Gidan ya fara cika da 'yan uwa da abokan arziki yan daurin aure da biki. Da gudu ya shigo gidan har yana zubar da abincin dake hannunsa wata yayarsu ta janyo shi. Adnan saurin me kake yi ne haka? Yauwa yaya ina baba? Ya amsa yana ta haki. Wannan mutumin da ake nunowa a tv na gani a waje sun zo a cikin motoci masu kyau sai wani mai bindiga yace babanmu suke nema. Kai mai bindiga fa kace...eh wallahi amma na hango na tv din mai kudi ne fa. Jin kamar yana shirme Zainab ta leqa wajen da kanta ai kuwa babu karya wasu jeeps ne guda uku duka bakake amma ta tsakiyar tafi kyau. Ga mutane sun sha suit kowa rike da bindiga.ba shiri ta koma cikin gida ta nufi dakin baban su sai dai a hanya suka hadu har Adnan ya isar da sako. Shima dai mamakin yayi ya matsa wurin daya daga cikin guards din yace shine mai gidan. Yana kallo yaje wurin motar tsakiyar sai ga wasu mutane su biyu sun fito. Ba ko shakka senate president ne Rufai Bukar yasha wata ash shadda kana ganinshi kaga kudi da tsantsar jindadi. Dayan kuwa saurayi ne kyakkyawa amma fa kayan jikinsa kamar anyi wasan kura dashi. Guard din yace ciki zamu shigo. Nan Alh Bashir yace to cikin hanzari yayi musu jagora. Suna shiga jamaa sai binsu ake da ido har falon sa. Maman su Saif ta bi bayansu. Ganin waye bakon ta fito da sauri ta bada kudi a siyo lemuka da ruwan roba.
Alh Bashir ya sake gaishe da senator sai yayi mamakin ganin da kansa ya taso ya bashi hannu. Bayan sun gama gaisawa yace ni sunana Rufai Bukar. Ranka ya dade ai tuni na ganeka ni sunana Alh Bashir. Senator ya kalli Junaid dake zaune kan kujera ba zaka gaishe shi ba. Nan take ya sauko ya gaishe shi. To nasan zaka yi mamakin ganina tare da dana a gidanka ba tare da an sanar da kai ba. Haba ranka ya dade ai nasan dole ce ta sa. To akan maganar yarona ne Junaid... ..haka dai senator ya labartawa Alhaji komai na halayyar dansa da Hafsa da ya gani yana so. Ikon Allah kawai yake fada sannan yace idan na fahimci inda zancen ya dosa so kake Saifullahi ya hakura kenan. Hular kansa ya cire ya dago kai idanunsa da kwalla Alhaji ina tsammanin Allah baiyi maka jarabawar haifar dan da....kai Junaid ku fita. Suna fita ya cigaba da magana wadda sai da hawayen da yake kokarin boyewa suka zubo. Junaid yaro ne me hazaka tun kuruciya amma yanayin aiki da jindadin kudi yasa na sangarta shi. Yaronnan ya janyo min magana fiye da yadda baka zato ga shaye shaye ga....da dai sauran aikin sabo. A bisa amana nake fada maka sirrina Alhaji wallahi wallahi mulki da kudi jarabawa ne sosai daga Allah. Ban farga da munin share lamuran yarana ba sai da naji waazi daga bakin wasu malamai kamar su Daurawa, Kabir Gombe dasu Dr Sani Rijiyar lemo. Nasan nayi barna mara iyaka har ina tsoron ranar mutuwata. To a yau bani da burin daya wuce yaron nan ya shiryu ina ganin wannan zai zama sanadiyar samun rahma a gareni. Da gaske mutumin nan kuka yake Alhaji Bashir ya fada a ransa ganin hawayen senator. Naji dukkan bayaninka ranka ya dade amma yarinyar ba tawa bace. Na sani kuma nasan haramcin nema akan nema. To idan haka ne ko zaka yarda na kira mahaifinta dashi yaron. Ai mai nema ke bi kayi mana jagora gidansu kawai.
********************
Baffa don Allah ka yafe min nasan nayi kuskure wanda bana fatan sake maimaitawa. Hmm Hafsatu kenan ki sani kaza tana taka danta ba don bata sonshi ba sai don ta koya masa hankali. Hakika muna cikin wani zamani da ake tallata zina kamar kayan miya, wanda bai siya ba ma kallon banza ake masa. Amma ina so ke da ku ma...ya kalli Amira da Anisa lallai ku tuna wutar Allah mai radadi ce kuma baya bata da kadan. Sai ka aikata abu ka manta ma dashi watarana ya dawo ma lokacin da baka tsammani. Ki je na yafe miki Allah Ya yi muku albarka. Da farinciki suka tashi dukkansu balle ma Hafsi zuciyarta fes fes. Suna fita Alh Bashir ya kira Baffa ya sanar dashi zai zo gidansa da baki nan da lokaci kadan idan yana gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐17
Sakin baki Baffa yayi yana kallon Alh Bashir, Senator Rufai da Saif. Wane irin rainin hankali ne suka zo masa dashi. Gyara zama yayi ya kalli Alh Bashir...yanzu kana nufin ranar asabar da wani zaa daurawa Hafsa aure ba da Saifullahi ba? Wai ni Alhaji me kuke nufi da ni da iyalina ne? Akan hoton da yaron nan ya sa Hafsa taje suka yi babu abinda banyi mata ba karshe kuma sai kawai kace min daban yana son aurenta kuma ka amince. To kai ma ka amince ne? Ya tambayi Saif. Sunkuyar da kansa yayi kasa. Shi kam kunya tasa har zuci baya son auren nan don bazai juri haduwa da mahaifinta yana tuna ranar da ya kama su a mota ba.
Zuciyarsa har neman tafasa take don a yadda yake ji a ransa ko gyada aka dora masa a kan kirji tsaf zata soyu. Ina amfanin dan cikinka ya dauko maka abin kunya. Ba don hoton nan ba sam bazai damu ba idan Saif ya fasa auren Hafsi. Senator Rufai da yake gefe yana kallon abinda ke faruwa a falon yayi dan gyaran murya don ya fuskanci kwata kwata kudinsa da mukaminsa baiyi wa Mal Aminu kwarjini ba. Kallon da ya yiwa Baffan hafsi yasa yayi shiru...malam tun a gidansu munyi magana dasu yaron yace indai ka amince to zai iya hakura da ita. To a wane dalili ne wai zaku mayar dani karamin mutum irin haka? Ko don ba 'yarka bace shine zaku rinka juya min ita kamar waina. Bakin Baffa har kumfa yake yana magana ba karamin bacin rai ya shiga ba kila kudi senator ya basu shine suke neman yi masa wannan cin kashin. Senator Rufai yayi masa bayanin halin da dansa yake ciki da tsoron karin lalacewarsa sai baffa ya kada baki yace wato lalataccen danka kake so ya shiryu sanadiyarta ko? Idan kuma abin ya faskara ya dora min ita akan turbar lalacewa fa? Haka yayi ta fada karshe yace ni dai gaba daya na fasa bawa kowa Allah Ya hada kowa da rabonsa.
Abin da senator yake ta kokarin boyewa game da jikinsa ne ya faru don kuwa yana tashi kirjinsa ne ya fara ciwo sai jiri ya debeshi ya fadi. Baffa ko kallonsa baiyi ba don a tunaninsa na karya ne tunda yaga kudi bai dauke masa hankali ba. Saif da Alh Bashir kuwa da sauri suka yi kansa Alh Bashir a tsorace yace haba Aminu taimaka mana. Idan mutumin nan ya mutu a gidan nan wallahi duk sai an daure mu ko a yanke mana hukuncin kisa.
*******************
Alh Bashir da Mal Aminu ne tsaye gaban gadon da aka kwantar da Senator Rufai bayan yasa iyalinsa sun dan basu wuri. Da kyar yake maģana yace nasan a dalilina kun sami sabani amma bisa amana zan fada muku sirrina. Hakika duk wata kujerar iko a kasar nan is addictive maana idan aka hau ba'a son sauka indai ba ta sama za a hau ba. Magudin siyasa da hadamar kudin talakawa duk munayi. Ina tsammanin ma shiyasa Allah Yake jarrabarmu da lalurori da kala kala da 'ya'ya marasa da'a. Yasa hannu ya share hawaye. Ina matukar son Junaid ganinsa nake tamkar mahaifina saboda kamaninsu. Duk abinda ya zama a yau laifina ne saboda yadda na sakar masa yake facaka da kudin talakawan kasar nan. Tun farkon abin mahaifiyarsa ta fara hanawa ni kuma ina ta ganin kamar lokacinsa ne. Maganar tasa sarkewa tayi saboda tari Mal Aminu ya rirrike shi. Sai da abin ya lafa ya cigaba da magana. Muna cikin wani lokaci da yaran da ka tsaya da kyau wurin tarbiyarsu ma baci suke balle wanda aka sakewa. Masifu sunyi mana yawa duk a dalilin nesanta kanmu da mukayi daga Allah da koyarwar Annabi SAW.
