Wannan kalma ta daki Walyn a lokacin da bata shirya ba,
Zurbat ta mike daga zaunen da take inda wayar dake saman cinyarta da jakarta suka fadi saman fari kal din careau din wajen,
A lokaci daya gaba daya jikinta ya dauki rawa, ba inda baya rawa a jikinta,
Bakinra ta kara budewa da bila adadin dan yin magana sai dai kawai hakoranta suke hadedewa bakin na rawa lebunanta na marmarmar,
Juyawa ta yi da karfi wajen da Agaishat take,
Kafarta ta daga da niyar karasawa wajen Agaishat din idan ya so idan ta isa sai ta aikata mata abinda ya samu koma menene,
Sai dai me, idannuwanta ne suka rufe ruf,
Bata gani sannan a hankali lumfashinta ya yi sama ya dauke dif, inda ta aniya zubewa a wajen,
Du hankalin mutanen wajen ya yo kanta inda du aka mimike hankali tashe, domin bata karasa kasa ba ya tarota jikinsa ta sume a jikinsa,
Tsai ya yi ya kurawa fuskarta ido, a sumen abin sha.awa da ita, ta yi fayau ta nuna fuskar innoscent,
Dan mayafin da ta yiwa wayo ne yake faman sabulewa inda Alhinayett ke tsugune inda suke hankalinta tashe ta shiga magana kamar haka" War, mu je asibiti, ta suma fa, bata motsi, Wardugu mu kaita asibiti,
Dubansa ya dago a hankali inda take ,
Murmushi ya sakar mata yana dubanta , muryarsa ya rage sosai domin ana faman zagaye su du kuwa da irin tsaron da sojawan ke faman bayarwa da tsare du wani wanda zai yi gigin karasawa inda suke sai wa.inda aka tabatar da kusancinsa da wardugu mai girma ne ake bari ya karasa inda suke, hakan bai hana mutanen dake wajen zaman amaren karasawa da sauri suna tambayar wai lafia? A hanzarta kaita asibiti mana?
Wardugu ya ce da Alhinayett, " Alhi, bafa wani abu na yi mata ba, ke ai kin san ina hakuri da ita ko? Gaskiya ce kawai na fada mata fa,
Alhinayett ta ce" menene ma.anar Orronur?
Wardugu ya lunshe idannuwansa ya kai dubansa inda Agaishat ke tsaye tana so a barta ta karasa wajensu aman an hanata dan gurin faman cakulewa yake sai kacaniya ke tashi kowa na faman a barshi ya karasa ya ga kwakwaf,
Ya dawo da dubansa wajen Alhinayett ya lumshe idannuwansa yana dan shafa gaban goshin Walyn dake kan kirjinsa sume kafin ya ce" *ORRONUR* na nufin *RAINA*
idannuwa Alhinayett ta zaro cike da tsoro ta kai dubanta da sauri kan Walyn, Balaki! Shi ne kalmar da ta fito daga bakinta, ai kuwa da sauri ta mike tana fadawa mijinta a saki hanya a kai Walyn asibiti, domin tana adu.ar Allah ya sa lamarin ya tsaya a iya sumar kawai, kar ta samu mutuwar barin jiki na bugawar zuciya,
A yanda Walyn ta baiwa kishi madaukakiyar daraja a rayuwarta, a yanda walyn ta dauki lamarin soyayar mijinta a zuciyarya da son kai mai girman gaske, a yanda Walyn ke taka tafiarta na rayuwa da izgili da fariwa da neman magana? A yanzu, wardugu , ya ce kau bani gu, Wardugu a yau zata iya kiransa da Masifafe, ohk so yayi ta daga bali, ta jawa kanta ya daki banza, tabas suma ta zama wajibi a rayuwar Walyn a yau, domin da wannan lamari bai razanata ta suma ba, zata tafka haukan da Wardugu zai sumar da ita, ya salam, ya salam, haka kai tsaye? Tabas tana hangen Wardugu zai zama jarumi wajen fadawa Walyn wannan lamarin a duk lokacin ta sani ya bayana, aman bata taba tunanin kai tsaye haka ba? Mata? Me ke yawo da kusoshin kanmu ne? Gashi dai, da darajarta , da girmanta, da dan shakunta da yake ji ta bale ta saka lokaci daya ya janye du wani laka na jikinta! Ribar me ta ci? Ana kishi, kishi halal ne, kowace mace na kishin mijinta, aman kishima ai taku ne, 🤦♀,
Da sauri aka bude wajen aka shigo da mota, du wannan tsare tsare haka mijin alhinayet ya take da mota har kusan matatakalar , aka bude motar ,
Mikewa Wardugu ya yi da ita a jikinsa ya samu ya sauka a hankali ya sakata cikin motar,
Bai shiga ba, ya dawo bayan ya cire rigarsa ta saman wato kaki din mai dogon hannu sai bakar body ta ciki ta bayana mai dan gaheran hannu sannan ta tantanke jikinsa baki daya, hakama ya sakata cikin wandonsa ya yi zanzaro da ita a ciki,
Hular kansa ma cirera ya yi, ya koma wajen da Alhinayett ke tsaye ya dubeta ya ce" ki zo mu je,
Da sauri ta juya dan dauko jakar Walyn da wayarta, har ta bude ta saka cikin motar ta ji muryarsa ya ce" ita fa?
Ba sai ta tambaya ba , ta san wace yake nufi , dan haka ta karasa kusan Agaishat ta damko hannunta kawai ta janyota suka nufi motar inda shi ya shiga gaba su kuwa suka shiga baya suka zazauna,
Gudu yake da motar, baka jin komai sai kuryar Agaishat tana ta tamabayar abinda ya samu Walyn, me ke damunta? Me ya sameta ? Bata da lafia ne? Ko gurdewa ta yi? Alhinayett ki bani amsa mana? Dibi fa ta suma fa,
Uta dai Alhinayett ta yi wani zuru tana kallonta, to me zata ce da ita? Ita bata ma san abinda ke faruwa ba, bata taba kawowa ranta haka ba, hasashenta bai taba hasaso mata haka ba, ita yanzu fatanta a karasa lafia kar ta farka ta ganta kusa da ita ta kashe su a motar nan, kai rana tsoron zafin kishin Walyn, macen da ta salwantar da gudan jinninta dan kar ta haihu da wuri a fara yi mata irgen abinda ya rage a mata kishiya idan hakan ta kama? Ina ga yanzu hakan na kokarin kamawar? Taf
A haka suka karasa clinik, wato asibitin kudi,
Nan da nan aka gungura gadon mararsa lafia aka dora Walyn aka shiga da ita, inda du suka fito suke zazaune a harabar wajen mai cike da shukoki masu fulawa masu kyau sosai,
Mutane na kai kawo masu zaman jinya, sai likitoci, sai motar sojoji biyu fa ra biyo su suka dan rarabu suka zagaye asibitin kowane ka dube shi ba alamar ya san kalmar dariya ,
Agaishat dake zaune kusa da Alhinayett ta yi zaman yan makaranta , ta dafe kuncinta da hannunta na dama ta zubawa gazon din wajen ido tana kallo aman fal tunani ne cikin ranta da sumar da Walyn ta yi, har ga Allah hankalinta a tashe yake, me ya samu Walyn din?
Wayar Walyn ce ta dauki tsuwa , Alhinayett ta mike ta mikawa Wardugu tana kule da yanda mijinta ke binta da wani kallon da ba zata iya gane fasararsa ba, aman kallon na bata tsoro itafa tsoronsa take ji, domin a daren jiya ba abinda ya yi mata bacinsu suka sha sosai ko hannunta mai taba ba, amab a yau sai wani kallon gididiga yake binta da shi!
Mahaifiyarta ce ke kiranta, hakan ya sa ya daga ya fada mata suna likita da sunnan GAZOBI sannan ya kashe
Agaishat dake dan satar kallonsa tana mamakin yanda ya amsawa sarakuwarsa, wani a dakile kuma kalmomin basu fi a kirga ba,
Taf, hakan na cikin hukunce hukuncen da zata gindayawa wanda zata aura, walahi au ya girmama iyayenta tamkar nasa au a hakura da auren koma waye, yo ita ina zata iya zama da irin halin wardugu? Namiji ne da ya fito mata na faman wawura kansu da kafarsu? Ina sam bata son namiji mai kyau da cika ko mai kudin da zai kasance ita kulun hankalinta a tashe yake, namiji ne da dan isar sa mace ko wacece baya duka mata? Du kuwa da irin son da yake mata? So dai ai bai kai wanda yake yiwa Walyn ba, aman ko ita sai ya dankari banza idan hakan ta kama? Anya wardugu na wasa da matarsa irin yanda annabi ya yi? Anya Wardugu nada lokacin sauraron matarsa? Kai ita zata so ta samu namiji irin wa.inda ba ruwansu, wa.inda zasu baka incinka su baka damarka su baka darajarka,
Ajiyar zuciya ta sauke a lokacin fa ta bude ido ta kale shi ta ga sun yi ido hudu, harare ya watso mata wanda ya bata mamaki da tsoro, me kuma na yi? Shi ne tambayar da ta yiwa kanta.
Dubanta ta maida wajen Alhinayet ta ce" Alhi, bani wayarki na yi kiran Ayyana dan Allah, na fada mata halin da ake ciki na kuma fada mata ta biyo min da hijab dina kin ga dan kwalin ya fadi fa,
Da sauri Alhinayett ta dubi kanta, Lah kanta ba dan kwali, gaba daya kyan gyaran gashin ya fito sosai ta yi wata yar caras da ita,
Ai kuwa wayar ta mika mata tana ayyana Wardugu sai ya hada daga ni da a aurena ne kika fito a haka da ke din ya ci ubanmu
Number Ayya dake kwakwaluwarta ta dora tana satar kallonsa, mamaki take wai kallon nan da ya same shi na meye? Sai ya tsurawa mutun ido tamkar yana kallon tv ko waya, kuma ba abinda ya dame shi dan kun yi ido hudu ya kawar da dubansa? Aa sai dai kai ka kawar, wannan ai musulunci ya hana irin kallon nan tsakani da Allah
Shi kuwa duban da yake mata, yana so ne lale lale ta iya yarensa na kallo, yana so idan ya dubeta ta gane me yake nufi da dubansa ba wai ya tsaya yana ta haikar baki ba, yana so ta gane wannan shigar batai masa ba, baya so, hankalinsa, ransa, nutsuwarsa duka yana nema ya rasa a lokacin da ta fito a haka, ku ji fa hankali kwonce yltana danna waya ta kara tana zubawa mamanta shagwaba ba ruwanta da wa zai kala ko me mutun zai kiyasta a kanta a ransa? Yana kallonta ta kashe wayar ta mikawa Alhinayet ta maida taguminta ,
Sai damun mutane take da tambayar me ya samu Walyn, ko meye damuwarta a ciki? Shi kadai ke fadansa a cikin ransa kafin ya yi kwafa yana tunanin idan ta kai shi bango bai san irin jijigar da zai mata ba,
Ba.a wani jima sosai ba mahaifiyar Walyn ta zo, tsakaninsu da Ayya kuwa bai fi minti biyar ba, sai gata itama an tukota a motarta
Kamar ko yaushe cikin kanshinta da lafayarta har kasa da san saukakun awarwarayenta hannunta dauke da leda kamfanin Butique wace ta sako hijab din yarta,
Salama ta yi masu kafin ta tambayi mai jiki?
Nan suka shaida mata docter ne ciki , yace ya daidaita numfashinta aman cikin ruwan da ya jona mata da na baci wanda zai saka ta farka a hankali,
Ayya ta yi fatan Allah sawake, ta tambayi daman bata da lafia ne?
Su kam basu da wannan amsar, hakan ya sa ta bude hijab din, maimakun ta bata ta saka sai ta budeshi da kyau ruwan shadar jikinta ne, ta juya Agaishat dake tsaye kusanta ta kama gashin kanta gaba dayansa ta hade shi ta yi masa dan tuntun madaidaici sannan ta zira mata hijab din mai hannu da wani dantel a jikinsa sannan zif ne da shi dan karami wajen wuya wanda mutun ke ja ya kama fuskarsa ,
Hijab din ya yi kata kyau das a jikinta sannan tsayinsa har kasa sosai,
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kawar da dubansa daga wajensu,
Docter ne ya fito da dan sauri yana tambayar ina wardugu?
Daidai nan su Mu.azam suka karaso ,
Wardugu ya nufi wajen docter, Inda Ayya ta je wajen su Alhinayett ta ce" ku kuwa me kuke har yanzu a nan ? Ku zo maza ku tafi gida haba dare ya yi,
Alhinayett zata yi magana wata nurse ta fito da gudu ta ce" Docter tafa tsoge allurar ruwan kuma du wanda ya je kusanta doke shi take,
Da sauri du suka nufi wajen hankali tashe,
Wardugu ya saki wani murmushi yana kallon yanda suke rige rigen shiga dakin,
Kansa ya girgiza ya bi bayansu,
Mahaifiyarta ce ta karasa da sauri kusanta yanda take rusa kuka tana fadin" Walahi, sai na kashe su, daga shi har tsinaniyar bakar fatar nan! Da raina ba.a yi ba, ba za.a yi ba yarinyar da Wardugu zai kira da *ORRONUR* ba, ita ita Wardugu zai ciwa mutunci?
Daneta uwar ke faman yi karta mike, sannan ta tambayeta wai meye? Meye? Me aka yi?
Walyn ta daga jajayen idannuwanta ta sauke saman mahaifiyarta ta ce" a wajen partyn banzan nan da suka tsara ne ya rakata wajen zama bayan ni ya barni nan zaune ni da nake matarshi, shi ne na tambaye shi wacece ita? Wani matsayi ke gareta da har zai lakaba mata wannan sunnan? Yar gidan waye ita?
Shi ne yace da ni wai *RANSA CE!*
dif dakin ya yi Agaishat dake bayan Ayya tana dan lekowa idannuwansu suka hade da na Walyn,
Wani kukan kura ta yi ta ture mahaifiyarta ta taso da gudu da karfin balaki ta nufi wajen Ayya tana furta" Walahi sai na ga ubanda ya tsaya maki, ko wani irin boka ko malan ya ci.......shi! Ya dura ashar mai yaji😋, shegiya bakar fata mai bakar aniya, mijina ya fi karfin buzuwa banza jahila!
Kafin take isawa ta ganshi tsaye, tsaye tsakaninta da Ayya da kuma Agaishat, kikam ya tsaya ya tsura mata ido
Zagaye shi ta so yi ta karasa wajensu, sai dai ya riko hannunta ya yi mata turawa daya da ta saka ta je can ta fadi,
Daga kafarsa ya yi ya tunkareta da wani irin sauri da niyar kasara wata gaba ta jikinta
Sai dai muryar Ayya ce ta dawo da shi daga wannan niya tashi wace du mazan wajen suka yi gagawar tarar shi, rike shi sukai suna faman bashi baki kan kar ya yi, ko ba komai mahaifiyarta a wajen a zaune, idan ita ta saki baki tana abubuwa irin haka shi ya ci girma,
Wani irin huci yake saukewa inda ya bi umarnin Ayya da ta nuna masa hanyar fita,
Shi ya fara fita sannan suka mara masa baya inda ta fashe da kuka da wani ihu ihu tana munana mangangannun kan ba dole ya tafi ba, ita ga mabaukaciya ai dole a bar mata waje, daman ita ta san Ayya bata taba kaunarta ba, gashi ta kawo masa karuwa har gida ana cin amanarta, ita kuwa zata ga yanda za.a yi soyayar nan!
Mahaifiyarya ce ta daka mata wata gigitaciyar tsawa kafin ta ce" dan ubanki ta yaya kikai masa tambaya kan wacece itan??
Kwashe du magangannun rashin da.ar da ta yi masa ta fadawa mamanta, inda ta shiga bata karfin gwuiwar cewa" ya fada maki haka ne dan ya tunzura ki ke kuwa kika hau banza, ko ni kika yiwa rashin kunyar nan ai sai na baki haushi bale Wardugu, me zai yi da wannan mumunar halitar in ba shirmen kishi da ya rufe maki ido ba? Ya fada ne dan ki zubda haukan, kin kuwa zubda hankalinki ya kwonta! .....haka ta yi ta dorata kan yayi haka ne dan ya bata mata itama aman me zai yi da Agaishat?
Tunda suka kama hanyar gidan ayya kansa ke jingine jikin madubin motar yana sauraron ajiyar zuciyarta , domin ta tsorata da gannin kamar ita walyn ke farauta,
Shiru motar ba mai kwakwaran motsi har suka karasa gidan Ayya,
Shi ya fara fita ya nufi falon ayya, kafin ya shiga ya iya sabule takalman kafarsa sannan ya ciro rigar dake cikin zanzaron jikinsa ya yi tsaya yana mai jin kansa tamkar zai rabe gida biyu!
*BAKA KYAUTA MINI BA!*
Ayya ta fada a lokacin da suka shigo da Agaishat, tana kallo Agaishat ta nufi dakinta,
Kanta ta juyi wajensa , ya dafe kai yana jijiga kafarsa, balaki na cinsa, da wanda zasu yi kawai yake nema, ta ce" Baka kyauta min ba, ka san sarai halin matarka dan me zaka sako min yarinya cikin shirmen ku? Me ya hadaka da fadin wannan maganar a kan yarinyata a wajen matarka?
*DAN INA SON TA*
Maganar ta fito daga bakinsa da amo mai karfi karfi,
Da sauri ya juyo wajen Ayya ya taka har zuwa inda take zaune ya duka ya dora kansa saman cinyarta,
Zuciyarsa ce ke wani irin dokawa ya ce" *Ayya, Wayo Allahna Ayya zan mutu, Ayya mutuwa zan yi, Ayya zafi nake ci a nan*
🙁
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
7️⃣5️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
*Walahi ma cherie, Madame dakoro ina jin nauyinki da kunyarki, kin kasance mai mugun alkhairi a gare ni, ki sani aminiya kuma yayata ko sako ne ki turo na wanda kike so a farantawa ta hanyar nvl da dukan abinda Allah ya hore min, in sha Allah ba zan baki kunya ba, na gode na gode*
Ya nuna daidai zuciyarsa still kansa na saman cinyarta,
Jinsa yake bashi da wani karfi, jinsa yake bashi da wata dabara, dan Allah kowama ya ji kuma ya shaida yana kaunar yarinyar Ayya,
Jikin Ayya ne ya mutu, a ranta tana fadin shikenan ya fada, eh lale, aman aurensa fa? Matarsa fa? Aurensu duka duka shekara nawa? Wannan tada ce al.ada ce ta iyaye da kakani, ba.a yiwa macen tubawa kishiya haka gatsal sai idan ta yi haihuwa uku zuwa hudu ko ta samu kwararun shekaru da mijinta a kafan bakwai abinda ya yi sama, daman a dangi a baki suke, an sako su a gaba, komai kanantar abu idan Wardugu ko ita suka yi zaka ji ya yi gagawar zagaya dangi a labe a yi da su aman a gabansu ba.a nunawa sai dai a yi ta masu fadanci, tana cikin rudani......sai dai kuma wannan lamari mai girma ne, ya kasa jurewa, ya kasa kawar da kai, abin na bashi wahalar da ya kasa hadiyewa sai da ya fada! To aman ba a nan gizo ke sakar ba, ita Agaishat din da bata san me yake ciki ba? Bai fada mata ba, bai nemi soyayarta karara ba, shi girma girma, shi bai san ta yaya gododo da shi zai tsaya gaban yarinya ya ce da ita yana sonta ba, gashi ya tada dan karamin yaki a gidansa wanda take fatan Allah ya tsawatarwa abin, aman kuma ya fake a bayan fage,
Ita kam, ba zata taba tirsasawa Agaishat ta so Wardugu ba, aa, ta yaya? Ace da ita me? Dan danta ne? Dan ita ta haife shi? Ita kam tana da kunya!
Yawu ta hadiye kafin ta saka hannunta ta dago da kafadarsa,
Abinda ya cika idonta ta mayar kafin take dan dukansa a kirji ta ce" Wardugu? Dama zaka taba sarewa kan mace? Ka zauna kanai min rigima tamkar wani baby kan yarinyata? To ni me kake so na yi maka bayan ka san lamarin nan ba zai taba yiwuwa ba dan duka duka yaushe ka yi aure?
Wardugu ya bude jajayen idannuwansa ya dora kan mahaifiyarsa , ya jima a haka kafin ya ce" a gabanki, sai na iya yin kuka, tunda kika haife ni, kika sha gwagwarmayar rayuwa wajen rainona da komai nawa ai ba zancen na kai kukana wani wajen,
Ayya ni ba zan bude bakina na dubi yarinya karama kamar Agaishat nace da ita ina sonta gatsal haka kawai salon ta raina ni, sannan Mu.azam dake wani takamar ya aureta ya saketa dan ni kennan ya ji dadin kara fada ko me?
Haka fa yarinyar samari ne da ita fa, kin ga wani shegen buzu wuyansa na lauyewa yana jawo shi kwana ya yi ya wuni yana kiranta yau shi ne har wajen dinern nan, Ayya kinfa san yaren nan na zamani ko wasa kake da su yanzu zasu samu hanyar rainaka!
Ayya ta shiga girgiza kai tana murmushi a kasan zuciyarta ta ayana" da sauranka, zako ka ga halin yarinta!
A fili kuwa ta ce" Wardugu, maganar Walyn fa?
Wardugu ya mike tsaye kafin ya koma saman kujerar ya zauna kusa da Ayya sosai ya ce" Ayya, shin adini ne? Aurena da Walyn kusan shekara hudu fa , Ayya kece shaidar irin rayuwar auren da nake da Walyn duda ba zuwa nake ija baki labari ba, aman du lokacin da kuka hadu sai haukan ya bayana , Ayya, yanda kika san rayuwar tumakai haka muke da Walyn,
Sam bata zauna bama, ta fahimci waye ni, ta fahimci menene ainahin zaman auren bale har ta wani kula da shi,
Takamarta kyau, wayonta yawo, isarta ta je wajen yawon ta yi gadara da kudin da ni ke nema,
Kishi....sakaran kishi, in ba dan ina tsaye a gidana ba Ayya da Na rantse maki Walyn ko ke sai ta hana ni yiwa magana bale wata mace a duniya, tarota nake , lalabata nake, kwatanta mata nake, fushina nake nuna mata , ko zata yi hankali ? Ko zata gane ni ne gaba da ita? Ni ya dace ta bi? Aman cikin kwakwaluwarta banda kusoshi ba komai, gashi ina zaman zamana, ta sa na shiga wata rayuwar ta shirme! Shirme mana Ayyana .... wai ka zauna tunanin yaro karami? Ayya zan koma kauyensu yarinyar cen, na fadawa iyayenta komai abubuwan dake faruwa, na fada masu ina neman aurenta,
Ayya ta mike ta ce " kul, kul, kar ka yarda yarinyata bata aminta da kai ba ka wani je neman aurenta, ba wanda zai mata karfi, kana magana rigima na yawo a harshenka, to ka zauna min ba inda zaka yau, dan na san in dai ka fita a gidannan sai ka tafka wani abin !
Ta karashe tana yafa mayafinta ta nufi hanyar kicin inda wardugu ya bita da kallon mamaki,
Ayya kennan, a duniya ba wace yake zuwa ya sanarwa sirinsa mafi sirri irinta, yana da rike abu gaban kowa aman ita yana gagawar sanar da ita damuwarsa ko farin cikinsa, tana kuma iya yinta dan gannij ta shige al.amarinsa, bata taba saka wani ya yi masa abu ba, sai dai yau gashi wai wai shi ya fada mata zai mutu ko zata tsorata? Aman wai tace da shi ya nemi soyayar yarinyar? Daga yanzu ya yarda yarinyar nan ba shi kawai ta gama halakawa ba, har Ayyansa ta kwace! Yar Buzuwa ta iya kwace,
Wayarsa ce ta dauki kuka,
Dagawa ya yi domin mijin Alhinayett ne,
Mikewa ya yi da kyar ya fice ya nufi can tsakar gidan,
Tarar da su ya yi cikin mota Alhinayett sai kumbura take tana karawa kan ita su biyo kafin su tafi,
Wardugu ya yi tsaye ya kare mata kallo, kafin ya maida dubansa wajen Colonel ya ce" walahi idan ka yi wasa ta fahimci halin da kake ciki na mugun sonta da kake zata mayar da kai hotiho!
Kai yanzu gabjejen kato da kai, ta sakoka gaba ka kawota wai ta ga lafiata lau? Da ni na haifeka yau da sai na baka shegen duka, yo ina anfanin wannan lamari?
Sai da wardugu ya gama yi masa fada tsaf sannan ya taka ya karasa wajen motar,
Kwonkwasawa ya yi ta bude, tana dubansa kafin ta ce" Wardugu lafiarka kalau? Ina Agaishat din?
Ce maki na yi bani da lafia?
Wardugu ya fada yana zazaro mata idannuwansa,
Da sauri ta dube shi da kyau kafin ta ce" gani na yi hankalinka a tashe,
Ohk shi ne kika tiso keyar danki ya kawo ki?
Ya kuma bata amsa yana hararanta,
A ranta ta fadi" To fa,
Wardugu ya nunota da yatsarsa ya ce" walahi na san ciwon kaina, ba zan bari ki wulakanta bawon Allah ba nima Allah ya kama ni ta hanyar saka wani dan rainin wayon ya wulakanta ni, ke yanzu da nine aka tiso keyata zuwa ganninki a lokacin da nake ango me zaki kalen? Alhi, bana son ki kaini wajen da zan rike makogworon wuyanki, walahi a kan aurenki idan baki zama mace mai kyawawan dabi.u abin alfarin mijinta ba, zan tarda ke har inda kike na ya gashinki a kasa ! Ke ni ba nasiha ko rarashinki zan ba, ke kanwata ce, idan kika zubar da mutunci da darajar gidanku , kika aniya wulakanta wannan mutumin ni zan masa aure da kaina sannan na tataka ki idan kina so ki rufe ni,
Kiwit kiwit take da ido bata ce da shi komai ba, dan ta san idan hakuri tace zata bashi yanzu abin zai girmama, yi masa shirun shi ne ya fi sauki, sannan ta yi dan daman bata matsa kan su biyo ba, ita wollah yannayin Agaishat ne ma ya tsaye mata a rai, bata so ko kusa Agaishat ta saka tsoron Walyn a ranta, ta so ta ganta yau ta fada mata abinda ya sa Walyn yi mata haka sannan ta karfafa mata gwuiwa, kanta ta sada har ya gama fadansa wanda tana tunanin taka kaya ne dai suka yi, dan kuwa har colonel din da ya biye mata sai da akai masa ,
Ja ya yi ya goya hannunsa daya a bayansa yana dubansu har suka fice da motarsu,
Agaishat dake tsaye bakin window din dakinta ta sauke ajiyar zuciya kafin wani murmushi ya kubuce mata,
Zama ta yi bakin bed dinta daga ita sai gajeran wandonta da yar riga karama na baci ta ce" Wai wai wai, rigimame yayana, kai aman gaskiya shi ne daidai da matar nan tasa , haba mace kamar wace aka haifa ana dambe? Ita kulun cikin fada da neman a gabzu take?
