Saleh dai ne ce komai ba, yana jin yadda ake tafiya dashi a mota 'yan sanda, a galabaice yake dan haka be san inda suke tafiya ba, harabar police station akayi parking, aka fito da Saleh, yana tangaɗi haka aka tankaɗa shi cikin cell aka ƙulle.
Duk da yamma ce amma sauro har ya fara shagali a gurin nan, ga zafi a gurin kamar oven, haka Saleh ya baje a ƙasa ƙirjinsa da cikinsa na masa ciwo kamar zasu tsage, saboda duk daya sha da katako.
Yana jin wani ɗan sanda yayi sallama, sauram suka dinga sara masa, ɗaya daga 'yan sandan da suka ɗakko Saleh yace "Oga gashi nan a cell, munje mun ɗakko shi"
Ɗan sandan yace "ok shikenan, ku rubuta statement ɗinsa"
"Yallaɓai tome zamu rubuta?"
"Kai baka san me zaka rubuta ba, ku rubuta bayani akan an same shi da laifin haɗa kai da Yusuf, sun sace 'yar gidan Nasir Daula, sun ɓoye su, ka dai rubuta abunda yakamata"
Ɗan sandan ya sara masa yace "ok sir, za' ayi yadda kace"
"Yawwa that's very good, and a matsa shi yadda yakamata ya faɗi abunda ake nema a gurinsa"
"Yes sir, za'ayi abunda kace"
Yace "good"
Daga nan ya wuce ya shige office ɗinsa.
Hankalin Nurat ya tashi sosai, ganin cewar dagaske mahaifinta yake ze raba ta da ƙasar, itama tayi ɗamarar wannan karon zata bijire masa, kome ze faru se taga ƙwal uwar daka, se taga ƙarshen abunda mahaifinta yake yi, dan barin mutum irinsa suna cigaba da abunda suke so a doron ƙasa hatsari ne ga al'umma, wataran za'a iya wayar gari mutanen kirki su ƙare, ta ɗau wayarta ta kira Khalil, Khalil ya ɗaga yace
"Hello my dear, ya akayine any news?"
Nurat tai ajiyar zuciya tace "bad news brother, Daddy ya dage akan cewar wai sena tafi imperial U. K Inyi karatau a can, me Daddy yake nufi dani ne?"
"Calm down dear, make your statement clear please, kamar yaya imperial Collage, ke kaɗai zaki koma UK ɗin kiyi karatu, wanda kika yi a baya be isa ba"
"Nima shi na gani brother, shifa yayi min alƙawarin zanyi school a Nigeria, a Nigeria zanyi high institution, Amma kawai yazomin da wannan maganar, da alama yana zargina ne da fara bin diddiginsa, ni kuma gaskiya i won't tolerate it dear, gaskiya zan bijire"
Khalil yace "subhanallah, Nurat don't say that again, haba Nurat na sanki da biyayya da haƙuri, me zesa ki fara faɗar haka kuma? Haba Sister na"
Kuka Nurat ta fashe dashi tace "Broz Khalil, iya biyayya da haƙuri kasan nayi, nayiwa Daddy biyayya yadda yakamata, nayi ƙoƙarin kasancewa a cikin 'ya' ya nagari masu haƙuri, tun taso wata fa kullum cikin tsangwama da kyarar mahaifiyata yake, amma ban taɓa kulashi akan hakan ba, Brother babu ɗan daze dinga ganin mutuncin duk mutumin daze dinga cin zarafin mahaifiyarsa, komai kusanci da soyayyar dake tsakaninsu kuwa, amma na share na ɗauke kai, nake masa biyayya, ni da mahaifiyata mun masa biyayya, amma baya gani Khalil, baya gani kullum cikin zagi da cin zarafin mu yake, har gara ni yana ɗagamin ƙafa, akan mahaifiyata lokaci yayi da zan nuna masa nima 'yar halak ce, zan nuna masa ni ma' yace, wallahi bazan sake masa biyayya ba nagaji Khalil "
Khalil yace " Calm down, calm down my dear, i feel your pain Baby, kiyi haƙuri dan Allah, nasan me kike ji a zuciyarki, amma dan Allah karki bijirewa mahaifinki, hakan ba halinki bane ba"
"Yanzu na koya, kuma shine ya koyamin, kuma zega canji tabbas, na masa biyayya har akan abunda be dace ba, haka kake so in cigaba da binsa yana jan rayuwata data mahaifiyata a ƙasa?"
Barrister Khalil yace "kamar yaya ya saki abunda be dace ba?"
Cikin kuka tace "Khalil, Daddy da farko ni yasa in hilaci Widad, aka sumar da ita za'a sace ta, Yusuf ya ceceta, wani abunma baze faɗu ba ni kawai ka ƙyaleni, idan kuma ya dage sena bar ƙasar nan wallahi sena kawo masa ɗan shege ya raina a cikin gidansa na rantse da Allah "
" Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Nurat kin san me kike faɗa kuwa? Ko kin fara shaye2 ne ban sani ba"
Ta ƙara sautin kukan ta tace "idan ma ban fara ba ina daf da farawa, dan wallahi ya takuramin zan bar masa gidansa in shiga duniya, ko in tafi England inyi irin rayuwar da yake ganin gara inyi irinta da ya kasa cinma nasa burin"
Khalil ya kwantar da muryarsa yace "kina jina Nurat, am sorry kinji, nasan a irin matsala da damuwar da kike ciki, amma kin san zukata nawa ne zasu shiga garari idan kika lalace? Mummynki da kike wannan damuwar saboda ita, ya kike gank idan taga tilon 'yarta ta faɗa mummunar rayuwa? Ya kike tunanin shi masoyin naki ze kalle ki idan kika koma mutuniyar banza? Family duk zasu shiga damuwa idan suka ji labarin yarinyar da suke so, suke ji da ita ta shiga wata rayuwa daban, dan Allah kiyi haƙuri ki bar wannan maganar "
" Brother idan na bar wannan maganar wacce zanyi? Am tired wallahi na gaji dayi masa biyayya, Khalil abun ba sauƙi fa, dama mutumin kirki ne da sauƙi"
"Nasani Nurat, ki kwantar da hankalinki kinji, Insha Allah zan shigo gidan naku, zanzo muyi magana amma ki dena kukan nan please, kuma karki sake faɗin wannan maganar kinji Light" gabata ne ya faɗi jin yace mata Light, sunan da Yusuf ke gayamata, ajiyar zuciya tayi tayi jifa da wayar, tana ci gaba da rushewa da kuka.
A hankali hannun Amal yana warkewa, an kwance mata bandejin kanta ma, se hannun da haryanzu akayi hangin ɗinsa a wuyanta, yanzzhma ta fito daga wanka tana tsaye a gaban madubi, daga ita se towel kanta a tsefe, ta baje gashin kanta, ba laifi gashinta yana da tsawo, ga hannuta sagale a wuyanta, ga goshinta inda yayi tabon ciwon da Alhaji Haruna yaji mata, ta dinga ƙarewa kanta kallo a mudubi.
A hankali tace "dubeni, mace har mace, bani da makusa sedai an gurguntamin rayuwa, an rabani da mutuncina saboda zalunci, kuma ya biyoni da wasu tarkacen banza saboda ya rainamin hankali, bayan tabo na sarari da yayi min, ya barmin na zuciya me matuƙar ɗaci da baze goge ba, me zanyiwa mutumin nan in huxe, wace irin illa zan masa daze dasa masa baƙin ciki a rayuwar sa ne? Me zanyi ne Amal kiyi tunani ƙwaƙwalwarki bata ja Sam "
Ta dafe kanta ta fashe da kuka, tana tuna yadda ya suka dinga kokawa, da muguntar da yayi mata yacinma burinsa, zubewa tayi a gurin tana wani irin kuka, me tsuma zuciya
" Duk laifinki ne Mummy, laifin kine, nace ba zani ba kika ce se naje, Mummy why? "
Jikinta har rawa yake saboda kuka, dukda daga wanka ta fito amma ta haɗa gumi, ga hawaye ga majina se shesheƙa take.
Ramlah ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune a ƙasa, idonta yai ja tana kuka.
Ramlah ta ƙaraso da sauri tace " ke Amal lafiya kuwa? Meye haka? Meye ya same ki"
"Bakomai"
"bakomai kamar yaya? Kalle ki fa"
Tsaki Amal Tayi tace "excuse me please, dan Allah ki bani guri, ina son kaɗaicine"
"wane irin kaɗaici kuma? Anya kina hayyacinki kuwa?"
"Na miki kama da Widad ne, balle kice na haukace? Kawai ki fita ki bani guri"
"Amma Amal"
"Dan Allah ki fita ki ƙyaleni, kad in haɗiyi zuciya in mutu, dan Allah ki fita!"
Tai maganar cikin kuka, Ramlah na fita taje ta dstse ƙofarta ta kwanta akan gadonta ta cigaba da rera kukanta, tana jin Ramlah ta kira Mummy, suka dinga buga ƙofar amma tayi musu banza kamar ba taji ba.
Bukar ya kira Alhaji Haruna, Ya ɗaga wayar suka gaisa, Bukar yace "kunyi waya da Musa ne?"
Alhaji Haruna yace "A'a gaskiya, na kwana biyu bamuyi waya ba"
Alhaji Bukar yace "ok, na zaci kunyi wayane, haryanzu be ce mana komai ba akan batun wanda ze saka mana hannun, kuma yace mu saurareshi zuwa Laraba, anjima zamuyi meeting kota zoom ne, sannan ya batun takaddar da aka ce wannan yaron ya bari? Ka karɓo mana ɗinne kokuwa?"
Alhaji Haruna yace "eh na karɓo, naje har gidan da kaina naje na karɓo takaddar"
Alhaji Bukar yace "good, kasan duk wata sheda da zesa a ganemu, dole mu ɓatar da ita kar wani ya samu, dan haka ka kawomin takaddar nan"
Yace "shikenan, Insha Allah zan kawo maka ita, sannan zan sanar dasu batun meeting ɗin nan da kace"
Alhaji Bukar yace "to shikenan, se kazo"
Alhaji Bukar ya ajiye wayar, ya miƙe ya bar ɗakin dayake, dan ya manta da ya karɓi tajaddar yazo da ita nan gidan ko kuma a can ya barta gurin da ta bashi?.
Hindu tana tsakar gida, suna ta aiki a tsakar gida, Hanne tana gefe tana gyaran wake zasuyi alala.
Hari tace "sannu da aiki Hanne, Allah ya kaimu bikinki mu kira masu kiɗan ƙwarya muyi ta juyi a gidan nan"
Hanne ta taɓe baki, dan ita sama gaba ɗaya haushin Auren nan ma take ji, dan Yanzu haushin mijin da zata aura takeji, dan gani take bashi da komai idan ta kalli Yusuf, ita dai tana son Yusuf sosai, tana jin ina ma ya aure ta, da tafi kowacce mace dace a ƙauyen nan, da yana ɗan kulata amma yanzu ya dena, saboda wannan koɗaɗɗiyar matar tasa me kama da Yahudawa.
Hindu tace "Allah dai ya kaimu bikin nan ds rai da lafiya, ban san wane irin shagali zanyi ba, nima sena gyagije nayi shagali, idan kika tattara kika tafi in gaje gurin kwanciyar ki da nawa, Abinci ma zan haɗe nawa da naki ne, dama yanzu ba ƙoshi nake ba" Hindu Tayi maganar cikin sigar wasa da zolaya.
Amma Hanne ta karkace ta kyaɓe baki, ta kalli Hindu tace "aifa dama ina zaki ƙoshi tunda mayya na gidan? Ai gara in tattara in bar miki gidan ki cigaba da haɗa kafaɗunki dana iyayen mu, tunda dai ke kinfi kowa baƙin jini, babu wanda yake sonki balle kisa ran zakiyi aure ki bar gidan nan, ai se kiyi ta zaman gidan ki ƙare ki tsufa a gida, mujiyar garin nan, shikenan mutum ba zuciya balle ya samo wanda ze rufa masa Asiri ".
Ai tuni idon Hindu ya ciko da hawaye, ita har ga Allah wasa tayi wa Hanne, amma harta fara yan kamata baƙaƙen maganganu da cin zarafi, Hanne na ɗagowa suka yi ido huɗu da Yusuf, da alama duk yaji abunda ta faɗa, sekuma ta shiga kame kame, dan wata irin kunyace ta kamata, bece komai ba ya sa kai ya fice, dan be fiye son shiga sabgar iyalan gidan ba.
Yana fita Widad ta fito tsakar gidan nan, taga yadda Hindu ta nutsu tayi shiru, ido duk ya tara hawaye saboda zafin maganganun Hanne.
Widad tace "ke Hindu, wai ita wannan banzar 'yar uwar taƙi haifarki tayi? Haifarki Tayi da zata dinga gaya miki magana kina jinta? Wai wane ɗan matsiyatan zata aura a garin nan da har take miki wannan gorin haka? Wanda zata aura ɗin ma ya kai a kira shi namiji da take miki gori a kansa "?
Hanne tana hura hanci, cike da ƙauyanci da jahilci tace " Wallahi, tallahi nafi ƙarfin auren matsiyaci, niba matsiyaci zan aura ba"
"wallahi kika bari nazo inda kike, na shaƙeki se na jefa ki a rijiyar nan, saboda me zaki takurawa yarinya dan bata magana, dan kinga tana da haƙuri, wallahi ki kiyayeni akan ɓata mata rai"
Hanne tace "idan anƙi fa?"
Wata irin zuciya ce ta kwashi Widad, sedai Hindu tai saurin riƙeta tace "A'a Amarya yi haƙuri ƙyaleta kawai"
Widad ta harzuƙa matuƙar gaske, ji take tamkar ta jefa Hanne a rijiya, mussman idan ta tuna yadda take juya manyan attajirai masu ji da kansu, amma wata kucakar 'yar ƙauye na gayamata magana, ƙwafa kawai tayi tace "ba alfahari ba amma Wallahi da kin san wacece Widad, da baki isa ki yadda in haɗa ido dake ba, dan wallahi ko masu gyaran gadon baccina sun fiki kyan gani, ki zuba ido zakiga mijin da Hindu zata aura, Jahila kawai"
Ta wuce ɗakinta tana huci, duk wannan budurin Gwaggo da Hari basa nan akayi shi, amma abun yana damun Widad taji an taɓa Hindu, setaji kamar ita aka taɓa, danma ita Hindun ce shashasha take tsayawa ana mata wulaƙanci.
Amal kam wani tunani tayi a ranta, dan haka ta miƙe da ɗan sauri, ta fita falo, Mummy ta kalleta tace "kinga damar buɗewa yanzu?"
Amal tace "Mummy Ramlah ta kasa fahimta tane, wani lokacin idan ina cikin jin zafin ciwo, bana son kowa a inda nake, nafison kaɗaici amma se a takuramin, kun kasa ganewa"
Mummy tace "madalla, shine nake ta magana kika ƙi buɗewa"
"Am sorry, bazan sake ba insha Allah"
"Hmm ai shikenan, ya hannun naki yanzu?"
Tace "da sauƙi, Mummy dan Allah aramin wayarki zan transfer ɗin kuɗi, ni banki sun hanani wai ba network"
Ba musu ta miƙawa Amal wayar, Amal ta karɓa ta koma gefe, ta tura lambar Alhaji Haruna wayarta, ta bata wayar tace "Mummy, ga wayar nagode"
Ta koam ɗakinta, tana zuwa ta kulle ƙofa ta zauna akam gadonta ta kira Alhaji Haruna.
