BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*
Cikin fusata yace, "raihan kasan abinda Kake faɗa kuwa? Kasan wacce Kake laƙawa wannan mummunar kazafin kuwa?
Rausayar da kansa raihan yayi yace, "wallahi ALLAH abba babu ɗigon karya ko kazafi acikin magana ta, idan kuma baka yarda ba,nina yarda kazo muje gunta da daddare zaka same ta dawani, abba harfa cikin gida take shigar dashi.
,"shikenan ALLAH yakaimu daran ina jiran ka kazo ka kaini inganewa idona ,tashi yayi ya shige ciki yana nazarin maganar da raihan ya faɗa masa kan AISHA labiba.
Safa da marwa raihan yashigayi dan samawa kansa mafita, murmushi yayi ya ciro wayar sa , kiran Sadiq yayi, cikin ikon ALLAH kuwa ringing ɗaya Sadiq ya ɗauka, hakuri sosai raihan yayita bawa Sadiq kafin ya sauko Dan sosai ya nuna masa bacin ransa,rausayar da murya raihan yayi yace, "Yauwa kasan abinda nake so kayi min?
Girgiza Kai Sadiq yayi kamar raihan din yana ganin sa yace, "saika faɗa "
Rausayar da murya raihan yayi yace, "Dan ALLAH sonake ka taimaka ka taho anguwar mu anjima da daddare, sonake karakani gun labiba na bata hakuri.
"lalai saida Nina zaka tafi bata hakuri?
"kayi hakuri aminina kasan halin Inna ta yanda take,bata son taga ko hanya ta haɗamu da labiba, bare ace zancan Aure, yanzu ma abba nane zai tsaya min, amma da sharaɗin babu Wanda zaisan Nida ita muna tare Dan yanzu ma cewa yayi saidai murinka Hira acikin gidan su.
,"Cikin gida fa kace ?
,"Eh Dan hakanne kawai mafita,yanzu ma zaka rigani zuwa domin zuwan nawa saida taku idan zaka taho ka kira ni.
,"Shikenan kawai sadiq yace sannan ya ije wayar.
Ana idar da sallar isha'i kuwa Sadiq ya kira raihan ya shaida masa zuwan nasa.
Cikin sauri raihan ya isa gida, kiran abban sa yayi yace,"abba kayi sauri Dan yanzu naga wucewar saurayin nata .
Cikin sauri suka nufi gidan su labiba, laɓewa raihan da abban sa sukayi, suna kallo Sadiq ya faka motar sa, Jim kaɗan saiga labiba ta fito dake yariga daya shaida mata zuwan nashi ,lokacin da sadiq ya shaida mata abinda raihan yace, "jiransa acikin gida da kuma inda zasu rinka yin Hira sosai Abin yabata mamaki, amma sanin Hali irinna inna yasa ta amince suka shiga cikin gidan.
Nunawa abban sa labiba da Sadiq yayi lokacin da suka shige cikin gidan, rike haba malam sule yayi yace ,"lallai yaran yanzu saidai abarsu, shiyasa akace ba'a shaida ɗan yau.
Murmushin samun nasara raihan yayi sannan suka nufi gida.
Suna isa gida raihan yakira Sadiq ya zura masa uban karya, da cewa abba bashida lafiya, hakuri yabaiwa labiba sannan ya shaida mata rashin lafiyar malam sule.
Washa garin ranar kuwa malam sule da 'yan uwansa suka tafi gidan su zakkiya dan nimawa 'dansu Aure, walakanci da kaskanci kuwa sun ganta gun mahaifin zakkiya, daga karshe ya amince bisaga sharaɗai daya gindaya.
Susai rai malam sule ya bace, saida 'yan uwansa suka rinka bashi hakuri kafin ya hakura.
Tsabar farin ciki ranar Inna sadiya bin makota ta rinkayi tana faɗa musu auran raihan da zakkiya.
Haka labari yaci gaba da tafiya har kunnan labiba, da farko ta karyata zancan,dan haka ta yanke shawarar kiransa dan taji da kunnan ta, saida kiran ta kusa tsinkewa sannan ya ɗaga murya adakile yace, "hello ,gyara murya tayi tace, "ina ini yaya, "lafiya kalau wacece?😲ware ido tayi jin tambayar da yayi mata, sannan Hali irin nasa yasa tayi murmushi tace,"nice labiba.
,"To ya akayi?
,"babu komai dama jinayi anata zance cikin anguwa wai zakayi Aure da gaskene?
,"Da gaskene kina da matsala da hakkanne?
Kuka ne yaso kwace mata amma ta danni tace, "a a banada matsala da auran ka,saidai inada matsala danso nake nasan matsayina agunka.
Dariya yafashe dashi saida yayi Mai isarsa sannan yace, "na daɗe ina tunanin wawanci irin naki, saida ban tabbatar ba sai yau, to inbanda shashanci aikin fi kowa sanin raihan mata ɗaya kawai yake da burin Aure,dan haka ki Sani bakida wani sauran matsayi agurina.
Bai tsaya jin amsarta ba ya katse wayar hade da jan tsake, tsaye Sadiq yake rungume da hannu duk da raihan yasan da shigowar sa amma hakan baisan yaji dar ba.
Murmushi yayi yace, "Sadiq yadai ka tsaya daga kofa?
Tsaki Mai sauti Sadiq yaja yace, "mamakin ka kawai nake .
,"Mamakin mee kenan ?
,"tsakanin ka da labiba mana.
Dakatar dashi raihan yayi yace, "dakata malam abinda ya kawo ka kenan?
Murmushi sadiq yayi yace, "a a ,tunda bakason gaskiya, yanzu nake jin labarin auran ka da wannan kucakar yarinyar raihan, Anya kasan kuskuran da Kake shirin tafkawa kuwa? shin kasan abinda zaka rasa kuwa raihan?
Batare daya tamkashi shiba ya fice daga office ɗin yana Mai jin zafin sunan da sadiq ya kira matar sa wato zakkiya, ware ido nayi nace lailai wato harma ta Zama matar ka ko?
Fita daga office ɗin shima yayi ya nufi gida, labartawa umman sa halinda ake ciki yayi.
