Inna Tani ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai tace "maigida lafiyarka k'alau kuwa,,, ka fito waje ka gayamin abinda ya faru dakai bayan kaje d'auko Gwamma,,, ko acan ne aka baka tsoro ne? ".Ta k'yalk'yale da dariyar mugunta.
Baba Labbo ya lek'o ta tagar d'akin yana wuru wuru da idanu,,, da nishin wahala alamar yasha wuya sosai da yake fitarwa yace "wallahi Tani danaje can d'auko Gwamma domin ta dawo gidan nan,,, bayan munyi magana da Gwamma ta shiga cikin d'akin saboda ta d'auko kayanta mu wuce ,,,tana shiga kafin ta fito daga cikin d'akin macijiya ta fito daga cikin d'akin Gwamma tana ta tsoratani!........ ".Ya kawo labarin komai ya sanar da ita duk irin abubuwan da ya faru a cikin gidan Gwamma,,,, ya sanar da ita babu abinda ya b'oye mata dangane da irin tashin hankali da bala'in daya gani...
Yana gama fad'ar wannan magana,,, bayan ya kawo k'arshen magana Inna Tani ta kama salati tana wuru wuru da idanunta cikeda matuk'ar tsorata da kid'emewa! "Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Lallai kaga tashin hankali da bala'i maigida,, Allah kawai ne yasa da rabon zaka kawo labari da ka mutu tunda dad'ewa,,,, dama saida nace karkaje kaje da yanzu ni aka bari cikin bak'in cikin rayuwa da kuka ".Inji Inna Tani cikeda matuk'ar sanyin jiki da tsananin tsoro!.
Baba Labbo yace "nima Tani banyi zaton Talatu xatabar macijiya domin tayi gadin Gwamma ba,,, saboda naga wanda ya mutu ya riga ya mutu har abada ".
Inna Tani ta fyace majina tace "haka ne amma dan Allah kada ka sake zuwa gidan nan,,, saboda ina tsoron kada macijiyar ta kasheka a banza da yofi! ".
"wa! Ni in kikaga naje gidan to saidai gawata ce aka kai,,, to ko gawata ban yarda akaita gidan ba idan har na mutu ".Cewar baba Labbo cikeda matuk'ar tsoro da fargaba!.
Inna Tani tace "Allah dai ya tsare gaba maigida,, to fito waje in wanke maka jikinka naga duk ya b'aci da zawo sosai ".
"inajin tsoro Tani ayau d'in nan naga tashin hankali da bala'i wanda ban tab'a gani ba,,,,bazan iya fitowa ba tsoro nakeji sosai ".Inji baba Labbo cikeda matuk'ar tashin hankali!.
Inna Tani tace "babu abinda zai sake faruwa sai alkhairin Allah,, kuma idan Allah ya yarda ba zaka sake mugun gani ba,, saboda wannan tashin hankali da rikicewa yaja ma harsu maigari gudu da sauran mutanen gari fargaba da zullumi! ".
Baba Labbo yace "nikam bazan fito ba inajin tsoro sosai wallahi Tani "..Dak'yar da lallashi,, rok'o,,, gamida da magana mai dad'i sosai Inna Tani ta samu baba Labbo ya fito daga cikin d'akin,,, yana fitowa ta tara masa ruwa a bokiti takai mishi cikin toilet,, ta d'auko towel irin na zane ta bashi ya shiga wanka kayan da duk suka b'aci sosai da zawo tasa klin da sabulun wanki ta wanke tass zad sha'awa,,,, tana gama wankewa ta shanya kayan a saman igiyar wanki,,,, ta shimfid'a tabarma ta zauna tana jiran fitowar baba Labbo daga cikin makewayi..
Ba'a jima sosai ba saigashi ya fito daga cikin toilet,, ya shiga cikin d'akin ya shafa manshafi sannan ya d'auko wasu kaya ya sanya,,, bayan ya sanya kayan ya fito waje ya zauna kusa ga Inna Tani,,,, ta tashi taje ta kawo masa abincinsa da ruwa masu sanyi cikin jug,,, yayi bismillah ya fara cin abincinsa cike da natsuwa da walwala,, ita Inna Tani sai firfita takeyi masa da fai -fai tana kallonsa cikeda matuk'ar tausayi da k'auna matuk'a..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Ab'angaren Sule da Gwamma bayan ya gama biyan buk'atarsa,,, babu abinda Gwamma keyi sai hawayen ciwo da rad'ad'i,,, yaje ya d'ebo ruwa a randa ya aza mata ruwan zafi a saman murhu,,, bayan ruwan sunyi zafi sosai yazo ya surka da ruwa masu sanyi ya kai mata ruwan acikin toilet,,,, yazo ya taimaka mata ta tashi tsaye ta dafa kafad'arsa,, ya kaita har cikin toilet ya gwada mata yadda zata gasa jikinta sosai da ruwa masu d'umin ya fito daga cikin toilet d'in.
Yana fitowa ta kama gasa jikinta sosai tareda zama acikin ruwan zafin,,, tana kuka a hankali cikeda matuk'ar rad'ad'in ciwo da zafi,,, haka dai ta daure ta cigaba da gasa jikinta sosai lungu da sak'o ko'ina a cikin jikinta,,, bayan ta gama ne taji zafi da rad'ad'in da takeji ya ragu sosai acikin jikinta,,,, sannan daga baya ta fito daga cikin toilet d'in ta shiga cikin d'akin ta shirya.
Bayan ta kammala shiryawa ne Sule ya bata maganin rage rad'ad'in zafi,,, ta amsa tasha da ruwa masu sanyi ya dubeta yace "sannu Gwamma nagode sosai da kika sanyani cikin farin cikin da ban tab'a jin irinsaba,, kika bani abu mafi daraja da tsada a rayuwarki,, kika sanyani cikin nishad'i da jin dad'i sosai matuk'a,,,, Allah ubangiji ya baki lafiya kuma yabarmu tare har abada ".
Saida Gwamma ta dubi Sule cikeda takaicin rabata da budurcinta da yayi,, acikin zuciyarta sai sak'e sak'e takeyi na irin mugun hukuncin da zatayi wa Sule can ta nisa tace "hmmmmm babu komai ai wannan yana daga cikin irin soyayyar danake yi maka har acikin zuciyata,,,, kuma kafi k'arfin komai a wajena Sule ".
Yayi murmushi yace "haka ne gaskiya masoyiyata dama haka so yake,,, gamon jini ne shi kuma farat d'aya yake shiga acikin zuciya babu sallama ko neman izni ".Cewar Sule cikeda matuk'ar yaudara da dad'in baki..
Gwamma tace "babu k'arya acikin maganarka masoyina,,, abin sona akodayaushe ".
Sule yace "Allah ubangiji ya baki lafiya da k'arfin jiki masoyiyata,, ni zan wuce zuwa gida ".Yace tareda mik'ewa tsaye alamar zai wuce. Tace "amin amin Sule ".Ta tashi tsaye domin ta rakashi a waje,,, suka nufi k'ofar gida ta kaishe har waje tana yi masa sai wata rana
Sule yayi tafiyarsa ita kuma tayi dawowarta cikin gida,,, ta zauna saman tabarma tayi tagumi tace "hmmmm Sule kajawa kanka masifa da bala'i wlh!,Budurcina daka amsa baka amshesa ga banza da yofi ba,,,, saina kasheka in kasheka banza! Saika d'and'ani zafin fitar rai amma ba yanzu zan kasheka ba saina k'ara shan zumarka ".
