Sun shiga ciki sukaga ba kowa a tsakar gidan, nan suka tsaya suna sallama, Basira kam jingina tai da bango.
Wata matace ta fito daga bayan gida rike da buta a hannunta ta amsa sallamar tana kallansu, nan Lantana ta gaisheta ta amsa, Lantana zatai magana sai taji muryar tsohon nan ta bayanta yana cewa " 'yata basu guri su huta sai suyi alwala ki basu abinci."
Ba tare da musu ba ta amsa da to, sannan tace " ku shigo."
Sun shiga wani d'aki wanda da alama nata ne d'aki ne an sa gadu guda biyu d'aya nai rumfa kato sannan sai d'an karami a gefe, sannan ancika d'akin taf da jere na samiru da 'yan china.
Akan tabirma data shimfid'a musu suka zauna, sannan ta zauna itama suka gaisa(wannan shine halin mutanen mu na da basa yarda ayi gaisuwa a tsaye ko me suke yi sunfiso suna daga zaune a gaisa)
Nan ta mike tai waje, Abu turab ya d'an fara abin kuka, hakan yasa Lantana ta kuntoshi daga bayanta ta fara jijigashi ganin ita kanta Basira yunwa takeji ina zai sami ruwan nonon da zaisha? Itakam tana tausayin Basira ganin tana tafe da d'anyen jego.
Matar ce ta sake shigowa rike da fitilar kwai ta ajiye musu sannan ta mike zata fita, kallan Abu Turab tai cike da sha'awa tace " Tabarkalla masha Allah sai dai da alama ba'a dade da haifarsa ba."
Lantana tai murmushi tace " yau fa kwanansu biyu."
Cikin tsananin mamaki ta kallesu tace "da jego haka d'anye kukai tafiya?"
Lantana tai shiru batace komai ba, kallan Basira tai wanda ganin yanda ta galabaita yasa ta fahimci itace Uwar, waje tai da sauri ta karasa murhu ta kada miyar kuka wanda dama ta saka komai kadawa kawai zatai.
Tana gamawa ta kawo musu tuwon dawa miyar kuka tasha manshanu.
Nan fa suka fara cin abinci, sosai Basira taci abinci.
Sai da suka gama sannan Lantana ta tashi tai sallah tunda Basira tana fashin sallah na jinin haihuwa.
Sunyi shiru a d'aki shikam Abu Turab bacci kawai yakeyi.
Basira tunani duk ya isheta da bakin cikin yanda rayuwa ta risketa.
Daga waje sukaji kamar ana dan fada, Lantana ta kalli Basira, jisukai ancigaba da fada " wlh yau bazan bar gidan nan ba sai Shehu ya biyani kud'ina kaf dan kuwa na gaji da wannan rainin wayan."
Hakuri sukaji ana badawa amma kamar zuga matar ake sai kara masifa takeyi da k'ak'aji.
Basira ta daure ta mike ta fita wajen, Matar da ta kula dasu ta gani zaune a gefe tana kuka, sai kuma wani mutumi a tsaye kusa da ita, ga matar nan da take ta masifa a tsaye a kansu.
Wata matace ta fito daga wani d'aki daga gefensu ta saki wani gud'a cikin farin ciki tace "Allah kasheni saboda farinciki, lalai yau take sallah a gurina, anje anci bashi anyi aure gashi an kasa biyan kudin da aka ranta, yo dama ina za'a iya biya tunda an auro mai farar kafa?"
Basira ta kalli matar yanzu ta gane inda abin ya dosa, da alama waccan din uwar gida ce, mijin yaci bashi ya auri wannan gashi kuma ba damar biyan kudin?"
Mai kudin ta kara zak'ewa tana ta zabga masifa, Basira ta fito ta zo kusa da matar sannan ta zare sarkar dake d'aure a wuyanta, sarka ce ta azurfa wanda a waccan lokacin kudi ce sosai, cikin mamaki matar ta kalleta sannan ta amsa ta shiga dubawa, tabbas azurface mai kyau da tsada wacce kana gani kasan sai mai hali sosai shine zai sa ta.
Shehu ya kalleta cikin mamaki sannan ya kalli matarsa yace " wacece?"
Hawayene ya zubo mata, zatai magana matar tace " kina nufin kin bani duka?"
Basira tace " ki saidata kid'au kud'inki ki ba matar nan ragowar."
Wannan d'ayar matar mai guda ta matso da sauri tace " baiwar Allah ked'in wacece?"
Basira ta juya ba tare da ta amsata ba ta koma ciki, Dattijon nan wanda ya kawo kai daidai lokacin da Basira ta mika azurfa ya share kwalla da ta taru masa, ba shakka dama yaji ajikinsa alhere ne su yana kallansu ya kalli yaron.
Matar ta kalli Shehu tace " Shehu ina ka samo wannan?wlh ka bincike ta in har ba matar wani hamshakin d'an kasuwan bane to tana da dangantaka da sarauta, inba haka ba a wannan zamanin waye zai baka wannan shamfad'ed'iyar azurfar?"
Shehu ya fizge azurfar daga hannunta yace "uwar san banza kud'inki dana ranta ko rabin wannan baikai ba, inyaso gobe kizo muje mu sai data inbaki kud'inki."
Haushi ya kamata, haka tanaji tana gani tai waje.
Uwargidansa ta matso da sauri tace "Shehu kawo na ajiye ma,kasan na iya ajiya."
Harara ya maka mata yace "kingama gud'ar?"
Kallansa tai cikin zolaya tace "kai bakasan wasa ba?"
Tsaki ya ja sannan ya mikama Amaryarsa azurfar yace " ajiye tukunna sai na nemi shawar Baffa."
Yana fad'a yai hanyar waje, a tsaye yaga Mahaifinsa, tsayawa yai kusa dashi kansa a kasa.
Mahaifinsa yace "biyoni ciki."
Nan yai gaba shima ya biyoshi.
A tsakar gida ya tsaya, nan Amaryar tai saurin shimfid'amai tabirma, ya kalleta yace "sannu 'yata, d'an shiga ki kiramin bakin nan."
Nan tai ciki da sauri, sun fito sun zauna a kan wata tabirmar, nan ya kalli Shehu yace " Zauna kaima."
Nan ya zauna matansa ma duka suka zauna.
Shiru ne ya biyo bayan kafin yace " Bismillahi Rahmani Rahim, ita bismillah ana san a fara ta akan duk abinda mutum zai aikata, dan haka yana da amfani mutum ya dinga yinta akai akai."
Kai suka jinjina sannan yacigaba " Baiwar Allah ya sunanki?"
Basira! Abinda ta fada kawai kenan kanta na kasa, yacigaba " daga ina kuke?"
Tace " katsina."
Yace " bazan tambayeki rayuwarki ba da yanda kikayi ta da abinda ya fito dake ba sai dai inaso inji abu biyu, na farko wannan yaron ta wani hanya kika sameshi?"
Lantana zatai magana Basira ta rike mata hannu sannan tace " Allah shine shaidata aure nai na sameshi."
"Alhamdulila!" Abinda ya fada kenan sannan yace " tambayar karshe, Yanzu da kuka fito ina zaku?"
Basira tace " ni kaina bansani ba, na rasa yayana wanda shi kadai ya ragemin sannan dole ne in taimaki d'a na."
Shiru yai kafin yace "Shehu."
Da sauri yace "Naam Baffa."
"a guara musu bangaren mahaifiyarka su zauna."
Ya amsa da to, sannan yacigaba " ku zauna anan har iya lokacin da kukaji zaku koma, ni limami ne a nan garin kar kusa komai a ranku ku zauna anan kamar kuna gidanku."
Godiya suka shiga yi, Shehu ya mika mata azurfarta, yace " karki damu zan...."
Kai ta jijiga sannan tace " karka damu nayi ne dan Allah da kuma darajar taimakon da aka mana, nima bani akai dan na bada kuma ba wani abin bane."
Da wannan aka tashi.
Amarya wato ( Kubra) ta mike tai b'angaren mahaifiyar shehu wacce ta rasu wata 5 da suka wuce, b'angarenta daban ne dan sai ka d'anyi tafiya kadan ka shiga kofa sannan zata sadaka da b'angarensu.
************
Tashin hankalin da Hisham ya shiga baya misaltuwa haka suka isa Zariya duk ya gama rikicewa, suna isa yai fada da sauri, Mai Martaba kam ana cewa Hisham ya iso hankalinsa ya kasa kwanciya saboda tsananin farin ciki, kofa kawai ya kurama ido yana jiran shigowar Hisham.
Ganin Hisham ya shigo yasa yai ajiyar zuciya, nan Hisham ya matso duk ya birkice ya gaidashi ya d'auka zai haushi da fada akan yabar matarsa ta taho ita kadai, sai jiyai Sarki yace "Hisham ka dawo lafiya? Sannu da kokari ba shakka ka sha tafiya."
Hisham ya share zufa cikin tsoron abinda zai faru, Sarki yace " ka je gida ka huta kasha tafiya."
Nan Hisham yai godiya yai waje.
Mai martaba yai murmushi, yau zaiga Basira da d'ansa, burinsa na sa wannan suna yayi.
Bazai taba mantawa ba tun sanda mahaifinsa ya bashi labarin sunan a lokacin da ya ganshi ya kwanta a kasa, ya sa aransa sai ya sa sunan nan.
(_Sunan Abu Turab sunane wanda Manzon Allah ya sawa Sayaddina Ali a yayin da ya ganshi ya kwanta a kasa, yai murmushi yace Abu Turab wato Father of Soil."
Murmushi ya sake yi.
Shikam Hisham na fita yai gun Magajiya da hanzari.
Tana tsaye ya sameta dan itama hankalinta ya tashi jin ance Hisham ya dawo amma shi kadai ne ba tare da Basira ya dawo ba.
Yana shigowa ta tareshi da cewa " Yaya meke faruwa?"
Hisham ya rikice yace " Magajiya muna cikin matsala."
Matsala?tame kenan?"
Nan ya kwashe komai ya sanar da ita, kanta ta dafe cikin tashin hankali tace " yanzu kenan bamusan a wani hali take ba daga ita har d'anta?"
Yace " tuba nake."
Wani tulu dake gefenta ta buga da karfi hakan yasa ya fashe, cikin tsoro Hisham ya kalleta, idanunta sunyi ja cikin fada tace " meyasa baka aiki da hankali? Me kake tunani zamu cema Sarki? Bamusan ta mutu ba ko tana raye, in mukace mai ta mutu ta dawo fa? Muce me? In kuma mukace tana raye to tana ina? Me yasa Hisham sam wani sa'in kanka baya aiki? Ni kaji daga bakina nace ka kona musu gida? Waye ya baka damar aiwatar da abinda ban umarce ka ba?"
Hisham takaici ya kamashi, me wannan yarinyar take nufi?
Cikin fad'a tace " jeka banasan ganinka sannan kar ka shigo gidan sai nan da kwana biyu ni zan san yanda zanyi."
Jiki a sanyaye yai waje, wani dogon tsaki taja ta d'aura hannu akai cikin takaici yanzu ya zatai?
Shiru tai ta shiga dogob nazari........
_Hmmmmm_
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
.. 🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
*12*
Ana Magrib Magajiya ta kintsa tsaf sannan ta aikama da Sarki zuwanta, alokacin hankalin Mai Martaba ya gama tashi dan yana tasowa daga fada ya aika wani bafaden sa akan ya dubo masa lafiyar matarsa da d'ansa kafin yazo sai dai abin mamaki dawowa akai aka sanar dashi rashin isowarsu gidan.
Magajiya ta iso a lokacin shi kansa ya matso ya ganta dan yana san jin abinda ke faruwa.
Bayan ta shigo ne ta zauna a inda ta saba zama wato d'an nesa dashi kadan, sannan ta numfasa cikin isa da kuma nuna alamar damuwa tace " Ranka ya dade muna cikin matsala fa?"
Kallanta yai cikin mamaki sai dai bai amsa ba, itama ta kalleshi sannan tace " Basira bata dawo ba."
Kallanta ya sakeyi nan ma bai tanka ba, idanu ta runtse cikin alamar kunar zuci na tausayi tace " gobara ce ta kama da gidansu a daren jiya."
Lalai wannan kalma ta d'agamai hankali wanda bai san sanda ya mike tsaye ba, Magajiya ta kalleshi cikin kulawa tace " Yayanta da matarsa sun rigamu gidan gaskiya."
Sarki a tsaye yake kawai dan hankalinsa ya kai koluluwar tashi, ta cigaba tare da share idanu kamar irin mai kwallar nan, tace Basira da d'anta dai ba abinda ya samesu sai dai firgita datai da abin yasa ta fita da gudu wanda har safiyar yau ba wanda ya ganta.
Hankalin Sarki ya kara tashi ya koma Ya zauna dabas kamar ba sarki ba.
