1⃣&2⃣
A kwance yake abakin wani tafkeken beach , yana kallon duk matan dake kaida kawowa a wurin cikin fitinannun bikini da kuma lafta laftan sun glasses, wani irin ya mutse fuskar shi yakeyi domin kamar kashi haka yake ganin su, ba Abinda ya dameshi, bayajin mace zata iya burgeshi just like that saboda shigar banza,
Kallon shi nayi dakyau, gayen ba laifi chocolate ne shi duk da banga idanun shi ba saboda suna boye a cikin sun glass, Amma nasan zasu kasance masu kyau da tsari, lips dinshi kuwa I can clearly see them suna sheki very soft and shinny, he is behaving like jinin sarauta Amma I don't know yet who is he? Gefen shi system dinshi ne tareda wayoyin shi guda biyu, daya tayi kara ya dauka cikin sauri domin ganin sunan dake jikin screen din wayar, "heartbeat, Hmmm no wonder mata basa burgeshi duk da yawon da sukeyi a gabanshi necked, sai dai me, yanda yake zuba shagwaba tareda maganar da yakeyi yasa mamaki ya cikani domin daga gani bada mace yake magana ba, is he a gay???
"Yaya please, wai kai are you really serious you are getting married??,
Banajin maganar dayan side d'in saidai Amsar shi, "of cos yaya dole inzo Auren ka nine fa best friend best brother and ur best partner in life, am coming insha Allahu, but kasan halin momy kuma I don't want problem shiyasa nake zama na a bangkok, is alright am on my way don't worry heartbeat, just for you.
Datse call din yayi ya mike, a lokacin na kalleshi da tsarin jikinshi daba riga sai guntun wando kawai ga six packs dinshi da suka fito gwanin burgewa alamar yana gyming, tareda kulada lafiyar jikinshi sosai, zare sunglass din yayi, na kalle sexy eyes da lashes dinshi kamar na mace zaro zaro, he is really handsome, one look zakiyi mai ki afka soyayyar shi indai zaki kalli wa'innan killer eyes dinshi, gashi ya iya juyasu, kamar wani karuwar namiji, cikin takun kasaita ya zura beautiful sleepers dinshi na maza ya kwashi kayanshi tareda key ya nufi can gefe inda ya parker open jeep dinshi, ya zube su tareda zama yajata a guje yabar wurin,.
Wani D'an madai daicin gidane a cikin jerin gidajen dake cikin unguwannin dake shahararriyar Unguwar ta
Phetchaburi Road, Makkasan,
Ratchathevi, Bangkok 10400 Thailand. unguwa ce ta wanda ya tada Kafada da Abubuwan duniya, duk da gidan da ya shiga ba wani kato bane amma kana ganin shi kasan ya gaji da haduwa, maid dinshi ne yayi saurin taron shi da gorar ruwa tareda towel, karba kawai yayi ya nufi bathroom, ya dauki Kusan hour guda kafin yafito kamar zai canjo fata,
Yana fitowa daure da guntun towel ya tsaya Turus tareda zubawa dakin ido yana mamakin ta, tayi mai dai dai tareda kashe shi da idanu, he just hate that character a wurin mace, shi so yake rana daya Allah ya hadashi da mace mai kunya, that is, tagama siyemai zuciya, but this kind of girls dake rayuwa a irin wannan garin wai in the name of study, Ahh he really hate them, karuwai kawai,
Ganin kallon rainin wayau Dayake watsa mata yasa ta zaburo tareda matsowa cikin rangwada, doguwar riga ce har kasa she cover all her body but akwai gyara a al' amarin ta, duk da kyakykyawa ce gata a dire, kuma fara tas bai hana kagano idanun ta sun bude,.
"Hey dear tafada cikin kashe murya, wani irin kallon don't touch me ya mata tayi saurin daga hannun ta sama tareda cewa "is ok I won't dear, but please just once give me chance to prove myself.
"Dont even try to suffer ur self, nafada miki fauzy am not interested, just back up. " am ready to follow you I promise zanyi duk y'anda kakeso am ready to change for you, nafada ma dady na kai nakeso zamu koma kano tare dakai please na horu ka soni don Allah, "Look don't even try, bazan Auri sauran wasu ba infact am not ready for marriage now shiyasa dana gama school naki komawa gida saboda nasan Abinda zai faru, don haka kifita a rayuwa ta banason naci. Kuka tasa mai tareda dukawa kasa, "I swear bantaba bari wani yasanni ba kawai romance ne kuma kasan is a normal thing ai, kana ganin saboda kai nakasa komawa gida kullum cikin karya nake musu please karka tarwatsa min Rayuwa kaine cikon numfashi na, tausayin ta yaji sosai domin ta dade tana wahala a kanshi tun baya kulata har yafara D'an sauraran ta, "Oh come on, kinsan natsani kuka ko, ki shirya am going tomorrow mutafi nija am going for good, if you are ready..... "Of cos dear am ready, tafada tana dariya mai hade da tausayin kanta, goge hawaye tayi tafita cikin sauri domin ganin ta tattara duk Abinda zata bukata.
"Ahhh yafada tareda dafe kai, this girl is headache I swear,
Shiryawa yayi cikin guntun wando da black singlet yafito gwanin burgewa sai tsadadden agogon shi da kuma dankwalelen zoben dake karawa hannun shi tsari da kyau wa'inda baya taba rabuwa dasu, infact ko shopping zaiyi agogo ne first a tsarin shi he just love watches saboda suna karamai tsari da kwarjini,
Abincin shi ya zauna yafaraci wa'inda duk ganye ne sai crabs roasted ones, saida ya dauki lokaci kafin ya kammala ya sanya tissue ya goge bakinshi ya mike, duk al'adar Chinese ta gama ratsa shi abincin su harshen su al adunsu, wainda zasuyi matukar wahalar dashi a nija,.
Saida yayi clearing komai a daren, about visa da sauransu, karfe uku na Asuba jirgin su ya daga wanda zai kasance long journey duk da a jirgine, tafiyace ta Kusan awoyi, tana zaune a gefen shi ta zuba mai ido sai faman danna system dinshi yakeyi like ba wata halittar dake existing a kusa dashi,
She don't bloody care tunda yace su koma nija tasan komai zaizo cikin sauki,
Saida ya dauki lokaci kafin ya rufe ya saka headphones ya rufe idanun shi yana farin cikin zaije wurin yayan shi wanda yafi kowa daraja a duniya a wurin shi yana mashi so mai girma yana kaunar shi fiyeda kanshi,
Duk da su marayu ne ubansu ya mutu tun yana D'an karami, baiyi lacking komai ba, domin baban su gawurtaccen D'an siyasa ne kuma D'an kasuwa wanda yanada share a manyan campanonin dake ciki da wajen kasar mu harma da ketare, subiyu ne kacal wurin mahaifiyar su, yayan shi Ahmed sai shi Ibrahim khalel wanda khalel din ne yafi amfani dashi,
Gatan da yake dashi baya faduwa haka kudi ba matsala bane a rayuwar su domin mahaifiyar su itama ba azaune takeba tana aiki da first bank tareda matsayi mai girma,
Akwai banbancin hali a tareda shi da d'an uwanshi, domin shi mai zuciya ne, shikuma Ahmed yanada sanyin hali da hakuri, shakuwa ce mai girma da tausayi a tsakanin Y'an Uwan biyu sukan iyawa juna sadaukarwa ta kowacce hanya, tun suna yara balle kuma yanzu, kowa yasan how they love each other, don haka ko ginin su a hade yake basu taba raba gida ba duk da sunfi karfin hakan, katoton gidan mahaifin su suka kara fadadawa tareda buga plat biyu nasu tangama tangama sai na mahaifiyar su wanda a ciki ma akwai part part dinsu, domin bataso suyi mata nisa, mace ce mai tsananin zafi da kuma rashin hakuri gashi bata son sunan talaka bare kuma talauci batason rashin Aji a rayuwar ta don haka kullum burinta ta fantama, bakaramin shiri takeyi a Auren ya'yan taba tunkafin su tashiyi ma, saidai kash ansamu akasi domin Ahmed ya kaucewa tsarin ta ta hanyar dakko Y'ar talaka tulus, wanda bakaramin daga akasha ba kafin ta Amince da zancen Auren bayan dogayen sharuddan data gindaya bayan Amincewar ta. To muje dai zuwa yanzu zamu fara,.
Karfe goma jirgin nasu ya sauka a babban filin jirgin na Aminu kano, wanda sukaci karo da motoci birjik a jere na taron su, tuni fauzy ta matso "you see kamar jira akeyi indawo kaga irin motocin da sukazo daukana please ka yarda muje gidanku after two days sai intafi gida. "Hmm yafada tareda watsa mata kallon you lost ur mind, kafin ya ce "al adar Chinese ce wannan ba ta bahaushe ba don haka go home zanyi inviting dinki to my brother wedding ok,. "Ok tafada cikin farin ciki, ta nufi masu taron ta wainda kana ganin motocin kasan itama Y'ar gidan wani kwallon barawon kasar muce,.
Hango yayan shi da yayi yasa ya tafi da sauri cikin farin ciki ya rungume shi, Ahmed din ma kyakkywa ne suna matukar Kama saidai shi fari ne while Khaleel chocolate ne, "my yaya kai kadai kazo were is mommy?
"Long story muje ko, yafada yana karbar jakarshi karama tareda bawa driver umarnin kwaso kayan da yazo dasu yakai boot, saida suka zauna yace "Am sorry yaya sai jiya nayi placing odar na kayan matar ka zasuzo tunda by air ne kafin bikin insha Allahu nasan zakaso su.
Rungume shi yayi cikeda farin ciki tareda cewa "tank you my kani, but please karka bari momy tasani kawai zamu Ajiye mata ne a dakina har akawo ta. "Why? Cos momy batason ta infact bakaramin yaki akayi ba kafin ta Amince ayi komai. "Mommy mommy bazata canja ba, so why she hate her? "Because she is poor. Saurin kallon shi yayi "so brother is your foult kasan momy tunfarko ai why ka dakko poor girl uhm?
"Because I love her so much I love Naziya a lot khaleel, she is innocent and young she is very cute I can't help it, bazan iya Auren wata ba in har aka hanani zama da ita. Rungume shi yayi cikeda so da kuma tausayin D'an Uwan nashi yace "is ok am here you know I will support you, don't mind mommy, but her name is unique. "Yeah she is also unique brother, yafada yana lumshe idanun shi tareda jin soyayyar ta mai zafi har wasu irin madarar ruwan hawaye ne suka taru a idanun shi,.
A cikin fitacciyar unguwar ta sulaiman crescent suka yada Zango cikin wani tafkeken gini na kece raini, tsarin gidan kamar a turai, ya fito tareda shakar iskar kayan marmarin dake zagaye da ginin gidan,
Harabar gidan shake yake da motoci different product da kuma runfuna na Alfarma dake karkashin bishiyoyin kwakwa ta ko ina irin na gargajiya da masu kudi keyi,.
Kallon shi Ahmed yayi tundaga kasa har sama "bazaka canja character dinka bako yawo daguntayen kaya imagine tundaga bangkok kazo da three quarter da t shirt baka ko jin sanyi? "Kamar ka mantani ko yaya nifa I hate heat wallahi shiyasa nake wuni a beach., zaka hadu da momy muje ciki,.
A tafkeken katon falon an tsara shi fiyeda tunanin mai karatu kujeru Kusan set uku ya mamaye amma da sauran fili kowane set da center carpet dinshi masu laushi da nutse kafafu, standing art tangama tangama ta koina bayan na jikin gini wainda suka zama kamar decoration a falon,
A tsaye take tanata kai da kawo kamar Y'ar sintiri tana jiran fevourite son d'inta, ya iso, ta hana masu aiki sukuni sun kalkale but parts dinshi yafi sau uku da safen nan, dishes kuwa kamar a hotel saboda d'oki,
Macece hakima kamar Aisha D'an kano margayiya taci Abuja style cikin tsadadden leshin ta wanda yafi karfin dari a jikin ta, da glashin ta na kara karfin idanu, wanda yakara fito da haiba da hutun ta harma da masu gidan ranar data tada Kafada a ciki,
Sallamar su yasa tamike cikeda fara'a tana "Oyoyo my happiness welcome back dear tafada tana rungume shi tareda bubbuga bayan shi, "tank you mommy munsame ku lafiya? "Alhmdulillah tafada tareda dagowa tana "ai dai tunda kadawo yanzu zanji saukin lamura na at least inada inda zancika burina, ka huta ka dage ka dakko min Y'ar gidan bayero ko buhari, ka huce min takaici. Tafada tana watsawa Ahmed harara, dukar da kanshi yayi tareda daukar Karamar jakar D'an Uwan nashi yayi ciki da ita, zama tayi a set daya tareda janyoshi tana faman korafi tun bai hutaba, " hope zaka dakko Y'ar gidan mutanen arziki kai ba Y'ar matsiyata ba? "Mommy mommy mommy please meyasa kike hakane? Nifa am here because of my brother, kinsan banason korafi kibarshi ya Auri choice dinshi koda cripple ce tunda shi zai zauna da ita please allow him to be happy I beg of you. "Shikenan tunda kaima kabi bayan shi, amma promise me zaka share min hawaye kaji? "Ok I promise bari inje in huta am tired, fresh up akawo maka abinci a ciki ko? "Yes please kinsan me nakeso ai ko? "Sosai karka damu na shirya maka komai.
A zaune yasamu brother dinshi yana dafe da kanshi ya zauna tareda dafashi cikeda tausayi "relaxed bro am here komai zaiyi normal kaji, Aunty what ma sunan ta? "Naziya, yafada fuskar shi na washewa domin sunan ta kawai nabashi farin ciki, "get ready zamuje unguwar su anjima kaganta kaji. "Ok my heartbeat. "Stop that name kafin my Naziya taji tayi kishi fa. "Oh no yaya zata shiga tsakanin mu ne, to nima zanbi bayan mommy fa. Rungume shi yayi tareda cewa "no no no tasan da zaman ka, tundaga lokacin da muka fara haduwa, da ita, ka huta zanfada maka komai game da ita kafin muje gidan,.
Karfe biyu ya farka daga baccin gajiyar da yayi yaga Ahmed zaune ya na baza kamshi cikin D'an datsesiyar getzner tana maiko, tashi yayi "yaya har kayi wanka? What is the time now? Agogon shi ya nuna mai ya zabura yana holy shit, ya diro a lumtsumemiyar katifar shi, yayi bathroom domin baiyi Azahar ba, cikin sauri sauri ya zura jallabiya ya tada sallah, domin duk abinda yake yi baya son wasa da ibadar shi amma idan ka kalleshi zaka dauka rayuwar duniya tafi komai ratsa shi amma yarone mai riko da Addini bisa ga goyon yayan kwarai da yazamo mai tamkar uba.
Saida ya idar ya bude jakar shi tareda ciro kananan kaya.
"Wait gidan kawu zamuje a mandawari kasan halin shi ka sa manyan kaya nasa an shirya maka new ones a wardrp dinka na nan dana can side d'in.
"What? Kasan nifa banason zafi ga garin nan da zafin tsiya kuma insa kayan da zasu hanani sakewa, "wait yaya ba an gama zuba komai ba a part dinmu why muke nan har yanzu? "Bisaga umarni na khaleel bazan yarda a saka Y'ar talakawa cikin ginin da na narkarda dukiyar mijina datawa ba, a kawo min gayyar k'uma da kudin cizoba ta zo nan ya isheta zama tunda bazata iya zama a katon giniba, domin ko dakin generator dinmu yafi gidan ubanta girma,. Saurin kaucewa khaleel yayi domin inda sabo sun saba, ya nufi katon wardrp din yaga kaya shake saida yayi murmushi saboda yasan aikin yayan nashi ne,
Fito da Kala daya yayi irin na jikin shi ya nufi hanyar bathroom domin ya canja saboda mommy dake dakin,
Tana zazzaga complain, fitowa yayi tareda rungume ta yana baza kamshi shima kanshi da yasha askin matasan zamani ya na sheki ya sha gyara ya ce" mommy please enough of your complains kibar yayana yasamu farin cikin shi mana,. "Oh wato kuna tunanin bansan what is best for him ba ko? Bayan na kawo mai yammata Kala Kala Yaran kawaye na masu ilimi amma ya nace sai Y'ar talakawa mtsww, ka kara Abinci kafin kutafi gidan kawun naku kafin yazo yana baza min fitinar shi shima yace na hanaku zuwa ku gaidashi, ta fita tana kasaita, "Hmmmm Sorry brother kariga kasan halin momy. "Is ok eat muje ko?
Hour guda ta kaisu gidan na kawun nasu Alhaji modu mai gwal wanda D'an kasuwa ne sosai a harkar gwalagwalai, mutum ne a tsaye akan zumuncin shi domin baida wasa yanada mata biyu da yara sunkai goma, shikadai Hajiya balkisu ke shakka domin yafita fitina kuma shima yanada kudi shiyasa take ragamishi domin sau tari yakan yimata Abu tace yaci Arzikin Aljihun shi.
