"Abbah dan......Katse ta yayi ta hanyar daga mata hannu yace." Meye amfanin zaman da kike a garin mutane bayan wanda kike zaune dominsa ya sake ki wace irin rayuwa kike tunanin zakiyi a inda baki da kowa! sannan kinzo kin d'orawa wata nauyi a wannan zamanin da yayi wahala wa kike tunanin zai dauki lalurar ki kamar yanda wannan matar ta dauka! kiyi wa kanki fad'a Naja'atu duk rayuwar da kike tunanin za kiyi a garin nan ba kamar kina gaban iyayenki ba."
Wani irin kuka takeyi mara sauti! tana so tayi magana amma ta kasa saboda kukan daya ci karfinta sai kawai ta kama hannunsa ta riqe gam a cikin nata....a haka suka isa inda Mmn Sajida take zaune....Jama'ar dake gurin duk suka zubo idanunsu suna kallonsu har suka karaso gurin, Mmn Sajida ta miqe tsaye cikin karramawa takewa Abba barka da zuwa sai washe bakinta takeyi tana fad'in ya shigo cikin gidan su gaisa sosai.'' Abbah cikin kulawa yace."Tayi hakuri ba sai ya shiga ba tunda a kan hanya yake, ya umarci Naja'atu ta shiga gidan ta dauki abinda take ganin zata dauka ta fito su tafi!
Mmn Sajida ta bita cikin gidan da sauri, shi kuma ya shiga nazarin gurin, matar na bukatar taimako ko ga yanayin sana'arta, barin gurin yayi saboda shi mutum ne da baya kaunar kallo a rayuwarsa sai yaje ya bude mota ya zauna yana jiran fitowarta.......Mmn Sajida na kuka Naja'atu na kuka a haka suka fito, suka shiga gidan Mmn Ladi sai gasu sun fito dukkaninsu su ukun suna kuka gwanin tausayi(sabo turken wawa ba) Mmn Sajida da Mmn Ladi sun shiga damuwa gami da alhinin tafiyar Naja'atu mutuka sun shaqu da ita mussaman Mmn Sajida gabadaya kasa magana tayi sai rintse hannun Naja'atu takeyi a cikin nata
A haka suka isa gurin motar, Abbah ya fito yana kallonsu sai kuka suke abun ya bashi mamaki sosai, yace."Kuyi hakuri ku daina kuka ba wai kun rabu da itaba har abada ba insha Allah zata dinga kawo muku ziyara sa'i da lokaci."
Mmn Ladi tace"Alhaji dole ne muyi kuka wallahi mun saba da yarinyar nan tana da hankali tana bani shawarwari masu amfani idan taga muna fad'a da mijina tayi ta bani hakuri tana kawo min misalai ni kam a rayuwar aurena ba zan ta'ba mancewa da wannan yarinyar ba." Abbah Abbas ya shiga mamaki mutuka Naja'atunsa har ta iya sulhun aure kai alhamdullhi ashe zamanta a garin ya haifar da alkairai amma yaji dadin wannan labarin.
Mmn Sajida tace"Ballantana kuma ni da muke kwana a guri daya mu tashi a guri daya kullum cikin nuna kulawarta take a kaina da 'ya'yana hakika ban ta'ba zama da mutum mai nutsuwa gami da iya mu'amula ba kamar wannan yarinyar kafin na saba da rashinta nasan zan sha fama."
Abbah yayi murmushi mai ma'ana kafin yace." Duk maganar da kuka fada akan Naja'atu naji dadinta kwarai da gaske inaso na sake jaddada muku kamar yanda na fada muku da farko cewar ba wai kun rabu da ita bane har abada insha Allah ni nayi muku alkawarin kawo muku ita a duk sanda ta bukaci hakan ina fatan zaku kwantar da hankalinku baku rabu da Naja'atu ba."
Naja'atu share hawaye tayi ta kallesu murya na rawa tace"Mmn Sajida kamar yanda Abbana ya fad'a muku cewar muna tare har abada hakane ku daina kuka da damuwa kuna ganin kamar kun rabu dani wallahi bamu rabu ba, domin ba zan ta'ba mance alkairinku a gare ni ba, kun tallafe ni a lokacin da nake bukatar taimako baku qyamace ni ba kun jani a jikinki kun bani kulawa ni kuwa me zance muku ai idan na cika 'yar halak baku cancanci na tsawar daku a rayuwata ba insha Allah zan dinga kawo muku ziyara kamar yanda Abbana ya fad'a muku."
To jin haka dasu Mmn Sajida sukayi sai hankalinsu ya kwanta suka daina kuke kuken da sukeyi...Abbah ya bude mota ya shiga minti biyu ya fito hannunsa ri'ke da kudi yan dubu dubu sun kai talatin ya miqa wa Naja'atu da fad'in ta basu." motar ya koma yana zauna yana qoqarin tashinta.....Mmn Sajida ta rungume Naja'atu tana zirarar da hawaye da kyar ta saketa Mmn Ladi ma tazo ta rungumeta sukayi sallama cike da alhini da damuwa Naja'atu ta bud'e mota ta shiga, suna tsaye a gurin suna daga musu hannu har sai da motar ta 'bace daga gurin.....Sannan suka juya da mataccen jiki, Mmn Sajida hada ido sukayi da Dantalle daya zubo mata ido yana kallonta shima tamkar yayi kuka! Yarinyar da yake qulafuci ashe ba tsararsa bace, yaso ya yaudareta da kudi da kayan kwadayi ya biya bukatarsa sai ya lura ba wannan ne a gabanta ba, sai yanzu ya qara tabbatar da cewar yarinyar 'yar manyan mutane ce ganin motar da'a kazo d'aukar ta yayi masifar sanyayyar masa da jiki da duk wani wanda yake mata kallon banza a gurin..
Abbah gabad'aya hankalinsa nakan driving din da yake sai dai kiraye kirayen wayar da yake shigowa wayarsa shine yake so yasa masa rashin nutsuwa a qalla an kirashi yafi sau ashirin bai daga ba, yasan dai labarin gizo baya wuce na'ko'ki duk wanda zai kirashi a yanzu zaiyi masa jajen abinda ya sameshi ne, wannan dalilin yasa ya'ki daga wayar kowa kawai ya mayar da hankalinsa kan driving din da yake.......Naja'atu kanta a qasa nauyi da kunya gami da nadama ya hanata kwakkwaran motsi! a duniya ita kuwa tana da masoyi wanda ya kai Abbahnta kuwa? Wai tambayar kanta takeyi....(To nima dai a ganina baki da masoyin daya wuce shi) Taji wasu hawayen na kokarin kwace mata data tuna zalintar kanta da tayi, yanzu data hakura ta zauna da auransa da tuni tana zaune hankalinta a kwance, da tuni ma wannan cikin dake jikinta nasa ne zata haihu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba tare da fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo ba, yanzu ya za tayi da d'an Bash idan ta haifeshi? wane namiji zata aura wanda zai ri'ke mata d'anta! hawayen da take ta kokarin dannewa suka shiga zuba a kumatunta.....Inama ace ana dawo da abinda ya wuce a baya data gyara kuskuranta, ita da kanta tasan ta aikata kuskure mai muni wanda har ta mutu ba zata daina nadama ba..............Wayar da yake ce ta dawo da ita hayyacinta.
"Halisa bana gari a halin yanzu ku kwantar da hankalinku dukkanin abinda ya faru da sanin Ubangiji na samu labarin komai bayan tafiya ta jos wuta ta cinye d'aya daga cikin rumfunana to bana mamaki da ikon Ubangiji da kuma abinda ya saukar a kan dukiyata, kada ku manta shine ya bani ita lokacin da banyi tsammani ba, nasan idan yaga dama zai mayar min da abinda na rasa cikin lokaci kankani babban farin cikina wutar bata ta'ba kowa ba shine abinda yafi komai faranta min rai! Dukiya a duniya na sameta kuma anan zan tafi na barta to banga abin tashin hankali ba, kuma ba wai gabadaya abinda nake dashi ne ya 'kone ba akwai kaya masu yawa a sauran rumfunana ina da kudi a banki wanda ban san yawansu ba to me zai sanya na kasa tawakalli dan Allah ya zartar da ikonsa, inaso dukkaninku ku kwantar da hankalinku kuyi addua akan Allah yasa haka shi yafi alkairi."
Halisa jikinta yayi sanyi tace"To shikkenan gabad'ayanmu ma muna gidan Alhaji kowa hankalinsa ya tashi gashi babu wanda ka fad'awa inda kake sai da Salim ya dawo yake fad'a mana wai tun misalin biyu na rana ka tafi jos dauko Naja'atu."
Yace."Eh nayi haka ne saboda wani dalili nawa amma yanzu gamu a kan hanya nida Naja'atun insha Allah kafin gari ya waye zamu sauka." Halisa a sanyaye tace"To Allah ya saukeku lafiya." Ya amsa da ameen tare da kashe wayar tashi gabadaya.
Halisa a sanyaye ta shiga sanar dasu Hajia abinda yace mata Zainab ta cika ta batse sai haushi takeji kishi kamar ya kasheta, akan me zai tafi dauko Naja'atu ya bar iyalinsa ai bashi ne yake da alhakin daukota ba tunda iyayenta da dan uwanta suna raye shi meye nasa, zainab sosai take kishin naja'atu dan Halisa bata gabanta tunda lura kamar ta tashi daga aiki........Naja'atu a sanyaye ta kalleshi tace"Abbah wani abu ya faru da kaine naji kamar kana maganar gobara." Ba tare da ya kalleta ba yace."Eh bayan na dauko hanya da niyyar zuwa nan sai al'amarin ya afku wuta ta cinye babbar rumfata dake cikin kasuwa." Jikinta yayi sanyi sosai tace"Allah ya mayar maka da alkairi Abbah Allah ya sadaka da rabo mai amfani." Yaji dadin adduarta sai ya amsa da "ameen ya Allah nagode sosai." motar tayi shuru kowa na tunane tunane a cikin zuciyarsa, Abbah Abbas sosai yake gudu kan kwalta dan gabad'aya ba yaso su kwana a hanya dalilin da yasa kenan ya kashe dukkanin wayoyinsa ya mayar da hankalinsa guri guda.......Sai gefin asubahi suka shigo garin kano a lokacin Naja'atu ta dad'e dayin bacci dan da yaga tana gyangyad'i sai tsayar da motar ya umarceta da ta koma bayan motar ta kwanta, Lokacin da ake kokarin shiga massalaci domin gabatar da Sallah asubahi yayi parking din motarsa a kofar gidan mahaifinsa, Allah ya godewa kafin ya bude motar ya fito da sauri ya nufi masjid din dake jikin gidan Alhaji, yana kokarin shiga massalacin Baba malam shima na kokarin shiga, sai sukayiwa junansu sallama suka shiga massalacin a tare, baba malam ya wuce ciki shi kuma ya tsaya bakin famfo domin daura alwala.....Naja'atu tun bayan fitarsa a motar ta tashi zaune tana muzarai gami da kalle kallen jama'ar dake shiga massalaci a gaban idonta Baba malam ya fito daga gida ya shiga massalacin ta dinga jin faduwar gaba da wani irin tsoro gami da kunya da nadama na damunta yanzu da wane ido zata kalli iyayenta da sauran jama'ar gari?..................
*Littafin na kudi ne.....!*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin littafin ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 idan katin waya zaki tura sai kiyi min mgn ta whasap da wannan number...... *07084653262 BINTA UMAR ABBALE*
64*********Ta jima zaune a cikin motar kafin ta yanke shawarar budewa ta fito a hankali tana waige waige, gidan alhaji ta nufa domin bata tunanin zata iya shiga gidansu dan bata san irin kar'bar da mahaifiyarta za tayi mata ba.
A sanyaye ta tura kofar palon hajia ta shiga da 'yar karamar sallama a bakinta, shuru palon babu kowa sai dai tana d'an jin motsi gami da magana sama-sama a dakin data zauna kafin auranta da Bash, A sanyaye ta zauna kan kujera tana takure jikinta ta kai minti goma a zaune babu wanda ya fito hajia na sama su kuma su Halisa da yaran na cikin wannan d'akin babu wanda yasan da shigowarta, ganin gari ya soma haske yasa ta yanke shawarar miqewa domin taje tayi sallah....Dakin dasu Halisa suke ta nufa tana tafiya salau salau wanda kana ganinta zaka fahimci karfin hali kawai take yi.......A hankali ta tura kofar dakin ta shiga da sallama a bakinta, gabad'ayansu suka juyo suna kallonta, Mussadiq ya miqe a guje yaje ya rungumeta yana tsalle da murna had'e da kiran sunanta duk ya cikwikwiye mata hijabin jikinta
Mufida taje gurinta tana ta murna da farin ciki....Saddiqa kuwa tana zaune a inda take ba zaka tantance yanayin da take ciki ba....Naja'atu ta miqa mata hannu murya na rawa tace"Zo." Saddiqa ta mayar da kwallar dake kokarin zubo mata ta miqe a nutse ta nufi inda take
Zeey dake bacci sakamakon ihun! da Mussadiq yayi yasa ta miqewa zaune tana 'bata ranta, tana kokarin yin magana Halisa ta fito daga toilet sai kawai idanunta ya sauka akan Naja'atu dake tsaye a bakin kofa ta rungume yaran sai hawaye take
Halisa tace"Naja'atu dama ke suka gani suke wannan ihun? ni ina bandaki naji ihu ina addua Allah yasa ba fad'a suke ba ashe kece." Tace."Nice aunty Halisa ya kuke ina fatan na sameku lafiya." Halisa babu yabo babu fallasa tace"Muna lafiya gabad'ayanmu." Daga haka sai ta wuce ta dauki dadduma da hijabinta ta tayar da sallah.....Ita kuwa Zainab komawa tayi ta kwanta tana jan qaramin tsaki ita dai tana bala'in kishin Naja'atu mussaman yanda taga maigidanta gami da yaran sun damu ita.
Tace"To kuje ku zauna nayi alwala nayi sallah sai mu zauna mu sake gaisawa."suka samu guri suka zazzauna suna kallonta ta nufi toilet sai murmushin jin dadi suke.....Mussadiq kasa hakuri yayi cike da farin ciki ya nufi gurun Zainab yana fad'in "Auntymu ki tashi ku gaisa ga Yaya Naja'atun ta dawo daga tafiyar da tayi.''
Zainab idanunta a rufe tace" Mussadiq bacci ne a idona idan na tashi a bacci zamu gaisa." Yaron jikinsa yayi sanyi dan baiji dad'in abunba jiki a sanyaye yaje ya zauna kusa da 'yan uwansa.......Ita kuwa Halisa bayan ta idar da sallar carbi ta shiga ja tana istigifari ga Allah(😅 Su Halisa an musulunta an koma ga Allah to Allah ya kar'bi tuban ta damu baki daya)
Abbah Abbas da kyar ya samu kansa dan ana idar da sallah jama'a sukayi caaa! a kansa suna masa jajen dangane da qaddarar data fad'a masa a kasuwa kowa sai fad'ar albarkacin bakinsa yake, to shi dai magana d'aya yake fad'a cewa komai ya sameshi daga Allah ne yana rokon Allah ya kare dukkanin musulmi da mugun ji da gani.......Sai kusan bakwai da kwata ya samu ke'bewa dasu Alhaji nan ya tabbatar musu da cewar ya dauk'o Naja'atu daga inda take kuma tana cikin koshin lafiya kamar kowa sai dai maganar cikin jikinta ya sanya duk jikinsu yayi sanyi suka shiga cikin halin jimami daga bisani suka barwa Allah ikonsa domin kuwa duk abinda Allah ya zartar a kan bayinsa shine daidai, babu wanda yasan abinda Allah yake nufi dangane da faruwar al'amarin shiyasa gabadayansu sukayi wa yarinyar adduar sauka lafiya tare da adduar Allah ya inganta abinda zata haifa.
