Mikewa Magajiya tai daga kan gado cikin tsananin takaicin abinda Turab ya mata, abin haushi jitai baiwarta tana sanar da ita isowar baki dan tayata murnar warkewarta.
Haka ta bada umarni suka shigo, kan gado ta koma ta zauna, kowa yazo tayata murna sai ya jinjinama Turab da kokarinsa wannan abu yafi kular da ita, wasu dan gulma ma so suke suji me ya had'a Abu Turab da Abdulmajid.
In taji haka sai dai kawai tace " zancen mutane ne kawai amma su ba abinda ya had'a su."
Sai wajen Magrib ta samu sauki tai wanka ta sa kaya sannan ta aika a kira mata Hisham.
*******
Mairo kuwa bayan ta ba Umma magani nan ta dafa mata abinci ta bata taci, suna zaune labarin abinda ya faru ya isomusu, wannan labari yasa Umma dan jin dama dama.
Mairo kuwa jitai Abu Turab ya kara birgeta, ba shakka jinin sarauta ma yawo a jikinsa, ba shakka kwakwalwarsa da basirarsa tana aiki.
Sai wajen Magrib ta baro bangaren, Basira nata mata godiya, tana tafe tana murmushi dan ba shakka hankalinta ya kwanta da abinda ya faru.
Sam bata kula da shi ba tadai san ta wuce wasu daga gefenta sai dai bata san su waye ba.
Tana tafiya kawai taji an cafko hannunta ta baya.
A tsorace ta juyo, dan sai da gabanta ya fadi lokacin daya rikota.
Kallan mamaki da takaici ta sakar masa, sannan ta kalli hannunta tace " Malam sakeni ko"
Yace " ina san magana dake."
Tace " To dan kanasan magana dani sai akace ka rike min hannu? Sakeni tun kafin mutane su gamu."
Ga mamakita gani tai ya kara kankame hannunta yace " kina tsoron aganmu ne?"
Kokarin kwace hannunta ta shiga yi tana cewa " meye hakan?"
Abdulmajid ya matso daf da ita kamar zai rungumeta tsoro yasa tai baya, karfi yasa ya rikota, cikin murya mai kama da rad'a yace " zaki biyoni ko sai na rungumeki anan?"
Idanu ta zaro ta cigaba da kokarin kwace hannunta.
Murmushi ya sakar mata yace " Gimbiyata muje ko?"
Ya karasa maganar tare da sakar mata hannu sannan ya nuna mata hanya.
Harara ta makamai sannan tai hanyar daya nuna mata.
Bangarensa ta nufa da ita a tsakar gida taja ta tsaya tare da hard'e hannayenta.
Kallanta yai yace " muje mana."
Tace " muje ina kenan?"
Da kai ya mata alama da ciki.
Harara ta kara makamai tace " d'ad'in abin ni d'in da hankalina bawai a bola ka ganni ina tsince tsince ba."
Dariya yai sannan yama masu kula dashi alama da su fita.
Suna fita ya fara matsowa inda take, hannu ta d'agamai tace " dakata daga nan Malam ko kuma wlh insama ihu."
Yace " Wayyo da naji dadi, ni ai so nake kisamin ma ihun kinga duk abinda za'ayi na riga na mallakeki kenan dan Sarki zai sani auranki saboda rufin asirin mahaifinki."
Kallansa tai kallan tsana tace " wai dan Allah in tambayeka? Ana so dole ne?" Sai kuma ta girgiza kai tace " bama haka ya kamata ince ba, dan ba so na kake ba."
Yace " Mairo abinda zakice kenan? Wlh tunda nake a duniya kece mace ta farko da zuciyata take so, inaji a raina in har ban aureki ba to tabbas zan shiga wani hali."
Baki ta tabe tace " da alama bada gidan sarauta ka dace ba da d'an siyasa ka dace, to ni ko soyayyar ce nace banayi, ko anayi dole?"
Kallanta yai sai dai yanzu fuskarsa ta nuna alamun jin haushin kalamanta.
Mairo tacigaba " Akwai wanda nake so, banaji akwai wani karin bayani dakake nema daga bakina."
Tana fad'ar haka ta juya zata fita.
Da karfi ya jawo hijab dinta, jikin bango ya sata, idanunta ne suka firfito. ya kalleta ransa a bace yace " badai wanda kike so d'in a gidan nan yake ba?"
Kai ta juyamai bata bashi amsa ba, cikin takaici ya kara cewa " badai wanda kike so sunansa Abu Turab ba?"
Juyowa tai ta kalleshi tace " koma wanene wanda nake so d'in banaji yazama dole na sanar dakai."
Hannu yakai kamar zai kifa mata mari dan har ta rintse idanunta, sai kuma taji shiru, a hankali ta bud'e idanunta.
Kallansa tai, hannunsa ya ajiye sannan yace "Mairo ko duk duniya zasu had'u dan ganin ban aureki ba wlh sai dai kowa yayi ya gaji, amma wlh nine mijinki, inkuma harni Abdulmajid ban aureki ba to wlh duk duniya ba namijin daya isa auranki sai dai in bana dorar kasa."
Kafin ta nemo amsar da zata bashi gani tai yayi ciki.
Da kallo ta bishi tama rasa me zatace.
Haka ta fito jiki a sanyaye.
Jakadiya wacce tazo wucewa dan ta dawo daga duba magajiya ta hango Mairo ta fito daga bangaren Abdulmajid, kai ta gyad'a tace " abin harya kai haka?" Dan dama an sha kawo mata gulmar an gansu.
************
Hisham zaune a kilisar Magajiya shi kadai, sai dai kana ganinsa kasan tunani yakeyi.
Magajiya ce ta shigo cikin takunta.
Ta karaso ta zauna sannan ta kalleshi tace " Yaya na d'auka na sanar dakai umarnin mikewa in har zam shigo guri ko?"
Kallanta yai yace " tuba nake Magajiya hankalina ne ya tafi."
Girarta ta d'aga sama tace " a kiyaye."
A ransa yace " ki jira hawan Abdulmajid mulki, lokacin ne zan kiyaye."
Kallansa tai tace " Abu Turab ya wargaza mana shirinmu na hukunta uwarsa."
Hisham yace " ni kaina abinnan ya kona mun rai."
Murmushi tai tace " Abu Turab! Abu Turab! Lalai na yadda jinin Abdussamad na yawo a jininsa, dole ne in zamuyi shiri na gaba sai mun shirya yanda ya kamata."
Kallanta yai sannan yace " ni Magajiya ina ganin kawai mu mikashi kabarinsa."
Wani kallo ta bugamai tace " na d'auka na fadama ba kisa ko?"
Yace " haka kikeso to muyi ta yin shiri yana wargaza mana?har sai yaushene zamu d'aura Abdulmajid akan mulki? Sai mun tsufa? Ko......"
Tsawa ta daka mai tace " YAYA!
Kallanta yai tare da yin shiru, tace " kana tunanin ni Magajiya? Ni Gimbiya Magajiya wacce mulki da takama da isa suka bi jinina, kanaso kace ni wannan Magajiyar har wani yaro wanda na girmi uwarsa, wanda aka haifa kwanan nan zaici galaba akaina?"
Kasa yai dakai yace " Tuba nake ranki ya dade, ni din wa? Ina na isa ince haka? Kawai dai gani nai mutuwarsa tafi sauki."
Idanu ta juya tace" to nace banda kisa, sannan ina tunanin ya kamata Saifullahi ya kawo kudin gaisuwa, in har bamu isa raba Turab da Bilkisu ba dolene mu nemi wanda yakeda mukami a gomnati saboda kudi dan neman taimako nan gaba
"
Hisham yace " to Ranki ya dade angama."
Mikewa yai ya fito, yana fita yabi d'akin da harara yace " wlh zakisan ni kikema tsawa, duk 'ya'yan da kike takama dasu na waye? Daga khadijan har Abdulmajid d'in?
Kiyi ki gama wlh sai nima na gasa miki aya a hannu, wa kike dashi? Wa kike dashi da zai taimakeki? Harni zaki dingama tsawa? Harni zaki ce in mike dan zaki shigo?"
Kwafa yai sannan yai gaba.
**************
Magana ta lafa a gidan Sarauta, yau take juma'a yau kuma Abu Turab ya shirya shida Sabi'u dan zuwa garin na Kano.
Mai Martaba yasa ankawo kaya sosai wanda zasu kai gidan.
*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*45*
Sabi'u kamar jira yakeyi su shiga mota, suna shiga ya kalli Turab yace " Mutumina wai ta yaya basirar taimakon Magajiya yazo maka? Gaskiya ka birgeni da ka nuna musu kai dasu d'aya ne."
Abu Turab ya dafa kafad'arsa yace " baka kawo komai a ranka ba da akacema nine na kawo mata magani?"
Cikin rashin damuwa yace " sosai ma, abu d'aya ne yazomin na tabbas kai ba ruwanka."
Murmushi Abu Turab Yai yace " then it's okay."
Sabi'u yamai kallan mamaki yace " ban gane ba? Ba kai kakai mata magani ba?"
Nine mana.
Sabi'u yace "yauwa sannan dan Allah inada tambaya, wai wannan yarinyar menene tsakaninku?"
"Yarinya? Wacce kenan?"
Fara tuki yai yana cewa " yarinyar gidan Waziru wacce da na d'auka ni take kallo, sai daga baya na fahimci kai take kallo tun kafin idanun ka su dawo gari."
Kallansa Abu Turab yai sai dai ya kasa cewa komai dan tabbas kasan zuciyarsa begen Khadija yakeyi, dan ranar ya tabbata da b'acin rai ta tafi.
Duk yanda yaso ya tsani yarinyar abin yaci tura.
Sabi'u ne ya kalleshi, gani yai Abu Turab yai saurin maida kallansa jikin window.
Sabi'u yace " yauwa Khadija, na tuno sunan dai sai dana tambaya saboda gulma dake cina."
Abu Turab ya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanunsa yace a hankali yace " wacce ya kamata in tsana, sai dai a duk lokacin dana b'ata mata rai nakejin zuciyata na zafi."
A hankali yai maganar wanda Sabi'u sam baiji ba yadai san magana yake sai dai bai san jeyake cewa ba, hakan ne yasa yace " me kace?"
Abu Turab bai bud'e idanunsa ba yace " bakomai."
A zuciyarsa yace " Allah ka cire mata sona, bazan taba addu'a ko dana sani akan san da nake mata ba, dan ko da ace za'a maida hannun agoggo baya na tabbata i will fell for her, i will always pray for her happiness."
Sabi'u ganin kamar bayasan magana yasa yad'an yi shiru, can yace " Mutumina ni daga waya ne kuka dinke da Gimbiya Bilkisu ne?"
Abu Turab ya bud'e idanunsa yace " kaidai kanasan kaji gulma, koma me mukai menene damuwarka?"
Sabi'u yai dariya yace " wlh kayi babban tunani, kun bala'in dacewa da Bilkisu, tun randa na ganta na san ....."
"To malamin had'aka na sanjin gulmar soyayyar da bata shafeka ba, wai ni Sabi'u kai yaushe zakai aurene?"
Turab ya katse shi daga maganarsa.
Sabi'u yai d'an ajiyar zuciya yace " lafinka ne da ka rufe kofa, ai da ka bari an ma kanwa da ba haka ba."
Turab ya girgiza kai kawai baice komai ba, sai murmushi kawai dayai.
Sun d'anyi niss ba tare da kowa yace komai ba, can kuma Sabi'u ya d'an cigaba da jansa da hira haka jefi jefi.
Bayan sun isa garin kano, Mai Martaba Sarkin kano yasa an gyara musu b'angaren da suka zauna waccan karan.
Shamaki yazo ya musu iso, sai daya tabbatar an kawo musu komai na bukata sannan ya tafi.
**********
A zariya kuwa Magajiya zaune a d'aki, Abdulmajid na kasanta.
Cikin muryar takaici take cewa " Abdulmajid wato kai bakada kishi ko? Bakasan darajar kanka ba ko? Kana kallo Abu Turab ya tafi kano gun Gimbiya Bilkisu amma kai ko a jikinka, wai me yasa ne sam kwanan nan baka abinda zai amfaneka?"
Fuskar Abdulmajid a had'e yace " Umma to ya kikeso nayi? Kina gani dai Mai Martaba ya fifitashi a kaina, in ba haka ba ta yaya banyi aure ba ya nema ma kanina aure?"
Magajiya ta mai wani kallon takaici tace " wannan matsalarsa ce, duk da inada takardar da take na shaidar amincewa da yardarsa akan kaine zaka gajeshi sai dai a koda yaushe zuciyata da hankalina sun kasa kwanciya, nasan Abdussamad sarai zai iya yin yanda takardar zata zama bata da amfani nan gaba, dan haka dole ne mu nemo ma mata kaima wacce take 'yar mulki."
Abdulmajid ya d'ago da sauri yace " Umma ki taimaken ki bar zancen wannan auren na 'yar mulki, ni Mairo nake so 'yar gid.
...."
Kamin shiru ko sai na kifa ma mari? Kana tunanin na sha guba saboda inji wannan shirman naka ne?
Shiru Abdulmajid yai kansa na kasa.
Ta cigaba " inasane da duk fa abinda kakeyi a gidan nan, kar in kuskura in kara ji ancemin ma anganka da wannan yarinyar."
Abdulmajid ya d'ago ya kalleta idanunsa yai ja yace " amma Umma bakya gani auran Mairo zai taimakeni? Kinfa san yanda Mai Martaba yakesan Barde bakya tunanin zaiji takaicin rabasu?"
Kallansa tai sannan tai murmushi tace " Lalai Abdulmajid da gaske san Mairo kakeyi, tunda har tsarani kakeyi, to ni nace banaso."
Fuska ya had'e sannan yai kasa da kansa.
Wani kallo tamai tace " tashi kaban guri."
Mikewa yai ca sauri kamar dama can jira yakeyi.
*************
Gimbiya Bilkisu tana zaune b'angaren Fulani, lale aka sa mata tana jiran yaci.
Munnira ta shigo da gudu tacemata "UmmaBilkisu ya iso."
Sam bata kula da Fulani ba bata kuma kula da Bilkisu dake ta mata alama datai shiru ba.
Tana gama fadar haka ta kalli Fulani da sauri ta tsuke bakinta tace "Inna Barka da warhaka."
Ta karasa maganar tana zama a gefen Bilkisu.
Bilkisu ta harareta sannan tace " Munnira Muhsin d'in ya iso?"
Sunan kanin Munnira ne, Munnira ta kalleta alamar rashin fahimta.
Bilkisu ta harareta hakan yasa tai saurin cewa " ya iso."
Fulani ta saki murmushi tace " Bilkisu ayi maza a cire lale aje a kimtsa kafin Muhsin ya iso, yo dama ai nasan domin Muhsin akai lalan nan."
Ta karasa maganar tare da mikewa tai ciki.
Bilkisu ta rufe fuska da bayan hannunta dan tasan Mahaifiyar tata ta fahimci me suke nufi.
Tana shigewa, Bilkisu ta harari Munnira tace " Ba wakafi ba alamar tsayawa, baki kalkalkal ya iya wassafa zance, wai ke in kina magana bakya kula da mutanen dake zaune ne?"
Baki Munnira ta turo tace " Ni murna ne yasa wlh sam ban kula ba."
Bilkisu ta kara harararta tace " murna? Dan kina murna sai kisa a gane komai?"
Munnira ta turo baki tare da kumburo fuska, Bilkisu tace " na daina ma had'awa dake."
Munnira tai kamar zatai kuka, Bilkisu tace " jeki ki duba to kiga ko akwai wani abu da suke bukata."
Munnira cikin zakwad'i ta mike tai waje.
