Adaran aka Kira Dr yazo yaduba MINISTER yaimasa dinki nabil ma se da Dr ya dubashi har da su allura Dan ya samu bacci
Iya kwana tayi tana ta ruwan masifa Akan abinda nabil da babansa sukai musu hadub kuwa ta yanda shatuwa zata zauna da su tashata wajan iya gajiya shatuwa tayi da sauraran iya har bacci yakwasheta sannan itama iyan tasamu waje ta kwanta
Washegari da safe bayan anhada abin karyawa Amina tace mommy yazaayi wajan cin abincin safe kinsan dai inhar gabadaya za ahadu aci har da su daddy da su iya to wlh ba abinci zamuciba raban fada zamuci Dan Haka meye abinyi Ni wlh baffah nafijin tausayi shine me Shari,a jiya fa se da na Kai Masa maganin ciwan Kai yasha bayan yaci abinci Allah yabani tausayi to yanzunma in har aka hadasu waje Daya to tarihi zekuma maimaita kansa Dan Naga daga iya har daddy Babu me gudun abin kunya Akan aurannan Dan basa ganin mutuncin juna kowa nashi yakeso baa Kuma mgnar ango da amarya wayannan Kuma se Dua,i jiya dazan kwanta nasha dariya sosai Ni mantawa ma nayi da har awaya Zan daukeso du ranan da suka shirya na nuna musu abin kunyar da sukayi ranar auran shatuwa da Nabil Ni tin Ina mamaki har abin yakoma bani dariya yanzu mommy me kikece Amma Dan Allah abar baffah yagama huta gajiyar jiya in kin yarda kowa akai masa abin karyawarsa har inda yake jiya har wasu daga Yan iakin gidannan sunsan meyafaru jiya har kunyarsu nadinga ji su da abin kunya mu da Jin kunya Allah yakyauta
Hajiya Fatima tace eh Haka zaayi Amina kisa akaiwa iya da shatuwa nasu alhaji da nabil mu hadu muci tare baffah shima akaimai nashi gwara da mijinki yabarki Kika kwana da abin yamin yawa ai wannan Kuma Babu maganar muje mu kama waje ayi Dinner Dan abin kunya zasu barmana Kuma ba damuwarsu bace Da ni yanda na tsara abokan nabil da na shatuwa da mu kanmu iyaye du zamu hadu mu tayasu murna Amma yanzu fitinarsu bazata bariba ayi abin arzikiba daga iya da alhaji har amarya da angwan Dan Haka mun hakura ahadu ahidimar haihuwa in Allah yashryasu suka haihu mayi shagalin suna Allah yabasu zaman lfy
Amina ta amsa da ameeeen
Amina ce da kanta Tai sallama takaiwa su iya abin Kari tare da rakiyar Yar aikin gidan
Amina tace iya antashi lfy yagajiyar jiya ya kwanan kanwar tamu shatuwa Babu mgn ko du gajiyarce tana dariya ta karasa mgnar
Iya tace lfyklau yarnan ainaga ke da matar gidan Kuna da mutunci bakamar ebanbuncanba wannann hajiyar itace ta haifi rabi mutun rabi aljani kema Kuma yayar sace
Amina tace eh iya wannan itace mahaifiyar mu uwa Daya uba Daya muke da nabil
Iya tace Amma albasa batai halin ruwaba ammafa hajiya na hakuri da ubanku da wannan Dan kwal uban yaran
Dariya Amina tayi tace iya tamu Kuma kakarmu amarya awajan mijin shatuwa to iya ke da angwan naki haka zakuyi zaman auran ko dai kishi kike Dan jiya ya auro shatuwa ya Miki kishiya
Iya tace Allah yakiyaye ajikoki wannan yazama jikana yaran da tashin farko ya karyamin jika jiya Nima yakusa karyani Allah ne ya kwaceni yaro da shegen karfi se kace me kashin mindiriki
Me Amina zatayi inba dariyaba tace iya tamu Bari na barku ku ci abinci anjima zandawo muyi hira
Ficewa Amina tayi tana dariya tana mamakin rikicin tsufa irin na iya
Lokacin da Amina takoma taje tatarar har nabil da MINISTER sunfito sun fara karyawa
mommy tace mu har munfara mungaji da jiranki
Amina tace Hira muka tsaya yi da kawar nabil iya
Nabil da MINISTER wani kallo su kaiwa Amina Babu shiri taja bakinta Tai shuru
Kowa yayi shuru ana ta cin abinci Babu zato Babu tsammani se muryar iya akaji tashigo tana masifa hannunta dauke da kulolin da Amina takai musu na abin Kari tare da rakiyar shatuwa
Salati hajiya Fatima tafara tace shikenan Allah yai dare gari yawaye za afara Kuma ko karyawa ba mu gamaba bare ya tsirgamana iya ke dawa me yafaru yihakuri ki fadamin
Iya tace Ina suke ebanbunnan wajansu nazo nasan da sa hannunsu sune zasusa aimana wannan abincin azaman abincin safe ke dai nasan babu ruwanki kina da kirki ba kamar wayancan Marasa mutuncin ba yauwa Ashe gasucan takarasa gaban alhaji sani da nabil ta ajje musu kololin abincin agabansu ta karbi na hannu shatuwa shima ta ajje musu ga tsiyarku Nan kuhada kuyi taci ku hankalinku kwance sekai Loma Baki kuke tayi mukuma inmunso mumutu Ni da jikata Dan mugunta kunsan Koko da kosai da dumaman tuwo da yartsala da Masa mukafi sani da safe shine zakusa adafo Mana wannan abincin masu jankunnuwan nasara akawo Mana Dan yunwa takashemu takalli nabil Kai mekiran zakuna hararar me kake Mana tin da muka shigo dakai da wannan uban naka me katan ciki
Hajiya Fatima rokar alhaji sani da nabil take da Ido karsu kulata suyi shuru Amma Ina abanza
zuciya ta ebi nabil hannu yasa yakaiwa dining table duka se da wasu daga cikin glass cup din dake Kai suka fado kasa suka fashe idansa yarine yakoma Jah saboda bacinrai Daman Kuma da haushin su yakwana aransa shima Kuma tinanin in sun hadu irin hukuncin da ze dauka akansu yakeyi se Kuma Allah yakawo su taruwan sanyi
