Barrister Sadik yace "zan fara gabatarwa da kotu shedarmu ta farko akan cewar Yusuf shine yayi garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula"
Nan Barrister ya kira wani mutum, mutumin ya fito ya tsaya ya fuskanci kotu, Barrister ya taka gaban sa yace "ko zaka iya faɗawa kotu sunanka?"
Mutumin yace "Sunana Sada"
"Kasan wannan" yai mavanar yana nuna masa Yusuf.
Sada yace "eh nasan shi"
"Meye a tsakaninka dashi?"
Sada yace "Eh nasan shi, sunanshi Yusuf, yana kawomin gyaran motoci"
Barrister Sadik yace "yaushene ganinka na ƙarshe dashi?"
"Eh ganina dashi na ƙarshe shine, ranar daya kawomin wata mota yace in siya, nace masa gaskiya ni bana siyan mota sedai zan haɗashi da masu saida mota, bayan na haɗashi dasu se aka kawon lambar motar da na kawo maka, wadda ta kasance lambar motocin gidan Daula ne "
Aikuwa aka kawo lambar mota aka nuna a kotu, wannan lambar ita ce lambar dake jikin motar da Yusuf suka fita aka sace su a cikinta, tunda Yusuf yake be taɓa ganin wannan mutumin ba me suna Sada, amma yau an samoshi an masa sharri.
Yusuf yai shiru ya dafe kai, ya kasa cewa komai.
Barrister Khalil yace "Sheda na gaba da zan gabatarwa da wannan kotu shine wanda ake zargin tare suka haɗa kai da Yusuf suka sace 'yar gidan Nasir Daula wato Saleh"
Aka shigo da Saleh, yana takawa da kyar wanda gaba ɗaya ya fita a hayyacinsa, kallo ɗaya zakayi masa kasan bashi da lafiya aka rakitoshi.
Akaje aka tsaida Saleh, Barrister Sadik yace "Malam Saleh, ko zaka iya gayamana waye kai a gidan Daula?"
Cikin murya ƙasa ƙasa yace "Ni tsohon sojane, kuma hadimi a katafaren gidan Daula"
"Waye wannan?" ya nuna masa Yusuf.
"Shine direban 'yar gidan Daula, shi yake kaita duk inda zata je"
Barrister Sadik yace "ya akayi kuka haɗa baki kuka sace ta, harka basu mafaka?"
Saleh ya kalli Yusuf, ya sunkuyar da kai yace "Bayan Yusuf yayi duk shirin daze, ya nemi da ina nema masa inda ze zauna ya ɓuya, ba tare da an gano inda suke ba, yayi Alƙawarin ze bani kuɗi, ni kuma na yadda na amince, daya sato ta na gaya masa inda zamu haɗu, shine na kaisu wannan ƙauyen daga baya ya je ya saida motar, muka raba kuɗin "
Yusuf ya ƙurawa Saleh ido, amma Saleh ya kasa ɗaga kai ya kalli Yusuf, ya sunkuyar da kai yai shiru, yakasa kallon Yusuf, shima Yusuf bashi da zaɓin daya wuce ya sunkuyar da nasa kan, Umma se kuka take tana mamakin, ya za'ayi ace ɗantane yai wannan abubuwan haka? "
Barrister Khalil yace 'idan kotu ta bani dama, zan gayyato Malam Audi, wanda shine Saleh ya nemo ya ɗauki Yusuf da' yar gidan Daula, a ƙurƙurarsa zuwa cikin ƙauyen da akayi garkuwa da ita"
Malam Audi ya fito shima, Barrister Khalil yai masa tambayoyin duk daya dace yai masa, shima ya bada amsa, kamar yadda aka buƙata.
Barrister Khalil, ya kira doctor Mustapha wanda shine Likitan daya duba Widad lokacin da aka harbeta, shima ya fito ya tsaya ya bayyana sunansa a gaban kotu.
Barrister Sadik yace "Doctor Almustapha, kaine Likitan daya karɓi 'yar gidan Daula, lokacin da Wannan bayin Allah suka kaita Asibitinka ha akayi?"
