gidan nn yanxu...." Mami xuciyarta ke ta bugawa ta matsa da sauri tace "ohh bismillanku" daya daga sojan dake tsaye yace "Kiyi hakuri Hajiya sae mun kira Col mun sanar da shi..." Yan sandan suka ce "Sorry plss amma mu ma a bakin aikin mu muke ae" Sojan yace "Ehh gaskiya knn wnn, amma sai mun kira mai gidan" a hasale Mami tace "Toh me xae yi idan kun kirasa xae hanasu yin aikinsu ne?" Wani inspector yace "Alryt kirasa ku sanar da shi...." Cikin kankanin lkci sojojin suka kira mahaifin Abuturrab dake Port Harcourt a lkcn suka sanar da shi komai, mikewa tsaye yyi daga xaunen da yake yayi shirun kusan second talatin a xuciyarsa kuwa ya nanata Aliyu ya kai sau biyar, can ya gyada kai yace "Alryt su shiga..." Daga haka ya katse wayar yan sandan suka shiga gidan tare da su Mumy, iya bincike duk anyi a gaba daya gidan bbu samantha bbu alamar ta kuma, Mumy sae kuka take tana cewa "Yesu why me, ya gudu min da 'ya na shiga uku, wllh duk inda yake ku nemo sa ya fito min da ita, xan dauresa har sae inda karfi na ya kare, xae san da ni yake..." Mami dai na tsaye gefe duk jiki a mace, lkci daya hawaye ya cika idonta, Ramla da su ilham ma banda kuka bbu abinda suke. Dago kai Abuturrab yayi da sauri jin an dafa kafadarsa yaga Hajiya Mariya ce, da mamaki tace "Tunanin meye haka Aliyu, ga ni ga ka na kira ka ya fi sau uku amma shiru!" Ajiyar xuciya ya sauke ya lumshe ido yace "Mumy jikina na bani there is something happening at home, my heart is throbbing..." Cikin kwantar da murya Hajiya Mariya tace "Kayi addu'a Allah ya kawo komai da sauki ka ji son..." Kai kawai ya gyada mata, tun shigowarsu gidan ya kasa cin komai, samantha kuwa tilasta ta Hajiya Mariya tayi ta yi breakfast daga nan kuma ta kai ta bedroom dinta tasa ta kwanta, tana kwanciya kuwa bacci ya dauketa.
*Haske Writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫
26.....
Karfe goma da kusan rabi Abuturrab na kofar gida zaune yana danna wayarsa kiran Abba ya shigo wayar, sosai gabansa ya fadi da kamar baxae dauka ba sae kuma ya daga ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Abba yace "Kana ji na, ka taho gida yanxun nan am waiting for you, i mean immediately!" kasa cewa komai yayi jikinsa yayi sanyi sosai, yayi karfin halin mikewa ya shiga gida, xaune ya samu Hajiya Mariya parlor hannunta rike da Hisnul muslim, ya isa gabanta ya durkusa yace "Mumy wai kin ji Abba in xo, ni nasan all is not well tunda har hankalina yaki kwanciya" ita kanta sae da taji hankalinta ya tashi, ya girgixa kai ya daura kansa a kafarta cikin sanyin murya yace "Mumy ni baxan iya rabuwa da ita, ban san irin son da nake mata ba..." Dago kansa tayi taga hawaye idonsa, wanda hakan ya bata mamaki sosai anya ma ita ta taba ganin hawayensa, ta girgixa masa kai tace "Be a man Aliyu, ko kaje yanxu just show you know nothing about her whereabout, ni kuma in'sha Allah i will take care of her a nan, baxan bari taje ko ina ba, tashi kaje tunda yace yana jiran ka" mikewa Abuturrab yayi jiki ba kwari ya fita, har ya isa gida gabansa bae daina faduwa ba, kallon motar yan sandan dake bakin gate har lkcn ya dinga yi, can ya dake ya fito ya rufe motarsa ya shiga gidan, ko kallon yan sandan dake tsaye tsakar gidan bai yi ba ya nufi inda ya hango Abbansa dake tsaye sanye da uniform da gani kasan saukansa knn, Mami na tsaye daga gefensa Ga Mumy da tawagarta da alama shi dae ake jira, yana isa kuwa Abba ya sauke masa lafiyayyen mari ya sunkuyar da kai ya kasa dagowa, cikin tsananin fushi Abba yace "Ina ka kai yar mutane?" Da sauri ya dago yace "Yar mutane kuma Abba" komawa baya yayi ganin Abba xae kuma marinsa, ya xaro ido yace "Bbu wata yarinya dake gu na Abba, gun aiki na fita, i know nothing about any girl...." Cakumosa Mumy tayi cikin tsananin fushi tace "Karya kake munafuki algungumi, gashi har ka koya ma 'ya ta karya, na rantse maku yasan inda take, don haka ya fito mun da ita idan ba haka ba a tada Nigeria, bbu ruwana da waye ubanka, ku fito min da yarinya ta....." Cikin kuka sosai ta kare maganar ta sake sa ta daura hannu a ka tace "Na shiga uku na lalace" Abba ya dinga yi ma Abuturrab wani kallo, Mami kam banda hawaye bbu abinda take, kasa kallon inda Mr David ke tsaye rungume da hannunsa Abuturrab yayi, cikin sanyin murya yace "Abba sharri ake son min, i know nothing about all this, toh ina xan kai yar mutane, xa a iya shiga ciki a duba ko tana nan..." Turasa Mumy tayi tana huci tace "Yesu! Kai baka jin kunyan karya ne, ina ce jiya birthday ka ja ta ku ka je, ina ce jiya ka bata zobe wae zaka aureta, ka mance hanyar jirgi daban ta mota daban, meye ya hada warce ta fito from a very good Christian home da musulmi, bbu hadin ku don haka ka fito min da 'ya ta idan ba haka ba in kashe ka har lahira!" Wani kallo Abuturrab yyi mata yace "Ni xa ki kashe kuma?" Girgiza kai yayi yana kallon 'yan sandan dake tsatstsaye yace "Ko da maganar nan xae kai mu kotu ku xaku xame min shaida kashe ni tace xata yi." Abba ya kalli sojoji uku dake tsaye gun yace "Ku saka min shi a guard room, ko ba shi ya dauketa ba sai ya fadi inda take, idan kuma yaki ba sae ta kashe sa ba ni xan harbe sa...." Ta gefen ido Abuturrab ya kalle sojojin kawai ya tafi kai kansa Guard room din kafin ma su nufo sa, Cikin tsawa Abba yace "Ku bi sa ku sa shi nace" Daga haka ya nufi yan sandan dake gun, Mumy ta watsa ma Mami wani kallo tana hawaye tace "Amma kin haifa ma kanki jaraba, don wnn d'an naki annoba ne a gari...." Vivian ta ja hannunta suka yi waje tana rusa kuka. Har bayan azahar Abuturrab na guardroom daga shi sae singlet da dogon wando, bai wani damu ba don sbda shi ma aka yi guard room din a gidan, don haka inda sabo yaci ace ya saba, ko d'an shekara 15 aka saka a gun sae yaji jiki tsabar k'ankantar gun ga uban zafi, ko kwakkwaran motsi bae iya yi, a takure yake waje daya kansa ma baya iya dagawa straight sae a duke, tun bai kai sha biyar ba Abba ke jefasa nn idan yayi laifi kuma sae yafi awa biyar a haka, rabonsa da guard room tun yana 27 yrs wato 3yrs back da ya dauko wani maganan, karfe uku yaji an bude kofa daga waje, ko ba a gaya masa ba yasan Mami ce don ita kadae ke xuwa idan aka kullesa, ae ko ita ce, ta durkusa ta bude karamin kofar da yake ciki da aka sa ma uban kwado, da ganinta kasan ta ci kuka, kamar jira yake tana budesa ya fito duk ya jike jagab da gumi, kasa kallon idonta yayi, ya dafa gwiwansa kansa a sunkuye don gaba daya jikinsa yayi tsami, ga wuyarsa da ya rike, muryarta yaji tace "Aliyu ina 'yar mutane" bai d'ago ba kuma bai ce komai ba, can dai ya dago da kyar jin tayi shiru, tausayinta yaji sosai shi dai yasan tun da kwakwalwarsa ta fara aiki irin na mutane rabon Mami da samun kwanciyar hankali, ko da yaushe cikin dauko magana yake ba babba ba ba karami ba kuma a kanta komai ke karewa don Abba cewa yake ita ta 6ata shi, kwanan nan ne ma abun ya lafa bayan ya fara aiki don ko lkcn yana sch hankalin iyayensa ba a kwance yake ba, kamar xae yi kuka yace "Mami ni fa ban san komai kan maganar nan ba sae xalina ake ci kawai!" Hawaye ya gani idonta ya xube nan kasa yace "Noo Mami don Allah kiyi hakuri...." Dakewa tayi tace "Ina yar mutane take Ali?" Shiru yayi kafin ya dago a hankali ya goge xufar dake fuskarsa yace "Mami...." Sai kuma yayi shiru, sauke idonsa kasa yayi yace "Tana nan!" Mami ta durkusa gabansa ta dago kansa tace "A ina?" Kallonta yayi murya can kasa yace "Mami.... Mami ita nake so and i want to convert her...." Komawa baya Mami tayi da mugun mamaki tana kallonsa kamar idanuwanta xa su fito, cikin rawar murya tace "Aliyuu!" Marairaice mata yayi yace "Mami ni idan ban aureta ba Allah xan iya mutuwa wllh, i will be nothing without her" hawaye ne ya cika idonsa, wanda rabon ta da ganin hakan tun yana d'an shekara goma, ko me xaka yi masa baxa ka taba ganin hawayensa ba sai dai idonsa yayi jajir kirjinsa yayi ta sama da kasa tsabar dacin rai da rashin ji irin nasa, ya daura kansa a jikinta muryarsa na rawa yace "First love support me plss, i love her, ni baxan iya rabuwa da ita ba, kuma Mami idan na musuluntar da ita lada xan samu fah..." Hawaye kawae Mami take duk jikinta yayi sanyi, ita kam tana ganin jarabawa tun da ta haifi Aliyu, ta saita kanta cikin sanyin murya tace "Toh tana ina?" Da kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "Tana gidan Mumy!" Da mugun mamaki tace "Mariya?" Yayi shiru bai ce komai ba, ta sauke ajiyar xuciya a hankali, jin tayi shiru ya dago da sauri yace "Mami plss kar fa ki ce ma kowa haka, don Allah kar ki fadi Mami...." A rude ya kare maganar, cikin kwantar da murya tace "Ka gwammace kayi ta shan wahala knn, to ai shknn, shiru xan yi da baki na idan ma ya kashe ka kai ka ja ma kanka, tashi ka shiga ciki kafin a ganmu dama cewa yake ni ke supporting din ka" kallon d'an kurkukun yayi kafin ya marairaice yace "Mami k'ishi nake ji sosai wllh" mikewa tayi tace tana xuwa snn ta fita, ya fi kowa sanin halin Mami yasan wannan duk pretending take masa, ya kalli bunch of keys din da ta ajiye nan kasa bayan ta bude sa, ya dauka da sauri ya cire biyu ya tona kasa ya boye a cikin d'an room din, yana nan durkushe yana yi yana lekan sojoji biyun dake tsaye waje har ta dawo ya sunkuyar da kansa da sauri, Ruwan babban gora me sanyi ta kawo masa da Hollandia yoghurt, sae dambun nama cike a plate tace toh tashi ka shiga kafin ya yo nan, karban ruwan yayi ya sha kusan rabi, Key din dake ajiye kawae take kallo can ta dauka tana weighing dinsa ta kallesa strictly tace "Ka cire key a nan bani!" Da sauri yace "Key kuma Mami" wani kallo tayi masa tace "mike tsaye" yana tashi ta sa hannu aljihunsa ta dudduba taga babu, ta leka guard room din ma bata ga alamar key ba tace "Toh shiga ciki" ya ajiye ruwan hannunsa fuskar nan tasa kamar xae yi kuka ya durkusa ya shiga ta tura masa abubuwan da ta kawo snn ta rufe gun da kwado ta juya ta nufi kofa, ya bi ta da kallo yana murmushi har ta fita. Ko minti goma ba ayi da fitarta ba yasa key ya bude gun a hankali ya fito, ya dau shirt dinsa dake rataye gun ya kakkabe ya saka snn ya saka takalmansa ya nufi kofa da sauri, lkci daya ya banke kofar ya fice a dari da sittin kafin sojojin su ankara, ae ko suka bi sa da gudu, gudu yake kamar jirgi xae tashi sama, wani soldier ya ciro whistle a aljihunsa ya dinga hurawa, ae ko sae ga sojoji har uku sun fito, Abba ma ya fito balconynsa a sama ya rungume hannu da mugun mamaki yana kallon Abuturrab, komawa yayi don dauko bindigarsa amma kafin ya dawo tuni ya isa gate da karfi ya finciko mai gadin sojan dake bakin gate yana kkrin datse gate din ya wani wurgar da shi ya fixgo gate din ya fice, gudu kawai yake kamar xae tashi sama, wanda hakan ya tsorata mutane duk suka fara gudu su ma, ko kallonsu bai yi ba har ya iso titi ya tsayar da mai adai daita bai jira ya tsaya ba ya afka ciki yace "Mu je muje da sauri....." Mai adai daita ya ja machine dinsa da sauri don shi ma ya tsorata, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya ya share xufar fuskarsa ya bude button din riga.
*Haske writers asso*📚✍🏻 It's Khaleesat Haiydar👌🏻
💫 *Noorul Huda*💫
27.....