A hankali ta taso tazo inda yake tasa hannu ta kamo nasa hannun tace " nasani sarai hankalinka ya tashi sosai kamar yanda nawa ya tashi, shiyasa na rasa mai zance maka, Hisham tun safe yake nemanta amma ba labari wanda hakan ne yaga dole yazo ya sanar dakai asan abinyi."
Kallanta yai ji yake kamar ya saki wani irin ihu na bakin ciki, Magajiya cikin murya taban tausayi tace " Basira ba yarinya bace na tabbata zata dawo hankalinta ne ya tashi har yasa tai wani hannu sai dai fatan Allah yasa ta fad'a hannu na gari."
Sarki ya d'ago cikin tashin hankali wanda tunda Magajiya take bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba, kallanta yai cikin kakkausar murya yace " inasan kad'ai cewa."
Kai ta jinjina alamar to, sannan ta mike ba tare da tace komai ba tai waje.
Tana fita ta kalli kofar d'akin tai wani murmushi tace " kai da Basira sai a lahira dan duk yanda kaso ko ita taso baku isa ku kara zama tare ba bare har kaga d'anka ka fahimci menene d'a na jini."
Juyawa tai tacigaba da tafiya ana take mata baya cikin kasaita da tak'ama.
************
Shikam tana fita ya runtse idanunsa kam jiyai hawaye ya gangaro mai sau d'aya, mikewa yai yaje jikin tagar d'akin ya bud'e ya kurama taurari ido,jiyake kamar zuciyarsa zata fashe ga zuciyarsa ta fara masa sake sake mara amfani, yana tsaye yana kallan taurari sai dai a zahiri tunani ne fal ransa, nan ya shiga tunanin rayuwarsu da abokinsa da kuma matarsa ga kuma bai taba ma ganin d'ansa ba,kasa jure abinda ke ransa yai ya tsugunna a gun tare da dafe kansa wanda ya fara sara mai....
A wannan ranar Mai Martaba ko gadonsa bai hau ba bare ya samu danar rintsawa.
************
Basira ma bataga bacci ba a wannan ranar, tunani ne kawai ke mata yawo a ranta, ido ta kurama d'anta tana ji wani abu na taso mata, ya zatayi? Zama zatai tayi anan saboda tsoron kar wani abu ya samu d'anta? In tai hakan kenan ta raba d'anta da mahaifinsa, sannan auranta fa?"
Wad'annan tunanukan sun mata yawa fal aranta wanda sukasa idanunta suka kafe kaf.
***********
Magajiya ta sanar da Hisham yanda sukai da Sarki sannan ta sashi yaje ya nema ayima Basira magani akan karta waiwayi gida, a mata maganin da zaisa taji sam batasan gida."
********
Tun bayan tasowar Abu Turab suka kula da rashin ganinsa, da farko sun d'auka lokacin ganin nasa ne baiyi ba sai dai ganin ya kai wata 4 yasa suka fahimci akwai matsala da idanunsa, haka ya taso ba idanu sai dai Allah ya bashi hazaka wanda ko zama kai dashi na awanni sai ka fahimci hakan, yanada baiwa sosai ta fahimta da rike abu.
A duk sanda Basira tai tunanin komawa gida sai taji zuciyarta ta kuntata, hakan yasa ko maganar batasan a mata, Lantana kam ko da wasa bata taba tambayarta ba, haka mutanen gidan.
Abu Turab har yakai shekara 5, Baffa shi yake koya masa karatu, yana tsananin san yaron saboda san karatunsa da hazakarsa, Basira ta d'aurashi a kan tarbiyya mai tsananin gaske, ko laifi ya mata wanda bai kai ya kawo ba haka zatasa shi a tsakiyar rana gashi bashida ido sai yayi kusan awa uku a tsaye, gashi bai isa yai kuka ba, dan kuwa in ya kuskura yai to fa lalai zai gamu da hukunci mai tsananin gaske, a haka in ka kalleshi bazaka taba cewa baya gani ba dan kuwa idanunsa garau suke, bata bari a taimaka mai har sai intaga yana neman faduwa ko yana neman taimakon sosai, komai da kansa yake yi, zakasha Mamaki in har kaga yanda Basira take tsananta tarbiyar d'an nata.
Abu Turab ya taso mai tsananin jarumta gashi dama magana bata wani dameshi ba dan ko abokai bashida shi sannan yaro ne wanda in yana abu dole ka kalleshi domin jinin sarauta na yawo a jikinsa yana da jinkai sannan ko magana yakeyi zakasha mamaki.
Shigarsa Shekara bakwai ga tsufa ya kara kama Baffa, yanzu ko fita zaiyi sai an taimaka masa, a yau ya tashi da zazzab'i wanda yasashi zama a d'aki, Abu turab na zaune kusa dashi yana mai karatu kamar yanda Baffa ya sashi.
Bayan ya gama ne Baffa yace " D'ana(haka yake cemai.) kiramin Mahaifyarka."
Abu Turab ya mike rike da karamar sandar da yake tafiya da ita ya isa b'angarensu, A waje yaji muryarta hakan yasa ya matsa kusa ya sanar da ita sakon baffa.
Mikewa tai ta zura hijabinta ta fita, Lantana na zaune tana sana'ar mangyad'a wanda dashi suke rayuwa, ya matsa kusa da ita dan yanajin sautin aikin datake, zaiyi magana yaji tace " Ka zauna."
Tai maganar tare da tashi a kan kujerar ta ta nuna masa gun zama.
Shiru yai hakan yasa ta rike hannunsa ta zaunar dashi.
Murmushi yai yace " Lantana baki tab'a kiran sunana ba tunda nake dake."
Kasa tai da kai a ranta tace " ina na isa?"
Murmushi ya sakeyi yace " Kujerar da kike kai kika bani ko?"
Batai magana ba sai dai a ranta tace " dole na ne ai."
Mikewa yai ya nufi hanyar cikin d'aki."
*********
Basira zaune kusa da Baffa wanda ya ke a kwance, Baffa ya kalleta yace "Banso na miki magana da kaina ba sai dai inaji a jikina lokaci na ya kusa hakan yasa dole na kiraki."
Kallansa tai sannan ta maida kanta kasa, Baffa ya cigaba" Basira ya kamata ki koma gidanki inhar akwai aure akanki to fa lalai kina d'aukan zunubi ne."
Kallansa tai idanunta suka kad'a sosai ga mamakinsa hawaye yaga tana zubarwa.
Kallanta yai cikin tausayawa yace " ba tillasta miki nake ba sai dai shawara nake baki, in har da aure akanki nace nima ba wani abu ba."
Hawayenta ta share sannan tace "Sunana Basira.........."
Kaf abinda ya faru da ita ta sanar dashi.
Baffa hawaye ne ya gangaromai saboda tausayi, shiru ne ya biyo baya a d'akin domin kuka sosai takeyi miken dake binne a zuciyarta ya tashi.
Sun dade a haka kafin Baffa yahau addu'a, sannan yace" nayi zargin wani abu sai dai rashin sanin labarinki yasa ban tab'a sanar dake ba, sai dai yanzu zargin da nakeyi inaji ajikina hakan ne."
Kallansa tai cikin rashin fahimta, Baffa ya cigaba " D'ana, wato Abu Turab banaji a haka Allah ya halliceshi." cikin mamaki tace " kamar yaya?"
Yace " sihiri baya taba zama daidai da kaddarar Allah."
Idanu ta zaro tace " kana nufin....."
"kwarai da gaske, bazan rantse ba kuma bazan miki alkawari ba sai dai kafin Allah yad'au numfashina in dai har sihirine to ni zan karyashi da yardar Allah, sannan inaso kimin Alkawari In har d'anki ya warke zaki koma gun mijinki, Allah ne kadai yasan halin da yake ciki na rashin ku."
Basira tace " Nagode kwarai sai dai Baffa na rasa dalili sam banasan ai zancen komawata gidan."
Hannayensa ya had'e ya shafi fuskarsa yace " dole ki cire tsoro a ranki ki taimaki d'anki, ba wai dan ya hau mulki ba a'a sai dan tsira da rayuwarsa, kina tunanin taimakonsa kikai na kawoshi dajin nan? Ko kina tunanin zaki iya canza abinda Allah ya kaddara a kansa ne?"
Kai ta girgiza alamar A'a.
Baffa ya cigaba " Abu Turab inaji a jikina yaro ne wanda za'ayi alfahari dashi nan gaba, kada ki kuskura ki rabashi da mahaifinsa, ki zamanto mai yarda da kaddara mai kyau da mara kyau."
Hawaye ta share sannan tace " na maka alkawari inhar sihirine yana warkewa zamu koma in kuma ba shi bane ma zan maidashi gun Mahaifinsa."
"Alhamdulila, nagode da amfani da shawarata da kikai sannan inkinje ki turomin d'ana sannan ki bashi kaya kala uku a guna zai dinga kwana, yaro ne mai hazaka da ilimi wanda a shekara 7 ya haddace izu 30 wanda tunda nake ban taba ganin yaro mai wannan baiwar ba, ni dashi zamuyi yakin ganin mun warware komai."
Godiya sosai Basira ta shiga yi.
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
ẞ 🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
*13*
Haka Baffa da Abu Turab suke wuni karatu da addu'oi kala kala sannan daga dare yashiga kashi uku Baffa yake tashinsa su shiga saloli da addu'oi, ko waje baya fita, a kwanansu na hud'u Abu Turab ya fara wasu mafarkai cikin dare yake farkawa wani sa'in da kuka sai dai daga ya tashi yake manta mafarkin.
Sun dage sosai da addu'oi, karatun qur'ani da saloli.
Yau satinsu d'aya kenan Abu Turab na kwance yana bacci hankalinsa a kwance, yau baccib dadi yake masa gashi ko mafarki baiyi ba, Baffa ya sa hannu ya tabashi yace "D'ana tashi lokaci yayi."
Mamaki abin yaba Baffa ganin bai tashi ba, kallan fuskarsa yai sai dai kana kallansa zakasan yana cikin kwanciyar hankali, Baffa yai murmushi sannan yai bismillah ya kara taba shi, addu'ar tashi daga bacci ya fara karantowa bayan ya gama ne ya bud'e ido a hankali duk da yasan duhu kawai zai gani sai dai me? Dishi dishi ya fara gani, cikin tsananin mamaki yace " Baffa ido na."
Baffa ya dafashi yace " menene? Me idan naka yai?"
Murza idan ya shiga yi, Baffa ya shiga karanto addu'oi yana tofa mai, Abu Turab ma yanayi.
Cikin tsananin mamaki da al'ajabi Abu Turab yaga tsohon dake kusa dashi, a hankali yakai hannu inda Baffa yake yace "Baffa!"
Kallansa Baffa yai shima ya kasa magana sai addu'a yakeyi Allah ya taimakesu.
Abu Turab ya tsugunna kusa dashi ya rungumeshi sai ya saka kuka.
Baffa ma hawaye ne ya zubomai dan ya fahimci ya ganshi.
Abu Turab cikin kuka yace " Baffa na ganka, Ina ganin komai ga katifarka, ga kayanka nan a lank'aye, ga kwanan abinci nan ga leda nan a tsakar d'akin, Baffa ina ganin komai."
Idanu Baffa ya lumshe yace " Alhamdulila lalai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah."
Tashi muyi alwala muyima Allah sujjada.
Mikewa yai cikin wani jin dadi mara misaltuwa yai waje.
Bayan sunyi addu'ar godiya ga mahallici ne ya kalli tsohon yace " inje gun Ummana?"
Baffa yace " ka barta ta samu bacci zuwa asuba."
Nan ya zauna cikin zakuwa, sai kallan abubuwa yakeyi......
Ana asuba yai b'angaren da gudu jin kofar a bud'e ya shiga bugawa, Basira ta mike a d'an tsorace ta matso tace "waye?"
Cikin jin dadi Abu Turab yace " nine Umma."
Mamaki ne ya kamata da sauri ta bud'e, ya matso da gudu ya rungumeta yana kuka yace " yau Allah yayi na ganki."
Idanunta ne suka ciciko da kwalla, ya saketa sannan ya kura mata Ido yace " Umma na ganki, Umma naganki."
Rungumeshi tai itama tace Alhamdulila.
***********
Satinsa d'aya da warkewa Baffa ya kara kiranta ya mata maganar tafiya nan, tace nan zuwa kwana uku zasu tafi.
Zaune take a d'aki tana kan gado Lantana na kasa haka shima D'an nata.
Kallansu tai tace "inaso duk ku bani hankalinku, akwai abinda nakesan sanar daku masu mahimmanci guda biyu."
Tai d'an ajiyar zuciya sannan tacigaba" na farko zuwa jibi zamu tafi Zariya."
Da sauri Lantana ta kalleta shikam baisan me hakan yake nufi ba shiyasa bai wani damu ba.
Tacigaba " abu na biyu wanda yafi komai mahimmanci shine inaso Lantana kada ki kuskura ko da wasa ki nuna Abu Turab na gani."
