Girgiza kai take tana kallon Annah kafin taci gaba da fad'in" Dan Allah kar ki kaini wajensa wallhi mutuwa zanyi, na tsanesa na tsanesa, bana son na sake ganinsa har abada..... Cikin kuka take kalaman nata.
"Cike da tausayawa Annah ta rungumota jikinta kafin tace "Bazan kaiki wajensa ba Zubaidah, kin yarda dani? Zaki zauna tare dani..?
"Samun kanta tayi da gyad'a kanta alamun ta amince.
"Annah ta sakar mata murmushi snn suka ci gaba da tafiya,..
"Da kanta tayi serving Zubaidah abinci snn ta mata wa'azi sosai kan kalman kisa da take ambata ma kanta, ta nuna mata illan hakan ka iya jawo mata fushin mahaliccin ta koda ace ita aka zalunta.
"Lokaci guda Allah Ya jefa k'aunar Annah a zuciyar Zubaidah, samun kanta take da bin umarninta. A b'angaren Jalal kuwa ko kad'an bai gigin shiga hark'anta, ko Annah ya shigo gaidawa Zubaidah tayita karkarwa kenan tana runtse idanu tana mannewa jikin garu had'i da k'ank'ame jikinta, wani lokacin ta shige d'aki a guje... Dukda sosai abin ke damunsa amma ganin ta sake da Annah har tana mata labarai yasa jin dad'i sosai cikin zuciyarsa, koda ace har yanzu shi Monster ne a idanunta, burinsa dama shine ta samu ingantaceccen rayuwa ...
"A b'angaren Hadiza kuwa sosai Annah ke taka mata burki da hallayanta, harta Jalal saida ya tan's mata concert warning akan tak'ura Zubaidah da take, toh abun ya d'anyi sauk'i saidai kunsan ance me hali bai canzawa, ..
"Hamma Habibu yaji dad'i sosai ganin yanda Zubaidah ta d'an sake ba kaman da ba.
"Yau satinsu guda knn da tarewa a unguwar Suleja. Kausar kuwa bata fasa k'udirinta ba don kullum cikn binkicen yanda su Zubaidh suka koma take amma har yau bata samu ba, a b'angaren soyayyarta da Salim kuwa bata nuna masa komai ba don kuwa ba tareda saninsa take gudanar da binciken ba..
"Yau ta kama alhamisa, Hamma Habibu ya fice bakin tasha yanda yake kasa lemu yana saidawa, su Annah da yaya Hadiza ma sun fice gaba d'aya harda Kamalu,
"Makarantar primary da Annah ta sami aikin kula da yara suka tafi yanda za'a sama wa Kamalu gurbin karatu,....
"Zaune take a maidaidaicin parlorn Annah yau har TV ta kunna tana kallo, lokaci guda tunanin Umar ya fad'o mata, ko wani hali yake ciki, shin a yanzu zai iya amincewa da soyayyar ta, take taji hawaye na neman kufce mata, koda shike zuban hawaye ya zame mata jiki......
"Ya jima yana tsaye yana kallonta, sai yanzu ya samu daman k'are mata kallo gaba d'aya, dukda ba farin sani ya mata a da ba yasan ta rame sosai, sabida damuwar dake k'unshe cikin zuciyarta. tausayinta na dad'a fizagarsa.
"Jikinta ne ya bata ana kallonta, aiko tana d'ago ido suka yi ido hud'u. Yana sanye cikin k'anan kaya red shirt da black jeans wanda ya fito da tsantsar farin fatarsa da kyawun halittarsa..... Ai tuni jikinta ya soma kyarma kaman mazari, a guje ta mik'e zata shige d'aki saidai tuni Jalal ya rik'ota ta fad'o jikinsa, k'ank'ame jikinta tayi tana k'k'arin k'walla ihu yasa hannu ya rufe bakinta, dukda yaji a jikinsa sosai kasancewar yanda jikinsu ya manne dana juna, don rabonsa da kusantar wata mace tun bayan had'uwarsa da Zubaidah,.....
"A hankali yake kallonta yana girgiza mata kai alamun tayi shiru, ...
"Batayi shirun ba sai ihu take dukda hannunsa na rufe saman bakinta, bata fasa kai masa duka da duka hannayenta biyu ba..
"Dad'a matseta yayi sosai cikin jikinsa suna jin bugun zuciyar junansu kafin ya soma fad'in" Dan Allah kiyi shiru kiyi hak'uri ki saurareni, babu abinda zan maki.....
"Jin kukan nata ya tsagaita yasa sa bud'e mata baki gamida sakinta a hankali..
"Aiko tuni ta matsa can gefe ta shiga jan rigarta tana rufe illahirin jikinta dashi.... "Cikeda tsiwa take fad'in" Malam ka fice kafin na maka ihu.....
"D'an fuzar da iska yayi kafin ya durk'usa a gabanta, nan da nan ta shiga ja da baya har ta isa k'arshen garu...
"Jalal ya k'urawa yatsun k'afanta ido wanda yasata saurin lullub'e k'afarta.
"Kauda kansa gefe yayi kafin yace " Meyasa kike tskrona...
"Jin tambayar tayi gatsau, d'ago rinannun idanunta tayi tana watsa masa kallon k'yama da tsantsar tsana, lokaci guda kuma taji ta kasa jure kallon nasa, Kauda kanta gefe tayi kafin tace " Sabida na tsaneka, na tsani ganin ka, sabida kai d'aya ne daga cikin mutanen danafi tsanar su fiye da komai a duniya, nafi tsanarka fiye da yanda na tsani shed'an. Kuma wllhi wllhi sai ka sake ni sabida ni Zubaidah matar wani ne akwai baikonsa akaina kafin ku bayyana a rayuwarmu, kafin ku canza mana farin cikinmu zuwa bak'in ciki, idan baka sake ni ba, toh ni ina iya tafiya na bar maku gidan.......
"Hannu yasa duka biyu ya shafi sumarsa gamida fuzar da iska" Ya jima kaman bazaice komai ba har ta cire ran bazaiyi magana ba ta jiyo muryarsa cike da taushi yana fad'in" Zubaidah bazan sake ki ba koda ace ba auren soyayya mukayi ba, dukda nida ke bamu son junanmu amma k'addara ta had'a.......... " Baikai aya ba ya jiyo siriryar muryarta cikeda tsiwa tana fad'in" No k'addara bai had'ani da kai ba, sabida ni ba matar aure bace, lokaci na d'ibar wa kaina kuma lokacin na cikawa zanyi tafiyata ba tareda neman shawarin d'aya daga cikinku ba not even my Hammah.
"Kallonta kawai yake yanda take maganar, lallai tanada courage sosai, girgiza kansa yayi dukda bata dubansa kafin yace " Ba sai kin tafi ba Zubaidah, ni zan taf har sai rananar da kika sami gurbi na yafe min a cikin zuciyarki. Amma akwai abu guda da ni Jalal nake so ki sani,......" D'ago ido tayi ta dubesa kafin ta kauda kai gefe.
"Jalal yaci gaba da fad 'in" Wllhi wllhi na rantse da mahallici na ban aikata ba......... " Da sauri tasa hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta gamida k'walla k'ara, don kuwa komai ya shiga dawo mata, bata manta wann farin fuskar nasa wanda a idanunta bak'kk'irin yake lokacin da ya soma rik'ota........" Ganin ya kasa controlling d'inta yasa mik'ewa da sauri, tuni ta shiga d'aukan duk abinda ke gefenta tana jifa masa tana fad'in ya fita ta tsanesa....
"Dole Jalal ya fice zuciyarsa cike da tausayinta, Lallai dole su nemi taimakon likitita dole su nemi taimakon *Therapist* dan kuwa abin yayi affecting Zubaidah sosai.......
*********************
*K'asar Gombe*
"Gimbiya Zahida ce kwance saman tapkeken gadonta na alfarma, waya manne a kunnenta da alama da k'awarta take wayan..
" Kai Kausar friend amma nai maki murna, Allah Ya baku zaman lafiya keda angonki Salim.
"Daga d'aya b'angaren Kausar ta murmusa kafin tace " Na gode " Princess Heeda, nidai babban farin cikin da zanyi shine ki halarci bikina...
"Zahida ta d'an ware ido had'i da yin murmushi kafin tace " Friend I can't promise you that, sabida na fad'a maki yanda mahaifina Mai martaba yake, bai barina ina zuwa bikin k'awaye koda a cikin Gombe ne balle har wani gari, idan kinga naje biki toh shakka babu bukin dangine a cikin fada. ..
"Kausar ta d'an juya idanu fuskarta d'auke da murmushi kafin tace " Pls try and ask him nasan shima me yuwa zaizo d'aurin aure, tunda shine babban mutum a gari, kinga fah dukanmu daga gari guda muke, pls Heeda ki kwatanta tambayarsa, Ummi tasa baki, pls pls pls.......
"Zahida ta murmusa kawai dan kuwa duk yanda zatayi bayni wa Kausar bazata gane ba.Dan haka ta amince zata gwada tambayarsa......
"Ummi ce ta turo k'ofar ta shigo bayan Zahida ta gama wayar......
Sameena ce đđž
[1/23, 22:15] +234 803 619 0581: đđđđ *ZUBAIDAH*
25
*©Sameena Aleeyou... ✍đž*
_Queen Samy Novels Forum... đđ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Zahida ta fad'ad'a murmushinta sanda Ummi ta zauna gefenta.
"Ummi barka da shigowa ta fad'i tana duban mahaifiyar nata.
"Murmushi mai cike da k'asaita Ummi tayi kafin ta shafi gefen fuskar d'iyar tata tace " Barka Princess, who were talking to on the phone, you seems very happy.
"Zahida tayi murmushi kafin tace " Ummi zaki iya tuna wata k'awata da nace maki we met on facebook.
"Ummi ta d'an juya idanunta kafin tace " K'warai na tuna, ba kince 'yar gidan Tahir Marafa Dukku ba, me neman takaran kujeran shugaban k'asa.
"Zahida tayi saurin gyad'a kanta kana tace " Eh ita fah Ummi, she's getting married in couple of weeks, so..... So.... Ta d'anyi shiru don tunanin abinda take shirin fad'i.
"Ummi ta rik'o hannayenta cikin nata kafin tace" uhum go ahead.
"Dama Ummi tunani nake ko Mai martaba zai barni naje...
"D'an kallonta Ummi tayi gamida sauk'e ajiyan zuciya don kuwa tasan abu ne mai kamar wuya.
"Girgiza kai tayi kafin tace " Zahida kinsan halin mahaifinki, kinsan irin kula da tsaron da yake baki bazai yarda ki tafi wani gari biki ba, bikinma na k'awa duka nasan shima na iya zuwa d'aurin aure amma kinsan bazai barki ba, don haka Karma kisa wa ranki abinda ba samu zakiyi ba. Idan ban manta ba rabonki da yin tafiya mai tsawo tun azumi da muka tafi harami don gudanar da Umra,.
"Zahida fuska a turb'une tace " Ummi ina son sarauta amma ko kad"an banson wann kulle da ake wa matan sarauta, ni shiyasa nafi so ni nazama sarauniyar komai saida iko na, and that's when da zan ringa barin matan babban gida suna fita kaman sauran mata.... "Ganin magaifiyar Tata ta zuba mata ido tana dubanta yasata gyara zama kafin ta jeho wa Ummi tambaya.
"Wai Ummi meyasa Abba nashi kullen yayi tsamari, har yau bai barni naci gaba da karatu ba snn yak'i ya min maganar aure har yanzu. Haba we are in a 21st century fah, ai an daina irin wann sarautar, naga k'awata Mardiya Saraki d'iyar sarkin Katsina kwatakwata Babanta bai masu irin wnn kullen ita da k'annenta, Wllhi Ummi they are leaving their lives like ordinary people..... Amma miyasa Abba yake haka.
"Dafata Ummi tayi kafin ta Kai Dubanta ga hoton jaririn dake ajiye gefen bedside d'in Zahida tace " Meyasa kike ajjiye da wnn hoton.
"Zahida tayi murmushi gamida shafa hoton da hannunta tace " *Hamma Lamid'o Modibbo* saida gaban Ummi yabada damm jin an ambaci sunansa.
"Zahida taci gaba da fad'in" Ummi wllhi wataran nakanji inama ace nima inada d'an uwa ko 'yar uwa, jiya na gani cikin d'akin Madaki na d'auko na kawo shi d'akina, ....
"Ummi tayi kicin kicin da fuska, wai har yaushene iyalanta zasu daina tuna Modibbo Lamid'o, a zahiri baya taredasu amma tabbas a bad'ini yana tare dasu, she wants to get rid of him completely.
"Murmushin da baikai wuya Ummi tayi kafin ta rungumo Zahida tace " Gimbiya Zahida, ke kad'ai kin ishe mu a gidan nan, muna sonki fiye da komai, a dalilin sonki da yawa da mahaifinki ke maki yake maki wann kullen. Dalili na biyu kuwa. Ta sake duban hoton Modibbo kafin tace " Tun lokacin da mahaifinki ya rasa Modibbo yake fatan sake samun magajj, shiyasa koda aka haifeki yake kafaffa da rayuwarki don gani yake kaman kema na iya rasaki.
"Murmushi Zahida ta d'anyj zuciyarta cike da tahsayin mahaifinta, mik'ewa tayi kana tace " Ummi barinje wajen madaki na mata alk'awarin zan shiga tayata hira. Kai Ummi ta gyad' mata kafin tace "A sauk'a lafiya Gimbiya.....
"Zahida ta dubi Jakadiya dake tsaye bakin k'ofa da sauri Jakadiya ta rusuna ta shiga mata kirari, ba tareda tabi takan Jakadiya ba tayi shigewarta don kuwa tak'i jinin matar gaba d'aya.....