Gani yake kamar ba tafiya mai adai daitan yake ba duk da yasan yayi escaping don baxa ma su san inda ya bi ba, yayi tsaki yace "Malam ajiye ni nan dan Allah" Mai adai daitan yayi parking Abuturrab ya fito yace "Sae dai kayi hakuri bani da kudi" daga haka ya yi gaba da sauri, mai adai daitan ya bi sa da kallo, yanxu kawae so yake ya gansa gidan Hajiya Mariya yasan tun da ya fadi ma Mami kamar an je an dauko Samantha an ba iyayenta ne, makullin motarsa dama tun da aka sa shi guardroom Abba ya karbe da wayoyinsa, wani bike ya tsayar yana kallon mutumin dake kai yace "Ehrm Don Allah malam ka goya ni xuwa Kofar Nasarawa idan ba damuwa..." Mutumin yace "Ba can nayi ba, nama kawo gida ka ga inda xan shiga..." Abuturrab yace "Toh don Allah ara min bike din... Xan dawo maka da shi" wani kallo mutumin ke ma Abuturrab daga sama har kasa baki bude, Abuturrab ya dafa sa yace "Na maka kama da barawo???" Shi dai mutumin kallonsa kawai yake, Abuturrab ya fixge key din yace "Nafi karfin satan machine, kuma i think da wuya a ga barawo Aliyu Haiydar! Sauka ka ban machine malam" kamar soko haka mutumin ya sauka, Abuturrab ya hau ya tada machine din ya figa da gudu ya hau kan titin, alarm mutumin ya saki bayan Abuturrab ya bace masa yana cewa ya hadu da d'an rufa ido. Cikin kankanin lkci Abuturrab ya iso gidan Hajiya Mariya, a sanyaye ya sameta a parlor ya karasa ya xauna yace "Mumy!" Ta kallesa tace "Me kace ma Mami" shiru yayi sae kuma ya mike da sauri yace "Tana ina Mumy?" Hajiya Mariya tace "Kaga ka hada ni da Mami sae da nace kar kace tana nan, to in'sha Allahu nasan duk inda suke sun ma kusa gidan nan yanxu" Abuturrab ya xaro ido ya nufi bedroom dinta da sauri ya samu Samantha kwance amma idonta biyu, ya karasa ya durkusa kusa da ita yace "Xa mu tafi yanxu samha!" Mikewa xaune tayi ya mike ya fita ta bi bayansa, durkusawa yayi kusa da Hajiya Mariya yace "Mumy babu kudi hannu na...." Mikewa tayi cikin harshen fullanci tace ya sameta a daki, bin bayanta yayi ta xauna tace "to yanxu ina xa ku Aliyu?" Ya shafa kai yace "Anywhere mum, kawai ki ban kudi kafin su karaso" Mikewa tayi ta dau purse dinta ta bude tace "Dubu uku kadai ke garen yanxu amma ga atm card!" Duk biyun ta hada masa ya karba, tace "Toh ta ya xan same ka, na kira wayarka duk switch off" yace "Abba ya karbe wayar, ina da number ki a kai i will call you idan na samu waya Mum," Daga haka ya juya ya fice ta bi sa da kallo, can ta fita ita ma, tana kallon Samantha tace "Toh xan kira ku kin ji daughter" Samantha ta gyada mata kai cikin sanyin murya tace "Nagode Mum" daga haka ta bi bayansa, Hajiya Mariya ta bi su da kallo cike da tausayi, suna fita Abuturrab ya kalleta ya langwabar da kai yace "Samha Bike xa mu hau fa!" Ta kalli machine din snn ta girgixa masa kai tace "Ban iya hawa ba...." Dariya ta basa yace "Toh ba sai in daura ki ba" ta koma baya da sauri tace "No ni ban taba hawa ba, bana so" gani yayi lkci xa su bata yace "Toh follow me fast..." Ta bi sa da sauri suka fita, wata hanyar daban ya dauka har suka iso main road ya tsayar da adai daita suka hau, mai adai daitan ya tambayesa inda xa su yace "Mu je gaba kawai" samantha ta kallesa tace "Ina xa mu je" kasa ce mata komai yayi ganin yanda idonta ya fada, ya kamo hannunta a hankali yace "Am sorry for everything samha" bata ce komai ba, ya kalli mai adai daitan yace "Jan bulo xaka kai mu." Suna isa mai adai daitan yayi parking dai dai inda Abuturrab yace yayi, yana sauka ita ma ta fito, ya mika masa dubu dayan hannunsa ya basa canji ya kalleta yace "Mu je" bin bayansa tayi ya kwankwasa gate mai gadi ya bude, suna gaisawa ya shiga gidan ita ma haka, sai a snn a hankali tace "Doctor ina ne nan?" Ya kalleta yace "Gidansu frnd dina ne nan, bbu wayar da xan kirasa shi yasa mu ka xo" Farida kanwar Mujaheed na xaune karkashin umbrella tree da alamar assignment take, tana ganinsu ta mike tace "Lahh ya Aliyu daga ina?" Yace "Mujaheed na nan?" Tace "Ehh yana nan" yace "Kice ina jiransa" tace "Toh" snn ta kalli Samantha tace "Sannu da xuwa" Samantha ta sakar mata murmushi tace "Nagode" daga haka yarinyar ta wuce ciki, ya kalli samantha yace "Mu je ki xauna" bin bayansa tayi suka xauna karkashin bishiyar, ba a dau lkci ba Mujaheed ya fito, ya xaro ido yana kallon Abuturrab yace "Daga ina haka?" Abuturrab bai tanka sa ba har ya karaso ya ja kujera ya xauna yana kallon Samantha murmushi dauke fuskarsa yace "Sannu yan mata!" Samantha ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" ya amsa da fara'arsa, Abuturrab yace "Kira farida su shiga ciki, xa mu d'an fita da kai ne yanxu" Mujaheed yace "Ohk" ya ciro waya ya kira kanwarsa ta fito, Abuturrab ya kalli Samantha yace "Samha ku shiga ciki am coming back soon" kallonsa kawae take lkci daya idonta ya kada, mikewa yayi da sauri yace "yanxu fa xan dawo Samha" dago ta yayi suka bar gun daga Mujaheed har kanwarsa suka bi su da kallo, jikin flowers ya tsaya ya daga kanta yana kallon kwayar idonta yace "Ko baki son nan din ne?" Ta girgixa kai bata ce komai ba, a hankali ya kai lips dinsa forehead dinta murya can kasa yace "am coming back soon dear" Daga haka ya kama hannunta suka dawo inda suke ya hada ta da farida suka shiga cikin gidan, A motar Mujaheed suka bar gidan, sun dan yi nisa Mujaheed yace "Kai malam wai ina xa mu" Abuturrab yace "Yi parking muyi magana" Mujaheed yayi yanda yace snn yace "Wnn ba yarinyar nan da ka taba kawowa clinic bace? Dama budurwarka ce?" Abuturrab yace "Ni dai ka saurareni ina son pls ka min wani favour" Mujaheed yace "Na me?" Abuturrab yace "Laifi na yi ma Abba, pls so nake kayi pretending baka san komai ba kaje can gidanmu da sunan kaje daukan ajiyar ka, sai ka duba briefcase a bedroom dina ka dauko min gaba daya Credentials dina, snn akwai atm cards dina har biyu a gaban mirror ka dauko min plss frnd" tun da ya fara magana Mujaheed ya bude baki yana kallonsa, can ya fashe da dariya yace "Me kayi kuma again?" Abuturrab ya tabe baki yace "Oho dai, kawai ni dai nasan tun safe ake cin xalina.... Kaje yanxu plss" mujaheed yace "Abban na gida ne?" Abuturrab yace "May be" Mujaheed ya girgixa kai yace "In dai yana nan baxan iya ba wllh" Abuturrab yace "Oh haka xaka min?" Mujaheed yace "No gaskiya kenan fa, to ita kuma yarinyar nan da kake yawo da fa?" Abuturrab ya shafa kansa yace "Kaga it's a long story yanxu kayi abinda nace idan ka dawo sai in baka labarin," Mujaheed yyi shiru snn yace "Ka fa san halin Dad dinka, xae iya gano hada baki muka yi, why not ka bari da daddare...." Abuturrab yayi tsaki yace "Kai dai kaje ynxu kawai, you have to pretend, sai kace kana ta kiran lines dina basa xuwa, but bani wayar ka daya in case of anything sai ka kira ni" Mujaheed yace "No gaskiya ka bari da daddare?" Abuturrab yyi shiru sai kuma yace "Toh shknn" Mujaheed yace "Da motata xan je?" Abuturrab yace "A'a kawai ka dau tricycle kaga bbu wanda xae xargi komai, kana xuwa kuma ni xaka fara tambaya" Mujaheed yace "Ohk" gidan wani abokinsu suka tafi, suka tsaya har bayan magrib, Abuturrab dai gaba daya hankalinsa na kan Samantha duk da sun yi waya ya fi sau goma ta wayar farida, Bakwai da kusan rabi Abuturrab yace "Toh kaga kar dare yayi kuma Mujaheed ka tashi ka je" Mujaheed yace "Ni dai anya xan je kuwa..." Abuturrab ya marairaice masa, da kyar ya kuma lallaba sa har ya amince daga karshe yace "Toh ina xan sameka?" Abuturrab yace "Ina nan xan jira ka har ka dawo" daga haka Mujaheed ya fita ya dau adai daita ya wuce, Mujaheed na isa yaji gate a kulle wato sai ya xaga ta daya gate din bbu yanda ya iya haka ya xaga, yana shiga ya gaida sojojin dake wajen, sae da gabansa ya fadi ganin Abba a compound suna magana da wani sanye da khaki da alamar abokinsa ne, don compound din akwae haske sosai, yana ganinsu yayi kasa da kai har ya isa gabansu ya risina ya gaidasu, duk suka amsa, Abba yace "Daga ina haka?" Mujaheed yace "Daga gida nake Abba, gun Abuturrab na xo..." Abba yace "Ohk!" Abokin Abba yace "Abuturrab din bai nan ai" Mujaheed yace "Ohk kuma ina ta kiran wayarsa tun rana baya shiga, dama akwai ajiyar da na basa xan karba ne bari in duba ko kofar a bude yake" Abba yace "Ohk" Mujaheed ya sauke ajiyar xuciya ya nufi part din Abuturrab, a bude ya tadda gun ya shiga ya dauko duk abinda Abuturrab yace masa snn ya fito, yayi mamakin ganin sojoji biyu tsaye kusa da balcony sai dai bai ce masu komai ba ya wuce su, yana isa tsakiyar compound ya samu su Abba yanda ya bar su a tsaye ya karasa yace "Abba na dauka xan wuce" Abba na gyada kai yace "Ohk...." Ko rufe baki Abba bai yi ba, Mujaheed ya ji an cafkesa ta baya ya juya da sauri ya ga wani soja ne, sojan ya karbe envelope din hannunsa ya ajiye sa kasa sannan ya fara cajin aljuhun wandonsa ya ciro atm cards din ciki da wayarsa ya jefar kan envelope din, Abokin Abba ya durkusa ya dau Envelope din ya bude ya fiddo abubuwan ciki, banda xare ido babu abinda Mujaheed yake, Abba ya karbi takardun ya kalla snn ya maida dubansa kan Mujaheed, Gyada kai yayi yana wani murmushi ya jefar da takardun kan Envelope din yace "That's a brave play, yeah kun yi kokari daga kai har shi" dukawa yayi ya dau wayar Mujaheed yace "Akwai waya hannunsa ko babu? Kuma kana min karya in sa a kai min kai barrack yanxun nan" Mujaheed da banda xufa bbu abinda ke karyo masa cikin dakiya yace "Ehh Abba akwae daya wayata a gun sa" Abokin Abba na gyada kai yace "Good, kirasa kasa a hands free kace ku hadu a filin polo yanxun nn ya karbi sakon" Da kyar Mujaheed yace "Toh" nn ya shiga kiran daya wayarsa dake gun Abuturrab, Abuturrab da ya fita yana jiransa a mota ya daga kiran da sauri yace "Yane Mujaheed ka dauko?" Mujaheed ya kalli Abba, Abba ya watsa masa wani firgitattcen kallo, da sauri yace "Ehh ehh wllh na dauko! Emm kana ji na mu hadu a filin polo yanxun nn ka karba" Abuturrab yyi shiru, murya can kasa yace "F**k you, ka bari an gano mu knn!" daga haka ya katse wayar ya jefar.
*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫
28.....