Bilkisu tai murmushi tare da yin kasa da kanta.
**************
Abu Turab yai wanka sunyi sallah sannan suka zauna cin abinci, Sabi'u ne yace " Turab jiya ai munsha hira da Babanmu, na tausaya ma Mahaifinka wlh."
Turab ya mai kallan tambaya, sannan yace "name?"
Sabi'u yace " ya dade bai samu haihuwa ba, har fa ya fitar da rai da samun haihuwa."
Abu Turab ya kalleshi sai dai baice komai ba.
Sabi'u ya cigaba " Magajiya fa har kasashen waje ta fita saboda neman magani amma ba labari, sai daga baya kawai akace ciki gareta, kumafa inaji sai da cikin yakai wata 3 sannan inaji itama ta sani."
Kallan sa yai cikin rashin kulawa yace " lalai."
Sabi'u yace " kasan abin dariya?"
Abu Turab ya kalleshi.
" duk fa farko wai mutane dayawa basu yarda da cikin ba, harshi Mai Martaban."
Abu Turab ya kalleshi yace " ban gane ba."
Sabi'u yace " kasan Magajiya kowa yasan yanda takesan ta haihu shi yasa mutane sukai ta zargin ko ta fadane ba wai gaskiya bane."
Abu Turab ya mike yace " Lalai, kace sai da ta haihu suka yarda." Yai maganar cikin salon rashin damuwa da kuma gamsuwa da labarin.
Sabi'u yasa dariya yace " shiyasa randa aka haifi Abdulmajid ai anyi murna wai kamar ba gobe."
Baki Turab ya tabe a ransa yace " ni kuwa sanda aka haifen mutane fiye da rabi bakin ciki sukai, wasu ma tunani hallaka jaririn yaron sukai."
Ciki ya shiga dan zuciyarsa ta karaya da tunowa da wahalar da mahaifiyarsa tasha.
Kwafa yai daya tuna sharrin da suka ma Mahaifiyarsa, tabbas dole ne ya sa tun a duniya a hukuntashi.
Mikewa yai ya d'auko turare ya fesa ya sa hularsa ya d'auko takalmi ya saka, yayi kyau sosai da sosai.
Yana fitowa Sabi'u yace " kai Ango, gaskiya yau inaji sai na rufe kofa dan banaji Gimbiya zata barka ka taho, ko dai in aikama da bargonka can ne? Dan banaji ana san rakiya ta."
Turab ya kalleshi yace " ba sai ka aikp da bargo ba itama ai tana dashi, d'an rainin hankali, ni taso muje karakani."
Sabi'u ya mike yana dariya........
***********
A can gidan Waziri kuwa Khadija tun ranar ko waje bata sake yi ba, kullum tana d'aki, abin duniya ya daneta, takaicinta d'aya yanda zuciyarta ta matso dasan ganin Abu Turab.
..
🤝🏻 *TEAM ABU TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
_Ina 'yan group na fans d'in kungiyar Haske Writer's? Ina kuke 'yan group d'in The Queen Bee? Ga taku sadaukarwar, wannan shafin sadaukarwace gareku....🤝🏻_
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*46*
Jakadiya ce tazo dan kaisu inda aka tanada dan ganawarsu, an kayata gurin sosai, gun kamar rumfa yake, salo da kayata gun da akai duk yanda kaso da karka nuna sai gun ya burgeka.
Gashi sai hayaki na turaren wuta ne ke tashi.
Sabi'u cikin mamaki yake kallan gun ya kalli Turab wanda shikansa abin ya kayatar dashi yace " Kai gun nan ya burgeni, amma dai ba dan kai aka shirya gun nan ba ko?"
Abu Turab ya kalleshi yace " kai kuma sarkin zuga zugi, to kardai ka wuce makad'i da rawa."
Sabi'u ya kara shan mamaki ne a sanda yaga yanda aka saka irin carpet da 'yan tumtum a gun sannan aka jera kayan ciye ciye kala kala, ya jinjina kai yace " Turab da alama gaisawa kawai zamuyi da Bilkisu banaji anyi wannan shirin dan mu biyu."
Cikin gatse Turab yace " Gaisuwar ma sai ka hakura."
Sabi'u yace " ahh lalai Turab abin ba kara? To bari inje waje in tsaya in yaso in kungama ganawar na shigo daga baya mu gaisa."
Turab kai kawai ya girgiza, ya juyo da niyyar mai magana yaga bayanan.
D'an tsaki yaja kad'an yace " Sabi'u kenan."
Zama yai a gun da aka shirya dominsa, irin zama na manyan 'ya'yan Sarki.
Sai dayai minti 15 da zama sannan wani dadadan kamshin turare ya bugi hancinsa.
Cikin isa da takama take takowa, tafiya takeyi irin ta kasaitatun mata masu mulki.
Bai d'ago ya kalleta ba haka itama ko data shigo kallo d'aya ta masa ta cigaba da takunta.
Har sai da ta iso gun da zata zauna sannan ya d'ago ya kalleta, itama a lokacin ta kalleshi.
Tabbas yarinyar tana da kyau, balle yau datai shiga mai kyau sosai sannan tai kwalliya haka, wani sansanyan murmushi ta sakar masa, shima murmushin ya maida mata, a hankali ta zauna sannan ta umarci bayinta dasu fita.
Shiru ne ya ratsa gun kafin cikin muryarta mai dadi tace "Barka da isowa Yarima Turab."
Kallanta yai cikin yarda da amincewa yace " Barkanki da isowa Gimbiya Bilkisu."
Murmushi tai sannan tace " ka dade a zaune ko?"
" Ya zama dole ai in jiraki tunda haka tsarin yake, sannan ba wani dadewa nai ba."
Bata ce komai ba sai shiru da suka sakeyi.
Kanta na kasa, batai zato ba sai jitai yace " Bilkisu." Yanda ya kira sunanta sai dayasa taji wani yarr a jikinta.
D'agowa tai a hankali ta kalleshi idanunta sun canza zuwa salon soyayya, murmushi yai yace " Naji dadi da yanda kika amince da ni."
Idanunta ta lumshe sannan ta bud'esu.
Yacigaba " ban taba zatan zaki yarda dani ba haka, duba da rashin sani na da kikai, tunda haduwarmu d'aya dake."
Nan ma idanunta ta kara lumshewa ta bud'e, yace " A wannan lokacin na sa ma raina tabbas zaki zama mace ta gari a gun duk wanda kika aura, sannan na yaba sosai da yanda kike da tunani."
Murmushi ta saki sannan ta maida kanta kasa, hannayenta ta had'e gu d'aya tana murza zoben hannunta da d'aya hannun.
Harya d'auka bazatai magana ba sai jiyai tace " I can feel the pain that hide behind ur smile Turab."
D'agowa yai ya kalleta sai dai jikinsa yai sanyi, kallansa tai tana murmushi tace " me zakace game da ni?"
Kallanta yai kallo mai alamar tambaya.
Kanta ta d'an karkatar tace " ka taba sanin Fulani ba ita ta haifen ba?"
Idanunsa ne suka fifito alamar mamaki, Tace " bansan ta ba, bansan ya kamanninta suke ba, tana haifata a gun Allah ya mata cikawa."
Tausayinta ne yaji ya kamashi.
Idanunta ne suka d'an ciciko tace " karka kallan da fuskar tausayi Turab, i am okay, tunda dadewa na cire san ganinta a raina, sannan ina ganin in har na nuna damuwata akan mahaifiyar data haifen ya Fulani wato mahaifiyata ta yanzu zataji?"
Turab ya kura mata ido yana nazarin kalamanta. Can yace " U are indeed a good woman, sai dai jin zancen nan naki yasa na fara tunani ban kai qualification na aurenki ba, kin cancanci saurayin da zai soki kamar ransa wanda zai kula dake har rabuwa ta rai ta zo."
Hannu tasa ta goge hawayen daya d'an gangaro ta kwarmin idanunta tana murmushi tace " kai bakada confidence na sona kamar haka?"
Jitai yayi shiru sai dai yanayin kallan da yake mata ya canza, kallansa tai tace " Me kake nufi?"
Yace " Bilkisu inada abubuwa da dama a gabana wanda sai na ga sun kammala ne hankalina zai kwanta, banida lokacin soyayya ko farin ciki sai na ga mutanen nan an musu hukunci."
Shiru yai dan tuno abinda aka ma Mahaifiyarsa.
Baiyi tsamani ba bai kuma ji alamun tasowarta ba sai gani yai ta mikomai kofi.
Kallanta yai idanunsa sunyi ja, sannan ya kalli kofin ruwa ne a ciki alama tamai da kai akan ya amsa.
Hannu yasa ya amsa yana murmushi, yace " sry......"
Katseshi tai tace " naji dadi."
Fuskarta d'auke da murmushi tace " naji dadin yanda ka nunamin, yarda harka ke sanar dani hakan."
Kofin ya ajiye bayan ya shanye ruwa ciki yace " Bilkisu i....."
Kara katseshi tai tace " is okay, na fahimceka, na kuma san tabbas akwai wahalhalu da kasha ko fansar wani abu da kake san d'auka, sai dai inaso in taimakeka gurin d'aukar wannan fansar, bazan nemi soyayyarka ba har sai ka kammala abinda zakai, sai dai kaima bazan yarda kaso wata ba har zuwa wannan lokacin, in kuwa har da wacce kakeso yanzu inaso ka ajiye soyayyar a iya kacin zuciyarka harsai ka gama aiwatar da abinda zakai, a wannan lokacin ne nakeso ka tambayeni abu d'aya."
Idanunsa na kanta tacigaba " inaso ka tambayeni in har banyi dana sanin auranka ba, in har nace ma banyi dana sani ba to inaso ka tirsasa zuciyarka ta soni in har aka kai wannan lokacin baka sona, in kuma har nace nayi dana sani inaso ka tambayeni abinda nakeso a wannan lokacin."
Tana gama fad'ar haka ta koma ta zauna sannan ta d'ago ta kalleshi tace " Deal?"
Bai san sanda wani murmushi ya bayyana a fuskarsa ba yana murmushi yace " Deal! sannan naji dadi da kalamanki, ba saki a tsarin aure na ko da shi kike tunani a karshe sannan yanda kika amince dani ba tare da kinji abinda nakesan aikatawa ba, zanyi kokari wajen ganin bakiyi dana sanin aurena ba."
A tare sukama juna murmushi nan tamai alama da hannu akan yaci abinda aka kawo masa.
Tabbas tana bala'in san yaran nan, ko da kuwa zatai dana sani akan auransa bataji zata iya rabuwa dashi a wannan lokacin, sai dai ta d'au alwashin taimaka mai da tayashi d'aukan fansa akan duk wani wanda ya cutar dashi ko da kuwa zatai amfani da karfin mulki na mahaifinta ne.
Kamar yasan me take tunani jitai yace " for using you, dole ne ma nemi yafiyarki, sai dai zan nemane in na gama komai, is that okay?"
Kai ta jinjina mai alamar eh, ta bishi da kallo na so tsantsa.
Bayan sun gama hira ne ya mata sallama sannan ya mike, har ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya tako a hankali zuwa inda take.
Awarwaro ya ajiye mata wanda suke cikin gidansu sannan cikin magana mai kama da rad'a yace " da kunyar badawa nakeyi, sai dai bani na siya ba Sabi'u ne ya siyo"
Mikewa yai ya fara tafiya, kallansa tai tana murmushi tace " nagode."
Bai kara magana ba yai gama yana murmushi.
Tabbas Bilkisu ta samu daraja a idanunsa, yanaji zai iya zama da ita a rayuwar aure dan dama ya ma cire burin ganinsa da Khadija daga sanda yaji abinda mahaifinta ya musu ko da santa zai zama ajalinsa bazai taba yarda ya bakanta ran mahaifiyarsa akan 'ya mace ba.
*🤝🏻TEAM TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*47*
Duk yanda taso ta danne zuciyarta ta kwanta ta kasa, mikewa tai ta zura alkyabbarta sannan ta kalli Mai kula da ita tace " yau kwanan waye?"
Kasa tai dakai tace " naki ne ranki ya dade."
Magajiya ta d'an d'aga gira sama sannan tace muje inasan ganin me martaba.
Tayi mamaki sosai dan rabon da Magajiya taje turakar mai martaba da niyar kwana har ta manta.
Haka suka fito suka nufi b'angaren Mai Martaba.
Sunje shiga soro bangaren nasa sukaji ana gulmar Abdulmajid da Mairo, d'ayar tace " wlh jakadiya ce ta gansu da idanta yar gidan Barden ta fito daga b'angaren Yariman."
Magajiya ta cusa kai suna ganinta suka rude a tsorace suka tsugunna sukace " Barkanki da zuwa Magajiya."
Kallansu tai fuskarta dauke da iza tace " ina san dukanku kuje bangarena ku jirani, kada kuma ku manta a tsaye nakeso kuntsaya har na iso."
Kara runkufawa sukai suna neman bada hakuri, wani kallo ta musu da ya sa sukaja bakinsu sukai dif.
Nan suka karasa ciki.
Jakadiya ce ta fito da sauri kana kallanta zaka gane abinci takeci ta taso.
Wani banzan kallo Magajiya ta mata, da sauri tai rusuna tana gaisheta.
Magajiya bata amsa ba sai alamu da ta mata na ta mata iso.
Mikewa tai ta nufi b'angaren Sarki.
Rubuce rubuce yake tayi, yana jin sallamar Jakadiya yai saurin had'e takardun nan ya sa a kasan carfet din da yake kai.
Jakadiya ta shigo ta gaisheshi sannan ta sanar mai da zuwan Magajiya, alama kawai ya mata da kai akan ta shigo.
Magajiya ta shigo ta zauna a inda ta saba zama, sannan ta kalleshi tace " Barka da dare Haikawa."
Sarki ya amsa sannan yace " lafiya dai da daddaren nan?"
Tace " ina tunanin yau kwanana ne? Banaji na cancanci inji wannan kalmar daga bakinka."
"Kwana? A tun wani karnin kenan?"
Murmushi tai sannan tace " Turab na garin Kano ko?"
Kallan ta yai sai dai bai amsa mata ba, a ransa yace abinda ya kawoki kenan?"
Murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace " na yaba da d'ana Turab ba shakka yanada hazaka da tunani, ina kuma kara godemai da maganin da ya bani."
Sarki ya jinjina kai yace " ai dama hakkin d'a ne ya kula da uwarsa, in har ita uwar tana neman cutar dashi to shi ya kamata ya nuna mata yana santa."
Kura mai ido tai dan tasab magana yake gwab'a mata.
Isakar ta d'an firzar kadan tace " haka ne, sai dai inaso uban d'an ya cigaba da nunama d'an nan hanyar dazai kula da mahaifiyar tasa."
Murmushi Mai Martaba ya saki tare da d'an juya kai kad'an harzaiyi magana sai kuma ya fasa.
Kallansa tai dan fuskarta cikin fara'a tace " yaushe zaka yima babban d'anka mata? Dan na tabbatar kanada babban buri akansa shiyasa ka kasa yimai cikin gaggawa
"
Ya fahimci me takesan cewa hakan yasa yace " ni ai danayake na d'aura buri akansa shiyasa nai tunanin barinki ki nemomai mata."
Fuskarta ta tsuke dan tabbas taji haushin maganarsa.
Takarda ta d'auko ta taso a hankali tazo ta ajiye mai agabansa.
Kallan takardar yai yace " na menene?"
Tace " tuni nake maka akan rubutu dakai na cewa Abdulmajid ne zai gajeka."
Fuskar shi ya d'aure yace " sai akai yaya kuma?"