Gashin kanta ta tatara ta daure kafin take yin bismillah ta bi lafiyar gadon,
Idannuwanta ta lumshe dan neman baci, sai dai me....idannuwansa ta ji sunna yawo a jikinta,
Wani irin tsammmmmmm ne ta ji tun daga kanta har yatsarta,
Da sauri ta mike zaune tana yatsina fuskarta,
Mikewa ta yi ta koma bakin window din ko zata kara ganninsa? Kai wollah ita bata gajiya da kallonsa, tana tsoron rigimarsa , aman kuma tana girmama irin yanda yake girmama mahaifiyarsa, ba mahaifiyarsa kawai ba du wani abinda ya shafeta yana masa mugun girmamawa, zata so komai ya daidaita tsakaninsa da mahaifinsa, zata so gobe kiyama ya samu rabauta, domin aljanarsa tana karkashin kafar mahaifansa, tana so alkhairinsa ya same shi gobe kiyama ,
Yana tsaye dai, da waya a hannunsa yana danawa, ba zata iya gannin me yake dannawa ba,
Bata shirya gannin ya dago da kansa ba sai gani ta yi ya kallo wajen windows dinta, da sauri ta duke kasa domin ba zata so ya kamata tsamo tsamo tanai masa kallon kurulah ba, me zai ce? Ina ai sai ya yi mata wata muguwar fasara,
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yake sakin murmushi, ya ji idannunta a jikinsa, ya san ta tsaya a wajen can.....
Juyawa ya yi ya koma fallon yana kara kiran abokinsa kuma direbansa kan a gobe su bi jirgi su jufi timiya, zai daki abin da karfi ya ga mai tsayar da shi daga Walyn, da Ayyar, da uta Agaishat din! Idan tana so idan ta ji ya aureta ta hadiyi shinkafar bera 😒
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
7️⃣6️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
A nan falo ya kwana , ko nace ya yi rabin kwana , domin bai shigo falon ba sai da ya dauro alwallah ya zo ya tayar da sallah ,
Ya jima yana sallah kafin ya zauna ya yi ta adu.a,
Ya roki Allah, ya kaskantar da kansa wajen ubangijinsa, ya roki zabin Allah, ya sani bai isa ya baiwa kansa ba, ya roki Allah ya sa alkhairi ce a gare shi da kowama,
Nan saman salayar dake falon ya jingina da kujera ya dan rintsa,
Asuba na yi ya farka ya fice a falon inda ya je ya sake daura alwallah ya fice a gidan dan zuwa masalaci,
Yana dawowa wajen karfe shida da yan mintuna ya zauna nan saman kujera idannuwansa suka kai kan wayarsa dake ta vibration,
Ikon Allah, shi ne abinda ya fada kafin ya ja dan tsaki kasa kasa yana mai jin haushin masu saukon kiran nan! Ko me zai masu?
Wayar ya janyo yana duba sunnan,
Mamaki ne ya kama shi, aa *GUKUNNI* kuma?,
Da sauri ya mike ya daga kiran, domin abu daya ya fado masa a rai ko wani mai laifi ne ya gudu daga cikin prison?
Salama ya yi masa , suka gaisa da kyau kafin wardugu ya yi shiru yana saurarronsa,
Gukunni ya ce" gani a kofar gidanka Wardugu,
Wardugu ya kara kamuwa da mamaki aman sai ya boye ya ce" ai ina gidan Ayya ne Honorable,.
Gukunni ya shafa sankon kansa ya ce" ka kwatanta min in sha Allah zan karaso, ina tafe da muhimiyar magana ne , wada na jima ina nemanka Allah bai yi ba sai yau na samu wayarsa
Wardugu ya dan tsurawa waje daya ido, anya kuwa zai kwatanta gidan mahaifiyarsa haka kai tsaye?
Sai dai wata zuciyar ke fada masa da ba komai bane sai alkhairi, dan haka ya yi masa kwatance suka katse kiran,
Rigarsa ta saman kakinsa ya nema ya dora saman bakar rigar dake jikinsa,
Kansa ya daga sama ya ga basu fito ba, bai ji motsinsu ba, dan haka ya zauna nan yana jiran karasowar Gukunni Bayan ya baiwa masu gadi damar idan ya zo ya shigo,
Ya kai minti arba.in kafin ya karaso, domin dai ba sannin gidan ya yi ba bale ya kai kansa kai tsaye,
Sai dai a lokacin da ya ga kofar gidan ya gane ko gidan waye, wato Elhaji Marahut, tabas sunnan Wardugu , Wardugu Marahut,
Murmushi ya yi ya lalubo wayarsa ya dannawa Marahut kira , da yannayin barkwonci yake sanar masa komai da fadin ai yana kofar gidansa,
Nan marahut ya yi jim kafin yace da shi baya kasar fa, aman zai shigo da wuri wuri, shima ya yi murna sosai sosai, sukai salama,
A tsakar gidan aka dakatar da shi, kafin Wardugu ya fito,
Tunda ya fito yake dubansa da yannayin farin ciki, kai shi dai yana son yaron nan ko dan kwazonsa da rashin tsoronsa,
Wardugu na zuwa ya bashi hannu suka gaisa sosai, sannan Marahut ya ce" Wardugu, tafe nake da magana mai mahinmanci, fatan zan samu lokacinka,
Wardugu ya amsa shi tare da yi masa jagora zuwa falon Ayya, domin ko ba komai yana kaunar datijon yana gannin mutuncinsa, dan kuwa su shara.ar da ya je ya gani da idonsa wace ya yanke hukunci na manyan kasa masu laifi, yana gani da idonsa yana yankewa ne da zuciya daya ba tare da wani dar ba, hakan ya sa ake bashi tsaro domin ya kasance yana samun hare haren mutanen da suka ji haushin irin hukuncin da ya yanke masu ko wani nasu!
Suna shiga suka tarar da Ayya na saukowa daga sama, sai naza kanshi take, zuwa lokacin duka duka karfe takwas ce, inda Wardugu ke duba lokaci dan kar karfe tara ta yi lokacin tashin jirginsu zuwa agadez,
Gaisawa suka yi, nan Ayya ta mike zata bar masu wajen aman ya nemi da ta zauna,
Cikin nutsuwa ya shiga warware masu abinda ke tafe dasa shi, ya dora da fadin" lamarin ne a cakule, lamarin ne a hargitse, kadara ce ta afka mana, sai dai mu ce Alhamdulilah, autata Allatchi ita ce mahaifiyar yarinyar, ta fuskanci rayuwa sai hamdallah, yanzu haka tana Chaina, tana karbar magani, nima nakan zo sati sati dan na kara duba tsohon da muka zo da shi duda akoy masu kula da shi, nakan zo na ga komai na tafia daidai kafin na koma wajensu,
Al.ajabi, tausayi, ne suka kashe Ayya a zaune, inda wardugu ya sada kansa yana jin wani lamarin da bai san menene ba,
Ayya cikin mamaki ta ce" ta yaya? Waye ya daura masu aure? Waye ya yi gigin daura masa macen da bai ga alwalinta ba???
Gukunni ya yi shiru, jikinsa ya kara mutuwa, hankalinsa ya rashi, ransa ya kara baci da lamarin, dubansu yake yana tunanin sun cancanta su ji haka kuwa?
Eh kwarai sun cancanta, idan ya so, idan mijin da ya aureta ya ce ba zai zauna da ita a haka ba ba laifi, Allah ne gatan bawa, dan haka ya dago fuskarsa da ta nuna yannayin da ya shiga lokaci guda ya ce" *BAI AURETA BA, BA AURE YA ZAUNA DA ITA , BA AURE SUKA SAMU ALBARKAR HAIHUWA*
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,
Shi ne abinda Ayya ta fada tana mai dora hannunta saman kanta,
Wardugu ya dago da kansa da mugun sauri tare da bugawar zuciya,
Bin innalilahin da Ayya ke maimaitawa ya yi,
Tausayi? Mugun tausayin matar ne ya dirar masa, sai tausayin Yaren, ya Allah, kowa da kalar kadarar rayuwarsa, Agaishana....shi ne abinda zuciyarsa ta ambata,
Ayya?
Muryar Agaishat ya katse masu halin da suka shiga,
Da sauri Ayya ta sauke hannunta daga saman kanta, domin hakan da Agaishat ta hango ne ya sakata saukowa da gudu daga sama dan jin ba.asi, sam bata lura da Gukunni ba, sai da ta ji an riko hannunta an juyota,
Tsarki ya tabata ga Allah, sarkin da ya halici bayi, sarkin sarauta rabih,
Ga yarinyar nan, wannan itace mai kama da shi din, ga kamarsa karara a fuskar yar, har irin yanda idonsa keda tsaga da girma,
Tsai ta yi tana dubansa, kwarai ta ga kamar fuskarta a tare da wannan mutun , sai dai tunanin ta ina? Ta yaya? Ita yar asalin timiya fuduk zata hada jini da mutun haka Wanda suturar jikinsa kadai ta isa ta shaida shi din ko waye?
A hankali ta bi hannunta da ya rike da kallo, yatsutsansa irin nata,
Da sauri ta dago zuwa fuskarsa, sai kuma ta juya wajen Ayya gabanta na dokawa ta ce" Ayyana, wanene wannan?
Ayya dake ta kokarin maida kukanta ta ce" Agaishana, kakanki ne, ta karashe tana mai sakin kukan dan ta kasa rikewa,
Agaishat ta janye hannunta tana dubansu su duka, da sauri ta je wajen Ayya ta ce" kukan me kike? Wani ne ya mutu? Kaka kuma? Ni nake da kaka? Me ya saka ki kuka Ayyana?
Wardugu dake duban Ayya kansa kawai yake girgiza mata dan kar ta fadawa Agaishat abinda ya sakata kuka, baya so, abin sai ya yi masa yawa, bai sanba ko zata yi tawakali ta yi hakuri?, dan haka a hankali ya lumshe idannuwansa yana ji Ayya na fada mata gaskiyar waye gukunni a wajenta, wato mahaifin mahaifiyarta,
Cikin nutsuwa ta warware mata yanda suka hadu da Algabit, sai dai sam Ayya bata fada mata dayar maganar ba,
Farin ciki kam ta ji shi, sosai ta yi murna, sannan ta yi adu.ar shiriya ga mahaifinta, domin bata da abin cewa kansa ita kam,
Nan aka kuma shaida mata rashin lafiar Anna dalilin tonuwar asirin ,
Da da uwa, nan ta yi sokoko ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, du sai ta ji duniyar ba dadi,
Kanta ta sada dan kar ta nuna mugun damuwarta har abin ya taba Ayya, domin zuwa yanzu ta gama yarda da soyayar Ayya a kanta tamkar ta uwa da d'a ne,
Dubanta ta kai wajen Wardugu idannuwansa a lumshe ko barci ma yake?
Bai ci komai ba , shi ne ya fado mata a rai haka kawai, dan haka ta mike ta nufi kicin ba tare da ta kara bi ta kan wani ba,
Nan Ayya ta fara fada masa maganar auren Agaishat din da ya mutu,
Sosai abin ya dake shi, har ya tambayi ba.asi?
Wardugu dake zaune ya ce" bashi da huja,
Ayya ta kai dubanta kansa, ta girgiza kai ta ce" ya gabatar da hujarsa, wace sam bai dace dan wannan hujar a saki mace ba, batai masa laifin komai ba, shima bai mata ba, hasalima tun kafin a yi masa aikin ya yi sakin, bisa hujarsa na aminin nasa ya fi shi son ta!
Dum gabansa ya fadi, da sauri ya kalli Ayya, la.ila ha ilala , shi ne abinda ya iya cewa, ya ake maganar yana magana kai tsaye bayan ga wada ke yi? Bai taba zaton, bai taba kawowa ransa cewar Ayya zata fadi maganar haka kai tsaye ba ,
Shiru ne wajen ya dauka, kafin Ayya ta ci gaba" na ji ba dadi, na yi fushi, Aure? Sai kace abin wasa? Ya tashi ya guntule igiyar auren yarinyar da bata san me ake ciki ba? Kan wani shirme? , shima Wardugun ya nuna masa ba dadi, maganar da nake maka har yanzu ba wani jituwa tsakaninsu,
Nan ta kwashe du abinda ya faru ta sanarwa Gukunni da da farko ya dauki zafi har ya ga kamar an wulakanta yarinyar ne dan anai mata kallon marar gata, sai dai daga baya da ya ji komai ya yi tsam ya dubi Ayya, ya kuma dubi Wardugu da ya dafe kansa yana tunani, aa, du wannan jawabin na menene? Ya Allah🤦🏻♂️
A daidai lokacin da Agaishat ta fito dauke da farantin da ta soyawa Wardugu dankalin turawa da plantain ta nufo falon,
Muryar Gukunni ta karade wajen da tambayar da ya saka ni ranaza har na saki biron hannuna,
Gukunni ya dubi Wardugu ya jefo tambayar da basu tsamaci zai yita ba, Gukunni ya ce" *SHIN DA GASKE KANA SON AGAISHAT NE? ZAKA IYA AURENTA KODA KUWA TABON DA RAYUWARTA KE DA?**************
MEMBERS BAK'A CE GRUP, WOLLAH INA JI DA KU TAMKAR NAMA DAYA A MIYA,
WATO KUNA SAKANI NISHADI DA COMMENT DIN KU,
HAR KUKE SAKAWA NA JI NI YESSSSSS NI DIN TAKU CE😌😌😌😌😌
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
7️⃣7️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
Da sauri Ayya ta ce" Aman ya Gukunni, ba shi ya dace a tambayi wannan abin ba, bana so a kuma yiwa y'ata abinda akai mata sai ta zaba! Kuma da ake maganar nan , bai jima da yin aure ba fa, ko cike shekara hudu bai yi, hasalima matarsa na kwonce asibiti dan ya dankara mata maganar cewa yarinyata *Orronur* dinsa ce! , dan Allah kar a tauye min yarinya,
Dubansa ya kai kan Agaishat da ta ja ta tsaya tana binsu da kallo, wai bata fahimci wa ake shirin hadata da shi kuma? Waye matarsa ba lafia? Wardugu ne, meye kalmar Orronur ke nufi? Ya Allah wani hadin za.a kuma yi mata ko me? Hadinma da Wardugu? Mutumen da ita ce shaidar irin yanda yake kwasa da matar so ma bale ita?, mutumen da ta yi imanin har abada ba macen da zata samu gurbi a zuciyarsa kamar yanda *AISATA* ta gama mamaye ko.ina? Domin a yi yawo da ganga ba zata hadiye cewar ba sonta da yake ne ya saka ya kasa yafewa mahaifinsa dan ya aureta ba! Mijin WALYN? ko ba wannan ba, ita ta yi imanin koda daura masa ita za.a yi a kafa zai ja banza a titi sannan ya take da ranjasss ya bale ya jefawa karnuka su cinye banza, ita a wa? Yar wa? Algabitt? Um, yayan manya, manyan kansu suna farauta ? Ita bata son mai kyau dan kar a ringa rububinsa, ita ita....
Tunaninta ne ya katse a lokacin da Ayya ta ce" kar mu yi haka da kai,
Tsai ta kai dubanta wajen Ayya a ranta tana fadin" ki yi wani abu, ni ban san wani kaka ba, yaushe ma ya zo gidan? Ki yi wani abu kar a kashe maki d'a, sannan a kashe maki y'a!
Wajen sai ya kasance Agaishat na kallon Ayya da wani yannayi, Wardugu kuwa tsai kawai ita yake kallo yana son sannin halin da ta shiga dan kuwa ya san ba kurma bace, kuma ba sakara bace, tabas ta fahimci maganar da ake,
Ayya kuwa Na duban Gukunni, inda Gukunni ya gyara zama yana sakin murmushi yana duban Wardugu da yannayinsa, ya san waye shi, ba zai taba amsa shi a haka ba, ya kuma lura da yannayin Agaishat da irin duban da take yiwa uwar rikonta, wani sanyi ya ji a ransa domin ya ga shakuwa, kauna ta Allah tsakanin Agaishat da mahaifiyar Wardugu,
Mikewa ya yi ya yiwa su Ayya salama, inda Wardugu ya mike ya bi bayansa dan yi masa rakiya yana mai jin ba laka a jikinsa,
Sai da suka dangana da motarsa ya dakatar da shi, inda ya dauki katuwar wayarsa ya danna kira,
Dagawa ya yi tare da kara yin salama sannan ya ce" honorable ka samu ganninsa ne?
Gukunni ya yi murmushi ya ce" wato Alhaji, ka manta ni lauta ne kafin na zama alkali, ? Bayan wannan ka manta numberka na niger ne na kira ya shiga ba cod ba komai? Kana ina ne? Domin ina so in sha Allah mu hadu kafin lokacin sallar azahar, ina tare da Wardugu,
Jim ya yi yana jin ba dadi, ya Allah, kowa dai ya san halin da suke ciki da matarsa uwar dansa, koda yake shekara da shekaru its normal,
Fada masa ya yi su hadu a Wardugu Palas, wajen da ya dawo operation irin na da,
Wardugu kam gum da baki, bai ce komai ba ya bi bayan Gukunni cikin motarsa da bodyguard dinsa biyu suka daga sai wajen da yake ainahin wajensa,
Murmushi Marahut yake tunda ya gama magana, ya dubi Wardugu ya ce" kana son ta kennan?
Wardugu ya hade fuskarsa ya kawar da kansa irin ba shi ya kawo maganar ba,
Marahut ya girgiza kai yana murmushi ya ce" mai hali, baya daina halinsa!
Honorable, kana nufin, ba zaka juya chaina a gobe ba sai an daura auren nan? Baka gudun rigimar Ayyansu? Ita yarinyar shin tana so?
Gukunni ya ce" ina tunanin su za.aiwa alfarma!
Marahut ya sada kansa,
Agogon hannunsa ya duba, sannan ya mike ya ce" karfe 2 ka zo da sadaki saifa millions arba.in. ka same mu a masalacin Elhaj Murtala ,
Yana gama fada ya mike ya shige ciki inda Gukunni baki bude ya mike ya bi bayansa yana fadan wani irin Millions 40 sai kace wata yar gwal ko wata budurwa?
Wardugu kam wani tsadaden murmushi ne ya saki daga zaunen da yake, yau ranar Asabar, 5 ga watan Jun , rana ta raba tsaka zai malaketa,
Jama.ar da suka halarci sallar azahar suka shaidi daurin auren, Daurin auren *WARDUGU MARAHUT* da *AGAISHAT ALGABITTT* bisa sadaki Millions 40 cefa ladakan, ,
Zamanin whatsup, zamanin android , nan da nan mutane suka fara watsa wannan lamari, inda ake yayatun buzuwa ce, suna yi har fiye da haka, Buzuwa ce General ya santale,
Nan da nan yan jaridu suka fara neman Wardugu cikin birnin Niamey,
Yan mata suka fara doka waya suna neman jin karin bayani,
Gidan redio ta saki labari,
Walyn,
Walyn dake kwonce tana shating ta ga kanwar kawarta ta dora saman status cewa" kaka kara kaka, wai da gaske ne ko da wasa? General ya bada sadakin buzuwa million 40 arma ta zama tasa? General wardugu ya watsa kuraye, abin son jinma ana cewa Black ce!....?
Ta karanta ya fi a girga , kafin kamar hadin baki, kira ne, mesage ne whatsup ne, facebook ne? Abu ya zama a lokaci daya ya shiga shigowa,
Bata gama tantancewa ba mahaifiyarya ta shigo dakin asibitin a fujajan ta ce.............
Ayya hankalinta ne ya gama tashi a lokacin da ta ji wannan bayani ta bakin Marahut da ya yi kiranta da bakuwar number ya yi mata murna da fada mata ya daurawa dansa aure da yarta ga sadakin nan zai zo ya kawo da kansa idan tana so ta saka a hana shi shiga!
Wardugu,
A lokacin da ya ji eh lale Allah ya damka masa igiyoyin jan ragamar rayuwarta ya mike ya shiga motarsa da kayan jikinsa na tun jiya da bai samu ya tsaya bama bale ya canza,
Zama ya yi ya jinginar da kansa, idannuwansa ya lumshe sai kuma Walyn ta fado masa a rai,
Wani tausayinta ne ya ji ya dirar masa, dan ya sani ne Allah kawai zai tsayar da ita kan saka kanta a uku,
Motarsa ya tayar da kansa ya harbata bakin titi da gudun balaki......
Bai zame ko.ina ba sai clinik din da Walyn take,
A nitse ya kashe motar ya zare kys din ya fice daga ciki,
Taku yake cikin nutsuwa da ingarma, ba zaka taba fahimtar halin da yake ciki ba har ya tura kofar ya bude,
Ido hudu suka yi shi da ita, tana zaune ta ziro kafafuwanta kasa, ta ja rigar clinik din can saman cinyoyinta, kanta bude gashin kanta ba ribom, ta tsurawa waje daya ido domin jinta da ganninta ne suka fauke na dan lokaci,
A hankali ya karasa kusan gadon da take zaune ya cire takalmin kafarsa ya dan saci duban mahaifiyarta ya ga tanai masa wani kallon da ba zai gane na kyama ne? Na tsana ne? Ko na deception bane!
Hannunta ya kamo yana dubanta,
Murya cinkushe ya ce" Walyn,
Idannuwanta kawai binsa suke da kallo, Namiji? Bata taba sannin kalmar da zata yi ajalinta bane sai yau! Namiji Namijinma wanda ta fi aminta da shi, Kishiya? Kishiya Wardugu ya yi mata? Ita Walyn? Me ta rage shi? Menene? Ita ya wulakanta a idon duniya? Ita ya wulakanta a dangi? Yanzu uban wa zata yiwa daga kai da jiji da kai a gari? An taka dokar al.adunta ma, an tarwatsa takamarta ma, an ci amanarta, dan me? Me ya yi zafi? Me na rasa? Ban taba haihuwa ba....hasalima ban bar kwan ya zama gudaji ba na watsa shi, du domin ka???
Muryarta na rawa ta ce" Wardugu, dandan me? Sex ne ko? Dan wannan ka tozarta ni? Nawa bai isheka ba???
Wardugu ya dane , ya ki nuna komai ya rikota jikinsa ya ce" aa, ba wulakanta ki na yi ba, kuma ba ramuwae gaya na yi maki ba Walyn, ba dan sex na kara aure ba, ina so ki kwontar da hankalinki, ki kwontar min da nawa, idan har kika yi haka Walyn, ina mai tabatar maki da zan canza, zan dawo maki yanda kike so Walyn, idan har kika yi hakuri da wannan jarabawa...zaki ci ribarta, ki yi hakuri, ina baki hakuri ne ba dan na aikata haramun ba, aa , sai dan kema matata ce, ina son ki, ba cusa min ke aka yi ba, Walyn haka itama ba wanda ya yi min dole, ki sani aure lokaci ne, kuma rai ne da shi, ki dauka lokacin yin ne ya yi na yi, kar ki yarda zugar mutane ko na shedan ya yi tasiri a kanki, dan Allah matata ki jure wannan karon, bana so mu raba hali, ki jure walyna......
Ya karashe yana mai shafa gashin kanta,
Wani irin kuka ne ta fashe da shi mai karfi da rudu,
Gaba daya ta saka hannunta saman kanta tana ihu,
Da sauri ya hade bakinsa da nata dan rufe bali ihun da take ......... aman ina cizo ta gantsara masa kafin take kokarin kwacewa daga rikon da ya yi mata tana jifansa da wani kallo irin na bakon halita mayaudari ko wani azalumi,
Aniya wartar du abinda ya zo hanyarta ta yi tana dokawa da kasa, ihu take wanda ya fara tsoratar da dakunnan kusa da ita sannan likitoci suka fara yowa dakin da gudu dan ko tunanin mutuwa aka yi wani marar imanin yake kuka irin haka!
Hannunsa na dama ya saka ya tokare habarsa yana kallon yanda mamanta ke binta tana kiran sunnanta aman cikin ikon Allah dan karamin frij din dake dakin kansa sai da tajanyo ta kifar tana ihun yau sai dai a yi daya, ko ita ko Agaishat!
Mikewa ya yi ya damki hannunta ya jata,
Kiiiiiiiiiiii inda du aka rufa masu baya wasu na tambayar lafia ? Cike da tsoro wasu na kallon ikon Allah da yiwa Walyn kallon wayo Mahaukaciya ce da alama?
Motar ya bude gidan baya ya turata ciki sannan ya koma gaba ya shiga ya rufe ya yiwa motar ky sannan ya tayar ya harba ba tare da ya tsaya daukan mamanta ba, dan ya sani ne, ba zata taba tausarta kan lamarin ba, dan shi kadai ya san abubuwan da ya tsinta uwar na fada a lokacin da ya karaso asibitin,
Hauka fa tuburam, Walyn fa ta zauce, magangannu take saki tare da fadin Warsugu macuci ne, ya cuceta a haka har suka karasa gidan su,
Wannan karron daukanta ya yi cimak ya nufi falonsa da ita, yana budewa ya direta cikin falon ya rufe fallon ya barta nan ya nufi cikin dakinsa ya shige bayi,
Wasa sabon girki, wato dabi.un wasu tubawan idan akaiwa kishiya , shi Walyn ta aro, inda ta aniya dira tana fasa du wani abin fasawa na falon Wardugu, ciki harda katuwar plasma din dake mamaye da bango, ta tarwatsa table din diner da na tsakiyar falon, ta dauko wuka ta yayaga wannan tanfatsetsiyar kujera ta alfarma, ta kawo ruwa ta makawa moket din ta aniya dira tana yagawa,
Ta kama labulayen bangon du ta yaga shegu, ta dira dakin bakinsa ta aniya yaye jibgegen bargon dake malale saman katifar dake kan bed din, ta saka wukar ta yayaga katifar, ta kama kyarta jikin gadon da sif din da komai na dakin, ta fasa madubin dake kawaye a dakin, ta dauki iphone dinsa kwara uku ta tanfatsa da kasa,
Aiki take na gangan, aiki na motsa mutun domin koda Wardugu mai kudi ne an masa asara ta kirki, gashi bai jima da canza komai na gidan ba,
Fitowa ya yi daga wanka daga shi sai tawul yana mai jinsa yana yawo a sama, sai dai me, turus ya ja ya tsaya yana hangen bayanta yanda ta dukufa take yaga bargon da ta yaye stilll tana ihun kuka,
Habarsa ya dafe da hannunsa yana bin dakin da kallo, kafin ya maida dubansa kanta,
Ikon Allah, shi ne abinda ya fada a ransa,
Zagayeta ya yi ya bude sif din yana bin inda akaiwa sabon zane da kallo , ya janyo boxer dinsa da wasu kayansa na kanfanin Gudd ya ciro yana ajiyewa nan jikin bed din,
Ai kuwa ta ankara da shi ta nufo kayan da ya ciro ta dauka ta saka wukar ta yaga,
Bakinsa ya rike ya ce" Walyn da tsada fa??