Koda ya duba cikin motar yaga bata ciki bai damu ba saboda yasan bai kulle motar ba zata iya budewa ta shiga cikin gida......sai kawai ya nufi gidan Alhajin dan nan yake tsammanin samunta.
Lokacin Naja'atu da yaran suna sama gurin hajia dan bayan tayi sallar jansu tayi domin suyi mata jagora zuwa gurin hajian masifar kunyar had'a ido take yi da ita shiyasa taja yaran domin su zame mata garkuwa.
Magana yaji 'kasa-'kasa a cikin dakin dasu Halisa suke, sai kawai ya nufi dakin dan yaji kamar muryar Zainab na magana......."Nifa aunty Halisa jikina yay sanyi wallahi anya kuwa Abbansu Mussadiq ba mayar da Naja'atun nan zaiyi ba? Kinga ni mahaifina malami ne amma ba malamin zaure ba malam ne mai fad'a akan abi sunna gami da dokokin ubangiji mu ba ma asiri da tsafi! amma tun kafin na auri mijinki muka samu labarin abinda ke faruwa ance shi wannan Baba malam din asiri yake yi ya asirce Alhaji dashi Abbansu Musaadiq din sannan kuma baya bari 'ya'yansa su wulakanta kullum cikin aiko musu da asiri yake shiyasa da waccar matar tasa ta rasu aka dauki qanwarta aka maye gurbin ta! wallahi ganin yanda kowa yake rawar jiki akan Naja'atun nan yasa jikina ya mutu wani irin tsanarta nake ji a cikin raina."
Halisa ta ajiye carbin hannunta tana wani irin murmushi kai da ganinsa kasan na takaici ne tace''Zainab kenan to ni kam bansan abinda zance miki ba, tunda kin yarda da cewar Baba malam asiri yake sai kiyi takatsantsan da kanki kowa ya iya allonsa ya wanke ni yanzu duk ba wannan ne a gabana ba, maganar wai Abban Mufida zai dawo da Naja'atu gidanshi, ban sani ba, idan ma ya dawo da ita ni babu abinda ya dame ni ko wacce tata ta fishsheta."
Zainab tace"Aikuwa mu bama boka bama malam Allah kad'ai muka dogara dashi saboda haka banga asirin da wani boka zaiyi yayi tasiri a kaina ba."
Duk wannan maganganun a kunnansa, gaskiya yayi mamaki sosai! wai me yasa mutane suke hakane? duk wanda akaga babu ruwansa da duniya yana bin Allah sau da qafa sai a takura masa , tunda ya taso a unguwar kofar na'isa bai ta'ba jin wani yayi mummunar kalma akan Malam Sani ba, sai Halisa itace kullum ke kiransa da boka ko dan tsubbu to yau gashi an wayi gari itama Zainab tana kiranshi da wannan sunan duk kuwa da cewar ta fito daga cikin gidan da ba'a yarda da shirka da asiri ba gashi kishi yasa tana gazgatawa! duk akan ya tsaya a cikin al'amuran Naja'atu suke wannan surutan har suna zargin ko zai mayar da ita dakinta hmmmm! baya tunanin zai sake zaman aure da Naja'atu a yanzu duk wani abu da yake a kanta yanayi ne domin Allah da manzonsa da kuma lalurar cikin da take dauke dashi,
Gyaran muryarsa ne ya dawo dasu hankalinsu, ya shiga dakin da sallama a bakinsa, Zainab da sauri ta riga Halisa magana tana wani irin murmushi na iyayi da kissa tace"Habibi sannu da zuwa ina fatan ka dawo lafiya." ? Ba tare da yayi mata cikakken kallo ba ya amsa yana kallon Halisa da tayi qasa'ke tana kallon ikon Allah...Zainab ganin yanda ya amsa mata a banzace sai jikinta yayi sanyi tunda take dashi bai ta'ba yi mata irin hakaba.
Halisa ta gaisheshi a nutse tana tambayarsa hanya ya amsa babu kyakkyawar walwala a tare dashi yace."Waye ya baku izinin zuwa nan gidan ku kwana."? Sai sukayi tsuru tsuru suna kallonsa domin duk cikinsu babu wacce take da hujja." Halisa da yake tasan halinsa idan yana fushi ba'a katse masa hanzari sai taja bakinta tayi shuru.....Ita kuwa Zeey sarki karambani tace"Habibi Hajia ce tac.......Hannu ya d'aga mata da fad'in "Rufe min baki sarkin magana! Hajia ce tace me? kina so kiyi mata karya ko.''? shuru tayi tana girgiza kanta, Yace."Dama ai so nake na dawo na tambayeki dalilin daya sa kika fitar da hannu kika mari Yaya Ramlatu ashe dama baki da kunya da tarbiya."? Halisa cikin zuciyarta tace " Anzo gurun.
Zainab ta fashe da kuka tana kallonsa tace"Waye ta fada maka na mareta wallahi ni sharri akayi min yaushe ma zan mareta ba haba sai kace mara hankali itace fa kawai ta shigo gurina tana zagina amma ni ban mareta ba sai dai itace ma ta dokeni iya son ranta."
Yace."Bakin daya fad'a min ba zaiyi min karya ba kin mare ta ko baki mareta ba."? Zainab ta dinga rantse ranste ita bata mareta ba sai kuka take tana neman mafita.....Yana 'kokarin yin magana hajia tare dasu Naja'atu suka shigo dakin...Ganin Zainab na kuka yasa hankalinta ya tashi tace"To me yake faruwa haba kai kuwa daga dawowa sai ka aikata abunda bai dace ba ." Yace."Hajia yarinyar nan bata da kunya wallahi wai sun samu sa'bani da Yaya Ramlatu shine ta fitar da hannu ta mareta."
Hajia tace"Subahanallahi yaushe akayi hakan."? Ya kalli su Saddiqa da fad'i! Saddiqa Zainab ta mari Yaya Ramlatu ko kuwa."? Saddiqa da sauran yaran suka sunkuyar da kansu saboda basu iya karya ba."
Yace."Yanzu kin tabbatar da ba sharri akayi miki ba ko, a gabansu kika tsinkawa uwarsu mari sabida baki da kunya ko me tayi miki ai sai ki bari na dawo ki fada min aa sai ki ka shirya karya da gaskiya kika kira ni a waya kika fad'a min to jiya Salim ya sheda min duk abunda ya faru a tsakaninku."
Zainab bakinta ya mutu murus sai hawaye dake zubo mata ta kasa magana ma ballantana ta kare kanta, Hajia tace'' Idan ya kasance Zainab ta mari Ramlatu sai mu kira al'amarin da sunan hakkin wasu ne ya kama ta! Shin Ka tambayi dalilin zuwanta gidanka? Ramlatu ni na haifeta amma nafi kowa sanin halinta taje gidanka domin ta 'bata maka iyali da mugun halinta ni banga laifin Zainab ba sabida hausawa nacewa(Idan babba ya zubar da girmansa sai na qasa dashi ya hau kai ya taka) sabida haka idan za kayiwa yarinyar nan fada kayi mata akan wani abu daban ba'akan Ramlatu ba wacce idan ta samu damar da take so ba zata bari ma ka zauna da iyalin ka ba." Jikinsa ne yayi sanyi kuma dajin maganganun hajian, Hakane tabbas Ramlatu ta samu damar da take so a kansa zata iya hanashi zaman aure da mugun halinta abinda yasa yake wa Zainab fada yana so ya nuna mata girma da mutuncin 'Yan uwansa kodan gaba zata kiyaye aikata abinda ta aikata.
Fita yayi daga dakin.... Hajia kuwa sai da ta tsaya ta rarrashin Zainab din kafin ta fita daga dakin.
Abbah Abbas yana zaune a kan kujera yana jiran fitowar mahaifiyar tasa su gaisa, a fakaice yake satar kallon Naja'atu dake zaune da yara suna magana, tayi wanka har ta sanja kayan jikinta sabuwar atampa hajia ta bata tasa a jikinta duk sai ta dawo hayyacinta, ya dinga satar kallonta ta'kasan idonsa yana mamakin uban haske da tayi a ganinsa hasken yayi yawa kuma baiyi kama dans ciki ba na rashin jini ne dan haka koda hajia ta fito suka gaisa yace yana ganin ko za'a kaita a asibiti a dubata dan yana tunanin akwai karancin jini a jikinta.....Hajia ta shiga duban Naja'atu tana nazarinta itama taga haskenta yayi yawa mussaman hannayenta da kafafunta, tace"To hakan ma nada kyau sai a bari sai zuwa gobe ko hajia Rabi sai ta kaita a dubata naga cikin nata ma yayi kwari." Yace." To babu laifi Allah ya kaimu goben lafiya......A nutse ya kalli Mussadiq yace."Jeka kira Mommy da auntyku zamu tafi gida."Yaron ya miqe da sauri ya nufi dakinsu................Yaya Ramlatu ce ta shigo gidan tana kuka sai kace 'kan'kanuwar yarinya ta wani fad'i gaban mahaifiyarta tana sheshsheka da fad'in "Hajia na shiga uku na lalace! Ayuba ya cuce ni ya sake ni." Sai ta fito da takardar sakin dake hannunta ta jefar da ita kusa da kafafunsa....Da sauri ya dauki takardar ya warware ya soma karantawa......Da gaske Ayuba ya saki Ramlatu saki daya amma bai fadi dalili ba yace sai yazo yayi bayani.
Hajia ta shiga rud'ani sosai! to wai wace irin masifa ce ta rikito musu a cikin lokaci guda, Allah ta shiga kira a cikin zuciyarta tana ro'konsa ya kawo musu mafita......Abbah Abbas ya miqe a fusace! yace."Wane irin sakin wulakanci ne wannan kawai babu laifin komai sai ya sake ki ai kamata yay yayi mana bayanin abinda yake faruwa.".......Ramlatu za tayi magana sai ga Alhaji da Ayuban da Salim sun shigo palon kallo d'aya yayi musu yasha jinin jikinsa ganinsu yayi wani irin kamar wasu marasa lafiya suka nemi guri suka zazzauna, Ramlatu ta sake fashewa da kuka! Da fad'in "Wallahi tallahi bani na tura shi ya aikata wannan aika aikan ba. Ya ma za'ayi na had'a baki da d'ana a cutar da d'an uwana."............
*Littafin na kudi ne...!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin ga yanda abin yake....Vip group #600 normal group #300 account....0542382124.....Binta umar gtbank..Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number...
*07084653262...BINTA UMAR ABBALE*
65 Gabakid'ayansu hankalinsu ya koma kan Yaya Ramaltu dake wani irin kuka tana sake nanata maganarta ta farko na cewar ita ba itace ta tura Salim yaje ya aikata abinda ya aikata ba....
Alhaji ya buga mata tsawa da fadin."Rufe mana baki.mutuniyar banza mai ba'kin hali Ramlatu nayi nadamar haihuwarki tun kina yarinya kike bani wahala na rasa a wane guri kika dauko wannan mummunan halin naki yanzu ki rasa wanda zaki cuta sai dan uwanki wanda kika sha nono kika bashi kike wa qeta shin me Abbas yayi miki a duniya wanda zai sanya ki had'a bakinki da d'anki ku sa masa wuta a cikin dukiyarsa."
Abbah da hajia sukayi saurin kallon alhjin jin maganar da yake, hankali a tashe hajia tace"Wai shin me yake faruwa ne ku fad'a min na rasa gane inda maganarku ta dosa.
Alhaji ya kalli Ayuba da fad'in "Yana da kyau ka fad'i maganar data kawo ka a gaban kowa yaji cewar wad'annan mutanan ba mutanan arziki bane." Yafada yana nuna Ramlatu da Salim dake zaune duk sun muzanta.
Ayuba yace."Hakika na jima ban shiga tashin hankali da mamakin abinda kunnena yaji min ba a yau .Na dawo daga sallar asubah nazo gifta dakin Salim sai naji maganarsa da mahaifiyarsa sama sama nayi mamaki sosai dan na dauka yaron yaje sallah kamar yanda na shiga na tashe shi kafin na fita, ashe bayan fita ta mahaifiyarsa ce ta shiga dakin ta hanashi zuwa massalacin........Lokacin da naji maganar da suke tattaunawa akai sai da na kusa fad'uwa sabida tsananin mamaki da al'jabi Salim na shedawa mahaifiyarsa cewar shine ya kunna wuta a cikin rumfar dan uwanta dake kasuwa, sai nayi shuru ina sauraran naji abinda zata ce. Kawai sa naji tana fad'in "Ya kyauta mata hakan da yayi dama saboda dukiya Abbas ke wulakantata har da dauko mata police yazo har gida yaci mutuncinta saboda haka idan ma da akwai wata hanyar da yaron zai sake bi yaga ya kassara dan uwanta to ta bashi goyon baya yaje yayi ya kuma cigaba da nuna masa cewa shi mai kaunarsa har dai bukatarsu ta biya suga sun kai Abbas d'in k'asa! wannan al'amari ya d'aga min hankali mutuka dan ban san sanda na fad'a dakin ba, suna ganina duk sai suka diririce alamun rashin gaskiya ya bayyana a idonsu.
Cikin takaicin da tsananin bacin rai da damuwa nace musu duk naji abinda suka aikata ashe dama sune silar faruwar gobarar data cinye dukiyar Alhaji Abbas? sai dukkaninsu suka shiga rantse rantse cewa basu bane gabadaya ma ba maganar suke ba.....Alhaji ku yafe min a lokacin ji nayi ina nadamar auran Ramlatu ina kuma nadamar hada zuria da ita! hakika tunda na auri wannan baiwar Allah na kasa samu nutsuwar zuciyata kasancewa ta matafiyi duk sanda zan dawo sai jama'ar unguwa makusantana sun kawo min magana a kanta, cewar kullum a kan hanya take bata zama gida itace shiga can fita can! tun a wancan lokacin zargi ya shiga tsakanina da ita sabida kowa akwai maganar da zai kawo min a kanta......Allah ya had'ani da mace tagari Sakina kullum itace ke hanani na aikata abinda nayi niyya akan Ramaltu Sakina mutuniyar arziki ce kuma tana kaunar zama da Ramlatu da shiriyarta shiyasa ta juri cin mutuncin da take mata.....Ban ta'ba jin tsanar Ramlatu ba irin yau! jin mummunan aikin data tunzura d'anta yaje ya aikatawa d'an uwanta wannan dalilin yasa naji kamar naje na dauko musu hukuma a tafi dasu dan gabadaya zama dasu annoba ne tunda sun zama 'yan ta'addah gwara suje su fuskanci hukunci sai kuma nayi tunanin cewar ai bani da hurumi yin hakan, wannan dalilin yasa ni na yanke shawarar rabuwa da ita dan gaskiya dama can zama hakuri kawai nake da ita, idan ina gurin sana'ata hankali kwata kwata ba a kwance yake ba saboda ina tunanin abubuwan da suke faruwa a gidana, jama'ar gari da abokaina gabadayansu babu wanda yake wa Ramlatu kallon mutuniyar kirki harda masu kiranta karuwa! wannan kalmar na daga min hankali mutuka! shiyasa na gaza samun nutsuwar zuciyata da ita gurin mu'amular aure..........Ina rokon ku afuwa kan hukuncin dana yanke a kanta kamar yanda na rubuta mata saki daya jikin takarda hakane na sake ta saki daya idan ta samu miji tayi aurenta kai kuma Salim babu ni babu kai na yafe ka a duniya tunda ka zama butulu maci amana." Ayuba ya kare maganar muryasa na wani irin rawa.