Tada motar yyi da sauri tunawa da Samantha da yayi, yasan in dai mujaheed yaga haza to fa xae iya cewa tana gidansu ma, cikin kankanin lokaci ya isa gidansu Mujaheed gabansa na faduwa, kusan a tare suka shiga compound din da kanwar Mujaheed Aysha ta dawo daga makaranta, ya amsa gaisuwarta yace "Kice ma bakuwar da ke ciki ina jiran ta pls hurry" tare samantha suka fito da Farida ta raka su har gun mota ya sosa kai yace "Kice Umma tayi hakuri ina nan xuwa gaida ta, kunya nake ji shi sa ban shigo ba" dariya kawae Farida tayi tace "Ya Jaheed fa?" Abuturrab yace "Ehh yana nan dawowa..." Daga haka ya sa samantha ta shiga mota shi ma ya shiga da sauri, farida ta d'aga masu hannu ya ja motar ya bar layin, yana fita layin motar sojoji na shiga, xaro ido yyi don bai san ko sun gansa ba ya kara gudun tukinsa, sae da suka dan yi nisa ya kalli samantha yaga idonta na waje, wani tausayinta yaji sosai ya kamo hannunta a hankali yace "Samha!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, yace "Kin ci abinci?" Kai kawae ta gyada masa, cikin sanyayyen murya yace "Ki kwantar da hankalin ki kar ki sa ma kanki damuwa plss am with you now and forever..." Hawaye ya ga idonta, yayi parking da damuwa yace "Baki yarda da ni ba kenan Samha..." Ta fashe da kuka tace "My parent...." Ya rike hannayenta duk biyun yace "Ni ma na bijire masu duk sbda ke, kinsan irin neman da ake min yanxu? A guardroom Abba na yasa aka kulle ni da safen nan amma sae da nasan yanda na fito, na tura Mujaheed can gidan ya dauko mun Atm cards dina shima yana can nasan an kullesa yanxu kuma nasan xae iya cewa kina gidansu shi yasa na dauke ki, am at risk Samha but i don't care in har ina tare da ke, i love you... I can do anything for your love" hannu yasa ya share hawayen da ke idonta yace "Kar ki damu Allah yana tare da mu!" Sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba, ya ci gaba da tukin, a wani atm ya tsaya yace yana xuwa snn ya fita, sae da ya fara duba nawa ne a account din Small Mum din tasa snn yayi withdraw din dubu hamsin, kamar ance ya waiga yaga motar sojoji na kokarin shan cornern gun bank din, da sauri ya koma ya labe jikin Atm din, ta gefen ido yake kallon motan gabansa yayi mugun faduwa ganin abokin Abbansa da ya fito daga gaban motar, sojoji hudu ma suka sauka daga baya, kamar kiftawan ido ya taho a 160 ya shige cikin mota yayi wani reverse bae damu da harbin da suka fara ba, ko kallon titi bai yi ba ko mota na xuwa ya hau titin ya ja motar a guje, Samantha da duk ta gama rikicewa ta dinga kwala ihu a cikin motor, ta madubi ya ga sojojin sun biyo sa a tasu motar da gudu, ya yo waje da ido yace "Kan bala'i" sae ka rantse tashi sama xae yi tsabar yanda yake gudu don ma titin bbu wasu motoci, samantha dake ta rusa kuka sae cewa take don Allah doctor ka tsaya, don Allah ka tsaya, Bai ko kalleta ba bare ya san me take cewa, hankalinsa ya gama tashi ganin sun kusa tadda su a lokacin kuma suna wajajen court road, bai damu da traffic da ya nuna masa green ba ya wani sha kwana da gudu har ya kusa karo da wata mota ya kauce mata ya ci gaba da gudunsa, traffic din nan ne ya taimaka suka samu distance tsakaninsa da soldiers din, sosai ya ga karfin halin samantha don yasan da wata ce da tuni ta suma, har ya hau titin unguwa Uku bai sassauta gudun da yake ba, a can baya sosai yake hango motar soldiers din, bai son ya shiga wani layi su tadda traffic shi yasa ya gwammace yayi ta gudu a express, hankalinsa ya tashi ganin man motan yayi kasa sosai, yana fara fita outskirt din kano yaga da nisa fa sosai tsakaninsu ya ja ya tsaya ya cire makullin motar ya fito da sauri, har lkcn kudin da yayi withdraw da atm card na aljihunsa, ya xaga ya bude inda take ya fito da ita, wani hanya kamar gona ya ja ta suka bi da gudu, daji ya dinga gani sosai a gaba amma hakan bae sa ya dakata ba, ita ko sai kuka take tana cewa "Baxan iya ba Doctor ka tsaya plss" a haka ya ja ta suka shiga dajin, bai damu da thorns din ciki da dogayen ciyayi ba ga uban duhu suka dinga ratsawa a haka, tafiya sosai suka yi a ciki ya ga kamar numfashinta na neman daukewa tsabar gajiya don jan ta kawae yake, rikota yayi da sauri ya nemi karkashin wani bishiya ya xaunar da ita yana kallonta bnda kyallin idonta bbu wani haske da yake gani a dajin, ta rike duk hannunsa biyu da kyar tace "Ruwa xan sha doctor!" Maida numfashi ya dinga yi yana kallonta, can ya runtse ido ya dinga maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un a xuciyarsa, bude idon yyi ya dafe kansa, ta xame hannunta daga nasa ta fashe da kuka, mikewa yayi yana dube duben inda xai samo mata ruwa yaji ya yi kick din abu, da sauri ya duk'a yana laluba meye wnn yaga kettle ne, da ruwa amma ba da yawa ba a ciki, dagawa yayi duk da bai san ruwan meye ba ya kai baki ya sha yaji dai ruwa ne sai dai da jin sa a baki kasan ba wani mai kyau bane, ya hadiya da kyar snn ya kai mata baki, karba tayi ta sha gaba daya, ya ajiye butan, ta rike hannunsa gam cikin rawan Murya tace "Am afraid doctor, tsoro nake ji" xaunawa yyi gefenta ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Don't be, am here to protect you, am with you" shiru tayi tayi lamo a jikinsa wanda hakan yasa ya dinga jin bugun xuciyarta, sun kusan minti talatin a haka taji ya kankameta, ta d'ago da sauri, taga idonsa a runtse, a hankali ya bude yana kallon kasa murya can kasa taji yace "Ant, i think it's an ant" kalle kallen kasan ita ma take, xaro ido tayi tayi wani uban ihu da sai da ko ina ya amsa, sai a snn ya ga me ta gani, wato kunama shi ba babba ba shi ba karami ba, ya toshe bakinta ya sa kafa yayi smashing dinsa, ko ina na jikinta rawa yake ta dinga cewa it's a scorpion, ya kai bakinsa kunnenta yace "Shhhh na fa kashe shi..." Jin baxata yi shiru ba ya lumshe ido ya rungumeta gam, tayi lamo jikinsa, a hankali ya xame dankwalin kanta ya daura a gun da kunaman ya harbesa, ba a dau lkci ba bacci ya dauketa.
*Haske writers assoasso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫
29.....
Daren ranan Abuturrab bai rintsa ba, har asuba yana rungume da ita, gari na fara haske ya kare ma dajin kallo, sai yaga ashe gona ce gun gaba daya, bishiyoyin mangoes da lemo ne yasa gun ya xama kamar daji da daddare, ya kalli wani tabarma dake can nesa da su a shimfide da wani sanda, da alamar dae mutane na xuwa gun, butoci har biyu ya gani bayan wanda ya samu ruwa a ciki jiya, kwance dankwalinta dake daure kafarsa yayi ya shimfida nan kasa snn ya kwantar da ita a hankali ya mike, wani mugun ciwon kai ya dinga ji ya taka a hankali har ya isa inda butan yake ya ga cike yake da ruwa ya dauka ya xaga ya daura alwala snn ya dawo, ya kalli gabas ya tada sllh, bai idar ba samantha ta farka, mikewa xaune tayi da sauri tana kare ma gun kallo, a hankali ta mike ta karasa gun butan da ya ajiye ta dauka, kallonta kawae yake bayan ya idar, ta juyo ya sakar mata murmushi cikin sanyin murya tace "I want to ease my self" yace "In raka ki?" Da sauri ta girgixa masa kai yana murmushi yace "Ohk" ya nuna mata inda xata tafi, ta juya ta wuce, ko da ta dawo bata gansa ba, ta fara kalle kalle da manyan idonta, muryarta na rawa tace "Doctorrr" tim taji fadowar mango a sama, ta koma baya a tsorace tana kallon sama ta gansa samar bishiyar yana tsinkar nunannun mangoes, ya kashe mata ido yace "Breakfast...." Daga haka ya ci gaba da tsinkar mangoes din masu kyau har ya tsinko fiye da ashirin, ji tayi ya diro kasa, ya karasa ya dauko dankwalinta ya dawo ya durkusa ya kwashesu, ta karasa inda yake ta durkusa gabansa a hankali ta shiga taya sa kwashewa, ya sakar mata murmushi yace "Bari toh in kara plucking din pawpaw ae kina so" bata ce komai ba ya mike ya isa inda sanda ke ajiye ya tafi gun bishiyoyin gwandan, can ya koma baya ita dae kallonsa kawae take, taku daya biyu yayi ya buga uban tsalle ya doki ripe pawpaw guda daya da sandar hannunsa ya fado, murmushi tayi ta dauke kanta ya dawo rike da pawpaw din yana murmushi ya ajiye mata, xaunawa yayi yace "Tunda bbu ruwa haka xa mu sha mangoes din..." Daga haka ya dau mango daya ya kai baki, dauka ita ma tayi ta kai baki a hankali, biyu kawae ta sha tace ta koshi, yace "Efizzy xa ki min" murmushi tayi ta girgixa kai kawai, duk yanda yayi da ita tasha kin sha tayi wai ta koshi, pawpaw din ma shi kadae ya sha kayansa wai bata sha, yana gamawa yace "We will leave yanxu...." Mikewa yayi ya dau sauran mangoes din da sanda yana rike da hannunta suka fara tafiya can gaba, da sandar ya dinga clearing masu daji don duk a tsorace take duk da kana ganin hanyar ma kasan ana bi sae dai ba sosai ba, tafiya kawae suke har kusan karfe tara ganin ta gaji sosai ya langwabar da kai yace "Ko in goya ki baby" kamar xata yi kuka tace "Doctor wae ina xa mu...." Yace "In da Allah ya kai mu" bata kuma cewa komai ba suna ta tafiya ga uban rana me xafin gaske har sha daya tayi, ta durkusa tana haki tace "Wayyo doctor i can't go futher am very thirsty" durkusawa shi ma yayi cike da tausayinta, ta fada kansa hawaye cike idonta tace "Na gaji, yunwa nake ji" ya rungume ta yace "Kiyi hakuri plss, so nake mu fita dajin nan ne so i will find you something to eat..." murya suka ji bayansu, ta kankamesa a tsorace ya juya yaga wani tsohon bafullatani sanye da katon hat wanda hakan yasa ba sosai yake yake hango fuskarsa ba, hannunsa rike da sanda cikin hausan sa da bai fitowa irin ta fulani yace ma Abuturrab "yarinya me ya kawo ku nan" Abuturrab da yaji sanyi sosai a ransa yace "Mun yi 6atan hanya ne Baffa!" Bafulatanin yace "Subhanallahi.... Ina ne xa ku?" Abuturrab ya sake samantha ya mike yana kallon dattijon cikin harshen fillanci yace "Daga kano muke xa mu kaduna barayi suka biyo mu tun jiya da daddare shine muka yo dajin nan" tsohon ya washe hakoronsa da goro yayi masa destroying da fillanci yace "Dama ina ganin ka nasan kai namu ne, ashe d'an uwana ne, barka da arxiki da barayin basu cutar da ku ba" Abuturrab murmushi kawae yake yana gyada kai, dattijon ya kalli Samantha da yaren yace "Sannu yarinya ta barka da arxiki" Kanta a kasa tace masa sun gode da harshen fillanci ita ma wanda hakan yayi mugun daure ma Abuturrab kai ya tsaya kallonta kamar idanuwansa xasu fito, dattijon yace "Rigar mu na nan kusa ku taso mu je ku huta, tafiyar minti talatin ne xae kai mu can, na fito kiwo ne dama na hango ku nayi xaton barayin daji ne, ga can inda na boye shanaye na" dariya Abuturrab yayi tsohon ma yayi dariya yace "Toh muje..." Abuturrab ya kalli samantha ya kama hannunta suka bi bayansa, ya matsa hannunta a hankali yace "Dama kina jin fulfulde shine ko sau daya baki taba gaya min ba" ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, haka suka dinga bin dattijon da shanayensa kusan ashirin, su sha wancan kwanan su fito ta wani su kuma shan wata kai hanyar dai gashi nan gashi nan, Abuturrab yasan ko kashe sa xa ayi kila baxae iya gane hanyar ba. Suna isa Rigar dattijon ya juya yana kallonsu da fulfulde yace "Ga 'yar rigar mu nan, da fatan xaku ji dadin xama a ciki na yau dai" murmushi kawai Abuturrab yayi, tafiyar minti goma suka yi suka iso wani gida dake xagaye da kara, Dattijon ya shiga hade da sallama suka bi bayansa, bukkoki hudu ne a xagaye a d'an karamin tsakar gidan, wata mata dake daka tsakar gidan tayi masa sannu da xuwa da yare tana kallonsu Abuturrab, ya amsa yace "Kin ganni da baki 'yan uwanmu koh?" Mikewa tayi ta dauko tabarma ta shimfida tana masu lale, Yace "debo masu nono kafin ki xauna Hansai" wani bukka ta shiga sae ga ta ta fito da kwarya cike da nono ta ajiye masu, Dattijon da ake kira da Alto yace "Ina yarinyar nan ta shiga?" Hansai tace "Taje kai fura gidan tuwaru nasan duk inda take ta kusa gida yanxu" Malam Alto yace "Toh akwae ruwa gidan koh? Allah ne yayi masu katanga da barayi suka afko daji shine fa muka hadu da su...." Girgixa kai Hansai ta dinga yi tana cewa "Allah yayi mana tsari" Wata yarinya da baxa wuce Samantha ba ta shigo gidan kanta dauke da icce, ta karaso ta durkusa ta sauke tace "Inna bak'i muka yi" Malam Alto yace "Ehh wllh gasu nan daga birni suke" ta kalli Samantha tace "Sannu da xuwa..." Hansai tace "Tashi ki shiga da ita ciki ki bata zani ta daura tayi wanka" Mikewa tayi samantha ta tashi