Amsar takardun hannunshi Adebayo yayi yana fad'in haba Sir muje na ajeka. Alhaji yace ka barshi ba gida zanje ba Mr. Kallah ne yake nemana. Adebayo yace muje na ajeka kawai. Murmushi kawai Alhaji yayi ya bishi yana fad'in kaima har ka tashi ko? Adebayo yace bana jin dad'i zanje na kwanta.
Mota suka shiga Alhaji yace amma dai ka duba masu aiki yau saboda ance kaya zasu zo. Adebayo yace munyi magana dasu kila cikin dare kayan zasu zo. Alhaji yace da kyau. Shiru sukayi har suka isa ya ajeshi yayi masa sallama.
Sai wajen k'arfe shad'aya Mr. Kallah ya bar Alhaji Mai Wada domin yasan zuwa lokacin bazai iya komawa wajen aiki ba dole ya nufi gida, duk da yawancin firar labarin yanda tsarin aikin yake yake ta fad'a masa, tun Alhaji yana ganewa har ya gaji, sosai yake jin bacci.
Direba Mr. Kallah yasa ya mik'a Alhaji gida, beyi musu ba domin shima baya buk'atar hawan motar haya. Kai tsaye gida yawuce, godiya yayi ma direba hada kud'i ya bashi kafin ya shige ciki.
**** ****
Washe gari da safe Malan Sani ya iso, alokacin har Alhaji ya shirya dan ya k'osa yaje yaga abinda ya faru. Bayan sun gaisa ya tambayi mai jego. Malan Sani yace lafiya lau ya gajiyar aiki? Alhaji yace akwai ta fa.
Kud'i ya bama Madu kafin sukayi masa sallama suka tafi. Lokacin da suka isa Alhaji yace ya tafi da motar idan ya gama zai kirashi. Malan Sani yace Alhaji da ka barni na zauna anan ai. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nima zanso zamanka anan, amma saboda hidimar da take gaban ka gara ka tafi, idan akayi suna sai ka fara zama a wajen aiki.
Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in nagode. Kayansa ya d'auka ya bishi abaya zuwa ofis. Bayan sun gaisa da Malan Bala Alhaji ya gabatar da Malan Sani a wajenshi. Malan Bala yace gaskiya nayi farin ciki da zuwan ka, ya masu jego? Malan Sani yace lafiya lau suke ya aiki? Malan Bala yace gashinan munayi. Malan Sani yace Allah ya taimaka ni zan wuce. Alhaji yace shikenan sai kaji ni.
Bayan da ma'aikata suka gama shigowa suka gaisa da Alhaji sai ga *Peter* wanda shine shugaban masu kula da kayan da ake saukewa. Bayan sun gaisa ya mik'a ma Alhaji takarda yana fad'in jiya wajen k'arfe 2:00 kayan Alhaji Marusa suka iso, na duba abinda ya samu sai muka sallame su kafin kazo ka gama dubawa.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in bara na kammala aiki sai nazo na duba. Risnawa yayi ya juya ya fita. Shiru Alhaji yayi yana nazarin yanda zai b'ulloma Alhaji Marusa idan har ya kamashi da laifi acikin kayansa, domin yasan babban mutum ne, karo dashi bazaiyi kyau ba, amma dole ya tsaya domin ya tabbatar da gaskiya.
Bayan daya gama komai yasa aka kira masa Adebayo, bayan ya iso suka fita tare da wasu ma'aikatan. Tunda suka isa Alhaji yasan an tab'a kayan, haka yasa aka fara bincika kayan, sai dai abun mamaki babu komai na laifi aciki. Adebayo yace ai na fad'a maka Alhaji Marusa baya shigo da kaya masara kyau.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in bazan tabbatar ba sai na gama bincike. Adenayo yace bincike kuma? Na d'auka za agama komai abasu kayan su ai. Alhaji yace ka sani ko akwai haramtattun kaya aciki kafin muzo aka cire? Da sauri ya kalli Alhaji yana had'iyar miyau.
Dafashi Alhaji yayi yana fad'in wasa nake maka, bayan yanzu muka gama dubawa kuma babu komai, amma dai zan sake bincike idan na tabbatar da komai lafiya sai abasu kayansu bayan sun gama biyan komai kamar yanda doka ta tanadar. Adebayo yace ai Alhaji Marusa baya kin biyan kud'in kaya, domin yasan yanda dokar take. Alhaji yace haka akeso ai.
Cikin dabara Alhaji ya ciro abinda yasa kafin ya nufi ofis, mukulli yasa ya kulle ya fad'ama Malan Bala duk wanda yazo yajirashi zai shiga band'aki ne. Malan Bala yace angama Alhaji.
Zaune yayi yana kallon abun mamaki, faskar Adebayo ya gani shida wasu ma'aikata hada Peter da yaran Alhaji Marusa suna ta aikin jidar wasu kwalaye wanda besan meye aciki ba.
Lokaci ya duba yaga k'arfe 3:30 na dare. Mamaki yayi ganin duk saboda su cire wad'an nan kaya ne suke tsaye a cikin dare. Gaskiya duniya ba gaskiya.
Bayan ya gama gani ya kashe dan ya baro (flash) d'insa agida bare ya tura aciki, dirowa ya jawo ya saka kemarar acikin jakarta kafin ya tashi tafiya. Tashi yayi ya bud'e k'ofar yana tambayar Malan Bala ko akwai wad'an da suka zo nemansa? Malan Bala yace Oga Adebayo yazo shida Umar.
Alhaji yace kaje ka kirasu. Bayan sunzo Adebayo yace dama Alhaji Marusa ne yakira waya idan angama duba kayan yana buk'atar su. Alhaji yace bana tunanin bada kayan nan yanzu domin bangama yarda dasu ba. Kallonshi sukayi cike da mamaki.
Alhaji yace akwai fararen kwalaye guda bakwai da akazo dasu wanda nasan da zuwansu sai gashi kuma ban gansu ba, kaga dole mu gano inda suke domin amana Alhaji Marusa ya bamu akan kayansa, yanzu idan yaji acikin kayan babu wasu bayan kuma anzo dasu har nan ai dole yashiga damuwa, kuma tunda naga sun b'ace na tabbatar suna da tsada da muhimmanci shiyasa akayi kokarin sace su, dan haka dole muyi bincike mu gano komai tun kafin Alhaji Marusa yasan da maganar, domin hakan zai iya tab'a aikin mu.
Zufa ce ta fara keto masu jin abinda Alhaji ya fad'a. Adebayo ne yayi kok'arin fad'in gaskiya Sir, babu wasu kaya da suka b'ace, domin Alhaji ya fad'a mani duk abinda yake ciki, kuma na d'auki hoto na tura mashi yace komai haka yake, kila dai ba'a fad'a maka da kyau bane.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in sai da na tabbatar kafin na fad'i haka, dan haka ka fad'ama Alhaji Marusa yayi hak'uri kayansa zasu iso zuwa wani lokaci akwai abinda ba'a gama ba.
Umar yace Alhaji ni ina ganin tunda shi Alhajin yace haka kayansa suke kawai mu bashi, idan ba haka ba zamu jawo ma kan mu wajen son bincike. Alhaji yace tunda nine nace zanyi binciken kawai kuje. Fita sukayi jiki a sanyaye.
Bayan sun koma ofis Adebayo yace ya akayi Sir, yasan da kwalayen da muka cire? Umar yace nima nayi mamaki, kodai wani munafukin ya fad'a masa ko cikin wad'an da mukayi aikin tare akwai wanda ya turo? Adebayo yace bana tunanin haka, dole akwai abinda yayi, domin duk cikin mutanan da mukayi aiki dasu kowa yana da amana, kuma kafin mu fara sai da na tabbatar babu kowa, dole akwai abinda yayi dai.
Umar yace to yanzu ya za'ayi, kada fa ya tona ma Alhaji Marusa asiri ba k'aramun kunya zaiji ba domin kasan kayan da suke cikin kwalin, gashi babban mutum. Adebayo yace Omar bari nashiga tunani dole na gano abinda Sir, yayi, idan yana tunanin zai iya kama mu zamu gani, domin na buga da wanda yafishi.
Dariya Umar yayi yana fad'in dad'ina da kai akwai basira, duk yanda aka k'ulle abu kana iya warwareshi, shikenan bara na barka kayi nazari. Bayan ya fita Adebayo ya kira Alhaji Marusa ya fad'a masa halin da ake ciki.
Sosai hankalinsa ya tashi, nan yace ma Adebayo duk yanda zasuyi kada su bari asirinsa ya tonu, akwai kyauta mai tsoka matuk'ar suka kashe maganar. Adebayo yace angama Alhaji, kasanni akan kud'i bani da wasa, zan iya yin komai.
****
Bayan la'asar Alhaji Mai Wada ya samu kira daga sama, Mr. Kallah ne ya kirashi yana tambayarsa abinda yasa basu sakar ma Alhaji Marusa kaya ba har yanzu? Alhaji yace Mr. Kallah akwai abinda na gani ne shiyasa nakeso ayi bincike kada mu bashi kayan bayan akwai cuta aciki.
Mr. Kallah yace wace irin cuta? Ka ce da kai aka duba kayan kuma babu komai aciki taya yanzu zaka kawo wata magana, tsaya kaji Alhaji Mai Wada, baza kazo ka kawo mana matsala ba, kowa yasan yanda aikin nan yake, matuk'ar aka duba kaya babu matsala, kuma mai kaya ya biya komai abisa k'aida to dole ne abashi kayansa, dan haka na baka nan da awa d'aya ka sakar masa kayansa.
Dafe kai Alhaji yayi yana fad'in Mr. Kallah ka tsaya nayi maka bayani, ana aikata binda bai dace ba, ana shigowa da kaya haramtattu idan bamu tsaya muka gyara ba tofa kan mu cutar zata dawo, domin idan ta tab'a yaran mu kamar ta tab'a mune, Allah kad'ai yasan abinda aka shigo dashi, ina da shedar da zan nuna maka ka tabbatar ina da gaskiya, kuma wallahi kaji na rantse komin girman Alhaji Marusa dole hukuma ta hukuntashi kuma sai tacisa tara, domin ya karya doka.
Ajiyar zuciya Mr. Kallah yayi yana fad'in wace irin sheda kake da ita fad'a mani? Alhaji yace bazan fad'a maka yanzu ba, amma zan kawo maka ka gani da kan ka, kuma ba kai kad'ai zaka gani ba dole sai an had'a taron manya kafin na fito da shedar.
Mr. Kallah yace shikenan Alhaji bazan hanaka aikin ka ba, wannan abun da kayi yana da kyau, nima na d'auka babu wata matsala a kayan shiyasa nashiga maganar bayan da Alhaji Marusa ya fad'a mani, amma tunda kaine shugaba a wajen bazamu hanaka aikin ka ba, domin irin ku k'asa take nema, bakomai Allah ya taimaka kayi aikin ka a natse. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nagode Yallab'ai.
Bayan ya kashe wayar yayi shiru yana tunanin ashe dai Mr. Kallah mutumin kirki ne, ya d'auka shima yana goyan bayan su ne, tunda har ya bashi goyon baya dole a gobe ya mik'a abinda ya d'auka manya su gani kafin a mik'a Alhaji Marusa kotu domin acan ne za'a yanke masa hukunci dai-dai laifinsa, kuma dole ya fito da kayan da aka b'oye domin asan abinda yake ciki.
Haka ya wuni yana aiki sallah kawai take fitar dashi, abinci ma anan Malan Bala ya kawo masa yaci. Har sukayi magriba kafin Malan Sani yazo ya d'aukeshi, sai da ya d'auki komai nashi hada kemarar kafin suka tafi.
****
Washe gari tunda safe ya kira Adebayo akan ya kula da ofis bazai samu zuwa da wuri ba zaije wajen taro. Murmushi Adebayo yayi yace sai ka dawo Sir.
Koda suka isa can babbar hedikwata haka Malan Sani ya koma gefe yana jiran Alhaji, kai tsaye Alhaji ya nufi hanyar shiga, yana dab da shiga wayarsa tayi k'ara. Yana dubawa yaga Mr. Kallah ne, saurin d'auka yayi. Bayan sun gaisa Mr. Kallah yace Alhaji Mai Wada ka sameni a ofis d'ina yanzu, akwai maganar da nakeso muyi dan ban fad'a masu zakazo a zauna ba. Alhaji yace shikenan gani nan zuwa. Mota yashiga suka nufi ofis d'in Mr. Kallah.
Kallonshi Mr. Kallah yayi yana fad'in Alhaji Mai Wada nasan ka dad'e kana wannan aikin, kasan kuma yanda halin k'asar mu take, k'ananan mutane ma ka kalli yanda ake gogawa dasu bare kuma manya, nasan kasan kad'an daga cikin labarin Alhaji Marusa, babban mutum ne shi, bana so kaje kayi abinda zaisa mutuncinka ya ragu, kome zakayi ka tabbatar kana da kwakkwarar sheda kafin kayishi, ko kotu kaje idan baka da sheda kwakkwara kotu tana watsi da k'ara, ajiya ka fad'a mani kana da sheda akan abinda ka fad'a, nace ka fada mani amma kace sai kazo, gashi kuma baka fad'a mani ba amma kake kok'arin kai shedar gaban Manyan mu, wannan dalilin ne yasa ko ajiya daka kirani kace na fad'a masu zaka zo na amsa maka kawai, amma babu wanda na fad'ama wannan maganar, koshi Alhaji Marusan besan kana da wata sheda akanshi ba, shiyasa kaji nace kazo domin mu fara gano komai kafin mu mik'a maganar sama.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in wannan gaskiya ne, ya kamata ace mun zauna mun had'a komai kafin afitar da maganar, domin ance idan baka iya kama b'arawo ba shi sai ya kamaka.
Hannu yasa ya ciro kemara yana fad'in ajiya ma naso na tura a (flash) sai kuma bacci ya d'auke ni, da safe kuma na manta kawai na taho da ita. Kunnawa yayi ya mik'a ma Mr. Kallah yana fad'in tun lokacin dana samu labarin kayan zasu iso cikin dare nayi niyar tsayawa ayi komai agabana, sai kawai na samu kira daga wajenka, hakan ya b'ata mani rai, har nayi tunanin wani abu, to da zan tafi sai na mak'ala wannan kemarar domin ina zargin wani abu, washe gari dana zo aka duba kaya babu komai na laifi aciki, bayan dana koma na duba kemarar sai na gano ajiyan an cire wasu kaya kusan kwalaye bakwai wanda bansan abinda yake ciki ba, kuma na tabbata kaya ne marasa kyau aciki, gashinan ka duba zakaga abinda na gani.
Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad'in Alhaji ai banga komai aciki ba, duhu kawai nake gani babu komai aciki. Da sauri Alhaji ya mik'e ya amshi kemarar yana dubawa, ya duba ko ina amma babu abinda ya d'auka aciki sai wata d'auka da akayi ta kusan mintuna talatin amma kuma duhu ne aciki, lokaci ya duba sai yaga k'arfe 1:30 ne lokacin sallar azahar.
