_Bismillahir-rahmanirraheem_
*1*
Qoqarin sauke kayan dake kan jakinsa yakeyi fuskarsa cikeda annuri da farin cikin jikinsa ma na nuna hakan sbd yanda yake sauke kayan da kuzarinsa da dukkanin himmarsa.,
Fitowa bayi matarsa Kuma uwar yayansa tayi tana kallonsa cikin tsananin mamakin ganinsa adaidai wannan lokacin,
Kallon sama tayi tana son kwatanta lokaci idan ta kwatanta daidai zata Kira lokacin da guraren uku zuwa hudu na yamma,
Duban uban kayan daya shigo dasu da jakin tayi tana sake bayyanarda mamakinta a fili na ganinsa Rana tsaka batareda lokacin zuwansa ganinsu yayi sbd a qaidancen aikinsa sai bayan sati bibbiyu yake zuwa ganinsu yayi kwana daya ya juya sai Kuma bayan satin biyu,
Yau kwanansa shida da komawa Amma gashi tana ganinsa harda kaya haka,
inda yake ta fito tsakar gidan tana ajiye butar hannunta tana Dan sake fuska kadan ta qarado tana karban qaton akwatin qarfensa dayake qoqarin saukewa daga kan jakin tana Dan nishin nauyin akwatin tace"
Abal Kaine yanxu?
Kallon kayan data sauke tayi tana maido kallonta kansa tace"
wannan dukannin kayan fa??
Fatan dai lafiya?
Yana qarasa aje daurin karshe dake kan jakin ya jasa zuwa wata rumfar dake can nesa da dakunansu wadda sukai daure dabbobinsu lokacinda suka taba kiwo yakaisa ya dauresa yadawo Yana zama kan saqin data shimfida Masa Yana cewa"
Alhmdlh ya ubangiji.
Ruwa taje tadebo Masa a qaton kofi me nauyi takawo gabansa ta ajiye tana zama gefensa cikin sauke ajiyar zuciya tana sake gaishesa wannan karon cikin yarensu na amheric tace"
_Dehina metahi_
(Barka da dawowa)
Shan ruwan yayi sosai Yana jinjina mata Kai Yana cewa"
Yawwa barkanku da gida,
Nasameku lafiya?
Alhmdlh"tace tana sake Masa kallon tambaya sbd gabaki daya hankalinta baa kwance yakeba da ganinsa gida yanxu sbd tafi kowa sanin tsanin qarfi da ikon masarautar delah take dashi akan ma'aikatansu Dan shekarunta ashirin harda yan Kai batareda mijinta ba saidai yazo yaganta duk bayan sati biyu yakoma saidai idan tace takai Masa ziyara wadda kafin tagansa ma aikine saiyanzu da shekaru sukaje saidai yayansu suje sugansa duk bayan kwana biyu saigashi yanzu tana ganinsa kwatsam haka ba tsammani.
Sauke numfashi tayi ahankali zatai mgn ya rigata da kallonta cikin tattara Yar nutsuwa a fuskarsa ta dattijantaka yace"
Jamila nasan hankalinki ba'akwance yakeba da ganina adaidai wannan lokacin,
Ki kwantar da hankalinki lafiyace tasanyani dawowa,
Babu wani abu daya faru kamar yanda kike tunani,
Nadawone gida wannan karon gabaki daya da yardar Allah shikenan zansamu yancina zanyi rayuwa taredaku cikin iyalina,cikin nutsuwa.
Wani guntun numfashi ta sauke wannan karon dukkanin jikinta nayin sanyi dajin abinda yake fada Wanda tasan ba iyakacin maganar kenanba akwai babbar maganar dake gaban wannan daya fara ta dago murya a sanyaye tana kallonsa tace"
*_NEGES?_*
'Dan dauke kai yayi ahankali cikin 'Dan jin nauyinta ya jinjina Kai ahankali yace"
Eh negestati.
Sama numfashinta yayi cikin wani irin yanayi na tsoro da muguwar bugawar da zuciyarta tayi ta sunkuyar dakai idanuwanta suka fara qoqarin cikowa da hawaye
Ya kalleta Kai tsaye yace"
Mahaifina yayi bauta a delah tun yanada kuruciya har tsufa ya kamasa Saida yakai baya iya wata bautar Ni yabayar ya yanci kansa a bautar dela,
Nayi bauta a delah tun Ina qaramin saurayina harna zama cikakken saurayi harna aureki muka Tara yaran dake gabanmu,
Nayi shekaru sama da talatin Ina bauta a delah,
Kinyi shekaru kusan ashirin ko fiye kina zaman kadaici batareda mijikinba,
Yarana sun taso Basu zauna da mahaifinsuba suka samu dukkanin kulawarsa,
Shin kina ganin bai kamata ba Nima nasamu yanci nadawo gidaba na huta 'daya daga cikin yayana ta fanshi 'yancina?
Jamila kinfi kowa sanin daganan har lokacinda Rai zaiyi halinsa ba barin delah zanyiba matuqar ba Wanda zan bayar maimakon yancina
Da inada 'da namiji bautar da mahaifina yayi haryabar duniya Nima nayi Shima ita zaiyi da haka zuriarmu zataita tafiya fa Amma yanzu daga kaina inshallah wannan gadon bautar yaqare sbd nine me 'yaya mata su ba bauta zasuje yiba *_NEGESTATI_* zasu zama.
Rintse idanuwanta tayi ahankali tana maida hawayenta sbd kada yaga rashin hakurinta ko rashin hankalinta ta dago batareda ta kallesaba tace"
Neges?
Acikinsu biyun waccece kazaba data zamo din?
Numfashi tasauke ahankali tana bayyanarda dukkanin damuwarta afili muryarta tayi tsananin sanyi tafara cewa"
Abal, dukkaninsu su ukun nice na haifesu,
Na rainesu,
Na zauna dasu nasan halin kowacce daga cikinsu,
MERIYAM bata cikin lissafi sbd itace qaramarsu gabaki daya shekarunta goma cif,
*_PADIMA_* da *_NURU_* sune ake magana akai.
Wani tsananin sanyi murya taqara zuciyarta tayi nauyi tanaji tun yanxu dukkanin burikanta da fatanta akan 'yayanta yana rushewa tareda dukkanin kuzarinta,
Hannu tasa ta dauke hawayen dasukeson sauko mata ta dauke kai ahankali tace"
Dukkaninsu inada burin ganin aurensu Kamar wanne 'yaya,
Nayi tanada da fatattaki akan rayuwarsu da aurensu,
bantaba kawo wani tunanin inda mahaifinsu yakeba zai iya juya qaddarar daya daga cikinsu daga zama Matar aure kamar kowace 'ya zuwa neges wato *_MACEN SARKI KO 'DAN SARKI KO JIKAN SARKI WADDA IYAKACINTA DASHI KWANCIYA DA HAIHUWANE_*,
Bantaba tunanin acikin yayana akwai wadda batada rabon igiyoyin aure su rataya akantaba saidai tazama _Negestati_ *(Kings mistress/kwarkwarah/abokiyar kwanciyarsa/abokiyar nishadin shimfidarsa).*
Kasa riqe hawayenta tayi wannan karon dukkanin jarumtarta saidai tanajin nauyi da kunyar bayyanarda damuwarta akan wannan hukuncin nasa sbd idan tayi Masa adalci ya cancanta ya huta Shima sbd ya bautu,
Ya hidimtu,
Ya wahaltu duk Dan qari sbd su da farin cikinsu baikamata ta nuna damuwarta afili ba duk da tasan aikin gama yariga Yagama tunda harya baro tasan yariga ya karbo shedar musayan yanci.
Abal kayi hakuri.
Girgiza mata Kai yayi Yana gyara zama yace"
Karki bani hakuri Jamila Dan dama dole zakiji ba Dadi saidai duk kuyi hakuri hukuncin Dana yanke kenan,
Maganar rashin jin Dadi anan dayace wato ta rabuwa da 'danka Amma kinsan irin rayuwar jin dadin da negestati keyi a daular nan banbancinsu da matan sarautar aurene Amma nawane suka sauya kaf zuriar danginsu daga talakawa zuwa attajirai.,
Banda burin 'yata tashiga delah dan ta maidamu attajirai saidai inada burin samun yancina Nima na huta daga bauta idan arziki yazo takawo Mana bazan qiba sbd kowa nason arziki kowa nason hada jini da delah dan haka Nima bazanqi naso samun jikoki daga delah ba sbd tabbaci ne na har abada da yardar Allah zuriarmu tagama bauta tashiga Kuma cikin littafin tarihin delah.
