Wayarta dake k'ara ta zaro Maryam ce ta d'anyi murmushi tareda d'agawa "ya akayine besty?"
"Yau Kuma yada makara beaty malamin nan fa kinsan bashi da kirki kuma gashi saura 10 min mushiga kuma kinsan Koda 1min ya rigaki bazai bari ki ahigaba" cikin damuwa tace "ganinan besty"
"Wai kina ina need?"
"Zan fad'a Miki idan na shigo"
"To kiyi sauri dan Allah"
"Insaha Allah"
Tana kashe wayar yana k'arasowa yana duba agogon hannunsa ta wani kalleshi tayi kicin kicin da rai, murmushi ya d'an yi batare da yace komaiba ya tada motar lokacin da suka isa tuni malamin ya fara da kusan 10 yana faking tace " maidani gida"
Kallonta yai da son k'arin bayani tayi masifar had'e rai tace "to meye amfanin barina tunda anriga an shiga kuma malamin baya barin kowa ya shiga muddun ya riga ka shiga" ta fad'a tareda zubowar hawaye sai da ya d'an kalleta na kusan 7 second kafin yama hannunta har department d'in nasu yayi sallama abakin hall d'in wanda ya lek'o ne yasa MD rik'e baki yace "kana ruwa yaro dama Kaine kake furgita mana kanne haka?"
Shima da mamakin yace "MD kana duniya gaskiya bamuda kirki zumunci yayi karanci me yafaru kake cewa ina firgita muku k'anne?" Maryam MD ya nuno masa "na d'an biya da ita office amsar wani muhimmin sak'o ina ajeta ta fashe min da kuka wai na maidata gida kariga ka shiga" dariya m Bash yayi yace
"Yarran ne koya sukaga wallenka sai su rainaka" ya fad'a yana dosar inda Maryam take yayin da MD ya biyoshi yana magana a waya.
Da sauri Maryam ta d'an russuna tace "good morning sir" ga mamakinta taji yace morning dear how fa maza wuce aji karki k'ara biyewa wannan yayanki ya makarar dake" ya fad'a bayan ya tambayi ya take batareda ya bari ta bashi amsa ba da alama yadda yai maganar akwai sanayya tsakaninsu da yayannata.
Da sauri ta doshi ajin inda ta hango Maryam tana ta faman lek'e ta window ta d'an kai mata dundu tace "me kike nema haka kamar zaki tsinka wuya tsabar lek'e?"
Ajiyar zuciya Maryam ta saki tace "ya akai yabarki kika shigo?"
"Uhm bross nefa ya makarar dani yana direni nasa masa kuka""""" nan ta kwashe yadda sukayi ta fad'a mata.
Bayan sun fito a lacca ne Maryam ta d'an dubi k'awar tata tace "besty yau ni naga masifa da tashin hankali ganin ido na,kai soja bala I ne wallahi besty"
"To yau kuma me ya had'aku keda sojan naki nasan dai dashi kike wannan maganar"
"Uhm besty wai ashe jiyan nan da muna hospital bross turowa yayi aka kama d boy karki ga yadda yasa yaransa suka mai dashi wallahi sai da nayi kuka"
"Ke banza ce wallahi besty mutum yayi miki irin wannan yarfin dan an bi miki hakkin ki shine har zai baki tausayi? bakisan d boy ba' bakisan waye shiba wallahi da bross bai masa hakaba ya rik'a tunda yaga yayi na farko yaji dad'i haka halinsa yake"
Ajiyan zuciya ta sauke tace Allah ya kyauta,yauwa dear kikace Abba yana harkan dillancin gidaje ko?"
"Eh me yafaru?"
"Gida nake son siya besty"
" Ke kuwa besty duk yawan gidajen ku me zakiyi da wani gidan?"
"Bakiji me kikace ba beaty a maganar ki, kinsaka jimlar ku nawa ni kad'ai nakeso"
"To shikenan kamar yaushe kike buk'ata sai muje"
"Ki kira wayarsa idan da dama mu wuce daga nan idan babu damuwa tunda Kinga yanzun bamu da wata lacca"
"Yadda Kika ce besty hakan za ayi"
Daga nan direct unguwar su Maryam dake tayima Abbanta waya ya dawo yana jiransu sai da suka fara gaida mamanta kafin tayi mata iso har d'akin Abbanta sosai kwarjinin sa yaima Maryam dan daka ganshi kaga kamilin mutum mai cikar Kamala da mutuntaka bayan sun gaisa Maryam ta fita ta basu waje.
Kallonta malam Abdullah yace "yarinya me sunan kine?"
Tace "sunana Maryam Abba murmushi Abba yayi yace "d'iya tace ashe" itama murmushin ta saki wanda ya k'ara mata kyau.
"Maryam tace kina son ganina Allah yasa lafiya?"
"Eh Abba lfy dama ina son siyen gidane to shine nakema Maryam magana tace kana harkar gidaje"
Kallonta Abban Maryam yayi na d'an lokaci yana nazarinta sannan yace"ke yar waye ne 'yata?"
"Baffa Abubakar" ta fad'a atakaice sosai ya jinjina take mamakin yadda akai tasamu k'udi ya d'auke tunda yanajin irin labarin jita jita cewa yarinyar tana mugun b'arin k'udi sannan akwaita da kyautar girma irin na mahaifinta sannan ansakar musu k'udi suyi yadda suke so, kasancewar su Kennan yaransa.
Kallonsa ya mayar kanta yace "to 'yata kamar wanne kike buk'ata?"
Abba na baka zab'i mai kyau nake so wanda bai gaza 7 million ba" da mamaki yake kallonta kafin yace "shikenan 'yata insha Allah zanyi miki kamar yadda zanyiwa Maryam" daga haka Maryam ta bashi dubu goma tace "Abba ga wannan ayi cefane"
Da k'yar tasamu ya karb'a dan shi d'in ba irin masu zarmewar zuciya bane.
Ba a wani dad'e ya samo mata gida mai kyau aka yi ciniki ta biya batareda sanin kowa nataba tabar komai awajen Abban aminiyar tata.
Tunda ga ranan dataganta da wasu 'yan k'udi masu nauyi sai tasai abinda tasan duk lokacin data tashi zata siyar ta samu k'udinta.
Shin wai duk meye dalilinta nayin hakan muje zuwa daga
'yar mutan YAKASAI
MAMAN Islam CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 21
Haka tacigaba da karatunta cikin nutsuwa tun tana tunanin maganganun maman har tasaba ta daina saka abun aranta amma hakan baisa ta daina siyan muhimman abubuwaba aduk lokacin data ganta da wasu 'yan k'udi masu nauyi, yayinda wani irin shak'uwa mai ban mamaki ya shiga tsakaninsu da name sake d'inta dan haka bata da aminan daya wuce Maryam da Halima.
Abangaren d boy kuwa da farko saida yaci alwashin d'aukan fansa Abban sa ya taka masa burki yace"kul dan ubanka karkaja min mutuwa kwanana basu K'are ba wannan yaron da kake ganinshi bashi da ruwan mutunci ko kadan dan iskane nake bafad'a maka nagaban kwatance dan haka ka nisanci wannan yarinyar domin ba 'yar kowa bace face'yar Baffa Abubakar"
Saida d boy ya razana dajin abinda Abban nasa yace domin kaf yankin nasu babu wanda baisan waye Baffa Abubakar ba saboda tarin dukiyar da Allah ya hore masa da d'umin karamcin sa ga bayin Allah, sannan agefe guda yasha mamakin yadda take rok'on yayanta da ya k'yale shi haka duk da yadda ake fad'an rashin mutuncin yarinyar take yaji duk wani burinsa akan d'aukan fansa ya ruguje saima k'ok'arin son kulla alak'a da ita.