Mal Aminu ya dan tabe baki don shima sheda ne akan rashin adalcin kasarnan da yadda yake ganin tarbiyar yara yanzu a matsayinsa na malamin sakandire. Ji yayi senator ya rike masa hannu wanda hakan ya dan tsorata shi. Sati biyar kenan da likita ya tabbatar min da cewar inada ciwon zuciya kitse ya lullube ta. Babu wanda na fadawa sai ku biyun nan da na hadu daku a yau. Likitan ya tabbatar min ko dai na cigaba da rayuwar shan magani ko na mutu. Subhanallahi Alh Bashir ya fada.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 18
Hakika mutuwa abin tsoro ce musamman ga irinmu masu aikata sabo muna sane. Kamar yadda na fada a gidanka Alhaji waazi naji yayi matukar razana ni. Ina tsoron mulki yanzu, ina tsoron kudi, ina tsoron haduwa da Allah akan laifukana sannan ina tsoron samun kamasho daga laifukan Junaid tunda laifina ne abinda yake yi. Akan yarinyar nan ya dawo gida da guduwa yayi. Akan ta yayi min alkawarin shiryuwa shiyasa kaga na dage. Idan har na mutu yana wanan rayuwar kabari zai min kunci. Kuka ne yaci karfin senator sai dai su uku mazan akwai hawaye a idanunsu. A wannan zamani hanyoyin dulmiyar da bayin Allah akwai yawa ga bayyana sabo saboda rashin tsoro. Mal Aminu yace zan amince amma sai anyi masa gwaje gwajen cutuka saboda lafiyar Hafsa. Ko sau daya kada yazo gidana sai na tabbatar da lafiyarsa sannan zaa fara maganar aure. Abu na karshe zamu rubuta yarjejeniya kai Alhaji ka zama shaida duk ranar da ya koma ga miyagun halayensa bayan aurensu kun amince kotu ta raba auren idan yaki shiryuwa. Na yarda na amince kawai senator yake fada. Ba zai iya fada musu mugun mafarkin da yayi yaga kansa cikin wuta yana ta shan azaba ba a dalilin dukiyar da suke wadaka da ita. Abin tamkar gaske ya gani. Mutuwar abokinsa washegarin mafarkin wani wanda yayi gwamna karo biyu sun shiga sun fita ya zama minista shi ya kara tada masa hankali. Gawar abokin nasa bakikkirin kamar an shafa gawayi gashi yaransa suna ta murna harda party ranar da yayi bakwai wai giwa ta fadi. Sosai ya tsorata har baya iya baccin kirki. Uwa uba kuma yaga yadda hukumar kama masu watanda da arzikin kasa su cinye a cikinsu tasa mutane a gaba. Wannan tonon asirin ma na duniya ya ishi bawa mai tsoron Allah.
*******************
Kuka take sosai a daki tunda Baffa ya sanar da ita abinda ke faruwa. Duk gidan al'amarin bai musu dadi ba Mama tana ta mita. Hafsi tayi fushi sosai da Saif da ace wani abu ma ya faru tsakaninsu haka zai fasa auren karshe duk wanda ta aura yaci mata zarafi. Yanzu duk farincikin da take baffa ya yafe mata ashe hoton nan bazai fasa jawo mata sabbin masifu ba kullum.
Ummati ce ta shigo da sallamarta Hafsi ni fa ban gane zancenki ba a waya. Rungume aminiyarta tayi tana kuka tana sake mata bayani. Ummati ta kalleta yanzu shi dan sanatan kin ganshi? Ke wa yake ta tashi ko sunansa ma ban sani ba. Ai kinji dadi Lawal baizo kun yi naku hotunan ba. Wannan hoto bai zo min da komai ba sai sharri. Ummati rarrashinta kawai take tana tuna yadda Allah Yasa ta auna arziki bata riga tayi hoton ba. A da suna wa abin kallon wayewa sai dai yanzu sunyi karatun ta nutsu. Duk wani hani ko umarni a musulunci akwai alkhairi mai kyau a tare da shi.
*******************
Da sassafe Junaid ya tafi asibiti. Sam daren jiya baiyi bacci ba tunda Hajiyan Dangi ta sanar dashi yadda mahaifinsa yayi dasu Baffa. Ya tabbatar ba wani abu Baffan ke tsoro ba sai HIV da sauran dangin cututtukan da ake kamuwa dasu ta wannan hanyoyin.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐19
Kwanaki uku kenan tana binsa yanzu ta gama gano gidan da yayi masauki abinda ya rage mata yadda zata sami damar yi masa abinda bazai taba mantawa ba har abada. Idan ka bari motar nan ta bace mana bazan biyaka ba yau...dreban taxi din ya kara gyara mirror din gaban mota yadda zai ganta da kyau. Mace har mace sai dai babu alamun mutumci a tare da ita. Kallonta yake yana hadiyar yawu saboda irin shigar da tayi ta matse dukkan jikinta ga kamshi kamar wadda tayi wanka da turare. A bakin gate din wani asibiti yayi parking inda yaga motar da suke bi ta shiga. Tafiyarta kamar da gayya don ta tada hankalin maza...a zuciyarsa dan tasi Allah Ya isa yayi mata shi ba aure ba kullum yana yawo da ita a gari.
Junaid ya kara kyau saboda shaye shayen da ya dena yan kwanakin nan. Bayan sun gaisa da likitan ya sanar dashi irin tests din yake so ayi masa wanda suka hada da HIV da hepatitis. Haka ya zauna aka debi jinin yasa kida a kunnensa yana jiran result. Ba karamin farinciki yayi ba ganin komai is negative. Tabba ba kowacce mace yake muamala da ita ba kuma yana amfani da hanyoyin kariya amma dai gaskiya ya tsorata. Ana bashi result dinsa wani tsalle yayi da ihun murna. Yana fita Tilly ta fito daga inda ta boya tabi layin ganin likita. Da kyar da salon bugun ciki taji abinda ya kawo Juni asibitin. Allah Ya kama ka Juni boy sai ka gane baka da wayo a hannuna.
******************
Baffa da Mama sun yanke shawarar Hafsi ta tafi gidan kanwar mama dake aure a Funtua har sai yaji makomar Junaid. Haka ta tafi ba musu ita duk abinda zai sa su manta da laifinta na baya nema take shiyasa suka yi shawara da ummati kan cewa bazata musa musu zancen auren dan senator Rufai ba. taso kwarai taga ko waye Junaid dinnan sai ta hakura ganin iyayenta basa yi mata zancensa.
A gajiye Tilly ta shiga gidan aminiyarta Rosie. To mutanen banza daga ina kike tun safe ba hi ko hello. Harara ta galla mata Ke ni bani abinci kizo muyi magana akwai gist fa. Rosie ta washe baki hala kin samo hanyar bi ta kan wannan shegen dan sanatan? Fadi ki kara Tilly ta amsa tana fari da ido. Yanzu dai cikina is empty.
Wata gyatsa tayi me kara sannan tasa kafa ta ture plate din abincin can gefe. Tana sakace hakori tace Rosie yar mutan Gaya kina ji na. Ni da tun dazu na matsu ki gama cin abincin, to ya akayi? Nan ta bata labarin yadda ta bishi asibiti da test din da yayi. Ni bansan me ya faru dashi ba these days amma naga baya zuwa wuraren shakatawa. Da na yanke shawarar na biya doctor din su fada masa yana da HIV to sai nayi tunanin kada yaje wani ya sake aga negative. Tunda ta fara magana Rosie take dan tunani. Ke banza magana fa nake. Ki fada min yadda zanyi ya aureni mu kwashi namu national cake din. Ai ki kwantar da hankalinki sister. Ki bani two months kawai sai muje gidansu. Two months kuma? Yi min bayani mana. No ki bari idan har naga titin da nake so mubi mai billewa ne zaki ji komai. Ke dai ki cigaba da sa ido don mu tabbatar da inda yake ko yaushe.
*******************
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah. Senator Rufai ya mayarda Alh Bashir wani abokin shawara don har yau Mal Aminu bai gama sakewa dashi ba. Alh Bashir yasha fada masa idan har suka dage zasu iya sawa ya aikata alkhairi a ragowar tenure dinsa. Shi kuwa Junaid a kano ya cigaba da zama wurin Hajiyan Dangi ya rage shaye shaye sosai. Har mamaki yake bai taba ganin Hafsi da idanunsa ba amma sai bin dokoki yake saboda ita kamar wanda aka asirce.
Saura sati uku bikinsa da Hafsi ta dawo kano. Baffa kam sai da yaga result din tests har daga asibitoci biyar ya gamsu tare da bawa Junaid damar yazo ganin Hafsi.