Kallon sa tayi naɗan lokaci sannan tace, 'ni dai aiya sanina na tarbiyantar dakai tafarkin addinin gaskiya wato muslumci, kuma ALLAH shaida ne akan hakan, Dan haka bana zaginka da bin wata
Hanyar dabata dace ba dan cimma manufarka kansu,dan haka nake kara gargadin ka, karda kayi sake kayi abinda zakaji kunya wata rana,tashi kaje.
Murmushi sadiq yayi yace, "Nagode umma kuma kisani ɗanki bazai taba bakanta ran wasu domin samawa kansa farin ciki ba.
ALLAH yabiya ki da gidan aljanna abisa tarbiyar da kika ɗaurani akai .
"Ameen tace tana Mai kara alfahari da ɗanda ALLAH yabata.
Ita kuwa labiba abu yaci tura ,domin kuwa kullum cikin ciwo take abu dai babu sauki ,Sadiq kuwa bai taba barinta cikin damuwa ba, Dan kowani dare yana kofar gidan su, yana sake jaddada mata raihan natane ita kaɗai.
Yaune aka saka ranar auran raihan wata biyu masu zuwa, ranar ne kuma mutanan dake haya agidan suka kwashe kayansu domin tafiya garinsu, kuma bazasu sake Dawowa garin kaduna ba, sosai rashin mutane masu kamala ya sake dagula lamarin aisha labiba.
Tana cikin haka shine taji shigowar raihan, Wanda Sanadiyar haka yasa bayan fitarsa tari Mai karfi ya sarke ta, cikin ikon ALLAH Sadiq ya kaita asibiti.
Back to story
Wasu zazzafar hawaye ne suka shiga zarya akuncin sa,yace,"Meyasa nayi miki haka labiba?baki cancanci haka daga gare niba Meyasa Meyasa .
Tashi yayi ya shige toilet Dan watsa ruwa dan ba karamin ciwo kansa ke masa ba, bayan ya kammala yakwanta da nufin gobe zaije yabata hakuri, saida bayajin zai iya sauke zancan auran sa da zakkiya , amma yana da yakinin labiba zata yarda ta jirashi zuwa bayan auransa sai suyi Aure, da tunanin haka barci barawo yayi awan gaba dashi.
[6/13, 14:37] Safnah: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*DUK A SANADIN SOYAYA*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_
https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial
*T. W. A✍🏻*
*STORY*
&
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*chaptar* 1️⃣0️⃣
*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*
,,,,,Sosai jikin labiba yaye sauki tunda yanzu zagewa take su kwashi hirar su Mai tsayi da Hafsah ,tun tana no ƙewa harta saki jiki da ita, mummy MA tazo har asibitin ta gaishe ta, sannan ilham MA ba'a barta abaya ba tana zuwa lokaci lokaci, Abu ɗaya ke damun labiba 'idan ta tuna kwanakin daya rage ayi bikin raihan,raihan kuma nata amma bada ita za'ayi auran ba.
Duk lokacin data tuna da hakan takan tsinci kanta awani mawuyacin halin, takanyi kukanta iya son ranta hakan yasa har yanzu magungunar da Dr yake bata basa aiki sosai Dan sosai take cikin damuwa.
Tunda sayin safiya Sadiq ya nufi asibitin yana shiga wayar sa ta fara ruri, koda yaduba raihan ne yarya tsinke bai ɗauka ba, murmushi yayi yace, "ina kwana aisha, yanda ya kira sunan nata saida taji yarrr acikin jikin ta, kasa ɗago Kai tayi tace, "kayi hakuri naga kamar zaka amsa Waya ne, ina kwana?
"lafiya lau aisha ya jikin naki?
Bata kaiga buɗi baki ba Dr ya shigo da murmushi asaman fuskar sa ,musabaha sukayi sannan ya shiga tambayar ta yanda takeji,rike kansa yayi yace, "kash aisha kina da matsala wai sai yaushe zaki cire damuwa acikin ranki ki bari ki samu lafiyar jikin kine wai?
Tsareta da ido Sadiq yayi yana karantar yanayin ta, kasa buɗi baki tayi dan ganin yanda duk suke mata kallon tuhuma.
Juyuwa yayi ya fuskanci Sadiq yace, "yallabai inaga zamu cigaba da riketa anan, Dan gaskiya har yanzu bugun zuciyar ta bai daidai taba, girgiza kai kawai sadiq yayi dan zuwa yanzu ta fara bashi haushi, har zuwa yaushe zata cigaba da saka kanta a damuwa saboda wani banza can wanda baima San tana Raye ba.
Saida dr ya tabashi sannan ya dawo daga duniyar tunani daya faɗa, takarda magungunar da za'asaya ya Mika masa, karba yayi yayi masa godiya sannan suka fice harshi.
Kuka Mai ɗan sauti ta shiga rerawa gwanin ban tausayi,harya dawo bata Sani ba sai jin muryar sada tayi daga sama yana cewa, "aisha make damun ki?
Cike da firgici ta dago Kanta Sam bata so yadawo yasame ta acikin wannan yanayin ba, duk tunanin ta yatafi ne, to Ashe sayo magungunar ya tafi ,shiru babu amsa banda hawaye babu abinda ke zarya kan fuskar ta.
Zama yayi dan nisa da ita yana sauraron yanda kukanta ke taba duk wata gaba ta jikin sa,sam kaunar ta da tausayinta sun kasa barin ilahirin ruhi da gangar jiki sa,buɗi idanuwan sa yayi cikin muryar sa Mai daɗin sauraro yace, "aisha nasan damuwar ki,ki Sani da ina da ikon dawo da raihan cikin rayuwar ki da tuni na yi miki hakan, Dan jinki nake kamar yanda nake jin Hafsah da ilham a jiki na, 😲😲buɗe baki nayi nace, "Kaidai faɗi gaskiya malam Sadiq.
"ki Sani idan kika cigaba ahaka tofa rayuwar ki tana cikin hadari duba da abinda Dr yafaɗa mana akan ciwon ki,ko sokeki ki rasa ranki kan wani can wanda harkar gabansa kawai yake.
Girgiza kanta tayi cikin sauri alamar aa ,Murtuke fuskarsa yayi yace, "idan har kina so mu shirya to ki cire duk wata damuwar raihan aranki, kinji?