Agidan su Maryam kuwa babu abinda ya sauya sai tsarin yawon inda yanzun haj. Zakiyya ce take zaryan zuwar musu wanda idan suka shige d'aka har mantawa ake dasu dakehaj. Amina babu ruwanta da ahiga abinda babu ruwanta bata tab'a sanin wainar da suke toyawaba.
Yayin da MD ya diga ayar tambaya akan wannan ziyarar takawar wannan matar mara yankewa hakan yasa batareda da sanin kowa ba ya nemo CCTV camera saida yabari ranan sun fita gantalin bin malamansu da suka saba yasa aka jona aka saita komai tareda recording d'in duk abinda zai rik'a faruwa akaf gidan ta ko ina har d'akin Ammey batare datasan anyi hakanba.
Rannan MD ya kawota makaranta dake sauri yake abakin get ya sauketa sannan yace idan lokacin tashinsu yayi ta fad'a masa zaisa driver ya maidata gida yau yana da wani meeting wanda sai dare yake tunanin zasu dawo k'ala batace masaba kuma dama yasan basatace d'in ba, bai jira komaiba yaja motarsa da azabar gudu yabar wajen.
A hankali tafara takawa zuwa bakin get d'in tunda tafara zuwa makarantar shekara d'aya kenan da d'an wani abun bai tab'a ajeta anan d'in ba sai yau, ta kusa kaiwa bakin k'ofar kamar yadda ta saba koda yaushe sai ya kaita har parking space na makarantar sannan zai ajeta ya juya.
"Hey hey" taji muryan wanda bazata tab'a mantawa ba arayuwarta domin shine mutum na farko da babu wanda ya tab'a yi mata irin tozarcin da yayi mata, batasan lokacin data saki wani matsiyacin tsaki ba ta juya yayin da shi kuma yayi saurin shan gabanta da motarsa, a mugun fusace ta d'ago ta watsa masa wani mugun kallo sanda yake fitowa daga cikin motar.
Yana k'arasowa bata bari ya fad'a mata wani abuba tayi saurin cewa "wai kai wane irin mutum ne mara tunani wanda baisan darajan kansaba bare na waninsa?
Yau kuma takeni kake sonyi komai?
Wai dan Allah me yasa wasu mutanen baau da tunani ne kwakwalwarsu irin na kifine?
Yo inba hakaba ni banga dalilin gamin kifi da gada ba dazaka wani zo ka shamin gaba ina cikin tafiyana idan kuma hukuncin farko ne bai ishekaba akwai wanda sukafi wannan sai ka jira.
Duk abinda take fad'a bai katsetaba saida yabari tagama maganar ta kafin yace 'Amincin Allah yatabbata ga sarauniya kuma shugabar masu yafiya, ba wani abune yasa na tareki anan ba sai dan na k'ara neman yafiyarki abisa abinda ya faru duk da nasan cewa saboda ke wannan boss d'in yayan naki ya k'yale ni amma duk da haka ina mai kara neman afuwarki na miki alk'awarin ko kallon banza bazai k'ara had'a ni dakeba pls pls pls" ya rik'a maimaitawa yayin da tayi masifar d'auke kanta ta juya da nufin bar Masa wajen batasan ya akayiba sai kawai ganinsa tayi zube agabanta basa gwaiwoyinsa yana cigaba da rok'on yafiyar ta bai ko damu da yadda mutane suka fara taruwa awajen ba.
Zaro idanu tayi ganin yadda ya zube saman gwaiwoyinsa ga mutane da abin kallo baya musu kad'an har sun fara taruwa awajen tayi saurin cewa "meye haka dan Allah jifa har an fara taruwa anan katashi"
"Ni ba damuwana masu kallona ba damuwana kawai kice kin yafemin"
"Tashi dan Allah" ta fad'a cikin sanyin murya "zantashi ne kawai idan kince kin yafemin"
"Na yafe maka amma bisa wani sharad'i to tashi" tasake fad'a can k'asan mak'oshi da sauri ya tashi yana fad'in"na gode na gode sosai ko wane irin sharad'i ne ki fad'a na miki alk'awarin tunda dai kin yafemin" fad'a yana binta lokacin data fara takawa cikin makarantar,bayan yabawa d'aya daga cikin abokansa mukullin motarsa suna takawa a hankali yayin da ta fara ce masa.
"Gaskiya yakamata ka gyara halinka da d'abi unka ba abune me kyau ba kowa ya rik'a maka shaidar baka da mutunci babu wanda ka ragawa har akai ga matakin da kowa zai fara jin tsoronka sam wannan zalunci ne babba dan Allah ka gyara kaga ni d'innan dakake gani duk abinda kake ji dashi nafika ko ranan ma shammata na kayi banda haka bazakayi nasara akainaba sai dai ni bana shiga harkan wanda bai shiga nawaba dan haka kaga ko makarantar nan banda kawa sai A A"
"Nasani sam ban kyautaba kuma na miki alk'awari insha Allah daga yau nima babu ruwana da sabgar kowa"
" Allah yasa" ta fad'a atakaice tana wucewa department d'insa.
Yana tsaye har ta shige murya k'asa k'asa yace "tamin Allah yasa tasoni nidai tamin badan komai ba sai dan nutsuwa da ajinta Abba kayi suruka irin wacce kake so 'yar wani wanin ma wanda yai suna aciki da wajen k'asar nan"
(Su Kamal d boy daga sannu sarkin fawa lol🤣🤣🤣)
Yau kam da wuri suka koma gida dake lacca d'aya ke garesu suna gamawa babu wani jinkiri Maryam ta nemi da A A ta rakata banki tana son bud'e sabon account, da mamaki AA take dubanta kafin tace "ke kuwa name sake duk yawan asusanku wanda ba ayi miki iyaka dasuba sai kin bud'a wani?"
Bazaki gane bane sam mama bata barina da k'udi ita zata bani kuma ita zata dawo ta rance na rasa abinda mama take da k'udi duk yawan kyauta irin na Baffan mu wallahi A A Saida mama ta kureshi" haka dai suka tafi tana bata bad habits d'in mamanta wanda abin yake masifar damunta ta kuma rasa dawa zata zanta taji sanyi saifa yanzun dataji ta aminta da ita.
Har sukaje suka bud'e account kud'ad'en da Maryam ta zuba a account d'in saida abin ya bata tsoro yayin da Maryam ta dinga mata dariya daganan tace Maryam ta rakata kasuwa zatayi siyayya sai da suka fara zuwa tasiyi kayan kwalliya da turarukanta dake Maryam mayyar turarece zai wuya ka kusance takaji bata k'amshi domin ita d'in 'yar gayuce tagaban kwatance hakan yasa take da masifar farin jini Saidai halinta bai barinta shiga sabgar mutane domin bata da kirki ko kad'an.