Cikin mamaki ta kalleta, Basira tace "wannan umarni ne ba shawara ba."
Da sauru Lantana tace " angama Ranki ya dade."
Basira ta kalli Lantana tace " d'an bamu guri."
Da sauri tai waje.
Basira ta kalli d'anta ta mikamai hannu hakan yasa ya mike tare da zuwa inda take.
Basira ta zaunar dashi kusa da ita sannan ta rike hannayensa biyu tace " nagode kwarai da baka tab'a tambayata mahaifinka ba."
Kallanta yai sannan yai murmushi, ta cigaba " ka nutsu sosai da abinda zance maka."
Kai ya d'aga alamar to sannan ya kada nutsuwa, tace " zamu koma gidan da mahaifinka yake wato gidanku sai dai ina tsananin tausaya maka, da farko inaso kada ka nunama kowa kana gani, hatta mahaifinka ka zama makaho a gaban kowa, ka zama mai ido agabana kad'ai."
Cikin mamaki yace " me....."
Kallan datai mai yasa yai shiru, tacigaba " banaso ka tambayeni dalilin hakan dan kuwa inka mallaki hankalin kanka na tabbata dakanka zaka sanar dani komai, domin zaka samu cikaken amsar tambayarka."
Kai ya d'aga alamar to,tace " Abu Turab!"
Yanda ta kira sunansa da kakkausan murya yasa ya kalleta jiki a sanyaye, tace "kamin alkawarin zakai wannan abin?nasan kasan me alkawari yake nufi a muslunci ka kuma san hukuncin wanda ya karya."
A hankali yace "na miki alkawari ko mai zai saman bazan nuna ina gani ba."
Ajiyar zuciya tai na jin dadin baiwar da Allah ya mata wato na azurtata da wannan yaron, tacigaba " gidanku ba kamar gidajan daka sani bane, dolene ka nutsu kaji me zance, da farko duk yanda ranka yaso da b'acci banaso ka nuna, sannan abu na biyu banaso ka zama ragon yaro."
Kallanta yai baice komai ba, ta riga tasan wannan sai dai ya zama tuni amma tun yana karami ta horar dashi akan haka, ita dama matsalarta shine taurin kansa dan inbaiyi niyyar abu ba ko za'amai dukan dazai kasa tashi tofa bazaiyi ba, wannan hali nasa shi take jiye masa.
Ta riga ta d'au alwashin sadaukar da komai nata dan ta kare d'anta.
Sun dade rike da hannu juna tana mai fada a karshe tace " in muka koma gun Mahaifinka banaso ka yawaita cewa komai sai ni, dolene ka rage nuna damuwarka akaina, kallan mamaki ya mata a ranta tace (in aka fahimci nice komai naka to lalai za'a nemi yin amfani dakai da sunana wanda nikuma ba lalai in iya kwatarka ba daga hannun makirai."
Abu Turab zaune kusa da Baffa yana jin nasiharsa sun dade suna hira kafin Shehu yazo su zauna, Abu Turab yanajin hirar tasu har bacci ya d'aukeshi.
Sukam sunyi hira sosai, da shehu ya mike zai tafi sai yasa hannu zai d'auki Abu Turab akan kaishi b'angarensu.
Baffa yace " barshi anan so nake na kwana dashi."
Nan Shehu ya ajiye shi ya tafi, Baffa ya d'auko rubutun daya wanke ya tashi abu turab yace ya wanke fuskarsa har zuwa kansa, yana magagin bacci ya wanke sannan ya kwanta, Baffa ya dinga mai addu'a sannan ya kwanta.
Jin kiran Sallah yasa Abu Turab ya mike, mamaki ne ya kamashi ganin Baffa a kwance yana bacci, kusa dashi ya matsa ya shiga tashinsa, hankalinsa ya tashi ganin ko motsi bayayi.
Da gudu yau cikin gida b'angaren Shehu, a waje ya sameshi yana alwala matarsa na tsaye kusa dashi.
Abu Turab ya kalli Shehu yace " Kawu kazo Baffa yaki tashi daga bacci."
Inalilahi wa ina ilaihi Raji'un wannan kalma ita Shehu yai ta ambata, dan ko ba'a fada ba ko bai gani ba yasan me hakan yake nufi.....
Allah ya jikan Baffa da Rahama Ameen........
*********
A ranar da akai uku su kuma suka shirya tafiyar tasu.
_Wannan kenan_
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
_'Yan grp na Kainuwa Dashen Allah ga naku shafin, tnx 4 d love....._
*14*
Sun shirya tsaf ba kaya suka d'auka ba dan komai nasu anan tabarma matan gidan saboda tasan inda zasuje.
Shehu shi ya kawosu inda zasu hau mota dan a wannan shekara wato ta 1978 (shekarar Abu Turab 7 sannan shekararta takwas da aure.) a wannan lokacin an sanu cigaban wata yar kurkurar mota bayan akuri kura da motar itace, sai da suka shiga sannan Shehu ya musu sallama ya juya ya tafi, matansa sunsha kuka dan kuwa Basira ce silar zaman lafiyansu.
A hanya Basira sai kara jaddadama d'anta takeyi akan abinda takesan yayi.
Daga baya bacci yai awun gaba dashi, Lantana ta kalleta sannan tace " Ranki ya dade inasan tambaya duk da dai ba hurumi na bane."
Basira ta kalleta alamar tana ji, Lantana tai ajiyar zuciya sannan tace " me zakice ya hanaki komawa? Dan ina tsoron kar a miki wani sharrin."
Basira tai murmushi tace " Lantana kenan, a da na yarda ni sukuwa ce wacce bata tunanin abinda zai faru, sai dai yanzu inada abinda nakesan karewa dolene in canza daga sukuwa zuwa nai dabara, karki damu." ta karasa maganar tare da dafata.
Sun dade suna tafiya kafin a d'an tsaya saboda wasu yaran na mota najin fitsari, nan fa aka fifita hardasu Abu Turab, bayan an dawo ne aka ci gaba da tafiya.
Sai yamma lis suka isa garin na Zariya.
Basira bayan sun sauka ta kalli Lantana tace "zaki iya gane gidan da na fara zama?"
Kai ta kada mata alamar eh, ta d'aura da cewa "sosai kuwa."
"Can zamu wuce."
Ba tare da tambaya ba Lantana ta amsa da to, Abu Turab ya rike sandarsa kamar yanda mahaifiyarsa ta umarceshi, dayake dama idanta a bud'e yake tarau a da d'in ma sai ance miki baya gani tukunna dan in kika ganshi haka bazakiyi tunanin rashin ganinsa ba.
Haka sukai ta tafiya har suka isa gidan, dan ma ba nisa sosai.
Suna isa suka karasa bakin kofar da fadawa biyu ke gadinta, Lantana ta kallesu sannan ta musu gaisuwar da take nuna alamar a masarauta take, sannan ta d'aura da cewa " Matar Mai Martaba ce Gimbiya Basira."
Kallan juna sukai alamar basu fahimta ba, dan kuwa su basu santa ba, ba'a dade da kawosu nan ba, sannan ko da ace ma sun santa ai shekarun dayawa dan kuwa mutane dayawa sun manta da ita, wasu sai da insun tunata susa dariya, wasu kuwa suyi tunani ko tana raye?
Basira ce ta kallesu tace " bud'e mana, shiga zamuyi sannan d'aya ya zauna dan ya tabbatar da mudin ba da wani nufi mukazo ba, sannan d'aya yaje Fada ya sanar da Mai Martaba yayi baki na sirri anan."
Kallan mamaki suka mata, Basira ta kalli na hannun dama tace " naga kamar kai bazaka iya mana komai ba in ma munzo da wani nufi ne, ganin yanayinka, dan haka so nake kaje ka samu sarki in ba hali ka samu Barde kace ya sanar da Sarki a kwai bakin sirri a gidansa na cikin gari."
Kallanta yai yana kokonto, Basira tace " kada ka kuskura ka sanarma kowa sai mutanen nan biyu, ganin kafin kaga Sarki abin zai zama mai wuya ina shawartarka ka sanarda Barde, kada ka fadama kowa inba shi ba."
To, ya fada yanzu kam ya fara yarda da sunsan mai Martaba duk da dai bai yarda matarshi bace sai dai gani kamanni iri na Abu Turab yasa ya san tabbas akwai hadin jini na sarki a jikinsa.
Nan yaja d'ayan yace "ka kula dasu kafin naje na dawo."
Nan ya fara tafiya, sukuma suka shiga ciki.
Suna shiga Basira tasa d'anta yai wanka sannan ta bashi rigar data taho mai da ita kala d'aya.
Itama wankan tai Lantana ta d'auko mata kaya tasa, dan kuwa dana akwai ajiyayun kayayyakin datai amfani dasu.
Nan Lantana ta shiga kitchen dan sama musu abin ci.
**********
Bafaden nan ya dade kafin ya samu ganin Barde nan ya sanar dashi sakon, mamaki ya kamashi bakon sirri? Ya kalleshi yace "sanar dani abinda ya faru tundaga farko."
Nan ya kwashe komai ya fad'amai sai dai ya manta sunanta shidai yasan ance matar sarki ce sannan yaganta da yaro."
Barde mamaki ya kamashi yace "shikenan koma gidan zan sanar dashi."
Har Bafaden ya juya Barde ya kirashi, ya karaso da sauri, Barde yace " yaron shekararsa nawa?"
Kai ya girgiza alamar rashin sani sannan ya dora da cewa "bazai wuce dai shida ko bakwai ba."
Gaban Barde ne ya fadi sai dai yai saurin girgiza kai a fili yace " bazai kasance ita bace kar na tadama Mai Martaba hankali."
Bafaden na tafiya shima ya koma fada, ko minti goma baiyi ba magrib tai, nan mai Martaba ya mike aka shiga takamai baya fadawansa.
Turakarsa ya shiga, yana kokarin shiga makewayi dan kama ruwa da alwala jakadiya ta fara sallama.
Amsawa yai tare da cewa " ya akai?"
Ta kalli Zagi sannan ta kalli Barde tai kasa dakai tace "Barde ne ke neman iso Ranka ya dade, a gafarceni."
Mamaki ya kama Sarki ganin Barde baya biyoshi, nan yai gyaran muryar dayake nuna alamar ya shigo.
Nan tace "Godiya yakd Takawa."
Nan ta kalli Barde tace " bismillah."
Barde ya bud'e kofar ya shiga, a zaune yaganshi nan ya karasa ya zauna a kasa kansa na kasa yace "Tuba nake Takawa na katsema lokacin al'amuranka."
Mai Martaba ya kalleshi yace "ya akai?"
Barde yai dan huci yace "wai baki ne na sirri suke jiranka a gidanka na ciki gari."
Cikin mamakin zancen yace " na sirri kuma? Me kake san cewa?"
Barde ya kwashe komai shima ya sanar dashi, a zabure ya mike yace " Barde Basira ce! Basira ce."
Barde yace "Mai Martaba kayi a hankali kasan bangon gidan sarauta akwai ji (azancin magana yai - yana nufin ya kula akwai masu lab'e.)"
Sai alokacin hankalin Sarki ya dawo dan jin ance Basira ba karamin tadamai hankali akai ba, cikin murya kasa kasa yace " ka shirya ka fara zuwa gidan ni zansan yanda zanyi na fito."
Barde yace "an gama Takawa."
Su Jakaddiya kuwa an baje kunne ana san jigo gulma ko dayake ba ita kadai ba wasu fadawan ma hankalinsu duk yana d'akin, sai dai ba wanda yaji me akace sai dai sunji kamar an ce Basira kamar kuma Barira kamar dai wai suna ake fada da ya fara da Bas, abinda yasa ba wanda yai tunanin Basira saboda ganin tsawon shekarun, na farko shikansa sarki ba kiran sunanta yake ba bare suyi tunanin wani abun.
**********
Mai Martaba kam wasu kayan yasa a jikinsa ana sallah ya samu ya wuce tare da bafadensa na kusa, sannan ya umarci d'ayan akan yace ya koma turakarsa ya kwanta sakamakon kansa dake sarawa.
Sun samu sun isa gidan tun a hanya yaketa add'ua akan Allah yasa sune.
Bayan ya shiga cikin gidan ya nufi kofar ya sa hannu kamar zai murd'a sai kuma ya fasa, karatun qur'anin dake tashi ya tsaya ji, can ya daure yai sallama, Basira tana zaune akan sallaya tanata addu'a akan Allah ya bata ikon shanye komai ya kuma sa komai yazo da sauki.
Abu Turab na gefenta yana karanto suratul Rahman cikin kira'arsa mai dadi.
Shiru Mai Martaba yai yana sauraron karatun.
Gaban Basira ne ya fad'i jin sallamar muryar da ta kasa b'ace ma kunnuwanta, mikewa tai a hankali tazo bakin kofar ta bud'e gabanta nata fad'uwa.