Bata bashi amsa ba sai harararsa da ta yi ta ce" walahi sai ka saketa, walahi ni na san dan ka rama abinda na yi maka ne, baka yafe mini zubar da cikin da na yi bane shi ne zaka hukunta ni ta hanyar yi mini kishiya, walahi sai ka saketa ko daga ni har kai mu bakunci lahira,
Murmushi ya yi kawai ya girgiza kansa ya kuma fitar da wasu, aman yanzu yana cirowa yana sakawa ne bai ajiye ba dan kar a maimaita abinda aka yi,
Juyawa ya yi bayan ya kile sif din dan akoy kayansa masu mahinmancin da ba zai so ta wulakanta ba ,
Da gudu ta biyo shi tana faman yi masa tijira inda ta nufe shi da wukar hannunta ta nufi cikinsa da ita ido rufe tana alwashin sai ta halaka shi tunda ya yi mata kishiya,
Da sauri ya goce ya tara hannunsa, nan ta yanki gefen hannunsa wajen kaurin hannun nasa da wukar ta yi masa baban yankan da jini ya bale ,
Idonsa ya rintse yana jin zuciyarsa na fara yaba gayatar balakin da take masa,
Kara nufo shi ta yi tana ta balaki da tubanci wanda zagi ne kawai bata saka ba aman har Ayya sai da ta dorawa laifin da bata ji ba bata gani ba tana fadin daman idan sarakuwa ta tsane ka ai ba ta inda ba za.a biyo maka ba,
Hannun mai wukar ya rike inda ya matse shi da dan karfin da ya saka ta kwala kara ta saki wukar,
Janyota ya yi inda yake tsaye ya fala mata mari ya kara mata,
Bai kuma yi mata magana ba sai janta da ya yi waje kujerar da ta yiwa ta.asa ya kama rigar asibitin dake jikinta ya yagata , toh daman rigar ba wani kwari ba sannan botira ne jikinta,
Bata gama gane ina ya dosa ba sai da ta ga daga rigar bai zame ko.ina ba sai wajen da baya faduwa ya saka hannunsa shima ya yage shi ya.......
Tumurmusarta yake da dukan karfin da Allah ya bashi ta wannan fannin,
Dukan da ya fi duka zafi ne yake bata ido rufe ko zai samu ta rufe masa bakinta ta daina magana kan mahaifiyarsa tamkar wata tsararta!
Shin wacece ita? A darajar masu daraja da Allah ya halita a duniya musulmai wacece ita da ba za.a yi mata kishiya ta yi hakuri ba?
Wacece ita da zata ringa budar baki tana jifan halitar da Allah ya halita ba tare da ya ce dan ya yi mata kalar fata haka laifi ta yi masa ba?
Wacece ita da zata ringa zagin kadararsa? Domin kuwa shi ya san Allah ne ya kama shi a kan Agaishat, ya ba zata bar shi ya ji da irin rigimar da yake hangowa kansa ba a tare da mahifiyarsa da kuma yarinyar da bai san meye a zuciyarta game da shi ba? Ya ba zata tarbe shi, ta kula shi, ta taya shi a wannan lokacin da yake cikin garari yana sakin magangannun da sai ya yi wata bai yi masu tsayi irin haka ba ? Ya bata lura da ya so su yi masalaha su fahimci juna, ya so ya rarasheta irin na kowace mace mai inci mai fada a wajen miji idan akai mata kishiya ba? Shin Walyn kwakwaluwarta a tabe take ko tsabar iskanci ne da samun guri? Shin ya fara sakin fuskar da har raini mai karfi ya kara yin tasiri tsakaninsa da Walyn da sauran mutanen?
Ya ga Alama ba Walyn ba, harta da ita Agaishat din idan ya yi wasa za.a samu matsala......
Ya Walyn zata manta ainahin Waye Shi a doron kasa? Ya zata manta shi ne asalin batube gaba da baya cikake mai jininsu dake yawo a jikinsa har ta nuna masa wuka?
Shin ta manta yaya suke da wuka ne?
Shi zata tarba da balaki hauka , da tashin hankali batan ta san adireshinsa ne complet??????
Morning
Idona ya fara ciwo, ni kam sai na huta😍😍😍
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
7️⃣8️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
Ups sauran kadan dai💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Dakinta ta tura ta shiga , jiki ba karfi ko kadan,
Wajen salaya ta hangota inda itama ta dago da kanta tana dubanta, salar la.asar ta gabatar kennan, ta zauna tana adu.a,
A hankali ta karasa inda ita kuwa take faman mikewa tana duban Yannayinta, tamkar tana cike da damuwa,
Mayar da ita ta yi saman salayar ta zaunar da ita sannan itama ta zauna ta rakubu da bangon dakin ,
Kanta ta daga sama tana kallon shilling,
A nitse Agaishat ta ce" Ayyana , lafia??
Shiru Ayya ta yi tana tunanin ta inda zata fara, can ta ce" ina jin kinyar Allah, ina jin kunyar amana , ina jin kunyar soyayar da kike min tamkar uwa,
Da sauri Agaishat ta dubeta da kyau kafin ta matsa kusa da ita sosai ta ce" Subahannalah,
Ayya ta dawo da dubanta wajen Agaishat ta ce" na yi wasa da ke sosai, a yanzu ban san wani hali nake ciki ba,
Agaishat ta dora kanta gefen kafadar Ayya tana fan girgiza kanta, dan ita bata san me zata ce ba, a hankali ta ce" Ayyana, baki yi min komai ba, ba abinda kikai min, me ke damun ki?
Ayya ta ce" Agaishat, na farko haka ya zo ya shige tamkar wasan yara, yanzuma gashi an kara maki wani mai hargitsi,
Agaisha, ni na haife shi da cikina, da aurwn soyaya, aman ni zan fadi dole matarsa ta yi hakurin zama da shi , shi din mai rigima ne, shi din mai taryan rigima ne,
Tun yana yaro nake fama da hakan, gashi abu guda dai shi din bai iya son abu ba,
Agaishana, basu saurare ni ba, basu ysaya sun ji me nake da shi na cewa ba, ko ke abinda ke cikin ranki mahaifinsa ya yi jagorar daurin aurensa da ke,
Da sauri ta dago ta dubi Ayya, idannuwanta du ta ruko da mamaki da tsoro, aure? Da da Wardugu?
Ayya ta kawar da kanta daga dubanta ta ci gaba da fadin" Marahut, jira yake, hanyar da zamu raba abin kallo yake nema, bai jima da fita a gidannan ba, a gadarance ya kawo min jakarnan ta sadakinki ce, tabas gaskiya ne an daura aurenki da Wardugu bisa sadaki Cefa Millions Arba.in,
Kanta sai da ya sara dan dukan da maganar ta yi mata, a hankali ta silale ta dora kanta saman cinyar Ayya kafin take kawo hannunta na dama ta rukunkume cinyoyin Ayya,
Ji take zuciyarya zata balli gangar jikinta ta fito dan tsoro , shikenan, ta faru ta kare,
A hankali Ayya ke shafa kanta ta ci gaba da magana kamar haka" ba zan maki tilas ba Agaishat, duda a yarena namiji nada cikenken iko da matarsa, domin ko ni mahaifiyarsa ban isa na takura masa da lamarin matarsa ba, kin ga a yau a yanzu idan wardugu ya yi niyar wulakanci sai ya zo ya dauke ki ya tafi da ke tafia ta har abada ba wanda ya isa ya tanka shi, musuluncima ya bashi iko a kanki a yanzu, sai dai na sani ne, yana da dar a kaina, ko a al.adunmu na tubawa yana daga abubuwa da yawa idan dai ya shafe ni, idan kika ce ba zaki zauna da shi, in sha Allah zan ci karfinsa,
Sai dai zan so ki nutsu, ki fara duba na rayuwarki kanta, yarinya ce ke karama, idan ba muguwar kadara ba , ba zan so a ce an kama yi maki saki saki kina shiga hannun maza kina fita tamkar kwalo,
Zan so ki saurare ni, ki dauki dabi.u kyawawa, ki rungumi aurenki, zan so ki zowa rayuwarsa da sauyi, ina da kyakyawan zaton ke din zaki iya tankwasa shi kan wasu lamuran na yau da kulun,
Agaishana , *ina rokar ki da ki tsaya ki yi tunani ki ganni, idan har ba zaki cutu ba, ki amshi auren nan, in sha Allah zaki ji dadinsa*
Agaishat da ta yi lamo tana sauraron Ayya ta dan dago da kanta , jikinta har rawa fa yake ta ce" Ayya, Ayya, matarsa, Ayya shi din kansa, ya ji wannan abin? Ayya zai sumar da ni ne, Ayya ni din me? Ni a wa? Ayya matarsa.....
Ayya ta saki murmushi tana kara shafa kanta ta ce" *MATARSA* bani da wata damuwa da ita, du yanda ta ga zata kwaba tuwonta ta ci , tukunyarta ce, abinda na sani shi ne, Bama hada mata gida guda, komai talaucinka indai ka ce mace biyu zaka yi ko sama , to fa kowace gidanta daban,
Sai abu na gaba matarsa, ba ruwanki da ita, sannan koda wasa, ko da wasa kar na ji, kar na ga tsoronta a tare da ke, na me? Aa, ba zamanta zaki yi ba!
*SHI KUWA* baki da damuwa da hakan,
Daga nan Ayya ta yi shiru, bata kara mata haske a abinda take nufi ba,
Baiwar Allah ajiyar zuciya kawai take saukewa, bata da abin cewa , ta san zata je ne a kara sakota ta dawo, toh a sakota mana, an saketa a auren so ma bale na hadi? Nan baci ya aniya sandarta har ya dauketa, ita fa ta sakwa kanta dangana, abinda ta sani daya ne, bama zata ishe shi kallo ba bare har ya wani zauna da ita, ita fatantama kar ya karya mata kafa ko hannu dan haushin an aura masa ita ko ya jirkice mata kanta,
Jin ta dan kara nauyi ya saka Ayya dubata,
Tausayinta ne ya kama ta, ta san dama da wuya ta yi mata wani diban albarka, aman bata yi tunanin ko kuka ba zata yi ba, yarinyar na da hakuri, sannan da alama zata bata hadin kai su baiwa marada kunya,
Gyara mata kanta ta yi da kyau kafin ta kuna mata ac ta dauki jakar kudin ta fice,
Mai aikinta ta kirawo ta aiketa kasuwa dan karo mata itacen magarya, bata ga ta zama ba, yarinya da kishiya gashi da alama tsoron kishiyar take dan haka dole ta zagine, ga irin yanda Wardugu ya yi kundumbala ya ce yana sonta ai sai ta dagewa yarta!
Walyn ta ga rana, Wardugu ya ware mata dukan karfinsa sai da ya kai bata koda iya daga hannunta kafin ya mike,
Bai koma dakin ba, ky din mita kawai ya dauka sai computern aikinsa ya fita,
Motarsa ya shiga yana mai jin kyankyamin kansa ya dauki hanyar gidan Ayya inda gabansa ke dokawa yana tunanin yanda zasu karke da ita,
A lokacin da hancin motarsa ta shiga gidan ya tatara du wani tunani ya watsar kawai ya nufi falon,
Tsaftsaftsaf kamar koda yaushe,
Bai tsaya neman kowa ba ya shige dakin da mu.azam ke sauka ya cire kayansa ya shige bayin da ya tabata a tsaftace take ,
Tsarkake kansa ya yi kafin ya fito ya nufi wajen da kayan ke cikin dakin,
Tsaye ya yi yana duban kayan, anya kuwa zasu yi masa? Shi kuwa ba zai mayar da wadacen ba, da kyar ya lalubo wata jalabiya fara kar sabuwa ya saka ya caje kansa da kumb, ya dauki turare ya fesa sosai ya tsaya gaban mirror,
Sakayau yake jinsa, ya rage nauyi dan haka ya fito da niyar kira da wayar Ayya kan a kawo masa waya,
Dan dakatawa ya yi sakamakon hango Ayya da ya yi tana kallon wajen dakin, sai bayanta ita kuwa tana tsaye da alama wani abu ne a hannunta,
A ransa ya ayana , ya Allah, tana son saka doguwar rigar da ta dan dara gwuiwarta ko dan ta san tanai mata kyau ne?,
Ayya ce ta ce" Wardugu? Yaushe ka shigo ?
Tea din da ta sirba ne ya so sarketa inda ta samu da kyar ta hadiye shi tana zaro ido tana duban Ayya, ta kasa waiwayawa ta kasa zaune ta kasa tsaye sai rike cofin da ta yi da kyau tana jin zufa na neman karyo mata,
Ayya ta dubeta ta yi murmushi, ta ce" ehem, me ma kika ce? Ke dai ina wayarki ina wayarki? Mu ci gaba.... ta fada tanai mata murmushi, domin tun da ta farka bayan magariba ta shiga rigimar ita ina wayarta ne wai? Ina aka kai mata wayarta ? Wa ya ga wayarta?
Salama ya yi kafin ya shiga yana duban yannayin Ayya,
Fuska sake ta amsa shi tana fadin" War, baci ba ka yi ?
Shi kam wata kunyarta ce ya ji ta lulube shi, dan haka ya zauna saman kujera inda yake ta kokowa da idannuwansa kan su yi hakuri kar su dubeta,
Ayya ta kaleta ta ce" Agaishar kawowa yayanki ruwa,
Kamar jira take a kunnata ta juya da dan sauri ta shige kicin,
Sai da ta bacewa ganninsa kafin ya tataro dukan jarumtarsa ya gitse ya hade rai tamkar ba shi bane ya kare mata yaren Wayo Allah zuciyarsa,
Ayya ta dubi yannayinsa kafin take sakin murmushi, wato ita zai rufewa tabarmar kunya da hauka ko? Kunya ta ishe shi shine ya aro jarumtar wawa ya afkawa kansa,
Cikin wayewa ta datijuwar da ta san kanta ta ce" Wardugu zo nan,
Ta nuna kusa da ita sosai,
Wajen ya bi da ido, kafin ya mike ya koma ya zauna yana kakawar da kai,
Ayya ta ce" Wardugu, barkan mu ko?
Kunya ya ji ta kara dirar masa dan haka sai ya sada kansa, kafin ya dago a hankali ya ce" Ayyana, hakuri👏🏻
Ayya ta sakar masa murmushi kafin taa ce" me na ce ni? Ina cikin farin cikin hakan, sai dai me ka tanadarwa zaman y'ata a gidanka? Sannan wani gida zaka kaita? Ka san dai ba.a hada mata ko?
Wardugu ya yi tsai yana dubanta, shi kam yaya zai yi ya raba Ayya da maganar al.adun nan ne? Shi ya so ya hada su, a hankali yau da gobe wata rana zasu yi zumunci, aman yanzu an ce ya raba su, yaushe Walyn zata yi hankali?
Ajiyar zuciya ya sauke bai ce komai kan lamarin ba, Ayya ta ci gaba" za.a yi biki kamar yanda ake yiwa kowace yar gata, za.a kai amarya kamar yanda ake kai kowace amarya, za.ai mata gyara , zaka yi bajinta irin namu domin da namu da nasun du kusan iri guda ne, Wardugu harta da garar namiji ban cire maka ba , sai ka yiwa y'ata,
Ta karashe tana gimtse fuska , daidai Agaishat ta dawo da ruwa cikin goran Awa da kofi na kwalba , abinda wardugu ya fada ne ya sakata jin ba dadi, duda ta san zata fuskanci hakan,
Warsugu yana duban Ayya ya ce" aman Ayya , sai nake gannin kamar ranki a bace kuma kina dariya, Ayyana, Marahut ya daura auren nan, kin ga kuwa tilas na yi masa biyaya,.....
A hankali ta karasa ta ajiye ruwan ba tare da ta tsiyaya ba ta juya zata fice a dakin ta je tsakar gida ko zata ji iskar Allah ta ratsa hancinta yanda ya dace,
*KE*, shi ne abinda ya daki kunnenta da kakausar murya,
Wa zai cewa ke a wajen da daga ita sai Ayya sai shi?
Dakatawa ta yi, a kasan zuciyarya kuwa fadi take, walahi da wani gaulan ne sai na bala masa harara wai wani ke, aman ba komai ba komai😕,
*Ki je dakin ki* , ya fada yana kawar da kansa daga dubanta inda ya ji ransa ya baci a tsakar ransa,
A hankali ta juya ta haye sama ta nufi dakinta,
Dubansa ya maido wajen Ayya ya ce" Ayya, ya zaki bari yarinyar nan tana yawo haka ne tsakani da Allah? Idan da kin ce igiyar wa ke kanta yanzu fa? Ayya, gidannan da maza fa, ga masu gadi, ga sojoji, ga direba, Haba Ayya,
Ayya ta hade fuska ta ce" toh ubanna, nace toh ubanna kawo min duka,
Dan yatsanta ta nuna masa ta ce" Wardugu ka kiyaye ni, bilahilazi na fika ciyayi, kai ku ji kin yaro da rainin hankali, ka je ka gindaya mata dokar mana dan raini ka sakani gaba bayan ka gama raina min wayo da maganar wai ka yiwa Marahut biyaya ka korar min y'a, sannan ka rufe ni da fada? Sauran duka sai na gane ba za.a iya taroka ba!
Habarsa ya dafe kawai yana dubanta, sai da ta gama fadan ya mike ya shiga haurawa saman dakin Agaishat din inda Ayya ta mike da sauri ta bi bayansa,
Gannin tana biye da shi ya saka ya haye da sauri ya shige dakin ya rufe,
Zaune take tana cila yan kafafunta saman kujera, ita bata wani saka abin a ranta ba, sai tsagal ta ga mutun a gabanta,
Fuskarsa ce ta kayar mata da gaba, inda ya nemi waje ya rike a jikin hannunta , kausasa muryarsa ya yi ya ce" ba sai na rantse maki ba, ki yarda ko aa, daga yanzu du wani katon da ya ga fuskarki dukanta wanda ba muharaminki ba , sai na kwakwalo idannuwansa na soya maki kin ci!
Ya zaki ringa fita da irin wannan shigar kowani gaula na gannin ki? Ke kin san me zai raya a ransa a kanki? Ya yarinya karama da ke tun da kika shigo rayuwana zaki ringa zigani uwa shayi? *KE* ya fada yana nunota da dayan hannun nasa wato da yatsarsa manuniya sannan sai a lokacin ya hada idannuwansa da nata,
Gaba daya ya ji ana janye iskar tashin hankalin da ya zo a yi daga jikinsa, fuskarta ta marairaice ta zama tamkar ta jariri, dan bakinta ta dan bude shi inda hakoranta na gaba kwaya biyu da suke da dan tsayi kadan ruwan na zomo suka dan leko haka kuma ana gannin na kasan jere reras fari kal da su suna dan shekin abin yawun bakinta,
Idannuwanta tar cikin nasa, sun dan canza kala daga fari kar zuwa orang kadan alamun suna daf da cika da kwala,
Dan girgizatan da ya yi ya saka gashin kanta dan hautsinewa suka bazo gaba kadan,
Kallon cikin idon da take masa, tafe yake da sakon ka ji tausayina, kar ka ilata ni👏🏻,
A hankali ya shiga sasauta mugun rikon da ya yi mata, tsayinsa ya rage kafin yake lumshe idannuwansa,
Abinda ke kara tarwatsa tunaninta ya yi mata, wato janyota ya yi a hankali ya rungumeta tsam a jikinsa inda idannuwansa ke lumshe yana daidaita bugun zuciyarsa tare da neman tayimakon Allah kan kar ta ci karfinsa😒,
A hankali ya ce" *ki daina fita a haka, kin dai san yanzu mijinki ne ni ko? Walahi idan kika ki bin magana na, Allah zai toya ki, ni kuwa in dai kan fita ba lulubi ne ba zan iya yafe maki ba, dan ina iya aikata aikin dana sani ORRONUR*......
TO KU BANI KIDAN COMMENT A SAMA...........
NVL YA KUSA KAREWA, ALLAHU YA NUNA MANA KARSHENSA LAFIA
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
7️⃣9️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
Sowie yau kadan ne😔😔😔😔😔😔😔😔
*Mijinki ne ni ko?* shi ne kalmar da ta fi kara sakata wani yannayi na firgici da shiga wani irin hali,
Kennan ya ji, ya sani, harma ya kirayi kansa da kalmar *MIJI* a gareta, wannan gayen mai tsada?
Idannuwanta ta lumshe ta kara shiga kirjinsa dan walahi kamshinsa daban ne, duda na yau ba irin na kulun bane aman na yau dinma wani silent kanshi ne,
A hankali take kara shigar da hancinta wajen botiran jalabiyar tana shakar kanshin, tana mai jin duniyarta ta kawata,
Shima dake rungume da ita caji kawai yake dauka, a hankali ya dora hancinsa saman gashin kanta, kamshin daban ne, kamshin mai ni.ima ne, mai sanyi ne, a hankali ya dora hannunsa wajen tsatsonta daga baya ya dan rike kadan kafin ya ce" *UM*?
Agaishat da ta hadiyi yawu da kyar , ta dan cire hancinta daga wajen kirjin masa , idannuwanta ta dan dago ta ce" *Um?*
Wardugu ya tsura mata ido shima yana dubanta, a ransa kuwa fadi yake....yanzu haka ya je wajenta? Haka ya ratsa min ita? Haka ya taba min jikinta? Har fadi min yake ni.imarta? Ya Allah😔,
A fili kuwa ya ce" baki ce komai ba, bayan na budi baki na yi ta maki zubar da bana yi!
Agaishat ta mayar da kanta saman kirjinsa dan walahi ita bata so ya janyeta a yanzun kam, a hankali ta ce" ni tsoro nake ji,
Wardugu ya yi jim tamkar ba zai tankata ba kafin ya ce" tsoro? Na me?
Agaishat ta yatsina fuska kafin ta ce" idan ranka ya bace, idan kana fada, tsoro nake ji, dan Allah idan na bata maka rai kar ka yi min duka ka ji? Ba zan kara fita a haka ba, dan Allah kar ka min mugun duka walahi ba laifina bane,
Ta karashe tana lumshe idannuwanta tana jin yanda zuciyarta ke dokawa,
Bai so ta yi shiru da magana ba, buzancinta na tafia da imaninsa, ta iya karya harshenta da fadin RRRRRRRRRRrrrrrrrr sannan tana magana tana lumshe idannuwanta ne, sannan lebenta na wani marmarmar gashi sam baya rabuwa da man lebe,
Dan haka Wardugu ya ce" *Laifin me kika yi?*
ya tambayeta a hankali ,
Dan haka ta dago da kanta ta kure shi da kallo, yanda fuskarsa ke fitar da wani yannayi mai fuzga, idannuwansa kuwa a limshe suke, dan haka tana duban nasa bata san da shima ita yake kallo ba ta dan yatsina fuska ta ce" na aura maka ni da ya yi,,
Bude idannuwansa ya yi gaba daya bisanta, hakan ya sa ita ta kawar da dubanta a kansa,
Janyeta ya yi kadan daga jikinsa dan lamarin ya fara karkata baya so ko daya ta gane shi,
A hankali ya karasa da ita bakin bed dinta ya zaunar da ita ,
Wani tsadaden murmushi ya yi mata kafin ya daga kafadarsa ya ce" zan yi tunani.......
Tana zaune ya juya ua je ya bude dakin , burum Ayya ta shigo tana dubansa tana duban Agaishat,
Bata ga wani yannayi na firgici ko tsoro a tatare da ita ba, haka shima bata ga wani bacin rai a tatare da shi ba, hasalima rabawa ya yi gefenta ya fice a dakin,
Ayya ta karasa inda take zaune tana dubanta,
Agaishat ta dago da murmushi mai sauti ta dubi Ayya ta ce" Ayyana, bai dakeni ba, Ayya wai menene ma.anar *ORRONUR*
Ayya ta zaro idannuwanta da yanayin mamaki karara a fuskarta,
Kawar da kanta ta yi tana boye murnarta, da fushi ya shigo dakin, aman ya fita wasai....shi ne abinda ya fi tsaye mata a rai, Alhamdulilah... shi ne abinda ta fada, sai ga wayarta na kuka,
Kanta ta dan dafe ta dana ta mikawa Agaishat ta juya bata bata amsar tambayarta ba, yo ita me zata ce mata? Kai gaskiya da nauyi.
Agaishat ta kara wayar a kunnenta, nan Alhinayett t saka ihun murna daga zaune fadi take" Agaishat, ina yake? Yana ina? Tun da na ji labarin nake doka wayoyinsa aman gaba daya a kashe, takima a kashe, wayo Allahna dan Allah bani labari dala dala tawan, fada mini yanda aka yi lamarin, ya furta? Ya fada ne?
Agaishat ta rafka tagumi tana sauraron Alhinayett kafin ta ce" wai an furta me? Waye zai furtan?
Alhinayett ta ce" wahala ne zaki bani dan kin san ba zan iya fitowa yau ba ko? Ki fada min ta yayane ya furta? Wayo ni baku tashi soyewar ba sai da aka shige daka da ni?
Agaishat kam du ta sakata cikin duhu, wai soyewa, wai ya furta? Murmushi kawai ta yi ta mata gum kan itama bata san da auren ba sai dazu Ayya ta shigo ta fada mata,
Alhinayett ta jinjina lamarin, ta fada mata in sha Allah da ta fara zuwa aiki zata roli alfarmar ta zo gidan, tana da magama da ita, sannan ta buda wayarta....
Haka dai suka yi salama , inda Agaishat ta yi tsai da wayar a hannunta, magangannun take kara bita tamkar karatu,
Guguwarsa bai hana shi zama special a wannan fannin ba,
Aa, ita da ba auren soyaya bane tana jin duniyarta sabuwa a cikin kirjinsa to ina ga matarsa?