Daga nan Kuma suka nufi wajen masu saida kayan abinci A A taga Maryam ta d'auki babban buhu na shinkafa da k'arami sannan ta d'auki taliya carton biyu haka makaroni da cous cous da semonvita irin buhunnan mai guda sha biyu shima guda biyu manja man gyad'a Maggi kanshi saida ta d'auki carton guda banda sauran spacies data d'iba ita dai A A kasa daurewa tayi tace "name sake nasandai abincin gidanku trela ake kawoshi me zakiyi da wannan abin da kike ta loda?"
"Ba damuwarki bane" cewar Maryam datakewa mai shinkafar maganan ko zasu samu motar da zai kwashe musu dukan kayan? dan adaidaita yayi musu kad'an.
"Akwai 'yar k'ur k'ura wanda shi dama aikinsu Kennan d'iban kaya sukai maka duk inda kakeso' ya fad'a yana kwalawa wani kira.
Tun tambayar da tayi mata tace ba damuwanta bane bata k'ara tofa nataba abinda ya Kuma d'aure mata kai shine ganin motar bai faka ko ina ba sai k'ofar gidansu da mugun mamaki ta rik'a kallon Maryam wacce ta d'auke kanta batare data bari sun had'a ido ba.
Suna tsaye har aka gama shiga da kayan abinci sannan ta sallami mai motar suka bi mai d'aukan kayan na k'arshe, shima ta sallame shi yayinda suna shiga suka tadda Umma da Abban Maryam da shima shigowarsa Kennan gidan aka fara shiga da kayan daya fara tunanin ko b'atan kai masu kai kayan sukayi amma yana ganin Maryam da Maryam sun shigo ya dingabinsu da kallo fuskarshi da alaman tambaya.
" Ku zauna mana Abba"
Maryam ta fad'a tana zaran buta tayi bayan gida, sam Maryam batada k'yamar mutane musamman inkana da tsabta dake it's mutum ce mai tsananin tsabta da k'yamar k'azanta, tana fitowa tayi alwala tayi d'akin Umman su A A ganin haka yasa itama Maryam tayi alwalar tabita d'akin.
Tana fitowa tanemi waje ta zauna tana gaida Umma da Abban kafin ta kalli Umman tace "nifa yunwa nake ji Umma yau bross ko kari bai bari nayi agidaba wai ya makara a office"
Kallon mijin nata tayi yayin da yayi mata alamar data bata abinda suke dashi,shi kuma ya saka takalmansa yayi waje Umma Kuma ta nufi kicin ta kawowa Maryam wake da shinkafar da suka dafa da salak da tumatur da cocomber, ta aje mata ta koma domin kawo mata ruwa sai ga Abba ya shigo da ruwan roba da lemo harda dafaffen kwai tunda yasan me aka dafa agidan.
Sam bata wani nuna bak'unta ba taja abincin taci ta k'osh har tana santi ita kam Maryam zuba mata ido tayi tana kallonta batareda data iya cewa uffan ba saida ta gama ta wanko hannunta ta dawo tasha lemon da ruwa sannan tace.
"Abba wannan kayan abincin nakane kai na siyowa dan Allah Abba kada ka k'ara zuwa kayi dako insha Allah idan Baffana ya dawo zansa yabaka jari ka fara business kaima insha Allah Allah zai dafa maka"
Rasa bakin magana Abba da Umma sukayi suka rik'a kallon Maryam da tsabar mamaki dama Maryam taji sanda yake cewa saida yai dako ranan sannan ya samo musu abinda zasuci?
Sosai Abba ya gode mata sannan yayi mata fad'an abin yayi mugun yawa tace "Abba wannan ba komai bane akan idan da ace Baffana na fad'a wa shi ya doramu akan wannan tsarin nida 'yan uwana" addu'ar da Abban Maryam ya rik'a yiwa Maryam da zuri arta harsaida yasata hawayen farin ciki itama.
Sai bayan la asar ta baro gidan ta kamo hanyar nasu gidan dake suna da tazara sosai sai yamma ta dawo maimakon Kuma ta shiga gida sai kawai ta shige gidansu MM wani class mate d'inta wanda har yau suna mutunci dashi kasancewar su unguwa d'aya.
MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 22
Bata zauna ba data tadda jm bayanan nayi b'ata last page jm zance na manta nace mm, tana zuwa bakin get taji mai gadi yana cewa "gatanan yallab'ai" MD daya gama rud'a driver da bala i saboda kawai yace tun biyu saura su Maryam suka bar makaranta kuma alhalin ba ama turashi ba sai wajen biyar saura shine fa MD ya hana shi sakat da masifa sai da ya koma makarantar har sau biyu.
Sannan kuma Ammey ta tabbatar masa da cewa tun fitar da sukayi tare bata dawoba amma kar ya damu wannan ba komai bane a wajen su dan takan fi hakama awaje, sosai ransa ya b'aci da jin abinda Ammeyn ta fad'a masa ya fito Kennan cikin wannan halin mai gadi da ba shine driver ba da ya had'a ya hasu sakat yace ga Maryam d'in nann
Duk zubawa get d'in ido sukayi yayin da Maryam ta shigo hankalin ta kwance babu wani damuwa tattare da ita, tana tafe cikin nutsuwar da Koda yaushe ka ganta zaka ganta tattare da ita.
Ran MD ne yai mugun b'aci cikin bak'in ciki ya k'arasa inda take wato shi yana nan hankali tashe ita Kuma tana can yawon gantalin ta hankalin ta kwance' wata irin fincika yayi Mata da mugun k'arfi har saida ta saki k'aran azaba, jakarta da wayarta sukayi nasu waje yayin tayi taga taga zata fad'i yayi saurin tareta ta fad'a jikinsa.
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke jin ta cikin jikinshi take ya ji wani irin abu ya tsarga masa tundaga tsakiyar kansa har zuwa babbar yatsarsa ta k'afa.
Ita kam Maryam wani irin takaicin jinta ajikinsa ne ya kamata batasan sanda hawaye ya sulalo mata ba saboda bak'in ciki kwace jikinta tayi daga nasa tace murya k'asa k'asa "ban yafe ba d'an iska kawai aidama Halima tace duk wanda yake irin aikinka to manemin mata ne anje neman na bariki ba asamuba shine akazo latsa k'anwa dan abin kunya tur" ta fad'a tare da fashewa da kuka.
Tunda ta juya tabar shi nan tsaye yake cikin suyar ran kalamanta tunda yake babu wanda ya tab'a fad'a masa maganar daya k'untata masa irin yau ba,amma sosai abin ya rik'a sukar k'irjinsa temakon da Allah yayi masa cikin rad'a tayi masa duk wannan wulak'ancin da cin fuskar.
Sai dai hakan baisaka yajanye alk'awarin da yayiwa Baffa da Ammey ba yayi musu alk'awarin zai ja Maryam ajikinsa yanda zasuyi sabon da duk abinda zaisa ta bazata tab'a Musa masaba ta hakane Ammey take ganin zasu samu hanyar gyarawa Maryam zama.
Bayan an idar da sallar issha suna d'akinta ita da Nassar tana tayashi assignment d'in da yazo dashi saiga sallamar shi abakin k'ofar ba k'aramin fad'uwar gaba ta tsinci kanta aciki ba d'azu bayan tagama masa fitsaran ta dawo d'akin tace sam saitaga bata kyauta masa ba kome ya mata ya kamata yaci darajan shi na d'an uwanta JININTA.