Sunada kanni biyu mata bayan mahaifin su khaleel shine babba sai Alhaji modu din, su Y'an Asalin garin maiduguri ne iyayen su ne suka kawosu babban birnin na kano, sunginu suma duka domin ba talaka a cikin su har matan ma domin suna gidajen kusoshin kasar mu,
Y'an mata ne birjik a gidan wainda kowaccen su nada burin samun daya daga cikin wa'innan zaratan mazan saidai sam su Hankalin su baya kan kannin nasu infact basa burin Auren zumunci ma, itama Hajiya balkisu bata ra'ayi domin batason ya'yan ta suyi Aure inda bazata iya juya Suruka ba,,
Domin tasan Y'an Uwan mijinta duk ba wai mutunci sukeda shiba wanketa zasuyi akan ya'yan su,
Sun samu tar bar bangirma daga uwar gidan Kawu modun kafin ya dawo,
Sundauki lokaci a gidan har kawun nasu yazo, wanda yayi farin ciki sosai ya musu nasiha tareda basu shawarori, "yanzu tunda kadawo khaleel saika tallafawa D'an Uwan ka domin yayi matukar kokari wajen tafiya da campanoni da kuma masana'antun ku, sai kuci gaba da tafiyar da kasuwancin ku cikin tsari, Sannan naje munyi magana da uban Naziya, Auren naku nan da sati biyu aka tsayar don haka ka je ka karasa shirin ka "na kammala komai kawu ni ta wajena. "Toh masha Allah, sai mu jira lokaci Allah ya tabbatar da Alkhairi, Amma dattijon nata mutumin Arziki ne baidamu da Abin duniya ba gaskiya karka damu da shirmen mata wannan gidan irin shi ya kamaci namiji ya nemi Aure. Wani irin dad'i yaji tareda sauke Ajiyar zuciya, saida suka yi magrib kafin su bar gidan, suna hanya yana bashi labarin Naziya,........ 🖊
*watch out, domin salon zai tafiyar daku masoya muje zuwa*
*Matar Soja*
🌻🌻 *AUREN GADO* 🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,
🆓 page
3⃣&4⃣
.............. D'an karamin gidane mai zaure a cikin tsohuwar unguwar ta jakara, almajirai ne birjik a zauren da Alama malami ne a gidan mai Y'ar Karamar tsangayar Almajirai, ko tsakar gidan ma akwai wasu dakuna dake dauke da Almajirai, rayuwar gidan sun dauki Almajiran kamar Yaran gida ba kyama ba wulakanci, matar gidan inna kulu mace mai hakuri, tanada ya'ya mata guda hudu manya biyu sunyi Aure sai Naziya da kanwar ta Shukrah, Yanzu Naziya nada shekara goma shatakwas sai shukrah mai shabiyar, ta kammala secondary dinta Bana a makarantar gwamnati, a tsugune take tana wanke kwanonin da suka bata Y'ar Karamar wayarta ce a kunne a gefen ta tana sauraron karatun Al'qur'ani mai girma tana bi a hankali cikin kwarewa,
Kare mata kallo nayi domin yarinyar batayi Kama da kalar talaka ba domin dai dai da duddugen kafarta farare ne tas kyakkywa ce sosai kamar wata Y'ar larabawa tana sanye da guntun hijabi akan al adar ta da kuma koyarwar inna kulu domin gidan su akwai mazajen Almajirai akoda yaushe, fitowa dattijuwar tsohuwar tayi tareda cewa "inkin kammala ki dora mana Abincin rana Naziya, shukrah ta kai mana markade tunda duk babu Almijirai yau, "toh Inna. Tafada tana wanke wurin data bata, she is really cool and beautiful ga tarbiya dake tattare da ita jikinta ba rama kuma bakiba duk da tana cikin hijabin ta nagano hakan jikinta D'an dai dai bazaka taba yimata kallon talauci ba duk da Abinci baifi karfin tukunyar suba, mahaifin su yana koyarwa yana sana'oin shi wanda yake daukar gidanshi da kuma hidimomin iyalin shi,
Haduwar ta da Ahmed wata rana ce tadawo makaranta a gajiye shikuma yazo unguwar su gidan wani yaron shi dabaida lafiya, tafiya takeyi cikin gajiya a kuma natse ta gefen titi, y'anda ya kwaso motar tashi yasa ya watsa mata ruwan datti kasancewar gari ne na damuna ga kuma yanayin unguwar da yatara guraben ruwa ta ko Ina, saurin jatayi ta tsaya domin gaba daya uniform d'inta ya baci Har fuskar ta ma ruwan ya fallatso mata, saurin fakawa yayi ya fito da sauri yana so yabata hakuri,
Dago kyawawan idanun ta tayi tareda goge fuskar ta da gefen hijabin ta inda jan ruwan bai bata ba, ta kuma kallon y'anda ya saki baki yana kare mata kallo batareda ya iya cewa komai ba, yarinyar ta gama tafiya dashi, juyawa tayi ganin baida niyyar cewa komai tayi gaba, saurin shan gaban ta yayi "Am sorry please ki tsaya muyi magana, ya zaki wuce batareda kince komai ba bayan nayi miki laifi?
Saurin Tsayawa tayi tareda dago idanun ta masu narkar da zuciya tace "nice zanbaka hakuri domin hanyar bata Y'ar talaka bace Nazo kuma na tsaya, sannan don Allah ka matsa in wuce kafin ayi wani tunani akaina a cikin unguwa ba mutuncin gidan mu bane tsayuwa da bako a kan titi. Tafada tana rabewa tayi gaba.
"Wow wow wow what a magic voice, yafada yana binta a hankali tana sauri har ta fada gidan su da gudu domin tana jin takun shi a bayan ta a mugun tsorace take dashi domin yayi Kama da Aljani a wurinta domin he is very handsome kana ganin shi kaga D'an hutu,.
Gefen Ahmed tunda yasa Naziya a ido yakasa sukuni saida yabi ta gefen yaron shi yaji komai akanta, tuni yagano Y'ar babban gidace wato gidan dattijan kwarai, baiyi kasa a guiwa ba ya dawo yasamu mahaifinta tareda neman izinin neman ta, Malam garba yaso ya hana domin ganin D'an gidan wani ne Bayason ya saka Y'ar shi cikin matsala, ya nuna mai mahaifin shi ya rasu kuma shike rikeda kanshi ba wata matsala, bai Amince ba saida ya turo kawun shi yazo suka tattauna ya Amince yabada izinin neman ta,.
Allah yagani bawai Ahmed baiyi mata bane, ita batada burin shiga gidan da yafi karfin ta wanda bata ma riga taga dukiyar ba tukun kawai shitake gani kudin su na bata tsoro, ganin irin k'a'i dar mahaifin ta, baya ko sake mata kudi infact tuni ya daina zuwa da shigar da zata hanata sakewa dashi domin ya lura da yanayin ta dana gidan su tsab, yasamu kanta ta hanyar nuna mata akarkashin wani yake shima yana hustling ne,. Shiyasa yasamu kanta har ta Amince suka Gina soyayya mai karfi a tsakanin su she really loves him domin he is very simple baida fushi baida girman kai saurayi ne mai natsuwa wanda ko yatsanta bai taba kokarin kamawa ba soyayya yake mata mai tsafta, har kawo yanzu da Al amarin yakai ga zancen Aure, zaman ta dashi tagano Abu biyu sune masu matukar muhimmanci a rayuwar shi, mommy and khaleel wanda basa hira sutashi bai kira sunan shi ba tagano irin tsantsar soyayyar da yakewa kanin nashi ta hanyar bata labarin shi a kullum zaice "in munyi Aure zaki rika dafa mai Abincin da yakeso baya son irin namu na nija zansa akoya miki irin dishes din da yakeso. Abun na bata mamaki ace mutum Abincin mu na nija mai shegen test baya burgeshi sai mara magi? she almost know everything about him by now saboda labarin shi, tasan yana karatu a waje kamar yadda Ahmed yafada mata kawun su ya kaishi waje karatu, Ita kanta so take taga wannan khaleel din da labarin shi baya karewa a bakin Ahmed,. Tana son Ahmed sosai halin shi, yanayin natsuwar shi ya banbanta da na samarin zamani masu burin cakumar mace da sunfara soyayya........
Wannan shine D'an takaitaccen labarin Naziya da Ahmed.
A hanyar su ta dawo wa daga sabon titi yake bashi labarin komai na su Naziya tareda fadamai boye mata kudin da yayi saboda batason mai kudi y'anda ta nuna mai. Khaleel yasamu kanshi da yin dariya, " she is funny wace mace ce batason hutu da kudi in this era? " my Naziya wants a simple life ba a ginata akan greedness ba, all this kyale kyalen duniya basa burgeta do you know nasha siya mata gifts in ajiye domin gudun matsala ko fushin ta, do you know tun zaman mu bata taba demanding tana bukatar wani Abu a wurina ba, "she is such a diamond in the rocks, she is different khaleel my Naziya is perfect I told you. "Hmmm Allah yasa tana sonka like you love her? "She do Insha Allahu, koda baikai wanda nake mata ba nasan tana sona,
Karar wayar khaleel yasa yace "my God this witch. Yafada yana cutting call din. "Fauzy right? "Yes yaya ta cika naci bana son mace mai naci. "Hhhhh you are lucky khaleel fauzy batada laifi and secondly irinta mommy keso Y'ar gidan wasu kaga babanta ne minister na kudi, don haka bakada matsalar mommy kabada kai musha biki bayan nawa. "Yaya why ake Aure? "Hhhh khaleel saboda Aure sunnah ce mai karfi, sannan ba Abinda ke karawa namiji mutunci irin Aure, ga kuma samun natsuwa da soyayya idan kayi dace. "Yaya I don't need any natsuwa a wurin mace ni. "Ah bakada lafiya ne? "Kalau nake kawai bana jin akwai macen da zatasa inji ni a namiji sai kawai in lafiyata ta motsa,. "You are wrong khaleel, kana samun macen da kakeso manhood dinka yadaina kwanciya cikin sauki, domin the moment you fall in love, zaka ji duk duniya ba Abinda kakeso sai kasamu kwanciyar hankali da farin cikin zuciyar ka, you are my younger brother but bazan boye maka ba na matsu ba a daura min Aure da Naziya ba am eager to have her ban taba jin lafiya ta tana aiki ba saida na hadu da ita, don haka kaima duk ranarda ka afka soyayyar wata zaka gano komai. Dariya kawai yayi domin shi yasan lokacin da kawai yake samun erection sai inya tashi a bacci yake sanin he is healthy ba wata Y'ar macen dake daga mai hankali domin bai sawa ranshi ba ma bare Abun duniya ya dame shi.
Cikin unguwar suka nufa wadda tuni yaji wani iri musamman irin kofar gidan dayaga sun tsaya Almajirai birjik sunata karatu ga hasken farin wata daya dallare KO Ina fiyeda hasken lantarkin dake wurin, wayar shi ya daga tareda danna number ta, ba bata lokaci ta daga hade da yin sallama, "Gimbiya kifito ku gaisa da heartbeat tare muke dashi.
Cikin murna ta mike tace "gani nan zuwa yanzu inga wannan kanin namu.
Yana kishingide ko motsi baiyi ba impact bayajin zai iya fitoda takalmin shi wajen wannan unguwar, dole momy tayi spark ai, don ma batazo tagani ba ma da in sama da kasa zata hade ba Yarda zatayi ba yasani.
Fitowa tayi cikin natsuwar ta sanye da hijabin ta, ta karaso jikin motar dayake tsaye nad'e da hannu, ya zubawa kofar gidan idanu har ta karaso kusa ta d'an tsaya nesa kadan kanta akasa ta gaida shi, "Ina wuni. "Lafiya kalau gimbiya ya kike? "Alhamdulillah, cikin muryar ta mai cikeda natsuwa, kwankwasa glass din motar yayi, ya sauke a natse tareda gyara zaman da yayi kamar wani sarki, kamshin shi mai matukar tsada ya huro tareda muryar shi mai cikeda wasu irin sirrika suka sakata dago kai cikin sauri,
A cikin kyawawan idanun shi nata yasauka domin hasken motar na haskashi dakyau, wani irin sanyi jikin ta yayi Mata domin Sam baiyi Kama da sunan kanin Ahmed ba a wurin ta saidai Yaya, irin cika motar da yayi da kwarjinin shi tareda kamshi da cikar haibar shi, kallo daya ta sauke idanun ta akanshi Wanda tsab da ita gwanace ya isa ta Zane hoton shi, daga ganin shi bazaiyi yawan magana ba, kuma zaiyi miskilanci sosai. Tunanin ta ya katse ne lokacin da taji saukar muryar shi a cikin kunnen ta "Yayana naga Auntyn zamu iya tafiya ko? Shine kalmar data fito kawai batareda gaisuwa ko wani dogon zance ba. Ta shirya sakewa dashi domin karo dankon soyayyar ta a zuciyar Ahmed, amma is impossible yanzu don taki jinin girman kai da nuna isa just because yaje waje karatu, tuni taji yafita a ranta takuma daura damarar Kama kanta da Al amarin shi koda ta shiga gidan nasu,. Saida Ahmed ya leka kanshi tareda zuba mai ido "come on brother kafito mana ku gaisa da kyau, "no mungaisa daga nan ka sallameta mutafi nagaji kasan bangama hutawa ba, yafada a mugun kagare yake subar wurin yanajin warin Almajirai daga inda yake Idan yakara more minutes a wurin he will surely vomit,. Ya lura da yanayin shi don haka a gurguje ya sallameta ta tafi tana mai jin takaicin wannan khaleel din,.
Yana tada motar yace "Yaya wannan Y'ar yarinyar zaka Aura? Why?? she is too young for you please, fuskar shi a kwabe, "hhhhh she is perfect banason Auren katuwar mace ko over twenty nafison irinta mutum ya mori kuruciyar ta yafi Amma Idan ka Auri wayayyun mata bazaka mori komai ba, nafison innocent girl da zankoya wa komai,. "Hmmm zakasha aiki wallahi ai wahala zakayi kafin wannan ta iya daukar ka, kuma Yaya iyayen ta suka yarda suyi mata Aure? "Yes saboda mu anan takai Aure tunda ta kammala secondary,.
"What? Yaya this is too much, da Ina nan bazan bari kafara sonta sosai ba gaskiya. "You are too late now, domin inaji a jikina Idan ban Auri Naziya ba zaku iya rasani so ku tayani Addu'a kawai Ina son ta fiyeda tunanin ka nasan you will always support my back. "Of cos brother Insha Allah.
Karfe goma suka isa unguwar su, Wanda mommy Saida taci gaba da fada "kunje ghetto Area ko nasani saiya jamun kai, ka wuce kayi wanka kazo kuci Abinci kaima wuce ka watsa wainnan kayan dustbin kafin ka dawo falon nan kajini ko? Wucewa yayi cikin sanyin jiki ya tafi dakin shi Yana mai jin bakin cikin halin na momyn shi, kasa fitowa yayi saboda rashin jin dadin Abun, shima khaleel kasa cin komai yayi ya kalli momyn dake kan korafi "mommy why please? Ki yi hakuri Ki daina fada akan abunda dole za ayi. "Yes za ayi Amma ni Balkisu bazan bari ya cakuda min iri da na talakawa ba mu zuba tunda dangin ubanku sun nuna sunfini iko akan shi ni kuma zan nuna musu sai naso komai ketafiya mu zuba nida su.
"Momy ji nake kamar in koma bangkok kawai domin bazan iya tsayawa inga d'an uwa na a damuwa ba, please Ki barshi ya samu natsuwa mana. "Khaleel, kana ganin uwa zataki d'an tane? Ina son Ahmed kamar yanda nake sonka saidai bazan iya kawar da idona akan kwashi kwaram din da zai debo min ba.
Mikewa yayi kawai cikin fushi yabar mata Abincin yayi dakin yayan nashi, a kwance yake Yana tunani, dafashi yayi, dagowa yayi tareda rungume Khaleel din, "brother am worried, bansan irin zaman da zamuyi da Naziya a gidan nan ba, bana so injefa Y'ar mutane a damuwa bayan an bani amanar ta. Bubbuga bayan shi yayi "karka damu Ina nan zan taimaka maka ba Abunda zai samu baby doll dinka. Yafada cikeda dariyar tsokana domin ya kwantar da hankalin d'an uwan nashi,
Shigowa tayi dauke da tray tana fara'a domin taga Alamar Idan tayi sake yaran nata zasu juya mata baya akan zancen Auren nan, Wanda bazata taba Yarda da hakan ba,
"Toh yaran momy ga Abincin nakawo muku ni na damu kuci, kashin awaki, ta ajiye a tsakiyar gadon tareda jansu da hira kamar zata mayarda su ciki, tuni suka ware suka kwashi deshes din, tana cewa "bayan rasuwar mahaifin ku nayi iya bakin kokari na ganin bakuyi maraici ba, Alhamdulillahi yau dukan ku kunkai matasa Abun Alfahari a wurina, forgive your mother Ahmed na dauki buri mai girma akan ku naso nice zanyi maku zabin matan da suka dace daku Amma ka watsa mun duk shirina Ahmed. "Am sorry momy, kuma nayi miki Alkwarin zaki samu Naziya a duk yanda kikeso bazakiyi dakin sani ba yarinyace mai tarbiya da kin Amince da tuni nakawo miki ita ma kingan ta. "Aa tunda ansa rana ai lokacin zaizo don haka basai ka kawo taba, bakomai zan cika burina akan khaleel. "No mommy khaleel ma yanada tashi zabin ai, yafada Yana kashe mai ido, "no no no bana sonta Yaya please meye haka she is my mate fa tare muka kammala karatu why zaka ce Ina sonta ita keso na ni banga Y'ar da zanso ba har yanzu'
Wani irin dadi mommy taji ganin khaleel bazai juyuba a wurin mace tunda ita keso shi bayaso ai irinta takeso, "wow Auta na wacece wannan yarinyar? "Mommy Y'ar gidan minister kudin Nigeria ce, "what? Tafada tana dafe kirji, "Y'ar gidan mai nasara kake fada? Oh my god khaleel, ta rungume shi, that's my son, ka kawomin ita kaji kace tazo inganta Amma ka gama wanke min zuciya d'an nan. Tafada tana mikewa bari inkira Auntyn ku infada mata tafara shirya mana babbar harka ta Fita tana danna kiran kanwar tata mai ra'ayi irin nata. Binta sukayi da kallo suna mugun mamakin halin na mommy, sai kace wadda bata jiku da kudi ba, kullum she is hungry for more, kallon Ahmed yayi da fuskar tausayi yace "why zaka fada mata Yaya kasan am not ready, kuma yanzu tunda taji bazata taba bari insha ruwa in Ajiye cup ba. "Is OK fauzy love you a lot kuma meye laifinta nasan tun lokacin da kuke tare, ya isa haka ka Amince bayan nawa kawai a daure min kai, do you know, Ina mafarkin ganin Auren ka? Ina so inyi witnessing Auren ka inga jinin ka. "Hhh oh come on Yaya kamar wani tsoho na barin wasiyya please tare zamu cika gidan nan da yara, "who know Khaleel? Allah kadai yasan me zai faru gobe, kasan cewa nan gaba kaine zaka rike gidan nan? "Why Yaya? Indai har kana nan bazan taba daukar girma ba saidai in tafiya zakayi dole in rike kana dawowa zanbaka komai domin ka shagwaba ni tuntasowa ta Abu daya nasani shine in saka master card dina inciri duk Abunda nake so ba tareda antanbaye ni me nayi dasu ba, Yaya nasan kudin da daddy yabari bawai haihuwa sukeyi da kansu ba kaine kakara habaka su har suka kai haka kaine jigon gidan nan bazan taba iya Abinda kakeyi ba...... "Shhhhhh zakayi Idan bana nan fiye ma da Wanda zanyi saboda I believe kai jarumi ne kafini iya tafiyar da Rayuwa. "Enough of this discussion kana sani a damuwa. "OK now kakira fauzy kafara bata kulawa domin tunda zancen yaje kunnen mommy ba fashi, yafada Yana dariya,.