Kallansa tai tace " ba abinda akai Takawa kawai dai ina tunatar dakai ne, saboda tsaru."
"Tsaro? Kina tunanin wannan takardar kad'ai zata iya canza abinda ke zuciyata?"
Idanunta ne suka canza ta kalleshi, yace " eh, kina tunanin ita zata canza min ra'ayi? In na ce bani nayi ba fa?"
Kallan tsananin mamaki tamai sam tama kasa magana, murmushi ya sakar mata sannan ya kamo hannayenta yana shafa samansu yace " kin tab'a ji nace miki inaso in d'aura Turab akan mulki? Banaso kidinga zargin abinda bakiji daga bakina ba, ko warkewa bakiyi ba kin sa abinda bashida tabbas a ranki."
Wani kallo tamai dan tabbas tasan bakar magana yake gaya mata a cukurkud'e, kai ta d'an rankwfo sai tin kuncinsa kamar mai shirin sumbatar sa sannan tace " ina fatan Takawa zai tsaya kan maganarsa."
Juyowa yai inda bakinta yake hakan yasa bakinsu suka kusa sumbatar juna, wani lalausan murmushi ya mata yace " banaji na d'auraki akan mai bani shawara."
Fuskarta ce ta canza hakan yasa ta mike tsaye, tace " Ranka ya dade zan koma."
Alama ya mata da ido akan ga fili ga mai doki.
Duk yanda kaso ka gane ranta a b'ace yake bazaka taba ganewa ba saboda fuskarta d'auke take da annashuwa.
Jakadiya tana ganinta ta taho da sauri, Magajiya ta kalleta tace " biyoni."
Haka kawai ta fada tai gaba.
Haka jakadiya ta bita har suka isa b'angarenta ta wuce cikin d'akinta nan ma Jakadiya ta bita.
Bayan sun shiga ta juyo tace " rufe kofar."
Gaban Jakadiya ne ya fad'i ta tura kofar a hankali ya rage daga ita sai Magajiya.
A jikin kofar Jakadiya ta tsaya tana tunanin abin cewa.
A hankali Magajiya ta tako har inda take, fuskarta tayi bala'in canzawa zuwa tsananin b'acin rai.
Tana zuwa kusa da ita ta d'aga hannu ta zubawa Jakadiya mari.
Da yake sam batai zatan hakan ba jin marin yasa hankalinta yayi tsananin tashi.
Kanta na kasa sai dai hankalinta ya tashi sannan takaici ya cikata, kamar ta?duk girmanta? A kalla ta tabbata taba Magajiya shekara 4 amma ko kunya ta sharara mata mari?
Magajiya ta kalleta sannan ta ce " d'ago."
Jakadiya ta d'ago sai dai yanzu ta dake tace " Mai na miki? Banaji nayi wani abu daya cancanci duka."
Magajiya ta kanne ido tace " ke harkin isa kidinga yad'a gulma akan Abdulmajid? D'an nawa? Da alama kin gaji da aikinki. "
Ran Jakadiya ya kara tunzura jitai tsoron da ke zuciyarta yakau ta kalleta tace " Magajiya d'anki fa kikace?"
Gaban Magajiya ne ya fad'i ta juyo da sauri ta kalleta.
Jakadiya ta daure tace " sharri na masa? Ki tambayeshi da kanki kiji wannan karan ya fara jan hannun Mairo zuwa b'angaren sa? Sannan maganar aiki da kikeyi ni da kaina zan sauka in lokaci na yayi, ina sanar dake hakan ne domin kar akaini bango dan zan iya sanarma Yarima Turab komai."
Tana kai nan ta rusuna tace " Tuba nake Ranki ya dade in bakisa wani sakon zan koma kar Mai Martaba ya nemi ni."
Gaba d'aya ma Magajiya ta kasa magana tana tsaye sororo har Jakadiya ta fita.
Tana fita Magajiya ta saki wani kara na takaici tace " me yasa komai baya tafiya daidai? Dole ne na saita komai su koma yanda suke."
*************
D'agowa Barde yai hankali a tashe ya kalli Abdulmajid yace " Yarima me kake nufi?
Abdulmajid yace " Mairo nakeso, kuma zan aura dan gobe nake shirin sanar ma Mai Martaba shiyasa naga ya dace in sanar maka a matsayinka na mahaifinta."
Barde cikin rawar murya yace " na kasa fahimtarka ne ai, ta yaya kamar kai zakace kanasan Mairo? Ta yaya? Dan Allah Yarima kabar maganarnan anan."
Abdulmajid ya mike tsaye yace " zan jira a waje inaso ka turomin Mairo in ganta kafin na koma."
Barde sam ya kasa yin komai tsaya wa yai sororo har Abdulmajid ya fita.
Mairo kuwa da yanzun nan Ummanta ta sanar da ita zuwan Abdulmajid ya sa ta shigo falon da gudu ko sallama babu tana shiga ta tsaya ganin Babanta.
Jiki a sanyaye tace " Baba!"
Kallanta yai a sanyaye yace " me nake ji Mairo?"
Kai ta girgiza dasauri tace " wlh Baba ba haka bane, shi kad'ai yake kid'ansa yake rawarsa, kaima kasani Baba wlh ni......"
Katseta yai da cewa " Me yasa baki sanar dani ba?"
Hawaye na fara zubo mata tana girgiza kai tace " wlh na d'auka shirmansa ne, na kuma d'auka zai hakura tunda nace mai banaso."
Mikewa yai yace " kije yana jiranki a waje, mayi magana daga baya, kije in har kinaso komai ya rabu lafiya."
Yana kai nan yai waje.
Dabas ta zauna a kasa, sai kuma ta mike a zuciye tai waje.
************
Hisham zaune a falo, gefensa matarsa ce sai kuma kasansu Khadija ce zaune kanta na kasa.
Hisham ya kalli Khaduja yace " Khadija ba zaki fad'amin me ke damunki ba? Sam kin daina ko magana a gidan nan, na tambayekinko bakida lafiya ne kince ba haka ba, Bazaki sanar dani halin da kike ciki ba? Saifullahin ne bakya so?"
Kai ta girgiza tace "bakomai Abba
"
Ran Hisham ya baci yace " to uban me aka miki kika fito daga gidan Sarki kina kuka?"
Khadija ta kalleshi da sauri, sannan ta maida kanta kasa.
Ganin batada niyyar magana yasa ya mike cikin takaici ya kalli Mahaifiyar Khadija yace " duk laifin ki ne da bakya kula da 'yar da kika haifa."
Ya juya yai waje.
🤝🏻 *TEAM ABU TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*48*
Mairo ta dade a tsaye kafin tai waje cikin tsananin b'acin rai.
A tsaye ta ganshi yana tsaye ya juya baya a jikin motarsa, hannunsa sanye cikin aljihun rigarsa.
Tama rasa dame zata karasa mai.
Tsayawa tai kawai tana tunanin wacce kalma ce mai tsananin muni da ya kamata ta fad'amai?"
Juyowa yai dan jikinsa ya bashi ana kallansa, a hankali ya tako har inda take, tana tsaye kawai tana kallanshi.
Yana zuwa inda take yace " Amince Agareki Matar Abdulmajid ko ince Gimbiya Maryam wacce zata gaji Magajiya."
Wani kallo kawai tamai dan ta ma kasa magana, murmushi yai sannan ya d'an kara matsowa yace " Kin rasa bakin magana ko? Na tabbata dama zaki fahimceni, zaki kuma amince da soyayyata."
Kallansa tai cikin takaici sai kawai ta tsartar da yawo ta gefensa ta juya zatai ciki.
Ransa yakai kololuwa gun baci da sauri ya sha gabanta yace " me kike nufi da abinda kikai? Kyama ta kike?"
Fuskarta a had'e tace "Kyamar hallayanka nake, ta yaya zakazo ka samu mahaifina bayan kasan ba sanka nake ba? Ko kana tunanin hakan dakai shine zaisa a auramin kai?"
Lab'ansa ya d'an ciza yace "me kika d'auken? Kina tunanin sanar ma mahaifinki danai nayi ne dan in aureki?"
Mairo tamai kallan ba haka bane? Gira ya d'aga mata ya na kad'a yatsunsa yace " kin makaro Mairo dan kuwa bazaki taba jin shirina a kan aurenki ba, sai dai na d'au alkawari a zuwa daren yau zakisan matsayina a garin nan zakuma kisan nid'in yaro ne ga Sarki Abdussamad."
Yana kaiwa nan ya juya ya shiga mota yai gaba.
Da harara ta bishi tace " ba zuwa dare ba inji an shafa fatiha a nan da awa d'aya." Tai ciki.
************
Sabi'e ne ya mike daga kan kujerar daya kwanta ya kalli Sabi'u yace " Me kake tunanin Mai Martaba zai tambayeka?"
Abu Turab dake rike da littafin Riyadul Salihin yana dubawa yace " ina na sani? Sannan meye naka na damuwa da abinda bai shafeka ba?"
Sabi'u ya d'an yi ajiyar zuciya yace "yau ma tafiya zakai kenan ka barni anan ni kadai? Da alama dai ba amfani a rakiyar nan dana maka."
Tsaki yai yace " Kai dai wlh akwai sanjin gulma ni na shiga ciki."
Ya mike ya shiga d'aki, Sabi'u ya shafa kansa yace " ahhh Sabi'u ka zama d'an d'aki, ni ba mace ba."
Abu Turab kam yana shiga ya kwanta yana tunani.
Ta yaya zai warware matsala da kuma hukunta wad'anda suka wulakanta mahaifiyarsa? Suka kuma halaka masa kawunsa? Ina ma bai tab'a sanin Khadija ba a rayuwarsa, ina ma itama muguwace irin iyayenta? Hakan shine zaisa yaji dadin hukuntasu, idanunsa ya runtse da karfi, baisan meyasa ba bayasan Khadija taga wulakantar iyayenta, kuma ya zamana shine silar wulakantarsu wanda takeso tun tana karama.
A da auran Bilkisu zaiyi ne saboda ya kuntatawa Magajiya da kuma umarni na sarki, sai dai a yanzu ya cire wannan a ransa zai auri Bilkisu ne saboda rad'in kansa, tunda wacce yakeso bazai taba samu ba to gwara ma ya aminta da wacce ta fahimceshi wacce kuma ya yarda da ita, Mairo fa?
Idanunsa ya bud'e daya tuno da ita, wata zazzafar iska ya furzar tabbas dama shi yasan a rayuwarsa ba auran soyayya ba kuma farinciki mai d'orewa ya yanke wannan hukuncin ne tun a sanda Mahaifiyarsa ta sanar dashi komai.
Wajen Azahar yai kwalliya sosai dan babbar riga ma ya saka ya saka hula akan sumarsa, yayi kyau sosai da sosai ya saka takalminsa irin mai lankwasan nan na sarauta.
A falo ya tada Sabi'u yanata baccinsa, fita yai.
A waje yaga dogarawa guda biyu a tsaye da alama sun d'an dade suna jiransa.
Suna ganinsa suka matso suka gaidashi.
Yace " tun yaushe kuke nan?"
D'ayan yai kasa dakai yace " tun d'azu muka zo, Mai Martaba ne yace mu tsaya a waje mu jira har sai ka fito karmu takura maka."
Kai ya jinjina kawai yace " muje."
Bilkisu ce ta shigo b'angaren Fulani, ta zauna kusa da ita sannan tace " Umma da gaske Baba ne yace miki zasu fita da Turab?"
Fulani ta kalli Bilkisu sannan ta kalli Munnira tace " Uwar gulma har kin kai mata rahoto?"
Munnira ta b'oye bayan Bilkisu tana dariya.
Fulani ta kalli Bilkisu tace " me? Kina tsoron kar a wahalar dashi?"
Da sauri Bilkisu tai kasa dakai cikin kunya tace " Umma wlh ba haka nake nufi ba kawai dai abin ya ban mamaki ne ganin baya fita da kowa, dan kosu Yaya ban tab'a ji ance ya fita da wani daga cikinsu ba."
Fulani ta murmusa tace " nima d'azu ya aiko a fad'amin sannan bai fad'i inda zasu ba."
Bilkisu tai kasa dakai tare da wasa da hannayenta tana murmushin kunya.
***************
Su biyu ne zaune a cikin mota a baya sai mai tukasu da dogari d'aya a gabansu.
Sai da suka fara tafiya sannan Sarki ya kalli Turab yace " baka tambayi ina zamu ba?"
Abu Turab yai kasa dakai yace " tuba nake ranka ya dade amma ina ni ina tambaya?"
Sarki yai murmushi yace " a kowani karshen wata ina fitowa inga yanayi da halin da 'yan gari na suke hakan na karamin karfin gwiwa wajen kula da basu hakkinsu."
Abu Turab ya kalleshi cikin jin dadi.
Sarki ya kamo wannunsa hakan yasa ya kalleshi cikin mamaki, Sarki ya mai murmushi yace " bansan dalili ba ina ganinka naji gamsuwa da yabawa da kai danai, duk da nasan hakan yasamu karfi ne daga mukamin mahaifinka sai dai dukda hakan matsayi da yardar da nake maka dabance."
Turab yai kasa dakai yace " Godiya nake."
Haka sukai ta shiga gari guri guri kafin daga karshe suje wani katon gida wanda kana ganinsa kasan gida ne na sarauta duba da zanen da ke jiki.
Sai da suka shiga ciki, Bafaden nan ya sa makulli ya bud'e gidan, nan suka shiga ciki.
Abinci ne kala kala an shirya musu an kuma ajiye da alama dama ajiye wa akai kawai dominsu.
Bayan sun zauna Sarki ya kalli Turab yace " Abu Turab!"
Kallansa yai sannan yai saurin maida kansa kasa yace " Ganinan Ranka ya dade."
Mai Martaba yace " Bilkisu 'yatace wacce duk cikin 'ya'yana nafi kauna, bawai dan wani abu ba sai dan maraicin ta, batasan mahaifiyarta ba, ita kanta mahaifiyarta ko riketa batayi ba Allah ya amshi ranta, hakan yasa nake tsoron auran da ita saboda banasan ta auri wanda bazai kularmin da ita ba, sai dai duk yanda naso ba yanda zanyi tunda mace ce ita."
Abu Turab yai kasa dakai, Mai Martaba ya kalleshi yace " Turab ka kularmin da Bilkisu wannan rokone daga bakin mahaifi zuwa wanda zai kasance abokin rayuwa ga 'yarsa ba wai roko bane daga bakin sarki ba."
Da sauri Abu Turab ya mike ya d'ora gwiwowinsa a kasa yace " ni ne ya kamata inyi roko inkuma yi godiya, sannan bazan ma alkawarin bata kulawa wanda take samu anan ba, dan in na fad'i haka to tabbas nayi karya sai dai ina zanyi iya kokarina wajen ganin na bata kulawar da ya dace sannan zanyi kokari wajen ganin bakai dana sanin auramin ita ba."
Kallo d'aya zakama Sarkin ka tabbatar ya gamsu ya kuma ji dadin kalamansa.
Mikewa yai yazo inda Turab yake ya d'agashi sannan ya rike hannayensa yace " Nagode Turab."
Nine da godiya.
Sarki ya zaunar dashi kusa dashi yace"muci abinci."
Cikin kunya haka Turab yake cin abincin.
************
Magajiya ce ta d'au kofin dake hannunta wanda take shan ruwa dashi ta shilo inda Abdulmajid yake, da sauri ya kauce.
Idanunta karara suke nuna b'acin rai tace " me? Auran Mairo?"
Abdulmajid ya daure yace " Umma kitaimaka ki amince dani inhar kika yarda da hakan nikuma na miki alkawarin hawa mulkin garin nan."