Gabad'aya palon shuru yayi kowa na mamaki da Tu'ajibun wannan al'amarin....Hajia Kuka take tana Kallon Ramlatu tana so tayi magana amma tsabar damuwa da 'bacin rai ya hana ta iya cewa komai.........Wani sabon kukan suka ji da sauri suka kalli inda kukan ke tashi...Halisa dake tsaye a bakin kofar daki ta karaso cikin palon tana hawaye cikin tsananin damuwa gami da nadamar abinda suka aikata a baya, ta kalli Ramaltu tace"Nima babu abinda zance dake sai dai na had'aki da Allah ya saka min kin cuce ni kin cutar da d'an uwanki sannan kin cutar da baiwar Allah Halimatu wacce ba taji ba bata gani ba! wallahi tunda uwata ta haifeni ban ta'ba zuwa gurin wani boka ko malami ba wai dan yayi min duba ko yayi wa wani asiri sai da kika shigo rayuwata kika lalatani da zuwa gurin bokaye! wane gari ne baki jani kin kaini ba, har tsutsa sai da kika kaini gurin bokan da ya bani naci! a matsayinki na 'yar uwar mijina bai kamata kiyi mana hakaba kin cutar damu Allah zai saka min gashi garin biye biyen bokaye gami da shaye shayen maganin mata kinsa na had'u da lalura mai wahalar magani ni kuwa me zance miki a rayuwata wallahi Yaya Ramlatu kinci amanar zumunci."!
Yaya Ramlatu ta dinga kuka tana had'a hannuwanta guri da fad'in "Ku gafarce ni nima ba laifina bane sharrin shedan ne wallahi kuyi min addua Allah ya gafarta min laifukana."
Gabad'aya palon suka zuba mata ido jin maganganun da takeyi tana kuka....Naja'atu murya na rawa tace"Salim idan ban manta ba ka ta'ba fad'a min wata magana a kan Abbah cewar a kwai lokacin da kake so ka rabu dashi bayan bukatarka ta biya a kansa! ashe wannan ne lokacin kana so ka cutar dashi ko? yanzu meye ribar abinda ka aikata masa? kada fa ka manta Abbah yayi maka abinda iyayenka da suka haifeka ba suyi maka ba me yasa kake cin dunduniyarsa? kana nufin dan kasa masa wuta a kan dukiyarsa ya gama arziki kenan? lallai ashe baka da hankali kuma baka san waye Ubangiji ba! a lokacin da hassada da ganin kyashi sukayi yawa a kan mutum a lokacin shi kuma Ubangiji ke qara daukaka darajarsa! wallahi wannan abun da ka aikata a banza domin duk zakaran da Allah ya nufa da cara sai yayi, daga karshe nake so in sake jaddada maka cewar ka samu nasarar raba tsakanina da Abbah ta hanyar zuga ni da nuna min aibunsa tare da tunzurani nayi masa rashin kunya to bukatarka ta biya amma ka sani duk abinda kayi mana mutukar muna da hakki sai Allah ya saka mana sannan kuma insha Allahu sai na koma dakina sai dai ka mutu da bakin ciki." Cikin kuka mai wahala take maganar.
Wannan tone tone da akeyi yayi masifar sanya shi cikin d'imuwa da tashin hankali......
*Ke duniya!!!* ina zaki damu? wai shin me mutane suka dauki duniya ne? duk yanda fa ka tafi da ita haka zata tafi da kai! Jama'a su sakankance a duniya suyi ta shirya mugun abu kamar sun samu madawwama! me yayi wa mutane da dama da suke cin dunduniyarsa ba'a gida ba ba'a waje ba, Yanzu ashe dama da sanya hannun Salim gurin fujirewar Naja'atu gurin rashin so zama dashi, meye ribar abinda Salim yayi masa gashi nan da yake bashi da hakkin kowa tun ba'aje ko ina ba daga shi har uwar tasa asirinsu ya tuno shi kam me zaice da wad'annan bayin Allah."
Alhaji ya kalli Ayuba da fad'in "Banji ciwo da takaicin sakin da kayiwa Ramlatu ba, shi aure anayin sa ne bisa amana da yarda da juna, kayi kokarin ma tsayin shekaru kana zaune da ita bayan kana zarginta! nima yanzu zargin nata nake saboda dukkanin abinda ka fad'a jama'ar gari suke a fad'a a kanta zata iya aikatawa saboda ba tsoron Allah take ba saboda haka kada ka sanya a ranka cewar ni Sama'ila zan qullace ka dan ka saki Ramlatu nayi maka farin cikin rabuwa da ita."
Ramlatu na kuka ta rarrafo gaban Alhajin tana kuka tace"Alhaji ka gafarce ni dan darajar annabi ka ro'ki Ayuba ya mayar dani wallahi duk abinda na aikata kuskurene da son zuciya hakika nasan nima ban kyautaba zuciyata ta tunzurani na cutar da dan uwana, sannan wallahi zargin da jama'ar gari suke min ba haka bane! ban ta'ba zina ba nasan dai kullum bana zama a gidana ina yawace yawace amma ba bin maza nake ba
*( qalubale gareku matan dake yawace yawacen banza da wofi haka kurrum ki kulle gidanki kiyi ta shige da fice a unguwa to wallahi yanzu kiwon mutum ake ba dabbah ba, shashahar mace itake yawon bid'id'i! fakal fakal ko wane namiji na qarewa tafiyarki kallo ke idan aka samu 'yan iska ma kiji wani yay miki magana idan kince ke matar aure yace ya raina miki hankali yace ai ya dauka bazawara ce! hattara mata mu mutunta kanku sai Allah ya mutuntamu)*
Alhaji miqewa yayi ya kama hanya zai hau samansa dan zamansa a gurin yana kallon fuskar Ramlatu zai iya sanyawa jininsa ya hau dama ba lafiya gareshi ba......Ramlatu ta rarrafa gurin Dan uwan nata ta rike masa kafafu tana kuka tace"Abbas ka gafarce ni wallahi sharrin zuciya ne ni kaina na rasa me yasa nake maka hassada duk da cewar babu abinda zan nema a gurinka ba kayi min ba, ka dauki d'ana ka ri'ke tamkar kai ka haifeshi kayi masa komai na rayuwa amma na kasa kyautata maka zuciya na ingixani akan na cutar da kai nima yanzu na gane zuciyata bata da kyau! kayi hakuri ka gafarce ni ka yafe min ka yafewa Salim abunda mukayi maka."
Abbah ya ciro hankici a aljihunsa ya goge zufar goshinsa hularsa ya dauka yasa cikin wani irin yanayi na damuwa da alhini yace."Na yafe miki sai ki cigaba da neman gafara gurin Allah ina rokon Ubangiji yasa wannan tuban da kikayi na gaskiya ne." yana gama maganarsa ya miqe! Salim cikin borin kunya gami da nadama Yace."Kawu ka duba darajar Annabi Muhammad ka gafarce ni wallahi shedan ne! ya tunzurani cutar da kai yanzu na gane qarya da yawancin wasu abubuwa na mugunta basa lasting Idan mutum naso ya zauna lafiya a wannan duniyar to ya kad'aita Allah shi kad'ai kuma ya ri'ke gaskiya d'aya mutukar yayi haka to zai zauna lafiya kuma koda mutum ya nufe shi da mugun abu to Allah zai kareshi."
Abbah Abbas ya jima a tsaye yana kallon Salim din dake hawaye kansa a kasa kunya ta hanashi ya dago kai ya kalleshi, yace."Salim kaima na yafe maka Allah ya yafe mana baki daya." Ya kalli Hajia cikin wata iriyar murya da bata fita sosai yace ''Zamu tafi." Hajia ta goge hawayen idonta cikin tausayi da jin kai irin na uwa da d'anta tace" Ina rokon Ubangiji Allah ya ji'banci al'amuranka Abbas Allah ya kare ka ga miyagun mutane da aljanu, duk wanda ke nufinka da sharri Allah ya maida masa kansa, Allah ya daukaka darajarka daukaka mai amfani Ubangiji Allah ya shi maka albarka Abbas hakika ina alfaharin haihuwarka Allah ya albarkaci zuriarka." Wannan adduar da mahaifiyarsa tayi masa itace ta wanke masa zuciyarsa tayi wasai gabadaya ma yaji ya daina jin takaicin abinda akayi masa........sai ya kasa 'boye farin cikinsa ya dinga amsa adduar mahaifiyarta sa yana jin wani irin dadi yana ratsa shi.
To bayan tafiyar Abbah Abbas da iyalinsa Hajia ta kalli Yaya Ramlatu cikin bakin ciki da takaici tace" Ramlatu bana tunanin zan zauna dake a gidan nan sabida haka tun wuri ki nemi inda zaki je ki zauna, Idan ya kama dole sai kin zauna to ni ina iya bar miki gidan dan ni wallahi sharrin ki tsoro yake bani."
Ramlata cikin sarewa da al'amarin ta nufi mahaifiyar tata murya na rawa tace"Hajia dan darajar Allah kada kije ko ina a kaina kiyi zamanki a dakinki wallahi na tuba nabi Allah na gane abinda nayi ban kyauta ba insha Allah ba zan sake ba ki yafe min Naja'atu kema ki yafe min abubuwan da nayi miki." Naja'atu ta goge hawayen idonta ta kalli hajia murya na rawa tace"Hajia dan Allah ki yafe mata tunda ta gane kuskuranta kin san adan adam ajizi ne kowa yana kuskure a duniya kinga shima wanda akayi wa laifi kafin ya tafi sai da ya yafe mata tukkuna." Hajia tace"Humm! Naja'atu kenan har yanzu ke yarinya ce kina ganin kamar abinda take fada har zuciyarta ne nafi kowa sanin halin Ramlatu da rantsuwa kan karya."
Hajia Rabi dake kokarin shigowa dakin tace"Ke kuwa Hajia ki daina wannan maganar mana, kiyi addua kan Allah yasa tuban Ramlatu na gaskiya ne ni a jikina ina jin cewar karshen matsalarta ne yazo akwai mutane da dama da suke aikata mummunan abu wanda yafi nata su tuba su nemi gafarar Allah ya gafarta musu, kema don Allah ki yafe mata tunda shi Abbas din ya nuna komai ya wuce kuma dan Allah ki daina fad'in zaki fita ki bar mata gida wannan maganar bata dace ba." Hajia tace"To shikkenan tunda kunce haka na hakura na barku da ita gatanan ta zauna idan halinta ne zaku gani ni tuntuni na dawo da rakiyar Ramltu shiyasa nake so tayi nesa dani da zuria ta."
Ramlatu tace"Hajia ashe har kin cire ni daga cikin zuriarki me yayi zafi hajia ki duba halin da nake ciki nice fa babbar 'yarki." Hajia taja tsaki gami da miqewa da fad'in "Kece babba kuma kece fitinanniya wacce bata kaunar zaman lafiya Allah dai ya shiryeki." Tana kare maganarta ta mike tare da kallon kishiyarta tace"Hajia gobe idan Allah ya kaimu da safe zakuje asibiti da Naja'atu a dubata." Hajia Rabi tace"To Allah y kaimu goben lafiya." Hajia sama ta nufa ba tare da ta saurari magiyar da Ramlatu take mata ba.....Hajia Rabi ta kalleta a nutse tace"Hakuri zakiyi Ramaltu ki cigaba da rarrashinta har ta sakko amma hakikanin gaskiya ke da d'anki kun aikata mummunan aiki sai dai kawai ace Allah ya kyauta ya kuma kiyaye gaba."
Ramlatu tasa gefan zaninta ta share hawayen idonta jingina tayi jikin kujera tare da tsirawa kasan kafet ido tana tunanin yanda rayuwa ta juya mata baya.....Naja'atu kuwa miqewa tayi ta shiga daki ta kwanta tana zubar da hawayen bakin ciki, tana kallon Abbah Abbas ya tattara iyalinsa suka tafi banda ita wannan al'amarin yayi masifar tsaya mata a rai! sai ta shiga tunanin ita yanzu mecece makomarta.
To washe garin ranar da wuri Naja'atu da hajia Rabi suka shirya direba ya daukesu suka nufi asibiti da yake pravite ne basu sha wahalar ganin likita ba.........Dr ya tabbatarwa Da hajia Rabi cewar Naja'atu ita da babyn dake jikinta lafiyarsu lau, hasken da fatar tayi ba matsala bane mafi akasari masu karamin ciki nayin irinsa, har scanning sai da yayi mata ya nuna musu tare da tabbatar musu da lafiyar babyn magunguna masu kyau ya rubuta a takarda sannan yace suna fita zasu ga gurin saida magani sai su siya...........Hajia Rabi taji dadin bayanin da Dr yayi kan lafiyar Naja'atu da cikin jikinta, dan haka kafin su nufi gida sai da suka tsaya a Pharmacy (gurun siyar da magani) suka siya kana suka shiga mota direba yaja suka nufi gida.
Koda suka isa gida hajia rabi bata bari direba ya shiga da motar cikin gidan ba ta umarce shi daya saukesu....Suna fitowa ta kalli Naja'atu a nutse tace"Zamu shiga gidan Baba malam ku gaisa ko."? Naja'atu tayi kwal kwal tana shirin yin kuka tace"Hajia ina jin tsoron haduwata da Baba Talatu." Hajia Rabi tayi murmushi tare da girgiza kanta tace"Ki saki jikinki kada ki damu bazan bari tayi miki fad'a ba! Baba Talatu macace mai ilimi tasan qaddara daidai gwargwado saboda haka ki kwantar da hankalinki nayi niyyar kaiki gurinta ku gaisa ba da wata munufa ba." Naja'atu ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace"Nagode hajia." Hajia rabi tace"Babu komai ai." Hannunta ta riqe kai tsaye suka nufi gidan baba malam d'in.........
*Wayyo hannuna😢 Ayi hakuri da typing error babu editing🤢 Nagode👌🏻*
*Littafin na kudi ne....!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake....Vip group #600 normal group #300 account... 0542382124...Binta umar gtbank idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number.... *07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
66****Baba Talatu na zaune a kan tabarma da karamar redio a kusa da ita tana sauraran shirin barka da hantsi wanda tashar redio freedom ke gabatarwa a daidai irin wannan lokacin Baba Talatu ma'abociyar jin redio ce shiyasa kullum kanta yake a waye ta iya mu'amula da mutane bayan hakan kuma tana zuwa isilamiyya irin ta matan aure duk ranakun asabar da lahadi( sauraran redio nada mutukar tasiri a rayuwar d'an adam akwai muhimman shirye shiryen addini da wasu tashoshin gidajen redion ke gabatarwa wanda idan mutum na saurara zai qaru da wasu abubuwan masu amfani, redio tamkar makarantar ce ta wanni fanni domin suna ilimantarwa )
Tunda suka shiga gidan Naja'atu take ra'be ra'be ta kasa sakin jikinta sai 'buya take a bayan hajia Rabi tana jin tsoron had'a idonta da mahaifiyartata......Baba Talatu ta gyara zamanta fuskarta da fara'a takewa Hajia Rabi sannu da zuwa, redion kusa da ita ta dauke daga gurin ta sanja mata guri tana fad'in'' Hajia bisimillah zauna ga guri nan."