Komawa yayi ya zauna jiki a sanyaye kamar an zare masa lakka. Kallonsa Mr. Kallah yayi yana fad'in kaga abinda nake fad'a maka ko? Yanzu da ace kaje agaban mutane ka gama wannan bayanin kazo kunna masu sukaga wannan abun ai zasuce kayi wasa da tunanin su ne, babu wanda ya tab'a kawo k'arar Alhaji Marusa, yanzu idan kaje ka kai kuma ka kasa kawo sheda me kake tunanin za'ace? Tun daga ranar za'a dena gazgataka, ko wata rana kazo da wata maganar bazasu d'auketa da muhimmanci ba.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in nagode da wannan taimakon da kayi mani, insha Allahu dana koma zan sakar masa kayanshi. Mr. Kallah yace bakomai ka k'ara kiyayewa, aikin kwastam akwai had'i acikinsa. Tashi yayi ya bashi hannu kafin ya fita.
Tunda suke tafiya yayi shiru, gaba d'aya kanshi ya d'aure, tabbas wani ne yashiga ofis d'insa ya goge abinda ya d'auka aka d'aukar masa wannan abun, amma *WAYE NE* (tsohon littafi na) yayi masa wannan abun? Babu wanda yasan ya d'auki wannan abun amma gashi an goge masa, da ace ya fad'ama Mr. Kallah yayi d'auka da sai ya zargeshi.
Hannu yasa ya dafe kanshi. Tabbas maganar Mr. Kallah gaskiya ce, aikin kwastam akwai had'ari acikinsa, kuma ya godema Allah da bai kai wannan shedar ba, dole ya sake sabon taku, domin Lagos tasha ban-ban da sauran wajen da yayi aiki, Lagos shu'umin gari ne, k'aramin yaron daya taso acikinta ma sai yayi maka wayau.
Malan Sani ne yace Alhaji kamar akwai abinda yake damun ka ko? Ajiyar zuciya yayi yana fad'in Malan Sani duniya babu gaskiya, son kud'i ya rufema mutane ido, zasu iya aikata komai akan kud'i, wani babban al'amari ne ya faru ajiya zuwa yau, amma na faad'i, domin ban samu damar aiwatar da aikina ba. Ai kasan Alhaji Marusa ko? Malan sani yace sosai kuwa, a Lagos waye bai sanshi ba........
Labarin abinda ya faru Alhaji ya bashi. Sosai Malan Sani ya tausaya mashi, kallonsa yayi yana fad'in Alhaji haka Lagos take, shiyasa nake tausayin bakon daya zo cikinta, mutane da yawa suna shan wahala idan suka zo Lagos kafin su waye da ita, haka idan aiki ya kawo ka nan matuk'ar baka da masaniya akan komai kana shan wahala, wasu sun sha rasa ransu akan aikin su, a tunani na dad'ewar da kayi kana aiki zaka iya aiki a Lagos, domin nasan ka zagaya garuruwa da yawa.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nima haka nayi tunani Malan Sani, ashe abun ba haka yake ba, duk yanda na d'auki Lagos ta wuce tunani na, shiyasa tunda nazo nake taka tsan-tsan da mutane, domin nasan yanda cin amana yayi yawa.
Malan Sani yace Alhaji maganar gaskiya kada ka sake yarda da kowa, ni jikina ma be yarda da Mr. Kallah ba, tunda kace mani yace kaje nasan akwai wani abu, dole akwai abinda ya sani shiyasa ya kira ka domin baya so kaji kunya, sai yayi amfani da wannan damar domin yasa ka yarda dashi.
Kallon Malan Sani Alhaji yayi cike da nazari. Kai Malan Sani ya jinjina kafin yacigaba da tuk'i yana fad'in Adebayo shu'umin mutum ne, kasan yaren mutum da kud'i, duk da bansanshi ba, amma labarinsa daka bani yanzu yasa na fahimceshi, bazan ce ga wanda nake zargi ya bada damar shiga ofis d'inka ba, domin nasan idan zakaje sallah dole ka rufe odis d'in ka, amma dole sai ka sake lura Alhaji.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in nagose sosai Malan Sani, hakika Allah ya had'a ni da abokin shawara, na yarda da kai, kuma daga yau bani da abokin shawara sai kai, insha Allahu zanyi kamar yanda kace, da sannu sai na gano gaskiya kuma sai na tabbatar da ita, wallahi kaji na rantse maka sai na tabbatar da ainihin fuskar Alhaji Marusa, domin fuska biyu yake da ita, amma zan kwantar da kai domin na samu damar aiwatar da komai cikin sanyi.
Malan Sani yace wannan haka yake, idan mage zata kama b'era kwantar da kai takeyi har sai ta cika burinta, dole sai kayi hak'uri kafin ka tabbatar da gaskiya. Alhaji yace nagode sosai.
Bayan da ya ajeshi ya wuce ofis, sam be nuna komai ba, haka yakira Adebayo yace a saki kayan Alhaji Marusa. Risnawa yayi yana fad'in angama Sir.
Bayan da ya dawo sallar azahar ya iske wasu mutane suna jiranshi. Izinin shiga ya basu. Bayan sun gama gaisawa d'aya daga cikinsu yace sunana Brr. Barau daga babbar kotu, wannan abokin aikina ne Brr. Hamza.
Alhaji yace madalla sannun ku da zuwa, akwai wani abu da kuke buk'ata ne? Brr. Barau yace wani mutumi ne ya shigar da k'ara a kotu saboda wani zalunci da akayi masa, ya kasance yana shigo da taliya dasu makaroni da sabulai daga waje, yau kusan sati d'aya kenan kayansa suka iso, yace ya biya komai amma kuma da aka tashi sakar masa kayan sai aka bashi ba yanda suke ba, wanda hakan ya jawo masa asara sosai, shine yashigar da k'ara, da muka duba sai naga a wajen ku ne, kuma ni ina mutunci da ma'aikatan wajen nan, wanda ya bar wajen ma nine Lauya d'inshi, hakan yasa nace zanzo domin naji yanda gaskiyar abun take, domin mutumin ya d'auko lauya, ni kuma ina giramama ofis d'in ku shiyasa nace zan tsaya maku domin a wanke ku daga zargi, dan idan har akayi shari'ar aka tabbatar daga cikin ku wasu sun danne masa kaya tabbas mutuncin ku zai zube, gashi kai sabon zuwa ne a nan baka gama sanin komai ba, idan akace ma baka da labarin abinda ya faru baza'ayi gardama ba, domin an fad'a mani ajiya ne ka fara sabon tsari.
Cike da mamaki Alhaji yake kallonsu, ak'asan ranshi yana fad'in kaji wata sabuwa kuma. Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in kada ka damu Alhaji, ni da ku babu wani shamaki domin akwai taimakekeniya atsakanin mu, tsofaffin ma'aikatan wajen sun san da haka, domin kowa ya sanni, dan kana sabon zuwa ne, amma shi Adebayo mutumina ne sosai, dan haka kada ka damu a shigar farko zan kada su, domin ni shari'a cin abinci ma yafi mani wahala akanta, domin ni haka nake, wasu ma da *MAI NASARA* suke kirana. (Tsohon littafina,)
Murmushi Alhaji yayi danshi ya ma rasa bakin magana. Tashi Brr. Barau yayi yana fad'in kada ka damu, wannan itace takardar sammaci daga kotu, zuwa ranar litinin za'a shiga, sai kayi kokarin gano wad'an da suka aikata hakan idan baka da masaniya domin kaja masu kunne, zanyi magana da Adebayo sai mu k'arasa komai dan naga baka gama warware wa da wajen ba, gashi lokaci ya k'ure dole muyi sauri domin mu kare mutuncin ku, saboda kai d'in sabon zuwa ne bazamu so ka fara da haka ba.
Kai Alhaji ya jinjina danshi gaba d'aya kanshi ya k'ulle, beda masaniya akan komai, bazai iya shiga abinda bai sani ba, dole ya zuba masu ido yaga abinda zasuyi dan shi yanzu yanda zai b'ullo ma Alhaji Marusa kawai yake damunsa.
Hannu Brr. Barau ya bashi yana fad'in sai ka jini mungode da lokacin daka bamu. Alhaji yace bakomai nagode. Bayan sun fita Alhaji yashiga dogon tunani, tabbas lokacin da aka aikata wannan abun beda masaniya, yanzu shikenan haka za'a danne ma bawan Allah kayansa kuma kotu ta bashi rashin gaskiya? To idan ma yace zai taimaka mashi ta yaya? Dole wannan karon ya aikata laifi kodan kare mutuncin aikin su, amma matukar aka gama da kotu saiya gano wad'an da suka aikata wannan abun kuma sai ya d'auki mataki, dole yajira litinin yaje kotu yaji komai.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263.*
0⃣7⃣
Tafe suke a mota ya kalli Malan Sani yana fad'in wato Malan Sani idan kana da rai zakayi ta ganin abubuwan al'ajabi. Malan Sani yace wani abun akayi maka ko Alhaji? Murmushin gefen baki yayi yana fad'in maganar da mukayi da kai jiya itace ta rushe, an duba kemarar babu komai aciki, an samu wani mai wayon ya goge abinda ta d'auka.
Kallonshi Malan Sani yayi cike da mamaki yana fad'in amma Alhaji ya akayi haka ta faru? Alhaji yace mai son abunka yafika dabara ai, naje sallar azahar lokacin ne aka shiga ofis d'ina.
Malan Sani yace ina Malan Bala to? Alhaji yace atare muka je masallaci dashi kum na rufe ofis d'in. Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in lallai ko waye ya san takan ofis d'in. Alhaji yace ko waye yayima kansa, kuma insha Allahu matuk'ar ina raye sai na kawo k'arshen zaluncin da akeyi.
Yanzu haka ranar litinin kotu zamuje, d'azu wani Brr. Barau yazo ya kawo mani takardar sammaci wai an zalunci wani ya shigar da k'ara, kayansa ne sukazo sai aka rik'e, bayan daya amsa sai ya samu abubuwa da yawa sun b'ata, yayi asara sosai shine yashigar da k'ara, abinda na lura dashi Brr. Barau ya dad'e yana ma ofis d'in mu aiki, da alama shid'in marar gaskiya ne.
Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in Alhaji waye besan Brr. Barau ba, wannan mutumin idan beyi wasa ba sai yaci wutar Allah, duk wata k'ara da aka kaita babbar kotu matuk'ar mutum ya saki kud'i Brr. Barau zai tsaya masa, kafin a kadashi a shari'a da wuya, shi kuma Alkali kwakkwarar sheda yake nema, matuk'ar ya sameta shikenan zai yanke hukunci, wannan adalci da Alkali yakeyi shine yasa mutane suke sonshi, duk da wani lokacin ba akan gaskiya yake yanke hukuncin ba amma babu yanda ya iya, domin abinda ya gani dashi yake aiki, kuma baya yanke hukunci sai kowa ya sheda gaskiyar abinda aka gabatar, shiyasa nake fad'a maka Brr. Barau shine babban azzalumi.
Alhaji yace abinda yake fad'a mani kenan da yazo, wai ni sabon zuwa ne shiyasa yazo da kanshi dan baya so daga zuwana na samu matsala, shiyasa yake so ya wanke mu. Girgiza kai yayi yana fad'in Malan Sani a wannan karon bani da zab'i, domin lokaci ya kure mani, idan nace bazan bi yanda yace ba tabbas nine a k'asa, domin bansan da wannan maganar ba sai zuwanshi.
Tausayi Alhaji ya ba Malan Sani, domin yasan yana son tabbatar da gaskiya amma be gama sanin kan wajen ba. Kallonsa yayi yana fad'in Alhaji kada ka karaya domin Allah yana tare da mai gaskiya, bakomai kaje kotun kaji yanda komai yake Allah yaga zuciyar ka, idan yaso daga baya sai kayi bincike.
Murmushin jin dad'i Alhaji yayi yana fad'in nagode Malan Sani, ina matuk'ar jin dad'in zamanka akusa dani, insha Allahu zanyi kok'arin bincike domin na gano gaskiya, kila ta wannan hanyar ne Allah zai haska mani komai. Malan Sani yace in Allah ya yarda.
***** ****
Ranar litinin haka babbar kotu ta cika, *Alhaji Usman* wanda shine ya shigar da k'ara yana daga gefe shida sauran abokansa tare da lauyen daya d'auko.
Alhaji Maiwada yana isowa Brr. Barau da Adebayo suka tarbeshi. Bayan sun gaisa Brr. Barau yace Alhaji komai ya kammala insha Allahu zamuyi nasara. Murmushin takaici Alhaji yayi yace Brr. Allah ya shige mana gaba. Brr. Barau yace amin.
Cikin lokaci k'ank'ani aka kammala shari'ar wanda Brr. Barau ne yayi nasara, domin ya gabatar da shedun bogi wanda kowa ya d'auka da gaske ne. Alhaji Usman kusan zubewa yayi lokacin da Alkali ya yanke hukunci, zama yayi ana ta yimasa fifitu.
Alhaji Maiwada yana zaune kamar wanda aka dasa, besan lokacin da idonshi ya cika da kwalla ba, lallai duniya babu gaskiya, yanzu shikenan an cuci wannan mutumin? Kallon Brr. Barau yayi yaga suna kashewa da su Umar da Adebayo. Murmushin takaici kawai yayi ya bar kotun ko ta kan Brr. Barau bebi ba suka tafi ranshi a b'ace.
****
Ranar Talata tunda safe Alhaji yaje ofis. Malan Sani shima be tafi ba saboda anyi suna, tunda yazo suke zaune da Malan Bala suna ta fira, a hankali Malan Sani yake tambayar Malan Bala yanda wajen yake. Haka Malan Bala yayi ta bashi labari.
Har zuwa azahar Alhaji yana bincike akan abinda ya faru, wasu daga cikin ma'aikatan da ya yarda dasu yarik'a kira yana masu tambayoyi tun daga ranar da abun ya faru.
Mutum d'aya ya samu mai suna *Abubakar*, shine mataimakin mai kula da kaya, kasancewar shima yana kwatanta gaskiya yasa ake maidashi baya tun lokacin tsohon shugabansu, musamman idan akace kaya masu tsoka sunzo.
Kallon shi Alhaji yayi yana fad'in Abubakar aranar da kayan Alhaji Usman suka zo ya akayi da aka rike masa wasu daga ciki suka b'ace? Gyara zama Abubakar yayi yana fad'in wallahi Alhaji aranar da abun zai faru Adebayo da Umar ne suka karb'i kayan, ina wajen amma sai Adebayo ya bani sako na kaima Alhaji Marusa, ban dawo ba saboda dare yayi sai kawai na wuce gida.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in dole sune suka d'auki kayan Alhaji Usman. Abubakar yace kuma sun amshi kud'i da yawa awajenshi kafin suka sakar masa kaya, kuma ina tunanin kayan nan basu raba su ba, dole akwai inda suka aje su, akwai *Moses* abokina ne yasan sirrinsu domin suna yaga masa wani abu saboda sun san halinsa, ina ganin zai iya sanin yanda akayi da kayan.
