"Addu'a itace maganin mayyu kuma takobin mumini ce,,,, sannan mace mai yara k'anana da basu iya yin addu'a ba,,,, ya zama dole ta dinga yi musu addu'o'in neman tsari tana shafe musu jiki akodayaushe,,,, ba wai mace ta nuna son jiki ko k'yuya ba ".Inji Inna Tani,,, "tabbas maganarki gaskiya ce Tani,,, babu yadda zaka saki baki bakason yin addu'a sannan kace wani abin cutarwa bazai tab'a cutarka ba ".Cewar baba Labbo yana murmushi,,, Inna Tani ta dubesa tace "aini yanzu lamarin duniyar nan tsoro yake bani sosai,,, yanzu kaga mutum lafiya k'alau jibi ace maka ya zama mayye cin naman mutane yakeyi ko takeyi ".Baba Labbo yace "kwarai da gaske ma ai kinga yanzu idan da ace Gwamma lafiyarta k'alau,,,, bai dace ace na barta zaune ita kad'ai tana aikata abinda ta gadama ba ,,,,saboda naji ance yanzu har namiji yake shigowa cikin gidan nan yana tayata kwana,,, to daga barcin tare da k'ato saimi zai faru? Sai iskanci da abinda ba'a so shine zai iya biyowa baya "."Af ai iskanci da yin maita yanzu ya zama ruwan dare,,,,, saboda yanzu yanada wuya kaga wanda baya aikata d'aya daga cikin wad'annan abubuwan dana ambata,,,,, kaga kuwa saidai mu dage da yawan yin addu'a akan Allah ubangiji ya karemu daga muyagun k'addarori muda iyalanmu ".Inji Inna Tani cikeda matuk'ar sanyin jiki da natsuwa,,, baba Labbo yace "amin ya rabbi Tani lamarin mutanen yanzu sai a hankali,,,, ai Gwamma ta koyar dani darasin rayuwa idan kace ka faye shiga cikin abinda bai shafeka ba,,,, matsalolin rayuwa mutum zai jefa kansa ciki kuwa "."Hmmm maigida kenan wata rana kana bani mamaki sosai,,,, ai duk abinda ya shafi Gwamma ya shafeka saboda koba komai 'yar yayanka ce uwa d'aya uba d'aya ba lafiya bane,,, sannan kuma ko kwatance za'ayi sai dai ace yanzu d'iyar Mamman da Talatu,,, Mamman yayan Labbo mijin Tani mai wake kaga kuwa anan hannunka bai tab'a rub'ewa ka yanke kayar ,,,,ka dai k'yaleta ne saboda kaima tafi k'arfinka ne,,,, amma ako'ina akaje kaine ya kamata ka rik'eta amatsayinta na marainiya domin kaine dolenta ".Baba Labbo yayi dariya yace "babu k'arya a cikin maganarki Tani shiyasa nake k'ara sonki,,, saboda kinada natsuwa da hangen nesa Allah ubangiji yayi miki albarka kuma ya barmu tare "..
Inna Tani taji dad'in addu'arsa k'warai da gaske,,,, wani farin ciki da nishad'i ne ke wanzuwa acikin sassan jikinta gaba d'aya,,, tayi murmushi tace "amin amin maigidana ".
Firarsu suka cigaba da yi mai dad'i da ma'ana sosai,,, daga ganin yadda suke gudanar da rayuwar aurensu babu abinda suka nema suka rasa a cikin zamantakewarsu...
*********************
***Aliya ce matar Lawwali zaune tana tankad'ar garin tuwo,,, ga d'iyarta nan mai suna Hajara tana wasar k'asa agefe,,,, ita kuma uwar ta mayarda hankalinta kacokam wurin aikinta,,, can bada jimawa ba saiga sallamar Lawwali ya shigo cikin gidan,,, fuskarsa murtuk'e babu alamun fara'a ko walwala ana hango b'acin rai acikin k'wayar idanunsa ,,,,Aliya dai ta amsa masa sallamarsa cikin sanyin jiki ta kawo tabarma ta shimfid'a masa cikeda ladabi da girmamawa,,,, bayan ya zauna ne ta kawo masa ruwa masu sanyi cikin kofi ya d'auki ruwan yasha,,,, sannan yayi ajiyar zuciya yace "Alhmdlilah Allah ubangiji yayi miki albarka ".
Aliya tayi murmushi tace "amin baban Hajara amma mi ye yasa ka shigo cikin gida da b'acin rai?Har baka iya b'oye b'acin ranka kafin ka shigo cikin gida ".
Lawwali yaja dogon numfashi sannan yace "kede bari Aliya abin ne akwai matuk'ar b'acin rai da ban takaici,,,, wai nine zanje wurin yaya Gwamma in bata shawara akan abinda take aikatawa bai dace ba,, shine ta kama yimin fad'a da cin mutunci abin babu dad'in ji balantana saurare ".
"ayyah baban Hajara hak'uri zakayi domin koba komai itace sama da kai,,, kuma yayarkace kaine ya zama dole kayi mata biyayya kuma shiriya tana hannun Allah,,, da kad'an kad'an sai kaga ta daina yin duk abubuwan da takeyi ".Inji Aliya cikeda matuk'ar lallashi da ladabi..
Lawwali ya nisa yace "Aliya kenan bakisan ainahin halayyar yaya Gwamma ba,,, mace ce mai matuk'ar taurin kai da tsattsauran ra'ayi kuma duk abinda ta sama gaba komai rashin k'yawonsa,,,, ba zata daina ba yanzu ma bari in sanardake gaskiyar lamari maigari yace idan aka kama mayyu akashesu! Sannan Ummaru d'an Sala mafarauci yawon nemanta yakeyi ruwa a jallo saboda itace ta kashe masa iyayensa da yayan babansa,,,, ta cinye namansu ni kuwa ina jiye mata mummunan k'arshe da mugun hukunci ".
Aliya tace"hmmmm amma kam wannan hukuncin yayi tsauri da yawa gaskiya,,,, ana kama mutum kenan ana kashesa! To ka cigaba da hak'uri kana zuwa kana lallashin yaya Gwamma har ta daina maita,,, kafin hukuncin maigari ya hau kanta akasheta abar mana abin gori da fad'a,,, surutu,,, gulmace gulmace ko munafurci ".
"abin gori da surutu na nawa kuma saboda ni idan na fita waje,,, har nunani akeyi ana zund'ena da nunena da cewa ga k'anen Gwamma mayya can tafe,,, wasu ma har guduna sukeyi wai saboda basu yarda niba mayye bane domin Innarmu wai gadon maita tabar mana! ".Cewar Lawwali cikeda matuk'ar takaicin yadda rayuwar Gwamma ke tafiya tana cin naman mutane da aljannu!.
Aliya tace "hak'uri zaka k'ara yi ai mutane iyawa dasu sai Allah,,, sannan ya zama dole ka toshe kunnuwanka daga jita jitar mutane da tseguminsu,,,,,,saboda haka ka daina damuwa akan anyi ance da surutun mutane ".
"idan banyi hak'uri ba mi zanyi musu? Kedai Allah ubangiji ya sawwak'a yasa mu dace ".Inji Lawwali..
Aliya tace "amin baban Hajara Allah ubangiji ya sanyaya maka zuciyarka ".
Aliya ta cigaba da yi masa kalamai masu dad'i,,, sannan kuma ta k'ara nuna masa muhimmanci hak'uri da juriya akan zamantakewar rayuwar duniya,,,,, ta dinga lurar dashi ya dinga toshe kunnuwansa daga jita jitar mutane......