Doctor Mustapha yace "eh hakane, Wataran da safs ina aiki, suka shigo cikin Asibiti na, ɗauke da wata matashiyar budurwa wadda take a galabaice, jini nata zuba daga jikinta, suka shiga da ita Office ɗina, sukace patient suka kawo in duba musu, nace musu bazan karɓi case ɗinba, saboda harbine a hannunta, amma Saleh ya ciro bindiga yace idan banba ze kasheni, haka na cire mata bullet daga jikinta, ko gama watstsakewa ba tayi ba suka ɗauketa suka gudu"
Justice Abdullah A dutse yace "wanda ake ƙara ko kana da abunda zaka ce?"
Yusuf ya girgiza kansa alamar A'a, ya juya ga Barrister Sadik yace "muna saurarenka Barrister"
Barrister Sadik yace "ya me girma me shari'a, wannan sune ƙwararan shedunmu da zamu gabatarwa wannan kotu, sannan in Allah ya yarda a zaman kotu na gaba zamu ƙarasa kawo shedunmu da tarin hujjojunmu, wanda zasu tabattar da wanda ake zargi shine ya sace 'yar gidan Alhaji Daula"
A dutse yace "duba da yadda barrister ya gabatarwa da kotu shedunsa, kuma aka tambayi wanda ake ƙara be musa ba, da kuma yadda Barrister ya nema, wannan kotu tayi umarni da' a maida wanda ake zargi gidan gyaran hali, zuwa sha biyar ga wata me kamawa"
Daga nan ya buga gavel, wato gudumar kotu.
Yusuf ko ɗaga kai baya yi, saboda bashi da idon daze kalli al'umma dashi mussman masoyansa, wani abun idan ba'ayi ba anyi wank, ga tarin hujjoji da shedu da aka gabatar, shi kuma gashi ba masanin fannin shari'a ba, to idan ya musa ma yace me? Bashi da zaɓin daya wuce ya amsa, haka aka kuma zura shi a motar gidan yari, ba'a bari 'yan jarida sunyi magana da shi ba, kowa wani yayi magana da shi ba aka tafi da shi.
Koda Nurat taga yadda kanun shari'ar ya gudana yau gaba ɗaya ta ɗimauce, ta rasa inda zata saka ranta yanzu shikenan babu wanda ze tsayawa Yusuf kenan? Dukda wannan shedun da aka gabatar har yanzu zuciyarta bata saduda ba, tana jin sharri ne kawai akewa Yusuf ɗin.
Ta fita taje ɗakin Mummynta, ta tarar tana salla, ta ɗauki wayarta akan gado tai waje, bata tsaya ko ina ba se ɗakinta, ta shiga ga kulle ƙofa ta ciki ta kira Khalil.
Yana ɗagawa ta fashe masa da kuka, yace "subhanallah, Nurat ya haka?"
"Khalil kana gani an gabatar da shedun ƙarya akan Yusuf, shikenan haka za'a bari a kulle shi, ba zaka iya komai ba?"
Khalil yace "Nurat, abun ya wuce tunanin ki, ke yarinya ce kuma kina gida a zaune baki san meke wakana ba, wallahi ana nan ana barazana ga duk wanda yai yunƙurin shiga shari'ar nan da nufin kare Yusuf, kedai ki cigaba da Addu'a, Allah zeyi ikonsa, kuma..
Ai bata jira meze ƙarasa faɗa ba, ta ajiye wayar tai shiru ta dafe kai, ta rasa abunyi dan yanzu kukanma bata iyawa, gaba ɗaya taji kamar jiri na kamata, ta buɗe ƙofa ta fito tana dafa bango, sedai tama zuwa falo kawai ta faɗi a gurin, hakan yai dai dai da shigowar Alhaji Musa, ya ƙaraso kanta da sauri yana kiran sunanta, sedai bata san meke cewa ba.
Ya ɗakko ruwa me sanyi yana shafa mata, a hankali ta dinga sauke numfashi, Mummynta ta fito falo kawai ta tarar da Alhaji Musa rungumen da Nurat yana shafa mata ruwa.
Tace "subhanallah, Daddy meye ya sameta?"
Alhaji Musa yace "nima ina shigowa na tarar ta faɗi ƙasa"
Tace "subhanallah, ko Asibiti zamu tafi?"
Yace "A'a, ɗan tsaya muga naga kamar ta farfaɗo"
Yace "Nurat"
Ta buɗe idonta ta kalle shi tace "Na'am Daddy"
Yace "meke damun ki ne haka? Ina shigowa naga kin faɗi, meke damun ki?"
Ta girgiza masa kai alamar bakomai.