Bata samu damar amsa masa ba sai Nassar ne ya amsa masa ya k'araso gefen da take ya zauna daf da ita tanaji Nassar yana gaidashi takasa had'a ido dashi bare wani gaisuwa ya had'asu.
"Nine d'an iska mai bin mata ko?"
Ya tambaye ta cikin wani irin murya mai kashe jiki wanda hakan yasata jin wani irin babu dad'i "kayi hak'uri bross dan Allah" maganar ya kwace mata batare data shiryawa hakan ba.
Sosai ya kafeta da idonsa wanda sukayi wani irin kyalli saboda kwallan daya cikasu, tunda yake babu wanda ya tab'a gasa masa bak'ar magana irin nata.
Jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago idanunta dake duk'e kan littafin Nassar daya jima da ficewa daga d'akin,ba k'aramin fad'uwa gabanta yayiba ganin kwallan daya ciki idanunsa sai dai bai basu damar zubowaba saboda nayasan taga logonsa amma maganar gaskiya yaji zafin maganar ta ainun wanda dama dan yaji zafin tayi masa.
Rasa yadda zatayi masa wani maganar tayi sai kawai ta fashe masa da kuka wanda zan iya kiransa da kukan shagwab'a, take ya k'arasa zaman durshen agabanta tareda kamo hannunta yace "haba k'anwarta me kuma nayi miki banfa yi miki ko mai ba" ya k'arasa maganar cikin rawar murya domin har ga Allah jiyai kukan yana mugun tab'a masa zuciya.
"Kayi hak'uri" ta k'ara fad'a masa cikin muryan kuka "nayi" yafad'a mata da sauri cikin rawan murya sannan ya d'an dubeta yace "k'anwata na miki wani tambaya mana amma ina son dan Allah ki fadamin gaskiya tsakaninki da Allah"
"To" kawai tace masa tana faman goge hawayen da suke zubo mata har lokacin "to ki daina kukan haka mana dan Allah kinji" yafad'a yana share mata hawayen data rasa dalilin k'in tsayawarsu.
"Wai me yasa kika tsaneni ne?"
Yayi mata tambayar dayafi komai ci masa rai tun ranan data furta masa ta tsanesa har yau baidaina jin amsa kuwwar abin cikin kunnen saba sosai abin ya tab'a shi.
"Ai nima baka sona nida mama ka tsanemu kafi son Nassar da Ammey kanawa mama rashin kunya agabana baka dukan Nassar agaban Ammey amma ni kamar jaka haka kake jubgata ko dan kaga Nassar d'an d'akinku shiyasa ni kake nuna min 'yan ubanci" ta fad'a cikin zubowar sabon hawaye, maganar ta na k'arshe ya mugun bashi tausayi har baisan sanda yasa hannu yajata jikinsa ba kamar jira take kuwa ta fad'a tareda sakin kuka irin mai cin rannan.
Dagajin yanda take kukan yasan akwai abinda yake damunta wanda ta barshi aranta takasa fad'uwa kowa, saida yabari ta d'an yi kukan da d'an yawa kafin ya soma d'an bubbuga bayanta har saida yasamu tayi shru da k'yar.
"Me yasaka ki kuka?" ya tambaye ta cikin sanyin murya, "ku kullum Ammeynku tana tareda ku tana kulawa daku duk abinda kukeso tanayi muku bata yawan fita unguwa bare tabarku cikin kad'aici, amma ni kullum mamana tana gidan k'awarta haj. Zakiyya danayi magana sai tabani k'udi ko tace bari ta had'a min wani d'an party bathday d'ina kuwa ko manta date d'in batayi dan Allah bross k'udi ne yake maganin ko wane matsala?"
Ta K'are maganan da tambayar abinda yake matuk'ar damun ranta,
"A a" yabata amsa cikin tausaya mata domin shima ya fahimci wannan abun yafara damunta hakan kuma ba k'aramin dad'i yayi masa a rai ba ko babu komai tunkafin ya fara tunanin hanyar da zaibi dan shan kanta ta yadda zajata jikinsa su kulle har akai ga maganar da ake son k'ullawa wacce babu wanda yasani dagashi sai Baffa sai kuma Ammey da Baffan yake jin tana da hak'k'i akan tasan komai.
"Amma Maryam bamune muka tsaneki ba kece Kika tsanemu bakya mutantamu da Ammeynmu ko kad'an har zaginta fa kikeyi taya kike tunanin zamu mutuntaki bayan bakya mutanta mana mahaifiyar mu?"
K'are maganar dayi mata tambayar wanda nan take ta gano kuskurenta amma Kuma sai tace "ai mama tace kada nasake nayi sabo da 'yan uba dan muddun nace zan dinga mu amalantar ku to babu abinda zaisa baku kashe niba tunda Kuna ganin agabanku Baffa yake nuna yafi k'aunata akan ku, kuma tace Ammey muguwace tun ina jaririya taso kashe mata ni kuma tace Ammey ce take asiri take had'a ta fad'a da Baffa shiyasa kullum yake mata fad'a baya bata k'udi saidai inya ajiye ta turani d'akin sa na d'ebo mata mai yawa amma baya isarta saita had'a danawa.
Tsabar tashin hankalin jin wannan mugun zantukan baisan sanda ya zube ak'asan wajen yace "maman?"
Yafad'a gamida zaro ido har saida yanayin sa ya mugun tsoratata.
Pls manage data taku har kullum
MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Wannan shafin nakune gaba d'aya kuyi yadda kuke so
MUHAMMAD KAREEM
HAYATU BABA ZUBAIRU (YAYA HAYAT)
ITS ABBAS
Allah yabar kauna
Page 23
Jikinta take ya hau rawa tace "wa lla hi haka tace min, shi yasa kaga nima bana son Ammeynku.
Kasa magana yayi da hannunta da ya kama ya rik'e gam cikin nashi, idanunsa kuwa kad'awa su kayi suka yi wani irin ja,
Me wannan matar take nufi?
Takasa kula da amanar data dauka, Kuma tana son raba hanta da jini wannan ba adalci bane, zalunci ne babba, ke baki kula da yarinya ba, sai ma d'ora ta da kikayi akan wata turba mara b'ullewa.
"Zaki abota dani?"
Ta tsinci muryarsa cikin wani irin yanayi batasan lokacin data d'ago kai ta dubeshi ba sai dai bata iya tace masa komai ba ganin yadda ya kafeta da runannun idanunsa
"Uhm?"
Ya k'ara tambayar ta again babu amsa sai faman murza idanunta take da d'aya hannun da bai rik'e ba.
"Kema Ammey mamanki ce, ta tsinci muryar shi yana rad'a mata a kunne daga yau zamu rik'a shiga d'akin ta muna hira tare dake, kuma kema duk abinda kike so ki tambaye ta zata baki, kuma tama fi sonki damu idan kina musu ki gwada".
Ya fad'a yana cigaba da murza hannunta dake cikin nasa.
"Mama bazata barni ba ta tsaneku" ta fad'i abinda tasan kullum maman tana tusashi agabanta, wanda tasan hakanne har cikin ranta.