ita ma suka shiga wani bukka, bbu komai ciki sae yar katifa da xani a kai, sae jakar gari yayi xafi guda biyu, cement din dakin duk ya farfashe, Samantha ta xauna kasa yarinyar da hausarta na fulani tace "Ki xauna kan katifa" samantha tayi yanda tace, yarinyar ta bude jaka ta fito da wani xanin kayan fulani a linke ta ajiye mata tace "Gashi ki daura" Samantha ta kalleta a hankali tace "ina son in huta ne" yarinyar tace "Toh ki huta" daga haka ta fita, Hansai tace "Kin bata xanin Binta?" Binta tace "Eh ta kwanta wai tana son ta huta" Hansai tace "Toh shknn, maxa ki xo ki hura wuta in daura sanwa tunda mun yi bak'i" Wani sabulu babba me kamshi Alto ya dauko a dakinsa ya mika ma Abuturrab yace "Aminina Hammadu ne da yaje birni ya kawo mun sabulun nn har uku... Gashi ka shiga wanka da shi xaka fi jin dadinsa" Abuturrab ya mike yana murmushi ya karba yace "Toh nagode Baffa" daga haka ya nufi 'yar kewayan dake tsakar gidan don Baffa ya kai masa ruwa Binta ta bi sa da kallo, ko da ya fito Baffa ya kai sa Bukkarsa ya dauko masa wani tsaftatattcen rigarsa irin ta fulani ya basa, Abuturrab ya karba hade da godiya Alto ya juya ya fita, yana gama shiryawa ya fada d'an gadon dake bukkar lkci daya bacci ya daukesa. Burabisko da miyar taushe da k'ashi Hansae tayi ta ajiye masu cikin langar tuwo da miya, Baffa dake xaune da yar radio a hannunsa yace "Bayin Allah da alama sun wahala, a dajin ma suka kwana" ana kiran Azahar Baffa ya tada Abuturrab yayi sllh, Hansae tace "Tafi ki tada ta ita ma tayi wanka tayi sllh" binta ta shiga ta tada Samantha tace "Ki tashi kiyi wanka sai kiyi sllh, Azahar yayi" Samantha ta mike xaune tana mitsika ido, can ta mike ta cire kayan jikinta ta daura xanin, ta kalli binta tace "ki ban mayafi don Allah" Binta ta nemo mata wani dankwali ta bata tace "Mu je in raka ki kewayen na kai maki ruwa" Abuturrab na xaune a tabarma tare da Alto yana shan fura da nonon da Hansai ta dama masu Samantha ta fito da Binta, kallonta ya dinga yi ita ko kallo daya tayi masa ta dauke kai Binta ta rakata har bayin snn ta dawo, Samantha na fitowa daga wankan Hansai tace "Ga buta can ki dauka kiyi alwala" shiru Samantha tayi bata ce komai ba, can ta kalli Abuturrab da idonsa ke kanta, ta girgixa kai a hankali tace "Bana yi" daga haka ta shige Bukkar Binta, wata yar top da xani binta ta bata ta sa, tana gama shiryawa binta tace "Ki fito ku ci abinci wae ke yake jira" Samantha ta mike suka fita a tare, Alto ya mike yace ta taho ta xauna, ta karasa ta xauna kan tabarmar, Fura Abuturrab ya mika mata ta karba ta ajiye, bata bari sun hada ido ba duk da irin kallon da yake mata, shi ya fara sa hannu cikin langar dake dauke da Burabisko da miya yayi bismilla ya fara ci, kasa sakewa Samantha tayi taki cin abincin sai fura da take sha a hankali Hansai tace "Ko xa ku shiga daga ciki naga kamar a takure take" Kamar Abuturrab jira yake yace "Toh" Hansai tace "Binta kai masu abincin daki" Binta ta je ta dau abincin ta shiga da shi bukkarta, Abuturrab ya mike yana kallon Samantha ita ma ta mike ta bi bayansa suka shiga Bukkar, suna shiga ya nuna mata kusa da shi ta xauna, ya dau cup din furan ya mika mata ta sa hannu ta karba yace "Finish it immediately ki ban cup din" ta yi d'an murmushi ta kai baki, kadan ta sha tace "Na koshi" ya hade rai yace "Sae fa kin shanye" girgixa kai tayi ya kwace cup din hannunta ya matso kusa da ita ya rike kan ta ya kai cup din bakinta, bbu yanda ta iya haka ta dinga sha kamar xata yi kuka, sae da ya ga ya wuce rabi snn ya ajiye ya ce "oya sa hannu" lekan abinci tayi tace "What's that" Hannu yasa ya deba ya kai bakinta, ta bude bakin a hankali ya xuba mata, da kyar ta dinga taunawa tana kallonsa kmr me taunar magani, ya dake bai bari yayi dariyar dake cin sa ba, tana hadiyewa tace "Baxan iya ci ba Dr " Ya girgixa kai yace "No, but da dadi fah, there's no other food than this!" Ta fashe da kuka tace "Baxan iya ci ba..." Shiru yayi yana kallonta, can ya kamo hannunta cike da tausayi yace "Toh me xa ki ci" cikin rawar murya tace "Rice!"
*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫
30.....
Shiru yayi ya rasa abinda xai ce mata, can ya sa hannu cikin aljihinsa yaga har lkcn kudin da yayi withdraw na nan, ya rufe burabiskon ya mike yace "To taso mu je" a hankali ta mike ta bi bayansa suka fita, yana kallon Hansai da Alto da yare yace "Baffa xa mu d'an xaga rigar nn...." Alto tace "Toh har kun cinye abincin ne?" Yace "A'a idan mun dawo xa mu ci, furan ya ishe mu" Alto tace "Toh bari Binta ta xaga da ku, sai dai fa ba wani girma ne da kauyan namu ba" tana dariya ta kare maganar shi ma yayi dariya yace "Ni kuma hakan ya burgeni sosai babu hayaniya" Alto ya kwalo ma Binta kira ta fito yace tayi masu jagora xa su xagaye Rigar garki, tace "Toh" snn ta koma ciki, dama shigar fulani tayi dogon gashinta da ke kai wa har kusan gadon bayanta an tufke mata shi gida uku, ta dau sandar kiwonsu tana kallonsu Abuturrab da fillanci tace "Mu je" Samantha dai ko kallonta bata yi ba har suka fita, tana tsakiyarsu suke tafiyar ko wani Bukka suka wuce sai ta fadi masu na wanene duk da fillanci, kai kawai Abuturrab ke kada mata, can ta kalli samantha da yaren tace "Ke bakya magana, ya sunan ki" Samantha bata ce komai ba, Abuturrab yace "Sunanta Fatima amma ana kiranta da Samha" kallonsa Samantha tayi ya wara mata ido, Binta tace "Lah ashe sunan mu daya, to me yasa kanwar taka bata magana?" Ya buda hannu yace "Haka take" tace "To kai ya sunanka?" Yace "Aliyu" ta xaro ido "Suna mai girma" Hira Binta ta dinga masa tun yana amsa mata da uhm da eh da A'a har dai ya fara magana, Samantha dai tafiyarta kawai take bata ko kallesu ba, Binta tace "Ina son wataran ni ma inje birni" kamar xata yi kuka ta kare maganar, yayi yar dariya yace "Kar ki damu xamu xo mu dauke ki wataran..." Tace "To a ina xan xauna ni da ban san kowa a birni ba" Yace "Gidanmu mana" tayi murmushi tace "Allah yasa kar ku mance da ni" yana murmushin shi ma yace "In'sha Allah" kallon Samantha yayi da fillanci yace "Are you okay?" Bata ce komai ba bata kuma kallesa ba, tsayawa yayi yana kallonta Binta ma ta tsaya, ita ko ta ci gaba da tafiyarta, ya jawota da damuwa yace "Samha tell me what's wrong?" Ta mayar masa da fillanci tace "Just want to be left alone" shiru yayi yana kallonta, ta kwace hannunta ta ci gaba da tafiya, Binta ta kallesa a hankali tace "Kilan so take ku je gun Ammin ku" Murmushi ya k'irkira bai ce komai ba suka ci gaba da tafiya, can ya kalli Binta yace "Akwai inda ake sai da abubuwan ci a Rigar nan" tace "Ehh mana akwae yar kasuwa, ana tsayar da warar fulani, hura da nono, gyada kai har da nama da...." Ya katse ta yace "Shinkafa fah?" Ta ce "Akwai mana" yace "Toh muje xan siya mata shinkafa xata ci" Binta ta kalli Samantha da tayi gaba can tana tafiya tace "Bata cin Burabisko?" Kai kawai ya gyada mata, ya karasa da sauri gun Samantha ya kamo hannunta da turanci yace "What's all this dear?" Bata ce komai ba, ya ci gaba yace "Did i offend you in anyway" Binta dake kallonsu ta gefen ido ta ci gaba da tafiya, ganin baxa ta kulasa ba ya ci gaba da tafiya yana rike da hannunta, shinkafar dari uku ya siya da wani miya da ke basa kyankyani, ita kanta Samantha da ganin yanda take kallon abincin kasan bbu yanda ta iya ne, suna gama siya yace su koma gida, wnn karan su biyu ya bari suka yi gaba yana biye da su a baya. Har suka isa gida bbu wanda yace komai cikinsu, Su Alto suka yi masu sannu da xuwa, ba laifi Samantha ta ci shinkafar sbda yunwar da take ji, ya tallabi cin dinsa yana kallonta har tace ta koshi, yayi murmushi yana gyada mata kai, murya can kasa yace "Kinsan me love?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, a hankali yace "Idan ance ki tashi kiyi sllh ki dinga cewa toh" ta kafe sa da manyan idonta, can tace "Ban gane ba" ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace "I mean idan aka ce maki ga ruwan alwala ki ce to, ki dauka...." Wani kallo take masa tace "In yi me?" Yace "Kiyi alwalan ko baki iya ba!" Da mamaki ta dinga kallonsa, can ta girgixa kai tace "No!" Shiru yayi yana kallonta, can yace "Let me ask you, what's Good about Christianity?" Ta wani hade rai tace "What's Good about Islam?" Kamar jira yake yace "A lot, it's a religion of peace.... The true religion, Christianity is not a religion, it's just a way of life.... Ki bani inda aka ambaci Christianity a bible nima kuma xan baki inda aka ambaci Islam a bible...." Wani kallo ta dinga yi masa ya gigixa kai yace "If you know ur bible too well John 14;27 Jesus said 'Peace i leave with you, My peace i give to you, not as the world gives, and do not allow ur heart to trouble you' here Jesus made mentioned of the religion he practiced and let to his disciples (Followers) as (Shalom) and did you know the meaning of Shalom?" Har lkcn kallon tara saura qtr take masa, ya matso kusa da ita ya d'ago kanta yana kallon kwayar idonta yace "In kinsan Bible din ki sosai sanin ma'anar shalom baxai maki wahala ba... Ashe kawae ke 'yar muna Christian ce" kwace fuskarta tayi tace "Shalom means Peace!" Murmushin da ya baiyyana dimples dinsa yayi yana kallonta yace "Good, And that's the meaning of Islam (peace!), Jesus ya gargadi mabiyansa (disciples) kan cewar kada su bi son xuciya, kada su bi ra'ayinsu, but unfortunately they all followed their heart desire and got their selves the name Christianity, a name not found in the bible, a name gotten from Paul the apostle, paul shine yayi naming dinsa Christianity for his selfish interest domin a da ai ba masoyin Jesus bane Paul, true or false? Jesus acted like we muslims do, he fall with his face to the ground, but never dance, clap, or beat drum as an act of worship, did he?" Ya tambaya yana kallonta, ya girgixa kai yana murmushi yace "He never, let me add a prove to this, Matthew 26:29 read thus 'Going a little further, he fell with his face to the ground and prayed......" Murmushi yayi yace "you see, ba ace he clapped his hands, beat drum or danced ba, even till date the Coptic Christians still pray the way Jesus PBUH did, the jews in the holy land still pray the same way also!" mikewa tayi ta bar masa wajen ta koma kan katifar dakin tayi kwanciyarta hade da lumshe ido, murmushi yyi ya mike ya fice waje.
Mami ce xaune parlor ta rafka uban tagumi, Hajiya Mariya ma na xaune gefen yayartata, sai Yakumbo dake tsaye kekam bakin nan uwa an taka teba a kan titi ta jefa ma Mami harara yayi sau ashirin a wajen, manyan 'ya yanta maza duk biyun na parlorn, sai Abba dake tsaye shima kamar dai the soldier he is, sojoji ne har biyu tsaye bakin kofa, ya juya ya kuma kallon Mami strictly yace "For the last time ki gaya min inda Aliyu yake...." buda baki tayi cike da bacin rai tace "Kai kana matsayin mahaifinsa baka san inda yake ba sae ni, ta ina xan san inda Aliyu ya tafi, haba a dinga adalci mana" a fusace yakumbo tace "Yo idan bai tambaye ki Aliyu ba uwar wa xae tambaya?? ba boyayyen abu bane kowa yasan bakin ku daya da d'an iskan, ni ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba kinsan inda Aliyu yake...." Sae kuma ta fashe da kuka tace "Tur!! Mu dai duk xuri'ar mu daga farkonta har ixuwa yanxu bbu crista, ko tu6a66e, ban dai san a naku yanda abun yake ba...." Mariya tace "Mu ma haka, hasalima iyayen mu da kakannin mu duk malamai ne..." Yakumbo ta jefa mata wani matsiyacin kallo tace "keee kar ki min fitsara ban sako da ke ba daga tambaya?" Ko kallonta Mariya bata yi ba, Abba ya girgixa kai yana murmushin takaici yace "Hajarah duk abinda Aliyu ya xama kece sanadi, ke ce sila...". Mikewa Mami tayi tana murmushi tace "Sae yau ka sani kenan, ae tun da na nema masa karatu a Uk na biya, na kama masa gida mai tsada, na xuba masa abubuwan more rayuwa, naki sauraran shawarar kowa ni da 'yan uwana nace ae namiji ne shi ba mace ba, na rufe ido ban ji ban gani na hada masa kaya na kai sa Airport ya tafi can yayi rayuwarsa in a free way, bbu sa wa bbu hanawa shekaru d'aid'ai har takwas, What did you expect Col???" Daga haka ta nufi stairs Hajiya Mariya ta bi bayanta, kasa cewa komai Abba yayi ya bi ta da ido, yakumbo ta tafe hannu tana salati tace "Wato mu matar nan ke gaya ma magana koh?"