Hhhhhhhh haka dai ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai,,, sannan ta murtuk'e fuska ta cigaba da surutunta na son rai da haukahhhh...
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN KWANA BIYU*
***Bayan faruwar mutuwarsu baba Labaran da Sala mafarauci da matarsa,,, garin duk ya rikice da kacamewa da mutuwar mutane ishirin acikin garin Gumi! Ko'ina ka duba acikin garin kukan mutane da ifface iffacensu,,, yara da mata sai kuwwace-kuwwace kawai sukeyi da kuka harna tashin hankali da bak'in cikin mutuwar mutane kusan ishirin.
Ganin haka ne yasa suka k'ara tsoracewa akan al'amarin mayyu,,, tsoro da fargaba ya bayyana k'arara akan fuskar mutanen gari,,, kowa ka kalla kuka sukeyi kamar ransu zai fita daga cikin gangar jikinsu saboda bak'in ciki da matuk'ar fargaba akan lamarin mayyu.
To da yake mutum biyu sun rasu daga cikin danginsu Sala mafarauci da baba Labaran,, shiyasa mutane suka fara zuwa gidan baba Labaran domin su sanardashi abinda yake faruwa,,, Innar Lado kawai suke iske zaune tayi tagumi zuciyarta sai fad'uwa takeyi da k'arfi da k'arfi rassssss! Sukayi mata sallama ta amsa mutum guda kawai ya shigo cikin gidan ya sanar da ita abinda yake faruwa acikin gari,, hankalinta ya k'ara tashi zuciyarta ta cigaba da bugawa da k'arfi d'immmmm! Dak'yar ta sanarda mai aike baba Labaran bai dawo gida ba,, tana ganin yana gidan Sala mafarauci suje can zasu samesa itama anan shi take jiran ya dawo,, dan aiken ya juya waje yaje ya sanardasu maigari abinda yake faruwa..
Batare da b'ata lokaci ba suka d'unguma gaba d'ayansu kusansu goma sha biyar zuwan gidan Sala mafarauci,, domin su sanardasu shida baba Labaran abinda yake faruwa acikin garin,, bada jimawa ba suka kawo bakin k'ofar gidan Sala mafarauci sukayi sallama a waje,, shiru babu amsa sukayita sallama babu adadi sunyi tsaye shiru harna tsawon minti talatin sannan daga baya suka yanke shawarar shiga cikin gidan gaba d'ayansu,, suna shiga filin gidan babu motsin komai saina awaki da kaji babu kowa nan ma saida sukayi shiru sannan daga baya suka yanke shawarar shiga cikin d'akin gabansu sai fad'uwa yakeyi yana bugawa da k'arfi da k'arfi! Tsoro ne da tashin hankali ya bayyana a fuskokinsu k'arara! Maigari shine shugaba amma yafi kowa tsoro da rawar jiki,, dak'yar suka daure suka afka acikin d'akin.
Suna shiga cikin gidan saida numfashinsu ya kusa d'aukewa,, tashin hankali da rikicewa ne akan fuskokinsu k'arara saboda ganin Ummaru sukayi kwance ya some sannan ga k'asusuwan mutane nan su baba Labaran yasshe acikin d'aki,,, sukaje wurin Ummaru domin su bashi taimakon gaggawa babu abinda ke fita daga cikin bakinsu ila "Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fi musibati wa'akhalufni khari minha!.......
_Share&Comments_
[7/2, 8:15 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 22*
"Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un Allahumma ajirni fi musibati wa'akhalufni khari minha!!!".Suka fad'a atare cikeda matuk'ar tashin hankali da rikicewa! Bayan sunje wurin Ummaru da sauri d'aya daga cikinsu yaje ya d'ebo ruwan sanyi a cikin randa,, ya kawo akayima ruwan addu'a mai tsawo sannan aka juye masa ruwan gaba d'aya ajikinsa saida ko'ina a jikinsa ya jik'e da ruwan,,, ganin da sukayi zasu gaji da tsayuwa yasa dole aka d'auko tabarmi guda biyu kowanensu ya zauna akai,,, sukayi jugum duk jikinsu yayi matuk'ar sanyi da fargaba akan abinda idanunsu suka gani,, sannan kuma ga k'asusuwansu Sala mafarauci nan yayyasshe ko'ina a cikin d'akin k'arnin jini kawai yake tashi,, ,,babu dad'in ji balantana gani sunyi shiru na tsawon lokaci da tagumi gabansu sai fad'uwa yakeyi da sauri da sauri,,, can dai sukaji Ummaru yaja dogon numfashi tareda yin tari yana farfad'owa ya tashi zaune yana kallonsu d'aya bayan d'aya,,,,, ganin ya farfad'o ne zuk'atansu suka cika da farin ciki da murna sosai sannan kowanensu ya matso kusaga Ummaru suna yi masa sannu,,, yana amsawa bayan d'an wani lokaci ne maigari Garba ya k'ara matsowa kusa ga Ummaru yace "Ummaru munzo wurin iyayenka da yayan babanka Labaran,, saboda in sanardasu abinda yake faruwa acikin garin Gumi na mutuwar mutane ishirin,,,,, biyu daga cikinsu 'yan uwanku ne,, amma sai muka tarar da kai ka suma sannan bamuga mahaifanka ba da yayan babanka,,,,sanardamu mi yake faruwa yakai Ummaru? ".Alokacin ne Ummaru yaji wani irin turirin bak'in ciki ya tokare masa gaba,,, wani abu ne ke yawo a cikin jinin jikinsa idanunsa sukayi jawur hawaye kawai ke fita daga cikin idanunsa,,, zuciyarsa sai tafasa takeyi da k'una sosai babu abinda kake hangowa sai tsananin b'acin rai da bak'in ciki acikin idanunsa,,, maigari ne ya sake cewa"kayi hak'uri ka sanardamu duk abinda yake faruwa,,, komai yayi zafi maganinsa Allah kuma komai yayi farko yanada k'arshe zaizo ya wuce kamar ba'a tab'a yinsa ba ".Wani dake gefen maigari mai suna Tukur,,, ya karkace baki yace "haka ne maganarka maigari Allah yaja zamaninka,,, hak'uri zakayi Ummaru ka gaya mana abinda yake faruwa saboda kaga anan babu wanda yasan abinda ke faruwa ".Madu yace "mu kanmu jikinmu duk yayi sanyi hankalinmu duk ya tashi! Saboda bamuga alamarsu Sala mafarauci da matarsa da yayansa a cikin wannan d'akin ba,,, kuma matar Labaran ta tabbatar mana yana nan yazo gurin Sala mafarauci domin ya k'ara diba yadda jikinsa yayi sauk'i sosai ".