Alhaji yace Abubakar kira mani shi Allah yasa ya bamu had'in kai. Abubakar yace kada ka damu nasan waye Moses, mutumina ne sosai. Waya ya dauka ya kirashi.
Beyi mintuna biyar ba sai gashi. Risnawa yayi ya gaishe da Alhaji. Wajen zama Alhaji ya nuna masa, bayan ya zauna Abubakar yayi masa bayanin abinda Alhaji yake buk'ata.
Murmushi Moses yayi yana fad'in Sir, wannan abu ai ya dad'e yana faruwa a wajen nan, tun lokacin da nazo Oga John yake abinda yaga dama shida su Oga Adebayo, Omar shima baya da gaskiya, saboda sun san nasan komai yasa suke yaga mani kasona, Sir kasan zuciya da kud'i shiyasa nima nake amsa, amma wancan ranar da suka sace kayan Alaji Osman ni nasan inda suka b'oyesu, sunce sai anyi kamar wata d'aya ko biyu komai ya wuce sai suzo cikin dare su kwashe abunsu su raba, acikinsu akwai wasu ma'aikatan da suke bin bayan su. Sir ina fad'a maka a wajen nan fa akwai b'arayi, ni dai bana sata, amma idan aka bani ina amsa
Alhaji yace yanzu Moses a ina suka aje kayan? Moses yace Sir, zan fad'a maka amma du Allah kada ka beri su gano nine na fad'a maka, ina son kud'i kuma idan suka gano bazasu rik'a bani ba.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in zan rubuta sunanka acikin wad'an da zan dakatar har na tsawon watanni biyu kuwa, domin kana amsar cin hanci wata rana zaka fara d'aukar kayan wasu.
Zubewa Moses yayi yana fad'in du Allah Alaji ka rufa mani asiri, wallayi daga yau zan zama kamar Abubakar, zan rikayin gaskiya. Alhaji yace naji, amma idan na gano kacigaba da karb'ar cin hanci sai na dakatar da kai. Tashi Moses yayi yana murza hannu yace na yarda. Nan ya fad'a masu inda kayan suke.
Jinjina kai Alhaji yayi yace suje. Bayan sun fita yayi shiru yana tunanin yanda zai b'ullo ma al'amarin, baya so ya watsa ma Brr. Barau k'asa a ido, domin idan yace zai bayyanar da gaskiya tamkar yaci masa fuska ne, amma dole ya hukunta duk wanda yake dasa hannu a cikin wannan abun.
Waya ya d'auka yakira Adebayo. Ba'afi mintuna biyar ba sai gashi ya shigo yana ladabin munafurci. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in Adebayo na samo inda kayan Alhaji Usman suke, kuma za'a mayar masa da abunsa.
A zabure Adebayo ya mik'e yana fad'in Sir, waye ya fad'a maka inda suke? Alhaji yace kasan b'oyesu akayi kenan? Zama yayi jiki a sanyaye yana fad'in Sir, ba haka bane, naga an gama komai a kotu be kamata amaido maganar baya ba.
Tashi Alhaji yayi yana fad'in na baka nan da anjima ka rubuto mani sunayen wad'an da suke dasa hannu a abinda kukayi, a sunan farko kasa naka dana Umar.
Hannu Adebayo yasa yana goge zufa, hannuwa yahad'e yana fad'in Sir, kayi hak'uri, shikenan zan fito da kayan amma kada a koma kotu domin zamu iya rasa aikin mu kuma za'a iya kaimu gidan yari.
Alhaji yace abu d'aya zakayi, matuk'ar ka rubuta mani sunayen wad'an da suke dasa hannu a abinda kukayi to bazan kai ku kotu ba, amma ina da sharad'i wanda dole ne ku bishi.
Da sauri Adebayo yace yanzu zan fad'a maka, mu biyar ne hada Omar, kuma zamubi sharad'in ka. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in doka zata fara aiki daga kanku, sai dai zan maku sauki zan dakatar da ku na wata d'aya kawai, sannan zanyi magana da Alhaji Usman, idan ya yafe maku shikenan, idan kuma yace sai an koma kotu bani da zab'i.
Cike da damuwa Adebayo yace ka bashi hak'uri kayansa suna nan babu abinda muka tab'a amma kada a koma kotu. Alhaji yace tashi kaje zamuyi magana dashi. Jiki a sanyaye Adebayo ya fita.
Bayan ya fita Alhaji ya d'auki waya ya kira Alhaji Usman domin ya samo lambarsa. Koda ya d'auki wayar ya gane har lokacin yana cikin damuwa. Bayan sun gaisa yayi masa bayanin kansa, cike da masifa Alhaji Usman ya fara magana, sai da ya gama Alhaji yace idan zaka yarda ina son ganinka amma agida, domin maganace akan kayanka dana gano, amma inaso kayi shiru kada ka fad'ama kowa. Cike da farin ciki Alhaji Usman yace kayi hakuri ban fahimceka daga farko ba, shikenan zaka iya zuwa anjima bayan sallar isha'i. Alhaji yace shikenan ka turo mani da kwatancen gidan ka. Sallama sukayi ya kashe wayar.
***
Bayan sallar la'asar su Umar da sauran mutane ukkun da Adebayo ya rubuta sunan su suka hallara ofis d'in Alhaji. Bayan ya gama masu bayani duk suka shiga bashi hak'uri. Alhaji yace bana magana biyu, kunci sa'a da na rage maku wata biyu, sannan zanyi kok'arin kare mutuncin aikin ku, amma daga yau idan na sake kama ku da aikata makamancin wannan abun to maganar sai taje sama.
Idan kunso zaku iya tona asirin ku, amma ni dai babu wanda zan fad'a mawa, kuma bazan dakatar da albashin ku ba domin daga banki yake zuwa, matuk'ar nace zanje adakatar dashi dole sai manya sun san da maganar, amma ni zan yanka ma kowa abinda zai bayar a bama Alhaji Usman amatsayin tara, domin wannan shine adalci, kuma baza ku zo aiki ba har sai nan da wata d'aya, sannan kowa acikin ku zai bayar da dubu hamsin ga Alhaji Usman domin kun jawo masa asara, ko ya amshi kayanshi wasu kud'in bazasu dawo ba, idan kuma kuna ganin wannan abun beyi maku ba, shikenan sai muje kotu ta yanke maku hukunci.
Gaba d'aya suka had'a baki wajen fad'in sun amince. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in da kyau, daga yau ba sai kun sake zuwa aiki ba, kowa yaje ya huta. Adebayo yace Sir, ka barmu muzo aiki wasu zasu iya gano wani abu. Umar yace dan Allah Alhaji ka rufa mana asiri abarmu muyi aiki sannan zamu bayar da kud'in.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in shikenan, tunda wannan shine karo na farko dana fara kama ku da laifi zanyi maku uzuri, amma akan biyan kud'i babu uzuri, sannan zan rubuta na ba kowa yasa hannu akan duk lokacin da aka sake kamaku da irin haka babu sauran uzuri. Gaba d'ayansu suka amsa da sun amince.
Bayan da suka gama sa hannu akan kowa zai bayar da kud'in kuma sun amince da lifin da aka kamasu dashi. Haka kowa ya fita jiki a sanyaye. Adebayo da Umar waje suka samu kowa da abinda yake fad'a. Adebayo yace Omar wannan mutumin sai yasan yayi mana haka, Brr. Barau zan kira na fad'a masa komai.
Umar yace kada ka fad'a masa, kasan Brr. Barau da surutu zai iya fitar da maganar, tunda dai Allah yaso Alhaji zai rufa mana asiri to mu bar maganar. Adebayo yace shikenan, amma wallayi sai na rama kasanni ai. Umar yace ba yanzu ba, dole mu kwantar da kai har zuwa wani lokaci. Adebayo yace shikenan.
***
Bayan da akayi sallar isha'i Alhaji ya tashi domin yana son zuwa wajen Alhaji Usman. Haka suka nufi gidanshi suna bin kwatancen da ya turo masa. Malan Sani yayi mamakin abinda Alhaji ya fad'a masa, kuma ya jinjina adalcin da Alhaji yayi masu.
Zaune suke a cikin rumfar da take a harabar gidan. Bayan sun gama gaisawa Alhaji ya sake bama Alhaji Usman hak'uri akan rashin adalcin da akayi masa. Alhaji Usman yace bakomai, nima ina baka hak'uri akan abinda nayi maka awaya, duk da nasan kai d'in sabon zuwa ne amma nayi tunanin kaima irin halin tsohon shugaba gare ka, domin daga zuwanka har na fara asarar kaya.
Alhaji yace bakomai, domin ni bansan da maganar ba sai da Brr. Barau yazo mani da maganar, alokacin bani da abinda zanyi hakan yasa nayi shiru da niyar nayi bincike bayan an gama komai. Alhamdulillahi kayan ka suna nan babu wanda ya b'ace, kuma na gano wad'an da suka aikata hakan.
Alhaji Usman yace acikin su akwai Adebayo. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in kaima kasan halinsa kenan? Alhaji Usman yace waye besan Adebayo ba, dashi da Mr. John halinsu d'aya, shegu arnan banza, babu Allah aransu sai cuta.
Alhaji yace nazo neman wata alfarma awajenka ne Alhaji, nasan zeyi wuya kayi mani ita, amma ina rokon ka da ka dubi girman Allah ka amince da abinda zan fad'a maka.
Alhaji Usman yace babu abinda zaka nema awajena banyi maka shi ba, domin kayi mani abinda Kotu ta kasa tayi mani, dan haka kayi maganar ka kawai.....
Bayanin abinda yake so yayi masa. Shiru Alhaji Usman yayi kafin can yayi murmushi yace saboda kai zanyi masu wannan alfarmar, domin ko alahira wani yana cin arzik'in wani, bakomai, ka d'auka baka fad'a mani komai ba, nayi maka alk'awarin babu wanda zaisan da faruwar haka, zan nuna cewar wasu kayan ne sukazo.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nagode sosai Alhaji Usman Allah ya k'ara girma. Alhaji Usman yace amin nagode, kuma acikin kud'in da zasu had'a dubu d'ari biyu da hamsin ka d'auki dubu d'ari na baka kyauta.
Girgiza kai Alhaji yayi yana fad'in hakkina ne nayi maka hakan, bana buk'atar komai. Alhaji Usman yace nima kyauta ce nayi maka ai. Alhaji yace Allah bazan amsa ba. Alhaji Usman yace shikenan na bama direban ka, domin nasan irin halinka gareshi. Alhaji yace to mungode sosai, anjima kad'an kayanka zasu iso. Alhaji Usman yace nagode.
****
Tun daga wannan rana Alhaji Maiwada yake aikinsa hankali kwance, kowa yashiga hankalinsa domin sun san Alhaji Maiwada ba wasa. Adebayo da Umar sun natsu tamkar babu su a wajen, su kad'ai sukasan abinda suke kullawa.
A yanzu duk wani wanda yake samun matsala da ma'aikatan kwastam na wajen su Adebayo yanzu hankalinsa akwance yake, domin idan kaya suka iso cikin lokaci k'ank'ani za'a duba a cike komai bisa tsari a sakar maka kayanka idan babu haramtattun kaya aciki.
Duk wanda aka kama da haramtattun kaya aciki babu batun ya bada cin hanci asakar masa, idan aka kama shikenan baza'a badasu ba. Alhaji Marusa yanzu ya dakatar da shigo da kayan da yake shigowa dasu, domin sun tattauna akan Alhaji Maiwada, sun yanke shawarar su d'aga masa k'afa zuwa wani lokaci ya gama zafin kanshi.
Kafin wani lokaci Alhaji Maiwada yayi suna a Lagos musamman a wajen wad'an da suke jin dad'in zuwansa.
Duk bayan wata yake zuwa Kano ganin iyalinsa. Alokacin Ra'eez yana aji ukku a primary, Alhaji yace zai maidasu Lagos saboda ya kusa kammala gininsa.
Nan Ummun Ra'eez ta nuna ya bari Ra'eez ya kammala firmare kada a lalata masa karatu. Alhaji yace shikenan Allah ya kaimu, kafin lokacin ma na kammala gini na, bara naje muyi maganar da Alhaji Mansur kada yaji maganar daga sama.
Lokacin daya fad'ama Alhaji Mansur yana so ya mai da Iyalinsa Lagos sai Alhaji Mansur yace wannan yana da kyau, bazai yuwu kayi ta zama babu mata akusa da kai ba, kasan yanda zuciya take, duk yanda muka kai da sabawa dole muyi hak'uri, amma kuma zumuncin mu yana nan, amma nafi so Ra'eez yayi makarantar kwana anan Kano, haka kawai bana so yaje yashiga cikin arnan nan, kaga anan akwai karatun addini a makarantar da nakeso na samar masu shida Labiba.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in wannan ai bakomai, Ra'eez 'Danka ne, duk abinda ka yanke akanshi yayi, nima ina masa kwad'ayin samun ilimin addini mai zurfi domin Kano dabance a wajen ilimin addini. Alhaji Mansur yace to nagode.
**** ***
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah Alhaji ya kammala gininshi, yayin da yasa Malan Sani ya sayar da gidanshi ya cika masa ya sayi wani gidan ya canza unguwa, yaso ya sama masa gida a unguwar da yayi gini amma babu gida mai k'aramin kud'i, hakan yasa ya saya masa a unguwa dai-dai kud'insa, sai dai tafi waccan unguwar da suke.
Sosai Malan Sani yaji dad'in abinda Alhaji yayi masa. Matarsa Halima tafishi jin dad'i, domin tunda taga Rumaisa tayi wayau kyanta sai fitowa yake ta fara tsorata da unguwarsu, domin unguwace ta marasa tarbiya, shiyasa har lokacin shigarta makaranta yayi Halima bata yarda ansata ba, lokacin da taji zasu tashi hada kukan farin ciki tayi, duk da zata rabu da makwabciyarta mai kirki.
Yanzu tsakanin Malan Sani da Alhaji yanda kasan 'yan uwa, d'aya baya zartar da abu ba tare da shawarar d'aya ba, akwai girmamawa sosai atsakaninsu, Malan Sani bai tab'a tsallake maganar Alhaji ba amatsayinsa na direbanshi, duk da Alhaji ya sakar masa komai amma baya masa almubazzaranci. Haka Alhaji da kanshi ya saka Rumaisa makarantar kud'i mai sauki, kuma shine ya d'auki nauyin karatun ta.
A wajen aikinsa kuwa yana kokarin adalci ga na k'asa dashi, sai dai yana samun damuwa daga na sama dashi, yasha kama kaya amma ya samu sako akan ya sake su, wani lokacin kuma a hanashi ya duba kayan, sosai wannan abun yake damunsa.