Kallan juna suka shiga yi cikin tsananin kewa da tausayama juna, a hankali hawaye ya zuboma Basira, Mai Martaba ya sa hannu ya riko nata hannu jin yake kamar a mafarki, ba shakka muryar d'ansa ne kenan yake karatu? Hakan yasa ya kamo hannunta ya shigo inda take a tsaye.
Cak ya tsaya yana kallan yaron dake zaune kan sallaya yana karanto Suratul Rahman cikin kira'arsa mai dadin gaske, zuciyarsa ce ta karye ya juyo ya kalli Basira sannan ya nuna yaron da hannu ya kuma nuna kanshi da hannu alamar ( wannan nawa ne?)"
Hawayenta ne ya gangaro sosai ta kada mai kai tana zubo dasu kamar ana zugo kukan.
Sakar hannunta yai ya karasa inda yaron yake a hankali dan jikinsa duk ya gama mutuwa, Zama yai a gaban yaron kan sallaya, Abu Turab ya kura mai ido amma bai daina karatunsa ba, yana kallansa.
Hannayensa Sarki ya kamo,hakan yasa yai sadakallahul azim.
Sarki yace "ya sunan ka?"
Ko kifta ido baiyi ba haryanzu yace "Abu Turab."
Kalla. basira yai cikin jin dadi.
Sannan ya nuna kansa yace "ka gane ni?ah ba haka zance ba, kasan ko ni waye?"
Tunowa da alkawarin dayama Mahaifiyarsa yasa yad'an kalli gefe kad'an ya girgiza mai kai alamar a'a.
Sarki yace "ina dama zaka sanni? Ni kaina sai yau na tab'a ganinka."
Kai Abu Turab ya sake girgizawa yace " ba haka nake nufi ba, ba na gani ta ina zan ganeka?"
Basira wacce ke tsaye tsoro duk ya kamata ganin yanda d'an nata ya kurama mahaifinsa ido ta d'auka ya manta alkawarinsu sai dai jin abinda yace yasa tau ajiyar zuciya.
A zabure ya kalli Basira, ganin yanda idanunsa sukai yasa ta daure ta d'agamai kai tana hawaye tace " tun yana jariri idanunsa basa gani."
Zuciyar Sarki ta kara karaya jiyake kamar ya sa kuka, da sauri ya jawo d'an nasa jikinsa ya kankameshi kam.
Sundade a haka kafin ya sakeshi.
Shiru ne ya biyo baya a d'akin, yana zaune kan kujera rike da hannun matarsa ya d'aura d'an nasa kan cinyarsa.
Basira ta kalleshi tace "in wani ya ganka fa?"
Murmushin yake yai ya shafa kan d'an nasa yace " duk laifinane, da bance kije gida ba d......."
Kai tai saurin girgiza mai tace " ko kad'an ba kaifinka bane."
Kallanta yai sai dai baice komai ba..
Sun d'anyi shiru kafin Basira ta kalli d'anta tace "koma can ka zauna zamuyi magana da mahaifinka."
Nan ya mike ya koma can gun 'yan tumtum ya zauna sai dai hankalinsa na kansu.
Jiyai Mahaifin nasa yace " basira ina kuka shiga?hankali na yayi matukar tashi."
Murmushi tai tace " ka yafeni nasani nayi babban laifi sai dai ba komai bane ya hanani dawowa sai d'ana, ina tsoron rayuwar da zaiyi a gidan sarauta ba ido, ina tsoron wulakanci da gulma da habaici da zai fuskanta, nafarko ni ba wata mai matsayi ba sannan ga d'ana ba ido, tsoron wulakancin da za'amai yasa na kasa dawowa, sai dai tunanin raba d'a da mahaifi da kuma raba kaina da kai yasa na dawo."
Tunda ta fara magana yake kallanta yauce rana ta farko da ta saki jiki take mai magana haka, murmushi yai sannan yace " na fahimcike na kuma gode da kika dawo gareni baki bari na mutu banga d'ana ba."
Shiru suka d'anyi kafin yace " ku zauna anan in har kina ganin zaman can zai ma d'ana wahala."
A ranta tace da kenan, yanzu in har na zauna anan wayasan me zasumin a bayan idanka?ai in kana tsoron kura ba inda yafi maka saukin zama irin raminta, domin duk abinta bazata taba kawo akwai wanda ya isa shigar mata rami ba bare tai farauta a ramin nata.
Murmushi tamai sannan tace " a'a nafisan zamana kusa da kai sannan in na zauna anan yaushe Abu Turab zai dinga ganinka? Sannan in akaji labarin zamana anan baka gani xai jawo ma da ni kaina matsala?
Kallanta yai yana kara mamakin yanda ta canza.........
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
*15*
Mai Martaba ya juya ya kara kallan d'an nasa zuciyarsa a raunane, ba shakka kam d'ansa na bukatar kulawa ji yake kamar laifinsa ne yasa yaron ya makance.
Basira ganin yanda yake kallan d'an nasa yasa tace " Ba laifinka bane, kaddararsa ce babu makawa sai hakan ya faru ko da kuwa a gunka muke."
Kai ya jinjina cikin tausayawa, tai murmushi tace " ka koma tun kafin mutane su farga da rashinka."
Yace " haka ne, kiyi hakuri zuwa wasu 'yan kwanaki zan san yanda zanyi ku dawo ba tare da mutane sunyi zargin komai ba."
Ta lumshe ido sannan ta murmusa tace " na yarda dakai."
Mikewa yai a hankali yaje kusa da d'ansa ya rungumeshi kam sannan yace "sai da safe d'ana."
Abu Turab ya d'aga kai.
Haka ya fito tana bayansa, a tsakar gida taga Barde nan ya gaidata sannan ta juya ciki, su kuma suka tafi.
Abu Turab ya matso inda take idanunsa fal kwalla sai dai ya rasa mai zaice, ya kuma rasa dalilin jin yana san yai kuka, kallansa tai tace " me kake shirin yi?"
Yad'iye kukan yai sannan yace " bakomai."
Ta mike ta wuceshi ta nufi cikin d'aki, zama yai dabas yanzu yana ganin mahaifinsa ba dama yace ya ganshi?
Shikam ya kasa gane mai mahaifiyarsa take nufi da hakan.
*********
Sarki ya kasa bacci sam sai juyi yake akan gadonsa, tayaya zai b'ulowa mutane da matansa? Mai zai fada wanda mutane bazasuyi zargi da korafi ba akan matarsa da d'ansa? Sam ya rasa amsar tambayarsa sai juyi kawai yakeyi.
*********
Washegari da sassafe sarki yasa bafaden nan nasa ya tuko mota ya kawo musu kayan abinci sosai, duk wani abun bukata ya kawo musu sannan ya aiko da kudi akan a siyoma Abu Turab kaya da wasu abubuwan bukata.
Wajen karfe 10 suka shirya itada Lantana da Abu Turab suka fito dan zuwa kasuwa siyo kaya.
Suna tafe suna 'yar hira itada Lantana jikin wani shago ya tsaya dan shi sam bayasan shiga mutane da alama hakan ya faru ne saboda inda ya taso.
Yana wajen shagon su kuma sun shiga ciki, kallan wata kantanga yake wacce akai mata zane da wasu rubutu wanda bai taba gani ba, ido ya kurama rubutun yanasan sanin namenene?
Wasu yara ne su uku suka fito daga ciki sanye da fararen kaya riga da wando da hijabi, basu wuce shekara 5 ba, su biyu ne mata d'ayan kuma namiji ne.
An tashi tara.
Suna tafe kamar masifa biyun babbar macen da namijin, d'ayar wace take karama itakuma da alama kuka takeyi, kura musu ido yai yana neman amsar tambayarsa, daga ina suke hakan?
Wata ce yaga ta fito da gudu 'yar karama bata wuce shekara hud'u ba, daga inda suka fito tazo ta d'akama babbar cikinsu duka ta kara zurawa da gudu, inda yake tsaye take yowa mamaki ya kamashi ya tsaya yana kallan ikon Allah, yana nan tsaye yaga tana nufoshi shi dai bai matsa ba sai kallan ikon Allah yake.
Da gudunta kuwa ta cigaba, kai ya girgiza ya juya ya kalli inda Mahaifiyarsa take, yana juyawa yaji an wani irin hankad'eshi iya karfinta, dukansu suka fad'i a kasa tim, shikam ya fita jinjiki dan sar da hannunsa na hagu ya kurje, cikin fad'a ya d'ago dan ya mata magana, mamaki ne ya kamashi ganin ko a jikinta kad'e jikinta tai tana shirin kara sa wani gudun.
Da karfi yasa hannu ya fizgo hijab d'inta ya dawo da ita inda yake.
Kallansa tai sannan ta kalli wacce ta daka tace " dan Allah yahkuri ka sakeni karta kamani."
A ransa yace wasa kike yarinya, saurin kauda kansa yai daga kallanta sannan yace " malama bakya gani ne?"
Kallansa tai taga yasa hannu yana neman gefenta yana jujuyawa kamar irin neman inda fuskarta take yakeyi.
Kusa da fuskarsa ta matsa ta kalleshi sannan ta mai gwallo, ganin baice komai ba yasa tasa hannu ta toshe baki tana dariya wato da alama baya gani.
Hannu tasa ta fara kokarin zare hijab dinta alamar zata cire hijab din ta gudu ta barshi, jitai ance " me ya faru Abu Turab?"
Kallan matar datai magana tai ta ciji leb'e cikin takaici ga waccan ta karaso daf, ganin yana neman sanar da matar yasa ta fizge hijab dinta iya karfinta, ta sakar mai gwalo tace "makaho kaje ka nemo sanda."
ta kara falawa da gudu kamar zata kifa.
Juyawa yai yana kallanta cikin takaici, yanaji d'ayar tana binta tana cewa " Mariya wlh ko me zakiyi sai na rama gwarama ki tsaya."
Daga can itama ta juyo ta jefo mata dutse tace " ki kamani in kinada karfi."
Yaja tsaki yace " Umma amma waccan batada hankali, bigeni fa tai kiga yanda naji ciwo amma ko hakuri bataban ba." yakarasa maganar yana nuna hannunsa.
Basira ta matso ta duba hannunsa tace " da alama daga makarantar boko suke amma wannan yarinyar kwai fitinaniya, kaga yanda taketa gudu ko ajikinta?"
Abu turab yai kwafa ahankali yace " Allah yasa inganta watarana."
Basira tace " me kace?"
Kai ya girgiza yace bakomai.
Lantana tace " inba dan yanayi ba inama ta isa ta ganka a haka? Bare har ta tureka?"
Basira tace " muje nikam."
Sun gama siyayarsu sannan suka koma gida, Abu Turab sai dayaga sunyi salla sunci abinci sannan yace " Umma menene boko?"
Tace " makarantace da ake koya karatu, menene?"
Kai ya girgiza alamar ba komai.
Kallansa ta sakeyi tai murmushin dan ta fahimci abinda yake nufi.
A waccan lokacin ba kowa bane ya damu da karatun, yawanci zakaga yara ba zuwa suke ba, wasu kuwa iyayensu ne malaman makarantar, wasu kuma turasu ake bawai dan sai sunyi karatun ba.
*********
Magajiya zaune a kilisarta tanacin inibi, gefenta d'antane Yarima yana zaune kusa da ita shima yanacin ayaba, ta kalleshi sannan ta kalli Jakadiya dake zaune tace " jiya ina Mai Martaba yaje?"
Jakadiya tace " ba inda yaje."
Wani kallo Magajiya ta mata tace " me kikeso kice?karya na miki ko me?"
Dasauri ta rusunnar da kai tace " tuba nake Magajiya ni kaina bansani ba daga gun sallah ne bai dawo ba."
Ta bud'e baki zatai magana wata yarinya yar shekara hud'u ce ta shigo da gudu ta zo ta fad'a jikin Magajiya.
Fara'a ce ta karfafa a fuskarta ta d'agota tace "wa nake gani haka kamar uwata?"
Yarinyar ta d'ago tana murmushi tace " nice Aunty."
Kallan d'an Auntyn nata tai wanda ke zaune ko kallanta baiyi ba, ta taboshi tace " Yaya bakaganni bane?" Kallanta yai yace " Yaushe zaki girma ne Khadija? Sai ki dinga gudu kamar wata....."
Magajiya ce ta katseshi tace " a mata afuwa Yarima yarinya ce, sannan na tabbata inta ganni ne take haka ko Uwata?"
Baki ta turo sannan ta d'aga kai.
Magajiya na tsananin san Khadija wacce take 'yace ga Hisham, wanda yanzu 'ya'yansa hud'u itace ta uku, duk da dai 'ya'yansa a matsayin uku suke tunda ba wanda yasan Abdulmajid d'ansa ne.
Har mamaki mutane suke yanda ta sakar ma yarinyar fuska, ko dan sunan mahaifiyarsu ne?