"Kyace fa bakomai? Gata nan ko Abincin kirki bataci, na rasa meke damunta, bayan tea ko biscuit, bayan nan bata cin komai, haka yake wuni duk tabi ta ƙare ta bushe"
Ya kalleta cikin kulawa yace "meke damunki ne Nurat, meyasa bakya cin Abinci? Duk kin rame"
"Daddy ni bana son tafiya karatun nan dan Allah ka ƙyaleni"
Yace "shiyasa bakya cin Abincin?"
Ta jinjina masa kai, yace "zanyi shawara, fitinarki da rawar kanki ce tai yawa, shiyasa nake son turaki can, zanyi shawara amma kidena ƙin cin Abinci"
Ya ƙura masa ido, yana sonta dukda halinsa dayake ita 'yarsa ce yana sonta, amma meyasa ze jefa rayuwar' ya'yan wasu cikin damuwa? Adalci kenan hakan? "
Hawaye ya shiga gangarowa gefen idonta, ya dinga share mata yana ya isa haka, tashi muje ki kwanta ki huta anjima zan kira likita yazo ya dubamin ke.
Ya kama hannunta, ya kaita ɗakin ta ta kwanta, sannan ya fito ya rufe mata ɗakin.
Yauma Widad na zaune, ta ari wayar sabuwa ta duba yadda shari'ar ta kasance, sedai babu wata hanyar mafita ko nasara akan lamarin, babu wata hanya da zata bi ta temaki Yusuf, gashi bata da tabbacin da wace manufar wannan matar ke nuna mata kulawa da tausayi, saboda Bulama makirine, babu abunda baze iya ba, haka ta bata wayarta ta, ta koma ta kwanta, tare da lumshe idonta.
Har yanzu tana jin alamun cikin ta na nan, dan babu abunda ya sauya na daga abunda takeji, na laulayi shikuma Doctor Hamisu ya tabattarwa da Bulama cikin Widad ya fita, gaba ɗaya ta koɗe kamar ba Widad 'yar ƙwalisan mam ba, matashiyar' yar hamshaƙin attajiri, 'yar gayu me cin zamaninta ba, duk tayi wani iri, ga tashin hankali da tunani ha pressure ciki, abunda bata saba ba bata san yadda yake ba, ga kuma sauran ciwukan da suke damunta, banda uban duka da take sha a hannun Bulama, da sauran mugunta da yake mata.
Yusuf yana zaune a gidan yari, akace yazo yayi baƙi, shi dai yasan an dena barin kowa yazo inda yake, Umma ma sau ɗaya aka bari ta ganshi, ko saƙo aka kawo masa ba bashi ake ba, haka yake zamansa a wahale, Yusuf ɗan gayu daya saba da tsafta, rayuwar gidan nan ba ƙaramin wahala take masa ba.
Aka fito da shi zuwa ofishin gandirobobi, yaga wannan ɗan sandan me kula da sashin manyan laifuka, daya zauna a sashensa lokacin da yana hannun 'yan sanda, wanda ya dinga azabtar dashi, Yusuf na ganinsa ya sake haɗe rai ya ƙaraso ya zauna.
Ya kalli Yusuf yai murmushi yace "haba Yusuf, ba faɗa meya kawo gaba kuma? Meye na haɗe rai dan ka ganni, ashe an fara shari'arka?"
Yusuf yai masa banza yaƙi magana, yace "shikenan, tunda bazakamin magana ba, na fuskanci kai dai halinka ne a haka, miskilanci da taurin kai, zamanka a hannunmu be sa ka canza ba, kai dai haka Allah yayi ka kenan?"
"mekazo yi gurina? Bayan an hana kowa yazo gurina kai meyasa aka barka kazo gurina, me zan maka?"
"kwantar da hankalinka, ai dole zan gaya maka ms zakamin".
Yasa hannu a aljihunsa, ya ɗakko biro da farar takadda a cikin wani file, ya miƙawa Yusuf yace "ɗan Yimin signing ɗinka a nan in gani"
Yusuf ya kalli takaddar ya kalli ɗan sandan yace "na menene wannan?"
"kai meye naka na tambaya? Ka saka hannu nace"
"bazan saka ba" ya bada amsa kai tsaye.
"Ni kake cewa bazaka saka ba, kai idanma tinƙahonka kaima ɗan sandane, aiko a aiki na girmeka, haka a shekaru ni zaka gwadawa taurin Kai?"