Yace ke tsohuwa wlh ya isheki haka cinfuskar da kike Mana Ni da ubana ya Isa Haka daga haduwarmu da ke zuwa jiya da yau kin kirani da kalar sunan banza yakai nawa ubanama Baki bariba Dan bala,i Kai se yanzu nagodewa Allah da nadage yarena na hausa be bar bakinaba du da zaman da nayi a America Kuma Allah yasa inasan yarena kome kafada min da yarena na hausa Zan gane Ashe da kin cuceni kamar nasan da wannan ranar narike yarena na hausa hannu binbiyu akasar da batamuba ga jikarki itama Babu kalar da sunan banzan da Bata kirani da shiba ita da kawayanta har da min Waka haduwata da ku akwana Daya tazamemin fitina wlh ke tsohuwa inhar kikai Wasa Kika Kuma kirana da wani sunan daba nawa wlh Sena gurza Miki Baki se na karasa cire wayannan jajayen hakwaran na gaban bakinki da suka rage Daman inajin haushin jikarki ta fasawa ubana goshi har da dinki Kuma se nadau fansa ko akanki ko Akan jikarki
Shatuwa Tai caraf ta anshe mgnar tace au Ashe Babu Dadi Ni da ka karyawa hannufa ai kome yafaru Kaine kaja ba waniba da baka Fara tsokana taba da du Haka Bata faruba gashi Ina ji Ina gani kabarni da jinya ai ko jiyan Ni ba shi nai niyar jefaba Kai nai niyar fasawa goshi yai maza yatarema Kuma wlh har yanzu ban hakuraba se narama Kuma ga tsiyar abincin kunnan Kuma Dole aje asamo Mana Wanda muka iya ci agarinmu
Nabil yace au har yanzu bakuyi sanyiba ko Dan ban gama nunamuku irin
Kalata bako
Plet da glasscup din Kan dining table din nabil yasa hannu yafara jifansu dshi suna tsalle suna kaucewa iya du tacika wajan da ihu da masifa shatuwa da taga abin bana Kare bane itama kome tasamu jifan nabil take dshi har abincin da yake gabansu ta dauka tana jifan nabil da shi lokaci Daya suka Bata ko Ina na wajan MINISTFR mutuwar zaune yayi yakasa motsi Yana kallan ikwan Allah Amina ita gefe ta koma tana kallansu anrasa me Basu hakuri hajiya Fatima tana boye abayan labulan wajan in taji anyi ihu se ta leko kanta daga taga ana niyar jifanta satai maza ta komar da kanta nabil kofin gaban MINISTER ya dauka da ruwan shayi ciki me zafi Yana tiriri garin ya watsawa shatuwa se awuyan iya wata mahaukaciyar Kara iya tasaki Dan azaba lokaci Daya du tabi ta gigice Dan zafi ai batasan lokacin da tashige karkashin dining table ta buyaba tana mai da numfashin wahala lokaci Daya wuyan iya yatashi abinka da tsufa ruwan shayin ya Kona Mata fata sosai ta gefan wuyanta
shatuwa ganin ruwan shayin da nabil ya watsawa iya da Kuma yanda iya take ta ihu yakuma konawa shatuwa Rai batasan lokacin da Tai tsanle ta finciko karfen labulan wajan gaba daya ta rikitosu sukayi kasa se ga hajiya Fatima abayan labule tana raba Ido tana ijiran ikwan Allah shatuwa Kan nabil tayi dagudu da karfen labulan ahannuta in takai Masa duka dshi se yai tsalle ya kauce Babu zato Babu tsammani garin shatuwa ta kwadawa nabil karfen se a gadan bayan MINISTER zafin karfenne yadawo da shi daga mutuwar zaunen da yayi tin dazu Dan azaba besan lokacin da shima yashige idan iya ta buyaba sun hadu susu biyu suna jinyar in da kowa aka illata shi Dan azaba bayansa rikewa yayi Dakar ma yakai kansa in da yabuya iya da MINISTFR Baki yamutu Babu me mgn
sunbar nabil da shatuwa na fafatawa fadan yakoma na manya nabil shima samu yayi yadauki karfen labulan daya yakan shatuwa da shi dagudu Yana kokarin kwada mata bakajin komai se karar karfe awajan Dan karfin Hali na shatuwa da hannu daya take wannan rigimar Kuma dudahaka shatuwa bakinta yaki mutuwa inbanda bakaken mgn Babu abin da yake fitowa daga bakinta tana gayawa nabil shikuma Yana dada tinzira ransa nadada baci gabadaya sunhada wani uban gumi Kai ace wani uban aikin wahala aka basu su keyi
Amina da taga suna niyar jiwa junansu ciwo kuma Babu Wanda yake da niyar hakura ya dena Dakar da dabara tasamu tafita wajan baffah ta gayomasa abinda ke faruwa da sanyin safiyar Nan da sauri baffah yabiyo bayan Amina tinkan yakaraso yakejin muryar shatuwa da Kuma karar karafuna natashi shikuma muskili Nabil baajin muryarsa akwai wata kofa tabaya Amina tacewa baffah sushiga tanan Dan asamu arike Daya daga ciki suna shiga Allah yabawa Amina sa,a tarike shatuwa tabaya shikuma baffah yasamu yarike nabil tabaya
Tsawa baffah yadaka musu ya wankawa nabil Mari yace kunutsu kushiga hankalinku meyake damunku haka ko kunsamu tabin hankaline bamu saniba daga jiya zuwa yau Kai nabil meyasa kake biyewa mace Kuma matarka Dan Allah jibi yanda dukanku kuke maida numfashi kamar wayanda sukayi aikin wahala Dan Allah kukalli barnar da kukayi awajannan gaba daya kun lalata komai nawajan har falo Baku bariba abincinma gabadaya kun zubar dshi saboda Bala,inku Ina sani da iya da fatima suke suka barku Kuna wannan danyan aikin
Hajiya Fatima ce tasamu tafito daga wajan buyar da tacanja tace baffah du munanan abinne yafi karfinmu in muka tsaya ciwo zasuji Mana abanza abarmu da jinya ai yanda suka haukace dinnan ran kowa yake abace acikinsu Babu me iya raba fadannan Daman se Kai baffah Suma masu daure musu gindin sunyi takansu sun kasa rabawa baremu Yan kallo baffah Ni banma San Ina suka buyaba tinda naji ihun iya dazu ban Kara jiba inaga sunsamu sunfice suna waje abin yafi karfinsu