Ya Allah dole ta yi kishin abinta, dole ta ji ba dadi,
Wani tausayinta ne ya dirar mata da tunanin magangannunta na asibiti,
To ko dai tun a lokacin aka ce za.a yi masu aure? Ko me fushi Walyn ke nufi a lokacin?
Kafadunta ta daga tana fadin" damanfa ba kaunana take ba, ba fadan wannan take ba, me yiwuwa na mata wani abin ne dan ni banma san me take fada a fadan nata ba🤷🏻♀️,
Ya jima tsaye kofar gidan nasa,
Ba wata anguwar manyan masu kudi bace , aman anguwar sai ka shigeta zaka ringa cin karo da gidaje na alfahari,
A boye take , gashi a bakin gari take, bai jima da gama gine gine a anguwar ba, inda tuni an fara kama hayar gidajen,
Tankamemiyar vila din da daman can ya ginata ne dominsa ya danna horn inda mai gadi ya bude masa dan ya san shi ne kawai mai zuwa,
Gidan du shukoki ne an yi tsari da su an masu kwaliya waje waje, sai wajen ajiyar motoci can kasan wata runfa,
Kana shiga zaka ga kanka a ciki, ko.ina madubi ne gaka tun daga kanka har kafarka,
A hankali ya sauka inda yaronsa ya dauko jakar da ya zo da ita yana biye da shi har suka sadu da accenseur din gidan ,
Shiga ya yi ya dana number etage hawa na shida wanda yake na karshe inda dakinsa yake,
Su ya ajiye su suka sauka, sai da ya kai masa jakar har kofar dakinsa sannan ya juya ya tafi,
Panneau solaire ne le aiki a gaba daya gidan, sai katon inji irin na ma.aikata dake boye nesa da dakunnan dan zafinsa ko kara kar ya damu kowa,
A hankali ya shiga da adu.a, dan bai taba zuwa ya kwana gidan ba,
Dakunnan dake bangaren nasa ya leleka, komai ya yi masa kamar yanda tsarin rayiwarsa yake, mutun mai son farin abu, sai dan maroon da aka sirka dan kar farin ya yi yawa,
Dawowa ya yi dakin da ya fi girma wanda shi ne dakin bacinsa ya shiga ya bude wajen kakinsa, domin a gidan nan abinda babu kawai mutane ne, mutanenma masu gidan, dan kuwa du abin bukatarsa ya saka, sannan gidan a boye yake bayi niyar zama cikinsa kwana kusa ba, kai shi ya yi niyar ya ringa sauke mutanensa idan zasu yi baban meeting da sojoji na harkar aikinsa dai da sauransu, ya so gidan ya zama na sirri, aman baki daya walyn ta fitar masa da wancen gidan a ransa, baya jin zai kuma rayuwa cikinsa domin ta fitine shi a gidan nan,
Ya yi masa tsarin da zasu rayu tamkar soyayar fari, tsaftataciyar soyaya sai dai bata zauna bama bale ta gina hakan ,
Wannan gidan ya yi shi da wani irin gini ne mai dakuna barkatai, sannan du wani bangare akoy hanyar da zata sadaka da bangarensa, inda maduban bangarensa bulet ba zai ratsa su ba,
Kai an fa zuba nema a gidan dake anguwar da ba wanda zai hasaso irin gida tamfatsetse haka a wajen ba wato *AEROPORT*,
Sai da ya gama uzuririkansa, kafin ya zauna ya hada wayoyin da ya shigo da su da layikansa ya jona ya haye saman bed dinsa domin zuwa lokacin dare ya yi sosai,
*idan kana fada, tsoro nake ji, dan Allah ka daina*, shine abinda ya fado masa, na daina fada?
Ya fada , to ni mafadaci ne ?
(Fans wardugu ya ce wai shi mafadaci ne ?)
Haka ya juya ya kuma juyowa yana duban memory card dinsa, wace a cikinta akoy hotonta da ta juya da niyar zuwa wajen zama a wajen diner Alhinayett,
Alhinayett, sai da ya ambaci sunnan ta fado masa a rai, aminiya, na san kin neme ni,
Kwonciya ya yi da tunanin a gobe gobe ba sai an kai nesa ba zai yiwa Ayya dukan abinda ta bukata a kawo yarinyar nan kowama ya huta, domin duda tace ba zata fita haka ba, shi kam ta dawo kusa ya fi,
Idannuwansa ya lumshe, yanda da ya rungumeta ta kwonta a jikinsa ya fado masa a rai,
Mikewa ya yi yana tsaki, a kasan zuciyarsa ya furta ba dole ba ita da ta taba aure! Malama ki bar min rayuwa na huta hakannan!
Haushin kansa yake ji irin yanda ya zauna tunanin wannan yar yarinyar! Dan haka ya mike ya saka kakinsa na aiki, ya dauki karamar wayar da ya saka layinsa na aiki ya yi kiran commisariar da ta fi kusa da gidansa ya tambaya wa.inda suka fito raful da hanyar da suka bi,
Haka ya fito a katon babut dinsa dake gidan ya tarbe su, daya daga cikinsu ya sauka ya dauki babur din dan kai shi ma.aikata su kuwa suka shiga bin anguwa anguwa sunna kama du wani mai laifi, da wanda ya cika dare kuma bashi da takarda, inda su ne har su plastomo, su rond poind 6em, du wani lungu na yan duniyar da basu da damar zama wajen sai da suka durfafa aka riga tserere da sojojin da masu laifi......
Chaina
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
8️⃣0️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
Tunda Gukunni ya fara bata labarin abubuwan da suka faru ita da jikokinsa wato yayan Anna kuma yayun Agaishat daidai lokacin da aka tafi massage din jikin Anna wace yanzu sosai jikin da sauki , suke dubansa da mamaki,
Dama akoy mutane irin haka?
Anmi, wato mahaifiyar Anna ta ce" wai kana nufin , Wardugugu dai general Wardugu ne ya auri Agaishat din,? Kuma ka ganta da idonka?
Gukunni ya yi murmushi ya ce" a irin halin da na ganta, ko mu iya walwalar da zamu iya bata kennan,
Fatimata ta ce" wai wai wai rayuwa, yanzu Agaishanmu ce ta yi aure har ya rabu har ta kara samun wani da gagawa haka? Ku a birni ba ruwanku da kalar fatar mutun kennan?
Gukunni ya ce" wanninma da ta samu ko a cikin mutanen baban mutun ne, ba kun ga sojan da ya je tare da mahaifiyar tasa ba? Uwar rikon Agaishat din?
Gaishat ta zaro ido ta ce" eh eh, wani irin mutun mai cika waje da ido, tunda aka je da shi bai cika magana ba aman idan ya dago ya yiwa mutun duba daya sai ka nemi kallon me ya yi maka ka kimtsa zamanka,
Gukunni ya saki murmushi ya ce" to ko a ma.aikata haka yake, shi dai ne ya biya sadakin auren Agaishat million Arba.in!
Gaba dayansu sun girgiza, sun ji dadin lamarin kuma sun kara yarda Allahn da ya yi bawa, shi ya san me ya kunshe tatare da shi, Wai Agaishat dai Agaishat, itace haka ya sameta, abun alkhairi da kaf timiya ba.a taba kawowa wata y'a haka ba, kai ko a cikin agadez sai yayan sarke ke samun haka,
Anmi ta ce" damuwana daya, ka ce bai jima da aure ba , kuma matarma batuba ce, fatan dai ya isa da gidansa, yana iya sakawa ko hanawa,
Gukunni ya girgiza kansa kafin ya ce" ban ce ba idan baya nan,
Idan kuwa baya nan ita jikar taki idan ta zauna kishiya ta cin mata ita ta gano,
Maganar idan yana nan da nake maki, ni na ga a idon jarumin ba lale ne ya yarda kuda ya taba fatar jikinta ba,
Zai iya da su!
Ai kuwa Mariama ta mike ta aniya kada harshenta ta rangada budar buzaye, inda Anmi ta yi gagawar tarota tana tina mata asibiti suke fa, kar a zo a yi waje da su,
Mariama kuwa dariya kawai take, ta zauna tana duban yan uwanta ta ce" ban taba sannin inada kaka mai kudi ba, da yan timiya sun gayawa yan garinsu! Ban taba sannin Bakar Anna zata yi kudin aure ba , da na koya mata fito na fito!
Yanzu ko yaya? Ko ta bar rabewar idan an tabata? Ko ta bar lafewa ta dora kanta inda ta samu ta yi hawaye? Ko ta gane Allah kawai zata kaiwa kukanta, du ubanda ya tarota ta taro shi?
Gaishata ta kai hannunta ta buge bakin Mariama kafin ta girgiza kanta ta ce" Allah ya shirye ki, gwarama wannan likitan dake bibiyarki a bashi mu tataraki mu bar masa a nan mu daga abinmu dan har yanzu baki shiryu ba,
Wai wa? Fahad? Baki ga zama cikin yan chaina ba shima tsayinsa da idannuwansa ne kawai basu koma irin nasu ba? Wata shegiyar kunya dazu fa da muka hadu wajen cin abinci kinga yanda yake hade hannu yana gaishe ni?
Fatimata da haushi ya gama tirniketa ta dubi Gukunni dake kallonsu da sha.awa ta ce" Papou, ka yiwa yarinyar nan magana, idan tana abu kamar itace Agaishat karamarmu, wai kawai dan yace da ita yana sonta abinda ta fara ce masa zai iya soyaya da shegiya? Wai ita bata da uba,
Gaba daya suka kai dubansu kanta, inda itama su take kallo,
Kanta ta girgiza kafin ta ce" menene? Karya na yi? Ni fa ban iya karya ba, kuma ganninsa na yi ya hade karshen haduwa, zan cuci kaina ne? Dan Nigeria ne, wai iyayensa suna zaune a abuja, shima nan ya yi karatun likitanci da ya gama ya yi zamansa nan yake kara koyon aiki tare da kwararu likitoci, gani na yi daga haduwa da shi ya bani cikenken ko waye shi, shine nima na bashi nawa asalin ko?
Anmi da suke kira da Mamou, ta girgiza kai kawai ta mike ta bar dakin, ita kam bata ga ta ibda za.a daidaita halayan Mariama ba, irin halayen Gukunni ne da ita, tamkar itace yar batuben, sam bata da dar ko shayi, magaifiyarta kawai take tsoron kallo cikin ido ta fadiwa magana, itama ta ci karfinta ta hanyar shareta da yi mata wa.azin girman darajar iyaye.
Gukunni kam sai da ya dan shafa habarsa yana dubanta kafin ya girgiza kansa shima ya ce" kin kyauta, kuma sai na hada ki da Annarki! (Ba ka ji ba, ba zai ga wani girman laifinta ba, domin shima halayarsa kennan🤣),
A wannan ranar da likita ya zo ya fada masu zasu iya kowani yama su fitar da ita ta dan rawata kadan kadan, sannan a ci gaba da kwontar mata da hankali, a yawaita saka mata abinda zai sakawa ranta dangana, idan musulmai ne su yawaita kusantata da wa.azizika, da astaghfari, su nuna mata girman kadara, su nuna mata ba kowa Allah ke jarabta ba👏🏻,
Idan har ta nutsu nan da satima zasu iya salamarsu...
Ai kuwa sun ji dadi sosai, inda Herde sai a lokacin ta tatara ta koma tare da Fatimata da dan gidan Gaishata wato Sultan wanda take jin yaron har bargonta, shima ya wani shaku da ita du motsinsa yana makale da ita.
Soyaya kuwa ta dinke da Mariama da Fahad, inda ya hadata da familynsa a vidio call suka gaisa da yar hausarta da bata taka kara ta karya ba, dan kuwa french dinma ba wani sosai take ji ba, buzanci ne shi kuwa ba yarensa ba, soyayar dai ana yinta ne karfi da yaji domin wani sa.in sai a rasa ta yanda za.a isar da sakon khalb.
Niger
Da gaske yake, ko nace da gaske suke,
Abu ne ake tamkar ba gobe,
Dukan bukatun Ayya kan lamarin tarewar yarta an cika mata, inda ake shan rigimar shi ba za.a yi wani taron diner ba, kawai a yi saukar alkur.ani, Ayya kuwa tace ai ko walima ne sai ta yi ta gayaci mutanenta an yi taro na kirki itama ta aurar da yarta,
Ido ya kawo ya zuba , yama maida hankalinsa kan aikinsa wanda kulun cikuluftu ke karuwa,
Ayya kam ba kama hannun yaro, wani irin shiri take yiwa yarta wanda siri ne,
Ya kasance ko masu aiki basa gannin Agaishat a dakin da ta kilaceta, daga ita sai ita,
Du a tunanin Ayya y'artata ta saan aure, hakan ya sa take wani irin shiryata dan ko ba komai ta iya zama a gidanta, kar a rainata ta wannan fannin,
Sosai ta bata magannin infection, kafin ta shiga bata lakaninika ciki harda yusufa da kankanna,
Kwata kwata ta haneta shan ruwan sanyi, inda take dumamata da masu dan dumi ,
Haka indai jikinta ya ji iska tofa wanka ta shiga, tana fitowa take maida lulubinta ta lulube, dalilin haka har yan kurajen zafi ta yi, suka mutu dan kansu jikinta ya saba ya kasance koda yaushe cikin dumi yake,
A kulun zai yi zuwa biyu gidan, yakan bi Ayya da kallo ne, tun lokacin da ta masa iyaka da tambayarta Agaishat, ya kawo ido ya zuba mata, wai tana gyarata, har sai da ya ce"Ayya, ni guaran na menene? Me kike gyarawa ne?
Ta yi masa shiru ta kawar da kanta, dan ba za.a ja maganar da ita ba, idan shi bashi da kunya ita kam tana da ita
Shi kuwa daga shi ya yi shiru ya daina tambayarta ita, kuma abinda ke bashi mamaki ko wulginta da baya gani, ya dai san lokaci ta deba, kuma saura kwana uku, hakan ya saka ya kawo ido ya zuba mata,
Yau sauran kwana daya kacal tarewar Agaishat,
Kowa ya dauka kan tarewa ne, dan ta taba aure,
Jama.a da yawa na mamakin wannan aure , General ya auri bazawara? Ayar tambaya, wa.inda suka san matar da amininsa Mu.azam ya saka ce kuwa suna yayata maganar daidai da mandan bakinsu,
Wardugu, bai san irin halin da zai kwatanta yake ciki ba, ga aiki da ya sako shi gaba domin ana yawan kawo hare hare yankin Diffa, tsaye kan kafafunsa , dan haka ya kara neman alfarmar kar a yi maganar diner, gannin halin da ake ciki ya saka Ayya amincewa , aman hakan ba zai hanata yin nata taron ba,
An kawo garar amarya da akwatuna,
Zama zanowa bata lokaci ne, Wardugu ya kashe kudi sosai, kaya kuwa an zuma na yar gata,
Agaishat kan fashewa da kuka wani lokacin , kukan murna, kukan godiya ga Allah, tana jin Ayya har kasan zuciyarta, girman Ayya daban ne, tana sonta so irin na da da uwa,
Saima idan ta zauna tana tuna hirarsu ta yau bayan salar asuba, yau da ya kasance za.a mikata dakinta, gidan mijinta, wanda take fatan sai dai a fitar da gawarta, Ayya ta dubeta ta ce" zan so biyayarki, tsoron Allahnki, ya kasance bayan zuciyarsa da kika shiga, ki shiga kowani motsi nasa,
Agaishat, ban hore ki da rashin kunya ba, ban hore ki da tsayaya ga miji ba,
Agaishat, shin wanda aljanarki take karkashin kafarsa wani irin motsi zaki yi dan gannin ya dage kafar nan tasa ya baki damar shigewa?
Ki yi masa biyaya,
Ki barshi ya fada,
Idan ya daga murya ki kaskantar da kanki,
Kar ki yarda yana fada kina fada Agaishat, da haka gwara ki yi nesa da shi! Ban ce ki zauna ya wulakanta ki ba fa, ko daya, ina dai doraki kan hanyar da zata kai ki ga ci ne,
Kin ga kar ki yarda daga saman salayarki ki sauka da asuba ba tare da kin furta kwali a kwayar idannuwanki ba, ki adana kwalin ki kusa da abin salar ki!
Kar ki haye gadon da kika gyara dominsa kafin shi ya hau (ina kuke ne mutanenmu , iyayen mu🤣, gafa wajen🤣),
Idan ya yo dare, ki kasance mai jiransa , kar ki je ki jibge saman gado, har ya zo ya gama abinda zai yi kina minshari (😅 kin ji ko maniu🤣🤣),
A duk lokacin da kika ga da hali, akoy robar wankin kafa, akoy dutsi, ki zauna a yar kujera ki saka kafarsa ki wanke, ba dan ta yi dati ba, sai dan kara shakuwa tsakaninku koda kuwa bai saba gani ba, kar ki wani damu ke dai ki koya masa irin zamanki da kike so ku yi,
Akoy wahala fa, domin kuwa ba ke ya fara aura ba, ba ke kika fara rainonsa ba, zaki ga abubuwa da yawa wanda haka matarsa ta hore shi da su, wasun zasu canzu cikin hikima da juriya da hakuri, wasun kuwa Agaishat sai dai ki rayu da shi a haka!
Sai maganar kananun kaya,
Ina mamakin zamani, ina mamakin yayi,
Wai idan za.aiwa yarinya aure da budurwar da bazawarar da datijuwar sai ki ga ta kama kwasar kananun kaya , kananun kaya ita dai,
Uhum, kuskure baba,
Ke Agaishat shin sex din ne kawai ya kai ki gidan auren? Tabas shi ne jigo, shi ne farkon gini, aman shi din an gaya maki zama kusan tsirara a kulun ne zai saka shi armashi?
To albishirinki, walahi ni na fada maki, du abinda ya kasance shi kulun a fili a bude yake komai darajarsa a hankali take raguwa har ya kasance ta bace bat!
Shigar kananun kaya, akoy lokaci, ba ina nufin kowani dare ba, no , aa, lala!
Ki sayi masu tsari, masu ma.ana , masu kai,
Masu taushi!
A cikin gidanki Agaishat, ki kasance cikin shiga ta kamala, ki ringa yawan yi masa rowar ganninki gaba dayanki arha,
Agaishat, ki ringa saka riga da zani da dan kwalinki, ki yi sasaukar kwaliyarki sannan ki zauna cikin kanshi,
Ki ringa saka sket da rigarki na atamfa, ki ringa saka doguwar rigarki au ta atamfa ko abayoyinki, ki ringa nada saharinki, ki ringa hawan lesh da shadarki kina zamanki, ke wani lokaci ki yi sasaukan shiri abinki,
Ki ringa daukan lokaci kafin ki yi masa shiri na kananun kayan, ya kasance a ranar yana kusa, ki saka abinki , ki juya a gabansa,..... Agaishat zaki baiwa wani labarin mahinmancin hakan, mijinki zai kasance yana mai jin zumudin riskar ranar da zaki hade masa cikin shirin nan, sannan koda lokacin da zai ziyarce ki ne, zaki ga zai warewa wannan lamari mahinmancin da za yana nuna maki, ( iyayen mu, na zaunar da mu ne, su yi mana huduba, fila fila, shin da wada take yarena ta tabatar? )
Sosai Ayya ta yiwa Agaishat nasiha, gargadi, ta ankarar da ita zaman duniya, dama hasashen na auren da take, kafin ta nanata mata maganar cewa *AGAISHAT* ,tabas kyau, fari, mulki, arziki, na jan soyaya,
Sai dai ki sani *ZUCIYA NA SON MAI KYAUTATA MATA* ,
Wannan kalma kuwa , ta tsaye mata a rai kamar yanda sauran suka tsaye mata,
Haka aka wuni shagulgula kamar ba gobe,
Sosai Ayya ta gayaci mata, mata kuwa sun amsa kira, inda aka wuni ana tafiar da taron yan gayu,
Kai amarya, ba.a tashi shirin amarya bama sai wajen karfe goma na dare,
Ayya ce da kanta ke darwaye yarta, kafin ta mulketa da turaren Angel,
Haka ta zaunar da ita ta saka mata kwali kadai a idannuwanta kafin ta damka mata shi a hannunta,
Wata arniyar Lafaya ce ta nada mata saman lafiyayiyar doguwar rigarta ta atamfa mai ruwan ja da fari kar,
Ba.a saka mata dan kune ko awarwaro ba, takalmin kafarta kansa wani plat ne,
Dirar motoci suke ji , tun suna hasashen za.a dakata abin gaba kawai yake,
Labule Alhinayet dake tsaye cikin shigar wata dakakiyar shada ta daga,
Gaba daya sai da tsigar jikinta ta tashi,
Hasbunalahu wani.imal wakim,
Shi ne abinda ta furta a lokacin da ta hango motoci layi biyu, kowace tana kilyoten yan wutocin gaba, kowace da soja tsaye a kusa da ita,
Sun layu gaba dayansu suna ta tafi ana shakiyanci irin na sojoji a cikin yannayin farin ciki,
Ta tsakiyarsu yake ratsowa a lokacin da Alhinayett ta hango shi ta saki wata buda tana kada harshenta ta shiga kwasar shoki,
Wato wani irin shirya daukan amarya ne aka yi wanda sai wanda ya gani,
Haka Ayya ta kamo hannun Agaishat dake ta hawaye tana jin wani irin lamarin a jikinta wanda bata taba ji ba a aurenta na farko,
Ya Allah, ya Allah,
Ayya na fitowa da ita daga dakin nayake ainayin nata aka shiga guda ana zuba mata kudi,
Ayya ta riketa da kyau suka shiga saukowa daga matatakala inda ta shiga neman aminiyarta dan ta mika Agaishat dakin mijinta,
Tsakiya suka saka Agaishat suna tarairayota,
Alhinayet kam har jikinta rawa yake , domin gaba daya wajen fa ba dama, muryar sojoji ne suna fadin"Hei Hei Hei Hei,
Inda Wardugu ke takowa a kafarsa, jikinsa sanye da kakin soja marroon , wandon da kadan ya zarce kaurinsa sannan ya rike shi daga kasa, rigar kuwa baka ce jikinsa aman bai sakata cikin wandon ba , janta ya yi ya dorata saman yar karamar bindigar dake tsatsonsa, sai ranjes maroon waro takalmin sojoji, rigar mai karamin hannu ce , hakan ya sa damatsunansa du a waje,
Du taku da zai yi sai kura hei tun karfinsu murya irin ta garada, sannan su yi wata yar rawa da kafarsu ta dama baki dayansu a haka har ya karaso wajen yan matatakalar da zai taka ya hau kafin ya shige dakin Ayya , aman sai ya ja ya tsaya,
Daidai nan su Ayya aka bude masu suka fito da amarya,
Gaba daya wajen ya kwashi wani busa na sojoji kafin a karashe da fadin *GENERAL HEI GENERAL HEI*
Tsura masu ido ya yi daga inda yake,
A hankali ya dora kafarsa ta hagu saman abin takawar na fari, kafin ya lankwashe kafar ya kasance gwuiwar kafar tasa ta hagun a kasa, sannan ya matso da ta damar saman na gaban ya dorata, ya yi irin taugunon nan da maza suke yi dan tambayar hannun budurwarsu (kasar larabawa da turawa),
Wani irin ihu wajen ya dauka a lokacin da ya mika hannayensa baki daya kan a bashi, ya zo a bashi...........
To fans saura kiris bilahi😔😔😔😔😔
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
8️⃣1️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
Dakatawa Ayya ta yi, kafin ta dubi tarin jama.ar,
Dubanta ta kai wajen mutanen da suka wunnin mata sannan ta kara duban yan matan dake wajen wato kannen Alhinayett da aka wuni da su,
A hankali ta yafito Alhinayett, ta karaso inda ta yi mata radar du rintsi a sada Agaishat dakinta da ita,
Ai kuwa Alhinayett ta amsa, kafin Ayya ta kama hannayen Alhinayett ta karasa kusa da Wardugu,
Hannunta na dama mai dauke da jan kunshi dan kadan ba mai yawa ba ta dora saman nasa na dama kafin a hankali ta ce" ka riketa mudin ranka War....,
Wardugu ya rike hannun da kyai inda ya kai dubansa da kyau domin jin wani laushi da hannun ya kara kan nasa na da, dubansa ya kai wajen mahaifiyarsa a hankali ya furta" Allah ya tabatar maki da shiga aljannah,
Aminiyarta da Alhinayett da Agaishat kawai suka ji, dan haka suka amsa kowane daga bangarensa, inda ya mike a hankali ya karasa hawa ya matsota jikinsa ,
A fakaice ya duba irin daurin lafayar da akai mata, aa yau sun yi abin kansu, an yi mata daurinnan na saman kirji wanda baya nuna surar mutun, dan haka ya sauke ajiyar zuciya ya sakali hannunta da kyau inda ya zame mata jagora yana takawa a hankali tana bin sahunsa ,
Sojojin gaba daya bindigoginsu suka daga sama kafin daya daga cikinsu da ya fi murya ya ce"REPOS!
Gaba daya suka sauke
A hankali suke takawa, inda Alhinayett ke bayansu, sai yan matan suma suka rufa masu baya , sai iyayen da zasu rakata domin fir Ayya ta ki ta saketa haka kawai,,
Motar da zata kaisu ce ta karaso ta tsakiyar sojojin, nan Wardugu ya bude ya sakata gefen dama kafin ya zagaya ya shige gefen hagu,
Mu.azam,
Shi ne abunfa Wardugu ya fada a lokacin da ya ga Mu.azam ne zai tuka su,
Mu.azam ya tsare shi da ido ta jikin madubin hakan ya sa ya yi shiru ya zauna da kyau yana duban yanda kowa ya je ya shiga mota suka dauki hanya,
Shiru ne ya ratsa motar, inda gabanta ke dukan tara tara, me? Mu.azam? Shi ne zai kaita dakin miji? Lale Mu.azam, kai itafa har yanzu bata san komai ba, kuma bata da niyar sani!
Haka dai ta yi shiru har lokacin da Wayar Wardugu ta dauki tsuwa,
Dagawa ya yi ya kara a kunnensa,
Ai kuwa a dake ya ce" ka gane, abu daya za.a yi da su su dan daidaita halayensu, dangina ne na san meye zuciyarsa, du wanda ya kashe ka saka bakin bindiga ka harbe shi a tsakiyar ido! Du wanda ya jigata wani, ka jigata shi, hakan zai sa su daina fadan da zasu jiwa junansu har a kawo su asibiti,
Ku kennan haka zaku kare? Kulun kuna fama da rabiyar fadan cikin kasa bayan ga wanda ya adabi duniya? Ba so suke su kare ba? Zan kuwa karar da su!