******************
Ba wata kwalliyar kirki tayi ba don ma yayarta Hadiza ta matsa mata ne. A falon gidan Baffa yace su zauna yadda mutane zasu rinka wucewa. Hafsi murmushi tayi daya fadi haka lallai laifi Allah kadai ke yafewa duka amma mutane abu kadan sai yasa su tuna baya. Tun kafin ta daga labulen falon gabanta ke faduwa wanda ta rasa dalilin hakan. Da wannan muryartata mai kamar shagwaba tace Assalamu alaikum. kamar a dauke masa wutar jikinsa Junaid me cika idon yan bariki ya kasa amsa mata. Ido kawai ya bita dashi.....you are so beautiful,so pretty. Kin shigowa tayi ganin yadda ya rude saboda ganinta. Tsoronta daya kada ta shigo ya nemi taba ta. Karaso mana Hafsi ko....ya fada yana daga gira daya. Sunkuyar da kanta tayi kasa baka amsa min sallama ba ai. Dan bata fuska yayi ke da gidanku. Anyway wa alaikum salam. Tana zama ya tashi daga inda yake ya dawo kujerar kusa da ita. Wallahi kin hadu sosai ma kuwa. Can't wait to have you. Gabanta taji ya fadi anya wanan ne Baffa ya aminci ta aura. sai ma a lokacin ta kare masa kallo. Don kyau dai yana da shi amma wani gashi ta gani ya danyi tsini daga tsakiyar kansa ga wani wando me fadi irin wanda black americans na ghetto suke sawa. Rigar jikinsa kuwa itama me fadin ce ta dan sauko masa. Nan take taji ta tsane shi bare da ta kalli wani kwantareren takalminsa. Yanzu fa sai ace duk kayan nan masu tsada ne ko ta fada a zuci.
Ganin yadda take kare masa kallo yasa yayi shiru shima yana dada kallonta. Can daya ji shirun yayi yawa yace yah nayi miki ko? Firgigit ta kalle shi bata fahimci zancen sosai ba kawai sai tace masa a'a. Ya zaro ido me kika ce? Kinsan yadda mata ke rububina kuwa? Ganin ya dauki wata hanyar sai ta katseshi da gaisuwa. Bayan yan mintuna tace zata shiga gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐20
Ke kada ki raina min hankali mana. Ya daga zuwana zaki ce wani zaki shiga gida. Ya kara kankance ido irin na 'yan duniya ko kina son nayi miki irin abinda wanan matsiyacin yayi miki ne a wadannan pictures din? Gyara zama tayi tana kallonshi. Kaddai ace a hotunansu da Saif ya ganta. Tasan ance a hoto ya ganta amma bata da details din abinda ya faru. Da kyar tace wane hoton kake nufi ne. Wata babbar waya da bata taba gani ba ya dauko ya nuna mata hotunan. Gabanta ne ya fadi a tsorace ta mike wallahi ni ba yar iska bace idan ma abinda ya kawo ka kenan. It was my first and it will be my last in sha Allah. Tafi ya rinka yi tana magana eyye! eyye yarinyar ta iya turanci ashe. Kunya taji ta kamata shi kuwa ya cigaba da magana. Kar ki damu fa Juni has done worst amma tunda naga babanki yana pretending kamar ke saint ce ba komai shiyasa ma zan aure ki. Daga nan har muyi aure zanyi kokarin dena kula wasu matan sai ki dage ki koyi jan hankalina. Da wuya ake impressing din Juni. Yana gama magana ya tashi ya good night Hafsi Hafsi. Daga bakin kofa yayi blowing mata kiss. Sai da ya fita taja wani numfashi. Lallai akwai matsala ina ita ina wannan mai zubin 'yan iskan.
*********************
Fuska ba annuri ya shigar mata daki ba ko sallama. Junaidu abin ya motsa ne ka shigo min daki kai tsaye. Dafe kai yayi oh sorry Hajiyata raina ne a bace. Dan murmushi tayi tana nuna masa wurin zama. Zo nan dan Hajiya bani labarin yadda kuka yi da Hafsa. Kara zumburu baki yayi wai don rainin hankali baki ga yadda take min wani irin kallo ba. Hajiyan dangi dariya tayi ya bita da ido me kuma ya faru kike min dariya? Yo dannan banda abinka ji irin shigar da kayi kamar wani tsohon dan tasha. Duk kayan jikinka sunyi maka yawa. Lah Hajiya gayun kenan fa. Black americans hadaddu ai irin shigar nan suke irinsu ice cube, snoop dog, kanye west da....kafin ya kara magana ta daga masa hannu dakata haka. Yanzu don Allah zaka iya kawo min sunayen Annabawa ko Sahabbai goma? Ka rasa wanda zakayi koyi dashi sai makiyan musulunci? Kaji tsoron Allah Junaidu ka gyara rayuwarka. Yanzu dubi wani gashi a kanka kamar juji kuma nasan kana sane ka tara shi. Kana girma kana kara cin kasa. Bakin nan na Junaid kam yayi tsine saboda yadda yake zumburo shi..dan me zaayi masa fada. Sai dai kuma maganar ta dan shige shi. Ya mike zai fita daga dakin Hajiya kiyi hakuri da yardar Allah zaki ga na zama salihin mutum ko, yanzu ma ai kinsan Juni yayi sanyi. Filo ta jefe shi dashi ya gudu don yasan ta tsani Junin nan da ake kiransa.
*******************
To baiwar ciki ina nan ina ta nema miki mafita wurin Juni ke banda ci babu abinda kika iya. Tilly ta hadiye naman da ke bakinta da kyar kin dai sanni tun farkon haduwarmu ina da son abinci musamman idan akwai nama. Rosie ta bata fuska to naji mayya amshi ki karanta wannan. Dafe kirji Tilly tayi me zan gani haka? Aure zaiyi, ai wallahi uban kuturu yayi kadan. Ni fa banda kudinsa shima kansa ina so. Wata takardar Rosie ta mika mata tace to wanan kuma fa. Ci...ci...ci me? Mun shiga uku Rosie ya akayi kika bari ciki ya shige. Rosie ta dakatar da ita tsaya kiji ai cikin nan shine license dinki for now. Ke dai ki saurare ni da kyau kinsan tunda muke bamu taba yin babban kamu irin haka ba dole mu rike wuta.
****************
Nafisa da Hamida sai shirye shirye suke dan uwansu zaiyi aure. Kashe kudi suke kamar babu talauci a nigeria har sai da mommy tayi magana. An hada lefe na gani na fada a cikin gidan daga baya Senator ya yi musu gine mai kyau babu abinda bai saka ba yace a nan zasu zauna har sai yaga kamun ludayin zaman nasu don bai gama yarda da dan nasa ba.
A kano ma su maman Hafsi suna nasu shirin duk da sun san Senator Rufai da iyalinsa ba tsaransu bane amma dai suna gudun gori ace sikau suka kai yarsu.
Ranar karbar lefe tazo dai dai da sati daya kafin biki Hafsi bata sake ganin Junaid ba shima bai neme ta ba don yasan ta kusa shiga hannunsa wannan yatsine yatsinen da take masa dole ta ajiye a gefe.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 21
Yan uwa da abokan arziki sun cika gidan. Yan ganin kwal uwar daka ma suna nan zaune suga irin abinda zaa kawo wa Hafsi.
Akwatuna ne ake ta shigowa dasu gidan har goma sha takwas. Hajiyan Dangi ita ce tayi jagora ta nuna musu kayan. Akwati set biyu guda sha biyu na amarya ne komai na ciki me tsada ne harda set din gwal uku. Sai daya na baffa, na Mama, na 'yan uwanta sai kuma wanda zaa bawa yan uwa da abokan arziki. Dukkansu shake suke da kaya. Ga kudin dinki dubu dari biyu. Wai a haka ma don kada su zake da yawa ne. Ranar bakunan mata sunyi magana har sun gaji kowa da abinda take fada. Mama dai dubu hamsin baffa ya bata na tukwici shima don su fita kunya ne. Wata yayarsa ta kira ta fadawa tare da dora nata dubu goma. Yayar da yake tana da dan rufin asiri ta kawo talatin itama Hadiza ta kawo goma suka cike dari. Hajiyan dangi mace mai kwarjini da kamala tace ko kwandala ba zasu karba ba yar da aka basu ma sun gode. Suna fita aka hau bude buden akwatuna ana kallon yadda ake wasa da kudi a kasar mu.
*******************
Hafsi tasha gyaran jiki sai sheki take ga lalle wanda mai lallen ma Hamida ce ta turo ta har gidansu. Ummati tace Allah Yasa kuyi zaman lafiya naga kamar basu da raina mutane. Haka akayi kamu a wani makeken filin senator wuri ya dauki mutane. Idan kaga Hafsi kamar wata yar tsana saboda mai kwalliyar ma tafiyayya ce. Tayi kyau har ta gaji. Su ummati ma da kannenta baa barsu a baya ba. Itama Batul Mamman sai wani shishshige musu take taga kudi.
Ranar dinner wasu kaya da mama ta kure basira ta dinka Hafsi ta saka. Ummati tana zuge mata zip din rigar Hamida ta shigo da wata riga da skirt na lace ne ko material gashi nan dai abin mai daukar ido golden brown. Tunda aka fara biki ta likewa su ummati sun zama kamar kawaye. Kayan hade suke da takalma da head and veil. Hafsi ta bata rai ni fa wanan zan saka mama ce ta dinka min. Hamida ta marairaice haba matar yaya anko yake son kuyi da kansa ya bayar aka dinka miki. Suka shiga ban baki ita da Ummati amma sam Hafsi taki yarda har zancen yakai kunnen mama. Nan tayi musu sulhu gobe idan zaa kaiki sai kisa nawan zan ga mai hanaki amma yau dai ki saka na angonki. Maman ummati tayi dariya to yar shagwabar Mama gobe dai zanzo da bokitin share hawaye.