Cikin b'acin rai tace " Abdulmajid fita ka bani guri, sannan kar in sake jin maganar nan."
Mikewa yai ya fito cikin b'acin rai.
Kofar d'akinta ya kalla bayan ya rufe yace " Kiyi hakuri Umma wannan karan zan saba miki, dan auran Mairo shine kadai zai sa in rama yawun da ta tofa a kusa dani."
Yai gaba.
Zaune ake a fada a cike taf, Abdulmajid ya shigo a zauna a gun zamansa sannan ya gaida Sarki.
Tunda ya shigo Barde gabansa ke fad'uwa.
Bayan Sarki ya amsa gaisuwarsa sannan Abdulmajid yace " inada magana Ranka ya dade."
Nan aka bashi izinin magana.
Durkusawa yai alamar roko yace "Ina neman alfarma gun Mai Martaba .
Sarki cikin mamaki ya kalleshi yace " ina jinka."
Abdulmajid ya kalli Barde wanda yake had'a zufa sannan ya kalli Hisham wanda shi kansa ya kosa yaji da wace magana Abdulmajid yazo.
Abdulmajid yai kasa dakai yace " Mairo 'yar gidan Barde nakeso a auramin."
Tsananin mamaki ne ya bayyana a idanun Mai Martaba, tashin hankalin dake idanun Hisham kuwa ba'a magana.
Sarki ya kalleshi cikin mamaki sannan ya kalli Barde.
Galadima ne yai caraf yace " Masha Allah wannan had'in yayi kuwa ranka ya dade, ba shakka wannan had'in zai karfafa zumuncin sarauta."
Nan kowa ya fara fad'in gaskiya kam.
Sarki ya kalli barde yace " me kace?"
Barde ya daure yace " Ai 'ya'yana da ni kaina umarnin ka ne, duk abinda ka yanke shi za'ayi............
Sarki ya d'ago ya kalli Abdulmajid.
🤝🏻 *TEAM ABU TURAB*
.🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
_Gareku 'Yan Ayusher Fan Club, wannan Shafin naku ne kacokal...Allah ya bar zumunci_
*49*
Sarki ya kalli Abdulmajid sannan ya kara kallan Barde wanda duk jikinsa ya gama mutuwa.
Gyaran murya Sarki yai yace " Zan duba maganarka, sannan bana jin hakan dakai ya kamata, Mahaifinta ya kamata ka sanarmawa sannan nima ka samen ka fad'amin hakan ne zai sa musan abinda ya kamata, bawai dan kana d'ana ba zakai tunanin dole namaka duk abinda kake so."
Abdulmajid yai kasa dakai yace " Tuba nakeyi."
Bayan ya fito, Hisham ya taho shima da sauri.
Tsayar dashi yai ta hanyar kiran sunansa.
Tsayawa yai sannan ya juyo ya kalli Hisham.
Hisham cikin sauri ya karaso yace " Abdulmajid menene hakan? Wace irin Mairo? Wacece ita da har zaka zo cikin fada kace kanaso a baka?"
Abdulmajid ya kalleshi cikin rashin kulawa da abinda ya fad'a yace " wacce nakeso kuma zan aura."
Hisham yace " Abdulmajid yar gidan barde ce fa, me kake tunani?"
Yace " D'an 'yar gidan Barde ce sai me? Ni wai kawu me yasa kai da Umma bakwa duba halin da nake ciki ne? Me yasa bakwa tausayawa soyayyar da nake mata?"
Mamaki ma sam ya hana Hisham magana, Abdulmajid bai jira jin wani abu ba kawai yai gaba.
Yana kokarin shiga b'angarensa, wata baiwa daga b'angaren Magajiya ta karaso da gudu tace "Yarima ana kiranka."
Nan ya juya zuwa b'angaren Magajiya.
A tsaye ya ganta a cikin d'aki yana shiga ya rufe kofa, matsowa tai inda yake ta zuba mai wani mari, jikinsa sai daya amsa, tsoro karara ne ya bayyana a idanunsa dan yanda yaga bacin rai karara a idanunta.
A hankali ya zauna a inda ya fara zama kansa na, juyowa tai cikin tsananin takaici tace "Abdulmajid kai harka isa har ka isa ince karkai abu kayi? In haifeka a cikina kace kana neman kafi karfina? To bari kaji tunda nake a duniya duk wani buri nawa ba wanda ban cikashi ba sai abu d'aya wanda shikad'ai ne nake danasanin gangancin danai, daga shi kuma bana bukatar wani danasani a rayuwata, baka isa kai ka sani bakin ciki ba....."
Katseta yai yace " Umma yanzu menene aibun auren Mairo?"
"Aibu? Shi kake san ji? Idan har ba so kakeyi rayuwarta ta shiga cikin kunci ba kai gaggawar janye maganar nan."
Yace " indai har a kusa dani zatai kuncin nikam banajin zai damen."
Kallansa tai cikin tsananin mamaki tace " Abdulmajid."
Kasa yai da kansa kawai baice komai ba.
Khadija ce tai sallama bata jira ba ta shigo da sauri ciki.
Magajiya ta kalleta, gaban Abdulmajid tazo ta tsuguna tace " yaya yanzun nan Umma ta aikoni in kawo sako naji ana zancen kana san auran Mairo, Yaya Meke faruwa?"
Kansa ya kawar gefe, hawaye ne ya fara zubo mata ta shiga girgiza kai tana cewa " yaya please kabar maganarnan, Mairo itace Ya Turab yake so ta yaya zaku zama kune sanadiyyar kuntata masa rayuwa, na sani ba santa kakeyi ba, in har ni bazan zauna kusa dashi ba dan Allah yaya kabar ta ta zauna gun Ya Turab......."
Kuka ne yaci karfin ta mamaki ne karara ya bayyana a idanun su duka su biyun, Magajiya ta juyo tace " Turab ne yake san wa? Mairo?"
Khadija kuka kawai takeyi tanacewa "Dan Allah yaya ka janye maganarnan."
Abdulmajid ya buga mata wani harara yace " Khadija kina nufin saboda farincikin Turab kinaso ni in kuntata? Farincikinsa ya fiye miki?"
Kallansa tai tana girgiza kai tace " ba haka bane yaya, inka duba rayuwarsa zakaga abin tausayi ne shi, yaushe ya fara gani? Sannan waye gareshi a kusa dashi?"
Jitai an fincikota a tsorace ta d'ago Mahaifinta ta gani, Magajiya na tsaya tana mamakin abinda takeji.
Hisham yace " Akan wa kike kuka?"
Kallansa tai sai dai batace komai ba, cikin fad'a ya kara cewa " Waccan karan ma akansa kike kuka? Akansa kika daina magana? Akansa ne kike neman ture auran Saifullahi?"
Hawaye ne kawai ke zubo mata sai kai kawai da take girgizawa.
Hannu ya d'aga kamar zai daketa sai kuma ya fasa, ya kalleta cikin takaici yace " Kin bani kunya Khadija......"
"Ya isa hakanan, Khadija wuce ki shiga cikin d'akina maganar ta isa haka." Magajiya tai maganar cikin kakkausar murya.
Khadija a hankali ta shiga ciki jikinta duk yai sanyi, Hisham kam bakin ciki yasa ko motsi ya kasa, yana bala'in san yarinyar.
Magajiya ta kalli Hisham da Abdulmajid tace " ku bani guri zan nemeku anjima."
Nan kowa ya mike.
Zama tai tare da had'e hannayenta guri d'aya ta matse su tai shiru.
" Turab nasan Mairo?
Abdulmajid na san Mairo?
Sannan Khadija nasan Turab?" Dolene ta fito da hanyar dazaisa komai ya warwarw mata.
***********
Mairo ta fito daga wanka tana shafa mai, mahaifiyarta ta shigo tace " kiyi sauri kisa kaya mahaifinki na nemanki."
Nan ta zura bakar doguwar riga bayan ta gama kintsawa.
Mayafin rigar ta yana a kanta ta fito zuwa falonsa.
A zaune ta ganshi yayi shiru, jin sallamarta ne yasa ya dawo daga tunanin dayake yi.
Zama tai sannan ta kara gaidashi.
Kallanta yai, idanunsa duk sun canza yace " Mairo, Abdulmajid ya sanar ma Sarki yana san auranki."
Idanunta ta zaro cikin tsananin tashin hankali tace " aure? Ni da shi?"
Barde ya kakaro murmushi yace " Kinfi kowa sanin kuma ban isa bijirewa umarnin sarki ba."
Ya mike yai cikin d'aki, da alama ya shiga ne dan kar yaji tausayin 'yar tasa.
Mairo tai shiru a zaune dan tama rasa ta inda zata fara.
Mikewa naga tayi da sauri ta zura takalminta tayi waje.
Tafiya take zuwa gidan Sarki, tana tafe tana cewa " Ya Turab ya zanyi? Menene mafita?"
Tunda ta shigo gidan ake gulmarta.
B'angarensa ta nufa a waje taga Garzali, da sauri tace " Ya Turab fa?"
Garzali yace " Yana kano."
Taku biyu tai zuwa baya dan ji tai kamar an kwad'a mata abu, cikin rikicewa ta nufi b'angaren Basira.
A zaune ta ganta tana shan fura ita kanta yau bata samu cin abinciba sai yanzu da yamman nan.
Basira tana ganinta tausayinta ya kamata, Mairo ta karaso da sauri ta zube gabanta tace " Umma ki taimaken."
Basira ta kalleta cikin tsananin kulawa tace " Mairo."
Mairo idanunta suka ciciko tace " ba sona yake ba, Umma haka ake so? Ta karfi? Umma kinsan halayen mutumin nan, ni na hakura da Ya Turab dan da alama dama naso kaina dayawa ne, Umma amma ba Abdulmajid ba, dan Allah Umma ki tai......."
Idanu ta runtse dan ji take kamar ta kwalla kara na bakin ciki.
Basira ta matso da ita ta rungumeta tana lallashinta, kuka sosai Mairo takeyi tana cewa " Umma ba Abdulmajid dan Allah, naji aban kowanenen amma bandashi."
***************
A can garin kano kuwa bayan sun dawo a kofar shiga Mai Martaba ya kalli Turab yace " Inka koma wannan karan kasa a turo domin sa rana dan ba'asan masarauta da jan magana ba."
Turab yace " Godiya nake Mai Martaba."
Bayan mai tuka motar yai parking, wani bafade ne yazo da gudu ya bud'e sannan ya rad'a mai magana a kunne."
Murmushi naga yayi sannan ya kalli Abu Turab yace " Turab muje kaima kwa gaisa da Minister."
Abu Turab ya kalleshi sai dai baiyi magana ba yabi bayansa.
Wani bangare aka kaisu, bangaren ya tsaru sosai wasu maza ne guda biyu a zaune kana ganinsu kaga uba da d'a duba da yanayin kamar su.
Suna ganin Mai Martaba suka mike, uban na ta murmushin jin dadi.
Sarki ma cikin fara'a ya kalleshi yace "Malam Haruna yau kaine da kanka?"
Wanda ya kira da Haruna ya karaso suka gaisa, yace " Tuba nake Ranka ya dade da alama fishi ake dani."
Zama Sarki yai sannan suka kara gaisawa.
Yaran nasa ne ya matso ya gaisheshi.
Shima Abu Turab ya gaida mutum.
Haruna ya kalli Sarki yace " Ga d'ana Saifullahi, kullum ina cewa zan kawoshi ya gaidakai sai yau Allah yai."
Saifullahi ya kara gaidashi.
Sarki yace " naji dadi, ni kuma wannan sirikina ne."
Mamaki ya kama Haruna ya kara kallan Turab.
Sarki yace " d'an Sarkin Zazzau ne, Abu Turab."
Fara'a ce ta kara bayana a fuskar Haruna, Saifullahi ya kalli Abu Turab."
Haruna ya kalli Turab yace " Kace na ganka kai tun yanzu kafin mu had'a zuri'a."
Turab yamai kallan mamaki da rashin fahimta.
Haruna ya kalli sarki yace " ai Saifullahi shine zai auri yar gidan Waziri sunanta Khadija."
Wani mugun fad'uwa gabasa yai da sauri ya d'ago ya kalli Saifullahi, wanda shima kallansa yakeyi.
Idanu suka kafema juna.
Sarki shikam bai kula dasu ba ya kalli Haruna yace " lalai Minister na tayaka murna Allah ya sanya alkairi."
Yanayin kallan da Abu Turab yakema Saif yasa Saifullahi yace " Lafiya?"
Turab yai saurin kauda kai yace " ba komai."
Kallan mamaki Saif ya bishi dashi, dan ya kasa fahimtar ma'anar kallan da yake mai.
🤝🏻 *TEAM ABU TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*50*
Mikewa Turab yai ya kalli Mai Martaba sannan yai kasa da Kansas yace " bari na baku guri." Ya fad'a kansa na kasa.
Sarki ya jinjina kai yana murmusawa yace " To Turab kaje ka huta."
Gaida Mahaifin Saif yai sannan ya musu sallama yai waje.
Jiyai ance Ina magana.
Tsayawa yai tare da juyowa dan duba mai magana.
Saif ya gani ya ya tsaye daga kan baranda, saukwa yai ya nufoshi.
Tunda ya taho Turab yake binsa da kallo ni kaina bansan me yake aiyanawa a ransa na.
Saif ya karaso sannan ya saki fuska yace " Naga kamar bai dace mu rabuba ba tare da sanin junan mu ba, duba da yanayin nan gaba zamu zama dangin juna?"
"Dangi?" Abu Turab yai fad'a sannan ya murmusa yace " Yama kace sunan?"
Saif.
Turab ya jinjina kai yace "Saifullahi, am sai dai kayi mantuwa Abdulmajid zaka fadawa haka bani ba."
Saif ya kalli Turab tabbas yaji haushin maganarsa yace " Amma na d'auka......"
Turab ya katseshi yace "Allah ya sanya alkairi."
ya juya ya tafi, dangin juna? Ya kara maimaita Kalmar tare da jan tsaki yace " kama rainamin hankali."
Yana shiga masaukinsu Sabi'u ya taso saga zaunen da yake yace " Ka dawu? Sirikin mu."
Turab ya bugamai wani kallo yace " wai ni har wani d'an rainin hankali zai kalla yace wai mun kusa zama dangin juna? Ha ha amma ya gama rainamin hankali ya karasa maganar tare da zama.
Sabi'u cikin mamaki ya kalleshi yace " Nikam kai da waye?"
Turab yaja tsaki yace " wai wani Saif, ko Khadija yakeso ko Khadija zai aura ni ban ma sani ba."
Sabi'u ya tuntsure da dariya yace " Turab? Kaine?"
Kallansa Turab yai baice komai ba sai dai takaicin dariyar yakeyi.
Sabi'u ya matso kusa dashi yace " Khadijan ka?"
"Eh ma......."
Sai kuma yai shiru sannan yai saurin mikewa tsaye yace " wace irin banzar tambaya ce wannan, ban gane Khadija ta ba? Wai kai Sabi'u me yasa ka iya abin haushi ne?"
Sabi'u yace "ohhh abin haushi? Sai naga kamar kishi ne ya ciwoka kake bukatar tausa."
Turab ya bugamai wani banzan kallo yace " kishi?" Mtsw kai fa sai a hankali wlh.
Ya fad'a tare da shigewa d'aki yanaji Sabi'u na cewa " karka manta anjima zakaje gaida Fulani mijin Gimbiya
"
Yana shiga d'aki ya zauna a bakin gado yace " me ya sameni? Why am i acting like this?"
Sai kuma ya nuna kansa cikin mamaki yace " don't tell me kishi nake?" Kai ya girgiza da sauri yace " inaa tayaya ma zanyi kishi akan wacce take zuri'ar makiyana?"