Allah ubangiji yaba kowa abokin rayuwa nagari..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN SHEKARU HUD'U*
Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda kama sauran mayyu,,, da suka addabi rayuwar mutane ana kashewa,,, Ummaru ya kama mayyu kusan ishirin yana kashewa acikin wad'annan shekarun da suka wuce,,, yayi yayi ya kama Gwamma shahararriyar mayya amma ya kasa saboda ita yanzu ta k'ara shahara da gunguma akan harakar maita! Duk wanda takeso take kwad'ayin namansa kamesa kawai takeyi,, duk da yake Lawwali yayi zuwa kusan goma yana yi mata nasiha akan ta daina maita! Amma wanda yayi nisa bayajin kira sai dai taci masa mutunci tana zaginsa,,, zuwa na goma da yayi tayi masa kashedi da inya k'ara takowa gidanta da sunan wa'azi saita kashesa ta cinye namansa! Yabar ganin uwarsu d'aya ubansu d'aya,,, jin ta fad'i haka dole yasa Lawwali yajawa k'afafunsa linzami ya daina zuwa kwata kwata saboda yasan duk abinda Gwamma tace tanayi,,, to tabbas zata iya aikatawa domin yasan halinta batada tsoro tanada dakakkiyar zuciya.
To acikin wad'annan shekarun ne Gwamma ta haifi 'yan biyu mace da namiji da Sule saurayinta,,, namijin sunansa Hassan macen sunanta Suhaila,,, bayan yaran sun fara girma da tasawa taga ai amfanin Sule ya k'are koba komai tagama morarsa,,, gashi taga yanzu shima har nasiha da wa'azi yakeyi mata akan ta daina maita! To ita kuma da mutum ya dameta akan tabar maita gara yahau risho da wandon leda,, ganin da tayi Sule yana neman takurawa rayuwarta yasa dole ta kame masa kurwa ta mayar ita zakara,,, arannan ne ta yanke zakaran ta cinye abinta tasha ruwa tayi gyatsa.
_Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un! Allah ubangiji ya rabamu da aikata masha'a da kuma biyewa *SON ZUCIYA*..._
Aka wayi gari Sule ya mutu abin kamar almara,,, akayi masa wanka aka kaisa makwancinsa na gaskiya,,, Allahu Akbar duniya ba matabbata bace duniya mai cikeda bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,, Gwamma ta cigaba da gudanar da rayuwarta cikeda kwanciyar hankali da jin dad'i,,,tareda da kula da yaranta cikeda matuk'ar k'aunarsu batason ko k'uda ya tab'asu idan da son ranta ne,,, babu abinda take so da k'auna fiyeda yaranta.
Ita dai cigaba da cin naman mutane dana aljannu kawai takeyi wata rana ta mayarda kurwar mutane zakara ko rago taje can kasuwar wani gari,,, inda ba'a santa ba tana samun kud'inta cikeda wayo da 'yan dabaru ta haka ne take samun kud'ad'e tana ciyarda yaranta da kashewa kud'i .......
_Share &Comments_
[7/6, 6:05 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 27*
**Ta haka ne take samun 'yan kud'ad'e tana kashewa da kuma kula dasu Hassan,,, haka dai take gudanar da rayuwar gidan da maitarta,,,, Lawwali kuma ganin irin walak'anci da korar kare da Gwamma tayi masa ya watsar da ita gaba d'aya ya fita harakarta,,, saboda yasan tunda ta bud'i baki tace zata kashesa to tana iya kashesa abanza da yofi yabar yaransa da matarsa cikin k'unci da tsananin maraici,,,, baba Labbo ne dama ya tsorace gameda lamarin Gwamma mayya,,, domin tun lokacin da yaje domin ya dawo da ita gidansa ta rikid'a ta koma macijiya ta koresa,,,,,to tun daga lokacin nan bai sake giftawa ko bakin k'ofar gidan nan ba,,,, balantana yaje ya shiga cikin gidan kunsan yadda baba Labbo yakeda masifar tsoron mutuwa da mayyu!. Ummaru mafarauci dai yana nan yana cigaba da bibiyar duk wani motsi na Gwamma,,, sannan duk inda taje yana hankalce da ita yana kallonta babu inda zataje ko tayi wani motsi ba'a kan idon Ummaru ba,,, ya damu sosai ta yadda take azabtar da mutane da cin namansu amma ya gagara kamata! Shiyasa dole wata rana yayi zaune yana tagumi da bak'in cikin rashin kama Gwamma mayya,,, domin zaluncinta da cin amanar mutane sai k'aruwa yakeyi,,, bata tunanin abinda zaije ya dawo a rayuwa bata tunanin ai wata rana dubunta zai iya cika,,, bata tunanin wata rana zata bar duniya baki d'aya taje can ta girbi abinda ta shuka? Ita dai Gwamma gatanan dai kamar ba mutum ba zuciyar nan babu d'igon imani da tausayi,,, ta k'ek'eshe zuciyarta daga barin tsoron kowa bata gudun abinda zai faru,,, bata tunanin kamar yadda aka kama sauran mayyu 'yan uwanta to ita ana iya kamata!.
Mutanen gari kuma kowa ya shiga taitayinsa,,, saboda kada su afka cikin tarkon Gwamma mayya,,,, kowane daga cikinsu ya tashi tsaye tareda dagewa da yawan addu'ar Allah ubangiji ya kawo musu k'arshen zaluncin Gwamma,,, domin susan Ummaru yana iya bakin k'ok'arinsa na ganin ya kamata amma abin yaci tura! Ya kasa kamata saboda yadda takeda k'arfin sihiri da gunguma acikin harakar maita,,, kunsan ta zarce mahaifiyarta Inna Talatu awurin shahara da bunk'asa domin ita har aljannu tsoronta sukeji balantana bil Adama,,,, bata shakkun tunkarar kamun kurwar kowa acikin garin Gumi,,, Ummaru kawai ne take d'an tsoronsa domin kada wata rana dubunta ya cika ya chafketa!.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Ummaru ne zaune yayi tagumi cikeda matuk'ar bak'in ciki da damuwar rashin kama Gwamma,,, ya rasa yadda zaiyi ya kamata.
Salma ce ta jaye hannun Ummaru daga yin tagumin da yakeyi,,, sannan ta dubesa tace "lafiya baban Husna kana tagumi?Babu k'yawo ka daina sama kanka damuwa ".
Ummaru ya d'ago idanunsa da sukayi jawur akan damuwa,,, yace "Salma ina cikin damuwa wai ace wadda tayi sanadin mutuwar iyayena da baba Labaran,,, na kasa kamata sai yawo da hankali takeyimin ta mayardani mahaukaci ko mara sa'a a rayuwa ".
Salma ta kallesa cikeda matuk'ar tausayawa da k'auna matuk'a,,, tace "haba farin cikin rayuwata miyasa zaka damar da kanka,,,akan abinda akodayaushe akowane lokaci kana iya kamata,,,kai bakasan komai yanada lokaci da k'addara ba? Idan Gwamma ce zaka kamata duk ta gama guje gujenta da b'oye b'oyenta sai dubunta ya cika! ".
"ni ba haka naso ba so nayi in kamata yanzu in gana mata azaba,,, sannan daga baya in kasheta kamar yadda ta kashemin iyayena! ".Cewar Ummaru d'an Sala mafarauci.
Salma tace "kayi hak'uri maigidana zaka d'auki fansar jinin mahaifanka,,, kuma ka daina saka damuwa da tunanin abinda bana damuwa ba,,, ni nasan komai daren dad'ewa zaka kama Gwamma ka kasheta har lahira! Lokaci yana nan zuwa ka daina damuwa ".