"Jakadiya ta shigo gamida duban Ummi cikin ladabi, mikewa Ummi tayi kafin tace "Ki sameni a d'akina, wucewa tayi ba tareda ta tsaya jin me jakadiya zatace ba sabida k'unan da zuciyarta ya shigayi tunda ta kula Zahida gudar jininta ma son wnn maceccen yaron take.
"Tafe take a hanyar da zai sadaka da Babban gwani da kuma b'angaren Madaki kakarta. Kaman daga sama ta hangesa sai sauri yake.
"Murmushi yayi sanda shima ya hangeta, maida masa martanin murmushin nasa tayi kafin tace " Yaya Shatima form where?
"My Lady!!!!! Ya fad'i had'i do sadda kansa k'asa lokacin da yake k'arasowa.
"Kai Ta Shatima ni dan Allah ka daina bani wann girman haka.
"Shatima yayi murmushi kafin yace "Be abunda kike so ba kenn ko kin daina son sarautar ne? Ya k'arashe maganar tensely.
"D'an murmushi tayi kafin tace " kaima kasan bazan daina so ba don ajini na yake kawai dai zan canza tsarin sarautar ne idan na hau....
"Shatima yayi murmushi mai bayyana hak'wara kafin yace " Haka ne Your majesty, gaba daya suka dara kafin yace " Zahida you'll never change, will you?
"Abokina dai yanada aiki.....
"Nan da nan Zahida tayi kicin kicin da fuska tace " Wllhi Karma ka fara, bakasan yanda na tsani wann abokin naka ba......
"Shatima na dariya yace "Au kema kinsan Khalifah jinin sarauta ne, kuma kince bazakiyi aure ba sai saraki toh kinga ai daidain ki knn....
đđž
[1/23, 22:15] +234 803 619 0581: đđđđ *ZUBAIDAH*
26
*©Sameena Aleeyou... ✍đž*
_Queen Samy Novels Forum... đđ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
_Dear Lovers kuci gaba da manejin gajerun posts pls, wllhi this days I'm fully occupied ne, will continue adjusting insha Allah .... Luv you allđ_
"Tafiya Zahida ta soma yi ba tareda ta masa sallama ba, .
"Da sauri Shatima yasha gabanta yana murmushi, Harara ta kuma galla masa a karo na biyu kafin tace " Ya Shatima Allah zamu b'ata.
"Still fuskarsa d'auke da murmushi yace " Allah huci ran Gimbiya kuma k'anwata, kiyi hak'uri na daina.
"D'an kallonsa tayi dole tayi murmushi don kuwa bata iya juran dad's da Shattima,
"Idan Gimbiya ta barni zan k'arasa Babban gwani wajen mai Martaba. Ya fad'i yana sadda kai k'asa.
"Murmushi tayi mai fito da asalin kyaunta kafin tace " Saurin me kake ne haka wai.
"Shattima ya d'ago Taliesin hanunsa gamida girgiza su yace " Wllhi kin gani tun jiya Mai Martaba yake expecting wad'an nan takardun ban kai masa ba, gashi aike na zaiyi zuwa Abuja cikin satin nan da zaran ya kammala sa hannu a takardun.
"Jin ya ambaci Abuja yasa Zahida ware idanu, inama Mai Martaba zai bari ta tafi tareda Shattima, sanin abune ba mai yuwuwa ba yasata d'anyi murmushi kafin tace " Ya Shattima kuma yaushe zaka dawo idan ka tafi, ...
"Business trip ne Princess bansan yaushe zan dawo ba gaskiya amma probably bazan wuce sati uku ba.
"Zahida ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace " Shiknn Allah Ya bada sa'a. Murmushi yayi kana ya amsa da ameen snn suka jera suna tafe, har cikin ransu suna k'aunan juna matsayin yaya da k'anwa.
"Shattima d'a ne ga mai girma Waziri, Mai Martaba ya aminta da Shattima sosai sabida hankali da kamala da Shattima kedashi, shiyasa tunda Shattima ya kawo girma ya kammala karatun degree d'insa Mai Martaba ya d'aura sa kan duk wani hidima na kasuwancinsa. Wanda yawan shigowa cikin gidan da mu'amala da ahalin gidan yasa suka sami shak'uwa sosai da Gimbiya Zahida......
********************
"Balele ya kallesa a karo na biyu kafin ya sauk'e ajiyan zuciya yace " Umar kayiwa ka cire yarinyar nan a zuciyarka, bata sonka ta sami madadinka, da ace tana sonka da ta dawo gareka, amma bata dawo ba bata waiwayeka ba, ka k'yaleta tunda ba itace autar mata ba, ka zab'a cikin 'yammatan da suke sonka ka Aura, amma har yaushe zaka bari tunanin mace ya maida ka haka.....
"Umar ya jefa d'an k'aramin dutsen dake hannunsa cikin rapin, kallon wajen yake yana tuna kalan soyayyan da suka sha da Zubaidah a wann waje, yana tuna nan shine wajen had'uwarsu, amma Zubaidah ta mance komai taci amanarsa....
"Kauda kansa gefe yayi kafin yace " Balele kasan irin son da nake ma Zubaidah, kasan itace farin ciki na a wann rayuwar, bazan iya auren wata mace ba face ita, ko kad'an ban tab'a kawo Zubaidah zata iya min abu makamancin haka ba, amma babu komai zan manta ta, zan manta da duk wani abu da ya shafeta, zan tafi na bar wajen nan, zanyi nesa da garin nan, zan fara daga farko a can yanda babu wanda yasanni...... "Ya k'arashe maganar yana nannad'e handkachip d'in da tab'a basa a hannunsa...
"Balele ya dafa kafad'ansa yace " K'warai abokina zaka iya aiki a wani garin ba nan ba da sannu Allah zai cire maka ita gaba d'aya daga cikin zuciyarka, Allah yayi maka jagora.... Bai iya cewa amin ba sai mik'ewa da yayi, a tare suka bar wajen suka nufi cikin gari shida Balele....
*Abuja*
*Dasuki Holding of companies*
_At the conference meeting_
"Da mugun mamaki Alhj Jamil yake bin documents d'in da shakka babu sa hannunsa ne akai, yaushe a ina ya amso wad'an nan kud'ad'e, dafe kansa yayi da hannayensa biyu yana karanto innalillahi.
"Daddy ya kuma tura masa takardun in a furious tune yake fad'in" Why why Jamil, Where do you expect us to get that kind of money, you are nothing but a disaster to business..... Shiru Alhj Jamil yayi bai iya cewa komai ba,
"Sauran shearHolders suka soma maganganu k'asa k'asa.
"Alhj Maina mahaifin Tariq yace " A gaskiya inada kusan 5% a wann company and idan aka samu Bankruptcy zaiyi affecting d'ina sosai don Banki ba yarda zata yi ba WA'adin da ta bada yana cika zata mallake company d'in gaba d'aya, snn Banki ba d'aya ba kuma Bankunan k'asashen waje, so gaskiya inaga zan cire shears d'ina, anyone from the shear holders wanna join me, Ya k'arashe maganar da alaman tambaya.
"Nan masu k'anan shears da manyan shears suka soma k'orafi suma.
"Alhj Kasim da Barr Munir suka shiga basu baki suna nuna masu lallai bazasu bari wann company mai tarin albarka ta ruguje ba.
"Wakilin Alhj Tahir Marafa yayi gyaran murya kafin yace" *Marafah Construction Company* zata saka hannun jarinta, zata ciro 50% daga company d'inta ta saka a Dasuki Holdings, take Daddy ya washe baki farin ciki ya lullub'e sa suka had'a idanu shida Barr Munir, plan d'insu ta tafi daidai... Da haka aka k'arashe meeting Alhj Kasim ya shaida masu lallai shida k'aninsa zasuyi yanda zasuyi su biya wad'ancan kud'ad'en...
"A b'angaren Alh Jamil kuwa k'rjinsa ne ya shiga masa zogi da rad'ad'i had'i da wani irin ciwo har ya isa gida......
"Tafe suke ita da Annah bayan sun ajiye Kamal a makaranta, don yau Annah mussaman ta d'au hutun aiki sabida Zubaidah tana so suyi spending time sosai, da k'yar Zubaidah tabi Annah saida Kamal yayi ta magiya kafin ta yarda ta rakasu...
"Daga yanda motar ta ke pake ta hangosu zasu shige gida, da sauri ta fito daga motar ta nufo su...
"Zubaidah....... Ta fad'i tana k'arasowa yanda suke, a tare Zubaidah da Annah suka tsaya cak gamida juyawa, cike da mamaki suke Kallon Kausar, Zubaidah kam k'irjinta ne ya shiga bugawa da sauri da sauri.
"Jan hannun Annah ta soma tana fad'in Annah pls mu tafi.....
'Kausar ta k'araso da sauri ta rik'o hannun Zubaidah tace "Don Allah Zubaidah listen to me I won't take much of your time, pls.... Ta d'an dubi Annah tace pls Annah.
"Gyad'a kai Annah tayi cike da mamakin wani magana Kausar zatayi da Zubaidah? Wata zuciya tace k'ila hak'uri zata bata lokacin da tayi kusan kad'eta.
"Toh ku shigo ciki mana Annah ta fad'i.
"Kausar ta girgiza kai tana murmushi har lokacin hannunta na rik'e da na Zubaidah kafin tace " No Annah karki damu ba jimawa zamuyi ba, daga haka taja hannun Zubaidah zuwa benchin dake gefen k'ofar gidan, Annah kuwa tayi shigewarta ciki...
Sameena ce đđž
[1/23, 22:15] +234 803 619 0581: đđđđ *ZUBAIDAH*
27
*©Sameena Aleeyou...✍đž*
_Queen Samy Novels Forum... đđ_
*Dedicated To Victims Of Rape...*
"Meye zaki fad'a mun, a ina na sanki, snn me ya tab'a had'ani dake da har kike son yin magana dake...???
"A jere Zubaidah ta jeho wa Kausar wad'an nan tambayoyin.
"Kausar ta karanceta tsaf kafin ta soma fad'ina, "Nasan zaki iya sani na, sunana Kausar Marafa, snn wacce tayi kusan kad'eki da mota sati biyu da suka shige a gidan Alhj Kasim Dasuki dake Maitama close Abuja, still nice Fiancee d'in Salim Dasuki....."Sunan Salim data ambata yasa Zubaidah saurin mik'ewa, Kausar tayi saurin rik'o hannunta.
"Malma ki sake ni na tafi, babu abu d'aya da ya had'ani da zantukan da kike min, idan kuma bugeni da mota da kika kusa yi ne, ba laifinki bane, laifi na ne, don Allah ki tafi ki k'yaleni....
"Kausar ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace " Zubaidah shin Jalal shi kadai ya maki fyad'e ko harda Salim..???
"Tambayan da Kausar ta mata yasata fara loosing control, cike da masifa ta fizge hannunta daga rik'on da Kausar ta mata" Cikin kuka take fad'in" Leave me alone, bansan abunda kike fad'a ba don Allah ki k'yakeni ki tafi and never come back.... Daga haka ta wuce cikin gida da sauri tana k'ank'ame jikinta, tana jawo rigar ta tana rufe jikinta.....
"Sosai ta bawa Kausar tausayi, da gani kasan pain d'in abun yana damunta zaiyi wuya ta sami had'in kanta a yanzu, cikin gidan ta shige itama da sauri....
"Zubaidah ba tare da tabi takan Annah ba ta wuce d'aki gamida banko k'ofa....
"Jin haka yasa Annah fitowa da sauri daga kitchen, a tare sukayi kicib's da Kausar ta shigo gidan.
"Annah ta kalleta da mamaki kafin ta tambayeta ina Zubaidah Kausar ta ciro wani d'an Card a jakarta ta mik'awa Annah tace " Pls Annah ki bata wann lambar wayata ce when ever she feels ta min magana she can contact me through this number, na gode..... Daga haka Kausar tasa kai ta fice daga gidan... Annah ta bita da kallo har ta fice kafin ta shiga juya takardan hannunta tana kallo.....
"A daidai k'ofar fita daga gidan suka had'u da Jalal, kallon mamaki yabita dashi, ita kuwa k'ak'aro murmushi tayi kafin tace " Jalal kayi wuyan gani, d'an maida mata murmushin yayi kafin yace " Me ya kawo ki nan...
"Kausar ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace " Jalal abunda nake son tambayarka nasan tanada nauyi but please be honest with me and tell me the exact truth.
"Jalal ya kuma binta da kallon mamaki kafin yace "Umhun inajinki go ahead.
"Jalal nasan ku hud'un nan ba'a raba ku, kai Salim Labib da kuma Tariq, Don Allah ka fad'amun gaskiya " Are you the rapist or all of you, pls tell me if Salim was involved?... I was told that you're the guilty one, pls ka fada mun iyakar gaskiyarka....
"Take idanunsa suka kad'a sukayi ja, tambayar data masa yayi matuk'ar sosa masa rai, but he don't want to ruin everything, he's doing this for the girl..
"D'agowa yayi ya dubeta kafin yace " Gaskiya suka fad'a maki Salim ya fad'a maki iyakar gaskiyarsa, now that you learned the truth kar ki sake dawowa nan pls kinji na rok'eki....
"Kausar da jikinta yayi sanyi ta gyad'a kai a hankali kafin tace " Bazan sake daowa ba insha Allah, your wife told me thesame...... "Da sauri ya dubeta kafin yace " You mean you talked to Zubaidah????
"Gyad'a masa kai tayi a hankali.......
"Fuskarsa cike da damuwa ya furta "Oh nooo, cikin sauri ya shige gidan Kausar ta bisa da kallo har ya b'ace mata kafin ta nufi yanda ta paka ride d'inta......