*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫
By Khaleesat Haiydar 📚✍🏻
31.....
Alhaji Umar ya saci kallon Abba da uwarsa bai dai ce komai ba haka d'an uwansa Alhaji Jibril, juyawa Abba yayi kamar xae tashi ya fice daga parlon, Alhaji jibril ya ce "Toh Allah ya kyauta, Allah ya kawo mafita yasa ya gane abinda yake shirin yi" Yakumbo ta fashe da wani kuka tace "Ae ni Allah ya isa tsakaninmu da Aliyu, wnn abun kunyar da me yayi kama da wani ido xa mu kalli 'yan adawan mu, me ya burgesa game da crista arniya, ni dai ina ganin jarabawa, Aliyu ya cucemu, yaro kamar shaidan, duk artabun da aka dinga yi jiya ace ba a kamasa ba har ya gudu ko ina ya tafi..." A bangaren mumy kuwa tun daga jiya har yau kuka ne ya xamto abincin ta da ruwanta, tayi kukan tayi xage xagen, tayi iface ifacen, banda bata hakuri bbu abinda yan uwa da abokan arxiki suke, har cewa tayi da ta sani tun daren shekaranjiya ta kashe samantha tasan ba ita a duniyar ne kawai da ace ta bi musulmi sun gudu, gidan nasu cike yake da members din Church dinsu, mata da maxa, pastors har daga kaduna da Abuja sae da suka xo, masu addu'a nayi, masu xirga xirga da Abban samantha xuwa gidansu Abuturrab nayi, da ace Dad din Abuturrab ba babban soldier bane da ya shiga uku don ba abu me kyau bane xae biyo bayan irin sintirin da suke fiye da su ashirin har da matasa, daga karshe tsawa yayi masu yace "Su je duk inda xa su su nemi Aliyu su kashe sa ya basu go ahead, kada wanda ya kara d'aga masa hankali tunda basa ganin kokarinsa, bbu yanda suka iya ga gida cike da sojoji, haka suka juya sumui sumui suka fita. Abuturrab na xaune tsakar gida suna labari hira da Abba bayan la'asar, Alto bata kuma cewa a ta da Samantha tayi sllh ba a tunaninta bata da tsarki ne, Binta na xaune tana sirfa gero sai dai duk motsin da idonta xae yi a kan Abuturrab yake sauka, yana lura da irin kallon da take masa, sae abun ya basa dariya ya dai ci gaba da hirarsa da Alto, Samantha ce ta fito ta nufi bandaki da sauri ta fara amai tun kan ta isa, mikewa Abuturrab yayi haka Alto da Hansae dake wanke wanke suka dings cewa subhanallahi, Abuturrab ya d'agota a rikice yace "Meya faru?" Ta fashe masa da kuka tana rike da cikinta tace "Ciwo yake min" Hansae ta kawo ruwa a buta tace "Ikon Allah to bara in jika ma sa6ara" Abuturrab ya karbi ruwan ya wanke mata fuskarta snn ta shiga da ita ciki. Kwanciya tayi ya xauna gefenta yace "It's ur period right?" Juyawa tayi bata ce komai ba, ya mike ya fita, Tsaye ya ga Hansai har ta jika maganin da tace, yayi murmushi yace "Ae baxa ta sha ba Baaba, bbu gun sayar da magani nan ne?" Alto yace "Kai da tafiya sosai, Binta ta raka ka gun da xaka samu babur ka hau, sae kayi kamar xaka shiga Gombe...." Abuturrab ya durkusa yace "ohh daga kauyen nan sae gombe?" Alto yace "A'a akwai kauyuka har uku a gaba..." Abuturrab ya mike yace "Toh shknn bari in je..." Tuni Binta ta dauraye hannunta tace "Mu tafi..." Ya kalleta yace "Ae na gane hanya yanxu, da kin yi xaman ki" Tace "Yo ae baka san inda xaka samu babur ba" Hansae tace "Gaskiya ne, bari ta rakaka gun sai ta juyo" toh kawai yace suka fita gidan, tun da suka fita Binta ke xuba bai kalleta ba bare ya tanka ta ba, tafiyarsa kawai yake, har suka isa inda babur uku suke sbda masu fita kauyen, duk machine din sun rube, Binta tace "Bako ne daga birni wae wajen kauyen nan xaku fitar da shi xae siya magani" Bata rufe baki ba ko wanne ya dinga cewa ya hau, na gabansa ya hau mutumin ya tada machine din, ya d'an kalleta yace "Sae na dawo" daga haka yace ma mai machine din su tafi. Sae kusan karfe shidda Abuturrab ya dawo rike da leda, Alto dake kade shanayensa a waje yace "Ka dawo?" Abuturrab yace "Ehh na dawo Baffa sannu da aiki" Alto yace "Ka dai samo maganin koh?" Kai Abuturrab ya gyada masa yace "Na samo" daga haka ya shiga, Binta kadae ce tsakar gida tana kwasan tuwo, ta washe baki tace "Har ka dawo Aliyu?" Kallonta yayi don sae da tasa Mami ta fado masa, ta fi kowa kiransa da Aliyu, yace "Na dawo! Bbu kowa dakin?" Tace "Ehh ita kadai ce" ya duka ya shiga Bukkar, xaune ya ganta ta hade kai da gwiwa, ya karasa a sanyaye ya ajiye ledan hannunsa ya d'agota yace "Samha!" Ta kallesa da idanuwanta da suka yi ja, cikin sanyin murya yace "Kuka kike?" Sauke idonta tayi ya kamo hannunta yace "Am making you suffer koh, i know you re not use to all this Samha.... But for the sake of my love endure it for just a while..." Ta fashe da kuka tace "Am not complaining" gefenta ya dawo ya xauna ya jawota jikinsa yace "Bance kina complain ba, but you re not use to this such of life..." Bata ce komai ba yace "Kin fara period din ne?" Ta girgixa masa kai, yace "But it's on it way koh?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya dago kanta yace "Shareni ma kika yi" kwace kanta tayi tace "How did you know?" Yayi murmushi ya daura kansa a kafadanta yace "I know because i am a doctor...." Tayi masa wani kallo ta gefen ido tace "Ko dai sa ido, kawai don ka ga na yi amai?" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, dariya yayi ya kai bakinsa kunnenta yace "Ni din, toh shknn in ma ya xo ya fara wahalar min da ke ko kallonku baxan yi ba, ya gama wujijjiga ki ya xuba abinsa ya wuce" murmushi tayi ta boye fuskarta a jikinsa, lkci daya Binta ta fado dakin, da sauri ya saketa ita ma ta ja baya, Binta na ganin haka ita ma da sauri ta fita, Ya kalli Samantha yaga ta wani hade rai, bai ce komai ba ya dau ledan da ya kawo ya bude, pad leda biyu sae inner wears da allurori da drugs, perfume, Toothpaste, brush soap da sponge sai gown har biyu da veil ya xube mata su gabanta, ta dauke kai bata ce komai ba, Ya bude daya ledan ya fiddo ledojin kaji biyu ya ajiye mata daya ya ajiye dayan a gefe, sae kuma Bread biyu da Blue band daya da ya siyo da kayan tea sae table water babba, mikewa yayi ya dau ledan kaza da daya bread din ya fita don kai ma su Binta. Bayan Isha Abuturrab na xaune tare da Baffa Binta ta fito tace "Aliyu ina jin fa ciwon cikin ne ya dawo sae juye juye take" Hansai dake cin tuwo tace "Subhanallahi, ka bata magungunan kuwa?" mikewa yayi ya shiga dakin Binta ta bi bayansa, ya durkusa gabanta yace "Sannu dear, but are you flowing?" Ta girgixa masa kai hawaye na sakko mata, dagota yayi ya bude ledan da magani ke ciki ya ballan mata biyu ya bata da ruwan goran ta sha, sae da yaga ta d'an nutsu snn ya mike ya fita, Hansai ce kadai a tsakar gida sai Binta da ta gaji da tsayuwa tun daxu dakin ta fito, Hansai tace "Ta samu bacci ne?" Yace "A'a ya mata sauki ne" Hansai tace "Toh Allah dai ya sauwake, dama ashe matar ka ce?" Kallon Binta yayi don yasan ta yi mata wata magana kenan, ya gyada kai kawai, tace "Allah sarki, ae ni nayi xaton kanwar ka ce, ashe mai daki ce, to shiga ciki sai ka tsaya tare da ita tunda ma bata da lafiya" yace "Toh" Hansai tace "Binta xata kawo maku bargo" juyawa yayi ya koma dakin, ba a dau lkci ba Binta tayi sallama bakin kofa ya fita ya karbi bargon ya dawo dakin, xaunawa yayi yana kallon samantha yaga har ta fara bacci, ya shimfida 'dan bargon a kasa ya rage lamp din dakin sosai ya kwanta. Can cikin dare ta kusa fadowa kansa bayan ta sauka daga kan katifa, ya mike xaune ya rikota yace "Me ya faru?" Rikesa tayi tace "Amai nake ji" ya rungumeta yace "Amma cikin ya daina?" Kai ta gyada masa, ya fara shafa mata bayanta a hankali murya can kasa yace "Aman xai koma kin ji?" Bata ce komai ba sae rufe idonta da tayi, haka ya dinga yi mata har taji aman ya koma, ta xame jikinta ta koma kan gado ta kwanta, ya jima xaune ganin kamar tayi bacci ya koma ya kwanta. Washegari da asuba tun da ya idar da sllhn asuba a dakin yayi ta tunanin inda xa su gashi bai da enough cash a hannunsa, kudin account din Hajiya Mariya ma bbu yawa, mikewa Samantha tayi xaune ya juya yana kallonta, ganin yanda ta bata fuska ya dawo kusa da ita yace "What?" Kamar xata yi kuka ta nuna masa cikinta, yace "Ya fara ne?" Ta gyada masa kai ta mike ta nufi inda ya ajiye kayan jiya ta dau pad da brush da toothpaste yana kallonta yace "In raka ki?" Wani kallo tayi masa yayi murmushi yana shafa kai yace "Ohk sorry" ko da ta dawo tilasta ta yayi ta ci bread da butter sbda alluran da xae mata, da kyar tana juye juye ta ci kadan ta sha ruwa yayi mata alluran ta kwanta, sae da gari ya fara wayewa snn ta samu bacci ya dauketa ya mike ya fita, Binta dake shara ta gaishesa da fillanci ya amsa yana tambayar ta tashi lfya, tayi murmushi ta tafi ta dauko wani flask da cooler ta dawo ta mika masa tace "Gashi karin kumallon ku" karba yayi yace "Mun gode" ya koma daki ya ajiye, tayi sallama bakin Hut din tace "Ga kofi" fitowa yayi ya karbi cup din ya koma ya ajiye, Muryan Alto ya ji da fillanci yana cewa "Ali na tafi kiwo sae na dawo" Abuturrab ya fito ya gaida sa, Alto yace "Ya mai jikin?" Abuturrab yace "Taji sauki Baffa, kilan baxa ka dawo ka same mu ba anjima xa mu dau hanya" Baffa yace "Allah mai girma, shi yasa ba a sabo da bako, baxa ku jira hat in dawo da rana ba" Abuturrab yayi murmushi yace "So nake mu isa gida da wuri ne" Baffa yace "Toh Allah ya tsare, ni bani da komai da xan baku, amma Binta xata tatsar maku nonon shanu ku tafi da shi bamu da komai baya ga wannan" Abuturrab yace "Ayya ba komai Baffa mun gode da karramawar ma" Alto yace "Toh Allah ya tsare, ku gaida mutan gida Allah ya tsare gaba" Abuturrab ya fiddo dubu goma cikin kudin jikinsa ya mika masa yace "Ga wannan ba yawa Baffa, in shaa Allah wataran xamu kawo maku ziyara" Alto ya bude ido yace "A yi haka?" Abuturrab yace "Kai dai ka karba Baffa" Alto ya karba da hannu biyu ya dinga sa masa albarka yana masu Allah ya tsare hanya har ya fita, Wanka Abuturrab ya shiga kewayen gidan yayi ya fito ya shiga Bukka, har lkcn bacci samantha take, ya shirya cikin kayansa da ya wanke jiya ya fita da na Baffa yana kallon Binta dake xaune tsakar gidan ita kadai yace "Baaba fa?" Bata kallesa ba tace "Ta je kauyen dake gaba da namu siyo gyero" yace "Ki ban sabulu xan wanke kayan nan" ta mike ta isa gabansa ta karba kayan tace "Xan wanke" yace "Noo, kar ki damu xan wanke" bata saurare sa ba ta nufi gun randar ruwansu ta diba, ya daga kafada ya juya ya koma daki ya bude flask din da ta basa ya ga kunu ne ya bude coolern ya ga kosai, diban kunun yayi ya dau kosan ya fita ya shimfida tabarma ya xauna ya shiga ci a nan, lkci lkci yake kallonta har ta gama wankin ta shanya kayan a igiyar dake tsakar gidan, ya koma inda take ta xauna, yace "Ke kin karya?" Gyada masa kai kawai tayi, yace "Yaushe Baaba xata dawo?" Tace "Kila tana hanya yanxu" yace "Bakya xuwa makaranta ne?" Ta kallesa tace "Yau alhamis" ya d'an buda ido yace "Haka fa" Bai kuma cewa komai ba, can tace "Bacci take ne?" Yace "Ehh" haka suka yi ta xama tsakar gidan shiru har Hansae ta dawo ya mike ya karbar mata kayan hannunta snn suka gaisa. Sai kusan tara da rabi Samantha ta tashi, har lkcn Abuturrab na xaune waje, ta mike ta dau sabulu da sponge ta fita, su biyu ne tsakar gidan shi da Binta dake wanke gyero, Samantha bata ko kallesu ba Abuturrab da ya bi ta da ido yace "Wanka xa ki yi?" Binta na jin haka ta mike tace "Bara in juye maki ruwan xafin ki" daga haka ta dau bokiti ta nufi gun murhu ta juye ruwan kai ta kai bokitin gun randa ta sirka ta kai kewaye tace "Bara in dauko maki sabulu" Samantha tace "Akwai sabulu a nn" Binta ta dauko kwando ta mika mata Samantha ta shiga bayin, mikewa Abuturrab yayi ya shiga daki.
