Salim na kasuwa a lokacin cike da zumudi ya daga wayar tare da ambatar sunanta.....Kuka tasa mai shashsheka tace"Salim ina cikin tashin hankali mai girma dan Allah kayi hakuri da abinda zakaji daga bakina wallahi duk abinda ya faru tsautsayi da kaddara ne amma nayi al'kawarin sai na salwantar da cikin da yake kokarin ruguza mana farin cikinmu." Cike da so yasan abinda ke faruwa yace."Naja'atu wai meke faruwa ne? naji kina wata magana wacce na kasa fahintarta." Hawaye tagoge tace"Salim ciki ne dani."? Yaji gabansa ya fad'i! sai yayi d'if takaicin kamar ya kashe shi...Ta cigaba da cewa"Dan Allah kayi hakuri salim kada kace na yaudareka ba laifina bane wallahi karfi ya gwada min har hakan ta faru gashi yayi min ciki ba tare dana fargaba wannan dalilin yasa na yanke shawarar zubar dashi dan wallahi ni bazan haihu dashi ba tunda bana sonsa." Salim yayi murmushin mugunta da fadin"Yanzu kina ina."? kai tsaye tace"Gani a cikin tasha zan bar garin gabad'aya dan nagaji da zama cikin wannan masifa.
Yace."Kiyi hakuri kada ki tafi ki dawo gida sai mu san yanda za'ayi." Tace"Salim nifa wallahi sai na zubar da cikin nan hankalina zai kwanta." Yace."To yanzu wane gari kika nufa haba Naja'atu kiyi hakuri ki kar'bi qaddara mana." a fusace tace"au abinda zakace kenan Salim? ashe dama ni kadai nake wahalar da kaina a kanka ko." Yace."Ai dama na fada miki tuntuni kinfi karfina ni yanzu ke auntyna ce dan haka hakuri shi yafi alkairi a tsakaninmu." Cike da bacin rai tace"Shikkenan salim nagode da butulci dama ai idan ba kayi min haka ba to baka cika namiji ba idan baka aureni ba akwai maza a duniya wanda suka fika komai da komai kuma ba zan fasa abinda na kudurta ba." Tana gama maganarta ta kashe wayarta....Salim yayi sauri yayi serving din rocouding din da yasa ya sake kiran wayartata, kin dauka tayi ta hada kanta da gwiwa sai kuka take...Salim ganin taki daga wayar sai yayi murmushi a fili yace."Alhmdullhi bukatata ta biya. numbar Kawun nasa ya shiga kira...Abbah Abbs ya daga wayar kafin ma yayi magana yaji muryar Salim din cikin tashin hankali yana fad'in "Kawu gida babu lafiya Naja'atu ta gudu ka bude whasap na turo maka muryarta yanzu muka gama waya da ita tana sheda min hukuncin data yankewa kanta.
Abba Abbas kasa gane maganar yayi yace." Kai ka nutsu kayi min bayani ina zata nufa bayan yanzu mukayi waya da abokina magaji yace tana gida lafiya lau...Salim yace."Wallahi kawu babu wasa a cikin maganata idan kana so ka gazgata ka bude audion dana turo maka ta whasap..Abbah Abbs hannunsa na rawa ya kashe wayar ya shiga whasap kawai sai yaga yayi exipire tsaki yaja yayi saurin shiga playstore domin dauko wani.
Can gida kuwa Baba Larai ta gama aikace-akaicen ta ta shiga dakin da naja'atun take domin ta dubata, taga bata dakin sai tayi tunanin kota tana toilet sai ta zauna gefan gadon Mufida tana jiran fitowarta.....Zaman minti ashirin tayi a dakin ba taji motsinta ba, sai ta mike da sauri ta isa bakin bandakin tana kiran sunanta. shurun da taji ne yasa da sauri ta tura kofar bandakin, tana rarraba idonta a ciki babu naja'atu babu dalilinta...Cikin faduwar gaba ta fito palon tana dubata hade da kiran sunanta. shuru taji babu alamunta a gidan, sai ta bude kofar palon ta fita da sauri ta nufi bakin gate.
Malam Ayuba maigadi na zaune shida Yunusa suna hira Larai ta karasa tace"Malam Ayuba kana zaune anan ko kaga fitowar Naja'atu." Malam Ayuba yace."Eh kwarai kuwa kimanin awa d'aya data wuce ta fito da akwati a hannunta nine ma na bude mata karamar kofa ta fita.
Baba Larai jin maganar akwati sai taji wani irin fargaba ya rufe ta, da sauri ta juya ta koma cikin gidan ta dauko mayafinta kai tsaye gidan aunty maryam ta nufa tana adduar Allah yasa kada yarinyar nan tace zataje wani gurin
Aunty maryam ta shiga rud'ani mutuka jin maganar da Larai ke tafe da ita, Gaskiya naja'atu bata da hankali kuma taurin kanta ne zai kaita ya baro.
Waya ta dauka ta kira mijinta a sanyaye ta fada masa halin da ake ciki...Abbah magaji bai nuna alhini ba dan shi a tunaninsa ina naja'atu ta sani da xata je? Yace."Kada ku damu naja'atu babu inda za taje watakila tana can kofar na'isa gidan malam ko gidan alhaji dan haka dukkaninku ku kwantar da hankali."
Aunty maryam jiki a sanyaye tace to shikkenan Allah yasa tana can din." Kashe wayar tayi tana wasiwasi a cikin ranta itafa ranta bai amince da cewar yarinyar na kofar na'isa ba, tafi zargin ta gudu ne kamar yanda kullum take cin alwashi sai ta bar gari gabadaya yanzu ta dawo daga rakiyar yarinyar,
Abbah Magaji na kashe wayar kira ya sake shigowa yana dubawa yaga abokinsa ne da sauri ya daga wayar da sallama a bakinsa....Abbah Abbas cikin tashin hankali da damuwa yace."Alhaji magaji ya akayi haka ta faru ? ya akayi kukayi sake irin haka har yarinyar nan ta samu nasarar fita daga gida da sunan guduwa inata nufa cikin halin lalura."? Abbah magaji yace."Subahanallahi! kada dai maganar da maryam take fada min gaskiya ne Alhaji."?
Abbah Abbas yace."Gaskiya ne naja'atu ta had'a kayanta ta gudu! Yanzu na saurari recoding wayarsu da Salim ta kirashi ta sheda masa hukuncin da ta yanke akan cikina dake jikinta zata zubar dashi kuma komai rintse sai ta rabu da aurena shin me yayi zafi har yarinyar nan ta yanke mana wannan mummunan hukuncin." Halisa dake gefansa a zaune wani murmushi ta saki ta sake gyara zamanta tana sake kasa kunneta a kan wayar da yake.
Abbah Magaji ya mike tsaye hankalinsa a tashe sai kiran kalmar innalilihi wa'ina ilaihi raji'un yake! gabadaya kansa ya kulle ya rasa abinda zaice..Da kyar yace."Wallahi Alhaji Abbas ban ta'ba tsammanin yarinyar nan zata aikata wannan mummunan aikin ba tabbas dana san haka zata faru zan dauko ta dawo gabana ta zauna har ka dawo! to rashin sani yafi dare duhu! babban tashin hankali anan shine ina ta nufa cikin wannan halin da take ciki.
Abbah Abbas kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a Nejeria yace."Nima shine babban damuwata amma babu komai dukkanin tsanani yana tare da sauki Allah zai tsareta ita da abinda ke cikinta idan Allah yasa dan dake cikinta zai taka duniya ina rokon Allah ya tsare min shi a duk inda zata shiga idan kuma bukatarta ta biya akansa sai na roki Allah ya maye min gurbi da wani."Wannan kalaman na abokin nasa sunsa jikinsa yayi sanyi yace."Alhaji kayi hakuri dan Allah insha Allah yarinyar nan ba tayi nisa ba tana kusa yanzu zan koma gida zansa aje a duba gidajen dangi ko can ta nufa dan Naja'atu bata san kowa a wani gari ba ballantana taje."
Murmushi takaici yayi yana jin wani irin d'aci a bakinsa yace."Allah ya jishshemu alkairi." kashe wayarsa yayi yana jin wata masifaffiyar tsanar yarinyar a cikin zuciyarsa babu shakka ta salwantar masa da gudan jininsa sai ya nuna mata shi d'an halak ne....
Abbah magaji ya jima ri'ke da wayar a hannunsa ya shiga tunani da nazari akan abinda yarinyar ta aikata gaskiya bai ta'ba tsammanin faruwar haka daga gurinta ba sosai yarinyar tayi masa bazata....Kafin ya nufi gida sai da ya kar'bi wayar Salim ya saurari muryar Naja'atun nan ya sake gazgata maganar abokin nasa...kai tsaye motarsa ya shiga ya nufi kofar na'isa domin shedawa iyayensu halin da ake ciki.
Halisa ta matso kusa dashi tare da dafa bayansa cikin tausasawa tace"Kayi hakuri abban mufida ni dama nasan da kamar wuya yarinyar nan ta bar cikin nan tunda da kunnena naji tafada cewar ita ba zata ta'ba haihuwa da kai ba tunda bata sonka kuma duk yanda za tayi sai tayi ka saketa ta auri wanda take so gashi kuwa ka gani kuma kaji da kunnanka wanda idan wani ne yazo ya fada maka cewa za kayi karya ne shiyasa kullum nake cewa dakai yarinyar annobace a cikin mu yana da kyau dai tun wuri ka nemawa kanka mafita amma gabadaya zama da ita ba alkairi bane."
Abbah shuru kawai yayi yana ta nazarin maganganun Halisan tabbas halisa tayi gaskiya yana da kyau tun kafin yarinyar tayi masa wanwar! yayi gaggawar cire ta daga rayuwarsa dan bazai iya jure wannan al'amarin ba, wato shi ya gama shan wahalar dasa 'kwansa lokaci guda ayi masa asararsa gaskiya bai zai iya daukar wannan rashin mutuncin ba dole ne ya dauki mataki a kanta..Halisa ganin yanda ya fusata! sai taji dadi ta cigaba da zugashi kancewar kada ya yarda har in dai yarinyar tayi nasarar zubar masa da ciki to ya dauki mataki mai tsauri a kanta.
Jinta kawai yake yi yana ganin ita bata isa ta nuna masa ga irin hukuncin da zai dauka akan yarinyar ba ko wane irin hukunci ya dauka akanta ya barshi a zuciyarsa sai ya tabbatar da cewar ta samu nasara a kansa sannan zai zartar dashi.
Duk inda aka san za'a ga Naja'atu an dubata ba a ganta ba, hankalin iyayenta da duk wani wanda ya shafeta ya tashi, baba talatu kuka kawai takeyi dan takasa daurewa sai salati take tana kiran sunan Allah da fadin Allah ya bayyanta yarinyar a duk inda take......Baba malam kuwa alwala ya daura ya hau kan dadduma domin shedawa Ubangiji halin da ake ciki......Abbah magaji da Abbah Alhassan kam gidajen redio suka nufa domin shigar da cigiya..to al'amarin ya fi karfinsu dole sai sun had'a da cigiya dan ganin duhun dare ya shigo babu wani labari.
Yaya Ramlatu ta samu labari a bakin Salim bayan ya dawo daga kasuwa ya kunna mata roconding din ta saurara! aikuwa bata bari gari ya waye ba ta dauki mayafinta tare da wayar Salim din ta nufi kofar na'isa tana shiga gidan nasu kai tsaye sama ta nufa dakin Alhaji suka gaisa kamar abin arziki kawai sai ta kunna masa roconding din tace ya saurari abinda Naja'atu ta aikata.
Alhaji Sama'ila da ba lafiya ya cika ba dalilin da yasa duk abinda akeyi be sani ba dan baba malam cewa yayi kada a fada masa saboda lalurarsa kada a tayar masa da hankali
Jin audion Naja'atu yasa jikinsa ya rikice! sosai ya dinga salati yana kiran sunan Allah jikinsa na wani irin rawa har sai da ta firgita da ganin halin da ya shiga...Abbah Alhassan ya shigo dakin ya ganta a zaune ga Alhajin na makyarkyata yana neman faduwa, da sauri yaje ya rikeshi yana salati! Yaya Ramlatu jikinta sanyi yayi ganin jikin mahaifin nata ya rikice sai ta shiga inda inda a lokacin da Abbah Alhassan ke tambayarta abinda yasa shi shiga damuwa tace"Itama tazo gaisheshi ta ganshi cikin wannan yanayi...Da sauri ya kira Salim a waya yace maza yazo zasu kai Alhaji asibiti....Minti goma salim ya iso gidan suka rirrike Alhajin suka sauka dashi kasa.....Hankali a tashe hajia Rabi amaryasa tabi bayansu...ita kuwa Yaya ramlatu a sanyaye ta fita daga gidan a maimakon ta nufi gidanta sai kawai ta shiga gidan Baba malam suna zaune cikin alhini da damuwa ta tsaya a kansu babu gaisuwa kawai ta kunna musu muryar 'yarsu! gurin yayi tsit! sai da suka gama saurara sannan ta kashe wayar ta kama hanya ta fita daga gidan ba tare da tace uffan ba, tana fita baba talatu ta cigaba da share hawaye tana girgiza kanta da fadin wannan yarinya kin janyo mana abin kunya a idon duniya innalilihi wa'ina ilaihi raji'un.
Naja'atu tana can tana gagaranba a garin jos dan tun bayan saukar ta a tashar garin tana fitowa daga mota wani matashi ya warce mata pose dinta da wayarta a ciki da kudadenta! abinka da tasha da turmutsutsu babu wanda ya ankara da abinda ya faru!! ta dinga kuka tana waige-waige a tashar ga duhun dare ya kawo kai yanzu ya za tayi ta kira Munira dan gabadaya ta manta sunan unguwar tasu ballantana ta shiga motar da zata kaita unguwar ta nemi gidan...Hannunta ta kalla taga dari biyar da dari biyu ajiyar zuciya ta sauke wannan 'yan canjin sune kawai suka rage mata, dan haka da sauri taja akwati ta fita daga cikin tashar lokacin anata kokarin shiga massalaci domin sallar magariba....Tafiya me tsayi tayi ba tare data san inda ta dosa ba, gajiya da yunwa yasa ta nemi gefan titi ta zauna tana kalle-kalle!! ta jima a zaune a gurin tana kallon mutane nata shige da fice wasu matasan samari na nuna ta suna dariya sai ta tsorata ta mike da sauri ta bar gurin...Sawun tafiya taji a bayanta tana juyawa ta ga wannan matasan suna binta sauri ta 'kara tana hard'ewa yayinda gefan cikinta ke wani irin murd'awa!!! Kafin ta ankara taga sun kewaye ta, a tsorace take kallonsu da fadin" Ni bakuwa ce a cikin garin nan dan Allah ku taimaka min kada ku cutar dani."
Daya daga cikinsu yace."Muma ki taimaka mana sai mu taimaka miki wane gida kike nema."? murya na rawa tace"Wallahi na manta address din gashi wani 'barawo ya fizge min jakata da waya ta a ciki ballantana na duba." Hahahaha! suka sa dariya suna nunanta dayan yace."Kizo kawai muje dake masauki baki da matsala tunda kin hadu damu.