"Bai samu kowa a tsakar gida ba don haka kai tsaye d'akin Annah ya nufah......
"Yanda ta gansa ya shigo parlorn cikin sauri yasata k'walla wani irin k'ara ta tak'ure jikin garu tana k'ank'ame jikinta..... A hanzarce Annah ta nufo parlorn, shi kuwa Jalal ko motsi ya kasa sai kallon da ya bita dashi.....
"Annah ta watsa masa mugun kallo kafin ta k'arasa ta rungume Zubaidah tana rarrashinta....
"Jikinsa a sanyaye ya ajiye b'akar ledan da ya shigo dashi kana ya fice, d"akinsa ya wuce gamida zama bisa katifa...
"When will all these end?? When? When????? Kwanciya yayi bisa gado tausayin kansa da rayuwar da yake fusakanta suka cika zuciyarsa.....
"Wayanta ta ciro tayi dialing lambar Asmah snn ta saka a speaker... Bugu uku Asmah ta d'aga.
"Hello Barrister kina gida ko school??
"Daga d'aya b'angaren Asmah tace " Ina school, akwai wani abu ne, ??
"Okay shiknn sai kin dawo gida we need to talk ASAP.
"What for, maganar me bani hint you sounds serious....
"Okay amma driving right now, when I get home I'll call you back....
"Wait driving, ina kikaje da safen nan, ?
"Suleja naje...
"Suleja, suleja, wajen wa, Asmah ta tambaya cike da mamaki.... Kufa Journalist d'in nan kuna da bin diddigi don kunfi mu lawyers ma...
"Kausar tayi murmushi kafin tace "We will talk at home...
"Okay bye...
"yeah see you then...... Daga haka tayi hanging up zuciyarta cike da jin dad'i at least yanzu tasan Salim d'inta is innocent, zata ci gaba da shirin biki da k'warin gwiwarta........
"Ko office bai fice ba sabida zafi da k'irjinsa ke masa, ciwo kaman wasa babu yanda Mami batayi a kira Family Dr dinsu ba Alhj Jamil yak'i yarda, Labib ne ya shigo fuskar sa cike da damuwa ya k'arasa ya d'an zauna gefen gadon da mahaifinsa ke kwance, ya dubi Mami dake k'ok'arin had'a masa tea kana yace " Wai Mami har yanzu yak'i yarda a kira Dr d'in, mik'ewa yayi yana k'ok'arin ciro wayarsa a aljihu yake fad'in "I'm calling Dasuki Hospital Mami, bazamu biye nasa ba..... "Bai gama yin shiru ba yaji Dad d'insa ya rik'e hannunsa, juyowa yayi yana dubansa da alama bakinsa ya karkace.... Hannun Mami ya rik'o ya had'a dana Labib, cikin muryarsa da bai fita sosai ya soma fad'in
"Na bar maku amanar junan ku, Labib kabi mahaifiyarka snn kema ki kula dashi and pls protect him........ "Baki na rawa Labib yake fad'in" No no Dad pls stop saying all this, you gonna get better, we taking you to the hospital right away, Mami kam ta kasa nagana sai k'unshe bakinta da tayi tana kuka..... Labib duk ya daburce ya rasa wanne zaiyi, k'walla kira ya shiga yi wa ma'aikatan gidan, Alhj ya kuma rik'e hannun Labib gam kafin yace " Be careful with your uncle son..... Daga haka suka ji kaman yana salati dukda muryar ba sosai take fita ba.... Cikin mintuna k'alilan suka ji difffff komai ya tsaya........
Sameena ce đđž
[1/23, 22:16] +234 803 619 0581: đđđđ *ZUBAIDAH*
28
*©Sameena Aleeyou...✍đž*
_Queen Samy Novels Forum... đđ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Jijjigasa ya shiga yi da iya k'arfinsa yana fad'in " Dad Dad, no pls wake up Dad....! Kuka mai k'arfi ya kufce masa sanda ya rungume Dad d'insa da k'arfin gaske yake kuka yana ambatan sunan sa, bai kula da Mami ba da tuni ta sume, ...
"K'aran kukan Labib da suka jiyo yasa sata nufo d'akin d'akin babu shiri, Iya Dala ta Saki salati ganin Alh Jamil tamkar maras numfashi ga Labib na kuka rungume dashi, wani k'arin tashin hankalin shine hango Mami datayi zube a k'asa tamkar bata numfashi.
"A tamanin Iya Dala ta fice ta nufi gidan Alh Kasim...
"Yanda Mummy ta ganta gaba d'aya a rikice yasa hankalinta mugun tashi, gankalinta bai gama tashi ba saida taji labarin da Iya Dala ta kawo mata....
"Momy duk ta rikice da k'yar ta iya duban Jane tace ta kira Company a fadawa Daddy ya dawo gida babu lafiya, a tare suka nufi gidan Alh Jamil ita da Iya Dala,...
"Tsaye yake a saman penthouse(sashensa) d'insa ya hangi Momy da alama bata san yanda take jefa k'afafunta ba, ai babu shiri ya sauk'o ya nufo su..
"Momy lafiya meke faruwa? Salim ya tambaya cike da damuwa ganin hawaye a fuskar Momyn tasa.. . Rungumesa tayi tana kuka take fad'in" It's your uncle Salim.... "Gabansa yayi wani irin fad'uwa,
"A hankali ya furta "My uncle, what.... What happened to him Momy...
"Jawo hannunsa tayi suka nufi gidan tana fad'in I don't know Salim, let's go and find out......
"Sosai hankalinsu ya tashi da irin abinda suka gani, Mami dai ta farfad'o da aka yayyafa mata ruwa, Alh Jamil kam sa'i yayi don kuwa ya amsa kiran mahaliccinsa,...
"Rungume gawar mijinta tayi tana kuka mai tsuma zuciya, " Jamil kar ka tafi ka barni, bazan iya juran rayuwa cikin rashinka ba, don Allah kar ka tafi ka barni mijina.... Momy da itama hawayen take ta k'arasa ta rungumeta tana rarrashi...
"Labib yana ganin Salim suka rungume juna yana fad'in" Salim tell me my Dad is'nt dead, tell me he will wake up, tell me he can go through this, tell me I'm not gonna loose him.... Sosai Salim Ya rungumesa hawaye shima na k'ok'arin kufce masa....
"A kid'ime Alh Kasim da Dr suka shigo cikin d'akin, Alh Kasim tamkar mutumin arziki ya k'arasa kan d'an uwan nasa yana fad'in" Jamil my brother, what on earth is happening to you?? Dr ne ya matso ya shiga yin aikinsa, ya buk'aci su d'an basu waje, gaba d'aya suka fice parlour....
"Alh Kasim da Barr Munir sai kai komo suke saika rantse har ransu abin damunsu yayi....
"Dr ne ya fito daga d'akin jikinsa a sanyaye, gaba d'aya suka nufo sa suna son jin ba'asi.....
"Alh Kasim yace " Dr ya d'an uwa na, wani hali yake ciki, kafin Dr ya bud'e baki Labib ya rik'o hannunsa yana hawaye yake tambayarsa" How's my father Dr, tell me I can see him right now and he can talk to me.....
"Sauk'e ajiyan zuciya Dr yayi kafin yace " I'm sorry there's nothing I can do, sorry for your loss....
"Tashin hankali maras misaltuwa suka shiga idan ka d'auke Alh Kasim da Barr Munir Wanda hakan ba k'aramin farin ciki ya jefasu ba, burin Alh Kasim na mallakan Dasuki Holding ba tareda k'aninsa ba ya cika, matansa da d'ansa kuwa abune mai sauk'i....
"Abunka da babban mutum kan kace me an yad'a a kafafun watsa labaru, kan kace me gidan ya cika fal da jama'a....
"Suna zaune a barander suna tsinkan zogale itada Annah, dukda bata san dadin uwa ba amma tabbas tana jin dadin zama da Annah, tana jin kaman ta sami wani abu ne wanda a da bata samu ba a iya zamanta da Hadiza, jefi jefi Annah take janta da hira.
"Kamar wacce aka wurgota haka Hadiza ta diro masu aka kunnenta manne da Radio sai faman k'ara murya take tana fad'in" Kuji k'anin Alh Kasim Dasuki, Alh Jamil Allah ya masa rasuwa yau da safen nan..... "K'irjin Annah ya yanke ta shiga karanto innalillahi..... A b'angaren Zubaidah kuwa ko kad'an basu bata tausayi ba tunda tasan mahaifin Labib ne, k'arshema tashi tayi a wajen ta shige d'aki abinta, Hadiza tabi bayanta da kallo don yanzu ko maganar arziki bai shiga tsakaninsu.....
"Alh Kasim na zaune at the center a babban parlonsa da aka wangame gaba d'aya don Karb'an gaisuwa, mutane sai tambayan Labib suke suna so su masa ta'aziya, ciki harda su Alh Marafa da sauran tawagansa na siyasa, da kuma tawagan Ministoci da sanatoci da dai manyan 'yan kasuwa masu fad'i aji a garin Abj,
"Daddy ya kalli Salim yace " ina d'an uwanka?
"Salim yace " Yana penthouse d'ina, Daddy ya gyad'a kai yayi kafin yace "Okay Daddy ya nufi sashensa.....
"Zaune ya taddasa ya k'urawa aquarium d'in dake gefen closet d'insa ido, bin kifayen ciki yake da kallo amma hankalinsa gaba d'aya baya wajen, Maganar mahaifinsa na k'arshe ita tafi yawo cikin zuciyarsa *Be careful with your Uncle* meyasa Dad zaiyi wnn furuncin, tabbas idan ya gano Alh Kasim has anything to do with his father's death, he will kill him for sure... Dafasa da Salim yayi ne ya katse masa tunanin da yake.
"Kallo d'aya ya masa ya watsar, Salim ya d'an zauna gefensa gamida jero masa kalamai masu taushi "
"Labib you need to be strong for your Mom, idan kai namiji ka kasa jurewa ya kake tunanin mahaifiyarka zatayi, she needs you now, she needs you more than ever, pls be a Man I know you can go through this, besides you are not alone, you have us all, together we will through this as a family, tashi muje people are waiting for you to give you their condolence greetings, Daddy yace ka fito they are all waiting for you....
"Jin ya ambaci Daddy yasa sa kallonsa kaman zai mik'e sai kuma ya zauna yana girgiza kai yake fad'in" Kaje kawai Salim banjin dad'i, pls ka rufe mun k'ofa idan ka fita....
"Da mamaki Salim ke kallonsa kafin yace " Haba Labib daurewa zakayi mekake tunanin zanje nace wa manyan mutanen da suke jiranka, haba haba, saikace wani k'aramin yaro.....
"A harzuqe yace " I said leave me alone Salim, I f go out there, I'm pretty sure I'll see that Bastard and I assure you things are gonna get out of control, so leave pls, go tell them what ever you think.... Daga haka ya koma gaban window ya shiga kallon waje......
"Da mugun mamaki Salim yake dubansa, zaiyi magana knn Tariq ya shigo don yaji shirun yayi yawa daga fitan Salim yaje ya shigo da Labib sun kwashe mintoci....
"Kallon Labib dake tsaye bakin window yayi kafin ya dubi Salim, alamun tambaya ya masa da ido, Salim ya ware hnnaye gamida bud'e idanu alamun bai sani ba.....
"Tariq ya k'arasa ya rik'o kafad'un Labib yace " Let's go Labib, . "D'ago kai yayi ya dubi Tariq kaman raqumi da akala haka ya soma binsa, Salim ya d'an fuzar da iska gamida bin bayansu, cike da mamakin maganganun da Labib yayi, a iya saninsa Labib kwana biyu bai tari fad'a da kowa ba toh ko da waye yake yi sai Allah.......
"Har ya gama gaisawa da illahirin mutanen dake parlorn idonsa akan Alh Kasim yake, banda watsa masa mugun kallo baya komai, kai k'arshe har Labib ya bar parlorn idanunsa na kan Alh Kasim, gaba d'aya Alh Kasim yasha jinin jikinsa da irin kallon da Labib ke masa, a hankali ya saci jiki yabi bayan Labib.....
Sameena ce đđž
[1/23, 22:16] +234 803 619 0581: đđđđ *ZUBAIDAH*
29
*©Sameena Aleeyou...✍đž*
_Queen Samy Novels Forum...đđ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Har aka gama kwana uku basu gane kan Labib ba, wuni yake zubur a d'aki ba tareda ya shiga sabgan kowa ba, ranar da Alh Jamil ya cika sati guda cif da rasuwa Daddy ya had'asu a parlor, Mami Labib da kuma Barr Munir.
"Banda mugun kallo da yake watsa ma uncle d'in nasa baya komai...
"Ko darajar gaisuwa basu samu daga Labib ba, .
"Alh Dasuki yayi gyaran murya ya soma magana dangane da business d'in marigayi Alh Jamil, kama daga yawan shears d'insa dake Dasuki Holding bashin da ya ciwo daga bankunan k'asashen waje, k'arshe ya tabbatar masu Alh Jamil bashida single cent da yayi saura a Dasuki Holding sabida mak'udan bashusshukan da ake binsa...... Ai bai ida rufe baki ba Labib ya mik'e yayi kansa gamida cakumo bababban rigarsa yana fad'in" How dare you Kasim Dasuki,..... Mami a zabure ta mik'e tana daka wa Labib wani irin tsawa, Barr Munir yayi saurin k'watar mai gudansa...
"Finciko Labib dake kan faman huci Mami tayi tana watsa masa mugun kallo mamaki ya hanata magana, "Har lokacin bai dana huci ba yake nuna Alh Kasim da d'an yatsa kafin yaci gaba da fad'in" Mami let me teach this Man a lesson, how dare he zaice Dad bashi da single cent a company d'in da kowa yasan hard working d'insa ne, wllhi kayi kad'an Kasim Dasuk...... "Muryarsa ne ya sarke sanda yaji sauk'an wata mari meji da lafiya a k'uncinsa, d'agowa yayi yana duban Mami dake faman huci ga hawaye na bin k'uncinta....