Yusuf yace "eh bazan saka hannunbau, bazan saka hannu akan abunda ban san meye ba"
Aikuwa ɗan sandan ya kashe Yusuf da mari, Yusuf kuma ya rama, kafin kace kwabo gandirobobin nan sunyo kan Yusuf da duka, kota ina suka haɗu suka masa lilis, ko motsi baya iyayi, sannan aka sureshi aka maida shi, a galabice.
Ɗaurarrun gidan dayawa sun sanshi, baya magana ba ruwansa da kowa, kamun kansa yasa suke girmama shi, musamman da suka jiya ana masa laƙabi da maitama, akace musu ɗan gidan marigayi Bashir maitama ne, su suka karɓeshi, suna mamakin wane laifin yayi aka kama shi aka dake shi haka? Suka samo ruwan zafi a kitchen aka dinga gasa masa inda ha farfashe a jikinsa.
Duk takurar da akayiwa Yusuf akan ya gwada yin signing ɗinsa, su sake gwadawa dana Bulama su gani ƙi yayi, aka ƙara tsananta masa a gidan kurkun nan, hantara cin mutunci zagi, ayyuka ma wahala amma Yusuf yaƙi sakawa fafur, danma wani abun fursunoni sukan shigar masa saboda suna ganin salihancinsa da haƙurinsa be kamata a dinga cuzguna masa ba. Ranaku gudu suke, lokaci na ƙara sauri, kamar ƙyaftawar ido, lokacin komawar Yusuf kotu yayi, suka sake shiga kotu domin cigaban shari'arsa.
A wannan karon kuma Barrister Saminune ya fito dan gabatar da shedu da hujjoji akan Yusuf.
Barrister Saminu ya gabatar da kansa, sannan yace "kamar yadda wanda aka yi ƙara yayi da'awa a hannun 'yan sanda cewar a hukumance aka bashi umarnin yayi aiki a gidan Daula, domin bawa' yarsa kariya, sedai a iya binciken 'yan sanda babu wanda ya sashi wannan aikin, sannan hukumar' yan sanda tayi Allah wadai da abunda yayi sun sallameshi daga aikinsa gaba ɗaya, kuma abokin aikinsa me suna Abbas Habib, wanda wanda ake ƙara yace shine shedarsa akan an sashi aiki a gidan Daula, ya tabattarwa da kotu cewa, Babu wanda yasaka Yusuf wannan aiki, Yusuf ƙarya yake masa dan haka Yusuf yayi basaja ne a gidan Daula, yaje da suffar mutanen kirki danya sace 'yarsa "
Babu abunda ya bawa Yusuf mamaki se jin sunan Abbas, da kuma abunda akace yace a game dashi, ya jinjina kai ya tuna yadda Widad take nuna tsanarta ga Abbas, ashe Abbas ze iya yi masa haka? Sekuma yai tunanin Amma Suleiman yana kotun nan, kenan shima baze iya taimakonsa ba? Yusuf yai shiru kawai yana sauraren ikon Allah.
Babban Abun mamaki, harda su Ramlah aka kira a matsayin wanda zasu bada sheda akan Yusuf ne ya sace Widad.
Barrister Saminu ya kalli Ramlah yace "ko zaki iya shedawa kotu wacece ke?"
Ramlah tace "Sunana Ramlah, kuma Widad 'yar uwatace"
"ko zaki shedawa kotu abunda kika sani game da Yusuf, alaƙar dake tsakaninsa da Widad yarinyar daya sace?"
Ramlah tace "eh to, lokacin da aka kawo shi zeyi aikin direba, da bata aminta dadhi ba ita Widad, saboda halinta na rashin yadda, ganin mahaifinta ya yadda dashi, shiyasa itama ta haƙura da hakan ta yadda dashi a matsayin direban nata, Daya ke mukan ɗan gaisa da shi, wataran yake tambayata wai dan Allah nasan Password ɗin Widad na banki, dayake daga baya ta ɗan yadda dashi har ɗakinta yana shiga, nace masa me zeyi da password ɗinta na banki, se yace min bakomai tambayata kawai yayi, se nace masa nima ban sani ba, to haka dai Widad ta kan yi complaining akan ana mata sace sace bayan babu wanda yake shiga ɗakinta seshi, har wataran sukayi sa'insa ta kusa korarsa, mahaifinta ya hanata, sedai ba daɗewa wannan lamarin ya faru aka neme ta aka rasa "
Barrister yace " Shikenan, mungode Malama Ramlah zaki iya komawa kije ki zauna "
Yusuf yabi Ramlah da ido, har taje ta zauna, me shari'a yace " ko wanda ake ƙara, yana da abun cewa? "
Yusuf ya girgiza kai, ya maida kai ya sunkuya, Umma ta tashi da sauri ta fice daga kotun, tana kuka.