Murmushin qarfin hali tasaki tana qoqarin miqewa takawo Masa kunun madarar nonon raqumi da sabuwar danyar shinkafarsu tace"
Allah yasa hakan ne mafi alkhairi abal.
Amin" yace Yana gyara zama ganin ta dauko tasar kunun Yana hango haskensa tun daga hannunta.
Aje Masa tayi tafara kwashe kwayan dayazo dasu takai daki tadawo kenan su NURU din na shigowa gidan kowacce sanye da dogayen rigunan asalin yadin kuta,
Padima ce agaba kyakkyawar asalin brown/chocolate kalar fata,
Doguwace tanada jiki kadan musammn kirjinta acike yake Wanda yasa bayyanarda shafewar cikinta.
NURU ce abayanta hannunta riqe dana meryam,
NURU doguwace itama kyakkyawa me yellow brown skin asalin kyakkyawar amhara,
Batai jikin padima ba Amma tafi padima bajewar qugu Wanda yasa tafi padima suturta jikinta da kaya masu Dadi da rashin kamawa sbd boye irin kalar siffar da Allah yayi mata ta Jan hankali,
Tafi padima manyan idanuwa da fuskar marasa hayaniya sbd koyaushe fuskarta is simple sabanin ita padima da daka ganta zakasan tanada rawan Kai da jiji da Kai tareda jin kanta sbd kyawunta datake alfahari dashi duk da dai NURU da meryam sunfitashi haddama hasken fata sbd su kamarsu daya sosai da sosai sbd su mahaifinsu suka dauko shine asalin amhara wato asalin Ethiopian sai ita ta dauko mahaifiyarsu asalin hausa data surka da amhara din.
NURU da meryam kusan halinsu daya na rashin karauniya kuma meryam tafi shaquwa da NURU sbd itace Bata dukanta ko mata fada sabanin padima da Bata daukar raini ko kadan fada take mata musamman akan yanayin yanda takeson gudanar da rayuwarta.
Akwai saquwa sosai da kauna a tsakaninsu su duka da iyayensu,
Suna son junansu matuqa,
Suna kulawa da junansu tareda tsayawa junansu ako yaushe,
Kaman yanda ake karatun addini Dana boko Suma sunada wani qarin karatun wato karatun al'ada,
Sunyi karatun addini daidai misali,
Sunyi na bokon Wanda duk fiyeda rabinsa na aladunsune Dan haka gabaki daya idan kagansu Kai tsaye bazaka tantance sudin musulmaine kokuwa Dan al'adunsu a bayyane suke sosai tattare dasu.
Ganin mahaifinsu zaune yasa dukkaninsu tsayawa cak suna kallonsa cikin mamaki Banda meryam data qaraso da gudu ta fado kansa tana Masa sannu da zuwa cikin yare.
Kallon mamaki sukam suke Masa musamman dasukaga amminsu itama su take kallo zuciyarta fal da tunanin to shin cikinsu waccece za'a bayar amatsayin negestati,
NURU batada hayaniya,Bata iya doguwar hayaniyaba bare rigima baiwar Allah bazata iya da gidan sarautaba musamman delah dake cikeda fitintinu na mulki da sarauta sbd yawa da girman delah din idanma anbarta anan delah din idan Kuma asalin can daular dake qasar waje aka kaita inda asalin masarautar delah din take zuba zallan mulkinta Babu yanda NURU zata iya rayuwa a acikin asalin zuriar delah Sam Sam NURU bazata iyaba.,
Idan Kuma padima ce to itama akwai babban akasi sbd padima mace ce me tsananin son juya kanta bazata iya rayuwa acikin wainda mulki da iko yagama ratsa jininsuba sbd ita din zata zama bakowa bace acikinsu zasu juya rayuwarta Kamar suna juya kujeran zamansune Wanda taurin Kai da bakin padima zai hallakata acikinsu cikin qanqanin lokaci gashi a iya saninta babban burin padima shine auren mijinda yagama fita hayyacinsa akan Sonta wanda itace zata mulkesa acikin gidanta,
Burinta na biyu samun gidan arzikinda zata juya rayuwarta ta moru kyawunta bayyanardashi duniya tasanta acikin jerin kyawawa shiyasa babban burinta yakasance auren Koda bawane dake asalin delah dake qasar waje wato GIZAH,
Tanada burin komawa can Dan acan ne zata samu rayuwar datake shiyasa takeda kyakkyawar alaqa me qarfi da Ahmed Dan babban sarkin fada dake can giza Wanda ta shirya ta aminta da aurensa tabisa delah ta giza inda zaibi mahaifinsa yasamesa acan Wanda sai mai rabo ne keda sa'ar zuwa can.
Numfashi ammyn ta sauke tana dauke kanta daga kansu suna qarasowa ciki da mamaki suke Kiran sunan baban nasu cikin bayyana farin ciki da mamaki NURU tace"
Abal kana lafiya dai Ina fata?
Murmushi yasaki Yana cewa"
Alhmdlh nake NURU ganinku nazo yi.
Ajiyar zuciya padima ta sauke tana qarasowa itama sbd da har zuciyarta tafara shiga wani fargaba jin abinda yace yasata sakewa ta qaraso tana sakin murmushin farin ciki ta zauna gefen ammynsu tana cewa"
Abal harnaji tsoron ganinka sbd jin labarin yau anrabar da shedar sauyin yanci.
Daga abal din har ammy tare suka dago suka kalleta da sauri zuciyar ammyn na harbawa sbd sanin akwai akasin ra'ayi a alamrin musamman sbd yanda suka sabawa yaransu da rashin takurawa.
##MAMUH#
*_Haske writers💡_*
ZAFAFA BIYAR! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!!
Ina masu tambayar yaushe za'a fara? Ina masu jiran ranar? Toh gata fa tazo, mun zo muku da salo na daban wanda bamu taba zuwa muku da irin sa ba.
Me kike jira yar'uwa? Biya naki ki karanta halaliyar ki a nutse cikin kwanciyar hankali da jin dadi. Karki bari a baki labari, maza mallaki naki ta hanyar da aka tanada domin biya.
Littafan dai sune👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban ta whatsapp shedan biyanku(evidence of payment/Account name)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_UBAYD MALEEK_*
_(Royalty versus love)_
_*Mamuhgee*_
*2*
Treat/repair your skin with mg's skincare today,are you battling with pimples,
Black spot
cream reaction
eczema,acne, sunburn,spot, stretch mark, discoloration/skin damage, stretch mark ❌then mg's skincare is the plug for you,mg's skincare gat solution to all ur skin prblms😍everyone deserves a blended skin🌿 when it comes to skin issue😢gv it to mg's skincare 💯🔥 now is the time to take care of ur skin,this product is the real deal 🙌clears white patches✅dark patches✅dark feet's/knuckles ✅reduces the appearance of greenveins,it clears pimples,spot and make ur skin fresh nd glow like never before just gv it a try nd ur skin will definitely thank you💋✅evn if you don't HV anything mg's skincare gat you a soap that will maintain ur skin nd make the skin to glow🥰
Soap price:3k
Chat 08062991549 to plc ur orders
Call:08064532391
We deliver Nationwide buh delivery is not free🙏
we can't wait to be a part of your beauty story🤭
*******
Fuskewa abal yayi Yana dauke kai daga zancen padima din ya maida hankali kan NURU dake tambayarsa lafiyarsa da qafarsa dake ciwo sbd yawan tsayuwa daya kashe qafafun sbd wani lokacin yakanfi awa uku hudu a tsaye a delah gurin aikinsa gakuma manyanci sai qafafun sukeson fara gazawa.
Fira sukahau Yi sosai da abal dinsu kafin daga baya NURU ta miqe tayi gurin ammynsu Dan tayata aikin sabuwar dahuwar dare datakeyi sbd abal din daya dawo badan haka ba kunun madarar raqumi sukeyi susha abinda da daddare sbd 'yaya matansu basacin abinci me nauyi da daddare a al'adarsu sai kayi aure kafara hayayyafa tukuna.
