Duk da yamma ce amma sauro har ya fara shagali a gurin nan, ga zafi a gurin kamar oven, haka Saleh ya baje a ƙasa ƙirjinsa da cikinsa na masa ciwo kamar zasu tsage, saboda duk daya sha da katako.
Yana jin wani ɗan sanda yayi sallama, sauram suka dinga sara masa, ɗaya daga 'yan sandan da suka ɗakko Saleh yace "Oga gashi nan a cell, munje mun ɗakko shi"
Ɗan sandan yace "ok shikenan, ku rubuta statement ɗinsa"
"Yallaɓai tome zamu rubuta?"
"Kai baka san me zaka rubuta ba, ku rubuta bayani akan an same shi da laifin haɗa kai da Yusuf, sun sace 'yar gidan Nasir Daula, sun ɓoye su, ka dai rubuta abunda yakamata"
Ɗan sandan ya sara masa yace "ok sir, za' ayi yadda kace"
"Yawwa that's very good, and a matsa shi yadda yakamata ya faɗi abunda ake nema a gurinsa"
"Yes sir, za'ayi abunda kace"
Yace "good"
Daga nan ya wuce ya shige office ɗinsa.
Hankalin Nurat ya tashi sosai, ganin cewar dagaske mahaifinta yake ze raba ta da ƙasar, itama tayi ɗamarar wannan karon zata bijire masa, kome ze faru se taga ƙwal uwar daka, se taga ƙarshen abunda mahaifinta yake yi, dan barin mutum irinsa suna cigaba da abunda suke so a doron ƙasa hatsari ne ga al'umma, wataran za'a iya wayar gari mutanen kirki su ƙare, ta ɗau wayarta ta kira Khalil, Khalil ya ɗaga yace
"Hello my dear, ya akayine any news?"
Nurat tai ajiyar zuciya tace "bad news brother, Daddy ya dage akan cewar wai sena tafi imperial U. K Inyi karatau a can, me Daddy yake nufi dani ne?"
"Calm down dear, make your statement clear please, kamar yaya imperial Collage, ke kaɗai zaki koma UK ɗin kiyi karatu, wanda kika yi a baya be isa ba"
"Nima shi na gani brother, shifa yayi min alƙawarin zanyi school a Nigeria, a Nigeria zanyi high institution, Amma kawai yazomin da wannan maganar, da alama yana zargina ne da fara bin diddiginsa, ni kuma gaskiya i won't tolerate it dear, gaskiya zan bijire"
Khalil yace "subhanallah, Nurat don't say that again, haba Nurat na sanki da biyayya da haƙuri, me zesa ki fara faɗar haka kuma? Haba Sister na"
Kuka Nurat ta fashe dashi tace "Broz Khalil, iya biyayya da haƙuri kasan nayi, nayiwa Daddy biyayya yadda yakamata, nayi ƙoƙarin kasancewa a cikin 'ya' ya nagari masu haƙuri, tun taso wata fa kullum cikin tsangwama da kyarar mahaifiyata yake, amma ban taɓa kulashi akan hakan ba, Brother babu ɗan daze dinga ganin mutuncin duk mutumin daze dinga cin zarafin mahaifiyarsa, komai kusanci da soyayyar dake tsakaninsu kuwa, amma na share na ɗauke kai, nake masa biyayya, ni da mahaifiyata mun masa biyayya, amma baya gani Khalil, baya gani kullum cikin zagi da cin zarafin mu yake, har gara ni yana ɗagamin ƙafa, akan mahaifiyata lokaci yayi da zan nuna masa nima 'yar halak ce, zan nuna masa ni ma' yace, wallahi bazan sake masa biyayya ba nagaji Khalil "
Khalil yace " Calm down, calm down my dear, i feel your pain Baby, kiyi haƙuri dan Allah, nasan me kike ji a zuciyarki, amma dan Allah karki bijirewa mahaifinki, hakan ba halinki bane ba"
"Yanzu na koya, kuma shine ya koyamin, kuma zega canji tabbas, na masa biyayya har akan abunda be dace ba, haka kake so in cigaba da binsa yana jan rayuwata data mahaifiyata a ƙasa?"
Barrister Khalil yace "kamar yaya ya saki abunda be dace ba?"
Cikin kuka tace "Khalil, Daddy da farko ni yasa in hilaci Widad, aka sumar da ita za'a sace ta, Yusuf ya ceceta, wani abunma baze faɗu ba ni kawai ka ƙyaleni, idan kuma ya dage sena bar ƙasar nan wallahi sena kawo masa ɗan shege ya raina a cikin gidansa na rantse da Allah "
" Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Nurat kin san me kike faɗa kuwa? Ko kin fara shaye2 ne ban sani ba"
Ta ƙara sautin kukan ta tace "idan ma ban fara ba ina daf da farawa, dan wallahi ya takuramin zan bar masa gidansa in shiga duniya, ko in tafi England inyi irin rayuwar da yake ganin gara inyi irinta da ya kasa cinma nasa burin"
Khalil ya kwantar da muryarsa yace "kina jina Nurat, am sorry kinji, nasan a irin matsala da damuwar da kike ciki, amma kin san zukata nawa ne zasu shiga garari idan kika lalace? Mummynki da kike wannan damuwar saboda ita, ya kike gank idan taga tilon 'yarta ta faɗa mummunar rayuwa? Ya kike tunanin shi masoyin naki ze kalle ki idan kika koma mutuniyar banza? Family duk zasu shiga damuwa idan suka ji labarin yarinyar da suke so, suke ji da ita ta shiga wata rayuwa daban, dan Allah kiyi haƙuri ki bar wannan maganar "
" Brother idan na bar wannan maganar wacce zanyi? Am tired wallahi na gaji dayi masa biyayya, Khalil abun ba sauƙi fa, dama mutumin kirki ne da sauƙi"
"Nasani Nurat, ki kwantar da hankalinki kinji, Insha Allah zan shigo gidan naku, zanzo muyi magana amma ki dena kukan nan please, kuma karki sake faɗin wannan maganar kinji Light" gabata ne ya faɗi jin yace mata Light, sunan da Yusuf ke gayamata, ajiyar zuciya tayi tayi jifa da wayar, tana ci gaba da rushewa da kuka.
A hankali hannun Amal yana warkewa, an kwance mata bandejin kanta ma, se hannun da haryanzu akayi hangin ɗinsa a wuyanta, yanzzhma ta fito daga wanka tana tsaye a gaban madubi, daga ita se towel kanta a tsefe, ta baje gashin kanta, ba laifi gashinta yana da tsawo, ga hannuta sagale a wuyanta, ga goshinta inda yayi tabon ciwon da Alhaji Haruna yaji mata, ta dinga ƙarewa kanta kallo a mudubi.
A hankali tace "dubeni, mace har mace, bani da makusa sedai an gurguntamin rayuwa, an rabani da mutuncina saboda zalunci, kuma ya biyoni da wasu tarkacen banza saboda ya rainamin hankali, bayan tabo na sarari da yayi min, ya barmin na zuciya me matuƙar ɗaci da baze goge ba, me zanyiwa mutumin nan in huxe, wace irin illa zan masa daze dasa masa baƙin ciki a rayuwar sa ne? Me zanyi ne Amal kiyi tunani ƙwaƙwalwarki bata ja Sam "
Ta dafe kanta ta fashe da kuka, tana tuna yadda ya suka dinga kokawa, da muguntar da yayi mata yacinma burinsa, zubewa tayi a gurin tana wani irin kuka, me tsuma zuciya
" Duk laifinki ne Mummy, laifin kine, nace ba zani ba kika ce se naje, Mummy why? "
Jikinta har rawa yake saboda kuka, dukda daga wanka ta fito amma ta haɗa gumi, ga hawaye ga majina se shesheƙa take.
Ramlah ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune a ƙasa, idonta yai ja tana kuka.
Ramlah ta ƙaraso da sauri tace " ke Amal lafiya kuwa? Meye haka? Meye ya same ki"
"Bakomai"
"bakomai kamar yaya? Kalle ki fa"
Tsaki Amal Tayi tace "excuse me please, dan Allah ki bani guri, ina son kaɗaicine"
"wane irin kaɗaici kuma? Anya kina hayyacinki kuwa?"
"Na miki kama da Widad ne, balle kice na haukace? Kawai ki fita ki bani guri"
"Amma Amal"
"Dan Allah ki fita ki ƙyaleni, kad in haɗiyi zuciya in mutu, dan Allah ki fita!"
Tai maganar cikin kuka, Ramlah na fita taje ta dstse ƙofarta ta kwanta akan gadonta ta cigaba da rera kukanta, tana jin Ramlah ta kira Mummy, suka dinga buga ƙofar amma tayi musu banza kamar ba taji ba.
Bukar ya kira Alhaji Haruna, Ya ɗaga wayar suka gaisa, Bukar yace "kunyi waya da Musa ne?"
Alhaji Haruna yace "A'a gaskiya, na kwana biyu bamuyi waya ba"
Alhaji Bukar yace "ok, na zaci kunyi wayane, haryanzu be ce mana komai ba akan batun wanda ze saka mana hannun, kuma yace mu saurareshi zuwa Laraba, anjima zamuyi meeting kota zoom ne, sannan ya batun takaddar da aka ce wannan yaron ya bari? Ka karɓo mana ɗinne kokuwa?"
Alhaji Haruna yace "eh na karɓo, naje har gidan da kaina naje na karɓo takaddar"
Alhaji Bukar yace "good, kasan duk wata sheda da zesa a ganemu, dole mu ɓatar da ita kar wani ya samu, dan haka ka kawomin takaddar nan"
Yace "shikenan, Insha Allah zan kawo maka ita, sannan zan sanar dasu batun meeting ɗin nan da kace"
Alhaji Bukar yace "to shikenan, se kazo"
Alhaji Bukar ya ajiye wayar, ya miƙe ya bar ɗakin dayake, dan ya manta da ya karɓi tajaddar yazo da ita nan gidan ko kuma a can ya barta gurin da ta bashi?.
Hindu tana tsakar gida, suna ta aiki a tsakar gida, Hanne tana gefe tana gyaran wake zasuyi alala.
Hari tace "sannu da aiki Hanne, Allah ya kaimu bikinki mu kira masu kiɗan ƙwarya muyi ta juyi a gidan nan"
Hanne ta taɓe baki, dan ita sama gaba ɗaya haushin Auren nan ma take ji, dan Yanzu haushin mijin da zata aura takeji, dan gani take bashi da komai idan ta kalli Yusuf, ita dai tana son Yusuf sosai, tana jin ina ma ya aure ta, da tafi kowacce mace dace a ƙauyen nan, da yana ɗan kulata amma yanzu ya dena, saboda wannan koɗaɗɗiyar matar tasa me kama da Yahudawa.
Hindu tace "Allah dai ya kaimu bikin nan ds rai da lafiya, ban san wane irin shagali zanyi ba, nima sena gyagije nayi shagali, idan kika tattara kika tafi in gaje gurin kwanciyar ki da nawa, Abinci ma zan haɗe nawa da naki ne, dama yanzu ba ƙoshi nake ba" Hindu Tayi maganar cikin sigar wasa da zolaya.
Amma Hanne ta karkace ta kyaɓe baki, ta kalli Hindu tace "aifa dama ina zaki ƙoshi tunda mayya na gidan? Ai gara in tattara in bar miki gidan ki cigaba da haɗa kafaɗunki dana iyayen mu, tunda dai ke kinfi kowa baƙin jini, babu wanda yake sonki balle kisa ran zakiyi aure ki bar gidan nan, ai se kiyi ta zaman gidan ki ƙare ki tsufa a gida, mujiyar garin nan, shikenan mutum ba zuciya balle ya samo wanda ze rufa masa Asiri ".
Ai tuni idon Hindu ya ciko da hawaye, ita har ga Allah wasa tayi wa Hanne, amma harta fara yan kamata baƙaƙen maganganu da cin zarafi, Hanne na ɗagowa suka yi ido huɗu da Yusuf, da alama duk yaji abunda ta faɗa, sekuma ta shiga kame kame, dan wata irin kunyace ta kamata, bece komai ba ya sa kai ya fice, dan be fiye son shiga sabgar iyalan gidan ba.
Yana fita Widad ta fito tsakar gidan nan, taga yadda Hindu ta nutsu tayi shiru, ido duk ya tara hawaye saboda zafin maganganun Hanne.
Widad tace "ke Hindu, wai ita wannan banzar 'yar uwar taƙi haifarki tayi? Haifarki Tayi da zata dinga gaya miki magana kina jinta? Wai wane ɗan matsiyatan zata aura a garin nan da har take miki wannan gorin haka? Wanda zata aura ɗin ma ya kai a kira shi namiji da take miki gori a kansa "?
Hanne tana hura hanci, cike da ƙauyanci da jahilci tace " Wallahi, tallahi nafi ƙarfin auren matsiyaci, niba matsiyaci zan aura ba"
"wallahi kika bari nazo inda kike, na shaƙeki se na jefa ki a rijiyar nan, saboda me zaki takurawa yarinya dan bata magana, dan kinga tana da haƙuri, wallahi ki kiyayeni akan ɓata mata rai"
Hanne tace "idan anƙi fa?"
Wata irin zuciya ce ta kwashi Widad, sedai Hindu tai saurin riƙeta tace "A'a Amarya yi haƙuri ƙyaleta kawai"
Widad ta harzuƙa matuƙar gaske, ji take tamkar ta jefa Hanne a rijiya, mussman idan ta tuna yadda take juya manyan attajirai masu ji da kansu, amma wata kucakar 'yar ƙauye na gayamata magana, ƙwafa kawai tayi tace "ba alfahari ba amma Wallahi da kin san wacece Widad, da baki isa ki yadda in haɗa ido dake ba, dan wallahi ko masu gyaran gadon baccina sun fiki kyan gani, ki zuba ido zakiga mijin da Hindu zata aura, Jahila kawai"
Ta wuce ɗakinta tana huci, duk wannan budurin Gwaggo da Hari basa nan akayi shi, amma abun yana damun Widad taji an taɓa Hindu, setaji kamar ita aka taɓa, danma ita Hindun ce shashasha take tsayawa ana mata wulaƙanci.
Amal kam wani tunani tayi a ranta, dan haka ta miƙe da ɗan sauri, ta fita falo, Mummy ta kalleta tace "kinga damar buɗewa yanzu?"
Amal tace "Mummy Ramlah ta kasa fahimta tane, wani lokacin idan ina cikin jin zafin ciwo, bana son kowa a inda nake, nafison kaɗaici amma se a takuramin, kun kasa ganewa"
Mummy tace "madalla, shine nake ta magana kika ƙi buɗewa"
"Am sorry, bazan sake ba insha Allah"
"Hmm ai shikenan, ya hannun naki yanzu?"
Tace "da sauƙi, Mummy dan Allah aramin wayarki zan transfer ɗin kuɗi, ni banki sun hanani wai ba network"
Ba musu ta miƙawa Amal wayar, Amal ta karɓa ta koma gefe, ta tura lambar Alhaji Haruna wayarta, ta bata wayar tace "Mummy, ga wayar nagode"
Ta koam ɗakinta, tana zuwa ta kulle ƙofa ta zauna akam gadonta ta kira Alhaji Haruna.