Tsorata tayi ta dan matsa gefe tana neman hanyar guduwa, wanda yake gefanta ya fizgo hijabinta yana kokarin sha'ke mata wuya! da sauri ta fizge ta bangajeshi a guje ta kama hanya! aikuwa suka rufa mata baya...Takalmanta da akwatin kayan dake hannunta ta watsar ta dinga gudu tana kiran a taimaka mata! Jos dai ba daya yake da sauran gaguruwa ba! yawanci gidajensu babu doguwar katanga mafi akasari ma a waje suke rayuwa dan haka tana shigowa cikin mutane tana wannan gudun jama'a suka kewayeta suna tambayarta abinda ke faruwa...Su kuwa matasan samarin nan ganin ta tsere musu sai suka koma da baya suka dauke akwatin kayanta data jefar sukayi nasu guri
Wata mata ce ta rike ta ta kaita gidanta ta zaunar da ita tana tambayarta daga wane gari take!? Naja'atu kwanciya kawai tayi tana zirarar da hawaye wannan wace iriyar masifa ce? matar ganin bata kulata ba yasa ta tashi ta bata guri, dama abinci take siyarwa a kofar gidanta sai kawai ta koma ta cigaba da sallamar mutane....Wani irin kuka take tana rik'e cikinta wani matsiyacin ciwo yake mata! sai kyarma jikinta keyi.....sai kusan sha d'aya na dare matar ta shigo gidan ita da 'yan yaranta biyu...Ganin Naja'atu a kwance a inda take yasa ta tsaya a kanta tace"Baiwar Allah nifa tausayi kika bani shiyasa har nayi sha'awar taimaka miki amma dan wulakanci tun dazu sai magana nake miki kinyi min banza
Naja'atu da kyar ta iya mikewa zaune tana share hawaye tace"Dan Allah kiyi hakuri bani da lafiya shiyasa na kasa yi miki magana.
Tace"Me yake damunki."? A hankali tace"Cikina ne yake ciwo."? matar sam bata dauka ita din matar aurece bace tace"Yanzu dare yayi dana kaiki chamis amma bari na dauki miki ja da yallow kisha idan baiyi miki ba sai kisha kanwa zaki ji dadi.
Naja'atu tace"To nagode." Daki matar ta shiga ta fito hannunta rike da plate a rufe da abinci a ciki tace ga abinci ki fara ci sai kisha maganin." da sauri ta kar'ba dama yunwa na damunta...Lomar farko ta raina kanta dan jin yanda bakinta ya game da yaji!n attaruhu! miyar sai kace ta mayu saboda tsananin yaji! ruwa ta dauka da sauri tasha, ta dauka ta karayin loma guda...Tana zukar bakinta ga abincin da dadi amma sai uban yaji!!! Miyar ta ture ta shiga cin farar shinkafar amma duk da haka akwai yaji, wani irin amai ne ya shiga yunkuro mata ta dinga danneshi amma ina!! a guje ta nufi bakin rariya ta shiga kelayawa tana kakari da rike kirijinta da yake mata wani irin zafi......matar ta tsaya a kanta tana yi mata sannu har ta gama ta riike ta suka dawo suka zauna tana mata sannu ta mika mata kwayoyin maganin ja da yallow da wannan maganin mai mugun dacin tsiya na tsayar da gudawa! ba tare da tunanin komai ba ta karbi maganin ta watsa a bakinta ta kora da ruwa!! (Shan magani barkatai ba tare da ka'ida ba yana janyowa mai ciki babbar matsala matar tace"Sannu bari na shiga na gyara miki guri ki kwanta gobe kafin na fita kasuwa zan kaiki asibiti a dubaki..Naja'atu daga mata kanta kawai tayi tana jin wani irin jiri na d'ibarta.
Misalin karfe daya rabi na dare ya tashi yaje ya dauro alwala ya fuskanci alk'ibula yana kaiwa Allah kukansa ni dai ban ta'ba ganin babban mutum na kuka ba sai akan Abbah Abbas gabadaya ya kasa daurewa ganinsa a gaban mai kowa da komai yasa zuciyarsa ta karye ya shiga zurarar da hawaye yana me kai masa kukansa.
A daidai lokacin shima baba malam ya kadaice kansa da Ubangiji yana nemawa rayuwar yarsa sassauci gami da za'bin alkairi dan yanzu gabadaya al'amarin ya fice masa daga rai sai dai neman zabin Allah duk abinda kuwa ya zartar shine daidai.
Karfe uku daidai Naja'atu ta mike zumbur! jin yanda wani irin mahaukacin ciwon ciki ya turnuketa kafin kice me ta fita a hayyacinta...salati ta shiga yi tana murkususu a kan shimfidar da take kwance...Maman Sajida ta tashi da sauri ta kunna fitila tana kiran sunanta, Naja'atu hannunta ta rike tana hawaye tace" Baiwar Allah ki taimaka min hakika ina azabtuwa a cikin wannan daran." Maman Sajida tace"Sannu ni wallahi dana ga kinyi bacci na dauka kinji sauki ashe ke kadai kika san abinda yake damunki sannu bari gari ya karasa wayewa na kaiki asibiti.'' Naja'atu kanta kawai take dagawa tana ambaton Allah a cikin zuciyarta...
haka suka kasance har garin Allah ya waye maman sajida taje tayi alwala tayi sallah agurguje ta fita ta kira makociyarta Maman Ladi suka fara kokarin kama Naja'atu domin su mikar da ita! Ita kuwa rintse idonta kawai takeyi cin yanda kwankwasonta ke amsawa sai kawai ta saki karamar kara ta koma ta zaune tana mike kafarta kawai suka ga jini na bin cinyoyinta...Sai suka shiga salati suka kamata da kyar suka kaita bandaki suka tsuganar da ita...Maman Ladi tace"Yariyar nan 'bari za tayi innalilhi! Maman Sajida tace "bari naje na dauko babur . da dauri ta fita daga bandakin...Wai Naja'atu kwanciya tayi a bandakin duk kaxantarsa bai dameta ba taimakon Allah kawai take nema...Kafin maman Sajida ta dawo ma ai akin gama ya riga ya gama tuni cikin ya bi rariya tunda duk ga daddaginsa nan a kasan bandakin sai uban karni ne ke tashi a gurin ....Maman Ladi ta ri'ke bakinta cike da mamaki take kallon Naja'atun tace" Ashe ma cikin baiyi kwari ba to Alhamdullhi tunda Allah ya rabaki da wahala haihuwar d'an shege a wannan zamanin ai masifa ce.'' Naja'atu a galabaice take kallon matar tace"Kina nufin cikin jikina ya fita."? Maman Ladi tace"Ga zahiri nan kina gani a kasa yana bin rariya sai ki godewa Allah! ajiyar zuciya ta sauke tana godewa Allah a cikin zuciyarta.
*Wayyo Allah Abbah Abbas😭😢*
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
43
Maman Sajida ta shigo bandakin da sauri tana fad'in" Maman Ladi kamata mu fito da ita ga babur can na samo a waje." Maman Ladi tace"Wane na kamata ai tuni cikin ya zube kada ma kiyi asarar kudin motarki." Sororo maman sajida tayi tana kallon Naja'atu dake durkushe kamar wacce take kan gwiwa!(mace mai naquda) A sanyaye tace"Ai shikkenan to Allah yasa haka shi yafi alkari ni wallahi ma ban dauka ciki ne da ita ba." Maman Ladi tace"Ke dai maza kije ki sallami mai babur ya tafi sana'arsa kin barshi a waje." Maman sajida tayi saurin juyawa ta fita daga bandakin...Maman Ladi ta kalli Naja'atu da fadin"Sannu yaya yanayin jikin naki."?
Murya na rawa tace"Jiri nake ji da ciwon mara." Ta'be bakinta tayi tace"Ai dama dole kiji haka tunda kin zubar da jini ciwon mara kuwa ai ya zama dole haka kawai da kuruciyarki da komai a maimakon kiyi aure ki raya sinna sai ki dinga bin maza duba dan Allah wani shegen gardi yayi miki ciki ya barki da wahala shi yana can a kwance wallahi kuyiwa kanku fad'a.'"
Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga zubo mata, ashe kallon karuwa suke mata...Da kyar tace"Baiwar Allah ki daina yi min kallon karuwa wannan cikin na jikina yana da uba." Maman ladi tace"Ai dama kun saba dauko ciki idan ku kaga asirinku zai tuno kuce cikin ku yana da uba to dama wane d'ane bashi da uba! kowa ne d'a yana da ubansa sai dai wani ana samar dashi ta hanyar da bata dace ba.
Naja'atu shuru kawai tayi tana jujjuya kanta gaskiya maganar da matar nan takeyi tayi bala'in 'bata mata rai....Maman Sajida ce ta shigo bandakin suka taimaka mata ta mike tsaye ta jingina da bango(garu) Maman sajida tayi saurin zuwa dakinta ta dauko mata daya daga cikin kayanta riga da zani na atamfa da sabon pant gami da audigar mata suka taimaka mata ta gyara jikinta, cikin kasala gami da jiri suka kaita suka ajiye a tsakiyar ledar dakin.
Maman Sajida ta dukufa aikin gyara bandakin yayin da ita kuma maman Ladi ta dage da surutai gami da farfadar mugwayen kalmomi akan naja'atu tana zuga maman sajida akan ta koreta dan daka gani ba mutuniyar arziki bace."
Maman sajida tace"Nima shawarar dana yanke kenan anjima kadan idan ta samu nutsuwa zan zauna da ita na tambayeta garinsu idan ta tsaya yi min inda inda to korarta zanyi dan ba zata janyo da mutuncina a gari azo anayi min kallon banza ba.
Maman Ladi tace"Wannan shine tunani mai kyau ni na tafi gidana dan zan shirya 'yan makaranta." Maman Sajida tace"To nagode."
Naja'atu duk irin maganganun da sukeyi a bandakin tana jinsu, wasu zafafan hawaye ne kawai suke tsere a kuncinta yanzu idan maman sajida ta koreta ina zata nufa na farko dai tayi al'kawarin ba zata koma kano ba domun har yanzu bata karaya ba, tana nan a kan bakanta , na biyu kuma bata san gidansu munira ba ballantana taje can tana ganin zata fadawa maman sajida labarinta watakila ita zata fahimceta.
Maman Sajida ruwan tea ta d'ora musu ta aiki yaronta ya siyo musu kayan shayi, sannan dama tana da ragowar miyar jiya me yajin tsiya ta du'mama da yake akwai nama a ciki sai ta samu dan madaidaicin abu ta zubawa naja'atu miyar ta hada mata tea din ta kai mata har inda take zaune, tace"Gashi nan babu yawa miyar jiya ce na d'umamaki sai ki dangwala da bread. ga tea nan kuma." A sanyaye tace"Nagode abinda kikayi min Allah yayi miki."
Maman Sajida tana kokarin fita daga dakin tace"Ayya ai babu komai dan na taimake ki kina cikin halin taimako....Naja'atu tea din kawai ta iya kur'ba tana jin yanda jini keta 'bul'bulowa daga jikinta, takure jikinta tayi tana adduar Allah ya takaita mata wahala...Gabadaya miyar naman da maman sajida ta ajiye mata ba tayi mata ba shiyasa ko kallonta ba tayi ba, tana gama shan tea ta mike da niyyar sanja guri! kawai taji jini ya tsinke mata! da sauri ta durkusa kasan dakin jikinta na rawa, zanin jikinta ta d'an janye nan taga jinin duk ya 'bata gurun..Maman sajida ta shigo ta ganta tana kuka gata a durkushe tace"Ke kuwa me yasa kike haka sai kace wata wacce zata haihu sai durkuso kikeyi." Tace"Kiyi hakuri dan Allah ina mikewa naga jini na bin jikina shine tsoro yasa na tsuguna.
Maman sajida tace"Ta'b! aikuwa gaskiya nayi miki na Allah da annabi ke zaki wanke kayan jininki...Dakinta ta shiga ta dauko mata wasu kayan ta fita tana jan karamin tsaki! gaskiya tayi abinda zata iya haka kawai azo ana sata aikin jini.
Naja'atu tana kuka tana kimtsa jikinta, tasa zanin data cire ta goge inda ya baci ta fito da kayan a hannunta, bandaki ta nufa tasa su cikin bawo ta zuba ruwa da omo ta shiga wankewa...Maman sajida ta koma dakinta ta sake gyarawa sai mita take ta dauko turaran wuta tasa sannan ta fesa turaran kamshin daki ta nemi guri ta zauna tana jiran shigowarta.
Naja'atu tazo ta zauna jikinta duk yayi sanyi idan kuka ganta sai kun tausaya mata, sosai take bukatar kulawa sabida jinin data zubar.......Maman Sajida ta kalleta a nutse tace"Meye sunanki. da sunan garinku"?
Tace"sunana naja'atu kuma ni 'yar kano ce nazo jos ne gurin kawata munira ina sauka a tasha wani 'barawo ya warce mun jakata da wayata da kudina duk a ciki..bayan na shigo cikin gari kuma wasu 'yan iska suka biyo ni da gudu suna so su cutar dani shine dalilin daya sa kuka ganni ina gudu.
Maman sajida tace"Ayya Allah y kiyaye gaba, sai dai abunda ya bani mamaki dake shine, dama kin san kina da ciki ko kuwa kema baki san kina dashi ba dan gaskiya ni kallo daya nayi miki naga kamar mutuniyar arziki ce ke."
Naja'atu tace"Nasan ina da ciki shine dalilin daya sa ma na bar garinmu nazo nan." Maman sajida tace"Abun kunya kika gudarwa ashe."? Da sauri ta girgiza kanta tace"Ko daya cikin nan da ubansa ba shege bane kamar yanda kuke tsammani...Auran dole akayi min da mijin yayata bayan rasuwarta........Tiryan tiryan Naja'atu ta sanar da mmn sajida labarinta...Maman sajida tace"Ni kam banji dadin abinda kika aikata ba na'jaatu da kinyi hakuri kin zauna da mijinki da yafi miki alkairi wallahi to da kikazo garin jos me kike tunanin zaki samu."
Tace"Nazo gidansu kawata ne amma bada niyyar na zauna ba idan an kwana biyu zan koma gida." Maman Sajida tace"To ai kince kin mance kwatancen gidansu kawartaki." Tace"Wallahi na mance Amma dai mahaifinta fitacce ne sunansa Alhaji Aminu d'an jarida! Maman Sajida tace"Ai nasan gidan can bayan layi ne."
Ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala a cikin ranta...Maman sajida ta mike da fad'in "Ni zani kasuwa yanzu idan na dawo da wuri sai na rakaki gidan idan kuma ban dawo ba sai dai gobe tunda kinga yanayin sana'ata ta dare ce." Tace"To nagode maman sajida ai tunda na samu gidan zuwan ba zaiyi wahala ba sai kin dawo." Tace"To su Walid da Sajida idan sun taso daga skull zasu shiga gidan maman ladi su zauna idan zaki shiga ki zauna kema sai ki shiga." Girgiza kanta tayi tace"babu komai har kya dawo ina gida." Maman sajida tace to tare da kama hanyar fita daga gidan kafadarta rataye da jakarta.