Hajia Rabi ta zauna a nutse Naja'atu ta zauna kusa da ita sai sunkuyar da kanta takeyi............Bayan sun gaisa da juna Hajia Rabi ta kalli Baba talatu tace''Naja'atu na kawo miki ku gaisa da juna." Baba Talatu tace'' Au ita bata da kafafu har sai anyi mata jagora."? Hajia Rabi tace" Haba ba dai haka bane wallahi munje na kaita asibiti ne nace lallai sai na kawo ta ku gaisa da juna.
Baba Talatu ta ta'be bakinta taja bakinta tayi shuru har yanzu tana jin ciwo da takaicin abinda naja'atu tayi musu.....Naja'atu ta dago kanta a hankali ta kalli gurin da mahaifiyar tata take a sanyaye tace"Baba ina kwana kunanan lafiya."? Ba tare data kalleta ba ta amsa da "lafiyarmu lau." A sanyaye ta mayar da kanta qasa jikinta duk ya mutu da yanayin kallon da mahaifiyar tata ke mata....Hajia Rabi tace"Baba don Allah ki yafewa yarinyar nan magana ta wuce nasan ke mai ilimin addini ce kin san qaddara daidai gwargwado dan haka ki sassautawa naja'atu taji da abu guda.
A sanyaye tace"Ai bani tayi wa laifi ba da kike wannan maganar ita tasan wanda tayi wa laifi shi zata nemi afuwarsa bani ba."
Hajia Rabi tace"Wallahi tuntuni Alhaji Abbas ya yafe mata da bai yafe mata ba ai ba zai tsaya a kan al'amuranta ba nasan kina sane da cewar shine yaje har can garin da take ya daukota ko.''
A sanyaye tace"Duk inada labarin komai wallahi ni kam na rasa wace zuciya ce da mutumin nan hajia Rabi ki duba kiga irin rashin arzikin da yarinyar nan tayi masa amma bai duba ba ba tare da yayi shawara da kowa ba yaje ya daukota daga wahala ai naso ya barta a can ta gane duniya ba rigar sanyawa bace."
Hajia Rabi tace"Haba Baba ya kike wannan maganar babu dadin ji idan rai ya 'baci hankali ake sawa ya nemo shi, kuma a duniyar nan babu wanda baya kuskure saboda haka dan Allah ki daina wannan maganar Baba kiyi hakuri da duk wasu abubuwa da suka faru a baya tunda shima wanda akayiwa laifin maganar ta wuce a gurinsa sai mu taru gabadayanmu muyi wa yarinyar nan adduar rabuwa da cikin jikinta lafiya shine babban abinda ke gabanmu
Baba Talatu ta share guntun hawayen idonta tace"Wallahi tuntuni magana ta wuce a gurina kuma na yafe mata har abadah sai dai duk sanda na tuna al'amarin nakan ji rashin dad'i a zuciyata nida malam munso yarinyar nan ta zauna zaman aure da Alhaji Abbas amma ta watsa mana qasa a ido duk sanda na tuno wannan al'amarin nakan shiga 'bacin rai mai tsanani."
Hajia rabi tace"Gaskiya da akwai rashin dadi a cikin al'amarin amma bakya tunanin rabo ne ya fitar da ita daga gidan Alhaji Abbas din, dukkaninmu fa bamu san gaibu ba sai Allah wannan cikin dake jikinta ya ishemu ishara gabad'ayan mu."
Baba Talatu tace"Eh nima bayyanar cikin jikinta yasa na jingina al'amarin a matsayin abinda kika fad'a yanzu babu shakka idan rabo ya rantse to babu mahalukin da ya isa ya dakatar dashi, san nan kuma wani baya ta'ba haihuwar d'an wani koda da akwai sauran zama a tsakanin Alhaji Abbas da yarinyar nan to tilas sai taje ta auri wani ta haihu sannan ta dawo hannunsa."
Hajia Rabi tace"Yawwa nima abinda nake taso ki fahimta kenan watakila akwai ragowar zaman aure a tsakaninsu shiyasa Ubangiji ya yanke alaqar auranta da Bashir bayan ya saukar da ikonsa na samuwar cikin jikinta."
Baba Talatu tace"To Allah yasa dan wallahi nafi mata sha'awa ta koma dakinta akan ta sake wani auran." murmushi hajia Rabi tayi a zuciyarta tace akwai yiwuwar hakan dan ganin irin kulawar da Abbas keyi wa yarinyar alamu sun nuna har yanzu yana muradinta.
Mi'kewa tayi da niyyar tafiya ta kalli Naja'atu da kanta ke sunkuye tace''Zaki zauna ku sake gaisawa ko? bayan sallahr azuhur rana tayi sanyi sai ki shigo gida.'' " A hankali ta d'aga kanta tare da fad'in "To shikkenan." Hajia tace"Ga magangunanki nan idan kinci abinci sai kisha insha Allah idan na shiga gida zanyiwa hajia bayanin abinda dr ya fada sai ta kwantar da hankalinta."
Murmushi ta d'anyi tana sake sunkuyar da kanta da tunanin yanda hajia ta damu da ita da cikin dake jikinta ita kam babu abinda za tace da Iyalan gidan Alhaji sama'ila sun nuna mata zahirin kauna gami da kulawa a cikinsu babu wanda ya kyamaceta duk kuwa da cewar ita din mai laifi ce a gurinsu, amma sun kauda kansu suna tattalinta gami da bata dukkanin kulawar data dace.
Bayan fitar hajia Rabi da minti biyar ta dago kanta tana satar kallon mahaifiyar tata wada take ta kokarin sanja tasha daga freedom ta mayar redio kanoAm a hankali ta matsa kusa da ita ta riqe hannayenta murya na rawa tace"Baba dan Allah ki yafe min wallahi nayi nadamar abinda nayi muku kuma ni kaina nasan nayi kuskure mai muni nabi son zuciyata na jefa kaina a wahala, sai dai kuma a duk sanda naji kuna maganar kan cewa qaddarata ce hakan sai naji sanyi a cikin raina, yanzu babban burina shine na haihu lafiya na koma dakin mijina dana bujirewa auransa hakika yanzu na gane alkairi kuke nufi dashi ba sharri ba, nagane kuma babu wani d'a namiji da zan aura yaso ni kamar yanda Abbah Abbas ke sona Baba ku taya ni addua akan Allah ya mayar da aurana dashi."
Baba Talatu ta ri'ke hannunta tace"Alhamdullhi dama ina adduar Akan Allah ya nuna min zuwan wannan rana da zaki gane muhimancin abinda mukayi miki *MADADI BA HARAM! BANE* kamar yanda kika dauka a baya kina ganin mun cutar dake saboda munce ki maye gurbin 'yar uwarki Halimatu Naja'atu mune muka haifeki ba zamu ta'ba cutar dake ba, cancanta da nagarta muka hango shiyasa muke miki shawarar auran wannan bawan Allahn, a yanzu dai zamu iya cewa rabon wannan cikin na jikin ki yasa abubuwa da yawa suka kasance, babu abunda zamu ce sai dai muce Allah ya sauke ki lafiya bayan nan kuma mu roki Allah ya daidaita auranku dake da Alhaji Abbas domin shine babban burin mu dani da mahaifin ki."
To har bayan la'asar Naja'atu na tare da baba talatu suna labari kamar babu abinda ya faru, sosai Naja'atu ta sake a gidan ta daina d'ari-d'ari dan abinci ma tare suka ci abin gwanin ban sha'awa, koda baba malam ya dawo ya tarar dasu suna hira sai yaji dadi sosai ya zauna kan abun zaman sa ana hirar dashi a fakaice yana yi mata nasiha kan zamantakewar rayuwa da yanda zata kula da kanta da duniyar baki daya....Sosai Nasihar malam take ratsa jikinta kafin ta bar gidan jikinta yayi sanyi sosai! ta dinga neman afuwarsa dangane da abubuwan da suka faru, lokacin baba malam ya nuna mata cewar shi dama duk abubuwan dake faruwa da rayuwarta bai qullace ta ba ya dauki al'amarin a matsayin qaddara wacce ko wane d'an adam yake tafiya da ita.
Daf da magariba ta fito daga gidan malam hannunta ri'ke da ledar magungunta kai tsaye gidan Alhaji ta nufa tana tafiya tana kallon kasa dan bata so ta dago kanta ta kalli fuskar wanda ta sani a unguwar gani take kamar ta zama abun kallo a gurin jama'a shiyasa ta sunkuyar da kanta.........Sai data isa daf da gate din gidan sannan ta dago kanta aikuwa suka had'a ido dashi yana kokarin fitowa daga mota, d'an tsayawa tayi a bakin gate din tana murmushi har ya karaso inda take ta d'an risina tana gaishe shi ya amsa a nutse tare da tambayarta daga inda take dan bai ga sanda ta fito daga gidan baba malam din ba.....bayani tayi masa cewar tun bayan dawowarsu daga asibiti take gidan sai yanzu ta fito. Yace."Ta shiga gida idan ya fito daga massalaci zai shigo yaga magungunan nata.
Cike da kuzari ta shiga gidan tana jin wani farin ciki na ratsa mata zuciya yanda ya amsa mata gaisuwarta da sakin fuska shine yafi komai faranta mata rai! jikinta na bata har yanzu da sauran sonta a cikin zuciyarta watakila shima yana jira ne ta haihu ya mayar da ita gidansa, wannan tunanin ya sanya zuciyarta tayi haske.
Lokacin data shiga gidan hajia bata falo ta hau sama domin ta gabatar da sallah, sai kawai ta nufi dakin dakinta da take kwana, ta ajiye ledar maganin kan drowar ta cire hijabin dake jikinta ta shiga toilet domin ta dauro alwala..........Tana fitowa ta shimfida dadduma ta saka hijabinta ta kalli gabas.........Bayan ta idar da sallar tana zaune kan dadduma tana jan istigifari a cikin ranta sai zuciyarta ta shiga kwad'aita mata abubuwan ciye ciyen wanda ta saba ci lokacin da take jos gidan Mmn Sajida...Duk daran duniya sai taci kaza mai ku'li-ku'li dasu albasa da sauran kayan had'i! ta kan rasa a ina Mmn Sajida take sanyawa ana siyo mata wannan kazar mai dad'in tsiya......Yawun bakinta ne ya tsinke hankalinta yayi masifar tashi idan fa ba ta samu damar cin wannan gashashshiyar kaza mai quli quli ba akwai matsala! miqewa tayi tana jin jiri jiri ta nufi falo tana had'a hanya kamar wacce bata ganin gabanta.
Kujera ta samu ta zauna hawaye na kokarin kufce mata, idan ta tuno da gashshiyar kazar jos mai dad'i ji take kamar tayi tsuntsuwa taje taci......Hajia ta sauko ta sameta a takure a guri guda..Tace"Naja'atu kin dawo kenan? nace ai yau kinyi yinin gidan malam ai naji dadin hakan sosai sannan Hajia Rabi ta sheda min bayanin da likita yayi a kanki gaskiya nayi farin ciki jin cewar lafiyarki lau dake da yaron dake cikinki."
Murmushi kawai ta iya yi tayi shuru tana kallon guri guda! Hajia tace"A'a yana ganki wani iri ko bakya jin dadi ne."? Girgiza kanta tayi tana yar dariya tace''Aa wallahi lafiyata lau." Hajia ta bita da kallo tana kokarin ta fahimci wani a tare da ita!
Yaya Ramlatu ce ta shigo ta samu guri ta zauna a kan kujera Yaya Ramlatu dai kunya tasa ta kasa zama a gurin hajia sai ta gudu gurin Hajia Rabi can ta kai kayanta da Salim ya kawo mata sai dai ta shigo su gaisa...........Hajia tace"Gaskiya ban yarda ba akwai abunda ke damunki kada ki 'boye min damuwarki naja'atu ni uwarki ce ki sheda min damuwarki.
"Murya na rawa tace" Wallahi bani da damuwar komai hajia." Taqi fad'in maganar ne domin kada suga zaqewarta bata so ta dinga nuna musu kamar sun gaza dayi mata wani abun shiyasa takasa fad'a mata abinda take so
Abbah ya shigo ya tarar hajia na maganar, sai da suka gaisa tukkuna ya shiga tambayar abinda ke faruwa.....Hajia tace"Gata nan dai tunda ta shigo na ganta cikin wani irin yanayi jikina na bani kamar akwai abinda ke damunta."
Naja'atu ganin Abbah Abbas din ya sake karya mata zuciya sai kawai hawayen da take 'boyewa suka shiga zubowa." Tasa gefan hijabinta tana kare fuskarta...su hajia basu gani ba amma shi ya fahimci kuka take, gyaran murya yayi as'usul kafin yace."Naja'atu kina da damuwa me yasa ba zaki fad'a ba shuru ba zai amfana miki da komai ba idan baki fad'i lalurar ki ba zaki cutar da kan ki duba da cewar ke d'in ba lafiya kika cika ba, idan wani abu ke damunki kiyi bayani insha Allah za'a san yanda za'ayi." Falon yayi shuru suna jiran suji ta bakinta.
Ita kuwa kukanta ne ya tsananta dan da alama shagwa'bar data kwana biyu bata ta'ba ba yau ita za tayi.
Al'amarin ya bashi mamaki ya kuma bawa su hajia mamaki sai kuka takeyi taqi magana....Yaya Ramlatu cikin kokarin sake wanke kanta tace"Haba 'yar nan daga tambaya sai kuka dan Allah kiyi shuru ki daina kuka kada ki tayar mana da hankali wai shin meke damunki ne me kike so."?
Cikin shashshekar kuka tace"Yaya Ramlatu kaza mai yaji da quli-quli nake so naci."
Gabad'ayansu suka saki baki suna kallonta, danshi Abbah kasa 'boye mamakinsa yayi yana 'yar dariya yace."Sabida kawai zaki ci kaza mai yaji da quli - quli sai ki dinga yiwa mutane kuka saboda shagwa'ba." Hajia tace"nima dai abun ya bani mamaki wallahi haba Naja'atu meye abin kuka da damuwa da kin fad'a ai da tuni an siyo miki a bakin titi haba banji dadin wannan abuba wallahi bari na kira Dan azimi yaje *Murtala soya* ya siyo miki." Kokarin miqewa take ya dakatar da ita da fad'in "Zauna hajia bari na siyo mata da kaina." Hajia ta koma ta zauna da fadin "Yawwa dan Allah kayi sauri oh! ikon Allah ashe matsalar kenan." Ya Ramlatu na murmushi tace"Ai hajia kin san dama wani cikin haka yake da azalzala idan yaso abu idan bai samu abunda yake so ba sai ya saka uwarsa a wani hali! na tashin hankali."