Haka ta sa Khadija a kusa da ita tana tambayarta 'yan gida da karatun ta.
Jakadiya kam ganin haka yasa ta samu ta sulale dan itakam taji dadin ganin Khadija.
************
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
*16*
Yau da sassafe kafin Mai Martaba ya tafi bada a aika a kira masa Magajiya.
Zama tai irin yanda ta saba sannan ta kalleshi, ba sai an fada mata ba ta fahimci magana yakesan yi mai mahimmanci.
Ya dade baice komai ba kafin ya ja numfashi yace " Magana nakeso muyi, ko ince abu nakesan fada miki."
Kallansa tai sannan ta maida kanta inda take kallo da.
Sarki ya nisa yace " akwai abinda na b'oye miki ko ince akwai abinda ya kasance sirri na ne da ba wanda ya sani."
Bata juyo ba dan bata taba kawo wani abu ne babba ba, Sarki yacigaba " Matata da d'ana zan maido gidan nan zuwa gobe."
Da sauri ta juyo ta kalleshi tana mamakin kalamansa dan sam bata fahimci ina ya dosa bama.
Sarki ya cigaba da cewa "Matata da ke zaune a cikin gari d'aya daga cikin gidajena, uzuri ne yasa take zaune acan saboda d'an data haifa ya kasance yanada lalura, wanda hakan yasa ta naimi zama acan dan ta kula dashi, ba wai dan tana tunanin nan din bazai samu kulawa ba a'a sai dan lalurar tasa babbace wacce take bukatar kulawa."
Tunda ya fara maganar take bin bakinsa da kallo dan ta kasa aminta da abinda kunnenta ke ji.
Daurewa tai tace " aure kai bamu sani ko me? Nifa na kasa fahimtar inda ka dosa."
Kallanta yai yace " Basira nake nufi da d'ana Abu Turab wanda suke gidana shekara bakwai kenan."
"me kace? Basira da d'anta?sannan suna zaune a gidanka shekara bakwai? Takawa mai kake san cewa ne?"
Mikewa yai yace " ana jira na a fada, sannan na tabbata zakiji abin banbarakwai sai dai gaskiyar kenan." kasa magana tai saboda tsananin mamaki, tana kallo ya juya ya fita.
Shikam ya sani in har ya mata lago lago tabbas sai ta bulomai da wani abun.
Ta dade a zaune kafin Ta mike tai bangarenta.
D'aki ta shiga ta rufe, tafiya ta dinga yi a d'akin cikin tashin hankali, me ke faruwa? Meke faruwa?
Ta dade kafin ta aika a kira mata Hisham.
Hisham kam ya taho ko a jikinsa dan dama yanasan ya mata magana akan a nad'a dansa matsayin Yarima mai jiran gado sai kuma ta aika a kirashi.
B'angaren d'ansa ya fara zuwa, yana shiga yaji alamar fasa abu, da sauri ya shiga ciki hankali a tashe.
Abdulmajid ya gani a zaune ga bayinsa sunsa gwiwowunsu a kasa suna bashi hakuri, a hasale Abdulmajid ya kallesu yace " ba nace banasan a kawomin ruwa a irin wannan kopin ba?"
Hakuri suke bashi hankalinsu a tashe, ya wani juya kai irin ba saukin nan yace " bazai yiwu ba Ummana zan sanarwa ta d'au mataki a kanku."
Nan suka shiga rokonsa, Hisham yai dariya ya juya ya fita yana jinjina kai, murmushi ya saki yace " haka akeso ai, gwara ya nuna musu a kasan sa suke hakan zaisa inya zama Sarki a dinga tsoronsa."
A zaune ya tadda Magajiya sai dai kana kallanta kasan tana cikin tashin hankali, nan Hisham ya d'an tabe baki kadan yace "wa ya tabo wannan zakanyar?"
Kusa da ita ya karasa ya zauna yace " Magajiya menene?"
Ta kalleshi cikin tashin hankali sannan ta bada umarni a basu guri, kallanta yai sannan yai dan dariya yace " menene? Khadija tace a gaisheki."
Hucci ta saki tace "ina amsawa amma ba wannan bane a gaba yanzu, kasan Basira ta dawo kuwa? Ko ince wai ashe tana nan?"
Kallanta yai yace "Basira? Wa ke........" ido ya zari sakamakom tunowa dayai yace " Basira dai?"
Ido ta runtse tace " ita mana, ba ita kadai ba ma harda danta."
Mikewa Hisham yai da sauri yace " ban gane ba? Basira tana nan a ina?"
Magajiya ta kwashe komai ta fada mai, shiru yai sannan ya zauna a kasa dabas ya dafe kai cikin tashin hankali.
Magajiya ta kalleshi tace " naji maganar Mai Martaba sai dai ban yarda da duk abinda ya fada ba."
Hisham yace "ban......"
Tace " kana tunanin Basira tana garin nan shekara bakwai amma sarki bai nuna alama ta zargin haka ba? Ko na fita? Ko na aika abinci ko wani sako?"
Hisham ya kalleta yace " haka ne kuma."
Magajiya tai wani murmushin takaici tace " kwanan nan ta dawo."
"kwanan nan?"
Tace " haka zuciya ta da kwakwalwata ke sanar dani, nasan hali Takawa, nasan yanda yakesan Basira da abin cikinta, na tabbata bazai taba kyalesu ba batare da ya dinga binsu ba."
Hisham yace " gaskiya ne,to yanzu meye nafita?"
Tace "nayi tunani sosai bayan naji abinda yace sai dai nasan babu abinda zamu iya yi, na farko bazamu sa ta koma ba sannan ba zamu kashe danta ba, sai dai akwai kafita."
Hisham ya kara matsowa, Magajiya tace " da farko mu nuna masa ba komai, sai dai ni zan sanar dashi akan in har yanaso in nuna dawowar matarsa ba komai bane har sai ya amince da bukatata."
Hisham yace "kina ganin zai yarda?"
Tai wani murmushi tace " yafi kowa sanin in na tsani matarsa zaman gidan nan gagararta zaiyi hakan zaisa ya yarda."
Hisham ya kata jinjina yace " haka ne, amma meye bukatar taki?"
Tace " ya rubutamin alkawari akan ba mai gadar sarautarsa sai Abdulmajin wato d'ana."
Hisham ya washe baki yace "kai Magajiya da ke namiji ce tabbas da kin taimaki kasar nan da kwakwalwarki."
Kai ta juya tace " sannan basai na damu da d'anta ba tunda yace min yanada lalura duk da banmasan lalurar menene ba."
Hisham yace "lalura?"
Ta tabe baki tace "oho musu sai dai dolene muyi amfani da dawowar yarinyar nan mu amshi takarda a hannun sarki.
Murmushi sukai na farincikin ganin sun warware matsalarsu....
_Nikam nace hmm ba giringirin ba dai........_
**********
Mai Martaba ya sanar a fada akan dawowar matarsa da kuma zamansu a can, mutane dayawa sunyi mamakin wannan al'amari da kuma san suji lalurar d'an nasa.
Sannan ya aikama Basira akan su shirya dan kuwa gobe ne ranar komawarsu.
*********
Basira yau tace Abu Turab yazo su kwanta tare a kan gado, sun kwanta shiru, ta kamo hannunsa tace " yauce rana ta karshe da zamu kwanta tare duk dadai mun dade bamu kwana tare ba."
"dolene ka zamanto mai kauda kai sannan mai gudun rigima in ka koma gidan mahaifinka, zakaga mutane kala kala masu hali daban daban sai dai fatana ka nutsu ka karanci ko wani hali na d'an adam din daka gani."
Kai ya d'aga mata alamar to, tai mumushi tace " kada ka kuskura ka nuna ma mutane kana gani, wannan alkawarinmu ne wanda nakeso ka rike har sai sanda nace ma ka nuna musu."
Ya kara d'aga kai, tace " zan zamo mai zafi a gareka, zan ki bin bayanka, zan ki nuna ma kulawa, sannan zan nuna rashin damuwata akanka sai dai inaso kasani hakan gata ne wanda zanma, a yanzu bazaka fahimta ba sai dai nan gaba kai da kanka zaka fahimci dalilina nayin hakan."
Abi Turab ya kalleta idanunsa sunyi raurau, ba komai yake fahimta ba a kalamanta saboda yarinta sai dai ya san abu d'aya tana nufin akwai dalili dazaisa ta daina nuna mai kulawa.
Kallansa tai, batai magana ba yai saurin had'iye kukansa, daurewa yai yace " nikam banasan gidan."
Kansa ta shafa tace " Allah ya albarkaci rayuwarka ya karemin kai, wannan itace addu'ata a ko da yaushe."
Shirun da sukai ne yasa bacci yai gaba dashi, ta dade tana kallansa zuciyarta na tsananin tausayama rayuwarsa.
_nikaina tausaya d'an yaron nan nake cewar Kanwata Yar Fara(Meema White)....Lol_😅
*#TEAM ABUTURAB 🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🤸🏼*
*17*
Itama Magajiya a daren ta shirya taje ta samu mai martaba da nata sharad'in, yayi mamaki kwarai dajin wannan zancen, ya kalleta harzaiyi magana sai ya fasa yace " shikenan ya amince, hakan datai ya nuna masa lalai ba zaman amana take dashi ba haka kuma ta nuna d'ansa ba nata bane."
Magajiya ta juya kai bata ce komai ba dan itakam a yanzu abu d'aya kawai ta sani wato ta tabbatar ta d'aura d'anta a mulki ba komai ba.
Haka mai martaba ya rubuta mata a takarda ya kalleta cikin takaici sannan yace "na dauka na sanar dake d'ana yana da lalura?"
Bata amsa mai ba ta dai amshi takardar hannunsa sannan tai murmushi tace " ba wai rashin yarda ne ko rashin san d'anka bane yasani yin haka sai dai nayi haka ne saboda kauda matsala dazata iya afkuwa nan gaba, me zai faru idan nan gaba ka tara 'ya'ya anzo ana takara da kishi akan mulki? Amma kaga in har mun riga mun tsaida babban d'a a matsayin magajinka banaji wata babbar matsala zata faru."
Kallan yai cikin mamaki duk da dai maganarta ba karya bane sai dai yana ganin sankai da san mulkinta ne yasata yin haka, yafi kowa saninta ya san abinda take tunani, tana tsoro kar nan gaba yaron ya warke in fara tunanin sashi a mulki.
Sallama tamai ta fita.
************
Washegari wajen sha biyun rana aka turo da mota dazata daukesu.
Kofar gidan sarauta aka bud'e, Abu Turab ya kurama kofar ido yana kallo, gannin tsari da girman gidan yasa ya shiga kalle kalle, mamaki yakeyi duk wannan katan gidan na mahaifinsa ne?
Basira ce ta tabashi, ya juyo ya kalleta hararar sa tai sannan ta nuna mai sandarsa, da sauri yai kasa da kansa sannan ya d'auki sandar.
Sun sauka Lantana ta kama hannunsa suka nufi b'angaren da wata baiwa tazo dan nuna musu.
Ba b'angaren ta na da bane wannan yafi girma saboda an warema Abu Turab nasa bangaren.
Haka akai ta zuwa ana gaidasu wasu gaisuwa sukazo, wasu kuwa gulma sukazo, wasu kuwa so suke suga lalurar da yaron ke dashi.
Kafin kace me? Zance ya baza gidan akan Abu Turab makaho ne.
Abdulmajid kam yana gun Magajiya tana kara huremai kunne akan karya kuskura ya bari yaron nan ya rainashi, dan nan gaba baisan mai zai zamar masa ba.
Sun dade a d'akin kafin tace ya tashi ya koma bangarensa.
Abdulmajid nada tsananin kishi, jin akwai wani d'a bayanshi a gun Mai Martaba yasa ransa ya bace, kallan masu kula dashi yai yace " muje in ga kanin nawa."
Haka ya taho dan ya matso yaga kanin nasa da sam baya farin cikin kasancewarsa, sannan yanasan yagani in da gaske baya ganin.
*******
Abu Turab na xaune aka dinga shigowa da kaya, sai dai ba dama ya nuna yana gani, kansa ya kawar gefe yana wasa da hannunsa, sun ajiye kaya dayawa daga na sawa, takalma da sauransu, sannan suka gaidashi.
Juyowa yai inda suke ya amsa tare da cewa "su waye?"
"Mai Martaba ne ya aikomu mukawoma kayan sawa, sannan ga abinci kala kala ya sa a girkama, yace a sanar dakai xai turo anjima a kaika gunsa."
Abdulmajid wanda ke tsaye dan ya shigo kenan yaga ana shiga da kaya yasa ya bisu, wani mugun kishi da tsanar yaron ne ya turnukeshi.
Abi Turab ya saki fuska yace " nagode kwarai."
Wasu kaya aka ajiye a kusa dashi, sannan wanda ya ajiye yace "wannan zaka sa in zakaje gunsa dan a fada yakesan nunaka."