To can gida haka suka wayi gari cikin alhini gami da damuwar 'batan naja'atu! hauwasa sukace labarin duniya baya 'buya sai ga mutane suna doko sallama da sassafe suna shiga gidan malam da Alhaji wai sunzo jaje! wannan al'amarin ya sake d'agawa baba talatu hankali da yake bata iya tashin hankali ba tsakanin jiya da safiyar ranar duk ta rame kuka kuwa tayi har ta gaji! Jama'ar da suke ta tururuwar shigowa gidan yasa ta shige daki ta kwanta duk wanda yazo sai dai Baba Magajiya wacce ta kasance 'yar uwa a gareta ta sallameshi wasu dai gulma suke zuwa wasu kuwa suna zuwa ne domin su jajanta al'amarin to komai dai menene kaddara bata wuce kan kowa ba.
'Bangaran Abbah Abbas kuwa duk yana samun labarin abinda ke faruwa daga bakin Abokinsa da Salim dukkaninsu sun sheda masa cewar babu wani cigaba dan har yanzu babu wani wanda ya kawo musu labarin ya ganta a wani gurun......Abbah Abbas kasa 'boyewa mahaifiyarsa al'amarin yayi duk ya sheda mata halin da ake ciki.....sosai hajia Abu ta shiga rudani da tashin hankali itama sai da ta zubar da hawaye tana fad'in "Ina yarinyar nan ta kai kanta da 'karamin ciki a jikinta me yayi zafi!? da har zata nemi salwantar da rayuwarta akan abinda babu dole a ciki, idan auran Abbas ne bata so to kam insha Allahu za'a warwareshi domun ta samu zaman lafiya in yaso daga baya sai ta auri wanda take so......Halisa kuwa sai nuna alhini da damuwarta take a kan lamarin gefe guda kuwa sai suyi waya sau uku da Yaya Ramlatu suna sake tattauna maganar da kuma 'karawa kansu kwarin giwa tare da sake gazgata maganar boka ai dama ya fada musu cewar yarinyar za'a nemeta a rasa yanzu abu daya ne ya rage a cikin maganganun da bokan yayi.
Naja'atu kasa zaman cikin gidan tayi sai ta lalla'ba tasa hijabinta ta fito wajen gidan ta samu rumfar kwanon da jama'ar maman sajida ke zama ta zauna tana kallon yanayin garin....Tamkar bariki kowa sai abinda yake so yake yi mafi akasari ma 'yan matan garin basa yawo da mayafi a jikinsu gasu yawanci duk 'kananun kaya ne a jikinsu da wuya ka gane kafuri da musulmi....Yanayin garin sam beyi mata ba sai dai kuma yanda suke gudanar da muamularsu ta babu ruwana da kai ya burgeta.
Babur ne ya ajiye maman sajida a kofar gida, ta mike a hankali ta iske gurin da take...Maman sajida ta shiga dauko ledojin kayan miyarta Naja'atu ta taimaka mata suka fito da kayan...Sallamar mai babur din tayi suka dauki kayan suka nufi cikin gidan......suna shiga mmn sajida ta shiga aikace akaice hura wuta tayi ta d'ora madaidaiciyar tukunya sannan tazo ta zauna tana gyara kayan miya, naja'atu kuwa suna hira tana taimaka mata da yankan salak da kabeji! maman Ladi ce ta shigo gidan yara na biye da bayanta.
Mmn sajida tace"Wallahi yanzu nake zancan ku a raina." Maman ladi ta zauna kusa da ita tana fad'in "Ai nasan yau zakije kasuwa shiyasa naje na dauko su daga makarantar da kaina amma gaskiya yau kin dawo da wuri." Maman sajida tace"Wallahi nima naga saurina yau ba cunkuso a kasuwar.....Naja'atu tana jinsu suna ta hirarsu bata sa musu baki ba, haka kawai Maman ladi bata kwanta mata a ranta ba....Taji maman ladi na cewa"Amma dai yarinyar nan ta fad'a miki daga wane gari take ko."?.
Maman sajida tace"Eh daga kano take ashe gidan Alhaji Aminu dan jarida take nema tazo gurin Munira ne." Mmn Ladi tace"To ikon Allah ai sai kiyi mata jagora zuwa gidan. Mmn sajida tace"Eh insha Allah gobe da wuri zan kaita gidan.
Naja'atu takaicin maman ladi kamar ya kasheta ta lura matar 'yar bakin ciki ce sai kace a kanta take tabi ta damu! Bai dace mmn sajida na k'awan ce da ita ba tunda ita zuciyarta mai kyauce ta tabbata da mmn Ladi ce ba zata ta'ba yarda ta zauna mata a gida na yini guda ba......Kafin mmn Ladi ta tafi gidanta sai da tayi wa mmn sajida wayo ta kwasar mata kayan miya har yankakken salak din sai da mmn ladi ta d'iba sai dariyar ya'ke takeyi irin ta dubara....Ita kuwa mmn sajida sai girgixa kanta take tana mamakin rashin imani irin na makociyar tata ita da take da miji mai bata kudin cefane amma bata godewa Allah ba tazo tana d'ebe mata kayan sana'arta bata duba irin wuyar da take sha da marayun 'yayanta kullum sai tazo ta dauke mata abu a gidan, ashana wannan mmn ladi bata siya sai dai duk sanda zata d'ora girki ta shigo ta dauki tata, idan taga maginta ta bude ta zazzaga gishiri ta zazzaga har manja da mankuli tsiyayar mata takeyi...al'amarin dai na mmn Ladi babu mutunci da tausayi a cikinsa.
*Ayi hkr ayi manège*
*Vip Mdd ba haram bane naga comments dinku akan pegenmu na yau kuyi hakuri da duk wani pege da zaku karanta anan gaba a yanzu ne sa'kon labarin yake so ya isa shiyasa kuke jin rashin dadi! kuyi hakuri ku cigaba da karantawa daki daki insha Allahu zaku fahimci inda na dosa*
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA🌴🌴*
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
Mdd 44
Naja'atu na zaune tana kallon yanda Mmn Sajida keta aikin abincin siyarwarta tana kallo ta kammala komai ta shirya cikin kuloli gwanin sha'awa, Mmn Sajida nada tsabta da kula sosai a kan sana'arta shiyasa take da costomas sam ba tayin kwantan abinci komai yawan abinci idan ta fita dashi tas take siyarwa ta had'a kan kudinta..Mmn Sajida haifaffiyar jos ce iyayenta da kaninta duk suna garin tayi aure shekaru goma da suka wuce sun haifi yara biyu da mijinta kafin Allah yayi masa rasuwa, tun bayan mutuwar mijinta ta soma fuskantar matsala ta rayuwa 'yan uwanta dana mijin nata kowa kansa ya sani babu mai taimaka mata da sabulu ko omo yace tayiwa yara wanki idan taje neman taimako kafin ayi mata sai an gama wulakantata tukkuna to tunda ta fahimci rayuwar duniya haka take sai ta kama kanta ta shiga neman kudi duk domin ta rufawa kanta asiri da yayanta inda Allah ya rufa mata asiri ma gidan da take ciki na mijinta ne shiyasa wasu abubuwan sukayi mata sauki sai kawai ta yanke shawarar zamanta a ciki domin tasan babu wanda zata jewa da marayun 'ya'yanta ya ri'ke su tsakani da Allah ganin yanda duniya ta koma kowa kansa kad'ai ya sani kad'an ne masu tausayi da tsoron Allah.......Sai kawai ta yanke shawarar siyar da Kayan d'akintata shiga sana'ar siyar da abinci cikin ikon Allah Ubangiji yasa mata albarka a ciki...Yanzu Mmn Sajida tafi karfin komai sai dai wani ma yazo yaci alfarmarta, Mmn Sajida bata da rowa ko kadan sai dai abotarsu da Mmn Ladi yasa ta d'an koyi wasu munanan d'abi'u daga gurinta.
Tare suka fita da Mmn Sajidan ta zauna kusa da ita tana d'an taimaka mata da wasu abubuwan....Mazan da sukayi yawa ne a gurin yasa taji zaman gurin ya fita daga ranta, ta tsani kallon k'urrula ko kadan ta fahimci mazan garin su kuma dabi'arsu ce..Da har tayi niyyar shiga gidan kodan ta huta da kallon da ake mata sai kuma ta hakura ta daure ta zauna ta cigaba da taimakawa Mmn Sajida dan ta lura abin yayi mata yawa kowa idan yazo da kalar abinda yake so.......Naja'atu na kallon wani magidancin mutum wanda tunda ya tsaya a gurin yake kallonta yana mata murmushi, har sanda Mmn Sajida tazo kansa tana masa magana hankalinsa gabadaya na kan Naja'atu sai kace zai cinyeta...Mmn Sajida tace"Haba d'anTalle tun dazu nake magana kayi shuru yanzu idan wani na sallama kace na tsayar da kai."
Mutumin da ta kira da 'DanTalle ya shafa gemunsa a sanyaye yace"Mmn Sajida yaushe kika samu yarinyar nan lallai na kwana biyu banzo gurin nan ba." Mmn Sajida sanin halin Dantalle yasa tasha kunnu sosai tace" Bakuwa ce wannan kuma ba irin taku bace kai dai ka fad'i me kake so na zuba na had'a maka."
Yace."Ki zuba min shinkafa da wake da miya." Mmn Sajida na kokarin zuba masa tace" 'Kashi ko nama wane zan sa maka." ? Hankalinsa na kan Naja'atu yace"Ki samin 'kashi." Mmn Sajida ta had'a masa komai ta mika masa ya dauki jarkar zu'bo guda d'aya a sanyaye ya nufi cikin 'yan uwansa dake cikin rumfar kwanon da Mmn Sajida ta tanadar musu.
Yana barin gurin Mmn Sajida taja tsaki tace"Narasa wane irin hali ne da Dantalle wallahi ko wace mace ya 'kyalla idonsa a kai yace yana so. Ta kalli Naja'atu da fad'in "Nasan shi da mugun bin diddigin tsiya saboda haka kiyi taka tsantsan dashi koda wasa kada ki sakar masa fuska har Allah yasa ki bar garin nan."
Naja'atu a sanyaye tace"Nagode Mmn Sajida nima wlh mutumin gabadaya beyi min ba tunda ya tsaya a gurin nan yake kallona kamar maye." Mmn Sajida tace"Kad'an kika gani ai haka yake mugun son mata ne dashi ga shegen aure auren tsiya hanzu haka matansa hud'u amma baya cin abinci a gidansa kullum yana nan yaci mai dadi ya barsu da garau garau shike nan yawon bariki da kashewa matan bariki kudi."
Naja'atu tace"Allah ya shiryeshi idan zai shiryu.....Koda DanTalle ya kammala cin abincinsa sai yazo ya tsaya yana gyara bakin aljihunsa domun fito da kudi Mmn Sajida taga ya dauko dubu hudu ya mika mata tace"A'a Ai dari shida ne kudin abincinka." Yace."Eh na sani nayi niyyar yi miki kyauta ne ki dauki dubu biyu sai ki bawa yarinyarki dubu biyu.'' Mmn Sajida tace"Anya za'ayi haka kuwa na fad'a maka komai kuma kasan ni bana cikin wannan shirman da kuke yi."
Yace."Haba Me yasa kike wannan maganar Mmn Sajida ni bada wata manufa na baku kudi ba nayi niyya ne kuma idan inason yarinyar nan da aure zan so ta bada wata manufa ba.
Mmn Sajida tace"To godiya mukeyi Allah ya 'kara budi." Ya amsa da amin yana kallon Naja'atu da wani shegen murmushi a fuskarsa..Girgixa kanta kawai take tana mamakinsa lallai kam ya ci sunansa 'DanTalle ita wannan ko a 'kafa a daura mata shi a ta kwance da gudu, daka ganinsa idanunsa a bude suke kar!! dasu irin na mayaudara! Ya juya baya da niyyar barin gurin tabi shi da kallo! 'Tab! gabad'aya bashi da tsarin mazan da take so wani siriri dashi kamar zai karye sai dogon wuya kamar mari'kin lema a ganinta ma ina yaga kuzarin da zai tunkareta..ita duk wani siririn mutum raina shi takeyi tana ganin kamar basu da wani karfi da kuzari( Kaji wauta irin tana Naja'atu 'kananun maza ma sunfi jaraba kuma babu abinda za'a nuna musu)....Sai kusan sha daya da rabi na dare Mmn Sajida ta siyar da abincinta suka harhada kayan suka shiga cikin gidan.
Karfe takwas na safe sun shirya Naja'atu tayi wanka ta shirya tsaf Mmn Sajida ta bata sabuwar atampa da mayafi tasa a jikinta sannan kuma ta hada mata wasu atampopin kala uku tasa mata a leda viva Naja'atu ta dinga yi mata godiya tana mamakin karamcin matar gaskiya samun Mai hali irin nata sai an tona.
Suna kokarin karyawa Mmn Ladi ta shigo gidan, ganin naja'atu cikin sabuwar atampa sai tayi kici kici da fuska ta wani dogare a bakin kofa tsabar bakin ciki da hassada yasa ta kasa shiga.
Mmn Sajida tace" Ki shigo mana ki zauna dama yanzu nake cewa zan aika Walid ya fada miki ko zaki zo muje tare."
Mmn Ladi ta ta'be bakinta tana girgiza kanta da fad'in "Babu inda zani aikin gidana ma ya isheni."
Mmn Sajida tace"To shikkenan ki shigo kisha tea gashi muna hadawa.
Babu kunya Mmn Ladi ta shigo tana ya'ke da fadin "Kamar kuwa kin san ban karya ba har yanzu dan yau mutsiyacin mutumin nan ko 'kwandala bai bani ba ya futa.
Mmn Sajida tace" Ke Mmn Ladi kiji tsoron Allah ki daina tsinewa mijinki wallahi ki dinga hakuri da yau da gobe idan kina ganin ba zaki iya jurewa ba to ki nemi sana'ar yi amma zagin miji da tsine masa bashi da amfani."
Mmn Ladi na had'a tea tace"Ke rabu dani dan Allah wallahi jiya da kyar nayi bacci saboda tsabar takaicin da mutumin nan ya 'kunsa min haba me za'ayi da talauci ace kullum a gidanka baka da sakakken abinci sai shinkafa da wake da mai da yaji haba jama'a wannan wace irin masifa ce ace kudin cefane dari biyu mtsssw!" takare maganar tare da jan dogon tsaki
Mmn Sajida tace"To ina laifi da kika samu shinkafa da waken ni na samu mana! kina kallo fa ni nake ciyar da kaina da 'ya'yana ke kin samu kina rainawa wallahi ki dinga godewa kad'an sai kiga Allah ya wadataki.'' Mmn Ladi kur'bar tea take tana dangwalar bread da miya tace"Duk yanda zanso ki fahimta ba zaki fahimta ba mu bar maganar kawai."
Mmn Sajida tace"To ai dole na bari tunda bakya so a fada miki gaskiya." Dariya kawai tayi ta cigaba da cinye musu naman dake cikin miyar gabansu.
Naja'atu tun abun na matar na bata mamaki har ya dawo bata dariya ikon Allah kenan wannan shi ake kira Allah daya gari bambam! Mmn Ladi sai da ta cika cikinta tsaf sannan ta karkad'e zaninta mike tare da kad'a kan yaran ta tafi kaisu makaranta...Naja'atu sai so takeyi suyi gulmar Mmn Ladi ita kuma Mmn Sajidan ta'ki yarda, ta lura da Mmn Sajida tana da kyakkyawar zuciya akan matar.