Sai magriba suka kammala lokacin padima hartayo wankan yamma tana zaune dakinsu tana shafawa jikinta mai batareda NURU ta kalletaba ta ajiye kallabinta data zame daga kanta dogon gashinta ya bayyana Wanda yasa padima turo Baki sbd Bata baiyi tsayin na NURU din ba,
Abu uku ne NURU takedashi duk nata kyawun takejin dama ita Allah yabawa duk ta hada,
Dirarriyar shape din NURU dayafi nata sosai sbd hips da Allah yabawa NURUn da qarin cikin NURUn dayafi nata shafewa sbd ita tafi NURU jiki sai gashin Nan na uku asalin yelloebrown fatar amhara da NURUn ta dauko Wanda yafi nata.
Wanka NURUn itama tayo taraka meryam itama tayo sukazo sukai sallah dukkaninsu atare kafin suka dungamo tsakar gida suka zauna cin abinci tareda iyayensu.
Kallon yanda sukecin abinci abal keyi Yana karantarsu Dan sake tantance wacce zai bada,
NURU yake kallo sosai Yana sake yaba sanyi da nutsuwarta saidai Sam bazai iya badataba sbd cutatuwa zatayi musamman idan yayi duba da baisan taqamaimai waye acikin delah za'a bawa 'yarsaba.
Kallonsa ya maida kan padima wadda Kecin abincin a kiyaye batason Bata bakinta sosai Sarai yasan halinta da babban burin son abun duniya shiyasa zuciyarsa ke wasi wasi akanta Dan idan taje giyar daular arziki da mulki suka bugeta Yana tsoron ta zama wata mutum dabam sbd tsananin son duniyarta da jijida kanta yanada yawa kowa yasanda wannan.
Numfashi yasauke Wanda yasa ammi kallonsa sbd tasan tunaninsa tana lure dashi da yanda yake karantarsu,
Itadai tunda abune na dole baza'a taba guje masaba to a gaskiyance gwara abada padima sbd tunda sunada wata 'yar bazata iya Bari abada NURU ba Dan baqaramar cutatuwa zatayiba,
Bazata iya rayuwa acikin sarautaba sam,
Tsaftatacciyar zuciyane da NURU zasu gurbato musu ita da rudin zalamar mulki da dukiya gwara padima tana zuciyar son abun duniya Dan haka zata iya gwagwarmaya acikinsu ta qwataci kanta dama 'yayan negestati dazata haifa.
Suna kammalawa dukkaninsu suka hau fira da abal dinsu bayan NURU ta tattare gurin itada meryam suka dawo suka zauna.
_________________
*_No 554 U.MALEEK DELAH Aptmt_*
_Jericho brighton New York City,New York._
Mum""Yar budurwar yarinyar da Bata wuce sha Tara ba ta furta cikin nuna takaicinta da damuwarta a fili tana kallon takardun hannunta data dauka daga gaban madubin bedroom din uwar Tata.
Qarasowa tayi idanuwa na cikowa da hawaye har gaban dining din ta daga takardun dake hannunta tana cewa"
Mum menene wannan??
Cikin wata irin cikakkiyar izza data gama Kama jininta ta dago a natse Kamar Bata fahimci damuwa da tarin baqin cikin data gani atattare da babbar 'yartaba wadda bazaka taba cewa 'yartaceba sbd itama tsufa ko wani manyanci ba gama kamata yayiba sakamakon auren wuri na sarauta da akai musu da mijinta shiyasa 'yartata tazamto Kamar wata qanwarta danma tafi Yar 'kyawun jiki da itakuma 'yar tafita kyawun fuska nesa ba kusaba sbd zallar Kamar mahaifinta data dauko.
Kallo daya tayiwa takardun kafin tamaida kallonta kan fuskar 'yar cikin wani irin sautin zallar iko da mulki tace"
AFIA menene naki akan wainnan takardun dake hannunki?
Wannan tsakanin nida abal dinki ne so stay out of it okay?
Dire mata takardun tayi da qarfi gabanta idanuwanta na cikowa da hawayen baqin cikin halin mahaifiyarta tace"
Mum wannan decision din naki na nufin rabuwa da abal fa,kinsan abal mgn daya yakeyi Wanda idan yayi Babu Wanda ya isa canzawa
Mum are you willing to take that risk?
Idan bakya tunanin kanki da rabuwa dashi mum please kiyi tunanin mu 'yayanki idanma Ni bakya tunanina kiyi tunanin farhat Mana,
Mum farhat bazata iya rayuwa Babu 'dayankuba tsakanin ke da abal idan kikai signing wannan contact din Kika tafi Tokyo shikenan fa kinbar delah har abada bazasu karbekiba kokin dawo daga baya please think and think and think mum"" taqarasa mganar hawaye na gangaro mata tanajin Ina zata Sanya zance mum dinta ta aje wannan rayuwar dama tafi ta turawa zama abin tsoro.
Spoon din boiled veggies da aka soya da kwai takai bakinta tareda shanye sauran black lemon tea dinta ta zari tissue ta goge bakinta kadan ta miqe tsaye sai alokacin ta fuskanci afia din dakyau ta kalleta cikin wani irin iko tace"
AFIA tuntuni nasan cewa zanbar delah duk ranarda na karbi contract din santrigo Tokyo na jirane dama sbd ki qara girma kiyi wayonda Zaki kula da farhat idan natafi hakama idan nadawo nasan Zaki tsaya tsayin daka su karbeni,
Santrigo Tokyo babban burinane Dana girma dashi na rayu dashi Dan haka aure bazai hanani cika burinaba ayanzu Dana samu dama,
Idan kinason duk wannan kar ayi azauna lfy kije kiyi convincing dad dinki yabarni naje Tokyo nayi aikina Dan bazan bar aikina Dana dauko shekaru fiyeda goma sha ba inayi akan tsantsar ikonsa da izzarsa ba.
Wani numfashin mamakin mum dinta tasake tana mata kallon mum kinyi nisa ta sake sauke wani numfashin tareda gyara tsayuwa ta kalleta cikin sanyin murya tace"
Mum kinfi kowa sanin mijinda Allah yabaki idan duk dukiyar Tokyo zakije abaki bazaki samu abinda yakai Wanda kike samu agunsaba,
Duk abinda Zaki samu a duniya bazaki samu abinda yakai _*UBAYD MALEEK DELAH*_ ba,
Mum Ina sake Baki shawarar kizauna adaki kiyi tunanin abinda kike Shirin aikatawa,
Zaki rasa mijinki,'yayanki biyu,dukiya,suna da matsayinki na Matar _MALEEK_ na GIZAH Wanda nake ji Miki tsoron rasawa har abada.
Ke mahaifiyatace bazanso ki rasa duka wainnan sbd abal shine abu na qarshe da mace zatai baqin cikin rasa samunsa a rayuwa.
Wani QAYATACCEN murmushi LAILAH tasaki tareda dafa kafadar 'yarta tace"
AFIA ke yarinyace
Kinason dad dinki fiyeda komai shiyasa kike ganin dukkanin hakan Amma abinda Baki saniba shine dad dinki mutum ne da duk duniya Babu me juyasa sai kakansa Wanda Shima halinsune yazo daya,
Inaga zaifi ki nutsu ki maida hankali kan karatunki ki Kuma kula da farhat Dan zata shiga damuwa sbd bananan Kuma dad dinku is a very busy man.
Kasa cewa komai tayi tabi bayan mum din Tata da kallon damuwa da baqin ciki harta haye sama.
Masu aikin gidan ne kusan su biyar sukazo suka fara tattara kayan dining din suna gaidata cikin tsananin girmamawa duk da dukkaninsu sun girmeta wasuma sun haifeta Amma sbd matsayinta na babbar 'yar maleek suke Bata mugun girma.
Ko kallonsu bataiba sbd halinda zuciyarta take ciki gabaki daya a jagule take bazataso auren iyayenta ya rabu ba akan iko,izza da isar dad dinta dakuma taurin Kai da burin duniya na mum dintaba,
Farhat kawai take dubawa sbd yarinyace sosai akanta sbd ita yanzu takeda 8years a duniya bazata iya ganin iyayenta sun rabu ba saidai abu daya tasani shine rabuwa kamarma sunyine Dan Babu abinda zai sauya taurin Kai irin na mum
Dad din Kuma aishi kankat ne Dan yafita zama riqaqqe saidai tana jin tausayinsa sbd mutum ne shi me tsananin qyanqyami na komaima
Suna rabuwa da mum za'a fara kawo Masa 'yayan manyan masarautu kokuma ma za'a iya kawo Masa negestati Wanda tasan tsananin qyanqyaminsane ya hanasa qara aure aure kamar sauran 'yan delah musamman shi dayake ubayd maleek na GIZAH,
Hakan nema yasa ya kebe kansa anan new York da iyalinsa Yana gudanarda rayuwarsa a qaidance yanda yake sonsa ba tarkacen hayaniyar masarauta duk da yasan dole wata Rana zai koma can da zama.