Taro yayi taro wuri ya cika da mutanen da suka amsa sunansu a naija. Yan mata anyi dinkunan rashin mutumci suna tafiya kamar sanduna babu lullubi. Matan aure sai hura hanci wai kar a raina su. A mota aka tsayar da hafsi har Junaid ya iso. Ko da ya fito da shaddarsa golden brown bata gane shi ba. Duk da yasa hula ta kula yayi aski, ya gyara fuska gaba daya ya canja. Shima kallonta kawai yake har ya karaso. A kunnenta ya rada mata ni kada ki cinye ne da kallo, it has been three weeks, kin kara kyau kema. Cak ta tsaya saboda yadda yayi kusa da ita. Ana fara musu alamar su shigo cikin hall din taji yana kokarin kama mata hannu. Kokarin fizgewa tayi shi kuwa ya matse hannun ga zobba a hannun har ta fara jin zafi. A hankali tace kaci bashi wallahi. Ya sassauta rikon suka shiga.
Dinner tayi kyau kuma ko liki baayi ba wannan kuma dokar Hajiyan dangi ce. Tilly da aminiyarta Rosie ma sun sami shiga a wurin daukar hoto Junaid ya gansu. Tsoro ne ya kamashi ya hau adduar kada tayi masa wani haukan a wurin don bai ma tsaya tunanin yadda suka sami katin shiga ba. Bayan sun dau hoto ta bashi wani envelop congrats Juni boy. Hafsi ta dan kalle ta Tilly tace amarya mun dai rigaki lasar zumar muna fata tayi miki dadi yadda....junaid ne ya katse ta get out...ba musu ta kama kawarta suka fita don idanunsa sunyi jazur tasan halinsa sarai. Babu wanda ya kula sai Hafsi kowa na shaanisa.
Dreba ne a gaba sai Ummati baya kuma Junaid da Hafsi don ya nace shi zai mayar da ita gida. Tayi kokarin daurewa ta kasa can kasa kasa tace wace wannan matar ne. Dama ransa ya gama baci gashi yana son dena shaye shaye babu ko taba a aljihunsa ya harareta idan zaki bude baki kiyi magana ki bude sai wani kasa kasa kike da murya kamar wata mumina. Ummati ta juyu don taji me yace...zare mata ido yayi ke bana son gulma me kike kallo. Ba shiri ta juyar da kanta. Tooooh wannan ne mijin da Hafsi zata zauna dashi. Hafsi dai shiru tayi tana kallon fuskarsa. Sai tayi da gaske akan wannan mutumin. Abu daya ta sani dai da yana cikin farin ciki kafin yaga wannan matar. Babu ko sallama suna zuwa gida suka fita yace da dreba yaja motar su tafi.
Daki ya shiga hankalinsa a tashe yana tarrabin abinda ke cikin takardar da Tilly ta bashi.
Juni boy
Nasan kana cikin farin cikin auren da zakayi gobe nima ina taya ka murna. Sai dai ina me tabbatar maka gobe zanzo Abuja a tawagar amarya. Ga wedding gift nan.
Luv Tilly
Bude daya takardar yayi gumi ya karyo masa ganin reult ne dake tabbatar da Tilly na da ciki har wata uku.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 22
Ko kayan jikinsa bai canja ba ya fita zuwa hotel din da abokinsa Imran yayi masauki. A waje ya tsaya yayi masa waya. Sai a karo na uku ya dauka ya sanar dashi yana wurin parking ya fito.
Suna hada ido Imi yace yace ya mutumin you sounded worried fa. Me ya faru ne? Envelop din Junaid ya mika masa. Imi ya rinka dariya bayan ya karanta harda hawaye a idonsa. Can ya daki kafadar junaid...haba mutumina kada ka bada ni mana. Yanzu har akwai wata chick da zata ce kayi mata ciki ka yarda? Matan nan fa sun fi mu tsoron faruwar hakan tunda su ke da wahala. Wani abin kawai take so. Fuskar Junaid babu sauran kwanciyar hankali uhm uhm Imi aure fa zanyi kuma Allah Ya sani ina son yarinyar ina kuma son gyara rayuwata. Kaima Allah Ya baka tagari. Kayya yaro gigin soyayya ke dibanka bari romon ya kare zaka neme ni ne. Bayan ina kallo dazu amaryar taka ta murguda maka baki. Kansa ya shafa yana dariya da irin tsokanar fada ne yaga tana kulashi shiyasa yake mata haka a fili yace Kai kam kamar ana kada maka gangar shaidanu..ya ina cewa zan shiryu kana min mugun baki. To yi hakuri na Hafsa Imi ya fada yana dariya...yanzu dai ka manta da wannan yarinyar kada ma ka sata a rai. Idan ta sake nemanka kaci ubanta da kyau wallahi zata kyaleka. Kada ma ka fara bata kudi don sai tayi blackmailing dinka. Nan suka yi ta shawara sai wurin ukun dare Junaid ya koma gida.
******************
Bacci sam yaki zuwa idanun Hafsi sai tunani take kala kala. Wannan Junaid din dabiunsa na bata tsoro( wai ma don ya rage!) Gashi haka hankalinta bai kwanta da matar da ta bashi envelop ba. Maganar Tilly duk ta tsaya mata a rai wai sun rigata lasar zumar.....ehew abin kyankyami ma zancen ta fada a fili tana yamutsa fuska. Anya ba yan is...sai tayi shiru zargi babu kyau don haka mafitar ta daya shine ta mike ta dauro alwala ta tayar da sallah. Haka tayi ta nafila har asuba tana addua sannan ta yi bacci.
Sai wuraren goma na safe ta farka. Shima Hadiza ce ta tasheta da dundu...to kasa ana shirin fita daurin aure kina kwance kina bacci hankali kwance. Mutssika idanu tayi ta mike...ina ummati ta tafi Yaya? Debo miki ruwan zafi kiyi wanka. Kinsan dai baffa yace karfe biyu zaa bar kano so kiyi da jiki kafin a dawo daga daurin aure. Ta kalli agogon wayarta...Allah sarki nan da mintuna arbain da bakwai kin zama matar aure. Cikinta taji yace kulululu da gaske abin yazo. Kuka tasa wa Hadiza inama basuyi wadannan hotunan ba tun kafin aure da yanzu Saif ta aura. Ummati ta ajiye bokitin hannunta ki gode Allah baa daura dashi ba don yadda aka ce Junaid yayi bayan yaga hotonki da kila a gidan auren zai biyo ki ko ma ya kashe auren. Hadiza tace kyale ta ummati ai tasan wani baya auren matar da ba tasa ba.
Kayan da mama ta dinka da aka hanata sawa daren jiya su tasa ai kuwa tayi kyau sosai. Katon mayafi ta yafa ga kamshi ko ta ina.
Taro yayi taro don manyan mutane na kusa da nesa sunzo bikin dan manya. Junaid yasha cream shadda harda babbar riga da brown din takalmi da hula maroka suna ta sanaar su. Daga karshe dai Liman ya daura auren Junaid Rufai Bukar da Hafsa Aminu Garba.
Mijin Hadiza ne ya bugu ya sanar da ita an daura auren kan sadaki dubu dari gida ya cika da guda da hayaniya. Wata 'yar makarantarsu tace gaskiya Hafsa Aminu kinyi saa muma Allah Yasa mu a danshinku. Yan Amin kuwa suka amsa.
Ansha koke koke lokacin dasu Hajiyan dangi suka zo daukar amarya. Mama kasa daurewa tayi ta kulle kanta a daki. Baffa ma yana mata nasiha yana sharar kwalla. Bai taba tunanin zata yi auren nesa ba, aure ma irin na gidan Senator Rufai Bukar. Motoci har wajen layinsu Hafsi. Cikin motocin kuwa harda wadda Rosie da Tilly suka dauko haya suka bi ayarin kai amarya. Don karfin hali har mutane uku suka dauka aka dauki hanyar abuja.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 24
Dakata Imi zanyi maganinta da kaina. Cheque ya bata na dubu dari biyu. Idan na sake ganinki duk abinda ya faru dake ki kuka da kanki. Suna jan mota ta fita ta tari taxi don yau Rosie bata biyo ta ba saboda laulayi daya fara damunta. Murna take sosai don wannan cheque din sabon makami ne a gareta.
Daki aka bawa Hafsi da kawarta sauran yan biki suna wani masaukin. Nafisa ta tafi da yayarta Hadiza gidanta ita kuwa Hamida ta nace tare zasu kwana da amarya kafin washegari a kaita side dinta.