Lokacin yana tsaka da bulayin neman takadda, ya ɗaga suka gaisa dashi, sannan tace "Naga saƙonka, amma meyasa kwana biyu ba kazo ka dubani ba"
Se ynzu ya ɗau muryar ta, yai murmushi yace "nima naji saƙonki, ance bayan mota zakizo karɓar gids ma"
Tace "eh hakane, ko idan na dawo bazan samu ba"
. Yace "idan kika dawo ina?"
"zuciya ta, ta fara rayamin kawai idan na warke zan bazama in nemi arziki, in more ƙuruciya ta, idan ka shirya nima a shirye naake zan dawo gareka, tunda aikim gama ya gama tunda fari"
Yai wata shegiyar dariya sannan yace "ni zaki yaudara, ko har kin manta abunda kika gayamin a Asibiti, kaina yana ja sosai dan haka abune mawuyaci kiyi galaba a kaina, tabbas naji daɗin kasancewa dake sedai bazan sake amincewa dake ba, tunda kikayi wannan fueucin, ki sake shawara kinji 'yan mata, idan da gaske kike ki bazama ki kama wasu alhazan, nikam na gama muma na biya tunda na bada motar miliyoyi"
Bata sanma yadda akayi ta ajiye wayar ba, tana jera ajiyar zuciya kamar wadda tai gudu, duk yadda take tunanin abun ya wuce tunaninta, ashema matan suna suka tara, ba kowaccece ke iya kaidin ba, shi kansa shirya makircin ba abune me sauƙi ba, tai sharkaf da gumi tana sake tunanin wata hanyar.
Yusuf na dawowa Widad ta manta da damuwar da take ciki, sedai duk da hakan seda ya gane, yace "Maman Baby, ya akayi ne naga kamar ranki a ɗan ɓace yake"
Tace "A'a ni ba abunda akayi min, Ina ɗan tunani akan Hindu ne, ina ma Megari ze bani ita idan mun koma gida"
Yusuf yace "gaskiya abune me wahala, ya ɗau 'ya ya bamu alhalin bamu da wata dangantaka a tsakaninmu"
Ta jinjina kai tace "hakane, Gaskiya nifa na damu Saleh yazo ayi wacce za' ayi, na fara gajiya hankalina yayi gida sosai fa"
Yusuf yace "ki kwantar da hankalinki, nima shi nake jira yazo, muji abunda yakamata ayi"
Tace "shikenan, Allah ya kawo shi"
Yace "Ameen"
A gurin 'yan sandan ma babu sassauci, baƙar wahala Saleh yake sha, dan yana kyautata zaton an masa illa saboda duka, dan a nan ɗinma' yan sanda ke sa kulki, suyi ta dukansa izaya daban daban wai lallai seya faɗi inda su Yusuf suke, ga rashin Abinci gashi ko Najasa ne sedai yayi a nan, nan da nan Saleh ya fita daga hayyacinsa, ya canza kamanni fuska duk ta kumbura, ko ina rauni me yake zubda jini, sun doddoke masa ƙafafuwa da ƙyar yake iya miƙewa.
Da Safe Yusuf yana kwance akan cinyar Widad, ta samu comb se jagwalgwala masa sumar kansa take yi, shi kuma yana lumshe ido, can yace "gaskiya ki ƙyalemin gashina mana, haba se izaya kikemin a kaina"
Ta ɗan tura baki tace "kitso fa zan koya"
"To aini na gaji se jagwalgwala min suma ake, ga zafi banda ma tsabar rigima irin taki ta ina za'a kitsa sumata?"
"Ni dai ka ƙyaleni"
Yace "shikenan, Allah sarki ni, gaskiya idan na kuma jin zafi sena rama, sena aske wannan gashin naki da akewa mutane iyayi dashi"
Tai murmushi tace "daka temakeni, dan ba dan babu kyau ba sena rage shi, kuma idan ka aske ai kanka kayiwa, kaine kake wasa dashi ai"
Yai murmushi yace "kuma fa hakane, to na fasa askewar"
"A'a gara dai ka aske ɗin"
Hindu Tayi sallama kawo musu Abincin Safe, akayi mata izinin shiga tana shiga ta tarar da Yusuf kwance akan cinyar Widad.
Ta sunkuyar da kai cikin matuƙar jin kunya, Widad tace "sarkin kunya, idan na aura miki ɗan birnin haka zaki dingayi masa?"
Hindu ta juya da sauri tana murmushi, ta bar ɗakin, Widad tace "Yuzarsef, wallahi da ina da Yaya, ko wani ɗan uwa da babu abunda ze hana in roƙi ya auri Hindu, she's very kind and innocent"
Yusuf yace "hakane tana da kirki kam, ga nutsuwa"
Yusuf yaga abun na Widad ba na ƙarewa bane, dan haka ya tashi daga cinyarta yace "ke nagaji, kaina se zafi yake duk kin jagwalgwala min suma"
"ni kayiwa haka ko? In ƙara ganin ka taɓamin gashi ni da kaine, kuma ma insha Allah ta mace zan haifa, saboda in dinga mata kitso ta zama ƙawata kuma"
Yusuf yace "sannu sarkin shirirta, da shirme, ga tsabar ƙuruciya mutum baze gane hakan ba, se ya zauna dake, to ni bame yiwa 'yata kitso balle a jagwalgwala mata kai, idan kin haifi namiji nakine, mace kuma ta wace"
"A' a ban yadda ba, gaba ɗaya nawane, bayan kace baka son Baby"
Yusuf yace "Nina ce miki bana so? So kai amma ki bari ki samu cikin tukuna, sekimin iyayi da tsari"
"wai dan Allah dagaske bani da ciki?"
Yace "zan miki ƙarya ne? Kin manta shekarata biyu ina medicine, baki da komai madam"
Ta kwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "insha Allah ina da shi"
"Seki zauna kiyi ta imagination ai, miƙomin abincin nan inci"
Ta ɗakko kwananon Abinci ta miƙo masa, suka ci tare suna hira.
Yusuf yace "idan na dawo da daddare, kwaɗon gurji da zogale zan mana, zaki ci?"
Widad tace "Sosai ma, ranar Gwaggo tayi naci da daɗi Sosai"
Yusuf murmushi yace "to kwaɗayayyiya"
"Eh anji ɗin"
A haka suka yi sallama, yana ta tsokanarta, kamar karsu rabu.
Duk iya dubawar da Saleh zeyi, yayi amma ya rasa takaddar nan, ya duba ya duba amma takadda tace ɗaukeni inda ka'a ajiyeni, gashi yacewa Bukar ya karɓo takaddar nan.
Ya koma guest House ɗinsa, inda suka dinga kokawa da Amal, ya dinga duba takaddar nan, yai tsai gana dubawa ya birkita komai, ya hango ta a ƙasan gado.
Hamdala yayi, ya durƙusa ya ɗakko takaddar, yana ajiyar zuciya ya buɗe takaddar, sedai me ba takaddar bace form ne na koyon kwalliya na Amal, tsaki yayi yai jifa da takaddar yana tunanin ina yasa waccan takadda data bashi, amma kuma lokacin da ta bashi takaddar ai be buɗa ba, balle yasan me ta bashi, hankalinsa na kan yai mata akuyanci kawai, ya birkita ko ina amma babu wata takaddar se wannan, nan take gumi ya shiga tsasttsafo masa.
Widad taita jiran Yusuf ya dawo, dan se nishaɗi take ji ze kawo gurji yayi musu kwaɗo, bayan ya dawo da kayan gurjin da yamma, ta zauna ta cire ɓawon tsaf, ta gyara zogalen suka ɗora zogalen akan wuta, suna zaune suna hira a ƙofar ɗakinsu suna aikin su, hankali kwance yayin da zamantakewarsu kan burge wasu daga mutanen gidan.
Ya gama suka haɗa Kwaɗon nan a roba, Suka bawa wanda zasu bawa, Widad se haɗiyar yawu take, ta zauna zata saka hannu ta fara ci Yusuf yace "tsaya waye yace ki fara ci, salon ki fini loma ki fini ci ko?"
Ai ba ta saurareshi ba, danji take kamar hanjinta ze fito idan bata ci ba, jiki na rawa ta sa hannu ta fara cin Abunta, Yusuf yana kallonta yana nazarinta, tunda ta fara ci bata saurareshi ba seda taji ta ƙoshi tukuna, ta miƙe taje ta wanke hannunta ta sha ruwa ta dawo ɗaki sannan tace " Yawwa ina jinka, mema kace ɗazu?"
Yace "cewa nayi, sannu da aiki acici"
"Yawwa mijin acici, kai dai ubangiji Allah yayi maka albarka, ya saka maka da alheri nagode sosai"
Yace "Ameen, amma a dena cinye Abinci ana barina"
Kawai ta kwashe da dariya tace "ba ruwana cin abuna zanyi ehe"
Yace "ai shikenan poor me"
Tace "shagwaɓaɓe kawai, me sexy eyes"
Yace "what, sexy eyes kuma sekace wani mace"
"baka sani ba, you are having sexy eyes fa"
"Mhmm Malam kawai kice abunda yake ranki kenan"
Tace "What? Wai Yoseef meye haka? Kawai ba damar inyi magana seka canza mata ma'ana"
Tai maganar tana kai masa duka, ya kwanta yana dariya yasa pillow yana karewa.
"Kuma ma kai mummuna ne" tace tana harararsa.
"Eh naji bakomai, a haka 'yan mata suke rububina, saboda munina a haka suke sona"
Widad tace "Wallahi idan muka koma gida, duk wadda tayi gangancin raɓarka zata ga matakin da zan ɗauka wallahi"
Tai maganar very serious, dan kamar ma haushi taji.
Yace "haka akeyi, shikenan duk suna kallo se kice baza'a kulani ba, bayan kin sanni da farinjini, cewa fa kika yi in Auri Hanne"
Tsaki tayi zata tashi, ya fizgota jikinsa, yasa fitila ya haske mata fuska.
"Ni ka dena haskani, bana so"
Yusuf yai ƙasa da murya yace "An taɓa gayamiki ke kyakkyawa ce kuwa My wife?"
"Ai ko ba'a faɗa ba, nasan ni me kyauce sakeni"
"in sake ki kuma?"
Da sauri tace "No, i don't mean you should divorce me, ka cikani i mean"
Yai murmushi yace "nima na sani ai, ni dake ai mutu ka raba Babayna me kama da teddy"
Tace "Yoseef me yake damunka ne yau? Duk ka takuramin nice kuma me kama da teddy?"
"Eh ramawa nayi, ko kin manta haka kika cemin cartoon jiya"
Yai maganar yana dariya, itama dariyar ce ta kamata, ta buɗe baki kamar zata cije shi, amma ta fara kissing ɗinsa.
Kamar ranar suka fara kasancewa da juna, sunyi nishaɗi mara misaltuwa, sun farantawa junansu rai sosai, kowanne yana sake jin ɗan uwansa a ransa.
Haka suka wayi gari cikin farin ciki, sedai dukda wannan farincikin Yusuf se fama yake da fargaba, ya rasa dalilin hakan.
Yana ta shiri ze fita, yaji kamar harbin bindiga, gabansa ya faɗi yace "Lovely, kamar harbi fa nake ji"
Widad tace "A'a ko dai tunanin gurin aiki kake, amma wane irin harbin bindiga ana zaune ƙalau? Bari inyi walha, idan na idar seka tafi"
Ta juya ta tada salla, tayi raka'ar farko zata yi ta biyu suka ji Hayaniya, aka sake harba bindiga a ƙofar gidan mutane nata guje guje.
Yusuf yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
Daga tsakar gida suka ji ana "duk wanda ya motsa, zamu fasa kansa da bindiga, kowa ya tsaya a inda yake"
Gaba ɗaya jikinsu se tsuma yake, Hari ta samu wani lungu a bayan randa ta shige, se zare ido take saboda tsoro.
Nan da nan sega jiniyar motar' yan sanda ta ƙaraso
Da gudu Widad ta fito tsakar gidan, amma taga 'yan sanda tare da Saleh hannunsa duk ankwa a cikin mawuyacin hali.
Tace "me zan gani haka? Meye haka?"
Wani ɗan sanda yace "Yusuf, ina Yusuf yake?"
Widad tace "ban sani ba, bazan faɗi inda yaken ba"
Hari daga inda ta laɓe tace "Wudas ki dena magana karsu kashe ki fa"
"Ina Yusuf yake!" a kai mata magana cikin tsawa.
Itama cikin tsawar tace "ban sani ba nace"
Yusuf ya fito daga ɗakinsu, jikinsa sanye da jallabiya, ya ƙarasa gabansu ya miƙa musu hannunsa cikin surrender
.
Widad ta fashe da kuka tace "No! This is impossible, me yayi muku? Laifin me yayi mijinane fa, ku cire masa wannan cuff ɗin"
Su kai mata banza suka tasa ƙeyar Yusuf, itama suka sata a gaba ihu take tana kururuwa akan su sake shi amma sukayi burus da ita.
Aka sashi a bayan motar 'yan sanda, idonsa yayi ja ya kasa magana, se kallonta da yake gaba ɗaya ta birkice se ihu take tana kuka, muryarta harta fara dashewa.
"Ina sonka, Yusuf ina sonka, I love you Yusuf, dan Allah ku sakarmin mijina, beyi laifi ba, beyi laifin komai ba"
Yusuf ya ƙura mata ido, ya lumshe idonsa a hankali, yayin da Widad ke zubda wani irin hawaye tana kuka, me sauti.
Aka sakata a motar gida seinna, shikuma a bayan motar 'yan sanda gashi ga Saleh, kowanne hannu da sarƙa!!!
(Rayuwa ƙaddarace kowa da irin tasa......... 🎶 )
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/17/21, 5:35 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
106_107
Sosai Widad ta cigaba da gunjin kuka, yayin da mutanen ƙauyen suka fito suka yi duru duru suna kallo, ɗaliban Widad se kuka suke, haka Hindu gaba ɗaya ta birkice banda kuka ba abunda take yi, ba Hindu ba kawai hatta Megari, da su Hari hankalinsu ya tashi sosai, ga Sunusi mijin Jamila baya nan akazo aka kama su Widad.
Ana tafe a hanya amma bakin Widad yaƙi mutuwa, kuka kawai take akan a sakar mata mijin ta, tun Yusuf yana iya juyo muryarta da kukanta, har muryar tata ta dashe ba ajin me take faɗa sosai, haka sukaita tafiya har suka fito daga wannan kwazazzaban, da ramukan dake hanyar garin, suka hau kan kwalta ɗoɗar suka kama hanyar Kano.
Alhaji Haruna fa ya haɗa uban gumi, saboda ya tabattar da babu wannan takadda, takaddar form ɗin koyon kwalliya ta bashi, ba shiri ya ɗau wayarsa ya kirata da lambar da ta kirashi ɗazu, tana ganin kiran nasa Amal ta tashi da sauri, ta duba har zata ɗaga kawai ta fasa, ta ajiye wayar yai mata kira yafi Ashirin, ƙarshema ta saka wayar a silent tai kwanciyarta.
Yai wujiga wujiga, saboda takaddar nan saboda yasan Bukar ba kyau, gashi ya riga yace aiya karɓo, tunda takaddar zata iya zama sheda a kansu, wannan wasiƙar zata nuna akwai halin rashin gaskiya da mahaifiyar Anwar take aikatawa wanda yasa ya bar gida, idan tuhuma tayi tuhuma kuma za'a gano su.
Ya tura mata saƙo kusan kala shida amma babu reply, can dai ta ɗau wayar ta duba saƙon daya turo, magiya yake mata akan dan Allah ta ɗaga wayarsa, mahimmiyar magana yake son suyi.
Tana cikin karantawa kuwa ya kuma kira, seda taja aji sannan ta ɗaga, yai ajiyar zuciya yace "habba kyakkyawa, tun ɗazu naake kiran waya, amma anyi biris dani?"
Tace "to me kake so in maka? Ko in ɗaga in ce maka?"