Muyar iya sukaji ta karkashin daining table tana fitowa da rarrafe tace kun ganmu Nan Ni da Mara mutuncinnan muna jinyar jikinmu konani da ruwan zafi mekirar zakunannan rabi mutun rabi aljani yayi daban gudu na buyaba da salibeni zeyi kamar kaza aruwan zafi gabadaya ko ya aikani lahira Babu shiri mutun amurmurde kamar samudawan farko fuska amurtuke sekace me gadin gidan wuta idanshi Dan mugunta har wani Jah da Kore suke komawa Dan masifa usuman kahada shatuwa da Bala,i rashin sani yasa na yarda ankawo jikata inda zaa kasheta nashiga uku Ni Aisha anfasa aurena billahillazi usuman kadau mataki Dan bazan yarda inaji Ina gani acutarmin da jikaba Dan Allah kaga yanda gabadaya Rabin wuyana yasale da ruwan zafin da wancan damisan yawatso min ko tsufana beganiba Dan rashin imani har da cewa ze karasa ciremin hakwaran bakina nagaba da suka rege Kuma wlh ze iya fin hakama Dan Babu tausayi da digwan imani azuciyarshi zantafi da jikata in komai yalafa sunyi hankali shi da ubansa na dawo da ita wlh inaji Ina gani bazan bar jikata akashemin itaba
MINISTER ne yafito shima Yana rike baya yace Ni bance inaji Ina gani jikarki zata kashemin yaroba Nima ta gurguntani se ke baffah kagani da idanka tin da aka kawo fitinanniyar yarinyarnan take hakona jiya kaga me tai min yauma gashi ta barni da ciwan baya Dan Allah Dan annabi baffah ka temaka kacire dokar da kasa Mana Ni da nabil ya sauwake Mata sukama gabansu su koma in da suka fito har in da muke Dan masifa muna karyawa tsohuwar Nan tazo ta samemu tahau Mana masifa Wai su tuwo da Koko da kosai suka sani Dan kauyanci tin ajiya nabil yakuma fadamin bayasan yarinyarnan ko ganinta bayaso yayi ya tsaneta karfa murasa nabil baffah kadau mataki Dan Allah
Baffah yace du kanku kunemi waje ku zauna zamuyi mgn da ku kowa Zama yayi baffah yakalli nabil Kai nabil dakai Zan Fara Dan Kaine yanzu komai yake hannunka na shatuwa zaman nan dan kai da shatuwa akeyinshi yanzu Dan Allah azamanka na mijinta abinda ka kulata kukeyi yadace kaifa yanzu girma ya kamaka ko kana so ko baka so Dole kana hakuri Akan wani abin in matarka tamaka karfa kamanta ko Babu aure sama kake da ita ka girmeta bare Kuma yanzu da take akarkashin ikwanka Dan Allah ba girmanka bane karka Kara kulata ku Kara raba abin fada haka gaban mutane da safiyar Allah yanzu girmannan da kake da shi agaban yaranka da yan aikin gidannan yanzu du kazubar dshi a idansu dakai da ubanka dalilin wanna abin kunyar da kukayi jiya da yau kaga kuwa yanda maaikatan gidannan suka taru awaje suna sauraran abin kunyar da kukeyi Kuma saboda suna tsoro ko rabawa Babu Wanda yashigo yayi kabi zabin da nai maka nabil insha Allahu zakaga alheri komai daran dadewa kaji jikana nimafa ina sanka Ina kaunarka kamar yanda sani yake sanka San da nake makane yasa na zabama matar aure da kaina Dan Allah kana hakuri da ita karka Kuma kulata Kaine babba itama Zan Mata fada se mgnar iya kakar shatuwa cefa matarka itace Kuma ta raini matarka tin tana cikin tsumma har zuwa yanzu kaga kuwa dolene ka girmamata karka Kara kulata kome tai maka kaima kakace awajanka yanzu kaga ka kona Mata wuya saboda zafin Rai irin naka Dan Allah karage zafin Rai bashi da anfani arayuwa kaji nabil Allah yai maka albarka
Kekuma shatuwa nabil mijine awajanki dolene ki bashi girma Kuma kibishi sau da kafa aure yafi karfin Wasa Babu raini tsakanin miji da Mata daga yau se yau karna karajin wani abin yafaru na fada tsakaninku Dan Allah kuji tsoran Allah ku zauna lfy kiwa mijinki biyaiya aljannarki tana karkashin kafarsa se yadaga Zaki shiga karki Kara dagawa mijinki ko da muryane bare har takai ga niyar zaku illata juna da makami yanzu kema kin girma bakamar da bane da Baki da aure tinda kike kin taba ganin babarki suwaiba da umaru suna irin abinda kukeyi daga jiya zuwa yau ko Kai nabil tin da kake kataba ganin Fatima da sani suna fada to karna karaji kun yi ku zauna lfy ku Zama abin alfahari adangi da duniya gaba daya kodan yaran da zaku Haifa gaba inma mafarki like ki farka aure dai anriga an daura Babu rabuwa mutu karaba ke da shi inma zaku koyi San junanku to ku ku koya Dole muma wasu daga cikinmu dahaka muka so namu matan shatuwa dolene ki girmama iyayan nabil wannanfa da kike gani Kika fasawa Kai jiya yau Kuma Kika kwadamai karfe abaya uban mijinkinefa karki kuma gida dayafa zakuyi rayuwa kuke haka karna karajin bakin wani daga cikinku ku tashi ku tafi nagama daku Allah yaimuku albarka Allah yabaku zaman lfy yakade fitina Amina maida shatuwa dakinta
Kafin su tafi iya ta kalli nabil tace me mugun Hali kadaiji me Wanda ya haifi ubanka yace saura kaki ji Dan Allah jibi yanda yake ta huci kamar wani mayunwacin Zaki Tai maza ta toshe bakinta au yacefa in na Kara kiranshi da wani suna ze ciremin hakwaran gaba da suka rege na bakina Wai jiya wanama suna naji kakira ubanka dshi ko miss miss kome Kai Kuma naji kace Wai kana Dan miss miss ko me usuman Daman gwaunati mukamin da tabawa danka kenan mukamin Kiran maguna miss miss Kuma naji yakira fetir Daman du uban kudinnan da yatara da mukamin kiran miss miss ya tarasu Ashe magunama na da daraja akasar Nan ban saniba dakai na kirkine sani ai da inna komawa mazagai da nasa na tarama maguna dayawa in zan dawo ganin shatuwa na tahoma da su to baka da mutunci daga Kai har danka me shigar Mata