Fita yayi daga dakin yayan nashi yanajin wani iri "Aure? Gaskiya bai shirya ba infact zaiyi ne saboda yayanshi ya insisting kuma koda baison Abu Idan yayan shi na sonshi dole shima ya soshi, Allah kadai yasan iyakar soyayyar da yake wa d'an uwan nashi, kwanciya yayi a kujera a dakin nashi Yana mai runtse idanun shi, so yake ya tuna komai na fauzy da quality's dinta just for Ahmed, Amma first thing da yafado mai a rai yasa ya zabura tareda girgiza kai, "no no no why her?
Cikin Sauri ya dauki wayar shi domin ya k'aryata tunanin shi, fauzy ya Kira, kamar mai gadin wayar ta ta dauka jikin ta na rawa "oh my goodness darling you call me? Tafada tareda Sanya kukan farin ciki, tundazu take kiranshi yaki dagawa har wani zazzabi takeji saboda damuwa tana yimai wani irin so mara misali. Tun isowar ta ake tarairayar ta Amma duk natsuwar ta bata tare da ita,
"Yes I call. Yafada Yana gyara zaman shi domin baisan ma mai zaice ba kuma. "Tank you darling for calling, please Ina so inganka kasan is hard for me kwana daya bansaka a idoba I can't. "Is OK zaki iya zuwa gidan mu gobe yanzu dare yayi. "OK am coming tomorrow tank you darling. Tafada tana buga tsalle tareda rungume filo, tasan yafara damuwa da ita tunda har yake so taje gidan su yanzu, hakurin ta ya fara aiki yanzu. Kwanciya tayi tareda Addu'ar gari yawaye ta ganta agidan su.
Gefen Naziya ta shiga gida da takaicin khaleel, domin yaron mugun d'an wulakanci ne, inba wai gizo idanun ta ke mata ba kamar kallon kyama yake mata, bayan duk unguwar su an shaida tsabtar su, duk da suna fama da Almajirai Inna kulu nada kokarin ganin ta tsabtace gidanta sosai,. Kwance take tana juyi shukrah ta matso gefen ta akan Y'ar madai daiciyar katifar tasu, tace "Aunty lafiya? "Hmm bakomai. "Aa Ina kallon yanda kike ta juyi tundazu kinkasa bacci, meke faruwa ne? "Kawai Ina tunanin yanda zan zauna da Ahmed ne tareda kanin shi shukrah dazu sunzo, baida k'irki irin Ahmed ya cika girman kai da nuna shiyayi karatu a kasar waje. "Ni kuwa Aunty kallon Arziki sosai nakeyiwa Yaya Ahmed fa. "No yafada min Yana da ubangida mai kirkine watarana motocin yake zuwa dasu, "nidai Aunty Ina tantama domin ko tsarin jikinshi ya isa ya nuna Yana cikin hutu. "Ni kuma me zakice dani? Tunda kowa kallon Y'ar masu kudi yakemin a school ko in munfita, halitta ce kawai. "Hmm tom kiyi bacci Ki kyale wani kanin shi Bashi zaki Aura ba.
Washe gari Karfe goma tayi mata a gidan su khaleel cikin tangamemiyar motar ta ta yayi, da kanta ta tuko kanta, da taimakon shi ta zo gidan domin unguwar su ba boyayya bace, momy ta zage sai rawar kafa takeyi an shirya mata tarba Kala Kala, cikin adon jan material doguwar Riga dinkin yayi na yayan masu daula, taci gwala gwalai wuya da hannayen ta tana zabga sheki da kamshi. Ta hadu ba sauki domin ta iya caba ado. Tasamu tarba gefen momy, Wanda koda tazo gidan bai tashi baccin safe ba,
Momy sai Ina ta saka Ina ta Ajiye takeyi da ita, sai zare idanun ta takeyi taga inda zai bullo. "Huh khaleel na bacci haryanzu bai tashi ba, kinsan da gajiya a jikin shi.
Shigowar Ahmed ne yasa Momy tace "ka duba d'an uwan ka ko ya tashi ga bakuwar ta iso. Gaisawa sukayi Yana Kara ganin wayewar ta da kudi Wanda yasan ba yanda za ayi Naziya tazo gidan nan saboda shi, banbancin yayan talaka kuma y'an gidan mutunci kenan da kuma ya'yan masu kudi. Yanzu meye Abun burgewa a nan mace ta nuna rawar kafa akan namiji, idanun fauzy ya gama budewa gaskiya and zasuyi kusan sa'a da Khaleel like he said, wucewa yayi Yana daya sanin bashi goyon baya akanta,.
A kwance ya sameshi Yana kallon saman pop, "oh you wake up? So kazo fauzy is here. "You see tunda Asuba mayyar ta tanbayeni address nafada mata don uwar ta a gidan mu zata karya? Dariya Ahmed yayi, "Auzubillahi yada zagi? "That's why Yaya bana sonta wallahi batada kamun kai Sam ace Karfe goma ta zo wurin saurayi saikace ba iyayen ta a gidan. "Yanzu dai katashi kayi fresh up kafito tana jira mother in law dinta ta bata big welcome. Tashi yayi ya shige bathroom, like Always Saida ya kwashe hour guda kafin ya fito Wanda shirin nashi ma Saida ya kwashi rabin hour cikin guntayen kayan nashi kamar yanda ya saba.
Cikin takun kasaita da shan kamshi ya fito falon, fuskar shi Sam ba fara'a, "ga shinan yaron kirki ya fito. Mommy Tafada tana mikewa tareda taroshi kamar wani kwai jitake kamar ta goyashi saboda so, jikin fauzy na rawa tace "hy darling kamar ta ruga ta rungume shi takeji. "Tashi kuje dakin shi zakufi sakewa bari insa a hado muku breakfast akawo ciki. Cikin sakewa tace "Saidai baby ni ai mommy kin cika min ciki tun zuwana kike duramin ciye ciye, Tafada tana Dariya, "Allah Y'ar nan, to bakomai ai gidan kune nan.
Zama yayi a falon fuskar shi a cakude yace "ke iyayen Ki basa gidane kika fito early morning? Kallon fuskar shi tayi tareda yin murmushi duk da tasan maganar banza yafada mata ranta bai baci ba, "mommy na nan dady na nan kuma sun san inda naje. "Really? Kuma basuyi kokarin hanaki ba? "Why zasu Hanani? Bayan su masu goyon baya na ne akan duk Abinda nakeso kasan cewa sun san komai akan ka dady na a shirye yake da katuro neman Aure na, please khaleel ka cika mun burina I promise zaka sameni yanda kakeso zan share maka damuwar ka duka zanbaka gatan da mata basa iya bawa mazajen su just give me chance.
"OK zanturo tunda mommy ta Amince dake and my brother too yanzu kije gida zanturo. Tsalle ta buga tareda Dane shi ta rungume shi kam" don Allah da gaske zaka tura? Oh my god khaleel zanyi suman dadi yau. Tafada tana share hawaye, ban bare ta yayi a jikin shi ya ce "oh come on a gidan surukai kike fa behave yourself.
"Farin ciki ne yamun yawa baby muje mota indakko wa momy tsarabar ta please, Tafada tana riko hannun shi, jinta takeyi kamar anyi mata bushara da gidan Aljannah....... 🖊
*Matar Soja*
🌻🌻 *AUREN GADO* 🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,
🆓 page
5⃣&6⃣
..,.......... Kaya na kece raini ta kawowa momy tsaraba Wanda tayi ta godiya kamar zata goyata, bayan tafiyar ta bata da wani zance sai na "Ibrahim khaleel bikin ka zamu gwan gwaje ba karya kaga Abun Arzikin da ta kawomin tun ba ayi Aure ba? Wucewa yayi cikin dakin shi domin shi yanzu daya sani yake mara iyaka daya Amince mata tazo gidan su har Mommy ta ganta, yanzu ya boni shikam.........
Wasa wasa Saida aka kwashe kusan sati daya bai kuma daukar wayar taba ta Kira ta turo msg yafi hamsin Yana shareta, momy tayi nacin zancen turawa gaisuwa Yana ja baya, domin shidai bai shirya ba infact baya ra'ayin zama da fauzy she is not his choice zai cutar da itane kawai, bazata taba samun kanshi yanda take soba. Bikin Ahmed da Naziya ya matso gefen gidan su shikadai ke shirin shi da Abokan shi Yana cikin tsananin farin ciki, momy tace bazata wahala akan Y'ar talaka ba, yan uwan tane dai suka fara cika gidan, musamman Aunty zarah, Wanda itace kanwar ta da sukazo hali daya, komai na Aunty zarah sai a hankali tana son gayu da babbar harka.
Duk akwatunan da Ahmed ya hada momy ta sa anrage duk wani gold tasa ancire ansa passion wai basu san darajar su ba talakawa ne. Baida yanda zaiyi saidai farin cikin shi daya Khaleel ya hadomai Nagani na fada a bangkok, don haka sunkai sun boye sai in ta tare, duk wani event mommy ta soke wai yarinyar da ba wayayya ba yaja musu Abun fada bada itaba, don haka ya hakura domin Albarkar Aure yake nema in Allah ya mallaka mai ita burin shi ya gama cika, sannan farin cikin shi daya itama tace bata son wani bidi'a walima ta isheta da za ayi a gidan su,.
Khaleel yana gefe baya cewa komai he just feel boring baiga Abun burgewa a yin Auren ba ba wani Abu da ya bashi sha'awa da har zaiji yanason yayi Auren ma, fauzy sarkin naci tazo tun Ana jibi Bikin ta tare duk inda Aunty zarah ta shiga suna tare gaba daya yabi d'an uwan nashi sun kauracewa gidan suna part din Ahmed saboda jama'ar da suka cika na momy, yaki ko Yarda su hadu da ita, ta d'an ji sanyi ganin tana cikin gidan su kuma no matter what sai sun hadu kafin ta koma gida, ita da ta samu daurin gindi a wurin uwar miji ma, ita kanta tasan mommy batason Auren Ahmed domin ta gama bata labarin ta tas.
Rana bata karya inji bahaushe, Alkawari ya cika, inda Aka daura Auren Ahmed da Naziya akan sadaki mafi daraja, sai muyi fatan Allah ya kade fitina, tunda aka daura Auren ya baro taron ya dawo gidan tareda kulle kanshi cikin dakin su, zazzabi yakeji mara dalili tareda jin wani irin bakon Al amari a tattare dashi, Ahmed nata neman shi, Saida ya kirashi ya dauka yafada mai cewa yana gida, dawowa yayi shima tareda barin Abokan shi ya same shi a dukun kune cikin bargo,
Cire babbar rigar shi yayi ya zauna gefen gadon tareda cewa "bakada lafiya ne? "Fever ke son kamani, "sorry namiji, kasan me? Yafada yana gyara zama, tashi Khaleel yayi ya jingina a jikin gadon yace what my brother? "Burina yacika khaleel, today Naziya is legally mine, but am worried me zata fuskanta a cikin gidan nan, how is she going to react after she find out about everything? "Like what brother? Like our wealth, this big mansion, and mommy. Yafada yana rage murya cikeda tausaya wa kanshi, kamar yarone yaga alawa Ana mai kwalelenta haka yakeji yanzu, yasamu farin cikin shi Amma baya cikin farin ciki.
Matsowa yayi sosai kusa da d'an uwan shi yace "Yaya this is the time da zakayi fighting back, ka tsaya akan ra'ayin ka, you have to talk brother, fight for your love, and Aunty Naziya will be happy bazaka samu Matsala da itaba, in tace zata sama yayana hawan jini bazan raga mata ba cos batasan irin fighting da kakeyi akan soyayyar taba. "Hmmm you known, nafison momy ta barni in zauna a gefen mu, bana son Naziya ta shiga cikin damuwa nasan zata sha wahala Idan akace zata zauna cikin gidan, she can't handle it, bata saba da irin wannan rayuwar ba. And mommy is our mother dole mubi Abinda takeso Auren Naziya da A hannu na yake Dana hakura for mommy happiness, but Allah kadai yasan mai ya boye a cikin Al' amarin,
Yafada cikeda damuwa, Dariya khaleel yayi mai d'an sauti wadda ta Kara bayyana kyanshi sosai, "Yaya this my Aunty is very lucky, tasamu miji mai sonta sosai Anya zaka kuma Aure nan gaba like the way mommy is planning? " no Khaleel bana son Naziyata ta zauna da kishiya Ina so tayi rayuwar y'anci ne, Ina son inganta cikin hutu da walwala, khaleel na gama tsara irin yanda nakeso rayuwar Naziya ta kasance, I love her beyond your imagination, ka tayani son Naziya kaima kamar yanda nake sonta.
Sundauki dogon lokaci yana daukewa yayan nashi damuwa ta hanyar k'arfa famai guiwa, Saida friends suka fara kiranshi ya Fita tareda barin khaleel cikin damuwa, Alwashi ya dauka mai girma akan zai taya yayan shi fighting akan duk Abinda zai daga mai hankali bazai so yaganshi cikin damuwa ba,.
Bai kuma Fita a gidan ba ko sallah a part din yakeyi ya koma ya kwanta, yarasa abunda duk ya Cire mai walwala da natsuwa bayajin dadin jiki da zuciyar shi baki daya, he just fee like going back to bangkok, baisan mai ke hana shi sukuni ba. Sai Karfe Tara Ahmed ya kuma shigowa dakin ya tsaya a kan shi tareda cewa "brother what is wrong? You look very dull. "I don't know Yaya kawai bana jina cikin natsuwa. "relax nima haka nakeji tundazu but now am fine, your Aunty is here khaleel, finally Naziya is here. Zama yayi tareda rungume Khaleel din yana fitarda hawayen da yarasa na menene ke fitowa daga idanun shi.
Saida ya d'an natsu yace let go and welcome your sister in law. Mikewa yayi ba musu, ya bishi sanye cikin kana nan guntayen kayan da ya canja tundazu.
Gefen Naziya kuwa tunda suka sako kai cikin wannan tafkeken gidan gaban ta ke faduwa gashi gwaggonnin tane suka rakota su uku bisa ga umarnin malam domin baison gayyar tsegumi, kanta a duke yake tunda motar da ta dakko su ta shigo, cikin Y'ar rakiyar ta daya tace "t'irk'ashi wannan gidan mutum daya ne ko dai gidan y'an yankan kai? Sauran suka fara salati, shikenan malam saida Y'ar nan yayi, irin wannan gidan saikace wata unguwar? Saurin daga kanta tayi ta saki baki tareda dafe kirjin ta tana karanto Addu'ar tsari a cikin zuciyar ta, jikin ta shegen rawa yafarayi. Har motar ta tsaya Abokin da ya dakko su yace "Hajiya kufito mu shiga ciki ko? Kamar way'enda kwai ya fashewa a ciki haka suka fito ji sukeyi kamar ace ar su ruga, shi ya musu jagora kowaccen su Addu'ar da duk tazo bakin ta takeyi, rike take da tsintsiyar hannu irin wainda ake rikewa na share dattin daki a wurin sabuwar Amarya bisa ga Al Ada, nasan wasu sun san wannan Al Ada akan ce ta share duk fitinar d'akin kafin ta zauna cikin dakin ta.
Daya cikin gwaggon nin nata tace "kawo Abar nan inrike da ita zankoma Y'ar nan domin ko takarda bazaki shara ba a gidan nan, "Toh ai gidan da waje ma babu ko Alamar d'aud'a bare ciki, ai wajen ma ni yafi dakina tsafta, haka suketa sambatu tsakanin su. Ita kuwa jitakeyi kamar ta ruga da gudu saboda tsoro, wasu irin zafafan hawaye ne ke zubowa akan kyakkyawar innocent face dinta. She is regretting today, wayace ta Amince mai? wayace ta yarda da Auren shi? gashi yayi mata karya yakawo ta gidan da bata taba zuwa kusa da irin shiba.