Kai ya daga alamar to, sannan suka juya suka fita.
Abdulmajid ya juya ya juya ya kalli bawansa yace " akwai almakashi?"
Mamaki ya kamashi sai dai batare da ya tambaya ba yace "akwai amma sai gun soro."
Yace " yi gudu maza ka amson."
Nan ya fita da gudu.
Shiga ciki yai ya tsaya a gaban Abu Turab, Lantana ta gaisheshi.
Kallanta yai sannan yace " bamu guri."
Hanyar waje ta nufa gabanta na faduwa, shi kuma Abu Turab ya mike ya mika mai hannu dan su gaisa duk da ba saitinshi ya mika ba, sannan yace " sunana Abu Turab."
Dariya Abdulmajid yai yace " ta ina zamu gaisa bayan ba gani kake ba? Sannan ni yayanka ne baka gani rusunawa ya kamata kayi?"
Abu Turab ya dan kalleshi kad'an sannan ya juya kai baice komai ba.
Shigowar bawansa ne yasa ya juyo ya mikamai hannu yasamai almakashin, rigar da aka kawo dan ya saka ya dago ya sa almakashin ya yanka bayanta takai har wajen wuya sannan ya ajiye ya kalli Abu Turab yace " ungo kayanka saka ni ne wanda zan rakaka gun Mai martaba."
Abu Turab yana kalan mai yai sai dai ba yanda zaiyi, ya kalli Abdulmajid yace "amma karar me naji?"
Kallansa yai a wulakance yace "abu na cire a rigata."
Abu Turab ya runtse ido, yana tunanin yanda zaiyi, in ya nuna ya sani alama ce ta yana gani kenan.
Haka ya amshi kayan ya
kankama a jikinsa bayan yasan duk bayansa a waje yake.
Abu Turab ya kalleshi yace " Amma ance turowa za'ai inje ai."
Abdulmajid ya kalli Bawansa yace "ga wanda aka aiko nan, sannan cewa akai in kaika."
Fitowa yai rike da sandarsa, Abdulmajid na gaba shikuma yana baya, masu kula da Abdulmajid na bayansu.
Tunda suka fito ake kallansa ana dariya, lalai wannan ba makanta bane kadai a kansa akwai alama ta hauka.
Shikanshi Abdulmajid sai dariya yakeyi sam baisan abin zai kayatar dashi haka ba, shidai kawai yayi ne saboda yasa amai dariya a fada bai dauka tun a hanua za'a fara ba.
Sai da sukaje kofar shiga fadar, ya kalleshi yace "shiga."
Abu Turab idanunsa suka kada sukai jaa, jiyake kamar ya sa ihu, mahaifiyarsa ya tuno da kuma kashaidinta akan idanunsa.
Haryaje shiga ya tsaya
Shi mamakinsa mai ya mai? Daga zuwansa ko awa biyu cikakke baiyiba ace harzai mai haka? To shi mai yayi?
Daga bakin kofa akace " Bawan Allah ya akai?"
Abu Turab ya juya zai bargun da gudu, nan fa akaga bayansa.
Barde cikin mamaki dan dashi akaje daukosu yasan yaran ya kalleshi yace "Ba......."
Shiru yai ganin yanda rigarsa ta baya take.
Dariya aka shiga guntsewa ganin kayansa kowa ya tabbatar d'an sarki ne.
Abu Turab duk ya rikice garin gudu ya fadi a kasa, hannayensa ne suka kurje, jiyai idanunsa sun ciciko, fadan mahaifiyarsa na ragonta ya tuna hakan yasa ya hadiye kukan ya mike jiki a sanyaye ya daina gudu, sandarsa ya rike kam yana tafe.
Yana fitowa daga fadar, Lantana ta taho da gudu dan labari ya kaimusu ga Abdulmajid can da Abu Turab suna tafe zuwa fada amma shi Abu Turab rigarsa ta baya a yage take sosai.
Lantana tunda ta ganshi hawaye yake zubo mata, yaron daya taso a kauyen kayau hankalinsa a kwance yau gashi daga dawowarsa gidan mahaifinsa an maidashi shashasha.
Hannunsa ta kama ta rufa mata babban kyallen data d'auko tana hawaye.
Kallanta yai sai dai jiyake kamar taimaka mai tai wajen yin kukan dashi yakesan yi.
Basira kam tun da aka fada mata take zaune ko motsi ta kasa yi, hannayenta kawai ta matse kam.
Abu Turab na shigowa ta shige d'aki da sauri, bayan ta ya kalla ya bita da gudu.
Yana kokarin shiga yaga ta rufo kofa.
Zama yai a bakin kofar.
Hakoransa ne suka shiga kadawa, sanyi ya fara kamashi.
Yana nan a zaune bacci ya daukeshi, wani zazzafan zazzabi ne ya kamashi.
*******
Magajiya kam jin abinda ya faru yasa ta cikin wani farinciki ba shakka lalai d'a dole ya gaji ubansa, bayan Hisham ga ta ai dolene Abdulmajid yai gadon makirci Da kissa.
Dadi ne ya kamata sai murmushi take.
Jin wannan labari yasa Hisham cikin farin ciki, shida Magajiya sunyi dariya sosai sun kuma yaba kwazon d'an nasu da alama in ya girma abinda zaiyi ba wanda zai iya tunani.
Hisham sai kara wasa Magajiya yake yanacewa "ai kwakwalwa da kwazonta ne ya gado yo dama kaza bazatai gudu d'anta yai rarrafe ba...."
Dadi sai kara kamata yake.
Da alama basai ta taimaki d'an nata ba, komawa zatai ta zauna ta dinga ganin yanda Abu Turab zai kasance gun Abdulmajid........
nαcє hmmmmmmmm....
*ⓐⓑⓤ ⓣⓤⓡⓐⓑ ⓣⓔⓐⓜ🤝🏼*
************
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
*18*
Lantana ce ta zo ta daukeshi tai b'angarenshi dashi, akan gado ta kwantar dashi har lokacin bata daina zubar da hawaye ba, bargo yaja ya luluba ita kuma ta mike ta fito.
A tsaye ta taradda Basira, kusa da ita taje ta tsaya ba tare da tace komai ba.
Basira ta juyo tace " yana ina?"
"nakaishi d'aki." ta fad'a tare da kara share kwalla, Basira ta had'iyi wani yawo na takaici sannan tace " ki amso mai magani yasha."
Tace to, sannan ta juya ta fita.
*********
Mai Martaba kam ana la'asar ya kalli Barde yace " a aika a kira Abu Turab."
Barde ya kalleshi jiki a sanyaye yace " Takawa kayi min afuwa amma ina ganin ka bari sai zuwa wata rana sannan a nunashi a fada." a hankali yai maganar.
Mai Martaba yasan halin Barde tunda ya fadi haka da alama akwai wani kwakwaran dalili, hakan yasa bai sake magana ba.
Ana tashi daga fada ya tambayi Barde abinda ke faruwa.
Barde ya nisa yace " bansan nikaina takamaimai menene ba sai dai naganshi ya taho gunka sai kuma ya juya."
Cikin mamaki Mai Martaba yace " ban gane ba?"
Nan Barde ya sanar dashi abinda ya gani.
Hankalin Mai Martaba ne ya tashi sosai nan ya juya afusace yai bangaren d'an nasa.
Bai jira Zagi ya isar da zuwansa ba ya fada ciki da sauri.
D'akinsa ya nufa ya bud'e, a dukunkune ya ganshi cikin bargo, da sauri ya karasa gunsa ya d'agoshi.
Jikinsa zafi rau wanda hakan ya kara tadamai hankali, ya kalli Abu Turab wanda idanunsa sai lumshewa suke, yace " Menene? Waye ya tabaminkai? Har yajama zazzabi?"
Kai Abu turab ya girgiza alamar bakowa.
Fuskarsa yace " bayin dana aiko da kayanka sune suka baka yagagge ko akwai wani abun?"
Abu Turab jiyai wani kuka yazo mai, baisan sanda yasa kuka ba, kuka ya shigayi sosai.
Mai Martaba ya rungumeshi tsam a jikinsa hankalinsa a tashe.
Abu Turab ya dade yana kukan sannan ya share hawayensa cikin murya mai raunin gaske yace " kayi hakuri na tadama hankali daga zuwana."
D'ago dashi yai ya kalleshi yace " ni zan baka hakuri na rashin kula da abinda ke faruwa dakai."
Abu Turab ya share kwalla baice komai ba.
Yana zaune kusa dashi har bacci ya dauke d'an nasa sannan ya mike ya fito.
Bangaren Basira ya shiga, zaune ya ganta tana cin abinci.
Sai daya zauna sannan ya kalleta yace " Abu Turab yaci abinci ne?"
Murmushi tai tace "in bashida lafiya bayacin abinci dan ko yaci zai dawo dashi."
Ya kalleta ya kalli yanda takecin abinci yace " Basira mai ya sameshi? Ance ya sa kaya bayan rigar a yage."
Abincin hannunta ta ajiye dan dama ci kawai takeyi, ta kalleshi tace " bansan me ya faru ba nima na dai san bashida lafiya."
Ido ya kura mata, tai saurin kauda kanta gefe, yace " wanene yamai haka? Na tabbata kinsani."
Ta dan kalleshi kadan tace " shi bai fadama ba?"
Yace "yace bakowa."
Murmushi tai najin dadin yanda dan nata yace bakowa, tace " tunda yacema bakowa hakan ne, koma ba hakan bane alama ce ta bayasan kasani."
Shiru yai, sannan ya kalleta yace " komai yayi daidai? Na gida nake nufi."
Kai ta d'aga tace " komai yayi daidai sai dai inaso ka bani dama na wani abu."
. Ya kalleta bai ce komai ba.
Tacigaba da cewa " so nake Lantana ta koma gun Abu Turab sannan inaso ka taimaken akan barinta ita kadai ta kula dashi banasan abashi bayi dayawa."
Mamaki ya kamashi yace " me kike fada haka! D'an nawa da bashida lafiya kikeso invar lantana kadai ta kula dashi?"
Tace" rokon ka nake akan hakan inya tasa lokacin sai ta dawo nan, ya saba da ita da ita kadai yakejin dadin zama."
Shiru yai baice komai ba, ita kuwa tana tsoron kar a turamai mutane ya zama harda mutanen Magajiya kada kuma tsautsayi yasa ya nuna yana gani tunda dai yaro ne.
Ta kalleshi tace " sannan yana san karatun boko."
Mai Martaba yai murmushi yace " akwai mai koyama Abdulmajid da 'ya'yan kanina da na galadima karatu a cikin gida, inyaso sai ya dinga zuwa."
Tai murmushi tace " nagode Takawa."
Kallanta ya sakeyi yace "amma kina ganin zai iya karatu cikin yara masu gani shida yake makaho?"
Tace " zai iya, kuma hakan zaisa su fuskanci juna da 'yan uwansa."
Kai ya jinjina alamar gamsuwa.
********
Washegari.
Da gudu ta shigo bangaren Magajiya, tana zuwa cikin zumudi tace " Umma ina kanin Ya Abdulmajid d'in?"
Abdulmajid ya maka mata harara yace " khadija me yasa bakida hankali ne? Ba na hanaki yima mutane gudu ba? Kina mace?"
Baki ta murguda kadan sannan ta kalli Magajiya ta shagwabe fuska tana neman yin kuka.
Tace "Umma kinga Ya Abdulmajid ko?"
Abdulmajid haushi ya kara kamashi, yace "banace karki kara cemin Ya Abdulmajid ba?"
Kuka ta saka sosai, Magajiya ta janyota jikinta tana lalashi.
Abdulmajid ya kalli Magajiya yace "Umma duk ke kika b'ata yarinyarnan."
Khadija ta d'ago daga jikin magajiya tace "Umma ina kanin ya....."
Sai kuma tai shiru.
Magajiya tai dariya yace "Abdulmajid kadaina zafafa mata."
Itakam ganin anki fada mata yasa tai waje da sauri.
Baiwar bangaren Magajiya ta samu tace "kaini gun yaron dayazo jiya."
Nan ta dauketa tai bangaren Basira da ita.
Ta nuna mata bangaren yaron.
Da sauri tai ciki, Lantana ta gani a zaune tana ninke kaya, cikin zumudi tace " sannu, ina yayan da aka kawo jiya?"
Lantana ta mata kallan mamaki ganin bata santa ba.
Abu Turab ne ya fito daga d'aki bai kula da wani a gun ba yace " Lantana dan bani ruwa."
Jiyai anzo an rungumeshi kam.
A tsorace ya kalli kasansa.
Yarinya ce karama ya gani, cikin mamaki ya tureta yace " waye hakan?" ya fada kamar bai ganta ba.
Khadija tai dariya tace " nice nan 'yar gidan waziri, kaine yayan dayazo jiya ko?"