"k'warai da gaske haka maganar take Ummaru,,, ba kai tsaye mukayo nan ba saida muka biya gidan babanka Labaran ".Inji maigari cikeda matuk'ar sanyin jiki da lallashi. Ummaru ya d'ago ya kallesu idanunsa sunyi matuk'ar ja,,, ya bud'i baki dak'yar yace "kuyi hak'uri bawai na k'yaleku bane saboda baku isa gareni ba,,, na k'yaleku ne saboda zuciyata k'una da tafasa takeyi alokacin amma yanzu zan sanardaku irin mummunan k'addarar data sameni nida iyayena da baba Labaran,,, k'addarar da ban tab'a zaton ko a mafarki zata afku gareni ba,,, mugun al'amarin da har abada bazan tab'a mantawa dashi ba ko bayan raina....... ".Ummaru ya kwashe labarin irin ta'adancin da tsutsar tayima iyayensa da baba Labaran harta kashesu,,, ya sanardasu yadda tayi masa mugunta har ya some baisan inda kansa yake ba,,, yana kawo k'arshen maganarsa ya fashe da wani rikitaccen kuka mai ban tausayi da tarin bak'in cikin rayuwa.
Gaba d'ayansu suka k'ara saka salallami "ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un Allah ubangiji ya jik'ansu Sala mafarauci! Yasa sun huta acikin kabarinsu ".
Maigari yace cikeda matuk'ar tashin hankali da rikicewa! "kayi hak'uri Ummaru Allah yana tareda masu hak'uri,,, amma wannan abin ya zamo d'aukar fansa ne ga Inna Talatu MAYYA saboda kasan babanka shine ya zamo ajalinta,,, kaga kuwa kenan tanada 'yan uwa ko abokiya wadda ta d'aukar mata fansar jinin Talatu harta kashe mutane ishirin da uku gamida iyayenka! ".
Madu yace "wannan abin babu shakka haka yake,, saboda kashe rayuka da akeyi acikin garin Gumi yayi yawa sosai wlh,,, ada muna ganin abin da sauk'i ayanzu yazo yaci uban na da ".
"ai wannan mayyar da ta kashe mutane ishirin da uku to ta wuce Talatu MAYYA,,, awurin hatsibibanci da zalunci! Saboda Talatu bata tab'a kashe rai kusan ishirin lokaci guda ba ".Cewar Tukur cikeda matuk'ar bak'in ciki da takaicin abinda ke faruwa..
Maigari yace "haka ne gaskiya amma zamu d'auki babban mataki acikin garin Gumi,,, na duk inda aka kama MAYYA akasheta saboda abin yayi yawa sosai idan ba haka harmu zasu shiga cikin gidajenmu suna kashemu da iyalenmu,,, kunga kenan muma bamu tsira ba akodayaushe akowane lokaci mutum za'a iya kame masa kurwa a cinye ,,,yanzu dai Madu tashi ka tattara k'asusuwan nan muje ayi musu sallah arufesu mak'abarta "..
"to maigari ".Cewar Madu ya tashi tsaye ya samo buhu ya tsince k'asusuwan baki d'aya,,, ya sanya cikin buhu ya dawo ya zauna.
Tukur ya dubi Madu yace "ba zama zamuyi ba tashi zamuyi yanzu nan muje can cikin gari,, akaisu tareda da sauran gawarwakin dake can ana jiranmu ".
Dogarawan sukace"maganarka haka take Tukur angaisheka".
Suka mik'e tsaye gaba d'ayansu harda Ummaru,,, suka fito daga cikin gidan cike da matuk'ar bak'in ciki da jimamin mutuwarsu Sala mafarauci da mutane ishirin,,, suka d'unguma zuwa inda aketa yima gawarwakin mutane wanka.
Koda sukaje har angama musu wanka da sallah,,, za'a kaisu gidansu na gaskiya maigari ne ya umurci mutane da su tsaya,,, suna tsayawa ya umurci Ummaru ya basu labarin da ya basu na mutuwarsu baba Labaran da Sala mafarauci sannan aka gwada musu yadda mayya ta cinye musu nama har ya dawo k'asusuwa,,,, ai kuwa mutane suka k'ara rikicewa da d'imaucewa! Akan mummunar annobar mayya data zarce Inna Talatu akan rashin imani da shahara a cikin maita! Haka dai sukayiwa k'asusuwan sallah sannan suka d'unguma zuwa mak'abarta domin akaisu makwancinsu na gaskiya.
Mutane kowa ka diba hawaye ne ke gangaroya daga idanunsu,,, tsoro da tsananin tashin hankali ne bayyane afuskokinsu saboda kowa yasan zai iya fad'awa cikin tarkon k'ursugumar mayya gagararriya acikin mutane da aljannu! K'arin takaici da haushi basusan ko wa ce ce sabuwar mayyar dake kashesu abanza tareda jaddada fitina a tsakaninsu ba..
**********************
Bayan sun dawo daga kaisu Sala mafarauci gidansu na gaskiya,, to alokacin ne maigari yayi sanarwa akan mutanen gari su taru bakin k'ofar gidansa,,, bayan mutane sun gama taruwa ne ciki kuwa harda baba Labbo,,, sannan maigari yayi bayanin cewa duk inda aka kama mayyu acikin garinsa to akashesu,,, sannan ya juyo ya dubi baba Labbo ya tambayesa rannan miye ya sanyashi gudu har ya kawo wurinsu da matsiyacin gudun ceton ransa,,, baba Labbo ya duk'ar da kansa ya kwashe labarin irin yadda macijiyar ta bashi tsoro da kuma gargad'insa akan kada ya sake dawowa gidan yayansa marigayi Malam Mamman.
Mutane sunka k'ara tsoracewa da rikicewa akan wannan labari da baba Labbo ya sanardasu,,, maigari yayi magana ya nuna musu za'a saka matakan tsaro acikin garin baki d'aya sannan za'a sanyawa Gwamma ido matuk'a,, saboda yadda take rayuwar cikin gidan batare da tsoro ko wani shakku ba.
Su kansu mutunen gari zuciyarsu ta basu akwai wani abu ab'oye ko lauje cikin nad'i,,, saboda sunsan babu mai iyawa zama cikin gida shi kad'ai idan ba hatsabibi ba,, aka umurci Malamai gaba d'ayansu dasu k'ara dagewa akan Allah ubangiji ya tonama mayyu asiri,,, mutane sukace amin sannan sukayi addu'o'i kowa ya kama gabansa cikeda matuk'ar zullumi da rad'ad'in ciwon mutuwar mutane ishirin da uku..
Musamman yafi kowa jin zafi da rad'ad'in ciwo har cikin zuciya ,,,,,yasha alwashin kowaye ya kashe masa iyayensa da yayan babansa sai ya d'auki fansar jininsu,,,, ab'angaren Innar Lado wato matar baba Labaran tanajin labarin mutuwar mijinta dana Sala mafarauci da matarsa ta fad'i k'asa ta some,,,,mata mak'wabtanta sukazo kawo mata agajin gaggawa kafin ace wani abu zuciyarta ta buga ta rasu! Haka dai itama akayi mata wanka aka kaita gidanta na gaskiya..
Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!!.
**Ab'angarensu Sule da Gwamma haka suka cigaba da mu'amalarsu kamar mata da mijinta,,, akodayaushe yana manne da ita,,, ita kuma ta cigaba da cin naman mutane dana aljannu komai cikin sirri da b'oye takeyinsa,,, shi kansa Sule baisan wa ce ce ainahin Gwamma ba kawai yana tare da ita ne........