"Rik'e k'uncinsa yayi yana dubanta da mugun mamaki, abune da tun tasowarsa babu wanda ya tab'a masa, mugun kallo kawai yake watsa wa mahaifiyar nasa kafin ya soma fad'in" Mami you slapped me because of this worthless Man, Mami wllhi na tabbata Dad bai amso bashi ba, idan ma ya amso toh for the sake of the company ne, snn na rantse Alh Kasim was behind my father's death......"Labiiiiiib....!
"Mami ta daka masa wani irin tsawa hawaye na bin k'uncinta, Daga Alh Kasim har Barr Munir mamakin Labib ya hanasu koda motsawa...
"K'arasowa yayi gaban Alh Kasim kafin yace " Sai na zama ajalinka, ka rubuta ka ajiye.... Daga haka ya wuce sama yana tafiya kamar wani kububuwa..... "Durk'usawa Mami tayi a wajen ta shiga rera kuka....
"Mik'ewa Alh Kasim yayi yana sab'a babbar rigarsa ya fice a parlorn, zuciyarsa kuwa tamkar zata fashe, wai shine Labib ke gaya masa maganganun da duk duniyar nan babu wanda ya tab'a gaya masa yana a matsayin yayan mahaifinsa, lallai kuwa zai saita yaron nan yanda baya tsammani.
"Kai tsaye office d'in cikin gidansa suka wuce shida Barr snn ya danna wayar Faisal yace yazo yana bemansa urgently......
"Annah ta dubesa a karo na biyu kafin tace " Kaje kayiwa su Labib ta'aziyan.
"Ajiye spanner d'in dake hannunsa yayi gamida goge gumin fuskarsa kafin yace "Annah zanje yau insha Allah da zaran na tashi a aiki,
"Gyad'a kanta tayi kafin tace " Toh shiknn make sure kaji pls, dan idan baka je ba yaukam nida kai za'ajimu,
"Murmushi yayi mai bayyana dimples d'insa kafin ya goge bak'in man da ya b'ata masa hannu ya kamo hannayen Annah yace " Annah na Annahn Jalal na maki alk'awarin zanje insha Allah.
"Murmushi tayi kafin ta gyad'a kai tace nasan zakaje Jalal, Allah shi maka albarka,...."Usman ne ya k'araso wajen yana fad'in" Ah ah Annah har kin gama kallon shagon namu, ni nan nazo na zagaya dake wajen da ake gyara manyan motoci ne....
"Annah ta murmusa tace "Kar ka damu Unman ai na gani a haka ma, ubangiji ya dafa maku cikin sana'arku.... Ameen suka amsa dashi baki d'aya fuskokinsu d'auke da murmushi.
"D'an bubbuga hannun Jalal tayi kafin tace" Toh Jalaludden ni zan wuce gida na bar Zubaidah ita kad'ai, ta juyo ta dubi Usman dake tura tayan mota tace " Usman Allah Ya saka maka da mafificin Alkhairi, ga boy d'ina ka kulamin dashi.... Murmushi Unman yayi kafin yace " Ai babu komai Annah ai nida Jalal abu guda ne, kuma insha Allah zan kula dashi kamar yanda kikace ya k'arashe maganar yana dariyawa Jalal,
"Harara Jalal ya watsa masa kafin ya k'arasa ya rik'o hannun Annah suka fice har waje ya tare mata adaidaita, har saida yaga barinsu wajen kafin ya dawo cikin workshop d'in..
"Unman sai masa dariya yake wai anya ba shagwab'a yake wa Annah ba shiyasa take treating nasa like a kid.
"Murmushi da gefen bakinsa yayi kafin yace "She's always like that, and I love her so much, she's my parents, bansan dad'in mahaifi ba sai nata, she was my only family until Zubaidah came into my life....
"Jikin Usman ya d'anyi sanyi da jin kalaman Jalal, .... Shiru ya d'an biyo baya kafin Usman yace " and you're very lucky to have them as family she and your wife Zubaidah..... "Kallonsa Jalal yayi kafin ya gyad'a Kai a hankali yace "Yeah I know.... A wani b'angare na zuciyarsa kuwa tunani yake anya shida Zubaidah zasu iya kasancewa wann family d'in kuwa, kai abun da kamar wuya tunda already ya amince zai tafi ya bata waje tasha iska, k'ila idan ta jima bata gansa ba ta mance komai...... "K'aran horn ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi....
"Wata rantsattsiyar BMW 2016 ne ta shigo cikin garejin gyaran motocin, gani yayi Usman ya mik'e da sauri ya nufi mai motan, handshake sukayi fuskokinsu d'auke da murmushi kafin yaji Usman yace "Allah taimaki Shattima, Allah k'arawa Shattima tsawon rai.... Dariya sukayi su duka biyu kafin Shattima yace "Likitan mota Allah ya shiryaka, wato dai bazaka daina min wann tsiyar ba, Unman ya kuma yin gajeren Dariy kafin yace" Rankashidad'e irin gaisuwar data kamaceku knn..
"Murmushi kawai Shattima yayi kafin yace " Kasan meye wllhi sauri nake zan wuce Kaduna yanzu yanzun nan shine nace barin zo ka kwance min wad'an nan tayun don jiya na iso Abuja kuma tun jiyan nake jin kaman suna rawa ...
"Wai urgent kake so, gaskya saidai ka barta ta kwana a nan don wllhi ni yanzuma gidan abinci muka nufa, cewar Usman
"Haba Car Doc, kar muyi haka wllhi idan sak'on nan bai isa Gombe jibi ba ran Mai martaba zai baci kaga bai kamata ayi failing d'insa ba.
"Usman ya d'an tab'e baki kafin yace "Toh wai kai inji ne, daga Gombe ka nufi Abuja daga nan Kaduna ka kuma dawowa Abuja snn ka koma Gombe shin bazai maka uzuri ba, kai sudai masu mulkin nan izza da isa ne dasu, yo ba dole mota kullum a gareji ba...
"Gajeren tsaki Shattima yayi kafin yace "Wllhi kaifah kanada iskanci Usman, ce maka akayi mai Martaba na magana biyu, yarda dani da yayi ai shiyasa ya d'aurani kan hidimominsa, snn wann sunnar sarakuna ne basu magana biyu.
"Kai Why do I have to explain my self ma, gyara ne dole ka mun yanzu yanzun nan...
"Nannad'e hannayen rigarsa yayi ya sunkuya gamida wanke hannunsa da ruwan dake a cikin buta, ya d'iba yana d'an buge wondon jeans d'insa ba tareda ya kuma ce ma Shattima komai ba.
"Karya k'afa kawai Shattima yayi gamida turo hula gaban goshi yana kallon Unman cike da mamaki, koda ke ba abin mamaki bane idandai Unman ne yayi fin haka.
"Jalal muje idan ka gama ya fad'i haka yana k'arasawa wajen Jalal da ya canza kayan jikinsa daga blue uniform d'insu na aiki zuwa shirt da Jeans, fuskarsa ruwa ya kwanta luff...
"Wanda aka kira da Jalal Shaittima yake kallo, haka kurum ya tsinta kansa da fad'uwan gaba, snn wann daga gani miskilin k'arshe ne don ko kad'an Shattima bai kawo akwai wani a wajen ba don tun fara maganarsu kanzil bai furta masu ba.
"Shattima ya k'arasa gamida mik'a masa hannu yayi masa sallama, a tak'aice Jalal ya amsa sukayi masabaha. Shattima yace "Don Allah Jalal ka taimaka min kar ka biye na wann maras kirkin wllhi tafiyace a gabana, kuma ni idanba wann garejin ba bana zuwa ko ina, ni shinema in particular yake gyara min mota, don yaga na rik'e amanarsa ne shiyasa yake min wulak'anci.....
"Usman ya katse sa dariya gamida zubar da ruwan dake bakinsa kafin yace "Ayya mai sarauta ai kuka kakai gidan mutuwa idan dai wann ne ya fini dizgi barikaji, don shi har backing d'insa ake, wann da kake gani ma sana'arsa ma miskilanci yake shiyasa nake son zuwa naga wani irin tarairaya matarsa ke masa.....
"Kallon Unman kawai Jalal yayi gamida girgiza kai kafin ya dubi Shattima yace "Am kar ka biye nasa nidashi zamu duba maka yanzun nan....
"Kutt zaka duba masa dai don ni wllhi yunwa nakeji. ..... Baibi takansa ba sai jifa masa kayan aikin dake hannunsa yayi. Shattima kuwa me zaiyi banda dariya ganin yanda Jalal yasa dole suka soma duba masa mota....
"Mintoci kad'an suka gama d'aura masa wasu tayu had'i da warming motar abinka da k'wararru. Hararansu kawai Unman keyi, k'arshe daga Sbattima har Jalal dariya suka ringa masa Shattima yayita rok'onsu Allah Annabi suje suci abinci tare a eatery fir Jalal yak'i amincewa don shi alk'awari ya d'aukar wa kansa bai kuma rab'an wani mai abin duniya..
"Haka dole Shattima ya hak'ura ba don yaso ba, Usman kuwa mita yayita masa wai ai don yasan yanada mata me girka masa a gidane shiyasa yak'i amsar tayin Shattima, Tab'e baki kawai yayi kafin yace "Ai ban rik'e k'afarka ba, a tak'aice..
"Har yau Unman baisan me ya had'a Jalal dasu Labib ba shi dai kawai yasa ma ransa lokacin shiryuwan Jalal ne Allah ya kawo har yayi aure snn ya nisanta daga su Labib.......
"Ya jima yana kalllan k'ofar gidan kaman bazai shiga ba, sai kuma ya k'arasa yayi sallama wa securities d'in kafin yace "Su masa iso da Labib, gaba d'aya mamaki ne ya ishesu don kuwa sunsan a baya Jalal bashida shamak'i da gidan amma gashi yau neman iso yake.
"Babu musu d'aya daga cikinsu ya d'aga land-line d'in dake gate d'in ya kira cikin gida ya isar da sak'on Jalal....
"Mintuna k'alilan Labib ya fito don yasan ko yace ace Jalal ya shigo ba shigowan zaiyi ba......
"Tun daga nesa suke hango juna, for the first time da Jalal yaji tausayin Labib tun bayan incidence d'in da ya auka masu, gaba d'aya Labib yayi looking aabuntausayi shakka babu mutuwar mahaifinsa ya shiga jikinsa....
"Gaisawa sukayi ta hanyar musabaha kafin Labib yace "Mu k'arasa ciki mana,.
"Girgiza kai Jalal yayi kafin yace "No ba jimawa zanyi ba, I just came to say sorry for your loss, Allah Ya jik'ansa ya gafarta masa...
"A sanyaye Labib ya amsa da "Ameen, na gode Jalal.
"Jalal ya d'an dafa kafad'arsa kafin yace "Babu komai, ka gaida Mami pls sauri nake..... Ni zan wuce,
"Har ya juya yaji muryan Labib ya kira sunan sa
. "Jalal!
"Juyowa yayi yana dubansa, har gavansa Labib ya k'araso kafin yace " Na gode k'warai, and pls ka yafe mana abunda ya fraru a baya..
"Jalal ya d'an saka hannunsa cikin aljihun wandonsa kafin yace " Nasan kun bani k'waya nasha a daren sabida hankalina ya gushe ku cimma burinku akan yarinyar, kar ka damu ni na yafe maku wann, abunda bazan iya yafewa ba shine, I'll never ever forgive my self Labib, snn tsakaninku da yarinyar wnn babu nawa a ciki, idan ta yafe maku fine, abunda na sani shine na aureta ne to protect her, and I turn out to be her worse enemy, well I promise her zan tafi far away from her until she forgets everything, I'm pretty sure my Mum will take care of her har naje na dawo......
"Labib ya shafi gashinsa cike da kunyar kansa ko ince guilty conscious da ganin idon Jalal, don kunyar duniya da Labib sunyi hannun riga.....
"I'm happy for you bro, I wish you success in life Jalal, ya karsa gamida hugging kafadarsa, sallma sukayi Jalal ya wuce, har ya b'ace ma ganinsa kafin ya shige gida......
*Gombe, Dukku*
Baffah ya kallesa a karo na biyu kafin tace " Ka tabbata tafiyan shi yafi maka zama damu a nan.
"Ummar ya rataya jakarsa a kafad'ansa kafin yace "Baffah kar ku damu insha Allah zan dawo nan bada jimawa ba, snn na tabbata aikin da zan samu a wani garin zai fiye mun nan, snn zan manta da Zubaidah mantawa ta har abada.....
"Innah ta murmusa gamida goge k'wllan da suka zubo mata ta k'arasa ta dafa kafad'arsa, addu'an samun nasara suka masa daga ita har Baffah, suna d'agawa juna hannu har ya fice daga gidan.....
"Har bakin tasha Balele ya raka sa yanda ya shiga motar da zata fitar dashi zuwa Gombe, daga Gombe naga ya nufi motar danaji ana kiran garin *Abuja*
_Toh fah readers ga Umar ya tunk'aro garin Abuja, shin Me kuke tunanin zai faru,......? Jalal yana gab da barin Zubaidah..... Would she be safe??????_
Ku biyo QueenSamy don samun amsoshin.......
Sameena ce
[1/23, 22:16] +234 803 619 0581: đđđđ *ZUBAIDAH*
30
*©Sameena Aleeyou...✍đž*
_Queen Samy Novels Forum... đđ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Wata kyakkyawar budurwa ce a gefensa wanda ak'lla bazata gaza shekaru 24 ba, farace tass amma saidai daga ganin farin zaka gane akwai surki da man kanti, tufafin dake jikinta kuwa kaida ka gani kasan me tsadan gaske ne, a hankali take taunar chewing gum kaman bata son yi.