Naja'atu tayi mamakin ganin gidansu Munira, ita kam bata dauka zata ganshi haka ba sabida irin karyar da Munira take musu a aji cewar babanta mai kudi ne tsohon dan jarida ne da yake aiki a tashar bbc ta kasar waje! bayan nan kuma yana da company na siyar da motoci da sauransu 'karya iri iri Munira keyi musu su kuma suna yarda sabida ganin irin yanda ake zuwar mata ziyara cikin babbar mota hade da kayan abinci iri iri shiyasa suka amincewa...........Munira bata gidan wai sun tafi shopping ita da Muktar..Mmn Ladi bayan ta huta ta mike da niyyar tafiya, Naja'atu taji kwallah na kokarin zubo mata dan zaman da tayi da matar taji bata son rabuwa da ita... Mahaifiyar Munnira na hakkince a kan kujera Cikin nuna isa da nuna ita wata me kudi ce ta kalli Mmn Ladi da fadin"Ba zaki bari a kawo abinci kici ba sai kice zaki tafi."
Mmn Ladi tace"Alhamdullhi Hajiya kafin na fito daga gida sai da na karya tukkuna." Mommyn Munira ta dan gyara zamanta cikin isa ta dauki pose dinta dake gefanta ta zuge zif din ta dauko dubu daya sabuwa kar da ita ta mika mata da fadin"Gashi ki shiga napep."
Murmushin takaici Mmn Ladi tayi tace"Nagode hajiya wallahi bazan karbi kudinki ba domun kuwa ina da kudin motar komawa gida ta kalli Naja'atu da fad'in" To Naja'atu saduwar alkairi idan kin koma gida ki gaishe da mutan gidanku.'' Naja'atu tace"Nagode sosai insha Allah zan fada musu." Mmn Ladi sa kai tayi ta fita daga palon tana mamakin izgili da wulakanci irin na matar gidan koda yake dama tun kafin ta tako kafarta cikin gidan take da labarinta sai 'karyar arziki alhalin kowa yasan aikin da babban d'ansu yake yi a gari 'Ri'ka'kken d'an 419 ne (damfara) Laya ta mussaman ce dashi wace yake ma'kalawa a 'kugunsa yana shiga ko ina yayi satarsa ya fito ba tare da an ganshi ba, shiyasa komai na rayuwa baya yanke musu a gidan kuma iyayensa sun sani basu hanashi ba sai ma 'kara masa kwarin gwiwa da suke!.....Duk kuwa d'an kasuwar da ya sake yayi mu'amula da *Bash* to ya zama sorry dan sai yayi masa tas! kuma yasa malamansa sun d'aure masa baki *Bash* mugun hatsabibin mutum ne.......Jama'ar garin kuwa tamkar masu jin tsoro an rasa wanda zai fito yayi magana kowa yaja bakinsa yayi shuru sai dai idan surutu ya tashi ayi a bayan fage.
Naja'atu har duhun dare ya shigo tana zaune a guri guda a rakube dan dama Mommyn Munira bata da sakin fuska tunda suka gaisa wata magana bata sake shiga tsakaninsu ba....Sai bayan magariba ne da taga zaman palon ya isheta ta mike salo salo ta nufi wani daki dake cikin palon taje ta zabga tagumi tana tunanin wannan wane irin shopping ne Munira ta tafi tun safe bata dawo ba gashi dare yayi...Gaskiya sai dai tana tunanin bayan shopping din sunje wani gurin ita da saurayin nata......Abinda naja'atu bata sani ba shine Munira ma kwata kwata bata kwana a gidan ba tana can gidan Muktar din kwananta biyu kawai dai Mommyn tata ce ta tsara cewar sun tafi shopping ne.............. Kwanciya tayi tana share hawaye abin duniya ya isheta gabadaya kuma hankalinta yayi gida tana tunanin yanzu wane hali iyayenta suke ciki sai Musaddiq da yake yawan fad'o mata a rai! Abbah Abbas kuwa dama tuni ta cireshi daga cikin ranta tana ganin ta ku'buta daga hannunsa har abada.
Mai Aikinsu ce ta shigo da sallama a bakinta tace"Wai ki fito kici abinci inji Hajiya." ta mike da sauri tare da fadin"To gani nan."
Mai aikin ta juya ta fita daga dakin minti biyu ta mike tabi bayanta..Tana fita taga Mommy a zaune a gurin cin abinci da waya a hannunta tana fad'in "Munira kina da hankali kuwa yau kwananki biyu a waje ko kiran waya bakya yi ashe kina so jama'ar gari su fargaba da lalacewar da kukeyi keda muktar din tun kafin auranku ace kungama sanin junanku wannan wace irin rayuwa ce? to komai dare ki dawo gida domun tun safe kike da ba'kuwa kawarki ce tazo daga kano.
sama sama taji muryar Munirar na fad'in " Ayya Mommy dama yau zan dawo wallahi Muktar din ne bashi da lafiya shine na tsaya na kula dashi." Mommyn tace"Bashi da iyayene da lallai sai kece zaki kula dashi ai koma meye zai faru sai ku bari a shafa fatiha tukkuna." Tace"mommy ba lallai ne ya samu kulawar da yake bukata ba daga gurin mamansa ni kuma shiyasa na tsaya na kula dashi har ya warware kuma mommy meye yayi saura a tsakanina dashi tunda iyayenmu sun mallaka mana junanmu muktar ya bada sadakina ni banga laifi ba dan na kwana a gidansa ba."
Tace"Ni ba cewa nayi kiyi min tsari ba duk rayuwar da kike so ita za kiyi ni dai nace ki dawo gida yau kinji na fada miki." Tace"Insha Allahu ko dan saboda Naja'atu zan dawo yau."
Naja'atu jikinta ne yayi bala'in sanyi jin irin abunda ke faruwa da rayuwar Munira! dama sai da tayi zargin wani abu ashe Munira bata da kamun kai tana bin saurayi har gidansa tana kwana dashi ba tare da aure ba, gaskiya al'amarin ya bata mamaki mutuka.......Mommyn ta kalleta bbu fara'a a fuskarta tace"Kixo ki zauna kici abinci munyi waya da ita tace"Gata nan a hanya." Naja'atu kawar da mamakin fuskarta tayi ta nuna kamar ba taji wayarsu ba taje ta zauna gurin cin abincin tace"To bbu komai Allah ya dawo da ita lafiya."
Tana kokarin mikewa daga gurin ta amsa da "amin'' *Bash* ne ya shigo palon yana sanye da k'ananun kaya wanda sukayi masa kyau sosai *Bash* irin mazan nan ne masu tsayi da murd'ad'adan jiki shiyasa k'ananun kaya suke masa kyau fari ne tas gashi kyakkyawan gaske! kyawunsa da kudinsa da kuma yanayin tsarin hallitarsa yasa 'yan mata suke haukacewa a kansa! shi kuma yana cin karansa babu babbaka a kansu duk wacce ya bukaci yayi sex da ita babu gardama zata amince masa *Bash* mugun manemin mata ne kuma dan shaye-shaye na bugawa a jarida ga neman nemanta ga *Luwad'i* duk yana yi...sana'arsa tafi kala goma domin *Luwadin* ma da manyan mutane yake suna bashi mahaukatan kudi....Shiyasa gabad'aya bashi da ra'ayin aure yana ganin aure kamar damuwa ne tunda babu abunda ya nema ya rasa to zai iya kare rayuwarsa ba tare da ya auri wata mace ba.
Naja'atu kallo guda tayi masa taji gabanta ya wani irin faduwa! a take taji wani irin sonsa ya sauka a zuciyarta, duk da ta kasance mace mai kyau amma kyawun *Bash* yayi masifar tafiya da imaninta Wow! irin maxan da take bala'in so wannan hand some din waye zai had'ashi da Salim bare kuma wani tsoho irin Abbah Abbas!sum she idonta tayi tana jin yanda gabanta ke faduwa kaunar *Bash* na sake ruruwa a cikin zuciyarta.
To shima nasa 'bangaran kallo guda yayi mata yaji yana sha'awarta dan yana bala'in son mace duguwa saboda tana da zurfi duk irin mi'kewar da joystick dinshi tayi idan yana sex da doguwar mace tana samu guri..Ya lura yarinyar za'a je da ita ga tsayi ga nonuwa tubarkallah...Yana shafa tarin sumar kansa yaja kujera ya zauna da murmushi mai kyau a fuskarsa...Mommy tace"Ashe baka fita ba dama."? Yace." Tun misalin shida na safe na fita ban jima da dawowa bane." Tace"Okey to bari na had'a maka abinci ko.'' Yana kallon Naja'atu yace"Mommyn wannan babyn fa duk cikin famliy naki dana Daddy ban san da ita ba." Tace"Sunanta Naja'atu friend din Munira ce ta kawo mata ziyara tun daga kano." Yace."Wow! beb sannu kinji ko ya kano me yasa ban ta'ba saninki ba dik da cewar duk wasu friends din Munira na sansu amma ke nayi mamakin da ban ta'ba saninki ba.
A sanyaye tace"Tare mukayi *Andal skull* da Munira sunana Naja'atu Abbas 'kofar na'isa." Yace."Okey sai yanzu na gane me yasa duk sanda muka je visiting bana haduwa dake.? tace"mybe bana kusa ne." Girgixa kansa ya shiga yi yana sakar mata kayataccen murmushi kafin yace."Amma kin san kina da kyau ko"? Murmushi tayi ta sinne kanta wani irin dadi na ziyartar zuciyarta da alama ta fahimci cewar guy ya fad'a tarkonta kamar yanda ta fad'a nasa....Mommy kuwa barin gurin tayi tana jin dadin ganin yaron nata ya tanka Naja'atu addua take Allah yasa su daidaita kansu dan tana bala'in so taga yayi aure.....
Cikin sigar Yaudara da sigar janye hankali ya kwantar da murya yace."Naja'atu kallon farko nayi miki naji ina sha'awarki ina fatan zaki mallaka min kanki koda na rana daya ne." Taji gabanta ya yanke ya fad'i! Ashe Sha'awarta yake ba sonta yake da aure ba?
Ta dan bata fuska tare da fad'in "Gaskiya bana cikin jerin irin wannan matan." murmushi yayi yace."Nima na fahimta ke me hankali ce okey idan kin shirya aure nima na shirya zan aureki ina tunanin zan karya al'kawarin dana daukarwa kaina a kanki....Jin wannan magana tasa yasa wani irin farin ciki ya lullu'beta babu shakka tazo garin Jos a sa'a tunda tayi nasarar samun wannan guy da yake da wahalar samu......
*Waye yake maganar Salim da Abbah Abbas idan su Bash na guri😅*
*Ammafa kada ku dauka ina team din Bash No!✖️ Har yanzu ina tare da Abbah😢 ina kuma taya shi alhini da jimamin faruwar wannan al'amari*
*Tofa gwanar taku ta tsinci dami a kala duk ta rud'e ta samu saurayi mai jini a jika wanda zai iya da jarabarta anata ganin Bash ne zai iya dauke mata dukkanin laluranta akwai dramar😅*
*Littafin na kudi ne..!*
Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake
Vip gruop #600
Normal gruop#300
accont: 0542382124..Binta Umar gtbank..Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA🌴🌴*
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
Mddbhrmbn45
*Bash* ya sake tausasa muryarsa kamar wani mutumin kirki yace."Idan kin amince min da wuri nake so ayi komai a gama dan akwai tafiyar da take tunkaro ni aiki zai kaini kasar Ghana inaso in tafi dake can sai muyi amarcinmu hankali kwance."
Lumshe idonta tayi tana jin wani irin feelings na taso mata jin maganar amarci yasa ta sake kwadaituwa da auran *Bash* domin tana ganin a yanzu za tayi irin auran da take muradi.......Cikin wani irin yanayi Tace"Zaka iya auran bazawara."? *Bash* yayi sak yana kallonta, da wani irin yanayi na alhini gami da damuwa tace"Ina da aure yanzu haka dalilin auran dolen da akayi min da mijin 'yar uwata data mutu yasa nazo nan garin.....Tiryan tiryan ta bashi labarin rayuwarta...
*Bash* ya shiga murza fatar goshinsa cikin damuwa yace."Amma banji dadin wannan labarin naki ba wallahi wannan dattijon yayi min shigar sauri amma babu damuwa tunda ina sonki zan iya auranki a haka yanzu babban burina ya sake ki dan yanda kika bani labarinsa na fahimci mai taurin kai ne watakila dik wannan abun da kikayi masa sai iya 'kin rabuwa dake amma idan yasa gardama da taurin kai sai kawai muyi maganinsa." Tace"Kada ka damu a jikina ina jin zamana dashi yazo karshe zai iya sakina idan yaji na zubar masa da ciki domin yana da bala'in son yara bana tsammanin zai iya hakura ya kyaleni.....Kuma zan tura masa text domin na tabbatar masa da cewar cikinsa ya lalace nasan hakan sai sake tunzurashi...
*Bash* yace."Okey ina ganin yanzu ma zaki iya tura masa text din ayi ta ta 'kare dan wani irin kishinsa nake ji a cikin zuciyata." Murmushi tayi tare da mika hannunta domin kar'bar tsadaddiyar wayar tasa.......Daidai lokacin Munira ta shigo palon hannunta rike da wasu ledoji sha'ke da kyan ciye ciye..Ganinsu zaune guri guda yasa tace" Kai gaskiya kunyi bala'in dacewa da juna kada dai har soyayya ta shiga tsakaninku gaskiya idan haka ta kasance zanfi kowa jin dadi wallahi... *Bash* na shegen murmushinsa yace."Munira kina da wannan Friend din baki ta'ba nuna min hotonta ba ai da tuni nine zan aureta amma kika bari wani tsoho yayi min shigar sauri." Munira ta 'karaso gurin tana wata irin dariya ta farin ciki ta bawa Naja'atu hannu suka tafa suna dariya..Munira ta zauna kan kujera tana fad'in"Wallahi Broth Allah ne kawai yayi ba kai zaka fara auran Naja'atu ba amma tuntuni na dade dayi maka sha'awar auranta kawai sabida nasan baka so ayi maka maganar aure yasa banta'ba nuna maka hotonta ba amma yanzu naji dadi sosai daka ganta da idonka kace kana so."
Cike da sha'awa yace."Munira Friend dinki tayi sosai dan lokaci guda ta tafi da zuciyata matsalata guda auran da yake kanta shin wace shawara kuka yanke akansa."
Munira tace"Haba broth kada ka damu wannan auran ai dashi da babu duk daya suke insha Allahu sai ya saketa komai nacin sa."
*Bash* ya mi'ke tsaye idanunsa kan Naja'atu yana mata wani irin kallo wanda kana ganinsa kasan na sha'awa ne yace"Ki rike wayar a hannuki zuwa gobe da safe zan 'karba amma ki tabbatar da cewa kinyi masa text din da kika fad'a."