Barrister Saminu yace "idan wannan kotu ta bani dama, zan sake gabatar da sheda akan wanda ake zargi"
Wani ma'aikacine daga gidan gonar Daula ya fito, aka gabatar da shi a matsayin Iliya.
Barrister Saminu yace "ranar da abun ya faru, ance kana nan da daddare kana aiki a gidan meyafaru?"
Iliya yace "eh to, a ranar sunzo gidan dashi da Ita, da Alhaji Nasir Daula, cikin dare suka fito shida ita kamar ze nuna mata wani abu a wajen mota, kawai ya buɗe motar ya dannata ta ƙarfi, lokacin ina saman benen dake kusa da inda suke, kafin in sakko wasu mutane sun ɓullo daga gurin fulawoyi a laɓe, da alama dama suna laɓe ne gidan a ɓoye suka buɗe masa gate, Jin motsi yasa Daula ya fito a guje, yace lafiya? Se Saleh yace ai wasu mutane ne suka shigo suka fita da Widad, shine Daula ya faɗi a gurin "
Suleiman ya sunkuyar da kai kawai, dan kowa yaji yadda ake gudanar da wannan shari'a, tsantsar son zuciya ne kawai da rashin imani, wata irin bahaguwar shari'a ake ba fasali babu komai, kuma duk wanda ya bada sheda babu wani bin diddigi a masa tambayoyi dan tabattar da abunda yake faɗa, kawai se a karɓi wannan shedar.
Barrister Saminu yace "idan kotu ta bani dama, zan gabatar da sheda ta ƙarshe wadda itace me ɗungurungum, wadda zata tabattar da Wanda ake zargi shine yai garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula.
Yusuf ya ƙura ido yaga waye ze shigo, me ze gani Widad ce aka shigo da ita, tayi haske amma da gani kasan hasken cutane, ta rame tayi wani iri, duk wanda yasan ta a baya, idan ya ganta baze ganeta ba se mutum yayi dagaske, saboda tsabar rama da fita hayyacinta da tayi.
Yusuf yabi Widad da ido, yadda ta koma yana tunani daban daban a ranta.
Akaje aka tsaida Widad, amma ta gaza kallon Yusuf, yayin da Yusuf ya kafe ta da idanuwa, Barrister Khalil yace "ko zaki iya bayyanawa kotu wacece ke?"
"Widad Nasir Daula" ta bashi amsa, ba tare da ta kalle shi ba, ya nuna mata Yusuf yace "kin san wannan?"
Ya nuna mata Yusuf, ta jinjina masa kai, waye shi? Meye alaƙarki dashi? "
Bata kalli inda Yusuf yake ba tace "da farko direbana ne, yayi aiki tare dani a gidanmu"
"Lokacin da yayi aiki dake, kin san cewar ɗan sanda ne?"
Ta girgiza kai, "Ana zargin shine ya sace ki, yai garkuwa dake, me zakice akan haka?"
"Eh Yusuf yayi garkuwa dani, na zauna a hannunsa tsawon watanni biyar, sedai babu wani abu na cutawarwa ko tsoratarwa da yayimin"
"Ya isa haka Malama Widad, zaki iya tafiya"
Barrister Khalil ya katseta, ganin hawaye ya cika idonta tana neman ta saki layi, aka fito da ita zasu tafi, se a lokacin ta ɗaga kai ta kalli Yusuf, taga yadda yake binta da kallon da bata gane na menene ba? Hawayene ke shirin gangarowa a idonta, ta girgiza masa kai, ta fita daga cikin kotun.
Tana fitowa tai karo da Umman Yusuf, cikin kuka Umma tace "Wallahi keda Allah, Allah ya sakawa ɗana, wallahi Allah ze bi mana haƙƙinmu, saboda rayuwarki ta ɗana ta kassara, a sanadiyarki aka kashemin miji, yanzu gashi sanadinki za'a kullemin ɗa, bayan danke duk ya shiga wannan halin, Allah yana kallonki fa, kiji tsoron Allah "
Umma na zubda hawaye, Widad na zubda hawaye, tana son tayi magana amma ta gimtse maganarta saboda abunda hakan ka iya haifarwa, ta shige mota ba tare da ta cewa da Umma Uffan ba.
