Zubomai shayin tayi a mug dakanta sanan tadawo kusada shi kafanshi tadauka tace "sit up my friend" dan murmushi yamata yatashi yazauna tareda mika hannu yakarbi shayin yace "thanks Grandma, you are the best you know that right" murmushi tamai tace "nasanar da Ammin ka kana nan, ya TV show dakayi angama lpy"? yatsine fuska yayi yakurbi shayin kadan yacire daga baki yace "it was stressful but Alhamdulillah nagama" dan dariya tayi tace "kai Asad, yanzu dai mezan dafamaka yau kaci ka koshi" ahankali yace "rice and beans nakeso Grandma" "kaida shinkafa da wake Asad shikenan zan dafamaka" murmushi yamata yace "Grandma bakiyi fushi dani ba tunda nadawo banzo ba" hararanshi tayi tace "ja'iri ashe kasan kayi laifi" dariya kadan yayi yana kurban tea, tace "ai nayi fushi dakai but Sharif nata gayamin how busy u were saisa andena fushin, yanzu daka gama bagaka kazo ba, ai ba'a raba jika da kakanshi" hira suka cigaba day haryana bata labarin aikinshi sosai taji dadi yanda yasake dudda batamai maganan abinda yasameshi jiya ba, saida yagama tass sanan ya ijiye cup din yace "Grandma bari naje na shirya natafi office, I have huge work awajen ma" tashi tayi tace "tafi Asad, Allah yataimaka kaji, nidai kadingayi kana neman mata inaso naga jikana kafin namutu" yatsine fuska yayi irin ewww dinan bayamason maganan sanan yawuce yafita daga falon yatafi itakuma Grandma takoma tai zamanta dan akwai shirin dazata kalla.
**
Zaunar daita Razika tayi akan gado sanan takoma tarufo kofa dagudu tanadan zaro idanu tace "naga mutumin jiya a falo Du'a biyomu yayi ne" cikin tsoro muryanta dabai gama washewaba sabida yanda tai kuka tace "nima shina gani bansan lokacin da kofi yafadi daga hannuna ba yanzu idan yafadi ma Grandma Yaya zanyi? Wai waye shi? Ya akayi yasan Grandma sosai har yafito daga lungun flawas din falon saman nan eh" hannu Razika tabude itama alamun oho cikeda damuwa tace "oho amman kaman Shemau tasanshi naga ta gaidashi da sauri tana ganinshi kinsan ita tadade tana aiki agidan nan ni ba'a dade da kawoni ba" shiru Du'a tayi har lokacin gabanta faduwa yake, zama kusada ita Razika tayi murmushi tayi takalli Du'a tace "sonshi kike ko Du'a"? wani irin kwalalo idanu waje tayi tace "so kuma" gyadamata kai Razika tayi tace "eh naga yanda kike ta kallonshi jiya ana koranki kinki tafiya kinata cemai thank you for saving my life keda bakima sanshi ba, sonshi kike ko? Yanada kyau sosai wlh gashi dan gayu gashi mai kudi har ana nunashi a TV, sonshi kike"? Girgixamata kai Du'a tayi tace "a'a kawai nasanshi ne tun a kano, shine yataba cironi daga rijiya saisa dana ganshi nace sainaje namai godiya" gyadakai Razika tayi da gamsuwa tace "to Allah sa shiyace yana sonki wlh danaji dadi" dan daure fuska tayi tace "ni banson maganan nan" yatsun kafarta dahar jan dasukayi yasoma washewa takalla tace "bazakije office ba? naga yatsun harsun washe kinga yau Monday fashi ranan Monday is a serious offense" Yatsun itama takalla tace "yadena zafi, tayani zabomin kaya kinga banda lafiya saina shirya natafi" hannu Razika tasa ta dungure mata goshi tace "kewai mai wayau ko" tai maganan tana zuwa gaban wardrobe dinta wani ja da bakin abaya taciro mata sabo fill tana kallonshi tace "wowwww abayan nan yay bala'in kyau, Hajiya tasai miki"? murmushi tayi tana girgixa kai tace "Aneesa tazaban min ranan damukaje shopping yay kyau" warware rigan Razika tayi tace "wlh kam yayi kyau kai yayi bala'in kyau ma, oya tashi kizo ki shirya" tashi tayi tana kallon yatsun nata jin sundena mata zafi, wucewa Razika tayi tafice daga dakin tace "saikin fito" tom Du'a ta amsata tana kokarin cire rigan dake jikinta sanan ta ijiye ta shirya cikin rigan kafin tazo gaban madubi tatsaya tana kallon kanta for the first time yau taga kyanta da ake fadi ja da bakin color ya bala'in mata kyau, zama tayi tana daukan ribbon parking kitsonta tayi a tsakiyan kan yay kaman acucu gashin goshinta sun wani irin bala'in kwanta, sanan tai rolling gyalen abayan, man baki talakata ta shafa a lips dinta dayay wani pink sanan ta tashi tana hada jakanta tadau pad tasaka dakomi da Grandma takoyamata sanan tazura wani flat takalmi mai budadden sama daya bayyana fararen cute kumbunan kafanta, ahankali tasa hannu tabude kofarta tana lekawa gabanta nafaduwa ganin babu kowa yasa takarasa karasawa wajen bene tashiga tafiya ahankali, Grandma kadai tagani zaune tana fere apple dawani karamin wuka, dago kanta tayi jin sahun tafiyanta, kasa daurewa tayi sabida yanda tai kyau tace "Masha Allah tubarkalla Du'a kinyi kyau sosai har kafan ya warke ne"? murmushi tayi tana zama kusada ita tana gyadamata kai, Hajiya tace "to dama banda shegen shagwaba naki ruwan lipton wani konewan kirki ne, kedai kawai rakin ki yay yawa, tashi ki tafi aiki yau Monday aka ciki taran latti baruwana wanan da Ogan ku yadawo ai kunbani" dan zaro idanunta tayi sai yanzu ma ta tuna Sharif yacemata this Monday Ogan su zaiyi resuming office, zumbur tamike tace "bye Grandma" murmushi Grandma tayi tabita da kallo sabida yanda yarinyar tai kyau tace "ayi addu'an fita daga gida Allah tsare" tsalle tayi kaman yar yarinya tace "tom" "kidena tsalle" Grandma tafadi tana murmushi ganin yarintarta.
Motan Grandma tashiga zama tayi driver yajata sai alokacin ma ta tuna batai breakfast ba, har campanin yakaita, yau kawai taji tana having wani irin wired feeling kaman tace sujuya su koma gida kartazo aikin.