Lokacin yana tsaka da bulayin neman takadda, ya ɗaga suka gaisa dashi, sannan tace "Naga saƙonka, amma meyasa kwana biyu ba kazo ka dubani ba"
Se ynzu ya ɗau muryar ta, yai murmushi yace "nima naji saƙonki, ance bayan mota zakizo karɓar gids ma"
Tace "eh hakane, ko idan na dawo bazan samu ba"
. Yace "idan kika dawo ina?"
"zuciya ta, ta fara rayamin kawai idan na warke zan bazama in nemi arziki, in more ƙuruciya ta, idan ka shirya nima a shirye naake zan dawo gareka, tunda aikim gama ya gama tunda fari"
Yai wata shegiyar dariya sannan yace "ni zaki yaudara, ko har kin manta abunda kika gayamin a Asibiti, kaina yana ja sosai dan haka abune mawuyaci kiyi galaba a kaina, tabbas naji daɗin kasancewa dake sedai bazan sake amincewa dake ba, tunda kikayi wannan fueucin, ki sake shawara kinji 'yan mata, idan da gaske kike ki bazama ki kama wasu alhazan, nikam na gama muma na biya tunda na bada motar miliyoyi"
Bata sanma yadda akayi ta ajiye wayar ba, tana jera ajiyar zuciya kamar wadda tai gudu, duk yadda take tunanin abun ya wuce tunaninta, ashema matan suna suka tara, ba kowaccece ke iya kaidin ba, shi kansa shirya makircin ba abune me sauƙi ba, tai sharkaf da gumi tana sake tunanin wata hanyar.
Yusuf na dawowa Widad ta manta da damuwar da take ciki, sedai duk da hakan seda ya gane, yace "Maman Baby, ya akayi ne naga kamar ranki a ɗan ɓace yake"
Tace "A'a ni ba abunda akayi min, Ina ɗan tunani akan Hindu ne, ina ma Megari ze bani ita idan mun koma gida"
Yusuf yace "gaskiya abune me wahala, ya ɗau 'ya ya bamu alhalin bamu da wata dangantaka a tsakaninmu"
Ta jinjina kai tace "hakane, Gaskiya nifa na damu Saleh yazo ayi wacce za' ayi, na fara gajiya hankalina yayi gida sosai fa"
Yusuf yace "ki kwantar da hankalinki, nima shi nake jira yazo, muji abunda yakamata ayi"
Tace "shikenan, Allah ya kawo shi"
Yace "Ameen"
A gurin 'yan sandan ma babu sassauci, baƙar wahala Saleh yake sha, dan yana kyautata zaton an masa illa saboda duka, dan a nan ɗinma' yan sanda ke sa kulki, suyi ta dukansa izaya daban daban wai lallai seya faɗi inda su Yusuf suke, ga rashin Abinci gashi ko Najasa ne sedai yayi a nan, nan da nan Saleh ya fita daga hayyacinsa, ya canza kamanni fuska duk ta kumbura, ko ina rauni me yake zubda jini, sun doddoke masa ƙafafuwa da ƙyar yake iya miƙewa.
Da Safe Yusuf yana kwance akan cinyar Widad, ta samu comb se jagwalgwala masa sumar kansa take yi, shi kuma yana lumshe ido, can yace "gaskiya ki ƙyalemin gashina mana, haba se izaya kikemin a kaina"
Ta ɗan tura baki tace "kitso fa zan koya"
"To aini na gaji se jagwalgwala min suma ake, ga zafi banda ma tsabar rigima irin taki ta ina za'a kitsa sumata?"
"Ni dai ka ƙyaleni"
Yace "shikenan, Allah sarki ni, gaskiya idan na kuma jin zafi sena rama, sena aske wannan gashin naki da akewa mutane iyayi dashi"
Tai murmushi tace "daka temakeni, dan ba dan babu kyau ba sena rage shi, kuma idan ka aske ai kanka kayiwa, kaine kake wasa dashi ai"
Yai murmushi yace "kuma fa hakane, to na fasa askewar"
"A'a gara dai ka aske ɗin"
Hindu Tayi sallama kawo musu Abincin Safe, akayi mata izinin shiga tana shiga ta tarar da Yusuf kwance akan cinyar Widad.
Ta sunkuyar da kai cikin matuƙar jin kunya, Widad tace "sarkin kunya, idan na aura miki ɗan birnin haka zaki dingayi masa?"
Hindu ta juya da sauri tana murmushi, ta bar ɗakin, Widad tace "Yuzarsef, wallahi da ina da Yaya, ko wani ɗan uwa da babu abunda ze hana in roƙi ya auri Hindu, she's very kind and innocent"
Yusuf yace "hakane tana da kirki kam, ga nutsuwa"
Yusuf yaga abun na Widad ba na ƙarewa bane, dan haka ya tashi daga cinyarta yace "ke nagaji, kaina se zafi yake duk kin jagwalgwala min suma"
"ni kayiwa haka ko? In ƙara ganin ka taɓamin gashi ni da kaine, kuma ma insha Allah ta mace zan haifa, saboda in dinga mata kitso ta zama ƙawata kuma"
Yusuf yace "sannu sarkin shirirta, da shirme, ga tsabar ƙuruciya mutum baze gane hakan ba, se ya zauna dake, to ni bame yiwa 'yata kitso balle a jagwalgwala mata kai, idan kin haifi namiji nakine, mace kuma ta wace"
"A' a ban yadda ba, gaba ɗaya nawane, bayan kace baka son Baby"
Yusuf yace "Nina ce miki bana so? So kai amma ki bari ki samu cikin tukuna, sekimin iyayi da tsari"
"wai dan Allah dagaske bani da ciki?"
Yace "zan miki ƙarya ne? Kin manta shekarata biyu ina medicine, baki da komai madam"
Ta kwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "insha Allah ina da shi"
"Seki zauna kiyi ta imagination ai, miƙomin abincin nan inci"
Ta ɗakko kwananon Abinci ta miƙo masa, suka ci tare suna hira.
Yusuf yace "idan na dawo da daddare, kwaɗon gurji da zogale zan mana, zaki ci?"
Widad tace "Sosai ma, ranar Gwaggo tayi naci da daɗi Sosai"
Yusuf murmushi yace "to kwaɗayayyiya"
"Eh anji ɗin"
A haka suka yi sallama, yana ta tsokanarta, kamar karsu rabu.
Duk iya dubawar da Saleh zeyi, yayi amma ya rasa takaddar nan, ya duba ya duba amma takadda tace ɗaukeni inda ka'a ajiyeni, gashi yacewa Bukar ya karɓo takaddar nan.
Ya koma guest House ɗinsa, inda suka dinga kokawa da Amal, ya dinga duba takaddar nan, yai tsai gana dubawa ya birkita komai, ya hango ta a ƙasan gado.
Hamdala yayi, ya durƙusa ya ɗakko takaddar, yana ajiyar zuciya ya buɗe takaddar, sedai me ba takaddar bace form ne na koyon kwalliya na Amal, tsaki yayi yai jifa da takaddar yana tunanin ina yasa waccan takadda data bashi, amma kuma lokacin da ta bashi takaddar ai be buɗa ba, balle yasan me ta bashi, hankalinsa na kan yai mata akuyanci kawai, ya birkita ko ina amma babu wata takaddar se wannan, nan take gumi ya shiga tsasttsafo masa.
Widad taita jiran Yusuf ya dawo, dan se nishaɗi take ji ze kawo gurji yayi musu kwaɗo, bayan ya dawo da kayan gurjin da yamma, ta zauna ta cire ɓawon tsaf, ta gyara zogalen suka ɗora zogalen akan wuta, suna zaune suna hira a ƙofar ɗakinsu suna aikin su, hankali kwance yayin da zamantakewarsu kan burge wasu daga mutanen gidan.
Ya gama suka haɗa Kwaɗon nan a roba, Suka bawa wanda zasu bawa, Widad se haɗiyar yawu take, ta zauna zata saka hannu ta fara ci Yusuf yace "tsaya waye yace ki fara ci, salon ki fini loma ki fini ci ko?"
Ai ba ta saurareshi ba, danji take kamar hanjinta ze fito idan bata ci ba, jiki na rawa ta sa hannu ta fara cin Abunta, Yusuf yana kallonta yana nazarinta, tunda ta fara ci bata saurareshi ba seda taji ta ƙoshi tukuna, ta miƙe taje ta wanke hannunta ta sha ruwa ta dawo ɗaki sannan tace " Yawwa ina jinka, mema kace ɗazu?"
Yace "cewa nayi, sannu da aiki acici"
"Yawwa mijin acici, kai dai ubangiji Allah yayi maka albarka, ya saka maka da alheri nagode sosai"
Yace "Ameen, amma a dena cinye Abinci ana barina"
Kawai ta kwashe da dariya tace "ba ruwana cin abuna zanyi ehe"
Yace "ai shikenan poor me"
Tace "shagwaɓaɓe kawai, me sexy eyes"
Yace "what, sexy eyes kuma sekace wani mace"
"baka sani ba, you are having sexy eyes fa"
"Mhmm Malam kawai kice abunda yake ranki kenan"
Tace "What? Wai Yoseef meye haka? Kawai ba damar inyi magana seka canza mata ma'ana"
Tai maganar tana kai masa duka, ya kwanta yana dariya yasa pillow yana karewa.
"Kuma ma kai mummuna ne" tace tana harararsa.
"Eh naji bakomai, a haka 'yan mata suke rububina, saboda munina a haka suke sona"
Widad tace "Wallahi idan muka koma gida, duk wadda tayi gangancin raɓarka zata ga matakin da zan ɗauka wallahi"
Tai maganar very serious, dan kamar ma haushi taji.
Yace "haka akeyi, shikenan duk suna kallo se kice baza'a kulani ba, bayan kin sanni da farinjini, cewa fa kika yi in Auri Hanne"
Tsaki tayi zata tashi, ya fizgota jikinsa, yasa fitila ya haske mata fuska.
"Ni ka dena haskani, bana so"
Yusuf yai ƙasa da murya yace "An taɓa gayamiki ke kyakkyawa ce kuwa My wife?"
"Ai ko ba'a faɗa ba, nasan ni me kyauce sakeni"
"in sake ki kuma?"
Da sauri tace "No, i don't mean you should divorce me, ka cikani i mean"
Yai murmushi yace "nima na sani ai, ni dake ai mutu ka raba Babayna me kama da teddy"
Tace "Yoseef me yake damunka ne yau? Duk ka takuramin nice kuma me kama da teddy?"
"Eh ramawa nayi, ko kin manta haka kika cemin cartoon jiya"
Yai maganar yana dariya, itama dariyar ce ta kamata, ta buɗe baki kamar zata cije shi, amma ta fara kissing ɗinsa.
Kamar ranar suka fara kasancewa da juna, sunyi nishaɗi mara misaltuwa, sun farantawa junansu rai sosai, kowanne yana sake jin ɗan uwansa a ransa.
Haka suka wayi gari cikin farin ciki, sedai dukda wannan farincikin Yusuf se fama yake da fargaba, ya rasa dalilin hakan.
Yana ta shiri ze fita, yaji kamar harbin bindiga, gabansa ya faɗi yace "Lovely, kamar harbi fa nake ji"
Widad tace "A'a ko dai tunanin gurin aiki kake, amma wane irin harbin bindiga ana zaune ƙalau? Bari inyi walha, idan na idar seka tafi"
Ta juya ta tada salla, tayi raka'ar farko zata yi ta biyu suka ji Hayaniya, aka sake harba bindiga a ƙofar gidan mutane nata guje guje.
Yusuf yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
Daga tsakar gida suka ji ana "duk wanda ya motsa, zamu fasa kansa da bindiga, kowa ya tsaya a inda yake"
Gaba ɗaya jikinsu se tsuma yake, Hari ta samu wani lungu a bayan randa ta shige, se zare ido take saboda tsoro.
Nan da nan sega jiniyar motar' yan sanda ta ƙaraso
Da gudu Widad ta fito tsakar gidan, amma taga 'yan sanda tare da Saleh hannunsa duk ankwa a cikin mawuyacin hali.
Tace "me zan gani haka? Meye haka?"
Wani ɗan sanda yace "Yusuf, ina Yusuf yake?"
Widad tace "ban sani ba, bazan faɗi inda yaken ba"
Hari daga inda ta laɓe tace "Wudas ki dena magana karsu kashe ki fa"
"Ina Yusuf yake!" a kai mata magana cikin tsawa.
Itama cikin tsawar tace "ban sani ba nace"
Yusuf ya fito daga ɗakinsu, jikinsa sanye da jallabiya, ya ƙarasa gabansu ya miƙa musu hannunsa cikin surrender
.
Widad ta fashe da kuka tace "No! This is impossible, me yayi muku? Laifin me yayi mijinane fa, ku cire masa wannan cuff ɗin"
Su kai mata banza suka tasa ƙeyar Yusuf, itama suka sata a gaba ihu take tana kururuwa akan su sake shi amma sukayi burus da ita.
Aka sashi a bayan motar 'yan sanda, idonsa yayi ja ya kasa magana, se kallonta da yake gaba ɗaya ta birkice se ihu take tana kuka, muryarta harta fara dashewa.
"Ina sonka, Yusuf ina sonka, I love you Yusuf, dan Allah ku sakarmin mijina, beyi laifi ba, beyi laifin komai ba"
Yusuf ya ƙura mata ido, ya lumshe idonsa a hankali, yayin da Widad ke zubda wani irin hawaye tana kuka, me sauti.
Aka sakata a motar gida seinna, shikuma a bayan motar 'yan sanda gashi ga Saleh, kowanne hannu da sarƙa!!!
(Rayuwa ƙaddarace kowa da irin tasa......... 🎶 )
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/22/21, 4:49 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
116_117
Sosai Widad ta cigaba da gunjin kuka, yayin da mutanen ƙauyen suka fito suka yi duru duru suna kallo, ɗaliban Widad se kuka suke, haka Hindu gaba ɗaya ta birkice banda kuka ba abunda take yi, ba Hindu ba kawai hatta Megari, da su Hari hankalinsu ya tashi sosai, ga Sunusi mijin Jamila baya nan akazo aka kama su Widad.
Ana tafe a hanya amma bakin Widad yaƙi mutuwa, kuka kawai take akan a sakar mata mijin ta, tun Yusuf yana iya juyo muryarta da kukanta, har muryar tata ta dashe ba ajin me take faɗa sosai, haka sukaita tafiya har suka fito daga wannan kwazazzaban, da ramukan dake hanyar garin, suka hau kan kwalta ɗoɗar suka kama hanyar Kano.
Alhaji Haruna fa ya haɗa uban gumi, saboda ya tabattar da babu wannan takadda, takaddar form ɗin koyon kwalliya ta bashi, ba shiri ya ɗau wayarsa ya kirata da lambar da ta kirashi ɗazu, tana ganin kiran nasa Amal ta tashi da sauri, ta duba har zata ɗaga kawai ta fasa, ta ajiye wayar yai mata kira yafi Ashirin, ƙarshema ta saka wayar a silent tai kwanciyarta.