******************
Wani sabon kukan Hafsi da Ummati suka dasa lokacin da aka fito rakasu bakin motocin da zasu mayar dasu kano. Yanzu haka zata zauna da mutanen da bata gama sanin halinsu ba. Ga uban gayyar wato Junaid ko doriyarsa bata sake ji ba tun a wurin dinner. Kamar yasan tunaninsa take sai gashi ya fito da kananan kaya a jikinsa. Yau ma yayi kyau tunda kayan ba oversize bane. Har kasa ya durkusa ya gaishe da gwaggwaninta dasu Maman Ummati. Hadiza ta rungumota tana ta bata baki akan ta dena kuka haka. Kyaleta Hadiza na gulma ne fa kuna tafiya zata sake. Harararsa tayi yace ai gara ki nuna musu halin da kike min. Hajiyan dangi ta kama hannun Hafsi rabu dasu zan miki maganinsu. Anisa ta Amira ma sunyi nasu kukan da alkawarin zuwa idan anyi hutu. Haka dai suka rabu abin tausayi ana janye Hafsi daga jikin Ummati.
Bayan duk sun tafi aka dawo falo. Hajiya da mommy suka yi musu nasihohi da fatan alkhairi. Nafisa da Hamida suna gefen amarya suna kula da masu dada share wurin kafin su kaita. Sai da aka gama fadan Junaid yace to Allah Ya saka da alkhairi amma yaushe zaku bani matata? Mommy ta cire takalminta ta jefa masa to tsohon mara kunya ai gara ka nuna hali. Ya dafe kai Hajiyan dangi tana duba masa...yauwa Hajiya duba ki gani ko kan ya fashe. Hafsi kuwa dariya tayi har sauti ya fito yace kinci bashi Hafsi Hafsi. Nan suka zauna ana ta raha sai kawai suka ji sallama.
Mata ne biyu sunsha hijab daya sai kuka take dayar tana bata hakuri. Dif Junaid yayi ya dena dariyar da yake saboda ya gane mai muryar. Zuciyarsa ke bugun uku uku yaji yawon bakinsa ya kafe. Itama Hafsi ta gane yarinyar ko baa fada ba tasan akwai matsala don ta kula da yadda ya kidime da ganinsu. A fusace ya kallesu ubanwa yace ku shigo har nan? Wai ma waye ya baku izinin shigowa.
Mommy da Hajiya cikin rashin fahimta suke kallonsa. Junaid kana hauka ne zaka ga baki kayi musu irin wannan tarbar? Rosie ta kiyi hakuri Talatu an gama cutarki shine zaa ci mutumcinki saboda baki da galihu. Mommy tace ku zauna muji abinda ya kawo ku. Tilly harda fyace majina ai yafi kowa sanin dalilin zuwanmu. Idanun Junaid kamar an bada masa yaji yayi kanta yana sirfa mata zagi.
Kana tabata zansa a kulleka mara mutumci kawai. Daga kai yayi suka hada ido da Senator Rufai. Alhaji wai me ke faruwa ne? Yace ku zauna muyi magana. Su Rosie aka wani rakube a kasan carfet ita da Tilly. A bakin gate na gansu suna fada da security yarinyar can ya nuna Tilly tana ta kuka. Ganin haka na tsaya aka kirasu tayi min bayani. Cheque ya dauko daga aljihunsa ta mikawa Mommy. Kingani kudin daya bata jiya wai taje a zubar mata da ciki. Kinga goshinta inda ya fashe lokacin da yake dukanta ta fadi. Kamar anyi masa wanka da ruwan zafi haka yake ji. Me tilly ke nema ne a tare dashi? Kokari yake su hada ido da Hafsi ita kuwa idonta na kasa tana kuka a hankali. Salati su Hajiya suka hau yi tace lalacewar taka har ta kai ka bada kudin yin kisa. Kuka ne ya kwace musu ita da Mommy. Junaid yana ta basu hakuri. Hafsi ta mike zata shige daki don taga zancen kamar ba nata bane. Dawo dawo ai gara kada a munafunce ki Hafsa. Senator ne ya kirata ta dawo ba musu. Ya maida kallonsa ga Junaid. Ka san yarinyar nan? Eh na santa amma wallahi ban dake ta ba. Rufa min baki shashasha. Kullum yadda zaka zubar min da mutumci yake nema. Ko tsoron mutuwa baka yi.
Ke ya daka ma Tilly tsawa ta dago a firgice garin yaya kika amince masa. Ta kara jan majina ta fara bada labari. Ni ina sayar da kati ne kusa da wani club da suke zuwa a gidan wannan yayartawa nake da zama shine ya biyoni wai yana sona. Rannan rannan sai kuka....Rosie tace kudin kati yace taje ta karba shine yayi mata fyade. To ganin cewa danka ne bamu daga zancen ba.
Wallahi Álhaji karya suke duk karuwai ne....bakinsa yaji Hajiya ta make. Rufa mana baki. Rosie ta cigaba to da mun hakura sai kuma ga ciki shine muka neme shi kawai jiya sai yazo har gida ya bata cheque ita kuma ta karba don taga bana nan.
Hafsi tayi saurin daga kai tace ba kece kika zo wurin dinner ba kuwa daren jiya? Junaid yace yauwa Alhaji wallahi kaga itama zata min sheda wurin dinner ta biyoni ba raping dinta nayi ba. Mommu tace Hafsa kada ma ki fara kare masa don bakisan waye Junaid ba. Duk abinda akace yayi zan yarda. Allah wadaran iskanci yau mahaifiyarsa ma taki yarda dashi.
Senato Rufai ya kalli dansa cikin bacin rai yace ka taba ganinta? Eh ya amsa masa. Muamala ta shiga tsakaninku? Shiru ya kasa magana. Ya daka masa tsawa kai kurma ne. Hawayen da yake boyewa ya sauko yace eh. Innalillihi wa inna ilaihi rajiun. Koda ba auren so suka yi ba amma ace mijinka yana neman mata akwai ciwo. Hafsi duk auren ya kara fice mata a kai. Senator yace to ke zaa kaiki asibiti a sake miki gwaji idan ya tabbata da gaske yayi wa Junaid wani mugun kallo zamu jira ta haihu a aura maka ita. Mikewa yayi a fusace su Hajiya suka bi bayansa.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐23
Tunda suka hau hanya basu tsaya ba sai a garin Abuja. Motar da Baffa ya hado da kayan da yayi wa 'yarsa ita ce ta karshe cikin jerin motocin.
Duk girman gidan ba duka motocin bane suka sami shiga ba saboda yawansu. Shima gidan cike yake da mutane gashi basu iso da wuri ba. Dakin mommy su Hamida suka kai Hafsi. Ita dai kanta a kasa taki dagowa ta kallesu. Mommy cike da murna tace nasan kun gaji ga magriba ta kawo kai a kai su masauki suyi wanka aci abinci sai su shirya akwai wata dinner din karfe takwas. Hafsi ta kankame hannun ummati sai Nafisa tace mommy wanan fa aminiyarta ce tare zasu zauna kafin anjima ta dan kanne ido ai sai kamarsu ta Junaid ta kara fitowa Hafsi tayi saurin dauke ido.
Suna idar da sallar magriba akace Hafsi ta shiga wanka. Komai na toilet din daban yake...oh su Hafsi a toilet din matar sanata. Tana fitowa Hajiyan dangi ta tarar suna hira da mommy sai ta kasa fitowa. Hadiza da Nafisa wadanda tuni jininsu ya hadu kamar sun dade tare suka fara mata dariya. To yan nema da girmanku kuna tsokanarta ko. Fito kinji Mamana ni da nake so nan da yan watanni nazo yi miki wankan jego. Ai Hafsi ji tayi kamar ta nutse a kasa Mommy tace Hajiya banda kwacen 'ya fa. Fita suka yi aka hau shirin amarya. Kwalliyar yau tafi ta sauran events din. Suna gamawa kowacce ta dau ado jiki da fuska aka fito. Motar da tafi kowacce kyau daga tsakiya wani abokin Junaid ya bude mata kofa ta shiga ya rufe. Taso kwarai Ummati ta shigo sai kawai taga angon nata ya bude kofa ya shigo. Ko tari bata yi ba don ganin yadda yake mata wani irin kallo. Ganin abin yayi yawa tace ya dai? Kamar ya, ya bata amsa. Ta dan turo baki kallo dai idan yayi yawa kuma zai shiga babin haramun. Yayi yar dariya Hafsi Hafsi kenan malaman karya. Wa ya fada miki kallon miji ga matarsa yana ciki. Yadda tayi da bakinta yasan sarai murguda masa shi zata yi. Yarinyar nan akwai tsiwa. Yace to basai kin murguda min baki ba idan kina son kiss, you just need to ask. Sakin baki tayi tana kallonsa lallai ma mutumin nan..dole ta fasa ta kara hararsa. Yayi dariya sannan yace karamar mara kunya kawai.Hular kansa yasa ya rufe fuskarsa. Idan mun isa ki tasheni jiya banyi baccin kirki ba. Ko kula shi bata yi ba ta juyu tana kallon garin da bata taba tunanin zuwansa ba nan kusa.