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
free page
EPISODE 2️⃣ 9️⃣
Parking driver yayi awajen parking motoci yana kallonta ta glass haryau yakasa daina mamakin inda Hajiya tasamo kyakkyawan yarinya haka a jika, yasan Zainab(Mami) baka ce to kodai mijinta irin fararen yan shuwa arab dinnan ne, bude kofa tayi ahankali tafito sanan tajuya tadauki wayanta da jakanta screen din wayan dayay haske ta kalla ganin 15mins after 9 nasafe yasa taji jikinta nadan rawa dan bata taba latti ba kuma batasan ko boss din nada kirki ba karya mata fada, maida kofan tayi ahankali tarufe tace "thank you Uncle" dan haka take kiranshi sanan tajuya tafara tafiya zuwa entrance sanan tashiga ciki, Sharif tagani tsaye gaban kantan reception yana sanye cikin cooperate kaya ba suit ba amman wando da riga yay tucking ga belt dayasa mai kyau yana duba Rolex din dake daure a wrist dinshi kaman akwai abinda yake jira, kaman yaji ajikinshi kallonshi ake yasa yadago kanshi yakalli entrance hada idanu sukayi ajiyan zuciya yasauki sanan yasakin mata wani irin cute smile yana dumfaro ta, saida yakai gabanta ya tsaya ahankali yace "you look ahhhhh mema zance"? Yay dan shiru yana kallon sama yadaura yatsanshi daya kan kumatunshi kaman mai tunani saikuma yakalleta ganin yanda take kallonshi irin ta kosa taji mezaice dinan yasa cikeda tsokana da wasa yace "you look like indon kauye" gabaki dayan murmushin datakeyi bacewa yayi tai raurau da idanu kaman zata fashemai da kuka hakan yasa yay dan dariya yace "just teasing you" saikuma ya tsareta da idanunshi da for the first time tunda tasanshi suke shiri sosai tana kallonshi kaman yayanta taji wani iri hakan yasa tadauke kanta, murya chan kasa yace "you look damn cute Du'a kaman in saceki in gudu" murmushi tadanyi kanta akasa dan tasanshi da wasa still tana wasada yatsunta, for a moment yamanta inda suke tsaye all yake gani wasa her tsaye agabanshi, ahankali yadan waiga yabi wajen da kallo sanan yajuyo yakalleta yace "I've been calling you baki dauka maisa" dago kanta tayi takalleshi ita bamatasan tayaya yasami number taba, saikuma tanunamai wayannata dake hannunta tace "anan ka kirani"? Wayan ya kalla yace "yes, I gave u about 3 to 4 calls I think" wayan tajujjuya takalla dan ko kadan bataji ringing ba ahankali tace "banji ringing ba" hannunshi yamika mata yace "let's see maybe kintaba wani waje ne" bashi wayan tayi yakarba yabude ganin ba key saikuma ya kalleta yace "bari zan miki setting nashi anjima wayan nason update, yanzu dai our Boss yazo he's in his office, maisa kikai latti, our Boss is such a wired dude fa" yay maganan kaman mai whispering din gulma da hakan ma yasa tai murmushi, tsayawa yayi yana kallonta yace "instead of kifara tsoro kinyi latti murmushi kike ko zaiyi deducting a salary ki sanan yau saikin biya bashi time din dakikaci by adding extra hours kan lokacin tashinki, oya let's get going" yay maganan yana tafiya tana biyedashi abaya yace "zai miki tambaya, so yanzu idan kinje as normal yanda any boss zaiyi he will ask u few questions ma sababbin staff nashi, yadan miki tambaya karkiji tsoro be very bold and answer him kinji" gyadamaikai tayi suna hawa stairs, yace "and idan yace maisa kikai latti me zakice? Uhmmm kuma banaso nakoya miki karya"? yay maganan yana tunani yadaura yatsanshi akai yana tafiya, dasauri tana kallonshi itama tana tafiya tace "zance mai nakone akafa" kwalalo idanu yayi ya tsaya yana kallonta, gyadamai kai tayi kaman wata yar yarinya tace "wlh dazu nadebo ruwan tea shine yazube akafana yay zafi sosai saisa nai latti" tunda take maganan yake kallonta saida tagama ahankali calmly yace "kinyi kuka"? Gyadamai kai tayi da zuciya daya tana raurau da idanu tana tafiya, chak yatsaya heart dinshi nawani irin racing he feels kaman yajawota ya rungumeta ya lallasheta, jin shiru yasa tawaigo ganinshi abayanta yasa tadan zaro ido tace "menene, ka manta dawani abu ne" dan murmushi yayi yataho da saurinshi yace "no, how's the leg now? Yadena zafi?" gyadamai kai tayi tace " yadena" daidai nan sukakai 5th floor, tsayawa yayi daganan yace "our Boss is a bit harsh but don't get scared okay" gyadamai kai tayi tanadan zaro manyan idanunta, dan yatsine fuska yayi yace "naaaay! I don't like that face, now smile and go you got this" 👍 yamata thumbs up da hannu dayasa tai murmushi sanan tawuce tafara tafiya mutanen dake wajen sai kallonta suke, gaban office dinshi da aka rubuta CEO taje ta tsaya, ga secretary dinshi awajen zaune gaban table tana aiki, ganin ta tsaya yasa tace "you can go in Mrs Du'a" gyadamata kai tayi batare datai magana ba sanan ahankali tadaura hannunta kan handle na kofan harwani kalan sanyi takeji sanan gently tabude kofan kanta akasa, wani irin kamshi da sanyi ne suka wani daki fuskanta dayasa tadan lumshe ido kadan sanan tabude idon kafin ahankali tasa kafanta tashigo sanan tamaida kofan tarufe ta jingina da kofan kanta akasa still hannunta duka biyun kan hannun handbag dinta data kankame gam gam tanajin wani irin sanyi tundaga kafanta har tsakiyan kanta dan sanyin office din yabaci kaman ankure AC gabaki, takai kusan 1min tsaye awurin tana kankame da igiyan handbag dinta kaman her whole life depend on it sanan ta daure still kanta akasa kaman wata munafuka tashigo har zuwa gaban hadadden table din office din ta tsaya gaban kujeran guest tana kara kankame hannun jakan tama rasa takamaimen mezatace a office din mai kamfanin nan, tunawa da maganan Sharif na kartaji tsoron yasa tahadiye tsoron ahankali tabude bakinta cikin muryanta data kara wani irin kankancewa sabida yanda ke faduwa tace "good morning Sir" takai kusan 30sec dagaidashi jin shiru yasa gently kaman wacce idanunta ke shirin fitowa sabida tsabagen rawan dasukeyi tadago kanta takalli kujeran zaman mai office, ido hudu sukayi da Asad dake zaune yana yasanya wani hadadden Italian suit white da blue, wanda keda wani monkey jacket da farin riga ke kasanshi, babu jacket ajikinshi ya rataya kan maratayan da ake ijiyewa a office dan hanging kaya monkey jacket da farin riganne kawai ajikinshi yana zaune kan kujeranshi hannunshi rikeda wasu papers dayake reviewing ga coffee agabanshi yana sipping, sai dayan hannunshi rikeda byro ko kallonta baiyiba, wani irin rawa jikinta yafara ganin Asad mutumin daya cirota daga rijiya a kano, mutumin data gani a TV, mutumin datagani a hotel hall, same mutumin da dazun nan taganshi agidansu shine kuma still take gani anan shine mai kampanin nan, the CEO boss dinta to kodai aljani ne, jitayi cikinta yawani irin murda kawai taji wani fitsari yataso mata yacika mata mara yana shirin zubowa duka acikin yan sakannin data dago kanta ta kalleshi, daurewa tayi ta harde kafafunta gam but still jikinta rawa yake takara kankame jikinta, saida yagama reviewing document din hannunshi yay signing tsaf sanan ya yunkuro ya ijiye papers din kan table sanan ya gyara zama da kyau ahankali yadago kanshi yazuba mata mayun idanunshi akanta, dawani irin sauri tadauke kanta tana kallon gefe tana kara harde kafanta sabida wani irin fitsari datakeji dake neman fin karfinta, cikin muryan nan nashi dababu alamun wasa cikinshi yace "kinyi latti awa daya da minti biyar da sakan lalatin, bayan kinzo aiki latti kika tsaya kina chatting da wani ma'aikaci anan did you know the gravity of laifin nan"? gizgiza mai kai tayi still kanta na kallon gefe, tsawa yadaka mata yace "nobody answers me with motion speak up" wanan karan batasan lokacin data saki hannayenta dake kan jakaba takai tadaura Ata wajajen abdomen dinta dan tana neman sakin fitsarin sosai, lips dinta narawa sosai tace "I am sorry sir......." yana kallonta still yace "well your salary will tell u if I accept the sorry or not, have a sit" gyadamai kai tayi saikuma da sauri tace "okay" kafin ahankali tasa hannunta taja kujeran gaban table din tazauna jikinta na bari.