Yin baya yai ya kwanta akan gado, yana takaicin wannan abu, inama shikam baisan Khadija ba a rayuwarsa?"
*********
A can Zariya kuwa Magajiya ta rasa abinda ya kamata tai ta dade tana tunani kafin daga baya ta wuce cikin d'akinta.
A zaune a kasa ta taradda Khadija kana ganinta kasan tana cikin wani hali.
Magajiya ta karaso kusa da ita tace "Mamana mike." Ta fad'a tare da miko mata hannu.
A hankali Khadija ta tashi sannan ta zaunar da ita a bakin gado itama ta zauna a kusa da ita.
Hannayenta ta riko tace " Khadija san Abu Turab kike?"
D'agowa tai da sauri ta zubama Magajiya idanunta wad'anda suka cika fal da hawaye, sai dai bata iya bata amsa ba.
Magajiya tai murmushi sannan tace " kin san waye Abu Turab?"
Kallan mamaki ta mata dan bata fahimci me take nufi ba.
Magajiya ta d'anyi ajiyar zuciya tace " Khadija baki san waye yaran nan ba, wannan maciji ne wanda dafinsa keda tsananin zafi, kinsan yaron nan idanunsa biyu amma yake nuna makaho ne? Kinsan ya tsaneni da mahaifinki amma yake nuna miki so dan kawai yai amfani da ke? Mune jininke, mu kad'ai ne muka san darajarki bazamu taba cutar dake ba."
Ganin Khadija ta zare hannunsa daga cikin nata yasa ta tsaya da maganar tana binta da kallo.
Sai kuma ta mike sannan tai murmushi tace " Umma Babba bazan ce nasan Ya Turab ba tunda ba tare mukai rayuwa dashi ba sai dai namanta ban fad'a miki kalma d'aya ba, nice nakesan Ya Turab ba shine yakeso na ba."
Ta juya tana tafe kamar wacce zata fad'i dan ba shakka kalaman Magajiya sun so kawo mata rud'u cikin kwakwalwarta, maciji?yana gani?amfani da ita? Ba shakka ba dan tayi saurin katseta ba da alama da sai ta canza mata ra'ayi a xuciyarta.
Kallan kofar data rufo ta Magajiya tai a ranta tace " Umma Babba please don't disappoint me anymore."
Abdulmajid ta gani a tsaye a waje da alama ma jiranta yakeyi.
Yi tai kamar bata ganshi ba ta fara tafiya.
Da karfi ya finciko hijab dinta yace " Wato ke Abu Turab ya fi miki ni ko? In taimaka in barma Turab Mairo? Ke meyasa bakida hankali ne?"
Khadija ta kalleshi idanunta sunyi raurau tace " Yaya me ka nema ka rasa a duniyan nan?"
Kallanta yai baice komai ba.
Tace " kanada komai na rayuwa, matsayi,iyaye, lafiya, girmamawa, me ka nema ka rasa?"
Ta share hawayenta tacigaba " Ya Turab na san yarinyar nan, kai ko tausayin sa bakayi?"
Kallanta kawai yake yama kasa magana, ta share hawayenta sannan tace " ku kanku kunki kyale bawan Allahn nan, bakin cikin abinda kuke mai shine na tabbata dalilin dayasa ko ganina baisan yi....."
Hawaye ne suka nemi fin karfinta, da sauri ta juya ta fara tafiya.
Abdulmajid baki kawai ya saki yake kallan mamaki.
Shi Khadija takema wannan banzan sharhin?
*********
Mairo kuwa baya ta gama fad'an kalamanta Baseera ta jawota jikinta tana lalashi.
Tace " Mairo dama kina san Turab? Na dade ina hasashen haka sai dai wani sa'in ina tunanin rad'in kainane yasa nake ganin haka ba wai kece kike sanshi ba, ki kwantar da hankalinki ki koma gida, tunda har nasan abinda ke ranki ni kuma xanyi iya kokarina naga komai ya dawo daidai."
Mairo ta d'ago sai dai batace komai ba.
Hisham na fita ya wuce gida ransa a b'ace a tsakar gida yaga mahaifiyar Khadija a zaune.
Rufeta kawai yai da fad'a.
" Aikin banza ace tarbiya wannan kin kasama 'yarki, inba rashin tsaro ba har yaushe ma kika bari yarinyar nan ta sakankance da wani can sokon yaro, yaron da zuwansa doron kasa shine abu mafi muni da ya taba faruwa a rayuwata, to wlh inma zaki sa Khadija ta cire wannan shirman a ranta kiyi dan wlh in har na sake kamata tana kuka akan yaron can wlh abinda zan miki sai kinsha mamaki."
Bai jira ta tofa komai ba yai gaba fuuuu.......
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*51*
Zaune yake a cikin wani had'ad'an gun hutawa, a hankali yana cin inibin dake gabansa sannan yana duba littafin hannunsa, lumshe ido yake yi saboda yanda yakejin dadin rayuwa, cikinsa ne yaji ya murd'a nan fa wani azababben ciwo mai tada hankali ya rutsashi, baisan sanda ya durkuso kasa ba yana murkususu saboda azaba, idannan nasa yayi jaa kamar garwashi, tsananin tashin hankali da rad'adin da ya ke ciki.
Jiyai an sakar masa wata irin dariya na keta da sauri ya d'ago dan ganin wani mugun ne wannan ba taimako sai dariya?
Magajiya ce cikin wani had'ad'an shiga tayi kwalliya sosai, dariya take sosai.
Abdulmajid ne ya fito daga bayanta shima yana dariya harda kyakya tawa.
D'ayan gefen kuma Hisham ne ya fito shima dariya yakeyi sosai, nuna shi suka shiga yi suna dariya.
Basira ya gani a kasansu a kwance wanda baisan ko tana raye ba ko ta mutu.
Sannan Abdulmajid yana rike da igiya yana jan wata yarinya a kasa, kallan yarinyar yai ga mamakinsa sai yaga Mairo.
Kirjinsa ne ya d'au zafi, Khadija ce ta taho da gudu gunsa tana kuka kamar ranta zai fita, da sauri Hisham yasa hannu ya fizgota.
Jiyai gaba d'aya ya kasa numfashi da sauri ya bud'e idanunsa.
Cikin tashin hankali yake kallan d'akin, ga zufa da yai sharkaf.
Zama yai cikin tashin hankali yana addu'oi, ba shakka wannan mafarkin ya tsoratashi, shi yasa baccin yamma bashida kyau.
Mikewa yai ya sauko daga kan gadon, sai dai jiyai kafafunsa na rawa.
Gado ya dafa tare da runtse idanunsa.
Ya dade a haka kafin ya daure ya shiga ban d'aki.
Bayan ya fito ne ya zauna a bakin gado, ba shakka mafarkin ya bayyana karara kamar gaske.
Ga kansa na mai wani azababben ciwo.
Sabi'u ne ya leko yace " Ranka ya dade ka tashi? Wai daga shigowa sai in tadda kai kana bacci?"
Turab ya kalleshi kawai baice komai ba.
Sabi'u yacigaba " dama aiko wa akai in anyi magrib zakaje ku gaisa da Fulani."
"Gobe da sassafe zamu koma gida."
Abinda Sabi'u yaji ya fad'a kenan.
Mamaki ya kama Sabi'u da sauri ya karaso cikin d'akin yace " Mutumina lafiya?"
Turab ya kalleshi, ganin yanda idanunsa sukai ja ya matso da sauri yace " Yarima Lafiya?"
Turab ya mike yazo kusa dashi kawai ya dafa kafad'arsa sannan ya wuce.
Waje ya fito ya tsaya yana kallan sararin samaniya, me yasa yakejinsa haka?
Bayan Magrib jakadiya tazo ta raja Abu Turab gun Fulani, sosai ta karbeshi sannan itama ta rokeshi akan rikon Bilkisu, irin amsar dayaba Mai Martaba ita ya bata.
Haka ya taso cikin gamsuwa da yanda sukesan 'yar tasu.
Munnira ce ta biyoshi da sauri ta mikamau wata takarda.
Amsar takardar yai ya kalleta yace " ta menene?"
Munnira tai dariya tace " UmmaBilkisu ce tace in baka."
Amsa yai yana cewa
" Yau Umman taki rowar ganinta take min?"
Munnira tace " zaka ganta gobe ai."
Bud'e takardar yai yana cewa "Gobe zan tafi da safe."
Kallan mamaki tamai tace " Amma UmmaBilkisu vata sani ba?"
Kai ya d'aga yace " nima dazun na yanke shawarar haka, amma zan dawo ko zuwa sati biyu ne."
Duba takardar yai, number waya ce ta landline a jiki a kasa tasa, inka samu time ka nemin a layin nan."
Murmushi yai ya kalli Munnira yace "kice mata nagode, dama nayi tunanin tambayarta."
Ya juya yai gaba
***********
Washegari.
A zariya
Basira tayi shiru tana tunanin mafita, ba shakka ko d'anta bazai auri Mairo ba bazata taba bari Abdulmajid ya aureta ba.
Mikewa tai ta kali Lantana tace "Lantana muje in duba Hajiya sannan muje gun Magajiya."
Mamaki ne ya kama Lantana sai dai bata ce komai ba.
Sunje gun Hajiya jikinta kam kamar kullum ba sauki sam, dan ko maganarta dama ba ganewa akeyi ba.
Yau kam jikin ya d'anyi sauki.
Mai kula da ita suka tarar tana bata magani, sai dai tana ganinsu ta daina bada maganin ta mike da sauri ta rufe maganin ta d'auka.
Basira ta kalleta tace " ta gama shan maganin ne?" Dan yanayin yanda yarinyar tai yasa ta kasa fahimtar hakan.
Cikin rawar murya tace " ta gama." Ta karasa magana tare da fita.
Basira ta zauna kusa da ita sannan ta gaisheta.
Kai ta d'aga mata, Basira tai murmushi tace " yau kam naga jikin da sauki."
Basira gani tai ta miko mata hannu alamar ta riketa.
Nan ta riketa tace " Hajiya."
Kokarin magana takeyi sai dai ta kasa da alama akwai abinda takesan fad'a.
Kunnenta ta matso dashi tace " Hajiya menene? Akwai abinda kike so ne?"
Ma ma ma ga.......
Basira tace " maga me?"
Hajiya ta kara daurewa tace " Abbbbb......"
Da sauri wannan yarinyar ta shigo tace " Hajiya a kawo miki ruwa?"
Yunkuri takeyi da alama akwai abinda takesan ta fad'a.
Basira ganin yanda taketa keta zufa tace " Hajiya ki barshi sanda kika ji dama in har abun daya kamata ne sai ki fad'amin."
Idanu ta runtse na takaicin kasa magana da take, gashi dama ko zama bata iyayi.
Sun dade kafin su fito, Hajiya tai shiru tana tunanin abinda ya faru shekaru hud'u da suka wuce.
Taya zatai ta sanar da d'anta abinda ke faruwa? Tundaga ranar da ta mata magana akan abin a ranar ta fara rashin lafiya wanda har yau ciwo sai gaba yake baya raguwa.
Kowa ya d'auka tsufa ce ta sata wannan rashin lafiyar sai dai ita tasan ba haka bane.
B'angaren Magajiya suka nufa.
Bayan ta zauna a kilisarta ne, aka shiga ciki dan sanar da Magajiya zuwan Basira.
Ta dade dan takai akalla minti 20 kafin ta fito.
Tafiyarta take cikin takama, tazo ta zauna cikin isa sannan ta kalli Basira a wulakance.
Basira ta gaisheta sannan tace " Zuwa nai muyi wata magana."
Magajiya ta kalleta tace " inajinki, sannan inaso ki hanzarta saboda inada abinyi."
Basira tai shiru tana tunani kafin tace " Me kike tunani game da auran Abdulmajid da Mairo?"
Magajiya ta zuba mata ido sai dai batace komai ba.
Basira tacigaba " Zuwa nai inji ra'ayinki akan auran......."
" nikam a iya sanin kwakwalwata ban ji ance kin sake haihuwa ba, ko ince banji ance kina d'auke da cikin wata yarinya Mairo ba, dan haka banaji kina da hakki akan auranta."
Basira ta d'ago cikin mamaki tace " ai ba sai ka haifi mutum ba kake da hakki akansa ba Ranki ya dade."
Magajiya tai wani banzan murmushi tace " ko? To in haka ne nima bari nai iko da Abu Turab wanda ban haifa ba, inaso kice ya dawo daga garin kano sannan ya janye auren Bilkisu ya auri Mairo wacce kike so."
Tsananin mamaki ya hana Basira yin magana, ta kalleta tace " ban gane......"
"Kurma ce ke? Ko kuwa fahimtace baki dashi?" Sai kuma tai wani lalausan murmushi tace " ko dayake wacce akai rufa rufa agun auranta saboda rashin matsayinta da abinda ta aikata a baya banaji tanada inda zatai tunani a kwakwalwarta."
Gaban Basira ne ya fad'i tama rasa me zatace.
" kin kyauta da kika zo, dama ko bakizo ba zan aika kizo, inhar kinaso in rufe sirrin da aka fad'amin ki tabbatar kin sa d'anki ya janye auran Bilkisu dan d'an sarki sai 'yar sarki, Abdulmajid zai auri Bilkisu shikuma d'anki Turab ya auri Mairo kinga in akai hakan komai yazo da sauki kenan, kema kinsamu abinda kikeso kamar ni."
Basira tai dauriya tace " me kikaji akaina? Banaji inada wani abu da zan......"
"Hmmm kin manta ba'a cikakiya aka aureki ba?"
Tashin hankali ne karara ya bayyana a idanun Basira, ta daure tace " ban....."
Wata irin dariya Magajiya ta saki ta kalleta tace " Basira sunana Magajiya."
Basira tai shiru sai jikinta dake tsuma.
Magajiya ta mike ta zo inda take ta tsugunna tare da dafata tace " Me yasa banyi tunanin komai ba da? Sai dai karki damu sirrinki zan tayaki ajiyewa in har kika sa d'anki ya janye maganar auran Gimbiya, dan ko za'a mutu bazan taba bari ya aureta ba."
Ta karkad'e mata kafada tai gaba.
Magajiya tana shiga d'aki tai wani mugun murmushi tace " lalai da gaske ne."
Tunowa tai jiya bayan ta rasa mafita kawai ta kira Hisham tace ya kira abokinsa dake garin Daura, yasa yamai bincike akan Basira, ba shakka sai yanzu ta fara tunanin tabbas haka kawai sarki bazai auri Basira a b'oyeba, duk da batai tunanin wannan matsalar ba tadai san akwai wani abun.
Basira kam da kyar ta mike jikinta na rawa ta fito.
🤝🏻 *ABU TURAB TEAM*
*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
_AyI hakuri da Jina shiru da kukai kwana biyu, azumi nakeyi_🙈
*52*
Abu Turab dama ya sanar da Fulani zancen tafiyarsa, nan sukai sallama da mai martaba cikin jin dadi dan bai tambayeshi dalilin tafiyarsa ba.
Sai da suka gama shiryawa tsaf sannan ya nemi ganin Bilkisu dan yin sallama.
Itakam Bilkisu tunda Munnira ta sanar da ita take tsaye tana zagaye d'akin, meke faruwa? abinda ke mata yawo kenan har mai kula da ita ta sanar da ita neman da Turab yake mata.
Cikin sauri ta duba fuskarta a jikin madubi sannan ta nemi fita, harta kai kofa sai kuma ta tsaya, taja wani dogon numfashi sannan ta kara neman nutsuwarta kafin ta fito.
Yana zaune yayi shiru ta shigo da sallama, dagowa yai tare da amsawa yana kallanta.