Nicon Hilton suka shiga. Manyan mutane da dama sun halarci taron. Su mommy ma da sauran matan manya sunzo amma shadaya suka koma gida. Sai wurin shabiyu da kwata mommy tayi wa Junaid waya kan su taho gida haka saboda Hafsi da suka yi zaman mota.
Ummati da Hafsi suna ta hira kafin motar da zasu shiga su karaso gabansu idon Hafsi yakai kanta. Tabbas matar da tazo wurin dinner dinsu ta kano ce. Matsowa tayi gaban Hafsi tana tafiya duk jikinta na girgiza amarya mun sake haduwa ko. Ga naki gift din nasan Juni boy da rowa baiyi sharing nashi dake ba. Wai wacece matar nan ne ta tambayi kanta? Tana mika hannu zata karba Junaid ya doke hannun. Da bomb ne ma haka zaki karba ko ya fada yana zare mata idanu. Mota na tsayawa yaja hannunta ya tura ta ya kalli ummati kema shiga zan biyo abokina. Yana rufe musu motar kafin su fara tafiya Hafsi taji yace cikin daga murya what the hell do you want? Suna tafiya a zuciyarta Hafsi ta kara yarda akwai wata a kasa tsakanin Junaid da yarinyar nan.
Ka zama uba ga abinda ke cikina. Ka rabani da rayuwar da nake ciki. Maana ka aureni. wadannan ne amsoshin da Tilly ta bawa Junaid. Imi dake ta yiwa Junaid horn ya shigo su tafi ya fito daga mota ganin yadda abokin nasa ya rude.
Ya mutumina wannan ce akuyar dake neman daga maka hankali? Ai ka barni da ita na farfasa mata jiki kawai. Yana magana ne yana kokarin dauko wani katon dutse cikin wadanda akayiwa wurin ado dasu. Imi baya daukar raini shiyasa Junaid ya tabbatar yana daukan dutsen nan jikin Tilly zai dire shi.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐25
Rigar jikin Junaid ta gama jikewa da gumi saboda tashin hankali. Yana ganin iyayensa sun shige yayo kansu ita da Rosie sam ya manta da Hafsi a falon. Ke don ubanki me kike nema ne a tare dani? Idan ciki ne dake ki sa a ranki har abada Junaid bazai taba zama uba ga abinda ke cikinki ba.
Hafsi tana jin furucinsa ta nemi hanyar barin falon rasa wurin shiga tayi don bazata bi su mommy ba a wannan yanayin da suka tashi. tana turo kofar dakin da take tsammani ma na masu aiki ne taji yo Tilly tana dariya...haba Juni boy ai kowa yaci tuwo dani miya ya sha. Ni ka zane a lagos daga na fadi abinda baiyi ma dadi ba. Rosie ta dan dake ta to banza rage muryarki. Ta maida kallonta ga Junaid ai kai karamin dan iska ne don giyar kudi ce ta kaika tashar iskanci mu kowa, ta nuna kanta da Tilly wahalar rayuwa ce ta kawo mu kaga dole mu fika rashin imani. Tsayawa yayi ya rasa yadda zaiyi dasu. Ya juya ya fita daga falon tare da buga kofa da karfi har sai da gaban Hafsi ya fadi.
Masu aiki ya tarar a barin nashi ya ma manta wai shara akeyi da sauran gyare gyare. Get out ya fada cikin karaji har su Nafisa suka fito daga ciki ita da Hamida. Sauri tayi ta dafa masa kafada Junaid what is wrong? Ban sani ba wannan karon hawaye yake sosai. Ku fita wallahi ko wani yaji ciwo. Ba shiri duk suka yi waje shi kuma ya shiga sabon bed room dinsa. Bai taba tunanin first day dinshi da Hafsi zai zo masa a haka ba. Tsakani da Allah yake sonta don a yadda ya tsara ma kansa ma bashi da niyyar takura mata. A hankali zai bita ya koya mata sonshi don yasan yanzu baya gabanta. Gashi yar tsiwarta da fadan da suke suna burge shi. Drawers ya rinka budewa kamar mahaukaci yana neman kayan maye ko yaya ya gusar masa da hankali ya manta da bacin ransa.
Wata taba dogowa ya dauko wacce Imran ya kawo masa tsaraba daga Italy. Kujera ya hau ya rufe idanunsa. Yana kunnawa yaji an fizge ta daga bakinsa yayi saurin bude ido. Hajiyan dangi ce tsaye kansa fuskarta jike da hawaye. Haba dan albarka. Yanzu ashe akwai wani maganin bakin cikin rayuwa bayan ambaton Allah da karatun Quran ko sallah? Ashe duk abinda ake fada maka bayan kunne yake bi. Bakin gado ta zauna dora kansa a kan cinyarta ya saki kukan da yake ta kokarin boyewa. Kyale shi tayi yayi mai isarsa har yayi shiru don kansa. Bai tashi daga kan cinyarsa ba yace Hajiya sai da nake son na canja halayyata kuma sai wannan masifar ta taso min? Kul ta ce masa tana girgiza masa kai. Allah sarki ne mai dinbin rahma da jinkai ga bayinSa. Shekararka nawa kana saba masa Yana hakuri da kai? Meye baka sha ba da aikin neman mata duk sai yanzu don Ya jarrabe ka kake neman kara fadawa ga halaka. Shin ka sani ma ko silar shiga aljanna ce wannan jarabawar? Dago kansa yayi yana kallonta. Hajiya wallahi yarinyar nan karuwa ce. Na rantse miki da Allah ita ta fara nema na a club. Abinda ta fada duk karya ne ya dan sunkuyar da kansa maganar cikin dai bazan karyata ba kila da gaske ne.
Kayi hakuri ka daure kaci jarabawar nan. To Hajiya zancen Hafsa fa? Ya zanyi da ita idan taki ni. Murmushi Hajiya tayi ,kasa Allah a ranka yarona komai zaizo da sauki. Hafsa tayi min yanayi da mutanen kirki idan ka nuna mata kai mutumin kirki ne sai kaga Allah Yasa ta zauna da kai lafiya.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐26
Neman Hafsi aka rinka yi a cikin gidan an rasa ina ta shiga. Mommy sai kuka take ko don taji zancen ciki ne ta gudu. Wata mai aiki mai suna Amaka ce ta tafi bakin gate ta tambayi securities din wurin ko sunga fitarta. Kusan awa biyu ana abu daya har Hajiyan dangi da Junaid suka shigo gidan don ta matsa masa akan yazo ya nemi gafarar iyayensa. Ganin gidan a hargitse Hajiya tace Salma me ya faru ne haka. Mommy cikin kuka tace bamu ga Hafsa ba Hajiya. Kinga har babansu ya fito nemanta.
Tunda akace Hafsi ake nema Junaid ya dena gane me ake fada. Na shiga uku Mommy ta gudu. Tilly da Rosie dake zaune a gefe ko a jikinsu. Ya nufo su cikin tsananin fushi ku sa a ranku indai banga matata ba wallahi kun gama ganin farinciki a duniya. Banzaye Matsiyata, karuwai....kafin ya kara magana Amaka mai girki ta fito daga dakinta da gudu. Madam amariya dey for my room. Bangaje ta Junaid yayi ya shige dakin. A daidai lokacin Senator ya fito yana waya da IG na police kan a baza masu nemanta. Me zai fadawa Mal Aminu? Duk kudinsa mutumin kwarjini yake masa sosai.
A kwance ya sameta kan gado tana ta rawar sanyi. Hafsi me ya faru ya fada yana shirin taba ta. Doke masa hannu tayi da kyar don wani zazzabi ne ya kamata sosai bayan tayi kuka mai isarta. Zuciyarta a cushe take da tsananin bakinciki. Badon abinda tayi ba tun kafin tayi aure tasan Allah bazai hadata aure da mazinaci ba.(don ma bata san yayi shaye shaye ba).
Ganin yadda ta hade fuska ga wasu hawayen sun taro a jajayen idanunta. Kasa ya sunkuyar da kansa kiyi hakuri Hafsi ki bari na taimaka miki ki tashi naga kamar ba kya jindadi. Harararsa tayi tayi tsaki a hankali zata mike. Ke ba kya gajiya da harare harare ne , wata rana sai na tsire miki ido. Duk da suna tare da damuwa da bacin rai amma sai da duk sukayi murmushi. Nafisa ce ta fara shigowa sannan su Mommy suka biyo baya. Hajiya tace mamana duk kin samu cikin damuwa tun dazu ana nemanki. Sai a lokacin suka kula da idanunta. Mommy ta zauna a bakin gadon. Kiyi hakuri yata nasan duk abinda zan fada zakiyi tunanin ko don bani na haifeki ba. Hafsi ta share hawaye ba haka bane mommy. Hamida tace wai ni me ya faru ne shi yazo yana mana fada dazu mun shigo kuma ance ana neman ta.
Babu wanda ya bata amsa. Mommy da kanta ta taimaka wa Hafsi ta tashi. Zazzabi ne a jikinki ko? A'a kaina ne kawai kuma zai dena idan nasha magani. Mommy tace ku zama shaida idan har yarinyar nan tace bazata zauna da Junaid ba sai an raba aurensu. Hajiyan dangi zancen bai mata dadi ba ta kama hannun danta. Muje Allah Ya kyauta.
