Mama ce ta katseta ta hanyar rungumanta datayi cikeda so da kauna mama tace yarana 3 a duniya Haneef,Umar da Ababakar siddeeq kuma duka mazane Aneesa tayi fuskar kuka dariya mama tayi kana tace toh ai ban karashe ba domin kuwa daga karshe Allah ya albarkanceni da diya mace kyakkyawa mai ladabi da biyayya kuma itace yar autarsu 1 mace wato Aneesa yar mama da baba π
Murmushi Aneesa tayi kana tace yauwa mama har naji dadi Allah barmu tare Ameen mama ta amsa
Zama sukayi a palo sunata hira har zuwa 6:30pm nan ne Aneesa ta mike tace mama bara na dauro alwala mama tace toh yar albarka shigewa tayi bathroom ta dauro alwala tafito ganin haka ya yasa mama tafita taje part din Aneesa ta dauko su fruits din ta dawo dashi part dinta tana shigowa taga Aneesa ta dauko sallaya ta shinfida a palon sannan tashiga cikin dakin mama ta dauko Al-Qur'ani mai girma nan tayita tilawarta hankali kwance har akayi kiran sallah nan tayi addu'a sannan ta rufe Qur"anin tana kokarin mikewa ne sai ganin mama tayi a gabanta dauke da tray tana smile itama Aneesar smile din ta mayar mata mama ta ajiyeshi sannan ta zauna tare sukayi budan baki wanda rabin abinda taci duk mama ce taketa bata a bakinta har suka kammala nan Aneesa ta mike taje ta kurkure bakinta tadawo tayi sallah mama itama alwalar ta dauro tazo itama tayi sallar koda suka idar karatun Qur'ani ne sukayita yi har ishaa 'i tayi bayan sun idar da ishaa'i ne Aneesa ta gaisheda mama nan suka koma kan dinning domin cin abinci Aneesa kam cewa tayi ta koshi mama kam tace ai bata isa ba suna kan dramar ne baba mai gadi yashigo da sallamarsa
Ai kuwa Aneesa sai shagwaba tafara tana bubbuga kafafuwanta smile yayi kana yace wai waye ke tabamin yar leleta ne eh?
Cikin shagwaba Aneesa tace baaaaa mama bace wai dole sai naci abinci ba bayan nakoshiiii.....
Dariya yayi lokacinda ya iso dinning din shima y nemi wuri ya zauna nan yace a toh ai da gaskiyar mama habaa diyata kici abinci mana mama ce tace rabu da ita wai ni nataba ganin yarinya budurwa haka da gobe zan wanketa in kaita gidan mijinta ace batason cin abinci kwata2 kunyace takama Aneesa nan ta mike da niyyar barin wurin mama ce tarikota tana fadin dan Allah kici koda alala ne rusunawa aneesa tayi har kasa ta gaida baba cikeda girmamawa baba ya amsa sannan yasa mata albarka
Juyowa tayi gun mama sai Tausayi mama tabata nan ta zauna mama tayita feedin dinta aneesa ko sai kallon mama taketayi da tayi concentratin akanta ita 1 ko kulawa da baba ma batayi ba a cikin ranta tace Allah nagode maka daka hadani dasu mama wannan irin so haka ai ko yayan cikinsu ne iyakacin kulawarda zasu basu kenan hmmm....
wata ajiyar zuciya tayi wanda yabasu mama tsoro baba ne yace yar Albarka lfy kuwa Aneesa tayi murmushin yake kana tace lfy lau baba Amma a ranta tana jimamin randa za ace ta rabu dasu batasan ya rayuwarta zai kasance ba a haka dai har tasamu ta cinye kulli 1 mama ta yanko na biyun kenan Aneesa tace mama nakoshi wallahi idan ba amai kikeson inyiba kibarni haka
Mama ta dauko ruwa tabata baba ne yace toh masu diya shikenan ni an manta dani ko toh shikenan bakomai bari in taahi inyi gaba since am not welcomed here
Dariya suka hauyi gabaki dayansu kana mama tace kayi hakuri kaima sanin kanka ne idan yar leleta tana nan bana ganin kowa sai ita
Aneesa tayi smile tace su baba ana kishine?
Smile yayi kana yace eh ....... sannan kuma yace aa
Ido aneesa ta zaro kana tace toh wanne zan dauka aciki kashe mata ido daya yayi kana yace ko wanne amma banda na farko dariya sukayitayi
Aneesa ce ta mike kasancewar wayanta na ruri kuma a palo ta ajiyeshi koda ta isa palon ta dauka da sallamarta Aisha a dayan bangaren tace Sweety kinsha ruwa lfy?
Lfy lau Aneesa ta amsa hira suka hau yi sannan Aisha take sanar mata cewar an samu cigaba a store dinta sosai murna Aneesa tayi tayi godiya ga Allah sannan tace Aisha Allah barmu tare
Ameen Aisha ta amsa bayan sun dan tattauna gameda rayuwar yau da kullum ne sukayi ban kwana mamace ta iso wurin ta zauna kusa da aneesa
Aneesa tamike tana fadin mama ni zanje in kwanta barci nakeji mama tace ai kuwa yakamata kije ki kwanta toh saida safe baba yafito yace har zaki je ki kwanta eh aneesa tace toh saida safe yar Albarka kardai ki manta kiyi addu'a dai kafin ki kwanta toh baba cewar aneesa mama ta rakota har cikin part dinta kafin takoma bayan sunyiwa juna saida safe
Aneesa nashiga..........
✍π»by LEEMAT
LOVE U ALLπππ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ tsintsiya muke madaurinmu 1 π€
13
Aneesa nashiga bathroom tafada tayi wanka ta dauro alwala tana fitowa tayi nafila sannan ta kwanta
A bangaren Ahraf kuwa tunda yakoma gida ya kasa samun sukuni sai tunaninta yake gashi baida numberta bare yakirata ummanshi ce tashigo part dinshi da sallamarta ashraf ya amsa bayan ta zauna ne tace son meke damunka ne yau kwata2 na lura dakai yau baka cikin hayyacinka sai faman tunane2 kake
Smile yayi na karfin hali kana yace umma lfy ta lau kawai .....