"A'a kwantar da hankalinki, ai duk abun bana zafi bame ko ɗaga hankali, magana zamuyi"
Tace "ina jinka"
Yace "Yawwa, dama cewa nayi wannan takaddar da kika kawomin, kinyi mistake ba wasiƙar kika bani ba, form ɗinki ne na koyon kwalliya, kinyi mistake gurin bani"
Tace "se akayi yaya?"
"A'a dama ba wani abu bane ba, cewa nai zanzo in karɓa in an jima, saboda takaddar tana da mahimmanci sosai"
"Karka sake ka soma zuwa inda nake, bazan bayarba ka riƙe wadda na baka a matsayin ta"
Alhaji Haruna yai gyaran murya yace "haba beautiful Baby, ai abun duk bekamata ya kaimu ga haka ba, meye na ɗaukar zafi haka? Ai abun bana zafi bane ba, ki gayamin me kike so ayi yanzu in karɓi takaddar nan? Ko nawane zan baki"
Amal ta janyo Jakarta, wadda yace tayi accident da ita, ta duba amma itama taga babu takaddar a ciki, amma tai ajiyar zuciya tace "nima nazo maka da buƙata ta, amma kaƙi amincewa, dan haka kowa ha riƙe buƙatarsa, bazan bayarba gara asirin kowa ma ya tonu a huta"
Yace "Subhanallah, hadda mamanki fa"
Tace "har ita ɗin"
Yace "dan Allah kar muyi haka dake, ki bani takaddar nan na riga na cewa Bukar na karɓo takardar yace in kai masa, kuma yanzu inzo ince bahaka ba, baze sauraramin ba"
Amal tace "Ai gara karya saurara makan, kamar yadda nima baka sauraramin ba, kuma baka karɓi buƙata ta ba"
Yace "dakata, yanzu idan na karɓi buƙatar taki shikenan?"
Am tace "A'a ai kuma mun wuce wannan maganar yanzu, zan baka takadda bisa sharuɗa, yanzu abu na farko zan gaya maka Account Number ɗina, ina son inji wasu kuɗi masu nauyi, domin inci kaji in warke da wuri daga raunin daka min"
"Shikenan zan turomiki, yaushe zanzo in karɓa"?
Tace "turo ɗin tukuna in gani mana"
Yace "shikenan naji"
Ta kashe wayarta, lumshe ido tare da faɗin "Alhamdilillah, cikin sauƙi Allah ya kawomin hanyar da zan rama cin zarafin da kayi min, tabbas inaga yadda takkadar nan nayi, dan babu ita a jakata, amma a haka zan maka rashin mutunci in rama"
Alert ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta duba 500k ne, ta jinjina kai tace yanzu aka fara wasan
Seda yayi mata kira biyar, sannan ta ɗaga a fusace tace "wai meye ne?"
"dama cewa zanyi, kinga alert ɗin?"
Tace "na gani, amma sunmin kaɗan, na kuma raina"
Ta katse kiran tare da kashe wayarta gaba ɗaya, ta kulle ɗakinta da key, tai kwanciyarta.
Tunda suka taho Yusuf bece uffan ba, yai shiru yana saƙawa yana kwancewa a zuciyarsa, tabbas duk sunan da za'a kira shi dashi, ko a tuhume shi dashi, bashi da abunda ze kare kansa dashi, tabbas shi dai tunda ya tashi a rayuwarsa a siraɗin ƙaddara yake, daga wannan ya faɗa waccan, daga waccan ya faɗo wannan, haka ya sunkuyar da kansa yana ta tsabihi ga Allah, akan ya sauƙaƙa masa wannan lamarin.
Sun shigowa cikin garin kano, akayi hanyar babbar headquarter hukumar 'yan sanda dake garin kano, motarsu Widad kuma tayi wani gurin, ai tana ganin haka ta kuma fashewa da ihu, tana bori tana kuka tana "ina zaku kaishi? Ina zaku kaimin mijina? Beyi laifin komai ba, babu abunda yayi muku, ku ƙyalemin mijina wayyo Allah na Yoseef duk nice sila, saboda ni ka shiga wannan tashin hankalin, Dan Allah ka yafemin Yoseef, Allah ka fitar da mijina daga sharrin Azzaluman nan, Allah ga bawanka ka fitarmin da mijina"
Ta ƙarasa maganar, tana wani irin kuka me taɓa zuciya babu wanda ya kula ta a cikin 'yan sandan suka cigaba da tafiya.
Wani ofishin' yan sandan aka tafi da ita, suka fito da ita daga mota zuwa gurin 'yan sanda, idanunta sun kumbura sunyi ja saboda kuka.
Wani ɗan sanda yace "gata yallaɓai, yanzu muka shigo gari, shi an wuce dashi headquarter, ita kuma gata"
Ɗan sandan ya kalleta yace "Good, Madam congratulations, you are now free, mun cetoki daga hannun wanda sukayi garkuwa dake"
"Niba garkuwa yayi dani ba, wanda sukayi garkuwa dani daban, Yoseef ceto na yayi, shine ya temakeni beyi garkuwa dani ba, ka gaya musu suje su sakarmin mijina"
Ɗan sandan yace "koma dai ya akayi, wannan ku ta shafa ke dashi, muba abunda ya dame mu, zamu rubuta sannan mu sanar da duniya cewar, munyi namijin ƙoƙari gurin bincike mun gano wanda yayi garkuwa da Widad Nasir Daula, kuma ba wani bane face direbanta, wanda ya kasance ɗansanda, yaje gidansu yai basaja dan yayi garkuwa da ita, nasan hakan ze sake ɗaga darajar rundunar mu a ga namijin ƙoƙarin da muke, ba dare ba rana gurin kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma "
" Shut up!!! "
Ta faɗa cikin ƙaraji, tace " idan har ina raye ina numfashi, ko komai nawa ze ƙare se Yusuf ya fita, babu wanda ze cutarmin dashi, baku isa ba azzalumai ma cuta, lokacin da aka yi garkuwa damu muna buƙatar taimakk, babu wanda ya taimakemu na kusa rasa rayuwa ta, se yanzu da yayi komai ya gama, Allah yasa ya kare rayuwata, shine za'a masa sharri wallahi bazan lamunta ba, he's my Husband "
Ɗan sandan nan yace " ku ɗaukemin wannan mahaukaciyar daga gabana, a tafi da ita Asibiti a duba lafiyarta, sannan ku kiramin Ubanta Bulama tunda babu wanda yasan inda wancan yake "
Widad bata gane meyake nufi ba ta cigaba da kukanta, haka suka kawo Ambulance dan iya makirci, aka sheƙa mata wani abu ta sume a gurin, aka kira 'yan jaridu suka cika gurin, aka ɗauki Widad aka saka ta a motar Agajin gaggawa wato Ambulance suka tafi da ita.
Jaridu kuwa da sassafe shafin farko, hotunan Yusuf ne da Saleh, musamman na Yusuf ɗaure a cikin sarƙa ya sunkuyar da kai, gefe ga hoton Widad da aka ɗauka an fito da ita daga ofishin 'yan sanda an sata a ambulance, daka kunna gidan radio, labarai ko talabijin babu abunda zaka fara ji se
"Me dokar bacci ya ɓige da gyangyɗi, kuma ƙarshen tika tiki tik inji hausawa A yaune jami' am tasaro sukayi nasarar cafke jami'in ɗan sandan nan na farin kaya wato Yusuf Bashir Maitama, wanda yayi garkuwa da 'yar gidan fitaccen me Arziki nan a gida da wajen Nigeria wato Nasir Daula,' yan sandan sunyi nasarar gano shi ya sace ta tare da ɓoyeta a wani ƙasurgumin ƙauye dake garin Bauchi, 'yan sandan sun ceto Widad Nasir Daula, wadda ke cikin mawuyacin hali, da zauwansu basu yi wata wata ba aka kira motar Asibiti aka tafi da ita domin duba lafiyarta, zamu ci gaba da bibiya da kasa kunne domin jin wani mataki hukuma zata ɗauka akan wannan ɗan sanda, wanda ake tunanin har shi Nasir Daula ɗin shine yai garkuwa dashi, mu dai anan se muce Allah ya kyauta, yai mana tsari da irin wannan jam'ian tsaro a cikin al'ummar mu"
Nan fa gari ya ɗau ɗumi, aka dinga cece kuce, wasu na Allah wadai suna Tsinewa Yusuf, yayin da wasu ke a bari a ga abunda bincike zeyi tukuna.
Widad kam bata sake sanin inda kanta yake ba, inda har a gadon Asibiti aka bita aka dinga ɗaukar hotunan ta, ga fuskarta tayi ja saboda kuka, da gajiyar tafiyar hanya, amma aka dinga ɗauka ana watsawa duniya wai tana cikin mawuyacin hali, hannunta ɗauke da drip.
Alhaji Haruna ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba a taɓa raina masa hankali kamar yadda akayi yau ba, ya kira layin Hajiya Halima, Ramlah na zaune a falo wayar ta fara ringing, Mummy tana ciki tana amsa wata wayar dan haka ta ɗaga wayar tasa a kunnenta tace "Hello"
Yace "Yawwa Amal ce?"
"No Ramlah ce"
"Dan Allah idan Amal tana kusa ɗan bata wayar muyi magana"
Tace "tana ɗakinta, bari in kai mata"
Ta miƙe ta tafi ɗakin Amal, amma ɗakin a rufe harta kashe fitila ma "
Ramlah tace " gaskiya tayi bacci, dan ta rufe ɗakinta ma ta kashe fitila"
Yace "Yasalam"
Ramlah tace "ya dai? Akwai matsala ne?"
"A'a babu wata matsala, ina son muyi magana ne kawai"
"to ka gayamin saƙon in bata mana"
Yace "A'a karki damu, idan ta tashi na sake kira"
Ya kashe wayar yace "Amma dai Allah ya Tsinewa yarinyar nan, kaga min shegiyar yarinya mara albarka" ya ciji yatsa yai ƙwafa yace "dani kike zancen wallahi, kema sema wulaƙantaki,"
Amal ta ɗau wayarta ta tura masa saƙo tace "ka cigaba da kiran Mummy, kana cewa kana son Magana dani, wallahi idan baka yi wasa ba sena gayamata abunda kayi min, kuma kasan halinta sarai, kasan buyaginta zata maka abunda kai kanka zaka kasa gane kansa, dan haka muddin ba zaka cika sharaɗina ba, wallahi ba zan baka ba na gaya maka, kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan, nima a account dina ina da wanda suka fisu"
Ta kashe wayarta ta sake kwanciya, ya duba message ɗin, yaja wata ajiyar zuciya yana cije leɓe, totally ta riga ta gama raina masa hankali, yama rasa me zeyi ko me zece.
Yana nan tsaye yana tunanin mafita kiran wayar Bukar ya shigo wayarsa, ya ɗaga jiki na tsuma, yace "Hello"
"Haruna, yau muna da zama na gaggawa, cikin dare dan haka duk ku tattaru"
Yace "harda Halima?"
"banda ita, sannan kazo min da wannan takaddar, zamuyi magana a kai itama"
Daga nan ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya yakice gumi, yana huci Amal ta masa rashin mutunci, dan kawai abu ya shiga tsakaninsu se tayi masa haka?.
Mutan ƙauyen da Widad suka zauna suka dinga taradaddi, kowa da abunda yake faɗa wasu suna dama megari yayi wauta, wataƙila dama can 'yan fashi ne ko wasu masu laifin ne, amma daga zuwansu ya karɓesu, be san daga inda suke ba.
Hindu kam kuka, kamar wadda aka kama uwarta, ita kanta Hari gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, wunin ranar gidan daga masu koke koke, se masu salallami, Hanne kuwa ko a jikinta.
Koda Sunusi ya dawo, Jamika ta gaya masa abunda ya faru, dan haka yace dole gobe insha Allah ya tafi kank, yaje yaji ba'asin abunda ya faru.
Jamila tace "dan Allah karkaje, kar kaima a kama ka, dan na san da kana nan wataƙila da kai zasu haɗa"
Sunusi yace "da nayi musu me? Kince an kama Saleh, kuma Saleh shiya kawo su nan, meyasa aka kama shi, dole zanje inji"
Daddare megari ya tara iyalansa yace "to wannan bayin Allah dai, ni dai a ɗan zaman da mukayi dasu, ban tunanin mutane ne marasa gaskiya, ko makamancin haka, zamanmu da su ma mu alkhairi ya zame mana a garin nan, dan haka dan Allah ina roƙonku da kuyi haƙuri ku dena kuka, kukan ya isa haka, Hasana nasanki da son 'ya' ya kuma zamanmu dasu jin shaƙu dasu sosai, dan Allah kidena kuka kiyi musu Addu'a, Hindu Baffa kema kukan ya isa haka, muyi musu Addu'a, Allah ya basu mafita sannan Hari a samo makulli a rufe musu ɗakinsu, kar wanda ya sake shiga tunda da kayansu a ciki "
Hari ta tashi ta shiga ɗakinta ta samo mukulli, tana ƙoƙarin rufewa taga bokitinsu a tsakar gida, ta tafi ta ɗakko bokitin, kawai ta fashe da kuka tace " Allah sarki Wudas, da yanzu muna faɗa akan ruwan zafin da zata yi wanka, tace sena bata na bawa mijin ta, ban taɓa ganin abun tausayi kamar yau ba, yadda ta rikice tana kuka, Allah sarki Allah ya fitar dasu"
A kaita bata haƙuri, aka kulle ɗakinsu aka bawa Megari mukullin, ya kai ɗakinsa ya ɓoye.
Yusuf yana kwance a cikin cell, an raba masa cell shida Saleh, sauro yana ta masa buduri a ka, yai rigingine yana tunanin ya Umma zataji idan wannan mummunan labari ya isheta?.
Aka buɗe ƙofar cell ɗin, wasu 'yan sanda suka shigo su biyu, ya tashi zaune yana kallon su.
Ɗaya ya kalleshi yace "munafuki, kalleshi kamar na Allah, amma ƙasurgumin Azzalumi ne, kai garkuwa da' ya ka koma kayi da Ubanta, saboda kai Azzalumi ne, kuma a haka wai kai ɗansanda ne"
Yusuf yai shiru be ko ɗaga kai ba, ɗayan yace "rabu dashi corporal Sani, zuwa gobe in Allah ya kaimu semun sauya halittun fuskarsa, kafin 'yan jarida suzo, a buga shi a nunawa duniya shi, azzalumin banza dana wofi kawai"
Yusuf dai yai shiru bece komai ba, suka gama zage zagensu suka fita, suka sake rufe shi, tun Abincin safe Yusuf be kuma cin komai ba, ga doguwar tafiyar da suka yi, amma sam baya jin yunwa tunanin makaomarsa kawai yake a wannan hali da yake ciki.
Nurat na kwance cikin dare, taji Mahaifinta yana waya ƙasa ƙasa, ya fito daga ɗakinsa da alama dai fita zeyi, ta kalli agogo ƙarfe biyu da rabi na dare, ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito falo, aikuwa yana fitowa ya ganta a falo, ya ɗan haɗe rai yace "ke me kike yi a falo a wannan tsohon daren haka?"
Tace "ruwa na fito sha"
"ina ma fridge ɗin dakinki?"
"yayi sanyi da yawa, duk ya zama ƙanƙara shiyasa na fito"
Yace "to kin sha ɗin ne kokuwa?"
Tace "A'a yanzu dai zan sha"
"maza jeki sha, kizo ki wuce ki kwanta"
Ta nufi hanyar kitchen, tana tunanin ina zashi a wannan tsohon daren, ta fito ta tarar da shi a falon a tsaye, yace "kinsha ruwan?"