Anatse yace "look up and introduce yourself" yay maganan bayabo ba fallasa as usual, gently tadago idanunta tadaura akanshi kaman yanda shima yake kallonta, kasa jure kalan idanun dayake dashi tayi hakan yasa tana kallonshi ne amman tadan karkata kwayan idanunta gefe sanan ahankali tace "My name is Du'a, I am 21yrs old, an haifeni a kano, Babana nada mata biyu awajen Mama na I am the first child, nayi school from nursery zuwa JSS 2 a makarantan Royal, that's were I stopped a school".
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
Free page
EPISODE 3️⃣0️⃣
Tai maganan tanadan moving da jikinta sabida yanda cinyanta ke rawa tanajin fitsari, jin shiru yasa kaman wata barauniya tadawo da idanunta back saitinshi hada idanu sukayi yana kallonta har lokacin wanan karan kasa rike fitsarin tayi batasan lokacin datawani zabura tamike kaman mahaukaciya ba tana yarfe hannunta dayan hannun kuma takai wajen abdomen dinta tadan kalleshi tana rawa rawa tace "I.....wan......pee...." bamata karasa maganan ba jin fitsarin yazo tasa tawani saki handbag dinta datake rikedashi kan table dinshi kayan ciki duka suka zubo kan table dinshi sanan tawani kwasa a guje tai kofan kofanshi tabude tafice dagudu.....
Wani mugun tsaki yasaki yanabin table din nashi da kallo da kayan cikin jakanta dasuka zubo, the first thing da idanunshi suka sauka akai was pad, dauke kanshi yayi yay tsaki, yana kokarin dauka wayanshi aka bude kofan aka shigo itane kanta akasa, maida kofan tayi ahankali tarufe sanan takaraso har gaban table din, ganin yanda kayan jakanta suka fito kan table din yasa tadan kalleshi ganin yana daddanna wayan yasa takwashe dasauri tazuba a jakan sanan tadaga jakan tarike kaman wacce zatai sata ta lallaba tazauna akan table din.
Ijye wayan dayake tabawa yayi tadau wani file yabude batare daya kalleta ba yace "I learned that HR dept basu karbi any of your detailed ba ID Card na this company kawai MD yasa amiki" gyadamai kai tayi kanta akasa tace "yes sir" still yana duba rubuce ruvuce yace "can I have ur personal ID Card?" dan dagokai tayi takalleshi hada ido suka sakeyi dasauri ta girgizamai kai tace "uhm bandashi" danjim kafin cikin wanan muryan nashi yace "voters card or national identity card dinki that's what I mean" sake dago idanunta tayi takalleshi ganin yana kallonta still yasa tadauke kai murya chan kasa kaman wacce ke tsoro tace "bandasu" cikeda haushi yace "what nonsense! Are you even a Nigerian citizen"? Yay maganan da fushi cikeda kuma fada, doguwan riganta takama tarike gam tawajajen cinya batasan maisa ba fada ko magana da ita da fushi sosai yana tuna mata da memory na gidansu, kuka ne taji yazo mata tadaure da kyar tace "ba....ba'a barina fita agidane saisa bandasu" tai karashe maganan tanakai bayan hannunta kan idanunta tana danne hawayen dake shirin zubomata tanajan hanci, Yatsine fuska yayi kaman irin dan dole yake mata magana dinan yace "give me ur account details we need to attache it to your file for ur salary pension, Sigma pension zasuzo subude miki pension account dinki, now ur bank details" dan dago kanta tayi takalleshi idanunta sunyi ja, hada ido sukayi dan har lokacin kallonta yake murya chan kasa tace "I don't have an account" goshhhh! yawani irin buga table din dayake kai dasaida tama firgita, cikeda bacin rai yace "what kind of a girl Ammi tasa nakawo into my company eh? How can I hire a person who doesn't have any identity card dazai nuna she's a Nigerian and a citizen, please get out of my office, and don't come back to this company saikin bude account sanan kinsami ID card, understood?" Gyadamai kai tayi ahankali hawaye yacika mata idanu fall, yatsine fuska yayi yace "now get out of here" ahankali ta tashi jikinta har bari yake irin na wanda ke shirin yin kukan nan, dawani irin sauri sauri tafita daga office din nashi tai stairs dasauri sauri take sauka kasa kanta akasa ta daure iya daurewa karta bari tai kuka tana kaiwa kasa tai hanyar fita, receptionist dinsu nabinta da kallo cikeda mamaki dan tasan kullum wanan yarinyar da duk suke kirada Matar MD Sharif ta shigo bata sake fita sia lokacin tashi.
Tana fita tai hanyar parking space, sai alokacin tafashe da kuka sosai ganin babu motar direban Grandma yasa ta tuna lokacin tashi baiyiba, ga wayanta bayama hannunta yana hannun Sharif dawani irin gudu tafita tana kuka sosai tana share fuskarta da bayan hannunta, bakin titi ta tsaya tana kalle kalle.