"Tun zamansa ta kafesa da idanunta, sosai ta kwad'aitu dashi, jikinsa ne ya basa ana kallonsa, d'an juyowa yayi aikuwa nan sukayi ido hud'u, murmushi ta sakar masa har lokacin idanunta na kansa,
"Bai maida mata martanin murmushinba saima kallon window da ya soma yi, budurwar ta ciro wayarta k'irara iPhone7 ta soma dannawa....
"Har suka kusa shigowa garin Abuja wann budurwa bata daina bin Umar da mayen kallo ba. Gaba d'aya ya tsargu da irin kallon da take masa, suna isowa tasha kowa ya soma fita daga motan.
"Raba ido ta soma yi tana neman ina ya shige, zaune ta hangosa saman wani benchi yana kallon mutane masu kaikomo, murmushi tayi kafin ta k'arasa wajensa cikin salo na tafiya da dogon takalminta mai d'ankaren tsini...
"Sannu bawan Allah, ta fad'i daidai sanda ta k'araso yanda yake zaune.
"D'ago ido yayi ya dubeta, tsaf ya ganeta budurwan nan ne wacce ta tsaresa da kallo a mota.
"A tak'aice ya amsa mata daga haka bai kuma cewa komai ba,..
"K'ok'arin zama ta soma yi gefensa yayi saurin mik'ewa tsaye yana binta da kallon mamaki kafin yace " Baiwar Allah lafiya kike bibiyata...
"Murmushi tayi kafin tace " Da farko dai sunana *Zulaihat* snn ba bibiyarka nake ba hanyace dai ta had'amu, da alama Kai bak'o ne a garin nan, don naga kowa na watsewa kai kana zaune, snn dokar wann tashar idan ka wuce lokutan rufewa za'a cika tara. Amma kodayake bansan dalilinka na zama a nan ba, ina ka nufa???
"D'an kauda kansa gefe yayi yana rage girman idanunsa kafin yace " K'warai ni bak'o ne a garin nan, snn kamar yanda kika fad'i vansan dokoki da tsarin tashar nan ba, na gode k'warai da kulawarki ni zan wuce, daga haka ya sab'i hakarsa ya soma tafiya
"Kallo tabisa dashi har ya nufi gate, d'an sauk'e ajiyar zuciya tayi kafin ta ciro wayarta cikin jaka ta shiga neman layin d'aya daga cikin samarukanta da take wanka...
"Hello Tariq, pls kazo tasha ka d'aukeni yanzu dawowata daga Gombe....
"Daga d'aya b'angaren Tariq yace " Uban me kikaje yi a Gombe Zulaihat, ki fad'a min kiran wani shegen Alhjin kika amsa...
"Gajeren tsaki Zulaihat tayi kafin tace "There you go again, shiknn bazanje naga dangina ba how many times do I have to tell you, Gombe garin iyayenane..... "Katseta yayi da sauri yana fad'in
" Look karki nemi raina mun hankali na sani sarai daga Yola kika zo Abuja neman abun duniya, kuma saida kika amince min bazaki sake bin wani ba bayana wato shine kika zaga kika tafi Gombe don kinga kwana biyu ban zauna ba koh, toh wllhi kikayi wasa zan k'wace makullan gidan dana kama maki haya.....
"Dalla malam ya isheka, Why do I even have to explain my self, you don't owe me any explanation, rayuwata ce nayi yanda naso da ita, kan wani shegen gidan da ka kama min kake neman yimin gori, wllhi kaima sanin kanka Tariq ni ba ajinka bane kuma kar ka sake nemata daga yau kashe wayar tayi gamida yin k'wafa....
"D'an gajeren tsaki yayi kafin yayi dialling lambarta, saida ya kira sau uku tana ejecting kafin a na hud'u ta d'aga tana wani yamutsa fuska, hak'uri ya soma bata yana lallashinta, da k'yar ta hak'ura kafin yace " Tayi hak'uri yanzu haka Dad d'insa ya aikesa ne urgent, he can't fetch her but he promised da zaran ya gama da Dad dinsa zaizo...
"Tana kashe wayar taja tsaki a fili ta furta k'aramin d'an iska,
"Tana fitowa gate ta hangesa har lokacin na tsaye bakin titi. Murmushi tayi kafin ta k'arasa wajensa....
"A firgice ya farka daga mummunar mafarkin da yayi, rufe fuskarsa yayi da tafukan hannayensa kafin yayi addu'a, mik'ewa yayi ya lek'a barrandan Annah, zaune ya hangosu ita da Annah suna duba litattafan da aka sayo mata na makaranta daga gani zaka gane suna cikin farin ciki, don ya nuna a fuskokinsu, sauk'e ajiyan zuciya yayi yana tuno mafarkin..
_"Wai gashi nan rataye da jakarsa zai tafi, har ya soma nisa yajiyo muryar Zubaidah tana k'walla masa kira, juyowar da zaiyi yaji ta rungumesa cikin jikinta, a hankali yaji tace "Na yafe maka Jalal duniya da lahira, rungumeta sosai yayi cike da farin ciki ta rakosa har k'ofa, har ya shige mota tana masa waving tana murmushi...... "Gefe da ita kwatsam ya hango Labib Salim da kuma Tariq suna Torrik'e da makamai suna wani irin dariya.... Da sauri ya fito daga motan ya nufota saidai kafin ya k'araso ya hangi tsohon saurayinta Umar ya sureta da k'arfin gaske yasa gudu, ihu take tana kiran Jalal, saidai kafin ya k'araso mota tabi kansa...._
"A hankali ya sauke ajiyan zuciya, ya dubi 'yar k'aramar agogon dake mak'ale bangon d'akin ya nuna k'arfe 5:30 na yamma, bathroom ya shiga ya sakar ma kansa shower sabida zafin da ake sosai a garin....
"Fitowa yayi cikin shiga ta k'anan kaya, sun karb'esa sosai, hayi taje gashinsa da yasha aski da gyaran fuska Wanda ya fito da asalin kyaunsa, kallo d'aya ta masa ta d'auke kanta sanda yake nannad'e hannun rigarsa, tsuka taja a hankali take annurin fuskarta ya d'aukewa ga wani irin fad'uwar gaba data tsinci kanta dashi. D'an karasowa yayi yana satan kallonta yake gaida Annah, Hadiza ne da d'anta Kamal suka shigo.
"Kamal ya tafi da gudu ya rungume Jalal yana fad'in "Uncle Jay, rungumesa Jalal yayi yana dariya ya d'agasa sama yana masa wasa, da gefen idonta ta saci kallonsu, sosai Kamal da Jalal suka shak'u......
"Gaisawa suke da Annah amma hankalinta naga Zubaidah dake faman shirya littafan gabanta, tab'e baki Hadiza tayi kafin ta dubi Jalal da har lokacin wasa yake da Kamal kafin yab'e baki tace "
"Ni ban tab'a ganin irin wann aure ba, ace miji bashida iko da matarsa halan kai ka bata izinin komawa makaranta, ta k'arashe maganar tana duban Jalal,..
"Mik'ewa Zubaidah tayi tana binta da mugun kallo kafin tace " Ni ba matar aure bace kar ki sake kirana matar aure, daga haka ta kwashi books din ta wuce d'aki kaman zata tashi sama..... "Dariya Hadiza ta kwashe dashi harda rangad'a guda, burinta knn dama ta k'untata wa Zubaidah....
"Daga Annah har Jalal kallo suka bita dashi, Jalal ya girgiza kai kafin ya sauk'e Kamal dake kafad"ansa yabi bayan Zubaidah......
Sameena ce đđž
[1/23, 22:17] +234 803 619 0581: đđđđ *ZUBAIDAH*
31
*©Sameena Aleeyou...✍đž*
_Queen Samy Novels Forum...đđ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Da saurin gaske ya finciko hannunta ta fad'o jikinsa, wani irin yanayi suka shiga su duka biyun,..Yanda k'irjinta yake bugawa da sauri kuwa har cikin jikinsa yake ji.....
"K'ok'arin k'wace kanta ta shiga yi da iyakan k'arfinta tana fad'in ya cika ta,
"Kallonta yake fuskarsa a tamke kafin ya shiga jan hannunta.....
"Tirjewa take tana fad'in "Malam ka cikani nace, ni ba 'yar iska irinku bane, dalla cika ni ina zaka kaini..... Bai kuma saurarenta ba sai suranta da yayi ya azata a kafad'a had'ida toshe bakinta da hannunsa.....
"K'ok'arin ihu take kanyi tana neman hanyar k'watan kanta, Bai ajiyeta a ko ina ba sai d'akinsa.....
"Innalillahi jikin Zubaidah ne ya soma kyarma sosai, take ta shiga tuno fuskokinsu, jada baya ta soma yi tana jawo rigarta tana k'ok'arin rufe jikinta, tama kasa ihun sai mannewa jikin garu da takeyi tana cije leb'enta tana girgiza kai...
"Sanda ya zauna gefe da ita, ta yunk'ura zata tashi had'i da k'ok'arin kwand'ara ihu.....
"Rik'ota yayi ta fad'o kansa suka zube saman katifar yayi amfani da d'aya hannunsa ya toshe bakinta.... Banda kuka da kyarma da jikinta keyi bata komai....
"Duk sai yaji babu dad'i it wasn't his intention to scared her... A hankali ya rungumeta tsam cikin jikinsa kaman me rad'a haka ya soma fad'in" I'm sorry, I didn't mean to scared You, I only want us to talk, babu abinda zan maki so pls listen to what I'm gonna say.
"Jin lallausar fatarsa take tamkar garwashin wuta ne a jikinta, d'akin kuwa jinsa take tamkar cikin wuta aka jefata,..
"Jin tayi shiru yasa sa bud'e mata baki still tana rungume cikin jikinsa,.
"Jalal yaci gaba da fad'in" Zubaidah nasan bazaki tab'a yafemin ba duk da ban aikata laifin ba, but believe me I will never forgive my self either for not stopping them, I'll live with the pain.....
"Jin maganganunsa take tamkar ana zubawa kunnuwanta ruwan dalma dukda dad'i da muryarsa kedashi, toshe kunnuwanta tayi tana ci gaba da hawaye....
"A haka take fad'in" Wllhi wllhi na tsaneka na tsani ganinka, don Allah ka tafi ka k'yalemin rayuwata ka sakeni kowa yaje yayi rayuwarsa, na tsani na tuna waini Zubaidah inada auren mutumin danafi tsana a duniya a kaina,.... A hankali taci gaba da fad'in" Bazan tab'a manta wann fuskar taka ba, kai ka fara rik'oni a lokacin da nake k'ok'arin tsere ma sharrinku, lokacin da nake k'ok'arin tserewa mutuncina da martaba ta, duk bakuga wann ba sabida bakuda 'Ya'ya snn baku da k'anne dukanku, kuka k'etan haddi na ba tareda d'and'ani tausayi ba balle imani, sabida kunada masu tsaya maku, aka hanani magana snn aka aura min mutumin da yafi kowa zalunta ta a duniya, shin kuna tunanin Allah zai k'yaleku, kun lalata rayuwar yarinyar da bata ci maku ba bata sha maku ba, an dunk'ule rayuwata an jefa cikin wani 'yar takarda na kud'i an damk'a maka sabida asirin 'Ya'ansu ya rufu. Ka sani bakufi k'arfin Allah ba da Sannu zai saka min d'aya bayan d'aya...... Kuka ya kuma kufce mata ta shiga matsewa cikin garu kamar wacce ta tuna wani abu....
"Zogi da rad'ad'i zuciyarsa take masa take idanunda suka kad'a sukayi jazur, tabbas duk abinda Zubaidah ta fad'i haka ne....
"Kallonta yake yanda ta matse jikin garu tana kuka, tausayinta ya cika zuciyarsa, k'ok'arin matsowa kusanta ya soma yi, tayi saurin d'ago kai had'i da girgiza kai tana fad'in kar kayi gigin matsowa kusana, ka bud'e mun k'ofa na fice....
"Jiki a sanyaye ya mik'e yayi yanda tace.
"Da saurinta tazo zata shige yayi saurin tare k'ofar da hannunsa, d'ago kai tayi tana dubansa, gani tayi gaba d'aya fuskarsa tayi ja sosai haka nan idanunsa, gajern tsaki tayi kafin tace " Malam zan wuce.
"D'an fuzar da iska yayi kafin yace " Tambaya d'aya nake so na maki....
"Murmushin takaici tayi kafin tace " Darajar Annah kaci wllhi shiyasa ma na tsaya saurarenka, tanada mutunci tanada kirki wllhi batyi deserving d'a irinka ba, so let pass....
"Gyad'a kansa yayi kafin yace "K'warai she deserves a son better than I, Na sani. Shiyasa nake so na sake cin darajarta ki amsa min wann tambaya nawa.
"Idan na tafi zaki yafe mun...
"Kallonsa tayi gamida kauda kai gefe kafin tace " Har abada bazan tab'a yafe ma d'aya daga cikinku ba, don Allah ka tafi ka bar rayuwata and never come back...
"Sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin yace " I hope one day you'll forgive me and you'll realize that I'm doing this to protect you....
"Murmushin takaici tayi kafin tace " I never need your protection snn ko gawarka ce a gabana bazan tab'a yafe maka ba...
"A hankali ya sauk'e hannunsa ya bata hanya kafin ya furta zan tafi as you wish.... Ficewa tayi cikin sauri kaman zata kifa k'asa...
"Hadiza dake lab'e taga fitowarta daga d'akin Jalal, tayi saurin k'arasa tasha gabanta tana dariya harda shewa kafin tace " Ashe a gabanmu ne kike gwada baki sonsa baku ko magana, ashe dai har turakansa kike zuwa, ayyirririr ni Dije naga Salon soyayyar zamani......