Ummaru yace "to babu damuwa Ummu Husna,,,, zan daina saka damuwa acikin raina da zuciyata ".
"da kam yafi baban Husna ka saki zuciyarka,,, komai yanada lokaci kuma zaizo ya wuce kamar ba'ayi ba ".Cewar Salma cikeda matuk'ar lallashi.
Ummaru yace "tabbas haka ne gaskiyar maganarki ".
Salma ta cigaba da bashi maganganu masu sanyi,,, da kuma lallashinsa da yayi hak'uri akowane lokaci zai iya kama Gwamma..
*********************
**Bayan shekaru goma ne alokacin ne su Hassan suka girma,,, sunada shekara ashirin da uku,,,, Suhaila ta samu miji mai k'aunarta tsakani da Allah ya aureta,,, amma saida suka kafta tashin hankali da bala'i da Iya Gwamma domin nuna tayi ita ba zata aurar da Suhaila ga Salihu ba,,,, shi kuma dayake yana sonta itama tana sonsa shiyasa ta nace saita auresa,,, babu irin kashi da zagin da Suhaila bata sha ba akan son da takeyiwa Salihu saboda itama Gwamma so takeyi ta gajeta a cikin maita! Ita kuma tak'i bin umurninta domin bataga wata ribar da mayyu suke samu ba idan suka zama mayyu,,, ganin irin haka ne yasa shima Hassan ya bid'i kud'in aure ya fara kasuwanci,,, ya nemi wata Aisha nan mak'wabciyarsu yayi aurensa,,, sannan ya kwashi matarsa ya samu wani gida madaidaici ya saye suka shige shida matarsa hankalinsu kwance..
Iya Gwamma ganin d'iyanta sun watse sun barta akan bala'inta da masifarta,,,, rana guda ta kama zaginsu tare da tsine musu albarka su suna can gidajensu basusan abinda yake faruwa ba,,,,, to dayake batada rik'o arayuwarta nan da nan ta fita harakar d'iyan tareda cigaba da cin naman mutane da aljannu,,, babu tsoron Allah ko kad'an a cikin zuciyarta..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*CIGABAN LABARI*
Mama Sa'ima da Alhaji Suleiman ganin yawon Maryam yayi yawa,, dole yasa uwar take sakawa 'yarta idanu da hana mata yawon zuwa ko'ina idan ba makaranta ba,,, saboda gudun kada mayyu su kamata basusan sun riga sunyi fad'a da Iya Gwamma k'usurgumar mayyar da ta addabi rayuwar mutane shekara da shekaru ba,,, Ummaru ya kasa kamata alamar sai taci zamaninta,,, shi dai bai hak'ura ba yana nan yana bibiyar rayuwarta kuma yasan yanzu duk d'iyanta sun gudu sun barta,,, saboda mummunan dabi'ar da take aikatawa wato yin maita da rikid'e rikid'e da tsafe tsafen da bayada k'yau ko addinin musulunci..
Mama Sa'ima ce zaune tana tsintar k'asa acikin shinkafa,,, Mubarak yana zaune gefenta yana tayata suna fira cikin natsuwa da kwanciyar hankali..
Alokacin ne Mubarak ya dubi Mama Sa'ima yace "amma yau ana zafi sosai agarin nan,,, baba yana can kasuwa kuwa gashi akwai rana sosai ".
"zafi ai lokacinsa ne Mubarak ai fita kasuwa ya zama dole ga Alhaji,,, saboda kaga yanzu idan bai fita ba yaran yanzu masu tsaron shago ba kowanensu keda amana ba,,, sai 'yan kad'an daga cikinsu sukeda amana da gaskiya ".Cewar Mama Sa'ima.
Mubarak yace "ai Alhaji yanada hak'uri da juriyar zama da mutane,,, musamman idan mutum ya samu masu tsaron shago ko marasa gaskiya sai yakai zuciyarsa nesa ko ya koresu".
Mama Sa'ima tayi murmushi tace "ai zaman duniya iyawa ne gaskiya idan baka iya zama da mutane sai zama ya gagareka da mutane,,,,, mutum yazo yana fad'a da mutane kowa ya tsanesa,,, ai rayuwar da kake ganinta gaba d'aya sai mutum yayi hak'uri da juriya a rayuwa ".
"haka ne gaskiya Mama ni abinda yake bani tsoro da takaici shine,,, yadda zamanin nan namu ya lalace kowane ka gani ya zama mayye ko mayya,,, saboda tsananin kwad'ayi da son abin duniya da dogon buri! Ni abin yana cimin tuwo a k'warya bansan yadda abubuwan suke faruwa ba? ".Cewar Mubarak cikeda jimamin abinda ke faruwa cikin gari.
Mama Sa'ima tayi murmushi taja numfashi,,,, sannan tace "ai lamarin mayyu sai addu'a saboda yafi k'arfin Al'umma,,, saboda haka koni abin yana damuna babu yadda zamuyi sai hak'uri akan lamarin mayyu! Sai addu'a da neman tsari daga sharrinsu".
Mubarak yace "Allah ubangiji ya karemu daga sharrin masu sharri a cikin mutane da aljannu ".
"Amin ya rabbi Mama ".Inji Mubarak.
*BAYAN KWANA BIYU*
Bayan faruwar wannan al'amarin tsakanin Iya Gwamma dasu Fatima,,, na rashin mutuncin da Fadila tayiwa Iya Gwamma saiya zamo iyayensu Fatima sun hana musu zuwa ko'ina kamar yadda aka hanama Maryam,,,, domin aran nan da suka kama yiwa su Fadila fad'a kamar zasu dokesu da yake Fatima tanada tsoro sosai shine ta sanardasu irin abinda ya had'a su da Iya ta aikesu,,, da kuma rashin kunyar da Fadila tayi mata duk saida ta gaya musu.
To sunsha fad'a sosai rannan akan rashin kunyar da Fadila tayi ma Iya Gwamma,,,,, kamar abasu mugun kashi saboda abinda Fadila tayima Iya Gwamma,,,,,Fadil yayan Fadila kamar ya bata kashi akan rashin kunyar Fadila tayi yawa da kuma tsiwarta..
Amma Iyayennasu mata suka hana ya bugeta saboda sunsan bugu baya horar da yara,,, sai dai addu'a da yawan jama yaro kunne ,,,to wannan maganar dai anan atsakaninsu Iyayen mata suka bar maganar,, basu sanarda Iyayen maza ba saboda sunsan sune da laifi,,, sannan su mazajen zasu yiwa fad'a kunsan ance laifin d'a baya wuce mahaifiyarsa.
Ana nan dai kwatsam! Fadila da Fatima rashin lafiya ya kamasu kusan atare,,, ita Fatima amai da zawo ne takeyi duk ta rame tayi bak'i sannan ta fige babu k'yawon gani,,, ita kuma Fadila ciwon zazzab'i da ciwon kai ne ya kamata sannan ga wasu k'ananan k'uraje nan da suka fara fitowa a jikinta,,,ciwon yayi matuk'ar ramar da ita yasa ta fita cikin hayyacinta k'warai da gaske,, Iyayensu hankalinsu yayi k'ololuwar tashi sosai,,, babu abinda sukeyi sai kukan zuci dana zahiri ga bak'in ciki da k'uncin rayuwa.........
_Share&Comments_
[7/9, 11:55 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 28*
Babu abinda sukeyi sai kukan zuci dana zahiri ga bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,, saboda suna matuk'ar k'aunar d'iyansu da gaskiya basa son ko k'uda ne ya tab'asu idan da son ransu,,, haka dai suka cigaba da jinyar yaransu tareda da basu kulawa ta musamman,,,, batare da sanin iyayensu maza ba.