_Share&Comments_
[7/3, 2:53 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*Hak'ik'a ban tab'a zaton zan samu tarin masoya a rayuwata ba,,, ban tab'a zaton novel d'ina yanada farin jini da masoya masu yawa sai yanzu,,, nagode da soyayyarku masoyana aduk inda kuke a fad'in duniya,, inasonku ina k'aunarku kamar yadda kuke k'aunata*.
*PAGE 23*
Shi kansa Sule baisan wa ce ce ainahin Gwamma ba kawai yana tare da ita ne,,, ita kuma bata yarda ya gano ita mayya ce ba saboda batason ya baza ta acikin gari,,, kowa yasan mummunan dabi'ar da take aikatawa na kashe rayukan mutane....
*BAYAN KWANA BIYU*
Bayan kwana biyu da faruwar wannan mummunan al'amari,,,mutanen gari gaba d'aya kowa ya k'ara tsoracewa akan lamarin mayyu gashi sunga ankashe musu babban mafarauci,,,, wanda ya shahara a wurin kamun namun daji da kuma maganin mayyu,,, sun riga sunsan cewa Inna Talatu MAYYA tabar mai d'aukar mata fansa amma basu gano ainahin wa ce ce ko wa ye yake d'aukar ran mutane,,, kamar ran dabba shiyasa maigari bayan yasa matakan tsaro ya kuma samu amintattun mutanensa asirrance,,,, su dinga lura sosai da shige da ficen Gwamma,,,, babu wanda ya sani daga maigari sai wad'annan amintattunsa,,, ita kanta Gwamma bata sani ba balantana sauran mutanen gari...
Ab'angaren Ummaru kuwa bayan rasuwarsu Sala mafarauci ya shiga cikin matsanancin hali na bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,, kullum kullum idan kaga Ummaru sai ya baka tausayi yayi bak'i sosai ya rame,,,, saboda damuwa da yawan tunani gashi yanxu shi kad'ai yake kwana acikin gidansu,,,, domin bayason yaje wani wurin ya kwana saboda kada yabar gidan babu kowa acikin gidan nan....
Wata rana Ummaru yana zaune shi kad'ai acikin gidan yayi tagumi,,, zaune yake saman tabarma ya fad'a duniyar tunani,,, kallo d'aya zakayi masa kasan yana cikin wani hali domin yayi babban rashi na har abada! Ya rasa iyayensa da yayan babansa da kuma matarsa alokaci guda,,, duk wani farin ciki ko walwala nasa ya tsaya cak sai dai ya zauna shiru shiru babu magana,,, ganin haka ne yasa Kabiru abokinsa yana yawan zuwa wurinsa domin ya d'ebe masa kewa da kuma bashi kalamai masu dad'i...
Can dai bada jimawa ba saiga sallamar Kabiru ya shigo cikin gidan,,,, yaji shiru ba'a amsa ba ya sake sallama ya shigo har kusaga Ummaru yasa hannunsa ya jaye hannun Ummaru daga yin tagumi,,, sannan ya zauna alokacin ne Ummaru ya dubi Kabiru yace "mutumena yaushe ka shigo cikin gidan nan ban sani ba? ".
"ya za'ayi ka sani inata sallama kanacan kana tunani Ummaru,,, wai miyasa ba zakayi hak'uri ka fallamawa Allah komai ba,,,, ka daina yawan tunani domin kada ka kamu da wani ciwon ".Inji Kabiru cikeda tausayin abokinsa.
Ummaru ya bud'i baki yace cikeda matuk'ar bak'in ciki da takaici "idan Allah ya yarda zan rage tunani Kabiru,,, amma har abada bazan tab'a mantawa da iyayena ba dasu baba Labaran domin sune jigon rayuwata,,, na zama maraya gaba da baya ba wanda zan kalla inji sanyi a raina Yaya Lado shima ita ta fara kashesa ".
"addu'a zakayi musu akan Allah ubangiji yasa sun huta kuma yakai haske kabarinsu,,,, sannan maigari Garba ya aikoni wurinka Ummaru ".Cewar Kabiru.
Ummaru yace "wa ne sak'o ne ya baka ka gayamin?,,, sanardani inajinka Kabiru ".
Kabiru yaja dogon numfashi yace "Maigari ne ganin halin da kake ciki na bak'in ciki da damuwa,,, gashi kuma kai kad'ai kake rayuwa acikin gidan nan kaga kuwa dole damuwa ta k'ara maka yawa,,,, sannan nayi nayi dakai kazo mu dinga kwana tare ka nunamin bakayi saboda inada mata,,, to maigari ya baka auren 'yarsa Ummu Salma wani sati idan ya zagayo za'a d'aura muku aure idan har ka yarda,,, saboda haka yace kaje ka samesa idan ka amince kanason 'yarsa ".
Ummaru yayi shiru na tsawon lokaci yana nazari da tunanin maganar Kabiru,,, ya lula duniyar nazari da tunani...
Babu jimawa ya d'ago kansa ya kalli Kabiru yace "hmmm to kai mi ka gani akan wannan maganar,,, na amince ko yaya abokina ?".
"ka amince mana Ummaru maigari yana sonka da alkhairi sannan ta haka ne idan kayi aure zaka rage damuwa da yawan tunani,,, domin sadaki kawai zaka biya ad'aura aure sannan kaga idan kayi aure sai mu fara shirin d'aukar fansar rayukan iyayenka da sauran mutanen gari,,, saboda ni jikina ya bani idan ba macijiyar da ake labari acikin gari wadda Talatu MAYYA tabar fakon Gwamma ta kashe maka iyayenka ba da sauran mutane,,, to mi Gwamma take tink'aho dashi dahar zata zauna ita kad'ai a cikin wannan gida mai cikeda sihiri? ".Inji Kabiru cikeda matuk'ar nazari da tunani.
Ummaru yace "na amince da auren Ummu Salma d'in zanje in samu maigari ,,, domin mu tattauna sannan inyi magana da yarinyar,,, kuma maganarka akwai alamun k'amshin gaskiya acikinta amma ba komai kowaye ma zan kamasa da hannuna saina kashe duk wanda yakeda sa hannun acikin mutuwar iyayena! ".
Kabiru yace "haka ne gaskiya ai da sannu koma waye Allah zai tona masa asiri,,, kowa ya gano mai aikata wannan mummun d'abi'a ta maita! ".
Ummaru yace "ai bawai haka na k'yale ba ina nan ina saka idanu akan shige da ficenta ita Gwamma,,, sannan idan ma itace wlh bazanyi mata sassauci ba ".
"sassauci kuma? Ai mayyu babu su babu sassauci har abada acikin rayuwarsu,,, saboda basu aikata alkhairi ba taya za'a yi musu da k'yau idan aka kamasu ".
Ummaru yace "haka take maganarka Kabiru ".
Haka suka cigaba da tattaunawa akan yadda zasu b'ullowa al'amarin mayyu,,,da kuma maganar aurensa da Ummu Salma d'iyar maigari....
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Bayan gari ya waye Ummaru ya tashi yayi wanka ya shirya,,, sannan yaje gidan Kabiru suka d'unguma zuwa gidan maigari.