Kome yatuna ohoo
Sai kuma yayi shiru
Ummansa tace habaa son kasan bana boye maka komai pls sanar dani damuwanka
Jin kalaman ummanshi yasa jikinshi yayi sanyi nan ya gaya mata komai bai boye mata ba
Smile umma tayi kana tace toh Alhmdllh yar wani gari ce kuma ya sunanta?
Nanfa daya wai ance da shege ina ubanka......
Aahraf yace wallahi umma bansan sunanta ba kuma bansan ko daga wani gari take ba nidai abu daya nasani shine dana kaima Mus'ab ziyara ne na hadu da ita kuma tunda na ganta sai naji ta kwantamin arai amma bari zan tambayi mus'ab din sunanta da garinta
Toh son Allah taimaka Allah sa alkhairi ameen ya amsa yana smile dan yaji dadin addu'ar umminsa
Koda tafita nan fa yakoma aikinda yasamu yau shine tunani yana kan haka ne barci barawo yayi awon gaba dashi
Aneesa ce da Ashraf tareda yara 2 kyawawa mace dana miji Aneesa sai firan soyayya suke cikeda nishadi dayar yarinyar ce wacce batafi 3yrs ba tace mommy daddy zan cha ice cream smile Ashraf yayi kana yace to kuje gun kande ta kaiku kusha tashiwa sukayi suna tsalle yesssss we love u daddy sannan sukama Aneesa gwalo nan suka fice daga dakin ganin haka yasa Ashraf yin maza yaje ya rufe kofar dakin Aneesa na kallon ikon Allah yana dawowa ya janyota jikinshi Aneesa tace Habibi da tsakar ranar nan kashe mata ido yayi kana yace bakisan na rana yafi........
Ai kafin tasamu bakin magana yariga ya hada bakinshi da nata sarrafata yake duk yabi ya kashe mata jiki yana kokarin zuge zip din rigarta ne yaji ana bubbuga kofar
Ai ba shiri ya mike domin zuwa dubawa ko wanene
Dalla cen guy tashi mana ka barni inata faman jiranka bude idonda zaiyi sai yaga mus'ab bata rai yayi yace kai amma kai banzane wallahi yanzu ina cikin soyewa nida masoyiyata acikin mafarki shine zaka wani zo ka tasheni
Dariya mus'ab yamashi sannan yace au yaushe kafara soyayya ban saniba?
Ashraf yace yau mana katuna danaje makarantarku dazu har nake cemaka nayi budurwa amma sai ka dauka wasane ko ai da gaske ne wata kyakkyawar yarinya ce na gani tamin wallahi zan iya yin komai akanta
Mus'ab yace kenen harda holewar da mukeyi zaka iya bari saboda ita?
Shiru yayi kafin yace holewar banza in dai zata aminta dani ta yarda ta aureni wallahi zan daina shirmennan
Dariya kawai mus'ab keta faman yi domin kuwa shi a tunaninsa duk shirme ne ashraf keyi
Tashiwa yayi yashiga bathroom ya watsa ruwa yafito ya shirya nan suka fita don zuwa sharholiyarsu
Toh jama'a wata irin waina Ashraf ke toyawa shida mus'ab?
✍π»by Leemat
Love u allπππ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
Wannan page din nakine ke kadai uwa mai gyara yarta nayi godiya gareki mahaifiyata, uwa bada mama, mai kaunata farin cikina Allah kara nisan kwana Gimbiya sarautar mata MAMA HABIBA DADA KUTA AKa Maman Titiwo Allah sadaki da alkhairin duniya data lahira Ameen nagode πππ»π❤ππππ✍π»
14
Shin wanene Ashraf?
Ashraf wani matashi ne maiji da kyau da naira irin tashin palonnanne wato Ajebo
Ashraf da ne daya tilo agun hamshakin mai kusdinnan wato Alhaji Sudais da matarsa Hajiya Saudat shidai Alhaji sudais dan kasuwa ne babba wanda sunarsa ta bazu a nigeria da kasashen waje ita kuwa matarsa hajia Saudat ita ba yar nigeria bace ita yar kasar egypt ce acen suka hadu lokacinda yaje kasuwancinsa kuma ya sami iyayenta nan aka bashi aurenta yaci gaba da zama acen har tsawon shekaru 12 basu samu haihuwa ba hajiya saudat ba karamin damunta abin yakeyi ba ana haka ne wata rana tace mijinta yakara aure nan ya nuna mata cewar shi baida ra ayin ajiye mace fiye da 1 dan hk tayi hkr haihuwa ta Allah ne in da rabonsu wataran zai basu
Haka dai rayuwa taci gaban ma ma auratannan 2 cikeda so da kauna abokan harkallansa sunyi2 akan ya kara aure don samun zuria amma yayi kunnen shegu saboda yanason matarshi
Kuma mutum ne mai tawakkali yayi imani wataran sai lbr wata ranar monday ce hajiya saudat ta dauki azumi ranar yini tayi tana rokon Allah har akasha ruwa Allah maji rokon bawansa ne cikin ikon Allah kuwa sai mijinta yake shaida mata cewar bazai samu dawowa a ranar ba ta dan ji ba dadi amma ta nuna masa shikenan Allah dai ya tsare mata shi aduk inda yake Ameen ya amsa ashe yana bakin kofar falon ne lokacin bude kofar yayi ita kuma lokacin ta taso da niyyar zuwa kulle kofarta tunda bazai dawo yau ba tana hawaye tana tafiya ganin mutum tsaye a kofar yana murmushi ne yasata tsaya chak
Cemata yayi kuka?
Cikin shagwaba taje ta rungumeshi tana fadin toh bakai bane ba wai bazaka dawo yau ba ta karashe maganar tana kuka........
Rarrashinta yayi nan ya dauketa kamar baby suka shige basu tsaya ko inaba sai bedroom ya direta saman gado
Cemashi tayi muje kayi wanka kafito kaci abinci sai shikuma yace sannan inzo in kwashi gara ko π
Kunyace ta kamata dan haka tashi tayi tafita da gudu smile yayi yace I love u wit all my hrt
Bayan yayi wanka yaci abinci nanfa suka shiga duniyar ma aurata ranar saida hajiya saudat tayita kiran sunar Ummanta da Abbanta tsabar ........