Alƙali ya sanya sati biyu, domin yanke hukunci na ƙarshe akan Yusuf, kotu ta watse ana Yusuf bashi da sauran mafita, tunda ita da bakinta ta tabattar da ya sace ta.
Gaba ɗaya hope ɗin Yusuf ya ƙare, tunda Widad ta tabattar da hakan ba shakka bashi da mafita sam.
Abun duniya ya ishi Widad, aka maida ita inda ake tsareta a gidan Bulama, ta ɗora hannu a kanta tana wani irin kuka, jikinta har rawa yake, zuwa yanzu tana jin yadda abunda ke cikinta yake ɗan motsawa kaɗan kaɗan.
Bulama ya shigo ɗakin da Widad take, yana kallonta ya kwashe da dariya yace "ban taɓa tunanin zaki so wani abu a rayuwarki bayan mahaifinki, kamar wannan shashashan Yaron ba, kamar ma kinfi sonshi akan Daula, sedai na ƙarar da soyayyar a nan, na saka mata aya, tunda gidan yari za'a kaishi"
Widad ta kalli Bukar tace "Kayi kuskure, kai Yusuf gidan yari baze taɓa kawo ƙarshen soyayyar da nake masa ba, dukda kai ba mutum ne me cika Alƙawari ba, nasan ba lallai ka cika Alƙawarin da kamin akan Yusuf ba, ni dai fatana kamar yadda mukayi da kai kar kuyi sanadiyyar rayuwarsa dan Allah "
Tai maganar tana kuka a gaban Bulama, yai dariya yace " wannan kaɗai be isa in bar yaron nam a raye ba, harse kin gayamin inda kayan nan suke "
Widad ta kalle shi tace " A zatonka kafini wayo da dabara ne, to bari in gaya maka abunda baka sani ba tsayin shekaru, Daula ba dukiyar ya ɗauka ya danƙamin ba, ya naɗi video akan yadda takaddun suke, da yadda dukiyar take da kuma a inda take, ni kuma dana tashi na bawa Amintacce na ya ajiyemin, nasan ko bayan raina, idan ya gano ajiyar dana bashi ze danƙa amana ga masu ita "
Tai maganar tana tsura masa ido, nata cikin nasa.
" me kike nufi, suna gurinwa? "
" Gurin masoyina mana, da kake so ya ƙare rayuwarsa a prison, seka bari ranar daya fito seya baka "
Ya wanketa da mari da wannan Ƙaton hannun nasa, idan ya mareta har wani jirine yake kwasarta, amma ta dake tace "idan ka kasheni, ka kashe dukiyar da kake nema, ka huta, shedar tana gurinsa, mabuɗin yana gurina, dan haka dabara ta rage game shiga rijiya"
IDAN KIN SIYA AMANACE, IDAN KIKA FITAR KUMA KINCI AMANA!!!
Ayshercool
07063065680
11/24/21, 10:26 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
136_137
Bulama ji yayi kamar ya shaƙeta ya huta da wannan baƙincikin, daga wannan se wannan, daga wancan se wancan se wasa take masa da hankali, ya miƙe kamar ze fita ya juyo ya kalleta, yasa ƙafarsa ya dinga dukanta yana taka ta, tasa hannu tana tare cikinta saboda karya dakar mata ciki, danshi ya sakankance cikin nan babu shi ya fita tuni.
Haka ya dinga Takata da ƙafarsa, ko kukan bata iyawa sedai hawaye dake zuba kawai kamar an kunna famfo, yai me isarsa ya dinga zaginta ita da Daula, yai ya gama yasa kai ya fice.