Ab'angaren gidansu Maryam itama ta kamu da tsananin rashin lafiya sosai,,, wato ciwon ciki mai tsananin gaske da hanasu barcin dare shine Iya Gwamma mayya ta tura mata,,, alokacin da ciwon cikin ya fara tashi Mama Sa'ima da Mubarak hankalinsu yayi k'ololuwar tashi sosai ga zuciyarsu sai bugawa takeyi da k'arfi da k'arfi! Kallo d'aya xaka yi musu kasan basa cikin kwanciyar hankali da jin dad'i,,,idan ciwon cikin Maryam ya taso har shure shure takeyi da kukan zafi da rad'ad'in ciwo,,,, su kuma su Mama Sa'ima babu mai kama wani akan hawaye kuka kawai sukeyi cike da tsananin damuwa da bak'in cikin rayuwa,,, wata rana idan ciwon ya lafa mata harda wasa takeyi da cin abinci sosai,,, idan ciwon ya tashi kuwa haka zata kama yin fisge fisge da shure shure kamar mai aljannu har kumfa ke fitowa daga cikin bakinta,,, saboda tsananin bala'in sihiri da magagin ciwo,, kunsan wani ikon Allah shine dukansu Allah ya mantar dasu su sanar da Alhaji Suleiman irin ciwon da yake damunta,,, domin shi bayada masaniya akan komai duk lokacin da baya nan gida to alokacin ne ciwon Maryam ke tashi..
Aranar nan suna zaune gefe saman tabarma sunyi tagumi,,, ga hawaye sai kwaranya yake daga idanun Mama Sa'ima,,, shi kuma Mubarak idanunsa sunyi jawur kamar barkono saboda damuwa da bak'in ciki,,, alokacin ne ya bud'i baki dak'yar yace mata "Mama inaga fa matsalar nan ya kamata asanar da Alhaji duk abinda ake ciki gameda ciwon Maryam,, idan muka sanardashi nasan zaice muje asibiti idan mukaje can duk abinda ake ciki gameda ciwon Maryam zasu sanar damu,,, ko mi ne ne shawararki? ".
Mama Sa'ima ta fyace majina sannan tace "haka za'ayi Mubarak domin barin kashi a a ciki baya maganin yunwa,,,, kuma ya zama dole babanku yasan wannan abu ".
"nima shine na gani amma munyi shiru munata b'oyon ciwo,,, kamar bamusan zafinta ba idan shiru yayi yawa gaskiya wani ciwon yana iya shigowa bamu sani ba ".Inji Mubarak cikeda jimamin rashin lafiyar k'anwarsa Maryam.
Mama Sa'ima ta nisa tace "duk abinda ka fad'a haka ne Mubarak,,, babu k'arya a cikin maganarka Allah ubangiji yaba Maryam lafiya da itada dukkan kullumin musulmi baki d'aya,,, amma ni agaskiya wannan ciwon nata yana matuk'ar bani tsoro da fargaba,,, sai ina ganin kamar ba ciwon Allah da annabi bane ".
"amin Mamanmu kiyi hak'uri karkice haka domin kada kiyi sab'on Allah,,, dukkan abinda kikaga ya samu bawa to muk'addari ne daga Allah,,, bawa bai isa ya cutar da d'an uwansa bawa ba sai yardar Allah mad'aukakin sarki,,, shiyasa akeson mutum ya kasance mai hak'uri da tawakalli akan lamuran duniya,,, da iznin ubangiji Allah Maryam zata samu lafiya ta warke garau kamar bata tab'a yin wannan cuta ba " .Cewar Mubarak cikeda da tunani da hangen nesa.
Mama Sa'ima tace "haka ne Mubarak Allah ubangiji ya k'ara mana juriya da hak'uri da kuma tawakalli da dukkan k'addarar da zata samemu,,, ita kuma Allah ya bata lafiya ".
Mubarak yace "Amin ya rabbi ".
Mubarak ya cigaba da kwantar mata da hankali,,, tareda bata hak'uri da kalamai masu sanyaya zuciyar mai sauraro..
*Allah ubangiji ya bamu d'iya nagari masu tausayinmu ,,,,da yi mana addu'a idan babu mu a duniya*.
*********************
**Ummaru da Kabiru ne zaune suna firar duniya data mayyu,,, cikeda matuk'ar natsuwa da kwanciyar hankali..
Kabiru ne ya dubi Ummaru yace masa "abokina kana fa k'ok'ari sosai sai rage mana mayyu kakeyi a cikin garin nan,, amma har yanzu ka kasa kashe Gwamma mayya wadda ta addabi rayuwar mutanen gari da k'auyukkan dake kewaye damu ".
Ummaru d'an Sala mafarauci yace "hmmm Kabiru abin ba'a cewa komai wlh,,, kadai sha kuruminka da yardar Allah k'arshen Gwamma mayya ya kusa zuwa,,,, ai komai b'oye b'oyenta na kusa kamata in kasheta ai jinin mahaifana bazai tab'a zuba a banza ba ".
Kabiru yace "haka ne gaskiya ai ka rage mana annoba cikin garin Gumi,,, saboda ka kashe mayyu fiyeda d'ari kaga kuwa sauran da suka rage nasan basuda yawa sosai,,, ai barin irinsu Gwamma acikin Al'umma bala'i ne da tashin hankali! ".
"wama zai barta a raye cikin duniya,, ai idona idonta k'aryarta ta k'are,,, sainayi mata kisan gillah saina banbance mata tsakanin wuta da ruwa,,,, har abada babu tausayi ko rahama atsakanina da ita ".Inji Ummaru d'an Sala mafarauci cikeda tunanin rayuwarsa ta baya tareda da iyayensa.
Kabiru ya dafa kafad'ar Ummaru cikeda tsananin tausayin abokinsa,,, domin shi har azuciya yana matuk'ar k'aunar Ummaru.
Sannan yace "kayi hak'uri Ummaru domin shi mai hak'uri wata rana zai cimma nasara da ribar hak'urinsa,,,,, sannan tabbas da yardar Allah zaka kashe Gwamma mayya kamar yadda ta kashe maka iyayenka! ".
Ummaru yace "na sani ai shiyasa kaga akullum akowane lokaci acikin shiri nake,,, domin bana fatar ranar ta riskeni ba ashirye ba saboda irinsu Gwamma shahararrun mayyu dole mutum yayi musu shirin tunkararsu na musamman ".
"wannan haka yake gaskiya ai rana dubu ta b'arawo rana d'aya tamai kaya ".Inji Kabiru.
Ummaru yace "haka ne tabbas ".
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Ganin irin ciwonsu Fatima yak'i ci yak'i canyewa yasa,,, uwayen hankalinsu ya k'ara d'unguma sosai gabansu sai fad'uwa yakeyi yana bugawa rassssss! Rasssss!.
Umma Nusaiba ce ta dubi Mama Nafisa cikeda raunin zuciya da damuwa,, tace "Nafisa wannan ciwon yayi yawa fa ya kamata mu sanardasu baban Fadila domin akaisu asibiti da gaggawa,,, kada muyi shiru muzo mu rasa yaranmu akan zurfin ciki da gudun laifi wurin mazajenmu ".
Mama Nafisa ta d'ago idanunta da sukayi ja akan kuka da damuwa,,, tace "ai ya zama dole mu sanardasu komi domin gujewa afkawa cikin nadama da dana sani,,, ni wallahi yanzu k'irjina sai ciwo yakeyi ga wani abu daya tokare min k'irji mai nauyi,,, sai nake ganin kamar bazasu tashi ba mutuwa zasuyi! ".