Girgiza kai kawai tayi masa, murmushi yayi yace Yauwa labiban Hafsah.
Murmushi ne yasubuce mata jin sunan daya raɗa mata.
Saida yabari hafsah da ilham suka zo sannan ya Tashi yafita da alkawarin zai dawo nanbada jimawa ba.
Fitarsa keda wuya Hafsah ta dawo inda take tace, "Kai lailai Abin daɗi da yawa haka yaya Sadiq ya kawo miki?
Murmushi tayi bata ce komai ba.
"lailai gaskiya anfara nuna wariyar launi anan wato ke kaɗai kawai yaya yasani ko? Hmmm nikam naji irin wannan soyayar,muma ALLAH ya haɗamu da maso kaunar mu hak...
Yanayin firgitar da tsoro da Hafsah ta gani akwayar idon labiba shiya tsayar da ita daga karasa maganar da dama tayi tane da gaiya.
Murmushi tayi kamar batayi wani abun ba tace, "aunty labiba yanaga kin razana, hmmm tunanin ki bamu Sani bane, hmmm kece fa kike boyewa, amma yaya ko ina yana nuna kece kwanar sa,dan haka MA ki daina boyewa.
Kuka Mai sauti ne ya kubcewa labiba wanda ita kanta bazata cega dalili ba, kuma sannan bazata ce taji zafin maganar Hafsah ba, saidai ma Dariya da shirmanta ya bata,to menene dalilin kukan ta bayan tasan raihan ɗinta zai dawo gare ta, domin ita kaɗai aka halilce shi, itama haka.
Sosai kukan nata yataba Hafsah da ilham dana sanin abinda tafaďɗ tashiga Yi Dan batasan Abin zaikai da kuka ba, hakuri ta shiga bata itama kamar zatayi kuka tace,"kiyi hakuri aunty labiba wallahi wasa kawai nake miki.
Girgiza Kai tayi tace, "baki min komai ba Lil sis,saidai kisani Nida yayanki mutuntakace kawai babu wata halaka data danganci soyaya, amma kisani yana da wani gurbi na daban acikin zuciyata wanda nikaɗai nasan ta, tabbas duk macan data samu yayanki a matsayin miji tabbas tayi babban dace.
Murmushi duk kansu sukayi, Sadiq kuwa da yake tsaye ajikin kofa tunda yaji sautin kukan labiba ya tsaya yana rauraron duk abinda suke faɗa, dafe kirjinsa yayi ya koma mota ya kwanta ,Shikansa baisan adadin lokacin daya ɗauka cikin wannan mawuyacin halin ba, saida yaji anata kiraye kirayan salla sannan ya sauke idanuwan sa saman agogonsa wanda tuni sun daɗe da canza launi su zuwa ja, karfe hudu yagani ajikin agogon.
Gyara rigarsa yayi haɗe da share zazzafar hawayan daya gangar masa, muryar Hafsah yaji tana cewa, "yaya harka dawo daga duniyar tunani?
Kallon ta yake ciki da mamaki dan sam baisan tana cikin motar ba, to yaushe mata shigo motar baisani ba?
Murmushi tayi tace ,"yaya kana mamakin gani na alhalin baka San lokacin dana shigo bako?" Karka damu lokacin kana cikin duniyar tunani na shigo.
Duƙar da kansa yayi dan gabaki ɗaya yarasa abinda ke damun sa,shidai yasan rashin labiba a rayuwar sa babu shakka babbar asara ce, dafeshi tayi tace, "kayi hakuri yaya ina mai tabbatar maka labiba taka ce da yardar ALLAH inajin hakan ajiki na.
Kallon ta yayi, ita kowa kara girgiza kanta alaman tabbatar wa, fita daga motar yayi batare da yace da ita komai ba, Dan babu shakka idan yabuɗe baki tofa hawaye zaiyi, shikuma bayason yatashi hankalin Hafsah.
*********
Shirye shiryan auran raihan da zakkiya ake gadan gadan babu kama hannun yaro yaune zasuyi kamu,amma gabaki ɗaya hankalin raihan Baya jikin sa ,Dan babu inda baiyi ba Dan ganin sun haɗu da labiba amma gabaki ɗaya abu yaci tura, kullum saiya je kofar gidan, amma ako yaushe kofar arufe yake ganin sa, gashi number ta baya shiga, koda yayi wa sadiq magana share shi yayi, ganin zai dame shi yasa ya kalle shi shekeke yace, "waikai raihan yaushe ka bani aikin gadin labiba?
Hakanan yanaji yana gani labiba tayi masa wuyar gani, murmushi yayi lokacin daya tuna da irin son da labiba take masa yace , "nasan duk inda kike bazaki taba daina sona ba labiba, da wannan tunanin ya shirya yanufi gidan su zakkiya inda ananne za'ayi wasan kamun.
Susai suka zubar da kuɗi kamar asama ake samunsu kuɗi yayi kuka ranar, anci ansha, Inna sadiya kuwa ansamu abinda ake so sai rawar Kai take adole ita uwar Ango.
Ahaka aka watse kowa ya nufi gida,sam barci ya gagari raihan da zarar ya kulle idanuwan sa da niyyar barci gabaki ɗaya labiba yake gani, janyo wayar sa yayi ya kira layin ta, cikin sa'a kuwa lokacin Hafsah ta fito daga toilet, labiba kuwa tadaɗe dayin barci sakamakon alurar barci da Dr yayi mata.
Da kamar karta ɗaga saidai ganin sunan daya fito baro baro a fuskar wayar *my heart desire* hakan yasa ta tabbatar da raihan ne, da sallama ta ɗaga,shikuwa harwani lumshe idanuwan sa yake duk atunanin sa itace yace, "da fatan kina lafiya RAI'ISH ina kika shig...
Wata uwar tsawa Hafsah ta daga masa wanda saida labiba ta motsa,ganin haka yasa tafita daga dakin tace, "ma yaudari ,azzalumi,munafiki mai mance tarin alkairi, mikuma kike nima da ita yanzu.
Mikewa yayi jin muryar dabana labiban Saba Tana zazzaga masa masifa, saida ta dire cikin Kunar zuciya yace, "wace irin jahila ce ke, sakarya waye ubanki acikin fadin garin nan daya baki izzar zagina.