Me hajiya Fatima da Amina zasuyi inba dariyaba hajiya Fatima tace nabil tafi daki ka kwanta kaji ka huta rabu da iya Wasa take muku kema shatuwa jeki kwanta ki huta Kan akawo Miki abinda kike din
Bayan su nabil sun fita
Baffah yace iya na dawo gareki Dan Allah Dan annabi karki Kuma kula nabil kome yai Miki jikankine shi Kuma sirikinkine ki Dena kula sani kome yai Miki kizo ki fa da min shatuwa Kuma namiki alkawari nabil Babu abinda ze Mata ga Fatima za tana kula da shatuwa da Nabil yanzu anjima Ni da ke zamu koma mazagai Kayan dakin shatuwa anyafe du za ai Mata anan ki kwantar da hankalinki Kuma in an kwana biyu akai akai zamuna zuwa Ni da ke muna ganin yaran muga Kuma ya suke Zama kije dakin shatuwa ki shirya anji zamu tafi Allah ya kiyaye gaba
Iya tace habawa ai in ban ciba Babu wani bayani bana Kuma Jin ko wace mgn Ni fa afah bani abinda nafi wayo naci bazan iya cin Kayan da mugayannan suke ciba akawo min Koko da kosai ko tuwo ko Yar tsala da kunun tsamiya
Baffah yace karki da mu du NASA ai Miki kije zaa kawo Miki
Tace to yanzu naji zance shimafa wannan kaja Masa kunne Dan Naga har yanzu wani gani gani yake min Kuma Ni da naso mu Dan Kara kwanaki Dan wlh bazan iya rabuwa da shatuwa ba Kuma wlh Babu inda zani Ina nan Kuma ai nazata nice Zan Mata zaman daki
Tatashi ta fice tana sababi
Baffah yace sani kaban kunya wlh kabani mamaki sani da iliminka da hankalinka kake kula tsohuwar Nan Kuna Raba abin kunya gaban yaranku Kai sani bakaji kunyaba ko mukamin da kake dash na MINISTER baka dubi girmanshiba saboda San danka yarufema Ido ka daka ta tsohuwar nan kuka dinga Raba abin kunya gaban su nabil ita ai yadace Kai Mata uziri akwai tsufa na damunta da rashin ilimin Kai kumafa wlh kaiwa kanka fada kayi kokari ka hada Kan yarannan su zauna lfy Kar na karajin makamancin haka yasake faruwa
Yace to baffah kayi hakuri Amma gaskiya inajin tausayin nabil wlh
Baffah yace au du abinda nake fada be shigi kunnan kana ko
Katashi ka tafi kaima da mgnar da zamuyi da fatima
New writer's
Hakan Take
*Husba'ahfama* 鉂ゐ煈� *'YAR KWALLIYA* 馃コ馃拑
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹
馃憼
馃拕馃拝 *DAN MINISTER* 馃拝馃拕
馃馃
Written by *Husba'ahfama*
*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*
Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*
9-10
MINISTER yace baffah kayi hakuri wlh tsohuwar ce bata da mutunci Dan Haka nake ajje komai agefe nake kulata yanzufa kaji me tace Wai MINISTER take Kira da Miss miss Wai mukamin Miss Miss aka bani Dan Allah Kar ta Kara kwanar Mana agida ta koma inda ta fito har jikar tata
Baffah yace Ni dai azamana na mahaifinka ka dena shiga harkar yarannan kayi kokarin hada kansu ba Wai kana hura wutaba Kana nuna bakaso tin daga jiya Allah yafara nuna maka ishara Akan auransu tashin farko anfasa maka goshi yau baya gaba in ka kuma shiga har karsu bakasan me ze faruba karabu da iya Kar ka daka ta halinta kaso shatuwa kamar yanda kake san nabil gaba bakasan wana alheri zata za me mukaba azuriarka gaba zakaji kunyar abinda ka aikata infa kaji nasihata in Kuma bakajiba to Allah yaba da sa,a tashi ka tafi
Bayan minister yafita
Baffah yace Fatima Allah yaimiki albarka Allah yabaki hakurin Kula da yarannan nasan daga ke har Amina Baku da matsala yanzu Dan Allah kiga me yarannan sukayi yau kowa acikinsu Yana Ji da danyan Kai ita rikwan Kaka uwa ba kwaba shikuma rikwan namiji uba bakwaba ga nabil da shegiyar zuciya da zafin Rai ga shatuwa da tsokana da taurin Kai shi ma Kuma nabil din akwai taurin Kai in Abu yafi karfinki atsakanunsu kina kirana ki sanar da Ni zan zo Dan sani ba ze musu fada na tsakani da Allah ba se yasa San zuciya aciki nashi ze so ita Kuma iya dole yau na jata mubar gidannan yakin badar din da akayima jiya da yau ya isa haka ai in har akabar iya agidannan bazamu iya gyara ko maiba yanzu kije kisa akai mata abinda takeso taci se mu tafi du abinda yashige Miki duhu Akan abinda na fada miki kiki rani kijin Allah yabamu sa,a Akan niyarmu ta alheri Kan yarannan
Tace ameeen baffah Ni yanzu damuwata yanda nabil da shatuwa zasu na kwana waje Daya wlh abinda kamar wuya Dan bakaga rigimar da mukayi dshi Akan su iya sun kwanar Masa adaki cewa yayi yabar bangaransa gaba Daya Kuma baya San komai na wajan shi sabo ze canja se da nacimai mutunci sannan yahakura Kuma kasan alhaji bayansa ze goya
Shawara baffah yai tabawa hajiya Fatima sannan yadada samun minister yadada jamasa kunne sosai Amina itama yafada Mata gudunmawar da yakeso tayi atsakanin nabil da shatuwa
Iya ankai ruwa Rana da ita sosai Kan ta yarda ta koma mazagai ta rabu da shatuwa bakara min kuka iya tashaba na rabuwa da jikarta har tausayi tabawa su baffah ana haka nabil yashigo falan yasamu iya tana kuka Baki yatabe yaja tsaki kawai se gani sukayi iya tatashi tsaye tabi ta bayan nabil babu zato babu sammani Dan Babu Wanda yakawo me zatayi tatakarkara ta dimawa nabil dundu a gadan baya se da yagantsare Dan abin yashige shi beyi zatoba se saukar hannunta yaji