Tace "eh na sha"
"to maza ki wuce, ki tafi ɗakinki ki kwanta"
Harta juya ta tafi, ta waigo taga yana tsaye yana kallon ta, tace "Amma naga kamar fita zakayi, ina zaka yanzu dare yayi sosai"
"Yaushe na fara wasa dake? Ko kuma kika zama uwata da zaki dinga tuhuma ta haka?"
"hmm Daddy kenan, ai kaine kake abun tuhumar, wani irin abune wannan da ba'ayi ido ma ganin ido ba se yanzu a tsakiyar dare haka hmmm Allah dai ya kyauta?"
Ta buɗe ɗakinta ta shige, ta barshi tsaye yana binta da kallo, yarinyar da idan ta ganshi jikinta ke rawa, itace take gaya masa magama haka, tabbas uwarta ce ke zigata kuma zeyi maganinsu gaba ɗaya.
Kamar yadda suka saba haɗuwa yauma sun hallara gabaɗayansu, suna zazzaune a ɗakin Hotel ɗin da ya zamana babu ma me kama shi sesu.
Bukar yace "kyakkyawan labari"
Alhaji Musa yace "muna jinka"
Alhaji Bukar yace "yaron nan yazo hannu"
Sukace wane yaron?
Alhaji Bukar yace "ku duk baku sani ba, dukda yadda da labarin ya yaɗu a daren nan? To ina nufin Yaron nan Yusuf, direbanta wanda aka yi garkuwa dasu tare"
Sukace "Alhamdilillah, abu yayi kyau"
Alhaji Bukar yace "An kamosu a wani ƙauye a Bauchi, inda Saleh ya basu mafaka, yanzu haka yana hannun 'yan sanda, za' a tattare duk wata sheda da ta kamata daga nam za'a kaishi kotu, zamu saki kuɗi ayi masa shari'a da hukuncin daya dace da shi, saboda babu wanda ya ta:a kawo mana cikas da tangarɗa a harkar nan kamar shi, kunga daga nan babu wanda ya isa yace mune muka sa akayi garkuwa dasu"
Alhaji Munir yace "good, wannan abu yayi kyawuuu sosai, kuma ya tafi yadda ake so, dan haka semu hanzarta, mu kuma samu hanyar da zamu ɓalli namu kason tun kan Daula ya bayyana, dan shi har yanzu bamu san fa inda yake ba, kar muje wasu su rigamu karɓa abun nan fa"
Bukar yace "na toshe duk wata hanya da zata saka wani ya mallaki abun nan bamu ba, sannan dole nasa a matsa yaron nan, idan ma abun yana hannunsa ya faɗi inda suke"
Alhaji Musa yace "kai amma abu yayi kyau wallahi, komai ya tafi yadda yakamata"
Alhaji Bukar yace "Haruna ina takaddar da wancan yaron ya bari, ɗan gurin Halima? Shima nasa a nemo shi, duk inda aka ganshi kawai a kawar dashi, bama san duk wani abu da zesa a samu sheda a kanmu"
Alhaji Haruna yai tsilli tsilli da ido yace "Amm.. Mm.. Wallahi an ɗan samu akasine, na rasa inda takaddar ta faɗa amma ina ta ƙoƙarin dubawa"
Alhaji Bukar yace "Amma kasan bana son akasi ko?"
Yace "Ayimin afuwa dan Allah, Insha Allah za'a nemota in kawo"
Alhaji Bukar yace "shikenan, nan da kwana bakwai, na baka isashen lokaci, nan kusa nake so a fara shari'ar yaron nan, ba da nisa ba, kuma ina son a rufe duk wata hujja da zata bayyana mu"
Alhaji Haruna yace "insha Allah, zan kawo takaddar nan ba da jimawa ba"
Haka suka gama tattaunawa sannan suka watse.
Widad ce ke ƙoƙarin farkawa, se jujjuya wuyanta take tana kuka cikin bacci, "Wayyo Allah na, yuzarsef yunwa nake ji, zuciya ta ciwo take, Yoseef dan Allah, dan Allah ka dawo please! Ta farka a gigice tana kiran Yoseef! Yoseef kana inane?"
Bulama ne da Matarsa Hajiya Sarah a gigice suka yi kanta gaba ɗaya, Bulama yace "Sannu daughter, sannu ki kwantar da hankalinki, kin ganni a tare da ke, ga Maman Iman ma, an kuɓutar dake ki kwantar da hankalinki"
"Ni bazan kwantar da hankalina ba, ina mijina yake? Ina Yoseef kace su sakarmin shi, ni ba saceni yayi ba, wallahi idan basu sake shi ba mutuwa zanyi, laifina ne, duk saboda ya ceceni haka ta faru dashi, beyi laifi ba, tun farko seda na gaya masa death contract ne amma ya amince, kaga abunda nake nufi Yoseef, dan Allah ku ƙyaleshi idan wani abu ya sameshi bazan yafewa kaina ba, dan Allah ka cewa Bukar na dawo, ni yazo ya kamani yasa a sakarmin mijina dan Allah "
Tai maganar wasu irin hawaye na ambaliya daga idonta, idanun da suka rine zuwa kalar ja jawur suka kumbure.
Bulama yace "toni ina na san wani Bukar, balle in nemo miki shi? Ke kaɗai kika sanshi, ni ban san a inda yake ba"
Kafin ya rufe baki...
Ayi subscribing YouTube channel ɗina please 🙏 🙏 🙏 🙏
Ayshercool
11/18/21, 7:47 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
108_109
Kafin ya rufe baki ta cire drip ɗin hannunta tayi jifa dashi tace "ni na sanshi, kuma zan nemo shi insha Allah, dole a sakarmin Yoseef ɗina"
Hajiya Sarah tace "haba Widad, baji da lafiya fa, drip ne a jikinki, ya zaki cire ki yar?"
"ni lafiyata ƙalau, ba abunda yake damuna se son inga an sakarmin mijina"
Bulama yace "wai waye mijin naki ne?"
Tace "Yoseef, mijina ne, Aure mukayi dashi"
Hajiya Sarah tace "wane irin aure ba tare da izinin magamabatnki ba? Anya ba ciwon nakine ya tashi ba?"
"Karka ƙara dangantani da hauka, na gaya maka in bahaka ba zan maka haaukan ganin idonka"
Ta diro daga kan gadon zata yi waje, aka Riƙeta da ƙyar tana fizge fizge seta ƙwace ta fita.
Da Alhaji Musa ya koma gida a harabar gidan ya tarar da Nurat a zaune yai parking ya fito ze wuce ta kalle shi ta dauke kai, ya kalleta yace "can't you greet your Dad?"
"I don't think my Dad still loves me"
Yace "why"
"saboda yadda kake treating ɗina kamar ba 'yarka ba" ta ƙarasa maganar tana tashi ta bar gurin ya bita da kallo.
Harta shiga ɗaki taji ta gaji da zaman, ga Khalil yace zezo amma shiru bezo ba, fitowa tayi daga ɗakinta ta haɗo tea, ta dawo falo ta zauna ta kunna TV ta nayi tana ɗan shan tea ɗinta a hankali.
Ta tarar har angama title ɗin news ɗin an fara labaran, sedai ana fara gabatar da labarin su Yusuf jikinta ya hau shaking, gabanta ya shiga dukan uku uku, ai ba'a gama labaran ba ta saki kofin tea ɗin dake hannunta, da ibu zata saka amma ta toshe bakinta, ta shiga ɗakinta da sauri ta kulle ƙofa, zubewa tayi a gurin ta shiga rusar kuka kamar wadda babanta ya mutu, ta dinga kuka tabbas babu ko tantama wannan ƙulle ƙullen mahaifinta ne, wataƙila shine ma dalilin kwanansa a waje jiya, wannan labarin sam babu ƙamshin gaskiya a cikinsa, ta yaya za'ayi garkuwa da mutane kuma an gano su ace Yusuf ne ya saceta baze yuwu ba.
Ta ɗakko wayarta ta shige toilet, ta nemo lambar Khalil, tana kuka Khalil ya ɗaga, yana ɗagawa ta fashe da kuka yace 'Nurat lafiya kuwa, meyafaru ne? "
"bakaga News ba na yau, wanda akayi da safen nan?"
Yai ajiyar zuciya yace "Na gani sister"
"Amma meyasa baka gayamin ba? Kaga abunda ya faru kaga abunda akace Yusuf yayi ko?"
Khalil yace "nagani, bana son in ɗaga miki hankaline, amma tun jiya da daddare na gani, gefw guda kuma Anwar ɗan gidan Hajiya Halima shima ba'asan inda yake ba, duk na ɓoye ne, dan gudun tayar miki da hankali"
Nurat ta share hawayenta tace "Yaya Khalil, ka dena min ɓoye ɓoye, lokaci yayi da zaka temakeni, Khalil mahaifina azzalumi ne wallahi, jiya be kwana a gida ba, nasan saboda wannan dalilin ne, Wallahi idan ba'ayi wani abu a kai ba, rayuwar Yusuf zata shiga garari"
"Nasani Nurat, but am doing my best kinji, bari kinga yanzu zan shigo gidan naku kafin in wuce office"
Nurat tace "No karkazo, ka san shi da zargi, zefara zargin wani abune dan Allah karka zo ka bari kawai, mu dinga communicating ta waya ya isa, bana son ya gane komai"
Khalil yace "shikenan, naji ki kwantar da hankalinki, komai zezo da sauƙi zancigaba da bibiya inga yadda zata kaya"
"Shikenan brother nagode sosai, dan Allah ka ƙara ƙoƙari"
"karki damu sister, Insha Allah i will do my best for you"
Ta jinjina kai ta ajiye wayar, tana ci gaba da jujjuya kai tana tausayawa Yusuf.
Ma'aikatan gidan Alhaji Daula suka rikice jin kabarin abunda ya faru da Yusuf, sun kadu matuƙar gaske dukda wasun su suna jin haushinsa amma a zaman da suka yi dashi sun sanshi da sanyin hali, basa tunanin ze aikata wannan aiki haka.
Ɓangaren Suleiman makuwa ya kaɗu Matuƙa da jin wannan labarin, hankalinsa ya tashi sosai ya tafi headquarter da kansa dan ganin Yusuf, amma fafur aka hanashi ganinsa, dukda shima babban jami'ine amma a kace baze ganshi ba, ana kan gudanar da bincike akansu ne.
Yusuf kam yaci duka da kulki a hannun kuratan 'yan sanda, yama rasa dukan me suke masa? Me suke yai musu su ƙyaleshi, ya daku iya dakuwa ƙafafunsa da bayansa ya gaya masa saboda duka, yana nan gurin a duƙe wani ɗan sanda ya shigo aka ajiye ɗan sandan kujera ya zauna, ya sallami kowa daga gurin, ya ɗan ƙurawa Yusuf ido sannan yace "Malam Yusuf"
Yusuf yai shiru be ɗagoba, yana nan zaune ya durƙusar da kansa.
"Ina so karka bamu wahala, kuma karka bawa kanka wahala, yana da kyau ka amsa laifinka tun a nan dan muyi gaggawar kaika kotu a yanke maka hukuncin daya dace, sannan abu na gaba shine, Widad ta baka bayanin inda dukiyar da mahaifinata ya ware take?"
Ɗago kai Yusuf yayi, ya kalli ɗan sandan, se yanzu ya ƙara tabattar da cewa wannan abun set up ne kawai, an shirya wulaƙant shi ne kawai.
Ya maida kansa ya sunkuyar, yaƙi magana.
Cikin shouting ɗan sandan yace" ba magana nake maka ba? Ta gaya maka ko kuwa, ka sauƙaƙawa kanka ka gayamin suna ina? "
Cikin dakiya da juriya irin na Yusuf, ya sake gyra zamansa ya ƙi kallon ɗan sandan, ai kuwa ɗan sandan nan ya harzuƙa, yasa aka kawo masa kulki, ya ding bugawa Yusuf, Yusuf ya dinga juyi a gurin saboda azabar wahala dayake sha, dan dukan kulkin nan ba ƙaramin shigarsa yake ba, amma sukayi sukayi, Yusuf yaƙi cewa uffan.
Widad kam aka hana 'yan jarida ganinta, aka gama bata magunguna da gwaje gwaje, Bulama ya ɗauketa zuwa gidan sa, Widad sam bata iya ma magana yanzu, haka aka tafi da ita gidan Bulama.
Likitoci suka bada rahoton, wai ta samu raunuka a jikinta, kuma ta galabaita saboda rashin Abinci da azabtarwar da ta sha hannun Yusuf da yayi garkuwa da ita.
Bulama ya tafi da ita gidansa, sedai banda sharar hawaye babu abunda take yi, ƙarshe ma maganar ta gagara, aka bata ɗaki, suna shiga ɗakin ta zube a ƙasa tana maida numfashi, saboda nauyin da taji ƙirjinta yayi mata, ta kalli Bulama tace "meyasa ka kawoni nan?"
Yace "A'a, daughter nanma ai gidanku ne, meye na damuwa kuma?"
"Nan ba gidanmu bane, ina Daddy yake tunda nazo ban ganshi ba, yana ina?"
Hajiya Sarah ta kalli Bulama, shima ya kalleta yace "Amm daughter kin gane, ki kwantar da hankalinki kinji, Daddyn ki yana nan lafiya, kuma yana nan zuwa insha Allah, kedai ki kwantar da hankalinki kawai saboda lafiyarki"
Widad tace "ni babu abunda ya sameni, ka gayamin ina mahaifina yake? Ina Daddy na"
Hajiya Sarah tace "Kaga, Ka gayamata gaskiya kawai, tunda har Allah yasa an gano ta bashi da wani amfani a cigaba da yi mata ɓoye ɓoye, dan haka kawai ka fito ka faɗa mata gaskiya"
Bulama yace "Sarah meyasa kike hakane? Kina ganin halin da take ciki amma kina wani zance daban meyasa kike hakane?"
Hajiya Sarah tace "dan meyasa ba zanyi haka ba, ka gayamata gaskiya mana da wuri, kasan halinta sarai ba baka sani ba, idan ta sani daga baya duk seta ɗaga mana hankali gaba ɗaya gidan nan, ni a yanzu hakama a tsorace nake, kafi kowa sanin halinta"
Bulama yace "koma meye halin nata ba haƙuri zakiyi ba, da 'yar kice haka zaki ce? Kiyi haƙuri mana muga yadda hali zeyi"
Sunata jayayya a tsakanin su, Widad ta zame jiki ta zauna a gurin, tai musu shiru ta lumshe idonta tana jin sautin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri kamar zata tsaga ƙirjinta ta fito.
Bulama ya durƙuso gabanta yace "ki kwantar da hanlinki kinji daughter, babu wata matsala Daddynki yana nan lafiya, zezo inda kike, amma sekin kwantar da hankalinki, kin san baki da cikakkiyar lafiya, mubi komai a sannu"
Idonta a lumshe bata buɗe ba tace "Daddy"
Yace "Na'am daughter"
"kasa a sakarmin Yusuf"
"saboda me? Meyasa zakice a sake shi, mutumin da yayi garkuwa dake, aka samoki da ƙyar a wani ƙungurmin ƙauye, sannan kice a sake shi, baki duba abunda yayi miki bane?"
"Yoseef beyi garkuwa dani ba sam, anyi garkuwa damune ni da shi, ba wahalar da beyi ba saboda in tsira da rayuwata, meyasa yanzu za'ace shine ya saceni? Anyi masa adalci kenan kasa a sake shi please, dan Allah a saki Yoseef bashi da laifin komai fa" ta ƙarasa maganar tana kuka.