,"Ubana shine ubanka daya kasa baka tarbiyar data dace harkake iya mance wacce tayi maka tarin al'kairai,malam gashawara zanbaka Kayi gaggawar fita daga rayuwar labiba idan kuma bahaka ba wallahi kayi kuka da kanka, wawa Mara rama ragon suna, harzata katse ta dakata sannan tace, "inaso kasani ka tabbata asararre domin kuwa matar da Kake shirin aura bakaramar karuwar bakin layi bace, karya zaka aura wacce duk wanda yayi mata haushi take bi, kitt ta kashe wayar gabaki ɗaya Zama tayi agurin ta fashe da kuka, abinda bata taba yiba shine tayi yau kuma duk asanadin soyayar da take yiwa labiba, sosai take jin zafin yaudarar labiba da raihan yayi, ďagowar da zatayi suka haďa ido da labiba tana tsaye rike da Kai GA hawaye gabaki ďaya yagama wake alahirin fuskar ta.......
*Love you all*
[6/13, 14:37] Safnah: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*DUK A SANADIN SOYAYA*
❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_
https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial
*T. W. A✍🏻*
*STORY*
&
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Chaptar* 1️⃣1️⃣
*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*
,,,,,Cike da tsoro da fargaba Hafsah ta nufi gurin labiba Tana Mai cigaba da zubda kwalla,ganin haka yasa labiba ta shige cikin ɗakin da sauri kifa kanta tayi asaman katifar tare da sakin kuka Mai tsuma zuciya.
Cike da dana sani Hafsah ta tsaya akanta cikin muryar kuka tace, "Dan ALLAH kiyi hakuri ni kaina nayi dana sanin shiga cikin lamarin daba nawa ba,harna aikata wannan babbar laifin, nasan yanzu kina mai cike da jin haushi na, koma ince kin tsane ni ,amma kisani tamkar yar'uwa nake ɗaukar ki shiyasa nake jin zafin abinda raihan yayi miki bayan duk halalcin ki agare shi.
Ɗago Kai labiba tayi ga mamakin Hafsah sai taga labiba ta rungume ta tana cewa, "bansan dame zan saka muku ba, kune kawai nake gani tamkar dangi na, kun kaunace ni alokacin da duniya ta juyamin baya,aku yaushe kuna ƙokarin mayar da damuwata taku, bansan dame zansaka muku ba, kun gamamin kumai.
Ɗago kanta Hafsah tayi haɗe da share mata hawaye tace, "Karki damu da akwai abinda zaki saka mana dashi aunty labiba.
Cikin sauri tace, "ki faɗamin ni kuma nayi miki alkawari Yi muku shi idan harbai sabawa addini naba.
Murmushi Hafsah tayi tace, "inaso ki cire damuwar raihan aranki, ki ɗauka baki taba sanin Saba, aunty labiba ki Mikawa ALLAH duk kannin lamarin ki, ina Mai tabbatar miki ALLAH zai musanya miki da mafifincin alkairi.
Murmushi labiba tayi tace, "nayi miki alkawari IN SHA ALLAH daga rana irin ta yau bazan sake saka damuwar raihan araina ba.
Aranar gabaki ɗaya su kwanan farin ciki sukayi wacce sun daɗe basuyi irin taba...
*********
Raihan kuwa wani irin bacin rai dabai taba tsintar kansa aciki bane yamai dirar mikiya cikin kankanin lokaci ya gama haɗa gumi,tashi yayi yashiga zarya adakin yana tunanin wace yariyan ce wannan wacce harta samu zarra zagin sa,banda haka harda yiwa matar sa kazafin zina,tashi yayi yashiga toilet Dan watsa ruwa ko zaiji daɗin jikin sa..
*******
Tun safe Sadiq ya iso gidan raihan, saidai gabaki ɗaya yanda yaga raihan ɗin tabbas yasan akwai wata akasa, murmushi yayi yace, "yallabai ya akayi ne?yau fa ranar kace Ango Kake angon zakkiya, dan haka yanzu ba lokacin haɗa girar sama da kasa bace, com on tashi ka shirya kasan 10-am za'aɗaura Aure ko.
Yake kawai raihan yayi haɗe da riku hannun Sadiq yace, "tabbas ni ɗin Ango ne amma ba angon labiba ba Sadiq, ba RAI'ISH ɗita zan aura ba, Sadiq shin banyi butulci ba? Shin ALLAH bazai kamani da hakkin AISHA labiba ba?ka taimake ni ka taimakeni Sadiq kaji abinda wata yarinya take faɗamin jiya dana kira RAI'ISH ɗita kuwa?.....zaiyana masa yanda sukayi da Hafsah yayi tare da fashewa da kuka.
Sadiq kuwa wani irin zufane ya keto masa Dan koba afaɗaba yasan tabbas Hafsah ce, jingina Kai sa yayi yace, "kayi hakuri yanzu ba lokacin wannan maganar bace raihan be a man mana idan muka dawo sai muyi magana.
Da haka yasamu ya rarrashi raihan yashirya suka nufi gurin ɗaurin Aure.
Bayan andawo daga daurin Aure sadiq ya wuce asibiti, sosai yaji daɗin ganin yanda labiba ta watsake Zama yayi shima aka cigaba da Hira Candai yatuna da zancan zagin da Hafsah tayi wa raihan.
Janta yayi zuwa harabar asibitin inda yake shiga batanan yake fita ba ,jin muryar labiba a bayan su yasa suka juya cikin sauri, murmushi tayi tace, "yaya Sadiq fadan ya isa haka mana, in fat nifa banga abinda Lil sis tayi ba, shin laifine Dan k'anwa ta taya yarta faɗa idan an cuceta? Shin bazaka iya faɗa akaina ba yaya Sadiq, shin dama ikiraran da Kake yi na cewa ni yar uwar kace kenan duk faɗane?
Fashewa da kuka tayi,gabaki ɗaya jikin sa yayi sanyi,matsowa kusa da ita yayi yace, "kiyi hakuri wallahi ba haka bane, da gaske ina jinki araina fiye da tunanin ki, ki Sani kece mace ta farko danake jinta yanda kikasan tsoka ɗaya amiya, ki yarda dani labiba zan iya mallaka miki komai arayuwa ta.