***
Bayan shekaru biyu Ra'eez ya kammala makaranta, haka Alhaji yaje akayi taron yayesu. Bayan kwana biyu sukayi sallama dasu Alhaji Mansur zasu tafi hada Ra'eez kafin jarabawarsu ta fito. Ummun Ra'eez da Matar Alhaji Mansur hada kukan rabuwa.
Haka suka d'aga zuwa Lagos cike da kewar babbar aminiyarta.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar. 08028525263.*
0⃣8⃣
*SURELERE* itace unguwar da suka koma, gida ne mai kyan gaske, domin Alhaji ya dad'e yana ginashi ta yanda zaiji dad'in rayuwa da Iyalinsa, acewarsa beda wasu dangi da suka wuce Iyalinsa, shiyasa ya tsara gida mai kyau saboda suji dad'in rayuwa aciki.
Tunda Ummun Ra'eez taga gidan taji ya burgeta, sosai tayi farin ciki da wannan gida. Ra'eez sai murna yake sun dawo gida mai kyau. 'Dakinshi daban babu abinda ba'asa mashi ba. Haka d'akin Ummunsa komai akwai aciki, jitake kamar wata sabuwar amarya, saboda farin ciki rungume Alhaji tayi hada kukan farin ciki.
Murmushi yayi yana shafa bayanta yace haba Ummun Ra'eez, meyasa zaki rik'a kuka haka? Hannu tasa ta share hawayenta tana fad'in Abbun Ra'eez dole nayi kukan farin ciki, ban tab'a tunanin kasancewa a irin wannan gidan ba, duk da gidan ka na Kano yana da kyau amma wannan daban ne, ginin zamani ne had'e da kayan zamani aciki, unguwar kad'ai abun kallo ce, bansan da wane baki zan gode maka ba.
Rungumeta ya sakeyi yana fad'in bana buk'atar godiyar ki Bilkisu, addu'arki kad'ai nake buk'ata, domin kinsan halin irin aikina, addu'a kad'ai zaki bini da ita, Allah ya albarkaci Ra'eez ya kuma kawo wasu masu albarka a sabon gida.
Guduwa tayi d'akinta tana murmushi. Dariya yayi yana fad'in yau kuma an tuno da daren amarci ne? Tana jinshi ta shige tana dariya. Madu ne ya danna kararrawa hakan yasa Alhaji yaje ya bud'e.
Kwando ya gani mai d'auke da kuloli aciki sai babbar roba wadda aka cikata da zob'o. Kallonsa Alhaji yayi cike da mamaki yana fad'in Madu wannan kuma daga ina? Madu yace Malan Sani ne ya bani yace na kawo maku.
Murmushin jin dad'i Alhaji ya saki yana fad'in ikon Allah!, ina shi Malan Sanin yake? Madu yace yana bani ya tafi yace baya son a taso ka kana hutawa. Amsar kwandon Alhaji yayi yana fad'in gaskiya naji dad'i sosai, yanzu nake shirin na fito na aike ka ka samo mana abinda zamuci saboda Ummun Ra'eez ta gaji bazata iya girki ba, ashe Malan Sani yayi mana tanadi, Allah ya saka masa da alkhairi. Madu yace amin. Alhaji yace bara nashiga ciki sai na miko maka naka.
Ciki yashiga yana kiran Ummu, fitowa tayi tana amsawa. Alhaji yace kinga Malan Sani ya kawo mana abinci, matarsa ce ta dafa. Murmushi Ummu tayi tana fad'in kai amma naji dad'i sosai, wallahi dama yunwa nakeji ina tunanin abincin siyarwa.
Ra'eez ne ya fito yana fad'in Abbu nima zanci. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in ashe dai kowa yunwa yakeji? Taho kaci Kawun ka ne ya kawo mana. Ra'eez yace Abbu anjima zamuje naga Rumaisa ko? Dariya sukasa Ummu tace daga yau dai andena baka labarin Rumaisa zaka rik'a ganinta tunda mun dawo garin su. Alhaji yace anjima muna hutawa zamuje ka ganta. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in yauwa nagode Abbu.
***
Bayan sallar la'asar suna shirin zuwa gidan Malan Sani sai k'arar kararrawa sukaji, Alhaji ne yaje ya duba, saurin bud'ewa yayi yana fad'in ikon Allah, Malan Sani kune haka? Yanzu muke shirin zuwa Ra'eez ya matsa mana sai munje yaga Rumaisa.
Matsawa yayi yana fad'in kushigo, kamo hannun Rumaisa yayi yana fad'in kema kinzo ganin Ra'eez ko? Kai ta d'aga tana murmushi. Malan Sani yace ai mune ya kamata muzo muyi maku sannu da zuwa. Ciki suka shiga Alhaji yashiga kiran Ummu.
Kallon Malan Sani Halima tayi tana fad'in lallai Malan idan kana raye zakasha kallo, ashe haka gidan nan yayi kyau? Ai baka fad'a mani komai ba. Malan Sani yace dama ai gani da ido ya kori ji, duk yanda zan baki labarin gidan be kai yanda kika ganshi yanzu ba.
Rumaisa tace Baba ni dai anan zan kwana yau. Malan Sani ya d'aure fuska yana fad'in idan na sake jin wannan maganar abakin ki saina zaneki kina ji na? Kai ta d'aga cike da tsoro. Halima tace nima zaneki zanyi idan kika sake fad'ar haka, idan ma ance kizauna bance ki amince ba, nasha fad'a maki duk abinda zakiyi arayuwa kada ki hangi na wani, ban tab'a duba da k'arancin shekarun ki ba kullum nake fad'a maki haka saboda ya zauna a kanki, kwad'ayi bashi da amfani kinji Rumaisa? Kai ta d'aga tana fad'in bazan sake ba.
Murmushi Malan Sani yayi ya jawota yana shafa mata kai yace yauwa Rumaisar Baban ta, haka akeson yaron kirki ya kasance. Sallamar su Ummu sukaji hakan yasa suka maida hankalinsu wajen su suna amsawa.
Zama sukayi nan suka shiga gaisawa. Ummu tace Maman Rumaisa yau dai Allah yayi mun had'u, koda yaushe sai dai muyi waya yau gashi mun dawo garin ku. Halima tace wallahi kuwa, tunda Alhaji yace zaku dawo nake cike da farin ciki, Allah ya kare ki daga sharrin mahassada.
Ummu tace amin. Hannu ta mik'a ta kamo Rumaisa tana fad'in zonan 'Diyata. Duk'awa Rumaisa tayi har k'asa tana gaishe da ita. Dariya Ummu ta saki don sosai Rumaisa ta burgeta, gaba d'aya shekarunta bazasu wuce biyar ba amma tana da tarbiya.
Shafa kanta tayi tana fad'in lafiya lau Rumaisa ya karatu ana zuwa ko? Kai ta d'aga tana fad'in duka biyu duk ina zuwa. Ummu tace da kyau, ki dage kiyi karatu kinji? Kai ta d'aga tana murmushi.
Ra'eez ne ya sauko daga sama sai sauri yakeyi dan lokacin da suka zo yana band'aki. Yana isowa falon ya dai-daita tafiyarsa, dan Ra'eez akwai natsuwa, ya samu tarbiya mai kyau. Da sallama ya shigo, gaba d'ayansu suka amsa suna murmushi.
Har k'asa ya duk'a ya gaishe da su. Malan Sani yace matsonan mugaisa abokina. K'arasawa yayi ya bashi hannu yana mai masa sallama. Dariya sukasa Malan Sani yace lallai Malaman Kano sun karantar da kai da kyau, to ya hanya, kazo lafiya ko? Ra'eez yace lafiya lau Kawu.
Sosai Malan Sani yaji dad'in yanda Ra'eez ya kirashi da Kawu. Halima tace Ra'eez ya karatu ka gama firamare sai ta gaba ko? Ra'eez yace na gama. Matsawa yayi ya kamo hannun Rumaisa yana murmushi yace yau baza kiyi mani magana ba bayan a waya muna gaisawa? Dariya tasa tana fad'in sannu da zuwa Yaya.
Gaba d'aya sai da sukayi dariya. Ummu tace ta waya ta k'are ai tunda ka dawo garin su, sai karik'a koya mata karatu. Ra'eez yace to Ummu kice ma Kawu ya barta nan. Kafin Ummu tayi magana Rumaisa ta kwace hannunta tana fad'in ni dai wajen Mama zan zauna.
Dariya sukasa Ummu tace nima ai Mamanki ce. Rumaisa tace ni dai gidan mu zan kwana. Alhaji yace nan ma gidan ku ne ai. Kafad'a ta mak'ale tana kwanciya saman cinyar Mamanta.
Ra'eez yace Ummu kinji abinda tace wai. Ummu tace kada ka damu zata rik'a zuwa, kaga itama ita kad'aice a wajen Mamanta, idan ta dawo nan za'a bar Mama ita kad'ai.
Jinjina kai yayi yana fad'in to nima zan rik'a zuwa gidansu. Dariya suka sa. Tashi Malan Sani yayi yana fad'in bari mu koma yamma tayi kada mu hana ku aiki. Alhaji yace ba wani aiki da mukeyi kuyi zaman ku. Malan Sani yace zamu dawo wani lokacin akwai gajiya ai.
Tashi Ummu tayi tana fad'in ina zuwa. Tsarabar data kawo masu ta d'auko tana fad'in Rumaisa ga tsarabar ki. Kin amsa Rumaisa tayi tana nok'e kafad'a. Murmushi Ummu tayi tana fad'in Rumaisa da wayau kike, gaskiya Maman Rumaisa kin bata tarbiya me kyau, a garin nan dama idan yaronka be samu tarbiya mai kyau ba abun tsoro ne.
Alhaji yace indai Rumaisa ce zakisha mamaki, wayonta har ya wuce shekarunta. Dariya sukasa Malan Sani yace ai Hajiya Lagos abun tsoro ce, addu'a kad'ai zamu rik'e. Ummu tace haka ne. Mik'ama Halima ledar tayi tana fad'in ga tsarabar kanawa. Amsa tayi tana fad'in mungode sosai. Ummu tace haba bakomai, munci abinci yayi dad'i angode.
Haka suka rakasu har bakin mota, sai da suka tafi sannan suka dawo. Ra'eez sai fushi yakeyi. Kamoshi Ummu tayi tana fad'in haba Ra'eez ai zaka rik'a ganinta tunda gari d'aya kuke. Alhaji yace ka bari zan kai ka wuni acan kaji.
Ummu tace wallahi dama su dawo wancan b'agaren na waje. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nayi tunanin haka tun farkon da aka fara zanen gidan, amma abinda nayi tunani ya hanani aikata hakan, akoda yaushe idan zaka taimaki mutum to kayi kok'arin d'orashi a hanyar da zai samu ba hanyar da zaka rik'a bashi ba, hakan yana kashe zuciya, hausawa suna fad'in daka d'auki abinci kaba mutum gara ka nuna masa hanyar gona, koba komai zai dogara da kanshi kuma zaifi tattala abinda ya samu, na duba naga gara na canza masa unguwa na cika masa ya sayi gida akan na kawoshi gidana ya zauna, domin kawoshi gidana da zama zai kashe masa zuciya ya kasa mallakar nasa, kuma zumuncin mu zaifi kwari idan akace muna nesa da juna, kinji dalilin da yasa ban maidosu nan ba.
Ummu tace kana da gaskiya kuma, shikenan Allah ya karemu daga sharrin mahassada kuma ya bamu zama lafiya. Alhaji yace amin. Ra'eez yace Abbu a wace islamiyar za'a sani? Abbu yace Ra'eez zamanka Lagos ba mai dad'ewa bane, bana son ma ka saba da ita har sai bayan ka mallaki hankalin kan ka, dan haka babu makarantar da zan saka, jarabawarku tana fitowa zaka tafi Kano, ko hutu akayi sati biyu kawai zaka zo kayi ka koma saboda islamiya, nafi buk'atar kayi ilimi mai zurfi dana zauna da kai anan, duk lokacin daka kammala karatun ka sai kazo mu zauna tare, domin wancan filin dana bari gidan ka ne za'a gina idan kayi aure ka zauna da matar ka.
Hannu Ra'eez yasa ya rufe fuskarsa ya bar wajen da gudu. Dariya sukayi Ummu tace Yarona fa akwai kunya. Alhaji yace ashe Yaron ki, Yarona dai. Murmushi Ummu tayi tace Yaron mu dai. Alhaji yace idan kina son naki to ki haifo Mamana. Murmushi tayi tana fad'in Allah ya kawo masu albarka, yace amin Ummun Ra'eez.
**** ***
Tunda suka dawo Lagos Alhaji ya k'ara samun natsuwa, aikinsa yake sosai, yayin da Ummu suke zumunci da Maman Rumaisa sosai, Ra'eez yana zuwa gidan su yayita koya mata karatu, itama ana kawota idan ba makaranta, sai dai babu wanda yake kwana gidan kowa, Malan Sani shine yake kaita kuma ya d'aukota koda tayi bacci, haka ma Ra'eez shine yake maidashi.
A wajen aikin su Alhaji Maiwada babu wanda yasan yana da 'Da, domin babu wanda ya fad'ama ya maido iyalinsa, ko walimar shiga sabon gida beyi ba, yayi addu'a kamar yanda addini ya koyar, shiyasa babu wanda yasan ya tare a sabon gida, asalima babu wanda yasan yana gini, dan Alhaji mutum ne mai son sirri, duk yanda kuke dashi baya bari ka sameshi agida musamman akan maganar data shafi wajen aiki.
***
Zuwa yanzu Boda d'insu ta samu lafiya, domin aiki ake sosai, duk wanda aka kama da laifi nan take ake yanke masa hukunci, shiyasa kowa yake kaffa-kaffa da aikinsa. Manyan masu kud'i wad'an da suke kasuwancin shigo da kaya sam basa son Alhaji Maiwada, sunyi-sunyi a canza shi sai dai abun yaki tasiri, domin har yanzu ba'a canzashi ba, ganin haka yasa suka fara shirya masa mugunta, sai dai har yanzu basuci galaba akansa ba.
*****
Jarabawar su Ra'eez ta fito kuma ya samu makarantar kwana shida Labiba, inda suka samu *FGC DAURA*, yayin da aka canza masu islamiya mai kyau idan suka dawo hutu surik'ayi. Sosai yayi farin ciki da samun makarantar kwana, saboda yana son makarantar kwana.
Haka aka kammala masa komai, lokacin da zai tafi hada kukan rabuwa da Rumaisa, Ummu tace tare da ita zata tafi domin tayi masa rakiya. Haka suka shirya kasancewar ta jirgi zasu bi hakan yasa basu tafi dasu Malan Sani ba.
Kwanansu biyu sai da suka kaisu har makaranta kafin suka koma Lagos. Rumaisa sai kuka take Ummu tana lallashinta.
Bayan komawarsu ne Ummu tace gidan yayi mata shiru tana son ta samu mai aiki. Alhaji yace ina tsoron mutanan garin nan, wane aiki ne agidan da sai kin samu mai aiki? Ummu tace kawai ina so na samu abokiyar fira ne, kaga idan ka tafi baka dawowa sai dare, wani lokacin ma har sai nayi bacci kake shigowa, bazan iya zama ni d'aya ba.