Idanunta sunyi jajir takasa daina kuka, taxi dayazo wucewa ta tare dan bataga keke napep ba kaman yanda lokacin nan kafin asa tadaina fita take gani akan titinsu, tsayawa yayi ba bahaushe bane yakalleta tsayarda hawayen tayi tashiga sanan tarufe yace "madam ba drop u want" gyadamai kai tayi tace "eh" sosai take kuka cikin keken kawai memory gidansu dakomi yake dawomata da yanda yawani korata kaman yana koran kare, jin yanda take kuka yasa mai taxi yakalleta ta cikin mirror yace "hope all is well o Madam, u no tell me where I go carry you go" murya chan kasa cikin kuka sosai dan daura hannayenta tayi akan fuskanta tana kukan tace "estate" dasauri yace "which estate" kasa amsashi tayi sabida kuka hakan yasa yace "eh which estate" ko kadan batasan sunan estate dinsu ba bama hakaba ita bamatasan ko estate din nada suna ba dan bata taba luraba ahankali tace "just go if we get there I will show you" gyadamai kai mai taxi yayi daba bahaushe ba yacigaba da sharara gudu tana kuka hardaga baya ta lallashi kanta tai shiru tajuya tana kallon hanya ganin bataga estate dinsu ba, sunyi tafiya fin awa biyu suna zagaye zagaye yana tambayanta duk wani estate dazasu gani a hanya konasu ne tace a'a, gajiya yayi yay parking akan wani titi cikin fushi yace "abeg give me my money and leave my car u donno where u dey go" girgizamai kai tayi cikin muryanta data dishashe tace "I know is estate, idan akabi titi ake kaiwa" tsayawa yayi baki bude yana kallonta ta glass din motar ganin kaman ma yarinyar batada hankali dan inba hakaba tayaya babban mace haka zata wani cemai idan akabi titi ne za'azo estate dinsu batasan ina zata bane, harzuka yayi yace "just give me my money find another taxi, the little petrol wey remain make i manage am go home" kalan titi dasuke tayi dababu ma mutane sosai babu motoci sosai dan irin titin sabuwar hanya dinan ne yasa cikeda tsoro tace "but this is not my estate, I don't know anybody here" cikeda nakan magana yace "me I no, see Madam gimme my money comot for my car" ganin yana magana kaman zai daketa yasa tashiga bude jakanta, she's not even sure kotanada kudi, kudaden dake cikin jakan taciro hakan yasa yace "my money na 5000, na drop u carry we almost round Abuja finish" gyadamai kai tayi tashiga kirga kudin jakan duka duka 4900 nema, ahankali tamikamai ganin baida mutunci tace "is 4900 sorry" fizgan kudin yayi yace "witch even if na send they send u my papa spirit still dey protect me, comot for my car" yay maganan yana wani irin bude kofa yafita yabude baya yana kallonta yace "I said comot for my car" fitowa tayi ahankali tana gyara rikon jakanta maida kofan yayi yarufe sanan yakoma gaba yazauna yarufe kofan lekowa tayi ta window yace "I pass ur power tell them u no fit do me anything witch" yay maganan yanajan mota shi duk kallon mayya yakema Du'a sabida yanda takeda bala'in kyau gashi tagama zagaye Abuja dashi zarginshi shine zatakaishi ashamai jini ne.
Hawaye tagoge daga fuskanta da sauri bayau aka saba kiranta da mayya ba, ahankali takalli gabas, kudu yamma da arewa tana tunani inane hanyan zuwa gidansu, gashi babu wasu mutane a hanya sosai, hakan yasa ta yanke shawaran bin hanyar da mai motan yabi da kafa, dan batada ragowan kudi kuma koma tanada shi bataga taxi ko keke napep dazata tare anan ba ga cikinta dayake ciwo dan bataci abinci ba gakuma MP datakeyi datakejin alamun na yakamata ta chanza pad dan kaman yajike.
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
LAST FREE PAGE
EPISODE 3️⃣1️⃣
Sosai take tafiya Instead of taga tana shigowa cikin mutane amman saitaga kaman tana kara komawa inda ba mutane ne, one one motoci ke gittawa, tun wuraren 1 da direban nan yasauketa itace har uku saura tafiya take kafanta yay budu budu sabida a bayanta dakejan kasa ga shegen kishin dayakeji ga yunwa ga gajiya, tsayawa tayi abakin titi duk motan dazaizo yawuce take tarewa amman basa tsayawa hakan yasa takoma gefen titi dan daji da bishiyoyin dake wajen tasamu ahankali tazauna akan wani dan dutse dake wajen tana maida ijiyan zuciya tanajin wani shegen kishi tana kalle kalle bataga komiba, daura jakanta tayi akan kafafunta kafin ahankali tadaura kanta akan jakan kawai tafashe dakuka ahaka akife kafin daga bisani wani wahalallen bacci yay awon gaba da ita awajen.
Wuraren 1 as usual Sharif yazo floor dinsu rikeda wayanta daya saita mata komi, knocking office dinta yayi tareda budewa duka at the same time, ganin babu kowa a office din babu jakanta yasa yadanyi kwafa yace "yauma ta tafi masallacin bata jirani ba ko" jan kofan yayi yamaida yarufe yafito daidai Asad yadawo shima daga mosque din yana tafiya ahankali yana gyara zaman necktie dinshi yana kallon Sharif din, tsayawa kusadashi Sharif yayi cikeda tsokana yace "how far kamana order pizzan" hararan Sharif din yayi yace " order with ur money" yay maganan yana wucewa office abinshi shikuma Sharif yahau dariya yawuce elevator yashiga zuwa kasa masallaci yashiga yay alwala yay salla sanan yafito yana kallon wajen ganin babu ita yasa yawuce Canteen dinsu, ganin babu ita awajen ma yasa yay fushi kawai baima tsaya cin abincin ba yawuce floor dinsu yace "nizata share yau duk tai abubuwan ta ita kadai" wayanta ya kalla dake hannunshi yace "she will come get it by her self" ijiye wayan yayi agefe kan table dinshi yacigaba da aikinshi...... Wuraren 3 yakasa hakuri rabon daya ganta tun safe tashi yayi yafito yay sama, office dinta yasake budewa ganin bata ciki yasa yafito yabi ma'aikatan wajen da kallo wucewa yayi yakarasa wajen receptionist din gaban office din Asad yace "have u seen Miss Du'a Patience"? Cikeda girmamawa tace "yes sir naga saukanta" juyawa yayi da sauri yashiga elevator yasauka kasa, shi yasan bata yawo iya kanta masallaci sai Canteen kuma duk tare suke zuwa toko tana restroom din mata ne, hanyar bayi yayi ya tsaya gaban macen security dake wajen yace "dan dubamin miss Du'a aciki" tashi matan tayi tac3 yes sir tashiga taduba tafito tace "babu kowa a rest room sir" shiru yayi yana tunani dan this is strange, daga kai yayi yana kalle kalle ganin receptionist din wajen yasa yakarasa yace "have u seen Miss Du'a"? Gyadamai kai tayi tace "yes Sir dazu naga tazo tawuce tafita tana kaman ma kuka take" dan tsayawa yayi yana kallonta saikuma chan yace "around what time kenan"? Dan shiru tayi kaman tana tunani tace "around eleven na safe" juyawa yayi dasauri cikin fushi yace "Assssadd! What have u done this time" elevator yahsiga zuwa 5th