Share hawaye tayi ilahirin fuskarta ɗauke da murmushi tace, "banida abinda zansaka maka dashi yaya Sadiq,nagode sosai da nuna kulawar ka aikaina, sannan kasani Aure da mutuwa ne kawai zai rabani dakai da ahalinka gabaki ɗaya.
Murmushi yayi ganin bata gani abinda yake nufiba yasa yashere suka koma cikin ɗakin.
Shikuma yaja motarsa yanufi gidan raihan domin shirye shiryan dinner da zasuyi karfe hudu.
Yana isa yasamu abokan aikin su cike da gidan hakannan ya kutsa cikin su akata shirye shirye ,saidai gabaki ɗaya raihan Baya cikin natsuwar sa gabaki ɗaya yayi wata irin rama lokaci ɗaya,jan hannun sa Sadiq yayi suka nufi dakin sa kasancewar dama afalo suke, murya kasa kasa yace, "shin raihan sukake ka jaza mana Abin magana? Com on raihan ka saki ranka Dan ALLAH koma menene nayi maka alkawarin taimaka maka kaji please do dat for mee.
Nod dakai kawai raihan yayi, shikam bama rashin labiba ke damunsa ba, domin kuwa yasan duk duniya babu wacce labiba zataso sama dashi, abinda yafi komai damunsa shine son sanin wacce Mara kunyar yarinyar ce ta zageshi.
Ahaka suka halalci gun dinner din ,sosai gurin ya ƙayatu da abubuwan zamani .
*Kuyi haƙuri wallahi ban kasancewa daga cikin mutane masu halartar gurin taro sosai ba, shiyasa bansan abubuwan da ake ,shirya wa ba , Please manage this* 🙏
Bayan ankammala aka mayar da amarya gidan iyayanta Dan shirin kaita gidan mijinta, agajiye ta faɗa saman gado,duka hibba wacce itace kawar cin mushanta tace, "Laila garama ke tashi muyi wacce zata fishemu, kisan dai yau gabaki ɗaya bamuyi ba, sannan wani karin haushi wai ace ina Raye baby zaki tafi wani katun banza yaji ya danne min ke ,mikewa tayi zata bar ɗakin cikin fushi, da gudu zakkiya ta sauko daga kan gadon ta rungume ta.
,"kiyi hakuri baby wallahi bahaka bane kinfi kowa sanin yanda mum ta matsamin akan zancan Auren nan sanin kanki ne, har cewa tayi zata hanaki zuwa gidan nan ,kinga nikuwa Gara na mutu dana daina ganin ki, cikin sauri hibba ta juyo saka bakin ta cikin na zakkiya tayi ta fara tsosa cikin salo wanda lokaci daya zakkiya ta nime natsuwar ta tarasa, nan da nan yaɗata mayar da martane cikin zafe zafe .
Sakinta hibba tayi ta rufe musu kofar, izuwa lokacin kuwa zakkiya tagama cire kayan jikin ta, itama cire nata tayi ta haye saman gadon, kissing ɗinta hibba take hade cike da salo irin tasu ta ƴan duniya,saida hibba ta tabbatar zakkiya ta faɗa tarkonta ,Murmushin mugunta hibba tayi ta cire bakin ta mikewa tayi zata sauka akan gadon, sanin halinta yasa zakiya ta Mike cikin sauri ta riko hannun ta,narkewa tayi ajikinta ,nan danan ta canza muryar ta zuwa kalar tausayi tace ,"haba mana yazakimin haka baby?
Turbune Fuska tayi tace, "hmmm ke harkina da bakin cewa karnayi miki haka? Kin mance irin magiyar danayi miki kan karkiyi Auren nan? Harce miki nayi Karki damu da zancan mum ko awaje basai mundinga haɗuwa ba,amma kika ki.
Janta zakkiya tayi ta fara rarrashinta cikin iya salon yaudara harta samu ta Shawo kanta, bugun kofar da ake yine yasa suka sadoda cikin sauri suka shiga mayar da kayan su, saida suka tabbatar da sun kimtsa sannan zakkiya ta buɗe kofar.
Mum tagani ranta abace take kallon zakkiya dan tuni hibba ta shige toilet dankar Mai bugun kofar yaganta harya gane abinda suke aikatawa, murmushi mum tayi ganin zakiya ita kaɗai rungume ta tayi tace, "yadai kika kulle kanki aɗaki gashi har angama shirye shiryan kaiki gidan ki.
Rungume mum tayi tasaki kuka Mai karfi, da sauri mum ta zare ta daga jikin ta tace,"menene zakkiya ?me aka miki?
Cikin kuka tace yanzu mum tafiya zanyi na barki wai Don ALLAH?
Murmushi jin daɗi mum tayi ganin yanda zakiya ta zakge sai risgar kuka take iya karfi ta tace, "kiyi hakuri kuwace mace ta gaji ganin irin wannan ranar wace take cike da abubuwa guda biyu, na farko farin cikin ganin ranar da ba kowace mace ke ganin Saba, Dan haka saiki godewa ALLAH , na biyu bakin cikin rabuwa da mahaifa, Dan haka ba kuka zakiyi ba saidai godiya ga mahalilcin ki...
[6/13, 14:37] Safnah: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*DUK A SANADIN SOYAYA*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_
https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial
*T. W. A✍🏻*
*STORY*
&
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
_
*Page* 1⃣➖2️⃣
*Bismillahi rahamanin Rahim*
Share hawayan ta Zakkiya tayi kamar gaskiya tace, "Nagode mum belive me you are de best mum in the world.
Mum kuwa kara rungume ta tayi tace, "maza jeki kishirya Karki bata lokaci.nod dakai kawai tayi ta rufe kofar.
Hibba dake toilet kuwa cike da mamakin kirsa irinta zakkiya ta fito tace, "lailai zakiya keɗin ta dabance harda wani kuka wato kega ta ALLAH ko?tafawa sukayi cikin salon yaudara kowace ta shiga shiri cikin sauri .