"Hararanta kawai Zubaidah keyi da idanunta da taci kuka, wani kukan ne ya kuma kufce mata, cikin kuka take fad'in nidae wllhi ba matar aure bace, kar ki sake kirana matar aure..... Daga haka ta nufi barandar Annah tana kuka.
"Hadiza tayi wani shewa kafin tace " idan baki sonsa me ya kaiki d'akinsa, dogon tsaki taja kafin ta wuce tana rangad'awa mijinta kira....
"Kan Annah ta fad'a tana kuka, har magrib Annah na lallashinta tana akin abu guda....
"Kallo yake kan faman bin layin dashi, yanayin mutanen da yake gani suna wucewa ya tabbatar masa babu kamun kai wajen.
"Juyowa Zulaihat tayi tana dubansa kaman ta gane tunanin da yake tayi d'an murmushi sanda ta saka d'an makulli tana bud'e k'ofar kafin tace " Kaga yanayin layin namu haka ko, kasan akasarin mazauna unguwar nan 'yan makaranta ne kaman ni, ka kwantar da hankalinka ka saki ranka.
"Gajeren murmushi yayi sanda tai masa nuni da saman sofa ya zauna.
"Kayi hak'uri fah gidan nawa babu wani abin tab'awa kasancewar yanzu na shigo garin. Amma barin dafa mana abu me sauk'i.
"D'an murmushi yayi kafin yace "Kar ki damu masauk'in da kika min ma na gode zuwa gobe zan tafi neman abinda ya kawo ni.
"D'an murmushi tayi kafin ta cire d'an mayafin dake jikinta, take suran jikinta cikin matsettsen d'inkinta wanda tamkar a jikinta aka d'inka ya bayyana, saurin d'auke kansa yayi daga barin dubanta, tayi wani murmushin cin nasara kafin ta soma tafiya cikin kwarkwasa ta nufi kitchen.
"Mintuna kad'an ta dafo masu indomie da soyayyen kwai.
"Gaba d'aya kasa sakewa yayi sabida kayan dake jikin Zulaihat, rabin k'irjinta a waje yake, snn da gangan take sunkuyawa komai ya bayyana, da kanta tayi serving nasa sai jansa da hira take tun yana basar da hiran nata har ya soma amsata jefi jefi...
"Amma me ya kawo ka Abuja Umar, nasan bai kamata na maka wann tambayar ba, but I don't may be I can help.
"Shiru yayi yana tunani cikin zuciyarsa, ya fad'a mata ne ko kuma kar ya fad'a mata, Wata zuciya tace ka fad'a mata k'ila tasan gidan da kazo nema.
"D'an karkad'a spoon d'in hannunta tayi saman fuskarsa tace " you there...
"Murmushi yayi kafin yace" Wani gida nake nema a cikin Abuja ko kin sani.
"Wani gida kenan, ta tambaya tana dubansa.
"Gidan Alh Kasim Dasuki.
"Murmushi Zulaihat tayi kafin tace "Ai duk garin nan babu wanda baisan gidan Alh Dasuki ba, k'ila ta'aziya kazo masu.
"Baison jan zancen Don haka kai tsaye ya gyad'a mata kansa ba tareda yace Komai ba, a fili yace zaki bani adress din gobe insha Allah.
"Ba tareda ta kawo komai ba ta gyad'a kanta kana tace " Yeah sure, for now finished your food I'll right back ta fad'i tana mik'ewa.
"Gyad'a kansa yayi a cikin ransa ya furta " JALAL, kwanan ka ya k'are your dead has arrived...
Sameena ce đđž
[1/23, 22:17] +234 803 619 0581: đđđđ *ZUBAIDAH*
32
*©Sameena Aleeyou...✍đž*
_Queen Samy Novels Forum...đđ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Shiru Zulaihat tayi tana tunanin anya batayi gangancin sauk'an stranger a gidanta ba, wata zuciya tace " But You fell for him the very moment you saw him.
"D'an jimm ta kuma yi kafin zuciyarta taci gaba da ayyana mata "Anya kuwa bazata kira Tariq ta tambayesa ba tunda he's related to the Dasuki's, toh kuma idan kika kira sa fah, what about your plans for this hot guy da kike tsananin sha'awan had'a jiki dashi?.. Just let him be, ki zuba masa ido kiga gudun ruwansa snn kiyi k'ok'arin samun abinda kike nema wajensa.. Da wann tunani Zulaihat tayi murmushi kafin ta mik'e ta nufi parlor cikin wasu arnan kayan baccinta wanda suda babu dangin juna ne.
"Yanda ta barsa kishingid'e kan sofa haka ta dawo ta taddasa, kafe sa da ido tayi komai nasa ya burgeta, irin mazan da take tsananin son huld'a dasu knn, a hankali ta k'araso gamida zama hannun kujeran, d'an rank'wafowa tayi ta tsura wa labb'ansa ido, a hankali ta had'iye miyau, d'an yatsanta tasa ta shiga lailaye fatar bakinsa gamida hura masa iskan numfashinta tana wani lumshe idanu....
"Kaman a mafarki haka yaji wani bak'on Al'amari na faruwa dashi, cikin sauri ya bud'e idanunsa masu d'auke da bacci ya sauk'esu kanta, a razane da yanayin nata ya matsa k'arshen kujeran gamida kauda kai gefe don kuwa wann shiga nata ko kad'an bai dace ya kalla ba.
"D'an saita kanta tayi don tasan wnn dole tasha wuya kafin ta samesa da gani baisan hark'arba.
"Ganin ya bita da kallon tuhuma yasata saurin mik'ewa tana had'a igiyar rigarta kafin tace " Sorry I didn't mean to wake you up, dama ce maka zanyi da ka koma d'aki ka kwanta kan gado you will be more comfortable kaman kujeran ta kasa maka....
"Gajeren tsaki yayi kafin yace " Nan ma yayi min na gode, daga haka ya juya da fuskarsa gefe, ba don yana so ta basa adreshin gidan Dasuki's ba da tuni ya cika ma rigarsa iska....
"Zulaihat ta sha jinin jikinta ganin irin dizgin da yayi mata, amma dashike ba kunya bace da ita, zagayowa tayi ta gabansa snn ta soma tafiya cikin kwarkwasa ta yanda duk wani gab'a na jikinta ke motsawa. Fuska d'auke da murmushi tace mu kwan lafiya.....
"Bai iya amsa mata ba sai had'iyan miyau da yayi snn ya kasa daina kallon salon tafiyarta, a hankali ya dafe kansa sanda ta shige d'akin, wani irin yanyi maras fasaltuwa ya ziyarcesa.....
*Washe gari*
"Mami zan amsa kiran Uncle ne sabida ke, dan idan ta nine wllhi ko fuskarsa banson gani... Bata amsa sa ba sai ci gaba da had'a masa buttons d'in hannun rigarsa data ci gaba da yi.
"Tallafo fuskarta Labib yayi da hannunsa kafin yace" Are you still mad at me, com'on Mami I said I'm sorry, shikenan fine I promise you I'll try to control my temper and I'll learn how to put up with him, but he would explain to me how the heck my Dad borrows those money.... Manna mata peck yayi a kumatunta sanda ta gama hada masa aninin hannun rigar, Jacket dinsa ya d'auka suka nufo downstairs a tare, da kanta tayi serving nasa breakfast, ma'aikata sai kai komo suke, suna masu mamakin yau Labib kaman ba shi ba, da alama na cikin farin ciki don kuwa har suma ya gaisa dasu yau...
"K'arfe 8:15am daidai ya fito daga mansion din ya nufi motarsa k'irar Mercedes Benz,..
"Cak ya tsaya da motarsa ganin wani mutumi sai faman fafatawa suke da securities both masu tsaron gidansu da masu tsaron gidansu Salim dashike gidan a manne ne komai iri guda idan baka sani ba ma saika d'auka gida guda ne., Tuhumarsa suke me ya biyo dashi layin.
"Horn ya masu sukayi saurin k'arasowa suna fad'in" Sorry Sir had'i da wangame masa babban gate d'in wanda yake k'arafuna ne sanda sanda kana iya hango waje.
"Labib yace " Who's that Man Jerry?
"Sir we have no idea who he's, but we are suspecting him hes up to something, or may be someone sent him to spy on you *The Dasuki's*
A hankali yayi wata silent smile, "what if this man is after Kasim Dasuki, what if he's planning to take revenge on Alh Kasim, k'ilma wani business partner dinsa ya cuta shine ya turo wnn mutumin ya masa bincike don ya tarwatsa Alh Kasim don yasan Uncle dinsa is a very wicked person, lallai kuwa idan zarginsa ya tabbata haka he'll work hand in hand da wann mutumin don su ruining Alh Kasim.... "Cikin sakanni da baifi biyar ba yayi wann tunani kafin ya murmursa a hankali ya furta " My Uncle.... Kafin ya wani foze ya dubi Jerry yace "
"Bring him to my penthouse dags haka ya fice daga cikin motar ya nufi cikin gida da k'afa don kar Mami tasan cewa bai wuce amsa kiran yayan mahaifin nasa ba a chan company.
"Yana zaune a bar D'ins suka shigo dashi a rirrik'e, da sauri ya mik'e gamida daka masu tsawa yace "Let him go "
"Sakesa sukayi kafin suka soma apologizing. D'aga masu hannu yayi kana yace " Kuna iya tafiya, a tare suka fice Labib ya d'an Bud'e murya ya kira Jerry,
"Yes Sir, ya amsa Gamida tsayuwa yanda yake, saitin kunn Jerry yace cikin rad'a" No one should know about this not even my uncle. Gyada kansa Jerry yayi cike da girmamawa yace " Okay sir, daga haka ya fice...
"Labib ya juyo suna fuskantar juna shida UMAR..
"Yanzu ke Zulaihat kan me zaki taimaka ma wann mutumin, baki sansa ba baki san shirinsa akan Dasuki's ba kawai kinsa mun kawo sa what if mugu ne, kema fah kinada kamisho, Cewar IMAM, matashin drivern taxi wanda kullum Zulaihat tayi shirin fita satark'fa muddin bata so Tariq yasan ta fita toh shi take kira ya Kaita, Zulaihat da Imam sun saba sosai tun yana mata nasiha tana basarwa tana tsigalesa tana fad'in ya tsaya matsayinsa na dreban taxi har ta gaji ta soma jure sauraren wa'azin sa, amma ko yayi wucewa take ta bayan kunne don ba shiga kanta yake ba. Shi kuwa Imam yasha alwashin bazai tab'a gajjiyawa dayima Zulaihat wa'azi ba yana junta tamkar k'anwarsa dukda ratan dake tsakaninsu a shekare akk'alla bazai wuce shekara d'aya zuwa biyu ba...
"Harara ta gallawa Imam kafin tace ka kama kanka nd pls stop talking n concentrate on your job.....
"Murmushi kawai yayi gamida maida hankalinsa kan titi.,
"Ina muka nufa? Ya tambaya sanda yake sharan kwana..
"A tak'aice ta basa amsa " Any nearby eatery don ni yunwa nake jima, ko karyawa bai bari munyi ba muka fito, ta k'arashe maganar tana mai saka hannu cikin Jakarta, wata 'yar takarda ta ciro, nan ta tuna jiya ne ya fad'i daga jakan Umar kuma ta manta bata basa ba. A hankli ta soma warware takardan, ta karace sa tass...
"A fili ta furta "Jalal, Zubaidah" innalillahi sai yanzu tasan asalin dalilinsa na neman gidan Alh Kasim Dasuki, shakka babu tasan sunan Jalal a wajen Tariq amma bata tab'a ganinsa ba, kenn Umar tattaki yayi tun daga Gombe sabida budurwarsa, take taji kishin Zubaidah ya tokare mata mak'oshi dukda ba saninta tayi ba.....
"Har suka isa gidan cin abincin hankalinta bai jikinta har saida ta jiyo muryar Imam yana fad'in" Na fito na rakaki ne, d'an harara ta watsa masa kafin tace " Ka raka wa, kana taxi driver d'in Allah sawak'eni, ai saika kashe mun market ka sani ko nayi new catch a restaurant d'in....
"Murmushi kawai yayi ya bita da kallo har ta shige kafin ya fito ya d'ale saman mota ya zauna......
"Labib ya mik'a masa hannu alamun musabaha kafin yace " Labib Dasuki,...
"Kallonsa Umar yake yi kaman bazai basa hannu ba sai kuma ya mik'a masa shima kana yace " Umar Sanda.
"Let me go straight forward kafin ka tambayeni, .
"I'm here to take my revenge on your brother or what ever JALAL Dasuki. Nazo ne na amshe abinda ya k'wace daga gareni the love of my life Zubaidah, and finally give him what he deserves.... KILL HIM......
"Gaban Labib yabada dummm, abu na neman juye masa yayi zaton mfaraucin Alh Kasim ashe mafaraucinsu ne don kuwa da ace zaisan Jalal bai aikata laifin ba su suka aikata da shine first on the list....
"Saurin saita kansa yayi kafin ya mik'e tsaye ganin yanda idanun Umar suka koma jazur he's capable of taking revenge.
"Dafe kafad'un Umar yayi kafin yace " So she was to marry you before Jalal ruins everything, I'm sorry I really pity your condition, it isn't easy to lose someone you love....
"Buge hannunsa yayi yana masa mugun kallo kafin yace " Ban rasata ba kuma bazan rasata ba, and to make it clear to you, that precisely why I came here, to take her back with me, to take back what was stolen from me, what's rightfully mine...
"Baki Labib ya hangame yana kallonsa he never thought wann mutumin can speak English fluently, lallai d'aukan revenge akansu bazai masa wahala ba, he needs to do something before he learns everything....