Yai wujiga wujiga, saboda takaddar nan saboda yasan Bukar ba kyau, gashi ya riga yace aiya karɓo, tunda takaddar zata iya zama sheda a kansu, wannan wasiƙar zata nuna akwai halin rashin gaskiya da mahaifiyar Anwar take aikatawa wanda yasa ya bar gida, idan tuhuma tayi tuhuma kuma za'a gano su.
Ya tura mata saƙo kusan kala shida amma babu reply, can dai ta ɗau wayar ta duba saƙon daya turo, magiya yake mata akan dan Allah ta ɗaga wayarsa, mahimmiyar magana yake son suyi.
Tana cikin karantawa kuwa ya kuma kira, seda taja aji sannan ta ɗaga, yai ajiyar zuciya yace "habba kyakkyawa, tun ɗazu naake kiran waya, amma anyi biris dani?"
Tace "to me kake so in maka? Ko in ɗaga in ce maka?"
"A'a kwantar da hankalinki, ai duk abun bana zafi bame ko ɗaga hankali, magana zamuyi"
Tace "ina jinka"
Yace "Yawwa, dama cewa nayi wannan takaddar da kika kawomin, kinyi mistake ba wasiƙar kika bani ba, form ɗinki ne na koyon kwalliya, kinyi mistake gurin bani"
Tace "se akayi yaya?"
"A'a dama ba wani abu bane ba, cewa nai zanzo in karɓa in an jima, saboda takaddar tana da mahimmanci sosai"
"Karka sake ka soma zuwa inda nake, bazan bayarba ka riƙe wadda na baka a matsayin ta"
Alhaji Haruna yai gyaran murya yace "haba beautiful Baby, ai abun duk bekamata ya kaimu ga haka ba, meye na ɗaukar zafi haka? Ai abun bana zafi bane ba, ki gayamin me kike so ayi yanzu in karɓi takaddar nan? Ko nawane zan baki"
Amal ta janyo Jakarta, wadda yace tayi accident da ita, ta duba amma itama taga babu takaddar a ciki, amma tai ajiyar zuciya tace "nima nazo maka da buƙata ta, amma kaƙi amincewa, dan haka kowa ha riƙe buƙatarsa, bazan bayarba gara asirin kowa ma ya tonu a huta"
Yace "Subhanallah, hadda mamanki fa"
Tace "har ita ɗin"
Yace "dan Allah kar muyi haka dake, ki bani takaddar nan na riga na cewa Bukar na karɓo takardar yace in kai masa, kuma yanzu inzo ince bahaka ba, baze sauraramin ba"
Amal tace "Ai gara karya saurara makan, kamar yadda nima baka sauraramin ba, kuma baka karɓi buƙata ta ba"
Yace "dakata, yanzu idan na karɓi buƙatar taki shikenan?"
Am tace "A'a ai kuma mun wuce wannan maganar yanzu, zan baka takadda bisa sharuɗa, yanzu abu na farko zan gaya maka Account Number ɗina, ina son inji wasu kuɗi masu nauyi, domin inci kaji in warke da wuri daga raunin daka min"
"Shikenan zan turomiki, yaushe zanzo in karɓa"?
Tace "turo ɗin tukuna in gani mana"
Yace "shikenan naji"
Ta kashe wayarta, lumshe ido tare da faɗin "Alhamdilillah, cikin sauƙi Allah ya kawomin hanyar da zan rama cin zarafin da kayi min, tabbas inaga yadda takkadar nan nayi, dan babu ita a jakata, amma a haka zan maka rashin mutunci in rama"
Alert ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta duba 500k ne, ta jinjina kai tace yanzu aka fara wasan
Seda yayi mata kira biyar, sannan ta ɗaga a fusace tace "wai meye ne?"
"dama cewa zanyi, kinga alert ɗin?"
Tace "na gani, amma sunmin kaɗan, na kuma raina"
Ta katse kiran tare da kashe wayarta gaba ɗaya, ta kulle ɗakinta da key, tai kwanciyarta.
Tunda suka taho Yusuf bece uffan ba, yai shiru yana saƙawa yana kwancewa a zuciyarsa, tabbas duk sunan da za'a kira shi dashi, ko a tuhume shi dashi, bashi da abunda ze kare kansa dashi, tabbas shi dai tunda ya tashi a rayuwarsa a siraɗin ƙaddara yake, daga wannan ya faɗa waccan, daga waccan ya faɗo wannan, haka ya sunkuyar da kansa yana ta tsabihi ga Allah, akan ya sauƙaƙa masa wannan lamarin.
Sun shigowa cikin garin kano, akayi hanyar babbar headquarter hukumar 'yan sanda dake garin kano, motarsu Widad kuma tayi wani gurin, ai tana ganin haka ta kuma fashewa da ihu, tana bori tana kuka tana "ina zaku kaishi? Ina zaku kaimin mijina? Beyi laifin komai ba, babu abunda yayi muku, ku ƙyalemin mijina wayyo Allah na Yoseef duk nice sila, saboda ni ka shiga wannan tashin hankalin, Dan Allah ka yafemin Yoseef, Allah ka fitar da mijina daga sharrin Azzaluman nan, Allah ga bawanka ka fitarmin da mijina"
Ta ƙarasa maganar, tana wani irin kuka me taɓa zuciya babu wanda ya kula ta a cikin 'yan sandan suka cigaba da tafiya.
Wani ofishin' yan sandan aka tafi da ita, suka fito da ita daga mota zuwa gurin 'yan sanda, idanunta sun kumbura sunyi ja saboda kuka.
Wani ɗan sanda yace "gata yallaɓai, yanzu muka shigo gari, shi an wuce dashi headquarter, ita kuma gata"
Ɗan sandan ya kalleta yace "Good, Madam congratulations, you are now free, mun cetoki daga hannun wanda sukayi garkuwa dake"
"Niba garkuwa yayi dani ba, wanda sukayi garkuwa dani daban, Yoseef ceto na yayi, shine ya temakeni beyi garkuwa dani ba, ka gaya musu suje su sakarmin mijina"
Ɗan sandan yace "koma dai ya akayi, wannan ku ta shafa ke dashi, muba abunda ya dame mu, zamu rubuta sannan mu sanar da duniya cewar, munyi namijin ƙoƙari gurin bincike mun gano wanda yayi garkuwa da Widad Nasir Daula, kuma ba wani bane face direbanta, wanda ya kasance ɗansanda, yaje gidansu yai basaja dan yayi garkuwa da ita, nasan hakan ze sake ɗaga darajar rundunar mu a ga namijin ƙoƙarin da muke, ba dare ba rana gurin kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma "
" Shut up!!! "
Ta faɗa cikin ƙaraji, tace " idan har ina raye ina numfashi, ko komai nawa ze ƙare se Yusuf ya fita, babu wanda ze cutarmin dashi, baku isa ba azzalumai ma cuta, lokacin da aka yi garkuwa damu muna buƙatar taimakk, babu wanda ya taimakemu na kusa rasa rayuwa ta, se yanzu da yayi komai ya gama, Allah yasa ya kare rayuwata, shine za'a masa sharri wallahi bazan lamunta ba, he's my Husband "
Ɗan sandan nan yace " ku ɗaukemin wannan mahaukaciyar daga gabana, a tafi da ita Asibiti a duba lafiyarta, sannan ku kiramin Ubanta Bulama tunda babu wanda yasan inda wancan yake "
Widad bata gane meyake nufi ba ta cigaba da kukanta, haka suka kawo Ambulance dan iya makirci, aka sheƙa mata wani abu ta sume a gurin, aka kira 'yan jaridu suka cika gurin, aka ɗauki Widad aka saka ta a motar Agajin gaggawa wato Ambulance suka tafi da ita.
Jaridu kuwa da sassafe shafin farko, hotunan Yusuf ne da Saleh, musamman na Yusuf ɗaure a cikin sarƙa ya sunkuyar da kai, gefe ga hoton Widad da aka ɗauka an fito da ita daga ofishin 'yan sanda an sata a ambulance, daka kunna gidan radio, labarai ko talabijin babu abunda zaka fara ji se
"Me dokar bacci ya ɓige da gyangyɗi, kuma ƙarshen tika tiki tik inji hausawa A yaune jami' am tasaro sukayi nasarar cafke jami'in ɗan sandan nan na farin kaya wato Yusuf Bashir Maitama, wanda yayi garkuwa da 'yar gidan fitaccen me Arziki nan a gida da wajen Nigeria wato Nasir Daula,' yan sandan sunyi nasarar gano shi ya sace ta tare da ɓoyeta a wani ƙasurgumin ƙauye dake garin Bauchi, 'yan sandan sun ceto Widad Nasir Daula, wadda ke cikin mawuyacin hali, da zauwansu basu yi wata wata ba aka kira motar Asibiti aka tafi da ita domin duba lafiyarta, zamu ci gaba da bibiya da kasa kunne domin jin wani mataki hukuma zata ɗauka akan wannan ɗan sanda, wanda ake tunanin har shi Nasir Daula ɗin shine yai garkuwa dashi, mu dai anan se muce Allah ya kyauta, yai mana tsari da irin wannan jam'ian tsaro a cikin al'ummar mu"
Nan fa gari ya ɗau ɗumi, aka dinga cece kuce, wasu na Allah wadai suna Tsinewa Yusuf, yayin da wasu ke a bari a ga abunda bincike zeyi tukuna.
Widad kam bata sake sanin inda kanta yake ba, inda har a gadon Asibiti aka bita aka dinga ɗaukar hotunan ta, ga fuskarta tayi ja saboda kuka, da gajiyar tafiyar hanya, amma aka dinga ɗauka ana watsawa duniya wai tana cikin mawuyacin hali, hannunta ɗauke da drip.
Alhaji Haruna ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba a taɓa raina masa hankali kamar yadda akayi yau ba, ya kira layin Hajiya Halima, Ramlah na zaune a falo wayar ta fara ringing, Mummy tana ciki tana amsa wata wayar dan haka ta ɗaga wayar tasa a kunnenta tace "Hello"
Yace "Yawwa Amal ce?"
"No Ramlah ce"
"Dan Allah idan Amal tana kusa ɗan bata wayar muyi magana"
Tace "tana ɗakinta, bari in kai mata"
Ta miƙe ta tafi ɗakin Amal, amma ɗakin a rufe harta kashe fitila ma "
Ramlah tace " gaskiya tayi bacci, dan ta rufe ɗakinta ma ta kashe fitila"
Yace "Yasalam"
Ramlah tace "ya dai? Akwai matsala ne?"
"A'a babu wata matsala, ina son muyi magana ne kawai"
"to ka gayamin saƙon in bata mana"
Yace "A'a karki damu, idan ta tashi na sake kira"
Ya kashe wayar yace "Amma dai Allah ya Tsinewa yarinyar nan, kaga min shegiyar yarinya mara albarka" ya ciji yatsa yai ƙwafa yace "dani kike zancen wallahi, kema sema wulaƙantaki,"
Amal ta ɗau wayarta ta tura masa saƙo tace "ka cigaba da kiran Mummy, kana cewa kana son Magana dani, wallahi idan baka yi wasa ba sena gayamata abunda kayi min, kuma kasan halinta sarai, kasan buyaginta zata maka abunda kai kanka zaka kasa gane kansa, dan haka muddin ba zaka cika sharaɗina ba, wallahi ba zan baka ba na gaya maka, kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan, nima a account dina ina da wanda suka fisu"
Ta kashe wayarta ta sake kwanciya, ya duba message ɗin, yaja wata ajiyar zuciya yana cije leɓe, totally ta riga ta gama raina masa hankali, yama rasa me zeyi ko me zece.
Yana nan tsaye yana tunanin mafita kiran wayar Bukar ya shigo wayarsa, ya ɗaga jiki na tsuma, yace "Hello"
"Haruna, yau muna da zama na gaggawa, cikin dare dan haka duk ku tattaru"
Yace "harda Halima?"
"banda ita, sannan kazo min da wannan takaddar, zamuyi magana a kai itama"
Daga nan ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya yakice gumi, yana huci Amal ta masa rashin mutunci, dan kawai abu ya shiga tsakaninsu se tayi masa haka?.
Mutan ƙauyen da Widad suka zauna suka dinga taradaddi, kowa da abunda yake faɗa wasu suna dama megari yayi wauta, wataƙila dama can 'yan fashi ne ko wasu masu laifin ne, amma daga zuwansu ya karɓesu, be san daga inda suke ba.
Hindu kam kuka, kamar wadda aka kama uwarta, ita kanta Hari gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, wunin ranar gidan daga masu koke koke, se masu salallami, Hanne kuwa ko a jikinta.
Koda Sunusi ya dawo, Jamika ta gaya masa abunda ya faru, dan haka yace dole gobe insha Allah ya tafi kank, yaje yaji ba'asin abunda ya faru.
Jamila tace "dan Allah karkaje, kar kaima a kama ka, dan na san da kana nan wataƙila da kai zasu haɗa"
Sunusi yace "da nayi musu me? Kince an kama Saleh, kuma Saleh shiya kawo su nan, meyasa aka kama shi, dole zanje inji"
Daddare megari ya tara iyalansa yace "to wannan bayin Allah dai, ni dai a ɗan zaman da mukayi dasu, ban tunanin mutane ne marasa gaskiya, ko makamancin haka, zamanmu da su ma mu alkhairi ya zame mana a garin nan, dan haka dan Allah ina roƙonku da kuyi haƙuri ku dena kuka, kukan ya isa haka, Hasana nasanki da son 'ya' ya kuma zamanmu dasu jin shaƙu dasu sosai, dan Allah kidena kuka kiyi musu Addu'a, Hindu Baffa kema kukan ya isa haka, muyi musu Addu'a, Allah ya basu mafita sannan Hari a samo makulli a rufe musu ɗakinsu, kar wanda ya sake shiga tunda da kayansu a ciki "
Hari ta tashi ta shiga ɗakinta ta samo mukulli, tana ƙoƙarin rufewa taga bokitinsu a tsakar gida, ta tafi ta ɗakko bokitin, kawai ta fashe da kuka tace " Allah sarki Wudas, da yanzu muna faɗa akan ruwan zafin da zata yi wanka, tace sena bata na bawa mijin ta, ban taɓa ganin abun tausayi kamar yau ba, yadda ta rikice tana kuka, Allah sarki Allah ya fitar dasu"
A kaita bata haƙuri, aka kulle ɗakinsu aka bawa Megari mukullin, ya kai ɗakinsa ya ɓoye.
Yusuf yana kwance a cikin cell, an raba masa cell shida Saleh, sauro yana ta masa buduri a ka, yai rigingine yana tunanin ya Umma zataji idan wannan mummunan labari ya isheta?.
Aka buɗe ƙofar cell ɗin, wasu 'yan sanda suka shigo su biyu, ya tashi zaune yana kallon su.