Tsafta fito daga ɗakin hibba nabiye da ita abaya ,da kyar aka bambare ta daga jikin mum kuka take tsakanin ta da ALLAH har aka shigar da ita mota, kamshin turaran sane yasanar da ita yana cikin motar, kwanciya tayi ajikin sa Tana maida numfashi alamar taci kuka, nikuwa nace aikya bari ya janyo ke dakansa ko malama zazkiya?lol🤣🤣🤣
Zagaye hannun sa yayi ya ɗago ta kallon ta yake cikin ido yayi wanda itama shiɗin take kallo yace, "shin zazkiya duk wannan kukan kiyayyace haka kome? Maimakon tabashi amsa sai kawai yaji bakin ta cikin nashi.
shikuwa tsabar mamaki kasa magana yayi kasan cewar yauce rana ta farko da hakan ta faru dashi 😲😲😲,duk da sosai taso ta burkita masa duniyar sa, amma sosai yayi mamakin rashin kunya irinta zakkiya dan yakanji abokin aikin sa suna hirar yanda amaran su ke nuna tsananin kunya aranar Suta farko, saida daga Baya su ware kasan cewar yau da gobe ta wuci gaban wasa.
(not kisani duk da lokaci yanzu ta kawa mana abubuwa na wayewa ta fannin kula da miji da nuna soyayar ki agare shi ,hakan bayana nufin ije kunyar ki bane, ita kunya GA mace adoce,duk yanda kika kaida wayewar ki ,ki kasance mai nuna kunya awasu Al'amuran ko kuma bayan kin gama wani Abin, saiki nuna kindai yine dan faranta ransa bawai Don baki da kunyar ba azahiri.ok misali idan kunzo Raya sunna Sam Karki nuna tsansar kwarewar ki, ki ɗingayi kena nukewa, idan kuma kum gama saiki nuna sosai kike cike dajin kunyar sa ,hakan zai kara miki kima agunsa Dan haka a kiyaye, tunatarwa ne kawai)
Cire bakin sa yayi daga nata ya juya kansa yana kallon motocin dake kaiwa da komawa azahiri titin yake kallo saidai abaɗili tunanin abinda zazkiya tayi yake, ganan tunanin zai bata masa daran sa yasa ya kauda tunanin ya janyo ta zuwa jikin sa, ahaka har suka iso gidan.
Fita sukayi cike da burgewa Dan babu shakka raihan handsome guy ne sosai,bayan anyi gaishe gaishe da wasannin barkwanci daya biyu bayan tafiyar iyayan amarya, daga karshe aka watse taro da Addu'a kowa ya kama gabansa.
Rakasu yayi yana Dawowa ya rufe ko'ina da ko ina sannan yanufi ɗakin sa, saida yayi wanka yayi alwala sannan yanufi ɗakin zazkiya, ganin ta yayi kwace da wasu mahaukatar kayan barci, duk ilahirin surar jikin ta ana hangowa, rintsa idonsa yayi wani irin abu yaji har tsakiyar kansa, tuni alwalar dake jikin sa yayi hanyar garin su.
Ganin yanayin daya shiga yasa ta taso ta rungume shi, wai haɗuwar boob ɗinta da kirjinsa bakaramar harzuka masa tunani yayi ba, kissing ɗinsa ta shigayi tana romancing ɗinsa kamar ALLAH ya aiko ta, shiɗinma kasa daurewa yayi yafara mayar da martane cikin sauri.
Ahaka harsuka faɗa gado wasa da ita yashiga aigabaki ďaya zazkiya mancewa da daďin da take ji idan suna tare da hibba tayi dan wannan kam yafishi nisa ba kosa ba.
shikuwa kasa tabuka komai yayi jin yanda yazurma ciki , ALLAH yasani shikam ba mazinaci bane, amma yasan yanda ake faɗan sai ansha wahala kafin asamu hanya acikin macan da ba'ataba saduwa da ita ba, kalaman Hafsah ne suka shiga amsa kuwa akunnan sa. *sannan kasani matar da Kake shirin aura bakaramar karuwa bace, bakaramar karuwa bace, bakaramar karuwa bace*
Rike kansa da hannu bibbiyu yayi dan wata irin ciwo daya saukar masa lokaci ɗaya.
It's kuwa gimbiyar jin shiru shiru bai koma ba yasa ta janyo shi Dan ALLAH yasani bazata iya barin Saba sosai ya tayar mata da sha'awa shida hibba Dan ɗazuma bagamawa sukayi ba mum ta shigo.
Fisgar hannun sa dayayi shiya dawo da ita daga duniyar ta tana cewa, "me kuma haka sweet kafara kuma ka bari kaji yanda nake ji kuwa? Kai gaskiya babu wacce ta kaini sa'ar miji, aikuwa baiyi wata wata ba yaɗauke ta da wani razananniyar Mari wanda saida ta kusa wantsilawa.
Ɗago Kai tayi tana masa kallon mamaki harta buɗi baki tayi zatayi magana taji yana magana cikin kakkausar murya ,"ke banza Mara tarbiyya kinyi gangancin shiga rayuwa ta, kin Zama sakarya dakeka zubda mutumcin ki tun awaje, sannan kisani bazan taba sakin kiba,anan zaki zauna saina gana miki azabar da saikin gwammace mutuwa da rayuwa banza sakarya karuwa kawai.
Tsaki yayi yajuya zai fita daga ɗakin, tsawa ta daka masa cikin dakiya ta miki ta nufi gaban sa tace,"kayi kuskuran ɗaukar mataki batare da katuna da wacce Kake Aure ba ayanzu, shin tunanin ka waccen kucakar ce wacce tayi maka halalci *duk asanadin soyaya* amma daga karshe ka nuna Bakayi da ita? Hmmm to idanma kana tunanin ni zazkiya zan wulakanta agunka wallahi wallahi karya ne karya ne.
Sai kuma ta fashe da kuka Tana tuno yanda sukayi da hibba jiya,kuka mai karfi ta sake harda burgima faɗi take ka cuceni uncle ka cuceni dama nasani wannan ranar zata iskeni, ranar da Nida iyayena muka ɗade muna jiran zuwan ta, tofa yau gashi tazo, Kara fashewa da kuka tayi harda bubbuga kanta, haba nandanan saiga jini.