floor, direct office din Asad yashiga dake magana dawani employee dinsu daya kawonai report, kallon employee Sharif yayi yace "excuse us Mr Bashir" "sure sir" yafadi yana tashi yafita sauda yarufo kofan sanan Sharif yakalli Asad babu alamun wasa kaman bashiba yace "ina Du'a Asad? Inaka turata" dan yatsine fuska Asad yayi yana jawo MacBook dinshi zuwa gabanshi yace "wace Du'a"? Cikin fushi Sharif yace "you know what am talking about, yarinyar dakai saving daga rijiya, jikan Hajiya, yarinyar da Ammi tasa kabata aiki, ina take"? Typing abu yashigayi a system dinshi abinci cikin halin I don't care yace "batada any means of identity sanan batada account so I asked her to leave my company duk randa tasamesu she can come back" cikin wani irin bala'in mamaki Sharif yace "you ask her to mene?" yay shiru yana kallon Asad dake harkan gabanshi, cikin wani irin bacin rai yace "Asad kakosan mekayi? Did you know that yarinyar nan batasan ko'ina ba a Abuja ko good 3weeks batayi a Abujan nan ba, tayaya zata koma gida? Look her phone is with me" yanuna wayanta dake hannunshi, dan tabe baki Asad yayi yana aikin dayakeyi a system yace "she's an adult she can take herself home" yanda yake maganan ma yafi komi cima Sharif rai irin ko ajikinshi dinan baimasan yayi wani abuba, cikin mugun fushi dabazai iya tuna the last time dayay irinshi ba yace "wlh katashi kanemo yarinyar nan ina gayama" wanan karan ko kalloma Sharif bai isheshi ba saima hannunshi dayakai yana taba screen din system din yana magana ahankali yace "there's an error in this FIFO calculation......" irin baimasan Sharif nayiba, sosai ran Sharif yabaci wayanshi yaciro ya danna ma Ammi kira yadaura a kunne ringing biyu Ammi tadaga kafinma tai magana yace "Ammi kina ina yanzu haka" cikeda rashin fahimtan abinda Sharif keyi tace "ganinan gidan Hajiya, takirani gwuiwanta naciwo shine na shigo" ahankali yace "Ammi Du'a na gidan" dasauri tace "Du'a kuma, Du'a dake office basai 4 kuke tashi ba, wai yau bakaje office bane" wani irin lumshe ido yayi yabude kirjinshi na bugawa yace "Ammi listen to me zangaya miki wani magana amman banson kice komi dan kar Hajiya tagane dan abinda kunya ace mune mukama jikanta haka" nan yakorama Ammi magana daga A to Z, tsabagen tashin hankali batasan lokacin data fito tsakar gida ba, cikin bala'in bacinrai tace "ina Asad din"? cikin bacinrai Sharif yace "yana zaune anan Ammi ko ajikinshi baimasan yayi abu" cikin fushi sosai tace "bashi wayan" cikin bacin rai yace "ni wlh bazan bashi wayataba saidai ki kirashi ta wayanshi bari naje naduba Nabi hanya kozan ganta" yay maganan yana katse wayan yawuce yafice daga office din straight waje yayi yashiga motanshi yabi hanya.
Wayan Ammi tabida kallo tunda take bata tabajin Sharif yayi fushi hakaba duk cikin yaran shi kadaine baida matsala gashida ban dariya, dialing number Asad tayi, yana zaune ganin Ammi na kiranshi yasa yature system din dake gabanshi yana kallon wayan harta katse bai daukaba, akaro nabiyu ne yamika hannunshi kaman mai tsoron wayan yadauka yakara a kunne baice komiba, cikin fushi sosai Ammi tace "aida itama wanan kiran baka dauka ba goga kaji" taidan shiru hakan yasa ahankali yace "Ammi I just told her to go idan tai national ID da bank saita da......""shut up Asad!" Ammi tadakamai mugun tsawan dashi zai iyacewaka tunda yake arayuwanshi Ammi bata tabamai tsawa hakaba, tace "Asad this is not how I train u wlh billahil azim, Asad where is your heart, Asad how can u asked that girl ta tafi gida yarinyar dabatasan ko'ina ba, kasan yarinyar nan kuwa? Kasan wacece ita? Eh? kasan mesa aka kawota wajen kakanta kasan labarin Du'a kuwa? Do you know what that girl has been through? Asad is this how I trained you? Duk duniyan nan banda Maman data wuce Hajiya Asad you know this morethan anyone matan nan babu abinda batamin ba aduniyan nan, Asad jikan ta zaka wulakanta eh?" jin yanda ran Ammin shi yabaci sai maganganu take awaya yasa yaji duk badadi, ahankali yace "Ammi" cikin fushi tace "don't you dare call me Asad, idan wani abu yasami yarinyar nan tayaya zankalli Hajiya nagayamata d'ane sila eh? Mezata cema iyayen yarinyar nan kasan case din dake kan yarinyar nan kuwa, Asad why are u like this? Maisa baka da imani bakada tausayin mata eh? kanada kannai mata idan wani yakorasu haka kaibamai zuwa kayi fada dashi bane, Asad listen to me if anything should happen to that girl wlh wlh bazan yafemaka ba dan bazan taba iya kara kallon idanun Hajiya ba..." dawani irin sauri yace "Ammi!" cikin fushi tace "yes Asad nasan kalman dana gayamaka, katashi duk inda yarinyar nan tashiga aduniya ka nemota kadawo da ita gida nan dakanka safe and sound inba hakaba wlh saina mugun sabamaka Asad dabazaka gane kaina ba mai bakin hali kawai" Ammi ta katse wayanta cikeda bacin rai tana kallon agogo dan tasan hudu nayi direban Hajiya zaitafi daukota.
TOH GGM DINA🥰🥰🥰 ANAN NAKAWO KARSHEN FREE PAGES THIS LABARI NADA TSAYI YANZU NAMA FARA.
SUBSCRIPTION IS 500 PAY INTO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK.
KUJI TSORON ALLAH KUBIYA KADA KU KARANTA BATARE DAKUN BIYABA DAN GASKIYA ALLAH ZAI SAKAMIN.
THANK YOU ❤
Assalamu Alaykum, inaso mu gina al'umma masu tsoron Allah da tsoron hakkin dan uwanshi musulmi, I was very kind and generous nayi pages talatin da daya (31) pages awanan littafin as free, dan Allah kudubi Allah badan niba badan halina ba karku karanta idan baki biya kin shiga group ba, dan idan kikai gaskiya Allah zai bimin hakkina.
Kudin karatun this novel is 500 kacal, pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting.
you can chat me up directly a watsapp by clicking on this link
wa.me/+2347012181461
M SHAKUR
EPISODE 3️⃣2️⃣
Kasa komawa cikin gidan tayi hankalinta yawani tashi gabaki daya number Sharif tai dialing ringing daya yadaga, cikeda damuwa tace "Sharif kafita nemantan kaganta"? Cikeda damuwa yana driving yace "Ammi ni banmasan ina zan dubaba gani nan dai akan titi within office dai ina dudddubawa" cikeda damuwa tace "shikenan In sha Allah nothing will happen to that girl In sha Allah, now inaso ka kira Hajiya kacemata Du'a will stay late akwai aiki zaku dawo da ita anjima, Sharif kunyan gayama Hajiya abinda d'ana yama jikan ta nake wlh just do that okay" ahankali yace "Ammi calm down Hajiya taganki ahaka zama ta zargi wani abu, kitafi gida kawai and relax we will bring Du'a back, nothing will happen to her kinji" asanyaye tace "Allah yamaka albarka Sharif" takatse wayan.