Kallanta yai kadan ya kauda kai yace " ni bansanki ba."
Dariya tai batace komai ba, itakam tun jiya ta matso ta ganshi.
Hannunsa ta kama tace "ai kai zaka dinga wasa dani ko? Bakaman ya Abdulmajid ba ko?"
Shiru yai baice mata komai ba, ta kara rike hannunsa tace " sunan ka Ya Turab ko?"
A hankali yace eh.
Dadi ya kamata tace " zanje gun karatu sai nazo gobe.
Nan tai waje da sauri.
Baisan sanda yadanyi murmushi ba.
Lantana ta kalleshi tana dariya tace " tunda kazo gidan nan sai yanzu naga fara'arka."
Ya kalleta yace " bani ruwa kishi nakeji."
Tai dariya ta mike, jikinsa ba karfi hakan yasa ya zauna.
**********
Jin labarin fara karatunsa agun Mai Martaba yasa Barde shima ya gurfana gaban Mai Martaba yace " Takawa nima inasan abani izini in dawo da yarinyata cikin gida dan daukar darasi."
Mai Martaba yace "ba da kace tanayi a waje ba?"
Barde yace " wlh Takawa yarinyar tawa ce kasan na fadama bataji sam, kullum ta fita makaranta sai an kawo kararta, ina ganin in anan take zatafi samun nutsuwa tunda ba wanda ta isa tsokana ganin darajar mutanen da zatai karatun dasu."
Mai Martaba yadan murmusa yace " shikenan ka kawota, Mairo sunanta ko?"
Barde yace "eh Takawa, ina godiya Allah yaja kwana."
*********
*ⓐⓑⓤ ⓣⓤⓡⓐⓑ ⓣⓔⓐⓜ*🤝🏼
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🤸🏼*
*19*
Da yamma suka shirya ita da d'anta dan zuwa gaida Magajiya.
Duk inda sukai kallansu ake ana 'yan gulmace gulmace har suka isa b'angaren Magajiya.
Tana kilisarta itada d'anta, bayan an neman musu izini nan suka shiga,ta kama hannun Abu Turab sakamakon sakeshi da Lantana tai da zasi shiga.
Abu Turab ya sauke idansa akan hamshakiyar matar dake zaune ta kafe kofar da sazu shigo da ido.
Kallanta yai sannan ya kalli d'an nata dake gefe sai kuma yai kasa dakai.
Magajiya kam ta kafeshi da ido tunda suka shigo har suka isa suka zauna.
Ta rasa me yasa tana ganinshi taji gabanta yayi wani wawan fad'uwa, Basira ta kalla sai dai yanzu taga alamar ba tsoro da gidadanci a idanunta kamar waccan zuwan nata na da.
Zama sukai,Magajiya ta kara kallan yaron a ranta tace " sak Mai Martaba lalai naji dadi da Yakumbo ta taimaka wajen nakasa idan nan."
Gaisheta Basira tai, i
Bata amsa ba ta maida idanta gun yaron, ya d'ago suka hada ido da sauri ya kalli gefe yace "Barka da Yamma."
Tabbas tasan sun hada ido sai dai dayake zuciyarta na farin ciki da kasancewarsa makaho yasa ta kasa dogon nazari akan haka.
Abdulmajid kam ya had'e rai da alama bashida niyyar gaida Basira.
Sai da Magajiya tace "Yarima baka gansu bane?"
"Barka."
Abinda ya fada ma Basira kenan.
Murmushi tai ta kalli Abu Turab tace " Yarima bakaga yayanka bane?"
Wannan kalma ta ba Magajiya da Abdulmajid mamaki, yarima? Haryaushe yazo?kuma ma a gabansu?"
Abi Turab bai kalleshi ba yace "Barkanka dai Yarima."
Magajiya zatai magana, Basira tai saurin cewa " haba Abu Turab sai kace ba yayanka ba? Ai kai basai ka kirashi Yarima ba ko Magajiya?"
Ta karasa maganar tana kallan Magajiya.
Magajiya ta juya ido a ranta tace " lalai wai so kike ki nunamin kin kile ko me?"
Murmushi ta saki sannan tace " hakane abinda kika fada sai dai kinsan tsintaciyar mage bata mage."
Basira cikin mamaki tace "bangane ba?"
Magajiya tai wani nishi na kasaita tace " Dafatan muhallinku an sa komai da komai? Dan ina nan ina fama da al'amuran cikin gida ban samu naje ba."
Basira ta daure tace " komai yayi."
Shiru suka d'anyi Magajiya na kallan yaran, can tace " naji ance ka fita riga a yage jiya? Meke faruwa? Ko dayake laifinki ne kinsan yaran makaho ne bai kamata ki barshi shi kadai ba."
Basira ta kalleta kadan batai magana ba,BU turab yai saurin cewa " Laifinane dan batasan ma nafita ba."
Magajiya a hasale tace " kada ka kuskura in inamagana da mahaifiyarka kasamin baki, ko kaga Abdulmajid na haka? Wannan alama kake nunawa na kataso a wani gun daba Gidan sarauta ba."
Basira ta kalleshi tace " kada ka sake, sannan yi maza ka bata hakuri."
Shiru Abu Turab yai wanda hakan yasa Basira tai dana sanin cewa ya bada hakuri, tasan halin d'anta sarai inhar tace yai abu ya tsuke baki to fa lalai bazaiyi ba.
Magajiya ta kalleshi tana jiran ya bata hakuri sai dai jitai yayi gum.
Abdulmajid ya kalleshi yace "bakaji me aka ceba?cewa akai ka bada hakuri."
Abu Turab aya dan juyar dakai saitin Abdulmajid yace " bansan laifin me nai ba."
Wannan kalma tasa ta basu mamaki sosai, a zuciye Abdulmajid yace "bakasan me kai ba? To me ya damemu? Kayi laifi dan haka bada hakuri ya zama dole."
Kasa ya maida kansa yai shiru, Basira tadan tabo hannunshi nan ma shiru, Magajiya tai wata dariya kadan ta takaici tace " kai? Nice magajiya gimbiyar sarki, sannan nice a matsayin mahaifiyarka babba dole ne kabi abinda nakeso ka kuma guji abinda banaso."
Abu Turab baiyi magana ba, Basira ta kwallama lantana kira tace " Lantana samo bulala."
Lantana ta kalli Uban gidan nata cikin tausayawa sai dai ya zatayi? Haka ta fita ta samu bulala na bishiyar maina.
Basira ta kalleshi yace mike, Abu Turab ba musu ya mike, ya d'aga kasan wandonsa dan yasa nan zata daka, zata fara dukansa Magajiya tace " Basira meye hakan?
Dan d'ana yamin laifi ai hakkinane in hukuntashi bake ba."
Basira ta tsaya sai dai a ranta tana addu'a Allah yasa kar tace ita zata hukuntashi.
Magajiya ta kalli Abu Turab tace "yi zamanka kaji d'ana." tai maganar fuskarta a sake.
Gani tai Abu Turab yaki komawa ya zauna, kallan mamaki tamai gani tai kansa na kasa kusa da mahaifiyarsa.
Ya saba da hakan inyai laifi sai tace dakanta ya zauna.
Basira ta kalleshi tace " zauna mana." nan ya koma ya zauna, ba shakka wannan abun ya kuna ran Magajiya ya kuma kona ran d'anta, sai dai bata nuna ba har suka tafi, tana tunanin lalai dole ta saita d'an nan.
**********
Yau satinsu biyu a gidan, sam Abu Turab baya fita saboda gudun kar wani abu ya faru a gane idansa na gani, sam bayasan gidan, sai dai jefi jefi Khadija na zuwa gunsa tai tamai zuba, shi mamakinsa ma ko mahaifinsa baya gani dan tun daga wannan ranar bai sake sashi a ido ba.
Yau ce ranar dazai fara zuwa makaranta da safe yai wanka yasa kaya, Lantana ta kawomai abinci yaci sannan suka fita, Basira ta mai fada sosai kafin su wuce makarantar.
Sun kusa isa makarantar sukaji ance Lantana, nan ta juya jin muryar kawarta.
Kallan Abu Turab tai tace " dan Allah bari in mata magana."
Murmushi yai yace " jeki, ba can bane?"
Tace nan ne.
Sandarsa yasa a gaba ya fara tafiya yana d'an kale kale kadan kadan.
Yaje zai shiga yaji an bangajeshi dakarfi wanda sai daya sashi ya fad'i.
Hannunsa ya kalla yaga ya kurje, ya d'ago dan ganin waye, sai dai ga mamakinsa gani yai ta mike tana neman kara mai.
Hannu yasa da karfi ya fizgota.
Mairo ta juyo suka had'a ido, da sauri ya kauda kansa wato yarinyar nan ce ta rannan?
Itama ido ta kuramai tace "la kaine makahon nan ko?"
Abu Turab yace " meyasa bakida hankali? Bakiga bigeni kikai ba? Kike neman gudu baki ban hakuri ba?"
Dariya tazo mata ta toshe baki, jakar buhun dake hannunta wanda ya rike gam ta zare ta rike da hannunta, yana kallanta a ransa yace " wannan ba karamar fitinaniya bace."
Waige waige ta shiga yi nan taga khadija ta nufosu.
Alama ta mata da hannu akan tayi sauri, itakam ganin yayanta ne agun yasa takara sa sauri, tana zuwa kusa dagun zatai magana Mairo ta mata alama datai shiru.
Mamaki ya kamata ta karaso, alama ta mata da hannu akan ta rike mata jakarta, nan khadija ta rike tana san ganin me zatai.
Duk wannan abun da suke Abu Turab na kallansu shi dariya ma abin yake bashi lalai yarinta da ciwo, inba haka ba ko baya gani tana san tacemai bazai fahimci me takeyi ba?
Khadija na amsa ta shige ciki da gudu.
Da kallo ta bita, can tace " Ya Turab haka zamuyi ta zama anan?"
Murmushi yama Khadija yace "cilar da jakar ki shiga muje."
Nan ta yarda jakar sukai ciki.
Suna shiga suka zauna gu d'aya dayake lokacin da ne, akan tabirma suka zauna, can gefe kuma Abdulmajid ne zaune akan wata daduma mai kyau ya hard'e kafafu.
Khadija na zaune kusa da Abu Turab.
Mairo tazo ta baya ta tab'ata tace " jakata fa?"
Tace tana waje.
Waje kuma?yarmin kikai?
Khadija tace eh yayane yace in yar.
Baki ta murgud'ama Abu Turab tace "yayan naki da ba gani yake ba?"
Abu Turab ya kalli inda Khadija take, Mairo ta kalleshi tace " ni anya baka gani kuwa?"
Abu Turab ya juya kansa bai tanka ta ba, ta harareshi tare da murgud'a baki ta mike tai waje.
*********
Sosai yaji dadin yanda yake fahimtar karatun, dan daga anyi tambaya sai yaga yasan amsar, sai dai ba damar ya fada indai ba tambayarsa akai ba, saboda umarnine na mahaifiyarsa.
Abdulmajid in yaji ya bada amsa daidai sai yai dariya a ransa yace duk kokarinka dai baka isa yin rubutu ba saboda rashin ido, yana tsananin jin haushi yanda Khadija ke zama inda yake, sam ma tadaina kulashi iyakacinta dashi gaisuwa.
Wata shakuwa mai karfi ce ta shiga tsakanin Khadija da Abu Turab ko makaranta zata ita take zuwa ta rike hannunsa su tafi, in an tashi kuma sai ta rakashi sannan take tafiya.
Mairo kuwa da Abu Turab banda fada ba abinda ke had'asu, rigimarta tayi yawa da sam ko kusa dashi bayasan tazo, haka kawai indai taganshi azaune sai ta tsokaneshi.
Abdulmajid kam na tsananin kishin Abu Turab ganin yanda ko Mahaifinsu ke nuna mai kulawa da kuma yanda mutane ke sanshi, yasa san ya tsaneshi farincikinsa yaga yamai sharri, sai dai duk sharrin da yakemai cikin ikon Allah sai komai ya warware.
_Wannan kenan_
Haka rayuwa ta kasance musu sosai Abu Turab ke kokarin ganin ba wanda yasan yana gani, sannan baya shiga gun mutane saboda tsaro, Mahaifiyarsa tana kara tarbiyantar dashi da nunamai abinda ya dace da wanda bai dace ba.
Baya zuwa gun Magajiya akai akai, sannan in yaje gaisheta ma yana zuwa yake cewa zai tafi in kuwa ta hanashi tahowa haka zai zauna gum, sosai ya fahimci matar fuska biyu gareta.
Haka ya taso cikin tarbiyya mai tsauri, haka ya taso cikin sanin halayen mutanen gidan, ya kuma fahimci lalai mahaifiyarsa gata tamai, ko daga yanda mutane suke mai kallan tsana sun dauka baya gani, sharrin da ake mai da kuma nuna halin ko in kula akansa.