"Subhanalillah! Nafisa ba'a yanke k'auna daga rahamar ubangiji kedai keyi fatar samun sauk'i da waraka,,,nima hankalina ba kwance yake ba amma ya zamuyi sai hak'uri da dangana,,, da kuma addu'ar Allah ubangiji ya basu lafiya ".Inji Umma Nusaiba cikeda matuk'ar sanyin jiki da damuwa.
Mama Nafisa tace "amin amin ya rabbi haka ne gaskiya lamarin duniya sai hak'uri da juriya ".
"bari adauko waya akira d'aya daga cikin mazajenmu ".Cewar Umma Nusaiba ,,,,, ta tashi tsaye ta shige cikin d'akinta,,ta jima kad'an tana waya da baba Nura tana sanardashi abubuwan dake faruwa,,, baba Nura yace mata gashinan nan zuwa yanzu yanzun nan karta damu,,, tace to sannan ya katse wayar ita kuma ta fito waje tace "Nafisa ga baban Fatima nan tafe yanzu je ki shirya ki fito kafin yazo,, yana zuwa wucewa kawai zamuyi ".
"to yaya Nusaiba ".Inji Nafisa ta tashi tsaye ta shige cikin d'akinta domin ta shirya.
Babu b'ata lokaci su dukansu suka shiryo cikin kayansu masu k'yau,,, suka tsaya jiran baba Nura bada jimawa ba saiga sallamarsa shida Fadil sun shigo kusan atare suka shigowa daga cikin gidan matan suka amsa musu sallama ,, babu b'ata lokaci aka kwashi su Fatima aka sanya cikin motar baba Nura,,,Fadil ya shiga gaban mota su kuma su Mama Nafisa a bayan mota,, baba Nura yaja motarsa ya nufi hanyar zuwa asibiti..
Suna zuwa asibitin aka amshi su Fatima domin afara basu taimakon gaggawa,,, gadajensu suna kusaga juna itama Maryam har babanta da mamanta sun kawota asibiti,, baba Nura yana ganin Alhaji Suleiman suka yi musabaha suka gaisa cikeda matuk'ar girmamawa da nishad'i sosai..
Umma Nusaiba ce ta dubi Mama Sa'ima tace"a'aaaa Sa'ima kece a cikin asibiti,,, wa ye ba lafiya? ".
"hmmm Maryam ce babu lafiya wlh ".Inji Mama Sa'ima.
Umma Nusaiba tace "to Allah ubangiji ya bata lafiya mu kuma su Fadila da Fatima muka kawo basuda lafiya sosai ".
Sai da gaban Mama Sa'ima ya buga da k'arfi d'immmmm sannan ta tattaro dauriya tace "to 'yan uku duk sun kamu da rashin lafiya alokaci guda,,, Allah ubangiji ya basu lafiya yasa kuma ba abinda nake tunani bane ya faru dasu ".....
[7/10, 12:17 AM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*MAYYA CE FANS hak'ik'a ina godiya matuk'a da comment d'inku masu dad'i sosai,,, Allah ubangiji yabar k'auna da zumunci har abada nagode masoyana*
*PAGE 29*
Saida gaban Mama Nafisa ya buga da k'arfi rassssss! Hankalinta yayi k'ololuwar tashi sosai zuciyarta tana yimata k'una da tafasa,,,, ta mik'e tsaye cikeda matuk'ar fargaba da tashin hankali tace "ban gane mi kike nufi da Allah yasa ba abinda kike tunani bane ya faru? "."Nima kaina ya d'aure wlh,,, na kasa gane inda maganarki ta dosa ".Inji Umma Nusaiba cikin tsoro da fargaba akan rashin lafiyarsu Fadila. Mama Sa'ima tayi shiru na tsawon lokaci sannan can tayi doguwar ajiyar zuciya tace "yanzu kuwa zanyi muku bayani yadda zaku fahimta sosai,, ina nufin Allah yasa ba mayya ce ta kamesu ba saboda wannan lokaci na yanzu yanada hatsari sosai,,, musamman ga yara su rink'a fita yadda suka gadama batare da mayyu sun kamesu ba "."Hmmm Allah ubangiji yasa ba mayya ce ta kamasu ba,,, dako mun shiga uku mun lalace! Wayyo ni Allah kaiconmu da wannan mummunan al'amarin daya samemu ".Inji Mama Nafisa cikeda da tashin hankali da *RUD'ANI*,,,,Umma Nusaiba tayi matuk'ar ajiyar zuciya da k'arfi! Tace "ina lillahi wa inna ilaihirraji'un! Dako haka ne gaskiya muna cikin matsalar rayuwa,,, saboda yadda mayyu suke addabar mutane agarin nan ya wuce misali,,, su kashe mutum su cinye namansa ba'a bakin komai yake ba "."karku damu idan Allah ya yarda abin zai zo mana cikin sauk'i sosai,,, zasu samu lafiya insha Allahu ".Inji Mama Sa'ima cikeda matuk'ar sanyin jiki da zullumi,,, Umma Nusaiba tace "to Allah ubangiji ya basu lafiya,,, ya kuma yaye musu abinda ke damunsu "."Amin ya rabbi ".Cewar Mama Nafisa cikin fargaba da zullumi..
*BAYAN KWANA UKU*
Jikinsu Maryam baiyi wani sauk'i ba gaskiya,,, saboda ciwon ya k'ara tsananta sosai sun k'ara bak'i da ramewa k'warai da gaske,, duk mai imani idan yayima su Fadila kallo d'aya saiya tausaya musu,,, musamman akan yadda ciwon yake hanasu barcin dare da iyayensu,,,, idan ciwonsu ya tashi har kuwwa da kururuwar zafin ciwo da rad'ad'i sukeyi! Duk asibitin gaba d'aya saiya gameda kuwwarsu da ifface iffacensu,,, kowa da yake asibitin saiya tausaya musu har zuwa ganinsu akeyi akan matuk'ar tausayawa rayuwarsu Fadila,,, ni kaina ganin yadda suka k'anjame da ramewa saida suka bani tausayi sosai,,, an canza musu yanayin kamanni sun koma kamar skeleton babu k'yawon gani,,, ganin haka ne yasa hankalin iyayensu mata da maza ya k'ara tashi fiyeda misali.
Suna zaune duk sunyi jugum sun fad'a duniyar tunani! Tashin hankali da bak'in cikin ne bayyane afuskokinsu k'arara saboda rashin natsuwa da kwanciyar hankali duk sun rame sosai. Can saiga doctor Sageer ya fito daga cikin office d'insa,,, yazo wurinsu Alhaji Suleiman dasu baba Nazifi ya kallesu na tsawon lokaci yana nazari can ya bud'i baki yace "Alhaji kaine baban Maryam? "(dayake yasan Alhaji Suleiman tun dad'ewa ).Alhaji Suleiman yace "nine Likita bokan turai ".Sageer yayi murmushi sannan yace "to ina iyayensu Fatima Nura da Fadila Nazifi suke? ".Sukace"gamu nan "atare da juna.
"OK i want see you now all of you,,, muje office akwai maganar da nakeson in sanardaku mai muhimmanci ".Inji doctor Sageer bai tsaya jiran jin maganarsu ba,, ya k'ara gaba su baba Nura da Alhaji Suleiman suka mik'e tsaye sukace matansu su jirasu yanzu zasu fito,,,, su Mama Sa'ima sukace to babu matsala Allah yasa muji alkhairi,,, baba Nazifi yace "amin "suka nufi office d'in doctor Sageer da saurinsu.