Tace"Insha Allah zan masa kada ka damu." Hannunsa ya zura a aljihun jins din dake jikinta ya wani tsira mata shu'uman idonsa gabad'aya jikinsa ya mutu ai dole ne ya fita ya nemi biyan bukatarsa...Munira ta dinga dariya tana fad'in "Lallai yau ina kallon soyyaya mai zafi! Had'uwar farko Naja'atu kin rikita min dan uwa gaskiya naji dadin wannan al'amarin." *Bash* Yayi saki murmushi had'e da sosa kanshi ya kama hanyar fita yana wata shegiyar tafiya irin ta marasa kunya.
Naja'atu murmushi kawai take dadi na ziyartar zuciyarta salon kallon soyayyar da *Bash* ke mata shine yake sake rikita ta tana jin sonsa na sake karuwa a cikin zuciyarta..
Tare suka shiga dakin ita da Munira ta zauna gefan gado tana ta duba wayar Bash din Hotonansa ne kala kala yawancin pictures din bana Najeria bane yayi su a kasashe daban daban! ganinshi rungume da turawa black americas bai dameta ba tana ganin ai wayersa da kudinsa ya cancanta yayi mu'amula da kowane irin jinsin mutum..Munira ta fito daga wanka tana kintsa jikinta tace"Gaskiya Naja'atu kinsha wuya na tausaya miki kuma wannan matar data taimake ki yana da kyau naje nayi mata godiya." Tace"Gaskiya kam yana da kyau idan an kwana biyu muje na rakaki gidanta...Munira ta zauna kusa da ita tare da fad'in "To alhamdullhi Yanzu mun samu ciki ya zube ba tare da munsha doguwar wahala ba yanzu babban abunda yake gabanmu shine rabuwa da wannan tsohon.
Hankalinta nakan wani had'ad'dan hoton *Bash* wanda ya dauke shi yana sanye da kayan wanka a bakin swimming hoton yayi masifar dauke mata hankali ganin zahirin *Bash din* ya sake firgitata sai ta sake kwadaituwa da auransa hakika ta samu nasarar auransa to ta kere sa'a kuma zata iya shiga koina dashi ta nuna shi da sunan mijinta ba kamar Abbah Abbas ba da take jin kunya a dangatata dashi a matsayin miji...
Munira ganin Naja'atu bata fuskantar maganar da take yasa ta le'ka cikin wayar tana dubawa! Dariya tayi tace" Naja'atu kenan naga alama kema kin mutu akan Brother d'ina Humm! na taya ki farin cikin samun zuciyar *Bash* 'Yan mata da yawa suna sonsa baya ta'ba sauraransu amma ke gani daya yayi miki ya haukace harda maganar aure duk da kasancewarki bazawara yana da kyau kiyi gaggawar nemawa kanki mafita tun kafin damar da kika samu ta kufce miki."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Yanzu wace shawara kike ganin ta dace? Ni da cewa nayi zan tura masa da text na fada masa cikinsa ya zube kuma ina nan ina jiran takardarta." Munira tace"Wannan shawarar tayi.....Kawo wayar na rubuta masa text din...Naja'atu tasa numbarsa da yake amfani da ita a saudia, Munira babu sallama ta shiga rubuta text din kamar haka.
_Ni ce Naja'atu ina so in tabbatar maka da cewar wannan cikin daka yi min yabi rariya dama tun kafin haka ta faru sai da na fad'a maka bani da ra'ayin zama da kai ballantana har na haihu dakai komai ya faru son zuciyarka ne ya janyo maka....Abbah banso muyi irin wannan rabuwar da kai ba amma ina ganin hakan shine daidai Ni ce dai Naja'atu ina nan cikin koshin lafiya bayan samun nasarar rabuwa da masifar daka 'kunsa mun a cikina ina nan ina jiran saki daga gareka idan baka sakeni ba to kuwa zanyi ta zama a inda nake har'karshen rayuwata_
Kafin a tura text din Naja'atu sai da ta karanta kusan sau biyar tana ganin kamar maganganun sunyi tsauri da yawa! amma kamar wacce aka sawa lemon tsami a baki ta kasa cewa komai tana kallo Munira ta tura text din ya tafi gabanta sai ya tsananta fad'uwa cikin zuciyarta tana ji kamar bata kyauta ba...Munira tace"Yana da kyau ma a tura masa ta whasap dan naga kamar yanayi ko."? A sanyaye tace"Duba ki gani." Munira ta shiga dubawa taga numbarsa tana whasap amma kuma kwanansa biyu bai hau ba, dan tun ranar daya bude ya saurari audion da Salim ya turo masa bai sake kunna data ba dan dama ba kasafai yake shiga whasap din ba.....Tace" Ya kwana biyu baya kai amma Bari a tura masa domin ya dauki abin da muhimanci."
Naja'atu dai shuru tayi Munira sai zartar da hukunci takeyi ita kuma gabanta sai faduwa yake tana adduar Allah yasa ya mayo da martanin saki.
Munira kayan ciye ciyen data shigo dashi ta baje musu suka dinga ci suna hira Naja'atu dai daurewa kawai take bini bini sai ta duba wayar dake hannunta wai ko ya turo amsa.....Jiki a sanyaye ta ajiye wayar ta nufi toilet din dake cikin dakin tayi wanka ta kimtsa jikinta tare da sanja pad ta fito Munira ta bata sababbin kayan bacci tasa tasa turare ta zauna tare da daukar wayar tana sake dubawa...Ita kuwa Munira tana kwance a bad daga ita sai 'karamar vest da gajeran wando wanda ya matseta sosai pictures take dauka kala kala tana turawa Muktar ta whasap.....
*Allah ya shiryaki Munira*
'Bangaran Abbah Abbas kuwa bai samu damar duba wayarsa ba sai lokacin da yazo kwanciya dan basu dade da shiga masaukin nasu ba sun fita duk gabadayansu sun dan shiga kasuwa dalilin barin 'kasar da za suyi jibi idan Allah ya nufa dama kwana goma sukeyi ko sati biyu suke dawowa........Halisa na kokarin kwanciya a kusa dashi taga ya mi'ke zumbur! Gabanta ne ya fad'i! tayi saurin matsawa dan ta dauka marinta zai yi! sai dai kuma ganin ya tsirawa fuskar wayarsa ido yasa da sauri ta 'leka kanta tana dubawa! Text din ta karanta tsaf! kuma ta fahimci daga Naja'atu yake...Wani matsiyacin dad'i ya rufeta wayyo yau da ita kadaice a gurin sai ta taka rawa ciki ya zube burinta ya cika.......Kukan munafurci ta fashe dashi ta shiga tafa hannu tana fad'in"Innalilihi wa'ina ilahi raji'una! yanzu yarinyar nan sai da ta zubar da cikin nan? anya naja'atu tayi maka adalci kuwa? me kayi mata take maka irin wannan 'kiyayyar Allah ya baka zuria tayi maka asararsa kuma sabida bata da kunya cikin izigila take fad'a maka ga abunda ta aikata maka kai jama'a amma wannan yarinyar bata kyauta ba wallahi."
Shuru yayi domun bakinsa mutuwa yayi murus! ya dinga kallon fuskar wayar yana ta karanta text din kamar me koyon karatu!! ya jima cikin wannan yanayin kafin ya samu damar furta kalmar innalilihi wa'ina ilaihi raji'un!!! Ya kashe wayar ya ajiyeta kana ya mike ya nufi toilet domun dauro alwala...Halisa murmushin jin dadi tayi ta juya bayanta tare da jan bargo ta rufe jikinta cike sa nishadi da farin ciki bacci mai dadi ya dauketa.
Dadduma ya tsaya ya fuskanci al'kibula ya tayar da sallah...Raka'a biyu yayi ya jima a sujjadar karshe yana rokon Ubangiji sassauci ya d'ago tare da sallame sallahr nan ma ya jima hannunsa a sama yana addua kafin ya shafa a fuskarsa ya mike yana jin wani kuzari a jikinsa zuciyarsa tayi wasai babu wani bacin rai tabbas tunda har Allah ya zartar da irin wannan hukunci to hakan shine alkairi a rayuwarsa.....'Yar jakarshi da yake tafiya da ita ya dauko ya zauna kasan kafet ya bud'eta a nutse ya dauko wani memo ya ya bud'e ya yagi pepar d'aya ya dauki biro a nutse ya soma rubutu a jiki....
*Jikina na karkarwa na le'ka domun naga mai yake rubutawa......😤 yanke jiki nayi na fad'i hawaye na ziraro min shikkenan Naja'atu ta cuci kanta*
_NI ABBAS SAMA'ILA NA SAKI MATA TA NAJA'ATU MALAM SANI SAKI DAYA INA RO'KON ALLAH YASA HAKA SHINE YAFI ALKAIRI A TSAKANINMU._
*Kuyi hakuri dan Allah👏🏻😢 Nima ba'a son raina ba Labari ne yazo a haka*
*Littafin na kudi ne..!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake.
Vip group #600
Normal gruop#300
accont 0542382124...Binta umar gtbank..Idan katin waya zaki turo kiyi min mgn ta whasap da wannan numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA🌴🌴*
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
Mddbhrmbn46
A nutse ya linke takardar da yayi rubutun ya bud'e tsakiyar memo d'in yasa ya mayar da jakar ya rufe tare da mikewa da ita a hannunsa zuwa yayi a dana ta a inda take kana ya nufi bed din ya kwanta yana jin nutsuwa da kwanciyar hankali na saukar masa a zuciyarsa tabbas rabuwa da auran Naja'atu shine alkairi a tare dashi, dan idan ya tilasta kansa zama da ita to kuwa zai ta had'uwa da takaici da 'bacin rai watakila ma sanadiyar hakan ciwo ya kamashi dan a yanda yake da kaunar 'ya'ya gami da adduar Allah ya bashi zuria da yawa baya tsammanin zai iya zama da kowacce irin macece mutukar zaiyi wahalar dasa 'kwai ta zubar masa babu shakka ko wacece zai iya rabuwa da ita rabuwa ta har abada...Cikin kwanciyar hankali yayi bacci da asubah ya tashi zuciyarsa wasai baya ta'ba nadamar abinda ya aikata ga yarinyar.
'Bangaran Naja'atu kuwa kwana tayi tana munanan mafarkai wanda taga Halimatu tazo mata da wasu fararan kaya masu kyalkyali sai dai yanayin yanda taga 'Yar uwartata ya bata tsoro fuskar Halimatun babu walwala ta tsira mata ido kawai tana kallonta ita kuma sai magana take mata tana kokarin rike hannunta sai ta fizge ta bar gurin da sauri ta dinga waige waige tana kiran sunanta amma bata ganta ba......Sannan kuma duk a cikin mafarkin taga mahaifiyar ta na kuka ita da Mussadiq suna kiranta....a tsananin firgice ta tashi tana had'a gumi! ta dinga kallon dakin gabanta na fad'uwa gaskiya mafarkin nan ya bata tsoro tunda Halimatu ta rasu bata ta'ba yin mafarki da ita ba sai yau shiyasa jikinta yayi sanyi...Wayar *Bash* ta dauka ta kunna ta haske dakin a maimakon ta tashi taje ta dauro alwala sai kawai ta shiga dube dube a wayar wai ko bayan kwanciyarta Abbah Abbas ya turo replay ta gama dube duben ta ba taga komai ba a sanyaye ta ajiye wayar ta mike ta nufi bandaki domin yin alwala.....Kafin ta tayar da sallah sai da ta tashi Munira tukkuna ta hau dadduma...Munira kuwa zuwa tai tayi fitsari ta dawo ta sake kwanciya dama can Munira bata sallah sai gari ya waye...Naja'atu bayan ta idar da sallah zama tayi kan daddumar abin duniya ya dameta mafarkin da tayi yayi masifar bata tsoro mussaman ganin mahaifiyarta na hawaye tasan duk inda suke suna can cikin tashin hankali da damuwa, ta dinga share hawaye tana fad'in Ba laifina bane tun farko na fada muku bana so bana sonsa kuka kasa fahimtata." Munira tayi firgigt ta mike zaune tana kallonta tace"Naja'atu lafiya kike kuka."? Hawaye ta share tace"Munira wani mummunan mafarki nayi wallahi tabbas iyayena na cikin damuwa da rashin ganina." Munira tace"To ai dama dole su shiga damuwa da rashin ganinki ai tun farko laifinsu ne yanzu dan sun neme ki sun rasa ai kansu zasu tuhuma sai su gane auran dole ba abune mai alfanu ba."
Girgiza kanta kawai tayi tace"Munira naga Yaya Halimatu a mafarki tana cikin 'bacin rai ga Mussadiq na kuka yana kiran sunana jikina ya soma sanyi da wannan al'amarin wallahi." Munira taja tsaki tace"Ai shikkenan sai kije kiyi tayi waye ya fada miki mafarki gaskiya ne? dan Allah ki daina wannan maganar idan zaki saki jikinki ki saki jikinki kawai ki watsar dasu koma meye ya faru ai sune suka janyo me yasa suka aura miki wanda bakya so."
Girgixa kanta ta cigaba dayi hawaye na sake zubo mata...Ita kuwa Munira ta mike ta nufi bandaki tana surutai kan damuwar da taga Naja'atun ta shiga....
Abbah Magaji na zaune yana karya kummalo Halisa ta fito daga dakinta hannunta rike da wayarta ta zauna kusa dashi, tace"Kaga ina ta kiran numbar ba dauka ba kuma wannan numbar itace nake tsammanin ta 'Kawarta, dan bana mance ranar da tazo tace na bata aron waya zata kira 'kawarta a jos."
Yana goge bakinsa yace."Bani numbar na gwada kira." Wayar ta mika masa yasa numbar a wayarsa cikin ikon Allah tana fara ringing aka dauka....Hands free yasa yayi sallama...Munira ta amsa da fad'in " Da waye nake magana."? Yace."Kina magana da wani bawan Allah ne daga kano shin ko kinsan wata yarinya Naja'atu."?
Naja'atu sai da ta kusa sakin fitsari a wando jin muryar Abbah Magaji radau a kunnanta!!! Munira tayi saurin kallonta idanunta duk sunyi gwale gwale. Abbah Magaji yayi gyaran murya had'e da fad'in "Hello kina jina kuwa."? Munira ta shiga inda inda da fad'in " A'a ban santa ba wallahi." Yanayin yanda take maganar cikin rashin gaskiya yasa ya fahimci cewar yarinyar da hadin bakinta dangane da faruwar al'amari...Yana kokarin yayi magana Munira ta kashe wayar suka 'kurawa juna ido ita da Naja'atu, ya akayi tun ba'aje ko ina ba asirinsu zai tuno..Naja"atu kuwa ai tuni hawaye sun 'balle mata fargaba da tsoro duk sun cika mata zuciya.
Abbah Magaji yabi wayar da kallo yana mamakin kashe masa da yarinyar tayi girgiza kansa yayi tabbas biri yayi kama da mutu, wayar ya sake kira....Munira ta zabura tana kallon wayar ta'ki dauka har ta katse Abbah magaji ya sake kiran wayar nan ma Munira taki dauk'a..Sai kawai ya ajiye wayar yana murmushi hade da kallon anty Maryam yace."Duk yanda akayi yarinyar nan tasan inda Naja'atu take kuma da alama da akwai hadin bakinta dangane da faruwar al'amarin." Anty maryam tace"Nima tunda naji yanda take amsa maka a tsorace yasa na fahimci tana da masaniya akan abinda yake faruwa yanzu koda anje jos din ai ba'asan a ina za'a same inda yarinyar take ba ballantana a tambayeta inda Naja'atun take." Yace."Kada ki damu mutukar layin yana aiki zansa ayi min bunkicen inda suke gobe zan shirya na nufi jos din.