Bedroom dinta ta nufi ta fada kan gado tareda rintse idanuwanta hawayen ciki suka gangaro ta share da qarfi cikin takaici tace"
Bazanyi kukaba mum tunda haka Kika zabar Mana shikenan zamu runguma mu rayu Kamar marayu duk da munada uwa Amma ta zabi duniya akanmu.
Miqewa tayi tafada toilet tayo wanka tana fitowa tashirya a gaggauce ta zari ipad dinta ta fito ta nufi library din karatunsu tana qoqarin fitarda damuwar dake cikin ranta sbd mum tayi nisa batajin Kira sbd sunfi shekara akan wannan mgnar taqi barinta yanxu harta karbi takardun contract din shikenan komai yazo qarshe.
'dagowa tayi bayan ta zauna cikin library din ta kalli qaton makeken hotonsu na family daya cinye kwatan bangon library din ta qurawa dad dinta fararen idanuwanta da nashine ta dauko Zak,
Bawai Dan tana tsananin son dad dintaba Amma Bata taba ganin mutuminda ya hada irin qualities dinda ya hadaba,
Dad dinta is 99% takowane fanni.
Mum dinta takalla ta rintse idonta ta bude tana cewa"
She's perfect, she's beautiful tanada komai but she's nothing compare to dad Amma takeson barinsa meyasa?
Farhat da kanta takalla a hoton take hawayen datake riqewa suka gangaro mata ta miqe tabar gurin tana fasa karatunma.
________
********NURU"" ammi takira sunan cikin tsoro da fargaba,
Abal meyesa kake ganin zabin NURU shine daidai bayan kasan NURU bazata iyaba.
Numfashi ya sauke Yana gyara kwanciya yace"
Padima gidan sarauta kamarna delah zaisa burinta ya fadada zai iya hallaka tunaninta da tarbiyarta.
Amma Kuma abal NURU tayi rauni da yawa kaduba.
Aa jamila kina dai tausayinta ne Amma itace zata fi mutunci a irin gurin sbd me hkr shine zaici ribar zama a delah.
Riqo hannunsa tayi tana marairaicewa da hawaye cikin idanuwanta sai jikinsa yafara sanyi Sam bayason ganin damuwarta sbd tsananin so da qaunarta dayake,
Kusan sati daya kenan sunata muhawarar wazasu bayar din kafin shi ya yanke NURU itakuma ta yanke padima.,
Ajiyar zuciya ya sauke sbd tunanin dayayi na girman Kai da burin padima na zuwa DELAH GIZAH bazai taba barin ta yardar musu ta yarda subadata a delah tanan ba tsaf yasan bijirewa zatayi sanin haka yasa yacewa ammin ya amince abada padima.
#MAMUH#
*_Haske writers💡_*
_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖
_ZAFAFA BIYAR_💘💘💘
_ZAFAFA BIYAR_💓💓💓
_(ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL)_
_(HUBILMAHX)🧡🧡🧡_
_ASSALAMU ALAIKUM! INA MASOYA MA’ABOTA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA?!_
_TO KU MARMATSO DOMIN NESA TAZO KUSA, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKE KAWO MUKU DA’DADAN LITTATTAFAN NAN ZAFAFA GUDA BIYAR, SUN SAKE ZUWA DA KASHI NA 4._
_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_
_RIGIJI GABJI DINFA KENAN, DOMIN WANNAN KARON MA MARUBUTAN SUN SAKE KAWO MUKU WASU DADADAN MASU FADAKARWA, NISHADANTARWA, NISHADANTARWA UWA UBA KUMA AKWAI LAGWADAR SOYAYYAH..._
_*SAFIYYAH HUGUMA:* TAZO DA NATA SALON RUBUTAN MAI SUNA: *ALKIBLA*❤️❤️_
_*HAFSAT RANO:* TAZO DA NATA TAKEN RUBUTUN MAI SUNA: *MABUDIN ZUCIYA*🥰🥰_
_*MAMUH GEE* TA KARA ZUWA DA WANI SAMFURIN MAI SUNA: *UBAYD MALEEK*😘😘_
_NANA- HAFSAT *(MISS XOXO)* TA SAKE ZUWA DA WANI KALAR NA: *DALAAL*💞💞_
_*BILLYN ABDULL* TA KARA ZUWA DA WANI TAKEN MAI SUNA: *MAKAUNIYAR KADDARA*💝💝_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_UBAYD MALEEK_*
_(Royalty versus love)_
*_Mamuhgee_*
*3*
Tafiya takeyi cikin nutsuwar datafi Kama da jin Kai da taqama musamman yanda jikinta ke girgizar daukan hankali shiyasa duk Wanda ta hadu dashi a hanya yake hadiye Mata yawu musamman wainda sukasan padima ai tafi karfinsu sbd kyanta da ikonta tareda sanin Wanda suke soyayya dashi din daga delah yake wato Dan babban sarkin fadawa bama Wanda yake Nanba na can gizah.
Daga gurin karbo baqin lallensu take sbd koyaushe ita mace ce da Bata rabuwa da qyale qyale shiyasa yanada wuya kaganta Babu lalle faratanta na hannu Dana qafa shiyane qarin banbancin tsakaninta da NURU wadda duk wannan ta daukesa Kamar bayyanarda kyawu ne Wanda ita tafi ganin burgewarsa idan kayi aure kayi acikin gidanka.
Daga bayanta taji anriqo hannunta ta tsaya cak tareda wani juya idanuwanta wani qayataccen murmushi na sauko Mata sbd sanin Babu Wanda yake iya riqota haka sai mutum daya saidai kafin ta juyo ta hango su NURU tafe da sauri ta juyo ta jasa da gudu suka boye bayan wata qatuwar bishiya tana Dora Masa hannun abaki qasa qasa tace"
Shihhh su NURU na zuwa.
Wani shu'umin murmushi ya sakar Mata Yana gyada Kai kafin ya juya ya zubawa NURU mayun idanuwansa dukkanin yawunsa na katsewa akan NURUn,
Meyesa ba NURU ce wadda Allah yabasa sa'a akantabane Dan wlh baitaba jin mugun kwadayin maceba Kamar NURU gashi padimanma tai Masa Amma da zaa basa zabi da NURU zai zaba Dan duk Wanda yagama samunta a Mata ko a abokiyar haihuwa yagama dacewa,
Mummunan faduwa gabansa yayi daya tuno da hadda abal dinsu acikin yan sauyin 'yanci take ya waiwayo da sauri ya kalli padima Yana girgiza Kai Dan wlh bazai yadda yabarta tashige zuriar delah ba tabarshi Dan har abada bazai taba samun kyakkyawar mace kamarta ba tunda dai NURUn yasan ba samunta zaiyiba Kuma dai dole cikin dayan biyun ne ko padima ko NURUn,.
Ina Ina ina""yafada cikin ransa da sauri Yana girgiza kafin ya maida kallonsa kan bayan NURU data wuce Yana tunano da kaf delah yanzu duk Wanda za'a kaiwa negestati Babu Dan yaro yaro sbd yara yara shekara daya kenan cif da aurarda yayan masarautar delah din su goma sha daya Kuma a qaida saikayi shekaru uku da aure zaka fara karban negestati sai wainda basuyi aureba sukuma baa Basu negestati sai sunyi aure.
Kallonsa padima tayi da manyan idanuwanta tana cewa"
Yaya dai?
Tunanin me kakeyi?
Wani murmushin bazata ya sakar Mata Yana sake jawota jikinsa Yana shafa hannuwanta Yana matsawa ahankali ya kashe ido Yana cewa"
Padi padi,
Padi nidai maganar gaskia zanje nasamu abal dinku yasan da maganarmu sbd so nake kafin kwana talatin dinsa tacika kinzama tawa mun wuce gizah..