Bulama yace "Ni yanzu ta yaya zan fara sakawa a sake shi? 'yan sanda sun fitar da rahoto akan abunda ya faru kawai ace nasa a sake shi, bafa a ko ina ake alfarma ba, yanzu gaba ɗaya case na hannun hukuma, babu abunda zan iya ni"
"Shikenan tunda babu abunda zaka iya, ni zanyi ko zan ƙarar da dukiyar Daula sena fitar da Yoseef, saboda ni ba butulu bace ba, Yoseef yayi min halacci"
Ta miƙe ta kwanta a gurin, tana ta kera gwaron numfashi, wani na bin wani.
Suleiman gidan su Yusuf ya tafi, yana zuwa ya tarar da Umman Yusuf a kwance, an kewaye ta ana yayyafa mata ruwa, sam bata san inda kanta yake ba, ga Asmarta ta tashi tana jan numfashi da ƙyar, an sheƙa mata inhaler amma a banza.
Suleiman yace "Subhanallah, ya ba'a kaita Asibiti ba? Meye ya faru da ita haka?"
Wata maƙociyarsu tace "wallahi yau da Asuba bayan ta idar da sallar Asuba, ya kunna radio taji ance an kama ɗanta Yusuf, shikenan muka jiyo kukanta, muna shigowa harta fara fita daga hayyacinta, numfashi yaƙi tsayawa a ƙirjinta.
Suleiman yace" da ba seku kaita Asibiti ba, koda kuwa na gwamnati ne ba, zata iya rasa ranta fa a haka, maza ku ɗakkota ga mota can, a sata a ciki mu tafi Asibiti "
Haka kuwa akayi, aka sa Umman Yusuf a mota, da wasu maƙotanta suka Tafi Kaita Asibiti.
Suna zuwa aka karɓeta a emergency, aka shiga da ita, likitoci sukayi gwaje gwajen da zasuyi suka ga jininta ya hau fiye da kima, dama tana zuwa shan magani ana duba jinin, tun lokacin da Yusuf ya ɓata ta haɗu da hawan jini.
Yanzu jinin ya hau fiye da kima, ga Asma ta tashi saboda kukan da take yi, gaba ɗaya bata a hayyacinta, a nata ƙoƙarin ganin jinin ya sauka amma abu ya gagara, ƙarshe seda aka haɗa mata da oxygen, da allurai da drip, Suleiman duk ya biya charges ɗin.
Da Safe Amal bata tashi ba se wajen sha ɗaya na safe, ta tashi daga bacci ta tashi da wata irin yunwa, ta tashi ta shiga toilet tayi wanka, ta canza kayan jikinta daga na bacci, har zata fita tace "bari dai in kunna wayata, inga me wannan jakin kuma ya kuma turowa" ta zauna ta kunna wayarta, ta buɗe data messages nata shigowa, amma babu na Alhaji Haruna, ta taɓe baki ta tashi zata fita, sega kiran wayarsa ya shigo wayarta.
Ta koma ta zauna sannan ta ɗaga, Alhaji Haruna yace
"yaushe zanzo in karɓi takaddar nan ne?"
"ba rana ba wata, muddin ba zaka cika sharuɗan dana sama ka ba"
"Waike ynzu 500k ne suka miki kaɗan? Haba ke kuwa dan Allah"
Amal tace "kaga sauraramin, meye wani 500k,duk kuɗin da kake sata na haram kakeci, seni zaka rainawa hankali, wallahi bazan baka takaddar nan a 500k ba"
Aikuwa ya fusata yace "ke wai wace irin yarinya ce, kwana bakwai fa kawai aka bani in kai takaddar nan, ya zakice bazaki bank ba haka akeyi?"
"Kai bari kaji in gaya maka wani abu, wallahi idan baka yi wasa ba sena sa takaddar nan ta zama hujja akanku gaba ɗaya"
"har babar taki?"
"Eh har ita, duk zaka ja muku ne, bari in maka magana ta ƙarshe, wallahi bazan baka takaddar nan ba har se ka bani kuɗin da zaka fanshi budurcina da ka karɓa ta ƙarfi"
"Ke, ni kike gayawa haka? Wace irin magana ce wannan?"
"ai kace min ka ga kaidi iri iri na mata a bariki, to zan nuna maka nawa na dabanne, zan kawo ƙarshen bunsurancinka, wallahi ko inje in haɗa maka masifa da tashin hankali a gurin Alhaji Bukar ɗin, baka san kalar nawa kaidin ba zan gwada maka Akuya kawai"
Ai kasa magana yayi, se bin wayar yayi da kallo, lallai yarinyar nan bata da mutunci sam.
Ta ajiye wayar tace za kaga tsiya ganin idonka, tai tsaki ta saka wayar a caji ta fito falo, Dariyar Mummy taji da Ramlah, Ramlah tace "dara taci gida, sunzo hannu Alhamdilillah, naji ance a ƙungurmin ƙauye aka gano su, koya akayi ta iya zaman wannan ƙauyen oho"
Mummy tace "su suka sani, ni dai tunda an kamo su na fara jin ƙamshin samun kuɗin nan"
Ramlah tace "Ance yana can hannun 'yan sanda ido ya raina fata, tun jiya ya fara cin ƙaniyarsa a hannunsu, ai gara yaji jiki, kafin a shiga kotu ya raina kansa"
Mummy tace "eh Bulama ya cemin idan aka gama bincike kotu za' a kaishi, dan haka ni yanzu ba ta tashi nake ba, ta Anwar nakeyi har yanzu shiru, tunda Amal ta kai musu takaddar basu sake cemin komai ba"
Ramlah tace "zasuyi miki magana ne, bari mu kunna TV mu sake ganin idon munafukin nan, dan ban manta lokacin da ake wulaƙantamu ana cin zarafin mu saboda shi ba"
Ajiyar zuciya Amal tayi, wanda yasa suka juya gaba ɗaya suka kalleta, wucewa tayi kitchen dan Samarwa kanta abunda zata ci.
Mummy tace "Auta ya jiki?"
Ta kalli Mummy ta ɗauke kai, ta wuce kitchen, ta fito daga kitchen tazo ta zauna tace "Mummy, hira naji kuna yi kamar an kama Yusuf ko?"
Ramlah tai farat tace "Eh an kama shi, seme ne kuma? Ko zaki fara wa mutane shirmen naki ne?"
Amal ta girgiza kai tace "No akanme? Ina Ita Widad ɗin take?"
"Tana gidan Bulama, dan shi ze iya wannan haukan nata"
Amal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi ɗakimta, tana jinjina kai, da sauri ta ɗauki wayarta ta shiga social media, aikuwa taga yadda labarin ya cika social media, yadda aka haɗa ƙarya da gaskiya.
Ta ajiye wayar tayi shiru tana tunani, kasa shan tea ɗin nan tayi, se tunani daya dabai baye zuciyarta, gaba ɗaya tausayin Yusuf ya mamaye zuciyarta, tama jin tsohuwar soyayyar sa na taso mata.
"Nurat" Alhaji Musa ya kira sunanta, ta amsa masa da "Na'am Daddy"
"ya maganar shirye shiryen tafiyarki ne, you should preparing for it fa, lokaci yana gabatowa"
"but Daddy, i thought we have discussed this issue since"
Ya kalleta yace "muka ce mene?"
"Daddy na gaya maka ni bana son tafiyar nan, ni ba inda zanje a gida Nigeria zanyi karatun"
"ba zakiyi a nan ɗin ba, ƙasar nan zaki bari, waike yaushe muka fara sainsa dake ne? Ni zance ga yadda za'ayi amma ki bijiremin? To baki isa ba nina haifeki bake kika haifeni ba"
Ya dinga banbamin bala'insa, yayi ya gama tsaf bata sake cewa komai ba, seda ya gama tukuna sannan ta miƙe ta bar masa ɗakinsa, tana zuwa ɗakinta tace 'wallahi ba inda zanje, bazan bar ƙasar nan ana wannan halin ba, se naga abunda ya turewa buzu naɗi"
Yusuf kam ya daku a gurin jami' an tsaro, akan lallai seya amsa shine ya sace Widad, amma Yusuf ƙemem yaƙi magana, dama shi Saleh ba'a maganarsa saboda ya galabaita fiye da Yusuf ko magana baya iyayi, bama shi da lafiya.
Juyin duniya Yusuf ya amsa shine ya sace Widad yaƙi, yaƙi ko ɗaga kansa ma balle yayi magana.
Mutumin da yake jibgarsa yace "ga 'yan jarida cam suka cika harabar gidan nan, zamu basu lokaci suyi magana da kai, ka furta kaine ka sace yarinyar nan koka samj sassauci, idan kuma kaƙi to haka zamu ci gaba da casaka a gurin nan, gara ka nemawa kanka mafita, ka amsa kai ka sace ta"
Yusuf dai beyi magana ba, aka taso ƙeyarsa a gaba aka saka masa handcuffs hannu da ƙafa, aka fito da shi harabar headquarter na 'yan sanda, fuskarsa duk ta kumbur saboda duka.
' yan jarida sun cika gurin nan, suka kewaye Yusuf da abun magana, kowa yana yanko masa tambaya, wasu ta gaske wasu ta cin mutunci, amma Yusuf yai shiru, sukayi sukayi har suka gaji, har ya juya za'a maida shi ya tsaya ya waigo, ya kalli' yan jaridar nan yace "Bani na sace ta ba"
Kawai ya juya, ds ƙyar 'yan sanda suka dakatar da' yan jaridar nan aka mayar da Yusuf inda aka ɗakko shi.
Nurat gaba ɗaya ta tayarwa da Khalil hankali akan maganar Yusuf, ga koke koken da take akan batun komawarta karatu, tana ta saƙawa da warwar akan ta gudu ta bar gidan gaba ɗaya, amma sedai tasan idan tayi hakan ba zata sake daraja a idon mutane ba.
Alhaji Haruna duk ya shiga damuwa da tashin hankali, akan takaddar nan da Amal keta rainamasa hankali akan ta, ya shiga part ɗin Amaryarsa ya tarar da ita ta ƙurawa TV ido cike da damuwa, ya zauna kusa da ita yace "Baby kallo ake ne?"
Ta ɗan ɓata fuska tace "ina kallon wani abune daya tsayamin a zuciya, wannan bawan Allah da aka kama akan 'yar gidan Daula ya tsayemin, i can't imagine ze aikata wani abu makamancin haka, ƙarya ce kawai akayi masa"
Yace "ke ya akayi kika san ƙarya akayi masa? Wannan shine abunda ya dace dashi, kuma zamu tsaya kai da fata se an hukunta shi anyi maganin irinsa a cikin al'umma"
Ta kalle shi tace "Nasan Yusuf, fiye da yadda kake tunani, inaga mahaufiyarsa ce kawai zata fini sanin waye shi, wallahi wannan maganar ƙarya ake masa, mutumin da yake kamar waliyyi dan haƙuri, wannan maganar ƙaryane wallahi"
Alhaji Haruna yace "Salma meye haɗinki dashi da kike wannan zaƙewar, meye haka kike yi akansa, kuma a gabana?"
Ta Harare shi tace "Yusuf unguwar mu ɗaya, kuma tsohon saurayi nane, wanda aka hanani Aurensa aka ƙaƙabamin kai"
Kawai ya kwashe da dariya yace "lallai baki da hankali, aikuwa kina ji kina gani ze tafi prison Salmata, sedai haƙuri"
Ya tashi ya barta a gurin, tausayin Yusuf ya kamata, tasan Yusuf baze taɓa aikata abunda akace yayi ba.
Widad tana zaune kamad wata mahaukaciya, tun jiya da safe rabonta da Abinci, tana jin yadda zuciyarta take bugawa ba daidai ba, tai shiru tunani da tausayin Yusuf ne yake ta ratsa zuciyarta.
Iman ta shigowa da Widad da Abinci tace "ga Abinci, ki daure kici dan Allah"
Widad tace "kiramin Bulama, zamuyi magana"
Iman tace to, befi mintuna biyar da fitarta ba sega Bulama ya shigo ɗakin, yana shigowa ya kalleta yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Widad har yanzu bakya cin Abincin, subhanallah ko mota za'a ɗakko mu tafi Asibiti ne?"
Tace "wani hali Mijina yake ciki?"
Bulama yace "waye mijinki kuma?"
"Yoseef" ta bashi amsa
"yaushe kikayi Aure bamu sani ba?"
Cikin tsawa tace "ka dena amsamin tambayata da tambaya, ina Yoseef yake?"
Bulama yace "yana hannun hukuma har yanzun"
Ta miƙe tsaye tace "har yanzu baka yi komai a kai ba ko? Ni ka maidani gidan mu gurin Daddy na, shiyasan ranar da Yusuf yayi masa, baze bari ya cutu ba akan laifin da beyi ba"
Bulama yace "kinga ki kwantar da hankalinki".
"Karka ƙara cewa in kwantar da hankalina, ina Alhaji Nasir Daula yake? Ina babana Daddyna nake maka magana, yana ina? Ta yaya za'ace tun jiya har yanzu babu shi babu dalilinsa bezo inda nake ba"?
Tai maganar a jere bako haɗiyar yawu, tare da ɗaga murya sosai.
Bulama yace "kinga zauna kici Abinci tukuna"
Ai be rufe baki ba tasa ƙafa tai ball da kayan breakfast ɗin, ta riƙe gaban rigar Bulama tace "ka gayamin gaskiya, ina Daula yake? Idan an kashemin shine ka gayamin, yana ina? Ina yake ina Daddyna?!"
Jin Hayaniya yasa tuni mutan gidan suka fara taruwa a ɗakin, Hajiya Sarah tace "babanki Nasir Daula, tun bayan ɓatanki ya kwanta rashin lafiya, aka bishi har gadon Asibiti aka sace shi, har yau babu wanda yasan inda yake"
A hankali Widad ta saki rigar Bulama, tana kallon Hajiya Sarah "Annn. An sace Daddyn Widad a gadon Asibiti, this serious, Daddyn how comes? Ta yaya za'a sace shi ba wanda ya sani, shikenan na rasa Yoseef ɗina, Daddyna ma ace ba'a ganshi ba, Noooooo! This impossible!!!
Tana maganar ta silale ta faɗi ta ruf da ciki, ko numfashi ba tayi.
Ayi haƙuri ba editing
Ayi subscribing YouTube channel ɗina dan Allah, me suna Cool Arewa TV
11/21/21, 7:45 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
110_111
Me Adda ya kawowa mutumin kujera ya zauna, ya kalli Saleh yace "ka dena mamaki mana, ai bekamata kayi mamaki ba, a zatonka kai kaɗaine me wayo, ko kuma kafi kowa wayo? Kifi na ganinka me jar koma, kallonka kawai nakeyi"
Saleh yace "hmm Bukar kenan, kaima kuka karya Alƙawari balle ni, haka mukayi daku? Ashe kun kashe min ɗan uwana, banma sani ba balle kua bamu gawar muyi masa sitira, dama haka akeyi, kunyi amfani dani ne dan cinma burinku?"
"ƙwarai kuwa, muna amfani da kaine dan cinma burinmu, kai bari in gayamaka wani abu, ku duka wanda nake aikin harƙallar nam daku, ina amfani da kune dan cinma burina nikaɗai, na ɗaukeku karnukan farauta tane kawai "
" Amma wallahi Bukar baka da imani, baka da adalci "
Me Adda ya yunƙura ze kaiwa Saleh duka amma Bukar ya hana shi yace "ƙyaleshi, ai baaka ga komai a cikin ƙudrina da AƘIDATA ba, kuma dama tuntuni kowannen ku nayi masa tanadin makomarsa idan deal ɗinmu ya kammala, sedai kai kayi gaggawa gurin riskar taka makomar, tunda ka yaudareni kaci amanata zaka riski makomarka a nan kusa, ina Widad take? "
Saleh yai masa wani irin mugun kallo yace "ni ka bawa ajiyarsu kokuwa? Kaje ka tambayi wanda aka sa su sacesu gasu nan a gabanka"
'bana son in wahalar da kai kafin ka mutu Saleh, ko dan irin wahalar da kayimin, amma gaddama da taurin kai zesa in maka uƙuba wadda zata yi ajalinka, Saleh kaine ka bawa Widad da direbanta mafaka, kasan inda suke kaine ka kuɓutar dasu, dan haka karka wahalar dani, ko ka wahalar da kanka kafin ka mutu, ka gayamin ina ka kaisu"?