A falon mommy ce hakimce itada y'an uwan ta, Zarah ce ke gefen ta da kuma uwar y'an kanzagi fauzy, sunayin Sallama mommy tace Zarah kusa katuwar tabar mar nan akan carpet din Idan sun tafi a fita a Y'ar da ita a waje kar k'uma ta shigo mana gida.
Sunji komai a kunnen su jikin su na rawa suka karaso akan tabarmar suka zauna tareda gaida su cikin girma mawa, cikin su daya tayi karfin hali tace "Hajiya toh ga Amanar Y'ar ki nan Allah ya tayaki riko.
"Ni Amanar me zaku bani saikace wata kishiya ta, to kuji infada muku tun mijina nada rai ko zance bai taba zuwa ba bare ayi zancen yimin kishiya, don haka karma ku fara ku jira Wanda ya Auro ta yazo kubashi...... Yauwa ga shi nan ma, Tafada tana nuna shi domin yana fitowa yaji zancen momyn wani irin zafi tareda damuwa zuciyar shi ta shiga. Khaleel ma yaji komai kuma he is not happy da irin yanda mommy takeyi ga su fauzy dake musu wata irin Dariya kamar sunga kashi itada zarah, wani irin baci ran khaleel yayi da Sauri ya matso tareda kallon Fauzy, " ke wace iri ce uban me kikeyi a gidan mu haryanzu baki tafi ba?
"Aa banson shirme Ibrahim, ya yarinya tazo maka k'ara zaka hauta da fada? "Mommy angama Bikin tazo ta wuce gidan ubanta tom. Jikin ta na rawa ta zabura ta nufoshi kamar zata fada jikin shi "no please na dauki permission wurin mommy na ta yarda inyi kwana biyu baby just for you..... "Oh come on, ke meyasa bakisan..... Saurin dafashi Ahmed yayi domin bayason more humiliation agaban y'an uwan Matar shi Dama ita kanta, yanzu yana tunanin how he is going to face her ne ma.
Shiru yayi tareda juyawa da Sauri ya yi cikin dakin shi dake part din momy, ranshi yayi mugun baci dole ya koyawa wannan fauziyar hankali gobe.
Fadin zuciyar Naziya da tunanin ta bata lokacine ma, daya daga cikin y'an uwan mommy ne tace "ku muje in nuna muku part d'in ta, Tafada tana mikewa kafin ya yar ta ta kuma kwab'a, sanyi Ahmed yaji domin yama d'askare yakasa ko motsi.
Suna shiga suka ware idanu domin basuga ko tsinken da sukasa aka kawoba, wadda ta rakosu ce tace "wannan dakin mijinta ne gidan su na waje a can akasa da kayan ta, kamar tasan me suke tunani,
Domin sunga gadajene na kasar waje ba irin nasu d'an wambai ba.
Cikin sauri sukace "tunda munrako ki Naziya mu zamu koma dare nayi, Allah yabada zaman lafiya da hakuri kinji ki rike tarbiya da mutuncin malam Dana kulu domin kinsamu tarbiya dai dai gwargwado kinsha nonon hakuri da kuma mutunci, Allah ya kade fitina. Suka juya cikeda sanyin jiki, riko daya daga cikin su tayi tasa kuka "Don Allah gwaggo karku tafi kubarni ni kumayar dani gida wurin Inna bana son nan gidan. Tafada tana kuka mai cikeda tausayin kanta da Rayuwar ta, daga shigowar ta harta karanto irin Rayuwar da zatayi a cikin wannan gidan.
Shigowar Ahmed ne yasa takara rike ta gam tana gunji. "Ahmed ka rike Amana ga Matar ka mu zamu tafi kaji. Babbar Tafada cikeda tausayin Y'ar tasu, hannu yasa zai rikota tayi tsalle ta koma gefe tareda sakin su tana gyara hijabin ta dogo.
Fita sukayi ta koma gefen dakin ta zauna tareda saka kuka mai zafi da kuma k'ara,
Rakasu yayi a gurguje yadawo domin kukan da takeyi bakaramin daga mai hankali yakeyi ba.
A zaune take ta hada kai da guiwa tana kuka mai ciwo. Zama yayi dabas a gaban ta cikin sanyin jiki, tanajin kamshin jikinshi daya cika ko Ina, takasa dagowa. Hannun shi ya dora saman kanta, da yasa tayi Saurin dagowa tareda ja baya tana Kara hade jikinta wuri daya,
"Am sorry bazan kuma tabaki ba tunda bakyaso, Amma please kiyi shiru haka kukan ki na tabamin zuciya sosai.
Yafada yana kallon yatsun Hannun ta farare tas da sukasha jan lalle Hannun ya mugun burgeshi, ji yake kamar ya riko ya tsotsa, bai taba ganin lalle ya burgeshi ba sai a Hannun ta. Jin shirun shi yasa ta dago tareda zubamai lashes d'in ta masu kyau da kuma fararen idanun ta da suka cabe da ruwan hawaye, taga Inda yake kallo da ya shagalar dashi sosai. Saurin cusa Hannun ta tati cikin hijabin ta da yabashi damar kallon na fararen kafafun ta, wani irin gauron numfashi yaja tareda d'an matsawa kusa da ita, ta kuma ja baya again. "Why Naziya? Please karki horani a haka zuciya ta zata buga, ki horani ta kowacce hanya but karkiyi min iyaka da zuwa gareki, am dreaming about it always, nasan ni mai laifine a wurinki, Amma kisani ni mai sonki ne shiyasa na boye miki gaskiyar rayuwata Naziya banason in rasaki I love you so much my wife. Yafada yanajin wani irin shauk'i da yanayi mara misali, kallon shi takeyi wani iri kamar zataga wani Abu daban, batajin zata iya Rayuwa a cikin wannan gidan tareda kuma mahaifiyar shi da itace farkon matsalar data Kara girgiza ta.
"Am sorry Naziya, nasan i'm wrong domin bakiyi planing zama a irin gidan nan ba, yafada yana murmurshi, domin itace mace ta farko dayaga wai batason daula. How silly? Maganar mommy tasa yayi Saurin ja baya tareda tashi tsaye ya kalleta "kazo ka zauna gaban jaririyar yarinya a daren farko to kazo ka wuce dakin d'an uwan ka kowa yasan ango baya shiga dakin Amarya sai anyi budar kai don haka wuce kabani wuri tun ban sab'amaka ba.
Daukar babbar rigarshi yayi yafita jikinshi a sanyaye. "Ke kuma ki tashi kidaina wannan kukan munafuncin kije kisha Ac anzo inda yafi gidan tsoho ga katifa mai numfashi aje a more, kin zo kina kukan munafurci. Tafada tana fita dakin cikin fada. Zubewa tayi nan kasan dakin tasa kuka, "Ahmed yasa ankawo ta inda bazata taba yin mutunci ba,har wani irin ciwo taji gefen kanta nayi saboda kukan da takeyi.
A kwance ya samu khaleel idanun shi a bude yana kallon saman dakin wani irin zazzabi yakeji har yanzu Wanda yarasa dalilin faruwar shi, jin takun d'an uwan nashi yasa yayi Saurin juyawa ya kalle shi, "Yaya ango me kakeyi a nan yau? Yanda yaga hawaye tareda ganin damuwa kwance a fuskar d'an uwan nashi yasa yaji tuni zazzabin shi ya tafi, tashi yayi cikeda damuwa yace "Yaya taki kulaka ne? Zan bata mata rai Idan ta nemi jefamin kai cikin cikin damuwa. Yafada jikinshi na rawa domin yaune karo na farko dayaga hawaye a idanun jarumin yayan nashi mai hakuri.
"Mommy. Yafada yana Rungume d'an kanin nashi domin yasamu sauki. "Me tayi kuma? Fadamai yayi yana jan numfashi, "oh Mommy, Bari inje inyi mata magana. Yafada yana kokarin tashi tsaye, rikeshi yayi tareda girgiza kai, "karkaje tace Al Ada ce sai gobe zan shiga wurin Matata.
"What kind of Al Ada? "Budar kai. Zabura yayi cikin haushi "let me talk to her. "No leave it, just do one thing please go and check on her please she was crying.
"No kabarta zatayi shiru ka kwanta yau ne kawai tunda ka hanani inyi mata magana.
"Please go Ina so inji ko tadaina kuka, inaji a jikina tana can tana kuka.
Bayason musu, especially da yayan nashi don haka mikewa yayi kawai ya fita.
Ba kowa a falon yanzu duk Suna cikin part din mommy Suna hira da shewa, girgiza kai yayi yana tunanin Abinda zai aikata gobe a gidan halin shi dasuka sani bai canja ba bayason rubbish. Tundaga falon yakejin kukan ta kasa kasa. Wani irin zafi yaji a zuciyar shi, da sauri ya shiga dakin, a kwance take a kasan kamar yanda take tundazu saidai yanzu Ana iya ganin kayan jikinta domin duk hijabin ya tattare ya koma wurin cikinta, zaka iya ganin perfect figure dinta, Wanda ko Ahmed bai taba samun damar ganin ta haka ba, kullum tana cikin hijabi, akan kafarta idanun shi yafara sauka.
Wanda wani irin attraction ya rika jansa ya kasa Cire idanun shi, "first time da henna designs ya Bashi sha'awa, ga kafafun ta kamar na turawa a mulmule farare tas dasu, "Wow she is Unique, zuciyar shi ta furta. Domin tsarin jikinta da yake gani, bai taba ganin small body with a perfect shape ba like her.
Motsinta yasa yadawo hayyacin shi cikin Saurin tareda tsorata ta zuba mai ido, tana zarewa, domin ita bata taba ganin katon namiji irin shi da guntun wando da singlet a gaban ta hakaba, wane irin gida Ahmed ya kawota, da Sam ba tsari ba wani sanin ya kamata. Saurin jan hijabin ta tayi kasa tana mikewa kukan nata ya dauke dif, fuskar shi mai natsar da yaro mai kukan banza, tuni ta hadiyi wani irin miyau, she knows he's khaleel domin ganin farkon da tayimai bazai taba bacewa a idanun taba. Gaba daya jitakeyi ya cika mata dakin da girman shi, ga fuskar shi mara walwala, idanun shi masu dauke da wani irin sinadari Wanda batasan ma ma'anar shiba. Juyawa tayi ta Bashi baya ganin ya dauke kanshi batareda ya iya cewa komai ba. Saida ya dauki lokaci kafin yagama tunanin yanda zaifara yimata magana, cikin karfin hali yace "good tunda ba kuka kikeyi ba, Yaya na is worried sosai shiyace inzo in dubaki, tunda kinyi shiru shikenan, yafada yana tafiya batareda ya kuma kallon gefen taba, a falon yaci karo da ledar da yayan shi ya Ajiye Wanda kowane ango ke shigarwa Amarya da ita, dauka yayi ya koma, dai dai ta kuma juyowa, idanun ta suka kuma cin karo dashi, wani irin Saurin juyawa ta kumayi ledar ya Ajiye "you have to eat karki kwanta da yunwa Yaya na zai damu. Yafada yana fita Hannun shi cikin pocket din guntun wandon nashi.
Cikin sauri bayan ya fita ta dannawa kofar key domin Allah yagani batason ganin shi again,............. 🖊
*Matar Soja*
🌻🌻AUREN GADO🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,
Ga masu son su biya ga account details dina, *NAFISA HASSAN SANI 7304736012 @ FCMB* Sai Ku min magana ta wannan number *09069200154*
🆓 page
7⃣&8⃣
............... A tsaye ya samu Ahmed yanata sintiri, yana ganin shi ya rikoshi "kuka takeyi ko brother? Yatanbaya cikeda damuwa. "No Yaya tayi shiru nabata ledar da ka Ajiye a falon relax am sure zataci ta kwanta. Yana gama fada ya haye gadon ya kwanta tareda juyawa yayan nashi baya. "Tank God, and tanks to you brother. Yafada yana d'an samun natsuwa, bathroom ya shige yabarshi idanun shi kur, baya kojin bacci, saida yaji fitowar Ahmed ya rufe idanun shi kamar maiyin bacci. Saida ya shimfida dadduma ya fara jero sallolin nafila tareda Addu'oi masu zafin akan Rayuwar shi data Matar shi, ba Abinda yake nema sai farin cikin Naziya a wurin Ubangiji tareda neman zaman lafiya a tsakanin su.
Ganin har Karfe biyu shima yakasa baccin ya diro tareda dauro Alwalar ya tada sallah shima, haka gefen Naziya bayan ta kulle bathroom tafara nema saida tayi da gaske ta gano inda zata latsa ruwan yafito kafin tayi Alwala tafito, dadduma tagani a gefe da Qur'ani ta tada sallah, saida tayi raka'a biyu ta zauna tana jan k'ira'a a zuciyar ta. Domin fadar manzon mune aduk halin da mutum ya shiga to ya koma ga Allah,
:(Fadhkuroonee adhkurkum washkuroo lee wa laa
takfuroon
"So remember Me; I will remember you. And be
grateful to Me and do not deny Me.) :
Wanda duk ya tuna da ubangiji shima bazai manta da shiba a duk halin da yashiga.
Sai Asuba ta tada sallah saida tayi nafila raka'a biyu kafin farillah, taci gaba da karatun ta, sai Karfe shida ta kwanta a kan daddumar, wani irin bacci mai cikeda salama ya dauke ta domin Qur'ani maganin damuwa ne Idan har kayi Imani da Allah.
Haka gefen Ahmed da Khaleel basu runtsaba saida sukaje Mosque suka dawo, saida Ahmed ya duba kofar dakin nashi yajita a rufe, bai bugaba domin kar momy taji, dakin khaleel suka koma, kwanciya yayi yana murmurshi "daga yau bazan kuma kwana nikadai ba, ko tareda kai "am going to sleep on my wife shoulder, yafada with so much excitement, Runtse idanun shi yayi tareda yin shiru yarasa abunda yakeji a Ranshi, a haka dai sukayi bacci har zuwa Karfe Tara na safe, Wanda Ahmed din ne yafara tashi domin ya matsu ya fita yaga halin da Naziya ke ciki.
Saida yayi wanka ya tashi Khaleel "get up sleeping beauty muje muga momy inaso in duba Naziya Yafada yana goge fuskar shi da towel, tashi yayi yana salati tareda wucewa batareda ya furta komai ba,
Saida yayi wanka ya fito, yasamu har Ahmed ya shirya sai kyalkyale jikin shi yakeyi domin so yake ya burgeta, Idan ta ganshi tasan bata zabi mijin banza ba. Shiryawa yayi shima khaleel cikin shigar tashi ta fama, kallon shi Ahmed yayi "yakamata kasa manyan Kaya zamuje gidan malam later gaisuwa tareda godiya inaso muje tare dakai. "no please banason zuwa wannan unguwar Yaya."For me please. "OK for you. Amma bazan sa kayan zafi ba sai zamu tafi. "No problem muje".
Naziya saida mai aiki ta tasheta ta tashi cikin sauri ta bude kofar tace "Hajiya tace kifito kitayamu aikin breakfast. Tace tom tareda gyara zaman hijabin ta ta fito, tareda taimakon mai aikin suka shirya irin Abincin da sukeci wainda idan aka barta bazata iya ko kunna gas din ba bare sauran kayan wutar. Wurin gasa crabs din khaleel ne tasha mamaki, domin ita tsawon Rayuwar ta bata taba ganin ta ido da idoba sai a text book, da kuma manyan d'anyun crayfish da Sam basuda kyan gani a idonta tana kallo aka gasa su a oven aka yanka mai salad da kuma tumatur manya aka jera su crayfish din da crabs din akan ganyen, so takeyi taga wazaici wannan Abun, sai kwai da ko kadashi ba ayiba ansaka mishi kayan kashe k'arni, kawai fasashi akayi a frying pan aka d'an barbada chilli powder asama kadan.
Tana gefe tana kallon ikon Allah sai d'an abinda zata iya yi kawai take tabawa kamar fere dankali da yanka kayan miyan da za'ayi source dasu, Karfe Tara da Rabi suka shirya komai a dining table, dai dai lokacin momy ta fito cikin shigar Alfarma da gwala gwalai, ta kalleta cikin fada, " Ina fatan bada wainna kayan kika shiga kitchen ba? Kanta tayi Saurin dukarwa tareda gaida momyn Ina kwana. Tace "mu nan wanka akeyi sau goma in antashi domin akwai ruwa basai anje tuka tuka ba ko rijiya ba don haka karki kuma shigar min kitchen da datti, yanzu ma Allah yasa khaleel ya iya cin abincin nan kin shiga kina yimai kakkabi da wannan katon hijabi kamar wadda keda nakasa, ke Kodai wannan kyan naki a fuska ne rufa rufa akayiwa Dana a cikin hijabi? Oya Cire shi yanzu ingani wallahi inkinada ko kuna guda dayane yau sai kunbiya mu sadakin mu. Tafada dai dai y'an kanzagin ta na fitowa tareda kuma su khaleel da suka sawo kai cikin falon.
Dariya Fauzy tayi tace "may be akwai inda keda illah Mommy, Tafada tana tafawa da Aunty zarah dake biyeda ita, "kwarai kuwa a Cire kar a cuci dana,.