Tace"To Allah yasa a dace ai gobe ma abokin naka zasu dawo ko."? Yace."Eh insha Allah bana tsammanin ma zai sameni dan da wuri zan tafi." ajiyar zuciya ta sauke tana sake tausayawa Naja'atu halin data jefa kanta.
Munira tace"Dallah ki daina kuka mtwwss wai sai me idan sunzo sunga inda kike ke ba zaki iya kaisu kuto bane alkali ya kwatar miki 'yancin ki ko dole ne akace sai kin zauna da wanda suke so ni wallahi banta'ba ganin inda akayi hakaba." Naja'atu na kokarin yin magana Bash ya shigo dakin yana sanye da t_shat fari tas da 3qutar wuyansa sanye da siririyar sarqa tamkar wani arne sai wani irin kamshin turare yake mai dadi! Yana ganin Naja'atu na kuka yaji hankalinsa ya tashi ba tare da tunanin komai ba ya zauna kusa da ita had'e da rungumo kafadarta yana tambayar abinda yasa ta kuka! Naja'atu tsorata tayi ta matsa gefe tana share fuskarta...Munira ce ta shiga fad'a masa abinda yake faruwa...Tsaki yaja ya dauko wayarsa dake cikin aljihun wandon jikinsa ya mikawa Munira wayar da fad'in "Ki samin numbar mutumin da ya kira yanzu ni zan fada masa Naja'atu tana jos sai me."?
Da sauri Naja'atu ta kalleshi yace"Baby maganar rufe rufe bata kamata ba gwara ayi komai a bayyane ni zan tsaya miki a duk inda za'aje ba zaki koma gidan wannan tsohon ba tunda bakya sonsa zan shigar miki da 'kara kuto."
Munira tace"Nima haka nace mata ta daina kuka tana tayar da hankalinta ai akwai sharia!
Naja'atu girgiza kanta tayi tana hawaye tace"Bash ina ganin kima da darajar iyayena bana so na 'bata musu rai ko kuma na tozartasu dan Allah kada wata mummunar kalma ta shiga tsakaninka da yayana kaji ko."
Yace."Baby ke kina daukar al'amarin da sauki ko? okey na fahimci kaunar da kikewa mahaifanki bai kai wanda kike min ba ina ganin zan cireki daga rayuwata kawai shi yafi alkairi.
Da sauri ta ri'ke hannunsa tana girgiza kai tace"Wallahi ba haka bane ban hanaka ka kira yayana kuyi magana ba amma kada ka zageshi ko ka fada masa mummunar kalma." Yace."Okey na fahimce ki insha Allah zan kiyaye."
Abbah Magaji na kokarin shiga motarsa kira ya shigo wayarsa koda ya duba sai yaga sabuwar numbar, zama yayi cikin motar tare da kara wayar a kunnasa.....Bash yace."Sunana *Bashir Aminu dan jarida Jos!* Abbah magaji jin an kira sunan Jos yasa yayi saurin amsawa da fad'in "Malam Bashir ni kuma sunana Magaji Sani ina garin kano ina fatan naji kyakkyawan labari daga bakinka.
Bash yace." Inaso na sheda maka cewar 'Yar uwarka mai suna Naja'atu tana hannuna yanzu hakama tana kusa dani." Abbah Magaji cikin farin ciki yace."Alhamdullhi Allah mungode maka daka bayyana mana wannan yarinyar dan Allah inaso ka bata wayar zamuyi magana.
Bash yace."Wannan lokacin baizo ba tukkuna Alhaji Magaji shin mai yasa kuka d'aurawa yarinyar nan aure da wanda bata so? kun san illar dake tartare da irin wannan auran kuwa.'"? Abbah Magaji yayi kasa'ke! jin irin maganganun da Bash din ke masa." Katse shi yayi ta hanyar fad'in "Kaga mu bar wannan maganar tukkuna domin yanzu mu ba itace a gabanmu ba ganin yarinyar nan da sanin halin da take ciki shine a gabanmu maganar aure dole bata taso ba."
Bash yace."Naja'atu na nan kalau kamar yanda kuke fata sai dai kuma cikin da take dauke dashi ya zube!!!
Abbah Magaji yace."Subahanallahi garin ya akayi haka ta faru."? Bash yace."To muma bamu san ya akayi hakan ta faru ba dan kafin tazo garemu al'amarin ya kasance." Cikin jimami da damuwa Abbah Magaji yace."Allah ya mayar da alkairi ku kuma Allah ya saka muku da alkairi insha Allahu gobe da wuri zan dauko hanya inaso ka bani cikakken address d'in inda zan same ku.''
Bash yace."Babu damuwa zan baka address din inda muke a garin jos zuwa anjima zan tura maka text sai ka duba."Abbah Magaji yace" To nagode sosai Allah ya saka da alkairi." Sallama sukayi da juna kowa ya kashe wayarsa.
Abbah Magaji jikinsa a sanyaye ya nemi numbar abokinsa domin ya sheda masa cewar anga matarsa amma kuma baya tsammanin zai iya fad'a masa cewar yarinyar ta samu nasarar zubar masa da jiki, shi yanzu gabad'aya kunyar abokin nasa ma yake wallahi hakika da yasan Naja'atu zata basu kunya da baiyi ruwa da tsaki ba gurin ganin tabbatuwar auran! yanzu dai bashi da wani abinda zaice da abokin nasa dangane da abubuwan da suke faruwa sai dai kawai ya cigaba da bashi hakuri duk hukuncin kuwa da ya yanke a kan yarinyar hakan ba zaiyi masa ciwo ba saboda yasan itace ta janyowa kanta babu shakka ba kowane mutum ne zai yarda a zubar masa da ciki ba bai dauki mataki ba......A nutse suka gaisa da juna kafin Abbah Magajin ya sheda masa cewar an samu labarin ganin Naja'atu a garin jos...Abbah Abbas ya nuna bai san komai ba sannan kuma ya nuna farin cikinsa sosai kana kuma yace kafin dawowarsu gobe lallai Abbah Magajin yayi kokarin zuwa domin daukota.Sallama sukayi da juna kowa na danne abinda ke cikin
zuciyarsa.
Mutanan kofar na'isa sunyi farin ciki sosai da labarin da Abbah Magaji yaje musu dashi na bayyanuwar Naja'atu dake garin Jos ya kuma sheda musu da cewar su sake kwantar da hankalinsu yana tsammanin tana hannu nagari, amma kuma koda wasa bai sheda musu lalacewar cikin jikin da take dauke dashi ba.
Alhaji Sama'ila dashi Baba malam sunyi farin ciki sosai kuma sun godewa Allah tabbas adduarsu bata fad'i a kasa ba.....Jama'a mutanan unguwa sai shigowa baba Talatu suke a cewarsu wai sunzo taya ta murnar bayyanuwar 'yarta, to ita dai sai ta rasa ma a'ina mutane ke samun labari tunda dai duk abubuwan dake faruwa a tsakaninsu sukeyi amma abin mamaki kafin kice me jama'a har sunji suna shigowa gulma da munafurci! haka nan ta daure ta dinga kar'bar mutane wanda da yawa daga cikinsu gulma da munafurci ne ke kawo su ba wani abunba.
To har duhun dare ya shigo Abbah Magaji bai ga text din da Bash yace zai turo masa.....Sai bayan yaci abinci ya nutsu tukkuna ya sake neman numbar Bash din kawai sai akace masa layin baya aiki yayi ta trying wayar na katsewa anty maryam dake kusa dashi a zaune tace" Jikina baya bani cewar mutumin da ya kira ka mutumin kirki ne idan da gaske taimakon yarinyar zaiyi me yasa tun dazu da kukayi waya dashi ba turo maka cikakken bayanin idan zaka same shi ba, duba fa tun dazu kake kiran wayarsa na katsewa.
A sanyaye Abbah Magaji yace"Naga alama yana so yayi mana wasa da hankalinmu ne kuma nima na soma zargin rashin gaskiya a tare dashi idan ba rashin gaskiya mai zai sa ya cire layinsa daga jikin wayarsa bayan yasan ga yanda mukayi dashi." aunty maryam tace"Gaskiya da akwai alamun rashin gaskiya Allah dai ya kare yarinyar nan daga fad'awa hannun 'bata gari." Cikin rashin jin dadi da tunanin neman mafita ya amsa da "ameen" shuru sukayi kowanne na tunani a cikin zuciyarsa
Da Asuba Abba magaji na dawowa daga massalaci ya kunna wayarsa ko minti biyu baiyi da kunnawa ba text din Bash ya shigo da sauri ya shiga yana dubawa! hamdala yayi a fili kana ya shiga kiran numbar Bash din...'Kin shiga wayar tayi kamar jiya yayi ta traying ta'ki shiga cike da mamaki yake kallon wayar tashi to anya kuwa guy nan bashi da wata 'boyayyar manufa? me yasa baya bari a sameshi a waya............Bash Layin kansa sunfi hamsin wayoyinsa kuwa sun kai koma saboda yanayin sana'arsa yasa baya barin layi ya kwana a wayarsa shikenan sanja layi yana basaja Bash ya iya taku shiyasa jami'an tsaro suka kasa kamashi.
Koda aunty maryam ta shigo dakin sai ya sheda mata cewar ya samu text din da suke tsammani yanzu ta kar'bi wayar ta duba tana godewa Allah......Abbah Magaji a gurguje ya shirya dan ko break ba tsaya yi ba ya fito aunty maryam ta rakashi har bakin motarsa tana masa fatan dawowa lafiya.....Abbah Magaji kafin ya isa garin jos sai da ya kira Abbah Abbas ya fad'a masa ga halin da ake ciki.......A Lokacin suma jirginsu na dab da sauka, cike da nuna komai ya wuce yayi masa fatan dawowa lafiya da kuma samun nasarar dawowa da yarinyar cikin koshin lafiya.
Naja'atu tun kafin Abbah Magaji ya sauka a gidan take cikin wani irin yanayi na damuwa tana tunanin ko da wane ido zata kalleshi, yanzu ne kunyar abunda tayi yake damunta hakika tasan ta aikata musu abunda zai zubar da kima da mutuncinsu a gari, to amma anata ganin ai sune suka janyo hakan ta faru tunda sun kasa fahimtar daidai sunbi son zuciyarsu.
Abbah Magaji daidai inda Bash yace ya tsaya anan yayi parking din motarsa ya fito da wayarsa tare da neman numbar Bash din yana adduar Allah yasa ta shiga kada ya barshi a cikin mota ba tare da yasan inda zai nufa ba......Abin mamaki kiran farko Bash ya daga suka gaisa yace masa gashinan zuwa." Abbah magaji ya kashe wayarsa yana jiransa gabadaya jikinsa yayi sanyi da yanayin halin munafurci da guy yake nuna masa....Bash ya iso guri cikin wata lafiyayyar mota mai muguwar tsada.!
Abbah Magaji kallo daya yayi masa ya tsinke da al'amarin guy sai kace wani kafuri yayi wata iriyar shiga irin ta 'yan iska hatta da gashin kansa ya sanja masa hallita ya dawo browan ga wani irin aski dake kansa irin na gararrun turawan america.....Cikin wata 'yar iskar tafiya ya nufi motar Abbah Magajin, sai yayi saurin bude mota ya fito ya tsaya yana kallonsa har ya karaso!
Cikin wani irin tantiranci ya bashi bayan hannu wai su gaisa! Abba Magaji ya girgiza masa kai had'e da bashi tafin hannunsa da fad'in"Salamu alaikum." Bash yayi 'yar dariya yasa hannunsa cikin nasa ya amsa da "Amin wa'alaikasalam." Abbah Magaji yace."Ashe kasan da haka me yasa za kayi min gaisuwa irin ta kafurai."?
Dariya bash yayi yace."Afuwa na riga na saba ne wallahi ya gida ya hanya ya ka baro iyalinka."?
Abbah Magaji yace."Kowa lafiya kalau abokina amma banta'ba tsammanin ganin ka haka ba." Bash ya sosa tarin sumar dake kansa yace."Saboda me kace haka."? Abbah yayi murmushi a nutse yace."Yanda kake hausa yasa na fahimci cewar kai bahaushe ne kuma musulmi to amma ganin da nayi maka a yanzu yasa na d'ora ayar tambaya a kanka." Bash yasa dariya yana kallon Abbah magaji kafin ya d'aga kafad'arsa sama yace."Kamar yanda kake tsammani eh hakane ni musulmi ne gaba da baya cikin famliy na babu tubabbe dukkaninmu a cikin musulunci muka taso yanayin dressing d'ina da yawanci wasu abubuwa nawa ra'ayina ne hakan so ina ganin hakan bazai shafi addinina ba." Abbah Magaji ya shiga girgiza kansa yana nazarin maganar........Bash yace."Muje gida na sadaka da kanwarka amma zaka bar motarka anan zamuje cikin motata." Abbah magaji yayi saurin juyawa domin kulle motarsa yana fad'in "Babu damuwa hakan yayi."
Abbah Magaji yana ta mamakin yanda Bash ke amsa wayoyin jama'a shi dai tunda ya zauna a cikin motar ba zai iya irga iya adadin mutanan da Bash ya amsa wayarsu ba, Nazarin motar kawai yake yana mamakin irin kwalaben giyar dake ciki ga tarin takardun wiwi nan da sauran kayan maye duk da motar na kamshin freshnar hakan bai hana shi jin warin kayan mayen dake ciki ba, haka dai ya daurewa zuciyarsa har suka isa gidan......
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA🌴🌴*
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
Mddbhrmbn47
*Bash* bai sauki Abbah Magaji a ko'ina sai a dakinsa Abbah Magaji ya samu guri ya zauna a nutse yana bin dakin da kallo..Bash ya bude fridge ya dauko masa ruwa da lemo masu sanyi a ajiye a gabansa Abbah magaji yace."Nagode." murmushi kawai yayi ya juya ya fita daga dakin ba tare da yace wani abuba. Abbah Magaji bai dauki lemon yasha ba dakin kawai yake kallo sa'ko da lo'ko gabadaya ya tsargu da yaron dan daka gani ba mutumin arziki bane! a hankali ya dauki ruwa ya bude ya d'an sha ya mayar ya ajiye, jin kira ya shigo wayarsa yasa yayi saurin dubawa abokinsa ne Ya kara wayar a kunnansa had'e da yi masa sallama, Abbah Abbas ya amsa a nutse yake sheda masa cewar sun sauka yanzu. Abbah magaji Yace masa shima yanzu haka yana inda yake tsammanin samun Naja'atun. Abbah Abbas yace."To Allah yasa adace."Sallama sukayi da juna Abba magaji na kashe wayarsa Bash da Naja'atu da Munira suka shigo dakin, Naja'atu sai 'buya take a bayan Bash tana sinne kanta kunyar hada ido take da dan uwan nata...Shi kuwa Abbah magaji tunda suka shigo yake binta da kallo yana mamakin irin kwalliyar da tayi wato su suna can hankalinsu a tashe ita tana nan tana ado da kwalliya..Kafin ya ankara yaga Bash ya rike hannunta ya zaunar da ita a kusa dashi. ya bisu da wani irin kallon mamaki! kujera ce 1sitar amma sun nani'ka da junansu. Kunyar hakan yasa ta sunkuyar da kanta 'kasa murya na rawa take gaishe shi shima a sanyaye ya amsa ganin abinda yafi karfinsa to hakan me yake nufi? ina kuma Naja'atu ta baro auranta? bashi da mai bashi amsa sai kawai ya zuba mata ido ya kasa cewa uffan! ganin irin kallon da yake mata ne yasa jikinta yayi sanyi sai ta fashe da wani irin kuka hade da had'a hannuwanta guri daya tace"Abbah magaji dan Allah kada kuga laifina dangane da faruwan wannan al'amarin wallahi ba laifina bane laifinku ne tunda tun farko na fada muku cewar bana sonsa bana sonsa kuka kasa ganewa har sai da kuka daura min aure dashi sabida haka yanzu duk wani mummunan abu daya biyo baya kune kuka janyo ni bani da laifi."