Kwanaki uku bayan zuwan su Tilly jikin Hafsi ya warware sosai ga kulawar da take samu daga wurin iyayen Junaid. Hajiyan dangi taso komawa kano amma dole ta zauna har a shawo kan matsalar data kunno kai gidan. Su Nafisa kuwa kowacce ta koma gidan mijinta. Kirikiri aka hana Junaid ganin Hafsi gaba daya gidan ya masa zafi. Addua da yawan sallah yanzu kamar sabon limami don tsoronsa baya wuce a raba shi da Hafsi.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐28
Fizgo ta yayi har jikinsu yana haduwa da juna. Bata yi attempting ta gudu ba ta dai ki yarda su hada ido. Thank you kawai ya ce mata a daidai kunnenta a hankali ya fice daga dakin. Tunane tunane ta rinka yi barkatai game da feelings dinta akan mijin nata. Karshe dai ta tabbatar tausayinsa kawai take ji. Sai kuma ta koma tunanin yadda zata yi da su Tilly. Ita dai bazata je tace karya suke ba kanta tsaye don tsoronsu ma take ji. Dadin abin ma tunda suka kawo kansu gidan ai sun san abinda suka taka. Ita a wa taje ta karyata su ace garin yaya ta sani. Da kunya aji amarya tana labe.
Tana ta tufka da warawara ita kadai har Hajiyan dangi ta dawo. Bayan sun gaisa tace kiyi hakuri na barki aikin jira ko. Ba komai Hajiya. Flask din kunun ta kalla au ina Junaidu? A nan na barshi fa zai sha kunu. Ya sha ya fita inji Hafsi. Kan wata kujera ta zauna tace Hafsatu. Naam ta amsa. Kin sanar da iyayenki abinda ya faru kuwa? A tsorace ta dago ido. Wallahi ban fadawa kowa ba. A'ah kwantar da hankalinki ai tambayarki nayi. Munyi shawara da su Rufai ne yace zaije har kanon ya sami babanki ya sanar dashi. Domin idan akwai cikin nan dole mu tsaya yarinyar ta haihu mu karbi dan. Gashi ma dai ana tunanin gara suyi aure saboda gori a nan gaba. Ko kadan ba haka muka so ba amma bazamu yi wata barnar ba don mu boye wata. Idan har kinsan bazaki iya zama da Junaid ba a haka kada kiji kunyar sanar dani. Ta dan gyara zama. Nasan iyayenki ma bazasu taba yarda ba. Kuma bazanga laifinsu ba ko nice abinda zanyi kenan.
Duk maganganun da Hajiya take Hafsi ta gane so suke suji ko zata bukaci a raba aure. Ko kadan bata so iyayenta ma su san maganar. Ai idan auren ya mutu wani kashin kazar zata shafa wa kanta. Dama ummati ta fada mata a groups din whatsapp babu irin abinda baa fada a kansu. Da masu zagi da masu kiranta karuwa ma. Ai auren rufin asiri ne gareta sosai. Dan murmushi tayi cikin kunya tace Hajiya in sha Allah zan zauna.
Har ranta taji dadi kuma tayi mamakin saurin amincewar Hafsi. Allah Yayi miki albarka Ya baku rayuwa mai albarka duniya da lahira. Ta kama hannayen Hafsi ta rike. Mungode sosai kuma zan kara jan kunnensa aka neman lahira da gudun duniya. Har hawaye Hajiya tayi tace bari na tashi na sanar da su Salma don su kunyarki ma suke ji. Baki ga baban naku bai neme ki ba. Yace bai san yadda zaiyi ya kalleki bane.
Ranar da Hafsi ta cika sati su Nafisa suka zo gidan zasu yini. Hira suke sosai da Hafsi kamar sun dade da sanin juna. Suna nan zaune Junaid ya shigo dakin. Rabon da su hadu tun a dakin Hajiyan dangi. Wata doguwar riga ce fitted a jikinta kanta ba dankwali Nabilan Nafisa tana ta jagwalgwala mata kai wai zata mata kitso. Yana yin sallama tayi saurin sunkuyar da kanta. Sis ina ta nemanku ance min kunzo sai Amaka ce tace kuna nan. Hamida ta ce ai yanzu mu Hafsi ce yar uwarmu. Ka zama dan karo ko Yaya? Nafisa tace Hafsi baki gaishe shi ba. Kafin ta amsa yace kyaleta bashi take ci. Nabilatu na kice kike ja min kan mata haka ko? Ku kuma duk kun kyaleta sai ta tsige mata gashi. Dariya duk suka yi kaji mai mata donma kayi saa tana mata gyaran gashi. Yace nasan dai kara kike musu to baa yiwa dangin miji haka sai su raina ki. Filo nafisa ta jefa masa. Sannu kanwa uwar hadi tun yanzu zaka fara nuna hali. Ke Hamida dauko min 'yata mu tafi kai kuma ka zauna ka gyara mata. Nabila sai ihu take da Hamida ta dauko ta...ni kichu kichu anti. Tanayi tana dukan Hamida.
Sai a lokacin tayi magana. Don Allah Hamida ku kyaleta. Ganin basu saurareta ba ta dauki hijab dinta zata bisu. Kafin ta gama sun fice harda rufo kofa.
Suna fita harda tafawa. Bawan Allah Ya Junaid duk ya zama abin tausayi. Kiri kiri anki kai masa matarsa gidansa. Nafisa tace nasan fushi su Mommy suka yi amma ai zasu bari ta koma. Ko ba komai yanzu da kudi Junaid bazai kara bin wasu matan ba a waje. Abinda ya wuce kuma Allah Ya yafe mana baki daya. Amin Ya Allah.
Batul Mamman💖
.TUN KAFIN AURE💐27
Hajiyan dangi ce kadai ke shiga sabgar Junaid. Shiyasa kullum yana dakinta. Hafsi kuwa dakin da aka bata kusa da na Mommy ne ko fita bata yi. Ranar laraba tana zaune a daki duk shirun ya isheta ta fito zata dakin Hajiyan dangi don yau bata leko sun gaisa ba. A bakin bene suka hadu Hajiya tace ina zuwa mamana? Ta dan sunkuyar da kai, dama gaisheki zanzo yi. Tayi mata murmushi to bazan amsa gaisuwar a nan ba. Karasa dakin ina zuwa. Zanje wurin babanku ne muyi magana.
Ba musu ta karasa sauka. Sai dai kuma bata san ina ne dakin Hajiyar ba gashi ba damar ta koma sama ta tambaya. Wani corridor tabi tana tafiya sai ta jiyo maganganu daga dakin. Babu shakka wadannan matan ne ke maganar. Kamar ta wuce sai ta tsaya daf da kofar. Daga ciki ta jiyo daya daga cikinsu tana magana da fada fada...kai banza so nake kawai kayi karyar kaine babana. Ka sami wasu da zaku zame min iyaye. Wallahi babbar harka zan baro mana idan kuka yi kuskure kuma Allah kashimu ne zai bushe. Sai wata tace ke komai akayi dake sai kinyi hauka ki rage muryarki mana. Wannan karon sai da Hafsi ta hada kunnenta da kofar take jin me ake fada.
Bayan dayar ta gama wayar tace ni yanzu Rosie ya zanyi idan suka kaimu asibitin ayi min test. Gashi kece mai cikin bani ba.
Hasbunnallahu wa niimal wakil. Ashe karya suke babu wani ciki. Bata san dalili ba amma har ranta taji dadin wannan zancen. Rosie tace kada ki damu Tilly nasan yadda zamuyi da komai. Ke dai idan kika yi kokarin yaudarata idan kika shigo gidannan sai na koya miki hankali, itama wannan matsiyaciyar amaryar tasa sai nasan yadda nayi aka saketa ko ta nemi sakin da kanta. Ni bani maganin nan na kara sha naji cikina ya fara ciwo ciwo. Gara shegen yayi ya bare kowa ya huta. Tilly ta kalleta ki hakura ki haifeshi ni yanzu da ko shege ne ina so. Ai tunda likitan nan yace mahaifata ta lalace nake jin son haihuwa. Rosie ta tabe baki...wanan dai sai suck away in kin matsu kije gidan marayu.