Alhaji yace ga Madu nan ai babu abinda zai sameki, wallahi ina tsoron mu kawo abinda zai halaka mu. Marairaice fuska tayi tana fad'i kayi magana da Malan Sani kila ya samo mana tagari. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in shikenan, tunda kince Malan Sani nasan bazai tab'a kawo mana abinda zai cutar damu ba.
***
Koda ya samu Malan Sani da maganar sai yace akwai wata mata mai suna *Ladi*, makwabtansu ne acan tsohuwar anguwarsu, ta iya aiki dan tayi aiki sosai agidajen mutane, yawanci abinda yake sa tana barin gidan aikinta wulakancin mutane, wasu kuma idan taga ana aikata wani abu marar kyau bakinta baya iya shiru sai tayi magana, wannan ne yake sa a koreta, ko kuma idan aka so had'a baki da ita ayi cuta sai taki yarda to sai su rabu, aikin da tayi na k'arshe wanda dagashi tace ta daina aikatau, dalilin barinta gidan aikinta shine, matar gidan tasa ta zuba ma kishiyarta guba a abinci, data ki amincewa sai matar taso taja mata sharri ta zuba abincin a b'oye kuma ta kai maganin cikin kayanta, gashi dama itace take dafa masu abinci, sai akaci sa'a matar bata ci ba, ta zuba zataci ta tashi ta shiga d'aki, da yake suna da mage sai tazo ta saci nama taci, tana gamaci ta fara shure-shure sai gawarta aka iske ga kumfa abakinta.
Tunda aka ga haka akace guba ce a abinda taci, da aka duba sai akaga abincin matar ne taci, nan aka fara bincike sai ga magani an samu akayan Ladi, da yake Allah yana tare da mai gaskiya sai tayi sa'a mai gidan ya yarda da rantsuwar ta ya sallame ta da kud'i yace ta bar aikin. Mutuncin da Mai gidan yayi mata yasa ta sameshi ab'oye ta fad'a masa gaskiya, kuma ya yarda domin yasan halin matarsa. Tun daga lokacin ta dawo gidanta tace bazata sake aiki ba, domin wata rana za'a jawo mata d'auri, a bayan gidan mu take, ita kad'ai take zama a k'aramin gidanta mai d'aki d'aya, na mijinta ne daya mutu taci gado, da ba anan suke ba cirani ya kawo su har ya samu ya gina gida suke zaune shekara da shekaru, da ya rasu sai ta cigaba da zama dan tace bata da kowa, hakan yasa take aikatau. To yanzu sana'ar k'osai takeyi.
Jinjina kai Alhaji yayi cike da gamsuwa yace Malan Sani abun mamaki baya k'arewa a duniya, gaskiya naji tausayinta, kuma tunda ka yabeta nasan tana da hali mai kyau, dan haka kayi mata magana sai muji yanda kukayi. Malan Sani yace insha Allahu bazaku samu matsala da ita ba. Alhaji yace amma ka fad'a mata gidan mu zata dawo da zama, idan yaso sai ta bada hayar nata. Malan Sani yace angama.
****
Cikin sa'a Malan Sani ya samu Ladi da maganar, kasancewar Ladi tasan Malan Sani sosai, kuma taji shima a gidan yake aiki hakan yasa ta amince. Sosai tayi farin cikin samun wannan aikin, domin sana'ar babu kasuwa yanzu, hakan yasa ta fara addu'ar samun aiki sai gashi Allah ya kawo mata. Babu b'ata lokaci ta amince tace zuwa jibi yazo suje gidan kafin ta samu wanda zai tsare mata gidan kafin a samu mai haya.
Malan Sani yace Ladi haya a Lagos ai bata wahala, ayau idan aka tallata gidan zaki samu wanda zai kama. Ladi tace yauwa dan Allah ka taya ni tallata gidan. Malan Sani yace insha Allahu, abinda nake so da ke ki k'ara kok'ari akan wanda na sanki dashi, domin nasan kina da Amana da gaskiya. Ladi tace insha Allahu zan kiyaye. Sallama yayi mata yana fad'in sai nazo jibin, idan kuma na samu wanda zai kama gidan zaki ganni. Ladi tace nagode sosai Malan Sani.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
0⃣9⃣
Cikin kankanin lokaci Ladi ta fara aiki agidan su Ra'eez, d'aki guda mai had'e da band'aki aka bata wanda yake a k'asa kusa da kicin, basu dade ba suka saba da Ummun Ra'eez saboda Ladi mace ce mai tsafta, kirki da natsuwa, rayuwar Lagos ta ratsata shiyasa take a waye, idan ka ganta sai kace bata manyanta ba, domin sam jikinta baya nuna shekarunta, yanda kasan tayi boko haka take, gata da ilimin addini.
Itace take shara, guga da wanke-wanke, sannan tana yima Ummun Ra'eez wanki da guga, duk da a injin wanki ne takeyi, abinci kuma Ummun Ra'eez ce takeyi duk da Ladi tana tayata wani abun, haka idan tana da sako a kasuwa itace take zuwar mata saboda tasan ta kan kasuwa sosai. Ummun Ra'eez tana jin dad'in zama da Ladi sosai, sam bata jin kad'aici yanzu.
**** ***
Adebayo ne da Umar zaune a ofis d'in Alhaji Marusa, bayan sun gama gaisawa Alhaji Marusa yace Adebayo maganar gaskiya hak'urina ya k'are, jiya mukayi magana da Brr. Barau akan wannan mutumin Alhaji Maiwada, duk wata dabara da zamuyi akan a d'aukeshi daga nan munyi amma abun yaki aiki, Mr. Kallah ya fad'a mani bazai yuwu a canzashi yanzu ba, da ace ba amatsayin shugaban kwastam aka kawoshi nan ba da tuni an canzashi, amma yanzu dole sai nan gaba kafin a canzashi.
Saboda haka jiya na yanke shawara ina ganin idan muka bita zamu samu mafita. Adebayo yace Alaji wace shawara ka yanke? Murmushi yayi yana fad'in mai zai hana idan kayana suka shigo musan yanda zamuyi a b'oye wasu idan yaso sai muce shine ya kwashe su.
Gyara zama Umar yayi yana fad'in Alhaji akwai abinda nake zargi a wajen Alhaji Maiwada, ina tunanin kamar ya samu wani canji mai tsoka, domin da alama ya maido Iyalinsa nan garin, ada nasan agidan haya yake zaune, domin lokacin da yazo aka nemi abashi gida yace baya so, to sai yaje ya kama haya, abinci ma direbanshi yake siyo masa alokacin na gane Iyalinsa basa nan, to a kwanan nan naga canji sosai, da alamu ya maido Iyalinsa nan, domin ina ganin Malan Sani yana kawo masa abinci da azahar tayi, kulolin da ake zubo abincin sun sha bamban da abinda yake kawo masa abinci da, sannan alamu sun nuna ya tashi daga tsohon gidanshi, domin shekaran jiya ina bayansu naga ba hanyar tsohon gidanshi suka bi ba, kuma alokacin ya tashi gida zaije.
Alhaji Marusa yace ko dai yayi sabon gini ne? Umar yace da alama, domin hanyar da naga yabi wajen Surelere ne. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in kasa mashi ido, idan har zargin mu ya zama gaskiya ina mai tabbatar maku Alhaji Maiwada ya shigo hannu.
Murmushi Adebayo ya saki yana tambayar Umar abinda suka fad'a dan be fahimta duka ba. Bayani Umar yayi masa. Saurin tashi yayi yana fad'in idan ya kasance gaskiya yayi gini Alaji kabarni dashi, zan kulla masa sharrin da zaiyi kuka. Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad'in nasanka Adebayo baka da kyau, idan kana nan bani da sauran damuwa, dan haka na baka wuka da nama. Jinjina kai Adebayo yayi. Kud'i masu yawa Alhaji Marusa ya basu kafin suka tafi.
**** ***
Lab'e su Umar suke a wani waje suna kallo motar Alhaji Maiwada ta tsaya a bakin gate suna jira a bud'e masu. Mamaki ne ya kamasu ganin irin tsalelen gidan da zasu shiga. Basu gama mamaki ba sai da aka bud'e k'ofar gidan, k'ara matsowa sukayi domin su gane ma idanuwan su.
Bayan da suka shiga Madu ya rufe k'ofa. Umar yace Adebayo ka gani ko? Adebayo yace tunda naga sun shigo wannan unguwar nasan Sir ba k'aramin sata yayi ba, kalli yanda gidan yake kamar na shugaban k'asa. Umar yace ka bari yashiga dole muje wajen maigadin muji ko gidansa ne ko kuma haya yakeyi.
Suna nan sai ga Malan Sani ya fito daga gidan shi kad'ai suna sallama da Madu, dan anan yake barin motar yana hawa ta haya, duk da Alhaji yace yarik'a tafiya da ita amma Malan Sani yace nan yafi tsaro acan yana tsoron b'arayi.
Har suka gama sallama da Madu yazo ya wuce su be gansu ba. Bayan 'yan mintuna suka fito suka nufi gidan. Umar yace Adebayo ka tsaya anan, bana so maigadin yayi saurin gane mu, kaga idan ya fad'ama Alhaji akwai wanda baya jin hausa zai iya d'agowa, dan haka ka tsaya naje. Murmushi Adebayo yayi yace shikenan kaje.
Madu yana zaune yaji alamun sallama daga waje. Lek'awa yayi sai yaga Umar atsaye. Fitowa yayi ya bashi hannu suka gaisa. Umar yace sannu da aiki kayi hakuri na tadoka kana zaune. Madu yace haba ai bakomai, dama aikina ne na kula da k'ofar ai.
Umar yace ni bako ne, akwai gidan da akayi mani kwatance anan unguwar gashi nazo kuma wayata ta mutu bare nakira azo a d'auke ni kuma kwatancen ya b'ace mani shine nace bara nayi tambaya.
Madu yace ka kyauta kuwa, domin matambayi baya b'ata, ya sunan Maigidan da kazo wajenshi? Murmushi Umar yayi yace ina neman gidan Alhaji Hamza mai naira ne. Murmushi Madu ya saki yana fad'in duk da sabon zuwa ne ni nasan Alhaji Hamza, muma ba mufi wata biyar da muka dawo nan ba, maigidana ne ya gina wannan gidan shine muka dawo kasan shine shugaban kwastam.
Umar yace lallai kace agidan shugaban kwastam kake aiki, lallai kaja kaya abokina. Madu yace sosai kuwa, domin Alhaji ba ruwansa, yana da kirki sosai, yafi shekara biyu da rabi yana gina wannan gidan sai wannan shekarar muka dawo bayan ya d'auko Iyalinsa. Umar yace kaji dad'in ka, ina ne gidan Alhaji Hamzan?
Madu yace da ka shiga wancan layin zakaga gida mai babbar katanka fitilu sun haske layin, gidanshi yafi na kowa tsawo a layin zaka ga hada sojoji a k'ofar gidan. Umar yace nagode sosai. Madu yace bakomai agaida gida.
Har ya k'arasa wajen Adebayo yana mamakin irin kud'in da Alhaji Maiwada ya kashe a wannan gidan. Yana zuwa yaja Adebayo suka nufi wajen da suka aje motar su.
Sai da suka bar unguwar sannan Umar ya fad'a ma Adebayo komai. Hannu Adebayo ya tafa yana fad'in da kyau, anzo wajen, wallayi sai Sir, yasan yayi mana rashin mutunci, wannan gidan daya gina sai yayi danasani, ya hana mu jin dad'i ya tsare komai ashe kanshi yake tarama kud'i, kalli gidanshi kamar na babban d'an siyasa, Umar ka bani zuwa gobe zan nemo shawara. Dariya Umar yayi yace bana jinka Adebayo.
***
Tun da safe Malan Sani yazo domin yau da wuri zasu fita. Ummun Ra'eez ce ta fito daga kicin hannunta rik'e da kwandon abincin data zuba masa. Kallonta Alhaji yayi yana fad'in sannu Ummun Ra'eez.
Murmushi tayi tana fad'in sai kace nayi wani aiki babba. Alhaji yace aiki ne mana, yanda kike faranta mani Allah ya faranta maki kema. Murmushi tayi tace amin Abbun Ra'eez.
Amsa yayi yana fad'in yau zamu kai dare saboda wasu kaya za'a kawo kuma dole na tsaya a gama duba su domin kayan Alhaji Marusa ne kuma kinsan na fad'a maki yana shigo da kaya marasa kyau yanzu ne abun yayi sauki dana saka ido, amma duk da haka idan aka kawo kayan manyan mutane dole sai na tsaya na duba duk da yanzu komai yayi sauki.
Ummun Ra'eez tace to Allah ya tsare mun kai, ya kareka daga sharrin mahassada, domin wannan aikin naku akwai had'ari, domin mutane basa son gaskiya gashi kai mutum ne mai gaskiya. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in kome zai faru dani bazan bari a aikata b'arna ba sai dai kawai addu'a.
Ummun Ra'eez tace to Allah ya tsare. Yace amin, yauwa na manta ban fad'a maki ba su Ra'eez zasuyi hutu amma nace ma Alhaji Mansur kada akawoshi ya zauna tunda sabuwar islamiya aka maidasu idan muka samu lokaci sai muje, wani hutun sai yazo ko sati daya yayi. Ummu tace bakomai nima nafison ya zauna yayi karatu ai.
Har bakin k'ofa ta rakoshi tana masa addu'a, sai da ya fita kafin ta koma ciki. Malan Sani yana ganin Alhaji ya fito yayi saurin tasowa ya amshi kwandon hannunsa yasa a mota. Bayan sun gaisa da Madu suka fita. A mota ma labarin kayan da za'a kawo Alhaji yake bama Malan Sani har suka isa ofis.
***
Yau har karfe biyun dare Alhaji yana ofis ana duba kaya, aciki kuma sai da aka samu abinda aka fitar kafin yasa hannu suka gama biyan komai ya sallame su, sauran kayan kuma yace sai zuwa gobe za'a duba, acikinsu akwai sauran na Alhaji Marusa aciki. Haka sukayi sallama suka tafi hadasu Adebayo.
Aranar dole Alhaji yasa Malan Sani ya tafi da mota saboda dare yayi. Bayan ya ajeshi yashiga ciki shi kuma ya wuce. Gaiswa sukayi da Madu wanda har yayi bacci, bayan ya shiga ya rufe k'ofar shima yashiga d'akinsa domin Alhaji yace yarika shiga d'aki yana baccinsa idan ya dawo Allah ne mai tsarewa tunda suna addu'a. Hakan yasa da Alhaji ya dawo Madu yake kulle k'ofa yashiga ciki.
***
Washe gari kasancewar asabar ce yasa Alhaji bai fita da wuri ba, duk da yasan yana da aiki akwai kayan da zaije ya duba yasa hannu kafin a d'auka amma ya kwanta domin jiya agajiye ya dawo yace sai zuwa goma sai ya fita. Tunda ya tashi kawai yake jin kasala da fad'uwar gaba, wanka yayi sai yayi nafila ya zauna yana karatun kur'ani.