Suna zuwa sukayi sallama a k'ofar gidan ,,,,Zubairu k'anen Ummu Salma,,, shine yayi musu jagora har cikin gidan zuwa wurin maigari,,, suna shiga cikin gidan suka iske maigari Garba zaune saman kujera ga tabarma shimfid'e gaba garesa,,, suna zuwa suka duk'a har k'asa suka gaida maigari,,,, ya amsa musu fuskarsa asake cikeda matuk'ar farin ciki da nishad'i sosai..
Maigari ya bud'i baki yace "Ummaru ina fatar sak'ona ya isa zuwa gareka,,, da fatar zaka bani had'in kai akan auren da nakeson in had'a ku kaida Ummu ".
Ummaru ya duk'ar da kansa cikeda matuk'ar ladabi da girmamawa yace "eh baba sak'onka ya iso gareni ".
"kayi hak'uri Ummaru komai ya samu bawa muk'addari ne daga Allah,,,, sannan bawa bai isa ya gujewa k'addararsa ba kuma komai nufin Allah ne shine masanin gaibu,,, saboda haka na baka auren 'yata Ummu Salma wani sati za'a d'aura aurenku ".Cewar Garba maigari.
Sai asannan Kabiru ya d'ago kansa yace "hak'ik'a baba babu abinda zamuce maka Allah ubangiji ya saka maka da mafificin alkhairi,,, sannan mun amshi auren 'yarka hannu bibbiyu kayi mana abinda bazamu daina yi maka addu'ar gamawa lafiya ba,,, mun gode sosai Allah ubangiji ya k'ara nisan kwana ".
Ummaru yace "amin ya rabbi na yarda na amince da auren Ummu Salma baba,,, kayimin abinda har abada bazan tab'a mantawa da halaccinka agareni ba,,, sannan ka nunamin nima d'an gata ne a wurinka duk da yake banida iyaye,,, ka nunamin k'auna azahiri da bad'ini Allah ubangiji ya k'ara girma da d'aukaka ".
"karku damu duk abinda nayi maka nayi maka ne domin Allah mad'aukakin sarki,,, sannan ba fad'uwa bane komai mutum yayi ladarsa tanaga Allah,,,, saboda haka ku daina yimin godiya kunfi k'arfin haka a wajena sai dai ku jira har lokacin biki ".Inji Garba maigari cikeda matuk'ar farin ciki sosai.
"tabbas haka ne gaskiya baba ".Cewar Kabiru.
Haka dai ya cigaba da yi musu nasihohi masu ratsa zuciya,,,, sannan ya nuna musu muhimmanci hak'uri da juriya da kuma zamantakewar rayuwa.
Bayan maigari ya gama yi musu nasiha mai ratsa jiki,,, sannan ya tashi tsaye yace musu "shi zai tashi ya kira Ummu Salma domin su gaisa da juna ".
Kabiru yace "to baba muna jiranta ".
Maigari ya tashi tsaye ya shige cikin d'aki domin ya kira Ummu Salma,,,, yana shiga ba dad'ewa ba saiga Ummu ta fito daga cikin d'akin ta duk'a har k'asa ta gaidasu,,, sannan suka amsa mata cikin fara'a da walwalar fuska.
Kabiru ya dubi sama da k'asan Ummu Salma da k'yau ba laifi tanada k'yau matuk'a ba k'arya ,,, sannan daga baya yace "Ummu Salma ina fatar kinsan dalilin da yasa mukazo wurinki,,,, saboda ku fahimci juna keda Ummaru ".
"baba ya sanardani komai dangane daku,,, saboda haka na amince da duk abinda babana ya gindayamin".Cewar Ummu Salma cikeda matuk'ar kunya ..
Ummaru yayi murmushi yace "masha Allah komai yayi k'yau matuk'a naji dad'i sosai da kika amince da kina sona,,, nima ina sonki fiye da tunaninki kuma ba za'a samu wani matsala ta wajena ba,,, zan rik'e ki amana da hannu bibbiyu Salma saboda haka kada kiji wani shakku ko kwankwanto akaina ".
Salma tace "babu matsala nima awajena zan kasance mai biyayya da ladabi agareka matuk'ar ina raye a cikin duniya,,, zan sanyaka cikin farin ciki da nishad'i mai d'orewa".........
_Share&Comments_
~Kuci gaba da bina ni Mugirat~
[7/4, 11:20 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 24*
"Zan sanyaka cikin farin ciki da nishad'i mai d'orewa,,, zan zamo fitila mai haskaka rayuwarka zan sadaukar da farin cikina domin samun farin cikinka,,, biyayya ga iyaye ya zamo wajibi agareni domin samun aljannata agobe k'iyama ".Cewar Salma cikeda matuk'ar natsuwa da hankali. Alal hak'ik'a Ummaru yaji dad'in kalamanta sosai wani sanyi ne da jin dad'i ke kwaranya acikin zuciyarsa,,, ayanzu ya tsinci kansa cikin tsananin farin ciki da murna mara misaltuwa,,, ya kuma k'ara tabbatarwa da yayi dace da masoyiya ta gari abar alfahari ga kowane d'a namiji,,, ya riga ya sadak'ar idan Allah ya yarda ba zaiyi nadamar auren Salma ba a rayuwarsa,,, saboda daga ganinta kasan yarinya ce mai tarbiya da natsuwa gata da hankali da girmama na sama gareta,,, gata da sanyin hali da k'yakk'yawar d'abi'a ta ko'ina tayi batada matsala a rayuwa,,, tanada tausayi da jink'ai musamman akan yara ko nakasassu,,, batada girman kai ko kad'an..
Cikin tsananin farin ciki da shauk'in so,,, Ummaru ya d'ago idanunsa ya kalleta cikeda matuk'ar farin ciki da samun mace tagari yace "hak'ik'a Allah ubangiji abin godiya ne daya had'a ni da mace tagari d'iyar mutanen kirki,,, wadda takeda tarbiya da girmama manya,,, nima zan rik'eki amana bisa gaskiya da tsoron Allah zan zama jigon rayuwarki abar alfaharinki akodayaushe,,, zan kasance inwa agareki domin kada rana ya illatamin ke ".Cewar Ummaru cikeda matuk'ar nishad'i sosai.
Salma tayi murmushi wanda ya k'ara bayyanar da tsantsar k'yawon fuskar da Allah ya bata,,, sannan tayi masa kallon soyayya tace "naji dad'i matuk'a Allah ubangiji ya gwada mana lokacin auren lafiya,,, sannan idan muka zamo miji da mata Allah ya bamu zaman lafiya da kuma juriya da hak'urin xama da juna ".
Sai asannan ne Kabiru ya sake magana yana murmushin jin dad'i,,, saboda yadda suka amince da juna farat d'aya ya matuk'ar bashi sha'awa.
Yace "hak'ik'a nayi farin ciki matuk'a ta yadda kuka fahimci juna batare da wata matsala ba,,, sannan kukayi biyayya ga maigirma baba maigari,,,, ku masu biyayya ne da bin maganar manya Allah ubangiji ya gwada mana lokacin aure lafiya,,, sannan kuma ya baku yara masu albarka da biyayya agareku ".