Ɗaya ya kalleshi yace "munafuki, kalleshi kamar na Allah, amma ƙasurgumin Azzalumi ne, kai garkuwa da' ya ka koma kayi da Ubanta, saboda kai Azzalumi ne, kuma a haka wai kai ɗansanda ne"
Yusuf yai shiru be ko ɗaga kai ba, ɗayan yace "rabu dashi corporal Sani, zuwa gobe in Allah ya kaimu semun sauya halittun fuskarsa, kafin 'yan jarida suzo, a buga shi a nunawa duniya shi, azzalumin banza dana wofi kawai"
Yusuf dai yai shiru bece komai ba, suka gama zage zagensu suka fita, suka sake rufe shi, tun Abincin safe Yusuf be kuma cin komai ba, ga doguwar tafiyar da suka yi, amma sam baya jin yunwa tunanin makaomarsa kawai yake a wannan hali da yake ciki.
Nurat na kwance cikin dare, taji Mahaifinta yana waya ƙasa ƙasa, ya fito daga ɗakinsa da alama dai fita zeyi, ta kalli agogo ƙarfe biyu da rabi na dare, ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito falo, aikuwa yana fitowa ya ganta a falo, ya ɗan haɗe rai yace "ke me kike yi a falo a wannan tsohon daren haka?"
Tace "ruwa na fito sha"
"ina ma fridge ɗin dakinki?"
"yayi sanyi da yawa, duk ya zama ƙanƙara shiyasa na fito"
Yace "to kin sha ɗin ne kokuwa?"
Tace "A'a yanzu dai zan sha"
"maza jeki sha, kizo ki wuce ki kwanta"
Ta nufi hanyar kitchen, tana tunanin ina zashi a wannan tsohon daren, ta fito ta tarar da shi a falon a tsaye, yace "kinsha ruwan?"
Tace "eh na sha"
"to maza ki wuce, ki tafi ɗakinki ki kwanta"
Harta juya ta tafi, ta waigo taga yana tsaye yana kallon ta, tace "Amma naga kamar fita zakayi, ina zaka yanzu dare yayi sosai"
"Yaushe na fara wasa dake? Ko kuma kika zama uwata da zaki dinga tuhuma ta haka?"
"hmm Daddy kenan, ai kaine kake abun tuhumar, wani irin abune wannan da ba'ayi ido ma ganin ido ba se yanzu a tsakiyar dare haka hmmm Allah dai ya kyauta?"
Ta buɗe ɗakinta ta shige, ta barshi tsaye yana binta da kallo, yarinyar da idan ta ganshi jikinta ke rawa, itace take gaya masa magama haka, tabbas uwarta ce ke zigata kuma zeyi maganinsu gaba ɗaya.
Kamar yadda suka saba haɗuwa yauma sun hallara gabaɗayansu, suna zazzaune a ɗakin Hotel ɗin da ya zamana babu ma me kama shi sesu.
Bukar yace "kyakkyawan labari"
Alhaji Musa yace "muna jinka"
Alhaji Bukar yace "yaron nan yazo hannu"
Sukace wane yaron?
Alhaji Bukar yace "ku duk baku sani ba, dukda yadda da labarin ya yaɗu a daren nan? To ina nufin Yaron nan Yusuf, direbanta wanda aka yi garkuwa dasu tare"
Sukace "Alhamdilillah, abu yayi kyau"
Alhaji Bukar yace "An kamosu a wani ƙauye a Bauchi, inda Saleh ya basu mafaka, yanzu haka yana hannun 'yan sanda, za' a tattare duk wata sheda da ta kamata daga nam za'a kaishi kotu, zamu saki kuɗi ayi masa shari'a da hukuncin daya dace da shi, saboda babu wanda ya ta:a kawo mana cikas da tangarɗa a harkar nan kamar shi, kunga daga nan babu wanda ya isa yace mune muka sa akayi garkuwa dasu"
Alhaji Munir yace "good, wannan abu yayi kyawuuu sosai, kuma ya tafi yadda ake so, dan haka semu hanzarta, mu kuma samu hanyar da zamu ɓalli namu kason tun kan Daula ya bayyana, dan shi har yanzu bamu san fa inda yake ba, kar muje wasu su rigamu karɓa abun nan fa"
Bukar yace "na toshe duk wata hanya da zata saka wani ya mallaki abun nan bamu ba, sannan dole nasa a matsa yaron nan, idan ma abun yana hannunsa ya faɗi inda suke"
Alhaji Musa yace "kai amma abu yayi kyau wallahi, komai ya tafi yadda yakamata"
Alhaji Bukar yace "Haruna ina takaddar da wancan yaron ya bari, ɗan gurin Halima? Shima nasa a nemo shi, duk inda aka ganshi kawai a kawar dashi, bama san duk wani abu da zesa a samu sheda a kanmu"
Alhaji Haruna yai tsilli tsilli da ido yace "Amm.. Mm.. Wallahi an ɗan samu akasine, na rasa inda takaddar ta faɗa amma ina ta ƙoƙarin dubawa"
Alhaji Bukar yace "Amma kasan bana son akasi ko?"
Yace "Ayimin afuwa dan Allah, Insha Allah za'a nemota in kawo"
Alhaji Bukar yace "shikenan, nan da kwana bakwai, na baka isashen lokaci, nan kusa nake so a fara shari'ar yaron nan, ba da nisa ba, kuma ina son a rufe duk wata hujja da zata bayyana mu"
Alhaji Haruna yace "insha Allah, zan kawo takaddar nan ba da jimawa ba"
Haka suka gama tattaunawa sannan suka watse.
Widad ce ke ƙoƙarin farkawa, se jujjuya wuyanta take tana kuka cikin bacci, "Wayyo Allah na, yuzarsef yunwa nake ji, zuciya ta ciwo take, Yoseef dan Allah, dan Allah ka dawo please! Ta farka a gigice tana kiran Yoseef! Yoseef kana inane?"
Bulama ne da Matarsa Hajiya Sarah a gigice suka yi kanta gaba ɗaya, Bulama yace "Sannu daughter, sannu ki kwantar da hankalinki, kin ganni a tare da ke, ga Maman Iman ma, an kuɓutar dake ki kwantar da hankalinki"
"Ni bazan kwantar da hankalina ba, ina mijina yake? Ina Yoseef kace su sakarmin shi, ni ba saceni yayi ba, wallahi idan basu sake shi ba mutuwa zanyi, laifina ne, duk saboda ya ceceni haka ta faru dashi, beyi laifi ba, tun farko seda na gaya masa death contract ne amma ya amince, kaga abunda nake nufi Yoseef, dan Allah ku ƙyaleshi idan wani abu ya sameshi bazan yafewa kaina ba, dan Allah ka cewa Bukar na dawo, ni yazo ya kamani yasa a sakarmin mijina dan Allah "
Tai maganar wasu irin hawaye na ambaliya daga idonta, idanun da suka rine zuwa kalar ja jawur suka kumbure.
Bulama yace "toni ina na san wani Bukar, balle in nemo miki shi? Ke kaɗai kika sanshi, ni ban san a inda yake ba"
Kafin ya rufe baki...
Ayi subscribing YouTube channel ɗina please 🙏 🙏 🙏 🙏
Ayshercool
11/23/21, 8:06 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
118_119
Alhaji Haruna kam juyi yayi ya farka ya ganshi kwance a gurin daya sha lemon nan, shi dai yasan da magariba Amal tazo, amma yanzu yaga kamar yammace, nan da nan ya tashi da sauri yana dube dube, ya kalli agogo yaga ƙarfe biyar na yamma, ya duba yaga wayarsa a gefensa a kashe, me yarinyar nan tayi masa haka? Ko kuma meye ya faru da shine?
Yai yai ya tuna wani abu amma ya kasa, ya gagara tuna komai daga inda ya sha lemon nan baya iya tuna komai, ya tashi ya fito falonsa amma komai yana nan yadda yake, babu abunda ya canza.
Duk ya lalleƙa babu wani canji daya gani, amma ya akayi yayi wannan baccin haka?
Ya tambayi kansa, tabbas wannan yarinyar ce tayi masa wani abu, sedai ya kasa gane meyafaru dashi.
Sunusi duk yadda yake tunanin lamarin ya wuce nan, dan daya zo Kano ya samu labarin inda su Saleh suke tsare, sedai tun daga bakin gate wani yace masa tun wuri yayi takansa, karma a san daga imda yazo ko kuma shi wanene a gurin Saleh, idan ba haka ba tabbas shima kamshi zasuyi su rufe har dashi.
Haka Sale ya koma babu wani daddaɗan labari, su kuma su megari suna can suna jiran sa yazo ya gaya musu yabake ciki, sedai yanayin fuskarsa kawai ya nuna musu babu nasara.
Me gari yace "Sunusi, kayi mana bayani, da kaje kanon menene ya faru? Ya kukayi dasu?kaga su Yusuf ɗin da Saleh fatan suna lafiya?" megari ya jero masa tambayoyin.
Sunusi yace "Baffa, lamarin nan fa ya wuce inda kake tunani fa, duk abun ba yadda muke tunani bane, ita wannan yarinyar daka gani, matar wannan Yusuf ɗin Wato Widad, 'yar gidan Alhaji Nasir Daula ce, wai ance Yusuf ɗin ne suka haɗa kai da Saleh sukayi garkuwa da ita, dan su karɓi kuɗin fansa, shine sukazo suka ɓoyeta a garin nan"
Hansai tace " wai Daula dai shahararren attajirin nan da ake labarinsa? Wanda ake yawan faɗansa ɗin nan"
Sunusi yace" to da daulan guda nawane? Shi dai 'yarsa ce"
Gwaggo tace 'biri yayi kama da mutum, kwata kwata yarinyar nan ba kalar wahala bace, yanayin yadda take rayuwarta da yadda bata iya wasu abubuwan ba ze tabattar maka da bata tashi cikin wahala ba, sedai gaskiya bazan taɓa yadda wai satota sukayi ba, nan fa suka zo da ita babu lafiya Yusuf ne ya goyota a bayan sa, bata yadda da kowa seshi farkon zuwa su, kuma da satota yayi da tabbas tayi yunƙurin guduwa wataran "
Hari tace " Akwai dai wani abu a ƙasa, amma yadda take ji da Yusuf ɗin nan ƙaryane a ce satota yayi, komai shi, kullum tana liƙe dashi, sannan ace satota yayi gaskiya ban yadda ba sam "
Sunusi yace " to kai Baffa da baka san daga inda suke ba, ka karɓe su?"
Megari yace " Saleh ne ya kawomin su, yace garinsu faɗa akeyi, babu kwanciyar hankali an kashe iyayensu, shida ita 'yan uwane, amma ba ciki ɗaya ba, na wuce gaba aka ɗaura musu Aure saboda dai ai baka ƙi taimakon mutum ba, amma ni dai gaskiya ban yadda ace wai satota sukayi ba, dan lokacin da suka zo gidan nan, shi kamsa Yusuf ɗin kamar a galabaice yake bashi da lafiya, zaka ce daga gurin da ake yaƙi suke '
Sunusi yace "Amma abun da mamaki gaskiya"
Hindu tace "kuma da kaje babu wanda ka gani a cikinsu, daga Amarya har mijin nata?"
Sunusi yace "ke, case ɗinfa babba ne, yafi gaban yadda kike tunani, kedai kiyi ta addu'a kawai"
Hindu tace "Allah sarki' yar uwata, gaskiya na tausaya mata, ashe 'yar gidan attajirai ce amma tazo tai rayuwa a wannan ƙauyen namu? Kuma taita binmu tana lallaɓamu mu koya mata abu, kuma da alama mijinta kawai ake nema, da akazo kamasu tambayarta suke yana ina"
Megari yace "koma dai yane, ubangiji Allah ya kuɓutar dasu"
Haka suka cigaba da tattaunawa suna salallami.
Aka buɗe ƙofar ɗakin da Widad ke ciki aka shigo, ko ba'a faɗa ba tasan waye ya shigo ɗakin, dan haka ko ɗaga kai batayi ta kalleshi ba, ta maida hankalinta ga wani gurin, ya ƙaraso ya zauna a gabanta yana ƙare mata kallo, still bata motsa ba balle ta ɗaga kanta ta kalleshi.
"koki kalli inda nake, ko karki kalla yin biyayya ga dukkanin umarnina ya zame miki dole a yanzu, tunda shine last option ɗinki, tunda kika riga kika gano waye Bukar, zan gwada miki aikinsa a aikace, ranar Litinin za'a kai wancan sakaram da kike iƙrarin mijinki ns kotu, kuma na ɗau dukkan wasu matakai dana san zasuyi amfani sena tura shi gidan yari ya ƙare rayuwarsa a can, babanki kuwa koma ina ya tafi ya tafi kenan, har Abada har gaba da Abada baze dawo ba, dama burina kenan in ɗaiɗai ta farincikin sa"
Widad dai bata motsa ba balle tayi magana, tai shiru ta cigaba da kallon waje ɗaya.
Ya cigaba da cewa "ki temaki kanki tun baki makara ba, ki bani takaddun da ubanki ya ware, yace wai dukiyar akwai me ita, duk wanda yasa hannu akan takaddun nasane suna ina?"
"Idan ubaka ne ya tara masa seka sa in baka, bazan bayar ba nayu Alƙawarin me ita zan bawa, kuma na riga na miƙasu ga masu ita"
"Niki ke gayawa haka?"
"Na gaya maka ɗin, tsakanin wuta da aljanna wacce kake da ita, balle ka sani? An faɗa maka ɗin kayi abunda zakayi karka fasa"
"Ina binki sannu sannu ne, saboda har yanzu akwai ɓurɓushin imani a raina, mahaifinki yamin ranar dabe yiwa wani a rayuwa ba, sannan dukiyar ki ce dalilin tsayawar kasuwancina da ƙafafunsa shiyasa nake son in kamanta miki adalci, ina takaddun suke? Ki gayamin cikin ruwan sanyi tun ban saɓa miki ba, kokuma na gwada miki"
"Ban sani ba!" ta faɗa cikin shouting,
"Idan kana so ka kashe ni hankalinka ya kwanta, kuma zalunci indai nakane wanne ne ban gani ba, ai babu irin wanda baka gwadamin ba, ko zaka gutststura naman jikina, bazan baka ba"
ai kuwa ya kifa mata mari, abun da ba'a taɓa yi mata ba a rayuwar ta, dan seda bakinta ya fashe.
"Wallahi ko kina so, koba kya so sekin bani kuma ba kimin wannan raunin a banza ba se na ɗau mataki a kanki"
"bazan bayarba, Amana ce kuma na danƙata a hannun masu ita suna rayuwarsu, me kake so inyi maka? Ko me zance maka?"
"ƙarya ki keyi, baki danƙata a hannun kowa ba, ki gayamin ina suke" yai maganar cikin tsawa.
Banza tayi masa, taƙi magana ta shiga goge jinin da bakinta yake yi, ai kuwa taji saukar tio a jikinta, tunda Widad take ba'a taɓa dukanta da abu me zafim wannan ba, bayan wanda aka mata da bakin bindiga, ta banƙare ta ƙwala ihu, take fatar jikinta ta tashi tai jawur kamar an ƙonata.