Abbah Magaji maganganun da Naja'atu takeyi sunyi masa tsauri sosai har hazar yanzu ya kasa magantuwa sai dai ido kawai yake binta dashi mamakinta na kashe masa jiki...Bash ya dan rungume kafadarta yana rarrashinta wai tayi shuru ta daina kuka komai yazo karshe insha Allah, Abbah Magaji yana zaune yana kallon ikon Allan Bash sai matse masa 'kanwa yake yi a gaban idonsa....Ransa a 'bace ya buga musu tsawa da fad'in "Kai ka kiyaye fa wannan yarinyar matar aure ce musulunci bai baka damar ta'ba matar da bata kaba." Bash ya wani sha kunu yana kallon Abbah Magaji da fad'in "A shirye nake dana d'aukaka 'kara akan auran rashin adalcin da kukayiwa wannan yarinyar wannan ai son zuciya ne me yasa wai mafi akasari mutumin kano baida wayewar kai ne? meye amfanin auran dole da kukewa 'ya'yanku tunda wannan yarinyar tace bata son mutumin nan to ya saketa mana dole ne."? Abbah magaji yaji wani irin gumi na yanko masa bakinsa na rawa yace." Waye yace maka auran dole akayi mata kuma kai meye ya shafeka da shiga cikin al'amarin da har kake maganar d'aukaka 'kara shin kasan waye Alhaji Abbas kuwa."? Bash ya zakud'a kafadarsa yace"Sanin waye Alhaji Abbas bashi ne a gabana ba abinda yake gabana anan shine ya saki Naja'atu na aureta shine abinda yake a gabana idan kuna ganin zaku yafe Yarinyar nan saboda ta bujirewa umarninku to ni Bashir zan ri'keta har 'karshen rayuwarta ta duniya." Abbah Magaji yace."Inaso ka fad'a min meye manufarka akan yarinyar nan."? Kai tsaye yace."Munufa ta ta alkairi ce inaso in aureta bayan kun warware wannan auran da kuka 'kulla." Abbah Magaji yayi shuru yana ta nazarin maganar Bash din *Aure! Aure! Aure!* wane Uba ne zai dauki 'yarsa ya bawa wannan lalataccen auranta duk wanda zai ga Bash mutukar mai hankali ne zaiyi kokarin nesanta kansa dashi saboda sam bai cancanta ma ka hada hanya dashi ba ballantana gaisuwa ta haka dashi!
Ya dago kanshi yana kallon Bash din gabadaya yanayinsa ya nuna yana cikin tashin hankali da damuwa yace."Wannan maganganun da ka fada min suna nuna cewar da sanya hannuka gurin zubewar cikinta kun hada baki da ita kun zubarwa da abokina ciki domin ku cimma wata manufa taku ko."?
Bash yayi murmushi hade da sosa kanshi yace."Bana munufarci Alhaji idan da sa hannuna gurun zubewar cikin nan da tuni na fad'a maka sabida nasan da kai da abokin naka babu wani abu da kuka isa kuyi dan haka ka ma daina wannan maganar kafin Naja'atu tazo gurinmu cikinta ya zube a wani guri." Abbh magaji ya shiga goge gumi yana kallon Naja'atu yace."Yanzu meye ribarki ta zubar da cikin halak Naja'atu kin manta waye Alhaji Abbas a tare dake ko? Abokina Abbas bai cancanci wannan sakayyar daga gurinki ba.
Tana kuka tace"Wallahi ni ban zubar da cikin nan ba da kansa ya zube amma ni ban zubar ba." a zabure! kafin kowa ya ankara ya kai mata wani bahagon mari! tasa kuka tana sake 'boyewa a bayan Bash! Abbah magaji ya mike jikinsa na kyarma! yace."Yaushe kika zama 'yar iska Naja'atu irin tarbiyar da akayi miki kenan? ashe kina so ki zubar mana da mutunci a duniya da auranki kike rungume wani namiji! zaki fito daga nan ko sai na sumar dake a gurin nan." Yakarasa maganar cikin hargagi!!!
Bash ya mike tsaye da sauri ya janye shi daga gurin ya zaunar dashi kan kujera yace."Alhaji duk wannan hargagin da kake ba zai taimake ka akan komai ba kawai kabi komai a sannu a hankali sai a samu maslaha na fada maka wallahi sai inda karfina ya kare akan wannan al'amarin dan ina son naja'atu itama tana sona babu wanda ya isa ya hanamu mallakar junanmu shi wannan tsohon mai zuciyar yara shi nake so ya yankewa kansa hukunci tun kafin a'lkali ya 'kira shi."
Abbah Magaji yaji wani irin kuttun bakin ciki da takaici ya tokare masa a makoshi tabbas zai zare hannunsa daga cikin al'amarin yarinyar kodan ya tsira da mutuncinsa gurin abokinsa... ya kalli Bash din da idanunsa wanda sukayi jajawur yace."Yanzu zaka bani yarinyar nan ko kuwa ba zaka bani ita ba."? Bash yace." Sai abinda tace idan tana da ra'ayin bin ka gatanan a zaune ta fada maka."
Abbah magaji ya tsirawa Naja'atu ido yana so yayi mata magana amma tsabar bacin rai ya hanashi cewa komai...
Kallonta kawai ya gaza furta kowace kalma ita kuma ganin haka yasa tace" Ni bazan koma ba har sai na tabbatar da cewar babu auran kowa a kaina sannan zan bika idan na koma zaku iya tursasani na koma gidan Wanda bana so.......Abbah magaji ya dauki wayarsa ranshi a bace ya shiga neman numbar abokinsa lokacin yana kofar na'isa tare da mahaifinsa suna tattauna maganar yana kuma sanar masa da irin hukuncin da ya yanke lokacin shi kuma Mahaifin nasa yake nuna masa ya janye hukuncin da yanke hakan bai dace ba......Wayar abokin nasa ya dauka yaji muryarsa cikin bacin rai yana sheda masa abinda ke faruwa... Kai tsaye yace ya bashi Naja'atun zasuyi magana da ita, da yake hands free ne Bash yana jin muryar Abbah Abbas din yana magana, Abbah magaji ya mikawa Naja'atu wayar da fadin "Gashi yana so yayi magana dake......'Kin kar'bar wayar tayi Bash ya kar'ba ya kara mata a kunnanta...jin muryar Abbah Abbas din yana magana yasa gabanta ya tsananta fad'uwa kiran sunanta yake ta gagara amsawa sai sheshshekar kukanta yake ji a kunnansa.....A nutse yace." Kince ba zaki dawo gida ba sai anyi miki abinda kike so ko? shuru tayi ba tace komai ba. Ya dan sauke ajiyar zuciya yana sake jin wani irin tsanarta na d'arsuwa a zuciyarsa yace."Kada ki damu tun ranar da kika tura min text na datse igiyar aurena guda daya dake kanki ina fatan Allah yasa hakan shi yafi alkairi kiyi hakuri ki dawo gida saboda samun kwanciyar hankalin iyayenki." Jin abinda yace yasa taji wani sanyi na saukar mata a zuciya shima bash dake kusa da ita murmushi yayi kawai ya cire wayar daga kunnanta ya kashe ya mikawa me ita...Abbah magaji rasa bakin magana yayi ya dinga binsu da kallon takaici.....Bash ya mike da fadin "Bari nayi wanka ina tsammanin tare zamu tafi inaso naje na nuna kaina a matsayin wanda zai auri Naja'atu." Abbah magaji uffan bai ce masa ba har ya shiga toilet dinsa.....Naja'atu ita da Munira suka fita daga dakin cike da farin ciki bukatarsu ta biya, shi kuwa bayan fitarsu daga dakin guri guda ya tsirawa ido kawai yana kallo babu shakka hukuncin da abokin nasa ya yanke baiyi masa dadi ba ko kadan! to amma yana adduar Allah yasa haka shine yafi alkairi Naja'atu kuwa ya tabbata da cewar sai ta girbi abinda ta shuka da hannunta yanzu shi dai zaiyi kokarin sadata da iyayenta shikkenan sai ya zare hannunsa daga kanta idan Allah ya kaddara auranta da Bash to shi kam dan kallo ne babu abinda ya shafe shi duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka.
Abbah magaji yana zaune Bash ya kintsa jikinsa cikin sabuwar shadda galila mai kalar sararin samaniya (sky blue) dinki tazarce da dogon hannu mai link yasa hula irin ta kanawa sai kace wani mutumin arziki yayi wani irin kwarjini da kamala, Abbah magaji na zaune yana ta mamakinsa babu shakka yaron ya shirya tsaf domin zuwa ya yaudari su baba malam to idan ba hakaba meye nasa manyan kaya harda hula, Bash na daura agogo ya kalli Abbah Da murmushi a fuskarsa yace."Nasan duk wanda ya gan ni cikin famliy naku zai yaba dani da cancanta ta a matsayin wanda zai auri Naja'atu ina fatan kai ma a matsayinka na makusancinta ka sanya mana albarka a cikin al'amarin."
Abbah Magaji na kallon rashin kunya da tsabar jahilci shikkenan daga anyi saki kuma sai a shiga neman aure ai ya bari yarinyar tayi iddah tukkuna....Yace."Bashir da alama baka da ilimin addini waye yace maka ana neman aure cikin iddah ai ka bari yarinyar tayi iddah tukkuna in yaso sai kayi wata magana....Bash yace"A'a da zafi zafi akan bugi karfe alhaji gwara naje na gabatar da kaina in yaso koma meye sai ya biyo baya." Abba magaji ya bishi da ido cike da tsantsar mamakin maganarsa gaskiya jahilci bai yi ba.
Abbah Magaji motarsa ya shiga a maimakon Naja'atu tayi masa kara ta shiga motarsa sai ta nuna jin tsoransa yana kallo ta zauna gaban motar Bash ko kallonsa ta'kiyi takaicin haka yasa yaja motarsa da karfi... ya bar gurin.. Bash na murmushin samun nasara yaja tasa motar suka dauki hanya......sai da sukayi nisa sosai ya kalleta yace."Baby wannan dan uwan naki fa na fahimci baya k'aunar alaqa ta dake ko kad'an!." murmushin takaici tayi tace."Bash bana tsammanin Abbah magaji zai kaunace ka dan shine babban abokin Abbah Abbas to kaga kuwa dole ya tsaneka." Cike da rashin damuwa yace."Hakan bai dame ni ba mutukar kina sona iyayenki sun amince dani ai bukata ta biya." Jin abinda yace yasa gabanta ya fadi addua ta shigayi kan Allah yasa su baba malam su amince mata da auran Bash dan yanxu gabadaya shine babban burinta.
Alhaji Sama'ila da Baba Malam dashi uban gayyar ne a zaune a guri daya suna tattaunawa kan al'amarin da yake faruwa. Alhaji Sama'ila yana ta nuna rashin jin dadinsa dangane da hukuncin da d'ansa ya yanke a kan naja'atu shi kuma Baba malam yana nuna masa hakan ba laifi bane dan Abbas ya saki naja'atu domin samun maslaha ga junansu ya kuma nuna masa shi bai ji takaicin faruwar hakan ba dan dama ya riga ya barwa Allah al'amarin yana ganin tunda hakan ya kasance to shine alkairin..........Dukaninsu suna zaune suna jiran tsammanin dawowar Abbah magaji tare da Naja'atun.........To Sai daf da magariba suka iso, Abbah magaji bai saurare su ba ya gyara parking na motarsa ya fito ya nufi massalacin dake jikin gidan Alhaji.....Naja'atu da kyar ta iya fitowa tana ta 'boye kanta a cikin mayafi gabanta kuwa sai faduwa yake...Bash ganin Abbah magaji na alwala a cikin massalaci sai shima kamar gaske ya nufi inda yake Naja'atu kuwa tsayuwa tayi ta rasa ina zata shiga gidan Alhaji ko idan baba malam...Munira tace"Wai tsayuwar me mukeyi ne? haba duk kinbi kin damu kanki dan Allah ki daina jin tsoron abinda zai faru babu fa wanda ya isa yayi miki abinda Allah be miki ba ki saki jikinki dan Allah."
Hawaye ta d'an goge tace"Mu shiga gidan Alhaji munira ba zan iya shiga gidanmu ba ina jin tsoron Baba Talatu da Abbah Magaji kada ya shigo ya doke ni." Munira tace"To muje gidan Alhajin tunda kinfi amincewa da nan." Kai tsaye suka nufi gate gidan tana tafiya tana hard'ewa saboda matsatstsen siket d'in Munira dake jikinta gashi ba hijab bane mayafi ne a jikinta shiyasa duk ta tsargi kanta! Abbah Abbas da Alhaji sune suke kokarin fitowa daga gidan Naja'atu jin 'kamshin turaransa yasa ta zabura! da sauri ta matsa gefe tana kauda kanta! Abbah Abbas karaf! idanunsa ya sauka a kanta duk da ta 'boye fuskarta hakan bai hanashi ganeta ba kallon zatin jikinta kawai ya fahimtar dashi itace! cike da mamaki yake kallonta kwana uku kacal a jos ya mayar da ita watsatstsiya wane irin suttura ne wannan a jikinta sun fito mata da jikinta! da sauri ya kauda kansa ya wuce domin shiga massalaci.....Tana ganin wucewarsa ta zube 'kasan gurin tana gaishe da Alhaji dake kokarin wucewa dan shi sam be ganeta ba, Jin muryarta yasa yayi saurin juyuwa yana amsawa da fad'in "Naja'atu kece."? murya na rawa tace" Eh." yace."To masha Allah ku shiga cikin gidan mu zamu shiga massalaci domun gabatar da sallah." A sanyaye tace "To" tana kokarin mikewa Alhaji kasa barin gurin yayi har sai da yaga sun shiga gidan tukkuna ya nufi massalaci zuciyarsa sam babu dadi dangane da faruwar al'amarin.