Da wani kallo ta katsesa tana Dan zamewa idonta akansa tace"
Kwana talatin kamar dai wadda aka gaji da ita,
Amed nafada maka banason auren gaggawa sbd inason aurena yazama abinda zai burge kowa,
Banice baiwa ba abal dinane bawa Dan haka Ni inada damar yin bikin aurena kamar na kowanne 'yantacce,
Hakama Ina buqatan shiga boyon wankan ruwan madarar nono na tsawon sati biyu hakama Ina buqatan siracin nonon raqumi na tsawon sati biyun Shima sbd ranar dazan fito muka isa gizah aranar za'a tabbatarda nafi fiyeda Rabin matan sarautar kyawu.
Wani murmushin manufa tasaki tana sake riqe hannuwansa cikin kisisina Dan kuwa itadai babban burinta tasamu isa delah gizah inda asalin arxiki, mulki da sarauta suke
Kyawunta shine zai cika Mata burinta shikuma amed shine mukullun tafiyarta.
Cikin marairaice fuska yace"
Padima bazan iya Bari kwana talatin din abal dinku yacikaba sbd zai iya zamtowa kece zai bada bazan iya rasakiba padima mutuwa zanyi idan bake.
Wani kallon rashin fahimta take binsa dashi fuskarta na sauyawa tace"
Badawa Ina?
Gyara tsayuwa yayi Yana sake tamke hannunta yace"
Abal dinku ya karba shedar sauyin yanci.
Wani irin bugawa kirjinta yayi tana qwace hannunta daga nasa cikin son qara tantancewa tace"
Negestati??
Gyada Mata Kai yayi Yana cewa"
Eh padima Kuma Nanda kwana talatin ne za'a karba wadda zai bada kowane lokaci za'a zo afara gyaran ko ke ko NURU.
Wani irin daure fuska tayi zuciyarta na harbawa da qarfi a matuqar zabure take cewa"
Meyasa abal zai Mana haka?
Meyasa zai yanke hukuncin badamu negestati baiyi shawara damuba bama wannan ba"" da sauri ta rqio hannunsa son tabbatarwa tace"
Amed ko kasan waye za'a karbanwa negestati din?
A delah tanan ne ko a delah gizah be?
Fadamun da sauri amed inason sani ne idan a delah gizah za'a Kai.
Kallo biyu yake Mata,
Kallon Sonta da kallon yasan manufarta akansa Dan haka cutar cuta za'ayi yasani Sarai sbd yace gizah zasu take taredashi ta yanda idan an isa zatasan yanda zatai ta watsar dashi ko negestati ta zama acan din ta yarda shikuma Yana sane Sarai ba gizah din dazashi hakama yasan wannan tambayar datake Masa Dan taji idan Wanda za'a kaiwa negestati a gizah ne tsaf zata samu abal dinta tace abadata Amma yasan yanda zaiyi da ita ko taqi ko taso ita din tashi ce shi daya.
Bata fuska yayi kalar tausayi ya riqota Yana cewa"
Padima shiyasa bazan iya Bari abadaki ba sbd anan delah ne za'a bada Kuma qarin cikin abin a yanda naji abeela za'a kaiwa qila mutuminda shine kusan babba acikin jikokin delah ya tsufa ko me zaiyi da mace yanzu?,
Padima bazanso kije rayuwarki ta gurbata ba Zaki samu arziki da mulki Amma baida amfani sbd bazaki more rayuwarki yanda kikeda buri ba gwara muyi aure mutafi gizah acan nasan rayuwa zatai Mana dadi.
Jin Wanda za'a bawa negestati din yasake daga hankalinta tafara girgiza Kai tana cewa"
Badai ni padima yonas ba,
Sam rayuwata bazata mutu ba agurin bautawa tsohoba duk ya zugemin kyau da quruciyaba,
Padima darajata ta wuce Nan wlh bazan yardaba saidai NURU koma meryam za'a bada abada nidai wlh bazan yardaba.
Juyawa tayi ta nufi hanyar gida cikin tsananin tashin hankali batareda ko takansa tasake biba,
Duk rashin hankalinta da girman kanta bazata iya bijirewa iyayenta ba saidai zata fada musu bataso idan sun nace bazata iya musu taurin kaiba saidai
Abu biyune tasani matuqar aka bada ita negestati to rayuwarsu kaf tana cikin hadari sbd duk Wanda aka kaiwa ita ya kwana da ita zaijita ba budurwa ba Wanda hakan babban laifine hukunta kisa itada iyayenta duka idan sunada jini acikin delah wadda ta taba zama negestati shine zata roqar musu sassauci baza'a kashesu ba saidai za'a koresu daga qasar gabaki daya to gashi basuda Yar uwa ko daya delah dama burinta ta auri amed sukoma gizah inda tasan kyawunta saisa kaitsaye tasamu Dan sarauta bayan tasan yanda tayi ta rabu da amed yanzu ga wannan babbar maganar ta bullo yau ita wazata fito tafadawa kada abadata sbd ita din ba budurwa bace.
Koda ta isa gida har wani murdawar tashin hankali cikinta keyi tayi danasanin bawa amed kanta yafiso cikin kwando dari Dan kuwa Sarai tasan masifar hakan a addinance dakuma al'adance.
Tana shiga gida dakinsu tayi da sauri ta ajiye kayan hannunta tafito ta zari buta ta nufi bayi tana kaucewa kallon inda abal da amminsu ke zaune suna binta da ido.
Koda tashiga bayin kasa yin komaima tayi tafito tana qoqarin sakewa tazo gurinsu abal din ganin su NURU sun dawo ta zauna anacin gasasshen dankalin dasukeci da ita.
Kallon NURU abal dinsu yayi hakanan yake sakejin hankalinsa yafi kwanciya da zuwan NURU sbd ita din tafi cancanta duk da baisan waye za'a kaiwa ita ba Amma dai yasan delah basuda tarihi mara kyau Dan haka duk Wanda za'a kaiwa baida fargaba ko shamaki.
Padima yakalla yasake kalla zuciyarsa nasake tabbatar Masa da kamar kaita wani kuskure ne koba komai yafison yabarta ta aura Wanda take Dan burintane ita Kuma NURU bada ita ba'a shiga haqqintaba sbd batada wani buri sai wanda su iyayenta suka yanke akanta.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda kallonsu cikin nutsuwa yafara koro musu bayani komai tareda dorawa da cewa"
Padima kiyi hkr da wannan al'amari daza'a Kira da qaddararre sbd tabbas kowane uba zaiso ganin ya aurar da dukkanin 'yayan da Allah ya azurtashi dasu,
Naso ganin hakan Nima kamar kowane uba saidai Allah be nufa zanga na dukkanin 'yayana ba saidai biyu daga ciki Dan haka padima Ina Baki hkr dakuma umartaki dakiyi biyayya wa Ni mahaifinki dakuma al'ada da dole ki karbi wannan qaddarar dan haka saiki nutsu Zaki daina fita daga gobe sbd za'a fara Miki wanka da siracin sabuwar Madara za'a fara kawowa daga DELAH.
Tsit sukayi dukkaninsu kamar ruwa ya cinyesu musamman padima da jikinta yadauki mazari tafara hada zufan tashin hankali Wanda yasa umminsa shiga tunani me firgitarwa kafin wani yayi magana padimar ta bude Baki murya na rawa tace"
Abal...abal NURU.... NURU..Ni inason A....zungurinta umminsu tayi tareda katseta da cewa"
Kutashi kuje kuyi tunani inshallah Zakiyi farin ciki da hakan ba dama gidan arziki da mulki kikeso ba Inshallah zakiji Dadi.
Cikowa idanuwanta ke neman yi ta girgiza Kai tana cewa"
Ammi ba hakan bane ni...Ni..
Kuje nace padima.
Kamata NURU da jikinta yagama sanyi tayi Dan ita gabaki dayama ta firgice dajin abinda yake faruwa sbd ita ko delah akace za'a saitaji duk ta firgice bare ace itace zata shiga delah ta zama jininsu Sam firgici ma tunanin hakan yasata shiyasa tausayin padima yashigeta me tsanani duk da tasan padima ita zata iya duk da idan tashiga ita din ba komai bace Amma dai gwara ita zata iya.
Suna shiga daki padima ta zube kan shimfida tana sake shiga tashin hankali wlh Bata shirya mutuwaba,batason mutuwa Ina zata saka kanta dole ta samo mafita.
Duk irin lallashi da kulawarda NURU ke Mata cikin tsananin tausayawa Sam Bata fahimta sbd hankalinta baya jikinta.