Tana zubar da hawaye tana girgiza kai, ji take kamar an saka mata wuta a bayanta, saboda azabar bala'i, ya sake zage ƙarfinsa ya shiga zuba mata, tun tana iya ihu harta kasa, se nishi da take yi yasa ƙafarsa da babu ciwon yai ball da ita, ai dukan da yayi mata be mata ciwo ba, kamar yadda yai ball da ita da ƙafarsa, ya ƙaraso inda take yana huci yace
"zaki gayamin ko bazaki faɗaba"
Ta ɗaga jajayen idanunta tana kallansa, ta shammaceshi ta kafa masa faratanta a inda aka masa ɗinkin nan a cinya, dayake naɗe ƙafar wandon yake, saboda karya sosai masa ciwon yaƙi warkewa.
Aikuwa haka ya buɗe baki ya ƙwala ihu shima, dan har jini gurin ya fara, ta janyo wuƙar nan da ta ji masa ciwo da ita akan taga, tace "wallahi idan baka fita daga gurin nan ba kashe ka zanyi, sena kashe ka wallahi '
Tuna yadda ya sha yanka da wuƙa ne wancan lokacin yasa shi fita da sauri yana faɗin " dawowata ta biyu bazata miki daɗi ba, zaya kasance dawowa me muni a gare ki "
Ya fita hannun sa riƙe da cinyarsa, tana masa wani irin zugi, har yanzu Widad ba tayi laushi ba, halinta be canza ba na baƙar zuciya da taurin kai na jaraba, gashi dukda dukan databsha da rashin lafiyar da take ciki, be hana ta fama masa ciwon nan ba, dan gashi har ya fara tstatsafo da jini, ta fama masa yai ƙwafa ya fita yana tunanin yadda zewa Widad izaya irin wadda ba'a taɓa yi mata ba, wadda zata tirsasata yin abunda yake so.
Ita kuwa Widad zama tayi tana kuka, saboda azabar raɗaɗin da jikinta ke mata saboda dukan da ta sha da tio, jikinta duk yayi tsami, tai kuka tai kuka harta fara tari daga nan kuma se Amai, gashi ba komai a cikin nata, dan baka ta dinga yunƙuri amma babu abunda yake fita, se miyau ga ɗaci da maƙogwaronta yake, se kuma ta shiga aman jini, haka ta dinga kakarin aman nan gwanin ban tausayi, abun da bata saba ba ya sameta, taji ba abunda take so banda ta samu ƙanƙara ta matsa lemon tsami ta sha ba.
Tan nan ta kwanta akan tiles, tana jin yadda sanyin ke ratsata, jikinta kuma yana ɗaukar zafi.
A hankali aka turo ƙofar ɗakin nata, ta tashi zumbur dan zatonta Bulama ne, wannan me aikince ta shigo cikin sanɗa, taga Widad a mawiyacin hali, dan tana jiyo kakarinta tun ɗazu.
Widad zata yi magana tai sauri ta girgiza mata kai, cikin ƙasa da murya tace "karki ɗaga murya mana, kinga Alhaji Bukar yace kar a kuma baki Abinci se sau ɗaya a rana, ya gindaya mugayen sharuɗa akanki, ni kuma ina jin tausayinki zan ɗan temaka mikine, ga Abinci na kawo miki kici"
Widad tace "bana ci, ki bani ruwa me sanyi sosai, ki bani in sha"
"A'a, kici Abinci mana, cikinki bakomai ga jikinki ya ɗau zafi sosai ki daure"
Ta tirsasa Widad yaci Abincin kaɗan, ta bata ruwan sanyi kamar yadda ta buƙata, sannan tai mata sallama ta fita.
Widad ta koma kan tiles ɗin nan tayi kwanciyarta, fatar jikinta duk jini ya kwanta akan fatar ta, ta lumshe idonta ga sanyin A. C gana tiles haka tai kwanciyar ta abunta.
Umma jikinta sauƙi an sallameta daga Asibiti, sedai jikin nata ya kasa ƙwari, saboda tsabar damuwa da tashin hankali da take ciki, ta rame sosai tayi zuru zuru duk ta fita daga hayyacinta, bata iya cin Abinci sam sedai abunda ba'a rasa ba, kullum tana cikin Addu'a ne, dan da kanta taje ganin Yusuf amma aka hanata ganinsa, haka ta dawo gwiwa a saɓule.
Tana zaune ta idar da sallar la'asar, tana lazimi idonta duk yayi ja saboda rashin bacci, sallama taji anyi ta amsa sedai kafin ta bada izinin shigowa Suka shigo ɗakin gaba ɗaya, ta ɗaga kai ta kallesu tace "Sannunku da zuwa Anty Asma'u"
"A'a riƙe sannu da zuwanki, zuwa mukayi muyi kallo sannan mu jajanta, yau dai kinga maganar da muke tayi tun shekarun baya, tsintacciyar mage bata mage, yau dai shege ya ɗakko miki magana, dama ina shege zeyi wani abun arziki, kina ta wahala kika saka ɗan uwanmu yaita wahala daku, ke juya shi kuma shege yau dak gashi ƙarshen Alawa ƙasa, ya zama gagarumin ɗan ta'adda ya sace 'ya yaje yai mata fyaɗe yana neman kuɗin fansa, Allah wadaran naka ya lalace "
Balaraba tace " Ameen dai Anty, alhakinmu ne ya kama su, da tasa ɗan uwanmu ya dinga wahala dasu, yana wulaƙantamu yau gashi kina kuka da idonki, kuka kam yanzu kika farashi, saura ke se sunzo sun haɗa ke dashi tukuna, tunda idan ya samo tare kuke ci"
Suka dinga zazzage mata rashin mutunci iri iri, ta inda suka shiha ba ta nan suke fita ba, Umma ba tace musu komai ba ta sunkuyar da kai kawai, ta cigaba da jan carbinta na tare da ta kulasu ba.
Suka yi suka gama san ransu, sannan suka tafi Umma ta girgiza kai kawai, tana share hawaye.
"Khalil ya ake cikine? Ka samu ganin Widad ɗin kuwa?"
Khalil yace "Nurat, ban samu ganin Widad ba, bata gidan Alhaji Bulama ance wai bata da lafiya an kaita Asibiti, amma ɗan nasa be gayamin ina take ba, wai shima be sani ba, nace masa zan kuma komawa inji abunda ake ciki"
Nurat tace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Yaya Khalil an kusa shiga kotu fa, Allah yasa dai a gano ta, na damu sosai dan Allah ka koma da wuri kaji"
"Shikenan insha Allah, karki damu zan koma inga yadda zamu yi dashi"
Alhaji Haruna ya kira layin Amal ba adadi amma taƙi shiga, ya rasa me yarinyar nan tayi masa ranar da tazo, ta barshi a yashe, yana ta tunanin ne kiran Alhaji Musa ya shigo wayarsa ji a sanyaye ya ɗaga.
Alhaji Musa yace "Haruna ina ka shiga ne? An kira layin ka ba adadi amma taƙi shiga, gashi baka bawa Bukar takaddar nan ba gashi za'a shiga kotu, kasan fa idan wani ya ɗau takaddar nan tsaf zamu shiga matsala, har saƙo aka turo maka na zamuyi taro amma baka ɗaga ba"
Alhaji Haruna yace "bani da lafiya ne, banga saƙon ba"
Alhaji Musa yace "ban yadda ba, akwai wani abu a ƙasa, ka gayamin ko menene mana? Kasan halin Bukar wallahi ze iyayi maka Akuya kasani sarai"
Alhaji Haruna yace "a bar zancen kawai, zanzo in same ka zamuyi magana"
"Shikenan, seka zo amma kasan yarinyar nan ta gano Bukar kuwa"
"Ahh haba dai garin yaya kuma?"
"oho masa dai, wallahi tayi masa sheda da wuƙa, ta yanke shiba fuskarsa da cinyarsa, kai baka ga yadda ya sha ɗinki ba, gaba ɗaya halittun fuskarsa sun sauya"
Alhaji Haruna yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Taɓɗijan dara taci gida kenan, to wani mataki ya ɗauka"
Alhaji Musa yace "eh to, yace tunda ga riga ta gano shi yasan yadda ze da ita, sedai kawai idan mun haɗu da kai tukuna, mayi magana mu tattauna maganar bazata yi ta waya ba, zan shiga meeting ne yanzu"
"Shikenan, sena zo tukuna"
Ramadan ne yai sallama ya shiga falon mahaifinsa, yana zaune yana kallon labarai, Ramadan yace "Daddy barka da hutawa"
Bulama yace "Yawwa barka, sannunka wai ni ina ɗan uwanka Fahad ne, yaushe rabon da in sashi a idona"
Ramadan yace "Daddy kasan halinsa fa, wallahi yau kwanansa huɗu baya gidan nan, nima ban san inda yake ba, babu wanda yayiwa sallama, dama hana yin haka fa, yakan kwana biyu ma baya gidan nan"
Bulama yace "da kyau, ze gauraya dani kuwa, dan ubansa"
Ramadan yace "Yawwa Daddy, nace a wane Asibitin Widad take ne, Nurat ta aiko a gayamata imsa take, tana son ganin tane kasan ƙawarta ce"
Bulama yai shiru yana nazarim Ramadan sannan yace "wata aiko?"
"Wani ne, nima ban sanshi ba, wai ko Khalil ne kowaye, ya cemin ɗan uwanta ne shi, yana so zeyi magana da Widad ne, Nurat na son sanin halin da take ciki"
Bulama ya jinjina kai yace "rabu dasu kawai"
"Daddy saboda me? Aikowa yasan tana hannunka, yakamata ka faɗi Asibitin da take, saboda masu dubiya sannan wataƙila 'yan sanda zasu samu wani rahoton daga gareta"
"Kai Ramadan ka kiyaayeni, ka fiye shisshigin tsiya wallahi, to ban saniba tunda nace maka tana Asibiti amma kama cigaba damin tambaya"
"Allah ya baka haƙuri, amma Daddy wannan yakan fa dake fuskarka da ƙafarka? Tun shekaranjiya nake son in tambayeka amma se inga kana bacci, na tambayi Mummy tace itama bata sani ba"
Bulama yace "Accident ne na samu, tashi ka bani guri tafi maza ka bani guri in huta"
Haka ya fatattaki Ramadan, ya kulle ƙofarsa ya ɗakko wayarsa ya kira Alhaji Musa, ya ɗaga yace "Allah ya temaki Bukar Bulama"
Alhaji Bulama yace "Musa kasan da ana shirin samun ɓaraka daga gidanka kuwa?"
"kamar yaya kenan?"
Bulama yace "Waye Khalil a family ɗinka kona matarka?"
Alhaji Musa yace "ɗan yayar Babar Nurat ne, cousins ne shida ita"
"Shine ta turoshi gidana wai azo agane mata ya Widad take? Wai aga halin da take ciki, da sanin ka akayi haka?"
Alhaji Musa yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wallahi ban sani ba saboda haka fa na kirsheta a gida, ko nan da cam bata zuwa, na hanata zuwa ko ina Sam, ban san yadda akayi tayi hakan ba, amma ka ƙyaleta zanyi maganin ta, zan ƙwace wayoyinta sannan in turata ƙasar waje, bakomai zan ɗau mataki a kai, hakan bazata sake faruwa ba"
"gara dai kayiwa tufkar hanci tun kafin inyi abunda yakamata da kaina, karka ƙara turomin wani yazo yana neman Widad, ka jawa 'yarka kunne"
"Insha Allah, hakan bazata sake faruwa ba, zanyi abunda ya dace base ka ɗau mataki da kanka ba"
Bulama yace "da dai yafi"
Litinin, tushen aiki kotu ta cika maƙil, domin ji da ganin yadda shari'a zata kaya, musamman shari'ar da mutane suke cike da sonji da ganin yadda zata kaya, wato shari'ar Yusuf Bashir Maitama, ɗaga jajirtaccen ɗansanda wato Bashir Maitama.
Umma ya halarci zaman kotun nan, dan shine kaɗai hanyar da zata ga Ɗanta Yusuf, 'ya' yan Bulama su Alhaji Munir, da Hajiya Halima da 'ya' yanta duk sun halarra a kotun.
Umma tana nan zune tana waige waige aka shigo da Yusuf, hannunsa ɗauke da sarƙa, 'yan sanda sun taso shi a gaba, yadda yake jan ƙafa da ƙyara da yadda jaabiyarsa tai baƙiƙirin saboda datti, ga fuskarsa duk a kumbure, kai da gani base an faɗa ba kasan Yusuf a wahala yake, Umma ta ƙunshe fuskarta a mayafinta ta fashe da kuka.
Haka akaje aka tsayar da Yusuf, 'yan sanda suka kewaye inda yake, Yusuf ya ɗaga kai yaga yadda kotu ta cika maƙil, masu masa kallon banza nayu, masu na tausayi suna yi, idonsa ya sauka akan ummansa wadda idonta yayi fururu saboda kuka, ya sunkuyar da kansa yana danne hawayen dake shirin zubo masa Allah kaɗai yasan me Umma takeji a rantava yanzu haka.
Aka karantowa Yusuf ƙunshin tuhumar da ake masa, amma Yusuf ya musanta yace "shi bashi ya sace Widad ba"
Barrister Saminu ya miƙe, ya gabatar da kansa a matsayin lawyoyin gwamnati masu gabatar da ƙara sannan yace "duba da yadda wanda ake zargi ya musanta abunda ake tubumarsa dashi, muna neman wannan kotu me Alfarma data bamu dama muje mu tattara hujjojinmu da zamu gabatar a gabanta, wanda zs tabattar da abunda ake zargin wanda ake ƙara ya aikata"
Me shari'a Justice Abdallah A dutse yace "duba da yadda lawayan gwamnati ya nemi a basu dama domin kawo shedunsu, wannan kotu ta ɗage sauraran wannan ƙara zuwa goma ga wata me kamawa, sannan wannan kotu tayi umarni da akai wanda ake zargi gidan gyaran hali zuwa lokacin da za'a sake wannan zama"
Haka aka tashi a shria'r yau, aka taho da Yusuf za'a sashi a motar 'yan sanda,' yan jarida sukayi dandazo amma aka hansu magana da shi, Umma ta taho da gudu Suleiman ma cikin hanzari ya nufi inda su Yusuf suke, Umma tana kuka tana "dan Allah ku barni in ganshi ko sau ɗayane, ɗana ne watana kusan biyar rabona dashi, ganinsa kawai zanyi Suleiman dan Allah kace su bari in ganshi"
Suleiman yace "Dan girman Allah ku bar baiwar Allah nan taga ɗanta, ko sau ɗayane uwace kunsan ba zata iya jurewa ba, dan Allah ku bari ta ganshi"
"Ba a bamu wannan damar ba, seta bari idan mun kaishi prison taje can idan sun batta seta ganshi"
Ayshercool
07063065680
11/23/21, 8:06 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
130_131
Haka aka ja mota aka tafi da Yusuf, umma tana ta zabga kuka, Yusuf ma ya sunkuyar da kansa yana kuka a cikin motar nan, shiba kaishi gidan yarin bane damuwarsa, kukan da Ummansa take shine ya tsaya masa a ransa.
Dan abun takaici, 'yan jarida sukazo suka kangawa Umman Abubuwan magana sun antaya mata tambayoyi, Suleiman ya janyeta suka hau mota suka tafi, ba tare da tace uffan ba, amma a haka suka naɗi muryarta tana kuka tana ambaton Allah dan suji daɗin yayatawa a duniya.