Yadade zaune kan table dinshi yana maimaita kalaman da Ammin shi takirashi dashi, yau Ammi ce ke cewa bazata yafemai ba, Ammi ce kecemai mai bakar zuciya, Ammi bata tabamai fada hakaba, ahankali ya fuzarda iska yamika hannayenshi da kyar yature system din gabanshi sanan yawani irin kife kanshi akan table, kaman wanda aka daka, saida yaji ana kiran sallan laasar sanan yatashi, mikewa tsaye yayi yashiga bathroom dinshi dake cikin office din, alwala yadauro sanan yafito ya tsaya gaban hanger jacket na suit dinshi yasaka sanan yadauki wayanshi da car key daga wajen yawuce fita yayi yasauka kasa saida yafara tsayawa yay sallan laasar sanan yafito daga masallacin tsayawa yayi yana kallon entrance door din shigowa company, shi yanzu ta ina Ammi takeso yafara neman yarinyar nan me eh ta ina?.
Ahankali yafara tafiya zuwa entrance din fita yayi yawuce special wajen dayake parking motarshi, budewa yayi yashiga yamaida kofan yarufe ahankali yasake fuzarda iska, wani irin tsaki yayi sanan takunna motarshi yaja saiya yakai daidai titi ya tsaya yana tunani, yasan estate dinsu babu suna agate wani irin mahaukacin estate ne na masu kudi saisa settings dinshi ma daban ne dana sauran estate, in shine ita baisan ko'ina agarin nanba yana tare abin hawa cemai zaiyi yakaishi estate, so now dole yabi hanyoyin all estate na within this yanki haka, tsaki yakara ja kaman yahadiyi zuciya sabida haushi yaja motar dawani irin mugun gudu yanabin hanya hanya estate estate yana duba kozai ganta amman har magrib baiganta ba at this point he was a bit worried bawai dan wani abu ba kawai sabida Ammi da kalamanta da fadan datamai, kuma yasan inda anganta da yanzu koda Sharif ne daya sanardashi anganta, ahankali yay parking yafito ya tsaya awani masallaci yay alwala sanan yay sallan magrib yasake fitowa yashiga mota yaja yana gudu akan titi yama dauki hanyan barin gari wani irin dukan sitarin mota yayi yana tsaki, saikuma yadagokai yadaura akan titi gani yayi kaman yawuce wani abu haka a gefen hanya dawani irin sauri ya leka ta side glass yana kallo maiya hango baya hango kaiko kafa kawai kaman abu yagani ciki ja da bakin kaya, murya chan kasa yace "can that thing be the girl"? Yay maganan ahankali yanayo reverse da motan ahankali harya tsaya daidai saitin ta yana kallonta daga wajen yar jakanta dake kasa agabanta dayagani yasa ya tabbatar da itace, dawani irin sauri yasaukar da glass din motar kasa yaleko da kanshi tareda danna horn, amman ko alamun motsi baiga tayiba, sake danna horn yayi sosai but still babu ko motsi, sosai ranshi yabaci shiyake yar yarinyar nan da duka kannenshi sun girmeta horn ne ta shareshi, wlh sabida maganganun Ammi ne daya rantse yaja mota abinshi yay tafiyanshi ita tasani, cikeda fushi yace "ke kitaso nakaiki gida" ganin har lokacin ko motsi batayi ba yasa yadanji gabanshi yafadi, dan jim yayi yana tunani saikuma yabude kofar motan yafito ya tsallaka dan kwatan gefen titi sanan yakaraso wajen dajin yana yatsine fuska ga uban kukan sauro dayake duhu yasomayi, akanta ya tsaya yana kallonta cikin muryan dolen nan aka tirsasashi yay magana yace "Ke bakiji ana kiranki bane, tashi muje nakaiki gida" jin shiru still ko gezau batayi yasa yaciro wayanshi daga aljihu dasauri kunna flash yayi ya hasketa baya ganin fuskanta sabida yanda takife fuskan kan kafafunta, bayanta ya tsare da ido yana kokarin detecting breath nata ganin baiga sign na numfashi ba yasa dasauri ya tsugunna agabanta ijiye wayanshi yayi agefe yakai hannunshi zai tabata saikuma ya tsaya kallon hannunshi yayi dasauri saikuma yakai duka biyun yadaura daya kan kafadarta yay tapping nata yace "Ke, Ke" ganin still ba response yasa yazare hannu daya daga kafadarta yakai dayan saman kanta dago kanta yayi sama hakan yasa dankwalinta gabaki daya ya salube kanta na resting a hannunshi, sauke dayan hannunshi dakekan kafadanta yayi yadauki wayanshi da sauri yana haska fuskanta, kumburin da idanunta sukayi saida yaji tsoro tsabagen kukan datasha, idanunta abude amman kadan tana kallon flash din wutan dake haskota, lips dinta sun mugun mugun bushi kaman zasu tsage tsabagen rashin ruwa dakuma rana ga uban iskan hanyan daya bugeta, juya flash din yayi akan fuskanta dan yaga ko she's conscious, ahankali yaga idanunta sunbi flash din, hakan yasa ya ijiye flash din yakai hannunshi yay tapping kumatunta yace "Ke....Ke....Du'a!" bakinta yaga yay motsi hakan yasa dasauri yakai kunnenshi saitin bakinta, ahankali yaji tafurta ru.....bata iya fura sauran ba, dasauri yasaketa yatashi motanshi yakoma wani bottle water dayakedashi yadauko yadawo dasauri yasake tsugunnawa yabude yakai hannunshi daya yadaura saman kalban kanta sanan yakai ruwan bakinta dawani irin sauri tashiga shan ruwan dakawai saiyaji he's feeling bad, katon bottle water nan saida ta shanye tass dazai karamata wani ma yasan dazata shanye, yarda goran yayi yakalleta sai alokacin idanunta suka budu da kyau, ahankali tazubamai nata idanun sabida wayanshi dake kasa they could see each other, tundaga gashin dasuka kwanta akan goshinta yake kallo zuwa gashin idanunta bakake sidik dogaye dasuka tattare sabida uban kukan datayi, zuwa manyan idanunta dasuka kumbura suntum idanunta sukai kanana kaman na yan Chinese sabida kuka, zuwa dogon hancinta dayake nan akan fuskanta tsaf zuwa sexy a little bit thick and slim towel lips dinta dakenan atattare tsukakke pink yirrrr dasu sun buce sosai sabida wahalan datashi, dan kawarda kanshi gefe yayi dasauri kaman wanda yatuna wani abu, wayanshi yadauka yatura a aljihun wandonshi sanan yacire hannunshi daga saman kanta yamike tsaye yace "tashi mutafi" ahankali tai kokarin tashi ta hanyar rike bishiyan dake side dinta tamike tsaye, ganin haka yasa yawuce yay gaba abinshi, gently tacire hannunta daga jikin bishiyan batasan meya faruba kawai tajita tazube a kasan wajenne kaman wacce kafafunta sukai paralyze.