Hajia tace"To ba ita kadai ba muma gashinan ya samu wani halin ikon Allah kenan Allah to Ubangiji Allah dai ya rabasu lafiya....Ya Ramlatu ta amsa da ameen tana jin dadin yanda mahaifiyar tata ta sake tana amsa mata maganarta.
Abbah yana fita motarsa ya shiga kai tsaye ya nufi inda yasan zai samo mata irin kazar da take buqata! *🤔 Ikon Allah a gaskiyar magana wannan soyayyar za tayi wahalar samu*
Ayi hakuri yau banyi posting a kan kari ba👏🏻
*Littafin na kudi ne....!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake.....Vip group #600 normal gruop#300...account... 0542382124...Binta umar gtbank...Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
67****To tundaga wannan rana Abbah Abbas ya d'orawa kansa nauyin siyo kaza mai yaji da qul-quli bama kazar kawai yake siyo mata ba harda sauran kayan kwad'ayi yake kawo mata, kafin kice kwabo Naja'atu ta sanja dik wannan ramar babu tayi qiba sosai saboda tana samun kulawa ta kowane bangare! Iyayenta kuwa rasa bakin magana sukayi danganin irin karamci da kulawar da 'yarsu take samu a gidan Alhaji Samaila ya sanya kullum basa gajiya dayi musu addua gami da fatan gamawa da duniya lafiya hakika Alhaji Sama'ila dashi da iyalinsa sun nuna musu kara gami da kauna sun dauki naja'atu sun ri'keta tamkar sune suka haifata basu da abinda zasu yi musu face adduar dacewa da samun rahamar ubangiji.
*Bayan sati biyu*
Al'amuran sunyi wa Abbah Abbas sauqi katuwar rumfarsa wacce wuta ta cinye ta dawo sabuwar dal kamar ma wani abu bai faru ba, a yanzu kayan da suke cikin rumfar sunfi nada yawa rumfar cike take da irin kayayyakin da jama'a ke bukata, kada ku dauka ko yaci bashi a gurin abokan sana'arsa ko daya Allah babu yanda baya zartar da ikonsa Abbah Abbas dalilin wannan abu da ya same shi ya janyo masa samun alkairi sosai daga gurin abokanan sana'arsa ta kwangila ita kanta gwamnatin garin sai da ta bashi tallafi dan ganin irin hidimar da yake mata hausawa dama suka ce wani hanin ga Allah baiwa ne, Abbah ya samu matasa wanda suka rasa aikin yi ya samar musu gurbi a cikin rumfunan sa dake kasuwar, Yanzu Abdulhamid shine a matsayin babban yaronsa ya yarda da yaron sosai ya amince da gaskiya da amanarsa shiyasa yaja shi a jikinsa yana nuna masa yanda harkokin kasuwanci suke saboda gaba baya so duk wanda yake karkashinsa ya dawwama a gurin yi masa bauta ya fiso kowa ya tsaya da kafafunsa shiyasa ko kad'an baya yiwa yaransa mugunta ta kowane fanni suna jin dadin zama dashi
*( Haka ake so shugaba ya zama adali mai kaunar cigaban na qasa dashi mafi akasarin abinda yake damun wasu 'yan kasuwar kenan kiga mutum kullum kansa ya sanyi daga zarar yaga wanda yake qasa dashi zai tashi sai ya mayar dashi ya dankwafe! kullum dai yafi so yayi ta zama a karkashinsa yana masa wahala.....Wannan ba adalci bane idan kana so kayi qarko jama'a su dinga fad'in alkairin ka to kada ka saka ganin kyashi da ganin ido a cikin al'amuranka idan ka samu abunda ka samu sai ka sakarwa na qasa da kai shima ya samu....Allah ka karemu da ganin kyashi da hassada)*
*BASH!*
To Bash ya samu nasarar k'etara kasar Najeria inda kai tsaye ya sauka a 'kasar ghana tare da maqudan kudaden da suka sato a bank....Akwai abokansa a garin saboda haka yana sauka a airport ya kira daya daga cikinsu, ko minti talatin baiyi ba a gurin wata zungureriyar bakar mota tazo ta daukeshi, koda ya shiga motar sai yaga duk guyz ne irinsa shi kadai ne musulmi ma a cikinsu dukkaninsu kafurai ne yawancin su ma had'uwa kawai sukayi da juna kowanne da kasar da ya fito.
A daran sukaje gurin canjin kudi zunzurutun kudad'en da bash yaje musu dashi su sanja aka basu irin na 'kasar..........Duniya sabuwa suka bud'e dama akwai 'yan garin guda biyu wanda suke da daurin gindi kasancewar iyayansu 'kososhi ne a cikin gidan gomanati. shiyasa duk ta'addacin da suke babu wanda ke musu magana, suyi shaye shaye su kama yaran mutane suyi musu fyad'e komai kankantar yarinyar mutukar tsautsayi ya ritsa da ita to basa saurara mata, dan akwai lokacin da suka shiga wata bording skull a garin, suka haikewa yaran mutane sai da sukayi raping din sama da mata talatin suka fito suka barsu cikin jini da wahala, abun mamaki gwamnati ba ta wani dauki mataki mai tsauri a kansu ba......Bash yayi masifar jin dadin had'uwa da guyz d'in nan suka bud'e shafin iskanci irin wanda suke so, sace sace shaye shaye fyad'e Luwad'i da duk wani mummunar aikin da Allah ya haramta yi sukeyi Bash tuni ya kafurta kansa ya zama kafuri tunda yaje garin bai kalli gabas da sunan zai gaishe da Ubangiji ba sharholiyarsa kawai yake babu abunda ya dameshi.
Munira kuwa tayi ciki da Muktar ya koreta daga gidansa yace tun wuri taje ta nemi uban danta kuma ya fasa auranta domin abinda yake bukata a gurinta ya samu saboda haka idan ta sake zuwar masa gida sai ya karya mata kafafu! Munira ganin bata da gata yasa ta hakura ta kyaleshi ammafa taci kuka ta koshi kuma tayi nadamar wautar data tafka, yanzu tana gidan kanwar mamanta mai suna Hajia Zulai bakar wahala take bata a cewar matar lokacin da ludayin su yake kan dawo basu taimaka mata da komai ba dan haka bata ga wanda zai dauko wahala ya dora mata ba, Munira hakuri kawai take a gidan Hajia Zulai ita taci mutuncinta 'Ya'yanta su wulakantata watarana da yunwa take kwana ga ciki a jikinta Munira ta gane duniya abar tsoro ce dan idan ta juya maka baya sai ka zama tamkar kashi a idanun mutane.
Alhaji Aminu da matarsa kuwa suna can a kulle dan har yanzu ba'a yanke hukunci ba an dai rufesu a kebantaccen guri, gwamnati tasa a cigaba da bukince inda Bash din ya fake dan tuntuni an yankewa sauran abokan nasa hukunci kisa bayan sun gama zaman gidan kaso na shekara goma......Tsanani tashin hankali Alhaji Aminu da Mommy suka shiga suka dinga kuka suna dana sanin abinda suka aikata na dora d'ansu a turba mara kyau, duk bayan sati biyu sai 'yan jarida abokanan aikinsa sunzo sun titsiye shi da tambayoyi kamar ma da gayya suke zuwa su turkeshi, takaicin hakan yasa ciwon hawan jini ya kamashi, yau da lafiya gobe babu.
****
To zamantakewar gidan Abbah Abbas sai dai muce alhamdullahi dan a tsakanin Halisa da Zainab an samu fahimtar juna duk ta dalilin jajurcewar jagoran nasu wato shi wanda ya ajiyesu a gidan, tuntuni Zainab ta daina rawar kai wanda ada take ta daidaita nutsuwarta yanzu ta kanta ma takeyi cikinta yayi wata hud'u! jikinta ya soma amsawa hankali ya fara shiga jikinta! gabad'aya sai tayi rauni ta kasa daukar lalurar mijin nata kamar wacce ta kusa haihuwa haka ta koma ciki wata hud'u, amma har ya fito kasancewar ta mai jiki da tumbi shiyasa cikin yayi saurin nuna kansa....Abbah nada tausayi sosai shiyasa baya takura mata da fitina lalla'bata yake da dukkanin abinda take so burinsa kawai ta sauka lafiya.
'Bangaran Halisa ta samu lafiya sosai dan a jikinta ma tana jin hakan ta daina jin kyaikyayi ta kuma daina zubar da ruwan da takeyi, sai ta fad'a masa cewar yana da kyau ta sake komawa asibiti su dubata domin su tabbatar mata da ingantuwar lafiyarta, da yake shima a cikin matsala yake sai ya dauketa da kansa ya kaita asibitin, Aikuwa kyakykyawan result ya fito Halisa kwayoyin cutar Gloria da take dauke dasu sun mutu yanzu mu'amula ta aure zata iya cigaba da gudana a tsakaninsu, amma dai duk da haka sai da Dr Sa'adatu ta rubuta musu wani magani wanda 'ka'ida ita dashi ne zasuyi amfani dashi.
Abbah Abbas yaji dad'in samun wannan kyakkyawan result d'in dan har sai da ya kasa 'boyewa ya nuna a fuskarsa kyautar kudi masu kauri yayi Dr din suka kama hanya suka tafi, Dr Sa'adatu ta dinga murmushi tana jin wani iri a jikinta hakika mutumin na burgeta mutuka tana adduar Allah ya bata miji mai irin halinsa.
Tun daga ranar Abbah da Halisa suka d'inke Halisa aka dawo amarya aka dinga gwangwajewa da ango ana biyan bukatar juna, sai dai bangaran mutumin naku daurewa kawai yake amma ba wani daidai yake ji ba dan ya tsani yaji ya shiga gurin yaji shi sakwaf-sakwaf! Halisa ta riga ta gama bud'ewa magungunan gurin 'yar Sa'adu sunyi mata mummunar illah! Haka dai yake hakuri yana biya wa kanshi bukata ba tare da ya nuna mata wani abuba, sai duk sanda takaici ya ishe shi kasa hakura yake a cikin kwananta zuwa yake gurin Zainab ya baje kolinsa yanda ranshi yake so sai bayan ya samu nutsuwa zai dawo yana da ya sani dan Zainab kwana takeyi tana kuka da fad'in cikinta ciwo yake hankalinsa ya tashi da kyar yake rarrashinta.
Salim abin duniya ya isheshi ya rasa makama kullum yana gida a kwance yana tunani gabadaya yanzu kunyar fitowa yake saboda irin kallon da Jama'ar gari ke masa! Ya kai sati biyu a gida baya fitowa sai da daddare nan ma baya dadewa zai dawo gida ya kwanta, mahaifinsa kuwa har ya koma bakin sana'arsa baya amsa gaisuwarsa fushi yake dashi sosai da sosai.........Ranar Lahadi ya shirya tsaf domin zuwa gidansu Salimat budurwasa wacce aka kai kudin aure da sa rana, ya fito da key din motarsa simi simi ya fita daga gidan kai tsaye motarsa ya shiga ya nufi gidansu Salimat..........
Salimat ta sameshi a cikin mota a zaune ta bude ta shiga ta zauna ta kalleshi tana ta'be bakinta tace"Wai dan Allah kwana biyu me yake damunka ne naga duk kabi ka susuce ka ma daina zuwa gurina kullum kuma idan na kira wayarka sai naji ka a cikin hali na damuwa wai ko ka daina sona ne."? Salim ya girgiza kansa yana kallonta yace"Ba haka bane salimat kwana biyu bana jin dadi wallahi shiyasa kika kasa gane kaina amma yanxu naji sauki sosai inaso ki fad'a min meye damuwarki."
Ta'be bakinta tayi tace"Kasan bani da wata damuwa sai ta kud'i yanzu ma inaso ka sanja min waya sannan na kwana biyu banyi ciye ciye ba inaso muje ka siya min kayan kwalliya da sauran abunda nake bukata."
Yace."Okey shikkenan kada ki damu." Motar ya kunna kai tsaye suka fita daga cikin unguwar.......Kafin su tafi shopping din sai da suka tsaya a P.O.S tana kallo Salim ya bada atm dinsa da accont number nasa, suka bashi abun yasa nambobin sirrin sa duk akan idonta kudin da yake bukata suka miqa masa ya kar'bi atm dinsa suka fita daga gurin....
Lokacin da suka shiga motar ya manta bai mayar da atm din cikin wallet dinsa ba ya fad'i kasan site a kan idonta sunayi parking a daidai gate din Jujin lambo ya bude motar ya fita ita kuma tana ganin fitarsa tayi saurin sunkuya ta lalubi atm din tasa a cikin pose din dake hannunta ta bude motar tabi bayansa cikin gurun......Siyayya yayi mata sosai da sosai suka fito da kaya a hannunsu, kafin ya kaita gida sai da ya siya mata kayan ciye ciye irin wanda take so sannan ya kaita gida, to yaso su danyi abun da suka saba kafin su rabu taki bashi damar hakan tace ita ta gaji gobe ya dawo da wuri zata bashi mamaki! yace shikkenan, sallama sukayi da juna yaja motar yayi gaba.........A ranar Salimat kasa bacci tayi saboda tunanin yanda za'ayi ta cire kudaden dake cikin account din Salim gashi ita ba account ne da ita ba, sai ta samu Yayanta Mai suna Naburago mugun dan son banza ne Naburago baya gudun Allah ya isa duk inda yaga bashi sai yaci bashi da sana'a sai buge buge da ita suke rufawa kansu asiri kasancewar su marayu ubansu ya mutu shine kuma namiji shiyasa wahala tayi yawa a kansa, talauci yasa Salimat lalacewa maza babu irin wanda bata sani ba shi kuwa Naburago rigima ko ta uwar uban waye saka kansa yake a ciki ayi ta fafatawa dashi a rabu dashi dan idan yaci bashi aka zo aka turkeshi ya biya sai ya mayar da abun wasa idan mutum ya kaishi gurin 'yan sanda kai tsaye yake fad'a musu bashi da kudin da zai biya bashi idan kuma ana kar'bar shekaru zai lissafa shekarunsa ya biya.....Su kansu 'Yan sandan sun sallamawa Naburago shegen kansa gashi da kwarjin tsiya komai takatsantsan di'nka a kan kayan sana'ar ka idan yazo kar'ba bashi mutum baya sanin sanda yake dauka ya bashi.......Salimat shi ta samu da maganar ta fada masa abunda ke faruwa, Naburago yayi tsalle da juyi a dakinsa yace."Bani atm din jeki kwanta ki huta kudi zasu koma account d'ina wahala ta yanke mana." Salimat ta fad'a masa numbobin sirrin na Salim din yace to magana ta kare.......Alwala yayi ya yay sallah ya fita da atm din cikin aljihunsa.
A ranar Naburago ya kwashe kudaden account din Salim tas ya mayar nasa accont din......Salim sai shigowar alert kawai yaji yana dubawa yaga a'lamarin daya afku babu abinda ya fara dubawa sai wallet d'insa ya nemi atm dinsa ya rasa a gigice ya nufi motarsa ya shiga dubawa sako da loko babu atm! cikin tsantsar tashin hankali ya shiga motar ya kunna a guje ya nufi P.O.S din da sukaje kawai ya fad'a musu guri kamar mahaukaci yana dube dube....Ai a take wani Police dake gurin ya damqe shi a cewarsa yaga yayi yanayi da masu laifi dan yanda yaga ya shigo gurin a kid'ime ya nuna masa hakan! aikuwa jama'ar dake gurin suka gazgata hakan dan ganin yanda Salim din ke muzurai yana wani irin gumi! sai rawar baki yake ya kasa magana.....Yana ji yana gani aka sashi a mota aka tafi dashi police stion kamar wanda aka daurewa baki ya kasa cewa komai zufa ce kawai ke tsatstsafowa daga jikinsa..........