Haka aka watse a zaman kotu, kowa da abunda yake faɗa, wasu su faɗi alkhairi wasu kuma su faɗi som zuciyarsu.
Aka wuce da Yusuf gidan gyaran hali, aka bashi kayan fursunoni, aka shigar da bayanan sa, sannan aka kaishi ɗakin daze zauna, mutane masu laifi sunyi su sittin a ɗaki ɗaya, ga rashin isashshen vantilation, ga cunkoso ga tsamin dauɗa da wasu suke yi, gaba ɗaya abun se godiyar Allah haka akaje aka gwamutsa Yusuf a cikinsu.
Bayan an tashi daga zaman kotune, Bulama yabi Justice Abdullah gidansa, aka masa iso ya shiga, yana ganinsa A dutse ya faɗaɗa murmushinsa yace "kaine da kanka haka baa aike ba?"
Bulama yace "Ai saƙonne, yafi da cewa in isar dashi da kaine ba aike ba"
"to barka sa zuwa, ya kaga zaman shari'ar tamu na yau?"
"To Aini dutse banyi zaton haka ba, muda muke da shedu tuni mun tanada, na gaskiya dana boge amma kace wai ka ɗage sauraren ƙarara, ina laifin a fara gabatar da shedun, nifa da wuri nake son ayita ta ƙare fa, ayi a yanke masa hukunci in rufe babainsa, saboda in dai yana nan ze hanani rawar gaban hantsi, dan gaba ɗayansa matsalane a gare ni wallahi "
A dutse yayi murmushi sannan yace " hmmm Bukar Bulama, ai ita shari'a saɓanin hankkalice, bar ganin ka saye ni ka saye lawyoyi da hukunar 'yan sanda, karka manta akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu, na kare haƙƙin ɗan Adam, akwai lawyoyi masu zaman kansu, dukda wasu abubuwa da akayi da suke fito da laifin shi yaron ƙarara, amma duk da haka zasu saka ido akan shari'ar, za' a samu wanda zasu bibiyi shari'ar, dan haka muje a sannu, ina sane nayi hakan komai a sannu akeyinsa cikin hikima da ƙwarewa irin ta aiki "
Bulama yace " Aini gaba ɗaya hankalina baze kwanta ba muddin ba a gama shari'ar nan ba, yaron nan fa ba ƙaramin bincike yayi akaina ba, kuma bana son Daula ya bayyana ba'a gama shari'ar nan ba"
"Calm down mana, waini haryanzu babu labarinsa, babu wanda yasan inda yake ne? Abunfa da mamaki"
"to waye ya sani, anneme shi am rasa kamar wani kuɗi, duk iya bincike na saka anyi amma babu labarinsa, ni dai kayi kayi ayi gaggawa a ƙarƙarw shari'ar nan da wuri, ka yanke masa hukunci, kuma hukunima me tsanani wanda ze ƙare a prison"
Justice Abdullah yai murmushi yace "Bukar Bulama, ai komai akan doka akeyinsa, dukda munawa dokar karen tsaye wasu lokutan, saboda irinku da mukewa alfarma, amma karka damu insha Allah zanyi duk yadda zanyi in ƙarƙare shari'ar nan, ba da daɗewa ba yanzu se Allah ya kaimu bayan sati uku zamu sake zama "
"Gara dai ayi a sake zaman, dan Allah karka zake jan lokaci dayawa, bazan iya jira ba, sonake a ƙare komai"
"Shikenan, kaje ka kwantar da hankalinka, nan kusa zan ƙarƙare shari'ar hankalinka ya kwanta"
Bulama yace "da dai yafi ai"
A dutse yace "Amma, wai ya akayi kaji wannan raunin haka? Gaba ɗaya kamaninka sun sauya kayi wani iri, fuskarka ko ina ɗinki"
Bulama ya miƙe yace "karka damu da wannan, ƙyaleni kawai daga nan wani guri zanje, ina nan ina sauraren yadda zata kaya"
A dutse yace "shikenan, nagode sosai ka gaida gida"
Sukayi musabaha sannan Bulama ya tafi.
Nurat! Nurat!! Alhaji Musa ya shigo yana ƙwalawa Nurat kira, ta fito falo tace "Gani"
"Ubanwaye yace ki aika wai aje a duba miki Widad?"
Ta kalle shi tai shiru, ba tace komai ba.
"Ba magana nake miki ba? Ubanwaye yace ki aika wai a dubo miki ita babarkice ita meye haɗinki da ita?"
Yai maganar yana zazzaro ido kamar ze daketa.
Nurat ta girgiza kai tace "A'a Daddy nifa ba da wani abu na aika ba, kawai naga ƙawata ce kuma ga abunda ya sameta, ni kuma ka hanani figa, shine nace aje a dubamin"
"Ƙawarki ɗin banza da ta wofi, kuma wallahi ki kiyayeni da wannan yaron Khalil, idan kika bari na sake ganinsa a gidan nan sena ci mutumcinsa, sannan kije ki kwaso min wayoyinki ki kawomin su nan, kuma ko kina so ko bakya so sati me zuwa zaki bar ƙasar nan "
Mahaifiyar Nurta ta fito tana cewa," Kwanan nsm bam san meyasa kake wannan abubuwan haka ba, meye laifi dan kawai tace aje a duba mata ya take? "
" Idan ina magana kika ƙara sakamin baki wallahi sena ci mutuncinki, na gayamiki kin sani sarai abunda ke tsakanina da uban yarinyar, amma take shisshige mata"
"Amma larura ai tafi ƙarfim wasa, abun jaje ya samu mutum kace baza'a jajanta masa ba?"
Yace "eh baza'a jajanta ɗin ba, wuce kije ki kawomin wayoyinki, daga yau har ranar da zaki bar ƙasar nan, bake ba fita ko ina, kuma kar wani ya sake yazomin gida, ɗakkomin wayoyinki gabaɗaya, har System ɗinki"
Nurat ta shiga ɗakinta, ta ɗauki wayarta ta ɓoye, ta ɗakko sauran ya kai masa, ya karɓi wayoyin da system ɗin yace "ina ɗaya wayar taki take"?
Yai maganar yana kallon ta, Nurat tace "Na bawa Khalil ya kaimin gurin gyara"
"to ki gaya masa maza maza ya kawota, ki aika direba maza ya karɓomin wayar nan, maza fice daga nan ki bani guri"
Nurat ta wuce ɗakinta, tana tunanin meye abunyi, koda tsiya koda tsiya tsiya dai bazata bar ƙasar nan ba, se taga abunda ya turewa buzu naɗi"
Wasa wasa fa fiye da wata guda babu Anwar babu labarinsa, duk neman dazaa'yi anyi amma ba'a samu Anwar ba, hankalin Hajiya Halima gaba ɗaya a tashe yake, da tana iya basarwa amma yanzu ta kasa jurewa, ga Shu'aibu ya sata gaba yana ta tatsarta kota ko ina, ta zauna tayi shiru a falo ta rasa abunda yake mata daɗi.
Sallamar Alhaji Haruna ce tasa ta ɗaga kai ta kalle shi, mamakine yakamata ganinsa da tai kamar korarre, tace "lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya, ina' yarki take?"
"wace 'yar tawa kake nufi?"
"Yarinyar da kika aiko ta kawon takadda"
"Wai Amal kake nufi?"
"Eh ita, wadda ta karye"
Hajiya Halima tace "to meye yasa kake nemanta? Wani abun tayi makane ko kuwa?"
"Eh nemanta nake"
Amal tace "gani nan, lafiya kake nemana haka? Ko kuma naci ban biys bane?"
Suka juya, suka bita da kallo, tace "meye kake nemana?"
Sekuma ya diririce, ya rasa me zece ganin ga Hajiya Halima ta tsatstsare shi da ido.
Amal tace "faɗi mana, ina jinka"
Hajiya Halima tace "nifa gaba ɗaya kaina ya kulle, kumin bayanin abunda yake faruwa"
Amal tace "Mummy, ki kwantar da hankalinki babu wani abu fa, Alhaji muje farfajiya muyi magana"
Amal ta janye shi zuwa farfajiyar gidan ta kalle shi tace "lallai kaci ksi, baka da hankali da nasani nz tona maka Asirin abunda kayimin a gabanta, tunda kanka baya js yadda yakamata"
"wace maganar banza kikeyi hakane? Me kika aikatamin?"
"ba wani abu na aikata maka ba, illa na saka maye na ɗauki wayarka na bayar anyi abunda yakamata na turi kuɗi daga Account ɗinka, na raba kuɗin gida biyu na ɗau rabi, shine fansar budurcina daka ɗauka, kuma bari in gaya maka wani abu, akwai mahimmin saƙo da na ajiye na rarrabawa mutane, wallahi duk abunda ya sameni kaine, seka ƙara wannan akan kaidim mata da kace mim ba wanda baka sani ba, wawa kawai kuma wallahi ka kuma zuwa gidan nan duk abunda nayi maka kaika siya da kuɗinka ba wani ya sai maka ba, kuma a taƙaice takadda dai babu ita dan nima ban san inda take ba"
Ta ƙarasa maganar tana masa wani irin mugun kallo, ta shigevta barshi a gurin kaman gunkin mutanen farko.
Har ta shiga zata wuce ɗakinta, Hajiya Halima ta kira sunanta "Amal"
Ba tare da ta juyo ba ta tsaya cak , "meye haɗinki da wannan mutumin?"
"Babu komai"
"Karkimin ƙarya, meye haɗinki dashi?"
Yace "yana so nane, nikuma nace bana sonshi, ya takuramin nikuma na zage shi, shine zezo ya ɗagamin hankali"
"to dan ba kya sonsa meye na zagin masa kuma? Ai bekamata ki zage shi ba"
"to Mummy ni kalarsa ce? Ko da ƙuriciyata zan Auri wannan dattijon mutumin ne? Ai uba na ɗauke shi, amma tunda bega hakan ba shine nai masa abunda ya dace dashi"
"koma dai meye karki kuma zaginsa, dan ya haifeki kuma koba komaiakwai mutunci, da alaƙa tsakanina dashi"
"karki ji komai Mummy, hakan bazata sake faruwa ba" ta wuce ɗakinta.
Bulama ya fito ze fita, yaga motar Fahad a harabar gidan, dan haka ya fasa fitar ya nufi BQ inda suke, a falo ya tarar da Fahad, yana ƙoƙarin kunna TV, ya kalli Fahad yace "kai daga ina kake? Na samu labarin seka kwanaki baka gidan nan, gidan ubanwa kake zuwa haka?"
Fahad ya sosa kai yace "Daddy gurin abokaina nake zuwa, shiyasa"
"wasu irin abokaine zakaje ka kwana huɗu a gurin su? Kai baku da gidane?"
"muna dashi"
"to ya akayi kake zuwa kwana wani guri?"
Fahad yai shiru, Bulama yace "Shikenan ka kiyaye idan na sake ji sena hukunta ka na gaya maka"
Fahad yace 'to, amma Dad what's wrong with you in your face, naga ɗinki a fuskarka"
"Da ka damu dani ai da baka fita ba, kaje kayi kwanaki haka ba, ban sani ba"
"Sweet heart, wai har yanzu me kake a falon ne?"
Wata yarinya ce ta fito da Towel ɗaure a ƙirjinta daga bedroom ɗin Fahad, Fahad ya shiga zazzare ido, Bulama yace what, mezam gani haka? Fahad wacece wannan? "
Fahad ya sunkuyara da kai yana sosa kai," ba magana nake maka ba? Wacece wannan ɗin me take a nan ".
" Daddy dan Allah kayi haƙuri "
" Sallameta tazo ta barmin gida maza maza "
" wallahi ka bani kunya Fahad, neman mata? Akanme kuma a cikin gida na dan asara"
Fahad yace "wallahi Daddy ni Aure nakeso, kuma har yanzu kaƙi ka auramin Widad shiyasa, ni gaskiya shiyasa kawai nake bi ta ɓarauniyar hanya"
Bulama ya dinga masa bala'i, ya kori karuwar nan, ya taho cikin gida yana zazzaga bala'i, "Sarah, kina gidan nan amma yaron nan yake neman mata, kai Ramadan ga ɗakinka ga nasa, amma yake kawo mata gidan nan baka taɓa faɗa ba?"
Ramadan yace "ai Daddy kafi sonsa, kuma kona faɗa ba yadda zakayi ba Shiyasa"
"Nika ke gayawa haka Ramadan?ke Sarah kina kallo amma baki ɗau mataki ba, ko ki gayamin ba?"
"Barewa bata gudu, ɗanta yai rarrafe" shine amsar kawai data bashi, ya tsaya sororo yana kallonta.
Nurat taje ta ɗauki wayarta, ta ɓoye ta shiga tunanin yadda zata bawa Khalil wayar nan, ba tare da mahaifinta ya sani ba, tunda an hanata fita, kuma Mahaifiyarta na ja maata kunne sosai akan shisshigi akan lamarin mahaifinta.
A hankali ta lallaɓa ta sato wayar Mum ɗinta, ta dawo ɗakinta ta kira Khalil, yana ɗagawa tace "Brother a gurguje, dan Allah karka sake zuwa gidan Bulama neman Widad, akwai wata ƙulallaiya a ƙasa, akwai wani abu ds suke ƙullawa shi da Daddy na, ya gaya masa kaje gidansa neman Widad, amma Daddy yazo yana ta faman min faɗa, ya ksrɓs wayoyina saura ɗaya kawai, ya za'ayi kazo ka karɓa? "
" Nima na fuskanci akwai wani abu a ƙasa a tsakanin mahaifinki da Bulaman nan, ina da wani plan ne a ƙasa, amma karki damu zanzo in karɓi wayar "
" karka soma zuwa Brother, akwai matsala, zan san yadda zanyi idan ina so muyi magana zan kiraka a wayar Mum, se anjima "
Tai sauri ta kashe wayar, ta lallaɓa ta mayar mata da wayar.
Bulama ya kalli Fahad dake zaune ya sunkuyar da kai yace " kai dama Aure kake so amma ka tsaya kana bin wannan sakarkarun matan? Bayan zan aura maka cikakkiyar mace "
" Daddy wane cikakkiyar mace, bayan har ciki gareta?"
"ina ruwanka da cikinta? Nayi wani planning akanta, yanzu haka tama gidana na can hanyar ƙuyukan nan ma bayan gari, in da nake noman albasa, wannan gidan can na kaita na ajiye, kuma ko tana so ko bata so, za'a zubar da cikin nan ka Aureta, amma wannan da kake kawowa aiba mata bsne, idan aka kamanta su da ita "
Fahad ya washe baki yace " to Daddy nagode sosai, wallahi idan na Aureta sema rama dukan da tayi min, bazan manta marin nan ba"
Bulama yace "kai dai ka bari, aure kamar anyi an gama ne ai"
Fahad ya dinga washe baki, kamar wani sakarai.