"Ni bani na ɗauke su ba, ban san inda suke ba, dan haka karka ƙara tambaya ta na gaya maka"
Bukar yace "Shikenan, tunda baka san rarrashi ba, bari a biyo maka ta inda ya dace, Me Addda ku gasamim shi tsawon kwana uku, muga iya juriyarsa a mtsayinsa na kurtun soja"
Daga nan Bukar ya tashi ya fita daga ɗakin suka rufa masa baya.
Amal tana ta sauri taje ta kai takaddun nan, daga nan ta kai wadda aka bata ta kaiwa Alhaji Haruna, yamma ta fara yi sosai kuma bata son Mummy ta kama faɗan nata akan bataje aiken da tayi mata da wuri ba, dan haka a harabar gidan gurin shiga mota ta ƙarasa saka takaddun a jakarta, da wasiƙar gurin Anwar, da takaddar form ɗinta, ta buɗe mota ta shiga ta fice.
Unguwar da guest House ɗin Alhaji Haruna take shiru babu mutane a unguwar, duk se kangwaye da sababbin gidaje, bata kawo komai a ranta ba tace bari taje ta fara kai masa tasa takaddar, daga nan kuma seta je gurin nata kai takaddar.
Tana zuwa megadi ya buɗe mata gate ta shiga, tace "yana nan kuwa?"
Megadi yace "Eh yana ciki"
Ta fito daga motar ta shiga, ta murɗa ƙofar falon tare da yin sallama, sedai babu kowa a falon, ta nemi guri tayi zamanta a falon, shiru shiru babu wanda ya fito, ta tashi ta koma gurin megadi tace "Anya kuwa yana nan? Naje nayi sallama amma shiru ba'a amsa ba"
Megadi yace "ai be fiye zama a falon ba, ki shiga yana ciki"
Tace "Cikin ina? Kaga ungo bari in baka takaddar ka ajiye masa"
Megadin yace "rufani ki saya, ai be yadda in karɓi kowane saƙo ba idan bashi yace ba, ki buɗe ƙofar dake cikin falon wasu falukan ne a ciki fa"
"kaga muje ka rakani da kanka, ni bazan shiga ni kaɗai ba"
Yace "shikenan muje"
Ya rakata, yana gaba tana bin bayansa, suka dinga ratsa faluka, sukaje wata ƙofa yace "yawwa a nan yake ganin baƙi, ki shiga ki bashi"
"kazo dai mi shiga tare, danni bazan iya maida kaina waje ba, wannan gida duk lunguna kamar gidan matsafa"
Yace "A'a shiga dai ki fito, ina nan ina jiranki"
Tace "to shikenan"
Ta buɗe ɗakin ta shiga da sallama ashe bedroom ne, ya amsa mata yana zaune akan gado yana danna system, yana ganinta ya faɗaɗa murmushinsa yace "Ashe kinzo, ai tun ɗazu nake jiranki" yai maganar yana binta da kallo.
Haɗe rai tayi tace "eh nazo, ina falo ne ga takaddar tace akawo maka"
Alhaji Haruna yace "ok kawomin nan"
Ta ƙaraso tana zumɓura baki, ta sa hannu a jakarta ta ɗakko takaddar, ta ƙarasa inda yake ta miƙa masa takaddar, sedai me se ya haɗa da hannunta, ya riƙe.
A fusace ta kalle shi tace "meye haka kuma? Dalla malam sakeni"
Yace "haba Baby, gaki kamar wayayyiya amma kina wani kidahumanci, ki kwantar da hankalinki karki ji komai kinji"
"Dalla ka sakeni ko in maka ihu wallahi"
Yai murmushi yace "to idan kinyi ihu kina tunanin akwai wanda ze kawo miki ɗauki ne? Ba wani abu fa rainane ya biya kawai, ki kwantar da hankalinki kici Arziki ki barshi"
Kici kicin ƙwacewa ta shiga yi amma ya riƙeta gama, yana wani lashe baki kamar kare yace "'yar uwarki ta fiki wayewa, ke kamar ba' yar birni ba"
Ya fara ƙoƙarin rabata da kayan jikinta, sosai Amal take ihu tana ƙwacewa, tana rirriƙe jikinta tana kururuwa, amma tsohon najadun nan ko a jikinsa, burinsa kawai ya cimma burinsa, Amal ta dunƙule hannu ta dinga kai masa naushi kota ko ina, wani naushi data kai masa a ido a gigice ya sake ta, yaja da baya, ta durƙusa tana ƙoƙarin mayar da kayanta, kuma taso mata yayi haiƙan yana kuma riƙeta, sosai kokawa ta ka came a tsakanin su, ya hankaɗata ƙasa ta faɗi akan hannunta, ta kurma wani uban ihu, saboda azababben zafin da taji ya ratsa hannunta, haka ta kuma yunƙurawa ta miƙe sedai ta kasa ɗaga hannun nata, ganin zata hana shi rawar gaban hantsi, be tausayawa halin da take ciki ba, ya shammaceta ya buga mata kwalba a goshi, ta kuma kurma ihu ta baje a gurin a sume.
Yusuf seda ya kwana biyu sannan ya iya cigaba da fita, sedai wata irin shaƙuwa da kusanci ne ke ƙara shiga tsakaninsa da Widad, wata irin kulawa take bashi ta musamman wadda bata masa a baya, ga Jamila dake ƙara sata a hanya yadda zata dinga kula da mijin ta, gefe guda kuma ta tara ɗalibai sosai, idan yamma tayi cika gidan megari ake yara da manya tana koyar dasu ilimin addini dana zamani.
Yau Widad ta haɗa kayanta dana Yusuf ta wanke su tsaf, gwanin ban sha'awa.
Yusuf ya dawo a gajiye, yana dawowa ya tarar da Widad harta dafa ruwan wanka ta ajiye masa.
Yusuf yayi murmushi yace "Waini wannan kulawar da ake bani fa, nifa abun yana mamaki, an maida ni wani ɗan gata meye sirrin ne?"
Widad tai masa fari da ido tace "tukuici kawai zaka bayar, if you really appreciate"
"to me akeso in bayar?"
Ba tace masa koma ba se murmushi da tayi, tana sake kashe masa ido, Yusuf yace "Ohh my God, wannan kallon da kikemin se in rasa ina zan sa kaina, gaba ɗaya narkamin zuciyata yake Baby"
Widad tai dariya tace "shagwaɓaɓɓe kawai, ji yadda yake magana kamar wani Baby"
"Baby ne mana, tunda na auri Baby nima na zama baby ai"
"Naji, je kayi wanka kazo in baka Abinci a baki zaka ci?"
"zan mana, dayawa ma zanci sosai tunda Baby ce zata bani a baki"
Yai murmushi ya fice daga ɗakin, yaje yayo wanka ya dawo ɗakin, sedai ya tarar bata ɗakin tana tsakar gida, yana zuwa yaga babu kayansa, ya duba Akwatin Widad yaga kayansa a wanke, ya ɗadɗaga ya haska yagansu a wanke fes, mamkine ya kama shi, ya fito ya ƙwala mata kira, ta taso taje Yusuf yace
"My Wife, gani nayi kamar an wanke min kaya, ya haka?"
Widad tace "to meye yafaru? Ko laifi ne?"
"Amma waye ya wanke min? Nidai nasan baki iya wanki ba, ni nake mana to yaya akayi aka wanke su?"
"Shikenan kuma a haka zan zauna ban iya komai ba,? To in gaya maka na iya aiki sosai yanzu, nice nan na wanke mana su ɗazu"
Yusuf yace "abun mamaki, yanzu ke kika wanke mana kayan nan duka? Ina mamaki fa"
"wallahi nina wanke mana, ko basu fita bane?"
"Ni na isa ince basu fita ba, sun fita fes, amma baki saba ba karki sake wankewa, zan wanke mana da kaina kinji matar Yusuf"
"A'a gaskiya, ni dai sena wanke"
Yace "bafa na son gaddama, kawai ka bari nagode Allah yayi albarka, amma ni zan dinga wanke mana kinji beautyna"
"A'a ai kai ba bawana bane, dan haka nima yakamata in dinga ƙoƙartawa, tunda ina iyawa ai bakomai kai ba murna zakayi ba ina koya ba"
Yusuf yace "naji amma ki bari mu dingayi tare, kinji Babyn Yusuf"
Tace "to naji"
"Yawwa Babyna I love you" yai maganar yana kissing din goshinta, bata bashi amsa ba se murmushi da tayi, tana lumshe ido, babban abunda yake bawa Yusuf mamaki da ita be wuce yadda idan har yace yana sonta, sedai tayi murmushi amma ita ta kasa gayamasa hakan, har yanzu yakasa gane haƙiƙanin abunda yake ranta, sedai yana ganin kishinsa da tausayinsa muraran a idonta, sedai tausayi da kishi suna cikin alama na soyayya.
Widad tace "zauna inzo in baka abincin, naga kwana biyu ba kaci kana ƙoshi, bana son mu koma gida a ganka a rame, bazanji daɗi ba, aga nayi ƙiba mijina kuma a rame ba'"
Yusuf yace "inyee kaga masu miji, kamar ba mutum ne yake cewa shi be yadda da Aure ba, baze aura ya zauna a ƙarƙashin wani ba, kawai se naji mutum yana cewa ina son Aurena Yoseef, Zan zauna da kai a yadda kake, ya akayi mutum ya canza ra'ayi ne haka da sauri?"
Murguɗa baki tayi tace 'bana son tsokana fa"
Yusuf yayi dariya yace "gayamin meyasa kike son Aurennaki ne? Gayamin mana"
Widad tace "nima ban san yadda akayi haka ba, a baya ina da dalilin da yasa nace bazan yi aure ba, amma yanzu na samu mijin marainiya, wanda yake lallaɓani ban yaɓa zaton akwai miji irinsa ba, ka bani farinciki mara misaltuwa, shiyasa nake jin kamar bazan iya bari kayi nesa dani ba, shiyasa nake son Aurena "
Yusuf yayi murmushi yace "Mutum ma ya faɗi gaskiya ma, se wani kauce kauce kike, zama ki faɗi gaskiya ne ai"
Widad ta buɗe baki tace "ba ruwana, Allah ya shiryeka, a haka kaman salihi amma mutum yaita sakin magana"
"Kyaji dashi dai, ni dai azo a bani Abincina inci yunwa nakeji"
Ta zauna tana bawa Yusuf Abincin sa a baki, suna hirarsu cikin nishaɗi da jin daɗi.
Amal kawai farakwa tayi ta ganta akan gadon Asibiti, taga kanta nannaɗe da bandeji, hannunta ma data faɗi akai haka, mamkine ya kamata ta juya ta ganta a ɗakin Asibiti a kwance, ga wani irin raɗaɗi da yake ratsata daga tsakanin ƙafafunta.
Shiru tayi taga Mummy ta shigo ɗakin hannunta da ledar magani, ta ƙaraso da sauri tana Autana sannu, ya jikin naki ne?"
Amal tace "Mummy meya sameni ne?"
Mummy tace "hatsari kika yi mana Baby, ina zaune a gida Alhaji Haruna yayi min waya yacemin bayan kin kai masa takaddar, kika samu hatsari a titin unguwarsu"
Wani uban ihu ta saki, da tuno abunda ya faru tsakaninta da Alhaji Haruna, ya mata fyaɗe kenan, kuma yake gayawa mahaifiyarta hatsari tayi.
Ta fashe da kuka, tana jujjuya kanta, wani irin baƙin ciki ne da takaici ya mamaye mata zuciya.
Mummy tace " Haba Amal, kiyi haƙuri dan Allah, ai abun be tsawwala ba Autana, karaya kika samu a hannu se kwalba daya fasa miki goshi, Ai Alhaji Haruna yayi mana mutunci, shiya kawoki Asibitin nan"
Kawai Amal ta dinga kuka, ji tayi kamar ta shaƙe mahaifiyarta jin maganar da take, ya cuceta ya kassara rayuwarta, ya raba ta da mutuncinta, kuma ya kawota Asibiti yace hatsari tayi, ji tayi kamar zuciyarta ta tsaga ƙirjinta ta fito saboda azabar baƙinciki da takaici, tama rasa me zata yi, kawai ta fasa ihu ta fizge ruwan dake jikinta tayi jifa dashi, ta dinga wani uban ihu, da ƙyar aka kira likitoci, aka daddanneta akayi mata allurar bacci.
Mummy ta kalli likitan cike da damuwa tace "Doctor, wai dan Allah meyasa meta ne? Naga kamar ta haukace"
Likitan yace "A'a ba haukacewa tayi ba, stress ne da damuwa suka ɗan dameta amma insha Allah komai zezo da sauƙi, zamu sake mata hoton hannun, idan hali yayi a goben ma insha Allah zamu iyayi mata aikin, tunda Alhaji Haruna ya gama biyan komai, dama anan yake da family file "
Hajiya Halima tace
"shikenan, mungode nidai Alhamdilillah tunda ba wani abunne ya sameta ba"
Bayan sallar isha'i Yusuf ya shigo, ya tarar da Widad a kwance ta kunna fitila, tana ta saƙa maficinta daga nan inda take kwance, yai sallama ta amsa, yana zuwa ya kwanta a kanta.
Cikin Shagwaɓa tace "wayyo Allah na, Yuzarsef meye haka? Kana fa da nauyi seka danne min kan Babyna"
Yusuf yace "wainine nake da nauyi, ina wani Baby yake anan?"
Tace 'ba a nan mana" tai maganar tana nuna masa cikinta.
Yusuf yasa hannu ya danna cikin nata yace "Malama bakomai anan hanji, waye yace miki a nan ɗa yake zama"
"wayyo Allah na, Yoseef yau cinzali kake ji, dan Allah ka dena danna min cikina, kar kasa in haifi ɗa da lotsatsen ƙeya mana"
Yace "Madam wannan cikin naki bakomai a ciki, inma akwai be zama mutum ba, amma duk kin ishi mutane, ke wannan idan cikin ya samu na shigesu, da langwai da Shagwaɓa"
Widad ta tura baki tace "Yuzarsef, da nace zan sakawa jaririna sunanka, amma na fasa tunda kana adawa da baybn nan nawa"
"Au da bazaki saka sunan Daddy ba, se sunana?"
"Eh mana sunanka zan samasa mana"
Yusuf yace "salon Daddy yace kinfi son mijinki akansa"
Tace "to ai dai ɗana ne naga, ko ɗan Daddyn ne?"
"Iyee, ba kara ba kunya Baby, Allah ya shiryeki wallahi za'aga uwa mara kunya gaskiya"
Tace "eh naji ɗin, ni ɗagani karka samin ɗa kuka"
Yusuf yace "iko se Allah, wai yanzu ke kin haƙiƙance ɗane a cikinki? Kwana nawa kika ƙara baki period ba?, ina shekaranjiya kika cemin mararki na ciwo baki period ɗinba?"
"Ai bezo ba tukuna, kwana biyar ya ƙara fa, Insha Allah ina da ciki"
Yusuf yace "mara kunya kawai" yai maganar tare da danna gefen mararta ɗaya, wani irin ihu tayi haɗi da zillo, se hawaye, Yusuf ya bita da kallo yana nazarinta.