Iya tace Dan kwal uba ai ga Wanda du yaja komai Nan yarabani da jikata muna zaman zaman mu Kuma Zan tafi saura ka Kuma karyamin ita Kuma har yanzu ban huceba se nayi zaman Yan bori akanka ko yaushene me zubin karfafa me shigar Mata dandudu kawai yau Kuma irin shigar da akayi kenan kuma ubanka nagani yaki ya hanaka Dan miss miss din uwa kawai takalli hajiya Fatima yarnan bakiya Saar Daba da mijiba du Basu da mutunci ke Kuma gaki saliha me kirki Amma auran Dole aikai Miki da uban Dan daudun Nan ko Dan Baku dace da junaba
wani irin juyowa nabil yayi cikin zafin nama da bacin Rai yadaga hannu ze damkota iya baffah yai maza yashiga tsakani
Yace haba nabil Kai ta hakuri kaji yau fa zata tafi shikenan Kuma in tatafi se Allah yasake hadaku Kar ka kulata yanzunma tsautsayine Bata saniba Tai maka
Baffah mgn yaiwa minister da Ido kar ya kula iya Dan yaga ranshi yabaci da abinda iya taiwa nabil
Nabil fita yayi daga gidan ko tafiyar baffah da iya be tsaya yagani ba cikin bacin Rai Yana ta huci zuciyarshi na Masa zafi ga baffah yahana shi yai maganin iya
Hamdalah hajiya Fatima tayi azuciyarta da nabil yafice gaba Daya daga gidan ahankali tace alhamdulillah gwara da ka tafi Dan Naga itama shatuwa kadan take jira Kai mgn ta kulaka ga alhaji shima ransa abace yake iya ta taba Dan gwal dinsa
Shatuwa Bata tashi yin kukaba se da taga da gaske zasu rabu da iya hankalinta yatashi Tai ta kuka rikicewa tayi se sun koma tare Dakar akasamu aka rabasu iyama kukan tafara Haka motar taja tafice daga gidan iya se waige take baffah yasha mitar iya Kan su je mazagai shidai ba da hakurine nashi har Allah yasauke su lfy
Nabil da yafita wajan da yake shakatawa yatafi yasamu abokansa acan suna ganinshi sukayo kanshi suna murnar ganinshi da murnar zasu hule tinda ga me kashe musu kudi yazo abokan nasa nasan suyi Masa maganar amaryarshi Amma kowa najin tsoro Kuma sunga yanayinsa Yana cikin bacinrai haka kowa ya hakura yaja bakinsa yai shuru
Da hannu yakira wani daga cikin abokan nasa yazo yabashi damin kudi yace gashinan kowa kabashi yai abinda yakeso in Basu isaba azo akarbi wasu
Yace to mutumina Dan Haka nake sanka kake burgeni baka halin karanta guri in bakai sunansa lami Ni da dashawarar da nakeso nabaka in zaka Dan bani lokaci yau Naga kamar kana cikin bacin Rai kaima kahau layi karabu da bacin Rai kadan Sha abinda muke Sha ko kadanne yau ka gwada lokaci Daya in kasha zakaji kafin yakarasa
Nabil ya daga Masa hannu cikin bacin Rai yace bani da raayin Shane tintini da inaso kaima kasan ko ana siyarwa nera nawa Ina da kudin siya Ni kwata kwata shaye shaye baya burgeni Kuma baya cikin tsarin rayuwata
Yace to ko finah ce yau Daya gatacan na kirama ita kuje ku huta da ita tinda kaga yarinyar na mutuwar sanka
Nabil yace tinkan nai maka rashin mutunci Kai maza ka bace daga wajannan Ni kake hadawa da mace ka kwasan wana Hali Mata suka jefani Kuma shine zaka zo kana bani wannan muguwar shaawar akan mace Kai maza kabace a idona
Jiki nabari yabar wajan
Finah na gefe du abinda yafaru tsakaninsu akunnanta da I danta ga taji labarin auran da yayi kishine ya rufeta afili tace in dai Ina raye nabil se kazama nawa se mun koma Abu Daya da Kai muzuba mu gani Ni da kai
Shatuwa ce kwance Kan makeken gadan nabil tana ta kuka idanta ya kunbura sosai sabo da kuka
Amina ce Tai sallama ta shiga tace kanwata har yanzu kukan kike tayi Baki hakuraba nanmafa gidane Babu abinda ze sameki kinji Kuma bawani dadewa zakiyiba za a Mai da ki wajan iya Kuma naji baffah na cewa da iya zata dawo Nan gidan gaba Daya da Zama saboda ke
Murna shatuwa ta fara tace dagaske kike
Kai Amina ta daga Mata
Nan Amina tasamu tafara janta dahira har tasaki jikinta Nan tasamu ta fara yi Mata tambaya Akan karatu
Shatuwa tace nifa Babu wata makaranta da nake zuwa iyace makarantata itace me koya min karatu Kuma iya tahana asani ako wace makaranta Dan bataso adakeni Nima Kuma banasan karatun Bari na biya Miki abinda iya ke koyar Dani kiji
Kema Kya karamin daga in da na tsaya
Biya Mata tafara ai ko nisa batayi da shirmen karatun taba Amina ta tsaidata tace ya Isa Haka shatuwa kinaso kema ki zama Yar birni Kuma Yar gayu kamar Yan matan garinnan ko da yake ban kaiki yawo Kinga yanmatan garinnan ba da sun birgeki sosai to kalarsu nake so ki Zama Zan sa akawo Miki me akoya Miki karatu daga na boko har na isilamiya Nima Kuma in nazo Zan na koya Miki Amma yanzu ki ajje karatun iya da ta koya Miki agefe har ki iya Wanda zaa na koya Miki kinji kanwata
Tace to ke ya zan na kiranki dashi
Tace anty Amina su nana yanzu abinda nakeso da ke wanka nake so muje na hada Miki ruwan da kaina kiyi muga kitsan kanki
Shatuwa na bude gashin kanta
Mamaki Amina ta fara yarinya me gashi Amma saboda rikwan iya ce ita kitsan kanta ya dankare ko tsagar kitsan baagani gawata uwar kasa akanta
Amina tinani tafara azuciyarta tafara mgn tace gaskiya da matsala yanzu Kai nasa ta budemin nagani to Kuma sauran wajanfa ga yarinya kyakkyawa Amma rashin kula yasa kyanta yabuya da zata yarda in na tsefe Mata Kai wlh dada kaina Zan Mata wanka yau dai Daya nayi Mata du abinda yadace na Kuma nuna Mata yanda zatana yi gaba yanzu yanda Zan Mata ta yardar ne matsalar