Suna shiga suka iske doctor Sageer saman kujera ga takardu masu yawa asaman table,,, yana rubuce rubuce sallamar da sukayi ne yasa ya d'ago kansa ya amsa musu cikin sakin fuska da walwala,,, yayi musu bismillah dasu zauna saman kujerin dake cikin office d'insa suka zauna.
Yayi musu duba na fahimta da natsuwa sannan yayi ajiyar zuciya yace "Alhaji Suleiman ina fatar zaku saurareni da k'yau kuyimin fahimta na natsuwa da ganuwa,,, sannan kuyi hak'uri da irin kalaman da zasu fito daga bakina ".
Alhaji Suleiman ya dubi baba Nura,,, shima baba Nura ya dubi Alhaji Suleiman sannan sukace atare "insha Allahu zamu fahimceka sannan duk abinda Allah ya k'addara mai k'yau ne ".Shi dai baba Nazifi babu abinda yace kansa aduk'e yake,,, saboda k'irjinsa sai zafi yakeyi masa sosai ga wani irin zogi da rad'ad'i da zuciyarsa keyi masa.
Doctor Sageer ya numfasa yace "agaskiya ciwon yaranku bana asibiti bane,,, domin munyi bincike bincike ta hanyoyi da dama saboda mu gano kan matsalar ciwonsu ko bakin zaren,,, amma ciwonsu yak'i ci yak'i canyewa sai k'ara cigaba yakeyi saboda haka amatsayina na doctor ina baku shawarar,,, da kuje gida ku gwada na malamai ku gani ko za'a dace ".
"Alal hak'ik'a munji dad'in bayaninka da yardar Allah zamuje mu gwada na malamai ".Inji Alhaji Suleiman cikeda matuk'ar sanyin jiki da fargaba.
Baba Nazifi ya bud'i baki dak'yar cikin rashin kwanciyar hankali da tashin hankali! Yace "babu wani taimakon da zaka iya yi mana ayanzu ".
Baba Nura ya juyo ya dubi baba Nazifi yace "haba Nazifi miyasa bakada hak'uri ne,, bakaji bayanin da yayi mana bane ko baka gamsu da bayaninsa ba? ".
Doctor Sageer ya tari numfashinsu yace "kayi hak'uri Malam Nazifi insha Allahu idan kuka gwada na islamic za'a dace,,, kudai ku dage da yawan addu'a akan Allah ubangiji ya basu lafiya "."Amin amin doctor Sageer mun gode k'warai da gaske Allah ubangiji yabar zumunci ".Inji Alhaji Suleiman.
"Amin ".Cewar baba Nura doctor Sageer ya basu hannu d'aya bayan d'aya sukayi sallama da juna,,, sannan su baba Nura suka fice daga office d'insa.
Kai tsaye wurin matansu suka wuce direct batare da b'ata lokaci ba,, suka sanarda iyalansu an sallamesu daga asibiti sun fara had'a kayansu kenan saiga nurse Umaima ta kawo musu takardar sallama,,, daga wurin doctor Sageer itace ta tayasu suka gama had'a kayayyakinsu duka,,, sukayi mata godiya sosai sannan suka shige cikin motocinsu sunka nufi hanyar komawa gidajensu,,, cikin rashin kwanciyar hankali da jimamin ciwon yaransu.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Iya Gwamma ce ta aza tukunyar tsafinta tsakar gida,,,,tana ta tsubbace tsubbacenta ga wasu irin surutai da takeyi na sihiri marasa dad'in saurare da ji,,, wani irin tururin hayak'i da rugugin tsawa fasss fasss fasss! Ya bayyana da k'arfin gaske ga wata irin razananniyar guguwa ta taso da k'arfi ta game wurin yadda ko tafin hannu ba'a iya gani akan duhu! Idanun Iya Gwamma sukayi jawur kamar wuta halshenta ya zazzago ya k'ara tsawo kamar maciji,,, jikinta gaba d'ayansa gashi ya tsiro zago zago kamar dodanniya! Can dai guguwar ta tsaya cak ta daina yawo tsawa da hayak'i suka tsaya wuri d'aya,,, tayi nuni da hannunta zuwa cikin tukunyar wani irin bak'in abu ya shige cikin tukunyar batare da b'ata lokaci saiga photonsu Maryam ya bayyana k'arara acikin tukunyar,,, duk abinda ya faru dasu tun daga lokacin da ta tura musu ciwon da kuma kaisu asibiti da komai ma saida ta gani da idanunta!.
Wata irin mahaukaciyar dariya ce ta bushe da ita sannan tace"hhhhhhhh saini Gwamma d'iyar Talatu k'usurgumar mayya na rantse da jinin mahaifiyata da kuma gadon maita! Yara yanzu kuka fara wahalar ciwo akan rashin kunyarku,,, musamman ke Fadila babu uban da ya isa ya hana in kasheki! In kashe ki!! In kashe ki!!! ".
Ta sake karanta d'alamisai na tsafi da sihiri,,, gidan gaba d'ayansa da tukunyar suka kama rawa da girgiza da k'arfi! Ga wata irin wuta jawur da ta tsago akan tsakiyar tukunyar can batare da b'ata lokaci ba boka LOK'ORO ya bayyana acikin tukunyar yana k'yalk'yalar dariya sosai!.
Iya Gwamma ta dubesa tace "boka LOK'ORO jikina ya bani na kusa mutuwa,, ajalina ya kusa gabatowa gareni! Saboda haka saina kashe yaran nan guda uku kafin inbar duniya! ".
Boka LOK'ORO yace mata "tabbas haka ne gaskiya baki fad'i k'arya ba Gwamma,,, kin kusa mutuwa har abada nima nasan bazasu tab'a barina in rayu ba,,, saboda haka ki zama cikin shiri domin Ummaru d'an Sala mafarauci yana gab da tunkaroki domin ya kasheki ya d'auki fansar jinin mahaifansa! "Da wata shegiyar murya tasa kamar tusar kare.
"zan zama cikin shiri akodayaushe ya mai girma boka LOK'ORO,,, na rantse da gadon tsafi da maita! Shima Ummaru bazai tab'a iya kasheni cikin sauk'i ba saiya sha bak'ar wuya sosai a rayuwarsa wadda bai tab'a shan irinta ba! ".Inji Iya Gwamma mayya.
Boka LOK'ORO ya bushe da mahaukaciyar dariya yace "karki damu zaki basa bak'ar wahala kafin ya zamo ajalinki! Kedai kiyi taka tsan tsan da Ummaru d'an Sala mafarauci ".Yana rufe bakinsa photon dake cikin tukunya ya b'ace b'at kamar k'iftawa da bismillah.
"to ya mai girma boka LOK'ORO zanyi biyayya agareka zan kiyaye da duk irin abinda zai biyo baya ".Cewar Iya Gwamma cikeda shed'anci da ta'addanci.
**********************
Komawarsu Alhaji Suleiman gida yasa dole kowane daga cikinsu ya tashi tsaye,,, domin ganin sun nemawa 'ya'yansu magani saboda su samu waraka daga cutar,,, haka yasa sukayi ta kashin kud'i ana kawo musu magani na malamai iri iri daban daban,, to kunsan ciwo farat d'aya yake shiga samun sauk'i kuwa da sannu sannu yake shiga,, ganin haka ne yasa hankulan iyayen suka k'ara tashi sosai! Saboda ana shan magani amma ciwon sai k'ara anzama yakeyi,, su dukansu aman jini kawai sukeyi sannan basu iya tashi a tsaye a zaune suke kashi azaune suke fitsari babu k'yawon gani.