Shiru ya yi kafin ya daga murya ya ce" commandan kana da ja ne?,
Amsa aka bashi kafin ya ce" ohk, ni na ce, a zartar!
Kit ya kashe kiran yana kokarin ajiye wayar sukai ido hudu,
Tsakaninsa da Allah sai da gabansa ya fadi, domin wani irin fayau ta yi masa, ga idannuwanta da yake gannin tamkar an kara masu girma, kawar da kansa ya yi, dan kuwa ya tabara fadansa ya sakata bude lulubinta harma ta tsura masa ido,
Haushin kansa ya ji ya kama shi, ya aka yi bai yi hakuri ba har ya fita a inda take kafin ya dauki kiran?
Wata zuciyar ta ce" kai sai me? Hala tsoronta kake?
Harare ya wurga kafin ya ja tsaki, sai kuma ya kai dubansa wajen Mu.azam ya ga bai kula shi ba, baima dubansa tuki kawai yake,
A yansa ya shiga mita, oh ni ga mahaukaci, ina fada ita ta tsareni da ido, kai kuwa ka mini halin ko.in kula ko? Ni ba mahaukaci bane, kuma ni ba mafadaci bane🙄,
Haka ya tamke fuska har suka karaso gidan, wanda du mutane ke fitowa baki wangale, a gaskiya, an tafka gini na zamani...fatan a mora lafia,
Fitowa ya sake yi ya zagaya ya fito da ita bayan ya ja mata rufarta ya mayar mata yanda yake da,
Hannunta ya ja inda mutane ke kallonsu ya nufi ciki da ita,
Sai da suka shige cikin accenseur ya kara kusancinsa da nata ya ce" kukan bai isa haka ba?
Agaishat ta dan dago ta saci kallonsa, danme yake da fada, wai fa a kashe mutane yace, ita tsoro take a je ta yi wani abu ya harbe banza,
Kuma mamaki take shi ya je ya daukota, dama haka ake a birni ko me? Sannan wai ta bar kuka, yo ita idan bata yi kuka ba me zata yi? Allah ya ceceta da fushinsa.
Kira ne ke ta shigowa dan haka ya rike hannunta ya daga,
Kukan da take rusawa ya saka shi yin dan tsam kafin ya duba number, Walyn ce, dan haka ya mayar a kunnensa ya ce" hm,
Walyn ta ce" kar ka mini haka, na tuba ba zan kara ba, na bi Allah na bi ka, ka rufa mani asiri kar ka kadaice da wata macen bayana,
Wardugu ya girgiza kai a hankali ya ce" dan me?
Walyn ta ce" dan ni kadai kake so, dan ni kadai nake da hurumin ganninka ba......, Wardugu kar ka zubda mutuncina a idon yarinyarnan,
Wardugu ya dan fakaici kallon Agaishat dake biye da shi a hankali, murmushi ya saki ya ce" kai, bazan iya ba, canza wani abin Walyn, yarinyar a shekaru take karama, aman a zahiri ke kanki zaki yarda da baba ce, waima dan ban ga ainahin zahirin ba, da na fayace maki ko dan ki yarda,
Idan ka tabata kashe kaina zan yi, na rantse maka,
Wani wawan tsaki ya ja, kafin ya ce" sai me? Dan kin kashe kanki walahi ba zai hana ni zama da ita ba, ke harma na kara wasu su yi ta min go slow a gabana, ke kuwa kin mutu kafira!
Wardugu.....ta fada murya shake,
Walyn ya fada yana mai ja ya tsaya,
Walyn ta ce" bani da lafia, sai da aka yi min dinki, ka zo ka duba ni ka ji? Wardugu ka zo ka min cikin na rantse ba zan zubar ba,
Kansa kawai ya girgiza ya kashe wayar yana tunanin bata dadara ba, shi kuwa zai yi watsi da ita har zuwa lokacin da zata yi hankali!
Dubansa ya kai wajen Agaishat, gani ya yi ta dan ja rufar ta bude fuskarta, ta yi wani shar da ita,
Da hannunsa ya nuna mata inda zasu yi kafin yake dora hannunsa wajen ya bude,
Shi ya fara shiga kafin ta yi adu.a a ranta ta saka kafarta ta dama,
Waouh shi ne take fada a zuciyarta, masha Allah, a hankali ta taka ta karasa tsakiyar dakin tana bi da kallo,
Ta shagalta da kallon sai da ya kama hannunta ne ta ankara da ita yake jira ,
A hankali ya yi mata jagora dakin baci,
Suna shiga ya ja ya jingina jikin garun dakin yana dubanta,
Kafafuwanta dake dauke da jan lale take takawa cikin nutsuwa , a hankali ta juyo tana dubansa, tsaye ya yi kawai yana kallonta dan haka wata kunya ta darsun mata,
Juyar da kanta ta yi, hakan ya sa bata ga zuwansa ba , sai hannunsa da ta ji kusan fuskarta,
Bayan yatsarsa ta tsakiya ya dora gefen fuskarta tun daga wajen girarta ya shafo har zuwa wajen habarta kafin a hankali ya kai wajen lebenta dake zagaye da dan lips kadan ba dayawa ba yana dan sheki,
Idannuwansa ya lumshe sannan a hankali ya saka hannayen nasa ya janye rufar lafayar,
A hakama an saka mata bakar hula marar ado daga ciki an rufe mata gashinta dake wanke tas ba.ai mata kitso ba, sai gobe!
Hannunsa ya kai wajen kulin da akaiwa lafayar wajen kirjinta, hakan ya sa gabanta dokawa har ta dan daga kanta ta saci kallonsa, sai dai ta ga shi yana yi ne tamkar aikin da zai yi ya gama ne, dan haka ta sada kanta duda ba wani mahalukin namijin da hannunsa ya taba zuwar mata nan, idan ka cire Ayya dake daura mata lafaya ba wanda ya taba samun kusanci haka da ita sai wannan bawan Allah,
Kwoncewa ya yi kafin ya zagaya ta bayanta ya yaye shi ya sake shi nan kasa,
A hankali ya sako hannayensa ta bayan nata ya rungumota jikinsa daga baya ya dora habarsa kan dokin wuyanta,
Muryarsa kasa kasa ya ce" Menene?
Agaishat da jikinta ke rawa rawa ta dan girgiza kai bata iya amsawa ba,
Wardugu ya dan kara goga mata sajen fuskarsa a dokin wuyan nata yana lumshe ido sannan a hankali yana lura da yannayinta yanda du ta firgice da bakon lamarin da bata taba gani ko ji a tare da ita ba, sai ya dauki hakan a wata fasara daban, ganninsa ta saba ne, har ta fara daukan caji... dan haka ya sasauta rikon da ya yi mata ya ja hannunta ya kaita kusan bayin dakin ya nuna mata da hannunsa, sannan ya nuna mata salaya ya juya ya fice,
Wata wawiyar ajiyar zuciya ta sauke kafin take dora hannunta daidai zuciyarta, wai Allahna, shine abinda ta fada....menene wannan? Me yasa idan na ganka nake jin irin wannan faduwar gaba da tsoron ka gusa daga inda nake? Me ya sa ka zama mai zafin taba fatar jikina aman maimakun na hana sai na bige da lafewa a fafadan kirjinka, Sadaukina....bakon mijina, zan kwatanta yi maka biyaya mudin raina, Allah ya bani ikon cin nasara
..
Haka ta shiga bayin da ta so zama yar kauye, du kuwa da irin wajajen gayun da ta rayu,
Da kyar ta samu ta daura alwallah ta fito ta yi sallah,
Ba wani wanka da zata yi, bata zo da wannan rawar kan ba, sannan kafin a kawota sai da Ayyanta ta cika mata ciki dan haka tana gama sallah mikewa ta yi ta nemi wajen kwonciya ta nade saman lalausan lafiyayen bed din da bashi da wani tsayi sosai sai dai fadi,
Bata wani jira gannin ya zo inda take ba, domin kuwa koda Ayya ke mata jawabi ta cika da tambayar kanta daman miji zai tardota inda take ko me? Ita dai a aurenta na fari, bai taba zama saman bed dinta ba, bale a kai ga kwonciya, dan haka bata cire doguwar rigarta ba ta yi kwonciyarta da abinta, (kar ku manta, budurwa take, du wani rawar kai wani a cire kaya a sake wanka , a wani canza kaya sai kace uwar mata ko wata wace ta jima a lamarin , walahi a kiyaye, zaki iya sakawa mijin dar a zuciyarsa, koda kuwa a bazawara ya aureta idan ya tardo cas cas malan ka8 nake jira ba wani aji ba wani dan kunya ina dalili? Dan Allah ku mu dauki al.adunmu na malan bahaushe, amarya amarya ce, ta bari a tardota, kai koda ta san lamarin ta bari ya ja daren farkon nan, aman ba wai daga an tabaki ba kema har kin koya! Yin farin? Zuwan farin? Yan mata yaya dai?🤣🤣🤣🤣😹😹😹😹😹),
Luluba ta yi cikin bargonta dake malale saman bed din, bayan ta yi adu.o.inta cike da kewar ayyanta ta lumshe ido da fatan Allah ya tasheta lafia cike da tunanin ta ina zata ji kiran sallah wannan gida tamkar ma.aikata ko hotel?
Wardugu kam, haka ya je masu shi kadai yana muzurai, domin sun shirya yar karya karya tsakaninsu idan an kawo amarya harda amaryar, sai dai ganninsa suka yi shi daya,
Ba wanda ya takura shi haka suka dan jima ana murnar karin aurwn general kafin suke watsewa , ciki kuwa harda Alhinayett da mijinta da yan uwanta inda suka tafi suna kunshe dariyar lamarin wardugu,
A nitse ya koma bangarensa, lokacin har karfe daya na faman yi, dan haka wanka ya fara nema ya dauro alwallah,
Shafa.i da wuturi ya yi, ya shafa adu.a inda yake jin cikinsa na kuwar yinwa, sannan abin mamaki bata zo inda yake ba, dan kuwa Walyn ita ke tardo shi koda yaushe, shi ba zai irga ranar da ya je mata ba,
Mikewa ya yi ya kai dubansa kan ledar da aka bashi, wai kajin amarci,
Murmushi kawai ya yi ya zauna ya bude,
Bridel ya gani ciki dan haka ya bude da bismillah ya kafa kansa, sai da ya yi kat ya ajiye goran ya rufe ledar ya mike ya zauna bakin bed,
Shiru ya yi yana tunanin me ya hanata zuwa inda yake?
*DAN BAKA ISA BA, BA KAI TAKE SO BA!* tunaninsa ya bashi haka,
A hankali ya dora kafarsa ta dama saman ta hagu yana kadawa, ya yatsina fuskarsa, wani sashe na zuciyarsa ya tunasar da shi.... Wardugu, amanar Ayya? Idan fa tana cikin wani hali? Gata bakuwa a wajen?
Agogon dakin ya kaiwa kallo, karfe biyu kennan, dan haka ya ajiye carbin hannunsa na dannawa ya mike ya fice a dakin nasa ba tare sa ya kashe komai ba nufinsa ya lekota ya dawo abinsa....
A hankali ya shiga, gannin tar dakin da haske ba.a kashe ba ya saka shi dan dudubata,
Hango tudu tudu saman bed ya saka shi gane tana sama baci take, aman ta shige gaba dayanta har kanta cikin bargon,
A hankali ya karasa bayan ya rufe dakin ya karasa har wajen gadon,
Hannunsa ya saka da niyar janye bargon, aman ta nadidiyeshi sosai kamarma bata samun isashen numfashi,
Kansa ya girgiza ya samu ya haye saman bed din da kyau, ya samu gefenta ya bude bargon kadan sannan ya saka hannunsa yana dan tapin din wajen da bai san ko menene ba yana kiram sunnanta a hankali,
Tsai ta yi da sauke lumfashi kafin ta bude idonta cike da nanauyan baci,
Shiru ta yi cike da tsoron meye? Waye? Wayo Allahna Ayya!
Ta fada can kasan makoshi kafin ta shiga neman wajen da zata yaye bargon jikinta sai bari yake,
Taimaka mata ya yo ta yaye bargon , inda gaba daya ta ruruko idannuwanta cike da tsoro take dubansa bayan ta dubi agogon bangon dakin fari kal mai adon dawissu fari kalkal da shi, ta ce" me me lafia? Me aka yi?
Wani kallo na kin raina min wayo ko? Ya yi mata kafin ya bi yanda gaba daya jikinta ke bari,
Da yatsarsa ya nunata ya ce" ke meye jikin ki ke rawa haka?
Agaishat ta hade hannayenta dan ta samu karfi karfi a jikinta, ta dube shi da kyau ta ganshi dare dare saman bed din da take tunanin nata ne na cikin dakinta ta ce" to aman me ka zo yi dakina karfe biyu na dare? Ko dai nan dakinka ne na kwonta har na yi baci?
Kan Uba, ido kawai ya zaro yana dubanta, a tunaninsa, salo ne irin na mata zatai masa na rainin wayo, lalalallala shi? Me ya zo yi inda take? Me yasa take son yi masa abinda zai iya mangareta ko ya dauke mata jinta ta hanyar wanka mata mari ne wai? Ko dan ta san baya son kai hannunsa jikinta ne?
Kafafuwansa ya tankwashe yana dubanta ya ce" zo,
Inda ya nuna mata ta kala, kusa da shi, koma tace gabansa, wai ta je?
Ido ta kikifta tana dubansa ta kasa motsawa daga inda take,
Kansa ya juyar yana tunani, wato shi bai isa ba ko? Bai kai wajen da zata zo gareshi ba ? Aman waninsa har yanai masa ikirarin ni.imarta?
Juyo da dubansa ya yi kanta, ransa ya fara baci ya mika hannunsa ya janyota jikinsa inda ta zo gaba dayanta luu ta shige jikinsa,
A ransa fadi yake kamar mage, aman a fili a hankali ya saka hannunsa ya dan dagota daga kwonciyar da ta yi jikinsa,
Fuskarta ya tsurawa ido yanda ta lumshe ido, a hankali ya kai dubansa kan lebunanta, duda ta yi baci man leben nan, bata side shi ba,
Yana kallon leben yana kara kusancin fuskarsa da tata, har ya hade lebensa da nata,.....
Lokaci guda ta bude idannuwanta tana zaro su,
Janye kanta ta so yi domin har ta yi nasarar raba lebenta da nasa dan kuwa dama ba wani harshensa ya zira bakinta ba, gannin tana neman daukaka rainin hankalinta a kansa ya saka shi rikota ya rike kanta da karfin da ba zata iya koda juyar da kan bane....
Ya yi haka ne dan ya horar da bakinta da fada masa magana gatsal, domin shi a ganninsa tana nan fitina da shi ne,
Sai dai ina , a hankali ya shiga sarafa yannayin kissing din, daga zafi zafi zuwa slowly,
A hankali ya sasauta rikon karfin da ya yi mata, sannan itama jikinta ya mutu ido kawai take zarowa cike da tsoro da mamakin bakinsa cikin nata? Wayo Allah, bata kara firgicewa ba sai da ta ga ya kai hannunsa bayan rigarta ya ja zif din rigar cikin wani yannayin da ba zata fadi lokacin da ya kai nan ba
,idannuwanta ta bude ta zuba cikin nasa kafin ta shiga mutsu mutsu da bakinta da ya mayar tamkar alewa a nasa tana fadin"umumumumumum sannan tana dan girgiza kanta da dan karfin da ya rage mata,
Aman me, gaba dayama sai ya kwontar da ita saman bed din ya yi mata runfa,
Bai tashi idasa rikice mata ba ya kasance idannuwansa sun rufe ba sai da ya ji bayin Allahn nan biyu tawaye fiye da yanda yake hasashe,
A hankali ya zare bakinsa daga nata ya bude idannuwansa da suka canza kala wa.inda ta yi dan daman bata hada ido da shi ba a wannan lokacin ya shiga yin kasa da kansa har wajen da bata tsamani............a takaice, a wannan rana, wajen karfe uku na dare, Wardugu ya yiwa Agaishat wani irin zuwa,
Ya salam bai yi haka dan ya cutar da ita ba, sai irin yanda ya kasa tsayar da kansa,
Wayo Wayo Wayo Allahna.... shi ne abinda ya yawaita fada , haka bayan ya samu nutsuwa zama ya yi ya dafe kansa ya tsurawa yannayin da ya kaita ido, cike da tausayawa, da wani matsanancin kaunarta ya koma gefenta ya rungumeta a jikinsa yana mai fadin.......
Ku yi hakuri, ba zan iya fayace wani lamari ba, 😔😔😔😔 bana iyawa😭
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
8️⃣2️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
A hankali yake shafa gashin kanta bayan ya dan luluba mata bargo har wajen kirjinta yana dubanta cike da tausaya ya ce" ki yi hakuri, kin ji? Ban, ban san baki taba ba,
Shiru ya yi yana mai jin yanda yake jin haushin kansa , a hankali take lumshe idannuwanta har wani wahalalen barci ya yi nasarar yin gaba da ita,
Ya dan jima zaune nan kafin ya mike ya je ya tsarkake kansa,
Yana fitowa zaman ya ci gaba da yi yana dana waya,
Dogon rubutu ya yi ya tura kafin ya kashe wayar ya juyo da dubansa wajenta,
Ta yi lamo baiwar Allah har abin tausayi,
Idannuwansa ya lumshe a karo na ba adadi kafin ya kai dubansa wajen agogo, har karfe uku ta gota, dan haka ya haye saman bed din , aman bai shiga bargon nata ba ya dai kwonta gefenta yana facing dinta ya tsare fuskarta da ido,
A ransa ya furta" ko tana baci kyau take, gashin idonta tamkar ta kara masu na kanti, lebunanta sun yi jajir bayin Allah,
Hannunsa ya kai wajen kansa kafin ya saki murmushi,
Ya aka yi haka? Tamkar ya kuna ruwa🙈, komai ya ji zanzan,
Abinda ya kara birgeshi da ita irin yanda ta nuna juriya baiwar Allah, kallonsa kawai take da abin ya ci tura, irin kallon nan na ka ji kaina,
Ya yi mamakin da bata aniya kwana tanai masa kuka ba, abinda har yanzu Walyn indai zai yi mata kwatankwacin zuwan nan to fa ba wanda zai rintsa haka zasu kwana yana jinya ita kuwa tana bali tana botsarewa,
Murmushi ya yi ya girgiza kai tuna a halin da ya tsalaketa ya yi tafiarsa, Allah ya shiryeta shi ne adu.ar da ya yi mata kafin ya kara juyar da kansa wajen windows,
Baya jin baci, baya jin farin cikin da yake ciki zai barshi ya iya rintsawa, so yake ya ga farkawarta a kan idannuwansa , so yake ya ga budewar idannuwanta a cikin nasa,
Du wani motsinta yana hankalilce, inda take baci tamkar jariri tana sauke ajiyar zuciya a kai a kai,
Idan ya tuna wasu abubuwan sai ya ji dariya ta zo masa, yana mai jin matsanancin farin cikin zamanta halalinsa, yana mai jin wani irin girma da darajarta, sai ma idan ya tuna irin firgicewar da ta yi a lokacin da ta ga abinda bata taba gani ba, inda ta nuna masa jikinta na bari dan kuwa cikin mayen inda ya kaita idannuwanta suka bude,
Kansa ya girgiza yana mai jin farin ciki, idannuwanta basu kiririce ba, bata yi kale kalen yan matan zamani ba, shi ya koya mata shi ya nuna mata,
Kiran salar fari ya doki kunnenta, a hankali ta shiga kokarin motsawa sai dai zafin azabar da ta ji a jikinta ya sakata dakatawa,
A hankali ta karanta adu.ar tashi daga baci kafin ta shiga bude idannuwanta inda take jin jikinta da cikinta tamkar an yi mata sata, sannan take jinta fayau da ita,
Tsuru idannuwanta suka shiga cikin nasa, a hankali tamkar ana tariyo mata abubuwa suka shiga dawo mata ,
Da sauri ta rintse idannuwanta sannan jikinta ya dauki bari,
Bakinta na rawa ta ce" dan Allah na tuba, kar ka min wannan abin , walahi da zafi, ba zan iya ba,
Wani sabon tausayinta ne ya ji ya darsun masa,
Mikewa ya yi ya zauna yana dubanta kafin ya mika hannunsa a hankali ya tayar da ita zaune,
Taki su hada ido, sam sai kawar da kai take tana neman inda zata saka kanta, dan haka a nitse ya ce" ba zan maki komai ba Orronur, zan taimaka maki ne ko zaki ji dadin jikin ki ,
Agaishat ta girgiza kanta a hankali ta ce" zan iya dan Allah ka bari zan iya,
Wardugu ya lumshe idannuwansa, da ya sani kawai yake yi,
Mikewa ya yi ya kare mata kallo kafin ya nade hannun rigarsa a hankali ya yaye bargon da ta ruko ido take rikewa kar ya cire mata, aman ya janye shi baki daya daga jikinta ya duka ya dauketa a yanda ta dukunkune jijinta ta nufi bayi da ita,
Yannayin yanda yake bata kulawa ta isa ta nuna irin yanda yake jinta a ransa,
Da doguwar jalabiyar jikinsa ya samu ya sakata cikin ruwa masu dumi sosai, yana yi yana gyara mata gashin kanta inda ita kuwa kanta ke kasa kamar ta je gaishe da sarki,
Sai da ya gamsu da yannayin yanda fuskarya ke nunawa du idan ya canza mata ruwa kafin a hankali ya ce" kin iya wankan tsarki?
Da sauri ta dago ta yi masa duban da bata shirya ba, irin kallon mamaki mai hade da dan hararen nan, sannan ta dan kada kanta sai kuma ta sada kanta,
Murmushi ya yi ya lakaci hancinta ya darwaye kafafuwansa da hannayensa ya juya ya fice
Bayan fitarsa kam Agaishat kanta ta sada ta shiga tunanin rayuwa,
Wannan shi ne auren, wannan shi ne zaman? Ya rab lale in ba aure ba, me zai hada shinfidarta da ta Wardugu? Ta isa ta kai nan? Ta tabata koda bariki yake take astaghfrullah ba zai dubeta ba,
Aman sai gashi darajar aure ya saka sun taka wani mataki mai girma na duniya,
Bata tunanin a halita a yanzu akoy wanda ya san sirinta irinsa, lale shi din sirinta ne!
A hankali ta kara gasa kanta ta hanyar kara shiga wani ruwan zafin , domin ta lura tunda ya sakata cikin ruwa ta ringa jin jikinta na yin sauki sauki,
Haka ta gama ta tsaftace jikinta ta dubi bayin ba komai ciki, ko tawul.ita bata gani ba dan bata ga inda aka adana su ba,
Dan haka ta kama tsayuwa cikin bayin kankame da jikinta tana mai jin lamarin wani iri, bata saba haka ba ita!
Burum ya shigo hakan ya sa ta kwala dan kara ta juya da niyar boye jikinta,
Murmushi ya yi ya karasa ya bude wajen madubin dake zagaye da bayin ya ciro farin tawul kal baba sosai ya kawo ya rufa mata sannan ya ciro irinsa dan madaidaici ya dora mata saman kanta,
Hannunta ya ja suka fito, nan ya nuna mata wajen kayanta da kuma darduma,
Da hannunsa ya nuna mata zai je masalaci...
Kanta ta daga masa kawai kafin ya juya ya fice a dakin,
Wajen kayan ta karasa cikin nutsuwa ta bude ,
Doguwar riga ja mai duhu ta dauko ta saka kafin ta saka pant ,
Hijab dinta ta zara ta karasa saman salaya,
Cikin nutsuwa ta gabatar da sallarta kafin ta dukufa azkhar ,
Kyar take zaune tana ta adu.a, ba komai take roko ba sai fatan cikawa da duniya lafia, ta yiwa iyayenta adu.a da uwar rikonta, ta roki Allah da ya basu zaman lafia da mijinta ya kade du wata fitina ya sa ya sota fisabililahi👏🏻,
ba ita ta tashi ba sai da ta hangi hasken rana sannan ta hakura ta shafa fatiha,
Kwali ta sakawa idannuwanta sannan ta mike a hankali ta nufi wajen turarukanta ta yiwa jikinta badede (😅🤣),
Gadon take kallo, yanda du ya fita hayacinsa,
A hankali ta yaye rufar gadon ta kai bayi ta ajiye wajen da idan ya zo zata tambaye shi yanda ake anfani da mashine din wanki,
Wata ta ciro ta shinfida ta bi dakin da kallo,
Kwarai zata so gyare gyare , sai dai zata bari ta ji karfin jikinta sosai, dan haka sai ta haye gadon ta nade abinta.
Ayya na saukowa da sasafe , domin kuwa karfe takwas ce, dirar motoci ya sauko da ita, inda ta hango Alhinayett daga sama, hakan ya daga mata hankali ya sakata saukowa da mugun sauri,
Alhinayett dake jagorar mutanen da suka kawo kyautar Agaishat, bisa kiran mijinta da Wardugu ya yi ya roki alfarmar hakan, dan kuwa shi bashida wata aminiya fa, kuma wannan lamari ya zama dole, du buzuwar da ta kai.mutuncinta dakin miji, mijin ma yin irin kokarin da yake da hali, dan haka ne Wardugu ya tayar da ita da jama.ar da ta gayata aka yiwa Ayya dirar bazata, bisa lamarin da ya sakata yin zuru tana bin su da kallo,
A sanninta ana irin wannan kyautar ne idan yarinya ta kai mutuncinta,
Me hakan ke nufi?
An kawo dankareriyar sarkar zinari, da ky din mota da ambulop din kudi kato wanda ba.a kifaya ko nawa bane ita kuwa bata tsaya dubawa ba, sai rakumi amale jibgege da ake janye da shi da Sa fari kal da sakon cewa a yankawa amarya a yi mata soye ta ci ( ku je ku yi tambaya, tabas haka al.adunmu suke, ana yiwa wace ta kai mutuncinta kyauta ta bajinta da abin yanka a yankawa amarya ta ci, dan dai rawar na zuwa daidai da kidan ne, wato barikinka aljihunka....iya kudinka, iya shagalinka)
Wayarta dake saman kujera ta rarumo ta shiga kiran numbersa,
Dama ya san a rina, cikin yan kaiwa kuwa harda khadija da ya nema da kansa,
Ayya sai da ta yi masa kira uku kafin ya datse ya biyo bayan kiran nata,
Gaisheta ya yi kafin ya yi shiru,
Ayya ta ce" am, Wardugu sai naga sako,
Wardugu ya amsa Ayya a takaice yana mai kunshe dariyarsa inda ya ce" eh,
Ayya ta dubi wayar ta mayar a kunnenta ta ce" sakon kuwa masha Allah, an gode , Allah ya saka da alkhairi,
Wardugu ya kara gimtse dariyarsa ya ce" amen, amen,
Ayya ta dane zuciyarta dai ta ce" harda su amale kai aman kosashe ne,
Wardugu ya ce" eh haka fa,
Ayya ta mike tsaye ta ce" Wardugu dan ubanka ina y'ata? Tana ina? Walahi maza maza a kawo min yarinya a yi mata kitso da kunshi a gabana, lahauli, Wardugu bana jin motsinta, tana ina me ka yi mata?