Haryakai mota yana shirin shiga yaji karan fadin abu dawani irin sauri yajuyo ganinta akasa still tana yunkurin tashi zaune ne dankwalinta gabaki dayama yacire yasada wani irin sauri yazo wajen, kamota yayi ya tsayarda ita jin kaman lema lema ajikinta yasa dasauri yasake saka hannu a aljihu yaciro wayanshi da flash din yake a kunne yahaska jikinta, ganin stain a riganta dudda baki da jane bai hanashi gane stain din jini bane, kallon fuskanta yayi yanda bamata iya bude idanu da kyau da support dinshi ma ta tsaya yasa kawai yamaida wayan aljihu, ahankali yacire jacket din suit dinshi, yatsine fuska yayi yadan matsoda ita yasata ajikinshi gudun karta sake faduwa dan yaga jiri take gani sosai, kaman jira take dawani irin sauri ta kankameshi gam gam tana tura kanta a kirjinshi tana nishi sama sama wani irin yunwa nacin cikinta kaman zata suma takeji, wani irin yirrrr yaji yanda gabaki dayanta take cikin jikinshi gashi ta kankameshi sosai, ahankali yakai jacket dinshi yasamata Ata wajen waist dinta sanan yakamo hannaye jacket din yazo dasu ta gefenta yarike sanan yafara tafiya da ita ahankali tana rungume dashi da sukazo wajen kwata daukanta yayi ya talla kar da ita sanan yabude gaba yazaunarda ita, dan dukowa yayi yana samata sit belt yana kallonta yanda ta lumshe ido ganin kanta ba dankwali yasa maida kofan motan yarufe sanan yawuce we amen dankwalinta yadauko sanan yadawo yashiga gaba ya zauna yatada motan yaja motan da bala'in gudu.
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️M SHAKUR
Assalamu Alaykum, inaso mu gina al'umma masu tsoron Allah da tsoron hakkin dan uwanshi musulmi, I was very kind and generous nayi pages talatin da daya (31) pages awanan littafin as free, dan Allah kudubi Allah badan niba badan halina ba karku karanta idan baki biya kin shiga group ba, dan idan kikai gaskiya Allah zai bimin hakkina.
Kudin karatun this novel is 500 kacal, pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting.
you can chat me up directly a watsapp by clicking on this link
wa.me/+2347012181461
EPISODE 3️⃣3️⃣
Sosai yake gudu yake kallonta yanda ta lumshe ido tana numfashi sama sama kaman ma bacci take, wayanshi dayahau ringing yakalka ganin Ammi ce yasa yamika hannu ahankali yadauka kafinma tai magana yace "I've seen her Ammi muna hanyan zuwa" ya katse wayan kafin tagayamai wani maganan, gaban wani eatry ya tsaya kashe motan yayi yakara juyawa yakalleta bayawani ganin fuskanta sosai sabida tajuya tana facing kofa tana bacci gashinta kawai yake iya gani da ribon din yafita kitson ya zuzzuba ajikinta, bude kofa yayi yafita yashiga eatry youghurt yasayo mata da jellof rice da roasted chicken sanan yafito, zagayawa yayi ta bangarenta yabude kofan fuskanta ya kalla taga da kyar take bude idanu, yogurt din yaciro daga leda yabude marfin yabata yace "Ke gashi ki sha" kallonshi take takasa ma mika hannu ta karba ko kadan batada karfi, ahankali tadanyi shifting hannunta zata mika ta amsa amman takasa, sosai yaji gabanshi nafaduwa yamaida yarinyar ahaka ai sai Ammi takusan kasheshi da masifa, dan tsaki yasakeja na mugun takaici sanan yabude marfin goran yogurt din yadanyi bending yakai kan bakinta wani irin zuman goran tayi tanasha sai lokacin wani karfi yazo mata batasan lokacin datakai duka both hannayenta tadaura kan nashi dake kan goran takara kankame goran da hannunshi tanasha sosai, wani yar yaji yadai daure ganin tana neman ta shanye yogurt din yasa yafizge goran yana kabar da hannunta yamaida goran yarufe ya ijiye sanan yabude take away abincin yadaura kan cinyanta yace "eat" sanan yamaida kofan yarufe yana zagayawa yanadan dunkule hannayenshi yana budewa jin warmth na tafukan hannunta haryanzu akan nashi, bude kofa yayi yashiga sanan yatada motan yaja batare daya kalletaba tafiya kadan yayi ya tsaya awani pharmacy shiga yayi yadan jina kadan aciki saichan gashi yafito yazo ta side dinta, bude marfin motan yayi yana kallonta idanunta biyu yanzu sundan bude ga abincin daya ijiye kan cinyanta yanda ya ijiye haka suke, hannu yasa yadauke abincin ya ijiye sanan yabude ledan magungunan dayasiyo, syringe yaciro yana budewa sanan ya karya kwalban alluran daya ciro kafin yasa aciki yazuko allura ita kawai kallonshi take dan ko kadan batada karfin ko magana ba, tsugunna wa yayi yaciro wayanshi ya kunna flash sanan yamika hannunshi kaman bayaso yawani kamo hannunta, dan yunkuri tayi dadan karfin daya zomata zata fizge hannun wani irin mugun kallo yamata yace "wlh in baki natsu ba saina chak miki alluran nan awuya in barar dake awajen nan inyi gaba" gyadamai kai tayi ahankali tana juyarda kanta tanajin kuka na zuwan mata, hannun abayanta yaja zuwa sama ya saiti jijiyanta yamata alluran akai, ko kadan bataji zafiba saiwani sanyi dataji ajikinta har kwakwalwa, tashi yayi ya yarda komi a kwaran wajen sanan yashigo mota yaja, lumshe idanunta tayi jin sanyin datakeji yay yawa gashi ya kunna AC a motan, saikuma ahankali taji wani karfi na saukanmata ajiki dayasa gently tabude idanunta tana mikarda hannunta dataga yana mikuwan mata freely, gyara zama tayi kaman ba itaba, ahankali tadaga hannunta ta taba gashinta jin babu dankwali yasa tashiga waige waige a gefenshi taga dan kwalin dan kallonshi tayi yanda gabaki dayan hankalinshi kekan tukin dayake yi, dauke kai tayi saikuma ahankali tasake juyowa kaman wata barauniya takalli fuskanshi hasken fitilun motoci nadan haska shi, bakaramin kyau yayiba yay looking different sabida yanda babu jacket ajikinshi sai faran riga, dauke kanta tayi ahankali tamika hannunta dataji yana rawa tadauki dan kwalin sanan tayafa akanta ta juyarda kanta tana kallon hanya, almost 1hr drive yayi sanan suka shigo estate dinsu, agaban gate din gidansu yaga Ammi zaune itada Sharif looking damn worried suna hango motanci suka mike tsaye hakan yasa yay parking agaban gidansu Hajiya su Mami kuma suka karasowa wajen da sauri, bude kofan motan yayi yafita yanadan waige waige Mami tai kanshi cikeda fushi yayinda Sharif yay side dinta, bude kofan yayi ahankali yadaura idanunshi akanta yanabinta da kallo daga sama zuwa kasa ahankali yace "Du'a why? Bazaki iya zuwa office dina ki sameni ba eh? Why inda ace something happened to you fa daya kikeso nayi dakaina, kinsan how much u mean to me kuwa? I love you so much" yay maganan yana tsugunnawa agaban motan, kallonshi take tunda yake maganan nan, yanda yanuna yadamu da ita he's worried and fuskanshi yanuna yasa kawai taji kuka yazo mata dasauri tasa bakin gyalenta akan idanunta tana sharewa, daidai Ammi datagama wanke Asad ranta abace tazo wajen, ganin Sharif atsugunne ga Du'a na kuka yasa tace "maiya sameta Sharif Asad yamata wani abune kuma"? girgixamata kai yayi yana mikewa tsaye ahankali Ammi takai hannunta takamo Du'a tafito da ita daga motan tana binta da kallo rungumeta tayi tace "Du'a dan Allah kiyakuri kinji" ganin stain a sit din data zauna yasa gabanta nafaduwa taciro Du'a daga jikinta tace "are u on MP ne"? gyadamata kai Du'a tayi tana goge fuskanta tass, Ammi takama hannunta tace "taho muje wajen Hajiya" sanan tajuya takalli Asad dake inda tabarshi kanshi akasa tace "kazo nan kayi bayanin abinda kayima jikanta da bakinka Asad nagayamaka" taja hannun Du'a sukai ciki Sharif biyeda su, rufe motanshi yayi cikeda kunci ya biyo bayansu ya shigo ciki.