*Haske writers asso*
Da fatan anyi sllh lfya Allah ya maimaita mana.
💫 *Noorul Huda*💫
By Khaleesat Haiydar📚✍🏻
32.....
Samantha na shigowa bayan tayi wanka bata ko kalli Abuturrab ba ta nufi gun kayan da ya siya ta durkusa, can ta kallesa taga kallonta yake ta bata fuska tace "Kaya xan sa?" Ya wara ido yace "Na rike ki? Ki sa mana" tace "Toh ka fita" murmushi yayi yace "In fita gun Binta ki kuma daure min fuska" daukar abinda xata dauka tayi ta nufi kofa ya fixgota tace "Wayyo ni ka kyaleni kaya na xan je in sa a waje..." Ya wara ido yace "Toh me xa ki boye min da ban sani ba jikin ki!" Ta yi masa wani kallo tace "Ae dai na wasu ka sani ba nawa ba malam" Dariya yayi ya kai bakinsa kunnenta yace "See you, ke nakin ma special sani xan masa, sanin da bbu wanda xai kara masu har abada.... Only me" kwace kanta take son yi ya ki saketa, ta boye fuskarta jikinsa kamar xata yi kuka tace "Bana son irin haka Doctor" yana dariya yace "Toh na daina baby, but a nan xa ki sa kayan ki" bbu yanda ta iya haka ta shirya a dakin, and he pretend he's not looking at her, tana gama shiryawa ya xuba mata kunu ya mika mata ta sha kadan ta ajiye kosan ma bata ci ba, yana kallonta yace "Xa mu tafi yanxu!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, can ta mike ta fara gyaran dakin, ya taimaka mata suka gama, sha daya suka fito xa su wuce, Hansai ta fito tana masu Allah ya tsare hanya tana cewa Allah sa ba shikenan an gama xumuncin ba, Abuturrab yayi dariya yace "In shaa Allah baxa mu mance ku ba Baaba wataran xa mu xo, dubu uku ya bata ta dinga godiya har da hawayenta, Abuturrab ya kalli Binta dake xaune nesa da su yace " Babu Sallama Fatima" kallonsu tayi yaga hawaye cike idonta, Hansai tace "Kaji shashanci to tashi ki rakasu mana" Samantha tayi ma Hansai sallama sannan ta fita, Ya karasa kusa da Binta ya durkusa yace "Nace maki xamu xo wataran fa..." Bata ce komai ba sae share hawayen idonta da take yace "Toh tashi ki raka mu" ba musu ta mike ta dau sandar ta na kiwo da nonon da ta tatsar masu yana gaba tana biye da shi a baya suka fita. Karasawa yayi ya kamo hannun Samantha yace "Baku yi sallama da Binta ba" ta kalli Binta ta gefen ido tace "Mun tafi Allah ya saka da alkhairi" kai kawai Binta ta gyada mata, daga haka yace "Mu je to ki raka mu inda xa mu samu Babur" gaba ta shiga suna biye da ita a baya, sun yi nisa sosai sai ga wata mota na tahowa a bayansu, Abuturrab yace "Wannan fa" Binta ta kalli Motar tace "Motar D'an lado ne, shi daya ne mai mota a rigar nan a birni yake aiki, da ka tsayar da shi ka ji inda xa shi ko?" Abuturrab ya tsayar da motar kamar yanda tace ae ko ya tsaya ya sauke glass, Abuturrab ya gaida sa mutumin da xai iya kaiwa arba'in ya amsa yana kallonsa, Abuturrab yace "Don Allah idan ba damuwa ina ka nufa?" Mutumin yace "Gombe xa ni...." Abuturrab ya d'an yi shiru, sae kuma yace "Toh mu ma can muka yi, xa a taimaka?" Mutumin yace "Ba matsala ku shigo" Abuturrab ya bude ma Samantha baya ta shiga ya rufe, ya kalli Binta da wasu hawayen suka cika idonta ya ciro dubu biyu duk da ya so bata fiye da haka ya damka mata a hannunta yace "Na maki alkawarin wataran xa mu dawo" da kyar ta yarda ya sa mata a hannunta ta mika masa nonon dake a leda ya karba yayi godiya sannan ya juya ya shiga front seat ya d'aga mata hannu ta juya da sauri ta bar wajen, D'an lado ya ja motarsa yace "Amma ba nn rigar kuke ba koh?" Abuturrab yace "Eh mu baki ne" D'an lado yace "Da alama kam, toh Allah ya sauke mu lafiya" daga haka ya maida hankalinsa kan tukin da yake da gani dae kasan hannunsa bai gama fadawa ba, ta madubi Abuturrab ya dinga kallon Samantha ganin yanda ta wani turo baki, dariya yake son yi amma ya dake, har suka isa gombe bayan tafiyar awa biyu da rabi bbu wanda yace komai cikinsu, Abuturrab sai kallon garin gombe yake yana tunanin to ina xa su, bbu wanda ya sani a gombe infact bai ma taba xuwa ba, D'an lado ya katse masa tunanin da yake yace "ina xa ku sauka kenan?" Abuturrab ya kallesa yace "Ko nan ne ka sauke mu" D'an lado yayi parking Abuturrab ya bude motar ya fita, ya xaga ya bude mata ita ma ta fito, ya karbi ledan kayan dake hannunta yayi ma D'an lado godiya ya ja motarsa ya wuce, kalle kallen wajen Abuturrab ya shiga yi, yana neman bankin da yake ajiya, yaga duka ukun a area din, yasan first bank da Gtb ba dai layi ba, hakan yasa yayi deciding ya shiga unity, ya kalle Samantha yace "xan shiga bank, sai ki jira ni waje or we go in 2geda" ta girgixa masa kai kawai tayi xamanta gaban bank din, shi kuma ya shiga ciki, direct ya tafi gun CC, bae wani jima ba aka xo kansa, yace yana son a duba masa ko nawa ne account dinsa, daga sama har kasa matar ke kallonsa, can tace "ATM din waje me yake yi, ko wayar ka fa?" Yace "Akwai layi sosai, waya kuma bani da, idan xa ki taimaka ki taimaka...." Da kamar xata yi magana sai kuma ta fasa, sai kuma tace "Fado account number" ya fada tayi danne dannenta snn ta kallesa ta kalli hotonsa dake jikin computer tace "Dubu dari shidda da ashirin" ya xauna yace "Good, na gode kwarai, ana sayar da withdrawal slip a nan?" Ta nuna masa gun da xai siya snn ta kira wani customer, yana xuwa ya dauka ya ciro dubu daya da aka ce ya bayar ya mika, ya ari pen ya cike slip din, dubu dari biyu ya saka yayi sign ya nufi gun Cashier, su ma sai da yayi masu jan ido wai wani yaje atm they re busy, yace "Haba wani atm xan je, ba fa dubu hamsin xan cire ba malam, kawai inje in bata ma masu cire dubu biyar lkci, awa nawa xan dauka ina cire dubu dari biyu? Plss answer me coz i wanna get out of here" Ba yanda suka iya haka suka karba bayan minutes din da basu wuce sha biyar ba suka basa kudin sa, nan ya roki alfarmar jaka aka basa ya xuba kudin yayi ficewarsa, ya isa gun Samantha yace "Am sorry Dear, tashi mu je" ta mike ya karbi ledan hannunta suka nufi titi, yana kallonta yace "Dear hotel fa xa mu je kafin mu samo solution" ta kallesa tace "Hotel?" Shiru yayi yana kallonta, ta dauke kanta, ya sauke ajiyar xuciya yace "Just for today dear.... Kinga bamu san kowa a gombe ba, it's my 1st time here" jin bata ce komai ba ya tsayar da mai adaidaita yace "Hotel mafi kusa xaka kai mu" sae da ya tsaya ta shiga sannan ya shiga, ba laifi hotel din na da kyau, ya biya kudin kwana daya dubu ashirin da biyar a reception aka basa makulli da room number, babban daki ne sosai da toilet a ciki, ya kalli samantha da har lkcn ta ki cewa komai ya xauna bakin gado bayan ya ajiye ledan hannunsa yana kallonta yace 'You followed me without trusting me kenan Samha..." Bata bari sun hada ido ba ta karaso dakin a sanyaye ta xauna can karshen gado, girgixa kai yayi ya mike ya bude jakar dake dauke da kudi ya cire dubu dari, ya sa a aljihu yace "Am coming back right away, me xa ki ci?" Cikin sanyin murya tace "Anything" ya juya ya fita ya kulle dakin, tagumi tayi tana tunanin anya did she made the right decision following him and neglecting her dear parent, hawaye ya cika idonta ta fada kan gadon ta fashe da kuka, Why is all this happening to her within just 2 months, she know God will never forgive her for doing this to her parent, but she love him and they will never allow her to be with him, tayi kukanta me isarta ta mike ta dau soap da sponge, toothpaste da sponge ta shiga bayi dake dakin, wanka tayi ta fito ta shirya tayi kwanciyarta nan da nan bacci ya dauketa, bayan azahar Abuturrab ya dawo, ya ajiye ledan hannunsa yana kallonta, bai tada ta ba ya shiga toilet ya dauro alwala ya xo ya gabatar da sllhn Zuhur, ya jima xaune yana addu'a daga bisanni ya mike ya shiga bayi yayi wanka ya fito ya shirya cikin daya daga cikin kananun kayan da ya siyo, ya bude fried rice din da ya siyo masu da drinks ya ci wanda xae ci ya ajiye sauran, kwalin karamar waya ya dauka ya bude ya ciro wayar ya sa sabon sim din da ya siyo ya kunna wayar, ya loda airtime yayi dialing number Hajiya Mariya gabansa na faduwa a xuciyarsa kuwa addu'a yake Allah yasa ita kadai ce a gun, bugu daya biyu ta d'aga, ya shafa kai a hankali yace "Mumy!" Hajiya Mariya dake xaune daki tare da Mami da frnds dinta biyu, ta saci kallon Mumy ganin kallonta take tace "Helloo!" Abuturrab yace "Ina ji Mumy ina yini...." Hello... Hello... Abinda ta dinga cewa kenan can tayi tsaki ta katse, Hajiya Maimuna tace "Network koh?" Hajiya Mariya tace "Ae kuwa...." Hajiya salaha tace "Toh da ki fita waje...." Hajiya Mariya ta tabe baki tace "Kila kiga ya dawo kuma" Abuturrab da sharp thinking yana jin reaction dinta yasan ba ita kadai bace a gun don haka bae sake kira ba, Mikewa Hajiya Mariya tayi tace "Bari dai ban san ko masu bani kudi bne bari inje waje" daga haka ta fita, bata ko kalli Abba dake parlor da abokansa ba tayi ficewarta waje, Abba ya bi ta da kallo, can ya girgixa kai yace "Wannan Mariyar ma ban yrda da ita ba bakinsu daya da Aliyu, ba abun mamaki bne ma tasan inda yake!" Col Usman na girgixa kai yace "ban taba ganin mai taurin kai da tsaurin ido irin Aliyu ba...." Abba yace "Duk ya kuskura ya shigo hannuna wllh sae bullet ya kare a kafafuwansa..." Har kofar gida Hajiya Mariya ta fita sanin halin mijin yayarta, tana fita ta kira number da sauri, Aliyu naganin kiranta ya daga, tace "Aliyu!!" Ya buda ido yace "Mumy..." Tace "Kuna ina Aliyu?" Shiru yayi, tace "Ohh ni din ce yanxu kuma baxa ka gaya ma inda kake ba" yace "Ke kina ina Mumy" ta hade rai tace "Ina tambayarka kana tambayata..." Ya sauke ajiyar xuciya yace "Kiyi hakuri Mumy, but don't say anything to anybody plss...." A fusace tace "Uwarka! ni kake gaya ma haka da can ban ce komai ba sae yanxu" bae san lkcn da yayi dariya ba yace "Yi hakuri Mumy, ina Gombe!" Ta xaro ido tace "Gombe kuma Abuu, wa ka sani a can?" Ya girgixa kai yace "Ba kowa wlh..." Da damuwa tace "Yarinyar fa?" Ya kalli Samantha dake ta bacci yace "Ga ta Mumy, she's sleeping" Hajiya Mariya tace "Kaji tsoron Allah Aliyu, kada kayi using wnn advantage din a kan baiwar Allah don tana sonka, kar ka manta ba fa matar ka bace, don't use her....." A sanyaye yace "Mumy baki yadda da Aliyun ki bane kuma, kema kin san ba hali na bane" Hajiya Mariya tace "No son! Kasan sha'anin rayuwa, bbu abinda shaidan baxae iya yi ba...." Sosai jikinsa yayi sanyi yace "In'sha Allah Mumy xan kiyaye.... Mami fa?"
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
33....