_*Yau tafe nake da 'yar tsaraba ta 😊*_
*'Kawata matso kiji wata muhimiyar magana☺️ A kwai gurare masu daraja da muhimanci a jikinki....1 Headquarter naki...2 Hamtarki....3 qasan nonuwanki.....4 Tsakanin cibiyarki! Wad'annan guraran nada mutukar mahimanci a gurinki yana da kyau ki kula dasu ki mutunta su.....Na farko dai ke kanki kin san barin gashin hammata dana headquarter babbar matsala ce a gurinki waccan ka iya janyo miki imfaction gami da rashin jituwa da miji kullum ya kasance kin zama abar kyama a gurinsa, barin gashin hammata a gurinki sam! bai dace ba, ba dan komai ba sai dan ansan ita mace daban take da namiji kada kiga mijinki da gashin hammata kice kema ba zakiyi aski ba a kull!🧐 ke daban shi daban! ke ai abun kunya ne a gurinki ki d'aga hammatar ki a ga gashi! Wallahi duk ranar da kikayi kuskure kika bar mijinki yaga d'audar hammatarki kin cuci kanki🤷🏻♀️ sannan kika sake mijinki ya shaqi warin hammatarki kin zubar da qimarki🤦🏻♀️ duk da kasancewar yanzu muna lokacin sanyi kada kice ai yanxu sanyi ne ba'a wari kiqi yin aski wallahi duk turaran da zaki saka sai yaji warin jikinki saboda haka kiyi hattara.........Warin qasan nono na mussaman ne😅 ba ko wace macece ke kula da da wanke qasan nononta ba, to bari kiji mutukar kika ga mijinki a lokacin da kuke sex yana kauda kansa daga gurin nono ki to wallahi wannan warin yake damunsa, ina amfani ace kinyi wanka baki d'aga nonuwanki kin wanke ba🤔 ai kamar ba kiyi wanka ba k'awata! Kisa sabulu ki wanke kasan nono tas kisa masa turare na mussaman sai kiga maigida na zumud'in kai kansa gurin........Ramin cibiya yana tara daud'a saboda gurin a tsuke yake baida spece sosai, yana da kyau kullum idan kinzo wanka kina sa bakin soso a hankali a hankali kina wankewa kada ki bar ramin cibiyarki da daud'a domin hakan na iya janyo miki matsala mai girma...........Wannan tsarabar tawa ba ta mantan aure bace kawai har daku 'Yan mata da zawarawa 'yan kwalisa 😻......To sai mun sake had'uwa daku a fita ta biyu🙋🏻♀️*
Vip gruop #600 normal group #300 account numbar....0542382124...Binta umar gtbank.....Wahasap number.... 07084653262
*BINTA UMAR ABBALE*
68******Salim har yamma yana police station a gar'kame hankalinsa yayi masifar tashi ganin duhun magariba ya gabato sai kawai ya fara zubar da hawayen nadama! babu shakka wannan al'amari daya faru dashi hakkin Kawunsa daya zalinta ne, yasa hannu ya dauko hankici a cikin aljihunsa ya goge idanunsa tare da sake ri'ke 'karfen da yayi masa katanga da ma'aikan gurin, zare ido kawai yake yana fad'in "Oga dan girman Allah ka saurari maganata wallahi ni ba 'barawo bane inaso kazo kaji uzirina ni abun a tausayawa ne qaddara da tsautsayi ne suka afka min."
'Daya daga cikinsu ya doki! tebur din dake gabansa yace."Rufe mana baki munafiki kai har kasan qaddara irinku ai ba imani ne daku ba kazo sata sai Allah ya tona maka asiri dama irinku muke nema duk muyi maganinku yanzu D.P.O muke jira yazo mu zartar da hukuncin da zamuyi maka."
Salim ya sake rikicewa cikin tsantsar tashin hankali yace."Wallahi wallahi bana daya daga cikin wa'yan nan mutanan da kuke magana a kansu, ku taimakeni kamar yanda Allah ya taimake ku wallahi ban shiga gurin nan da sunan sata ba Atm dina naje nema a gurin kasancewar kwanaki uku da suka wuce naje na cire kudi a gurun.........Tiryan tiryan ya fad'a musu abinda ya faru, yace"Idan kuna so ku tabbatar da maganata to ku duba waya ta zaku ga text din da banki suka turo min cewar gabadaya kudin dake account d'ina babu."
Da sauri wanda wayar ke hannunsa ya shiga dubawa, aikuwa da text din yaci karo cike da mamaki ya shiga nunawa 'yan uwansa sai duk jikinsu yayi sanyi, wanda key din cell din ke hannunsa ya miqe da sauri yaje ya bude shi yace."Kayi hakuri kaji ko Allah ya mayar maka da alkairi."
Cikin tsananin damuwa da tashin hankali ya kar'bi wayarsa da key din motarsa ya kama hanya ya futa daga gurin, sai suka bishi da kallon tausayi kud'i kimanin miliyan daya da rabi an kwashe masa ai dole su jajanta al'amarin........Salim na fita daga station din kai tsaye gidansu Salimat ya nufa, yayi parking a kofar gidan cikin damuwa ya kira wayarta......Salimat ta fito cikin shiga ta alfarma kamar yanda ta saba ta bude mota ta shiga, ganinsa a burkice yasa tasha jinin jikinta, ya kalleta dan jan ido yace."Salimat 'barayi sun kwashe min kudin accont dina yanxu bani da ko kwabo Atm dina ya fad'i a lokacin dana kaiki shopping ban ankara ba sai da naga bank sunyi min alert sannan na duba naga abunda ke faruwa...Hakika ina cikin tashin hankali mai tsanani."
Cikin alhini tace"Innalilihi wa'ina ilahi raji'un Salim yanzu ya zamuyi da wannan qaddara sai kawai ta fashe da kukan munafurci......Naburago ne ya fito daga gidan, yasha shaddarsa harda hula kamar mutumin kirki kai tsaye motar ya durfafa. Dama sun riga sun gama shirya plan dinsu tun a gida. hannu yasa ya kwankwansa gilashin motar. Da sauri Salim ya sauke gilas din ganin Naburago a tsaye yasa da sauri ya miqa masa hannu suka gaisa Naburago ya gyara tsayuwarsa yana kallon Salim din yace."A matsayina na wakilin wannan yarinya Salimat na yanke shawara kancewar mun fasa baka auranta dan sabida munyi kyakkyawan bunkice a kanka mungane kai d'in azzalimi ne macuci maha'inci mun samu labari daga bakunan mutane da yawa kancewa kaine ka kunnawa ubangidanka wuta a cikin dukiyarsa wannan dalilin yasa muka yanke shawarar dawo maka da kudin auranka." Yana gama maganarsa ya kalli Salimat din cikin tsawa! yace."Maza ki fito daga motar nan ki shiga gida babu ke babu wannan macucin."
Salimat ta bude mota da sauri ta nufi gida tana kuka kamar gaske, Naburago yasa hannu aljihu ya dauko kudin Salim dubu Hamsin yasa masa a jikinsa yace "Ga kudinka nan babu mu babu kai kada ka kuskura na sake ganin kafarka a kofar gidan nan." Yana gama maganarsa ya bar gurin.
Salim jikinsa ji'kewa yayi da gumi! tsabar tashin hankali makogwaronsa bushewa yayi qamas ya rasa ma wane irin tunani zaiyi sai kawai ya kifa kansa akan sitiyarin mota yana zubar da hawayen nadama.
****
*'Yar Sa'adu* ta jangwalowa kanta masifa, matar wani babban soja za'ayi mata kishiya sai ta samu labarin *'Yar Sa'adu* da magungunanta sai kawai ta wanko kafarta ta ciko jakarta da kud'i taje 'Yar Sa'adu ta had'ata da magungunan mata iri iri.........Matar ta tafi gida ta dinga shan magani babu qa'ida ta dinga cusa maganin matsi wai ita lallai sai gabanta ya matse dan saboda kada amarya ta fita a gurin miji...
Aikuwa matsalar data afku da Halisa irinta ce ta afku da ita, Soja mazan fama ya bud'e mata wuta danshi har da duka ma ya had'a mata dashi yace sai tayi masa bayanin yanda akayi al'amuranta suka kasance a haka! Ganin rufa rufar da take bashi da amfani sai kawai ta fad'a masa yanda al'amarin ya kasance, takaici yasa shi yayi mata dukan tsiya da blet kuma ya daina kulata, ashe duk hukuncin da yayi mata bai hakura ba mota ya cika da sojoji ya sata a gaba suka nufi gidan *'Yar sa'adu me kayan mata*.....'Yar sa'adu na tare da baki kawai sukaji ihun yara ga unguwar ta cika da kururuwar motar sojoji ai babu shiri ita da matan da take a gidan suka fito waje, ganin zaratan sojoji sun durfafo kofar gidanta yasa ta kusa sakin fitsari a wando! a tsaroce tayi nufin komawa cikin gidan gabanta na wani irin faduwa ganin matar sojan data zo ta hada mata magani makwanni biyu da suka wuce babu shakka akwai abunda ke faruwa, takalmin kafarta ne ya gurde ta tsaya zata gyara matar soja da sojojin dake bayanta suka karaso gurin ba tare da jin tsoron komai ba matar ta nuna 'Yar Sa'adu da fad'in "Gata nan itace matar da siyar da magunguna kan kudi masu yawa."
'Yar sa'adu ta diririce ta hau inda inda, Sojan dake kusa da ita ya taska mata mari da fad'in "Kece kike cutar mata ko kin zama 'yar damfara ki tara mata ki dinga kar'be musu kudi kina siyar musu da abunda zai cutar dasu ko to yau sai kin gane kuranki." doguwar bundigar dake hannunsa ya dora mata a wuya a tsawace! yace."Wuce muje yau kin fad'a komar mu sai kin gane baki da wayo." Yar Sa'adu kuka ne ya kufce mata jikinta ya shiga kyarma! sai ta shiga d'aga hannunta sama tana basu hakuri....Kafin kice kwabo gurin ya cika da jama'a, su kuwa matan da suke tare da ita ganin an shigar da ita mota yasa da sauri kowacce ta fece! tsoro da tashin hankali duk ya cika musu zuciya.
****
Watannin Naja'atu biyu da dawowa gida inda ya kama wattanin cikinta shida kenan yanzu cikin nata ya fito ana d'an ganinsa amma ba sosai ba kasancewarta doguwa yasa cikin bai bayyana kansa ba sai dai amma ita kadai ta san abinda take ji a jikinta, kusan kullum sai ta 'buya a daki taci kukanta ta koshi haka kawai Bash ya had'ata da wahala ya gudu ya bar mutane da jigilar d'ansa duk sanda ta tuno wannan al'amari takan kwana ta yini cikin kunci da damuwa, mussaman idan taga yanda Abbah Abbas ke hidima da ita da cikin jikinta duk sai hankalinta ya tashi ta shiga nadamar abinda tayi masa a baya, itace ta zama sanadiya gurin lalacewarsa cikinsa gashi ita taje ta dauko ciki ta kawo masa wahala, yanzu saboda ita kullum da safe kafin ya tafi harkokinsa sai yazo ya kofar na'isan sannan bayan ya dawo daga kasuwa ya sake dawowa gabad'aya jama'ar gidan sun fahimci saboda ita yake wannan sintirin dukkaninsu su gane ya damu da yarinyar da cikin jikinta, sai hankalinsu ya kwanta mussaman hajia da Alhaji burinsu kawai yarinyar ta haihu lafiya sai ai maganar kome domin su a ganinsu yanda yake nuna damuwarsa a kan yarinyar suna ganin kamar yana so ya mayar da ita gidansa ne. wanda shi kuma kwata kwata ba haka bane a cikin zuciyarsa haka kawai take bashi tausayi da ita da abinda ke cikinta shiyasa ya mayar da hankalinsa a kanta duk da bashi ne keda alhakin kula da itaba , a yanzu dai cikin zuciyarsa bai dauki Naja'atu a matsayin komai ba face 'Yarsa.
Yau asabar yana zuwa da wuri dalili kenan daya sa takasa komawa baccinta na safe ta fito palo ta zauna tana jiran zuwan nasa, lokacin daya shigo hajia na sama ita kadai ya samu a zaune tana kallon tashar sunna tv Malam Aminu Daurawa na gabatar da shirin tambaya mabudin ilimi, a nutse ta amsa masa sallamarsa ta dan gyara zamanta a hankali tana gaishe shi....Ganin yanda take ya mutsa fuska ne yasa ya mayar da hankalinsa kanta a nutse yace."Ina fatan kina lafiya ya jikinki."?
Kamar za tayi kuka tace"Da sauki inasu Mussadiq." Yace."Suna gida lafiya lau ina hajia."? Tana sama." Tafada tana kallon kasan kafafunsa, kai tsaye saman ya nufa sai ta bishi da kallo tana girgiza kanta ita kam a duniya akwai mutumin dake sonta irinsa kuwa? gaskiya babu.
Ya kai mintina goma sha biyar a saman ya sakko da sauri yana duba agogon hannunsa, dan kallon gefan da take zaune yayi ba tare da yace wani abu ba ya kama hanyar fita.....Da kyar ta kira sunanshi, tsayawa yayi yana kallonta....Murya na rawa tace."Ina so mu gaisa dasu Mmn Sajida matar nan data taimaka min."
Jim! yayi kafin yace."Yanzu dai sauri nakeyi ana jirana idan nazo da yamma sai ayi yanda kikace." tace."To Abbah Allah ya bada sa'a."Ya amsa yana kokarin futa daga falon.
Sai bayan futarsa ne ta shiga tunanin yanda za'ayi ma tayi magana dasu Mmn Sajidan tunda lokacin data barsu daga ita har Mmn Ladin babu me waya a cikinsu , wannan dalilin ya sanya jikinta yay sanyi taso da hanyar da zata sadata dasu da sun gaisa da juna ta 'kara yi musu godiyar abinda sukayi mata.
To koda ya dawo gidan da Yamma batai masa maganar ba shima al'amuran dake gabansa sun mantar dashi, sai kawai ya ajiye mata abubuwan da ya saba siyo mata ako wace rana yay tafiyarsa gurun iyalinsa.