Da sallama Ammi tabude kofar falo Hajiya na zaune kan kujera tana karanta news, ganin Ammi da Du'a datai butu butu ga jacket daure a wrist dinta idanunta sunyi ja yasa tasauke jaridan dake hannunta takalli Sharif dake tsaye gefensu saikuma ga Asad da tana kallon fuskanshi taga kalan bacin ranshi, juyawa Ammi tayi takalli Asad cikin fushi tace "shigo nan, shigo ciki kayi bayani da bakinka" ahankali yashigo ciki yazo ya tsaya gaban Hajiya daya kasa hada ido da ita kanshi akasa, cikeda masifa Ammi tace "i said talk Asad"! hannu Hajiya tadagama Ammi tace "Zainab yahaka! Ba'a ma Babba fada agaban karami" tajuya takalli Du'a dake tsaye tace "wuce sama kije kiyi wanka ki chanza kaya" gyadama Grandma kai tayi tawuce ahankali saida takai sama sanan Hajiya tajuyo takallesu Sharif takalla tace "Ya akayi Sharif bakacemin Du'a will stay late zaka dawo da itaba, lafiya kuka tasomin d'a haka kunamai ihu aka" tai maganan tana murmushi kaman bata gane komiba, cikin wani irin kunci Ammi tace "Hajiya wanan ne d'a" tanuna Asad da kanshi ke kasa tace "inda yaci d'a dabai wulakanta Du'a haka ba, kinsan meyayi kuwa...." daidai da abu daya Ammi bata boyema Hajiya ba tafadi mata tace "wlh yau Asad na kunyatani" dariya Hajiya tayi tace "yanzu akan wanan ne kika taso yaron nan haka kina humiliating nashi agaban kannenshi Sharif da Du'a haba Zainaba" sake baki Ammi tayi tana kallon Hajiya, juyawa Hajiya tayi takalli Asad ahankali tace "Asad" dago kanshi ahankali yayi cikeda kunya ya kalli Hajiya murmushi tamai tace "thank you Allah yamaka albarka" sanan takalli Ammi tace "wlh wlh Asad baiyi kuskure ko kadan ba, hasalima mai laifin Du'a ne" Hajiya tadanyi shiru tace "nagaya muku sabida Du'a na jikata banso kubata wani special treatment yanda Asad will punish other employees that should apply to Du'a too as well, tambayan means of identity na mutum da bank account is normal procedure dakowani organization keyi, idan batadashi yanada right yacemata tawuce tatafi duk randa tayi tadawo I love that yes! Asad shows leadership skills awajen, laifin Du'a is boss dinta yabata punishment she could have pleaded kan ya yakuri zatayi gobe that's 1, secondly is dataje office din Sharif takarbi wayanta daganan zata iya gayamai shima yay pleading da Asad tazauna, thirdly is kodama yakoretan zata iya hanging around a mosque canteen kowani waje zuwa 4 direban ta yazo yadauketa su koma gida" Hajiya tai murmushi tace "Alhamdulillah I can now say that Du'a tafara girma, this girl spend about 8 zuwa 9yrs indoors ko falo haka ba'a barinta tasauko, tun Du'a na JS2 mahaifinta yay grounding nata, saisa idan ka dauko Du'a kasata cikin age mates dinta zaka gani she's totally different in the sense sunfita wayau sunfita iya da sanin komi, Du'a bata taba experiencing something like this ba, so it's time at 21yrs tasan what is life and what is life all about, thank you Asad, I promise zan kaita tabude bank sanan zamuje tayi national identity card sanan zata dawo" tunda take maganan Ammi ke kallonta harta gama tace "Hajiya yanzu bazaki ma Asad fada ba kan abinda yayi inda tabace fa" cikeda wasa Hajiya tace "idan mutum yay abin fada kinsanni nafi kowa iyama mutum fada but trust me this time Asad baiyi komi ba, and listen what all of you did today dagake Sharif Asad just shows ko bayan raina u all will stand for Du'a and support this my innocent child sanan kutayani training nata, so wlh harga Allah har cikin raina banji haushi ko riki Asad ba rather I am thankful dayake treating nata without sentiment and that's what I want bansan sabida ni aki ayi abinda yakamata" wani irin makirin murmushi Asad yayi kawai yaje yazauna kusada ita ga mamakinsu kawai rungumeta yayi yana murmushi sosai, murya chan kasa batare dasu Ammi sunji ba yace "I am sorry Grandma I didn't know that she will leave the whole building daban korata ba I am not that cruel" murmushi sosai tayi tana kallon Ammi dake kallonsu baki bude, tace "Yaya za'ayi ba'a shiga tsakanina da yaran nan sai hakuri Ammin su" wanan karan dariya Ammi tayi har cikin ranta takeson Hajiya, Hajiya mutum ce wlh she's super duper educated ga iya zama da mutane ga sanin yakamata.
Daure fuska Sharif yayi yakaraso yana kallon Grandma yace "Hajiya ni wlh kobazaki mai fadaba ni zanyi duk randa yakara something like this Allah saimun kwashi yan kallo" dariya sosai Hajiya tayi tace "to Oga Sharif tuba Asad yake" lekowa Asad yayi yamai gwalo Sharif yay kwafa, tashi Ammi tayi tana kakkabe jikinta tace "tunda mu aka watsama kasa a idanu bari mu nemi hanyar gidanmu mutafi, kai kuma Asad zamu gamu agida" tawuce Sharif biyeda ita, Ammi takalli Asad tace "Ammin ka tai fushi tashi kabita" gyadamata kai yayi yatashi yafita.
Assalamu Alaykum, inaso mu gina al'umma masu tsoron Allah da tsoron hakkin dan uwanshi musulmi, I was very kind and generous nayi pages talatin da daya (31) pages awanan littafin as free, dan Allah kudubi Allah badan niba badan halina ba karku karanta idan baki biya kin shiga group ba, dan idan kikai gaskiya Allah zai bimin hakkina.
Kudin karatun this novel is 500 kacal, pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting.
you can chat me up directly a watsapp by clicking on this link
wa.me/+2347012181461