Shikuwa nan yamata kyautar kujeran makka tsabar.........π
Niko nace saikace yaune darensu na farko
Bayan sati 6 ne tafara zazzabi alhaji duk yabi ya rude koda yakaita asibiti bayan yan gwaje2 da aka yimata nan aka shaida masa cewar tana dauke da juna 2 har na tsawon sati 5 murna agun alhaji baya misaltuwa nan aka basu magunguna tun daga ranar ya hanata yin komai har Allah yasa cikinta yakai wata 5 nan ne yace su dawo nigeria dazama taji dadin jin hakan ai kuwa haka akayi
Cikinta na wata 9 kuma gashi lokacin tafiyarsu hajji yayi haka tashirya suka tafi cikin ikon Allah acen nakuda ya kamata ta haifi danta namiji kyakkyawa kamar balarabe
Koda ranar suna ta zagayo a cikin masallaci aka rada masa suna Ashraf koda lokacin dawowar yan hajji tayi ita bata dawo ba dan mijinta cewa yayi saitayi 4months tukuna kasancewar yanada gida acen cikin madina haka kuwa akayi
Tun da ta haifi Ashraf shikenan Allah bai kara bata wani ba
Don haka ne suka dauki son duniyarnan suka daurawa ashraf saidai bai bata tarbiyyarshi ba ko kadan har sai lokacinda ya cika 19yrs llkacin ne ya kammala 1st degree dinsa a oxford university dake amurka inda ya hadu da wani mai suna micheal wanda baida aikinyi daga shaye2 sai bin matan banza
Saidai shi ashraf bai taba yarda yayi hurda da matan banza ba amma yana shaye2 wannan kenan
Cigaban lbr koda suka isa club nan ya zauna saidai yau anyi2 yasha kayan maye amma sam yaki sha gaba daya ma hankalinshi ba anan yake ba
Aneesa tana cikin barci ne sai taji..........
✍π»leemat
Love u so very much sweet mom π❤ππππ»
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ€
15
Aneesa taji kamar a zahiri cewar gata ga Ashraf suna soyayya wanda har takaisu gayin aure infact mafarkinsu iri daya dana Ashraf saidai ita babu wanda ya tasheta ita da kanta ta farka tayi addu'a sannan ta zauna tana mamakin irin wannan mafarki haka
Ta dade kafin barci barawo ya saceta
A bangaren Ashraf kuwa ranar bai sha komai a club ba har suka dawo hoton Aneesa keta masa yawo a brain dinsa
Washe gari da asubahi bayan ta idar da sallah tayita kira'a tana kan kira'ar ne taji kamar ana kuka ta danji tsoro amma ganin Al Qur'ani mai girma ne take karantawa yasa taji bata tsoron komai hasalima sai taji tasamu nutsuwa fiye da da
Cen taji kamar an bude kofa an rufe cigaba da karatunta tayi ko ajikinta bata damuba har gari ya waye nan tayi addu'a tashafa sannan tashiga bathroom tayi wanka
Karfe 7:30am tafito cikin wata riga da skirt tayi mata kyau da yar karamar gyalenta part sinsu mama tayi tana zuwa ta rusuna ta gaida baba sannan tawuce ciki nan ta gaisheda mama sannan tafito don wucewa makaranta mamace tace ga abincinki fa ki tafi dashi tunda yau bakison kici abincin a gida smile tayi kana tace mama ai kinsanni inba 10am ba ban fiya son cin abinci da safe haka ba shiyasa kuma kinga yau inada lectures 8:30am
Toh Allah taimaka kidai dauka kitafi dashi toh mama Aneesa ta amsa sannan tafito Allah bada sa'a Allah tsaremin ke Ameen aneesa ta amsa sannan baba yace toh masu diya dariya suka saka Aneesa tayi gun motocinta dake parke wata mota tashiga kirar KIA brown colour ne wato colourn jakarta,takalminta,yan kunnenta,agogon hannunta da bangul din da gyalenta sannan kuma a atamfar datasa akwai brown aciki sai kuma wayarta datasha kwalliya da brown case domin kuwa duk kayanda tasaka tomatch ne komai nashi bata saka any how dress haka motar hawanta different colours ne daidai da wayoyinta suma haka Aneesa kenan yar Presidor
Shiga tayi bayan tayi addu'a nan ta kunna wayrta takira Adama take shaida mata cewar gatanan tafe tajirata toh sai kin iso inji adama
Baba ya bude mata gate sannan yamata addu'a cikin jin dadi Aneesa tamasa goma ta arziki sannan tayi tafiyarta kaji diyar albarka
Ashraf ne a gefe cikin motarsa kirar hilux yana jiran fitowar Aneesa domin tunda garin Allah ya waye yarasa meke mashi dadi kawai fuskar aneesarshi yakeson gani wanda hakan ba karamin bama daddynshi mamaki yayiba dan yasan Ashraf bai tashiwa da wuri koda ya tambayeshi cema daddynshi yayi yau yanada appointment ne da safennan toh son Allah taimaka Allah bada sa'a Ameen ya amsa sannan yace zai wuce Ashraf kenan
Ai kuwa ganin mota tafito yasashi jan tsuka domin kuwa ba motarda aneesa tahau bane jiya har zai maida kansa kan kujera sai yaga kamar mace ce ke jan motar ai kuwa kafin kace me Aneesa tazo ta giftashi tawucewarta bashiri yatada motarshi yafara bin bayarta duk da ta lura ana binta saidai bata kawo komai a rai ba domin kuwa shima ashraf ba motarda yashiga bane jiya ba
Har ta iso unguwarsu Adama ba bata lokaci kuwa saiga Adamar tafito tashiga mota hira suke har suka isa makarantar
Parking tayi suka fito Ashraf sai binta yake da kallo ganin ta fi jiya kyau kuma ga kayan jikinta sun mata kyau wowww mashaa Allah ya furta sannan yace gaskiya gimbiyata komai nata na daban ne smile yayi sannan ya fito da wayrsa yakira Abokinshi Mus'ab
Mamaki mus'ab yayi da ashraf ya shaida masa cewar yana school dinsu ba bata lokaci ya iso gun ashraf nan ashraf ya nuna masa motarda Aneesa tashigo saidai baisan sunanta ba
Mus'ab yayita dariya kafin yace guy i don fall oooo amma bakomai nasan dolema tasoka domin kuwa kaima ajin farkonnan ne wanda yan mata ke mutuwar so
Ashraf yace shege abokina ka iya zuga mutum shiyasa nake ji dakai mus'ab yace bari ina zuwa fita yayi yaje ya sami wani guy dake kokarin shiga department dinsu Aneesa bayan sun gaisa ne yake tambatarshi time dinda zasu fito bayan first lecture 11 guy din yace masa nan ya nuna masa motar Aneesa yace kasan mai ita?