"Amin amin abokina amma fa ka iya addu'a mai k'yau,,, Allah ya sauki matarka Hanne lafiya".Inji Ummaru cikeda zolayar Kabiru.
Salma tace "amin ya rabbi ".Kanta duk'e tana mai wasa da yatsun hannunta.
Alokacin ne Kabir ya harari Ummaru da wasa,,, sannan ya d'auko dubu hud'u daga cikin aljihunsa ya mik'awa Salma yace "gashi ta sayi kayan kwalliya ba yawa tayi hak'uri ".
Salma ta nok'e tak'i amsa,,, tana jijjiga kai alamar a'a ba zata amsa ba,,, "bangane mi kike nufi da haka ba Salma ".Cewar Ummaru.
"ai shine na gani ina bata tana wani jijjigar kai kamar mage ".Inji Kabiru cikeda fara'a.
"ina nufin ni bazan amshi kud'inka ba saboda babana ya gargad'eni akan na daina amsar kud'in samari ".Inji Salma cikeda ladabi.
Kabir yace "dama kin saba amsar kud'in wasu ne? Kuma naga Ummaru ba wani bane mijinki ne idan Allah ya yarda ".
"a'a nidai kawai ku barshi baba zaiyimin fad'a agida wlh nagode sosai da soyayyarka agareni,,, ina sonka ba domin abin hannunka ba Ummaru idan kukaje gida ina gaida Hanne da sauran mutanen gida,,, na barku lafiya cikin aminci da k'auna ".Inji Salma cikeda natsuwa tana gama fad'ar wannan magana tayi shigewarta cikin gidansu,,, batare da tsaya ta saurari kalaman da zasu fito daga cikin bakinsu ba..
Sukayi tsaye suna mamakin irin tarbiyar da Salma takedashi,, sannan ga iya tsara magana mai ma'ana da muhimmanci.
Can dai Kabiru ya dubi Ummaru yace "abokina mu wuce zuwa gida Allah ne ya tausaya maka,,, ya baka mace mai tarbiya da sanin ya kamata ".Yace tareda mayarda kud'in cikin aljihunsa ya ajiye.
"haka ne Kabiru mu wuce zuwa gida yanzu,,, aini nayi matuk'ar farin ciki domin kakata ta yanke sak'a ".Cewar Ummaru tareda da jan hannun Kabiru suka d'unguma zuwa gida,,, suna tafiya suna fira cikeda matuk'ar farin ciki da walwala sosai..
*********************
***Bayan sati d'aya ya zagayo mutane da dama aranar assabar,,, suka shaida d'aurin auren Ummaru Sala mafarauci da Ummu Salma Garba maigari akan sadaki dubu talatin lak'adan,,,,d'aurin auren ya samu halartar mutane da dama daga wasu garuruwan daga nesa abokanin maigari,,, anyi taro lafiya an watse lafiya cikeda mutunci da karamci,, anyi abinci kala kala aka rabawa mutane k'yauta ,,,,an raba lemun k'walba irinsu fanta,, coke da dai sauransu..
Komai na bikin anyisa a wadace cikin rufin asiri da wadatar zuci,,, amarya tasha kwalliya da chanza kaya kala kala masu k'yawo sosai..
'Yan uwa da abokan arzik'i sunzo na nesa da na kusa,,, dare nayi da misalin k'arfe 9:00pm na dare dai dai aka d'unguma akaje aka kai amarya d'akin mijinta,,, sai dai muce Allah ubangiji ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba mai tarin albarka.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN SHEKARU UKU*
Bayan shekaru uku abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda k'aruwar haihuwar da Ummaru mafarauci ya samu,,,,,matarsa Salma ta haifi d'a namiji na farko mai suna Habibu,,, ta biyu kuwa ba'a dad'e da haihuwarta ba mai suna Husna. Shima Kabiru d'iyansa biyu da Hanne matarsa ta farko Yusrah na biyu Yusuf shima dai k'arami ne,,, haka dai suke kula da iyalansu tareda basu kulawa da nuna soyayya na gaskiya,,, zumuncinsu ya k'ara k'arfi sosai a tsakaninsu komai tare suke yinsa cikeda yarda da aminta da junansu,,, idan kaga yadda sukeyin zumunci saikayi mamaki sosai saboda kana rantsewa da Allah kace 'yan uwan juna ne amma abin ba haka yake ba sone gamon jini da kuma k'auna matuk'a..
Ba laifi Kabiru da Ummaru yanzu sun zama shahararrun masu kud'i,, musamman Ummaru da ya zamo shahararren mafarauci wanda ya gaji ubansa Sala mafarauci,,,,,yafisa zamowa babban mafarauci a cikin garin Gumi da sauran k'auyukkan dake kewayenta,,, babu inda labarin jarumtarsa da shahararsa baije ba,,, kowane irin daji komai hatsarin daji da aljannunsa yana iya shiga ciki yayi farauta ya dawo gida lafiya k'alau,,, babu dabbar da take gagararsa kamawa ba sai dai idan baiyi idanu biyu da dabbar ba,, alk'awarin daya d'auka na fansar jinin iyayensa dana baba Labaran bai manta ba yana nan dai yana shirye shiryen d'aukar fansa!.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
***Ab'angarensu Sagiru,, Ila da Lawwali sun zama shahararrun 'yan kasuwa masu kud'i dai dai gwargwado,,, ganin sunyi kud'i yasa suka gina gidajensu kusaga juna,,, sannan kowane daga cikinsu ya nemo mata budurwa baba Labbo yayi musu auren soyayya.
Lawwali sunan matarsa Aliya,, Sagiru Adama,, shi kuma Ila Ladidi haka dai aka d'aura aurensu cikin wadatar zuci da rufin asiri sosai,,, d'aurin aurensu ya tara mutane da dama 'yan uwa da abokan arzik'i duk sunzo wurin bikinsu Lawwali,,, haka aka kai kowace amarya gidan mijinta cikin mutunci da lumana..
_Allah ubangiji ya bada zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba mai tarin albarka,,, wad'anda basuda aure ya kawo musu mazajen aure nagari masu halayyar k'warai._
Gwamma kuwa haka dai ta cigaba da cin naman mutane da mu'amalar iskanci da Sule,,, duk da irin matakan tsaro da aka sanya mata bai hana mata aikata maita ba! Babu abinda ta bari na naman mutane dana aljannu kowa bata bari ba,, gashi mutane sai tsoronta sukeji saboda amintattun maigari sun tabbatar masa da Gwamma *MAYYA CE* babba kuwa,,, komai na Gwamma cikin wayo da dabara takeyinsa na kamun kurwar mutane da aljannu!.
Maigari yanajin wannan maganar hankalinsa ya d'unguma sosai gabansa ya bada rasssss! Jikinsa sai makarkatar tsoro yakeyi saboda yaga alamar Gwamma ta zarce Inna Talatu MAYYA rashin imani acikin maita,,, ya aika dogarinsa guda ya kira masa surukinsa wato Ummaru d'an Sala mafarauci,,, batare da b'ata lokaci ba sukazo tare maigari ya kwashe labarin komai ya gaya masa cewa Gwamma ce shahararriyar mayyar da ta addabi rayuwar mutane sosai,,, Ummaru ya nuna masa ya kwantar da hankalinsa shine zai kamata da hannunsa sannan daga baya ya kasheta har lahira,, Ummaru yaba maigari shawarar asanarda mutane domin susan irin abubuwan da suke faruwa agari,,, maigari ya sanardasu komi gameda Gwamma mayya da kuma irin tsafe tsafen da take aikatawa ya gaya musu tafi mahaifiyarta shahara da gunguma akan maita,, domin ita har naman aljannu ci takeyi bawai ga mutane kawai ta tsaya ba.