Cikin hawaye tace "Yusuf meye haka? Da zafi fa wallahi"
Yusuf yace "yi haƙuri, am sorry kinji babyna, yi haƙuri bazan sake ba insha Allah, abu nake son ji"
"Ni ƙyaleni, kawai se cin zalina kake, kuma bazan kwana da kai ba a katifata ba, tunda haka ka koma"
"Ke kin isa ki koreni daga kan katifar nan, ina nan tare zamu kwana semun samo Babyn Baby"
"Ni na samu Babyna in gaya maka, kuma sena rama abunda kayi min, ni wanka zanje inyi"
Yusuf yace "ina nan ina jiranki, kije kiyi wankan kizo kimin tausa inyi bacci"
"bazan ba" tai maganar tana hararasa, sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin tana murmushi.
Haka suka kwana tare abunsu, cike da soyayya da ƙaunar juna, tana sake jin Yusuf a zuciyarta, bata jin zata iya rabuwa dashi.
Saleh kam iya azaba ya shata, su ciko bokiti su danna kansa a ciki, seya suma, banda wutar lantarki da suka dinga jona masa, ga ba Abinci babu ruwan sha, ya galabaita fiye da tunani, banda duka da suke masa da katakwaye, sun masa laga laga gaba ɗaya Saleh ya zama abun tausayi, ya galabaita ya lalace saboda azaba, suyita buga masa itace a ciki, kai da ƙirjinsa, ya dinga fidda jini ta baki da hancinsa, gaba ɗaya ya suma baya hayyacinsa a haka se da aka kwana uku, sannan suka yi waya suka sanar da Bukar, yace musu yana nan tafe zezo gidan da ake ajiye da Saleh yaji idan yayi laushi zuwa yanzu.
"Alhaji Bukar, kana sane da cewar mahaifinmu yazo har gidanmu ya saka hannu ya mareni?"
"Eh, naji na samu labarin zuwansa, amma ni sam ban san da zancen ya dakeki ba"
Ramlah tace "to ya saka hannu ya dakeni, bayan tsawon shekaru be san cina shana ko suturata ba, an gayamin cewar hatsabibine, dan haka sonake in nuna masa ya haifi wadda ta fishi hatsabiban ci"
Alhaji Bukar yace "Anya zakifi mahaifinku hatsabibanci kuwa? Amma me kike so ayi masa?"
"Sonake a nemo shi duk inda yake, a sauke masa hannun da ya mareni dashi"
"Amma fa naga mahaifinkine, idan kikayi haka baki kyauta ba"
"Naga dai shima ba mutumin kirki bane, koda bama tare dashi, labarin aika aikar dayayi duk na sani, dan haka rama cuta ga macuci ibadane, zan kawo ƙarshen iya shegensa, a sauke masa hannu nake buƙata"
Alhaju Bukar yace "kin samu yarinya, kije kin kwantar da hankalinki, za'ayi abunda ya dace, yadda kike so haka za'ayi ai".
Koda Amal ta sake farkawa ta ganta a Asibiti ta tabattar ba mafarki take ba, ta sake fashewa da kuka, ta tuna yadda suka yi da Alhaji Haruna, shikenan Ya kassara mata rayuwa, ya cuce ta, ya gama da ita, tinƙahon kowace mace shine budurcinta amma a banza wani tsohon najadu dabba ya kassara mata rayuwa, ya tarwatsa mata rayuwa ya cuceta, wasu irin zafafan Hawaye suka shiga yi mata sintiri a fuskar ta, tana tunanin me zata yiwa Alhaji Haruna ta huce, me zata yi masa wanda zesa ta huce, ita gaba ɗaya Yusuf ta tanadar wa kanta, saboda babu komai a zuciyar ta inba shiba, dole tayi wani abu wanda zaya rama abunda Alhaji Haruna yayi mata.
Ramlah ta kalleta tace "Amal wai wannan wani irin kukane haka? Ki saurarawa kanki mana, Allah ya taƙaita miki wahala baki mutu ba, kuma hannun be cire gaba ɗaya ba, amma se kuka kikeyi, ki kwantar da hankalinki dan Allah kiyi haƙuri.
Mummy da ta idar da salla tace " tayani gaya mata dai Ko zataji, tunda abun nan ya faru take kuka, na rasa kukan ubanme take haka? Ni kin kai masa takadda makuwa kafin abun ya faru?"
Banza tayi mata, ta ɗauke kanta ta cigaba da kukanta, Alhaji Haruna ne yai sallama, ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, hannunsa ɗauke da manyan ledoji, ya shigo suka gaisa da Mummy, yace " Ya jikin Auta kuwa? "
Mummy tace "Jiki da sauƙi, sedai se kuka take, taƙi yin shiru, kuma ga abun be tsawwala da yawa ba, karayace kuma ance yau za'a mata ɗori"
Alhaji Haruna ya zauna a gefen gadon yace "Auta ya jikin naki?"
Lallai mutumin nan ya cika gardin ɗan iska, ya mata wannan aika aika, sannan yazo wai yazo dubata, shiru tayi taƙi magana.
Hajiya Halima tace "Amal ba magana ake miki ba kika yi shiru? '
Alhaji Haruna yace "Halima ku ɗan bamu guri dan Allah, zan mata magana"
Ba musu suka fice, sedai kallo Ramlah ta dinga binsa dashi na tuhuma.
Yace "Haba Baby, daga abu ya faru shikenan seki ɗaga hankalinki, haba Baby Amal, kiyi haƙuri kinji ai is not that painful, zaki warke kuma karayar nan is just an accident, zaki warke insha Allah, amma kidena kukan haka kinji"
Ji tayi kamar ya kunna wuta a zuciyarta, tabbas ds da makami seta kasheshi kome za'ayi mata ayi, ga mahaifiyarta sam batayi hankalin gane abunda ya faru ba.
Ganin tayi shiru, yasa ya janyo ya jikinsa yana faɗin "you make my day jiya, na daɗe ban samu mace kamarki ba, ki kwantar da hankalinki mucigaba da rayuwar mu babu wanda ze gane kinji"
Amal tai shiru, taƙi buɗe ido zuciyarta ta dinga tafasa, ganin tayi shiru batayi magana ba, yasa seda yayi shagalinsa sannan ya dunƙulo bandir ɗin kuɗi ya zube mata.
Seda yaje bakin ƙofa ze fita tace "idan ba'a gaɓa gwada maka kaidin mace ba, ka fara ƙirgawa daga yau zaka fara gani, wallahi Haruna sena maka abunda bazaka manta ba har abada, sena maka Baƙin tabon da yafi wanda kayi min, wallahi sena ƙulla maka makirin da duniya basu isa su kwance maka ba, zaka gane baka da wayo daga maina bazaka sake gwada akuyanci akan wata 'ya ba, ka saurareni....'
.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/21/21, 7:45 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
112_113
Alhaji Haruna yai murmushi irin na tsofaffin 'yan duniya sannan yace
"hmm Yaro man kaza, wato shi dai yaro yarone kam, ke a gwagwarmayar da nayi, babu kalar karuwar da ban gani ba, babu kalar barazana da kaidin matan da ban gani ba, nayi Aure Aure, nayi biye biye ba irin matan da ban gani ba, dan haka' yar ƙaramar barazanar ki bazata tsoratani ba, you better calm yourself down, ba'a kanki aka fara ba kuma ba'a kanki za'a ƙare ba, karki ƙarawa kanki ciwo akan ciwo, ki kwantar da hankalinki ki more ƙuruciyarki ki tara abun duniya"
Wani gululun baƙin ciki ne yazo ya tokare maƙogwaron Amal, wanda yasa ta jan numfashi da kyar, ta rasa me zata yiwa Alhaji Haruna wanda zesa taji ta rage azabar da zuciyarta ke mata, ga karaya data samu ga rauni a kanta, ga uwa uba fyaɗe da yayi mata, kuma yazo ya tsaya yana gayamata maganar banza, ta lumshe idonta wasu irin hawaye na takaici da baƙin ciki suna bin gefen idonta.
Tana jinsa ya buɗe ƙofar yai waje abunsa hankalinsa kwance wani nishaɗi yana ratsashi, dan ba abunda yake ji na damuwa ko tashin hankali a tare da shi dangane da abunda ya aikata.
Kusan mintuna ashirin da fitarsa, Ramlah tai sallama ta dawo ɗakin, ta janyo kujera ta zauna a gaban gadon Amal, Amal tace "Ina Mummy ne?"
"Taje gida zata yi wanka ne, ta canza kaya"
Amal ta jinjina kai, tana sake jin wani irin zafi a hannuta da ƙasanta, ta ɗan rintse ido tana girgiza kai, an mata illar da bazai taɓa gyaruwa ba ta gyara kwanciyarta tana ajiyar zuciya
.
Ramlah ta kalleta tace "Amal meye tsakanin ki da wannan mutumin ne, naga fa kamar akwai damuwa a tare da ke? Meyafaru ne"
Girgiza mata kai tayi tace "bakomai"
Ramlah tace "ki gayamin gaskiya, ko akwai taimakon da zan iyayi miki, naga kamar akwai wani ɓoyaayyen al'amari a tsakaninku ke da shi, naji yana yiwa Mummy wasu maganganu ne marasa kan gafo, wai ai shi ya gani yana so, wai idan zata bashi ke yana so, ni ina tunanin ma wannan hatsarin da akace kinyi, gaba ɗaya na kasa yadda abun kamar wani shirin film ko tatsuniya fa"
Amal taji kamar ta gayawa Ramlah gaskiya, se taga yin hakan tamkar tonawa kanta asiri ne, kuma idan harta nemi taimakon wani, to bata cika mace ba, yakamata ta nunawa Haruna tsantsar kaidi da makirci irin na 'ya mace.
Amal ta dake tace "Idan ma yana nufin sona yake, gaskiya ni bazan auri tsoho kamarshi ba, amma in dai zan fizgi rabona a jikinsa ai shikenan, zan iya biye masa nima in tatsi arziki som raina, Amma dan Allah ki temakamin da ruwan zafi mana, zan gasa jikina, dan duk ciwo yake min"
Ramlah ta jinjina kai, taje samo mata ruwa me zafi ta rakata banɗaki, da ƙyar ta iya kintsa jikinta, saboda karayar hannunta, ga ciwo da kanta keyi, haka ta tsaya tai kuka me isarta a toilet sannan ta fito.
Saleh ya jigata sosai, Alhaji Bukar yaje yaga halin da Saleh yake ciki seda ya ɗan tsorata, dan kar Saleh ya mutu, dan muddin Saleh ya mutu shikenan, abubuwa sun lalace, dan haka yasa aka kira likitansa, ya duba shi yai masa allaurai ya samasa ruwa, da ƙyar Saleh ya farfaɗo koda ya farfaɗo ruwan leda ɗayane se garau garau na shinkafa da aka kawo masa, mutumin daya kwana uku babu abinci, amma ya faraka a bashi bushshsiyar shinkafa da wake, abunka da me jin yunwa ya kama Abincin nan ya dinga turawa, sedai ba'aje ko ina ba yaji kamar yana cin duwatsu ne, dan haka ya dinga aman abincin nan, Saleh ya galabaita sosy, dan kwanakin nan gaba ɗaya a ɗaure yake a igiya kamar rago, dan haka kowace gaɓa tasa ciwo take masa, ga shedar igiya ta fito raɗa raɗa a jikinsa duk fatarsa tayi jajawur, ga ciwon ƙirji saboda dukan da yake sha da katako kamar Ɓarawo.
Bukar ya kalli Saleh yace "wuya koda magani ba daɗi, ina fatan zuwa yanzu ka ɗanɗana kuɗarka kuma zaka bani haɗin kai, ka gayamin abunda na buƙata, ko kuma in sa a ninka maka wannan azabtarwar da ake maka.
Shiru Saleh yayi beyi magana ba, se suka numfashi dayake na wahala, yayi zuru zuri dashi kamar wanda yayi amai da gudawa, maganar duniya Amma Saleh yaƙi cewa uffan.
Me Adda yace "wai ba zakayi magana ba, semun ƙarasa sauke maka allon ƙirjinka?"
Bukar yace "saurara tukuna, wannan idan aka yi ƙwaƙwaran yunƙuri ze iya mutuwa, kuma idan ya mutu ze jamin gagarumar asarane a yanzu haka, dan haka ƙyaleshi tukuna, zuwa anjima idan be faɗa ba, a kamashi kusamin kansa a ƙasa, ƙafafunsa a sama a samo ruwan zafi ku saɓulemin fatarsa dashi, ku barshi anan gurin "
Saleh yabi Bukar da kallo, yana jinjina mugunta da zalunci irin na Bukar, haka Alhaji Bukar ya fice ya barshi a hannun su me Adda yayi tafiyarsa.
Akayiwa Amal aiki a hannunta, aiki yayi kyau an ɗorata, mutane nata tururwar zuwa dubata a Asibiti, kullum a can Hajiya Halima take kwana, kwana uku da yin ɗorin likita ya sallameta, yace su dinga zuwa duk bayan sati biyu ana dubawa harya gama warkewa gaba ɗaya.
Aka basu magunguna da sauran abun buƙata suka tafi gida, ma'aikatan gidan su Nura su Murtalah duk suka shiga suka dubata, suna fitowa Nura yace "Allah ya ƙara, Allah yasa karta warke da wuri hannunma ya ruɓe, jakar matar nan da yake 'yarta ce ta samu matsala, ji yadda ta dinga zarya a Asibiti, amma lokacin da megida yana kwance a Asibiti, sefa ta ga dama take zuwa, ɗantane kawai yaita wahalar jinya, shiba ubansa ba ba komai ba"
Isa yace "karkiya wa Amal wannan muguwar addu'ar, da dai waccan me ƙaton bakin ce Ramlah, ai gara Amal sau dubu da Ramla, dukda itama Amal ɗin ta iya rashin mutunci"
Murtalah dake gefe yace "hakane kam, Allah sarki, Allah ne kaɗai yasan inda megida yake, kaga kaman ma sum rufe babinsa, basa neman inda yake Yusuf kawai suke nema"
Nura yace "Allah sarki, wallahi tsayinsa nakeji, koba komai ba ruwansa wallahi"
Isa yace "kai dai bari, aiko ni da nake jin haushinsa da addua nake masa yanzu, na dinga duba yadda wasu abubuwan suk dinga faruwa amma baya magana, nan ze zauna in ta gayamasa baƙaƙen magana amma ko kallo bam isheshi ba, ima dana sanin wasu abubuwan da nayi masa wallahi "
Nura yace " nima inayi, amma ka fini zaƙewa sosai, kaga nifa da ace wani ne wallahi ko dagaske sace yarinyar nan yayi, wallahi sena hana a kama shi, yasha wahalrta sosai wallahi, ta gara shi san ranta "
Isa yace " Ai wannan akwai sa'a, duk garawar da take masa basu rabu ba, ya dinga mata biyayya, nifa wallahi ban yadda shiya sace ta ba, makirci ne kawai "
Murtalah yace " makairci kamar yaya kenan? "
"Nan Hajiya ta kirani falonta tace min, duk yadda zanyi inyi in nemo mata inda adireshin gidansu Yusuf yake, nayi nayi ya gayamin yaƙi, in ba makirci na Meza tayi da adireshin sa, kuma kun san wani abu, babu ma'aikacin da ake ɗagawa ƙafa a gidan nan kamarsa saboda 'yar masu gida"
Murtalah yace "ƙwarai kuwa, dan ba ƙaramin ci musu mutunci take ba saboda shi, amma dagaske an saka nemo inda yake?"
Isa yace "wallahi dagaske nake, sedai sam kamar yasan an sani fafur yaƙi gayamin, shegen wayone dashi kamar dila"
Nura yace "ba ɗan sanda bane, kai ka isa ka masa wayo nan da nan, ai kaima kasan baka isa ba"
Isa yace "kamar ya ɗan sanda wai?"