Sai data zauna sannan ta gaisheshi tare da cewa " Lafiya dai ko?" kallanta yai yace " nikaina abinda nake san sani kenan."
Kallan mamaki tamai sannan ta d'ora da cewa " badai wani abu mara kyau bane ya faru ko?"
Hannunsa ya sa yad'an shafi saman goshinsa sannan yace " Ina ji nane ba dadi, inajin kamar da wata babbar matsala datake faruwa a gida."
Kallansa tai sannan ta d'anyi murmushi tace " Insha Allah ba abinda ya faru sai alkairi, sannan in har wani abu mara kyau ya faru ko ka fuskanci kana cikin tsaka mai wuya ina rokonka da karka yanke hukuncin da nan gaba zakai dana sani, ka jinkirta yanke hukunci har sai zuciyarka ta aminta da wannan hukuncin."
Murmushi ya sakar mata yace " Nagode."
Itama murmushi tamai sannan ta sunkuyar da kanta kasa.
Mikewa yai yace " zan wuce."
D'agowa tai ta kuramai ido sai dai batace komai ba, a hankali ya tako zuwa inda take sannan ya tsuguna a gabanta tare da zaro abu a aljihu, ya nuna mata takardar databa Munnira na layin waya, yana murmushi yace " na gani na kuma gode."
Kallansa tai sannan ta saki wani lalausan murmushi.
Mikewa yai yace " kafin in dawo maybe an tsaida rana."
Da sauri ta maida kanta kasa, wata yar karamar dariya yai wacce batada sauti yace " wannan d'in kunya ce?"
D'agowa tai ta harareshi tace " dama haka ake yi? da kanka ya kamata ka fad'amin zancen?"
Dariya ya sakeyi yace "au haka ne? to goge abinda na fad'a a zuciyarki inyaso sai a sake sabon la le."
Murmushi tamai tare da juya kanta gefe tace " na goge." cikin zolaya yace " nikam me ma nace?"
Hararar sa ta sakeyi sannan ta maida kanta kasa tana murmushi, ashe yanada side na zolaya, farkon ganinsa ta d'auka mutum ne wanda bayasan wasa sam, sai dai yanzu ta fara tunanin tsauri da jinin mulki ne ya sashi haka.
Dagowa tai ta kalleshi sai dai batace komai ba.
Murmushi ya mata sannan yace " zan kira." kai ta d'agamai, yace " zan wuce" nan ma kai ta d'agamai.
Lab'ansa ya d'an hade sannan yace " nagode."
Murmushi tamai, nan ya juya yai hanayar fita.
Sai dayaje kofa yaji muryarta a hankali tace " Allah ya kiyaye hanya."
Juyowa yai yana murmushi yace " Ameen."
Nan ya juya ya fita, yana zuwa ya tadda Sabi'u ya sa an fita da komai, nan suka kama hanyar gida.
Basira kam abin duniya duk ya gama damunta tama rasa ina zata saka kanta, da farko tayi tunanin fad'ama Sarki sai dai tace me? wad'annan tunanin sun hanata sakat, fatanta kawai d'anta ya dawo, ta sanar dashi hukuncin magajiya.
Magajiya kam tana zaune a kilisarta tana kurb'an shayi wanda yaji kayan kamshi, tana sha tana lumshe ido, kana ganinga kaga wacce take cikin nishad'i da jin dadi.
**********
Da rana su Abu Turab iso, Sabi'u yana ajiyeshi ya sauka daga motar yace " ni nayi gida mutumina."
Turab kai kawai ya d'aga mai, fadawa ne suka taho da sauri suka shiga kwashe kaya.
Kallansu yai yace"ku kai kayan b'angaren Umma ni zan shiga fada na gaida Sarki." nan suka amsa da to, shi kuma yai gaba.
Bayan ya shiga fada ne ya kwashi gaisuwa, Sarki cikin mamaki yace " me ya dawo dakai yau? bayan sai gobe kace?"
Shiru yai na wasu dakiku kafin ya d'an sosa keya yace " zuwa nai na sanar da Sarkin Kano mahaifin Gimbiya yace ya na jiran lokacin sa rana." ya karasa maganar tare da maida kansa kasa.
Galadima yace " Alhamdulila abu yayi kyau, nikam Takawa mai zai hana ka had'a auran yarima Abdulmajid da na Yarima Turab kawai ayi a rana d'aya?ko har yanzu ba'a tsaida maganar ba?"
D'agowa Turab yai cikin mamaki sannan ya kalli Galadima, cikin neman karin bayani yace " Abdulmajid ya samu mata ne?"
Galadima yana murmushi ya kalli Barde wanda yai shiru kamar wanda aka daka haka yake jinsa, sannan ya kalli Wambai yace " au ashe fa bakanan? ai 'yar gidan Barde yakeso yama sunan ta?"
Wambai yace " Mairo."
Idanu Turab ya zaro cikin tsananin mamaki yace " Mairo? ya fad'a yana kallan Barde, sannan ya kalli Hisham wanda shima yaci magani."
Murmushi ya kakaro sannan yace " Bari na shiga ciki Ranka ya dade."
Sarki wanda shima ya rasa ta cewa yace " Ya kamata kam, kaje ka huta."
Turab ya kara gaidasu sanan yai waje.
Cikin hanzari yake tafiya Mairo? lalai ma yaran nan ba karamin mahaukaci bane, an tab'a aure dole?
Hangoshi yai a gabansa kamar irin yasan maganarsa d'in nan yakeyi.
Tsayawa Turab yai ya kafeshi da ido, shima Abdulmajid wanda ke hanyar Fada dan jin hukuncin da aka yanke ya tsaya tare da kafe Turab shima da ido.
Cikin kasaita kowannen su ya fara takowa, idanunsu na kallan juna har zukazo daf da juna.
Abdulmajid ya kalleshi yace " Sirikin sarkin kano ka iso?"
Wani murmushi na gefe Turab ya saki yace " Sai ina?" Abdulmajid ya tab'e baki sannan yace " ya zanyi? kasan na kusa zama ango dole ba zama."
Turab baisan sanda yai wani banzan murmushi ba har hakwaransa suka fito ba yace " Ango? Are u kidding me?"
Abdulmajid ya had'e rai sannan ya kara takowa jikin Turab daf yace " Kana tunanin zaka hanani? to ka bud'e kunnuwanka da kyau kajini, yanzu ba lokacin damuwa da abinda bai shafeka bane na aurena da matata Mairo ba kaje ka duba lafiyar tsohuwarka dan naji Umma tace ta saita komai akanta" sannan ya murmusa yace " ka kuma san Umma in tace abu to da abun ne."
Sosai Turab ya harzuka da kalamansa, ya juyo ya kalleshi sannan ya sa hannu ya kade mai kafadarsa kamar irin abu ya hau kai d'in nan yace " Ya za'ayi? dan nasan in Magajiya tace abu tofa abun ne sai dai ni kuma in nace abun nan ya isa to fa dolene ya dakata."
Ya karasa hannu ya kad'emai d'aya bangaren yace " Ka tabbatar ka sanarwa Ummanmu kalamai na sannan auran Mairo?" yai dariya yace " ko a mafarki kama daina dan baka isa kasa baiwar Allah cikin kunci da bakin cikin auranka ba." ya juya yai gaba ransa a b'ace, da alama an ma Ummansa wani abun, Idanu ya d'an rufe kad'an yashiga fad'in _Innalilahi Wa Ina Ilaihi Raji'un_
**********
Har yaje sai shiga bangaren Umma sai kuma ya fasa yai b'angaren Magajiya.
Batai mamaki ba sam da aka sanar mata da zuwansa dan dama tasan in har ya iso to da dole ta ganshi.
Kara gyara fuskarta tai ta kalli wacce ta sanar da ita zuwan nasa tace " Muna bukatar abu mai sanyi."
Nan ta amsa da to sannan ta juya.
Magajiya ta zura takalminta mai kyau sannan ta kalli kanta a madubi kawai sai gani nai tayi wani murmushi, sannan tad'an cije lab'anta ta kara murmusawa.
A hankali ta tako cikin izarta ta iso kilisarta.
Abu Turab na zaune ya had'e hannayensa guri d'aya.
shigowa tai cikin takama ta zauna, sannan ta kalleshi tace " Bakaga shigowar mahaifiyarka bane?"
Kallanta yai sannan ya d'aga gira yace " Au banji shigowarki ba, sannan yai kasa dakai ya gaidata."
"Me ya kawo ka?"
Kallanta yai yace " zuwa nai na gaidake na kuma sanar dake abubuwa biyu a matsayinki na Uwata."
Kallansa tai batace komai ba.
Yace " Sarkin kano yace yana jira daga bangaren mu, na tabbata kin san me yake nufi, sannan abu na biyu ki fadama d'anki ya janye auren......"
Wata dariya ta saka sannan tace " Turab? da alama bakaje ka gaida wacce ta haifeka ba ko?"
Kallanta yai cikin shakka yace " Na'am?"
Dariya ta kara sawa tace " me yasa ne nikam na girma amma haryanzu nakejina kamar yarinya? fatata bata canza ba sam."
Ta karasa maganar tana kallan hannunta, kallanta yai cikin tashin hankali idanunsa suka kada sosai, yace " me kikana Umma na?"
Baiwar nan ce ta shigo d'auke da tire da jug da kofuna ta ajiye sannan ta zubama Turab ta kuma zuba ma Magajiya.
Magajiya ta amsa sannan ta kurba tace " sha akwai sanyi dan ka d'auko rana."
Kallanta yai sannan ya kalli kofin, yarinyar ta fita.
yace " me kikama Ummana?"
Yai maganar cikin kakkausar murya.
Kara kub'a tai sannan tace " ta yaya zan sani?"
A harzuke ya mike yai waje cikin tashin hankali.
Me tama Umma haka? da yake ganin tsantsar confidence a idanunta???
🤝🏻 *TEAM TURAB*
*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*53*
Har ya murd'a kofa sai yaji tace " Ahh na manta ashe akwai wacce kake so?"
Tsayawa yai cak sai dai a hankali ya juyo zuwa kallanta.
Murmushi ta saki tace " Hmm na kula da gaske ne, dama Khadija ce ta sanar dani akwai wacce kake so, nayi mamaki da naji haka da alama san mulki ne yasa ka ture wacce kakeso zuwa auran Gimbiya."
Idanunsa ne suka kad'a sosai Khadija?
Da karfi ya bud'e kofar ya fita cikin b'acin rai.
Magajiya ta bishi da harara tace " Mairon yakeso da gaske? Ko kuma akwai wata a kasa? Dama hakan ne yasa batace Mairo ba kai tsaye saboda tanaso taga yanda zaiyi, sai dai ta kasa ganewa."
Abu Turab tsaya wa yai a waje yai shiru, wata zazzafar iska ya fitar daha bakinsa yana kokarin juyawa ya ga Khadija ta taho.
Kallanta yai sau d'aya ya d'auke kansa, kalaman Magajiya ya maimaita na game da wacce yakeso, kenan kila na Khadijan har fada musu tai ita yake so? Wato gaba gaba amfani zasuyi da san da yake mata su cutar dashi? A da yana tunanin Khadija bazata tab'a cin amanarsa ba amma a yanzu ya cire wannan abun a ransa, bai san ta iso inda yake ba.
Sai jiyai cikin muryar tausayi tace "Yaya."
Kallanta yai fuskarnan tasa a d'aure tamau, ta d'auka jin abinda ya faru ne yasa shi cikin wannan hali, a hankali tace " Yaya kayi hak........"
Katseta yai da cewa " Alhamdulila banaji a yanzu zanyi kokwanto akan hukuncin da zuciyata zata yankemin, a da ina tunanin halin da zan sakaki, nagode kwarai da kika nunamin ke jinin Magajiya ce."
Yana kaiwa nan ya wuceta.
Sam ta kasa ma magana saboda ta kasa fahimtar abinda yake fad'a.
Ita datazo dan yima Abdulmajid magana da kara bashi baki akan ya janye maganar nan, me Turab yake nufi?
***********
B'angaren Mahaifiyarsa ya nufa, a zaune ya ganta ganin yanayin datake yasa yaji idanunsa sun ciciko, shiga yai ciki ya zauna sannan ya gaisheta.
Fuskarta d'auke da murmushin data kakaro tace "Turab akacemin ka dawo, nayi mamaki sosai ganin ba yau ne kace zaka dawo ba."
Mikewa yai jiki a sanyaye ya karaso inda take a hankali ya kwantar da kansa a kan gwiwarta idanunsa sun ciciko yace " Ba sai kin b'oye damuwarki ba a gabana Umma, na sani akwai babban matsala data kunno miki kai, ki sanar dani Umma ko na nemanr mana mafita."
Jitai hawaye na neman zubo mata da sauri ta mike tsaye ta juya mai baya tace " Ba komai Turab kawai dai jiya na d'anyi zazzab'ine shi yasa ka ganni haka."
Mikewa yai shima ya kalleta sannan yace " Me Magajiya take nufi da inzo ki sanar dani?"
Basira ta juyo tace " Haka tace ma?"
Kai ya d'aga alamar eh sannan tace "Maganar Abdulmajid ne da Mairo bayanshi banaji akwai wani abu."
Kallanta yai sai dai bai gamsu ba ya dai fahimci batasan yasan ko menene.
Juyawa yai yace "bari na koma ita ta sanar dani."
Cikin tsawa tace " Turab dakata."
Juyowa yai ya kalleta cikin yanayi na tausaywa yace " Umma kin manta wahalar da mukasha a rayuwa ni da ke? Kin manta matsala da tashin hankalin da kika fuskanta? Ta yaya zakiso ki b'oyemin wani abu?"
Idanu ta runste tace "Turab muna cikin tashin hankali, in har abinda Magajiya ta sani ya bayyana banaji zamu kara samun kwanciyar hankali a gidan nan."
Cikin shakkun kalamanta yace "Umma badai tasan maganar lahanin da aka miki ba?"
Kallansa tai hawayen dataketa dannewa suka zubo tace "Turab ya zamuyi? In har maganar nan ta fito ban san yanda mutane zasu kallemu ba, ba kuma naji za'a yadda da kai."
Idanunsa ne suka kad'a sosai lalai Magajiya bala'i ce yanzu mikin da ke b'oye a zuciyar matarnan sai data taso mata dashi hankalinta ya kwanta, lalai yaji dadi da mahaifiyarsa ta sanar dashi komai kafin rana irin ta yau, da bai san yanda zaiji maganar nan ba.
Murmushi ya sakar mata ko ince yake ya mata yace " Sai me Ummana? Iya kace mutane su gujemu to sai me?"
Kallansa tai cikin kunar zuci tace "kanaso kacemin baka fahimci me take nufi ba? In har magana ta fito zargin tsatson ka za'a shiga yi, in kuma ba haka ba sai dai kabi umarninta ka auri Mairo shikuma Abdulmajid ya auri Gimbiya."
Gani tai yasa dariya mara sauti yace " ohh wannan shine dalilinta?"
Basira ta kallshi tace " Kana tunanin Sarki zak taimakemu ko? Ka cire wannan a ranka in har kana wannan tunanin, Sarki ne shi kafin mahaifinka ko ince kafin ya zama mijina.'
Turab yace " Umma kin taba gani nace Sarki ya ya shiga ko ya taimakamin a yayin da matsala ta kunno min kai? Sai dai inje gun Abba na dan neman shawara, sannan maganar auran Bilkisu da Mairo duk wannan lamari ne na ubangiji Allah shine yasan matar da Abu Turab zai aura, Allah shine yasan ko dukansu zai aura, Allah ne yasab ko duk cikinsu ma ba wanda zan aura, sai dai nasan abu d'aya duk yanda zanyi bazan bar Abdulmajid ya auri Mairo ba saboda kamar kanwa take a gurina, sannan bazan bari ya auri Bilkisu ba saboda yarinya ce wacce bata cancanci miji kamar Abdulmajid ba."