Abu biyu da biyu ga zama negestatin tsoho mara amfani,ga tsoron agano ta taba kwanciya da wani Kuma ta shiga delah ga tsoron hukuncin hakan duk saitaji tana neman haukacewa wlh bazata iyaba Gwara abada NURU Dan ita tunda duniya Bata dametaba zata iya rayuwa da tsoho ko baida amfani itadai ba ruwanta can su qarata.
Har gari ya waye Bata rintsa ba sbd tsananin tashin hankali Koda ta fito da safe babu Wanda bai fahimci Bata hayyacintaba duk ta firgice gashi tanason ganin amed suyi magana Kamar me ba halin fita Dan idan Bata samu magana dashiba komai lalacewa zaiyi.
Da maraice saiga manyan bayin delah kusan guda goma sha biyu sunkawo tarin kayan wankan Madara daza'a fara Mata washe gari tana ganin hakan hankalinta yasake tashi jama'ar gari kuwa suna gani suka tabbatar aka fara zarya gidan tayasu ammy murnar samun yancin abal da murnar shigar 'yarsu delah.
Kwanaki goma sun shude da fara gyaran Negestati padima Amma Sam hankalinta a hargitse take takai yanxu ko rintsawa Bata iyayi tun abin na wasa tadawo ko abinci Bata iyaci take tafara wata irin rama da duhun tashin hankali daganan sai kukan dare Wanda yayi masifar daga hankalin NURU da duk duniya taqi jinin ganin damuwa akan fuskar iyayenta da 'yan uwanta ta tashi cikin tsakiyar dare tareda lalubar qaramar fitila ta kunna taga padima zaune hannunta riqeda wuqa tana faman wani irin kuka da sauri ta qaraso ta fixge wuqar cikin tashin hankali da tsoro jikinta yadau rawa sbd ita qaramin abu ke firgitata tace"
Padima me Zakiyi da wannan tafada ta wurgi da wuqar cikin tsananin tsoro.
Sabon kuka padima tasake tana qwacewa tace"
Mutuwa zanyi tunda ko ban kashe kaina yanxuba naje delah mutuwa zanyi.
#MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖
_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN K xxAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
*_UBAYD MALEEK_*
_(Royalty versus love)_
*_Mamuhgee_*
*4*
Cikin tsoro da rawar murya NURU tace"
Padima kidena cewa mutuwa kina bani tsoro sosai kidaina kuka menene Dan Allah ki dena kina bani tsoro.
Ganin yanda NURU duk ta firgice cikin tsananin tsoro yasa tadan sassauta tayi tunanin amfani da tsoron NURU sbd dama can ita abu kadan yake Bata tsoro saita sake marairaice fuska tana faso wani kukan tace"
NURU idan Banga amed mukai magana ba akwai babbar matsala wlh komai zai lalace zamu rasa komai da iyayenmu duk mutuwa zamuyi.
Zaro manyan fararen idanuwanta NURU tayi jikinta na daukar rawa tana sake padiman takasa magana tana neman yin baya ta fita a rude padima ta riqota da qarfi tana cewa"
NURU wlh dagaske nake idan bangansa munyi magana ba komai zaifaru Dan Allah kimin hanya naganshi idan nadawo zan fada Miki komai Amma wlh rayuwata na cikin hadari danasu abal ma..
Kasa fahimtarta NURU tayi sbd firgici sai rawa da jikinta keyi ganin hakan yasa padiman taja wani qaramin tsakin takaici tareda girgizata da qarfi ta jawota ta direta zaune tafara shafa bayanta tana hura Mata iska tana kiranta ahankali ahankali hartafara nutsuwa tana dawowa hayyacinta saidata rarrasheta tadawo hankalinta tsaf tukuna ta janyota ta kwantarda kanta kan cinyarta tafara Sabin hawayen samun yaddar NURUn tasake fada Mata abinda tafada Mata da farko NURUn daketa ajiyar zuciyar ta qanqame padima cikin tausaya Mata murya amatuqar sanyaye tace"
Padima idan kikaga amed din shine zesa bazaki kashe kanki ba ko?
Eh NURU bazan kashe kainaba Ni sbd ma kune nakeson ganinsa na nema mafita.
Haka ta lallaba NURU taringa marairaice Mata da kuka hartayi nasarar cika tunanin NURU da tausayinta akan alamarin shiyasa washe gari da za'aje wankan ruwan Madara saita lullube fuskarta taje amaimakon padima bayan tayi Mata hanya sunyi sauyin kaya ta fitar da ita gidan masu wankan dasuka ganta saisuka tambaya tace ai yanzu ita za'a ringawa ba padima ba dayake bayin qasane gabaki daya saisuka yarda sbd manyan bayi basa fitowa delah bare akawo musu irin wannan.
Dama Shima NURU taje ta sanar dashi padima zata fito tanason ganinsa shiyasa yaje inda suke haduwa Yana jiranta danshima a mugun qage yake da ganinta Dan wlh Shima be shirya mutuwaba tunda yasamu labarin ita aka bayar yasan qaryarsa taqare kashesa zaayi duk ranarda akaji shine yafara kwanciya da ita.
Kamar munafuka haka take tafiya tana waiwaye tana boye fuska harta iso Yana ganinta da gudu ya qaraso yakama hannunta suka nufi can nesa da gidajensu cikin wani lambu bayan bishiyar ayaba ya rungumeta Yana cewa"
_Ya Allah Padima nafekushi_
(Ya Allah padima Nayi kewarki sosai)
Kuka tafashe dashi tana turesa daga jikinta tace"
Amed duk mutuwa zamuyi
Banason mutuwa guduwa zanyi da qasarnan zanshiga duniya bazan tsaya akasheni ba...
Riqota yayi da sauri Shima cikin firgicin yake yace"
Padima ki nutsu musamo mafita Nima angaya Miki na shirya karban wannan hukuncin ne?
Bazan iyaba nikaina mafitar nake nema.
Zamewa tayi qasa tayi zaman dirshan tana cewa"
Amed kayi gaggawar samo mafita kokuma kawai mu gudu.
Mu gudu muje Ina padima?
Idan muka gudu burirrikanmu fa damuka Dade muna....
Cikin masifar tashin hankali ta katsesa da cewa"
Burin banza tunda Saida rayuwa zamu cika burin,
Ni kaga kawai musan abinyi wlh na cikin masifa wannan wane irin balai ne nasaka kaina aciki amed ka cuceni...
Kinga yi hakuri kidaina kukan yanxu mafitarmu dayace ajanye badake abada NURU.
Wani kallon takaici da baqin ciki tai Masa tana cewa"
Sun San da NURUn suka badani sbd tunanin ita wawuyace batada wayo Ni bansan inda zansaka kainaba zuciyata fashewa zatayi....
Da sauri ya durqusa gabanta cikin Dan samun sa'ida yace"
Muyi amfani da sanyin halinta kiyi Mata wayo ki gurbata Mata tunani da tsananin tausayinki ki Bata tsoro da rayuwar iyayenku da kanta zata bada kanta.
Dakatawa tayi da kukan datake ta dago idanuwanta dasuka gama kunbura sukai jajir ta kallesa tana qoqarin karban abinda yafada din cikin nazarin maganar tace"
Kumafa hakane..
Batada wayo zan iya sata ta bada kanta da kanta.
Zabura tayi ta miqe tsaye tana share hawayenta cikin farin ciki tace"
Meyasa banyi tunanin hakanba tun farko?
Meyasa na tsaya Bata lokacina cikin tsoro da tunanin zan mutu bayan inada NURU.
Riqosa tayi da sauri cikin tsananin farin ciki tace"
Amed kashirya komai zai tafi yanda mukeso zanji da NURU sauran aikin idan mukazo tareda ita saikayi naka.
Rungumeta yayi Yana cewa"
Karki damu tunda munada wadda zata shiga tarkon mukuma mu fita kuka yaqare sai Dadi da rayuwar delah gizah dake jiranmu.
Shafarta yashiga yi Yana lallashinta da qara Bata shawarwarin yanda zasuyi hardai suka samu suka sake biyan buqatarsu agurin Saida duhu yadan yi yarakota har bayan gidansu ta zagaya tashige yakoma cikin farin ciki.