"Ai bazata sani ba saboda kinga kullum bata zaman, gida Kinga kafin ta dawo munyi hiranmu, bawai ki rik'a shigowa d'aki, ke kad'ai ba, Kinga tunani sai ya miki yawa"
Ya fad'a yana kallon ta, tabbas abinda ta fad'a gaskiya ne, tunani yana damun sosai wani lokacin har sha daya mama tana kaiwa agidan hajiya zakiyya.
Shi kam zama ya gyara tareda zuba tagumi ya kafeta da idanunsa, yayin da tausayin ta ya game mai jiki,yana mai jin haushin kansa, na yadda tun farko bai jata a jikin sa ba bare har yasan damuwar ta.
"Zaki iya abota dani inzama amininki wanda zaki dinga fad'awa dukkan wani damuwar ki wanda zai dinga magance miki duk wani matsalar ki da yardan ubangiji?".
Ya sake mata tabayan shi na farko,
"Idan mama tagan mu tare akwai matsala" ta fad'a masa haka, matsayin ta na wacce tafi kowa kusanci da mama dan haka tafi kowa sanin halinta.
"Karki damu Baffa bazai bata damar raba masa kanmu ba, kinsan burin ko wanne ubane ya ga kan yaransa ya had'u" ya fad'a yana d'ago hab'ar ta yana kallon, cikin idonta.
"Shi kenan na amince ta fad'a cikin sanyin murya"
Ihun murna ya saki tareda rungumeta"na gode my happiness na gode my Lovely sis dan Allah daga yau ki daina wannan had'e min ran baya min dad'i"
Ya fad'a mata a hankali "to" tace masa daga haka ta maida hankalinta kan aikin da suke da Nassar, tayata yayi suka gama aikin, daga haka ya rik'a janta da hira.
Waahegari motar ta ya iso, motar da Baffa yace bata gift idan taci jarrabawa, tun tana maganar motan har sai datayi fushi ta daina maganan bata san cewa mak'alewar motar daga MD bane shi ya hana saboda rawan kanta, yanzun ma sai yana yi yana sa mata ido sosai.
Washe gari kuwa tun kafin ya fito tuni ta shirya ta bar gidan a sabuwar motan ta sai da ya fito yaga Abdul Nassar yana shiga cikin motar da yake kaishi makaranta.
"Kai ina Adda?" Nassar ya tambaye shi "tab'Adda yanzun ai ta jima a schl, kasan cewa tayi bari tayi sauri ta tafi kar ka fito ka hanata kace Kai zaka kaita".
Murmushi MD yayi Yana shafin sumar kanshi daya sha gyara, daga haka ya juya ya shiga motarsa security d'insa yaja shi suka wuce.
Uhm su o o anyi abun kai yaushe rabon duniya tunda bross ya dawo ya hanata sakat hatta motar mama da take hawa sai da ya hana ta k'arfin bala i, dan haka yau take jinta cikin wani irin farin ciki.
Tunda ta doshi cikin makarantar ido ya koma kanta domin motar tayi mugun d'aukar hankalin mutane, da yawan su basuyi mamakin ganin wacce ta fito daga motar ba domin ansan tafi k'arfin, wacce ta ninninka wannan ma, dan da yawa wasu suna mamakin yadda bata da motar kanta sai dai akawo ta.
Maryam kuwa da gudu tazo ta rungumeta tace "eye had'uwa ta iso kenan" ta fad'a tare da k'arasawa tana shafa motar, wani k'awata taccen murmushi Maryam ta saki tace "humm kinga wannan bross d'in namu sai a hankali, nasan wallahi shiya hana akawo min motar amma Baffa yafi shekara da biyan k'udinta"
Itama murmushin tasaki "ina ganin akwai wani abu tsakaninki da bross d'in nan"
"Kamar ya?
"Kamar yadda na gani bross sonki yake Maryam"
Manyan ta bata amsa
"Humm baki da hankali kin tab'a ganin inda akayi aure uba daya shifa d'an Ammey ne"
"Ammey shekarunta baikai ta haifi kamar bross dinku ba ki dai k'ara bincike"
"Humm kawai tace batare data d'auki abin serious ba.
Haka dai abubuwa suka cigaba da faruwa cikin k'aramin lokaci Maryam tayi wani mugun sabo da 'yan gidansu batare da sanin maman taba wacce ta mik'a dukkan yarda da imaninta wajen malaman tsubbu da 'yan bori dan haka bata da masaniyar cewa tufkar da take yi ta cikin gida ya gama warewa tas.
Wata rana kamar yadda akasaba "Zakiyya takaiwa Sailuba ziyara akan yadda suka kasa fahimtar jina ta waya,
"Nifa nagaji da wahala so nake na watsata tabi duniya ta lalace ta zama k'asaitacciyar karuwa bana buk'atar akai ga d'aura wannan auren"
"Humm Sailuba kenan wani lokacin kwwnyar ki atoshe yake wallahi, banda ke da abinki idanmma zatayi auren taya zamu bari tayi auren hutu?"
"Ni auren ne ma bana son tayi kwata kwata, so nake rayuwar ta ya wulak'anta fiye da duk wani wulak'antacce a duniya.
Tofa
Muje zuwa
Daga taku maman islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Shafinki ne wannan'yar laleta SA'ADATU USMAN MUSA (ISLAM)
Allah ya rayamin ke tareda dukkan yayan musulmi badaya
Almustapha Usman Musa shalele na kenan kuma nagaban goshi Allah ya tsaremin ku.
Page 24
"Kina bani ciwon kai Sailuba nifa komai da kike gani da mugun shiri nakeyin sa, Kuma bana bawa na kusa dani damar gane akwai wani abu a cikin raina dan haka zai wuya kiga idan nayi, abu ayarda ni d'in ce nayi saboda babu fuskan da za a gane hakan, ke kuwa gajan hak'urin ki kawai ya isa tonaki, Kinga alhajina da kike ganinsa bansa me shi da sauk'i ba saboda mugun taurin Kai da Allah ya d'ora Masa, shi yasa kuma kikaga bana masa ta dad'i, domin naci bak'ar wuya kan nasame shi, sannan Kuma kina ganin har yau tak'i amincewa ta saurari Deedah shegiya mai kafirin wayon tsiya na rasa dalilin da yasa bata Sona"
Ta K'are dogon sharhin ta da k'orafin yadda Maryam take masifar d'auke mata kai 'yar dariya haj. Sailuba tayi kafin tace" ashe kin manta da cewa nonon wannan shegiyar 'yaalaman tasha, kai wannan mata ta zame min annoba a rayuwata nasa ta yadda zanyi maganin tsinanniya"
"Hum ai irin su idan dubunsu ya tashi cika saikin ji kamar kiyi musu kuka wallahi" cewar haj. Zakiyya cikin ya tsina fuska
Sun jima suna k'ulle k'ullensu.
Tana tunkaro gidan ta tuna da yadda bross ya rik'a kwala mata kira tanaji ta d'iba da gudu dan kar ya hanata fita, tunda suka sam d'an hutun nan ya wani sa mata ido yanzun ta lura aikin ma ba sosai yake zuwa ba sai jifa jifa damma yanzun Allah yasa ko ba kowa zata shiga d'akin Ammey suyi ta hira yadda Ammeyn take mata ne yasa ta jinjinawa k'aryar mamanta da tace Ammey muguwace ko kad'an bataga hakan ba saima wani irin mugun shak'uwa daya soma shiga tsakaninsu da Ammeyn ganin yadda take mata.