Cikin tsoro da firgici raihan ya nufi inda take, ɗagota yayi yace, "wai menene haka zazkiya sokike ki kasha kanki sanadin ace Nina kasheki ko?
Bai saurare taba ya ɗauke ta cak zuwa toilet wake mata goshin yayi sannan ya ɗauko auduga ya goge mata jinin, Jingina da jikin gadon yayi yace, "ina jinki faɗamin wanine uncle da kike cewa ya cuce ki?
Matse hawayan dake idonta tayi cikin shakshakar kuka tace, "tunda nataso babu abinda na tsana irin karatu duk yanda abba na yayi amma Sam koda natafi wasata kawai nake Bandamu na sa kaiba, lokacin dana fara wayau ina s-s 2 gabaki ɗaya sai naji babu abinda nake so sama da makaranta Dan ganin yanda yarinyar makuciyar mu kullum ake canza mata makamai a makaranta, amma saidai kash bana da ilimi.
Damuwa sosai nasawa abba na sannan ya samu min uncle da zai dinga zuwa gida munayin lesson, mun ɗibi lokaci munayi amma Sam karatun yaki Zama, haka yasa kullum sai nayiwa malamin kuka kan zanbashi komai da yake so indai zaisa na iya karatu, Wanda ni duk atunanina kuɗi ne Don kullum abba yana bani kuɗi mai yawa.
Wata rana mum da abba sun fita ziyara uncle yazo, sosai ranar naga yanda ya haɗa Fuska babu alamu Dariya afuskar sa, cike da mamaki nake tambayar sa malam wani abu aka maka naga fuskar ka ahaɗe.
Kara haɗa girar sama data kasa yayi yace, "ke nifa nagaji da koyar dake bakya ɗauka gaskiya bazan iya ba daga yau bazan kuma Dawowa ba, nanfa nashiga tashin hankali kuka nake kamar karamar yarinya harda Hawa jikin uncle ina burgima, nanfa naji ya saka hannun sa cikin rigana yana matsa min nono wanda alokacin basu wani Yi girma ba.
Wani irin daɗi naji ya ziyarce ni lumshe ido nayi bance dashi komai ba, har saida ya cire min kaya yana shirin min fyaɗe nanfa muka fara kokawa, amma ina saidai uncle ya karbemin mutumcina aranar aika aika na rashin imani wanda saidai kawai na ganni kwace agadon asibiti da kyar aka samu na dawo haiyaci na.
Kara ɗaga sautin kukanta tayi.
Shikuwa raihan tuni dana sanin abinda yayi mata yashiga Yi tasowa yayi ya nufi inda take kwace tana burgima ɗagata yayi ya zaunar da ita sannan yafara magana cikin muryar lallashi yace, "kiyi hakuri nakasance Mai sonkai, amma Dan ALLAH ki gafarce ni.
Murmushi zazkiya tayi aranta tana mamakin yanda akayi ta iya shirya labarin karya haka.
Rungume tayi tace, "babu damuwa na yafe maka, nandai suka shiga kissing juna, kankace me tuni sun koma ruwa.
*Nikuwa nace lailai raihan ka rufta*
[6/13, 14:37] Safnah: ❄❄❄❄❄❄❄
*DUK A SANADIN SOYAYYA*
❄❄❄❄❄❄❄❄
*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERIN OUR READERS_ 💪)
https://www.facebook.com/100452275039839/photos/a.100452311706502/100452611706472/?type=3
*P.W.A*✍️
*STORY*
&
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
1⃣3⃣
*Alhamdullah dukkan godiya su tabbata ga ALLAH mahalilcin kowa da komai da yayi min sauyi, wacce nake fatan ta zama alkhairi agare ni.*
_Tabbasa agari ni kun kasance jigo,ƴan A T k musamman hasanan da Muhammad karim, tabbas baki bazai iya furta adadin godiyar data kamace kuba, ALLAH ya saka muku da mafificin alkairi_
*Bismillahi rahamanin rahim*
Sai kusan asuba raihan ya samu ya sarara domin kuwa, duk lokacin daya nuna ya gaji lokacin ne zazkiya zata nuna tsansar bukatar ta, babu yanda ya iya haka ya biye mata saidai,shi Kansa yasan yau dai daƙer ya moru.
Tashi yayi ya nufi toilet ya sarkake jikin sa,alwala yayi sannan yazo yayi nafila raka'a biyu, sosai yaji mamakin ganin zazzkiya tana barci harda minshari,kiran sunan ta yashiga Yi yana cewa, "Dan ALLAH zazkiya ki tashi ki tsarkake jikin ki.
Mutsuka ido tayi tace, "haba sweet wallahi barci nake ji, kabari zanyi.
Haka ya hakura ya nufi ɗakin sa,sai kusan karfe goma ya farka, toilet ya shiga yayi wanka ,saida ya shirya tsaf sannan ya nufi &akin ta,baki buɗe yake kallon ta ganin zazkiya akwance babu alamar ta tashi tayi wanka bare wani abu wai shi Sallah.
Cikin kunan rai ya nufe ta, wani wawan duka yayi mata a ƙaffa, a firgice ta farka, ganin raihan ne yasa ta saki murmushi tace,"haba sweet wannan wani irin abune? Haka ake tayar da mutum?
Murtuke Fuska yayi yace, "malama ki tashi kiyi Sallah.
Tsaki tayi tace,"wai ni honey karfe nawa yanzu da kake damuna?
Watso mata harara yayi yace, "wallahi idan baki tashi ba saina Saba miki.
Mikewa tayi tana gunguni ta shige toilet.
Zaune yake yana jiran fitowar ta, sallaya ta shimfiɗa ta tada Sallah, tun daga tsayuwar ta, raihan yafara ganin kuskure,da mamaki yake kallon ta ganin yanda take dungure wai adole tana Sallah.
Babu batun Addu'a ta Mike ta nufi gurin shi, Zama tayi akan cinyan sa tace, "baby wannan kallon fa?
Rike hannun ta yayi yace, "zazkiya shin wani islamiya kike zuwa lokacin da kike gida ?
Dariya tayi harda rike ciki tace, "hmmm nikam wallahi harka bani Dariya nikam namance shekara.