Yana kaiwa nan ya juya zuciyarsa fal da bakin ciki.
Sam ya rasa ma ta ina zai fara.
Har bayan Magrib ya rasa mafita kawai ya nufi b'angaren Mahaifinsa.
Jakadiya ta matso ta gaisheshi sannan tace "Ranka ya dade Magajiya tana ciki."
Magajiya?
Ya maimaita yana kallan Jakadiya.
Jakadiya tai gyad'a kai tace "Sai dai ka dawo gobe inkuma kanaso in sanar masa."
Turab ya girgiza kai sannan yace "Barshi, sannan karki sanar mai da zuwana ko daga bayane."
Tace "to."
Harya juya ta biyoshi da sauri tace "Yarima."
Tsayawa yai sannan ya juyo ya kalleta yace"Lafiya?"
Daurewa tai tace "naji abinda ya faru, sai dai abu d'aya na isa fad'ama wannan abinda ta shirya reshe zai iya juyawa da mujiya, dan kuwa Magajiya tanada babban sirri duk abinda ake tunanin nata ne ba nata bane."
Turab ya kalleta cikin mamaki yace "Jakadiya ni fa......"
"Na barka lafiya Ranka ya dade, kai mutum ne mai zurfin tunani da kaifin basira zaka gano abinda nake nufi in har Allah ya nufeka da ganowa."
Ta juya tai gaba.
Da kallo ya bita sannan ya juya yai gaba.
*************
Abdulmajid wanda bayan shigarsa fada yana neman yin magana mahaifinsa ya mai wani kalli wanda kwarjini yasa ya kasa karasawa.
Ana magrib kuwa ya zari mota yai gidansu Mairo.
Tana xaune a waje ta kurama sararin samaniya ido tana kallan yanda yanayin duhun gari yake, yaro ne ya shigo yai sallama sannan yace " wai ana kiran Mairo."
Mairo ta kalleshi tace "inji wa?"
Yace "wai mijinki."
Kwafa tai sannan ta ciji lab'anta ta kuma mike da sauri, mayafita kawai ta zura tai waje dan ko Mamanta bata sani ba.
Yana cikin mota yana ganinta a tsaye a soro ya fito da sauri yana murmushin jin dadi.
Itama murmushin ta maida mai hakan yasa yaji kansa ya fasu.
Ya karaso gunta yace "Mairo na."
Tace "Yarima na."
Kallan mamaki ya mata sannan yasa dariya sosai yace "Mairo kece kuwa?"
Tace nice, kana mamaki ne?
Fuskarsa ya shafa cikin jin dadi sannan yace " Sosai ma "
Wani banzan kallo tamai tace "Kana tunanin haka zan ma in ka min ta karfi?"
Kallan tai yai yace "me kik....."
Katseshi tai tace " please Abdulmajid ka tashi daga wannan wawan baccin da kakeyi, wlh wlh in har ka kuskura ka dage da aurena har aka yi wlh ina tausaya maka da ni kaina dan a yanda nakejin tsanarka komai zai iya faruwa, dan wlh dana aureka gwara na auri talaka wanda bashida komai."
Jiyai zuciyarsa ta d'au zafi yace "Mairo how can u?"
Tace "me? Kana tunanin sunyi kadan kalaman nawa Busuru kawai, ka lalata 'yan mata sannan ka nemi auren wacce batasanka? Ko kana tunanin nima so na kake?"
Ta kalleshi cikin takaici tace "Aurena? Hmm please go ahead, a kaini gidanka inga ko zaka samu abinda kakeso."
Taja dogon tsaki zata juya.
Hannunta ya rike da sauri yace "Mairo taya zaki fadamin bakaken maganganun nan ki tafi?"
Ta makamai harara sannan ta kalli hannunta daya rike tace " sakeni ko?"
Kallanta yai sai taga ya sa dariya yace " Mairona in baki shawara? Ki bala'in kwantar da hankalinki ki aureni cikin farinciki dan wlh duk duniya ba wanda ya isa ya aureki sai ni nan Abdulmajid d'an Magajiya da Abdussamad."
Hannunta ta fizge tai cikin gida.
🤝🏻 *SASSANIN KUNGIYA TA ABU TURAB SADAUKI🏇🏻*
*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*54*
D'agowa yai cikin tashin hankali ya kalleta yace" me?"
Idanu tad'an juya tace " Na yaba da kokarinka wajen ganin ka kare hakkin matar so, sai dai duk yamda kaso ka b'oye sirrin nan matar ki ta gano komai."
Tambayar ki nakeyi me kike nufi?
Ta sakar mai lalausan murmusji sannan tace " Ya zamuyi ai dolene mu cigaba da b'oye sirrin nan, gaskiya na tausayawa kanwata Basira fyad'e ai mugun abu ne."
Tai tagumi kamar wacce take cikin halin tausayawa tace " Ya zamuyi in zancen nan ya fito? Sannan wace dabara kai nikam dan a sanda ka kawo Basira gidan nan tabbas ankawomin zanin gadon dake d'auke da budurcin ta."
Tai ajiyar zuciya tace " Hmm ni yanzu tsorona ma kar a maida zancen daga fyad'e ya koma karuwanci kasan mutanen mu akwai matsala."
Tsananin tashin hankali je ta gani karara ya bayyana a idanun Abdussamad.
Mikewa tai ta tako a hankali zuwa gabansa sannan ta tsugunna tace " Tuba nake ranka ya dade dan bakina yayi kuskure dan tuni na tura mata d'anta akan yaji meke faruwa."
Zuciyata ta turnukoshi ya kalleta wani irin kallo na tsana da kiyayya, kai ta juya sannan ta kalleshi idanunta sun canza kala tace " Ba sai ka min kallan tsana ba, na dade da sani tsana da kyamar da kakemin, kana tunanin banajin haushi? Ko kana tunanin nid'in ba mace bace? Tunda ka auro Basira zan iya kirgama sau nawa ka kusanceni."
Ta mike tsaye tace " Baka min kara a harkar abinda kakeso, nima bazanyi kara akan zartarda abinda naga yayi daidai da zuciyata ba."
Da karfi yasa hannu ya fincikota sai gata a gabansa, idanunsa sun kada sosai da sosai yace " Kara? Ke har kinsan kalmar nan ta kara? Duk karar danake miki? Kina tunanin shakkarki ce tasa nake shanye duk laifin da kike min?"
Kallansa kawai take saidai tsoro da shakka sun d'arsu a zuciyarta dan tunda take yauce rana ta farko dataga Abdussamad cikin irin wannan b'acin rai.
Daurewa tai tace " Kadaifi kowa sanin hukuncin matar da take ba cikakiya ba a matsayin matar Sarki..."
Hannu ya d'aga kamar zai kifa mata mari wanda hakan ya tsoratar da ita sosai, sauke hannunsa yai sannan ya runtse ido cikin takaici yace " ke ba mace bace? Tayaya rashin imaninki zaisa ki taso da mikin daya riga ya warke a cikin zuciyar marainiyar Allah, Magajiya wani irin rashin tausayi da imani gareki?"
Bakinta ta d'an rufe dan magana take san yi taji yana rawa, kallansa tai bayan ta cije tace " inhar ka damu da ita ba kuma kasan mutane su san kazantar data aikata kasa d'anka ya janye auren Gimbiya sannan ya auri Mairo, sannan kayi murabus ka barwa Abdulmajid kujerarka."
"mene?" ya fad'a sannan ya d'anyi dariyar datake kunshe da tsantsan takaici yace " kinaso kicemin akan auran Bilkisu kike neman halaka rayuwar Basira?Ko kuma tsoron Turab ne yasaki b'ulo da wannan makircin?"
Kallansa tai cikin tsananin takaici tace "mene?"
Sarki yace "Ahhh yanzu na fahimta, tsoron kar Turab ya samu power ne ta b'angaren auransa yasaki haka, kina tsoron abinda zai miki inhar daga baya yaji abinda kika aikata masa."
Idanunta ne suka firfito tace "mena aikata masa?"
Sarki yace "kin dauka bansan kece silar nakashewar idanunsa ba? Ke har zakiyi maganar kara da matar so? Ko kina tunanin tsoronki ne yasa na kasa miki hukunci?"
Da sauri ta juya mai baya tace "bansan wannan zancen ba, meye nawa na nakasa mai ido?"
Sarki yace " fita."
Juyowa tai ta kalleshi tace " koma waye ya fada maka haka karya yamin sannan kace ya kawo shaida, sannan maganar aure da Murabus ina jiran amsarka inba haka ba Basira da d'anta subar gidan nan." Ta juya da sauri tai waje.
Hannunsa dake kan cinyarsa ya dunkule tamau saboda bakin ciki da takaici.
***********
Abu Turab jeka ka dawo ya shigayi a tsakar falonsa.
Da sauri naga ya fito ya yi waje.
Bangaren Basira ya nufa, lokacin tana bandaki, sai daya jira ta fito sannan ya mike yazo inda take ya tsugunna yace " Umma akwai wani laifi da Magajiya ta tab'ayi ko kuma wani Makirci da kikasan ta tab'ayi?"
Kallansa tai alamar tana nazari sannan ta girgiza kai tace "kasan halinta duk makircin da takeyi bata taba yarda tabar wata shaida da zata sa a ganeta."
Shiru yai kafin can yace " ki sake tunani Umma ko wani abu ne wanda kikasan baki yarda dashi ba sai dai bakida tabbas akanshi, abu d'aya ne zaisa muci galabarta wato yanda tasan weakness d'inmu muma musan nata."
Basira ta girgiza kai bayan dogon nazari tace "ban tuno komai ba Turab."
Mikewa yai jiki a sanyaye yace "shikenan Umma, inkin tuno ko daga bayane."
Har ya fara tafiya tace Turab.
Juyowa yai da sauri.
Tace " Akwai wani abu da take bamu kamar shayi a farkon zuwana gidan nan, to ni dayake banashan ruwan zafi na sanar da ita, sai dai abinda yaban mamaki tursasamun tai sai dana sha, sai dataga abinda nai sannan ta daina bani."
Tai ajiyar zuciya tace "nasan ba wani abun zargi bane amma na kasa cireshi a raina, sannan Turab mai zai hana ma hakura da auran Bilkisu?"
Kallanta yai yace " Umma kina tunanin saboda hana aurena ne kawai yasa tai wannan maganar? Sannan in ma haka ne kina tunanin nan gaba bazata sake amfani da wannan kalmar ta kara samu abinda tai ra'ayi ba?"
Basira tai shiru, murmushi ya kakaro yace " Na tafi."
Yana shiga d'akinsa ya rufe kofa yai shiru yana tunanin kalaman Ummansa, tabbas akwai abinda ake sawa a cikin ruwan zafin nan, to amma menene? Kalaman Jakadiya ne suka kara fad'omai, da sauri ya girgiza kai yace " inhar na tambayeta ta fad'amin gulma ina da tabbas gaskiya zata fad'amin?matar da sam bai yarda da ita ba? Sannan tayaya ma zata bi bayansa ta ajiye Magajiya?
********
A kano kuwa Bilkisu kwance a makeken gadonta ta kwantar da kanta a kan matashi ta lumshe idanunta ta shiga zazarfan tunani, tunanin da ni kaina bansan wani iri takeyi ba.
Murmushi ne d'auke a fuskarta kai kace wani albishir aka mata wanda yasa ta fara'a har a cikin bacci.
A hankali ta bud'e idanunta, da sahri ta mike tai baya tare da d'an zabura tace "Munnira meye hakan?zakizo ki sani a gaba, wlh na tsorata."
Munnira tace " Gani nai kinata murmushi shine nakesan ganin abinda ke saki murmushin."
Harara ta maka mafa tace " an kirani a waya?"
Munnira ta girgiza kai alamar a'a, baki Bilkisu ta turo tace " Lalai ma Turab ai ka kira kacemin ka isa ko wani abun." tai maganar cikin d'an kukuni.
Kallan Munnira tai rai bace tace "Fitarmin daga d'aki."
Munnira tai waje tana mamakin abinda ya samu UmmaBilkisun ta.
************
Duk wani tunani yayi amma ya rasa mafita mai karfi, cir ya kwana bai runtsa ba yana neman mafita sai dai bai samu ba.
Yanayin sallar asuba Mahaifinsa ya aika a kirashi.
Sun zauna shiru a d'akin bayan sun gaisa, Sarki ya kalleshi yace " Naji ance kazo jiya."
Kallansa yai baice komai ba, Sarki yace "naji kuma ance kace kar a fad'amin kazo."
Turab yai kasa da kansa.
Murmushi Sarki yai yace " To ya? Ka nemo mafita?"
Kallan Mai Martaba yai sannan cikin sanyin jiki ya girgiza kai alamar a'a.
Ajiyar zuciya Sarki yai yace " Murabus takeso nayi."
D'agowa Turab yai cikin tsananin mamaki yace "Murabus?"
Sarki ya murmusa yace " ya ya? Kana mamaki ne? Ko so kake kacemin bakasan Magajiya ba?"
Idanu Turab ya zaro yace " amma....."
"Hakura zakai da auran?" katseshi yai da wannan tambayar.
Kallansa Turab yai sai dai bai iya cewa komai ba.
Sarki yace " Hakura zakai saboda mahaifiyarka ko saboda ni?"
Kallansa TURAB yai yama rasa me zaice, kai ya girgiza yace "bansani ba Abba, kwakwalwata ta rufe, Magajiya ta fara sani shakkar makircinta, how can she ask u..How c...."
Dariya Sarki yai mara sauti yace " baka taba tunanin zatai haka ba?"
Abu Turab idanunsa suka ciciko yace "Abba ta yaya zaka cigaba da zama da matar da bata ganin girma da darajarka? Ta yaya zaka cigaba da zama da matar da take neman muzguna maka?"
Sarki ya kalleshi cikin wani yanayi yace "Kasan me yafi komai wuya a harkar sarauta? When u have something to protect."
Turab ya mai kallan rashin fahimta, murmushi sarki yamai yace " me kake tunanin zai faru in na rabu da ita ba tare da babban dalili ba?"
Turab yace "matarka ce fa ka kuma rabu da ita, me zai faru?"
Kai Sarki ya girgiza mai yace " Turab kenan, Magajiya zata iya sa a kwace mulki daga hannuna duk da kuwa sarautar tawa ce."
Me kake nufi?
Sarki yai murmushin yake yace " shiyasa na ke san ka auri Bilkisu wacce tasan kanta ta kuma san darajar sarauta wacce mulkin a jininta yake ba koyarsa tai ba."
Turab ya kalleshi yace " is she that powerful? Magajiya nake nufi"
Sarki ya kalleshi yace " Tasan hanyar makirci kala kala, ta kuma san manyan mutane kala kala, ta kuma san yanda zatai ta samu duk wani abu da takeso ko ta wani hali ne kuwa ko da hakan zai zama silar halakar nata ne."
Turab ya kalleshi yana kokarin magana Sarki yace " Turab kasan kai kad'aine zaka iya sa Magajiya ta amshi hukuncinta? Ni bazan taba iya cin galaba a kanta ba ko dan saboda zuri'ar dake tsakaninmu, bazan taba san d'ana ya shiga halin tashin hankali ba saboda wani buri daya ke nawa, zan kula da Basira in ta kama ma zan iya d'auketa daga gidan nan kn maidata inda ta fara zama, kada ka kuskura Magajiya tasan wani lago naka, kada ka kuskura ka bari ta nemi cin galaba akanka, na sani zaka iya, a duk lokacin dana tuna da kai inaji a raina komai zaizo da sauki da yardar Allah."