A sanyaye Hafsi ta cigaba da tafiya. Wata mai aiki ta gani ta tambayeta dakin Hajiya ta nuna mata. Tana shiga ta tarar dashi zaune kan carfet yana shan wani abu a cup. Ganin tayi turus ita bata shigo ba ita bata fita ba yayi dan murmushi mai cike da bakin ciki. Hafsi Hafsi ko na fita ne don ki sami sakewa? Dan kwarin gwiwa da samu data tuna cikin ba nasa bane ta shigo. Ina kwana ta fada tana dan durkusawa. Ajiye kofin yayi yana kallonta cike da mamaki. Hala ta manta abinda ya faru a kwanakin da suka wuce. Kai fa ka fiye kallo kuma na fada maka babu kyau. To ranki ya dade na dena daga yau. Rufe idanunsa yayi ya dauki cup din kununsa ya cigaba da sha. Jin wani daddadan kamshi kusa dashi yasa ya bude idon. Hafsi ce zaune a kasa kusa dashi. Tayi yar ajiyar zuciya. Junaid, bata taba kiran sunansa ba sai yau shiyasa yaji wani dadi. Sai ya wayance. Ke mijin naki kike kira haka ba ko yar alkunya irin na matan hausawa. Komai bacin rai baya rabo da wasa. Kafin tayi magana yace kina hararata fa zan...sai ya kashe mata ido daya tsire miki ido zanyi. Ai kayi kama da mugaye dama. Ya mike tsaye ni din? Ashe baki da ta ido yar nan. Yadda ya rike haba yasa tayi dariya. Duk da yana tare da damuwa ya koyawa kansa hakuri. Har yana tsokanarta. Wani serious look ta gani a tare dashi. Yace Hafsi Hafsi why are u being nice to me? Ta dan kalle shi, saboda i believe you. Bangane ba ya fada cikin rashin fahimta. Bazan miki karya ba nasan Tilly kuma cikin jikinta maybe nawa ne. Na sani ta bashi amsa. Na dai yarda ba...ba raping dinta kayi ba. Tana gama magana ta mike zata gudu.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐29
Hannun kofar ta kama amma saboda yadda take hanzarin fita sai ta kasa budewa. Hijab din ma saboda karar jan kofar da Nafisa tayi a baibai ta saka shi. Duk abinda take idanunta na kansa don tsoro take kada ya karaso inda take. Wani irin kallo ya rinka yi mata ko kifta ido baya son yi. A hankali taga yana matsowa inda take. Cikinta har wani sauti yake bayarwa saboda yadda ta kideme. Da kyar ta iya cewa nifa bana son kallo. Bai dakata ba da tafiyar sai da yazo gabanta. Da zaa taba kirjinta sai anji bugun zuciyarta da sauri da sauri. hannunta ya kama ya jawota ciki ya zaunar da ita kan kujerar gaban dressing mirror. Ji yadda jikinki ke bari kamar kinga wani dodo ko irin kinzo yi min sata na kama ki. Yadda yake maganar ne ya sata dan guntun murmushin yake. Shiru tayi tana tsoron kada Hajiya ko Mommy wani cikinsu ya shigo dakin tunda suna shigowar kullum. Ganin yana neman cire mata hijab ta fara kokawar rikewa. Ya kalleta ya sha kunu wai ni da jikina ki rinka rufe min. sai anyi magana ki rinka wani abu kamar wata malama. Ta zumburo masa baki, to yanzu me kake so ayi. Da faraarsa yace ki cire na gyara miki gashinki ko baki ji me Sis ta fada ba. Tayi masa fari da ido ai da ka sani salon ka bude sai ka rinka gyaran gashi. Gaba daya ta ruda shi da yadda tayi masa fari da ido har ya kasa magana. Tana ta surutu ita daya sai gani tayi yana kici kicin cire mata hijab. Ihu ta fara masa wallahi idan ka matso zan bude murya. Ganin duk a tsorace take yayi dariya duk wanda ya shigo taimakonki sai ya tayani cire miki hijab din, bari ma na kulle kofar kinsan leke dakin newly weds hatsari ne. Yana zuwa bakin kofar duk cikinta ya gama durar ruwa sai kawai taga zai fita daga dakin...take care Hafsi Hafsi. Murmushi ta sami kanta da yi bayan ya kulle kofar ta fada gado ta kwanta.
Hajiyan dangi suka gani a dakin Mommy suna ta hira. Suna zama Mommy tace dama jira nake ki fito Nafisa. Lafiya dai ko Mommy? Ta tambayeta. Eh to wannan makociyar taki nurse nake son ki kira tazo gida tayiwa yarinyar can test a tabbatar da cikin. Hamida tace Mommy ana yin scanning fa dashi ake fadar EDD. Nafisa ta buge mata baki to banza wa ya fada miki we are intrested muji lokacin haihuwar. Hajiya tace kunga ni ku nutsu idan kinje gida ki fada mata ko zuwa gobe ne sai kuzo tare. Amma abinda Hamida ta fada gaskiya ne. Idan anyi mata gwajin sai ayi scaning din. Nafisa ta mike bari naje na fada musu don su zauna cikin shiri.
Hafsi tana fitowa zata dakin Mommy ta ga Nafisa tana dawowa daga dakinsu Tilly. Hannunta Nafisa taja suka shiga wani karamin falo. Suna zama Nafisa ta ce Hafsi what do you think of Junaid? Kasa ta sunkuyar da kanta. Tana jin nauyin Nafisa sosai don ma ita din tana da wayewa ta iya jan mutane a jiki. Ta dan taba ma Hafsi kafada ina jinki kanwata. Jin ta sake yin shiru tace nasan Junaid ya taba rayuwa mara kyau irin ta 'ya'yan masu kudi marasa kwaba amma duk irin halayensa he is not a rapist. Kuma a irin ji da kansa na da fa banda yanzu, bazai kula mai kati ba. Ko da wasa bamuyi tunanin zaiyi aure ba nan kusa amma sai gashi yana ganinki ya canja sosai. Banda degree yana da masters har biyu amma yaki aiki sai kashe kudi. Sai gashi jiya Alhajinmu yace yayi masa maganar yana son fara aiki. Hannayen Hafsi ta kama ki daure ki zauna dashi don Allah na tabbatar he will be a better person. Ganin Nafisa na hawaye Hafsi ta suma kuka itama. Cikin kukan ta fadawa Nafisa abinda taji daga dakinsu Tilly. Murnar Nafisa har zuci tace kada ki fadawa kowa da sannu asirinsu zai tonu. Scanning zan kaita shegiya gayyar tsiya. Har suna da guts din shigowa gidan nan. daga nan suka zauna suna tattauna yadda zasuyi karshe Nafisa tace idan kin amince zanyi magana a kaiki wurin mijinki. Dammmm zuciyarta tayi don tsoro.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐30
Washegari gari da safe Nafisa tazo da Mariya nurse. Ita tayi musu jagora zuwa dakin su Tilly. Senator Rufai tun da suka zo gidan zama ya gagare shi ko kadan baya kaunar haduwa dasu gashi bazai iya korarsu ba har sai sunga yadda al'amarin zai kasance.
Tun daren dama Tilly ta gama tsorata Rosie tace ki kwantar da hankalinki nifa abu irin wannan baya tsorata ni. Zamu sami mafita cikin ruwan sanyi. Ko da su Nafisa suka shiga dakin a kwance suka tarar da Tilly , Rosie tana rirriketa tana ta amai. Laulayi dai kamar gaske. Nafisa ta kawar da kai gefe dama bata sanar da Mariya ainihin alaqarsu ba. Ita ko sunansu ma bata sani ba. Ta yi mata kallon banza ki tashi za'ayi miki test. Rosie ta yi kalar tausayi to bari na taimaka mata ta gyara jikinta. Mariya tace ai fitsari kawai nake bukata ma idan kun shiga ga wannan robar ta mika mata irin sample bottle din asibiti sai ku kawo min a ciki. Kadan ma ya isa. Nafisa tace kiyi mata na jini kawai ance yafi nunawa. Nan da nan suka hada ido a tsorace. Tilly ta fara hawaye don Allah kuyi hakuri bana son allura. Nafisa tace ke da zaki haihu meye abin tsoro a allura. Mariya tace ki bari kawai muyi na fitsarin idan bai zama clear ba sai na debi jinin. Rosie ce ta kamata tana tafiya a hankali har suka shiga toilet suka rufo kofar. Tilly ta gyara jikinta tana tsaki ta sassauta murya kinji waccan yarinyar wai blood test? Idan ta shiga hurumi na bazan mata ta dadi ba. Rosie ta rufe mata baki sai an ji mu. Ungo ni ta mika mata robar data cika taf da fitsari. Kamar ta rike kashi haka Tilly ta karba ta fito ta ajiye a gaban Mariya.
Duk suna kallo ta saka PT strip din a cikin robar ta fito dashi ya nuna layi biyu alamun ciki. Mariya tace ai kinga ma Nafisa ya nuna basai munyi na jinin ba. Nafisa a ranta tayi kwafa dama tunda suka shiga toilet tare tasan akwai abinda zasuyi. Ta kalleta harda dan guntun murmushi sannu Allah Ya raba lafiya. Yanzu gobe zan kaiki asibitin da nake zuwa sai ayi miki ultrasound gara mu gani kila ma biyu ne babies din. Nafisa dai dariyar da take harda ta mugunta suka fice ita da nurse.
Suna rufo kofar Tilly tace na shiga uku ya zanyi ne Rosie gobe asirina zai tuno. Kwantar da hankalinki kamar tsumma a cikin randa. Wannan yar kwailar matar tasa zamu kullawa. Idan zai aureki ai gara ki zauna ba kishiya muci karenmu ba babbaka Talatu. Suka tafa sannan tace akwai dan taimako daga wurin malam fa sunansa makalemata. Idan lokaci yayi zan baki ki yi amfani dashi.
0 comments:
Post a Comment