Cikin sauri ta Cire hijabin kanta bako d'an kwali sumarta mai tsananin tsawo da kyau kamar buzuwa na nade cikin sabon ribbon, gashine kwance har gaban goshin ta Wanda ke sanarda kai akwai sumar. Kayan jikinta kuwa atamface dai dai talaka wadda malam ya dunka mata tafitar biki akalla zatakai dubu goma, domin kawai ya fitarda Y'ar tashi ranar Aure ya dunka mata su kusan guda uku,
Atamfar mai golden ce blue, dinkin nata nazamani mai kyau na Amare Riga da sket ya mata cif mai d'an shoki ta baya perfect figure dinta ya fito fiyeda tunanin masu sa idon dake wurin, duk sun gama yarda cewa Naziya mace ce kuma kyakkyawa ajin farko ba kamar na Y'ar talaka ba. D'askarewa Ahmed yayi domin yau ne yasan ya tsinci dami akala, yau yake ganin wacece Naziya, wani irin yanayi yakeji, burin shi bai wuce ya ganshi daga shi sai itaba a kebe ya samu ya rage damuwa da wahalar da yasha kafin yasameta.
Gefen Khaleel kuwa bazaka taba gano komai ba sai tsantsar bacin rai da bakin ciki Wanda yarasa dalilin shi, cikin zafin zuciya ya kalli fauzy " you come and get lost from my house, angama biki ki koma gidan ubanki right now. Yafada cikin karaji da fitinar da ba Wanda yataba jin yayi irin ta. "Aunty zarah I thought Aure kikeyi kema kije gidanki mungode da zumunci we need privacy that's enough.
Fadan da yakeyi ba Wanda za a iya tsaya wa ayi musu dashi bane, mommy ma mamaki takeyi tareda kallon shi saida ya kuma cewa "I said get lost. Tace "khaleel " cikin tsawa, "ka kiyaye ni ba inda zasuje, kuma don iskanci ka manta Zarah kanwa tace uwa daya uba daya, don't forget your manners and Fauzy, karka manta she is your bride to be. "Momy tell them to stay within their limit, ita Aunty zarah ba girman mu tayi ba I can talk to her any how, and Fauzy Auren ta kikeso inyi zan iya fasawa anytime idan naso, don haka before I change my mind leave". Yafada yana nuna mata hanya.
"Innalillahi, ni Balkisu daga zuwan ki kinfara hada mana gida" Tafada tana nuna Naziya, lallai kuwa yarinya kintabo tsuliyar dodo, Ahmed kaga Abun da ka debo, yarinya mai farar kafa bad luck to our family. Wani irin zafi yakeji tareda kallon momy yana girgiza kai, "no mommy me tayi, Ina bin duk Abinda kikeso momy saboda ingama lafiya please na rokeki kibarmu mu koma gefen mu zamufi samun kwanciyar hankali.
"Naga takaina ni Balkisu kaga ni ko yarinya ta shigo da mugun Asiri, toh wallahi kunyi kadan keda iyayen ki zan nu na muku ni Balkisu in kun kwana akan buzu ni akan dadduma nake kwana mu zuba, daga shigowar ki Dana yafara musu dani. "Momy please stop" this drama is enough. Khaleel yafada yana matsawa kusa da ita tareda riko Hannun ta Alamar lallashi domin yaga Alamar nuna fushin su b'ata Al amarin zai karayi, domin kwanciyar hankalin d'an uwan nashi yace "Fauzy kuzo muyi breakfast Aunty zarah please komai ya wuce OK. "Dama Ibrahim kai raini ne dakai tun kana yaro shiyasa Ahmed yafika Abun kirki.
"Oh am sorry my Aunty yafada yana Dariya kadan, zama sukayi, ita kuma ta wuce dakin da ta kwana tana share hawaye masu ciwo da dumi, domin all her life bata taba tsayawa gaban mutane ba hijabi ba, yau gashi an wulakanta ta saboda me? Saboda tana Y'ar talaka, shiyasa batason tasa Rayuwar ta inda tafi karfin ta.
Ahmed kokarin bin ta yakeyi mommy tace "zonan d'an anace shiryawa zatayi tafito kuma kiyi sauri don bazamu tsaya jiranki ba hamshakiya. Komawa yayi ya zauna tareda zubawa bayanta ido har ta shige, ga koshi ga kwanan yunwa shine wannan.
Gudun fada yasa tayi wanka cikin sauri bayan ta gano inda zata Tara ruwan, domin ko bakomai tanajin labarai tareda gani a TV sometimes duk da ita ba ma'abociyar kallo bace, bisaga Al'adar gidansu na riko da Addini tareda kaucewa duk wata Rayuwa ta nasara, sai gata a yau tana Rayuwa cikin nasara baki daya domin a ganin ta gidan baki daya ma Rayuwar nasara sukeyi.
Ganin bataga kayan taba yasa ta mayarda na jikin ta, tareda daura d'an kwalinta ko mai bata shafa ba ta fito cikin sauri. Suna zaune yanda ta barsu, sai Ahmed da ya rike Haba yana kallon ta inda zata bullo, Ajiyar zuciya yayi ganin fitowar ta, yanzu ya samu damar karewa gabanta kallo da take tahowa toward him, Ajiyar zuciya ya jera tafi goma, domin shidai yana ganin samu da rashi ga mace Allah ya Bashi ta huce takaici Amma mommy taja layi, "bazamuga tsiya ba mudai ki kwana da Kaya ki tashi dasu ki shiga kitchen kifito yanzu kuma kizo ki zauna cikin mu kina tsami, maza ki koma ki canja Kaya, Ahmed kaga illar Auren irin wannan yaran ko? yanzu da akwai bakon ido da munsha kunya. Shiru tayi takasa cewa komai. Cikin sauri Ahmed yace "mommy kayanta na part din mu ne shiyasa duk can aka kaisu, "oh kace kagama planing din tarewa acan to kaje ka kwaso mata kayan zuwa nan ban Amince maka zama da wannan ignorant din ba a cikin wannan gidan ba sai in kashirya yin wani Aure kwa tare da Amaryar Arziki ba wannan ba, Tafada tana nunata sama da kasa, da Alama kalaman mommy nayiwa khaleel zafi fiyema da Ahmed domin yasan d'an uwan nashi hakuri ne kawai yasa yakasa cewa komai shikuwa hakurin shi yafara karewa. "Mommy please am hungry ko intafi ne waje inci yau bazamuci breakfast din ba? "Kizo ki zubawa kowa yarona najin yunwa kinja kin tokare. Matsowa tayi jikin ta NA rawa, " gefen da Khaleel yake ta fara nufowa kanta akasa bata ma iya kallon idanun mutanen, infact haryanzu bazata iya tantance kamannin fuskokin su ba. Wani irin kamshin turaren wuta d'an mai duguri mai sanyin kamshi, Wanda ya Kama jikinta ya daki hancin shi, Hmmm yana matukar son kamshi a Rayuwar shi, ga wannan da yake shaka mai wani sirri na daban.
Plate ta dauka ta fara zuba musu chips din dankali da source, Ahmed so yake ta kalleshi, just once ko zaiji sauki domin Allah kadai yasan Abinda ke cikin zukiyar shi, damuwar da yake ciki bata faduwa.
Saida ta zubawa kowa tazo kan Khaleel, ya daga mata hannu tareda janyo tarkacen shi gabsnshi domin shi cimar shi daban take a gidan, zuba mai ido tayi tana kallon shi zaici wannan Abun? "Naziya ". Ahmed ya Kira sunan ta cikin wani irin kashe murya tareda tsareta da idanu, batada choice dole tadaga idanun ta takalle shi, nuna mata kujerar gefen shi yayi tareda mata Alamar tazo ta zauna. Ba musu ta nufi gefen shi, mommy nata hararar ta kasa kasa, Su fauzy kuwa kallon village girl suke mata, zama tayi a takure da kanshi ya zuba mata Abincin tareda hada mata tea very thick, "toh shanyayye ita batada hannu ko? Inji mommy shidai shiru yayi, saboda jin ta a zaune kawai a kusa dashi yaji ya d'an natsu kadan.
Tsit kakeji sai karan cokula, ganin hankalin kowa nakan plate ya sauke left hand dinshi tareda dafe Hannun ta daya dake Kan laps d'in ta, gam gam, wani irin zabura tayi, Wanda khaleel ne kawai idanun shi yagani, idanun ta a gefe take kallon Ahmed din tareda kokarin kwace wa ta kasa , wani irin bakon Al amari takeji domin zata iya cewa wannan ne karon farko da namiji ya rike mata hannu, gashi ba rikewar kawai yayiba wani irin murzawa yakewa Hannun kamar kwadayin shi akan Hannun yake,
Har wani irin zafi takeji, shi kuwa laushi da santsin Hannun ne ke rikitashi domin tuni yama daina cin Abincin, jiyake kamar ya dauketa suyi tsuntsuwa subar wurin, he really need privacy with his wife.
A haka kowa ya kammala batareda taci ko cokali daya ba, kuma yunwa takeji ta fitar hankali, domin tunjiya batasa komai a cikin taba, domin ko kallon ledar da khaleel ya Ajiye mata batayi ba.
Shiyafara mikewa tareda barin wurin, saida yaga hankalin mommy zai dawo kanshi ya saki Hannun tareda gyara natsuwar shi da ta dade da zuwa bulaguro sanadin jin shi cikin wani irin yanayi mara misali, bai taba jin kanshi in needs kamar yanzu ba, Hannun ta ya rike duk ya rikice idan ya Rungume ta fa? Ai suma kila zaiyi kai tsaye,
Saurin tashi tayi jin ya saki hanun tayi daki cikin sauri, dakyar ya karasa breakfast yana bawa kanshi laifi domin yaga ko tea bata shaba, mommy ta kalli plate din ta tace "Ahmed aiki ya sameka saikaje ka siyo mata kosai da koko kasan ba asaba da shan shayi ba bare kuma chips, ta fada tana barin dining din zuwa tsakiyar falon ta hakimce tareda su fauzy,
Shigowar y'an matan kawu modu ne yasa ya saki fuskar shi tareda tasowa, yana murmurshi "sai yanzu zakuzo ganin Amaryar? "Yaya Ahmed ai jiya ma muna gidan nan saboda kana hidima ne yasa baka sani ba. "OK kun fita. "Ina Amaryar mu? Tana ciki, and please muje kutayani kwaso kayanta zuwa nan. Yafada yanayin gaba, binshi sukayi,Suna hira a tsakanin. Akwatunan da yayi mata ne kawai ya kwaso mata yabar na Khaleel a can, gudun fitinar mommy, domin ko wainda yayi hanawa tayi akai wai kar su kwaso musu kudin cizo da k'uma, inda Allah ya taimake shi malam yace bayason bidi'ar kawo akwatin abarta a dakin ta idan ta tare, Wanda hakan ya mugun sanyaya mai rai. shigowa yayi da katuwar akwatin zai shige tareda kanin nashi, "Ahmed Ajiye a nan zasu shiga da ita ciki. "Momy bazasu iyaba tanada nauyi sosai. Zabura tayi tace "Zarah kuzo ku kamamin, yana gani haka suka dauka tiki- tiki saboda dai kar Abarshi ya kebe da Matar shi, yadawo tsakiyar falon ya zauna tareda dafe kanshi, Allah yagani angama shiga Rayuwar shi, Mutum yayi Aure Amma jin dadin Aure ya gagare shi.
Fitowa tayi tana sababi tareda zama gefen shi, "na fada maka miji baya zuwa wurin mace ba ayi budar kai ba, don haka karka sake inga kafarka cikin dakin nan bada izini na ba.
Saurin kallon ta yayi "mommy ai yaune kuma shike nan ko? "Nadai na fada maka kar inga kafar ka ciki inba haka ba zan daga maka nono. Tashi kawai yayi yabar gidan cikeda tsantsar damuwa da kuma bacin rai.
Uwa uwace shiyasa kawai baida yanda zaiyi saidai ido.
Dakin Naziya kuwa ta saki jiki sosai da y'an matan wainda sun Cire mata damuwa da kadaici tareda kewar gida, su suka ware suka shirya mata komai na kayan ta a wardrp, da kayan shafan ta wa inda tasan sunja kudi sosai, kayan akwatin sunyi matukar girgiza ta domin saiti biyu ne, wai don ma mommy ta hana shi yayi yanda yaso kenan. Su suka sata ta caba Ado tareda ciro mata wani tsadadden less baki, Abunka da farar fata tuni ta haska ga dinkin kamar angwada ta, suka murza mata dauri, tafito gwanin burgewa, Karfe daya gidan ya cika da y'an uwan ta masu kawo gara Wanda sun kure kokarin su sunyi dai dai gwargwado, inji bahaushe yace ka fada wa mai zuciya biki ba mai dukiya ba.
Mommy ma tasan sunyi kokari saidai hassada da idan bakason mutum ko tsarki da madara kake mai bazai taba kaunar kaba............. 🖊
*Matar Soja*
🌻🌻AUREN GADO🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,
Masu son su biya ga account details dina ,
*NAFISA HASSAN SANI 7304736012 @ FCMB* Sai Ku min magana ta wannan number 09069200154
🆓 page
9⃣&🔟
............ Khaleel yabar gidan bayan ya gama breakfast shima domin shikadai yasan damuwar shi, bayajin zai Amince da wannan Auren tareda ci gaba da zama a Nija yana ganin irin wainnan Abubuwan, he can't take it. Saida Ahmed ya nemeshi a waya yafada mai inda yake a can suka hadu, dafashi yayi "why kafita bayan nafada maka zamuje gaisuwar surukai? "Yaya tunda na duba naga baka gidan I know you're hurt shiyasa nafita, and please Yaya don't just sit down and watch things ka dauki Action mana. Yafada yana kallon shi cikin damuwa, murmurshi Ahmed din yayi tareda cewa "my brother, a wurin wa zandauki Action? Don't forget she is our mother dole mubi ta duk yanda takeso. "Its unfair", haka zakaci gaba da kallon Abubuwa nafaruwa till when? "Ko zuwa yaushe ne Am ready inyi mata biyayya khaleel am ready to obey what ever she said, can't you do that for your mother? I can't Yaya gaskiya am seeing everything you need privacy with your wife amma an tauye ka, yakamata tunda ka rabota da y'an uwan ta ka bata kulawa, itama tanada right akan ka fiyeda mommy don haka dole ka kula da yarinyar nan, kasan yanda kukayi and you disappoint her daka boye mata gaskiya I know she is in pain, please Yaya she needs your comfort.
"Hmmm my brother has grown up, yafada yana rungume shi gam gam tareda jin dadi, "khaleel kasan how hard am trying? Banda zabi ne, Amma Inna fada maka bana damuwa k'arya nayi, "I needs my wife like any other man da yayi sabon Aure I want her very badly, yazanyi in iya Cire idanuna akan matata bayan she is closer to me, this is the hardest time for me. Yafada yana tunano yanda yaganta dazu without hijab, her shape her chest her hair, oh God! he has the most beautiful girl as his wife.
Rungume shi khaleel yayi tareda cewa "I will help you through this brother. "Thank you". Daga nan suka wuce gidan kawun su tareda godiya akan hidimomin shi, ya musu Allah yasanya Alkhairi, tareda nasiha mai zafi akan zaman Aure, kafin ya dawo kan Khaleel, "kai balkisu Tafada min komai akan Y'ar gidan mai Nasara, and am happy da zakayi Aure kaima, kuma ni bazan hanaka Auren zabin kaba, zankuma shige maka gaba har kaima Allah ya cika maka naka burin, Amma Ahmed kayi sa'ar surukai nagari Allah ya kad'e fitina, kunje kun gaida su? " yanzu zamuje kawu friends dina ma na jirana daga nan can zamuje. "To to to, kuje Allah ya muku Albarka, zan Dauki Abokina mu samu ganin mai nasara, idan komai yayi dai dai zanfada muku. "Mungode sukafada baki daya, Wanda itace kalmar farko da ta fito daga bakin shi bayan gaisuwa domin Allah yagani Fauzy saidai idan Allah yayi baida ta cewa, fuskar shi kawai zaka kalla kasan baya farin ciki. "Relax brother, bakasan me zai faru gobe ba, kayi hakuri may be haka Allah ya tsara dole zaka yi Rayuwa da fauzy, don haka ka nemi zabin Allah, inba Alkhairi bace sai ya baka wata. "Mata biyu Yaya? "Yes kaiba namiji bane? " no please kai kace bakason biyu nida nake kanin ka inyi biyu, ni mace daya is OK for me. "You can handle two wife's nasan kanina, I believe in you. Yafada yana Dariya, haduwa sukayi suka tafi jakara tareda Abokan Ahmed din. Wanda khaleel ya daure har cikin gidan da Akwai Sauran mutane suka shiga suka kwashi gaisuwa cikin mutunci da girma. Wanda idanun shi nakan Inna kulu wadda yasani ba tantama kyanta Naziya ta dakko, haka yabi Shukrah da kallo yana ganin tsantsar kamar su tareda yayyin ta masu Aure duk Suna Kama, Amma no one like Naziya she is more beautiful a cikin su.
"Shiru yayi kawai yana nazari har suka gama gaishe gaishe suka fita waje domin gaida Malam dake dakin zauren tareda manyan Almajiran shi, a nan khaleel ya Amince yes yayan shi yayi Aure inda ya dace, dattijo na gari mai mutunci, nasihar farko itace "sai kayi hakuri da duk wani shiririta ta mata zakaci ribar zama a duniya ka rike gaskiya kabi maganar mahaifiyar ka kagama lafiya, Allah ya kade fitina ya kuma baku zuri'a tagari. Wani irin girman tsohon khaleel yagani tareda tsantsar mutuncin shi, tabe bakin shi yayi tareda kada kai kawai Wanda shikadai yasan meke zuciyar shi.