Eh guy din yace sannan yace ai wannan motar yar presidor ce yarinyar arziki mai taimakon talakawa ai tafi president kyautaπ
Mus'ab yace ya sunanta nan fa yace ni bansan sunanta ba domin kuwa kowa da yar presidor yake kiranta dukda batason sunar amma ba yadda ta iya da mutane sannan wasu kuma suna kiranta da kinfi president kyauta
Ok nagode sai anjima guy din yace amma lfy kake tambaya akanta mus'ab yace lfy lau kawai tamin ne guy dinne yace tabbbbb
Lallai kam dama kabar wahalar da kanka domin kuwa batada lokacin samari barta da karatunta mus"ab yace nagode guy sai anjima ok ooo nan yajuyo yazo yashiga motar ashraf
Ya kwashe komai ya gayawa ashraf ajiyar zuciya ashraf yayi kana yace indai wannan ne badamuwa
Nan mus ab yace inajin yunwa fa guy smile ashraf yayi sannan ya tada motar suka fito sai gidansu Ashraf da shigarsu part dinshi sukayi bayan sun shiga ciki kan dinning mus'ab yanufa shikuwa ashraf bedroom yawuce domin sake yin wanka
Dashigarsa bayan ya rage kaya ya fsda bathroom ya sakeyin wanka yafi 30mins sannan yafito
Wata hadaddiyar shadda yasa mai tsada ga kyau brown colour hulama brown takalmi brown yana shirin yana smile saida yafi 1hour kafin ya kammala
bayan ya kammala ne ya furta komai namu colour daya gimbiya
Sannan yafito kamshi yakeyi kamar wani sabon ango mus'ab da har yafara gajiya da jiranshi ne yamike don shiga dakin yaga ko me ya tsayar da ashraf har yanzu
Mutuwar tsaye yayi ganin yanda ashraf yasha kwalliya kai ka rantse zai angwance ne yau
Har ashraf ya iso gabanshi bai saniba clappin yayi wanda ya dawo da mus"ab hayyacinshi dan tunda yake da ashraf bai taba ganin ashraf yayi mashi kyau irinna yau ba
Amma wallahi baba ka hadu kai dolenema yarinyarnan tasoka ko wacece ita smile ashraf yayi sannan yace mashi ka koshi koh? Eh yace sannan suka fito mus'ab sai faman zuba yaketayi kamar fanfo shiko ashraf sai smile yake
Gun wata hadaddiyar mota ya nufa kirar Hilanda brown colour ce itama mus'ab yabishi da kallo alamar tuhuma smile ashraf yayi kana yace inasonta ne shiyasa komai namu nake son ya zama daya
Mus'ab bai tankashi ba har suka iso makarantar Ashraf ya dubi agogonda ke hannunshi ta gold yaga 10:20 nan yace wai mus'ab yau bakada lectures ne
Mus ab yace ahhh dole kacimin fuska kawai kacemin in wuce kar na ga beb dinka kawai kabar yimin kwana2
Ashraf yace ba hk bane na sanka ne dason kyawawan yan mata mus'ab yace toh wane darene jemage bai ganiba a duniya?
Dallah cen mallam ni nayi tafiyata nan yafito yanata banbanmi cewar tun ba akai ko inaba beb na neman rabasu dan hk yazama dole yayi maganinta
11 dot mutane suka fara fitowa cen saiga Su Aneesa sun fito itada Adama fitowa yayi lokacinda suka karaso gun motar Aneesa sallama yamasu suka amsa Aneesa taje tashige mota Adama ko ko motsi ta kasayi kasancewar ta folama kyawun Ashraf ganin taki shigowa ne yasa Aneesa yin horn Adama tace Ashraf ya kk lfy lau ya amsa mata nan tace mashi tana zuwa zasuci abinci ne toh shine dan rowa kawarki kota kirani koh?
Aneesa ta sauke glass tace wai me kk jirane nifa zan fara....
✍π»by leemat
Godiya agareku masoya Allah bar kauna πππ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ€
16
Koh me ta tuno oho sai kuma tayi shiru Ashraf ne yace me zaki fara eh gimbiya smile tayi batareda tace dashi uffan ba
Adama tace muna zuwa dan Allah kabamu 5mins bakomai yace sannan yace ina jiranku a acen inda naganku jiya ok tace mai sannan tabude tashiga shima juyawa yayi yai gaba gindin bishiyar mangoro ya zauna yana jiransu
Abinci sukeci hankali kwance Ashraf sai bin Aneesa yake da kallo kasancewar suna fuskantar juna ne wowwww yafada
Kana yace komai nata na burgeni kama daga cin abincinta,maganarta,nutsuwarta hmmmm komai ma nata abin burgewa ne
Aneesa ce takai chokali baki daga idonda zatayi sai suka hadu dana Ashraf ai kuwa nan da nan ta rude Adama ta juya ganin Ashraf na smile yasa itama tayi smile sannan taci gaba dacin abinci har suka kammala cin abinci Aneesa bata kuma dago kanta ba gudun kar su hade dana Ashraf
Suna fitowa bayan sun iso gurin da yake zaune nan Adama ta zauna Aneesa kam cewa tayi sai kin shigo Adama tace habaa Mana kizo muyi hira da abokinmu na jiya mana
Ashraf yace shawaranku nazo nema akan wata santaleliyar budurwarda na gaya maku jiya sannan yace yauwa gimbiya jiya wata shawara ma kika ban?
Smile Anesa tayi sannan tazo ta zauna Alhamdulillahi ya fada Aneesa tace ka sanar mata sai Ashraf yace yauwa wato tsabar rowa ko bismillah ma babu ko?
Kunya Aneesa taji dan yakirata da mai rowa Adama ce tacw ai kuwa bata rowa domin kuwa duk wanda yasan kinfi president kyauta dole ......