"Calm down pls, kayi hak'uri ka zauna and let's talk sensibly.
"Sauk'e ajiyan zuciya Labib yayi kafin yaci gaba da fad'in" Jalal, Jalal, ba d'an Family d'inmu bane hasalima mahaifiyarsa aikatau take a gidan nan, mahaifanmu sun ruk'esu bisa gaskiya da amana, muma haka muka d'aukesu gaba d'aya, cuz we followed our parents steps.
"Bamu ragesu da komai ba, a lokacin da mukaje Dukku bikin sakun ranar cousin d'ina Salim Jalal saw her, yayita bamu labarin yanda yake sonta coz we're like brothers we didn't hide things from each other.
"Duk mun zaci son gaskiya yake mata until the incidence happens, although yace da son ranta hakan ya kasance coz duk sun kamu da son juna,
"His poor mother cried hard lokacin da labari ya isketa, sukayita rok'on Uncle d'ina kan ya Aura masu juna don kar su zamo abun nunawa a gari, My uncle did as they wanted, na fada maka iyayenmu basu vanbantamu da Jalal, babu wanda yace masu su bar gidan nan suka tattara suka koma yanda babu wanda ya sani cikinmu, despite all the good things da aka masu basu mana sallama ba balle musan yanda suka koma,
"Ya d'an fuzar da iska kaafin yaci gaba da fad'in" But I'll help you find him, I promise you that, you have my word..
"Kallonsa Umar keyi cikin wani irin yanayi without saying a word, ashe dama Jalal ba d'an Dasuki Family bane, he's just no body like him, lallai yak'in bazai masa wuya ba,........ Amsa wayan da yaji Labib nayi ne ya katse masa tunanin nasa.
"Hello Buddy. Ya akayi ne, cewar Labib bayan ya k'ara wayar a kunnensa.
"Daga d'aya b'angaren Salim yace " What's wrong with you Labib, kowa Ya taru a conference hall kai kawai ake jira, the meeting is about to start Don Allah kayi ka k'araso....
"Okay okay fine, I'll be there right away, you know me I never dose things on time... Sai na iso daga haka ya katse wayar....
"K'arasowa yayi yanda Umar yake kafin yace " Ni zan wuce office inada meeting ni kawai ake jira and kaga bai kamata na bar mutane suyita jirana ba, You'll continue daga yanda muka tsaya, za'ayi serving naka breakfast to lunch har na dawo, just feel at home, ya nuna masa wani d'aki wanda basai ance maka guest room bane yace " You can keep your luggage in there.... Daga haka sukayi sallama har lokacin jikin Ummaru na mace....
"Tunda ta shigo restaurant d'in take kallonsa yanda yake cin abincinsa cikin tsanaki, waiter na tambayarta order ko saurarensa batayi ba ganin guy d'in nan ya ciro cell phone d'insa yana waya....
"Hello Jalal, gani na shigo cikin Abuja yanzun nan, yeah wllhi meeting nake dashi 10:am yeah, da zaran na gama zan d'auki hanyar gombe shiyasa ma na kiraka don karkuyita jira na, eh na kira layin Usman bai zuwa, yauwa na gode ka gaida min amarya Zubaidah pls, next time dai zanzo mu gaisa,
"Ya d'anyi murmushi kafin sukayi sallama ya katse wayar....
"Kallo ta bisa dashi, a hankali ta furta Zubaidah Jalal, tabbas sune mutanen da Umar yazo nema, ganin yana gab da k'arasa cin abincinsa yasata mik'ewa ta nufi Table d'insa.....
Sameena ce đđžđđžđđž
[1/23, 22:17] +234 803 619 0581: đđđđ *ZUBAIDAH*
33
*©Sameena Aleeyou...✍đž*
_Queen Samy Novels Forum...đđ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Zama Zulaihat tayi kujera mai kallon nasa fuskarta d'auke da murmushi, ..
"Ajiye fork d'in hannunsa yayi yana dubanta fuska d'auke da alaman tambaya.
"Sannu bawan Allah ta fad'i tana mai fad'ad'a murmushinta.
"A tak'aice ya amsa mata had'i da yin gajeren murmushi, ganin murmushi saman fuskarsa yasata samin k'warin gwiwa, kan tayi magana ya d'anyi gyaran murya kafin yace " How may I help you?.
"Em..em da Allah dama so nake ka ajiye min jakata I want to use the restroom.
"Ba tareda ya kawo komai ba yayi muushi yace " It's not a problem, kina iya zuwa, amma idan kika wuce 10mins zan tafi don akan hanya nake..
"Murmushi tayi kafin tace " I won't take long, daga haka ta wuce tana sakar masa wani shu'umin murmushi...
"Mintuna kadan ta dawo don dama babu abinda ya kaita restroom d'in wanke hannu kawai tayi ta fito,
"Nan da nan Zulaihat taja Shattima da hira, shi da kansa ya tambayeta me zata ci, cike da kwarkwasa da Mad'e ta fad'a masa, waiter yayima alama da hannu yazo kafin ya fad'a masa abinda zai kawo wa Zulaihat, hira sosai Shattima da Zulaihat suka sha har saida ya kusa makara zuwa meeting d'in nasa, k'arshe exchanging phone number sukayi yace mata zai dawo Abuja soon...
*Dasuki Holding*
"Babban ofishin taron tayi tsit yayinda suke gudanar da meeting d'in cikin tsanaki.
"Shaidun da suka gabata gaban Labib yasa jikinsa yin sanyi, tabbas da gaske ana bin mahaifinsa bashin mak'udan kud'ad'e snn yaga yanda Alh Kasim ke k'ok'arin ganin ya saving company d'imsu from going bankrupt...
"Muryar Alh Kasim ya katsesa sanda yaci gaba da fad'in" As you all know we are not financially stable, taimakon Allah guda da yasa muna tare da mutane da suke son ganin ci gabanmu, thank you all for your financially supports, snn nayi alk'awari zanyi clearing duk wani bashin da marigayi k'anina ya ciyo da sunan wnn company...
"Haka har aka k'arashe meeting d'in mutane na allason barka da Alh Kasim...
"Sanda kowa ya watse ya rage daga shi sai Barr Munir sai kuwa Labib dake zaune tamkar dutse a wajen, kallon juna sukayi shida Barr Munir kafin suka sakar ma juna mayaudarin murmushi, a hankali ya d'an d'agawa Barr Munir babban yatsan sa a sace kafin ya k'araso ya dafa Labib yace
"Son wnn shine abinda nake kan fad'a maka ka kasa fahimta, shiyasa nace gara kazo ka gane wa idanunka, ba don taimakom Allah da kuma taimakon Alh Tahir Marafa ba, who knows wani irin karayan tattalin arziki zamu fuskanta. Yanzu abinda nake so da kai ka tashi ka tafi office d'inku kaida Salim yana nan floor d'in office d'ina..
"OK kallo basu ishesa ba, haka kurum yake jin bai yarda da Uncle d'in nasa ba, tunowa da yayi da Umar yasa sa sakin wata murmushi, da wnn tunanin ya gwada masu komai ya wuce harda hugging uncle dinsa ya basa hak'uri kan abubuwan da ya masa kafin ya nufi office d'insu shida Salim....
"Salim yana hangosa ya kwashe da dariya kafin yace " Dan iskanci saida ka gama shanya manyan mutane snn ka sami isowa.
"Tab'e baki Labib yayi kafin yace " So...
"Salim ya girgiza kai kawai kafin ya soma turo masa files gabansa yana fad'in" here there's alot of work.
"Kallonsa kawai Labib keyi yana wata murmushi kafin yace " If I ruined you I know Kasim Dasuki will definitely die coz you are his life, his only precious son.....
"Wai murmishin Me kake tayi ne, Salim ya tambaya sanda yake Bud'e McBook me d'auke da tambarin Dasuki holding wato *D¤H*
'Bai cemasa komai ba sai mik'ewa da yayi ya nufi fridge......
"Sanda Labib ya koma gida basu samu sunyi magana da Umar ba, don ya Sanar dashi yana son komawa gida gobe da sassafe an yo masa waya Baffansa bashida lafiya sosai, Labib yace babu komai har gida zaisa a kaisa snn idan ya tashi dawowa waya kawai zai masa ya tura driver, har wani d'an sabo sukayi a rana guda... Duk wann wainar da Labib ke tuyawa a gidan Mami batada masaniya.....
"Zaune suke a parlor Annah tana koyawa Kamal assignment, Annah na zaune gefe tana kallon Tv jefi jefi tana tayasu home work d'in...
"Sallama yayi had'i da turo labulen a hankali, Annah ta amsa masa gamida masa iso,
"Kaman wani b'arawo haka ya soma shigowa cikin sand'a.
"Murmushi Annah ta sakar masa ya k'arasa gefenta ya zauna yana satan kallon su Zubaidah, gaba d'aya tun shigowar sa ta canza, Kamal kuwa tuni ya tafi wajensa yana zuba masa surutu, wani mugun haushi takeji idan Kamal Ya kirasa Uncle Jay, ta tsanesa ta tsani ganinsa babban farin cikinta shine saura sati guda chif ya tafi kaman yanda ya fad'a mata.
"Da dabara Jalal yasa Kamal komawa wajen karatunsa da shike ta d'an gefen parlorn suke zaune...
"Hiran wajen aiki Jalal da Annah suke tab'awa amma rabin hankalinsa baya gareta yana ga Zubaidah da ta had'e rai kaman taga ajalinta.
"Labarun tara da aka soma ne yasa Jalal canza tashan, kaman daga sama sukaji ana sanar da auren Salim Kasim Dasuki da kuma Kausar Tahir Marafa, sati me zuwa wanda za'ayisa a babban masallacin gwamnantin tarayya National Mosque Abuja..
"hotonsu da aka hasko kuwa ba k'aramin kyau sukayi ba.
"Take taji zuciyarta ya soma mata zafi zogi da rad'ad'i, fuskokinsu cike da farin ciki alamun auren soyayya zasuyi, yayinda ita suka tarwatsa nata rayuwar suka rabata da masoyinta na asali snn suka Aura mata mak'iyinta d'aya daga cikin mutane hud'un data tsana a rayuwarta....
"Da sauri ta tashi ta shige d'aki gamida rufo k'ofar da k'arfin gaske ta fad'a kan gado tana kuka mai tsuma zuciya.
"Annah ta bita da kallo cikin rashin gane dalilinta na barin parlor, wata zuciya kuwa ce mata tayi k'ila hakan nada alak'a da shigowar Jalal, kallon Jalal tayi wanda har lokacin kallon k'ofar d'akin yake.
"Murmushi Annah ta sakar masa kafin tace " Kar ka damu it will pass, gyad'a mata kai kawai yayi gamida yin gajeren murmushi kafin ya gyad'a kansa alamun eh.
"Cikin ransa kuwa yasan dalilin da yasa Zubaidah barin wajen ba bai wuce ganin tallan auran Salim bane a TV... Jan hannunsa da Kamal keyi yana fad'in" Uncle Jay ka k'arasa min home work d'ina Kata Didi tak'i k'arasa min... Wnn magana na Kamal shi ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi.
"Murmushi ya sakar ma Kamal kafin yace " Of course Champion let's go to my room, d'aukansa yayi ya azasa a wuya suka fice daga parlorn sai murna Kamal keyi, yana tsananin son Jalal.
"Annah kuwa kallo ta bisu dashi fuskarta cike da murmushi tana mai jin Dad'in yanda Jalal da Kamal suke son junansu....
"Ficewarsu da kad'an itama ta mik'e ta shige d'aki wajen Zubaidah.....
*Gombe Fada*
"Zaune suke saman wasu kujeru wanda basai an ce maka na shak'atawa bane, da ganin fuskokinsu zakasan suna jin Dad'in hiran da suke.
"Ya Shattima wllhi biki nake dashi a Abuja Next Week amma nasan Mai Marta won't allow me to attend the wedding. Zahida ta fad'i sanda take gyara zaman alkyabban jikinta.
"Murmushi mai sauti Shatima yayi kafin yace " Princess kinada kayan dariya, ai ya kamata ace by now Kin saba da dokan mahaifinki, kiyi mata addu'a daga nan ya wadatar basai kinje ba...
"D'an b'ata fuska tayi gamida turo baki gaba tana kallonsa a shagwab'ance tace " Aw kaima irin halinka knn kulle wa mutane, instead ka rokar min shi for the first time ya barni naje shine zaka ce na hak'ura...
"Dariya taso basa ya d'an dake kafin ya soma lallashinta, Com'on lil sis, kema kinsan ba haka bane, da inada iko dake zakije duk yanda kike so fad'in duniyar nan matuk'ar zai sakaki cikin farin ciki. Kawai dai ya kamata ki saba da wnn tsarin ne, tunda kinsan mai Martaba baya magana biyu.
"Sauk'e ajiyan zuciya tayi kafin tace " Haka ne ya Shatima that's why nake ji da kai da Madaki sabida kuna saurin fahimta ta......
"Wayarsa data soma ringing ne ya katse masu hiran tasu.
"Zulaihat ya gani kan screen din wayar, sai yanzu ya tuno da wata Zulaihat tun bayan barinsa restaurant d'in...
"Tunda suka soma magana fuskar Zahida ya canza, haka kurum ta tsinci kanta da jin haushin wacce yake magana da ita.
"Zulaihat kuwa gogeggiyar 'yar bariki tuni ta kalallame Shatima da kalamai masu Dad'in saurare, har yaso ya mance Zahida na zaune a wajen.
"Mik'ewa tayi tana kakkabe alkyabban ta alamun zata tafi.
"Da sauri Shatima ya rik'o Alkyabban gamida d'aga mata yatsa guda alamun ta basa minti d'aya...