Turab duk yanda yaso ya daure sai da kwalla ta gangaro masa kad'an.
Ashe haka mahaifinsa yake zaune cikin takaici?
Jiyai Mahaifinsa yace " Kuka ba wai ana yinsa bane saboda bakin ciki, sannan dariya bawai ana yinsa bane saboda farinciki, a koda yaushe zuciya tanayin abinda tasan hankalinta zaifi kwanciya dashi ne."
Idanunsa ya runtse yai kasa dakai, mai yasa yakejin kansa yayi nauyi sosai yakeji kamar an d'auramai wani babban nauyi na kare mahaifansa da kuma duk wani abinda yake so?
"Idanunka itace silar lahantasu, banso sanar dakai ba sai dai a yanzu na fahimci dolene na fada maka, ni dakai dolene mu had'u dan ganin mun kawar da masifar dake nanad'e damu, bazan taba bari Abdulmajid ya gajeni ba dan kamar naba Magajiya kujerata hakan zai kasance, ita kuma nasan bazata taba bari na baka kujerata ba."
Turab ya daure kansa na kasa ya d'ago ya jinjina kai yace " Na fahimci me kake nufi, sannan ni kaina na dade da zargin itace silar matsalar idona sai dai ganin ba wanda ya taba zancen ba kuma wanda ya nuna yasa ban taba maganar ba."
Sarki ya mai murmushin tausayawa yace " Kayi hakuri Turab da samun Mahaifin da bashida karfin hukunta wad'anda suke da laifi."
Turab ya girgiza kai yace "Ba haka bane Abba, a koda yaushe ina alfaharin kasancewarka uba a gareni."
*ABU TURAB TEAM*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*55*
Turab na fitowa daga b'angaren sarki ya hau tafiya, Garzali ya biyoshi da sauri yace "Ranka ya dade ina zamu?"
Juyowa yai ya kalli Garzali yace " akwai makullin mota a hannunka?"
Kai ya girgiza alamar a'a.
Turab yace "d'an hanzarta ka d'auko fita nakesan yi." Garzali ya juya da sauri.
Turab ya shafi fuskarsa zuwa kansa sam jiyake gidan ya mai zafi, duk hirman masarautar jiyai kamar a takure yake.
Inama ya iya mota? Da dakansa zai d'auka yai waje, sai dai matsalar idanunsa yasa bai tab'a koya ba gudun kar asiri ya tuno.
Bai dade ba sosai sai ga Garzali nan ya bud'emai gidan baya ya shiga shikuma ya shiga gaba sukai waje.
Tafiya kawai sukeyi, ganin baice komai ba yasa Garzali yace "ina zamuyi Ranka ya dade?"
Turab yana kallan window yace " ka cigaba da tafiya kawai, ni kaina bansan inda zamu ba."
Jin haka yasa Garzali ya cigaba da jan mota.
Komar da kansa yai jikin kujera ya rufe idanunsa kamar maiyin bacci.
Sai da sukai tafiyar a kalla awa d'aya sannan yace mu juya.
Nan Garzali ya juya da kan mota, kasancewar safe ne dan lokacin karfe 10 ne na safe, gashi lokacin damuna ne yasa garin yai luf abin sha'awa ba kuma rana.
Sai da suka shiga garin Zariya sannan ya kalli Garzali yace " kasan gidan Barde?"
Garzali ya murmusa sannan yace "eh."
Turab ya d'anyi karamin tsaki yace "Garzali a idanuna dana mutane ina ganin kamar nid'in mutumin kirkine sai dai a zahirin gaskiya banida kirki ko kad'an."
Garzali yace "Ranka ya dade ta yaya zaka ce haka?"
Turab ya jingina kansa jikin kujera ya hard'e hannayensa tare da maida idanunsa ya rufe yace " Duk yanda yarinyar nan ke kula da Mahaifiyata da nikaina ace ko gidansu ban sani ba, sai dai ita tazo inda muke."
Ya karasa maganar tare da juyar da kansa gefe.
Garzali yai shiru kafin can yace " Ai kai kaga baka fiya fita ba, sannan yaushe ma ka warke Ranka ya dade?"
Turab bai ce komai ba, sai da suka isa gidan Garzali yai parking sannan ya kalli Turab wanda ya bud'e ido jin tsayawar motar yace " mun isa, a kira maka ita?"
Turab ya kalleshi yace " Cema akai zance nazo ko me? Ka sanarma Barde da zuwana."
Garzali yace to, sannan ya fita.
Yana fita Turab ya kalli waje, unguwar ya shiga kallo.
Garzali ne ya dawo da sauri yace " Kunye sab'ani ance d'azun nan ya tafi fada."
Turab yace "ayya, Mairo fa?"
Garzali yace "Ban tambaya ba dan nima dama bance kai bane kazo."
Turab yace " kira min ita, tunda nazo harnan mu gaisa."
Nan ya juya, yaron d'azu wanda da alama a gidan yake ya kara turawa yace "ya kida masa Mairo." yaran yace ince inji wa?
Garzali yace kace inji Yarima Turab.
Nan yaran yai ciki da gudu.
Mairo ta gama cin abinci kenan tana tattare kwanuka yaran dayake d'an babbar yayarsu ce da aka kawoshi hutu ya shigo da gudu ya rike mata riga yace " Ana kiranki a waje."
Tace " Khalid meye hakan? Waye yake kirana?"
Yace " Wai kije inji Yarima Turab."
Hararar sa tai sannan ta kwace rigarta tai kitchen tana cewa "Lalai Abdulmajid ma Ya raina mata hankali, taje inji Turab?"tai tsaki tace ko kunyar karya ma mutum bai iya ba.
Hannunta ta wanke sannan ta fito tai d'aki, kan gadonta ta kwanta, can kuma ta mike zaune tace karfa inje da gaske ya Turab ne.
Hijab dinta ta jawo tai waje.
Lekowa ta fara yi ganin duk suna cikin mota yasa ta kasa ganewa.
Ta kara lekowa, Abu turab ne ya zuge glass d'in window dinsa sai daya tabbatar itace sannan ya bud'e motar ya fito.
Mamaki ne ya kamata ganin shi d'in ne ya fito, kallansa kawai take d'auke da tsananin mamaki har ha iso soron.
Bayan kofa ta shige fa sauri tare da bin jikinta da kallo, ko kwalliya batai ba, jitai kamar ta ruga ciki.
Turab ya tura kofar yace " ko dai in juya ne?"
Tana bayyan kofar tace " Ya Tutab."
Takowa yai zuwa ciki yana cewa " Ba dai Abdulmajid har ya fara hanaki kula yayan naki ba."
Fito tai tare da had'e fuska tace " waye shi kuma?ni ai banaji a list d'in yayuna inada mai irin sunan."
Yace " To ko a kirashi sai a tambayeshi? Inga ko zaki iya tambayarsa."
Dariya tai mara sauti tace "Yaya kana tunanin bazan iya ba?"
Hannunsa yasa ya rufe bakinsa yace " Tab ai na manta ashe fa Mairo ce. mairon data yardani sau biyu."
Juyawa tai da sauri cikin shagwab'a tace "Haba yaya"
Murmushi yai yace " Barde nazo nema ashe bayanan."
Juyowa tai tace " ya tafi fada."
Turab ya kalleta yace "Are u okay?"
Yanayin fuskarta ne ya canza tace " akan me?"
Kallanta yai sai dai baice komai ba, murmushi ta masa tace " I am okay yaya."
Kara kallanta yai idanunsa d'auke da alamar kokonto, jitai idanunta na neman cicikowa, kanta ta d'aga sama tana neman maidasu, sannan ta kalleshi tare da girgiza kai tace " Yaya i am not okay, na rasa yanda zanyi, Abba yace bashida yanda zaiyi, kai baka nan, kunya nakeji in koma gun Umma sannan yaya bazan iya auren mutumin dana san ba sona yake ba, wlh yaya da ace Abdulmajid san tsakani da Allah yakemin ko da banasan sa zan jure na aureshi ko dan neman gyara halayensa." hawaue ne ya zubo mata ta girgiza kai tace "Sai dai yaya ni nasan Abdulmajid nasan irin kallan da yakemin, na tsani kallan da yakemin, na rasa ya....."
Kasa karasawa tai ganin tana neman yin kuka, gashi batasan Turab yaganta cikin wannan halin.
Tsananin tausayinta ne ya kamashi, kallanta yai sannan ya zaro handkerchief daga aljihunsa ya mika mata.
Ansa tai ta goge hawayenta sannan ta kakaro murmushi ta kalleshi tace " Ya yayar tamu? Ka barota lafiya?"
Murmushi ya mata yace " Bilkisu ce yayarki?"
Tace "eh mana, a yanzu dai ba yaha ta bace amma inta aureka ai ta zama yayata."
Kallan tsananin tausayawa ya mata dan tabbas yasan yanda take sanshi, yace " Tana garinsu, sannan Mairo ba kya ganin ya......."
Gabanta ne ya fad'i tana tsoron kar yace ya kamata ta daure ta auri Abdulmajid, da sauri ta katatshi tace " Yaya kasan me? Khadija fa ta d'auka ni kake so, tun kwanaki nakesan fadama sai in manta."
Kallan mamaki ya mata yace " mene?"
Daurewa tai tace " nima bansan ya akai tai wannan tunanin ba."
Iska ya d'an furzar yace " share wannan zancen sannan ni in tambayeki kinji na cemiki Khadija nakeso da bakina?"
Tace " Au sai ka furta? Banda abinda idanunka suka nuna?"
Handkerchief dinsa dake hannunta ya fizga sannan ya kwad'a mata akai, hannu tasa agun da ya daketa tace " Yaya da zafi fa."
Murmushi sukayi a tare, sannan ya saki wani hucci na tunowa da matsalar dake gabansa.
Kallanta yai yace " Karki damu, ke dai kicigaba da addu'a In Allah ya yarda komai zaizo da sauki."
Kai ta d'agamai tace "Nagode Yaya."
Juyawa yai ya fita, kallan bayansa tai har sai da ya shiga mota.
**********
A gidan Waziri kuwa, Khadija ce tsugunne gaban mahaifinta.
Hisham ya kalleta fuskar nan tasa ba wasa yace " Khadija mun riga mun yanke hukunci akan aurenki, dan Magajiya harta sa an sanar ma iyayen Saifullahi akan maganar sa rana, dan haka ki shirya, bazan tab'a yadda da wani zancen banza ba...."
Kallan mahaifinta tau idanunta fal hawaye tace " Abba tunda akai maganar Saifullahi ban tab'a cewa a'a ba ko wani abu, ni dai naji zan aureshi amma yaya Abdulmajid dan Allah ya janye auren nan na dole da yake neman yima baiwar Allah."
Kallanta yai ransa ya kara tun zura, mahaifiyarsa ya kalla da take zaune shiru, dan ko baki bata sa musu ba.
Yace " biyoni ke kuma."
Ya fad'a tare da yin ciki, Khadija na ganin haka tasan shikenan ta jama mahaifiyarta, da sauri tace " Abba...." bata soma fad'in komai ba Mahaifiyarta ta kalleta tare da girgiza mata kai alamar kartace komai.
Suna shiga d'aki ya kalleta yace " wai wani irin tarbiyya kikama Khadija? A da na d'auka duk gidan nan tafi kowa jin maganata da hankali amma yanzu na fara tunanin zugata kikai inba haka ba yarinyar da nasan komai nacemata tanayi akan me yanzu akan wani can sokon yaro ta nemi bijiremin, kece kike zigata kome?"
Kallansa tai ranta ya tunzuro dan itakam ta tsani yanda suke neman yima Khadija auren wanda bataso tace "Tunda nake dakai na tab'a musa ma? Ko a sanda ka d'auki d'an dana haifa ka kaima yar uwarka magajiya na hanaka? Ko har izuwa wannan ranar na tab'a kaucewa akan sharad'in daka gindaya min?ko kuwa kana tunanin banajin zafin ganin d'an dana haifa na fari agun kanwarka? Yaro bai san matsayin ba, ko suna uwa bai taba kirana dashi ba."
Hawaye take sosai, kallanta yai rai a b'ace yace " Bazakiyi shiru ba?"
Cikin b'acin rai tace" kana tunanin tsoronka nake daga kai har Magajiya? Sannan yanzu ni kun gama min abinda kukaga dama 'yar tawa ma haka kuke san juya mata rayuwa? Ko kana tunanin duk wani abu na makirci da kuke kai da Ma"
Da baya da baya ta fara ja tana girgiza kai, sam ta ma rasa me take ji, tahowa tai dan taba mahaifinta hakuri sai dai me?
Juyawa tai da gudu ko takalmi bata sa ba tai waje, ko mayafi babu a jikinta.
Tafiya kawai take bata ma san knda takesa kafar ta.
Sam bata kula da motar da take mata horn ba, jan burki yai da sauri ganin taki kaucewa, duk da haka sai da motar ta d'an bigeta kadan.
Turab ya kalleshi da sauri yace " lafiya?"
Garzali yace " bansan wacece ba, inajina bigeta. " ya karasa maganar tare da bude motar.
Kusa da ita yaje yana tambayarta lafiya?
D'agowa tai ta kalleshi ganin bibiyi take, mikewa tai kawai tana neman cigaba da tafiyarta.
Da sauri ya kalli Turab wanda ya bud'e motar ya fito yana tsaye rike da kofa, yace " Ranka ya dade Khadija ce."
Da sauri Turab ya kalli inda yarinyar take, ganin Khadija yasa ya taho da sauri yace "Khadija?"
Kallansa tai sai tai baya luu kamar zata fad'i da sauri yasa hannu ya tareta, suka tsugunna, kallanta yai cikin tsananin tashin hankali yace "Khadija?"
Kallansa tai sannan ta shiga girgiza kai tana cewa " Abba meke faruwa? Wani d'ane umma ta ba kanwarka? Abba...."
Jijigata yai yace " Khadija? Meke faruwa?"
Kai ta shiga girgizawa, ta shiga kankame jikinta alamar tsoro.
Turab ya rasa abinda zaiyi d'aukanta yai cak ya sakata a mota, ya rufe ya koma gaba sannan ya kalli Garzali yace " mu tafi mu kaita gida, da alama bata cikin hayyacinta."
Sun isa gidan ya rikota ya kalli Garzali ba sai ya tambaya ba dan kana kalla tsari da fentin gidan kasan gidan mai mukami babba ne na sarauta.
Nan ya nufi gidan da ita.
Hisham wanda ya fito ransa a b'ace da rainin hankalin da matarsa ta masa yai kicibis da su.
Mamaki da takaici ne ya kamashi yace " Malam wani irin iskanci ne haka zaka rikomin 'ya......."
Bayan Turab ta b'oye ta rikemai riga tana cewa " wayyo Allah, dan Allah tafi dani daga nan, wad'an nan......"
Tsawa Hisham ya daka mata yace " Khadija bakida hankali ne?meye hakan?"
Turab ya juyo ya kalleta yace "Khadija menene?meke faruwa haka?"
Kallan Turab tai sai yanzu ta gane shine, hannunsa ta kamo da sauri tace " Yaya Abba da Umma Magajiya..."
Hisham ya fahimci akwai wani sirri da take san fad'a, da sauri yasa hannu ya fizgota.
Tace " Kanwar Abba? magajiya kenan, kenan Ya Abdulmajid......"
Toshe bakinta yai ya sa hannu ya finciketa da karfi yai ciki da ita.
Turab ya kalli inda suka shiga yace " me ke faruwa?"
0 comments:
Post a Comment