Itama cikin farin cikin tadawo gidan ta tararda NURU a daki tana jiranta cikin firgici da tsoron rashin ganin dawowarta kan lokaci tana ganinta ta taso da sauri cikin tsoro ta rungumeta tana sauke ajiyar zuciyar ganinta tace"
Padima kinbani tsoron rashin dawowarki kan lokaci.
Murmushin jin Dadi padiman tasaki tana rungume NURUn tace"
Wallahi Bet'ami afek'irihalewi NURU.
(Wallahi Ina tsananin sonki NURU)
Ajiyar zuciya kawai NURU ta sauke suka qarasa komawa ciki suka zauna ta marairaice fuska tana Shirin fara hawaye NURU ta katseta da cewa"
Padima karkiyi kuka Dan Allah tunda kingansa kinsamo mafitar matsalarki ko?
Girgiza Mata Kai padima tayi tana tsoyayo hawaye tace"
NURU banason mutuwa,
Banason abal da ammi suma su tafi su barku dagake se meryam qilama duka tafiya zamuyi mubar DUNIYAR bansan yazanyiba duk nice na janyo shiyasa nakeson na kashe kaina nahuta kowama ya huta.
Da sauri NURU ta girgiza Mata Kai tana cewa"
Padima bazan iya Bari ki kashe kankiba gwara mu mutu gabaki dayan koma menene yafi Mana sauqi bazamu iya juran rashin 'daya daga cikin ahalinmu ba kidaina fadar hakan muna tsananin sonki bazaki mutuba yanzu inshallah.
Jan numfashin kuka tayi murya na fita daqyar tace"
NURU kinsan menene yake faruwa ga duk negestati dinda aka Kai aka tararda batada budurci tabawa wani??
Ras Ras qirjin NURUn yayi wani mummunan bugawa harsaida jikinta ya nuna hakan sbd rawar daya Dan dauka ta kalli padima da fararen idanuwanta cikin rashin fahimta tace"
Meya kawo wannan tambayar padima?
Sunkuyar dakai tayi tana tsoyayo hawaye tace"
NURU nida amed mun.....
Wani mummunan tarine ya qware NURU idanuwanta suka firfito tafara tarin cikin azaba da tashin hankali tun tana shafa Mata baya hardai dole suka fito daidai fitowar amminsu Nan sukai kanta akaita Bata ruwa Ana fesa amata Amma sosai ta sarqu idanuwanta sunyi jajir sbd azaba cikin fada ammi tace"
Menene ya sarketa padima?
Ammi kawai zaune take saita fara tari shikenan ne kawai.
Fitowa abal yayi daukeda sabuwar madarar raqumi yabata yakuma fesa Mata take abin yafada Mata tafara fidda numfashi daqyar tana rufe idanuwanta cikin galabaituwa.
Padima ta tayata ta watsa ruwa takaita daki itama tadawo tayi wankan tazo tayi sallah saikuma takejin kunyar NURU din Amma Kuma tunda dai amfani takeson yi da ita dole zata fada Mata hakan.
Kwanciya dukkaninsu sukayi babu ko me dogon motsi sbd tunanin da kowa keyi musamman NURU dake cikin tashin hankalin jin masifar dazata samu ahalinsu.
Washe gari ma NURU ce taje wankan ruwan madaran haka zalika takasa sake tankawa padima maganar dasukai din sbd har lokacin shock din maganar Bata saketaba.
Padima ganin ankwana biyu NURU taki cewa komai gashi zuwa lokacin kowa ya shaida NURUn Bata cikin hayyacinta tana cikin tsananin tsoro da tashin hankali saidai anyi tambayar duniya taqi fada sai kuka.
Hankalin iyayensu yatashi sosai musamman da itama padima suka lura duk a firgice take ta bangare daya wankan haryanxu basuda masaniyar idan anzo NURU akewa sai gidan yakoma Kamar gidan da akai muguwar mutuwa sbd gabaki daya kowa baya cikin nutsuwa anyi anyi NURU tafada abindake damunta taqi fada sbd gabaki daya tsoro da firgicin abinda zaisamesu yasa ta kasa dawowa hayyacinta tsoron fadama takeji.
Yau dai padima da takaici da baqin ciki ya isheta sbd saura kwana goma sha biyu cikar wa'adin cikin tsakar dare ta tashi ta sake dauko wuqa yauma tadawo ta zauna tsakar dakin tareda fashewa da kuka yanda NURU zataji Dan dama tasan ba bacci takeba saigashi tana bude ido taga padiman ta daga wuqa zata sokawa kanta da gudu ta zaburo ta riqeta cikin tashin hankali tace"
Padima.
Qwace wuqar ta hau Yi padiman ta riqe cikin tsananin kuka take cewa"
Kibarni NURU gwara na mutu sai kowa ya huta matsalarmu da tsoronmu zai qare idan na kashe kaina shikenan Babu Wanda zaisan abinda nayi bare rayuwar abal da ammi tashiga hadari duk laifinane Dana Bari harnazo yanxu ban Kai qarshen matsalarba gashinan kema nasaki a damuwa bazan iya ganinki cikin damuwa da qunciba NURU sbd Ina tsananin sonki 'yar uwata.
Cikin hawaye NURU tace"
Bazaki iya ganinaba cikin qunci kike tunanin Ni zan iya ganin kin kashe kanki.
Zamewa tayi ta zube qasa tana rusa wani sabon kuka tace"
NURU komai ya lalace a rayuwata
Mutuwata itace salama agareku sbd matsalar ta wuce yanda kike tunani NURU cikine Dani yanxu haka...
Neman zubewa NURU keyi padiman tayi saurin riqota tana cewa"
Kingani ko gashinan kina neman sumewa sbd jin wannan muguwar masifa gwara na mutu kowa ya huta NURU kibarni kawai....
Kokuwa suka hau Yi akan saita dauki wuqar NURU na riqeta cikin tashin hankali take gabaki daya hankalinta yakasa dauka wai padima harta San bawa wani kanta,mutuncin,qimarta hadda ciki.
Zubewa tayi qasa tareda rushewa da wani irin kuka Wanda yasa padiman itama zubewa tana sakin nata kukan.
Kwana sukayi kuka Koda gari ya waye kowacce fuskarta da idanuwanta sunyi suntum ai Nan hankalin abal da ammi yatashi musamman dasukai tambayar duniya kowacce tayi shiru har Saida abal din ya harzuka yace aqyalesu koma menene idan sunji uwar Bari sunzo dakansu sufada itadai ammi hankalinta bai kwantaba taringa lallabarsu Amma ba wata mgn saima Kamar zurfafa da NURU keyi da tunani.
Jan padima NURU keyi Kamar wata qaramar yarinya harsuka isa inda tacewa amed su hadu suna zuwa kuwa Yana gurin NURU ta jefesa da kallon qyanqyami da baqin ciki take zuciyarta ta gaurayu da tsanarsa saidai Babu yanda ta iya tunda dole cikin biyu daya za'ayi dole shine zataji idan zai auri 'yar uwarta daya lalatawa rayuwa.
Wani abu ta hadiye me Kama da dutsi ta zuba Masa manyan fararen idanuwanta dasuka kusa gigitashi ya dauke Kai da sauri sbd wlh kallon cikin qwayar idanuwanta kawai na iya sumar dashi da duk wani ma'abocin begenta.
Ka yadda da Kaine kawai kasan padima amatsayin 'ya mace?
Da sauri ya gyada Kai Yana satar kallon padiman dake Masa wani kallo.
Sake jeho Masa qata tambayar tayi da cewa"
Kasan cewa tanada juna biyu yanzu haka a jikinta Wanda yake nakane?
Nasani Kuma ashirye nake da aurenta kafinma kowa yasan da akwai cikin Amma Kuma sbd zata zama negestati wannan al'amari yazama mafi hadari ga rayuwarmu mu duka hadda ta iyayenmu,
Wlh inason padima sosai itama tana Sona NURU Amma yanzu tsautsayi daya gitta mukai wannan abin yasa yazama Kamar wata mummunar qaddararmu da iyayenmu da basujib Basu ganiba..
Rintse ido NURU tayi wani nauyi na ziyartar zuciyarta idanuwanta sukai jajir tace"
Idan harka aminta zaka aureta shikenan kaje kashirya kawai.
Juyawa tayi tabar gurin idanuwanta na sake rinewa da tashin hankali ta nufi gida ko gabanta Bata gani sosai ta fada dakinsu ammi dake zaune tsakar gida tana gyarawa meryam gashi tabita da kallo zata miqe tabita saiga padima tashigo itama tafada dakin.