Murmushi takaici yayi ya Miƙe yace, "kizo kici abinci mum ta aiko mana dashi.
"Wani mum ɗin?
"Wani mum kika Sani bayan mum ɗita.
Rike haba tayi tace, "tab nikam wallahi bazan ci abincin mum ɗinka ba, kawai kabari mum zata aiko mana dashi.
Wani irin bakin ciki yaji ya ziyarce shi lokaci ɗaya yace, "kisan me kike faɗa kuwa, to bara kiji duk rashin kunyar ki da rashin iya maganar ki, Karki yarda tsausayi Ya kaiki gun mum ɗina idan kuwa ba haka ba wallahi saina sassaba miki.
Wucewa yayi ya shige cikin ɗakin sa ransa na mugun zafi.
Bin bayansa tayi da kallo tace, "ka daiyi kagama danni wallahi ko yunwa zata kasheni bazanci abincin wannan kazamiyar tsohuwar ba.
Bata tsaya bata lokaci ba koma ta kwanta.
*****
Sosai jikin labiba yayi sauki Dan yau suke saka ran sallama, tuni tayi watsi da lamarin raihan, saidai lokaci zuwa lokaci takan ɗan taba tunanin sa.
Da gudu hafsa ta shigo ɗakin rike da Leda fuskarta kuwa kamar anmata albishirin gidan aljanna.
Da mamaki labiba tace, "hmmm yau kuma wani labari little tazo mana dashi?
Waro ido tayi tace, "tab salon nafaɗa miki yaya yamin duka,a a kibari shida kansa yafaɗa miki.
Suna cikin haka sadiq yashigo yace, "badai kin karya alkawari ba?
Girgiza Kai tayi tace, "a a wallahi bankarya ba.
Dariya duk kansu sukayi labiba tace, "Kai little shine harda rantsuwa?
Gyara murya sadiq yayi yace, "aisha kishirya daga gurin likita nake ya tabbatar minda cewa babu wata matsala zamu iya tafiya.
Labiba batasan lokacin da tayi wani tsalle ta rungume Hafsah ba, domin kuwa ba karamar gajiya da asibitin tayi ba.
Rintsa idonsa sadiq yayi ganin yanda mazaunannan ta suke rawa ta cikin rigar dake jikin ta wanda bashida wani nauyi kasan cewar yadin materiyal ce.
Kunya sosai labiba taji lokacin data fahimci irin shirman data tafka.
Cike da jin kunyan sa suka haɗa kayansu suka shige mota, duk atunanin labiba gidan su za'akaita, amma taga sunyi wata hanyar daban, harta juya zata tambaye shi, amma ganin yanda ya hada girar sama data kasa yasa taga yayi mata kwarjini, juyawa tayi gun Hafsah ,amma me sai taga kamar Hafsah MA tafi tsare gida, haka tanaji tana gani ta kasa tambayar su har suka isa wani tangamemen gida.
Wani irin kara taji cikin ta yabada tuna cewa bata fa taba sanin sadiq ba sai ta sanadiyar raihan ,kuma shima duk shakuwar su da irin halalcin da tayi masa duk asanadin soyaya amma Kalli abinda yasaka mata dashi,wasu zazzafar hawaye taji yafara saukar mata wanda ita kanta batasan tanayi ba.
Juyowar da zatayi suka haɗa ido da Hafsah ,abinda yakara firgitar da ita shine ganin wani irin muguwar hararar da Hafsah ta aika mata da shi, aituni taji wani irin jiri na ɗibar ta, haka tayi ta binsu bakinta ɗauke da duk addu'ar da tazo mata har suka karasa cikin gidan, babu kowa Afalon asalima ko motsi bata jiba bare ta saka ran ganin mutum.
Kallon yanda falon Ya kayatu take tana cikin haka taga an ɗauke wutar dake tsakiyar falon wani irin duhu Ya gauraye ilahirin ɗakin, harta buďe baki zatayi ihu taji anrufe mata baki da Fuska gabaki ďaya .ana cikin haka taji anfara zare mata kayan dake jikin ta ,Addu'a kawai labiba take domin kuwa ta sadakar kwananta Ya Kare.
Tsaf Tana ji tana gani aka cire mata Riga aka canza mata wata, sannan aka &auko dankwali aka ɗaura mata.
Saida aka gama tsaf sannan aka fara Janta tafiyan mintina biyu sukayi sannan aka sake mata baki,gabaki ɗaya kasa magana tayi, kusan mintina biyar taga wani irin haske ya gauraye ilahirin gurin gabaki ďaya da mamaki take kallon yanda yanayin gurin ya kayatu , ko ina Kwan fitila ne Mai hasken gaske ga wasu irin furanni masu sanyayawa Mai kallon su rai, gabaki &aya hankalin taya tafi ga kallon furanni taji ana she wa da Dariya Ďago Kai da zatayi tayi ido hudu da sadiq, yasha wata shadda Mai masifan kyau ,kasa ɗauke idonta daga kansa tayi dan ganin sabon mutum take masa.
Iskan daya Hura mata shiyayi sanadiyar dawowar ta daga duniyar tunani data shilla.
Saukar abu tayi akanta Mai kamshin gaske ga wakar dake tashi abakunan mutanan dake Zagaye dasu taji Wanda ita kanta batasan lokacin da suka iso gurin ba Mai taken happy birthday to you.
Kasa buye mamakin ta tayi Mai Makon farin ciki tuni kuka Mai karfi ya kubce mata,ganin haka yasa hankalin sadiq yayi mummunar tashi cikin sauri ya nufi gunta jikin sa har kerma yake, rike mata hannu yayi yana tambayar ta abinda yasaka ta kuka, ganin batada niyyar amsawa yasa ya saka hannun sa ɗaya yana share mata hawaye, bai Ankara ba yaji an wake masa Fuska da wani irin gigitatciyar mari, cikin sauri ya ɗago Kai dan ganin wanene da wannan mugun aikin,raihan yagani yana Huci kamar mayunwacin zaki.......
[6/13, 14:37] Safnah: ❄❄❄❄❄❄❄
*DUK A SANADIN SOYAYYA*
❄❄❄❄❄❄❄
0 comments:
Post a Comment