Bayan kwanaki biyu da faruwar hakan.....Yana tsaka da shiryawa domin tafiya kasuwa kira ya shigo wayarsa, Zainab yasa ta miqa masa wayar ya daga tare da karawa a kunnansa.......Mmn Sajida dake d'aya bangaran ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah da sauri tace"Sannu ina kwana sunana Mmn Sajida daga jos." Sai yayi saurin duba number yana so ya tabbatar, ya mayar da wayar kunnansa yace." Lafiya kalau Mmn Sajida na gane ina fatan kuna lafiya."? Ta amsa da lafiya lau Alhaji muna fatan kunje gida lafiya." Yace."Lafiya lau alhmdullhi." Tace."Dama na kira ne idan da dama inaso a bani Naja'atu mu gaisa wallahi har yanzu alhinin rabuwa da ita bai sakemu ba." Yace."Ayya! kada ki damu insha Allahu anjima kad'an idan naje Inda take zan bata wayar ku gaisa." Tace."To Alhaji mungode sai anjima." Yace."To masha Allah." Kashe wayar yayi ya ajiye kan drowar dake gefansa, Zainab tunda taji ya ambaci sunan Naja'atu ta sanja fuska dan har sai da ya fahimci sauyawarta alhalin labari take bashi amma lokaci guda yaga ta 'bata rai! kwanciya ma tayi ta juya bayanta kishin Naja'atu naso ya dargagaza mata zuciya. Sai da ya gama shiryawa tsaf ya juyo yana kallonta a nutse yace."Zainab lafiya dai ko.? ba tare data jiyo ba tace."Lafiya lau bacci zanyi shiyasa na kwanta." Yace."Okey ni zan fita." Tace"A dawo lafiya." ya amsa a nutse ya bude kofar dakin ya fita, mikewa zaune tayi tana jan tsaki! kai gaskiya ta gaji da wasiwahsi gami da takurawa zuciyarta dole yau idan ya dawo ta tambayeshi tsakaninsa da Naja'atun nan da ya damu da ita idan mayar da ita zaiyi gwara ya fad'a musu su ya daina wani 'boye-'boye...........
*Littafin na kudi ne.....!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar karanta littafin ga yanda abin yake.....Vip group #600 normal group #300 account.... 0542382124...Binta umar gtbank...Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
69*******Lokacin daya isa gidan Alhajin Naja'atu na daki tana baccinta na qa'ida dama idan tayi sallar asubahi komawa take ta kwanta tayi ta bacci watarana hajia da kanta take shiga dakin ta tashe ta sannan fa tayi break fast.... tunda cikinta yayi kwari take wannan bacci mara qa'ida daddare ma tana idar da sallar isha'i take kwanciya, hajia da taga abun yayi yawa cewa tayi aje asibiti a dubata, Yaya Ramlatu tace" Lafiyarta lau kawai yanayin cikin nata ne yazo a haka dama ana samun ciki mai sanya baccin tsiya ta ce ta kwantar da hankalinta bacci lafiya ne. bana cuta ba to wannan maganar da Yaya Ramlatu tayi itace tasa hajian ta kwantar da hankalinta amma dai duk rintsi da daddare bata barinta ta kwanta sai ta tabbatar ds taci abinci ta koshi tukkuna.
Koda ya shigo gidan bai samu kowa ba, wai ashe sun tafi jana'izar 'yar 'kanin Hajia Rabi dake mandawari, da yake mutuwar ta dare ce shiyasa bashi da labari sai daya ya shigo gidan tukkuna maigadi ke fad'a masa.......... Juyawa yayi da niyyar fita daga gidan sai kuma yayi wani nazari, yana tunanin ko zasuje gidan mutuwar bai zama lallai suje da ita ba shima yasan a daidai lokacin take baccin data saba, dan wani lokacin idan yazo baya samun ganinta sai dai kawai ya tambayi hajia lafiyarta.
Shuru falon lokacin daya shiga, bai jira komai ba ya nufi dakin da take..........Kallon sharia yayi mata yayi saurin kauda kansa, yanayin kwanciyar da tayi taso ta saka shi cikin wani yanayi yayi saurin kawar da abun daga cikin ranshi...Ya karasa bakin gado tare da tsayawa saitin kafafunta yana kallon fuskarta dake kallon rufin dakin, da yake irin kwanciyar da ba'a masu ciki suyi ita tayi (rigingine) ta tayar da kafafunta sun taka gadon kana ta d'ora dukkanin hannayenta a saman cikin nata......Sunanta ya shiga kira yana korar shad'en d'in da yake ra'barshi....idan da baiyi wa Mmn Sajida al'kawari ba da yana ganin tafiyarsa zaiyi dan tsayuwarsa a dakin na nema ta haifar masa da matsala.
Kamar a mafarki taji muryarsa na kiran sunanta! ta bud'e idonta da sauri! shi take gani dishi dishi a idonta, shi kuwa yanayin yanda yaga idanunta sun sauya yasa ya dauke kansa yana kallon gefe guda, yace."Tashi ku gaisa da Uwar dakin ki ta jos dazu ta kira waya tana so ta dubaki."
Da sauri ta miqe zaune jin cewar Mmn Sajida ta kira waya...Wannan gaggawar miqewar da tayi yasa yaron dake cikinta ya kai mata wani irin naushi! yayi fushi! ya samu guri guda ya dunkule mata! Rintse! idonta tayi murya na rawa tace"Wayyo cikina."! Kafin kice me zufa ta tsatstsafo mata a saman goshi!
Rikicewa yayi yay saurin ajiye wayar a kan drowar dake gefan gadon, be san sanda ya zauna kusa da ita ba yana kokarin kamo hannunta......."Wayyo Allah cikina ya 'kulle a guri d'aya."Abinda take fad'a kenan tana janyo zanin gadon da hannayenta......Kamota yayi yasa a jikinsa yana shafa bayanta a hankali a hankali duk ya rasa nutsuwarsa ita kuwa sai kokarin cire jikinta take tana kiran cikinta! Yace."Me yasa kikayi irin wannan kwanciyar bayan kin san masu ciki ba'aso suyi sannan me yasa kike gaggawa a cikin al'amuranki kin jima a kwance rigingine gashi kin tashi cikin gaggawa dole shima yayi fushi! ya zauna miki a guri guda, sannu ki dinga kula kinji ko."
Wannan maganganun yake mata yana dan shafa bayanta a hankali a hankali! Shuru tayi a jikinsa, tana jin yanda yaron ke motsi inda ya d'aure yana saki a hankali a hankali cikin nata ya koma daidai ta daina jin ciwo.....A sanyaye ta cire jikinta a nasa ta sunkuyar da kanta tare da kokarin gyara botiran rigarta....Daidaita nutsuwarsa yayi ya dauki wayar daya ajiye yana kallonta yace."Ina fatan cikin ya daina ciwo." Kanta ta d'aga tana jin nauyin abinda ya faru...Yace."To sai ki kiyaye gaggawa kuma ki daina irin wannan kwanciyar cikinki yayi kwari yanzu kiyi hakuri kina kwanciyar da yaronki zaiji dadi kema ki inganta lafiyarki."
A hankali tace"Wallahi bana sanin sanda nakeyi nafi jin dadin irin kwanciyar." Dan murmushi yayi yace."Baki damu da lafiyarki ba shiyasa kike biyewa son zuciyarki kisa a ranki kin daina irin kwanciyar sai kiga kin zauna lafiya." Tace"To shikkenan insha Allah."
Dakin ne yayi shuru Abbah na traying din number Mmn Sajida tana fara ringing ta dauka yay saurin miqa mata, gani yay ta fad'ad'a fuskarta da fara'a tana dariyar farin ciki tace."Mmn Sajida ina kwana ina Mmn Ladi."? Mmn Sajida cikin da walwala da farin ciki ta amsa da fad'in "Ga Mmn Ladi a kusa dani muna tare Naja'atu ya kuke je gida? Ya kuma jikinki muna fatan duk komai lafiya." Tace"Wallahi alhmdullhi Mmn Sajida gaskiya naji dadin jin muryarki ina nan ina kewarki ki bani Mmn Ladi mu gaisa insha Allahu idan na haihu zanzo nayi muku kwanaki."
Mmn Sajida tace."Muma muna nan duk kewarki ta ishemu dan Walid ma sai da yayi zazzabi Sajida kuwa kullum sai ta kira sunanki tayi kuka." Najaatu murya na rawa tace"Ayya Allah sarki Walid dan Allah kice ina gaishi da kyau Sajida kuma kice mata idan zanzo zan zo mata da kayan wasa irin wanda take so.
Mmn Sajida tace"To insha Allah zan fad'a mata ga Mmn Ladi ku gaisa." Mmn Ladi na washe bakinta ta kar'bi wayar da fad'in "Naja'atu 'yar albarka mai gyara sinnar ma'aiki ai ni kam babu abinda zance miki daba dan keba da tuni na dade da rabuwa da Saleh wallahi yanzu zaman lafiya muke da juna yanzu ina hakuri da duk abinda ya bani kuma na daina yi masa rashin kunya yanzu Saleh daidai gwargwado yana kyautata min muna zaune lafiya da 'ya'yanmu.
Naja'atu tace" Amma gaskiya naji dadin wannan labarin naki Mmn Ladi Allah ya qara muku zaman lafiya sannan kuma inaso in tuna miki cewar kada ki manta da al'kawarinmu insha Allah idan nazo garin zan tallafa miki ki fara sana'a kema."
Mmn Ladi tace"To nagode kwarai da gaske Naja'atu Allah ya saka da alkairi Allah kuma ya sauke ki lafiya." Ta amsa da amin tana jin wani irin farin ciki a cikin ranta.
Abbah na zaune yana kallonta sai dariya take Mmn Sajida ce take bata labarin halin da Dantalle ya shiga bayan tafiyarta harda kuka ya dinga yi.....Naja'atu ta dinga kyalkyala dariya tana fad'in "Lallai Dantalle to ki bashi hakuri yaje ya rungumi matanshi ya kyautata musu shine abinda ya dace yayi".........Kallon agogon hannunsa yayi yaga lokaci yaja a qallah sun dauki minti ashirin suna wayar gyaran mirya yayi tayi saurin kallonsa, hannunsa ya miqa alamun ta bashi wayar....Da sauri tace" Mmn Sajida nagode da karamci Abbah zai kar'bi wayarsa insha Allahu idan na haihu lafiya zaku ga nazo muku." Mmn Sajida tace"To Naja'atu Ubangiji Allah ya raba lafiya sai anjima." Sallama sukayi cike da farin ciki da kewar juna.
Tana miqa masa wayar tace"Abbah don Allah kayi serving number ta Mmn Sajida ce." Wayar yake dubawa a tsanake ba tare da ya dubeta ba yace."Waye Dantalle."? Sai tayi saurin kallonsa....Hankalinsa nakan wayar yana kokarin serving din number Ya sake maimaita tambayarsa......A sanyaye tace"Wani mutumi ne a garin tun zuwa na na farko yake naci wai sona yake."
Miqewa yayi tare da mai da wayarsa aljihu Yace."Okey na fahimta to Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninku Wannan number kuma nayi serving insha Allah gobe ko jibi zan kawo miki waya sai ku dinga gaisawa idan kin haihu sai ki fad'a musu dan na fahimci matar tana kaunarki sosai."
Maganar Allah ya tabbatar musu da alkairi da Dantalle itace duk ta ragargaza mata duk wani farin ciki da annushuwar da take ciki! sai ta shiga tunani gami da nazarin inda maganar tasa ta dosa! Me yake nufi ne?? Bayansa tabi da kallo har ya fice daga dakin bata samu damar yin wata magaba ba
Jiki a masifar sanyaye ta koma ta kwanta ai sai hawaye suka 'balle mata suka dinga fita tamkar wanda aka kwance famfo yanzu idan yace ba zai mayar da ita ba to wa zata aura? waye zai riqe mata d'anta? Waye zai tallafa mata kamar yanda yake mata, gaskiya idan yaqi mayar da ita gidansa ya cuceta dan ta riga ta gama sa rai ganin irin wahalar da yake mata shiyasa ta sakankance da cewar yana jira ne ta haihu ya bijiro da maganar da kowa yake tunaninta a kansa
Shi kuwa yana fita motarsa ya shiga a gurguje ya nufi gidan mutuwar domin yayi gaisuwa ya wuce harkokinsa, gabad'aya bai sanya lamarin Naja'atu a cikin ransa ba ballantana ya dameshi yana fitowa daga inda take ya ajiyeta a gefe guda ba zaije ko'ina da damuwarta ba bare ta hanashi gudanar da abubuwan da suke gabansa.
Koda su hajia suka dawo kasa gane kanta sukayi, hajia ta dinga tambayarta ko wani abu na damunta, girgiza kanta kawai takeyi tace"Babu komai baccin data yini tanayi ne ya sanya yanayin ta ya sanja to hajia dai taji ne amma bata amince da maganar ba, haka yamma tanayi data fahimci ya kusa shigowa gidan sai kawai ta shige daki ta kwanta bata so ta ganshi saboda gudun abunda ka iya zuwa ya dawo tana ganin zata iya fashewa da kuka mutukar zata kalli fuskarsa.
To shima a nasa 'bangaran bai damu da rashin ganinta a falon ba bayan sun gaisa da mahaifiyarsa sai kawai ya ajiye ledojin hannunsa wanda ita tasan ko na menene kayan ciye ciyen Naja'atu ne wanda yake siyo mata kullum ta Alla.....Sallama yayi mata yace."Idan ya fito daga massalaci gida zai wuce ba zai dawo ba. Hajia tayi masa fatan alkairi tare da bashi saqon gaisuwarta gurin su Saddiqa, ba tare da damuwar komai ba ya bar gidan.
Koda ya isa gidan nasa kai tsaye gurin Halisa ya nufa duk da cewar ba itake keda girki ba, sai da ya duba ta sosai sannan ya fito ya nufi gurin Zainab....Ita da yaran suna zaune a falo gwanin sha'awa sukayi masa sannu da zuwa ya amsa a sake, yana kallon Zainab yau tayi kwaliya sosai sai dai babu walwala a tare da ita, bece mata komai ba ya nufi dakinsa, ta mike tabi bayansa tana wani cika da batsewa.
Ya tu'be kayan jikinsa yana kokarin shiga wanka ta shigo dakin sai ya tsaya yana kallonta har ta qaraso ta samu guri ta zauna tare da fadin." Abban Mufida sannu da zuwa." Ya amsa yana sake nazarinta yace."Da alama yau akwai abunda ke damunki na karanci rashin walwala a fuskarki ina fatan ba yaro na bane yake takura miki."
Girgixa kanta tayi tana dan ta'be bakinta tace"Idan shine yake takura min ai da sauqi Abban mufida zuciyata ta kasa nutsuwa kwana biyu sai tunani nake da wasiwahsi dan Allah kada ka dauki maganata da wata manufa naga kamar kana so ka dawo da Naja'atu gidanka saboda dawainiyar da kake mata har taso tayi yawa wani abun ma sai dai mu samu labari, nida aunty Halisa kullum cikin tunani muke idan dawo da ita za kayi gwara kawai ka fad'a mana mu sani dan ina ganin kamar 'boye-'boyen da kake mana sam bashi da wani amfani.''
Tunda ta soma maganar ya zuba mata ido yana kallonta mamaki yana kasheshi! shi dai tunda Allah ya had'ashi aure da qananun yara yake ganin rashin kunya iri iri....Wai Zainab ce ta turkeshi take kokarin sai ta 'kure shi a ganinta yana 'boye musu abinda ke tsakaninsa da Naja'atu, idan tunaninsu kenan to babu shakka zai basu mamaki! Dauke kansa yayi daga kanta ba ta tare da yace mata komai ba ya nufo toilet cikin d'umbun mamakin yarinyar.