Widad duk ta ƙare saboda larura da rashin kula, gashi cikin nan ya sakata gaba da Amai komai taci baya zama in dai ba Ruwan sanyin nan ba da lemon tsami, a ɓoye take zuwa ta turasasa Widad taci Abinci, sam bata kwanan kan katifar nan sedai kan tiles, duk ƙibarta seda ta ƙare ta rame sosai, duk tayi wani iri.
Yauma meaikin me suna Sabuwa tazo tana bata ƙosai da kunu, tana ci ds kyar, can Widad tace "Dan Allah ina labarin mijina kuwa? An fara shari'arsa ko?"
Sabuwa tace "gaskiya an fara, dan har Alƙali ya kaishi prison se bayan sati uku za'a cigaba da shari'ar"
Widad ta girgiza kai cikin ƙunar zuciya tace "Allah sarki mijina, Allah ya kawo maka mafita ta inda baka zata ba, babu abunda zan iya yi a kai, Allah ya fitarmin da kai Yoseef"
Sabuwa tace "Addu'ar dai da kike masa ita yakamata ki cigaba amma ba wannan kukan ba"
Widad dai nata shiru ba tace komai ba, dan tayi nisa bata jin kira, can tace "zan kwanta, ina son inyi bacci"
Sabuwa tace "to shikenan"
Ta tashi ta bawa Widad guri, ta rufe mata ƙofa, Widad yau taji bata san kwanciyar tiles ɗin ta koma kan ƙatuwar katifar dake baje a ɗakin, ta rage kayan jikinta ta kwanta tayi shiru, ko yaya Yusuf zeyi a prison, tana kwance akan katifa, amma bata ds tabbacin a inda Yusuf yake kwance a prison, ta tashi da sauri, taje ta leƙa tagar dake ɗakin.
Ko ina da haske, ga wasu ƙarti ne ke sintiri a harabar gidan, babu hanyar guduwa, gashi dama hanyar gurin gaba ɗaya babu gidaje, se kangwaye da gonaki, da manya manyan filaye fetal a gurin, dan haka babu hanyar guduwa.
Ta koma kan katifar nan, ta kwanta wani irin ƙaunar Yusuf da tausayinsa na ratsa jinin jikinta, ga wani irin mugun kewarsa da take yi, tana buƙatarsa a kusa da ita, ta tabattar da yana kusa da ita yasan da cikin nan, zata sha kulawa sosai.
Ta ƙanƙame filon nan a ƙirjinta, tana hawaye, a hankali tace "i miss you Yoseef, ina kewarka sosai, Allah yasa abunda ya faru karyasa ka dena sona, ina sonka Yoseef ka yafemin please, dalilina ka shiga wannan halin Yoseef, ina sonka Yoseef dan Allah ka dawo gare ni" a hankali take furta maganar tana zubar da hawaye.
Kwana uku da kai Yusuf prison Umma ta damu ta ɗaga hankalinta, akan lallai seta je ta ganshi, dan haka Suleiman yaje har gida ya ɗakko ta suka tafi gidan yarin tare.
Kasancewar Suleman ɗansanda ne yasa har gurin shugabn gandirobobi na gidan suka shiga, suka gaisa Suleiman yace "wannan mahaifiyar Yusuf ce, da aka kawo gidan nan, dan Allah munzo a bamu dama dan Allah muganshi"
Shugaban gandirobobin yace "a gaskiya ba'a bamu wannan damar ba, daga sama akace karmu bar kowa ya kawo masa ziyara"
Suleiman yace "saboda shi ba mutum bane? Ko kuma ba ɗan ƙasa bane ba? Haba dan Allah, wallahi kwata kwata babu adalci a shria'r da za'ayiwa Yusuf, dan Allah ka dubi girman Allah ka bari mu ganshi"
Umma cikin kuka tace "dan Allah dan Annabi ɗan nan kabari in ganshi, kusan watanni biyar zuwa shida, tynda akayi garkuwa dashi, ban sashiba idona ba ka temakamin"
"Wannan ce mahaifiyarsa?"
Suleiman yace "eh mahaifiyarsa ce"
Yace "kaman ba ita ta haife shi ba, kamar yayarsa, anyway gaskiya na lura da yanayinsa, tunda aka kawo mana shi gidan nan, ba sawa ba fitarwa, ko magana ba ruwansa da kowa, bashi da Hayaniya sam hakan yasa na fara tausayinsa, kuma nake jin ina shakku akan laifin da akace yayi, sedai baya iya cin Abincin gidan nan kunsan yanayin yadda Abincin namu yake, kuma gashi ance ba'a yadda kowa yazo gurinsa ba, nayi nayi inyi interview dashi amma yaƙi magana Sam "
Sulaiman yace " ai ba lallai yai maka ba, kaima Allah ya saka maka da alkhairi, shima abokin aikinmune ɗan sanda sakamakon wannan abunda ya faru, naji an sanar da an kore shi daga aikin, amma ita gaskiya ai zata yi halinta, nidai fatana ka mana wannan alfarmar dan Allah, ka bari mu ganshi"
Yace " Shikenan, kuyi zamanku bari aje azo dashi"
Suna nan zaune yai umarnin, aje azo da Yusuf suka cigaba da tattaunawa da gandiroban nan.
Aka shigo da Yusuf sanye da kayan prison, yana jan ƙafarsa da ƙyar da alama ƙafar ciwo take masa, da Gudu Umma ta tashi taje ta rungume shi tana kuka, Yusuf yasa hannayensa ya rungumeta shima, hawaye na gangarowa daga idonsa.
Tana so tayi masa magana amma takasa, se kuka da take Yusuf ya share nasa hawayen sannan ya ɗago Umman ya kalleta ya ƙaƙalo murmushi yace "Umman Yusuf, baki da lafiya ne? Kinyi baƙi kin rame sosai"
Girgiza kai take tace "Yusuf ka ganka kuwa? Gaba ɗaya ka fita hayyacinka kamsr ba kai ba, fuskarka duk ciwo Yusuf garin yaya haka ta faru?"
Yusuf bece komai ba, se cigaba da share mata hawaye da yayi, ya samu guri ya zauna, suka gaisa da Suleiman, Suleiman yace "nayi iya ƙoƙarin da zanyi, akan a barni inzo inda kake amma abu ya gagara, se yanzu da aka mana alfarma"
Yusuf yace "Aini bani data cewa, na barwa Allah shine ze fidda ni"
Suleiman yace "waini ina Saleh nema, Saleh yasan komai fa"
Yusuf yace "Anyiwa Saleh illafa saboda duka, inaga wani abu ya taɓu a cikin sa, yana kwance a Asibiti"
Umma tace "Yusuf wai ya akayi haka ta faru ne? Ya akayi aka kamaka kaida ita? Ance kai kayi garkuwa da ita harda fyaɗe, garin Yaya Yusuf"
"Umma kin yadda zanyi haka?"
"Kasan bazan taɓa yadda ba ai, ina son jin dahir ne"
"Umma, na shiga wannan halin ne dan kawai na temki Widad, ita kaɗai zata iya bada sheda akan abunda ya faru, se kuma Saleh, kinga bansan ma inda Widad ɗin take ba"
Suleiman yace "tana hannun abokin babanta Bulama"
Yusuf yace "Bulama kuma?"
"Eh tana hannunsa"
Yusuf yai ajiyar zuciya, Umma tace "wai ya akayi aka kamaka da ita a ƙauye? Garin yaya Yusuf?"
"Umma Aure mukayi da Widad"
Ta kalle shi tace "Aure kamar yaya?"
Gandiroban nan yace "Hajiya lokaci yayi, yakamata ku tafi haka"
Umma tace "to hakanma nagode sosai Allah yasaka da alkhairi"
Suleiman ya bawa Yusuf siyayar da suka yi masa, suka tafi yakasa waigawa ya kuma kallon Umma saboda yasan kuka take.
Suka juya suka bar Yusuf a gidan yari.
Bayan tafiyar su Umma, wannan gandiroban yasa aka canzawa Yusuf ɗaki, zuwa me mutum Ashirin, yana nsn kwance yana tunanin rayuwa, mussman Widad ya damu da yaji Widad wai tana hannun Bulama, shifa tun farkon saninta da yayi ya tsani Bulama, mussman da yayi bincike a kansa, sosai yake kewar matarsa, yana son sanin halin da take ciki, yana missing ɗinta sosai, kawai Fahad ya faɗo masa a rai, take yaji gabansa ya faɗi ya miƙe tsaye da sauri.
Cikin dare bacci da ƙyar ya ɗauki Widad, baccin beje ko ina b taji an motsa ƙofar ɗakin da take kwance, a hankali an buɗe ƙofar.
Banyi editing ba amin afuwa
A siya kafin a karanta dan Allah
Ayshercool
0009450228
11/23/21, 8:45 AM - Buhainat: Ki tura document din nan anjima takwara🙏🏻🙏🏻
11/23/21, 8:48 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
132_133
Widad ta buɗe idonta a hankali, tana son ganin waye wannan ya shigo mata haka a wannan daren, Kasancewar ɗakin da duhu shi baya ganinta se ita ke ganinsa, ya ɗakko ƙaramar wayarsa ya kunna ya haskata, tana kwance ta lumshe ido kamar me bacci, ya tako ya ƙaraso a hankali inda take, ya ƙara hasketa da fitila ya kai hannu a hankali ze taɓata ta miƙe zaune da sauri.
Tace "waye wannan? Ɗan dena haskani mana, waye wannan zaka shigomin ɗaki babu izini ko baka san ni matar Aure bace"?
"Aurenki na banza dana wofi, nazo in rama marin da kikamin ne, yadda gobe in ance ki kuma yiwa wani abunda kikamin, bazaki ba"
Se yanzu ta ɗau muryarsa, Fahad ne ba wani ba dan haka tai zumbur ta miƙe tsaye, shima kuwa ya miƙe, ya kai hannu ya riƙota ze gwada mata ƙarfi, sedai tarihi ya maimaita kansa, kamar yadda ta taɓayi masa shekarun baya, ta saka masa haƙora a hannunsa, wata irin azaba yaji ta ratsa shi tun daga yatsunsa har kansa, ya danƙi kanta yai jifa da ita a ƙasa, ai kuwa kanta ya gwaru da bango, hancinta ya fashe, ta saki wani marayan kuka, saboda zafi da taji, ya kuma yo kanta amma cikin sauri da zafin nama, ta tashi tai waje da gudu tana ihu, sedai duk wannan ihun da take babu wanda yayi yunƙurin kawo mata ɗauki, nan suka shiga guje guje dashi, Allah ya bata sa'a ta samu wani ƙarfe ta buga masa ya gigice, ta koma ɗakinta da sauri ta rufe ƙofa, gigicewar da yayi tasa yakasa komai ya shiga tangaɗi a gurin, duk ta bashi wahala sosai.
Ta shige banɗakin dake ɗakin ta rufe, ta dinga rusa kuka, gaba ɗaya ta rasa mema zata yi? Ta ding kuka me sauti.
Haka nan Yusuf ya dinga jin faɗuwar gaba a wannan daren, yakasa bacci sam, ƙirjinsa ya dinga bugawa da sauri, yakasa zaune ya kasa tsaye kawai yake jin kamar wani abu yana faruwa da Widad ɗin, ya dinga addu'a a haka har gari ya waye ba tare da ya rintsa ba.
Alhaji Haruna ya rasa me zeyi wa Amal ya huce, kuɗin data kwasa a account ɗinsa ba ƙananan kuɗaɗe bane, ya rasa meze mata wanda ze huce.
Yana zaune yana wannan tunanin Salma ta shigo ɗakinsa a fusace, ya ɗaga kai ya kalleta yace "lafiya kuwa?"
"dole ka tambayeni lafiya mana, munafuki macuci, to bari kaji in gaya maka, barin gidanka zanyi bazan zauna ba da kai ba Wallahi, dama can ba sonka nake ba aka ƙaƙabamin kai"
"Ni se wasu maganganu kike wanda ban gane inda kika dosa ba, kimin bayani yadda zan gane mana"
Jefo masa wayarta tayi, ya ɗauka ya duba, message ne aka turo mata da wata baƙuwar lamba "Ki saka ido akan mijinki, in bahaka ba watarn ze shafa muku ciwo, dan yana ta'amalli da mata a guest house ɗinsa, idan kin musa ina da sheda, zan iya turomiki idan kina da buƙata"
Wani gumine ya fara tstatsafo masa, ya dake yace "wannan wane irin shirme ne za'a turomiki ki yadda, kawai a turomiki magana ki yadda, wataƙila ma bake za'a turowa ba"
"ɗan saurara karka rainamin hankali mana, idan ƙarya ake maka saƙon ya rasa wayar waze faɗo se tawa? Kuma yawan fitar cikin dare da kake wataran bako sallama ina kake zuwa?"
"wannan kuma harkar aikine ke fitar dani"
"harkar banza dai, wans irin aiakine baza'ayi shi da rana ido na ganin ido ba se a takatainin dare, wallahi kaji tsoron Allah, kome kake aikatawa Allah yana kallonka, kuma wallahi idan na tabattar da abunda naake zargi seka sakeni wallahi, kuma sena tona maka Asiri a idon duniya, bani wayata ni"
Ta saka hannu ta ɗauke wayarta, tai waje ranta a matuƙar ɓace, ya dafe jansa kallai wanna kafon ya ɗebo ruwan dafa kansa, ga ya haɗu da mskira 'yar damfara.
Kiran Bukar ne ya shigo wayarasa, jiki na rawa ya ɗaga suka gaisa yace "Haruna na gaji da wannan zagaye zagaye da raini hankamin da kakemin, ka fito ka gayamin gaskiya mske faruwa, ina takaddar nan take? Idan kuma wata manufar ce da kai kuma seka ajiye agurinka"
Alhaji Haruna yace "Babu yadda za'ayi takaddar nana tana gurina inƙi kawowa, wata 'yara matsala aka samune, kuma ba da daɗewa ba zan warwarwta a ɗan ƙara ɗagamin ƙafa"
"Bana alfarma a karo biyu, daga ta farko bana ta biyu, Amma ka sani daga wannan shikenan, idan wani ya samu takaddar nan Asirinmu ya tonu, ze zama hujja akanmu, gara idan ɓataraa kayi ka nemota tun wuri, idan kuma ɓoyewa kayi kaje ka cigaba da ajiyar ta karka fito da ita "
Ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya rasa abunda zeyi, aka kuma kiransa da ovt number, kamar kar ya ɗaga amma ya ɗaga," ɗan duba what's app ɗinka akwai saƙo"
Be ɗauki muryara waye ba, amma dai muraya mr mace ce, ya kunna data ya shiga what's app ɗinsa, messages suka gama shigowa sannan ya shiga dubawa.
Video ɗin tsiraicinsa ne da wata wadda besan kowacce ba a guest house ɗinsa, daga ƙasa aka rubuta "dukda wannan abubuwan da na maka banji na fanshi mutuncina daka keta ba, wallahi idan baka biniba sannu ba sena yaɗawa duniya, kuma yanzu a haka akwai video ɗin nan a wayar mutum huɗu, isan har wani abu ya faru dani zasu watsa a duniya"
Ko ba'a gayamasa ba yasan message ɗin Amal ne, yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, be taɓa gamuwa da masifa a rayuwar sa irin wannan ba, ya ɗebo ruwan dafa kansa over.