Rungume NURU tayi cikin tsananin farin ciki ba kunya tahau yimata kukan godiya NURU da baqin cikin al'amarin ya danne Mata zuciya tace"
Padima menene ribar wannan masifar dakika saka kanki damu aciki?
Shin bakiyi tunanin abinda zai faru da iyayenmu ba lokacinda Zaki bawa wani kanki?
Shin bakiyi tunanin wace rayuwace makomar nida meryam ba idan hukunci yahau kanki keda iyayenmu?
Menene laifin su abal dabasujiba Basu ganiba idan anhukuntasu akan laifin da Kika aikata bayan dawainiyar dasukai akanmu suka bamu tarbiya.
Riqota padima tayi cikin marairaicewa tace"
NURU nayi nadama nayi Dana Dani Kuma tunda kin amince da rufa min asiri ki sauyeni ai matsalar ta wuce......
Ta wuce?
Ta wuce fa kikace padima?
Cikine fa ajikinki na namijinda ba mijinki kike cewa shikenan yawuce.....
Qarar sakin kofin silba sukaje daga bakin qofa take suka juya da sauri cikin firgici ganin ammi hadda abal tsaye yasa padima fara rawar jiki cikin tsananin tashin hankali NURU kuwa zamewa tayi ta zaune al'amarin na isarta Sam kanta baya iya daukan doguwar pressure.
*************
_Jericho new York_
Setin akwatinanta guda biyar cif aka jera Mata cikin mota guda qirar Mercedes Benz beymach 10/2607 2021 ta fito daga bedroom dinta sanye cikin wata doguwar turkian royalle satin gown red me kyau wadda ta fidda kyanta da kyan jikinta hannunta riqeda handbag din arkins irin qamshin datake fitarwa me yawa zaisa kasake tabbatarda ta aje auren tun daga cikin dakinta Dan Vail din rigarma rolling dinsa tayi iya wuyanta tafara saukowa cikin yanayinta na yanga da aji kamar ko yaushe.
AFIA dake zaune Palo riqeda hannun farhat daketa kuka kamar ranta zai futa tana ganin fitowar mum din tasu ta miqe tsaye itama idanuwanta na fara tsiyayar hawaye tafara girgizawa mum din tasu Kai tana cewa"
Please no mum,
Mum please please no.
Itama lailar tanason 'yayanta tanason kasancewa dasu saidai tasan ko zatayi mushe ubayd maleek bazai barmata 'yayansaba Dan haka tunda tasan zasu samu kyakkyawar rayuwa tareda dad dinsu bazata wani damuba ta qaraso ta rungumesu suka qanqameta suna kuka sosai suna roqonta sai Basu hkr takeyi tana cewa"
Zakuyi alfahari da mum dinki idan kukaga tazama cikin top 20s Inshallah.
Zamewa tayi zata wuce farhat ta maqalqaleta tana sakin sabon kuka cikin firgici tana Kiran sunanta.
Ganin haka hankalin afia yatashi taga mum din dagaske tafiya zatayi batasan yazatayi ta hanata tafiya ba batada zabin daya wuce takira _NEGES MUHAMMAD KALEEB DELAH_ asalin kakan dad dinta, tsohon NEGES(sarki) Wanda shine mafi soyuwa da shaquwa agurin dad dinsu sbd shine ya riqesa tun yarinyarsa sbd mahaifinsa dashine yakama yazama sarkin yanxu ya rasu sai qaninsa ya hau bayan an aura Masa mahaifiyarsa Wanda haryanxu shine asalin sarkin delah gizah na yanxu mahaifiyarsa Kuma sarauniyar delah gizah hakan yasa kakansa shine mafi kusanci dashi arayuwarsa danma shine ya tsaya Masa aka taka dokar mulki yabari ya auri LAILAH OMAR masoyiyarsa dasukai karatu tare 'yar asalin ghana dasuka hadu a San Francisco.
Duk da ba wani yabawa KALEEB yayi da LAILAH ba Amma sbd farin cikin ubayd yasashi amincewa yakuma rufe idonsa ya taka doka Dan haka yakeda burin qarawa ubayd maleek Mata Amma ubayd Yana qaidojin rayuwarsa Dan haka abin be yiyuba.
Akwai lokutan da ba'a Kiran KALEEB kaman dad dinta dashima akwai lokacinda ba'a kiransa Amma yau dole zata kirasa sbd shikadaine zai Hana wannan rabuwar sbd iyayen nata Babu Wanda ya tsaya ya saurareta.
Cikin sa'a Kira biyu a na uku aka daga cikin sauri tayi bayanin ita wacece tanason mgn da KALEEB sanin matsayin UBAYD da iyalansa agurin KALEEB yasa aka Kai Masa wayar cikin girmamawa aka miqa Masa ya karba sbd sanin ba'a kawo Masa waya sai me mahimmanci idan bashi yace akawoba.
Tanajin nutsatsiyar muryar Kaleb ta nutsu jikinta na rawa zata fara Masa bayani taji durin motar dad dinta yadawo Wanda yasa gabanta faduwa.
A nutse ya zuro dogayen qafafuwansa dake sanye cikin black brian Atwood brand loafers kafin yafito gabaki dayansa cikin Ralph Lauren brown suit data fiddo da dukkanin hasken fatarsa ta asalin amhara ethopiano.
Kallo daya zakai Masa kasan shine ya haifi AFIA sbd Kamar dasukeyi tayi yawa duk da Kamar yanda bazakace LAILAH ce ta haifi budurwa kamar afia ba haka Kai tsaye Shima bazakace shine ya aje budurwar 'ya ba sbd kyawun jikinsa da dukda yafara girma bai rabu da geamin ba ma'ana motsa jiki uwa uba ajinsa da asalin kyawunsa tareda izzarsa datake cikin jininsa da har gobe fresh take zamar masa Dan ko ita lailar har gobe duk gayunta da kyanta da Jan ajinta Rena kanta take agabansa shiyasa har gobe take kishin tazama wadda zata tsayu da kanta duniya tasanta da sunanta bada sunan waniba.
Ciki ya nufo qanshinsa na sauya atmosphere din gidan afia na ganin hakan tafara fadawa Kaleb abinda yake faruwa cikin nutsuwa da sauri....
Daidai shigowarsa farhat tasaki Laila tayo kansa da gudu ta fada jikinsa tana sakin sabon kuka Wanda yasashi sake tsuke fuskarsa tsaf wadda tasa Laila dauke Kai daga kallonsa ta nufi qofa zata fita baice Mata qala ba hakama AFIA qafafun lailan dasuka fita ta qurawa ido daidai Kaleb yagama jin komai zaiyi mgn sukaji daddadar muryar dad dinta data ratsa har cikin wayar zuwa kunnen Kaleb yace"
Na datse igiyan aurena dake kanki na sake ki you're free to go MSS LAILAH OMAR.
Dif afia ta dauke wuta cikin tsananin tashin hankalin jin abinda dad dinta yafada Kamar daga sama taji muryar Kaleb cikin ikonsa na tsohon sarki yace"
Ki dakatar da ita injini.
Muryarta na rawa idanuwanta na dishi dishi tace"
Mum Kaleb yace ki tsaya karki tafi Injishi.
Qin juyowa tayi bayan Sarai taji me afia tace saidai bazata iyaba ta daga qafafunta ta isa bakin mota aka bude Mata tashige suna kallo ta tafiyarta idanuwanta na cikowa da hawaye ta maida tana qoqarin kawarda abinda yake taso Mata saidai takasa Saida ta fashe da qaramin kuka tana rufe fuskarta da hannuwanta har suka fice daga qatuwar harabar gidan.
Murya na rawa cikeda firgici afia tace"
Kaleb Ta fita,ta tafi tabarmu.
Wani numfashi Kaleb ya sauke akaro na farko a tarihin rayuwarsa da wani ya bijire Masa Kai tsaye Kamar agaban idonsa Wanda shikansa ubayd hakan yasa dukkanin wata sauran kaunar Laila yaqarasa fice Masa daga zuciya har abada.
Cikin wata irin murya me babban sauti Kaleb yace"
Ki sanarwa da mahaifinki Ina buqatar ganinsa cikin gaggawa zuwa delah.
#MAMUH#
0 comments:
Post a Comment