Haka iyayen nasu mata suke cigaba da kulawa dasu tareda zubar da hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,, domin su kansu ciwon yaran har tsoro yake basu saboda aganinsu kamar ba zasu tashi ba mutuwa zasuyi,,, hmmm duniya ina zaki damu hak'ik'a ta'asar da mayyu sukeyi da kashe rayuka cikin Al'umma baki d'aya yayi yawa sosai,,, saboda su mayyu da kuke ganinsu basuda d'igon imani da tausayi ko kad'an a cikin zuciyarsu,,, komai suna iya aikatawa domin ganin burinsu ya cika,, jama'a mu kiyaye dan Allah mu yawaita karatun qur'ani da addu'a akan neman tsari daga shairin masu sharri,,, da iznin ubangiji Allah idan mutum ya kiyaye yawan addu'a da karatun qur'ani babu abinda mayyu ko aljannu zasu iya yiwa mutum da iznin Allah........
[7/10, 11:50 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 30*
Da iznin Allah ba zasu iya cutar da mutum da komai ba,,, saboda haka mu kiyaye mu tashi tsaye da dagewa da yawan yin azkar,,,, da yardar Allah babu abinda zai iya cutardamu komai tsafinsa da sihirinsa.
Ciwon Maryam ya tsananta sosai ayanzu,,, duk da yake magani kala kala iri iri daban daban ake bata domin samun dacewa da waraka,,,, duk ta k'ara lalacewa da k'anjamewa babu k'yawon gani,,, Mama Sa'ima da Mubarak hankalinsu ya k'ara tashi matuk'a saboda irin wahalar da Maryam kesha akan wannan ciwo!.
Mama Sa'ima ce zaune tana shafar kan Maryam tana zubar da hawayen bak'in ciki da takaici,,, domin aganinta kamar ba zata warke daga wannan mummunan ciwon ba,,, Mubarak agefe yana lallashinta shima kansa idanunsa sunyi jawur jijiyoyin kansa sun tashi rud'u rud'u! Saboda rashin kwanciyar hankali da tashin hankali,,, amma ganin mahaifiyarsa tana kuka dole yasa ya b'oye damuwarsa,,, ya tattaro natsuwarsa cikin dauriya yace "kiyi hak'uri Mama ki daina zubar da hawayenki,,, babu abinda Maryam ke buk'ata yanzu idan ba addu'arki ba,,, sannan cikin tsanani akwai sauk'i komai mai wucewa ne insha Allah ".
Mama Sa'ima ta d'ago jajayen idanunta,,, b'acin rai da bak'in ciki ne k'arara akan fuskarta tace "ya zama dole in yi kuka Mubarak,,, idan Maryam ta mutu bansan yadda rayuwata zata iya kasancewa ba,, duk nice silar faruwar hakan saboda ban hanata fita ba alokacin da zataje wasa ba ".Ta sake fashewa da wani irin rikitaccen kuka mai cike da k'unci da bak'in cikin rayuwa.
"bakida laifi Mama ina son ki sani komai ya samu bawa muk'addari ne daga Allah,,, sannan wannan ciwo da ya samu Maryam *K'ADDARA CE* bakida laifi ko kad'an,, ya kamata ki daure ki sassautawa zuciyarki domin ki samu sauk'in rad'ad'i da zugin da kikeji acikin zuciyarki ".Inji Mubarak cikeda matuk'ar tausayin kansu da Maryam.
Mama Sa'ima tace "bawai ban yarda da k'addara bane Mubarak,, wallahi na yarda da k'addararmu amma har cikin zuciyata ina jin tsoron mayyu saboda zasu iya aikata komai,,, domin babu imani acikin zuciyarsu ".
Mubarak ya dafa kafad'arta yana share mata hawayenta,,, shi kansa zuciyarsa sai tafasa takeyi da k'una amma ya zama dole ya b'oye damuwarsa,,, agaban mahaifiyarsa domin kada ya k'ara tayar mata da hankali,,, shi kansa yasha b'oyewa acikin d'akinsa yana zubar da hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,, ga tunane tunane da fargaba akan ciwon Maryam!.
Ya numfasa sannan yace "ki daina cewa haka Mama mayyu basu isa cutar da d'an Adam ba saida yardar Allah mad'aukakin sarki,,,, sannan inason ki daure ki dinga hak'uri akan wannan lamari,,, tabbas zata samu waraka ta warke kamar bata tab'a yin wannan ciwo ba ".
"Mubarak kenan nasan kana cikin damuwa,,, amma kake daurewa kana bani hak'uri tabbas kai mai albarka ne a rayuwa,,, sannan Alhaji yace zaizo da wani shahararren Malami mai suna Malam Usama,,, domin shima yayi nasa maganin ko za'a dace ".Inji Mama Sa'ima cikeda matuk'ar fargaba da zullumi!.
Mubarak ya nisa yace "za ma adace da yardar Allah dama ciwo farat d'aya yake shiga acikin jiki,,, lafiya kuma da sannu sannu take shiga jiki saboda haka ki kwantar da hankalinki,,, babu abinda zai faru sai alkhairin Allah ".
Mama Sa'ima taja doguwar ajiyar zuciya da k'arfi! Tace "haka ne gaskiya amma zan daure inga idan zan iya,,, domin kasan tsakanin uwa da d'a sai Allah ".
"tabbas haka ne Mama amma zaki iya daurewa domin gujewa kamuwa da wani ciwon ".Cewar Mubarak cikeda tausayi da *SOYAYYAR GASKIYA* na tsakanin uwa da d'a.
Mama Sa'ima tace "to zan gwada Mubarak ".
"dako kin k'yautamin mahaifiyata ".Inji Mubarak.
Mubarak ya cigaba da kwantar mata da hankali,,, tareda lallashinta yana gaya mata maganganu masu dad'i matuk'a,,, ita kanta taji bak'in ciki da rad'ad'in da takeji acikin zuciyarta ya ragu sosai saboda Allah ya bata d'a nagari na kowa..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Suma Fatima da Fadila ciwonsu ya k'ara tsananta sosai,,, duk da yake suna nan suna shan magani iri iri daban daban daga malamai kala kala,,, amma ciwon sai k'ara cigaba yakeyi,,, k'urajen da suka fitowa Fadila ajiki sun k'ara girma sosai sai wani ruwa ruwa yake fitowa daga jikinta mai shegen wari da d'oyi! Bakinta har wani kumfa yake fitarwa akodayaushe akowane lokaci idan ciwonta ya tashi.
Ciwon Fatima da Maryam yanada sauk'i bisa ga na Fadila! Saboda ciwon Fadila yafi tsanani da firgitarwa!.
Ganin haka ne yasa hankalinsu Umma Nusaiba ya k'ara tashi matuk'a!.
Mama Nafisa ce take zubar da hawayen bak'in ciki da takaicin rayuwa,,, idanunta har sun kumbura sosai akan kuka! Ga wani irin abu da takeji daya tokare mata k'irji,,, gabanta sai yawan fad'uwa yakeyi da k'arfi da k'arfi! Zuciyarta sai zafi takeyi mata sosai.
Shesshekar kuka takeyi tana cewa "wayyo Allah ni Nafisa mun shiga uku mun lalace! Ya zanyi da rayuwata da wannan mummunan al'amarin daya samemu ".
Umma Nusaiba tana jiyo kukanta da maganganunta ta fito daga sauri cikin kitchen,,, ta nufi wurin Mama Nafisa tana cewa "haba Nafisa,, haba Nafisa miyasa bakida hak'uri ne,,, miyasa baki yarda k'addara ba? Ai komai na duniya hak'uri akeyi da kuma dauriya akan abinda Allah ya k'addari bawa dashi ".