*NA DAWO🙋🏻♀️*
*'Kawata matso kiji wata magana mai muhimanci👌🏻 nasan kin san da cewar yanxu muna lokaci na sanyi jiki na bushewa kammani na sauyawa🤦🏻♀️ to bari kiji wata magana maza a irin wannan lokacin jaraba da fitinarsu take tashi, me ya kamata kiyi domin ganin kin gyara kanki da kowane lokaci mijinki na samun nutsuwa dake😊 Kada ki mayar da hankalinki kacokan kan gyaran fatar jikinki baki inganta ni'imarki ba🥳 Ina amfanin fatar ki tayi luwai luwai kina gayu da tunkawo kuma sai dare yayi maigida yaji guri a bushe🤦🏻♀️ kada ki sake haka ta faru 'Kawata! kamar yanda zaki kula da fatar jikinki to ki kula da Ni'imar ki ya kasance kullum idan maigida yazo yaji zam!zam😻 kada kiyi wasa da shan ruwan kaninfari had'e da shan kayan marmari ina ganin koga wannan kika tsaya zaki gamsar da maigidanki........Wannan itace tsarabar da nake tafe da ita🙋🏻♀️*
Vip gruop#600 normal group #300 account.. 0542382124.//Binta umar gtbank .....WhatsApp number.... 07084653262
*MADADI*
70Zainab na zaune tana sa'kawa da kwancewa ya fito daga toilet yanda taga fuskarsa a had'e! shine yasa jikinta mutuwa gabanta ya dinga fad'uwa, tana kallonsa har ya kimtsa jikinsa ya kama hanya ya fice daga dakin ba tare da ya tanka mata ba...Jikinta a mace ta miqe salo salo tabi bayansa falon gurin cin abinci ta sameshi a zaune yana duba karamar wayarsa Saddiqa na kokarin zuba masa abinci.
Da sauri ta karasa gurin, cikin kokarin wanke kanta ta kar'bi plate din dake hannun Saddiqar tace taje ta zauna.
Abbah duba wayarsa kawai yake yi bai kalleta ba har ta gama zuba masa abinci ta ajiye masa a gabansa, ya ajiye wayar a nutse ya dan yanyo plate din gabansa yayi bisimillah kamar koda yaushe ya fara cikin abincin.
Ta kalleshi a sanyaye tace"Abban Mussadiq naga kamar maganata ta 'bata maka rai dan Allah kayi hakuri wallahi ni haka nake bana iya ajiye abu a raina."
Yayi mata wani kallo mai kama da harara yace."Surutu da fad'i ba'a tambaye ki ba shine yake damunki ba abinda kika fad'a ba, Okey zan kira Halisa yanzu itama naji ta bakinta akan maganar da kika fad'a min tunda kun dauke ni munafiki wanda ke 'boye muku tsakaninsa da Naja'atu."
Da sauri tace"Wallahi ba haka nake nufi ba shiyasa fa tun farko kafin na fad'i maganar nan sai da nace ka fahimceni amma meye sai an kira anty Halisa dan Allah kada ka kirata."
Yace."Ai a inda ba qasa nan ake gaddamar kokawa tunda kince keda ita kuna cikin wasiwahsi kullum kuna tunani da zargina kan na 'boye muku wani abu to dole itama tazo ta fad'a min da bakinta kamar yanda kika fad'i naki."
Zainab idonta ya ciko da kwalla! Tunda suke basu ta'ba zancan Naja'atu da Halisa ba, tunda ta ta'ba yi mata maganar a gidan Alhaji Halisan ta nuna bata son maganar bata qara tunkararta ba ita kadai abun ke damu kawai ta sako sunan Halisa a cikin maganarta ne wai ko zai dauki abun da muhimanci ya fad'a musu abunda ke zuciyarsa.
Yana kammala cin abincinsa ya barta a gurin yaje ya zauna kan kujera yana kiran wayar Halisa.....Zainab kasa motsawa tayi tana zaune a inda take har Halisa ta shigo falon.....Umartar su Saddiqa yayi dasu je su kwanta, yaran suka miqa da sauri suka nufi dakinsu.
Halisa ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa itama tunda taga yanda yasha kunu sai tasha jinin jikinta, barka da dare tayi masa taja bakinta tayi shuru.
Ba tare daya juya ba yace."Zainab zo nan." Ta miqe a hankali taje ta zauna nadama da dana sani kawai takeyi data san tozartata zaiyi a gaban kishiya da ta daure ba tayi masa maganar ba.....Ya kalli Halisa a kaurare yace."Ashe idan bana nan munafurcina kukeyi? Har kuna zargina akan ina 'boye muku tsakanina da Naja'atu shin idan nace zan dawo da ita akwai wacce ta isa ta hanani dawo da ita a cikinku."!
Halisa ta bud'e bakinta cike da mamaki da tsoro tace"Yaushe akayi hakan Abbah Mufida wallahi duk wanda ya fad'a maka maganar nan karya yake ni meye nawa a ciki idan ka dawo da Naja'atu gidanka gaskiya ka 'kara yin bunkice a kan maganar nan.."
A tsanake ya kalleta ya kalli Zainab da tayi tsuru tsuru nan ya tabbatar da cewar 'karya yarinyar tayiwa Halisan, yace."Ba wani ne ya fad'a min ba Zainab ce gata nan tana jinki abunda yasa kuma na yarda da maganarta saboda ina ganin zaki iya aikata hakan tunda kema ba qaunar Naja'atun kike ba."
Halisa tace."To ikon Allah idan da ranka kasha kallo ina zaune anyi min sharri yanzu ke dan Allah dan annabi Zainab yaushe mukayi wannan maganar dake ashe kin manta maganar da mukayi dake a gidan alhaji, haka kawai zakiyi maganarki sai kisa sunana."!
Ganin yanda Halisan ta hasala! ne yasa ya daga mata hannu yace."Ya isa! kina nufin ba kiyi ba kenan."? A fusace! tace"Wai dan Allah wace irin magana kakeyi? da da yanzu ba d'aya bane kai kanka ka san yanzu na gyara kuskurena sannan naji kana wata magana wai bana qaunar Naja'atu shiyasa zan zauna da Zainab mu zageta! a kan wane dalili ni Naja'atu da iyayenta basuyi min komai ba wallahi saboda haka ko yau ka dawo da ita gidanka ina maraba da ita."
Tana gama maganarta ta miqe rai a 'bace! ta fita daga falon........Maganganun da Halisa tayi ya nuna masa gaskiyar abinda ke cikin zuciyarta, kuma yaji dadin hakan Halisa ta daina adawa da Naja'atu ta barwa Zainab, a nutse ya juya yana kallonta tayi tsilli tsilli kunya da nauyi duk sun rufeta sai yanzu ta gane itama wauta da kuruciya na damunta to idan ba haka yaushe ma zata turkeshi da irin wannan maganar.
"Zainab." Ya kira sunanta tare da tsira mata idonsa, ta amsa murya na rawa. Yace." Saboda ina yiwa Naja'atu hidima kike ganin kamar zan dawo da ita gidana." Fashewa tayi da kuka tace"Aa wallahi." Yace."Hakane mana! kina kishi da Naja'atu alhalin zama bai ta'ba had'aki da ita ba, to ki kwantar da hankalinki kinji ko dik wata hidima da kika ga inayi mata inayi ne dan Allah da manzonsa da kuma tausayawa abinda ke cikinta, amma babu maganar na sake zaman aure da ita! saboda haka ki samu nutsuwa ki daina wasiwahsi kamar yanda kika fad'a! Sai dai da kowane lokaci zan iya kawo muku abokiyar zama dalili ni mutum ne meso ya cikasa sinnar ma'aiki Annabi Muhammad (slw) inaso kafin Allah ya dauki raina na had'a mata hudu a gidana su haifa min tarin yara masu albarka saboda haka kisa a ranki cewar akwai sauran abokanan zamanki da zasu zo mutukar Allah ya qaddara min hakan."
Zainab shuru tayi tana goge hawaye itakam wauta da rashin dubara na damunta amma daga yau tayi alqawari zata dinga kiyaye harshenta domin gudun abunda ka iya zuwa ya dawo, dan gaskiya itama ba laifinta bane kishin naja"atu ne ya tunxura mata zuciyarta amma dai za tayi kokarin ganin ta dauke kanta akan dukkanin abinda zata gani ko taji labarin yayiwa Naja'atun..
To kamar yanda yayi mata alkawarin zai siya mata waya hakan ya faru dan Abbah Abbas waya mai kyau da tsada ya siya mata sabuwa dal a kwalinta, ranar da ya bata wayar tayi ta murna da farin ciki tana masa godiya. babu wanda ta fara kira da wayar sai Mmn Sajida. suka shafe mintina da dama suna hira A gaskiya Naja'atu tayi farin ciki da samuwar wayar a hannunta dan sabida tasan ba qaramin kewa zata d'ebe mata ba.
******
"Kaga Salisu ina jin tsoron ranar da asiri zai tuno ni dai da zaka bi ta shawarata da kaje ka samu mutumin nan kayi masa bayani watakila ma yace mu rike kudin tunda nasa ne ." Mahaifiyar Naburago ce take wannan maganar
Gyara zamansa yayi yana kallonta yace."Haba Mama ki daina tsoro mana babu ta yanda zaayi asiri ya tuno kudi sun riga sun shigo hannuna." Tace."A'a ni daina nafi so kaje kayi masa bayani wannan kudin ba zasuyi maka albarka ba tunda na sata ne kaga kenan sata ta saci sata kaima idan da tsautsayi wani sai ya damfare ka tunda dai kasan inda zaka samu mutumin nan to kaje kayi masa bayani ka bashi hakuri ni na fada maka ba zaice komai ba watakila ma yace ka rike kudin."
Naburago yace."Mamma wannan shawarar taki gurguwa yace yama za'ayi na samu kudi a sama kice naje fad'awa wanda yake dasu ni ba zanje ba wallahi, na riga na shirya tsaf akwai sana'ar da nake so na fara dasu sana'a ce mai inganci kuma ina da ya'kinin zata kawo min kudi dan lokaci guda zan zama multi mollonia.".. Girgiza kanta kawai tayi tace."Shikkenan ai tunda kaki daukar shawara." Miqewa yay ya kama hanya ya fita, kai tsaye ya hau sabon babur dinsa wanda ya siya dubu dari biyu da hamsin, sannan yayi sabbanin d'unkuna ya kuma bibbiya bashin da ake binsa, daga haka sai kawai ya cigaba da facakarsa da kudin, dan ita kanta wacce tayi sanadiyar samuwar kudin da kyar yake bata wani abu, Naburago ya tattare kudin yayi bukatarsa dasu yanzu saura dubu dari takwas dasu yake so ya fara sanar cah-cah dan yana ganin yanda sana'ar take sanya mutane da yawa suyi mahaukanta kud'i to shima dama rashin kudi a hannu ne yasa bai fad'a harkar ba tunda yanzu ya samu dama to zai shiga a dama dashi, babur dinsa ya hau ya nufi mahad'arta su.
*****
'Bangaran 'Yar Sa'adu kuwa sai da tayi sati a barikin sojoji suna azabtar da ita sannan suka saketa ta dawo gidanta a mutukar galabaice jikinta duk yayi rud'u rud'u da shatin bulala abinka da farar mace ko'ina yayi tabo a jikinta, haka ta kwanta ciwo duk a cikin matan dake mata fadanci a kara rasa wacce zata zauna tayi jinyarta, sai da ta dan samu sauqi ta tattara komatsanta ta tafi garinsu tana ganin ba zata iya cigaba da zama ba haka kawai tana zaune wata ta sake janyo mata masifa gwara ta koma garinsu ta cigaba da harkokinta a can.
****
To kwanaki na tafiya wattani na shiga suna mutuwa, komai na tafiya ne da ikon Allah da kuma amincewarsa Naja'atu al'amuranta sun tsananta dan dab take da haihuwa cikinta ya shiga wata na tara har yayi kwanaki! gabadaya hankalin wanda yake kusanci da ita ya tashi saboda tunda cikin ya shiga wattanin haihuwarsa ta kumbura mussaman qafafunta, duk da Likita ya dubata ya tabbatar musu da cewar babu matsala hankalinsu bai kwanta ba. Abbah Abbas da hajia sunfi kowa tada hankalinsu a kan al'amarin....Baba malam da baba talatu kawaici da alkunya yasa duk damuwar da suke ciki game da 'Yar tasu sun kasa nunawa gabad'aya ma Baba talatu d'auke kanta tayi da kanta sai dai kullum cikin yi mata addua take......B'angaran Abbah Abbas kuwa gudun zargin da mutane ke masa yasa yake boye damuwarsa akan halin da Naja'atu take ciki amma zahirin gaskiya yana cikin tsanani da damuwa mussaman idan yazo gidan ya ganta a jibge a kan kujera! sai dik jikinsa ya mutu kullum haka yake yini ya kwana cikin alhini da jiran tsammani yanda ma ya damu da haihuwar Naja'atu kamar bai damu data Zainab ba su kansu matansa sun fahimci hakan sai dai kowacce na kokarin dauke kanta akai amma hakikanin gaskiya abun yana damunsu mutukar aka cigaba da tafiya a haka to suna cikin matsala gwara ya dawo da ita gidan hankalinsu zaifi kwanciya akan ya dinga shiga halin damuwa akanta.
Ranar Alhamis da daddare ta farka da ciwon haihuwa mai tsanani dama tun sanda cikin nata ya tsufa Yaya Ramlatu take kwana da ita a daki, jin motsinta yasa ta tashi da sauri tana tambayarta, Naja'atu na zufa tana kiran sunan Allah tace"Watakila haihuwa zanyi dan ciwon da nake ji yafi na kullum." Ya Ramlatu tace"To ikon Allah bari na kira hajia sannu kinji ko." Fita tayi daga dakin da saurin gaske..........Tare suka dawo dakin da hajia da sauri ta d'ago ta ta rungumeta a jikinta, tana mata sannu! Yaya Ramlatu ta shiga hada kayan haihuwa! Hajia t"Ta kalli Ramlatu da fadin''Ki sanar da hajia Rabi Naja'atu na kan gwiwa." Ya Ramlatu da sauri ta futa daga dakin...Hajia ta rike ta sosai tana tofa mata adduoi.... lokacin ita Naja'atu, ciwon ya tsananta dan dab take da haihuwa, shiyasa ta kasa tsugunawa sai kawai ta silale a gurin ta kwanta tana wani irin kifkif da idanunta! hannunta tasa ta janyo na hajian tana jan salati! Hajia ta shiga tashin hankali ganin irin abinda Naja'atun takeyi sai hawaye ya soma zubo mata addua take Allah y yanke mata wahala.....Hajia Rabi da Ramlatu na shigowa faya ta fashe! sai yunkuri kawai sukaji tana wani irin nishi!! da sauri suka rufu a kanta kowanne na iya bakin kokarinsa.....Naja'atu Ganin Yaya Ramlatu itace mai kwari a cikinsu sai kawai ta d'amko ta ri'keta gam! gam! a tare suka dinga nakud'ar suna nishi! tare! Sosai Ramlatu taji jiki ta kuma tabbatar riqon bana Naja'atu bane na mala'iku ne.......Cikin ikon Allah da hukuncinsa yaro ya fad'o a cikin zanin da suka rufa mata, sai kawai kukansa sukaji....Ajiyar zuciya suka sauke dukkaninsu suka had'a baki gurin fad'ar "Alhamdullhi."
0 comments:
Post a Comment