Ai kuwa wardugu ya saki murmushi kafin ya ce" haba yanzu na gane Ayyana, meye za.ana bin wani layi da ni kuma? Lafiarta kalau,
Ayya ta ce" aman wannan kyautar ai da manufarta ko? Gashi yaran da suka kawo ni basu ce min komai ba, ta yaya hakan zai faru?
Wardugu ya girgiza kai yana murmushi kafin ya ce" eh manufar dai da kike tunani Ayyana haka ne.
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ai Ayya ita ta datse kiran dan walahi kunya ce ta kamata, sintiri take tana zancen zuci, ba mai hanata wankawa Agaishat mari kan shiru da ta yi mata ta yi ta shiryata tamkar wace ta san hanyar,
Ba mai rabata da Wardugu idan ya jiwa yar amanarta ,
Zama ta yi tana duban Alhinayett da ta rage, domin ta salami sauran mutanen, ta ce" kin san ai ba.ai mata kitso ma sai yau ko Alhi?
Alhinayett ta amsa Ayya tana dubanta, kafin Ayya ta ci gaba da fadin" to bara ki ji, zuwa zaki yi ki dauki Melina daga saloon mun gama magana da ita ki kaita gidan Agaishat, idan kin je ki yi min vidio call na ganta, idan wani abu bai gamshe ni ba, zaku ganni a kanku, kun jima baku ce na dauko y'ata ba!
Ai kuwa Alhinayett ta maida hankali, domin yannayin Ayya ba wasa,
Ita kanta sai da ta je ta gane ba kyautar tarin kauna bane ya yi kata, kyautar cika al.adunmu ne, kuma ya yi haka dan a san da eh ruf ta je,
Sosai ta tausaya mata, ita da kanta kunyarsa ta ringa ji dan a gabanta ya tsare Agaishat da abinci sai da ta ci ya shirya ya fice aiki bayan ya jadada a bar waya a kusa, inda ya wuni yana aikin kira ya ji ya take, me take,
Daga nan ma wajen Ayya ya fice inda suka sha daru, ta dage tana fada, aman ta ki fadin asalin fadan, ita dai fadi take du wanda ya takura yarinyarta zata je ta daukota ne!.....
Kwonci tashi, zaman Wardugu da Agaishat zama ne na amana,
A hankali take binsa, shima a hankalin yake binta,
Ya kusanta kansa da ita, ya mayar da ita abokiyarsa, ya saka shakuwa ta kirki tsakaninsu, inda ta sakankance take afkawa cikin kogin soyayarsa aman har yau ba wanda ya fadawa dan uwansa kalmar so.
Sau daya ta yi masa maganar Walyn, maimakun ya fahimceta sai cewa ya yi" Walyn dai matata ce, kika san ko idan na fita daga inda kike wajenta nake tarewa? Ba ruwanki da rashin raba kwanakin ku, ko so kike ki nuna min na isheki dan bakya so na?
Shiru ta yi ta shiga goge masa zufar motsa jikin da ya yi, inda ta mika masa tea mai zafi ta shiga tatare wajen,
Kamar yau, ya kama wajen sati uku da aurensu, kuma har yau ya ki ya bata wayarta da ta gane tana hannunsa,
Zaune yake yana kallon France 24, ana ta hasko labarun duniya,
A nitse ta zauna kujerar dake facing din inda yake zaune,
Kallon yake aman yana cirewa yana dubanta, sai kuma ya maida dubansa kan tvn,
Kafarta take dan karkadawa a hankali, ta hade cikin doguwar atamfa, rabonta da wardugu ya kai mata hari tun na daren farkonsu,
Ya kasance komai dare idan ta yi baci zai janye ya kwana daban daban da ita, ta sha kama shi yana dibgar lemun tsami, ta sani, ta sha azaba ya ba gobe, qman kuma ta fara shiga damuwa, ta dai san mijinta namiji ne lafiyaye, kuma ta san ba ita daya ne da shi ba, idan wajen matarsa yake zuwa ita hoto ce? Aa fa, ba zata so ta zama hoto a fadar Wardugu ba,
Zaman kafar ta canza tana kadawa, dan haka a hankalce ya ce" menene?
Agaishat ta zumburo bakinta ta ce" wai me sunana ne?
Wardugu ya tsura mata ido, a ransa ya ayanna yau kuma fitina take ji,
Murmushi ya yi ya tashi ya koma kusa da ita ya zauna, habarsa ya dafe yana duban kwayar idannunta,
A hankali ya ce sunnanki...Orronur,
Agaishat ta zumburo bakinta ta dube shi da kyau ta ce" menene ma.anar Orronur,
Tsareta ya yi da ido, zai bata amsa kira ya shigo wayarsa dan haka ya daga yana dubanta,
Walyn...ya fadi sunnan a sanyaye,
Walyn ta amsa shi da Wardugu, dan Allah ka lamuncen ganninka, ka bani damar ganninka, na tuba, ka tuna fa, hakina dake kanka idan har ka tauye min Allah ba zai barka ba, ba sakar min kudi bane kawai hakina dake kanka,
Wardugu ya lumshe idannuwansa kafin ya bude yana kallon yannayin Agaishat ya ce" kina ina ne?
Walyn ta amsa shi da tana gidansu na da,
Wardugu ya saki murmushi a zuciyarsa dan kuwa zai so ya ga yannayin da Agaishat zata nuna, dan haka ya ce" ki shirya min tarba, zan so shinfidarki ta yi kamshi, gani nan zuwa,
Kamar an doka mata ice a kanta ta ji, a zaunen da take ta lumshe idannuwanta tana kiran sunnan Allah, domin kuwa juwa ce take ji daga zaune,
Bata tashi jin kamar an gaura mata mari ba sai da ya mana mata kiss, ya mike yana gyara belt din wandonsa ya yi mata wani murmushin shegantaka sannan ya juya ba tare da ya ce da ita zai fita ba , ko zai je wani gurin ba, ya fice a gidan inda ta gane haka ta tvn bangon dake nuna mai shigowa ko mai fita daga gidan dan ba.a jin dirar motoci in dai dakunnan a rufe,
A hankali ta silale saman kujerar ta rushe da kuka dan zuciyarta take ji zata balo kirjinta ta fito,
Dan me ba zan zama mace mai inci irin na kowa ba?
Zaman kwana ashirin da daya da na yi da kai, zaka yi min wasa tamkar wata baby, na san bana yawan neman zama inda kake ba suturar kirki a jikina, aman irin idan ta kama ka shigo na fito a wanka zaka yi gagawar juyawa ka bara min dakin, wari nake? Ko kaima kana kyamar *BAK'A CE?*, ni na san kana zaune da ni ne dan girman kaunar da kake yiwa mahaifiyarka, aman kuma kaunar ba zata sa ka nunan nima mace bace? Ko na zurmi da yawa ta hanyar bin nasihohi ta hanyar kyautata maka? Na san matarka ce, ta fi ni fada a wajenka, aman idan ka yi niyar raba mana kwana ne ka hada mu mana ka yi kamar yanda kowace mace ke samu? Ba ko salama ko? Ni ko? Ba komai Wardugu, nima zan kama kaina, na farka daga yaudarar kaina da nake cewar so ne, aa *Kyautatawa ce*,
Nima zan kyautata maka!
Wardugu kam na fita sai da ya gama shawaginsa a gari kafin ya je gidan,
A bangarensa ya sameta, an gyagyara dakin ba laifi, sannan dai cikin shigarta ta kananun kaya,
Ga mamakinsa bai yi wani zumudin shigarta ba kamar kulun, saima zama da ya yi yana son kwadaitawa kansa ita dan fita haki, da kuma samun nutsuwar kansa, dan ba karamin takure yake ba dagawa Agaishat kafa da yake, yana matukar tausaya mata , yana so ta karasa yarda da shi, ta idasa sakewa da shi, kafin a hankali ya kara dirmiyar da ita ruwa ta hanyar da ya dace, so yake ta fada soyayarsa komai kankantarta, yana so ta so shi koda da wasa ne, shi dai ya samu soyayarta kamar yanda yake ciki,
Sai dai yarinyar ya lura tana zaune da shi ne kawai dan biyaya, domin sha nawa zai samu kiran yan mata a gabanta, maimakun ta nuna bacin ranta irin na Walyn, saima ta shiga sabgar gabanta, kennan dai bata son sa bale ra yi kishinsa ko? Dan me? Dan me jarabawarsa ta diro ta nan? Ya Allah......
Walyn dake zaune kanta kasa tana share hawaye cike da tsoronsa, kar ta yi abinda za.a maimaita wanda aka yi kafin ya bar gidan ta budi bakinta na rawa ta ce" War.....
Hararar da ya watsa mata ne ya saka ta hadiye sauran maganar,
A hankali ta taso ta dawo kusa da shi tana duban yannayinsa ta ce" .......
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
8️⃣3️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
Ta ce" Wardugu, har ka manta da ni? Tun ba.a je ko.ina ba har ka manta da ni? Wardugu ni ce fa matarka, uwar gidanka, danme maza bakwa yiwa kanku adalci bale ku yiwa wani? Wardugu saboda wata can bakar mace zaka yarda ni? Dan an cusa maka mace an baka shi ne ni zaka yi watsi da ni?
Wardugu ya dade kansa da hannayensa bibiyu kafin ya dago da dubansa,
A hankali ya ce" me yasa ba zaki yiwa kanki adalci ba? Waye bai san irin yanda nake daga maki kafa ba? Walyn, kawai dan na yi aure sai karin tijara? Walyn yaushe iyayena zasu yi daraja a idannuwanki? A lokacin da na je wajenki na kasance mai matsanancin girmama iyayenki, a sanu kika koya mani halayen tafka rashin kunya a gabansu,
Walyn nima fa mutun ne, ina so na ga canji a rayuwana,
Mahaifiyata da kika gani, ta fi min kowani halita a nan gidan duniya, da kina da hankali, kina da wayo, koda kin tsaneta ne sai ki boye tsanar nan ki kyautata mata,
Aman ina, a gaban idona sha nawa zaki bita da wani kallo idan ta bada baya? Ina sane, ina gani , ina lure, kawar da kai ne nake dan a zauna lafia!
Da ace rashin hankalin ki iya ni kika tsaya, da zan ci gaba da jan kwababiyar rayuwar nan,
Aman walyn bayan ni, kika tsalake kika haura iyayena, sannan kika tashi kika je kika cire kwaina? Mahaukaci ne ni da ba zaki hada zuri.a da ni ba? Meye aibuna? Me na rage ki da shi?
Walyn dake sauraronsa sosai zuciyarta ke kuna, au fadama zai dora daga inda ya tsaya kennan? Du irin yanda ta zubar da ajinta take son su fuskanci juna shi ne zai rufeta da fada? Mahaifiyarsa, mahaifiyarsa,
Walyn ta dube shi, walahi ita tsoron haukansa take da ta fadi magana, dan haka ta ce" aman ai ba.a kyauta min ba ko?
Wardugu ya kausasa murya ya ce" waye bai kyauta makin ba?
Walyn ta so tace Ayya, aman gannin yana cikin yan maganan, kar ta kwabe komai ya sa ta ce" kai mana, ka kyauta min ne?
Da na yi me?,
Walyn ta kifta ido tana du dubansa ta ce" da ka yi aure kafin lokacin ka yin ya yi, da ka yi aure baka sanar mon ba kafin ka yi, da ka auri wannan yar yarinyar har ka juya min baya tsayin sati uku, da ka dauketa ka kaita gidanka na aeroport ni ka barni a nan ana ci min amana,
Wardugu ya sakar mata murmushi, ya kawar da kansa, can ya ce" adinina bai zo min da salon al.adata ba, dan na yi ban yi sabo ba,
Sannan da na yi ban sanar maki ba uwata ce ke? Nan ana daura aurena ban je na ga kowa ba sai ke, aman kika take ni!
Dubanta ya yi cikin ido ya ce" Agaishat kuwa, Wollah sonta nake!
Kyam ta yi tana dubansa,
Kanta ta kawar ta ce" ba zaka huce ba kennan?
Mikewa ya yi ya dauki ky dinsa ya juya da niyar tafiarsa,
Da sauri ta mike ta ce" Wardugu tafia zaka yi?
Juyowa ya yo yana dubanta kafin ya tako zuwa inda take tsaye ya dubeta da kyau ya ce" ban tsara saki wa mace ba, da na jima da rabuwa da ke bisa rashin hankalin da kike tafka min na yau da kulun Walyn,
Ban waiwaye ki yau ba dan isarki, kyanki, ko farin ki kamar yanda kike takama sai dan tsoron Allah da tunanin ko kin nutsu ne ?
Baki nutsu ba, har yanzu baki sauka daga inda kika hau ba,
Allah kawai nake tsoro, ina jin tsoron haduwata da shi da laifin wani a kaina, idan kika cire wannan, ki je du abinda zaki yi ki yi!
Yana gama fadar haka ya juya ya fice tana kugin kiran sunnansa ya yi mata banza,
Tsaki ta ja kafin ta wurgawa hanyar da ya bi harara ta yi kwafa ta ce" in dai rawar kan amarci ne, zaka yi ka kare, ba wani ka waiwaye ni dan wani abin face kana so na, ba zaka iya ba sai da ni! Wannan bakar ba zata girgiza ni ba!
Barci Agaishat take saman kujera a takure, da alama tsoro take ita daya,
Haka ya shigo dakin ya kai dubansa inda take,
Bai tasheta ba, bai yi mata magana ba ya fice ciki ya duba wajen abinci ya ga bata ci ba,
Bai tasheta ba ya fito ya nufi bangarensa ya kwonta domin ransa a bace yake, indai zai tasheta ne dalilin bata ci abinci ta kwonta ba yana iya bata mata rai,
Kamar yanda ta saba kiraye kirayen sallah suka farkar da ita, da kyar ta iya mikewa domin kwoncib da ta yi du jikinta ya yi tsami,
Dakinta ta zarce ta je ta kimtsa dan yin sallah,
Koda ta gama sallah zama ta yi ta tsurawa waje guda ido, zuciyarta ke mata fada, ba na komai ba sai na ta yi sabko, ya zata damu haka da son ganninsa bayan ta san ba ita daya gareshi ba?
Ita fa zuwa ta yi ta tarar da wata, idan ta tsiri damuwa da jinsa a kusa bata so kanta da yawa ba kuwa?
To aman ai sai ya min bankwana ko? Wayar da ya yi ita kawai ta shaidan inda zai je, daga shi bai ce min komai ba,
To meye dan wannan a halayan wardugu? Ke dai ki kiyaye,
Wata zuciyar ta bata amsa,
Dan haka a hankali ta mike ta ninke salayar, yau kam sai ta ga masu gyara gidan nan, a kulun kafin ta fito daga sallah an yi komai an gama, har kulun mamaki take, danma ita ke shiga kicin abinta, aman tana kyautata zaton da masu aiki a gidan, dan kuwa har yanzu tunda ta shigo bangaren nan nata kafarta bata fita ba, du sati Ayya ke turo mai kitso ta zo ko ta yi mata kitso ko ta mata gyaran kai, kunshin kafarta da hannayenta kuwa da sun fita ake dora wasu domin wannan lanlan ne na zamani mai saurin fita,
Labule ta dage ta leka sosai,
Ai kuwa sai shige da fice suke kowa da abubuwan aikinsa, hakan ya tabatar mata da har cikin ma da masu gyarawar kennan, ita dai abinda take yi da kanta saka turaran wuta, wanda take yin garwashin a kicin ta saka da toka mai zafi ta saka dan turaranta ya game dakunan da kamshi,
Murmushi ta yi ta je ta salo wankanta,
Tana gama shiryawa cikin doguwar atamparta an yi mata dinki simple, sai hannayen ne kawai akaiwa ado , ta daura dan kwalin atampar ta tsaya gaban madubi tana kallo,
A hankali ta sauke ajiyar zuciya a fili ta ce" Ba sofona, ina yawan mafarkinka, Allah ya sa lafiarka kalau ka ji? Zan so ka ganni Ba, tabas maganarka haka ne, birni ga girma ga abubuwan girma, birni mai dauke da wardugu da Ayya da kuma Walyn,
Birni mai mota mai jirgi,
Birni mai kalolin fata ba biyu kawai ba,
Sai da ta gama kalon kanta kafin ta yafa mayafi saman shigarta ta fito a hankali ta nufi wajen abin turaran wutarta ta dauka ta nufi kicin,
Sai da ta hada shayi ta zuba a dan cofi ta dauko biredi mai beurre sannan ta kuna garwashin ta hado turaran wutar ta fito da su a hannunta ta dorashi wajen da yake gana dakin sannan ta je saman cafet ta zauna ta yaye mayafin ta ajiye ta zauna ta fara karyawa,
Tana tsaka da ci ta ji kanshin turaransa hakan ya sa ta yi dan tsai kafin ta dago da dubanta,
Cikin shirin zuwa aiki yake, yannayin fuskarsa ba fara.a hakan ya sa ya shaida mata da ransa a bace yake,
A hankali ta kawar da dubanta daga fuskar tasa ta ajiye kofin glass dun dake hannunta ta mike daga zaman da ta yi tana goge hannunta da tissu duda ba abinda ya yi, ta kai dubanta wajensa,
Tsaye yake kikam yana dubanta,
A hankali ta mike ta karasa dan kusa da shi kadan kafin ta duka ta gaishe shi,
Mutanen kam a kusa suke yau, domin gaisuwarma da kai aka amsa mata, dan haka ta mike da niyar shiga kicin ta hado masa abin karyawa kafin ya fita,
Hannunta ya riko da hannunsa na dama ya dawo da ita gabansa,
Hannayenta ya kamo baki daya ya kai wajen botiran rigarsa dake bude ba.a bala ba,
A hankali ta shiga bala masa tana duban kasa ,
Sai da ta bala masa har daidai wanda yake tsayarwa sannan ya zauna saman kujera ,
Cikin nutsuwa ta juya ta shiga daki ta dauko kumb,
Dawowa ta yi ta caje masa sumar kansa da kyau ta juya ta mayar ta dawo da niyar shiga kicin din dai,
Rikota ya yi , ya juyo da ita suna kallon juna,
Kansa ya girgiza mata a hankali sannan ya mike ya dauki ky dinsa ya juyo ya mika mata wata dankareriyar samsung bai mata bayanin komai ba ya fice a gidan,
Ta jima tsaye cikin yannayin damuwa, me ke damunsa? Me ya bata masa rai haka?
A hankali ta zauna bakin kujera tana duban hanyar da ya bi ya fita,
Ya Allah, shi ne abinda ta fada a fili, azumi yake ko kuwa cin abincin ne ba zai yi ba? Yaushe ya shigo gidan ma ni ban ji ba?
Idannuwanta ta lumshe tana tuna maganar Ayya cewar wani lokacin zaka rasa gane kansa, zai dulmiyar da kai cikin tunanin waye shi? Dan haka ki yi ta hakuri Agaishat!
Wardugu, ka taimaka, ka bani hanyar da zan fahimce ka, ka taimaka ka ringa fara.a tare da ni ba sai ranar da ka yi niya ba, ka taimaka na zama wace ke gane du wani motsinka!
Wayar da ya ajiye mata ne ta shiga kuka ta hanyar salama da muryar mace zazaka tana karawa,
Sai da ta zabura dan ta zurfafa a tunani, kukan ya ankarar da ita dan haka da sauri ta dauko wayar tana duba sunnan wanda ke kiran, Anmou, waye Anmou????
Dagawa ta yi da salama sannan ta yi shiru,
Daga can kuwa sai da aka daga ta mika mata wayar tana dubanta da murmushi inda ita kuwa ta karba ta dan yi tsai , bata san da me zata fara ba, bata san me zata ce da ita ba, marabinta da ita tun kanta na cikin duhu,
Dan haka a hankali ta ce' Agaishat!
Tsai Agaishat ta yi, lokaci guda zuciyarta ta buga,
Wayar ta cire ta kali numbobin sannan ta mayar a kunnenta,
Muryar matar ta kara cewa " Agaishat, kina ji na kuwa? Da yaren buzanci, da irin yanda take rrrrrrrr dinta sak irin na Agaishat din,
Da sauri Agaishat ta kai zaune muryarta na rawa ta ce" Anna? ANNA ke ce?
Anna ta lumshe idannuwanta ta amsa da " Eh Agaishat,
Ai kuwa Agaishat ta fashe da kuka tana sauraron limfashin mahaifiyarta,
A hankali ta ce" Anna, ina kike? Kun dawo ne? Kin warke Anna? Anna ina yan uwana? Ayya ina Ba Sofona? Annata kin kama sunana sak Annata kin kama sunnana,
Anna ta lumshe idannuwanta tana mai jin nauyin yar da ta haifa da cikinta, tabas ta saki rayuwar Agaishat dandaja, Allah ne kawai ya zama gatanta, ita yanzu haka bata wani hadiye maganar wai dan amininsa na sonta ya saketa, ita fa tsoro take ko bai sameta daidai bane ya saketa? Sakin yaro karami na kutse kutse kofa kofa waje waje dan neman gurin da zai ji sanyin rayuwa , neman abinda zai saka a bakinsa, a haka har ta rago ta kawowa baba sofo da kuma Anna, a haka ta iya tatalin dan kudin da ta samu ta kawo masu, a haka take zuwa ta rabu tana tsoron wani abin ya faru ko mahaifinta ya zo ya karta mata abin wulakanci dan kawai kalar fatarta na da duhu? Tausayin yar ne ya saka Anna kasa yin magana, dan haka Mariama dake tsaye tana ta so a bata wayar ta yi dabara ta karbi wayar ta bushe da dariya ta ce" Agaishat, Agaishat din Ba Sofo, Agaishat an girma?
Kafin ta amsawa Mariama Fatimata ta sabce wayar ta tsere kusa da Gaishata ta ce" Agaishat, Agaishat din Ayya Agaishat kina ina, ina ne gidanki?
Ai kuwa ta kwalalo ido cike da murna ta mike ra budi baki ta ce" Fatimata, Fatimata....
Sai kuma ta ji muryar Gaishata,
Ita kam bata taratsinsu, cikin nutsuwa ta ce" Agaishana,
Agaishat ta zauna tama rasa ina zata saka kanta dan dadi, muryarta nitse ta ce" Gaishata, Gaishata ina kuke ne? Gaishata Anna da sauki jikin nata? Kuna Timiya ne?
Gaishata ta girgiza kai tamkar tana gabanta ta ce" aa, muna garin da kike, mijinki ne ma ya kira jiya, Gukunni ya bashi number Anmou,
Agaishat ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Gaishata kin haihu? Me kika samu?
Gaishata ta yi murmushi ta ce" du wannan tambayoyin adana abinki abinda zamu zo? Dama muma zumudin mu ji muryanki ne, aman Anna da sauki sosai alhamdulilah, nima kuma na haihu, Agaishat, lafiarki kalau dai ko? Ba abinda ke damunki gidanki ko? Agaishat amarya, yar Ayyanta aure sai da hakuri kin ji?
Agaishat ta yi murmushi tana ta sauraron muryar yayarsu ta fari, wani dadi take ji na ratsata har suka kashe kiran bayan sun tabatar mata da suna gari da zama , da sun huta zasu zo inda take,
Suna kashewa ta ji wani karfin gwuiwa ya zo mata, hakan ya sa ta zauna ta shiga game d wayar hankalinta kwonce,
Ta so kiran number Ayya, sai dai tunanin kar ta huce gona da iri ya saka ta bari idan ya zo sai ya kira mata kamar yanda ya saba , ta bata albishir,
Fararan hakoranta kawai take yawan washewa,
Ta jima nan kafin ta mike ta nufi kicin dan shi ne kawai aikinta a gidan,
Da yama bayan ta gama salar la.asar ta zauna da wayar da ta wuni game tana jujuya abinda ta rubuta da yarenta, inda ta samu da kyar ta gama message din kamar haka
*Salam*
Ina yini Ya, ya aiki?
Zan kira ayya ne......................na gode
Agaishat
Numbersa da ta shanye tun tana gidan Ayya saboda tarin zero din dake ciki irin number nan mai shige da juna ne ta rubuta ta tura dan ita ta kagauta ta ji muryar Ayya ta fada mata sun yi waya da yan uwanta da Annarta,
Wardugu dake tuki daga justice ya fito ransa a mugun bace sakamakon kiransa da Gukunni ya yi kan case din AISATA matar Marahut, za.a salameta nan da wata biyu domin a lokacin da ake binciken asalin masu shigo da kwayar Niger ta bada hadin kai wajen fadin sunnayen wa.inda ke siyar mata baki daya, ta bada sunnayen wa.inda ta san suna siya a wajensu, sannan ta yarda bata baiwa sharia wahala ba ta hanyar gardana ko kin hada kai, hakan ya sa ta samu sasauci bayan kason da take yi an dankara mata tara ta millioyin kudi sannan wai za.a salameta!
Hakan ne ya kunno shi, ido rufe ya fito ya dauki hanyar neman Marahut, nemansa yake ido rufe, shi ya san koda da haka, to fa da saka hannun Marahut ta hanyar gannin masu Niger din dan a salamo masa matarsa marar mutunci,
Wayar ce a hannunsa yake dannawa yana neman layin Marahut, aman amsar daya ce, number a kashe, layin ba zai shiga ba,
A haka message ya shigo, da yake orange ne yake kiran da shi sai ya yi tunanin ko zasu shaida masa number ta bude ne?
Yana budewa ya ga message din,
Kallon number ya yi ya ga number wayarta ce da ya saka mata layinta cikin wayar nan,
Wai wardugu gatsal tamkar wani sa.anta? Sannn shi zata turowa message da umarni? Me take tunani? A me ta dauki kanta? Ba damuwarta bane da damuwarsa itama ko? Bata damu ba da halin da yake ciki ko?