Aneesa tasa hannu ta rufe mata baki ganin haka yasa Ashraf smile sannan yace woww sunan gimbiyar kenan koh kinfi presidor kyauta wowwww
Sai gashi ni tamin rowa domin kuwa harda wani sauri2 taketayi tana katon loma wai dan kar yarage ince zan ci Aneesa tayi maza tace Allah Ashraf bansan sharri fa
Yanda tayi maganar ya burge ashraf lumshe ido yayi na seconni kafin ya bude sannan yace to yanzu ga abinda zai faru zan fara learning soyayya da daya daga cikinku in gani ko zan iya apprching din masoyiyata Adama tace gud thinking Aneesa kam tace bad idea hakan baiyi ba sam
Ashraf yace ai na sati biyu ne kacal kinko ga kafin nan nasamu ilmi akan soyayya sosai Adama tace haka ne Ashraf yace toh da wace zan yi soyayyar sati biyun
Aneesa tace da Adama mana domin kuwa ita ta saba da yin hira Adama tace gaskiya kam sannan kuma kafin hakan saina sanar wa masoyina na gaskiya tukuna Ashraf yace toh ita gimbiya fa batada saurayi ne
Adama tace ai ita bata kula mata ma bare samari nima haduwarmu daga Allah ne domin kuwa mutane da dama sunata mamakin yanda akayi muka zama aminan juna
Ka ganta nan barta da books dinta kawai kwanakin baya ma da dan sarkin Zazzau ya kawo ziyara nan makarantar yana yin arba da ita sai ya fola amma koda yayi mata magana bata kulashi ba cemashi tayi ba soyayya yakawota ba karatu tazo yi kuma kasan me?
Ashraf da zuciyarsa ke faman yimasa zafi kasancewar abinda Adama ke fada kada kai kawai yayi alamun aa sai kin fada dinnan
Ai kuwa adama taci gaba da fadin zo kaga yanda yan mata keta mutuwa akan prince amma wai sai kawata ta basar daahi
Haka yayanta ya kawo mata ziyara shida abokinshi wato dan sarkin makka shima ya fola mata amma ita ko ajikinta in takaita maka resently yaron dangote yazo shima wai acewarsa ya hadu da ita ne a kasar india ai kuwa har nigeria yabiyota amma taki amincewa dashi
Ashraf ne yayi ajiyar zuciya wanda yasa dukkansu yimai kallon tambaya ai kuwa sai ya wayance yace lallai kam ai dole tayita rejectin din su domin kuwa Allah baiyi dasu za ayi ba
Aneesa tace oh harma kasan ko dawa za ayi koh?
Smile yayi kana yace inshaa Allahu dani za ayi dariya ce ta subucema Aneesa jin hakan daga bakin Aahraf dariya take shiko sai faman smile yake acikin zuciyarshi kuwa yana addu'a Allah bashi ita Allah mallaka masa gimbiya niko nace Ameen
Saida tayi mai isarta sannan tace wait a moment wai kana nufin kai ta nunoshi da hannu Ashraf yace yes nifa Ashraf nan Aneesa tace lallai kam Ashraf yace idan baki yarda ba toh kiyimin exam yanzu2 nan idan har naci toh yazama dole kiyi soyayya dani
Adama tace aa tayi maka tambaya dai idan har kaci toh sai tayi soyayya dakai na sati 2 Aneesa tace ni?
Soyayya?
Da Ashraf?
Har na tsawon sati biyu?
Hmmmmm lallai ma kam ai hakan ma bamai yiyuwa bane
Adama tace habaa kawata wallahi banajin dadin ganinki ke 1 pls ki koyi yanda ake soyayya koda na sati 1 ne in yaso ni zan cikasa na sati 1
Ashraf yace gud gimbiya kin yarda ?
Aneesa tayi shiru nadan seconni kafin tace eh na yarda
Ashraf yace toh me tambayarki?
Aneesa tace tambayata ta farko itace
....... .............
✍π»by Leemat
Love u olπππ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
Wannan page din nakune yan group din HAUSA NOVELS ina mai jinjina agareku akan kaunarda kuke mani da addu'arku agreni nagode Allah bar kauna ana tareπ€
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ
17
Aneesa tace tambayata ta farko itace ya sunana?
Na biyu me nake karantawa?
Na uku.........
Sai kuma tayi shiru Ashraf yace ina jinki gimbiya na ukun fa sai tace ba yau ba amma biyunnan yanxu nakeso kabani amsarsu
Ashraf yayi shiru cen yace a gaskiya bansan sunanki ba kuma bansan abinda kk karantawa ba
Smile Aneesa tayi kafin tace ai dama nasan za a rina tunda naji kana kirana da gimbiya sannan kana kiran Adama da sunanta nasan baka san sunana ba
Shikenan ka fadi dan haka babu zancen soyay........ ai Ashraf bai bari ta karasa ba ya katseta da cewar dan Allah karkimin haka Angel
Bani 10mins zan shiga zuciyarki inyi binciken sunanki idan har ban fadeta daidai ba toh na yarda babu love tsakanina dake
Aneesa tace ok ooo shiga ai kuwa nan Ashraf yashiga sake2 yana tunanin wani suna ne zaiyi matching da angel dinshi
Aneesa ko sai smile take dan tasan da kyar yasan sunanta
Ganin ya kasa samun sunarda ya dace da ita ne yasashi hkr kana yace a gaskiya bansan sunanda yayi matching dake ba amma kibani dama in kira sunaye 3 kacal idan babu naki aciki shikenan
Aneesa tace aa ban yarda ba Adama ce tace haba kawa ki bashi dama mana sunaye 3 fa kacal ok ok ok na yarda cewar Aneesa
Nan yafara da Ummul khairi noooo
Yakuma cewa Badariyya hahahahah nooooo
Remain only 1 guy cewar Aneesa tana smile
Shiru ashraf yayi kirjinshi na bugun 3 uku
Aneesa tace oya now d last one
Addu'a ashraf yafarayi yana rokon Allah yasa na ukun yazama sunanta
Na ukun mana malam inji Aneesa shiru Aahraf yayi dan harga Allah ya rude sai tsoron fadan na ukun yakeyi kar ya kasance ba dai2 ba amma bakomai na barma Allah zabina
Nan ya furta ANEESA.........