Zama Amina tasa shatuwa tayi ta tsefe Mata Kai tashiga bandaki tahada Mata ruwan wanka shima se da takirata tahada komai agabanta takuma nuna Mata du abinda yadace saboda gaba in zatayi tace yau komai Ni Zan Miki da kaina gashin kanki Zan Fara wanke Miki daga baya maje gidan gyaran gashi agyara Miki shi nifa yau ni zan miki wanka da kaina kinji
Shatuwa kitayi tadai yarda ta wanke Mata gashin Kanta lfy se da akazo wanka da gyaran jiki da du inda yadace aga Babu gashi da kazanta jikin mace shatuwa Taki yarda Dakar da rarrashi ta yarda Amina Tai Mata du abinda yadace ta Kuma nuna Mata kalar du wani Kayan da mace in tatashi wanka zata na anfani da shi da Kuma to du inda yadace aikuwa Amina bakaramin wankar shatuwa tayiba ta wanketa tas sannan ta barta Shatuwa se runrufe kirji ake abinma dariya yabawa Amina ganin ita kirjin tafi damuwa dshi
Suna fitowa shatuwa tasa hannu tarufe Ido tasa dariya tace wlh kunyarki nake ji anty Amina Kuma fa naji Dadi ako Ina na jikina sakayau nake jina ga wata iska me Dadi nashiga jikina nifa amazagai bana wani wanka sosai Kuma iya bata min fada Kuma fa Ni banasan kitso wlh
Amina tace ai Dole kice bakyasan kitso Daman ku Masu gashi bakwaso ataba muku Kai du wannan me saukine akwai inda Zan na kaiki ana wanke Miki gashi agyara Miki akai akai Kinga Babu mgnar yin kitso se haka in kina so wataran se ana miki Kuma mu anan wanka kullin akeyinsa safe da yamma da yammanma anfiso in Zaki kwanta kiyi inma sansamune Ni kullin sau uku nake so kinayi kinji kanwata zakifi Kyau da kanshi har maganar wanke Baki shima du yanda nakoya Miki da yanda nagaya Miki zakinayi kullin haka nake so kinayi Kinga yanzu kin Fara Zama Yar gayu Kuma Yar birni yanzu Kinga du yanda na koya Miki yanda Zaki shafa wayannan Haka zakiyi Banda kwalliya me yawa kinji kishirya inkin Gama kizo bangaran su mommy muyi Hira Kan natafi gida Kuma ko natafi akwai mommy zata nuna Miki du abinda Baki saniba Nima Kuma zanna zuwa wajanki akai akai muna gaisawa natafi Ina jiranki
Shatuwa Zama tayi tashafa du abinda Amina ta nuna Mata kamar abin arziki bayan tagama tadau jambaki da Hoda da jagira tazuba wata kwalliyar hauka itanan tafara Zama Yargayu kayan da Amina ta kawo Mata tace tasa su tasa wasu riga da siket ne na atamfa sunyi Mata Kyau sosai sun karbi jikinta abinda yabata kwalliyar fuskarta tsayawa tayi gaban mudubi tajuya takuma juyawa wani Dadi yakamata
tace Yasin du Wanda yaganni yau seya hargitse saboda mugun kyan da nayi
Amina tana shiga falan tasamu Hajiya Fatima azaune
Hajiya Fatima tace Amina ansamu ta hakuran ko har yanzu kukan take Allah yasa kinfara naki aikin
Amina tace eh ta hakura Kuma nafara aikina mommy ammafa akwai matsala sosai wlh yarinya kyakkawa Amma iya ta cuceta tabarta ba ilimi tana zaune cikin jahilci in kinji yanda mukayi da ita wlh se takaici yakamaki in yarinyarnan tagyaru wlh yarinya kyakkawa zaayi Kuma nabil seya rude Akan Santa se yasota sosai wlh Allah dai yabamu saa
Suna cikin hirarsu nabil yashigo ko sallama Babu bare gaisuwa yanemi waje ya zauna Yana kallan kofar shigowa yawani hade Rai kamar bega mutane awajanba
Hajiya Fatima tace Allah yakyauta Allah yashiryeka nabil Dan Allah yaushene zakayi hankali yaushene zaka Fara jin fadan da nake maka Akan sallama da gaisuwa yanzu kashigo Mana ko sallama Babu bare Musa ran gaisuwa Kuma me yakawoka wajena ko kamanta kana da Mata kamanta yamukayi da Kai jiyako tin wuri katashi katafi wajan matarka tinkan nakira baffah na gayamasa me kake niyar yi
Nabil yace haba mommy meyasa baka Sona yaushene Zaki Fara Sona kamar yanda sauran iyaye Mata suke San yaransu Dan Allah yaushene Zan samu kauna da kulawa awajanki yaushene mommy yanzu Dan Allah kin goyi bayana auran kandarar da akayimin na mara hankalin yarinyarnan da ita da kakarta Mara mutunci na tsaneta na tsaneta bazan kwana gu Daya da itaba
Hajiya Fatima tace nabil nikuwa nake sanka Kuma nake kaunarka Ni nake so kagama da duniya lfy nabil Babu uwar da zata haifi da a cikinta tace bata sanshi nabil kowace uwa burinta taga Dan da ta Haifa Yana hanya madaidaiciya hanyar da zata kaishi aljana Amma nabil kaki ganewa nabil kullin inamaka addu'ar shiriya Allah yashryeka Allah yaganar min dakai gaskiya kasan irin San da nake maka Kuma insha Allahu nasan Allah natare Dani Kuma ze cikamin burina ya amshi addu'a ta akanka har yanzu inasa ran zaka Zama yanda nake so na ganka insha Allahu nasan Kuma lokacin zakasan gaskiya nake fadamaka
Fitowa tayi zuwa bangaran Hajiya Fatima tana wata irin tafiya abin dariya ita adole tazama Yargayu du Dan aikin da yaganta na gidan tazo shigewa ta gabansa seyayi dariya aboye
wani daga cikin Yan aikin yace Allah kenan abinda kake wulakantawa arayuwa nabil Daman wataran se kunyi rayuwa tare Kai da kake wulakanta mutane musamman Mata gashi yanzu abin dariya kuga wanta ya aura azaman matarsa ai wannan tsohon arzikin yaburge Ni wlh
Dariya sauran sukayi Daya daga cikinsu yace ku dai yi ahankali Dan wlh kunsan Yana ciki bedade da shigowa ba Kuma kowa yaga yanda yake tafiya yasan ransa abace yake Babu ruwana