Mutum d'ayace yake zama da ita yaji dadi, daga mahaifiyarsa da Lantana sai kuwa Khadija.
*TEAM ABU TURAB🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*_Gaisuwa Gareki Fatity, Meela Adeel, Rasheeda, Zaliha, Safeena, wannan shafin sadaukarwace gareku._*
*20*
Ganin irin tsananin shakuwar da ta shiga tsakanin Turab da Khadija yasa hankalin Magajiya ya fara tashi, ga yanda take tsananin san yarinyar, Hisham tasa aka kira ta umarceshi akan ya maida Khadija kano gun 'yan uwan mahaifiyarta, a lokacin Khadija nada shekara 10, sai tazo gidan sau nawa amma ko b'angaren Magajiya wani sa'in harta fita bazata ba, Hisham ma ya aminta da hakan dan kuwa shikansa abin ya fara damunsa jin komai a gida zancenta kenan Ya Turab.
A ranar da za'a tafi da ita ma tazo gun yayan nata tana ta sashi magana, dan dama kaf gidan ita kadai ce mai sashi yai ta magana, suna cikin hirarsu aka turo tazo Mamanta na nemanta, mikewa tai cikin sauri dan ko d'ankwalinta bata d'aura ba kawai ta sa hijab dinta ta fita, hartaje kofa Turab yace " Khadija."
Juyowa tai cikin fara'a, murmushi ya mata ya kalleta yace " karfa kiyi gudu ki tafi a hankali kije ki dawo."
Itama murmushi tamai tace " yanzu zan dawo Yaya, in na dawo zan cigaba da baka labarin."
Kai ya d'aga mata alamar to, kusa da shi ta dawo da sauri ta kura mai ido, kallanta yai tare da saurin d'auke ido, tace "wani sa'in sai inga kamar kana gani."
Fuska ya d'an hade yace " zaki fara ko?"
Dariya tai tace "karka damu yaya a kullum in nai sallah addu'ar da nakeyi kad'ai kenan 'Allah ya baka lafiya ka dinga gani.'
Fuska ya saki yace "dafatan ba ita kadai kikeyi ba? Addu'ar nake nufi."
Mikewa tai da sauri ta fara tafiya, hannu yasa ya riko hijab dinta ta fizge da karfi sai dataje kofa tace " ita kadai nakeyi."
Tai saurin tai waje.
Dariya yad'anyi tare da girgiza kai, ba shakka Khadija itace take d'ebe mai kewan zaman kad'aici, dan ko sharri akamai ko aka b'atamai rai inyazo ya zauna a d'aki shiru ita ce ke zuwa gunsa, bazatace komai ba sai dai zata zauna kusa dashi harsai taji ya fara mata magana, ya rasa menene dalilin dayasa mahaifiyarsa ma zancenta kenan akan ya rage kula Khadija, ko Lantana ma wani sa'in sai yaji tace " Uban gidana ka rage sa Khadija a ranka."
Bai tab'a tambayar dalili ba dan kuwa yasan ba mai fadamai, kuma yana tunanin dan tana 'yar yayan Magajiya ne yasa ake fadamai haka.
A can kuwa Khadija na zuwa aka sa ta amota, mamaki ya kamata ta kalli Mamanta tace " ima zamu?"
Rufo kofar motar Hisham yai sannan ya kalleta ta yace " ki koma kano gun kanwar Mamanki ki zauna acan, kiyi karatu, inkinyi hankali nida kaina zanzo d'aukanki."
Ihu ta saka tace "itakam bataso abarta anan, gub Ya Turab."
Tana ihu tana kuka aka ja mota akai gaba, kuka take sosai harda shesheka, sai dai Mahaifiyarta kawai ta jawota jikinta ta kwantar.
Tana kuka har bacci ya d'auketa, bata farka ba sai da akai parking a kofar gidan.
Da kuka ta shiga gidan.
*******
Haka rayuwa ta kasance tun Turab na jiran Khadija kwana d'aya, biyu ba labari, nan ya fara tunanin ko batada lafiya ne.
Satar jiki yai ranar datai kwana hud'u ya fito, tunani ya fara ta inane ma inda zaije shidai ba yawo yake ba, ga gidan katon gaske, yana tsaye yana tunani yaji anzo tabayansa ance woo da karfi akai wanda sai daya d'an tsoratashi ya juyo da sauri ganin Mairo ce ya had'e rai tare da dauke ido daga kanta, hannu takai kamar zata dakeshi ta makamai harara tace a hankali " nima ba farincikin ganinka nake ba."
Fuskarsa a had'e yace " kinga Khadija?"
Bakibta tab'e tace " khadija?"
Sai kuma tasamai dariya tace " niban ganta ba."
Kallanta yad'anyi kamar ya tambayeta inda zaije yaganta sai kuma ya fasa, Mairo tace "la ga Yayanta nan zuwa ka tambayeshi."
Juyawa yai da sandarsa zai koma, jiyai Abdulmajid yace " Abu Turab."
Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba, Abdulmajid ya karaso inda yake, ya mai wani kallo na sama da kasa yace " kana d'an sarki menene dalilin fitowarka kai kadai?"
Abu Turab ya kalli gefensa baice komai ba, Abdulmajid yacigaba" in har kanada ido ma ba wani abin amma kana makaho ka dinga yawo kai kadai?"
Ba kalmar daya tsana irin a dinga cemai makahon nan, Mairo dake tsaye ta kalli Abdulmajid dan dama ba kunya gareta ba tace " yau naga ikon Allah, wani inyaji kana fadar haka daukama zaiyi ka damu dashi."
Abdulmajid ya maka mata wani mugun kallo yace " ke kuma uban waye ya sa bakinki?"
Tab'e baki tai tace " wai da...."
A hankali tai maganar, sai dai yajita, juyowa yai ya kalleta yace " wlh kika batamin rai bakeba har ubanki sai na sa an hukunta."
Baki ta murguda kadan tace "badai nawa uba...."
Abu Turab yai saurin daka mata tsawa yace "ke Mairo!"
Idanu ta zaro dan sosau ta tsorata, yace wuce ki tafi gida.
Kallansa tai batace komai ba tai gaba, yauce rana ta farko da taji bazata iya maida murtani ba akan fadan da aka mata.
Tana tafiya Abu Turab ya juya zai tafi, kafa Abdulmajid yasa mai ya kifa kuwa tim.
Kasa duk ta shiga bakinsa, Abdulmajid ya matso da sauri ya kama hannunsa yace " tashi sannu, kaga irinta ko? Yanzu dan Allah yasa ina nan ne da bamai d'agaka."
Mamaki ya kama Abu Turab, sai dai ya daure ya mike ya kade jikinsa baice komai ba ya juya zai tafi.
Abdulmajid yace " Khadija fa? Badai cemin zakai ita ka fito nema ba."
Abu Turab baice komai ba.
Abdulmajid yasa dariya ya dawo gabansa yace " duk amintar ku bata fadama zatai tafiya ba?"
Abu Turab yad'an juyo inda yake, Abdulmajid ya dan dafashi yace "yaro man kaza."
Baijira mai zaice ba ya juya ya tafi.
Jikin Turab ne yai wani mugun sanyi a hankali ya dinga tafiya har ya isa b'angarensa dan yanzu an fitomai da kofa daga b'angaren Basira.
Yana shiga yaga Mahaifiyarsa a tsaye a tsakar gida, ga bayinta da nashi duk a tsatsaye.
Da alama fada take musu, jin bude kofa da shigowarsa yasa duk suka kuramai ido.
Wani mugun kallo tamai ta kallesu tace " ku bamu gu."
Nan kowa ya juya ya fita, Lantana kam jiki a sanyaye ta fita dan tasan Ubangidanta yayi laifi.
Basira tana matsowa ta wanka mai mari.
Hannu yasa a gun bai d'agoba kansa na kasa, cikin kuluwa tace " gidan ubanwa kaje? Sau nawa ina cema karka fita kai kadai?"
Kansa na kasa yai gum da baki.
Ta kalleshi dan tasan bazai magana ba, ita kanta tayi dana sanin marin nasa sai dai itakam tana tsoron abinda za'amai in aka ganshi shi kadai, balle yanzu dataga gefen kuncinsa kasa ta tabbata wani abun ne ya faru.
Juyawa tai a harzuke tai waje.
Abu Turab ya tsugunna a gun idanunsa suka ciciko, ga jin khadija tayi tafiya, ga bakincikin Abdulmajid, gashi ya b'atawa mahaifiyarsa rai.
Lantana ce ta dawo ta d'agashi ta shiga dashi ciki, a wannan ranar kam Abu Turab sai daya zubda hawaye.
***********
Tundaga wannan rana komai na rayuwarsa ya canza, magana wannan sai ya zamarmai dole yake yi, kullum yana b'angarensa, rayuwarsa ta koma ta da, sai dai ko makarantarsu ko kuwa inya fita gaida Mai Martaba ko Magajiya.
A makaranta ne dai Mairo take dan mai magana bayan ita kuwa kaf ajin daga gaisuwa ba abinda ke hadasu da kowa.
Tun randa ya ma Mairo tsawa kuwa ta rage rainashi, sai tausayinsa ma data darayi, gashi yanzu ya canza kullum fuskarnan tasa ba fara'a.
A kwana a tashi ba yuwa yau gashi Abu Turab ya cika shekara 22.
Yau an tashi a gidan Sarki anata shirye shirye sakamakon hawan Sallah na karama da za'ai.
Zaune yake a d'aki ya saka kayan da aka aikomai inji Magajiya wai ya saka, tunda ake hawan sallah Abdulmajid ne kadai yakeyi, amma wannan sallar wai ta aikomai da kaya akan shima zaije hawa.
Murmushi ya saki sannan ya d'aga kayan sama ya tabbata akwai wani makirci da aka shirya mai.
Yana nan azaune yaji ana kwankwasa mai kofa.
Mikewa yai ya tako yazo ya bud'e.
Mahaifiyarsa ce hakan yasa ya matsa mata ta shiga ciki.
Zama tai a bakin gado sannan tace " akacemin an aikoma da kayan hawa?"
Kai ya d'an jinjina yace " gasu can."
Kallan kayan tai sannan tace " Turab amma dai....."
Murmushi ya mata yace " zanje."
Kallan mamaki tamai tace " baka tunanin so take a mutanen gari su fahimcu baka gani? Ko kuma wani abun sukama dokin kaje ya yarda kai mutane su gane baka iya doki ba? Sannan su fahimci makantarka?"
Idanunsa ya d'an rufe kadan sannan yace " Umma."
D'agowa tai ta kalleshi yace " har sai zuwa yaushe ne zan nunama mutane ina gani?"
Kallansa tai tace " Abu Turab!"
Yacigaba " Wani irin tsoro ne damu da haryanzu bamu cireshi a ranmu ba? Kina tunanin wannan tsoron namu akwai inda zai kaimu?" bai jira amsarta ba ya cigaba "a'a, wannan tsoron haka zai cigaba da dawammar damu a inda muke ba tare da mun tsinana komai ba? Na sha wahala tun ina yaro har zuwa wannan lokacin, har sai yaushe ne zamu kwaci 'yan cinmu? Har sai yaushene zaki bari d'an da kika sha wahala akansa zai sama miki farin ciki?"
Kallansa take yi cikin tausayawa da tsananin kauna.
Hannayenta ya kama yace " na gaji da wannan tsoron, nifa namiji ne, jinin mahaifina haka kuma d'a gareki, haka kikeso incigaba da zama? Ana nuna ked'in ba kowa bace balle ni? Bayan kuma ni nasan ked'in mace ce wacce kaf duniya a gurina banga kamarta ba?"
Idanunta ne suka dan tara ruwa kadan, kai ya girgiza mata yace " tun ina d'an yaro kika haneni da ragonta da kuka, Umma kina tunanin Mai Martaba shine zai kwatar mana 'yancin mu?"
Kallan mamaki tamai, kai ya girgiza yace " ko kad'an in har kina tunanin wannan ki cire a ranki, Mai Martaba sarki ne, sarkin mutane masu dumbun yawa wanda yake mulkarsu sai dai ba sarki bane a tsakanin matansa, Magajiya bazata taba barinsa yai yanda yakeso ba akan matansa, yaci ace a shekaru goman nan kin fahimci haka."
Murmushi tai sannan tace "nasan da haka Abu Turab sai dai ina tsoron karmu lakutowa kanmu abinda gaba bazamu iya magani ba."
Dariya yai sai dai mai dan sanyi, wanda rabon dayai dariya haka ya dade yace " ina Umma na ne wacce take tsaidani in nai laifi? Ina Umma nane wacce take hanani kuka? Ina Umma nane wacce ke marina duk sanda na b'ata mata rai?"
Harara ta makamai tace " da alama girma ya fara kama wannan Umman taka."
_Nikaina sai da na saki wata bazawarar dariya....Lol_
0 comments:
Post a Comment