Wani kuuuuu ya taka birkin motar kafin ya samu ya yi riboss da matsiyacin gudu ya dauki hanyar Aeroport din, ba zai hadiyi cewar, shi yana hana kansa komai idan ya ga koda yannayin fuskarta ya canza ne aman ita bata damu ba, da damuwarta kawai ta damu, zai warware mata rashin mutunci ne ta san cewa bafa shayinta ko taoronta yake ji ba! Zai je gidan ya.......
Wayo yar muleka😕😕😕😕
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
8️⃣4️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
Yana sake saken tarin mugunta ya karasa gidan,
Bai yiwa kowa magana ba, bai shiga hurumin kowa ba kamar yanda ya fita ya nufi hanyar sada shi da ciki, inda kowa ya shiga tatara kafafuwansa yana barin wajen dan ba zai so abinda za.a kula da wani laifi nasa ba,
Bata falo, hakan ya sa ya zarce dakinta na barci,
Nanma bata nan, dan haka ya fito ya nufi kicin,
Dago kan da zata yi ta ganshi ya nufota,
Yannayin fuskarsa ya sakata sakin nade naman da take cikin kabeji zata yi name,
Da sauri ta mike daga kan kujerar mai ruwan silba ta daga kafarta,
Kafin ta shige inda zata shige dan ta san wannan zuwan nata je, dan irin kallon zaki ci yan garinkun da ya yi mata ya saka hanjin cikinta motsewa waje guda,
Rikotan da ya yi da karfi sannan ya fincikota baya ya jefar cikin kicin din,
Yau ta ga rana ta ga tashin hankali domin binta ya yi inda take yaden nan ya wanka mata wani lafiyayen marin da ya dauke jin ta,
Tabas wani dummmm ta ji na lokaci mai dan tsayi domin za.a kai second ashirin hakan ya saka bata ji fadansa na farko farko ba sai da kunnen nata ya dawo ta fara tsintar fadansa kamar haka" *Ba zai yiwu kema ki wulakanta min zuciya kamar yanda ta wulakanta min ba!* ta yayama zan fita daga gidannan raina bace , baki damu da yi min wani abin da zai faranta min ba sai faman ki dura min abinci kafin na fita bayan ina azumi? Ya zan je ma.aikata kin san wani irin aiki nake yi aman ki turon message gatsai gatsai da rashin tauna zance ya zama dadi kamar ke ce gaba da ni ki turo min, oho o na ji abinda zan ji ko? Da wannan dan iskan ne da ya zo wajen diner mai dogon wuyan nan yana launi uwa lagwani da kin zauna kin ware yare kin masa tausasa ko? Da ace tsohon mijinki ne kin iya yi masa kalamai, wanda nima shaidar shi mai daraja ne ana bashi kulawa ne ko? Ni zaki turowa sako da kama sunana kai tsaye tamkar dan gidanki? Sai mutun ya gama mutuwar muku ku wulakanta shi ku zubar da shi ku kara gaba abinku ko? Ku buzayen nan haka halayenku yake? To bari ki ji, a kaina an tsaya, walahil azim Agaishat hanya a bude take, kafarki ke ta taka waje da niyar barina sai na harbe ki! Sai dai a kashe ni! Jarabawata ce soyaya da buzuwa? Na karba, aman kuma rantsuwata ce ke ce buzuwar karshe da zan ringa mafarki ina juyi kanta! Ke ce zan yiwa son karshe a cikin buzaye na wahala dan buzuwa! Ke ce wace zata rayu da ni ko a wani hali, ke rabon haihuwarki da wani namijin sai dai idan ajali ya dauke ni!
Hannunsa ya buga jikin madubin kicin din da aka kafa kato domin ado inda ya fashe dan kuwa mai fashewar ne, ya tako zuwa gaban Agaishat dake zaune, cikin wani irin firgici da bugawar zuciya mai tsanani ya dubeta ido cikin ido ya ce" ke ko mutuwa na yi, Allah ya isanmin idan wani ya shiga gonata (Dankari, ka ji masifa fa, an taba yin haka dama?),
Sai da ya gama tashin hankalin da ya dirmiyar da ita cikin wani yannayi na furgici da tsoro, kara jin shayinsa, tashin hankalin abinda ya ringa maimaitawa a fadansa *ba zata wulakanta masa zuciya kamar yanda Aisata ta wulakanta masa ba,* sannan ya juya ya fita a kicin din,
Kafafuwanta ta hado gaba daya ta hade a jikinta, barin da jikinta yake yi ta samu ta daidaita ta hanyar adu.a,
Mikewa ta yi ta je wajen kayan da take gyarawa ta harhada komai ta kimtsa still jikinta na rawa sannan tana share hawaye ta ajiye komai wajensa ta fito,
Sai da gabanta ya fadi ganninsa a fallon, bai fita ba kennan, yana waya da alama da Ayya yake dan a tubancin da yake tana tsintar yan kalmomi da kuma sunnan Ayyan
So ta yi ta koma kicin din, sai dai wani abin ya hanata dan haka ta taho a hankali ta raba ta nufi dakinta,
Da kallo ya bita ya ci gaba da wayar, sai da ya gama ya taka zuwa dakinta, tun da ya fara fadan nan ko ci kanka bata ce da shi ba, yanzun ma da ya shigo yana ta muzurai ya bala mata harara kafin ya karasa ya tsaya kusa da ita ya ce" wato ga mahaukaci ko Agaishat? Shine kike nufi na yi na gama ko?
Agaishat ta dago da idannuwanta da suka rine dan tsabar shiga tashin hankali ta dube shi,
A hankali ta ce" ka yi hakuri,
Wardugu ya ce" hakuri? Hakurin me zan yi a ciki? Na rashin bani muhali a rayuwarki ko na raina ni da kika yi?
Agaishat ta kuma dago da kanta, wannan karron bata sada duban nata ba ta kafe shi tsai da kallo,
Fitina kawai yake ji, so yake ta biye masa kamar yanda suka saba da matarsa ya tataka banza ya yi gaba abinsa, tabas ta yi rayuwar rashin sannin ciwon kai, aman bata tunanin zata yi rayuwar duka a gidan miji,
A hankali tana dubansa ta ce" menene laifina? Meye na yi mai girma haka? Ka taba nunan baka son sunnan nan? Ince kulunma da shi nake kiran ka kuma ka amsa ba tare da ka nunan bai yi ba, menene? Ganninka a irin halin nan an taba *AISATA!*
ido ya zaro yana dubanta, kai kai kai,
Agaishat ta ci gaba" dan Allah ka yi hakuri, kar ka saka ni a irin wannan rayuwar, ban iya ba, ban iya wannan rigimar ba, idan na bata maka ne ka yafe min, sannan ka daina tuna baya kana hada ni da wasu gardawa da aurena kuma na san darajar auren nawa,
Tana magana ne gabanta na dokawa, aman dan karfin hali sai da ta gama cikin sanyin hali tana hankalce da yannayinsa, kafin ta juya a dabarance ta yi wajen bayi ta tsaya gannin bai juyo ta tabatar da tunanin abinda zai mata yake dan haka da dan gagawa ta bude bayin ta shige ta rufo kofar sannan ta duka daga kasa ta ce" kuma Aisata dai ko? Zamu kai kukanmu wajen Allah ya raba tsakanin nan dan haramtace ne!
Da sauri Wardugu ya juyo sai dai ganni ya yi wayam, bata nan,
Kafarsa ya daga ya je ya tura bayin , aman a rufe ruf,
Wai waiwai dukan kofar ya shiga yi yana fadin" me kike nufi? Me zan yi da wannan banzar da ta banzatar da kanta? Me zan yi da macen da ta auri ubana dan abin duniya? Ki bude ki fada min abinda kike nufi da wannan maganar,
Haka ya yi ta bambaminsa kafin yake yin sanyi a hankali ya kai kasa ya zauna jikin bayin ,
Muryarsa ta tabatar mata da kamar ya shiga duniyar tunanin maganarta, inda ya ce" Ya zaki saka na mare ki?
Agaishat dake zaune itama tana sauraronsa, ta lumshe idannuwanta, walahi da ita fara ce ta tabata yau da sai ta nemi maganin tashin fata, aman yanzu haka jin idonta take da nauyi, ta maru fa,
A hankali ta shafa wajen , muryarta na rawa ta ce" dan me ba zaka mari matar cushe ba?
Wardugu ya dubi kofar bayin , bai san lokacin da ya saki murmushi ba ya ce" ke ce matar cushen?
Agaishat ta gyada kanta tamkar yana kallonta kafin ta ce" haka ne,
Wardugu ya ce" to fito ki ji,
Agaishat ta yi murmushi sannan ta yi irin na yara kafin ta ce" aa,
Aa? Ya maimaita a hankali yana zaro idannuwansa da mamakinta,
Agaishat ta ce" eh, ina tsoron duka, bana son duka,
Wardugu ya yi shiru, nan ya ji tausayinta ya kama shi, bata son duka, ya zo da bacin ransa ya sauke saman kanta,
Idannuwansa ya lumshe ya ce" kin san menene ma.anar Orronur?
Agaishat dake zaune dandabar cikin bayi daga ita sai yar doguwar riga ta kanti da ta saka take aikinta rigar bata da nauyi , sannan da kadan ta fi gwuiwarta tsayi, kanta ko dan kwali babu
A hankali ta dago dubanta kamar shi ne kofar ta dubi kofar kafin a sanyaye ta ce" Me yake nufi??
Wardugu ya saki murmushi mai dan sauti, ya ce" ki yarda da amon kuryana, ki yarda da yannayina, ki bude min , ki zo gareni, ki sauke min fushina, ki ririta ni, ki bani na tsotsa (😳🙆🏻♀️), ki bani na samu nutsuwa, Agaishat , ki karanci menene Orronur a tare da ni, ki bani amsa da kanki,
Wani irin yamyamyam ta ji tun daga yatsar kafarta har tsakiyar kanta, idannuwanta ta lumshe da karfin gaske dan kuwa har jikinta sai da ya amsa sannan ya dauka,
Wayo Allah, shi ne abinda ta fada a kasan makoshinta, domin kuwa a yanda ya yi maganar, ya karashe tamkar yaron dake neman mamansa ido rufe,
Hannunta na dan rawa rawa ta mike ta kai hannunta wajen budewar ta dana inda ta yi kundumbala da tsoron haduwar da shi, ta tataro jarumta ta bude kofar (Agaishat😳, idanfa ya yi haka ne dan ya damke ki? Baki dadara da marin ba ko? Wayo Agaishat😔)
Budewa ta yi baki daya kofar ta bude, sai gata bayane gabansa, gaba dayanta yar ficik a gabansa,
Taku daya ya yi ya karasa gabanta, hannunsa ya mika ya.................
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
8️⃣5️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
*ASALAMU ALAIKUM FANS, BAK'A DAI BA NA SIYARWA BANE, DU WANDA YA KARBI KUDINKU DAN YA SIYAR MAKU YA CUCE KU NE, NI BAN RUBUTA BAK'A CE DAN NA SIYAR DA SHI BA*
A hankali ya mika hannunsa ya janyota jikinsa,
Bata ki ba ta kwonta a jikinsa luf,
Cikin nutsuwa ya lalubi lebenta , bai tsaya dogon turanci ba ya shiga aika mata kis cikin sauri sauri dan kuwa a matukar matse yake da ita,
Kokarin kaita kasa yake nan, ta samu a hankali ta kai bakinta daidai kunnensa ta ce" Dati jikina Yah, ka bari na yi wanka daga kicin na fito, karnin nama nake,
Idannuwansa ya lumshe domin ji yayi tamkar tana yi masa susa a kunnen dan kuwa a hankali ta yi maganar ga kuma lebunanta dake gugar kunnen nasa,
Tsai ya yi, kafin ya lumshe idannuwansa,
A hankali ya samu ya janyota jikinsa sosai,
Hannunsa yake bi dukan jikinta yana neman hanyar cire rigar kafin ya iya fuzgo maganar bakinsa ta hanyar cewa" kin fi armashi a haka.........
Da gudu na baro dakin, domin kuwa Agaishat ta zagine tana baiwa mijinta goyon baya dan raya sunna ,
Sun jima suna maida numfashi bayan komai ya lafa, a hankali yake shafa gashin kanta, kafin ya ce" kin san me?
Agaishat ta girgiza kanta tana lumshe idannuwanta, dan kuwa ya yi kokarin binta a laluma , sai tarin gajiyar da take ji dai na rashin sabo a jikinta,
Wardugu ya ce" Oroonur, na nufin *RAINA*
Da sauri ta dago da dubanta daga kwoncen da ta yi lamo a jikinsa,
Ido ta tsura masa tana dubansa,
Hakan ya sa ya hade fuska shima yana dubanta,
Murmushi ta saki kafin ta mike ta shige jikinsa gaba dayanta, a hankali ta ce" ni? Ni ce Ranka?
Wardugu ya rungumeta da dan karfi a jikinsa, hakan ya sa ta yi lamo, still ta kuma cewa" *KANA SO NA?*
Wardugu ya yi murmushi bai bata amsa ba,
Can har ta cire rai da jin amsarsa ya ce" me kike so na maki a duniya na kare min mutuncin kanki da kika yi?
Agaishat ta dago da kanta tana dubansa, ita kuwa me ya rageta da shi? In mutunci ne ya siya mata, in kaunar ce ya kilaceta a gidansa, ba yunwa, ba kishirwa, ba rashin mutunci, ba ruwansa da kauyancinta, kuma yanzu ya gama shaida mata ita din Ransa ce, ita kuwa me zata nema bayan shi nashi jin dadin? Kai walahi ta dauki aniyar faranta masa mudin ranta!
A hankali ta dora kanta saman kirjinsa, hannunta dake kusan keyarsa ta dan karawa tsayi ta duko da kansa wajen fuskarta,
Kanta ta daga ta kai lebenta kusan bakinsa,
Yana tsaye tamkar ya kurma ihu dan dadi yana jiran ya ga ikon Allah me zata yi,?
Ba zato ba tsamani ya ga ta ciro harshenta a hankali, kuma idonta cikin nasa ta kawo harshen daidai lebensa, idannuwanta ta lumshe kafin ta lashi lebensa na kasa,
Tana lashewar ta bude idannuwanta sanadiyar kara matseta da ya yi a jikinsa, idannuwansa ta gani a lumshe,
Murmushi ta saki sannan a hankali ta ce" burina shi ne, ka yi hakuri, ka zama mai hakuri, ka zama mai yafiya, Yayana da ciwo, da mugun ciwo, aman a yau idan ka dubi wani abinda ya gani a rayuwa naka mai sauki ne, ka duba ka ga yanda kake cikin rufin asirin Allah, ALlah ya baka rai kyauta, ya baka lafia kyauta, ya baka iyaye kyauta, ya bata yan uwa kyauta, ya baka mata masu kaunarka domin Allah kyauta, ya baka arziki ta hanyar halal kyauta, ga kyau,
Ta yi tsai ta dago tana duban idannuwansa, ta yi wal da idannuwanta ta ce" Mijina ga jarumta, ga farin jini , ga karfi, duka ba dan karfinka ko dan dabararka ba,
Shiru ta yi ta kuma dagowa tana duban yannayinsa, gani ta yi kawai ya tsura mata ido yana sauraronta,
A hankali ta dan zame kadan tana dubansa ta ce" duka bai tambayeka komai ba sai ka yi masa bauta, ka yiwa iyayenka biyaya, sannan ya ce *ALJANARKA TANA KARKASHIN KAFAR IYAYENKA* ,
Ka san me?
Dubanta yake bai amsata ba, bai kuma nuna bacin ransa ba, kai hasalima ba zaka fahimci wani yannayi yake ciki ba, yana dai kallonta ne,
Ji ta yi ta fara jin tsoron yannayinsa, dan haka a hankali ta yi shiru ta mike dan daukar rigarta zata saka,
Hannunta ya riko, ya kawota bakin bed din,
Maimakun su hau bed sin sai ta ga ya zauna da ita nan kasa ya sakata tsakankannin kafafuwansa ya dora bayanta saman jirginsa sanna ya saka hannayenta cikin nasa, a hankali ya ce" *sai kin fada*
Gabanta sai da ya wulwula ya fadi, anya kuwa zata iya ci gaba da magana a haka ? A hannunsa fa take dumu dumu, idan ta yi garaje daga haka yana iya juyar da kanta zuwa dubansa wato ya karya kan,
Yawu ta hadiye ta ci gaba da fadin" ni ba zan yi wasa da aljanata ba, du rintsi, du wuya, zan bi aljanata da gudu, a kanka sujada ne kawai ba zan maka ba shima dan haramun ne, zan tarbi mai tarbanka, zan banki mai yi maka mugun kallo, zan harbi mai zundenka, somin kai din uban gidana ne, mijina ne, mai take da aljanata ne,
Wani irin gingirigin kansa ya yi, wollah jinsa ya yo ya cika dakin dan girma, wani yuuuu ya ji gaba daya jikinsa, mace bata taba fada masa haka ba, macen ma Orronur, yarinya karama, yarinyar da ta yi girman daji, dama ta iya dadadan zance haka? Yaushe ta koya? Yaushe ta san tace da shi mijinta, yana jin dadi da gannin girman kalmar bale da ta fito daga bakinta, wai wai dadi, a hankali ya lumshe idannuwansa sannan ya kara rike hannayenta, muryarsa kasa kasa ya ce" Orronur,
Kina so na?
Shiru ta yi, tana mai kara tunanin hikinkimun da zata bi da shi,
Sai da ta kwontar da kanta saman kirjinsa ta yi lamo, sannan ta ce" *ARREKI DI IMANINE DU IDINETTE* (U.R TH MAN OF MY LIFE......TU EST LHOMME DE MA VIE),
sannan ta rike hannunsa ta kawo daidai zuciyarta ta dora, a hankali ta ci gaba da fadin" sun ce, daga na fara so, idan na ga abin son zuciyata zata fara bugawa, za.ina son gannin abin, za.ina son kasancewa da shi koda yaushe,
Tabas a kanka na san wannan abubuwan,
Gaba daya ya juyota tana facing dinsa, hannayensa dake rawa rawa ya saka ya dago fuskar tata daidai tasa yana kallonta, A hankali ya ce" fada, fada min , na roke ki,
Agaishat ta lumshe idannuwanta ta bude ta ce" *INA SON KA*
Bai bari ta karasa ba ya shigar da ita jikinsa, ajiyar zuciya kawai yake saukewa tamkar yau ya fara jin kalmar so a bakin mace,
Sai da ya jima sannan ya sasauta mata rikon, aman kuma tana cikin jikinsa tamkar wani zai kwaceta,
A hankali ta ce" zan so gobe kiyama na yi alfahari da kai, zan so yayanmu idan Allah ya nufe mu da samu su yi koyi da halayanka,
Ba zan iya budar ido na ga danka yana gaba da kai ba, zan iya samun arret cardiaque (heart attack) dalilin haka, domin kuwa d'a ko na wace mace ne, in dai naka ne toh bugun zuciyata ne,
Tsai ya yi yana kallonta, zuciyarsa fesss , inda ya dago inda ta nufa da magangannunta,
Shirun da ta kuma yi tana mai daidaita bugun zuciyarta da tsoronta ya saka shi dan tapping din bayanta ya ce" Uhum?
Dan dago da idannuwanta ta yi ta ga ya tsareta da kallo, irin kallon nan na ya fara kausasa,
Takwaf takwaf ta yi da fuskarya ta samu ta mike tsaye inda ta yayumo abin shinfida tana kare jikinta da shi,
Hannunsa ya saka ya dangwarar da ita gabansa tamkar baby, ya daga girarsa duka biyu ya ce" karasa,
Da sauri ta girgiza kanta ta ce" shikenanma , abinda zan fadi kennan,
Wardugu ya girgiza mata kai shima ya ce" karya ne, fada min karshen maganar
Agaishat ta lumshe idannuwanta, a hankali ta fashe da kuka tana dubansa da yannayin yanda zai dauki kukan,
Ai kuwa ya nunan domin kansa ya dafe ya ce" meye na kukan kuma ? Me na miki?
Agaishat ta ce" to ai na san idan na fada kana iya dukana, ni kuwa bana son duka,
Wardugu ya sauke ajiyar zuciya ya ce" nima bana son taba lafiayarki, ki yafe min na dazu kin ji?
Agaishat ta gyada kanta ta ce" to, ka sani idan ka dake ni, ba komai, na yafe maka, aman dan Allah kar ka min mai zafi,
Shi dai kallon yannayinshagwabarta yake kafin ta ci gaba da fadin" yaya kake son haduwarka da Allah ta kasance? Ni mahaifina ya tsane ni, baya son ganina, aman ba Sofo yace na yi ta masa biyaya dan na samu rabauta gobe kiyama, ka ga ina son mahaifina komai mumunan halayan da yake aikata mana da mu da Anna,
Da sauri ya dubeta, wani tausayinta ne ya ji, tana son mahaifinta? Koda kuwa ta ji a irin hanyar da ya same su su duka?
Katse shi ta yi ta hanyar fadin" kuma ka ga kaima zaka haihu, idan ka haihu yayanka suka yi maka haka fa? Mace? A kan mace? Ka dora muguwar gaba da mahaifinka haka? Dan Allah ka min rai, ka gyara tsakaninku da Aba, da kuma tsakaninsu da Ayya, na tabata idan yau ka yi niya sun gama shiryawa kennan, idan ya so ka barsu su gani da kansu, zasu koma rayuwa tare ne ko ba zasu koma ba? In dai an samu sulhu, zaka samu ladan hakan, kaima kuma Allah zai yafe maka, zaka ga daukaka sai dai ta yi ta kara zuwa, Allah zai kara kareka daga du wani shari, yayanka zasu mutuntaka su yi maka biyaya, matanka zamu ci gaba da mutuntaka mu yi maka biyaya,
Hannunsa kawai ya saka ya dafe yana dubanta,
Sai da ta gama sannan ta sake mikewa da sauri ta nufi bayi,
Tana shiga ta rufe tana sauke ajiyar zuciya, wai wai wai, bai kara tsinka min marin ba.....shi ne abinda ta fada kafin ta je ta shiga kiciniyar kimtsa kanta tana mai adu.ar Allah ya sa ta ci nasara,
Ya dan jima zaune kafin ya mike ya nufi bangarensa,
Shima wankan ya yi ya fito ya zauna bakin bed,
Shiru yana duban waje guda, wa ya koya mata? Dukan magangannun nan da ta yi, ba wanda ya taba yi masa su haka a dukan masu neman sulhunta shi da mahifinsa, ko kuwa ita dan yana jinta a ransa ne magangannun suka yi tasiri a zuciyarsa haka? To aman ai Walyn ya fara aura, hasalima bata taba tayar masa da maganar ba, tana tsoron ta yi ne ya mara fada ko me ya hanata yin? Ko bata damu da gobensa bane?
Wani abin yace...aaa, ba rashin damuwa da gobenka bane, just ita dai bata da kula a wasu abubuwan ne ai,
Ya jima zaune, kafin yake gannin haske a wayarsa,
Marahut ne ke maido masa da kira,
A hankali ya daga, yana dagawa Marahut ya ce" Wardugu, walahi babu saka hanuna a sakin wannan yarinyar, hasalima ni tun da na gane irin mugun aikin da take yi, da bin maza da urena a kanta na saketa, ban san wa ya shige gaba wajen sakinta ba, yanzu nima Gukunni ke fada min sakinta za.a yi, Wardugu ka fahimc.....
Wata kunya ce ta lulube shi, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, mahaifinsa? Mahaifinsa ne ke rawar murya dan ya wanke kansa a wajensa? Wata irin masifa ce wannan? Dama haka suke rayuwa? Dama haka Marahut ke masa magana ko yau ne haka ta faru?
Muryarsa ya ji tana rawa, a hankali ya ce" ABIH,.
Marahut dake ta faman kare kansa ya yi dif,
Kunnensa ne ke jiyo masa abinda yake son ji daga bakindan nasa ko kuwa gaske ne,?
Dan haka sai ya ci gaba da maganar a darare,
Wardugu cikin yaren tubanci ya ce" Abih, dan Allah ka bari, ya isa haka, ka bar mini rantsuwa,
Da sauri ya dubi wayar, number Wardugu ne, dan haka hankalinsa ya tashi, mikewa ya yo ya ce" me ke damunka? Baka da lafia ne? Me akai maka? Kana ina ne? Wani abu ya sami Ayyanka? Ko wani abu ya samu iyalinka? Menene War?
Wardugu ya ce" ina gidana , dake aeroport, kai kana ina Abih????
Marahut kashe wayar ya yi, daga inda yake sai cikin motarsa ya tayar cikin tashin hankai ya nufi gidan Wardugu,
Wardugu kam kansa ya dora gefen gado yana jin wani irin tausayin mahaifin nasa, yanzu da shi ne haka ke faruwa da shi , da dansa ina zai saka kansa? Ya zai rayu da haka?
Bai san adadin lokacin da ya dauka a haka ba, sai kiran masu tsaron kofar suka shaida masa Marahut ne,
Cikin tsawa tsawa ya bada umarnin a barshi ya shigo ko.ina, babansa ne fa!
Ai kuwa suka bar Marahut shiga ,
Yana parking din motar ya fito yana neman ta inda zai fara dan samun gannin Wardugun,
Sai dai hango shi ya yi tsaye yana kallonsa,
Takawa ya shiga yi yana duban yannayinsa har ya isa gabansa,
Ya budi baki zai yi magana kennan ya ga Wardugu ya duka..... ya duka har kasa, kansa na kallon kasa,
Jijiyoyin jikinsa du sun daga dan yannayin da yake ciki, muryarsa wani irin ya ce" dan Allah ka yafe mini, ka yi hakuri ka yafe mini,
Marahut da ya ji wani iri zuciyarsa ta buga da karfi ya saka hannunsa ya dago wardugu yana dubansa, hannunsa ya saka yana taba lafiar jikinsa sannan ya ce" me ke damunka? Baka da lafia ne?