Hajiya Fatima na Kan yiwa nabil nasiha Sega shatuwa itama tashigo tana wata tafiya tana karkada idanu itama tashigo Babu sallama tanemi waje ta zauna irin zaman da nabil taga yayi yadora Daya Kan Daya itama shi tayi tana ta hura hanci ita ala Dole tahade Babu Wasa daga Hajiya Fatima har Amina kallan shatuwa suka koma yi
Hajiya Fatima tace ohh Ni Fatima du gautan jahne daga mijin har matar lanlai akwai aiki
Nabil Kare Mata kallo yayi besan lokacin da dariya ta kwasheshi yace tofa abin nayine Dan Kauye yashigo birni ba lfy se ya warke Dan Allah kiga wata kalar kwalliyar mahaukata Wai kenan gayu kikayi anan kenan gani kike Wai ke macace ko ahakan Allah yakyauta gaskiya baffah ka cuceni ka gama da Ni Wai arasa Wanda Zan aura azaman matar aure se wannan akuyanlen kuga wani kwalliya kamar anyiwi akuya kwalliya wlh bazan taba Sankiba kome Kika Zama aduniya na tsaneki bana san ganinki adalilinki da wannan tsohuwar na dada tsanar Mata aduniya
Tashi tsaye shatuwa tayi tadaka tsalle taje gaban nabil ta tsaya ta rike kugu tace Nima kamar yanda kake fada ka tsaneni Nima Haka na tsaneka ko ganinka bana san yi da idona kafara yiwa kanka dariya kafin kafara yiwa wani kaifa me shigar Kayan Mata dandaudu matamaza rabi mace rabi namiji adalilinka na rabu da iya me kaunata karabani da ita Ina ji Ina gani ta Ina Zan soka har naso Zama da Kai yasin baka isaba Kar Kuma ka kaini bango Dan wlh akwai abinda na dauko tin daga mazagai saboda Kai Dan na koyamaka hankali karka Bari nafara ma anfani dshi Dan yanda kabarni da jiyar hannunna kaima se na wahalar da Kai kaji jiki kamar yanda Nima naji wannan alkawari nane Ni bana yafiya Kuma bana manta ranar daukan fansa ga du Wanda ya tabani Dan Haka kabi ahankali kashiga hankalinka
Nabil tashi yayi yadauke shatuwa da wani gigitancan Mari me zafi yakuma dauketa da wani lokaci Daya tafara ganin duhu hannu yasa ze Kama hannunta me karaya dasauri hajiya Fatima Tai maza tarike Mai hannu se wani huci yake Dan bacin Rai
Yace mommy Dan Allah kibarni na karasa ragargaza hannun Naga me zatayi ita da kakarta kinafa ji mommy irin kalaman da take fadamin baa Mai damin da mgn baa Kuma yimin rashin kunya baa nunani da yatsa ban karyawa mutun hannuba Dan Haka kiki,yaye ko Dan gaba ki fita harkata har murabu Danni bazan iya Zama dakeba rikwan tsohuwa kazama kawai yau zanga yanda Zaki zo kice za mu kwana daki Daya wlh da yau sekinyi Dana sani arayuwarki
Shatuwa neman abin ramawa tafara yi da sauri Amina tazo takama hannuta tajata dakar suka bar falan Dan taurin Kai irin na shatuwa ko alamar hawaye Babu a idanta burinta kawai itama ta rama abinda yai mata jitayi takara tsanar nabil azuciyarta takuma dau alkawarin se ta dau fansa itama se tabashi wahala
Amina bangaran nabil tamai da shatuwa ta zaunar da ita itama Zama tayi kusa da ita tace haba shatuwa yakike,yin Haka bakiji fadan da baffah yai mikiba ko in har bakya,bin abinda baffah da mommy zasu fada miki Zan Dena kulaki Nima tinda nasan Nima bazakiji nawaba yanzu Dan Allah wace irin kwalliyace wannan afuskarki karki Kuma mu anan ba a irin wannan kwalliyar in kayi mahaukaciya za a dauki mace Zan koya Miki irin kwalliyar da Zaki nayi afuskarki Kar na karaji kin kula nabil Kuma kome zemiki Kar ki kulashi mijin,kine
Shatuwa tace to aini tin Ina yarinya baamin Abu ban ramaba in ban ramaba har bacci kasawa nake Kuma Iya tace karnabi fadan da baffah yai min Dan shima dandaudun baji zeyiba Kuma Ni iya itama tamin fada irin nata Kuma Ni Dole nabi fadan da iyata Tai min Kuma nata fadan yafi tinda cewa tayi du abinda yaimin narama Kar na raga mishi tace bashi da mutunci Kuma Ni gaskiya bazan iya kin bin mgnar iya ba kowadai acikinku zanji nashi in yamin Kuma Zan na aiki da kowanne kiyi hakuri Ina sanki karki Dena zuwa wajena Dan Allah
Shuru Amina tayi se da tagama tinani sannan tace naji shatuwa Allah yashiryeku se mgnar kirki kin iyako
Baki tawashe tace eh na iya sosai makuwa
Tace to zaayo Miki siyaiyar du abinda yadace na Kayan abinci in kin warke in Zaki koma saban gidanku ke da nabil se kifara girki yanzu anan mommy ce zatana sawa ana kawo Miki har kiwarke yanzu kije ki wanke fuskarnan Taki kiyi alwala kiyi sallah naji ankira Nima Bari naje nayi
Nabil dakin alhaji sani yashiga yaje yakwanta Dan shi abin ya zamemishi kamar Al,Ada in aka batamishi Rai dakin mahaifinshi yake zuwa ya kwanta ko yashiga yazauna har yahuce Zama yayi Kan kujerar da ke dakin se furzar da numfashi yake afili yace senayi maganinki yarinya yanda in kin ganni ko gaba zakina guduwa
Minister ne yashigo dakin Yana ganin nabil yasan ranshi abace yake dasauri yakarasa wajansa yace Kai dawa nabil badan tin abinda baffah yai maka bane kake fishi baka huceba nacema ai Zan rarrashi baffah yahakura ka saketa har mazagai zanje na rokeshi jira nake akwana biyu tukunna Nima kaina wlh basan yarinyar nakeba gakuma wannan maramuncin tsohuwar Nan tata ai Dole murabu da mugun iri nidai nafadama kaganawa yarinyar azaba karka taba raga Mata da kanta zataje tasamu baffah tace yasa ka saketa kome Tai maka karka barta kai Mata abinda yafi Wanda tai maka kaji ni nasaka
Nabil yace ai du abinda kace,min nayi du senayi daddy har dama Kari yanzu yanzu kaga me ta min mommy ce ta hanani hukuntata da se ta Raina kanta