"Au kai a labaran da aka sanar ba gani bane, to ɗan sandan farin kaya ne, aikin bincike yake a gidan nan"
Isa yace "la'ilahaillalah illalah, dagaske? Yo aini ban sani ba"
Murtalah yace "to an barka a baya, baka san kanun Labaran ba kam, ɗan sanda ne ai shiyasa hankalin mutan gidan ya sake tashi"
Isa yace "tir ƙashi, amma wannan anyi munafuki, shine be taɓa gayamana ba, muka zauma dashi muyi ta sakin baki"
Nura yace "to mutan gidan ma basu sani ba, balle kai ance maka jami'in sirrine kawai seya zo ya fara gayamaka ai shi ɗansanda ne? Saboda be san aikinsa ba kobe san ciwon kansa ba? Kai dai Isa naga ranar sa zaka waye"
Haka suka cigaba da surutansu dai.
Ita kam Amal ta tsunduma a kogin tunanin me yakamata tayiwa Alhaji Haruna ta huce, da wani makami yakamata ta yaƙeshi ta ɗau fansar budurcinta daya rabata dashi? Sam ta kasa ko da cin Abinci, se uban tunani da koke koke, idan ta kulle kanta a ɗaki se tayi me isar ta, dan sam bata san me yakamata tayi masa bama, ta gama barazanar da zata yi masa amma bata san meye zata yi masan ba ta huce, gashi ta kasa gayawa kowa wannan labarin balle ta samu shawara, gani take zata tinawa kanta asiri ne a banza a wofi, tazo ta kasa samun mafita kuma, ta kalli hannunta dake nan naɗe da bandeji ga goshinta ma, ta lumshe idanunta tana jin zafi a zuciyarta.
Ramlah ta shigo ɗakin tace "Amal kizo ga matan Alhaji Harun nan sunzo dubaki"
Kallon Ramlah tayi kamar bata gane me tace ba, Ramlah tace "ko bakiji bane?"
Amal tace "Ai abunne naji wani iri, sun sanni ne daza suzo dubani?
Ramlah tace "oho muku, sun san Mummy ai, idan ke basu sanki ba"
Amal tayi tsaki tace "ba inda zani"
Ramlah tace "meyasa?"
"haka kawai, bazan zo ba, ki koma ki san abunda zaki gaya musu"
Tai maganar tare da kwanciya, Ramlah ta ɗan taɓe baki ta juya ta fice.
Amal ta sake jinjina rashin kunya, da iskanci irin na Alhaji Haruna, saboda ya gawurta har matansa ya turo su dubata, to suce mata me? Ji tayi kamar taje ta tona masa Asiri a gurinsu, amma meye shedarta? Taja tsaki tai shiru tana ci gaba da tunani.
Kamar wadda aka mintsina ta miƙe da sauri, dan seda ta kusa fama hannunta, ta tako a hankali ta fito, a hanya suka haɗu da Mummy, dan Ramlah ta gaya mata saƙon Amal, Mummy tace "da meyasa kikace bazaki fito ba?"
Amal tace "gaba ɗaya jikina ciwo yake, bana son hayaniya ne, sedai kuma naga babu daɗi, shiyasa nace kawai bari inzo mu gaisa"
Mummy tace "da dai yafi"
Suka fito gaba ɗaya falon, uwargidansace se Amaryarsa wadda take yarinya sosai, Amal ta ƙaraso suka gaisa, sukayi mata ya jiki, Amal ta amsa tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Da zasu tafi uwargidan tace "ga mukullin mota yace a baki, gata can yace a baki tunda taki ta lalace, Allah ya ƙara sauƙi"
Amal tai murmushin takaici tace "Amma fa nagode sosai, ai masa godiya ace masa naji daɗin motar nan fa, sannan ina nan tafe karɓar mukullin gida kuma"
Basu kawo komai ba, tunda ce musu yayi 'yace a gurinsa tunda sun san Hajiya Halima, Amal ta karɓi lambar wayarsu, tace sa dinga gaisawa.
Nurat tana zaune suna hira da Mummynta, ta gwada layin Anwar harta gaji amma shiru bata shiga, tun abun baya damunta har ya fara damunta, ta kalli mahaifiyarta tace "Mummy fita nake son yi fa"
"Kije ina?"
"Mummy duk inda ta kama, tunda aka samin doka yau kwana nawa ban fita ko ina ba, gashi ina buƙatar in ɗan fita ɗin in rage zafi, kullum ina cikin gida kamar wata mara gaskiya"
Mummy tace "nidai babu duwana, duk abunda kika jawa ka ki shikenan ba ruwana, kin san yadda kuka ƙareta dashi wancan karon dai"
"Mummy gidan Daula nake son zuwa, ina sin jin ko lafiya, layin Yaya Anwar baya shiga fa Sam"
"gidan Daula ko? Sekin dawo tunda baki da hankali"
"Mummy ba haka bane, ai gaida me gaishe ka ko baze amsa ba, amma tunda hakane, bari in jida zuwan bdk Khalil, idan yazo ya biya ya dubamin ko lafiya"
"Ke wani Khalil ɗin, baki san ranar da yazo ya tarar dashi ba kirana yayi yana masifa ba, wai zaryar me Khalil yake masa a cikin gida ba? Wai in dakatar da shi da zuwa ba"
Nurat tace "to Mummy ke kuma baki ce masa komai ba, sannan me Khalil yayi masa?"
"Oho kin san halinsa na rashin gaskiya ai, shi duk wani motsi seya zata bin diddiginsa ake, shiyasa kullum bashi da nutsuwa ai, shima dole zanyi masa waya, ya rage yawan sintir a gidan nan, ya bari se an kwana biyu yazo"
Nurat ta dafe kai tace "Ohh my God, ba dai gudun tinon Asiri yake ba, Insha Allah ya gamu da shi kenan, in Allah ya yadda se asirinsa ya tonu"
"Ke rufemin baki, kar yazo ya tarar dske kina wannan maganaganun, ya zata wani abun muke shiryawa"
A fusace Nurat ta miƙe ta e "to ya zata iɗn mana Mummy, na gajiya walilahi, am tired"
Ta juya ta bar falon ranta a ɓace, zuciyarta na wani irin tafasa tana tururi.
Yusuf na zaune yana zaune, Widad na kwance akan cin yarsa, yana ta wasa da gashin kanta, tana masa hira sedai gaba ɗaya hankalinsa baya kanta, ya tafi can duniyar tunani, ƙirjinsa nata bugawa haka kurum, yaka sa gank dalikin bugawar ƙirjin nasa, "Yoseef" ta kira sunansa, da sauri ya dawo hayyacinsa yace "Na'am"
"Me kake tunani ne?"
Yace mata 'bakomai "
Ta gyara kwanciyarta tace "Yuzarsef, kwana biyu Saleh bezo na, nifa hankalina yayi gida, gaba ɗaya na ɗan fara damuwa tunda yake zuwa be taɓa cemin komai akan mahaifina ba, zuciyata na son ganin mahaifina, ina yawan mafarkinsa ina son jin abunda ke faruwa gaskiya"
Seda gaban Yusuf ya faɗi, dan Saleh ha tabbatar masa babu wani sahihin kabadi har yanzu akan ɓatan mahaifinta, gashi ita bata sani bama, ya dake yace "tabbas nima ina ta fama da kokwanto a raina, ina son sanin meke faruwa a gida, gashi naga kwana biyu Saleh bezo ba"
Tace "hakane, dukda ni ba shiga sabgarsa nake ba, amma dole zan tambaye shi ya Daddyna yake, in dai lafiya ƙalau ne, baze jure tsawon wannan lokacin be gannj ba, dase yazo har nan kota halin yayane, amma tunda naji shiru something is going wrong somewhere, gidanmu nake son komawa "
" Insha Allah nothing is wrong anywhere, komai yana tafiya dai dai, am yakamata mu koma gida haka kam"
Tace "Allah yasa hakan"
Yace "Ameen, but Baby ta yaya zamu tabattarwa da al'umma Aurenmu, meye shedarmu?"
Widad tace "Allah"
Yace "hakane Allah sheda ne, amma baze yuwu mu gayawa mutane haka ba, dole mu nuna shedar aure mukayi, tunda au can babu wansa yasan hakan"
Widad tace "karka damu, Saleh ya sani, ga al'ummar garin nan da muka zauna tare dasu, suma sun isa sheda ai"
"Hakane, Allah yayi mana jagora"
Tace "Ameen"
Alhaji Musa yana zaune a ɗakinsa yana cin Abinci, ya ɗau waya ya kira Nurat yace yana son ganinta a ɗakinsa, Mamanta ta kalle shi tace "lafiya kuwa? Ina fatan dai ba wani laifin tayi maka ba?"
"ina ruwanki ne? Nida 'yata bazan kirata ba, ki zuba ido kawai"
Tace "Ai gara in dingayi ina bin ba' asai, saboda naga kai abun naka se a hankali gaba ɗaya"
Nurat tayi sallama ta shigo da dogon hijjabinta a jikinta, yace "Bacci kike ne?"
Ta girgiza masa kai tace "A'a salla nayi"
Yace "madalla fatan a nayiwa Daddy addu'a"
Ta jinjina masa kai yace "yawwa 'yar gidan Daddy, dama ba wani abune yasa na kiraki ba, zan sanar dake jn the next couple of weeks zaki koma Karatu"
Nurat tace "A ina kenan?"
Yace "can inda kika baro mana abroad, na nema miki imperial College London, kije kiyi business administration ɗin da kike so a can"
Girgiza masa kai tayi tace "Amma Daddy ai ba haka mukayi da kaiba, ka tambayeni nace maka ni a Nigeria nake son in cigaba, ka amincemin kuma yanzu kace ba haka ba"
Yace "look Nurat, ina nema miki sauƙi ne da kuma safe environment, inda zakije kiyi karatun ki cikin nutsuwa da kwanciyar hankali"
Tace "Nan ma akwai nutsuwa da kwanciyar hankali ai, ni dai kawai ka ƙyaleni a nan, bana son zuwa"
Aikuwa ya harzuƙa yace "ke, nine zance ga yadda za'ayi kice ke ba hakaba? Waye ya haifi wani tsakanin nida ke?"
Nurat tace "kai ka haifeni, amma kaima ka cika Alƙawari mana Daddy, baka gudun yadda tarbiyyata zata kasance, ni ina can ku kuna nan ni gaskiya bazanje ba"
Ya kalli Maman Nurat dake gefe tana jinsu yace "wato ke kike ziga yarinyar nan take rashin mutuncin da taga dama ko? Idan ba hakaba ya za'ayi ina magana tana magana?"
"Malam babu ruwana ni, 'yarka ce yau da gobe ai tafi ƙarfin wasa, ka fiye son kanka da yawa, shiyasa tun yarinyar nan na maka biyayya harta zo ta dena yi maka saboda son zuciyarka, kuma nima gaskiya ban yadda inyi nesa da ita ba, tunda mun baro ƙasar ma meye kuma ita za' a maida ita"
Alhaji Musa yace "lallai ba shakka, na ƙara tabattar da cewa ke kike ziga yarinyar nan, in faɗa ki faɗa tana gani ai dole itama ta fara, to bari kijin in gayamiki tafiya daram, seta tafi dole ta bar ƙasar nan taje inda na nema mata karatu"
Nurat ta fashe da kuka tace "ni gaskiya bazani ba, kuma idan aka takura sena je, wallahi barin gidan nan zanyi, dama naga yanzu ba'a ƙauna ta, tunda har yunƙurin rabani da rayuwata akayi" tai maganar tana ficewa daga falon, tana ji yana ƙwala mata kira amma tai banza dashi tai tafiyarta ko waigowa ba tayi ba.
Yusuf yana kwance har wajen shaɗayan safe, idonsa a lumshe yayi rigingine yana jin yadda gabansa ke cigaba da faɗuwa akai akai, Widad ta shigo ɗakin ta fito daga wanka tace "Yoseef, wai ba zaka tashi bane haryanzu shaɗayan rana, seka sa Hari tazo tana gayamin magana ko? Ina jinta shekaranjiya wai na fiye jaraba goma na safiya ina rufe ƙofa saboda shegen sa ido irin nata"
Yusuf ya kwashe da dariya yace "Ai gaskiya ta faɗa ba ƙarya ba, hakane abunda ta faɗa waike dole sekin samo Baby ba"
Widad ta buɗe baki tace "lallai Yoseef sannu, hakama zakace ko? Kaifa kace in rufe ƙofa sanyi kake ji, shine zakamin sharri"?
"Ba wani sharri malama, ni bance ki rufe ƙofa ba"
Widad tace "Ikon Allah, ni nama rasa me zance maka"
"dole ki rasa mana, kuma yau bazan kwana akan katifarki ba, a ƙasa zan kwana"
"Kaje kaita kwanan mana ina ruwana?"
"A'a dai karkizo kina min kuka, wai kai Yoseef meye haka? Dan Allah kazo ka kwanta" yai maganar yana kwaikwayon muryarta.
Tace "Nikam na shigesu a gurinka, Allah ya shiryeka"
"to kice ba'ayi haka ba mana"
"Aini bazan sake magana ba, nayi shiru"
Yai murmushi ya maida idonsa ya lumshe, ta ɗan ƙura masa ido, ya ɗan faɗa sedai masha Allah Yusuf ba dai kyau ba.
Tai murmushi tace "Mutum da hanci kamar an zana cartoon"
Yace "Kyau yai miki yarinya, shiyasa kike min ba'a"
"Ba wani kyau a nan gurin, wannan zanƙalelen hancin kaman cartoon"
"Kyaji dashi dai, yabawa kika yi"
Tazo tasa hannu ta matse masa hanci, Yusuf yace "ko ki sakarmin hanci, ko kuma yanzu in ɓaro ɗan dake cikin ki"
Da sauri ta cika shi tace 'yi haƙuri "
Yai dariya yace " Yarinya baki da komai a wannan cikin naki "
Ta murguɗa masa baki tace "aini nasan akwai"
Tai maganar tana tura baki, yayin da ya bita da kallo yana jin sonta na ƙara ninkuwa a zuciyarsa, idan ya tuna lokacin da take garashi da izza da rashin mutunci, ga gefe guda azabtuwa da soyayyarta daya dingayi ba tare da ta sani ba, idan akace masa akwai rana da zata zo su kasance a haka baze yadda ba, amma shine zaune da ita a ƙarƙashin inuwa ɗaya ta Aure, suke zaune ba tare da ya ɗaga masa hankali ba, wani farinciki ne ke ratsa zuciyarsa, tabbas da Widad ta rayu da masoya na gaskiya, mussman tare da mahaifiyar ta ba zata yi wannan izzar da jin kai ba, sedai rashin masoya, da kuma tsantstsar zalunci da butulci da aka gwada mata yasa tayi wa mutane gaba ɗaya kuɗin goro mussman talakawa.
Saleh gaba ɗaya ya sadaƙar, jira yake kawai suzo su fara gana masa azabar da Bukar yayi umarni, sedai basu yi masa komai ba sedai ɗaɗɗaureshi da suka kuma yi.
Yana zaune a inda yake aka buɗe ƙofar ɗakin da yake kwance a ciki, ya ɗaga kai seya ga 'yan sanda sun shigo, tare da Alhaji Bukar, ya nuna musu shi yace "gashi nan, ku tuhume shi yasan inda suke, kuyi masa duk wata izaya da duk wani abubda zesa ya faɗi gaskiya, karku saurara masa dan Allah"
Ɗaya ɗan sandan yace "karka wani damu, zamuyi abunda ya dace" suka kwancewa Saleh wannan igiyoyin suka ɗauke shi suka sashi a mota suka tafi dashi.
0 comments:
Post a Comment