Saida sukabar gidan sukaje harabar katon gidan nasu ya dafashi "Yaya I don't know much about Al Ada, Amma nagani Ina yaro idan Ana Aure a familyn mu idan ankai Amarya the next day y'an uwan ta nazuwa, why your bride basu zoba kuma sun san zata bukace su? "Hhh Khaleel mutunci kenan da gudun Abin duniya na gidan su Naziya bakaga komai ba ma Indai zuri'ar malam Abubakar ce, "but Yaya naga younger sister d'in ta ko ita batazo wurin Y'ar uwar taba. "Kasan Abinda momy tayi musu jiya shima zai iya sawa su hana wani zuwa gidan nan. Yafada fuskar shi na canzawa,
"Is OK muje ciki yau dai zaka tare dakin ka enough of the budan kan. "Hmm Allah yasa. Anyi la'asar koda suka shiga gidan, Wanda tana takaiwa da dawowa daga kitchen zuwa falo domin shirya Abincin Dare, duk Abokan hirar nata suntafi, gashi momy tace tayi tuwo miyar kubewa da kuma farfesun kan rago.
Tana cikin Adon ta sosai haryanzu tareda baza kamshi kamar Amarya. Har zata fito cikin kitchen din taji muryar su Suna Dariya ta koma, wani irin zafi takeji a kirjin ta she thinks kamar da gangan ma Ahmed ya Aurota ya kawo cikin gidan su domin ta wulakan ta, toh yayi kuskure, kuma zata nuna mai Abinda Aka koyar da ita daga gidan su, zai gani tarbiyar Inna bazata taba faduwa kasa banza ba, she cried yerstaday, kuma bazata kuma zubar musu da hawaye ba, aiki kuma Alhamdulillah, bazai gagare taba domin ta horu girki ma zatayi Amfani da nata salon domin gujewa damuwa, da izinin Allah zata basu mamaki.
Da taimakon mai Aikin take Amfani da kayan wutar, tsab tuwon shinkafa ta dora Wanda tasa mai ruwa wadatacce da zai dahu lugub, sai kan ragon data wanke tas ta zuba a wuta tareda neman kayan kamshi na gargajiya ta daka ta watsa, tuni kamshi ya cika ko Ina.
Tayi dai dai kuma hankalin ta kwance tana aikin ta, ya shigo ciki, turus yayi yana kallon ta cikeda mamaki domin dai bai kamata ta shiga kitchen ba, tana Amarya kuma kwana daya a gidan miji a ce tafara aiki bayan ga maids cike da gida, wucewa yayi wajen firij saida ya bude taji motsi tareda Saurin juyowa tagan shi ya daga gorar ruwa sama yana sha, Saurin juyawa tayi tana cigaba da aikin ta, domin ta lura ya cika girman kai, and she promise zata kiyaye shi tunda baice Mata ba itama bazata taba yimai magana ba.
Har ya Ajiye gorar ya juya Abun shi yana mamakin halin ta, ko kallo bai ishe taba Wato? Hmmm".
Karfe shida ta kammala tuwon tareda miyar kubewa lafiyayya da taji namomi a ciki, maid tace"Aunty Saura Abincin master karami. Kallon ta tayi "da daren ma bayacin Abincin mutane? "Yes saidai Ana dafamai ruwan tea ya hada ko coffee. Shiru tayi kafin tace ta kwaso shrimp d'in da su crabs, da kanta ta gyara ta wanke tas tasa ta gyara Mata Y'ar citta dasu garlic tace ta daka mata su da Albasa da tarugu saida suka daku ta d'an sa ruwa ta shafe su tsab harda spices, ta saka a oven, ta saka lowest yanda bazai kone ba kafin tayi wanka, maid din ta yanka mai salat ta wanke su tumatur.
Dakin ta ta koma ta tube tareda shiga wanka, cikin Sauri Sauri, ta dauro Alwala domin ankira magrib, bata tsaya yin dogon Azkar ba ta mike cikin Sauri ta canja zuwa wata doguwar rigar Atamfa mai flay cikin dinkin da malam ya Mata, tayi kyau sosai,
ta daura dankwali ta fito. Yanzu duk sunfito Suna falon momy dasu Ahmed harma da Khaleel, yana Rungume da katuwar tab yana dannawa, Suna hira kasa kasa su duka. "Toh hamshakiya abamu Abinci yunwa mukeji. Mommy ta fada. Muryar ta a kwance tace na gama momy zan shirya ne kawai a dining. "Noo ki sa maid ta shinfida mana dadduma anan bazamu hau saman ba,.
Bakomai yasa tace hakan ba saidan kar su zauna kusa itada Ahmed. Domin sa idawan ta dazu sun tsegunta Mata kamar yana rike Mata hannu ta kasan table, Wanda bazaka taba gane munafukan sungan suba.
Tunda ta fito Ahmed ya zuba Mata ido wani irin numfashi yakeja a ciki, domin Allah yagani shiba dutse bane, idanun shi ko kyaftawa basayi akan kirjin ta da yake gani, tareda Ayyana irin cika mai Hannun da zasuyi, har wani irin Aunawa yakeyi, he know dai dai Hannun shi ne. Kallo ta yakeyi sosai har mommy ta lura. Tareda Ayyanawa a ranta "Ahmed Indai ni Balkisu ce na haifeka bazaka taba hadamin iri da yar matsiyata ba muje zuwa.
Tayi k'wafa, Saida ta jera komai tareda turawa khaleel nashi cimar ta koma gefe ta zauna itama, gaba daya kamshi ya gama cikasu, ita kanta mommy miyon ta ya tsunke, wani irin murmurshi Ahmed keyi na jin dadi, domin yana ganin yanayin Abincin yasan zaiyi dadi sosai.
Khaleel ma kallon Abincin shi yakeyi, domin ba ataba hadamai shi da komai ba yana ganin yanda yayi wani irin kyau ga Aroma na tashi. Momy kallon yanda yake kallon Abincin tayi tace "idan bazaka iyaci ba ayi maka wani? "No is OK, yafada yana daukar fork yafara ci. Wani irin test yaji tareda dadin da baitaba jin yayi ba, domin ta yimai hadin da kowama zai iya ci. Kallon shi Ahmed yayi "yadai brother its good? "Of cos Yaya she is a wonderful cook. Batareda ya kalli side d'in ta ba.
Shiru kakeji a wurin kowa na zuri, saida taga kowa baiyi complain ba itama ta debi kadan tafaraci, Ahmed sai aika Mata da sakonni yakeyi ta gefen ido, ta dukar da kanta dama suna facing juna itada shi.
Saida mommy tayi nak tace "next time idan zaki tuka tuwo ki tabbatar yayi sulbi sosai. To kawai tace domin idan dai ba tuwon masara takeso ya koma ba, tasan ko hasidin iza hasada yasan tuwon nan ya tuku. Maid din ce ta tayata suka kwashe komai zuwa kitchen, tayi daki domin yin sallah. Suma fita sukayi masallaci.
Mommy ce zaune a falon tana waya da Zarah "So nakeyi Auren khaleel ayishi cikin Sauri, don haka zanturo miki kudi kifara yomin odar Kaya na gani nafada, domin bikine zamuyi shi na kece raini.
Shigowa sukayi tayi Saurin Sallama, ta Ajiye wayar, zama sukayi tareda gaidata, tace tom dare yayi ku wuce ku kwanta Allah ya tashemu lafiya. Taci gaba da latsa wayar ta, "mommy in tafi dakina? "Ahmed yafada cikin sanyin murya mai hade da lallashi. "Saurin uban me kakeyi? Da da bakayi Auren ba uban me ya sameka? Kaga Ahmed ka fita idona in rufe, saboda aji dadin Asirce ka shiyasa kake kokarin shige Mata, to kabari sai nan da sati daya idan Agumun da aka kullo Mata ya sirace ehem. Saurin kallon ta khaleel yayi tareda cewa "Haba momy haka ake Aure fisabilillahi? Ai da kin hana kawai yayi Auren wannan irin kwalelen ya isa Haba. "Toh ubana ai kai nasani zaka iya dukana ma, to dak'ar ni kaji, ku tashi ku wuce kubani wuri kafin in canja shawara.
Khaleel ya fara mikewa fuuu ya wuce saboda takaici, Ahmed ya tsaya tareda zamewa kasa ya dafa kafarta "don Allah momy in laifi nayi miki ki yafemin don Allah, kibarni in sauke hakkin Y'ar mutane ko lekata inyi infito minti biyar ya isa don Allah. Yafada yana zubo da kwalla, tace "minti biyar idan ka wuce hakan zan shigo kuma wallahi bazakaji da kyau ba.
Tashi yayi da sauri yana share kwalla "na gode mommy, ya nufi dakin yana Ajiyar zuciya, a zaune take tana waya da Shukrah a wayar Inna, tanajin motsi ta kashe tareda mikewa tana jan hijabin data Cire ta Ajiye a gefen gadon nashi. Rufe jikinta tayi a cukurkude tareda daburcewa ta rasa Ina zata shige ma, "Hmmm yayi doguwar Ajiyar zuciya. Ya fara takowa cikin natsuwa tareda zuwa gaban ta. Hannayen ta ya riko. "Naziya"Am sorry please kinji komai zai wuce please don't be angry with me I love you, hannu yasa ya zame hijabin dake kafadar ta ya fadi kasa ya zuba Mata ido tundaga sama har kasa.
"I don't know you baby, yanzu nake sanin God gift da nasamu batareda sani na ba, you are beautiful baby, yafada idanun shi na kadawa kamar zaiyi kuka, cikin natsuwa ya bude hannayen ta yajata saman kirjin shi, jikinta na wani irin rawa domin wannan ne karon farko da namiji ya rungume ta, shikuwa jin kirjinta a nashi tuni yajishi a sama, Abunka da pure man da bai saba da cakuduwa da mata ba, Saura kiris su zube kasa, yana fesar da iska bakinshi domin samun sauki ya dago fuskar ta tareda dora lips dinshi kan kyakkyawan bakinta yaji kiran momy, " Ahmed karka Bari inshigo ciki ranka zai baci nafada maka. Saurin janyewa tayi domin a tsorace take dashi tanajin yanda yake murza jikinshi a laps dinta she can feel his hardness, da bata kawo komeye ba ma. Muryar shi a shake yaja baya "please kibiyoni Anjima Kinga mommy tace infita anan please wife kifito ko kitchen ne muyi magana. Yafada yana fita cikin hanzari da Sauri, wasu irin kwalla ne suka taru a idanun shi.
Zamewa tayi kasa ta zauna tanajin wani irin yam yam a jikin ta, Allah yagani tana son Ahmed, Abinda ya boye mata Wannan ta fahimci dalilin shi domin ita ta nunamai batason namiji mai hali, Sannan yanzu ta Kara fahimtar shi Waye daga jiya zuwa yau, yana matukar son familyn shi yana bin umarnin mahaifiyar shi mai cikeda matsaloli Wanda ta daura damarar zata yi mata biyayya muddin ranta domin Ahmed, wani irin tausayi yabata yanzu, hawayen data hango akan kyakkywar fuskar shi kawai ya karya mata zuciya, me zatayi da zai sanyaya mai rai?
Daukar wayarta tayi ta Kira yayar ta bayan ta kulle kofar ta, Aunty Raliya, itace babbar yayar su ita ma tana Auren mai d'an hali saidai kamar yanda Al Adar su take suba masu yawon gidajen y'an uwa bane, "Aunty Raliya Ina wuni. "Amarya yadai kina kirana Karfe goma lafiya ko? "Lafiya kalau Aunty yasu Abba? Duk sunyi bacci, Ina fatan ba Matsala ko? "Um um, "Ina mijinki kike Kira na by this time? " baya nan yana dakin su. "What bangane ba, kodai kinki yarda dashi ne? "Aa. "Naziya, ki fadamin damuwar ki Kinga ke ba kawaye gareki ba da zaki fadamusu ni yayar kice bazan so ki cutu ba, bakomai Aunty. "OK listing to me kije ki dafamai ruwan tea mai kayan hadi ki shirya ki kaimai dakin nashi, kinsan wasu maza basa son shiga dakin mata saidai mata su bisu, "Aunty sai inje? "Karkije kinji, ki tsaya shirme wawuya kawai. Ta datse kiran kit, domin tanada zafi, tasan duk Abinda ke faruwa kuma sunada labarin uwar mijin Naziya domin Zarah kusa da ita take kuma haryau batasan Naziya kanwar tabace don haka ko dazu tashigo tana bata labarin Hajiya bilkisu da yanda take juya Ahmed, tana dariya da jin dadi,
Shiru Naziya tayi tarasa ta Ina zata fara, tashi tayi cikin Sauri, saida ta leka falon taga bakowa domin mommy nada nauyin bacci tana shiga dakin ta ta bingire, kitchen ta shiga ta dafamai ruwan tea harda na'a na'a, yana tashin kamshi, ta samu tea jug da cup ta zuba ta fita tana tunanin Ina zata ganshi harta bashi tea din takoma dakinta, jitayi anriko Hannun ta, tayi Saurin juyawa zata Sa ihu yace "Shhhhhh, nine, ware idanu tayi, jikin ta na rawa tace "ga tea Dama shi zankai......... Rikota kawai yayi ya nufi hanyar dakin khaleel da ita, yana kan computer yana duba harkokin company dinsu da Ahmed ke gabatar mai yanzu, ganin su yayi kawai ya sauke kanshi. Saida ya zaunar da ita ya koma gefen Khaleel yace "brother please excuse us. Dago kai yayi tareda kallon yayan nashi cikin idanun shi kuma yasan sarai me yake nufi yace "Ina zanje Yaya nida dakina? "Go to my room please, "zan tsaya a falo idan kungama magana indawo but I can't go to your room yanzu na Matar ka ne, "OK tanks ten minutes kafin mommy ta farka,.tashi yayi tareda daukar wayar shi ya fita yana "quick brother kaga Ina aiki na ka tsayar dani,
Kulle kofar yayi tareda nufar inda take tsaye cikin hijabin ta,....... 🖊
*Matar Soja*
🌻🌻AUREN GADO🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y'an 🇳🇪 Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,
🆓 page
1⃣1⃣&1⃣2⃣
................rikota yayi zuwa jikin shi tana zamewa yace "wait Naziya please magana zamuyi kawai. zama yayi agefen gadon, ya dorata akan kafarshi, "Kiyi hakuri da duk Abinda yake faruwa that's our destiny, komai zaizo karshe, nasan kinada tarbiya kinada hakuri please keep it up, zamuci ribar Abun, idan kikaci gaba da tafiya a haka banida wata damuwa, yakamata ace yanzu mun zama daya, yakamata ace muna cikin bargo daya, yakamata mu zauna muyi hira in kula dake kamar kowane miji, but don't worry komai zai wuce, yafada yana zagaye west dinta da hannayen shi, tareda kwantar da kanta cikin kirjin shi, wani irin Abu takeji yana mata yawo a cikin jiki duk lokacin da ya tabata, kodon bata taba experiencing irin haka a Rayuwar ta bane. Jin yanda yake cusa kanshi a wuyan ta yasa take d'an zamewa domin tanajin yanda yake kokarin daga hijabin jikinta tareda nufar kirjinta yana so yaji how they are. Tayi Saurin riko Hannun shi tareda Saurin juyawa tana girgiza mai kai cikeda marai raicewa. Kallon ta yayi cikeda roko yanaso tabarshi yayi yanda yakeso ko zai rage zafi domin yasan bazai yuwu ya nemeta a dakin khaleel ba, kuma yana falo zai iya jinsu domin yasan bakaramin aiki zaiyi ba, kuma yasan zata iya mai kuka tunda ko kirjinta bai fara tabawa ba . "Naziya " yakirata cikin wata irin murya, "inaso intaba inji, nonon ki nada kyau dazu kamar inyi tsalle in cafka nakeji Dana ganki ba hijab, kibani Dama ingansu inyi wasa dasu ko kadan ne. Wani irin tsalle tayi tareda zamewa ta rufe fuskar ta saboda kunya da maganar shi ta bata, kai namiji baida ta ido, saikace ba Ahmed innocent man ba yafada har yana dariya, "is OK tashi in rakaki wata rana da kanki zaki bani insha. Saurin mikewa tayi ya dafata "da munkwana tare da tuni sunzama toy dina, Amma lokaci ne. Kunya kamar ta nutse kasa, shikuwa ko ajikin shi,
Fitowa sukayi yana tsaye a falon rikeda ruwa mai sanyi yana kwankwada idanun shi cikin nata karab, idan ba gizo idanun ta suke mata ba tana ganin irin kallon rainin hankalin da yake mata, hartayi Saurin kwace Hannun ta ta wuce da Sauri, yana "baby ba Sallama, ita kuwa bazata iya tsayuwa kusa da d'an rainin hankalin nan bane Sam, mai halin yahudawa, ace mutum kullum cikin guntayen kaya kamar wani nakan dutse, mtsww.
Saurin wucewa dakin yayi yana karewa gadon nashi kallo yaga yanda zanin ya zame gaba daya, saboda zaman da sukayi a gefen shi, kuma bakaramin jujjuyawa Ahmed yarikayi ba saboda mugun feelings din da yakeji, shigowa yayi yace "Sorry Bari in gyara mana gadon, shiru yayi har yagama ya wuce bathroom, yana kallon yayan nashi bai ce tak ba, ganin yayo wanka yafito yaganshi a tsayen yace "yadai ko wankan kaima zakayi? "No ba munyi wanka ba kaima naga weather din is OK why you bath again? "Hhhh oh come on brother ko bakaga ma tata ta shigo ba kaima kasan dole inyi wanka ai. "in ten minutes? Ya fada batareda ya san maganar ta fito ba, "of cos is enough for me. Ya bashi Amsa tareda hayewa gadon ya kwanta cikeda farin ciki, kafin ya tuno da tea ya diro ya tsiyaya ya farasha yana lumshe idanun shi.