Minister yace kamin dedai Dana Ni wlh narasa me hajiya Fatima take nufi da Kai kullin Bata goyan bayan abinda kake yi Ni ma kaina mijinta Bata goyan bayana yanzu abinda nake so da Kai ka kwanta ka huta kafin zuwa anjima in kanasan kudi ma ka iba in katashi
Minister wajan hajiya Fatima yaje ya sameta yace Fatima yanzu Dan Allah meyake da munki kekuma haka kike bakya kishin danki da mijinki kowama yatakasu badamuwarki bane Ina Yar sadakar da akabawa nabal dan kaniyarta nemanta nake me nabil yai Mata tabata Masa Rai ke Kuma da yake basan Dan naki kike ba shine Kika hanashi ya daketa ko kefa Naga alama kamar kina goyan bayan auran da baffah yaiwa nabil Anya kuwa basa hannunki aciki nifa nafara zarginki Dan ke basan nabil kike ba
Dariya hajiya Fatima tayi tace gaskiya girma yafadi Alhaji abin naka dada cigaba yake yanzu Kai bakaji kunyaba da kazo kana kunfar Baki akan yarannan gaskiya kaiwa kanka fada saboda gaba Kar aji kunya Ni wanka Zan shiga kaga tafiyata Dan kome Zan tsaya cemaka ba shiga kunnanka zeyiba bakaji na baffah ba bare Kuma nawa Kai da danka Allah yaganar da ku
Dare nayi lokacin kwanciya bacci yayi nabil yafito daga wajan minister yazo shigewa yaga shatuwa da Hajiya Fatima afalo suna Hira ko kwallan inda suke beyiba yashige yana Jin abinda zewa shatuwa in ta kuskura ta shigo bangaransa Yana shiga yakarewa ko Ina na wajan kwallo afili yace Allah ya temakeki yarinya Baku batamin waje naba yau da kinga rashin mutunci Ina jira yau Naga a Ina Zaki kwana dakinshi yashiga yaje yayi wanka yayi Shirin kwanciya bacci kwanciyarsa yayi hankali kwsnce
Bacci yafara ibanshi yaji ana buga kofa kamar zaa balla can Kuma yaji muryar shatuwa na mgn ka budemin kofa wlh ko na hanaka bacci wlh Babu inda zanje na kwanta se awannan dakin kafuto ka barmin dakina Ni karka samin kazanta adaki
Dataga baze fitoba fita tayi taje kicin ta dauko ludayin miyi tazo tahau yin kida da kofar dakin da nabil yake ciki akulle tacika ko Ina da karar kidan Amma can da taga bemataba tahau Waka dandudu matamaza meshigar Mata rabi aljani rabi mutun anji kunya me zamanman wando me wuya du sarka me fanti agashi me tafiyar Yan kaciya
Kidan da take be batawa nabil Rai sosaiba se Wannan Wakar da take Masa ai awani zabure yaduro daga Kan gado yahau neman abin da ze zaneta dashi dube dube yafara yagano belit dinshi yadauka yanufi kofar dakin yabude cikin bacinrai yayo kanta ze daketa itakuma Daman ta shiryawa hakan tasan yanzu ta tunzuroshi ransa yabaci Dan ta fahimta bayasan tana kiranshi da sunayan banza da Kuma wakar da takemai Dan taga ransa yabaci ranar da tasa kawayanta sukai Masa Waka tana ganin yabude kofar yayo kanta zefara zuba Mata ajiki Tai maza ta bude ledar dake hannunta ta Hura Masa kararar da Tai alkawari se tasamasa ajiki shi da minister in har shima be Dena yiwa iya rashin mutunci ba tindaga can takwaso shi agidan megari da zasu taho Abuja takwayi saa ta fesamai da yawa yashiga jikinshi sosai Kuma du dukan da ze Kai Mata baya samunta kaucewa take suna ta zagaya falan wajan nashi intaga ze cimmata ya sameta se Tai maza ta tura kujera wajan da yake shikuma seyai tsalle ya tsallake
Tace lokaci kadan nabaka zakayi sanyine yau zamuga ainahin rawar dandaudu me tafiyar Yan kaciya ai kowa yaci tuwo Dani Miya yasha yanda ka karyamin hannu nasha azaba wlh kaima se kasha tawa wahalar yau se kayi kwanan zaune yanzu muka Fara wasan muzuba mugani Waze gaji tsakanin Ni da Kai bawai bakasan mataba aikuwa zakaga aikin Mata ka kirani Yar Kauye to ga aikin Yar kauyenan kafara gani Dan yanzu nafara ban Fara komai ba Ina da salo kala kala kuma du se ka shasu gobema ka kara shiga gonata
Allah yabawa nabil sai,a yakama shatuwa yadaga hannu kenan ze zuba Mata belit din yaji lokaci Daya kamar anzuba Masa wani mahaukacin kaikayi ai besan lokacin da yasaki hannun shatuwa ba yatsaya Yana daurewa ai tin Yana daurewa besan sanda yafara tsalleba Yana Susa Yana tsalle Yana zagaye falan Yana Hawa Kan kujerun wajan ai besan lokacin da yacire rigar jikinshiba yafara ihu Yana Kiran daddy
Me shatuwa zatayi inba dariyaba har da kwanciya yanda taga yanayi yake dada Bata dariya Waka tahau yi masa asosa asosa asosa Babu ciwo cinnaka ya cijeshi asosa Masa asaso waiyo Allah asosa kaga yanda zaka nayi in kanaso kadena Jin kaikaiyin kaga yanda ake agarinmu du yanda nayi kayi
Ai dasauri ya yarda da abinda tace danshi Yama manta fadan da sukeyi Dan azabar kaikaiyin da yake ji rawa tafara tana juyi tana wakar asosa shikuma bawan Allah Dan azaba rawar yake yi da wakar bill hakki yanda taga yake rawar dariya take tayi Dan mugunta dogwan wandanma shima cireshi yayi yakoma dagashi se gajeran wando
Tace zuba dagudu katafi wajan su mommy ka nuna musu kafin kaje zaka Dena ji
aikuwa yace to Ina hanyar
tace kaganta Nan
Aikuwa yazuba da wani mahaukacin gudu yafice
Shatuwa takuma fashewa da dariya tace kadan kagani in dai nice yanzu kaga Ni se naje nai baccina hankali kwance Kai Kuma ka kwana azaune
Tashige daki Tai kwanciyarta tahau bacci cikin kwanciyar hankali
0 comments:
Post a Comment