Gaban Aneesar ne ya buga dan bata taba tunanin zai fada dai2 ba shiko Ashraf tsabar fargaba har rumtse ido yayi dan kar yaga ta masa dariya akan bai fada dai2 ba sannan yana tsoron rasa Angel dinshi kawai saboda baisan sunanta ba hakan yasa yaki bude idanuwanshi sai Addu'a yaketa faman yi
Adama kuwa cewa tayi Alhmdllh Aneesa shikenan daga yau sai soyayya jin hakan ne yasa Aahraf bude idanuwanshi da ya rufesu saboda tsoro
Ai kuwa ganin Aneesa tayi tsuru2 da ido ne yasashi ajiyar zuciya Adama kuwa tace shikenan soyayya dole kallon Aneesa yakuma yi kana yace gimbiya naci? Adama tayi saurin cewa eh mana Ashraf congratulations ka cinki sunan dai2 sunanta kenan Aneesa
Alhmdllh Allah nagode maka to yanzu sai love koh Sweet Anee.......
Ido ta fiddosu waje kamar zasu fado kasa kana tace ai toh baka gama bani amsa ba me nake karantawa????
Damm..... zuciyar Ashraf ce ta buga akaro na biyu amma daya tuno da cewar Allah ne yabashi sa'ar na farkon sai kawai yaci gaba da addu'a acikin zuciyarshi
Budan bakinshi sai cewa yayi kina karanta biology/chemistry ne
Kaiiiiii....... Allah ban yarda ba dama yasan sunana da abinda nake karantawa Adama nasan kece kika fada mashi
Dariya suka fara mata ganin yanda taketa zuba duk tabi ta rude kawai saboda zata fara soyayya Adama ce tace wallahi Anee ban gaya masa komai ba kawai ki dauka wannan hadin daga Allah ne
Kuma ma da kikabi kika daga hankalinki soyayyarnan fa ta sati biyu ce kacal fa Smile Ashraf yayi kana yana fada a zuciyarshi cewar Adama kenan ai wannan soyayyar ta har abada ce nida Aneesa ta sai mutuwa kai ko mutuwarma........
Adama ce ta katseshi dacewar bari nabaku guri kufara soyayya kana ya furta a fili cikin razana cewar har a kiyama ma muna tare inshaa Allah
Aneesa tace kaida wa?
Shiru yayi dan baimasan lokacinda ya furta hakan ba
Adama tace toh sarkin love nidai kwaga tafiyata sai kin shigo
Ashraf ne yace haba Adama dawo kiyi zamanki toh kawai tace sannan ta zauna Aneesa da duk tabi ta rude tace nidai zan shige ciki sai anjimanku Ashraf yace haba Sahibata dan Allah ki zauna mudanyi hira
Aneesa tace ba yanzu ba Adama tace ohhhh wai so take kaje gidansu
Aneesa tace waneshi ai baisan gidanmu ba idan kuma ya sani toh in ganshi acen yau kafin in isa gida smile ashraf yayi kana ya furta shiyafi komai sauki
Aneesa tace me?
Yace zuwa gidannaku mana nan Aneesa tace toh shine na ukunda zaka cikasa kafin in aminta da soyayyar 2 weeks din takarashe maganar tana smile
Shima smile din ya mayar mata nanfa sukaci gaba da hira har 1:30pm ganin lokacin sallah yayi ne yasa dukkansu mikewa ashraf yayi gaba sukuma suka wuce masallaci don sauke farali
Ina labarin Hajja rahma????
✍π»by Leemat
Love u all❤ππ»
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ€
18
Hajja Rahma tunda taje gidan bokanta tasa aka turama Aneesa bakin aljani shikenan hankalinta ta kwanta sai taji kamar an mata kyautar Aljannah
Alokacinda taji lbrin abinda ke faruwa da Aneesa taji dadi kuma bataji dadi ba abinda yasa bataji dadi ba kuwa shine ba haka taso ba taso Aneesa tayi hauka ne ko kuma tayita tafiyarta ta bar nigeria gabaki dayanta na har abada sai gashi hakan bai samu ba
Toh fa nan takuma komawa akan ama Aneesa kurciya tabar nigeria amma kar a haukatarda ita asa ta dan dimauce kadan da zarar tabar nigeria hankalinta ya dawo amma kar ta tuna komai gameda rayuwarta hmmmm niko nace kunji wata sabuwa
Karfe 4:30pm su Aneesa na hango cikin mota sai faman hirarsu suketayi abinsu hankali kwance har ta isa kofar gidansu Adama nan ta sauketa sannan sukayi bankwana kasancewar gobe basuda lecture Adama ta shaidama Aneesa cewa gobe tana nan zuwa mata hira toh kawai aneesa tace kana tace Allah kaimu Allah kawomin ke lfy Ameen Adama ta amsa sannan ta dagama Aneesa hannu
Aneesa nakaiwa kofar gate dinsu ai kuwa sai ji take kirjinta na buga 3 uku
Ai kuwa me zata gani?
Motace anyi parking kusa da gate din ganin Ahsraf jingine da motar yana smile yasata daure fuska ai kuwa sai tayi kamar batasan ma da mutum a wurin ba
Baba na bude mata gate sai tayi shigewarta ganin haka yasa Ashraf zuwa daidai baba zai rufe gate din ganin Ashraf yasashi smile Ashraf kuwa ya gaidaahi cikin girmamawa
Sannan baba yake tambayarshi wa yake nema ai kafin ya bude baki da sauri Aneesa tace baba ai kuwa juyowa yayi yana kallonta har ta karaso wurin nan ta gaida baba sannan tace baba jeka abinka dan makarantarmu ne
Ok toh yar Albarka juyawa yayi ya karasa rufe gate din sannan yashige cikin gida
Nan ta maido da kallonta ga Ashraf wanda shima ita yake kallo tace Ashraf kk koh ma menene ya akayi kasan gidanmu
Kagafa ni bana soyayya ban tabayi ba kuma bana sha'awar yinta yanzu
Ashraf yana kallon yanda Aneesa keta yimai masifa har takai aya bai amsa mata ba sai faman smile yaketayi
Hakan ne yabata haushi ai kuwa tajuya zata shige cikin gida Ashraf yace Sweet Anee dan Allah ki bani minti 2
Juyowa tayi amma batace dashi kala ba
Smile yayi kafin ya fara magana
Yace Angel ina kaunarki dan Allah kibani dama muyi soyayya koda na 1 week ne idan har bakiji komai akaina ba toh ni Ashraf nayi alkawarin barinki har abada
Hmmmm... yaci gaba da magana har saida yakai aya sannan aneesa tace ok naji nakuma amince amma pls banda takura kuma .......