Komawa yayi kan kujera ya zauna yana danna waya har Ahmed yagama ya haye gadon yana cewa "ga coffee idan zakasha narage maka. "Uhm. Kawai ya Amsa, ganin Sam bazai iya bacci ba ya mike ya shiga bathroom wanka yayi tareda Alwala yadawo dakin yatada sallah.
Gefen Naziya kuwa, tayi bacci cikin kwanciyar hankali tareda farin ciki, tasan Allah yabata miji mai halin kwarai kuma da yardar Allah zata tayashi yiwa mahaifiyar shi biyayya.
Sabo da tashi da wuri Karfe hudu ta tashi, saida ta yi sallar nafila kafin biyar tayi farillah, ta zauna Azkar zuwa Karfe shida ta fito cikin karamin hijabi zuwa kitchen, ta shirya musu breakfast mai lafiya. Kafin bakwai da rabi ta kammala ta gyara ko Ina takoma tayi wanka, shiryawa tayi cikin Riga da zani, tafito tsab, tana kamshi.
Kiran mommy yasa ta fito da gudu tana amsawa ta ganta hakimce, dukawa tayi ta gaida ita, "ke bakisan kiyi pleasing uwar miji ba ta hanyar shiga dakina ki gyaramin da kuma dakin khaleel, toh daga yau gyaran dakunan mu na Hannun ki idan kin tashi. "Toh mommy. "Oya a shirya mana breakfast anan yau ma.
Fitowa Ahmed yayi idanun shi kur akanta yana aika Mata da sako tareda murmurshi mai cikeda sirrika. Itama tayimai tareda dukar da kanta tafara aikin ta,
"Ina Ibrahim din? Bacci yakeyi jiya baiyi bacci da wuri ba yace sai ya tashi. "Aa nifa banason wasa da ciki, ke Naziya yi Sauri ki kaiwa dana Abinci a daki karya kwanta da yunwa. "Mommy da kin Bari ya tashi. "Wuce maza ki kaimai. tafada, tana cewa "jeki zanyi serving din mu maza ki tabbatar yaci kafin ya kwanta. Jim tayi kamar bazataje ba tace "me kike jira? Cikin tsawa, da Sauri ta dakko tray ta shirya mai komai nashi ta wuce jiki a sanyaye "Allah yagani itadai jinin ta bai hadu dana gayen nan ba, baiyi mata ba Sam, da Sallama ta shiga dakin, yana kwance a tree seater a kudun dune, fuskar shi ce kawai a bude. Idanun shi biyu yana kallon sama, Sallamar ta yasa ya d'an juyo cikeda yanga, ta tsaya daga nesa muryar ta na rawa ga shi inji Mommy, ta dora akan karamin table zata juya, "Serve me. Yafada cikin isa, tayi Saurin juyowa "wannan mugun d'an rainin wayau ne, batason musu don haka cikin Sauri ta juyo batareda ta kalle shiba ta hada mai komai tafita cikin Sauri.
"Hmmm kawai yace yafara cin Abincin shi. Yana lumshe idanun shi.
Komawa tayi falon tace tabashi. Kafin ta zauna tafara nata Karin.
Toh haka dai kwanaki keta tafiya yau Naziya ta kai wata daya cur Agidan komai na gidan tundaga gyaran dakunan su zuwa kitchen ya koma Hannun ta, complain din momy ya riga ya shiga jikinta, Ahmed kuwa yanzu ganin shima gagarar ta yakeyi domin dokar mommy tayi nisa yanzu, tun yana rokonta harya hakura ya zura ido, sai rama yakeyi a tsaye saboda damuwa baya ko son haduwa da Naziya saidai suyi chart da wayar da ya siya mata katuwa wadda ta boyeta a dakin ta bata Bari mommy tagani ba, by now ta fuskanci muguwar kiyayyar da mommy ke mata. Idan ya fita aiki kuwa yana kiranta kullum bata hakuri yakeyi,. Tana kwantar mai da hankali domin ta saki jiki dashi sosai, yanzu har marmarin ganin shi takeyi akusa da ita she is missing his touch, rabon da ya rungume ta tun a dakin Khaleel, kullum Aunty Raliya shawarwari take bata wainda Sam basuda Amfani a wurin ta tunda an hanata sakewa da mijin ta. Iyakar ta dashi sai ban hakuri tareda Sanya mata Albarka a kullum "Naziya ke Y'ar Aljannah ce, watara na zakiyi farin ciki, ki Kara hakuri komai mai wucewa ne.
Bikin khaleel Ansa rana wata daya mommy sai shiri akeyi An shirya event Kala Kala, khaleel ko a jikin shi domin Amaryar ma ko wayar ta baya dauka, Wanda ta watsa shi a kwandon shara tunda dai uwar miji na sonta ai zata wataya kuma dole ya sota.
Zaune suke a office din yayan nashi ya kalle shi "brother sai ramewa kakeyi are you Alright? "Am not khaleel, yama zan zama cikin kwanciyar hankali bayan kana ganin me yake faruwa? "Am sorry Yaya bansan yanda zantaimake kaba. "Is OK yanzu kaga maganar shigo da kaya zai zo dai dai da lokacin Auran ka naso kaje da kanka, ko zaka Bari kaje honey moon gaba daya? Yafada yana d'an murmurshin karfin hali. "Noo wane irin honey moon? Zantafi kawai idan nadawo ai ba guduwa zatayi ba. OK kafadawa mommy ba ruwana.
Karfe biyu suka shigo gidan, an baje akwatunan sunkai saiti bakwai an narka dukiya kamar za asiyo mutum, suna shigowa tace "Yauwa khaleel zoku gani komai yaji? Tafada cikeda farin ciki, ya zauna yana kallon kayan tareda mamaki " mommy kayan Waye duka? "Ga rainin wayau, na Matar ka ne mana. "Duka? Yes gaskiya aa a raba biyu abawa Naziya rabi. "Why zan bata rabi? Saboda am sure ba ayi mata irin haka ba. Yafada cikin zafin rai, "bazan bayar ba domin batasan darajar suba, fitar kunya nakeson inyi dasu gidan minister guda dole akai Abinda baza a raina muba, Kuma ka nemo motar da za a hada mai tsada ta mata. Ahmed ne ya katse maganar "Zamuyi placing oder momy na kayan mu sai kasa a turo motar da kakeso kafin katafi.
Saurin kallon shi tayi tareda cewa "Ina zaije? "China zai shigo mana da wasu kaya. "Yaushe? Nan da sati uku. "Saboda mugunta? yaro zaiyi Aure ya Amarce shine zaka turashi wajen kwaso kaya? "Mommy, ni nace zanje ba Yaya ya sani ba, I want to go. "You are not going don haka ya shirya shi yaje, tunda nashi Auren baida Amfani, idan kanaso kaji dadi Ahmed sai ka Auro zabin zuciya ta Amma Indai Inada rai bazan hada iri da yar masu zama akan buzuba a mallake min da'.
Kallon momyn yakeyi wani iri, sometimes sai yaji kamar ba ita ta haifeshi ba, domin duk uwa tana son farin cikin d'an ta. Tashi yayi kawai yayi dakin shi dai dai tana fitowa ya ganta Amma saboda ciwon da kirjin shi ke mai yakasa ko tsayawa yayi mata magana. Kallon shi tayi sosai, taga ramar shi a yau tareda yanda yayi sanyi sosai, duk da ba mai hayaniya bane,
Jikin ta yayi sanyi, Allah yagani yanzu ba Abinda takeso irin su zauna suyi hira ido da ido ita dashi domin kullum soyayyar shi karuwa takeyi a zuciyar ta.
Kallon momyn khaleel yayi "mommy me kike nufi da d'an uwana? "Kamar ya? "Momy ki barshi ya samu natsuwa mommy don't you see how sad he is? Bakya ganin yanda yake ramewa? Mommy Yayana na cikin damuwa sosai, I beg of you kibarshi ya huta haka. Wani irin kallon zanci ubanka tayi mai kafin ta mike cikin fada tayi dakin Khaleel din, "zanje inji dalilin da zai rika hadani da kai kana titsiyeni kamar ubana.
Binta yayi yana yi mata magana tayi banza tayi dashi. Zaune yake yana dafe kirjin shi, ta shigo "toh kanin uwata Wato da kun hadu saika rika zugo d'an uwan ka yana titsiyeni kamar ubana ko, toh ka fita I dona kuma ka saurare ni, nayiwa Kawata magana Hajiya sa'ade maganar Y'ar ta Salifa idan ka shirya zama da Matar son taka toh ka yarda ka Auri zabin rai na lokacin zanbaka damar da zaka zauna da Matar son taka.
Kallon mahaifiyar tashi yakeyi tareda yin tagumi saida ta ci gaba da fada yace "am sorry momy bazan iya musu dakeba kiyi duk Abinda ya dace insha Allahu zanyi miki biyayya. "What Yaya? Me kake fada? This is too much gaskiya Haba momy p...... "Quit Khaleel Yafada cikin dakamai tsawa, tareda nuna shi da yatsa "not a word again, why are you challenging our mother? Kar in kuma jin kalma daya daga bakin ka. Fita tayi kawai tana amsa wayar fauzy tana dariya "Y'ar Albarka wane irin product kike Amfani dashi na kayan kwalliya?
Wani irin bakin ciki khaleel yaji tareda kallon Ahmed din ya wuce domin shima ya batamai rai. kwanciyar shi yayi kawai yana kallon sama. Dawowa yayi ya tsaya akan shi "Yaya what ever is happening is not right. why zaka zuba ido kana over looking komai, how could you accept the second marriage? Ka manta me kafadamin, kaman ta kafadamin bazaka taba hada Naziya da wata mace ba? She didn't deserve All this life Yaya, she deserve to be happy. "Hmmm ya kakeso inyi Khaleel? Inyi disobeying mommy oh what? "She is my mother Ina so mu rabu lafiya, and Naziya yes I love her more than my life, yazanyi dole inbi mommy in inaso inga dakyau, ba wata mace da zata samu matsuguni a zuciya ta, ita kadai nakeso ita kadaice zabina, if Auren da mommy zatayi min shine zaisa tabarni da matata in zauna lafiya then be it, am ready to obey what ever she said that's final. Yafada yana mikewa cikin fushi yayi bathroom.
"She didn't deserve it. Yafada yana naushin iska, he feels as kamar shi yafi kowa jin ciwon Abinda akeyi mata, ita kanta nuna wa take ba Abinda ke damun ta, tun ranar da tazo gidan nan yaganta tana kuka bai kuma ganin ta cikin bacin rai ba, sai kace bata da zuciya?
Fita yayi fuu dai dai tana shiga kitchen, cikin zafin zuciya ya bi bayan ta, kafin ta ankara jin hucin mutum kawai tayi yana fesa mata numfashi cikin zafi a bayan wuyan ta, kurawa kwantacciyar Sumar dake wurin idon ta yayi, idanun shi sun kada, he don't really know why zuciyar shi ke tafasa, he is trying to control his Anger da baisan dalilin taba.
"Auzubillahi. Tafada tana ja baya da Sauri domin tsayuwar da yayi a bayan ta ya kaucewa tsarin Addini, kuma shi ba muharramin ta bane, wani irin kallon bakada tarbiya take watsa mai tareda nisan ta kanta daga kusa dashi, he can clearly read her reactions, don haka tuni zuciyar shi ta Kara hawa, "what? Why are you looking at me like that? Yafada yana describing da hannun shi, A haka zaki karasa zaman Rayuwar Auren naki you don't care about your husband, kawai kiyi bacci ki tashi ki dafa Abinci, shine damuwar ki, you are pretending as if you don't care about All this wealth, you are such a jocks, kin zauna kin baje ba Abinda ya dameki sai kici kiyi bacci you forget All your responsibilities, look if anything happen to my brother because of you, I won't forgive you.
Tunda ya fara magana kallon shi takeyi, kuma irin kallon you won't get away with this, yanayin shiru ta gyara tsayuwar ta tareda daga gira daya, and she look very cute, "oh really? So nice bansan responsibility dina ba? Saboda nayi shiru Ina kallon komai, waya fada maka Ina farin ciki da duk Abinda yake faruwa da zaman Aure na? Nice nakeda complain ba yayan kaba because I know my right, and da kake cewa duk Abinda ya samu yayan ka bazaka yafemin ba, ni kuma in wani Abu ya same ni fa? Kana tunanin iyaye na zasu yafe muku? "And don't forget he is my husband, kuma munyi Aure saboda Ina son shi ba kiyayya ba, this house Hmm who told you am happy in this house? hakuri nakeyi bisa ga irin tarbiyar da aka dorani akai, iyaye nagari suka daga rayuwata, yawo da shigar da bata dace ba duk iyayen mu sun hane mu, shiga hurumin da bana muba duk iyayen mu sun hane mu, Saboda sudin iyaye ne nagari......... "Nice ba uwar kwarai ba kenan? Mommy tafada cikin tsananin bala'i
Jikin Naziya na rawa tayi Saurin kame bakin ta, tareda dana sanin biyewa zuciyar ta ta tsaya kula khaleel bayan hakan ma bai dace ba, yanzu tun ba aje ko inaba she is regretting....... 🖊
*Matar Soja*
🌻🌻AUREN GADO🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun bankina nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, 500 ne kacal nagode,
🆓 page
1⃣3⃣&1⃣4⃣
.............. "Mommy, magana mukeyi please don't interfere please. "Karya ne wallahi duk naji Abinda ke faruwa tundaga farko, Wato munafuka sai ki rika nuna halin kirki Wato mugun halin ki na can cikin zuciyar ki ko, "toh kin fada son ranki yanzu ki saurare ni mai miji, yau nawa ga wata? Aure zanyi wa mijin naki rana daya da Khaleel, zan Auro mai Matar kwarai Matar nunawa sa'a ba Y'ar gidan masu kwana kan buzu ba, munafuka kinayi kamar tagari Ashe bakin hali na nan a gefen zani, kin tsaya kina musayar miyau da kanin mijin ki sai kace sa'an ki. Dafe kanshi kawai yayi, you mess up things kawai, Naziya durkushewa tayi for the second time ta saki kuka mai ciwo "kishiya Aure? Bayan ita ko dama ba abata ba ta mori Auren shine ake wani zancen za ayi mata kishiya?.
Tashi tayi da gudu tawuce zuwa daki tabar aikin domin wani irin zafi zuciyar ta keyi mata.
Kukan ta ya taba mishi zuciya fiyeda tunanin mutum wani irin sarawa kanshi keyi kamar zai tsage biyu.
"Kai kuma ka tsaya yarinya karama na zuba maka rashin kunya kana kallon ta, bazaka watsa mata Mari ba, kauce ni in wuce ka batamin rai. Tafada tana fita, sintiri yakeyi a kitchen din yarasa Ina zai sa kanshi, kallon da ta watsa mai ne yafi komai daga mai hankali, she really hate him. Fita yayi da sauri ya Kira maid yace ta karasa aikin girkin yayi dakin shi,
"Ahmed yasamu akan dadduma yana lazimi, yace "Yaya please go to your wife she is crying please. Saurin mikewa yayi me yake faruwa? Wa ya sata kuka? "Is you Yaya kaine sanadi, mommy Tafada mata zakayi Aure please go to her. Yafada zuciyar shi na wani irin rawa, komawa Ahmed yayi gefen gadon ya zauna dabas, "I can't go khaleel. "Why? Yaya Matar kace, she needs your comfort please. "Mommy tayi min iyaka da ita. "Iyaka? What iyaka? "Yaya hakkin yarinyar nan bazai barka ba karka manta ba mommy ce kawai keda hakki akanka ba, why ka Auro ta idan bazaka iya ba?
Kukan da yaga Ahmed din nayi yasa yayi Saurin zama gefen shi ya rungume shi yana Ajiyar zuciya, "am sorry Yaya please nasan komai, amma kaine kabada kofar komai dake faruwa. Bai iya cewa komai ba sai shesheka yakeyi "am sorry khaleel banda karfin zuciya irin taka am weak.
Saida ya fitar da kwallar tausayin d'an uwan nashi.
Naziya kuwa tana shiga ta kulle kofar ta fada bathroom ta shako kukan ta son ranta, Karar wayar ta tasa ta fita ta dauka ganin number Ahmed dince yasa ta datse kiran kit tareda kiran Aunty Raliya.
Tana dauka tasaki kuka mai ciwo. "Aunty wallahi nagaji ni zankoma gida nagaji bazan iya ba, zan mutu a rasa dalilin mutuwa ta Aunty please kizo ki tafi dani.
Saida tayi ma ishinta ta yi shiru tana jinta, "Naziya', ta kirata, bata iya amsawa ba sai sheshsheka tace " kin taba ganin ko kwana muntaba yi agida tunda mukayi Aure, bare kuma yaji? Dagani har Aisha ba wadda ta taba kai Karar mijin ta cikin gida ko gaban malam, muna hakuri tareda bawa junan mu shawara in Matsala ta taso, infada miki gaskiya? Ba macen da batada kalar tata Matsalar Aure, please Naziya ki dauki halin Inna, kina gani kullum malam yabon ta yakeyi domin yasan mace ce tagari, nasan duk Abinda yake faruwa a gidan Auren ki, ba kanki farau ba, ki jajirce kici gaba da hakuri, yanzu fa aka fara Naziya, ni nafada miki tun farko kibi mijin ki tunda shi an hanashi binki, biyayyar Aure kikeyi bauta kikeyi, ki rungumi taki kaddarar Allah zai kawo miki mafita.