Sam ta manta da yadda ya rik'a kiranta ta gudu kanta tsaye ta shigo gidan har da yar wakar ta, daman tun fitar ta yake dakon dawowar ta.
Tana shigowa taji anyi ram da ita ya damk'e ta a bazata taji an rik'o ta sai abin yabata tsoro ta bud'e baki zatayi masa ihu yayi saurin toshe bakin da hannunsa yace "wa na kama?"
Sam ta manta da abinda ya farun dan haka ta hau rarraba ido tana neman hanyar gudu, gane hakan da yayi ne yasa yaja hannun ta zuwa Pat d'in shi.
Dan" Allah bross kayi hak'uri banjika bafa"
"To in bakiji ba taya kikasan mai ya faru wato bakijin magana ko my happiness?" ya fad'a yana kallon yadda tayi tsuruvtsuru shi wallahi dariyama take bashi, yadda duk ta koma kamar wadda ta aikata wani babban abu tun ranan da suka shirya yake kiranta da wannan sunan hakama Nassar ya daina kiranta da Adda ya koma my happiness.
Shiru tayi ba tare da ta tanka ba dan in bata ga dama ba itama wani lokacin muguwar muskila ce sai kayi ta magana tak'i tankaka.
"Kina jina ko?" Ya k'ara sanda yake bud'e k'ofar falonsa, Maryam da take shirin bashi amsa kasawa tayi saboda ganin irin had'uwa da tsaruwan falon kasa daurewa tayi tace "wow gaskiya nima bari Baffa ya dawo wajena daban nima nake so kamar naka"
Ta fad'a tana shigewa cikin falon tana lumshe ido saboda daddad'an k'amshi da sanyin da ya bugi hancin ta sai da ta gama k'arewa falon kallo sannan ta juyo ta dubeshi"waye yake gyara maka wajennan?"
Ta tambaye shi saboda yadda taga wajen kalkal kamar d'akin mace.
D'an murmushi ya saki ya shafi fuskar ta "Ni nake gyara abuna indai ina so yamin yadda nakeso amma yanzun tunda gaki na dunga maleji danaki ko?"
Ya K'are da tambayarta, d'an tura baki tayi gaba cikin shagwab'a tace "hum um ai tunda maneji ne kawai kaci gaba da abunka,
Zo kiga ya fad'a yana jan hannunta zuwa saman benan dake falon, ta bishi har zuwa d'akin baccin shi take taga gado lafiyayye mai kyaun gaske "gyaramin zakiyi yau bani da lafiya" ya fad'a mata yana kallon yanayin ta, kafin ya juya ya fita, tana ganin fitar sa tayi wani irin sufa ta haye gadon tana wuntsilawa, wani irin taushi taji kamar auduga aranta kuwa fad'i take wallahi da sake bari Baffan ya dawo nima komai irin na bross na ke so ji gadonsa dan Allah kamar na wani yar sarkin ta k'ara nutsewa akan gadon.
Shi kam Muhammad har ya sauka ya tuna wayarshi da yabarta tun d'azun saman madubinsa dan haka ya koma ya dan d'aukowa nan ya shagala da kallon yadda take ta faman tsalle tsalle sam bataji motsin shigowarsa ba sai dai maganar sa taji.
"In kin gama Ammey tana kiranki" yafad'a yana d'aukar wayar shi datake saman meerrow ya juya ya fice ya barta batare da ya Kuma kallon inda take ba,
Ita kam sai da ta gaji dan kanta kafin ta gyara har bandaki sai da ta wanke masa kafin ta fito baya falon wani d'aki data gani ak'asan ta lek'a kawai sai taga computers da yawa aciki Maryam da Karam bani sai kawai ta shige kafin takai ga tab'awa sai gashi ya shigo kamar an jeho shi.
Ganin abinda take k'ok'arin yi yasa yai masifar had'e rai yace "me kika ajiyemin aanan" ya fad'a cikin dakakkiyar muryasa data sanshi da ita tun asali.
Maryam da kwata kwata bataji motsin saba sai maganar sa yasa ta juyo a d'an firgice ganin yanayin sa yasa jikinta ya kama rawa tace "nazo ne naga ko kana nan sai banganka ba shi ne shi ne
"Shine kika zo duba ajiyar da kikayi anan ko?"
Ya tambaya a dake take jikinta ya kama rawa ganin yadda yanayin sa ya koma kamar bai tab'a dariyaba
Muje zuwa
MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 25
"Ni ka dai na min irin wannan Kal lon" ta fad'a a d'an tsorace cikin rawan murya, k'ara tamke fuska yayi yace " tambayar ki nake me kika ajiya anan?"
"Dan Allah bross ka matsa na wuce kar Mama ta dawo bata ganni ba" ta fad'a idanunta na cikowa da kwalla tana nadamar shigo masa d'akin data lura kamar na sirri ne.
"Kar ki min kuka idan ba hakaba tattaka ki zanyi yanzun anan" ya fad'a cikin dakewa.
Take ta had'iye kukan, tana jiran yabata hanya ta wuce, Saida ya gama hukuntata da mayun idanunsa kafin yaja kunnenta da d'an k'arfi yajata zuwa bangarensu.
Fashewa tayi da kuka domin bada wasa yaja mata kunnen ba sannan Kuma ya k'ara da muguntar murd'ewa, ai Nassar yana hangosu yayi saurin ficewa daga gidan daman ya lura yau yayan nasu akan tsini yake.
Shigan su yayi dai dai da sallamar Mama wadda dawowar ta kenan taga yanda yake ja ma 'yar ta kunne cikin bala i tace "kai bak'in mugu azzalumi mai tayi maka' ko kuma muguntar daka saba ne ya motsa sakar mata kunne kar ka tsinka azzalumi mugu"
Ta fad'a tana daga bakin k'ofar atsaye dan tana masifar shakkar sa domin idan ya juye bashi da mutunci acewar mama kenan.
Shi kam yi yai kamar baijiba saida yagama jigata ta kafin ya hankad'a ta jikin uwar ta ya juya ya fice, yana jiyo yadda take ta surfa masa ashar tana tsine masa ya saki wani murmushi mai ciwo yana shafa kwantacciyar suman kansa.
Alwala yayi ya fice masallaci domin lokacin anfara kiran sallar magriba.
Acikin gida kuwa bayan Mama tagama tujaranta ta juyo Kan Maryam tace "ke kuma me kika Masa yake neman lahanta min ke?"
Cikin kuka Maryam tace "wai dan na shiga d'akin compute sa shine fa yazo ya kamani shine tun acan yafaramin bala I"
A firgice tace "na shiga uku ni Sailuba me yakaiki d'akin wannan d'an iskan?
Baby me had'inki dashi dazaki je d'akin shi?
Kodai kin fara shiga sabgarsa ne baby ki rufamin asiri kada ki ruguzamin shirin daya kusa kammala"
Da mamaki Maryam take duban maman nata ganin yadda ta fita hayyacin ta daga cewa ta shiga d'akin MD anya babu wani mugun abinda maman take k'ullawa kuwa?
Girgizata haj. Sailuba tayi da k'arfi tace "Maryam ki fad'a min yaushe kika fara mu'amala da Muhammad?
"Mama ba d'an uwana bane?