Hajiya Mariya tace "She's inside" ya d'an yi shiru sai kuma yace "Abba fa" tace "Yana nan.... But you re in trouble in har ka shigo hannunsa" Aliyu yayi murmushi yace "Na sani" da damuwa tace "Ka dai kula Aliyu tausayin yarinyar nake, tunda har ta guji iyayenta sbda kai, jan ra'ayinta xuwa musulunci baxai yi wahala ba" Yace "Hakane Mum, dama am planing of marrying her soon don ban son in cuceta, i don't want her to regret trusting me, idan nayi haka komai xae fi zuwa da sauki" Hajiya Mariya tace "Anya, naga kamar ya fi ka jira sae ta amshi musulunci, kar ta ga kamar kana using advantage din auren ne..." Bude gate ta ji anyi da sauri tace "Za mu yi waya Aliyu, don't call again xan dinga kiran ka..." Daga haka ta katse wayar, Abba ta gani bakin gate waya kare a kunnensa ya rako abokansa xa su wuce, tayi dialing din number wata da xata bata kudi suka yi magana snn ta juya ta nufi gate din ya bata hanya tayi wucewarta, bin ta yayi da kallo har ta shiga cikin gida, ya juya ya koma ciki shi ma bayan abokan sun shiga mota, ya shiga part dinsa ya kira Mami, bbu bata lkci Mami ta iso, yana tsaye bakin window rungume da hannunsa (Inda Aliyu ya gado rungume hannu knn, lol" ya juyo yana kallonta yace "Hajarah! i won't take it likely with ur sister idan naga da sa hannunta a abubuwan nan da Aliyu yake, xan ajiye cewar yar uwarki ce a hukuntata yanda ya kamata...." Mami tace "Ban yi mamaki ba... You can do more than that, yanxu kuma ka bar xargina ka koma xargin yar uwata" ya daga kafada yace "Ni dae na gaya maki" juyawa tayi ta fice daga dakin, dakin su Ramla ta shiga ta ci kukanta Ramla na lallashinta kafin ta fita ta koma dakinta, Hajiya Mariya na ganin Abba ya kira Mami dama ta yi saving din number Aliyu da wani suna daban tayi deleting dinsa daga call log, ko da Mami ta shigo dakin Hajiya Mariya na bathroom, ta dau wayarta ta fita, kiranta na karshe ta kura ma number ido, can tayi dialing taji muryar mace, ta dudduba dai bata ga alamar komai ba ta koma daki, Hajiya Mariya bata tambayeta dalilin daukan wayarta ba sae harkan gabanta take. Tunani Abuturrab ya dinga yi ko dai gida xae kama masu nan gombe ne, duk ya rasa takamaiman solution, kallonta yayi ganin tana juye juye kan gado, can ta mike xaune yace "Cikin ya fara koh?" Ta gyada masa kai, ya mike ya dauko mata abinci yace "Sauko ki ci in maki allura" ba musu ta sauko ya bude mata abincin ta fara ci, alluran ya hada ya ajiye yana jiran ta gama, bata wani ci da yawa ba ta mike yace "Sauran fa" da kyar tace "Anjima xan ci" daga haka ta kwanta ya mike ya karasa kusa da ita yayi mata alluran, Finger dinta ya kura ma ido ganin har lkcn xoben da ya sa mata na nan, ya kama hannunta a hankali yace "Samha!" Dago kai tayi ta kallesa, ya sakar mata murmushi ya kai lips dinsa kan hannun cikin sanyin murya yace "I will never let you down dear, i will be ur hero, i will be ur everything...." Hawaye ya cika idonta ya dago ta ya rungumeta, ta fara kuka a hankali, jin tayi shiru ya dago kanta a hankali ya ga idonta a lumshe, kwantar da ita yayi ya mike ya nufi window yana tunanin next action din da xae dauka, can ya dau kudi ya fita, wani me taxi ya tsayar bayan tsayuwar kusan minti sha biyar a bakin titi duk yana duba responsible cab man da xae tsayar su yi magana, yana kallon mutumin yace "Pls ina d'an tambaya ne" cab man din yace "Allah yasa na sani" Abuturrab na shafa beard dinsa yace "Kasan inda xan samu agent... I mean their office, anywhere around?" Mutumin yace "Wae na gida?" Abuturrab yace "Yes!" Mutumin yace "Wanda na sani da nisa daga nan, sae dai..." Abuturrab yace "No mu je kawai ka kai ni" daga haka ya shiga mutumin ya ja taxi din. Tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso office din wasu agent, Abuturrab ya fito yayi masa godiya ya basa dari biyar ya shiga office din, ba shi ya fito ba sae kusan karfe shidda bayan an basa tabbacin nan da xuwa gobe xa a karbar masa gida. Ko da ya dawo lodge dinsu tana bathroom tana wanka, ba a dau lkci ba ta fito daure da towel, tana ganinsa ta tsaya nan bakin kofa, yace "Naga alamar ba kya gajiya da wanka yarinyar nan...." Murmushi tayi bata ce komai ba ya mike xae shiga yayi alwala ta durkusa da sauri tace "Nooo" xaro ido yayi yace "Ina ruwana da ke?" Murmushi yayi ya shiga toilet din, ta mike da sauri. Ko kafin ya fito har ta gama shiryawa, yana kallonta yace "Xan je mosque, will be right back" ta gyada masa kai ya fita, sae bayan Magrib ya dawo dakin, ya ganta xaune shiru da alamar tunani take, ya karasa kusa da ita ya durkusa ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace "Sorry Dear, na jira anyi magrib ne" ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, ya xauna ya bude mata ledan fruits din yana kallonta, Apple ta dauka ta kai baki a hankali, shi ma ya dauka ya kai daya baki, wayarsa dake kan gado ya fara ring, ya dauka yana kallon screen din yaga Hajiya Mariya ce, ya daga ya kai kunne yace "Hello Mum!" Tace "Aliyu where is she?" Kallon Samantha yayi ya mika mata wayar yace "My mum!" Ta sa hannu ta karba ta kai kunne, Hajiya Mariya tace "Ya kk Samha?" Samantha tace "Lafiya Mumy ina yini?" tace "Lafiya lau, kiyi hakuri kin ji, Allah na tare da ku, kar ki sama kanki damuwa...." Kai kawae Samantha ke gyada mata kamar tana ganinta.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
34.....
Mikewa tayi a hankali ba tare da ta kallesa ba ta dau rigar baccin ta shiga bathroom, ba a dau lkci ba ta fito, kallo daya yyi mata ya dauke kai, ta nufi kan gado a hankali ta kwanta ta juya masa baya, bayan kusan minti goma ya mike ya cire shirt din jikinsa ya shiga bayi, ko da ya fito kashe tvn dake aiki yyi ya kashe wutan dakin ya karasa gado ya kwanta, a hankali ya birgina inda take, cikin sanyin murya tace "Doctor..." Yace "Samha...." Bata ce komai ba ya juyo da ita ya kwantar da ita kan faffadan kirjinsa yace "Sleep tight love, am with you" ta lumshe ido tayi lamo jikinsa, a haka har bacci ya dauketa, a hankali ya kwantar da ita ya mike ya koma kujerar dake dakin yayi kwanciyarsa amma ya kasa bacci sae juye juye yake, can dae ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito ya tada sllh, sae kusan karfe uku da rabi ya samu yayi bacci, da asuba a masallacin dake cikin Hotel din ya fita yyi sllh sae da gari ya waye ya shigo masu dakin da breakfast, har ta shirya ya sameta, yana kallonta da mamaki yace "Ina fita kika tashi amma koh?" Kai kawai ta gyada masa, yayi murmushi yace "Alryt xo kiyi break kafin in shirya" daga haka ya shiga bathroom, ko da ya fito har ta gama cin abinda xata ci, yace "Are you sure kin koshi?" Ta gyada masa kai, shiryawa yayi ya ci chip da egg din kadan ya mike yace "Bacci nake ji Samha, let me sleep small" murmushi tayi ta mike xata gyara masa gadon yace "Noo don't worry dear...." Daga haka yayi kwanciyarsa, ta koma ta xauna ta rufe sauran breakfast din, yana kwanciya bacci ya daukesa, ita dai tana xaune idonta a kan tv, sae dae ko kadan ba sanin kan film din da ake tayi ba, tayi nisa a tunanin da take, Abbanta kawai take tunani wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, why did she accept to leave her family because of Aliyu, hade kanta da kujera tayi hawaye na sakko mata sae a snn take jin bata kyauta ba, tayi kukanta mai isarta daga nan ita ma bacci ya dauketa don yanda bai yi wani bacci ba haka ita ma bata jiya ba daren jiya duk tana kallonsa yana sllh, sai kusan goma da wani abu Abuturrab ya tashi, ganin yanda ta kife kai ya mike da sauri ya isa gabanta ya dafa ta yace "Samha" dagowa tayi da sauri tana kallonsa, kallon idonta ya dinga yi, da damuwa yace "Kuka kika yi?" Ta sunkuyar da kanta ya dago ta yace "Samha you re regretting everything koh?" Ta fashe da kuka tana girgixa masa kai, duk ya rikice yace "No plss samha, kar ki min kuka don Allah, naji xan maida ki gida...." Da sauri ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "Am not regretting" yace "Toh me yasa kike kuka" goge hawayenta ta shiga yi cikin sanyin murya tace "Its just.... We re in trouble" ya lumshe ido ya kamo hannunta yace "Allah na tare da mu Samha, kar ki damu kin ji" sunkuyar da kanta tayi, yace "Tashi ki raka ni!" Ba musu ta mike ya kashe kayan kallon yace "Mu je" kofa ta nufa ya bi bayanta, suka fita ya kulle dakin, gun agents din jiya ya tafi, suna isa daya daga agent din yace su je ya ga gidan ko yayi masa, a motar agent din suka tafi, gida ne babba hadadde mai flats biyu, gidan na dauke da dakuna uku manya, Abuturrab ya kalli Samha yace "You like it?" Sunkuyar da kai tayi, yayi murmushi yace "Alryt, yallabai gidan yayi, thanks much" bbu bata lkci Abuturrab ya biya komai na gidan kusan 450k, da yamma bayan sun dawo hotel din yace "Xuwa jibi sae mu koma can koh dear?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace "Kin yi shiru?" Murmushi tayi bata ce komai ba. Washegari Abuturrab shi kadae ya fita ya bar ta tana bacci don xuwa can gidan ya ga abubuwan da ya kamata ya xuba, a ranan yayi furnishing gidan gaba daya, har food stuffs sae da ya siya, ya kashe kudi ba na wasa ba, da yamma ya koma hotel, Wanka ya sameta tana yi, yyi kwanciyarsa don ya gaji, washegari da ya kasance alhamis misalin sha daya suka tafi can gidan, nan ya fara tunanin anya xae yi ynda Hajiya Mariya tace masa kuwa, bai jin xae iya xama gida daya da ita bayan ba muharramar sa bace, idan shaidan bai ci galaba kansa yanxu ba yasan ko a jima ko a dade akwai ranan da abinda yake gudu xae iya faruwa, don yanxun ma he's just fighting his self from inside, kwanciyarsa yyi a parlor yana tunanin next step din da xae dauka, ana kiran Azahar ya mike ya shiga toilet dake nn parlor ya daura alwala ya fita xuwa masallaci, ko da ya dawo a kitchen ya sameta ta daura girki, ya rungume hannayensa yana kallonta yace "Weldone dear..." Murmushi kawae tayi ta ci gaba da wanke shinkafar da take yi, ya juya ya fita xuwa balcony yayi xamansa, wata dattijuwa da baxata wuce 50 ba ce ta fito daga daya flat din idonta sanye da medicated ta rike jaka ta nufi parking space dake part din nasa ta bude daya daga motocin dake wajen ta shiga ta tada, horn tayi bayan ta fito compound din, Abuturrab ya kuma kallon motar ya dauke kai don yasan lkcn da yake dawowa daga masallaci lkcn mai gadin ya tafi, tayi horn yayi sau uku, can Abuturrab ya mike ya isa gate din ya bude mata, sauke glass tayi ta karasa gate din da motar tana kallonsa murmushi dauke fuskarta tace "Nagode kwarai..." Ya dukar da kai yace "Ina yini?" Tace "Lafiya lau, kai ne new tenant din Apartment din can kenan?" Kai ya gyada mata yace "Nine..." Tace "Maa sha Allah, you re welcome, tare da mai dakin ka koh?" Ya d'an yi jim sai kuma da sauri yace "Ehhh" tace "To sannun ku da xuwa, ni ce occupant din flat din can with my 3 kidz... Hope xa mu dinga ba makwabtaka hakkin sa" murmushi yayi sosai yace "In shaa Allah" ita ma tayi murmushin tace "Maa sha Allah, it's nyc meeting you, na fita aiki sae na dawo" yace "Toh Allah ya tsare" daga haka ta ja motarta ta fita ya rufe gate din, haka kawai yaji matar ta burgesa sae yake ganinta kamar Maminsa, yana murmushi ya koma balcony yayi xaman sa. Shinkafa da miya Samha ta girka tana gamawa ta fito ta gansa har lkcn yana balcony, ta jingina jikin kofa tace "Na gama" ya kalleta ya wara ido yace "Weldone sweetheart" murmushi tayi ta juya ta koma ciki ya mike ya bi bayanta, a tare yasa ta xuba masu abincin don yana son ta ci da yawa, ai ko haka yayi ta forcing dinta har suka cinye abincin, ya tagumi yace "But wa ya koya mamaki girki haka dear?" Tace "Uhm My mum" ya lumshe ido yace "You are a very good cook" a