Sai k'arfe tara da rabi ya fito domin ya karya. Zaune suke yana cin abinci, kallonshi Ummun Ra'eez tayi tana fad'in Abbun Ra'eez yau sai naga kamar kana cikin damuwa ko? Murmushi yayi yace kawai na tashi da mutuwar jiki da fad'uwar gaba ne.
Hannunshi ta kamo tana fad'in kacigaba da addu'a nima ina taya ka, insha Allahu babu abinda zai faru da kai, Allah yana tare da kai domin kana rike da gaskiyar ka. Alhaji yace nagode kicigaba da yi mani addu'a kinsan aikin mu. Murmushi tayi tana mika masa abinci abaki. Amsa yayi yana sakar mata murmushi, da haka tacigaba da bashi abaki tana masa fira har yaji damuwar ta tafi.
Bayan ya gama Malan Sani yazo ta rakashi tana ta masa addu'a suka tafi.
Bayan da sukaje ofis suka kammala duba sauran kayan yasa hannu kafin aka d'auka. Aranar haka ya wuni baya jin dad'i, ko la'asar beyi ba ya tashi suka dawo gida.
****
Washe gari tunda safe wayar Mr. Kallah ta tadashi, yana ganin sunan sai da gabanshi ya faad'i, d'auka yayi tare da yin sallama. Bayan sun gaisa Mr. Kallah yace Alhaji jiya na samu waya daga Alhaji Marusa wai kayansa sunzo amma babu rabi acikin kayan kuma masu tsadar ne aka cire masa, ya fad'a mani abubuwan da babu kuma naji babu abinda ya sab'a doka bare ace an ciresu.
Ajiyar zuciya Alhaji ya saki yana fad'in Alhaji gaskiya babu wasu kaya da aka cire na Alhaji Marusa, wani kwali guda biyu ne kawai aka cire acikin kayansa domin akwai abinda ya karya doka, kuma agabana aka gama komai nasa hannu aka d'auki kayan kafin nabar wajen.
Mr. Kallah yace Alhaji Marusa yace bazaiyi asara ba dole a nemo masa kayansa ko kuma yashigar da k'ara domin yana da hoton komai kuma an kawo masa kaya babu wasu aciki, shiyasa nace bara na kira ka domin kayi bincike kafin yashigar da k'ara. Alhaji yace shikenan zan bincika tunda kace ayi haka. Sallama sukayi ya kashe wayar.
Kai Alhaji ya dafe yana fad'in innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Da sauri Ummun Ra'eez ta tashi dan tunda aka kirashi ta farka. Dafashi tayi tana fad'in lafiya Alhaji? Labarin abinda ya faru ya bata. Jinjina kai tayi tana fad'in kayi binciken kamar yanda ya fad'a, gaskiya Mr. Kallah yana sonka da har ya iya kiranka ya fad'a maka, kila dai bayan daka gama duba kayan aka samu matsala bayan ka bar wajen.
Alhaji yace Ummun Ra'eez matuk'ar ba'a gano inda kayan suke ba akwai matsala, domin kayan da suka b'ace na miliyoyin kud'i ne, dole Alhaji Marusa bazai kyale ba domin hakan zai jawo masa babbar asara, dole ma yashigar da k'ara saboda kayan suna da tsada.
Ummun Ra'eez tace yanzu idan ba'a gano inda suke ba mai zai faru kuma? Alhaji yace Allah kad'ai ya sani, domin sai abun ya shafemu duk wani wanda yake wajen alokacin da aka duba kayan. Ajiyar zuciya ta saki tana fad'in insha Allahu haka bazata faru ba.
Tashi yayi yana fad'in bara nayi wanka na fita. Ummun Ra'eez tace yau fa lahadi taya zaka fita da wuri haka. Alhaji yace dole na fita domin wannan babbar matsala ce. Waya ya d'auka ya latso Adebayo.
Bayan ya d'auka ya fad'a masa su had'u ofis ya kira sauran wad'an da sukayi aiki ajiya da shekaran jiya. Adebayo yace Sir, zanje coci anjima sai dai idan mun dawo. Alhaji yace na manta, shikenan zan jira ku a ofis. Kashe wayar yayi ya kira Umar, yana dauka yace su had'u a ofis. Kashe wayar yayi yashige band'aki.
****
Zaune suke a d'akin taro kowa yayi shiru yana jimamin abinda ya faru. Alhaji ya rasa abinda yake masa dad'i, tun d'azu da yazo yake bincike amma be samo komai ba, har sauran ma'aikatan sukazo aka cigaba da bincike. Adebayo yashiga damuwa yanda kasan kayanshi ne. Sallah kad'ai take fitar dasu.
Har yamma suna bincike amma basu gano komai ba, sun duba komai gashinan kayan sunzo, kuma an duba su amma gashi ba'a kaisu ba, hatta da wad'an da suka d'auki kayan sun tabbatar iya abinda suka kai sune abinda aka basu. Sosai abun ya d'aure ma kowa kai, haka suka gaji kowa ya tafi.
Alhaji kuwa wajen Mr. Kallah ya wuce, alokacin suna tare da Alhaji Marusa, acan ma maganar d'aya ce Alhaji Marusa yace k'ara zai shigar, gaba d'aya ya tashi hankalinsa saboda kaya ne na makudan kud'i suka b'ace. Mr. Kallah sai hakuri yake bashi amma yaki hakura, yaki bari ma a cigaba da binciken yace yayi magana da lauyenshi gobe za'a shigar da k'ara.
Ganin Alhaji ya damu yasa Mr. Kallah yace ya kwantar da hankalinsa gara aje kotu za'afi saurin gano wanda ya d'auki kayan domin hukuma zata shigo ciki. Jin haka yasa Alhaji yaji hankalinsa ya kwanta domin shima yafi buk'atar hukuma tashigo ciki. Haka sukayi sallama ya tafi.
Yana barin wajen suka kwashe da dariya. Alhaji Marusa yace ai na fad'a maka, bani da kyau Mr. Kallah, dama can kyaleshi nayi amma yanzu yashigo hannu na, sai na sashi yayi dana sanin zuwanshi Lagos, haka kawai muna zaune lafiya wani yazo ya nemi tada mana hankali, wallahi rabon dana shiga damuwa har na manta sai zuwan wannan mutumin.
Mr. Kallah yace baka da kyau mutumina, wallahi banji tausayinsa ba, domin tun farko naso na d'orashi a hanya ya nuna mani shi mai gaskiya ne, yo yanzu waye yake wani aiki da gaskiya, ai yanda kazo kaga kowa da bindi kaima nemi ko tsumma ne ka d'aura domin agudu tare a tsira tare, wannan matsayin fa ba daga gidanku kazo dashi ba, anan ka sameshi kuma nan zaka barshi, ka bari kaci wasu ma suci amma ya tsaya yana nuna mana shi mai gaskiya ne, zaiga gaskiya kuwa Allah ya kaimu aje kotu gobe zai gane baida wayau.
Alhaji Marusa yace baka ga gidan daya gina bane, yasan beda gaskiya shiyasa ko walimar tarewa beyi ba. Mr. Kallah yace ai tunda kace mani a surelere yayi gidan nasan akwai wata ak'asa. Alhaji Marusa yace ka barshi da gidan zamu kamashi ai, yau da dare su *Peter* zasuyi aikinsu. Mr. Kallah yace kai dan Allah? Alhaji Marusa yace wallahi kuwa, ai kaidai kasa ido kayi kallo. Dariya suka kwashe da ita.
Ur's.
Nabeelert Lady[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣0⃣
A daren ranar Alhaji Maiwada kasa runtsawa yayi, Ummun Ra'eez ce take kwantar masa da hankali, sosai hankalinsa ya tashi domin jikinsa yayi sanyi, yana ji aransa kamar wani mugun abu ne zai faru, yayi mamaki da akace wai masu d'aukar kaya basu dauka duka ba, bayan yasan sai da aka gama komai suka tafi kafin ya bar wajen.
Haka yayo alwala ya fara nafila yana neman tsarin Allah daga kowane sharri da yake tunkaroshi. Bayan ya idar ya bud'e kur'ani ya fara karatu har sai da aka kira sallar farko kafin ya tashi ya yo alwala yayi nafila sannan ya fita zuwa masallaci.
Beshigo gida ba sai da gari yayi haske, yana shigowa wanka kawai yayi ya kwanta anan bacci ya d'aukeshi saboda gajiya. Sai k'arfe takwas ya farka dalilin wayarsa da aka kira. Sunan Adebayo ya gani, yana d'auka bayan sun gaisa Adebayo ya fad'a masa an aiko da takardar sammaci daga kotu k'arfe goma za'a shiga. Alhaji yace shikenan sai na fito.
Band'aki yashi bayan ya fito ya shirya sannan ya fito falo. Bayan sun gaisa da Ladi ta shige ciki yayin da Ummu ta zuba masa abinci. Ruwan shayi kawai ya sha yace ya koshi. Zama Ummu tayi tana fad'in haba Abbun Ra'eez, ka sani damuwa bata haifar da komai sai ciwo, ka yi addu'a Allah bazai barka haka ba, idan kuma kaga wani abu ya faru da kai kada kace addu'ar ka bata karb'u ba, kasa aranka Allah yana so ya jarabceka ne kawai, kuma kasan muhimmancin yadda da k'addara.
Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in naji dad'in maganarki, kuma tasa zuciyata tayi sanyi haka kuma kin k'ara mani kwarin guiwa, bakomai, duk abinda ya faru zan d'aukeshi amatsayin k'addarata, domin bawa baya zama haka dole sai da jarabawa.
Murmushi Ummu tayi ta zuba masa abinci ta fara bashi abaki tana kwantar masa da hankali, a haka yarika amsa har yaci sosai, yaji dad'in yanda Ummu tayi masa, shiyasa akoda yaushe yake k'ara sonta domin tasan yanda ake kula da miji.
Bayan ya gama ta rakashi har k'ofar gida inda suka gaisa da Malan Sani kafin tayi masa fatan alkhairi ta koma ciki. Amsar jakarsa Malan Sani yayi yana fad'in Alhaji yau ka makara. Murmushi yayi ya shiga mota bece komai ba.
Bayan sun fita ya kalli Malan Sani yana fad'in babbar kotu zamuje. Da sauri Malan Sani ya kalleshi yana fad'in maganar ta tabbata kenan?........ ....... Labarin abinda ya faru Alhaji ya bashi. Malan Sani yace ikon Allah, Alhaji wannan abu akwai alamar tambaya fa.
Alhaji yace Malan Sani kawai mu barma Allah komai, jikina yana bani akwai abinda suka shirya, dan haka zan d'auki duk wani abu da zai taso. Tausayin Alhaji ne ya kama Malan Sani, yasan wani kullin ne suke so suyi mashi. Malan Sani yace Allah ya saukaka koma menene. Alhaji yace amin.
****
Bayan sun isa kotu da Mr. Kallah ya fara had'uwa, wucewa yayi wajensa suka gaisa kafin ya jashi suka nufi wajen motarsa. Kallon Alhaji yayi yana fad'in kayi hak'uri da duk abinda zai faru, nayi magana da kwamishinan 'yan sanda yace zasuyi bincike dole a gano inda aka b'oye kayan, dan haka zasuzo suyi bincike duk inda ya kamata, Adebayo ya bani sunayen mutanan da suka tsaya akan kaya tun daga kanka har k'asa, kuma kowa za'a bincikesa, dan haka kada ka damu idan suka zo bincike, hakan ne kawai zaisa a gano gaskiya.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in babu damuwa, suzo zan basu damar yin bincike duk inda suke so, nima nafison hukuma suyi bincike domin na kasa gano komai.
Ganin motar Alkali yasa sukayi saurin nufar cikin kotun. Haka kowa yashiga ciki ya samu waje ya zauna suna jiran shigowar Alkali.
Brr. Barau ne yashigo bayansa Alhaji Marusa yana bayansa suna magana a hankali, wajen zamansa ya wuce Alhaji Marusa ya zauna gefen Mr. Kallah. Alkali yana shigowa kowa ya tashi, bayan ya zauna kowa ya zauna.
Gaba d'aya kotun tayi shiru ana jiran a fara. Magatakarda ne ya tashi ya fara karanto k'ara kamar haka.... *Yau sha biyu ga watan janairu shekara ta dubu biyu, (12/1/2000), wannan kotu zata saurari k'arar da Alhaji Marusa ya shigar akan tuhumar hukumar Kwastam da salwantar masa da kayansa na mukudan kud'i bayan sun iso a jirgin ruwa, wanda aka rik'esu har tsawon kwana d'aya da yini guda kafin aka sake su, sai dai aciki babu wasu daga cikin kayan da suka iso wanda ya tabbatar da zuwan su kuma an dubasu kafin a kaisu wajenshi aka cire wasu daga ciki. Alhaji Marusa yana rokon wannan kotu mai alfarma data kwato masa hakkinsa a wajen hukumar kwastam*.
Risnawa yayi ya mik'a takardar wajen Alkali. Bayan daya gama dubawa yace lauyoyin da zasu gabatar da shari'ar su fara.
Brr. Barau ne ya tashi yana fad'in sunana Brr. Nuhu Barau, nine lauyen da yake kare wanda yake k'ara. Alkali yace ina lauyen da zai kare wad'an da ake k'ara? Tashi Alhaji Maiwada yayi yana fad'in bamu d'auki lauya ba domin yau da safe takardar sammacin ta same mu, nine zan kare hukumar mu.
Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in Brr. Barau zaka iya farawa. Risnawa yayi kafin ya fito yana fad'in ina so nayima shugaban kwanstam wasu tambayoyi. Alkali yace an baka dama.
Bayan Alhaji ya fito Brr. Barau yace kotu zata so taji sunanka da kuma matsayin ka.
Sunana Alhaji Hamza Maiwada, nine shugaban kwastam.
Brr. Barau yace kaji bayanin da aka karanta yanzu, shin ko zaka iya yima kotu k'arin haske akan abinda ake tuhumar hukumar ku dashi? Gyara tsayuwa Alhaji yayi yana fad'in tabbas nine wanda ya duba kayan Alhaji Marusa, kuma sai da na tabbatar da komai lafiya kafin nasa hannu aka gama komai sannan muka sakar masu kayan suka d'auka, agaban mu suka d'auki kayan babu abinda aka rage kafin muka bar wajen.
Brr. Barau.. Amma Alhaji Marusa yace kafitar da kwalaye biyu acikin kayansa kace sun sab'a doka, kuma gashi kai kace ba'afitar da komai ba? Alhaji yace ina nufin acikin kayansa da aka duba wanda nasa hannu babu abinda aka rage, wad'an da aka fitar kuma dama bandasu acikin wad'an da nasa hannu, haka ne nasa acire kwalaye biyu acikin kayansa domin sun sab'a doka.
Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in tun bayan zuwanka garin nan Alhaji Marusa ya fara fuskantar matsala da hukumar ku, kuma kowa yasan irin dad'ewar da yayi yana kasuwanci a k'ashashen waje, akwanakin baya ma sai da kayansa suka samu matsala, shin ko akwai wata matsala da take tsakanin ku ne? Girgiza kai Alhaji yayi yana fad'in nifa ma'aikacin al'umma ne, su nake ma aiki tare da k'asata, bani da wata matsala tsakanina da Alhaji Marusa, kamar yanda kowa yake shigo da kaya muke dubawa shima haka muke duba nashi, sai dai kawai kasan kowa da tsarin aikinsa, to nima haka nawa tsarin yake, matuk'ar kaya suka iso dole sai mun tabbatar da ingancin su kafin musa hannu a sake su, matuk'ar muka kama kayan da suka sab'a k'a'ida dole ne mu ciresu, bayan wannan ni banida wata matsala da kowa.
Brr. Barau... Amma yace kayan kwannasu d'aya da yini guda, baka tunanin kafin ku kammala duba kayan aka samu wani ya d'auke wad'an da suka b'ace? Alhaji yace babu wanda ya tsaya akan kayan, bayan da muka duba na farko haka kowa ya tafi sai washe gari aka k'arasa duba sauran, sai dai kasan zuciya bata da k'ashi, Allah ne kad'ai yasan gaskiya, tun bayan da aka fad'a mani wannan matsalar na tara duk wad'an da sukayi aiki aranar muka tattauna, sai dai maganar d'aya ce, babu wanda yasan inda suke, dan haka ina rokon wannan kotu mai albarka data bada izini hukuma tayi bincike akan wannan matsalar hakan zaifi mana sauki.
Jinjina kai Brr. Barau yayi ya juya yana fad'in ya mai shari'a, ina rokon wannna kotu mai albakar, kamar yanda Alhaji Maiwada ya nemi alfarma a d'aga wannan shari'a domin hukuma ta samu damar yin bincike hakan zaisa a samu cikakkar sheda. Nagode.
Bayan da Alkali ya gama rubutu ya d'ago yana fad'in wannan kotu ta bama hukumar 'yan sanda dama da su tsananta bincike zuwa nan da kwana biyu za'a dawo kotu domin acigaba da gabatar da wannan shari'a. Tebur ya buga gaba d'aya akace kottttt .
Gaba d'aya kowa ya fita yana jajanta abinda ya faru, yayin da wasu suke tausayin Alhaji Maiwada domin sun san halinsa.
Bayan da suka fito Mr. Kallah yaja Alhaji Maiwada suka nufi wajen motar kwamishinan 'yan sanda wanda be dad'e da zuwa ba saboda wayar da sukayi da Mr. Kallah.
Bayan sun gama gaisawa Mr. Kallah yayi masa bayanin halin da ake ciki akan abinda Alkali yace. Kwamishina yace kada ka damu Alhaji zansa yarana suyi bincike, ina so ku bamu had'in kai ta haka ne zamu ji dad'in yin aikin. Alhaji yace insha Allahu bazaka samu matsala da mu ba.
Haka suka gama tattaunawa kafin sukayi sallama ya shiga mota suka nufi ofis. A hanya Malan Sani sai kwantar ma Alhaji da hankaki yakeyi har suka isa.
***
A can ofis kuwa hankalinsa atashe yake, Adebayo da Umar ne kawai hankalinsu yake kwance domin sun san bakin zaren, Alhaji ya sake tara kowa ya rokesu akan idan akwai wanda yake dasa hannu akan wannan abun ya taimaki mutane ya fito da kanshi kafin hukuma ta ganoshi, domin duk wanda aka gano shi kad'ai za'a kama.
Nan kowa yace beda masaniya akan abun. Haka dai taron ya tashi babu wani labari. Haka Alhaji ya wuce ofis jiki a sanyaye. Yinin ranar haka yayishi jiki babu kwari.
Bayan anyi sallar azahar sai ga DPO da yaranshi sun iso. Haka suka fara nasu binciken cikin kwanciyar hankali. Duk ma'aikatan da sukayi aiki aranar sai da aka d'auki komai nasu tun daga kwatancen gidansu da bayanin bankinsu. Bayan da suka gama sukayi sallama da Alhaji sukace akowane lokaci za'a iya ganinsu a gidan mutum. Godiya Alhaji yayi masu suka tafi.
Sunayin la'asar ya tafi gida domin baya jin dad'in jikinsa. Malan Sani bayan ya ajeshi yace zaisa Malamin unguwarsu ayi addu'a. Alhaji yace nagode sosai Malan Sani, bara na baka kudin da za'a basu sadaka. Malan Sani yace wallahi bazan amshi ko sisi ba, nine nayi niya dan haka ka barni kawai. Murmushi Alhaji yayi yace nagode agaishe da Rumaisa.
****
Ana gobe za'a koma kotu da misalin k'arfe bakwai bayan anyi sallar magriba Alhaji yana zaune a tsakar gida shida Malan Sani da Madu suna fira kawai sukaji k'ararrawa. Da sauri Madu ya tashi ya nufi k'ofa, sai da ya lek'a kafin yayi saurin bud'ewa.
Tashi Alhaji yayi tsaye ganin 'yan sanda, lokaci guda yaji gabanshi ya faad'i, duk da yasan suna zuwa gidaje suna bincike amma haka kawai yaji gabansa ya faad'i.
Bayan sun gama gaisawa DPO yace Alhaji sai dai kayi hak'uri yau gamu munzo bincike yazo kan ka. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in haba ai bakomai, ai haka mukeso domin ta haka ne za'a gano gaskiya. Bismilla ku shigo, bara nayima Iyalina magana. DPO yace bakomai kayi masu magana.
Suna tsaye suna k'arema gidan Alhaji kallo ya fito yana fad'a masu su shigo. Suna shiga suka iske Ummu da Ladi a falo sanye da hijabi suna zaune. Gaishe dasu sukayi Alhaji ya samu waje ya zauna yana fad'in DPO kushiga ko ina abud'e yake. Jinjina kai yayi kafin yasa yaranshi suka fara bincike.
Tunda suka haura sama Ummu tasa kuka, rungumeta Alhaji yayi yana fad'in kidena kuka, ina da gaskiya ta dan haka su shiga duk inda suke so. Ummu tace yanzu har d'akin kwanan mu sai sun bincika mana? Alhaji yace daga binciken fa shikenan, bana so kisa damuwa aranki.
Suna nan zaune kusan mintuna goma sai gasu sun sauko, DPO yace zamu shiga kicin Alhaji. Jinjina kai yayi ya nuna masu hanyar kicin d'in. Bayan sun gama duba komai suka fito. DPO yace Alhaji babu abinda muka samu acikin gidan ka, sai dai zamu duba can waje zuwa bayan gidan ka dan kamar naga akwai ginin da kakeyi acan baya wanda ba'a kammala ba.
Alhaji yace akwaishi muje ku duba. Cire Ummu yayi ajikinshi yabi bayansu. Suna fita Malan Sani yace Alhaji mujirasu anan kada suga kamar muna binsu. Kai Alhaji ya jinjina ya samu waje ya zauna.
Kusan mintuna ashirin sai ga wani d'an sanda ya fito da gudu, Alhaji yana ganinshi yayi saurin tashi tsaye. Yana zuwa yace Alhaji Oga yana son ganinka. Jiki a sanyaye Alhaji da Malan Sani hada Madu suka bi bayan shi.
Tun kafin su k'arasa suke hango kaya daga cikin wani d'aki da aka bud'e. Da sassarfa Alhaji ya k'arasa wajen. Turus ya tsaya yana kallon DPO. Girgiza kai DPO yayi yana fad'in meyasa haka Alhaji? Meyasa ka zab'i ka bamu wahala bayan kasan komai? Salati kawai Alhaji yakeyi jikinsa yana rawa, idan ba gizo idanuwansa suke masa ba kaya yake gani a cikin d'akin da yake gabanshi kuma kayan da ake tuhumarsu akansu, sai dai kayan da suke wajen basu kai rabin wanda akace sun b'ace ba, da alamu ba duka bane a d'akin.
Da sauri Malan Sani ya rik'e Alhaji yana fad'in wallahi Yallab'ai bamu da masaniya akan wannan kayan, sai dai idan wani ne ya shigo dasu.
Murmushi DPO yayi yana fad'in meye matsayinka awajen Alhaji? Malan Sani yace direbansa ne. Dafashi DPO yayi yana fad'in Malan Direba ka tsaya amatsayinka, wannan mune muke da ikon yin bincike, dan haka kaja bakinka kayi shiru domin duk abinda zaka fad'a zai iya zama hujja akan ka.
Kallon Alhaji yayi yana fad'in bincike ya k'are Alhaji, dan haka zamu tafi da kai kafin gobe akoma kotu, sai dai na lura kamar kayi amfani da wasu kayan saboda yanda na samu labari kayan sunfi haka yawa, amma dai koma meye zamuji daga bakin ka gobe. Shiru Alhaji yayi ya kasa magana. DPO yasa mai d'aukar hoto ya d'auki komai kafin su tafi.
Kallon yaransa yayi yana fad'in ku taho dashi. Alhaji yace zan iya sallama da Iyali na? Wani d'an sanda yace babu inda zakaje. DPO yace barshi ka rakashi yaje yayi magana dasu. Bayansa Malan Sani yabi suka wuce jiki a sanyaye.
Tunda Ummun Ra'eez taga Alhaji taji gabanta ya faad'i, saurin k'arasowa tayi tana kuka. Rungumeta Alhaji yayi shima ya saki kuka. Sun dad'e ahaka kafin ya goge idonshi yana fad'in kiyi mani addu'a Ummun Ra'eez, abinda nake tsoro ya tabbata, Allah ne kad'ai zai fitar dani, sun samu kayan a ginin Ra'eez wanda bansan da suba.
Hannu tasa ta goge masa fuskarsa tana fad'in wallahi nasan k'arya ne, nafi kowa saninka, baka tab'a ciyar damu da haram ba, kuma Allah zai fitar da kai. Gyaran murya d'an sandan yayi yana fad'in Alhaji kana b'ata mana lokaci.
Cireta yayi daga jikinsa yana fad'in kada kiyi kuka, kiyi mani addu'a gobe zan dawo. Kai ta jinjina tana hawaye tace Allah ya tsare mani kai. Ladi ma kuka takeyi tana masa addu'a. Haka suka tasa keyarsa Malan Sani da Madu sai kuka sukeyi. Suna kallo suka tafi dashi yayin da aka sa kayan amota aka tafi dasu.
****
*Washe gari a kotu.*
Ur's.
Nabeelert Lady
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣1⃣
Zaune Alhaji Marusa da Mr. Kallah suke a ofis d'in Brr. Barau. Dariya Alhaji Marusa yayi yana fad'in Mr. Kallah ai na fad'a maka bani da kyau, yanzu Alhaji Maiwada zai san ya ja dani, babu wanda ya isa yazo ya kawo mani matsala akan kasuwancina, domin bana had'a kud'i da komai, saboda ina samun had'in kai da ma'aikatan Lagos yasa ban damu da shigo da kaya ta bodar portcourt ba, amma saboda shi sai da na koma ina shigo da wasu kayan ta can saboda ya kasa ya tsare, duk da ba huruminsa bane diba kaya amma sai yayi hakan, ya tsaya ofis yayi aikinsa bazeyi ba ya koma shine yake duba duk kayan da aka shigo dasu, wanda yake kula da b'angaren duba kaya ya zama hoto, kuma saboda raini yafi tsayawa ya duba kayana fiye dana kowa, amma ai yanzu nayi maganinsa, Mr. Kallah kayi mana wannan taimakon a saukeshi daga wannan matsayin, naji dad'i da ya kasance kana hutu abun ya faru, tunda litinin zaka koma Abuja idan kaje ofis inaso a aiko masa da takardar rage matsayi saboda an kamasa da babban laifi.
Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad'in Alhaji Marusa baka da kyau, kasan nine shugaban kwastam na k'asa baki d'aya, duk da ina goyon bayanka dole wani abun sai an duba saboda idanuwan mutane, ba kai kad'ai ba, manya da yawa nine nake tsaya masu saboda nidai inason kud'i, duk wanda zai yaga mani dole na bashi goyon baya, amma duk da haka muna kimantawa saboda mu kauda hankulan mutane, hutun dana d'auka litinin yake k'arewa, tunda yau za'a yanke hukunci bayan na koma zamu tattauna akan abinda yayi.
Brr. Barau yace rankaidad'e ai ko da abinda kotu zata yanka masa aka barshi ya isheshi ya tsani aikin kwastam, domin miliyoyin kud'i zai biya, inaji ma kila ya saida gidanshi saboda Kwamishna yace da suka binciki bankinsa babu wasu kud'i da yawa aciki duk ya zuba su a gini, domin wannan binciken sai da suka had'a da EFCC saboda babban abu ne, kaga kuwa dole ya sayar da wannan makeken gidan ya biya kud'in da kotu zata yanka masa.
Murmushi Alhaji Marusa yayi yana fad'in kuma nine nan zan sayi gidan, sai dai banzan bari yasan haka ba, zan aika wani yaje ya siya mani shi. Dariya sukasa gaba d'aya. Brr. Barau yace ina ganin lokacin shiga yayi. Mr. Kallah yace bara na fara fita kada azargi wani abu.
***
Duk girman kotun sai da ta cika da jama'a, domin tun jiya ake fad'ar an kama shugaban kwastam na Lagos da laifin satar kayan Alhaji Marusa, wannan dalilin ne yaja hankulan mutane da yawa suka kawo ziyara a kotun, hada manyan mutane sai da suka ziyarci kotun saboda suji abinda za'ayi, 'yan jarida kuwa sun cika kotun kowa yana jira ya samu abun k'araswa.
Bayan da Alkali yashigo kowa ya natsu. 'Yan sanda ne suka shigo da Alhaji Maiwada, kowa kallonsa yakeyi yayin da Alhaji Maiwada yake ta addu'a, gaba d'aya jikinsa rawa yake masa, idanuwansa a k'asa ko kallon mutanan bayayi.
Ummun Ra'eez kasa zuwa kotun tayi, domin bazata iya ganin ana cima mijinta mutunci ba. Malan Sani da Madu sai Alhaji Mansur kawai suka zo kotun, shima a safiyar yau ya biyo jirgi saboda tun a jiya Ummun Ra'eez tayi masa waya. Maman Rumaisa da Ladi sune suke ta bama Ummun Ra'eez hakuri.
Ma'aikatan ofis d'insu Alhaji Maiwada da yawa sun zubar masa da kwallah musamnan wad'an da suke jin dad'insa. Adebayo, Umar da sauran mabiyansu sunfi kowa murna, sai dai a fuskarsu suna nuna jimami.