Mutane suka k'ara rikicewa da d'imaucewa akan tashin hankali,,, gashi yanxu sun k'ara tabbatarwa Gwamma tafi mahaifiyarta shahara da gunguma akan maita da mugunta iri iri daban daban,,, sannan batada tausayi da imani ko kad'an,, bayan maigari ya gama nasa jawabi.
Ummaru yayi nasa jawabi inda ya nuna musu dasu kwantar da hankalinsu zai d'auki babban mataki akanta sannan zai kamata ya gana mata azaba sannan ya kasheta! Ya k'ara nuna musu dasu k'ara dagewa da yawan yin addu'a domin Allah ubangiji ya kawo musu k'arshen zaluncin Gwamma,,, kuma su kulada iyalansu tareda yin taka tsan tsan domin gujewa afkawa cikin tarkon Gwamma mayya,, yana kawo k'arshen maganarsa suka umurci mutane kowa ya watse ya kama gabansa,,, kallo d'aya zakayiwa mutane ka hango tashin hankali da rikicewa k'arara akan fuskarsu,,, masu raunin zuciya banda hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa babu abinda sukeyi,,, suna tafiya suna jimamin abinda yake faruwa marasa dad'in saurare da kuma ji,, ga kuma zullumi da fargabar akan kodayaushe mutum ana iya kame masa kurwa ya mutu har abada.........
_Share&Comments_
[7/4, 11:36 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 25*
**Mutum ana iya kame masa kurwa a cinye ya mutu abanza,,,, batare da anyi saurin ganowa ba sai daga baya ai kuwa mutane suna komawa gidajensu,,, maganar Gwamma k'usurgumar mayya ce ya bazu ko'ina a cikin garin Gumi,,, mata da k'ananan yara suka tsorace da rikicewa! Wasu ma babu abinda sukeyi sai kuka da zubar da hawayen bak'in ciki da tsoron mutuwa,,,, gashi babu halin mutum yace zai gudu yabar gari yayi gudun hijira,,, to ganin haka ne yasa mutane suka rage yawan fitar dare ko irin gungu nan da samari da dattijawa keyi acikin dare suna fira yanzu babu shi,,, saboda kowa yana tsoron masifar Gwamma da kuma ta cinye mutum a banza babu me cetonsa,,,, Ummaru mafarauci shi kad'ai kawai ke fitowa acikin tsakar dare yana yawon farautar kamun Gwamma mayya,,, kullum kullum yake fitowa nemanta amma har yanzu shiru Allah bai bashi ikon kamata ba,,, domin duk yawon nemanta da yakeyi tana ganinsa acikin madubin tsafinta,,,,, idan taga yadda Ummaru d'an Sala mafarauci yake yawon nemanta kamar yadda mafarauci ke neman namun daji saita bushe da muguwar dariya sosai tace "hhhhhhhhhhh Ummaru kenan ba zaka iya kamani cikin sauk'i sosai ba sai kasha bak'ar wahala,,,, kafin ka kamani sannan kashe mutane yanzu na fara! Babu ubanda ya isa ya hanamin cin naman mutane dana aljannu duk duniya,,, kafin na mutu sainayi abubuwan da har abada ba zaku tab'a mantawa dani ba,,,,,,saina shayar daku ruwan guba da bak'in cikin da zai kasheku d'aya bayan d'aya,,,, babu gudu babu ja da baya wannan alk'awari ne na d'auka araina kuma saina cikasa,,, saina cikasa! ".
Haka dai takeyin maganganu iri iri daban daban na d'aukar fansar jinin mahaifiyarta,,,,,saboda ita Gwamma duk da mutane sun gano ita mayya ce bata damu ba,,, sannan hankalinta kwance yake alokacin ne ma ta k'ara k'aimi wurin cin naman mutane da aljannu,,,,, mutum sai yana zaune cikin kasuwa ko majalisarsu akirasa ace 'yarsa ko d'ansa ko wani d'an uwa nasa ya mutu! Kullum safiyar Allah idan gari ya waye saita kashe kusan mutum goma ko fiyeda hakan,,, ganin mutuwar da akeyi ne yasa maigari da sauran mutanen gari suka fita cikin hayyacinsu,, tsoro,, tashin hankali,, fargaba duk suna taredasu akodayaushe akowane lokaci,,, Ummaru ma abin yana matuk'ar damunsa na yadda Gwamma take shammatarsa ya kasa kamata,,,, amma sai ya nasa acikin zuciyarsa duk daren dad'ewa sai ya kamata sannan komai b'oye b'oyenta da sihirinta tabbas wata rana sai dubunta ya cika..
**Washe gari da safe misalin k'arfe 11:00am na safe,,, bayan Gwamma ta share gidan gaba d'ayansa tsab,,, dayake nan Sule yake kwana acikin gidan akodayaushe sukayi wanka tare,,, sannan tayi musu breakfast tea da bread suka karya.
Bayan sun gama karyawa ne kowanensu ya shirya cikin sabbin kayansu mai k'yau,,, sannan Sule da Gwamma sukazo har bakin k'ofar gidan zatayi masa rakiya,,, suna zuwa bakin k'ofar Sule ne ya dubeta cikeda so da yaudara yace "farin cikin rayuwata mi kike buk'ata ne,,,, Idan zan dawo in sayo miki ?".
Gwamma tayi murmushi tace "zumana ka siyomin kifi mara k'arni da lemu da ayaba,,, sannan ka biya wurin Iya Abu mai saida langab'u ka sayomin shi ".
"hmmm duk a ina zaki saka wad'annan abubuwan da kika lissafo?,,,mata dai akwai ku dason cin dad'i da kwad'ayi".Cewar Sule cikin zolaya da wasa.
Gwamma ta hararesa da wasa sannan tace "duk acikin cikina kaidai ka sayomin babu ruwanka,,, muradinka dai kada nak'i ci ya lalace a banza aiku maza bakuda son dad'i ko kad'an sai d'aci ".
"ke ni ban iyawa da masifarki wasa nake nakeyi miki,,, zan siyo miki duk abinda kike buk'ata Gwammata,,, ai bakisan yadda nake sonki ba saboda haka ki daina shakku akan zan sayo ko bazan sayo ba ".Cewar Sule cikeda matuk'ar lallashi da dad'in baki.
Gwamma tace "to naji yanzu dai kayi magana mai ma'ana sosai ".
Sule yace "to ni dai yanzu zan wuce saina dawo ko ".