hankali tace "Thank you..." Yace "No thanks baby, bari in je masallaci it almost time for salat" tace "Toh" ya mike ya shiga toilet ya daura alwala ya fita, ta kwashe plates din don xuwa kitchen ta wanke.Bayan magrib yana dawowa daga masallaci matar daxu na shigowa, tsayawa yyi har tayi parking ta fito kafin tace komai ya gaisheta, da fara'a ta amsa tace "Mai dakin naka na ciki in shiga mu gaisa mu san juna..." Yace "Da ki bari xamu shigo yanxu tun da daga aiki kike ai" tace "Toh shknn ina jira" daga haka ta nufi bangarenta. Abuturrab ya juya ya shiga cikin gida, bedroom ya sameta yace "Samha, taso mu gaisa da new neighbor dinmu" ta kallesa tace "Do we need to?" Yace "Yess dear!" Mikewa tayi yace "Ki sa Hijab..." Ba musu ta dau daya daga sabbin Hijabs din da ya siya mata ta saka snn suka fita yana gaba tana biye da shi a baya, kararrawa ya danna ba a dau lkci ba wata yarinya da baxata wuce Samantha ba ta bude kofar, kallonsu ta shiga yi, Abuturrab yace "Hello, mum dinku na ciki koh?" Ta basu hanya tace "Ehh, welcome" Abuturrab ya shiga parlon Samha ta bi bayansa, sosai parlon ya hadu da gani dai kasan Naira ta xauna, xama yayi kan kujera ya nuna ma Samha gefensa ta xauna, yarinyar ta wuce ciki sae ga ta tafito tare da Mum din tasu, da fara'arta ta karaso parlon tana kallon Samha tace "Sannunku da xuwa" Samha ta sauke kai kasa ta gaisheta, ta amsa mata da murmushi tace "It's nyc meeting you... Ya sunan ki?" Satan kallonsa Samha tayi, yana murmushi yace "Samha!" matar tayi murmushi ita ma tace "toh kai fa?" Yana shafa kai yace "Aliyu...." Ta buda ido tace "Maa sha Allah ashe Abbana ne, amma sabon aure kuka yi koh?" Yar dariya yayi yace "Ehh haka ne" tace "Ae naga alama, Allah ya kawo Zuri'a dayyaba, ni sunana Hajarah...." Wara ido yayi yace "Mum dita knn..." Tace "Kai haba, shknn na samu d'a kuma babana..." Yayi dariya tace "Allah kuwa, muna xaune da kidz dina uku a nan, babban son dina Muhd na Uk, sai kanwarsa Maryam da ke Cairo tana aure, snn Fatima da Khadija da autata Rabi'ah, Ba mu yi shekara a garin Gombe ba don da a Abuja muke, yanxu haka ma Mai gidan na can sae dai yaxo week ends, am running my late dad's clinic dake nan ne shi yasa...." Abuturrab ya kalleta yana murmushi yace "Maa sha Allah Mami, Allah yayi jagora" tace "Ameen, amma a gombe ku ke?" Ya girgixa kai yace "A'a kano muke..." Tace "Ikon Allah, toh Allah dai ya bada zaman lafiya, kaga bata da kowa nn dont make her feel lonely ka dinga kyautata mata a ko da yaushe Abbana" yace "In shaa Allah Mami nagode" Hajiya Hajarah ta kalli Fatima dake xaune tana dannan waya tace "Ko ruwa baxa ki kawo masu ba Teemah" Abuturrab yace "Noo Mami Alhmdllh, xamu koma ne ynxu" Hajiya Hajarah tace "Toh shknn Boy, na gode kwarai" yar dariya yyi ya mike ya kuma yi mata sallama haka ma Samha snn suka fita. Sae da suka koma part dinsu yana kallonta yace "You like her?" Murmushi tayi ta xauna bata ce komai ba, da damuwa yace "Why ba kya son magana Samha, you re just nt ur self" ta wara ido tace "Ba komai fa, is just change of environment" yace "U will like it soon dear, nt when am with you" murmushin dae tayi, ya gyada mata kai snn ya shiga daki. A parlor yyi isha sbda hadarin da ya hadu ga iska ana yi, ita dai tana xaune parlon sae kallonsa take har ya idar, yana kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "Ko kema kina son ki iya sllhn ne?" Tace "Uhmm" yace "Yeah dear sae in koya maki it's nothing ae" yar dariya tayi yayi shiru yana kallon fararen hakoranta tace "Wa yace maka ban iya ba?" Yace "A ina kika iya?" Tace "Uhm, na xauna gun kanwar Abbana Anty Aisha a kaduna, during my jss can nake xuwa yin long holiday, idan su Mumy xa su Jerusalem can ake kai ni, tare take hada ni da yaranta mu je islamiyya, in dai xa ayi sllh nima sae nayi a gidan, har na xo na saba idan na dawo gida sai in ta yin irin abubuwan islam shknn Mumy ta hana Abba ya kai ni kaduna kuma, at that time ina jss3, har yau kuma ban sake xuwa ba" Abuturrab dake ta kallonta ko kiftawa bbu yace "Yanxu kin iya alwala knn?" Tace "Uhm har da sllh ma, kasan suran da muke lkcn a islamiyyar da muke xuwa?" Da sauri yace "A'a" tace "Mulk" ya lumshe ido yace "Kuma kin iya?" Dariya tayi tace "May be xan iya yi da qur'an because i know the arabic letters very well" kallonta kawai yake can yyi murmushi yace "Gobe xa ki min in ji" mikewa tayi tace "Xan yi bacci...." Yace "Ohk dear ki rufe windows sbda ruwa" kai ta gyada masa ta nufi daki tana adduar Allah yasa kar ayi ruwan sbda tsoron tsawa da take. Washegari da safe wajajen karfe tara tana daki tana bacci Abuturrab kuma na xaune parlor sae missing system dinsa yake ga parlorn bai sa kayan kallo ba tukun, yasan accnt dinsa ya d'an girgixa da cire ciren kudin da yake in kuma xa aci gaba da haka to fa karewa xa suyi, ga credentials can gida bare ya fara neman wani aiki, Tausayin Maminsa kawae yake amma in dan Abbansa ne ko a jikinsa don dama sun saba irin haka, Ring din bell aka yi, ya mike yana kallon kofar, can ya karasa ya bude, daya daga yarinyar Hajiya Hajarah ce tsaye bakin kofar rike da basket me dauke da breakfast, ya d'an koma baya, tace "Mum tace a kawo" yace "Ohkk thanks soo much" daga haka ya karba ta juya ta wuce, ya koma parlor ya ajiye, ji yyi matar ta burgesa sosai sae yake jin ta a ransa kamar Mami, bude abincin yyi yaga wainar shinkafa ce ta miya sae brown yam and egg da fries egg with plantains, a wani karamar warmer kuma ga Irish, murmushi yayi ya koma yyi kwanciyarsa kan kujera, sae kusan karfe goma Samha ta fito cikin shirin doguwar riga amma ba abaya ba, karasowa tayi parlon ta xauna kasa ta sunkuyar da kai ganin yanda yake kallonta cikin sanyin murya tace "Ina kwana" ya mike xaune yace "Lafiya lau dear, ashe kin iya bacci kema haka" murmushi tayi bata ce komai ba, ya nuna mata breakfast yace "Gashi Mami tace a kawo mana" ta kalli abincin a hankali tace "Mun gode" ya mike tsaye yace "Dama ke nake jira, let eat" ba musu ta mike suka isa gun breakfast din. Da rana mai aiki ne ta kawo masu lunch, Abuturrab ya karba yana kallonta yace "Hajiya na nan ne?" Ta girgixa kai tace "Ta fita aiki tun safe" yace "Alryt" Da yamma bayan la'asar yana zaune bakin gate tare da mai gadin gidan Hajiya Hajarah ta dawo, gaisheta yayi ta amsa da murmushi tace "Ya gidan?" Yace "Alhmdllh Mami ya aiki?" Tace "Alhmdllh, ina Samha?" Yace "Tana ciki" tace "Toh a gaisheta" yace "Mami mun gode for the food" tace "Ohh it's nothing Boy" daga haka ta ja motar ta ta shiga gidan.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
35....
Yau kwana goma sha hudu da xuwan su Gombe, yana xaune parlor laptop a gabansa sae dai gaba daya hankalinsa baya kan abinda yake, damuwarsa daya yanda yake cire kudi a account gashi ba shigowa wasu ke yi ba, at all shi bai iya sana'a ba bae ma san yanda ake yi ba, he don't want to run short of money, ya lumshe ido ya rike kai yana tunanin mafita, dago kai yayi bayan kusan minti goma jin fitowar Samha daga kitchen, kallonta yake har ta karaso parlor ta xauna, ya sakar mata murmushi yace "Weldone" jin bata ce komai ba yace "Dear!" Ta kallesa ya ce "An fara Reg din Jamb, gobe sae mu je ki yi koh?" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, yace "Yeah gobe da safe in shaa Allah" daga haka ya mike ya shiga daki. Suna breakfast the next day ya sa ta shirya suka fita reg din Jamb din, sae kusan da rana suka dawo gida, bae bari tayi girki ba ya fita ya siyo masu abinci, daren ranan ya dinga tunanin ko dae ya kira small mum dinsa yyi mata maganar CV dinsa ne, yanke shawarar yin hakan yayi daga karshe, washegari lahadi yana xaune balcony ya hango Hajiya Hajarah xaune daga nata Balconyn da laptop gabanta, ganin ta kallo inda yake ya mike ya nufi gun ta, ya d'an dukar da kai yace "Ina kwana Mami?" Tana murmushi tace "Lafiya lau Boy, ya gidan?" Yace "Alhmdllh..." Tace "Ina Samha?" Yace "Tana ciki Mami" tace "Alryt wai in tambaye ka boy..." Kallonta yayi da sauri yace "Ina ji Mami" ta ajiye pen din hannunta ta nuna masa kujerar gabanta tace "To xauna" Ba musu ya xauna tace "Transfer aka yi maka xuwa garin nan?" Ya sunkuyar da kai yace "A'a Mami" tace "Ohk, naga kuma har yanxu baka koma aikin ba ko hutun mai yawa ka dauka, or rather let me put it this way...." Shiru ya d'an yi sai kuma yyi murmushi yace "Mami bana aiki yanzu" da mamaki tace "Baka aiki kuma?" Shiru yayi nan ma, ta sauke ajiyar xuciya tace "It's ohk Boy kar in shiga rayuwar ka koh!" Yar dariya yayi yace "Noo Mami ba haka ba, laifi nayi ma Abbana ya amshe CV dina and everything, that was why i left kano" kallon mamaki take masa, can ta girgixa kai tace "Duk a dalilin auren da kayi knn?" Ya gyada mata kai yana murmushi, tace "Toh ba a son yarinyar ne a gidan ku" nan ma ya gyada mata kai, tayi shiru tana kallonsa, sosai ta ji tausayinsa, can tace "But me yasa ka xabi aurenta da kayi ma iyayenka biyayya" A hankali yace "Mami haka Allah ya so" tace "Toh iyayenta fa?" Yace "Su ba ruwansu" Tace "Satin ku nawa da auren yau?" Yyi shiru kamar mai nazari sai kuma yace "Sati biyu da kwanaki" girgixa kai tayi tana kallonsa tace "Ur field?" Dago kai yayi ya kalleta yayi d'an murmushi yace "Am a Medical Doctor" kallonsa kawai take kafin tace "A doctor?" Yace "Yes Ma'am" ta cire glass din idonta tace "Where did you schl?" Yace "Uk nayi karatu Mami!" Tace "Ina matakin karatun naka?" Yace "Nayi degree, snn nayi masters duk a fannin medicine..." takardar dake gabanta ta dauka da pen ta mika masa tace "Am ur patient suffering from Malaria Typhoid, prescribe me drugs and injections...." Yar dariya yayi ya karbi takardar yace "Alryt Ma'am" ya gama rubuce rubucensa bayan kusan minti shidda sannan ya mika mata takardar ta karba ta sa glass dinta tana kallo, gyada kai ta shiga yi, sai kuma ta mika masa wani takardan tace "Prescribe for someone suffering from chronic stomach ulcer!" Karba yayi ya kuma rubuce rubucensa ya mika mata, ta karba tana dubawa tace "Um! Yayi kyau, kana theatre ne?" Yace "Ina yi Mami" ta basa wani takardan tace "Rubuta min procedure din yanda xa ayi operating din patient that's suffering from Appendix...." Karba yyi cikin yan mintuna ya gama ya mika mata ta karba tana kallo, murmushi tayi tace "Alryt Doctor, am offering you work at my clinic daga gobe, sai ka shirya da safe mu fita tare..." Ya buda ido yace "Am soo grateful Mamina" tace "My pleasure, but try to reconcile with ur parent kaji boy, kar mace ta hadaka da iyayenka" a hankali yace "In shaa Allah Mami" aikin da take yi a laptop ta juya masa gabansa tace "Idan baxan takura ka ba pls go on with this it's understandable, am already exhausted dama..." Yace "Alryt Mami" daga haka ya fara duba abinda take yi, duk abun nn da suke Fatima na lekensu don tun da taji muryarsa ta taho da sauri ta labe, tana ganin uwarta ta mike ta bar gun da sauri, Hajiyar na kallonsa tace "Xaka iya tafiya da shi boy, idan ka gama sae ka kawo min" yace "Alryt Mami," daga haka ya dau system din da takardun dake ajiye yayi mata sallama ya wuce, ita kuma ta shiga ciki, shara ya tadda samha tana yi a parlor ya girgixa kai ya xauna yace "Kin san me?" Ta kallesa ta ce "Mene?" Yace "Three things you never get tired of are, bathing, cooking and sweeping i notice" dariya ya bata sae dai bata yi ba tayi murmushi ta xauna tace "Toh sae ka tashi kayi" ya wara ido yace "Haba in tashi in yi" ta hararesa tace "Ehh" mikewa yayi ya nufi gun da ta ajiye broom din ta dauke da sauri kafin ya isa, karba yake son yi taki sake masa tace "Nooo, ka kyaleni...."
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
0 comments:
Post a Comment