Sai kuma tayi shiru ashraf yace kuma me sai tace kuma bkm smile Ashraf yayi kana yace ok toh yanzu dai bara nazo na tafi saboda kisau ki huta yanzu in yaso sai zuwa anjima kamar 8pm dinnan sai nazo muyi hira koh
Ido Aneesa ta fiddosu waje kana tace aa karkazo ni kaga ka rufamin asiri nidai babu ruwana wato kanaso baba da mama su dauka na fara soyayya ne ko bacin ba soyayyar gaskiya bane.......
Ashraf yayi maza yace inji waye yagaya maki ba soyayyar gaskiya bace?
Tabe baki Aneesa tayi kana tace toh dama na gaskiya ce ai soyayyar 2weeks ce kawai
Aahraf yayi smile kafin yace ok naji ba soyayyar gaakiya bace amma inaso mu daukeshi kamar na gaskiya ta inda mutane zasu gamsu da soyayyarda mukema juna harda kula da juna zamu rika yi
Aneesa tace nidai bamuyi haka dakai ba Ashraf yace ai basai munyi hakan dake ba kinga kyan alkawari cikawa ina nan zuwa anjima sannan kuma karki manta saida kika bani aiki har 3 kafin nan kika amince da soyayyar dan haka yanzu turn dina ne ya karishe maganar yana kashe mata idoπ
Aneesa tace kai dama nasani da ban yarda da hakan ba kaga nifa banason takura toh kaga tafiyata Ashraf yace toh sai nazo
Aneesa bata juyoba har saida takai bakin gate sannan ta juyo har lokacin idon Ashraf na kanta sai ji yayi tace toh naji din saika zo amma karkazo ka takurawa babana idan ka iso kawai ka kirani ta waya
Ashraf yace toh zo kibani number taki smile Aneesa tayi kana tace ba ka iya searching sunana da abinda nake karantawa ba?
Toh kaje kayi searching din number ta a google dinka idan har kasamota shikenan an gama takarashe maganar tana dariyar mugunta dan ita aganinta bazai samu ba nan tace sai najika anjimar koh?
Bata tsaya jiran amsarshi ba tayi shigewarta abinta smile ashraf yayi kana ya furta Aneesa kenan lallai bakisan waye Ashraf ba Allah akanki sai ince nafi kuda naci wurin shan mangwaro
Shigewa cikin motarshi yayi ya tadata bai tsaya ko inaba sai kofar gidansu Adama yana isa yayi sa'a sharif ya dawo daga aikenda ummansu tamasa zai shiga gida kenan sai Ashraf yace ji mana dan Karamin abokina
Sharif ya juyo yana washe hakora nan ya gaida Ashraf bayan ya amsa ne yace halan kai kadin adama ne dan naga kuna kama da ita eh ni kaninta ne kasan Anty Adama muguwa ce idan bamuyi homework dinmu ba sai ta zanemu ko kuma ta hanamu kallo kasan saurayintannan mai zuwa nan shikuma ba.... ....... Ashraf ne yace kai abokina shiga ka kiramin ita kace ana nemanta a waje
Toh sharif ya shige ashraf dariya yayi kafin yace ohhhhh God........... me nayi ne wai yau.......
Niko nace oho
✍π»by Leemat
Love u allπππ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
Wannan page din nakune sisters yan MUNEERA HAUSA NOVELS group ina mai jinjina maku banida kamarku Allah barmu tare Ameen ❤πππ»ππ»
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ€
19
Ashraf yace wai me nayi ne yau?
Ban tambayi yaronnan sunarshi ba gashi ya shige anyway ba matsala idan Adama tafito sai ta fadamin sunanshi ai
Yana jingine da motarshi Adama tafito ganin Ashraf ne ba karamin bata mamaki yayi ba ta kasa boye farin cikinta tace Ashraf?
Ashraf yace yes shine Adama karaso mana ta matso bayan sun gaisa ne take tambayarshi yanda akayi yasan gidansu smile yayi yashare zancen kamar baiji ba kana yace da ita number gimbiya nakeso kibani zan samu?
Smile tayi kafin tace tabbas zaka samu amma me zakayi da number?
Ashraf yace pls kibani nan ya kwashe komai yanda sukayi da Aneesa ya fada mata dariya tayi mai isarta kana ta furta inama ace ku tabbata a haka har tsawon rayuwarku da nafi kowa jjin dadi domin kuwa ba karamin matching da juna kukayiba wallahi kun dace da juna
Jin haka yasa Ashraf yace adama zan iya yarda dake?
Adama tace y not? Zaka iya mana Ashraf yace inaso in sanar dake wani abu mai muhimmanci kuma inaso yazama sirri tsakanina dake don Allah karki fadawa kowa Adama tace toh shikenan bakomai inshaa Allahu bazaka jishi a bakin kowa ba har sai in kaine kafadawa wani
Smile yayi kafin ya fara zazzage mata abinda ke cikin zuciyarshi yana gama wa sai Adama tace habaaa......