"Sallama sukayi da Zulaihat kafin ya dawo da hankalinsa kan Zahida da ta cika tayi fam..
"Tsokanan ta ya soma wai kodai kishin yayan nata take ne, dariya kalamansa yaso bata don bata ga dalilin da zaita kishi akansa ba.
"Suna a haka suka hangi Khalifah ya doso yanda suke cikin tafiyarsa na isa da gadara wanda ya zame masa jiki.
"Take ta had'e rai kaman ta ga dodo, Khalifah ya k'araso gamida mik'awa Shattima hannu sukayi masabaha, yana masa kirarin "Ranka ya dad'e Allah baka gidanku....
"Khalifah yayi wani k'asaitacccen murmushi don babu abinda yake so kaman a kod'asa.
"Kaman bata san ya iso wajen ba haka taci gaba da danna wayarta har saida Shatima ya mata ido kafin ta gaishesa a dak'ile ko sakon biyu mai kyau bata k'ara a wajen ba ta shige cikin gida.
"Nan Khalifah da Shattima suka ci gaba da hira, yana fada masa tsarin da mahaifinsa yayi masu shida Zahida.
"Khalifah d'a ne ga k'anin mai martaba kuma Chiroman garin Gombe, basuda buri shida mahaifanda kaman suga ya auri Zahida. Ita kuwa ko kad'an tak'i jinin Khalifah, tun tana 'yar k'arama ta tsani Khalifah wanda hakan yasa harta 'yan gidansu tsanar ya shafa, dukda bata da wa ko k'ani bata fatan bayan ran mahaifinta sarautar garin ya koma gidan Ciroma, don kuwa gaba d'aya shida iyalansa mugun hali ne dasu, basuk'i mai martaba ya mutu a yau su d'ale mulki ba......
*Abuja.....*
"Gidansu Kausar babu masaka tsinke kasancewar bikin ya k'arato sosai, Su Mumsy su Asmah babu zama, hidima ake kanyi babu kama k"afan yaro, Pappy kuwa daga k'asashen daban dabam Ya gayyaci mutane zuwa d'aurin aure da bikin tilon 'yarsa.
"Ana saura kwana uku d'aurin aure suka gudanar da brutal shower ita da k'awayenta, washe gari aka yi kamu, kai tunda satin bikin ya shiga ake gudanar da events.
"Gidan Alh Kasim Dasuki ma ba'a barsu a baya ba, gayya sosai yayi, toh gayyan nasu ma kusan dangin abu guda ne, tunda yawancin mutanen da suka gayyata sun san juna, Mummy hidima babu kama k'afan yaro, Mami ne dai take takaba bata samu halartan shagulgulan ba, su Momin Tariq da matan ministoci da sanatoci kawai kake gani a event d'in....
"A ranan da aka d'aura aure ake shirin gudanar da dinner a babban hall d'in nan na wane da wane dake birnin tarayya Abuja wato AClass Hall.
"Tun a wajen daurin aure Umar ya masa waya ya sanar dashi ya iso Abuja, Labib yace " ya shiga kawai gurds sun san da zuwansa, akwai duk wani abin buk'ata, bazai samu dawowa gida da wuri ba sabida bikin cousin dinsa da sukeyi.....
" wajajen k'arfe 6:56pm Gidan babu kowa daga ita sai Kamal kasancewar su Hadiza da Annah sun bi sawun Hamma Habibu don har yanzu bai dawo daga kasuwa ba wajen sana'ar saida kayan lambunsa....
"Abubuwan suka ringa dawo mata kwanyarta, ta tuna sanda Salim ya fincike rigarta, ta tuna yanda sukayita ihu suna shewa suna dariya, ta tuna cewa har yanzu cikin farin ciki suke, she's the one suffering, sun zalunceta snn suna ci gaba da rayuwarsu peacefully, ta tuno zuwan Kausar lokacin data zo tambayarta gameda Salim.... Kaman wacce aka zabura haka ta mik'e ta nufi akwatin kayanta, takarda me d'auke da lambar Kausar wanda ta bata kwanaki ta d'auko, duk ta cukwikwiya sa, warwarewa ta shiga yi a hankali kafin ta hangi wayan Annah kan gado da alama mancewa tayi.
"Cikin ssauri ta k'arasa ta d'auki wayar gamida dialing lambar Kausar.......
Sameena ce đđž
[1/23, 22:18] +234 803 619 0581: đđđđ *ZUBAIDAH*
34
*©Sameena Aleeyou...✍đž*
_Queen Samy Novels Forum...đđ_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Tuni dama an kai amarya gidansu ango dashike an d'aura aure...
"Tayi kyau cikin doguwar rigarta da yake sharan k'asa, fuskar nan kuwa tasha makeup, Asmah sake baki tayi tana kallon yanda aminiyar tata k'anwa kuma k'awa a gareta tayi kyau...
"OMG! You gorgeous Kausar, rungume juna sukayi cike da murna, Makeup artist d'in sai murmushi kawai take masu, Mumsy da masu d'aukan pics d'in amarya ne suka shigo.
"Mummy ta shigo don ganin komai ya tafi Saudi kallo tabi surkar tata dashi kafin ta k'arasa ta rungumeta tace,
"Oh my daughter you look so gogorgeous....
"Murmushi Kaiser tayi cike da kunyan Mummy *"Mai Gaskiya photography* yace" Em Madam let's take a picture of yours... Gyarawa sukayi akata kashe masu pictures suka k'arasa parlorn Daddy suna d'aukan wasu pics d'in....
"Daidai nan su Salim da friends d'insa suka k'araso cikin luxurious cars d'insu, Nan fah aka soma kwasan friends da wasu daga cikin dangi.
"Komawa d'aki Kausar tayi sabida cellphone d'inta data mance..
"Cak ta tsaya tana sauraren Asmah dake receiving call da wayarta.
"Baiwar Allah kiyi hak'uri but you really can't talk to Kausar right now..... D'an jim tayi kafin tace Okay acemata waye....
"In a shock Asmah ta furta *ZUBAIDAH*.... "
"K'irjin Kausar ya bada wani irin k'ara, da sauri ta fizge wayan daga hannun Asmah, kallo Asmah ta bita dashi don ta d'auka har ta isa wajen event.
"Hello Zubaidah nice Kausar ce,
"Daga d'aya b'angaren Zubaidah tace " Kar ki auri mutumin nan,..
"Bugun k'irjinta ya k'aru, baki na rawa take furta " Ban fahimce ki ba,
"Zubaidah da tuni muryarta ya soma shaking alamun kuka taci gaba da fad'in" I said don't get married to that Man, he's a heartless a miserable jerk. ....
"Kausar da tuni ta soma zuban hawaye take fad'in" How dare you, how dare you ruin the most important day of my life, are you trying to frame him or what.....
"Kukan Zubaidah Ya k'aru sanda take fad'in" Kince kina son sanin gaskiya kince kina son sanin idan mijin da zaki aura was involved or not, well believe it or not he's a monster a criminal, dukansu mugayene azzalumai wanda suke laifi su b'uya da inuwan kud'in mahaifansu..... Kuka yaci k'arfinta bata sanda ta latsa wayar ta kashe ba ta durk'usa a wajen tana kuka, Kamal da tuni shima ya soma hawaye ganin Didin sa na kuka ya k'arasa Ya rungumeta....
"Jifa Kausar tayi da wayar gamida toshe bakinta ta durk'usa kan gwiyoyinta, Asmah ta k'araso a razane ta rungumeta ta shiga tambayarta lafiya meke faruwa..
"Kausar na kuka take fad'in" She's saying the truth Asmah, gaba d'aya click dinsu ne sukayi raping d'inta, Asmah I married a rapist,.....
"Mikewa Asmah tayi ta saka Key ma k'ofan kafin ta dawo ga Kausar,
"Pls Kausar don't be so naive, bakida tabbasa akan abinda ta fad'i, who knows she might be making stories, ta yaya za'ace maza sama da biyu sunyi raping din Mace guda a dare d'aya bata mutu ba, kema kinsan hankali bazai kama ba, snn Jalal da bakinsa Ya fad'a maki gaskiya, com'on tashi ki gyara fuskar ki, kar ki bawa iyauenki kunya.... Asmah bata kai aya ba sukaji ana buga k'ofa,
"D'aya daga cikin friends d'insu ne, Mardiya Aleru...
"Asmah what the heck you guys doing in there, ku fito mana pls....
"Mummy ce ta k'araso ta dubi su Mardiya da sukayi cirko cirko a k'ofa tace " Yaya dai ina amaryar
. "Mardiya ta d'an Tab'e baki kafin tace " K'ila dai mummy sai Salim yazo da kansa ya fito da ita, murmushi Kawai Mummy tayi kafin ta shiga knocking k'ofar a hankali tana fad'in "Kausar lafiya dai ko, ko kina son wani abu ne....
"Asmah ne ta sami strength d'in amsa Mummy Kausar kam gaba d'aya ji take ta tsanesu...
" " Mummy ga mu nan fitowa..
"Okay Asmah maza ku hanzarta ko the Grooms are waiting, cewar Mummy kafin ta wuce.
"Tsaki Kausar tayi a ranta wai uwar miji ne haka babu kamun kai.
"K'arasa gyara ma Kausar Face d'inta Asmah tayi kafin tace oya muje kuma pls kiyi yanda nace if you really don't want you embarrass your parents..
"Harara kawai Kausar ta jefa mata fuskar nan kana gani kasan babu lafiya haka ta fito, Ko kula su Mardiya bata yi ba ta wuce, Asmah ta d'an basu hak'uri snn suka wuce kowa na mamakin sudden change d'in Amarya Kausar.....
"A daidai tangamemen k'ofar glass d'in parlon Daddy ta hangosa, yayi kyau sosai cikin shiga irin nata, tun daga nesa yake washe baki, Labeeb na gefensa yana karantar amarya, a ransa yace " I hope you two will never be happy.
" Bayan lemozin d'in aka bud'e masu, Salim Ya tattara mata bayan rigarta suka shige, su Labib suka kwashi sauran k'awayen da suka rage.....
"Gaba d'aya bai gane mata ba, a hankali ya mataso dab da ita yana k'ok'arin shigewa jikinta yake fad'in "My beautiful bride is anything bothering you, huh Baby na, ya jawota gamida kwantar da ita cikin jikinsa yana faman shinshina wuyarta......
"Kausar da gaba d'aya hankalinta bai tare dashi sai snn taji abinda yake mata, tayi saurin turesa tana hararansa take fad'in" What's with the rush huh? Bazaka iya hak'uri akai maka ni bane or what....
"Da mugun mamaki yake kallonta, d'an matsawa gefe yayi gamida latsa wani waje ruwa ya zubo a cup snn ya kurb'a, he couldn't believe it, kaman ba itabace d'azu suka gama waya kaman su cinye juna, Kallon yanda ta k'urawa window ido yake kafin yace with a soft voice " I'm sorry sweedy I didn't mean to upset you kinji, but I can't keep my distance with you especially yau that you are completely mine,....
"Gajeren tsaki tayi kafin tace " You know what I already have headache.... Kallo ya kuma binta dashi bai kuma cewa komai ba har suka isa hall d'in....
"Koda Salim Ya sakalo hannunta ma janyewa tayi a hankali, Asmah ta mata alama da ido, Kausar ta d'auke kanta, Labib kuwa kallo yabisu dashi yana son gano wani abin....
"Ko gama event ba'ayi ba, k'arfe 8:30 Kausar tace bata jin dadi ita tafiya zata yi, babu yanda Salim beyiba haka dole ya hak'ura suka baro wajen,
"Wasa wasa dai babu Hamma Habibu babu labarinsa, duk sun tambayi masu zama bakin kasuwa sunce tabbas sunga tafiyarsa, Hadiza fah ido ya raina fata, haka tayita rok'on Annah kan su k'ara shiga cikin Kasuwa, gashi Annah bata d'auko wayarta ba balle su kira Jalal gashi empty suka fito babu sisi... Haka suka Dad'a kutsawa cikin kasuwa dukda dare da ya soma ja......
"Su Mummy gaba d'aya sunji mamakin saurin dawkwarsu,
"Ana bud'r mata k'ofa ko ta kansa batayi ba tayi shigewarta, Labib yayi saurin rik'o hannun Salim dake k'ok'arin bin bayan Kausar kafin yace " Wai meke damunta ne??
"Gajeren tsaki Salim yayi kafin yace " I don't know, she's been acting strange, tace dai wai kanta ke ciwo,
"Silent murmushi Labib yayi kafin yace " Kaje kaji abinda ke damunta bro, we are here for you, nida Tariq, ya k'arashe maganar yana kallon Tariq da kwana biyun nan ya koma wani sukuku dashi, yanzu haka ma kansa kife yake a stairry d'in mota...
"Gus's kansa kawai yayi kafin yabi bayan Kausar....
"D'an k'wank'wasa k'ofar yayi daidai lokacin da take k'ok'arin zuge zip d'in rigarta, Asmah tayi masa iso, gaba d'aya k'awayen suka soma zolayarsa wai ko koransu yazo yi, biye masu dai yayi suna ta hiran barkwanci kafin suka fice suka basu waje....
"Ko kallo bai isheta ba vlballe tasan da hallita a wajen, k'arasawa yayi ya kame hannunta yana k'ok'arin zuge mata zip d'in yake fad'in let me help you with it Baby.....
"Da k'arfin gaske ta turesa gamida jawo mayafi ta rufe jikinta tana watsa masa mugun kallon k'yama take fad'in " Allah Ya sawak'e someone like you Ya Kalli jikina ko nima Raping d'inanan kazo yi.....
Fozzzz yayi yana binta da kallon mamaki yayinda k'irjinsa ke lugude....
Sameena ce đđž
0 comments:
Post a Comment