Maryam tayi mata tambayar cikin mamaki kafin taci gaba da cewa mama dan Allah ki fad'a min illar hakan naga kin rud'e ko zai iya cutar danine?"
Tayi mata tambayar tana mai wani irin kafeta da ido, take haj. Sailuba ta dawo hayyacin ta tace "ba haka bane baby kinsan in mace da namiji suka keb'e to na ukun su shed'an ne shiyasa kikaga ina kaffa kaffa dake"
Cikin k'osawa da zancen tace "babu ma abinda zai faru insha Allah mama, kuma ni ban tab'a shiga d'akin ba sai yau" boyayyar ajiyar zuciya ta sauke tace "to kar ki k'ara"
"Naji tafad'a tana shigewa d'akin ta domin harga Allah zancen ya gara gundurar ta.
Itama haj. Sailuba tana shiga d'akin ta ko maganar salla bata tsayiba ta lalubo no haj. Zakiyya ya doka mata kira,jim kad'an bayan ta daga babu sallama babu komai tace,
"Na shiga uku na na lalace" cikin rud'ewa haj. Zakiyya tace "lafiya k'awata me kuma ya faru daga rabuwanmu yanzu yanzun?
"Zakiyya'yar iskar yarinyar nan tana neman lalata mana shiri, nace zanyi maganin ta kin hana wallahi zata rusamin shirina na shekara goma sha bakwai adai dai lokacin danake hango nasara na kusantoni"
"Wai duk me yafaru kike irin wannan zantuka kamar na sambatu?" Haj. Zakiyya ta tambaye ta cikin sauri domin tanason tasan abinda ya firgita k'awar tata haka.
Batare da wani jinkiri ba haj. Sailuba ta kwashe duk abinda yafaru daga dawowar ta gidan ta fad'a mata ta k'ara da cewa "inajin tsoron kar su rusamin tsohuwar gabar da na dasa atsakaninsu tsayin shekaru,adaidai lokacin da nake son yarinyar ta kasance mara"""'''' da kata haj. Zakiyya tayi saurin katse ta "wai kina tantama akan aikin sabon bokannan ne?"
Haj. Zakiyya tayi mata tambayar cikin son karfafa mata gwaiwa" bana shakka amma ina tsoron tugun uban shegiyar matar nan kinsan shima tsohon d'an tsubbu ne"
"Karki damu k'awata idan yanzun yatashi mu atafe muka kwana" nan taci gaba da karfafa mata gwaiwa akan mugun shirin su.
Tana shiga d'akinta ta yi gaggawar shiga wanka domin ana shirin shiga massalaci ne lokacin, wanka tayi ta d'auro alwala ta fito d'aure da tawul bata tsaya wani shafe shafe ba ta zura doguwar riga ta saka hijab ta haye saman abin salla.
bayan ta idar da sallar ne tayi zikiri da sauri ta tashi ta cire rigan ta hau shafe shafe kafin tagama har an kira Isha kasancewar lokacin magriba ya kwace mata sosai.
Sai da ta gabatar da sallar tayi karatun alqur ani mai girma kafin ta shirya cikin wasu riga da wando masu masifar kyau da daukar hankali farare kar, sai wani bluen rubutu da aka yi agaban rigar ONLY FOR YOU shine abinda aka rubuta, wandon kuma da kad'an ya wuce gwaiwar ta kayan sunyi masifar yi mata kyau ta taje dogon gashin kanta tayi parking d'inshi takawo wani bluen Vandana ta sakawa kanta ba d'an k'aramin kyau tayi ba haka nan ta hauyiwa kanta salfie da wayarta.
Tana cikin d'aukan kanta a hotunan MD da Nassar suka shigo d'akin tana ganin MD tayi masifar d'aure fuska, saboda abinda yayi mata d'azu, murmushi ya saki yana shafar gefen face d'inshi.
K'arasowa yayi kusa da ita ganin haka yasa ta maida kanta kasa tana wani cin magani, kafeta yayi da ido yanajin kamar ya had'iye ta tsabar masifar kyuan da tayi masa,
Hannu yasa ya d'ago habanta ya manna mata kiss a goshi kafin amshe wayan ya d'an rab'a ta da jikinsa kad'an ya soma d'aukar su hotuna.
Nassar yace "wow gaskiya bross kunyi kyau sosai kamar wasu masoya" da sauri ya dafe bakinsa saboda kallon dayaga MD yana masa fuskansa d'auke da wani irin murmushi.
"Nima ayi dani Nassar ya fad'a yana shiga tsakiyar su haka suka kasance ashiriri ce yayin da halin na Maryam ya motsa dan bata kula MD ba saboda abinda yayi mata.
Suna haka wayan Muhammad yai k'ara yana ganin layin Baffa na nageria yai saurin d'agawa"Allah ya temaki Baffa na" cewar MD yana sakin wani k'awataccen murmushi, duk shiru Nassar da Maryam sukayi jin MD ya ambaci Baffa
"Kuzo ka d'auke ni ina airport" shine abinda Baffa yace wa MD ya katse kiran "yeee" MD yafad'a da d'an tsallensa,duk suka kafeshi da ido kafin Nassar yace
"Baffa ne ya dawo?"
Hannu ya mik'a masa suka tafa "dad'i na dakai gane wa" inji MD yana murmushi "zo muje mu d'auko shi" yafad'a yana kama hannun yaron
"Nima zani" ya tsinkayo muryanta d'an juyowa yayi ya kalli kayan dake jikin ta sai kuma ya d'an girgiza mata kansa "gaskiya bazamu iya jiran har ki canja kaya ba yafad'a yana d'aure fuska"
"Dan Allah after kawai zan d'ora akai" ta fad'a cikin marairaicewa
" Minti biyu ya fad'a suna ficewa rik'e da hannun Nassar.
Taku ce MAMAN Islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 26
Jikin mota ta same su sai zance Nassar yake zuba masa yayin da shi kuma hankalinsa yake kan phone d'insa yanata faman latsawa.
Kamshinta ne yasa shi saurin d'agowa ya kafeta da ido yayin da zuciyar sa ya hau wani irin bugawa har d'an rawa rawa jikinsa ya soma abinda bai tab'a faruwa dashi ba.
"Muje" ta fad'a cikin fad'uwar gaba saboda shegen kallon dataga ya kafeta dashi, aranta tana bitar kalaman Mama anya ba wani abun ta hangoba kuwa?
Take raya hakan aranta sanda take shiga cikin motar, "my princess dan Allah kintaho da wayarki ki aramin?"
Cewar Abdul Nassar da ya zuroda kansa ta b'angaren datake,
"Kayi me dashi?" ta tambaye shi batare da ta d'ago ta kalleshi ba
"Boy zan kira anty dan Allah"
Kafin tace mai wani abu wayan yayi k'ara hakanan taji gabanta ya fad'i ganin no ba suna da mamaki aranta tace waye Kuma yake kirana ?
"Ki daga mana" take tsinkayo muryansa,
Dagawar tayi ba tareda ta k'ara kallonshi ba kafin tayi magana taji ance
" Amincin Allah yatabbata agareki yake saurauniyar kyawawa" wani irin murmushi ne ya sub'uce mata, zuwa yanzun ta fara sabawa da halin d boy wanda yabi ya mak'ak'ale mata ga d'anbanzan iya kalami me sanyaya Rai"
"Tareda kai ma aboc...........wani irin burki da MD ya take ne yasaka tayi wani tsalle ta gwaru da murgin motar wayar Kuma bata fad'i ko ina ba sai saman cinyarsa.