Bayan da Magatakarda ya sake karanto k'arar Alkali yace a fara gabatar da shari'ar. Tashi Brr. Barau yayi yana fad'in inaso kotu ta bani izini na kira Alhaji Maiwada domin nayi masa wasu tambayoyi. Alkali yace kotu ta baka dama.
Bayan ya fito Brr. Barau ya k'arasa wajensa yana fad'in Alhaji inaso kayima kotu cikekken bayani akan yanda aka samu kayan Alhaji Marusa wanda ake tuhumar hukumar ku dasu a gidan ka.
Ajiyar zuciya Alhaji yayi yana fad'in tabbas an samu kayansa a gida na, amma maganar gaskiya bani da masaniyar zamansu agida na, sai dai idan saka mani akayi, domin duka kwali ukku ne aka samu a gidana.
Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in Alhaji kada ka bama kotu wahala, 'Yan sanda sun tabbatar mana a cikin d'akin da yake bayan gidanka aka samesu, kuma tambayar anan itace, Alhaji Marusa ya bamu iya yawan kayansa da suka b'ace hada kud'ad'en su, sai dai kuma kayan da aka samu a wajenka basu kai kwatar kud'insa ba, haka kuma ko rabin wad'an da suka b'ace basu kai ba, domin lokacin da aka duba gidanka an iske saura kad'an ka rage, shine muke so muji ina ka kai sauran? Idan kuma siyarwa kayi to ina kud'in suke, domin a binciken asusunka da akayi kud'in da suke ciki ba wasu masu yawa bane, shine muke so kayi mana bayani.
Wani lauya ne ya tashi yana fad'in ya Mai shari'a nine lauyen da nake kare wanda ake k'ara. Sunana Brr. *Kamal Auwal*. Kai Alkali ya jinjina yana fad'in Brr. Kamal akwai maganar da kake da ita ne? Risnawa yayi yana fad'in ya mai shari'a ya kamata lauyen da yake kare wanda yake k'ara ya sassauta maganarsa akan wanda ake k'ara, be kamata yarik'a masa wasu tambayoyin ba. Nagode.
Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in wanda ake tuhuma ba zarginsa ake ba domin anga zahiri a gidanshi, dan haka dole ya amsa tambayar da akayi masa saboda shi kad'ai ne zai iya warware mana wannan matsalar.
Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in Alhaji kotu tana sauraron ka. Gyara tsayuwa Alhaji yayi yana fad'in kamar yanda nace bansan da zaman kayan Alhaji Marusa agidana ba, haka zalika bansan ina sauran suke ba, kuma ni ban siyar da komai ba saboda ban tab'a zaluntar kowa akan kayansa ba, iyakar abinda na sani kenan.
Juyowa Brr. Barau yayi yana fad'in ya mai shari'a inaso wannan kotu tayi duba da abubuwa guda biyu da zan gabatar mata yanzu, wanda sun isa su tabbatar ma kotu lallai Alhaji Maiwada shine ya d'auki wad'annan kaya.
Na farko Alhaji Maiwada ya gina katafaren gida na makudan kud'i, kuma babu wanda yasan lokacin daya fara ginin da lokacin da aka gama, sannan be gayyaci kowa ba alokacin da zai tare agidansa, haka zalika Alhaji Maiwada baya son kowa yasan inda gidansa yake acikin ma'aikatansa gaba d'aya, duk wanda yake son ganinsa sai dai su had'u a ofis, domin baya bari aje gidansa.
Abu na biyu alokacin da aka kawo kayan Alhaji Marusa bayan Alhaji da ma'aikatan da suke aiki aranar sun gama duba kayan aka barshi akan sai washe gari zasu k'arasa, bayan da kowa ya tafi Alhaji Maiwada shine wanda aka bari na k'arshen tafiya, wanda maigadi ya tabbatar mana da cewar ya dad'e kafin ya tafi, kuma kafin ya tafi sai da ya aikeshi ya d'auko masa wasu takardu wanda hakan ya d'aukeshi kusan mintuna ashirin kafin ya dawo, da wannan ne Alhaji Maiwada yayi amfani domin ya fitar da abinda yakeso wanda shine yasan ta yanda ya fitar da kayan a cikin lokaci k'ankani.
Da wannan nake rokon kotu data kwatoma Alhaji Marusa hakkinsa. Nagode.
Bayan Alkali ya gama rubutu yace lauyen da yake kare wanda ake k'ara ko kana da abinda zakace? Tashi Brr. Kamal yayi yana fad'in ina dashi ya mai shari'a, ina so zanyima Mai gadin da yayi aiki aranar da aka kawo kayan Alhaji Marusa tambaya. Kotu ta baka dama.
Matsowa yayi kusa da Maigadin bayan ya fito yana fad'in ko zaka iya fad'a ma kotu wajen da Alhaji ya aike ka d'auko takardun da kace? Maigadi yace a cikin ofis d'in da ake aje kaya ne inda suka zauna shine ya mantasu acan sai yace na d'auko masa.
Brr. Kamal... Idan na fahimceka Kenan shi Alhaji ya fito wajen motarsa, daya tuna yayi mantuwa shine ya aike ka?
Kai Maigadi ya jinjina yana fad'in yashiga mota ma sai ya aike ni, to kafin na d'auko masa na d'an jima saboda ban gansu a inda ya fad'a mani ba.
Jinjina kai Brr. Kamal yayi yana fad'in ya mai shari'a inaso kotu tayi duba da abinda Maigadi ya fad'a, Brr. Barau ya ce Maigadi ya fad'a masu Alhaji ya aikesa bayan kuma Alhaji yana cikin mota, hakan zai nuna mana cewar Alhaji baya cikin d'akin da kayan suke taya zai d'aukosu ya fita dasu bayan Maigadi yana cikin d'akin? Inaso wannan kotu mai albarka da tayi duba da wannan sheda da aka gabatar, duk da an samu kaya a gidan Alhaji ba shine yake nuna Alhaji ne ya d'aukesu ba, nagode.
Tashi Brr. Barau yayi yana fad'in ya mai shari'a wannan hujja da abokin aikina ya kawo bata isa ta kare wanda ake k'ara ba, domin kowa ya sheda an samu wad'an nan kaya agidan Alhaji, idan akace yana cikin mota ya aiki mai gadi mai yasa da Maigadin yashiga baiga takardun a inda Alhaji yayi masa kwatance ba? Dama yana da wata manufa shiyasa ya barosu kuma ya aiki Maigadi domin yasan kafin ya gansu ya gama abinda yakeyi.
Ina rokon wannan kotu data yi amfani da shedun da aka gabatar mata domin ta kwatoma Alhaji Marusa hakkinsa, domin ga kwararun hujjoji nan mun gabatar. Nagode.
Bayan da Alkali ya gama rubutu ya d'ago kai yana fad'in Alhaji Maiwada kana da ja akan abinda aka gabatar? Girgiza kai Alhaji yayi wasu hawayen bakin ciki suka zubo masa, hannu yasa ya goge idonshi yana fad'in iya gaskiyata na fad'a, bani da sauran ja akan abinda aka gabatar ma kotu Allah ne kad'ai yasan gaskiya.
Gaba d'aya kotun akayi shiru, mutane da yawa jikinsu yayi sanyi akan maganar Alhaji, su Malan Sani sai kuka sukeyi.
Bayan Alkali ya gama rubutu ya d'ago yana fad'in abisa kwararun shedu da aka gabatar ma kotu, kuma wanda ake tuhuma ya kasa kare kanshi a gaban kotu, wannan ya tabbatar mana cewar Alhaji Hamza Maiwada yana dasa hannu acikin b'acewar wad'annan kaya, inda wasu daga ciki suka salwanta.
Abisa adalci irin na wannan kotu Alhaji Maiwada zai biya Alhaji Marusa duk abinda ya kashe akan kayan da suka b'ace, tun daga siyosu, kud'in kawosu zuwa nan, sauran da suka rage kuma za'a mik'asu ga Alhaji Marusa, 'Yan sanda da hukumar bincike zaku tsaya a kammala komai, domin a tabbatar Alhaji Maiwada ya biya komai daya b'ace, hukumar kwastam sai ku d'auki mataki domin akiyaye sake faruwar irin wannan.
Tebur ya buga gaba d'aya akace kotttt!.
Duk'awa Alhaji yayi ya d'ora kanshi saman katakon da yake tsaye wasu zafafan hawaye suna zubo masa. Malan Sani da Madu sai Alhaji Mansur ne kad'ai suka k'araso wajenshi.
Kamoshi Alhaji Mansur yayi yana lallashinsa. Haka suka fito 'yan sanda suna binsu abaya. Mr. Kallah ne yayi magana da DPO tare da mai jagorantar cibiyar bincike akan su bar Alhaji ya koma gida zasuyi magana da Kwamishna dan ayi komai cikin hankali kwance tunda Alhaji babban mutum ne.
Haka Mr. Kallah ya samu su Alhaji Mansur yayi masu bayani, sosai sukaji dad'in abinda yayi masu, godiya sukayi mashi sannan suka k'arasa wajen Brr. Kamal sukayi masa godiya akan abinda yayi masu domin sun san basu d'aukeshi ba amma ya tashi domin ya kare Alhaji.
Brr. Kamal yace haba bakomai, wallahi naji tausayinsa hakan yasa na tashi domin na kareshi, rashin hujjoji yasa aka kadamu, amma bakomai Allah yana gani.
Godiya sukayi masa suka wuce gida. Duk yanda 'yan jarida suka so suyima Alhaji tambaya hakan be samu ba dole suka hakura.
***
Zaune suke a falo Alhaji yana kwance saman doguwar kujera zazzab'i ya rufeshi. Alhaji Mansur ne yasa Ladi ta had'o masa shayi dan Ummu tana zaune kusa dashi sai kuka takeyi, sosai hankalinta ya tashi da abinda aka fad'a mata.
Malan Sani yana gefe ya kalli Alhaji Mansur yana fad'in Alhaji yanzu shikenan haka zamu kyalesu an yanke ma Alhaji hukuncin zalunci? Alhaji Mansur yace Malan Sani najeriyar kenan, gashi dai munsan sharri ne aka kulla masa amma babu yanda zamuyi, domin sun fimu hujja, kasan ita kotu da hujja take amfani, duk wasu hujjoji da zasu tabbatar Alhaji ne ya d'auki kayan Alhaji Marusa sun gabatar dasu, babban abinda yasa suka k'ara cin galaba akan Alhaji shine samun kayan a gidanshi, amma dan sun gabatar da irin ginin da yayi wannan ba hujja bace, sunyi amfani da hakan ne dan su k'ara ma hujjarsu girma, amma bakomai, akwai Allah, kuma shi kad'ai ne zai bayyana gaskiya.
Ummun Ra'eez tace wallahi na tsani garin nan, bana son wannan aikin na Abbun Ra'eez, tunda abun ya fara zuwa da haka dan Allah Abban Labiba kasa baki ya aje masu aikin su yazo mu koma Kano mucigaba da rayuwar mu, sun fara neman kassarashi ta hanyar dukiyarsa da goga masa bakin fenti, nan gaba wallahi rayuwarsa zasu nema, bani da kowa saishi, idan suka rabani dashi ina zansa kaina.
Rungumeta Maman Rumaisa tayi itama tana kuka. Alhaji Mansur da jikinsa yayi sanyi ya kamo Alhaji Maiwada yana mik'a masa kofin shayin.
Amsa yayi ya shanye dan yunwa yakeji saboda beci komai ba. Komawa yayi ya kwanta yana runtse idonshi. Alhaji Mansur ne ya kamashi suka mik'e tsaye, kallon su Malan Sani yayi yana fad'in bara nashigar dashi ciki nayi waya da likitansa zaizo ya dubashi yana buk'atar hutu saboda jininsa yana iya hawa.
Tashi Ummu tayi tana fad'in ko zaiyi wanka? Alhaji Mansur yace aa abarsa yayi bacci. Ciki suka nufa wani d'aki da yake ak'asa. Bayan sun kwantar dashi wayar Alhaji tayi k'ara, Alhaji Mansur ne ya duba sai ya ga likitan ne, fita yayi yana fad'in bara nashigo dashi.
Bayan ya gama dubashi ya bashi magunguna yayi masa allurar bacci, cikin lokaci kad'an bacci ya d'aukeshi. Fitowa sukayi likita yana fad'in jininsa ya hau, dole ya samu bacci mai yawa hakan zai taimaka masa. Godiya sukayi masa ya tafi.
Kallon Ummu Alhaji Mansur yayi yana fad'in ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru, abarshi ya samu hutu zuwa gobe zamuyi maganar. Ummu tace mungode Abban Labiba, kashiga ga d'akin baki can ka huta Ladi ta kai maka abinci. Jinjina kai yayi ya nufi wajen Malan Sani.
Bayan yayi masa bayanin da likita yayi masa Malan Sani yace shikenan abari zuwa goben sai muji abinda za'a yanke. Sallama sukayi masu suka tafi. Alhaji Mansur ya nufi d'akin da aka saukeshi.
***
Dariya ce take fitowa daga harabar gidan Alhaji Marusa inda suke hutawa, Mr. Kallah ne sai Brr. Barau, Adebayo, Umar sai Alhaji Marusa a zaune, daga gefe guda wasu manyan maza ne sunci sun k'oshi, fuskarsu babu alamun fara'a, d'aya daga cikinsu Peter ne, sai abokinsa na hannun damarsa.
Lemu Mr. Kallah ya kurb'a yana fad'in gaskiya Alhaji Marusa wannan karon bansan dame zan saka maka ba, rabon da muyi irin wannan samun har na manta, kodan an dad'e ba'a samu masu irin halin Alhaji Maiwada ba? Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad'in ai dama haka irinsu suke k'arewa, yanzu gashinan ya rasa kimarsa, zai rasa dukiyarsa abanza, kaga mu gaba ta kaimu, wata kilama hukumar ku ta dakatar dashi.
Mr. Kallah yace baza'ayi haka ba, kasan dan an kama mutum da laifi so d'aya ba'a saurin dakatar dashi, tunda dai nasan abinda ya faru bazan bada goyon baya a dakatar dashi ba domin ya bani tausayi zafin zaiyi masa yawa, amma ranar litinin zan koma aiki hutuna ya k'are, zamu tattauna dole aja masa kunne kuma ya tsaya a aikinsa ya bar masu kula da sauran wajen suyi nasu aikin, idan ya kama dole saiya duba abu sai yaje amma ya tsaya a inda ya kamata.
Adebayo yace Wallayi Sir da an canza manashi kawai. Mr. Kallah yace kada ka damu da kanshi zai nemi canjin wajen aiki, yana nema kuma zamu masa sai mu kawo wanda mukeso. Umar yace shikenan ma mun huta.
Alhaji Marusa yace idan komai ya kammala kowa zaiji sak'o a asusunsa, Peter kunyi kok'ari dole wannan karon ku samu k'ari. Murmushi Peter yayi yana fad'in mungode Oga. Haka suka cigaba da tattaunawa suna shagalinsu.
***
*Alhaji Marusa da Mr. Kallah*, *menene labarin asalin su*?
0 comments:
Post a Comment