Widad kam seda gari ya waye yayi haske sannan tai alwala ta fito tayi sallar Asuba, ta dinga kai kukanta ga Allah, kuka kama dama ya zame mata jiki, dan inda sabo ta riga ta gama sabawa.
Tana cikin kukan ne Sabuwa ta shigo mata da abun karyawa, Widad ta kalleta tace "yanzu dan Allah jiya baki ji ihuna ba cikin dare?"
Sabuwa tace "idan nace vamji ba nayi ƙarya, sedai kona fito ba abunda zan iya yi miki, saboda Kinsan nima aiki aka ɗaukeni inyi, idan na shiga hurumin da ba nawa ba, zasu kasheni ne, seda akamin wannan sharaɗin sannan na fara aikin kula dake ɗin nan"
Widad ta jinjina kai tace "ɗauke wannan Abincin bana ci"
"Saboda me?"
Widad tace "kawai bana ci"
Haka Sabuwa ta kwashe kayan Abincin nan ta fita dasu.
Widad tana nan zaune sega Bulama ya shigo ɗakinta, shida wasu ƙarti su biyu, aka kawo masa kujera aka ajiye, ya hau kai ya zauna ya kalli Widad yace "karo na ƙarshe, ki gayamin inda takaddun nan suke"
Widad ta kalle shi tace "gargaɗi na farko kuma na ƙarshe, ka jawa ɗanka kunne, idan ya sake zuwa inda nake, wallahi sena kasheshi har lahira"
"ina miki magana kina gayamin wani shirme daban? Ki kasheshi ɗin karki fasa, ina takaddu suke su nake tambayar ki"
"Na miƙasu ga masu shi"
Bulama yace "zan azabtar dake, azaba irin wadda ba'a taɓa yi miki ba, ina suke?"
"Duk Azabarka a duniya ne kawai, kuma babu wanda yake da ikon yin azaba se Allah, na gaya maka na bawa masu dukiyar nan dukiyarsu, ka ƙyaleni ka rabu da rayuwata haka"
Bece mata uffan ba, taga na jona wani abu a jikin socket, an miƙawa Bulama ya karɓi abun yayo kanta gadan gadan, bata motsaba ta tsaya tana kallonsa, kawai ya jona mata abun a hannunta, ji tayi kamar ba a duniya take ba, ta rasa meke mata daɗi gaba ɗaya ta fita hayyacinta.
"zaki faɗa ko bzaki faɗa ba?"
Girgiza kai ta dingayi tana kuka, amma taƙi magana, yasa ƙafa ya take yatsunta yana murzawa ciki mugunta, amma dayake Indai taurin kaine Widad ta iya shi taƙi magana.
Ba azabtarwar da basu mata ba amma taƙi faɗa, haka suka gaji Bulama ji yake kamar yasa wuƙa ya yanka ta, amma yaga idan ya kashe ta beyi Achieving komai ba, haka suka tashi suka fita, suka barta a galabaice.
sedai fitar sa babu daɗewa wani irin ciwon kai ya kama Widad, ko iya gani ba tayi sosai, ga ƙirjinfa daya riƙe gam, nan ta kwanta tun tana kwnace, harta fara juyi ya zamana bata iya ganin komai, se dishi dishi daga baya kuma ta dena gani gaba ɗaya.
Daga nana bata sake farkawa ba se a gadon Asibiti, taji anayiwa Bulama bayanin zuciyartace ta kumbura kuma ga jininta ya hau, Ba tausayi ba imani Bualama yayiwa doctor Hamisu umarnin ya cire ɗan cikin Widad koda tsiya ne.
Ta buɗe idonta fes a kansu, amma hakan besa Bulama yai shiru ba, ya bada umarnin a cire cikin.
Haka doctor Hamisu yaje ya ɗakko allurai, yazo ya haɗasu yayi mata duk tana kallonsa, sedai ta kasa motsa koda ɗan yatsanta ne, gaba ɗaya tama rasa inane yake mata ciwo, haka ya kwance cannula yai mata wata allura, sannan yasa wata a ruwa, ya gama ya fice tana kallonsa.
Sosai Yusuf yake jinsa a damuwa, hankalinsa yaƙi kwanciya sam, yake jin jikinsa ba daɗi, tunanin Widad ya cika masa zuciya.
"To wai kai Haruna ya akayi ka bari haka ta farune? Ta yaya yarinya ƙarama zata dinga wasa da hankalinka haka?"
Alhaji Haruna yace "kai dai bari kawai Alhaji Musa, wallahi nikaina ban san abun ze kai haka ba, ganin irin kuɗaɗen dana bata, ni nama rasa abunyi wallahi, babban abun tsorona shine video na data ɗauka, karta saki a duniya mutuncina ya zube"
Alhaji Musa yace "rabu da ita, duka barazanar banzace ba zata saki ba ƙarya take"
"Ya zakace ƙarya take? Bayan har Salma ta turawa message a kaina?"
"ni nace maka ka ƙyaleta ai, to ka ƙyaleta ba zata iya yaɗawa ba, sannan batun takadda ka gayawa Bulama gaskiya kawai, ai da tun farko ka faɗa masa ma da tuni an wuce gurin, ƙilma yai maka maganinta"
Alhaji Haruna dai yai ajiyar zuciya yai shiru kawai.
Bacci ne ya ɗauki Widad me nauyi, sedai wani irin gigitaccen ciwon mara yasa ta farka babu shiri, ji tayi wani irin ciwo yana ratsata, tun daga mararta zuwa bayanta da ƙafafuwanta, wani irin ƙarfine yazo mata, ta zabura ta fizge cannula, aikuwa take jini ya shiga zuba daga inda ta cire cannulan.
Ta faɗo daga kan gadon, Nurses ne suka shigo da sauri, suka ga yadda Widad ta faɗo ƙasa, ta riƙe mararta hawaye na zuba daga idonta, alamar tana jin jiki, ɗayar ta kalli ɗaya tace "Sister, ki kira likita da sauri yazo ya dubata"
Tace "shikenan bari inje"
Tana zuwa ta sami doctor Hamisu a Office tace "doctor, patient ɗin Alhaji Bulama ta Amenity she's unconscious fa, harta faɗo daga kan gadon"
"Ku kaita labor room kuyi mata abunda yakamata, Abortion ne cikin jikintane ze faɗi"
"doctor, amma naga kaman ba case ɗin Abotion aka kawota ba, cardiac failure ne, da hypertension kawai, ya za'ayi within a minutes ace kuma Abotion yai occurring"
"Are you going to teach me my job? Wace makarantar kika yi ne, baki san cardiac failure na uwar ze iya shafar abunda ke cikinta bane? Get out from here kije kuyi abunda nace"
Jiki a saluɓe Nurse ɗin ta fita daga Office ɗin ta koma ɗakin Widad, ta tarar da ɗaya Nurse ɗin rungume da Widad tana mata sannu.
"Sister ina doctor ɗin?"
"naje yamin wulaƙanci, wai mukai ta labor room abortion ne, muyi mata abunda yakamata, shikenan babu wani taimako da za'a bata se a bari cikin ya fita?"
'haka yace miki? "
" Gashi kuwa ina gayamiki, zan masa ƙaryane? "
Widad kam banda aikin gumi babu abunda take yi, fuskar nan tayi jawur saboda azabar wahala, haka taita wannan wahalar tana addu'a tana ambaton Allah, tana roƙon Allah ya bar mata cikin nan.
Ɗayar taje ta samo wata allura a pharmacy tayi wa Widad, cikin ikon Allah se bacci ya ɗauketa, can sega doctor Hamisu ya shigo yana cewa "Yaya? Cikin ya fita dai ko?"
Ɗayar tace "ta samu relief bacci take yi"
"Ya faɗin dai ko?"
Nurse ɗin tace "Eh ya faɗi, mun gyarata ne ta samu hutu, amma babu wani wanda suka zo tare da ita ne?"
"Ba ruwan ku da wannan, tunda mun samu ya faɗi Alhamdilillah, a bata medication ɗinta na dare"
"To insha Allah, za'a bata"
Bayan fitarsa ɗaya ta kalli ɗayar tace "Sister Habiba, kijimin ikon Allah, ni anya ba doctor ne yai mata wani abuba akan cikin nan ba kuwa?"
Sister Habiba tace "ya za'ayi in sani, amma nima ina zargin hakan wallahi, Allah sarki tana murƙusus amma fatanta Allah ya bar mata cikin ta, Insha Allah be zube ba, ko akanme ze damu cikinta ya zube oho"
"Hmm kedai bari, shida wannan Bulaman dama basu fiye ƙulla abun Arziki ba, naga shiya kawota kika bibiya karuwarsa ce, ko kuma dai cutarta sukayi suke so su rabata da cikin, kin san ɗan Bulaman Fahad ya saba kawo mata nan a cire musu ciki"
Sister Safiyya tace "ai kedai bar masu kuɗin nan kawai, Allah dai ya shirya naga ta samu bacci, gashi babu kowa a gurinta, balle idan ta farka a bata Abinci"
Sister Habiba tace "ai kamar yadda kika faɗa ɗinne, kika bibiya dai ba ta hanyar Allah aka samu cikin ba, shine suke son su zubar mata ta ƙarfin tsiya"
Baiwar Allah, ita Widad sam bata san meke faruwa ba, wani galabaitaccen baccine ya ɗauketa, wanda fal yake da mafarkin Yusuf cike da bege da shauƙin son ganinsa, se kuma mafarkin daddy da take yi.
Ɓangaren Ramlah kuwa, taga kwata kwata kusan Fahad yayi dumping ɗinta aside, kwata kwata baya ta tata yanzu, dan haka ta shirya da kanta ta tafi Hotel ɗin da yake zuwa, tana zuwa kuwa ta sameshi da wata mace a ɗakin, Ranta ya ɓaci matuƙa ta dube shi tace "Lallai Fahad, ka cika tantirin butulalle, a wani postion ka ajiyeni ma tukuna?"
Fahad yai murmushi yace "postion ɗinki dai na farko, a nan ns ajiye ki, me kike tunani"
"dalla saurara, karka gayamin maganar banza mana, ban gane postion ɗina na farko ba, ina maganar Auren mu da kai?"
Fahad ya kwashe da dariya yace "haba tawan, meye muma na ɗaga jijiyoyin wuya haka? Maganar Aure tana nan mana, ki bari idan na Auri Widad kema se inzo daga baya in Aure ki"
Ta kalle shi tace "Fahad, yau wace irin giya ka Shane haka? Data gaya maka ƙarya wadda harta saka ka kalli idona kake gayamin maganar banza da iska?"
"irin wadda na saba sha ce dai, sedai ban sani ba ko nasha expired ne"
"Lallai Fahad kana wasa, baka san abunda ka aikata me ze haifar ba ko? Ds kyau wallahi ka ɗebo ruwan dafa janka in dai Ramlah ce, zakaga tsiya"
Ta juya buguzun buguzun tai waje, bata zame ko 'ina ba se ofishin Bulama, tana zuwa ta tarar yana aiki a Office, sedai tayi mamaki ganin ɗinki haka a fuskarsa, koda yake ba wannan yakawo ta ba.
Ya ɗago ya dubeta yace "Ramlah lafiya kuwa? Ya kika shigomin Office haka?"
"Kamawa tayi na shigo a haka, ina maganar ds mukayi da kai?"
"wace maganar kenan?"
"Maganar da mukayi akan wannan mutumin, da yake iƙrarim shi mahaifin mu ne, kace zaka ɗau mataki akansa, amma har yanzu bani da tabbas na ka ɗauka kokuwa?"
"Banda abunki Ramlah, nima fa ban san takamaimai inda yake zaune ba, ta yaya zan ɗaukar miki matakin? Nasa aje inda nasan shi, amma baya nan baya zama a guri ɗaya sam"
Tai tsaki sannan tace "waima ni wane irin hatsari ne dashi haka, wanda yasa Mummy ke tsoronsa?"
Bulama yace "wannan tambayar ai ita zakiyiwa bani ba, kije ki tambaye ta zata gayamiki komai"
Tai ajiyar zuciya, tare da jinjina kai tace "idan kai baka ɗau mataki ba, nika gayamin inda yake in ɗau matakin daya dace dashi mana"
"Haba Ramlah, kema kin san da nasan inda mutumin man yake aida da kaina zam ɗauksr miki mataki akansa"
Kallon Bulama kawai take, ba wai dan ta gamsu da abunda yake faɗa ba, ta suri jakarta tai waje tana ƙwafa.
Fafur Nurat ta dena fitowa ko falo, saboda karma su haɗu da mahaifinata yai mata zancen komawa ƙasar waje.
Dayake yau Weekend ne sam be fita ba, yana gida amma still bega gilmawar Nurat ba, ya tafi ɗakin matarsa ya tarar tana kwance tana chatting, yace "wai ina yarinyar nan ne? Wunin yau banga gilamawarta ba"
Ta tashi zaune tace "tana ɗakinta mana, kasan halimta wasu lokutan bata san shiga mutane, tafi son zaman kaɗaici a ɗakinta, balle kuma ka ƙwace wayoyin ta"
"Ina fatan dai tana nan tana shirin tafiya?"
"tafiya ina? Ai wannan maganar kuce kai da ita"
"kamar yaya kenan?"
"kamar yadda nake gayamaka mana, kai ds ita kukayi magana, dan haka babu ruwana ka tambaye ta idan tana shirin da kanka"
Ya jinina kai, kwanan nan yaga zam iyalin nasa sun dena tsoronsa kamar yadda suke tskronsa a baya, ya rasa dalili.
Yana shiga ɗakin Nurat, ya tarar tana tilawar Al'qur'ani mai girma, ya jira ta kai aya ta ɗago ta kalle shi, dan taga magana yake son suyi.
Yace "dama zuwa nayi in ji ko kina shirin tafiyar nan kuwa? Jirginku ze tashi jibi in Allah ya kaimu fa"
Nurat ta miƙe taje ta ajiye Al'qur'anin ta sannan tace "nifa ba inda zanje Daddy, tsawon shekaru ina maka biyayya, dukda yi maka biyayya umarnin Allah ne, amma nima kayimin adalci mana, wallahi idan na tafi karatun nan bashi zanyi ba, rayuwata kawai zanyi"
A fusace yace "ni kike gayawa haka?"
"wallahi Daddy kace sena tafi guduwa zanyi daga gidan nan, ni bana son tafiyar"
Ya ƙura mata ido na wasu mintuna, sannan yai ƙwafa ya tashi ya fita.
Widad tana gadon Asibitin nan, ko iya miƙesa ba tayi, amma a haka aka sakata a wheel chair, Aka kaita mota aka maida ita wannan gidan da ake ɓoye ta.
Haka aka maida Ita, yau s bsta wannan maganin gobe a ɗurma mata wannan Allurar, haka take ta fama ga ciwo yaƙici yaƙi cinyewa, banda izayar da Bulama ke mata akan ta bada takaddun nan.
Kwanci tashi asarar rai, Yusuf ya cika sati uku cif a gidan yari, rana ta zagayo aka koma dashi kotu domin ci gaban shari'arsa.....
0 comments:
Post a Comment