Hannu yasa ya d'auke wayar ya zurata acikin aljihun sa ya ya zagayo a zuciye yace "zoki ki fice min a mota" da mamaki ta tsaya kallonsa domin bataga abinda tayi masaba da zaiyi irin wannan fusatar haka lokaci guda "zoki fita nace malama" ya fad'a cikin wani irin buga tsawa, ai batasan lokacin data fito cikin wani irin rawar jiki ba, tana kallonsa ya koma yaja motar sa da wani irin matsiyacin gudu ya bud'e ta da qura, agogon hannunta ta duba tara saura batasan lokacin data fashe da wani irin kuka ba ta daga kai tana kallon sama yadda wani irin hadari ya murtuke bak'i k'irjinta ta dafe dayake wani fitinannen bugu tace "na shiga uku ni mero, me kuma nayiwa wannan mugun mutumin da zai ajeni anan" ta fad'a afili cikin muryan kuka yayin da aka wani irin kece da ruwa mai mugun k'arfi ga Maryam da mugun tsoron hadari bare ya sauketa a wannan wajen da babu kowa sannan babu gida kusa, jitai wani irin tsanar shi ya dawo mata sabuwa dal, tafara takawa a hankali yayin da take kuka sosai jikinta na wani irin rawa.
Nassar kuwa ganin yadda bross d'in nasu yake wani irin tuk'in ganganci yasaka yai tsuru abayan mota yayin da tausayin Maryam ya cika ransa domin baiga abinda tayi masaba zai ajeta wajen da babu kowa sam bai kula da hadarin ba sai zuban ruwa yaji wanda yasa MD ta ka burkin dole.
Fashewa da kuka Nassar yayi da mugun k'arfi kafin yace fili "shikenan Addana ta mutu" yafad'a yana kuka sosai kafeshi MD yayi sosai kafin yajawo yaron jikinsa yana cewa "kai me kace?"
Memakon ya amsa masa sai cewa yayi"me tamaka bross zaka ajeta inda babu kowa ita kad'ai idan wani mugun abin yasameta fa?
Gashi kuma tana tsoron ruwan sama sosai idan ana ruwa babu inda take fita"
Sosai gabansa ya fad'i da maganganu yaron har baisan sanda ya tada motar batareda ya Kuma cewa komai ba ya figeta yana maijin haushin kansa akan abinda yay mata duk da cewa har lokacin zuciyar sa masifar zafi yake masa na yadda yaji tana magana da wani wanda yarasa me yasashi jin hakan?
Ita ko Maryam fara takawa tayi a hankali cikin wani irin tsoro jin yadda wajen yai tsit babu komai sai k'aran zubar ruwa yayin da zuciyar ta yake wani irin bugun dayasa jikinta rawa sosai tayi nisa da inda ya ajeta sosai tana tafi tana share ruwan dayake feso mata afuska wanda yake wanke hawayen dayake tafaman zubo mata babu ka'k'k'autawa.
Yana cikin tuk'in kiran Baffa ya k'ara shigowa faking yayi a gefe kafin ya d'aga "karka zo naga garin da hadari na hau tixi" abinda Baffa ya fad'a kenan ya kashe wayar batare da yace komaiba, saboda kar Baffa ya gane halin da yake ciki.
Sanda yazo inda ya sauketa ta ya rage gudu sosai zuciyar sa ya buga dan ganin bata wajen yayin da Nassar ya kuma fashewa da kuka dan a tunaninasa wani abun ne yasamu 'yar uwarsa.
"Dalla malam ka karka damemu ka rufe mana baki d'if ya d'in ke bakinsa saboda yadda yaga bross d'in yai wani irin canza kama fuskar nan tayi wani irin ja yayinda ya soma zargin kansa akan abinda yayi mata sam baiga kyautawar saba ko kad'an.
A hankali ya cigaba da jan motar yana d'an duddubawa ko zai ganta Maryam wacce taci kuka ta k'oshi ga d'an banzan dukan da ruwa yake mata wanda yasa wani mugun zazzab'i ya saukar mata lokaci guda ta sami gefen hanya ta zauna tana ta faman shashshek'a.
"Gata can bross" Nassar wanda shima yaci kuka ya k'oshi ya fad'a yana nunota tana zaune kan wani dutse data gani abakin hanya jikinta yana wani irin rawa.
Da mugun gudu ya bud'e motar ya fita yana cewa Nassar kar ya fito a cikin ruwan nan, bak'aramin sanyin jikinsa yayi ba ganin yadda ta had'e Kai da gwaiwar ta tana faman shashshek'a, a hankali ya durk'usa agabanta ya dafa kafad'anta.
D'agowa tayi a mugun firgice domin batayi tunanin ma zai dayiba asanin datayi mai na tsantsar rashin mutunci sannan kuma tasan ba wai yana sonsu bane kamar yadda mamanta ta fad'a Mata.
Wani irin kallo ta watsa masa da idanunta da sukayi wani irin ja wanda har lokacin basu daina zubo da ruwa "sorry" ya fad'a can k'asan mak'oshi cikin d'an rawa rawan murya "sorry for what?" ta tambaye shi cikin tsantsar b'acin rai da bak'in cikin abinda yai mata.
"Zo mu tafi" ya fad'a yana kallon yadda ruwa yake tsiyayo Mata tundaga kanta yana kwanrawa kayan jikinta duk sun wani lafe mata ajiki dake ruwa ake tsugawa bana wasa ba, banza tayi dashi kamar bataji me yace ba.
"Dan Allah" ya k'ara fad'a kamar maijin tsoro, yayin da shima sanyin ruwan yafara ratsashi " ba ruwana da kai kar ka k'ara shiga harkana babu ni babu kai mugu kawai" ta fad'a cikin rawan murya sosai yayin da wani irin sanyi yake k'ara shigarta hatta hak'orinta yana jin yadda suke bugan juna
"Dan Allah" ya k'ara fad'a kamar zai mata kuka mak'e mai kafad'a tayi tace "um um na tsan..........wani irin fisgota yayi kafin ta k'arasa ya had'e bakinsu waje guda yana mata wani irin shan mugunta sai da ta raina kanata kafin ya sakar mata bakin cikin wani irin b'acin rai yace "sai wancen dan iskan saurayin naki ne baki tsanaba ko?
Ni kikewa wannan abun akan na nuna b'acin raina akan kina kula wani banza can daban ko na gode" ya fad'a muryan shi na d'an rawa kad'an.
Sai yanzu ta gane dalilin dayasa ya gane mata wannan bala in yabarta a cikin tashin hankali da tsoro jitai ranta ya dad'a mugun b'aci zuciyar ta ya wani irin dakewa ta mik'e kawai ta kama tafiya dan taci alwashin bazataje a motarsa ba "ke meye haka?" ya fad'a cikin d'an tsawa tsawa ko kallon inda yake batayi ba taci gaba da tafiya.
Duk irin yadda yaso rarrashin ta abin gagara yayi hakan yasaka shi tattare hannun riga ya sunkce ta tana wuwulla k'afa tana komai ya nufi mota da ita
Plss manage
0 comments:
Post a Comment