"Aunty banki ta taki ba, Amma inayin iya bakin kokari na, kinaji fa wai Aure zai karayi. "Toh sai me? Baki yarda da kanki bane? Ke ba mace bace? Look ki nuna musu Auren ba komai bane idan bakida hakki zakiga saka mako, nasan kinada hakuri ki Kara akai kar taurin kanki ya motsa Wanda bakya juyuwa.
"Hmmm nagode Aunty, insha Allahu zanyi hakuri. "That's my sister, kuma insha Allahu zamuzo karshen satin nan nida Aisha. Dadi taji sosai domin Y'ar uwarta ta bata shawara mai kyau, tareda sanyaya mata zuciya.
Sharewa tayi da komai cikin ikon Allah, ta Kara rungumar hakuri tareda daura damarar share komai, tana ganin yanda aketa shirin biki kamar da gayya itama Amarya anyo mata kayan fitar kunya, Aljihu tasa Ahmed ya bude yana bata kudi ta zabgi kaya, ciwo yakeyi a tsaye batareda ya fadawa kowa ba shikadai yasan damuwar shi, Naziya tuni ya nesanta kanshi da ita domin ya rage mata damuwa, itama ta Ajiyeshi a kwandon shara, badon bata damuwa ba, biki nata matsowa shikuma yana shirin tafiyar shi.
Khaleel yayi yayi yabarshi ya tafi yace no shi zaije Ana gama biki Washe gari zai wuce. Mommy ma basu fada mata shirin su ba.
Khaleel ma tuni ya kiyayi Naziya domin ya lura tsanar tashi ta Kara yawa fiyeda da, yana ganin yanda take hada girar sama data kasa in sun hadu, shi yasan halinta Wanda Ahmed bai san shiba ma yanzu, daga gani macece kaifi daya inbata yinka shikenan, ga taurin kai.
Tana lura da Al amarin shi yanzu sama sama in sun hadu ta lura yanzu baya fitowa da kana nan kaya ko falo, tun ranar da tayi mai gori.
Biki fa yazo Amare nata rawar kafa, angwaye kuwa ko motsi basayi, ko Khaleel Yafada mata karta sake ta sakashi cikin shirmen party d'in su. Momy ta tattara su duka ta watsar tana hidimar ta, itadai tasan burin ta zai cika ya'yan ta zasu Auri irin zabin ranta, don haka ta zage ta bude bakin Jakarta.
Lafiyayyan mothers day suka shirya a tafkeken hall da yaji kudi, ta gayyaci manyan mata masu kudi da Aji, da kanta tayowa Naziya dunkuna Kala goma wai na dannar kirji tasa na fitar biki.
Lokacin da malam yaji labari, waya yasa aka hadashi da ita ya mata nasiha tareda Sanya mata Albarka, Wanda ta Kara mata kwarin guiwa, bawai Abun baya taba ta bane a'a "ya za'ayi bazai zafeta ba, kawai dai ta rungumi hakuri da kuma waraka, Wato Alqur'ani mai girma. Wanda shine maganin duk wata damuwa da yayewar bakin ciki.
Ana Saura kwana uku biki tasa Shukrah tazo domin ta yi mata lalle, Wanda saida tayi da gaske Malam yabari, tazo suka baje a dakin suna hira tana yimata lalle, "Aunty Kinga magana ta ko, nafada miki Yaya Ahmed mai kudi ne, gaskiya kin more irin wannan katon gidan. "Hmmm. Kawai tace, "Amma Aunty kin d'an rame kadan sai haske kawai da kika Kara, Ina Yaya Ahmed din? "Yana nan, kuma ki rage surutu kiyi sauri kafin lokacin da Malam yabamu yayi, Amma Aunty da gaske Aure zai Kara wai? "Eh. "Auren ku wata daya da y'an satika shine zai Kara? "Ya isa maganar shukrah, tafada domin batason zancen,
Maid ta kawo musu kayan ciye ciye a dakin, domin mommy tafita, har suka gama ta rakota tareda bata kyautar kayan shafa, domin batada kudi a hannun ta, suna fitowa su Ahmed sukayi Sallama, tayi Saurin dauke kanta. Shukrah baki har kunne domin tayi mugun sabo dashi tace "lah Yaya Ashe zangan ka kafin intafi? "A a shukrah kece a gidan namu? "Eh Yaya Ahmed har nagama wa Amaryar taka lalle zantafi, Saurin kallon hannun nata sukayi dukan su, khaleel yayi Saurin dauke kanshi, "kai Amma mungode shukrah da wannan zuwan Yafada yana matsawa kusa da Naziya ya riko hannun ta, shukrah tayi Saurin rufe idanun ta saboda kunya ta ruga hanyar waje tana ni na gudu gida Aunty bye, Dariya Ahmed yayi yace "please Brother ka kaita gida. Amsawa yayi kawai ya fita, motar shi ya fada dalleliya yabi bayan ta, tareda yimata horn, ta tsaya don har tafita wajen gate d'in, "muje ko' Yafada ba wani walwala, "nagode zansamu adai daita ma. "Come on ki shigo Yaya Ahmed yace inkai ki.
Budewa tayi kawai saboda batason musu, gashi ya cika mata ido, maganar gaskiya zaiyi wulakanci domin fuskar tashi Sam ba fara'a ko walwala, don haka batayi yunkurin cemai komai ba har ya Kama hanya yana driving slowly, sai kamshin shi da kwarjini da ya cika motar, "me yasa bakya zuwa kina ganin Y'ar uwar ki? Yafada batareda yako kalli gefen taba, itama Abun yazo mata a bazata duk ta diririce, saida ya mai maita, tace "ba a barin mu fita zuwa yawo. Tabe bakin shi yayi kawai bai kuma cewa komai ba har ya kaita kofar gidan tace ta gode, ya ciro kudi a gaban motar shi ya mika mata masu yawa, Saurin kallon hannun shi tayi ta koma gefe tana girgiza kai, domin kudin zai kai dubu Ashirin, "nagode bama karbar kudi a waje. Mayar wa yayi kawai yaja motar shi tareda bade ta da kura yayi gaba, "tab Aunty Naziya wannan ai yafi Yaya Ahmed girma da cika ido ga girman kai kamar d'an gidan Sarki,. Tafada tana bin bayan motar shi da kallo har ya bace.
Su khaleel na fita ta fisgi hannun ta tayi dakin ta da gudu, yanzu ne wani irin bakin ciki yake rufe mata zuciya, bin bayan ta yayi batareda ya shirya ba, zubewa tayi agadon ta kife tareda sakin kuka mai taba zuciya, dafata yayi tayi Saurin zabura fuskar ta shabe shabe da hawaye "don't touch me. Tafada kai tsaye tana mai kallon kai ne sanadi, "Ina dana sani, nayi hakuri tunda ga ranar farko da Nazo gidanku, bawai nace mommy bata isa tayi min fada bane, a'a kaine Matsala ta, kai kakawo ni gidan nan, Amma sai dai in hadu dakai a hanya, duk na daure nayi hakuri, yanzu kishiya...... Takarasa tana kife kanta a cinyar ta, shiru yayi tareda dafe kanshi yazame gefen gadon ya Rungumo ta baki daya zuwa jikin shi tana kokarin Sauka. "Nasani Naziya, ki yafemin don Allah, nasan sai Allah ya tanbayeni hakkin ki, domin banyi miki Adalci ba, yazanyi Naziya Ina gudun bakin uwa, yanzu ma na kaucewa tsarin ta da dokar ta, don Allah kiyi shiru ki yafemin kar Kisa ni a cikin damuwa, kinsan cewa ganin kwanciyar hankalin ki ke kwantar min da nawa, Amma yanzu idan kina wannan kukan zuciya ta zata iya bugawa kowa yarasa ni. Saurin yin shiru tayi tareda share hawaye da bayan hannun ta "meye laifi na? Saboda Ina Y'ar talaka? Meye illar talauci tunda bamu nema a wurin wani ba, Alhamdulillah da gidan da na fito bama raina Abin da Allah ya bamu. "I know" Naziya please forgive me, kuma Kisa a ranki wata rana komai zai wuce, zakiyi farin ciki insha Allahu, ni nasan banda wata kalma da zanyi Amfani da ita domin baki hakuri Amma nasani na zalunce ki, ki yafemin. Naziya na gaza akanki ban sauke nauyin ki dake wuyana ba. Yafada yana dora fuskar shi akan wuyan ta, wasu irin hawayen shi taji suna bin wuyan nata, da sauri ta dora hannun ta saman kanshi tareda cewa "don Allah kayi shiru nima kaga na hakura nayi shiru, kaga bakyau babba na kuka. Tashi yayi tareda ita ya zauna gefen gadon, tareda fuskantar ta yana share idanun nashi yana mai murmushi kadan, "wayace miki ni babba ne a wurin ki? "Kai babba ne ai ka girme ni sosai. "No ni jaririne a wurinki domin wata rana shayar dani zakiyi,,, wani irin saurin rufe fuskar ta tayi saboda kunya, "Hhhhhh ko za a bani ne yanzu, Yafada yana riko west dinta cikin tsokana, ta zame cike da kunya, dadin moment din sukeji sosai, ta kalle shi cikeda tausayin shi tace, "bakada lafiya ne? Murmurshi yayi, "yes. "Meke damun ka? "Soyayyar matata, you know banason in rasaki Naziya idan nayi tunanin zaki iya gajiya ki gujeni hankalina natashi, bazan iya ganin ki kina Rayuwa ba agidana ba, banason inganki tareda wani Naziya saboda Ina sonki Ina kishin ki, ganin ki a inuwar Aurena yana sani inji farin ciki, yana rage min damuwa, please stay with me, my wife komai zaizo karshe wata rana zamu kasance a cikin inuwa daya zanganki da jini na atare dake a wannan shafaffen marar. Yafada yana shafo cikin ta, d'an zamewa tayi kadan domin yanasa ta jin wani iri a jikin ta. A wannan lokacin ya bata farin ciki mai yawa Wanda zata sakashi a tarihin Rayuwar ta domin yamata Alkawura da yawa akan yanda zaman su zai kasance, anan yake fada mata bayan bikin Khaleel da kwana biyu zaiyi tafiya, Kinga da momy zata Amince tare zamu tafi dake, muje musha soyayyar mu a can har in zagaya dake kasashe da dama.
Maganar mommy ce tasa ya mike tareda cewa mommy is here bari inje. Ya fita da sauri, tana tsaye tareda Khaleel Wanda shigowar shi kenan, tare suka zuba mai ido suna kallon shi, Wani irin mugun kallo ta watsa mai, "uban me kakeyi a ciki? Shiru yayi ya kasa Amsata, "Ahmed idan ka ketare iyakar da nayi maka banyafe maka nono na da kasha ba. Tafada tana nuna shi da yatsa, saurin daga kanshi yayi tareda girgiza kai kawai ya wuce domin bazai iya magana ba,
Khaleel ne yakalleta "why mommy? d'an ubanka, wallahi kaima kaji ko a mafarki naji ka fada soyayyar Y'ar talaka bazamu kare lafiya dakai ba. "Saboda me? Talaka ba mutum bane mommy? "Me ake da sunan talauci ma? Ni wuce bani wuri kuma kaji Abinda nace maka ko ku nemi Amaren ku sallame su banason harkar tsiya tunda dai Allah ya Azurta mu, idan bazaka iya cirewa a jikin ka ba kazo inbaka kabasu. "Wallahi mommy ba shegiyar da zanbawa kudina saboda tayi taron banza ai sunada kudi kowacce Aljihun ta yayi kuka, yafada yanayi gaba batareda ya tsaya saurarar taba, "kaga d'an banza, ai da Ahmed ne yanzu zaiyi Abinda nace Amma wannan mai taurin kan tsiyan sai mun sha fama.
Biki fa yazo, Amare nata shan even, momy yau ne take nata taron gidan makil da mutane ta gama cika gida da manyan mata y'an karya unguwar kawai daka shigo zakasan biki akeyi na kece raini, Naziya tun da gari ya Waye take jinta wani iri, mugun sanyi da zazzabi ke rufeta ma saboda damuwa, yau dai ba aiki domin komai odar momy tayo har Abinci,
Don haka tana kwance tana lazumi da carbinta na yatsa, Shigowa tayi cikin fada, "ke banason bakin ciki da kishi ki tashi ki shirya ki fito, kinzo kin kunshe a cikin daki kamar tsohuwar munafuka, Aure dai gobe insha Allahu sai an daura shi ko zaki mutu, in banda Abunki keda ko dadin Auren baki sani ba meye na kishi, don haka fito maza yanzu mutane natanbaya Ina uwar gidan Ahmed.
Tashi tayi cikin Sauri, tace "toh mommy, ta wuce bathroom ta sheko wanka, cikin kayan da momy ta bata ta ciro wani lafiyayyen leshi riga da sket kamar dinkin Amare ta saka, tana taje sumar ta taji Sallamar y'an uwan ta, Aunty Raliya da Aisha harma da Shukrah, wani irin tsallen dadi tayi domin Wannan ne karon su na farko a gidan nata, ta karbi d'an karamin goyon Aisha tace "Aunty my kalefa ya Kara wayau. Kallon ta sukeyi kawai domin sunga Alamar rama atareda ita ga kuma damuwa, basuce komai ba saida suka natsu shukrah ta tayata kwalliya ta murza dauri, sukace muje ki rakamu mugaida uwar mijin ki. "Toh tace suka fita, tana can kuryar dakinta da kawaye sai shewa sukeyi ita tafara Sallama wasu suka Amsa wasu suka zuba mata ido, suga Ina wannan kyakkywar ta fito, "mommy ga yayyina sunzo su gaisheki. "Toh sannun ku da zuwa, tafada tana gyatsina, kije dasu can dakin ki kisa Abasu komai domin akwai wadatar shi anan kuje. Tafada batareda tajira ko gaisawa suyi ba. Aisha dayake tanada fushi, har ta juya, Raliya ce ta tsaya tace "Allah yasa ayi a sa'a yakuma kade fitina, wasu sukace Amin. Ta juya Naziya tabi bayan ta,
Suna shiga dakin Aisha tafara sababi "wallahi Aunty Raliya wannan Matar batada mutunci yanzu dama Abunda ake fada gaskiya ne, gaskiya ni da malam zaiji magana ya raba Auren nan kawai. "Kinsan me zakiyi? Dakin bar nan saikije ki same shi kuyi magana kinji Aisha. Raliya tafada cikin haushi, wane irin Abu ne zaki tadawa yarinya hankali da mugayen kalaman ki, to sai me akanta farau da irin wannan uwar mijin? Don Allah kirika tausasa zuciyar ki. "Kiyi hakuri Aunty Abun ne yabata mun zuciya kalli yanda yarinya ta koma saboda fitinar wannan Matar, yanzu yarinya ko wata biyu kwarara batayi ba za azabgo mata kishiya wallahi ba adalci. "Ya isa bashi yakawo muba munzo ne mu debe mata kewa don haka don Allah ki daina mitar haka. Shigo musu da Abubuwan ciye ciye tayi ta baje musu tareda daukar kaleefa tana mai wasa,
Domin su dauke mata damuwa suka saki jikin su sosai tareda yimata hira tareda shawar wari, ta saki jiki a ranar, lokacin da aka fara taron ma tare suka shirya suka fito wanda tun shigowar ta gidan wannan ne karon farko data tako kofar gidan a yanzu ne take sanin Aljannar duniyar da take ciki, Suna fitowa khaleel na shigowa rikeda key cikin manyan kayan da ta lura yanzu yana kokarin sakawa, kallon ta yayi ya dauke kai tareda matsowa ya gaida su Aunty cikin girma yace kuzo muje inkai ku. Taso tace bazata shiga motar tashi ba Amma ba hali domin sun Ansa har suna godiya, Aunty Raliya tace munko gode domin bamu san wurin ba, shukrah ce agaba ita dasu Aunty a baya fuskar ta turbune domin Allah dai yagani tamafi kaunar mommy akan khaleel, a harabar wurin ya Ajiyesu dai dai ana kawo Amaryar tashi fauzy wadda tasha ado kamar zataje gasa cikin tsaddun bridal dress, Washe baki tayi tayi saurin nufoshi "baby "kazo. "No banzo ba mutane nakawo am going back, yafada yana shigewa cikin motar ya datse, su Aunty sukayi mai godiya yace bakomai batareda ya ko kalli gefen Naziya ba, gaba daya kawayen ta sukayo mata cah, "angon kenan Fauxy gaskiya gayen nan yaje, Amma akwai wulakanci. "Ba ruwanku I love him like that. Tafada tana juyi tareda cewa suje, suka take mata baya tana yiwa su Naziya kallon banza,
An barar da kudi a wannan taron na gagaruman mata da hamshakai, to suma dai ba laifi domin sunyi kwalliyar su cikin mutunci ba wadda tasaka gyale dukan su hijabine, Wanda ya janyo suke musu kallon rashin wayewa da tsantsar kauyanci, su momy an barar da rawa da kudi itada sauran iyayen Amaren, su Naziya na gefe itada y'an uwan ta har akaci aka sude, fitar tata tasata cikin farin ciki at least tafito a cikin wannan gidan dayake kamar kurkuku a wurin ta.
aka yi komai suka yi gidajen su, tayi farin cikin kasancewa tare dasu domin sun Cire mata kadaici da damuwa, Wanda sukayi mata Alkawarin dawowa Washe gari yinin bikin, throughout ranar har dare batasa Ahmed a idoba, an zubawa Amaren kayan su a sababbin ginin nasu dake gidan, kowacce an narka mata dukiya fiyeda tunani, dama haka Hajiya bilkisu takeso.
Kayan Naziya da ko a ido bata taba ganin suba tuni antattare an zuba su a store an zuba na Amarya........ 🖊
*Matar Soja*
0 comments:
Post a Comment