Ai daman biri yayi kama da mutum ai ni na dagoka tun jiyannan so bkm Allah taimaka saidai samun kan kawata zai maka wuya tunda kaga batada lokacin love smile yayi kana yace ai kibarni da ita kawai nan adama tace ammanfa karikemin ita amana banda......Ashraf yace habaa adama ai ba haka nakeba kinga nima ban tabajin ina kaunar diya mace a rayuwata ba kamar Aneesa ba
Dan haka karki damu inshaa Allahu babu abinda zai sameta sai farinciki toh shikenan Allah taimaka Ameen ya amsa
Sannan yace toh yanzu ki taimakamin da numberta in ba haka ba zan iya rasa ta kuma idan na rasa Aneesa zan mutu tausayi yaba Adama yanda yake maganar kamar zaiyi kuka
Adama tace zan baka karka damu nan tabashi number farin ciki agun Ashraf baya misaltuwa ai baisan lokacinda ya bude mota ya ciro makudan kudade wanda shi kansa baisan ko nawa bane ya mikama Adama ita kuwa tace tagode taki karba yi yayi kamar zai mata kuka hakan yasa ba yadda ta iya ta karba nan yake tambayarta sunan kaninta smile tayi kana tace sharifulla woowww nice name nan yasa hannu a aljihunsa yaciro bandir din 100naira yamika mata yana fadin kibawa abokina shariff adama tace aa kabarshi zan bashi acikin wannan Ashraf yayi juyin duniyarnan amma sam Adama taki karban na shariff ok bkm nasan abinda zanyi cewar ashraf
Nan sukayi sallama da juna har zata shiga gida sai ashraf yace laaaa baki bani numberki ba babbar kawa
Smile adama tayi tace ok gashi nan tabashi yana murna yawuce koda ya isa gida part dinshi yashige yayi wanka sannan yaje part din iyayenshi
ummanshi tayi mamakin yanda yashigo mata yau cikeda farinciki sai smile yaketa faman yi yana duba agogo kasa hkr tayi tace son yadai?
Lfy kk ta duba agogo ko wani secon?
Smile yayi baice da ita uffan ba cen minti 5 haka sai yace umma inajin yunwa fa cikin jin dadi yau danta tilo yace yanajin yunwa wanda bai damu da abinci ba umma tace son muje gasucen jere akan dinning sai wanda ka zaba
Ai kuwa yayi kan dinning ya zauna umma duk tabi ta rude sai faman tambayarshi taketayi wanne zata zuba mar
Ya nuna mata wani hadadden fried rice wanda yaji kayan hadi bayan ta zaba mashi ne yace umma costlow nan ta zubamai cin abincin yayi hankali kwance har ya cinye umma ce tace Allah nagode maka yau dana ne yacinye abincina nan hawaye yafara zubo mata ganin haka yasa Ashraf smile kana yace habba umma yanzu dan na cinye abincinki ne kk hawaye toh inshaa Allahu bszan kara ci ba nan da nan ta share hawayenta tana fadin haba son ai hawayen farin ciki ne wannan tunda na haifeka baka tabacin abunci......
Ashraf yace ummata takaina zan baki mamakine amma ba yanzu ba kici gaba dayimini addu'a Allah bani sa'a akan abinda nake nema nikuma nayi maki alkawarin cigaba da cinye abincinda kika dafamin
Allah bada sa'a son kullum addu'ata kenan Allah taimakeka yabaka mace ta gari jin haddu'arnan daga bakin ummanshi yasashi yin smile dan harga Allah yaji dadin addu'ar Ameen ya amsa
Aneesa ko tunda tashiga cikin gida bayan ta kammala abinda takeyi sai taje ta kwanta ai kuwa sai hoton Ashraf kawai taketa gani tajuya nan ta juya cen ganin ba sarki sai Allah ne yasata fito waje a varandarta ta zauna sai faman tuna yanda sukayi da ashraf taketa yi smile tayitayi data tuna yanda yaketa mata yau
Mama ce ta iso wurin ta zauna tana fadin yar mama yau kin gaji koh
Jin shirun aneesa ne ya bata tsoro taba aneesar tayi nan tadan razana kafin tace mama yaushe kk zo nan mama tace yar mama meke damunki ne
Aneesa tace bkm mama ta lura da yanda taketa smile itama smile din tayi nan tafiddo da dambun shinkafar da tayi dazu aneesa na ganin dambun shinkafa ta fara smile tana fadin mamata2
Tashiwa tayi taje ta dsuko ruwa tafara cin dambun mama kuwa shigewa tayi don gyara mata ciki koda mama tashiga sai taga ko ina a kimtse
Karfe 7:30pm Ashraf na hango yafito daga bathroom nan yayita kwalliya kamar mace karfe 8pm yafito yashiga motarshi kirar infiniti sai gidansu aneesa a kofar gate din ya faka nan ya fiddo da wayarshi ya kira aneesa
Aneesa da take zaune itada mama da baba sunata hira ita tama manta da wani wai ashraf jin wayarta na kara ne ya katse masu hirarsu tana dubawa sai taga bakuwar number taki dagawa rejectin tayi ganin anyi rejectin ya dagama Ashraf hankali kara kira yayi akaro na biyu nan ma taki dagawa mama ce tace kiba baba ya daga tunda bakuwar number ce haka kuwa akayi tamikama baba ya sa a kunnensa baice kala ba a cen dayan bangaren akace Amuncin Allah ya tabbata agareki ma abociya kyau da nutsuwa gimbiyata ina... . Jin haka yasa baba yamika mata yana fadin kiji abinda ake fada ai kuwa aneesa tasashi a handsfree nan Ashraf yace gimbiyata kinajina kuwa gani a kofar gidanku ina jiranki
Datse kirar aneesa tayi batareda tace uffan ba kirjinta ne ya hau dukan 9 tara
Mama tafara cewa Allah abin godiya
Baba yace shine wannan dayazo da rana?
Aneesa tace eh kanta a kasa toh tashi kije mana kice yashigo kallon kayanda ke jikinta ne tayi mama tace haba ai kayan baida matsala je kishigomin da suruki na Aneesa tace mama bafa surukinki bane wannan a....
Mama tana dariya tace toh naji maza jeki cemai yashigo ba yanda ta iya haka ta mike cikeda kunya jiki ba kwari tafito ai kuwa mutuwar zaune Ashraf yayi ganin yanda kayan jikinta suka mata kyau dukda ba kwalliya a fuskarta amma ba laifi tayi kyau
Fitowa yayi dan yasan batasan shike cikin motar ba gimbiya jin sunar yasa tagane shine ai kuwa kafin tayi magana sai ji sukayi..............
✍π»By Leemat
Love u allπππ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ€
20
Sai ji sakayi baba ya bude gate abudai kamar wasa soyayya mai karfi ya kullu tsakanin Ashraf da aneesa yau takama friday
Karfe 2 da rabi na rana Aka daura Auren Aneesa Abbas Da Ashraf Sudais
Ankai Amarya dakinta Ashraf ne yashigo kafin kace me har sun fara . ......... cen najiyo ihun Aneesa tana fadin.............. ...
Ba abakina zakuji mutuwar sarki baππππππ
0 comments:
Post a Comment