*Littafin na kudi ne..!*
Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina bukatar biyan kudin karatu toga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 account 0542382124...Binta umar gtbank..idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA🌴🌴*
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
Mddbhrmbn49
Halisa da Yaya Ramlatu ne a zaune a palon Hajiya sai hira suke cikin nishadi sunayi suna ciye ciye kana kallonsu zaka fahimci cewar suna cikin walwala da farin ciki...Hajia Abu lokacin ta hau sama domin daura alwala su kuma bayan barinta gurin ne suka tsiri gulmar abinda ya faru inda Yaya Ramlatu ke fad'in"Ai wallahi Halisa na sake gazgata al'amarin mutumin nan da 'yar shagamu ta kai mu gurinsa kinga ni dai duk abinda ya fad'a zai faru gashi ya kasance gaskiya kiyi kokarin siyawa 'Yar shagamu turaman atampopi muje tare dake gidanta mu kai mata domin mu sake nuna mata jin dadi da farin cikinmu sabida kin san hausawa nacewa dan towon gobe ake wanke tukunya nan gaba zamu iya zuwa mu sake neman wata alfarmar gurinta shiyasa nake so ki kyautata mata sosai dan itama taji dadi."
Halisa na shirin yin magana su Naja'atu suka shigo palon..Naja'atu ganin Halisa da Yaya Ramlatu a zaune yasa jikinta yayi sanyi da kyar suka shiga palon suka zauna cikin kokarin aro jarumta tace"Anty Halisa sannunku Yaya Ramlatu Ina wuni."? babu wanda ya amsa mata a cikinsu Halisa sai binta da ido take tana ta'be bakinta, ita kuwa Munira ganin Naja'atu tayi musu magana basu amsa ba yasa ta kama kanta 'kafarta ta d'ora kan d'aya tana taunar cingum had'e da duba tamfatsetsiyar wayarta....Yaya Ramlatu ta ri'ke bakinta tace"Oh! ikon Allah ke kuma Naja'atu garin yawon karuwancin naki kika samo wannan mara kunyar yarinyar daka ganinta 'yar isaka ce da wasu idanunta a tsaye irin na marasa kunya."!Munira ta zubawa Yaya Ramltu idonta ranta a 'bace da jin irin mugwayen kalaman da take jifanta dasu. Za tayi magana Naja'atu ta rufe mata bakinta tace"Dan Allah kada ki kulata ki kyaleta duk wanda ya wulakanta wani kansa ya wulakanta." Halisa tace"Ke Naja'atu Yaya Ramlatu kike kokarin gayawa magana? ai gaskiya ta fad'a a kanki dake da kawarki idan ba yawon karuwanci kika tafi ba to me ya had'a ki da wannan me wankakken idon." Munira ta nuna Halisa da hannu tace"Wallahi kika sake kirana da wannan kalmar sai na wanke ki da mari zan nuna miki tsageranci na yanzu." Halisa ta ri'ke bakinta tana kallonta tace"Sai ki mareni mara kunya kawai. Naja'atu tace"Kinga Halisa mu ba tashin hankali ne ya shigo damu gidan nan ba saboda haka dan Allah ki fita daga sabga ta kada ki sakeyi min magana tunda dai yanzu bani da al'aka dake." Da sauri Ramlatu tace"To dan ubanki tashi ku fice mana daga gida tunda da bakin ki kin fad'a baki da al'aka damu ubanki kika shigo kiyi mana a gida." Naja'atu jin zagin yayi yawa yasa ta fashe da kuka da fad'in "Ki daina zagina dan banga abin zagi ba anan." Ai kamar 'kara tunzura ta take ta dinga zabga mata zagi tana ambato sunanan Baba Malam tana cusa masa ashar! Munira tace"Amma ke kam anyi tsuhowar banza." Yaya Ramlatu ta fusata ta fitar da hannu ta tsinka mata mari wanda yayi dai-dai da sakkowar hajia daga sama kuma duk akan idonta komai ya faru...Cike da bacin rai ta zauna tana kallon Ramlatu tace"Yanzu meye amfanin abinda kikayi da girmanki da komai kina shiga sabgar yara."
Sai kawai ta fashe da kuka da fad'in" Wallahi hajia raina ne ya 'baci! shiyasa na kasa daurewa wai yarinyar nan itace take fad'a mana cewar dasa hannunta gurin zubewar cikin Naja'atu ko kunyar idona ba taji ba take fadin haka ita kuma Naja'atun na sake tabbatar mana da gaskiyar magana harda cewa wai yanzu bata da wata al'aka damu tunda ta rabu da auran jaraba ciki kuma ta zubar duk abinda zamu yi sai dai muyi."
Naja'atu da Munira kasa magana sukayi suna mamakin iya sharri na matar sai kuka take tana fyatar hanci kamar gaske.....Halisa kan dariya kawai take cikin zuciyarta itama mamakin iya sharri na ramlatun take.
Hajia Abu ta kalli Naja'atu tana so tayi magana sai ta riga tana kuka tace"Wallahi hajia ba haka bane sharri ne ni ban sha wani abu domin na zubar da ciki ba da kansa ya zube amma wallahi duk cikin magabar da Yaya ta fad'a babu gaskiya a ciki." Ya Ramltu tace"Ubanki ne yake miki karya kaji ni da mara kunyar yarinya wa zaki yaudara? ashe har kin manta irin maganganun da kika fad'awa Salim to idan ke kin manta mu bamu manta ba munufuka kawai kin bar zuriarmu har abada."
Hajia tace"Ya isa dan Allah duk zancan tashin tashina bai taso ba abinda ya faru ya riga ya faru kuma zamu ajiye shi a matsayin kaddara haka Allah ya hukunta sabida haka kada na sake jin kin zagi naja'atu ko kin fadi mummunar kalma a kanta Naja'atu bata isa ta tsarawa kanta abunda take so ba komai ya faru da rayuwarta kaddara ce ciki kuma da ya zube dama can Allah ya hukunta ba zai taka kasar duniya ba munafatan Allah yasa haka shi yafi alkairi."
Yaya Ramlatu 'kus! tayi dan ba tayi tsammanin hajiyan zata goyi da bayan yarinyar ba ganin yanda ta nuna 'bacin ranta lokacin da taji labarin zubewar cikin..Halisa da yake neman gindin zama take a gurin hajiyan sai ta 'kaskantar da kanta kamar mutuniyar kirki tace"Wallahi kuwa hajia ai nima haka nace duk abubuwan da suke faruwa kaddara ce Allah yasa Auran Abbah Mufida da yarinyar ba zaiyi tsayi ba shiyasa duk haka ta faru amman mu munso Auran yayi albarka ya zama mutuwa ce zata rabasu kamar yanda ta ratsa tsakaninsa da Halimatu."
Hajia tace"Ke da yake mai hankali ce kin gane yanda lamarin ubangiji yake amma ita waccan da girmanta da shekarunta tana abubuwa irin na yara."
Yaya Ramlatu sunkuyar da kanta tayi kunyar duniya ta isheta hajia ta kunyatata gaban yara kananu ita kuma halisa da yake ta fita dubara ta wanke kanta kasa d'ago kanta tayi dan tana jin kunyar had'a ido da yaran Munira kuwa sai dariya take 'boyewa taji dadi sosai da hajiyan tayi wa matar wankin babban bargo.
Sai bayan sun fito daga sallahr isha'i ne suka samu zama gabadayansu a kofar gidan baba malam da yake dogon dakali ne mai fadi da tsayi kuma yana sawa kullum a share a shimfida katuwar tabarma saboda masu daukar darasu! Suka zazzauna harda Bash da yake ta wani sunkuyar da kansa, cikin nutsuwa yabi kowansu yana mik'a masa hannu har yazo kan wanda yake tunanin shine abokin adawarsa Abbah Abbas ya rike hannunsa suka gaisa cikin kulawa da mutunta juna sabida shi bai san abinda ke tsakaninsa da tsohuwar matar tasa ba to koma dai ya sani bashi da abinda zaice tunda ba huruminsa bane....A nutse Bash yayi musu bayanin yanda akayi Naja'atu tazo garesu ya kankantar da kansa sosai ya nema mata afuwa a gurinsu gami da cewar su dauki dukkanin abubuwan da suka faru a matsayin qaddara sannan kuma kodan gaba su guji yiwa 'ya'yansu auran da basa so ko dan gujewa faruwar matsala makamciyar wannan." Baba malam da Alhaji sai godiya suke masa dan gabadayansu sun yaba da hankalin yaron kuma abinda yayi musu ba zasu ta'ba mantawa dashi ba shiyasa suke tayi masa godiya tare da yiwa iyayansa addua....Cike da jin dadi Bash yake amsawa yana shafa wuyansa hade da sunkuyar da kansa irin na munafukai.....Abbah Magaji da Abbah Abbas kallonsa kawai suke baran Abbah Magaji da yasan waye Bash d'in shiyasa bakinsa ya mutu yakasa cewa komai yana jin yanda Bash yake ta basu labarin waye mahaifinsa, ba'aje da nisa ba suka gane mutumin tunda gabadayansu masu sauraran redio ne shi kuma Aminu dan Jarida yayi suna sosai akan aikinsa kuma yayi aiki a gidajen redio da dama shiyasa su ganeshi nan take.
Alhaji yace."Duk da bamu ta'ba ganin mahaifinka ido da ido ba amma muna sauraran muryarsa hakika mahaifinka ba 'boyayye bane kuma munji dadi da yarinyar ta kasance a gurunku idan ka koma gida kayi wa mahaifinka godiya a bisa karamcin da akayi mana." Bash yace." Ya kwana biyu baya gida aiki ya kaishi amuruka amma idan ya dawo zan fad'a masa sa'kon gaisuwarku." Baba malam yace to babu damuwa Allah ya dawo dashi lafiya." Gurin ne yayi shuru na minti biyu kowa na sa'ke-sa'ke a cikin ranshi, Bash ya gyara zamansa kansa a 'kasa yace"Malam ina neman alfarma a gurunku idan zan samu." Da sauri Baba malam yace."Wace irin alfarma kake nema yaro." ? Bash yace."Inaso idan Naja'atu ta 'kare iddah na aureta idan babu damuwa." Baba malam yayi murmushi yana kallon Alhaji yace."Kaga mahaifinta nan dashi za kayi magana." Bash ya kalli Alhaji yana dan murmushi....Abbah magaji mikewa yayi had'e da zura takalminsa ya mikawa abokinsa hannu da fad'in "Zan nufi gida Sai ka shigo kenan." Abbah Abbas yace."Ka zauna a 'kare maganar da kai mana." Girgiza kansa yayi yace."Tunda duk kuna gurin ai babu matsala ina fatan Alheri a cikin al'amarin." Baba malam da Alhaji suka amsa da ameen.'' Shi kuwa Abbah Abbas ido kawai ya zubawa Bash yana kuma sauraran amsar da Alhajin zai bashi....Alhaji Yace."Babu komai Bashir shi aure rabo ne idan Allah yasa wannan yarinya matarka ce sai kaga ka aureta idan kuma baka da rabo sai kaga wani ya aureta amma dai musulunci bai baka damar tunkararta a yanzu ba ka bari tukkuna ta kare iddah sai ka shiga layin zawarawan ta." Bash yace."To nagode sosai Alhaji nagode da karamci ina kuma addua Allah yasa Naja'atu rabona ce." Suka amsa da ameen banda Abbah Abbas da yake jin takaici na neman dagargaza! masa zuciyarsa mtwsss! mi'kewa yayi dan ganin zaman ma da yake a gurin bashi da wani amfani ya daure ya bawa iyayan nasa hannu da fad'in "Shima zai wuce gida domin yaje ya huta, Bash ya bashi hannu da fad'in " To Alhaji a huta gajiya nagode sosai da kulawarku a kaina." Abbah Abbas ya daure ya amsa da babu damuwa kai ma ina maka fatan alkairi tare da adduar sauka lafiya."
Kai tsaye cikin gidan Alhaji ya nufa yana tafiya tamkar zai tsaga 'kasa sabida yanda yake taka ta da karfi! wai! kishi ne ko me? Koda ya shiga palon samun Naja'atu yayi da Munira sai ciye ciye suke na irin tsabar da sukayi ta saudia sun sake suna hira harda shewa ga Halisa a zaune a gefe kamar wata mujiya!!! dan tuni Yaya Ramlatu ta tafi.......Saboda ba kunyar da hajia ta bata shi yasa ta kasa zama sai ta tattara tsarabarta ta 'kara gaba cike da takaicin abinda hajiyar tayi mata..... Halisa ta tsurawa tv ido kamar mai kallo amma ita kadai tasan takaicin dake cikin zuciyarta gefe guda kuma tana mugun mamakin d'aurin gindin da yarinyar take dashi a gurin hajia.........Naja'atu tunda ya shigo palon bakinta ya mutu sunkuyar kanta 'kasa tayi Munira nata magana amma bata tanka mata ba..To itama Munirar kamshin lafiyayyan turaran da taji ne yasa ta kalli bakin 'kofa....Ta tsira masa ido tana tunanin inda tasan shi...Abbah Abbas ne mai zuwa musu visiting makaranta sai taga kamar ya dawo matashi gabad'aya mutumin ya'ki tsufa! wallahi bata ta'ba tsammanin zata ganshi hakaba ta dauka za taganshi furfura ta baibaye masa fuskarsa sai taga akasin haka ya sake zanzarewa yayi wani fresh dashi...Gaskiya ya burgeta tana son namijin da yake kula da kanshi kuma dan gayu....Muryarsa ce ta katse musu tunaninsu inda yake magana da Halisa yana tambayarta ina Hajia? Halisa na fari da ido tace"Bata jima da hawa sama ba." Ba tare da yace komai ba ya nufi saman...Gabad'ayansu har ita Naja'atun suka bishi da kallo.....Halisa ta juyo tana kallonsu tare da ta'be bakinta tace"Sai dai kallo daga nesa dan wutsiyar raqumi ta riga tayi nesa da 'kasa komai na babba yafi na yaro! wannan dai mijin mace d'aya itace Halisa."! Munira ta d'age! girarta tana murmushi had'e da girgixa kanta tace"Wallahi kiyi mana shuru da bakinki idan ba hakaba ki raina kanki ko yanzu mukayi ra'ayin komawa zamu koma har kike wani cika baki..... Ji wata magana dan Allah "Wai komai na babba yafi na yaro hahahaha to me zaki nuna mana."? tafada tana she'ka mata dariya hade da nunata da hannu." Halisa tace" Eh ai dole nayi magana naga kun bishi da kallo sai kace zaku cinye shi." Naja'atu ta tab'e bakinta tana girgiza kai tace"Dan Allah Munira kiyi mata shuru ni bana son damuwa wallahi so nake ma su tafi su bamu guri mtwws! Halisa tace "Aikin banza kawai ki daina dena za'kewa a gidan da baki da gado dashi sai kace gidanku sai wata fuffuka kikewa mutune." Naja'atu shuru tayi bata tanka mata ba, Munira kuwa ta mayar da Halisa kamar mahaukaciya sai dariya take mata, Halisa ta cika tayi fam fam! takaicin ya isheta, aikuwa yana saukowa wai zata kai mai 'kara! ya kuwa buga mata razannaniyar tsawar da tasa ta dauki jakarta babu shiri tayi waje! bayanta yabi ba tare da ya kalli iskar da ta d'ebo su ba.
0 comments:
Post a Comment