"to saika daw...... ".Bata k'arasa maganar ba saiga Lawwali yayi musu sallama,,, Sule ya amsa masa cikeda fara'a da murna sosai yayinda Lawwali ya dubesa ya tamk'e fuskarsa alamar bayason wata magana da Sule,,, Sule ya hango k'iyayyarsa acikin idanun Lawwali saboda haka batare da b'ata lokaci ba yaja k'afafunsa yayi wucewarsa zuwa inda zaije,,, Gwamma kuwa tana ganin irin kallon da Lawwali keyiwa Sule dole itama tasha masa toka tareda da yi masa jagora zuwa cikin gidanta.
Suna shiga cikin gidan ta d'auko tabarma ta shimfid'a masa,, tareda da kawo masa ruwa masu sanyi cikin jug,,, Lawwali ya zauna saman tabarma tareda yin bismillah sannan ya dubeta duba na fahimta da natsuwa yace "yaya Gwamma mun yini lafiya,,, ya bayan rabuwa? ".
"lafiya k'alau bayan rabuwa kuma ai kasan inda nike baka nemeni ba,,,, sai yau ka tuna dani ashe dai naka naka ne duk yadda ya lalace ".Cewar Gwamma cikeda jin haushin maganarsa .
Lawwali yaja dogon numfashi yace "Allah ubangiji ya huci zuciyarki yaya Gwamma,,, niba tashin hankali ya kawoni wurinki ba magana ce mai matuk'ar muhimmanci da amfani ta sanya nazo gareki,,, sannan kuma ai nasan hannunka bai tab'a rub'ewa ka yanke kayarsuwa ".
"to ina saurarenka mi yake tafe dakai? ".Inji Gwamma.
Lawwali ya nisa yace"da farko dai inason komai zakiyi a duniya ki sanya tsoron Allah azuciyarki,,, sannan duk abinda mutum zaiyi arayuwarsa yasan Allah ubangiji yana ganinsa koda lullub'e yake acikin rami,,,, shaidun duniya shine shedun lahira yaya Gwamma aikata alkhairi komai k'arancinsa arayuwarki ta duniya ki guji aikata masha'a komai k'arancinsa,,, amatsayina na d'an uwanki kuma k'ane agareki ya zamo dole in sanardake gaskiya koda zakiji haushina ki tsaneni,,, koda hakan zai zamo silar b'acin ranki abinda kike aikatawa acikin garin nan dai bai kamata ba,,, sana'ar maita bata dace dake ba !Ko'ina acikin gari maganarki kawai akeyi ana cewa ke *MAYYA CE* sannan abin takaici da bak'in cikin rayuwa gashi yanxu na gani da idona har namiji kike kawowa acikin gidan nan kuna aikata abinda kuka gadama,, ansha kawomin gulma da jita jita amma ban yarda ba gaskiya sai yanzu ,,,,ki ji tsoron Allah domin ina guje miki yin mummunan k'arshe! Duniya bakiji wani dad'i ba hakama lahira ba zakiji dad'i ba ".
Gwamma ta hararesa tareda jan mugun tsoki mtsssss! Sannan tace "ka gama tsohon munafiki wato an turoka ne domin kazo ka cimin mutunci ko,, wallahi kam baka isa ba kayi d'an k'arami da kai Lawwali maita kuma bazan daina ba! Duk ubanda zaka gayawa jeka gaya masa bana tsoron uban kowa ciki kuwa harda kai! Shege wanda baisan d'an uwa ba ".
Lawwali yayi hucin mai cikeda takaici da bak'in cikin Gwamma,,,sannan yace "Alal hak'ik'a na k'ara tabbatarwa da wanda yayi nisa bayajin kira acikin aikata masha'a da mummunan dabi'a,,, daga fad'in gaskiya ayau shine zaki cimin mutunci ki nunamin ni ban isa in gaya maki gaskiya ba,,, Allah ubangiji ya shiryeki yasa ki gane gaskiya gaskiya ce kuma k'arya k'arya ce ".
"aini ashirye nake kuma kowa shiriyar Allah yake nema bata mutum ba,,, ehehhh maita ce da kuma yin zina bazan daina ba koda kuwa mutum zai fad'i k'asa ya mutu har lahira! ".Cewar Gwamma cikeda jin haushin maganarsa da bala'i..
Lawwali yace "to yayi miki k'yau matuk'a duk dai abinda kikeyi marasa k'yawo,,, Allah yana sama yana kallonki kuma shi zai musu sakayya tun anan duniya ina k'ara tabbatar miki muddin baki daina aikata miyagun ayyuka ba,,, karshenki bazaiyi k'yawo ba !".
"kar yayi k'yau d'in ina ruwanka idan har nayi mummunan k'arshe? To idan aljanna taka ce ka hana in shigeta,,, kuma tun yanzu kazo kasa inyi mummunan k'arshe mara mutunci wawan banza dolo wanda babu tunani da nazari acikin kansa ".Inji Gwamma cikin takaici da haushi..
Lawwali ya tashi tsaye yana cewa "to tunda bak'yajin nasiha na k'yaleki,,, kije kiyita aikata duk abinda kika gadama babu abinda ya shafeni! ".Yana k'arasa maganar yayi tafiyarsa batare da ya tsaya ya saurarin irin martanin da zata mayar masa ba.
"aikin banza yima karen mak'wabta wanka mtssssssss kai har ka isa kace zakayimin wa'azi ko nasiha,,,, to wallahi ka kiyayeni idan ba haka ba barin ganin uwarmu d'aya ubanmu d'aya ina iya kasheka in cinye namanka d'anye! Kuma ba'a komai babu maija dani Gwamma mayya ".Inji Gwamma ta kama sambatu tana zage zage na cin mutunci da tozarci.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Baba Labbo ne zaune da Inna Tani suna fira cikeda matuk'ar farin ciki da nishad'i sosai,,, saboda su yanzu Alhmdlilah babu abinda suka nema suka rasa komai su Sagiru kawo musu sukeyi,,,, na dangane kayan masarufi da mak'ulashe abinci kala kala sukeyi wani buhun shinkafa,,, masara,,,wake da dai sauran kayayyakin abinci wani saiya tadda wani,,, nama sai sun ture da kuma kayan marmari..
Inna Tani ta karkace baki tace "Hhmmm maigida ashe dai Gwamma ta zama k'usurgumar mayya,,, shiyasa rannan ta zama macijiya ta koraka daga cikin gidan yayanka ".
Baba Labbo yace "aike wallahi lamarin akwai ban mamaki da al'ajabi da maigari yana gaya mana,,, ba kiga irin yadda mutane suka rikice suna hawaye ba!Wai ashe ta zama babbar mayya tafima uwarta shahara ".
"ai Allah yasa kanada k'arar kwana agaba da yanzu Gwamma macijiya ta lak'umeka zama guda,,, ni wallahi abin har mamaki yake bani wai cin naman mutane takeyi ".Inji Inna Tani tana kallon baba Labbo tana masa dariyar k'eta.
Baba Labbo yace "haka ne gaskiya da yanzu ina can cikin kabari kwance,,, aini yanzu ko bakin k'ofar gidan nan bazan iya k'ara giftawa ba saboda in tsira da rayuwata ".
Inna Tani ta bushe da dariya sosai tace "maigida akwai ka da tsoron bala'i,,, ai b'oye b'oye baya maganin mayyu saboda ko'ina kake suna ganinka,,, addu'a itace maganin mayyu kuma takobin mumini ce "............
0 comments:
Post a Comment