Wardugu ya girgiza kansa yana mai jin haushin kansa, wai ace dan ka yi dadan magana wa mahaifinka sai ya shiga rudu? Lale ya jima yana tafka barna,
Kansa ya dafe da hannun nasa kafin ya ce" lafiyata kalau, ina neman yafiyar irin abubuwan da na yi maka Abih, tabas matar mutun kabarinsa, tun ran gini tun ran zane, ka yafe min ,
Ai kuwa Marahut ya saki murmushi ya rungume Wardugu a jikinsa, bai iya cewa komai ba sai jan hannunsa da ya yi suka nufi motarsa suka shiga, Wardugu ke ja, Marahut kuwa sai sakin murmushi hamdallah ga ubangiji yake, baima san me yake ji ba, fatansa ya shawo kan Ayya cikin sauki
(Mace ta gari kennan, masha Allah)
Bayan kwana biyu da faruwar wannan , Walyn ta zo gidan,
Sun sha daru da masu tsaro , inda suka hanata shiga fir,
Ta kusan wuni a kofar kafin Wardugu ya dawo, ganninta a zaune a waje ya saka ya barta shiga cikin gidan, inda ta ringa bin ginnin da kallo, tana mamakin nan ya kawo bakar mace dan zubar aji?
(Ku gane, shi fa gyaruwar halayan mutun abu ne mai matukar wahala ba kamar yanda muke zano mugayan halayan mutane sannan mu nuna lokaci daya sun gyara a cikin novel ba ko an sake su ba, kowa kuma na zaune da ra.ayinsa ne, shi shiryuwama sai Allah ya nufa, sannan ba lale mutun ya daina dukan halayansa ba, sai dai a rage a samu sasauci, sannan idan ya hadu da daidai kugunsa sai a yi ta buga game din wardugu dai ba zai saki mace ba, domin wani irin mutun ne shi mai kishin balaki, ku gane ba wai wani so ko wani abin ya hana shi sakinta ba, sai kishin ya saki macen da ya malaka wani ya malaketa, shi fa izgili yake yiwa al.adu da canfe canfe inda yace rabon ya jima bai.kashe shi ba! Idan abu ya yi kamari ne sai ya watsar da ke, ranar da kikai hankali kya nemesa ) ,
Tsayuwa ya yi yana dubanta ya ce" me kika zo yi?
Walyn ta yi kalar tausayi ta ce" aman ai gidan mijina ne ko? Na zo a bani part dina na zauna a gidana nima ,
Murmushi ya yi ya girgiza kai ya ce" yau kuma ina maganar al.adu? Yaushe batube ke hada mata gida guda?
Walyn ta ce" aman ai adalci na nema ko?
Wardugu ya yi murmushi ya gyada kansa, ya ce" kin ga, bama son rigima, idan nan din kike so, ita sai ta koma can, ko ta koma wani, idan kuwa wani kike so ki je ki zaba ai kin sansu gidajen sai a kara gyara maki ki koma kin ji Walyn?
Walyn ta gyada kanta, can ta ce" dan Allah ka maida ni gida,
Wardugu ya dubeta da kyau ya ce" ki je zan zo,
Walyn ta ce" to motana ba mai, kuma bam fito da cart dina na banki ba,
Wardugu ya gyada kansa, daman ya san maganar dai ba zata fice hakan ba, dan haka ya mika mata cart dinsa ya bata sabon cod din da ya saka , sukai salama ta tafi da niyar sai ya zo,
Cike da kurna take tuki, zako ta zabi gida, gidan da ya hada haya take so, wanda gwamnati ta dauka ake projet a ciki, shi take so a gyara mata ta koma, dan kuwa ta san zata bada kala,
A haka ta karasa gidan mamanta ta kai mata kudin da ta yi mata alkawar sannan ta juya ta nufi gidanta dan kuwa yanzu du ta watsar da kawaye, dan ta san idanma ta koma cudanya da su zata sha habaici a fakaice ne,
Tana zuwa ta zauna bakin kujerar falonta ta yi jigum, bafa ta da mahaifa! Abinda ko.mahaifiyarya bata sani ba,
An juya mata mahaifa, du dan gudun ta kara samun cikin da wuri, ko kuwa ta haihu du ta lalace dan ta ga daga an haihu ake zama rusheshe ko du a lalace , tana yawan tuna maganar Wardugu da ya ce" me na rage ki da shi da ba zaki haihu da ni ba?
Yana son yara har haka? Yanzu ina zata je a gyara mata mahaifarta? Dan kuwa bata yarda da maganar doctern garinnan ba,
Zata kwontar da hankalinta, ta sada kanta, har ya amince mata ta tafi india a dubata, a yi mata aiki a gyara mata mahaifarya, itama ta dawo ta haihu sai ta ga yanda za.ayi gata ta haifar masa abinda yake so, ta tabata soyayarta zata dawo kamar da a ransa!
(BAK'A CE BA NA SIYARWA BANE, FANS DU WANDA YA BIYA DAN KARANTA BAK'A CE NI DAI MARUBUCIYARSA KYAUTA NA YI SHI, SAJIDA CE)
washe gari ya kama asabar, tana zaune ta gama waya da Ayya kan ta tsife kanta za.a zo a yi mata kitso, tana zaune tana tsifar kan tana mai jin zuciyarta na tashi haka kawai , bata san me ya shiga turaran wutar da ta saka yau ba, du sai take ji kamar an canza mata shi kamshinsa baki daya,
Tana cikin haka ta ga shigowarsa,
Tana kokarin ta hade gashin ta mike ta hango su,
Su duka uku ne da wata datijuwa mai kama da Anna,
Bata san lokacin da ta mike ta kwala karan murna kamar yanda suka yi ai kuwa da gudu suka makalkale juna,
Ihun murma suke kowace na kama sunnanta, itama sai kama sunnayensu take suna latsa jikinta da mamaki itama sai kallonsu take da mamaki inda Wardugu da Anmou ke tsaye shi yana sakin murmushi dan ba a gidan ya kwana ba, zuwansa kennan ya zo ya sanyo su , anmou kuwa na dariya itama gannin yanda Agaishat ta rasa inda zata tsaya ta kalli wannan ta juya ta kalli wancen sai kawai ta saka kuka ta dora kanta saman kafadar Gaishata ta ce......
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
8️⃣6️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
*ALHAMDULILAH ALHAMDULILAH ALHAMDULILAH*
*ND*
*ND*
*ND*
Wardugu kam juyawa ya yi ya nufi gidan Ayya domin a jiya da ya je gidanta fatatakarsa ta yi kamar kwanakin nan da suka shige,
Yau kuwa da kanta ta yi kiransa tana son ganninsa,
Yana zuwa gidan Ayya ya zarce dakinta,
Kwonce take saman bed sinta idannuwanta lumshe, aman kwonciyar ta mutunci ce domin ko.inanta a rufe ruf,
Da sauri ya karasa ya duka inda take ya ce" Ayya, baki da lafia ne? Me ke damunki Ayyana? Tashi na gani Ayya?
Ayya dake kwonce ta lumshe idannuwanta ta ce" Wardugu, ka zabi mahaifinka yanzu ko? Ka zabe shi a kaina ko?
Wardugu ya kama hannun nata da ta janye ya janyo ya dora gefen fuskarsa ,
Muryarsa ce ta raunana, ya ce" bani da tamkarki du duniya,
Sai dai shima haka,
daga ke sai shi a duniyata,
Ayya ta yi shiru, can ta ce" mutumen da ya zabi mace a kan iyalinsa? Mutumen da ya auri yarinyar da na guji dana ya aura dan ban yarda da tarbiyarta ba, mutumen da mai yiwuwa ya yi zaman aure da macen da dansa ya gama gannin sirinta, na san baka aikata zina da ita ba Wardugu, aman kuma na san da ba yanda ba zata yi ba dan jan ra.ayinka,
Sai yanzu da ya rasata zai waiwaye mu? Sai yanzu zai san da zaman mu?
Wardugu ya rike hannun Ayya da kyau yana dubanta ya ce" ki yi hakuri,
Gani gabanki, duke saman gwuiyoyina, ina mai neman sulhu,
Sulhu kawai na roka a wajenki mahaifiyata, ba zan roke ki kara zaman aure da shi ba idan hakan bai maki ba,
Aman ina so ku daina gaba, a fitar da fushin nan ,
Ayya ta mike zaune tana dubansa,
Kanta ta girgiza kawai sannan ta ce" ba komai, Allah ya shige mana gaba, ni na yafe masa, ba maganar gaba tsakaninmu, aman kuma bana tunanin zan iya rayuwar waje daya da shi again,
A barni na huta,
Wardugu ya amsata yana mai gyada kai, ko ba komai ya ji dadin cirw fushin dake tsakaninsu,
Maganar wancen kuwa, ya barwa Allah zabi,
Haka suka jima suna hira da Ayya , nan yake fada mata zuwan yan uwan Agaishat, daman sun zo sun gaisheta Gukunni ya kawo su satin da ya shige, nan ta yi murna kafin ta ce" Allah ya sa dai kar su fada mata wannan lamarin,
Gabansa ya ji ya fadi, Ruwan tea din da ya dauka zai kai bakinsa ya dakata,
Mikewa ya yi ya yiwa Ayya salama ya dauki hanyar gidansa,
Yana zuwa ya shige ciki direct dakinta domin bata falo, kuma da alama bakin sun jima da tafia,
Kwonce ya ganta cikin bargon, sai rawar dari take,
Da sauri ya ajiye kys din hannunsa ya karasa inda take kwonce ya yaye bargon yana dubanta ya ce"Orronur, lafia? Menene?
Hawayen da ta sha ne ta yo gagawar gogewa cikin dabara da hannunta, kafin ta mike a hankali dan ya kamata so yake ta mike din,
Jikinsa ta shige ta yi lamo tana duban gashin dake kwonce saman hannunsa,
A hankali ta dora hannunta tana shafawa , cikin nutsuwa ta ce" kuma du wannan abin da aka yi dan a tara dukiya aka kare ba komai, karshema yanzu mijin Gaishata ke fadin an nemesa an rasa,
Ribar me ya ci? Ko zaman da aka yi idan ya karbi kudin auren yan uwanmu basa jimawa yake batarwa ta hanyoyin da basu da kyau kuma ya dawo ya shiga hangen wasu, uku sun rasa ransu ta haka,
Ashema duka zaman bai gina shi da aure ba? Ashe mu dukanmu ba daya da aka haifa da aur..........
Hannunsa ya saka ya rufe mata bakinta,
Cikin nutsuwa ya ce" wanda ya halice ku, haka yake son ganninku,
Kuma muma bamu da damuwa da hakan,
Kanta ta dora saman kirjinsa tana mai jin wani girmansa, kunyarsa, kaunarsa na kara shiga cikin jinnin jikinta,
A hankali ya karkata ya sauka da ita ya ja hannunta bayan ya dauki yar ledar pharmaci din da ya shigo da ita ya nufi bayi da ita,
Yar robar dake cikin abin ya mika mata , fuskarsa ya shagwabe kamar wani yaro ya ce" Orronur, dan bani fitsarinki kadan a nan kin ji??
Da mamaki ta zaro ido, fitsarinta kuma? A wannan yar robar mai shegen kyau? Me za.a yi da fitsarinta?
Tsaye ta yi tana dubansa da iyakacin gaskiyarta, sai dai gannin da gaske yake ya sakata fadin" to ka juya mana
Murmushi ya yi ya juya bayansa inda ta samu da sauri ta yi tana kallonsa dan kar ya juyo ya shanmaceta,
Kallonsa take har ya dauka ko kyankyami baya ji, ya ciro dogon abin dake cikin wata yar farar leda mai kabar kabar ya saka kan abin sannan ya dawo kusa da ita ya janyota jikinsa sukai tsaye su duka sunna kallon abin
Ita kallon da take dan ta ga menene? Me kuma zai yi bada da fitsarinta?
Shi kuwa jiran lokaci yake dan gannin result din test din
Bayan minti biyar ya dauko ya duba,
Radau suka nuna kansu sanda biyu, wanda hakan ke nuna ciki ne jikin Agaishat,
Idannuwansa ya lumshe, can kasan zuciyarsa yake godewa Allah,
Aman kuma wani tsoron ta sani ya darsun masa, yana tsoron kar aje itama bata son haihuwar, dan haka sai ya yi shiru ya kamo hannunta suka fito daga bayin,
Bakin bed ya kwontar da ita, ya rankwafa yana gyara mata gashin kanta, sai wani bibinta da kallo yake fite da da, hakan ya sa du ta tsargu,
A hankali ya mana mata kis a goshinta, sannan ya kai hannunsa kamar cikinta yake shafa , ya shafo wajen mararta ya saki murmushin da bata san ko na meye ba, sannan ya mike ya fice a dakin bayan ya dauke abin test din, yace da ita yana zuwa....
Kwonci tashi kayan Allah,
Agaishat wajen wata biyar da aurenta da Wardugu,
Zuwa yanzu, koda sun yi fitinarsu da matarsa baya nuna mata , yakan nuna ya tafi gidan Walyn din da ta koma itama gida ne na gani na fada, sai ta yi baci ya yi zamansa abinsa,
Cikinta kam na tafia cikin nutsuwa, bai yi wani girma sosai ba, ya tasa dai, wanda Zuwan Gaishata garin da ta je ganninta ita take fada mata ciki ne da ita fa? Ta sha mamaki, ita kai, tana gannin cikinta na dan kara girma, bata jin motsin komai kuma,
Kakarta kam dariya kawai ta yi, tana yiwa Anna tsiyar ta daina jin kunyar nan da take na yayan nata fa, domin su sun jima da sani, Ayya ta fada masu Wardugu ya rangada mata albishir din, a takaive dai ita mai dauke da shi ne bata san da shi ba, kai harta da baba Sofo ashe ya san da maganar, taimakon da yake bata na sha ashe dan cikin ne? (Domin kuwa alhamdulilah, baba Sofo na samun kulawa ta musaman, yana dan ciwoce ciwocensa na jikin tsufa, aman kuma hakan baya hanashi walwala da jin nutsuwar zama tare da wadinnan bayin Allah, ga Agaishat ba.a kwana biyu bata yi kira an bata shi a waya ba, koda bata zo ba, yana jin wani gurbi da ya rasa ya cike masa, yana jin kaunarsu tamkar ciki daya, Gukunni na zuwa ya taya shi zaman fada idan baya aiki, aukan yi shayi su sha, sannan su yi hirar rayuwa, inda Ba sofo ke bashi sirika na tsari)
Itama kunya ce ta ji kamar ta nitse kasa, ya Salam ciki? Cikin mijinta, bangonta, abin alfaharinta, yanzu Ayya ta san tana dauke da ciki take zuwa gidanta ta bararaje abinta?
Yo ita ba laulayi, dan zazabin dare dai take tabawa shima ba wani mai zafi ba, haba gaske idan ta je take samun kayan kwadayi, kuma wardugu na yawan kawo mata kayan kwadayi ,
Kanta kawai ta sada dan tsabar kunya, gashi ana cikin cuwa cuwar auren Mariama da docternta dan Nigeria, Fatimata kuwa da wani dan kasuwa mai sunna Muhamadu,
Walyn, a yanzu lamarinta, zan iya cewa da sauki, domin kuwa tana kare lamarin Ayya tun karfinta,
Abu daya ne take fama da shi dai kishinta, har yanzu ba zata iya wani kishin kissa ba, gashi wace take haukan dan ita a garin, take zuba kayan, tana zubawa makadan kudin dan sunnanta ya kara dagawa fiye da na kishiyar tata bata ma san tana yi ba, domin kuwa fitar Agaishat fita ce ta idan ta kama, idan ka ganta waje zai kaita gidansu ne, wato gidan kakaninta, ko ya kaita gidansu, wato gidan Ayyanta,
A hankali ta ci gaba da rainon cikinta, sannan ta ci gaba da fuskantar lamarin mijinta, wani lokacin daga waje za.a kuno shi ya zo ya yi ta neman fitina, wai danma ciki ne a jikinta ya yi ta jajensa sai ta yi masa gum, idannuwansa su kade masifa kawai yake nema idan ta ki kula shi sai ya shiga mota ya bi cikin gari ko ya tarda walyn , ita kuwa har yanzu ta kasa gane lamarinsa sai ta biye masa ko ta hanyar korafin ita dan ya tsaneta ne yake mata haka, ko kuwa sakma ta mike ta maida martani, wani lokacin ya tumurmusheta wani lokacin ya mayar da ita tamkar doki ba abinda ya dame shi,
Cikinta na da wata shida aka yi auren su Mu.azam, nanma an sha darga domin cewa ya yi bata yi masa barka ba ko ta ji haushin Mu.azam ya yi aure?
Murmushi kawai ta yi masa sannan ta mike ta bara masa wajen, bafa wani laushi ko a kanta, danma tana cin albarkacin cikin jikinta sam baya gigin taba lafiarta ko ya yi mata fadan da zai sakata kuka
A haka aka yi auren yan matan Anna biyu, inda Ayya ta zama aminiya kuma kirjin biki, domin kuwa ita ta sada Mariama har garin iyayen mijinta kafin su daga ta damka amanarta, inda Agaishat ta yi ta fushin ba.a tafi da ita ba, harda kukanta, aman lokacin sai aka yi ta rarashinta domin kuwa ciki ya tsufa sai fitintinun masu ciki kala kala,
Cikinta nada wata tara da sati daya wani yamacin alhamiss suna tafiya da Wardugu a tsakar tankamemen gidanta ya rike hannunta suna dan takawa dan kafafuwanta su rage kumburi, da kuma yanda docter tace da ita su ringa tafiar kafa idan haihuwar ta kusa zata samu saukin nakuda,
Sanye take da irin kayan indiyawan nan riga da wando blue, manya ne sosai domin ba daidai da ita bane, tunda cikinta ua taufa suka zama suturarta , ciki take bulmuya ta yi ta yawa abinta,
Hannunta rike da kasar da take sha a boye tana so ta sha tana tsoron ya gane abinda take boyewar su casu a wajen nan, ta ji ciwon bayan dake sandarta sai kara yawa yake,
Dan dakatawa take dan yi idan ya lafa sai kuma su ci gaba da tafia, yana mata labarin abin dariyar da yake gannin na dariya ne, wanda ita kuwa binsa dai take ta yi dariyar dan kuwa du abin wani fadansa ne da wani, wani rikici da suka yi dai da sauransu, du ba wani abin dariya saima abin tsoro da mamakin irin yanda fada ke saka shi nishadi da take,
Ji ta yi wani irin das das das tun daga bayanta yake sarawa har ya sauka kafafuwanta sannan lokaci guda cikinta ya wani irin hautsina ya rikide da wani irin ciwo tsakurw tsakure gefe gefe kafin ya garwaye ta rasa takamaiman indama zata ce yanai mata ciwon.
Da sauri ta tsaya, tana son dukawa aman ina, wani yawu ta ji a bakinta na wuya mai wani taste daban, sannan wata zufa ta karyo mata,
Da sauri ta damko hannunsa da wani irin riko mai karfin gaske, hakan ya saka shi juyowa da dan sauri yana dubanta,
Yanda ya ga tana faman kaiwa gurfane ne ya saka shi tarota jikinsa yana mai tambayarta lafia? Menene??
Da kyar ta iya juyar da kanta ta ce" Wardugu , zan mutu, zan mutu,
Ido ya firfito mata kafin ya ce" ke, ba zaki mutu ba, .....
Yana fada yana dabarar yanda zai dauketa ne kar ya ji mata kuma kar ya jiwa abinda ke cikinta,
Da kyar ya sungumeta ya nufi motar da ta fi kusa inda yake ihun a bashi kys a bude masa gida,
Kanta kawai take juyawa, domin abin wani tashin lokaci guda ne ya yi mata, daga ya dan lafa sai ya kuma tashi, hakan ya sa a fili take fadin *ALLAHUMA LA SAHLA, ILAMA JA.ALTAHU SAHLA, WA ANTA TAJ.ANUL HAZNA, IZA SHI.ITA SAHLA* (ALLAH KA SAUKAR MIN KAWAR KWARAI AMINIYA SAMIRA LAFIYA , AMEN YA RAB),
haka har ya karasa da ita asibiti,
Sai da aka karbeta aka shiga da ita yana ta sintiri kafin ya tuna da Ayya, gashi ya fito ba waya ko daya a jikinsa, gashi mutane sun fara ankara da shi ne a wajen,
Waje ya samu ya zauna ya yi bakam yana kallon waje guda, adu.a kawai yake a zuciyarsa wace bai san bama me da me yake ja,
Yaren gidansa ne suka shaidawa Ayya abinda ke faruwa, dan haka bata tsaya wata wata ba ta je gidan ta dauki abinda zata dauka sannan ta bi bayansu asibitin da take awo dan ta san can za.a kaita haihuwa, asibitinsu ta sojoji
Zaune kawai ta tarar da shi, hakan ya sa ta zauna tana tambayarsa yaya dai??
Dago da kansa ya yi a raunane yana dubanta ya ce" Ayya, wai wai cewa ta yi mutuwa zata yi, Ayya idan ta mutu ni kuwa na yi yaya?
Ayya ta girgiza kanta tana dubansa ta ce" Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi Wardugu, aman kuma zafin ciwo ne ka ji? Mu yi mata adu.a in sha Allah zata sauka lafia,
Shiru ya yi yana gyada kansa, shi kam ko ciwon kai take sai ya jishi bashi da wani anfani, wollah dan ba makoki bane, da ko yatsarta ke ciwo sai ya yi kuka, dan sosai yake jin abin a ransa, bale yanzu,
Agaishat kam ta sha wahala ba laifi, nakudar awa shida ta yi, da kyar Allah ya sauketa lafia ta haifo baby boy dinta, bashi da girma sosai domin cikinta bai yi mugun girma ba,
Zo ka ga murna wajen Wardugu Ayya da duk wani sojan da kafarsa ke cikin asibitin,
Nan da nan wajen ke ta daukan harama duda dare ne sosai, haka aka yi kiran su Gukunni aka fada masu, inda Anna ta shiga murna a cikin ranta tana tausaya yar tata da adu.ar Allah ya raya,
Wardugu kam dariya yake hakoransa waje, mutane sai murna suke taya shi, inda ya yi kiran Walyn dake baci ya sanar mata yana mai farin ciki,
Bai tsaya ya ji amsarta ba ya kashe yana ta doka kira,
Walyn kam daga saman bed din ta doko kasa, idannuwanta du ta zazaro tana kallon dakin, me me ta haihu? Ciki ne da ita daman? Daman ciki ne da ita? Yaushe har cikin ya girma? Yaushema aka yi auren? Ni ina zaune ban yi cikin ba? To walahi sai na je indiar nan nima sai na haihu!
Haka ta yi ta sambatunta wanda sam bata san halin hasadar dake cin zuciyarta ba, a wajenta normal ne, itama muradinta take fada .....
Biki ne aka yi a tsare, bikin da ya hada dangin Tubawa da na Buzaye,
Du girman gidan nan sai da ya cika ya batse,
Walyn ta sha wata danyar shada wace takanas ta tada mutun aka je dubai aka kawo mata kala uku dan ta saka ta uagawa kishiya a bikinta,
Ta sha zinariya tun daga wuyanta, hannayanta, yatsutsanta, harda ta kafa,
An sha gyaran hashi an sha mak up an kawo mahaukatan jaka da takalmi an saka sai baza kamshi ake ana daga kai inda maroka ke ta waketa, sai dai abinda ya tsaye mata a rai gannin bata ga mai jegon da yaron ba,
Wajen karfe biyu ake walima, dan haka du aka taru ana gabatarwa,
Nan Agaishat ta fito, cikin shirinta na doguwar rigar lesh mai ruwan golden,
Ta sha sarka da yan kunaye da awarwaraye sa agogo da abin hancinta kowane na zinare ,
Kwaliya yar daidai ce a fuskarta wace ta kara fitar da tsararen kuma nitsatsen kwaliyarta wace sai da Wardugu ya duba da kansa cewar babu kowa sannan ya yarda da ta fita a haka domin kuwa ta jima da aka yi mata tana son fita sai jaje yake wai ta yi kyau sai binta yake da kallo,
Ba kwaliyarta ta girgiza walyn ba, domin kwaliyarta nitsatsiya ce duda tsadar leshen da kuma su sarkar, ta san wardugu ne ya siya mata dan haka bata wani damu ba saima hura hanci da ta ringa yi ta biya marokiya na yi mata kirarin uwar gida,
A lokacin da aka fara rabon kyauta wa du wanda ya zo , a lokacin ta haukace da mamaki, kyautar daga kakar Agaishat, bata ifasa sarewa ba sai da ta ga wacece kakar ta agaishat, Matar GUKUNNI? ita ta haifi mahaifiyar Agaishat,
Ambulop ce ake baiwa mutane dauke da kudi, sai ka buda ka ga adadin abi da aka baka, nan da nan wajen ya kara rikicewa da murna da shewa, kamar da wasa aka fasa zuzuta walyn din , kudi ya karbe hasken nata, nan da nan maroka sai suka gane bikin wanda suka zo suka juyar da akalar wasawar zuwa ga amarya shalele,
Basu kara sarewa ba sai da garar amarya ta shigo, wace iyayenta sukaiwa ango,
Ba wai wani abinda ba.a taba gani bane aa, abin ne ba.a yi zaton za.a yi shi haka daga wajen amaryar ba, inda Ayya ta zagime itama ta bada kyauta wa yaron da ya ci sunna *ABDALLAH* Bawon Allah, da kuma mahaifiyarsa,
Haka aka gabatar da kyautar da Wardugu ya dankara mata, aman bai yiwa yaronsa kyautar komai ba, ya dai yi dogon rubutu na saka albarka,
Kai bude bude ne ya cike gidan, inda ba wanda ya san fitar Walyn sai kofa...
Bayan wata bakwai.....
Rarafowa ya yi ya karaso kusan kafarsa,
Ya kama kafar ya mike ya rike kafar da kyau sannan ya washkale da dariya yana duban Wardugu dake zaune yana kada kafa ya gama tashin hankalin ba zata je wajen sunnan matar Mu.azam ba, ita kuwa tace a na me? Ba.a zumunci su ke kai kawo hanya?
Ai kuwa ya hayayako yana fadin" Orronur ni ne sai me? Ni ne sai me? Bara na gwada maki sai me!
Da gudu ta afka dakinta ta dani kofar tana kilkila dariya ta kuga ta ce" Wardugu bana son duka
Shi kuwa daga zaunan da yake ya saki murmushi ya dauki yaronsa dake ta bangalar masa dariya ji yake wasa ne ake masa ya rungume a jikinsa kafin ya ce" ORRONUR, BA DAI NI NE WARDUGUN BA KO? KUMA NI NE SAI AN JE DIN KO? BA ZAN DAKE KI BA, AMAN WALAHI CIKI ZAN JARA MAKI!
IDO ta zaro kafin ta shiga kiciniyar bude kofarta dan zuwa ta baiwa mijinta, amininta, yayanta, ubanta, masoyinta, abokin wasanta hakuri ta rarashi abinta cikin hikima....
Tamat bi hamdika👏🏻👏🏻👏🏻