"wallahi yaya Nusaiba ba haka bane,,, zuciyata zafi da rad'ad'in ciwo takeyimin,,, hankalina yak'i kwanciya gabana sai yawan fad'uwa yakeyi,,, sannan jikina ya bani akwai mummunan k'addarar da zata samemu! Dan Allah ki fahimceni laifin zuciyata da gangar jikina ce! ".Cewar Mama Nafisa ta sake fashewa da wani irin rikitaccen kuka,,, mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro.
Umma Nusaiba jikinta yayi matuk'ar sanyi da fargaba akan kalaman Mama Nafisa,,, ta faikaci idon Mama Nafisa ta share hawayen da yake fita daga cikin idanunta!.
Sannan ta tattaro natsuwarta da dauriya tace "kiyi hak'uri Nafisa dukkan tsanani yana tare da sauk'i,,, komai na duniya yanada farko yanada k'arshe hak'uri da yarda da k'addara shine jigon zaman duniya,, da yardar Allah zasu samu lafiya ".
Mama Nafisa tasa hannu ta share hawayenta,, sannan tace "shikenan yaya na daina kuka Allah ubangiji ya basu lafi.........."Bata k'arasa maganar ba suka jiyo kuwwa da kururuwar Fadila mai matuk'ar tashin hankali! Suka shek'a da gudu suka nufi d'akin dasu Fadila ke kwance,,, suna zuwa suka iske sai kumfa da jini ke fita daga cikin idanunta,,, sannan idanunta sai k'ak'k'afewa da juyewa sukeyi akan rad'ad'i da zafin ciwo,,, can dai Fadila ta bud'i baki dak'yar tace "Umma,, Mama duk abinda nayi muku zamana na duniya ku yafemin,,, sannan ku rok'armin gafararsu baba su yafemin duk abinda nayi musu! ".Mama Nafisa ta saki wani irin gigitaccen kuka mai cike da k'unci da tarin damuwa,,, Umma Nusaiba ce ke zubar da hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa ta matso kusaga Fadila ta rik'i hannunta tace "a'aaa Fadila ki daina fad'ar wannan magana bakiyi mana komai ba,, koda kinyi mun yafe miki cuta ba mutuwa bace "."dan Allah Fadila ki daina cewa zaki tafi ki barmu zaki warke da yardar Allah,, bakiyimin laifin komai Allah ubangiji ya tashi kafad'unki ".Cewar Mama Nafisa tana kuka sosai mai tarin yawa,, Fatima dake kwance tana kuka ta amsa ak'asan mak'oshinta "amin".Fadila ce ta juyo ta kalli Fatima tana murmushi sannan tace"ina sonki Fatima keda Maryam har abada kuna cikin zuciyata da ruhina,,, ku kasance masu biyayya da ladabi ga manyanku kada ku kasance masu rashin kunya da tsiwa nasan rashin kunyata ne yaja muku silar wannan ciwon,,, ku gafarceni ya k'awayena na tub......."Bata k'arasa maganarta ba tari ne ya sark'eta idanunta suka k'ak'k'afe suna rufewa da juyawa,,, can ta kama fisge fisgen fitar rai harta mutu Mama Nafisa tana ganin abinda ya faru ta fasa razananniyar k'ara da gigitacciyar kuwwa da k'arfi! Ta fad'i k'asa ta some Fatima dake cikin ciwo numfashinta ya d'auke da sauri akan tashin hankali da magagin ciwo!.
Umma Nusaiba ta saki gigitaccen kuka mai cike da rikicewa da d'imaucewa akan rashin kwanciyar hankali da masifa! Ta kama fad'ar kalmar "ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!! Na shiga uku ni Nusaiba wannan bala'in dami yayi kama?,,,, dan Allah ku tashi karku tafi ku barni cikin bak'in cikin rayuwa da k'unci ".Ta shek'a da gudu ta d'auko wayarta ta dialling numbar baba Nura cikin tashin hankali da rikicewa! Tana kuka ta sanardashi abinda yake faruwa cikin gidan yace mata gashi nan zuwa shida su baba Nazifi,, ya katse wayar ita kuma ta dawo wurinsu Mama Nafisa tana wani irin rikitaccen kuka jikinta sai rawa da makarkata yakeyi akan tsoro da fargaba!.
Babu jimawa sosai sai gasu baba Nura sun shigo cikin gidan cikeda matuk'ar sanyin jiki da tashin hankali,,, damuwa ce da bak'in cikin rayuwa da ya bayyana akan fuskokinsu suna zuwa wurin gawar Fadila sukace "ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un Allahumma ajirni fi musibati wa'akhalufni khari minha!!.
Baba Nura ne yayi k'arfin halin d'ebo ruwa ya yayyafawa Mama Nafisa da Fatima,,, sannan ya umurci Fadil da yaje ya sanarda mutane da kuma maigari abinda yake faruwa,,, Fadil ya fice da saurinsa cikeda k'unar zuciya da tashin hankali!.
Baba Nazifi ya shiga cikin wani yanayi mai cikeda tashin hankali da rikicewa! Ya kasa koda k'wakk'waran motsi akan ya shiga cikin yanayi mai ban tsoro da tausayi,,, baba Nura yaja hannunsa ya zaunar dashi sannan su Mama Nafisa suka farfad'o daga suman da sukayi,,, babu abinda yake tashi sai shasshekar kukansu cikeda matuk'ar damuwa da bak'in ciki!.
Bada jimawa ba saiga Fadil ya dawo da mutane akayiwa Fadila wanka,,, sannan baba Nura da baba Nazifi sukayiwa gawar addu'a suna zubar da hawayen tausayin kansu,, Umma Nusaiba ma tayi mata addu'a itadasu Nabila amma Mama Nafisa kasawa tayi sai kuka takeyi mai cikeda bak'in ciki da k'uncin rayuwa,, haka dai aka sallaci gawar Fadila bayan angama sallar ne aka kaita makwancinta na gaskiya!.
Aranar nan iyalan gidansu Fadila sun kwana suna zubarda hawayen rashinta da bak'in ciki mara misaltuwa,,, ita kanta Fatima da batada lafiya sai kuka takeyi cikin k'unci da bak'in cikin rayuwa.
_Duniyar kenan Allah ubangiji yasa muyi k'yakk'yawan k'arshe yasa aljanna ce makomarmu_..
*********************
Duk abinda yake faruwa Iya Gwamma tana gani acikin madubin tsafinta,,, babu abinda takeyi sai k'yalk'yalar dariyar mugunta harda fad'uwa k'asa akan makirci da k'eta,,, saboda murnar ta kashe Fadila burinta ya cika wani irin farin ruwa ke fitowa daga cikin jikinta sosai ga wata sansanyar iska mai dad'i da take buso mata,,, babu abinda takeyi sai surutai da tsafe tsafenta can ta bud'i baki tace "dama na gaya maki ba'a ja da mayyu akwana lafiya,,, saboda haka yanzu na kasheki na kashe banza sauran k'awayenki suma na gama dasu saboda ni arayuwata babu tausayi ko sassauci acikinta !".
"amma bari yanzu inje insha iska in dawo sai inzo in d'ora daga inda na tsaya! In kashesu Fatima Hhhhhh hhhhhh".Inji Iya Gwamma tana gama fad'ar wannan maganar,,, ta b'ace b'at kamar bata tab'a wanzuwa awannan wurin ba.
0 comments:
Post a Comment