Widad tai kuka har hawayen suka gagara zuba se ƙunar rai da take, tana jin abunda ke cikinta yana motsawa kaɗan kaɗan, ta tuna yadda Yusuf ya dinga binta da kallo, kana ganinsa kasan a tsatsanr wahala yake, fuskarsa duk tabo da raunuka na ciwo.
idanunta sukayi jawur, kamar wadda aka zubawa barkono saboda kuka, ta sunkuyar da kanta ta shafi cikin ta, da take jin motsinsa kaɗan kaɗan a can ƙasar mararta, cikin zubda hawaye tace "wace amsa zan bawa abunda yake cikina, idan har ya girma ya samu labarin mahaifiyarsa taje kotu ta bada sheda akan mahaifinsa an kai shi prison? Shedarma ta ƙarya, nasan duniya zata zageni ga duka wanda yasan ainihin abunda ya faru, sedai ba yadda na iya, nayi hakanne da ceton rayuwarsa, kaicona haɗuwa ta da Yusuf ta zame masa babbar ƙaddara a rayuwarsa, ya sadaukar da rayuwarsa don inganta tawa, amma maƙiyana suna ƙoƙarin cin galaba akanmu, abun da basu sani ba shine, tun ran gini tun ran zane, ita gaskiya duk daren daɗewa zata yi halinta"
Tai maganar ranat yana mata wani irin zafi da raɗaɗi.
Yusuf kam ya sha mamaki da Widad taje ta bada sheda a kotu, akan cewar saceta yayi sedai yanayin daya gantabya tabattar masa akwai lauje cikin naɗi, akwai abunda yake damunta, da gani duk inda take ba'a kwanciyar hankali take ba, amma duk da haka ya zaci zuwanta kotu ze zama sassauci a gareshi, sedai zuwanta kotu ya zama ƙarin tsanani a gareshi, yanzu kam ya haƙura yasan idan ba ikon Allah ba, bashi da wata hanyar kuɓuta sam.
Alhaji Haruna kwana biyu ya samu sauƙi, Amal ta dena bibiyar sa, sedai ba ƙaramar kassarawa tayi masa ba, kwashe masa kuɗin Account da tayi, gashi ba damar kai rahoto yaje ya ɗaure kansa da kansa, gashi gaba ɗaya yanzu wanda zs nemi shawarar tasu hankinsu na kan wannan shari'a da'ake fafatawa.
Bulama gaba ɗaya yakasa nutsuwa, dukda wannan shirin da wannan shirin da yake yi, slide mistake Asirinsa ze iya tonuwa, kuma yasan koda tsiya, koda Arziki Yusuf baze bada abun nan ba, yayi signing ma a tabattar wannan signing ɗin nasane, me shige dana Daula amma yaƙi, babu irin dukan da baa'yi masa a gidan yarin nan ba amma fafur Yusuf yaƙi sakawa, wane ma tabbaci yake dashi akan cewar Recording ɗin yana gurin Yusuf, dan rainin hankali ba wani abun wahala bane a gurin Widad, zata iya raina masa hankali tace yana gurin Yusuf amma baya gurin nasa, nan ya dinga takura Ƙwaƙwalwarsa, akan lallai seya gano mafita.
Umma kuwa tun daga ranar da Widad ta bada wannan shedar taji ta tsane ta, bata sonta duk wannan halin wahalar sanadiyyarta ya shiga amma taje ta bada shedar zirr, gashi a maganar da Yusuf yai mata ranar da sukaje ganinsa a prison ya gayamata wai Widad ɗin matarsa ce, ko ta yaya oho? Umma gaba ɗaya tunaninta ya tsaya, bata da yadda zata yi wanda zata temaki Yusuf dashi.
Ta kira Suleman tace "dan Allah idan baya komai yaje tana son ganinsa"
Bayan awa ɗaya da rabi, sega Suleiman yazo suka gaisa sannan tace "Suleiman, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi da ƙoƙarin da kake ta min, amma ina neman wata alfarma ne a gurinka"
Suleiman yace "To Umma ina jinki"
Tace "dama cewa nayi, ko zaka samo me siyan gidan nan, ai masa kuɗi a siyar, a saida Babur ɗin Yusuf, da gurin furnitures ɗinsa, a ɗauki lawyer me zaman kansa yaje kotu ya tsayawa Yusuf , ko Allah zesa a dace"
Suleiman yace "Umma da hakan ze yuwu, da tuni nayi wallahi base an siyar da gidan nan ba, har Office akamin aike daga sama, akace muddin nace zan saka kaina a cikin case ɗin nan, to tabbas zan rasa aikina, kuma nima za'ace dani aka haɗa baki, sannan a hanya aka kuma tsareni, akace idan nai involving kaina a case ɗin nan, to za'a kasheni da iyalina, kuma irin wannan barazana akewa duk wanda yai yunƙurin taimakon Yusuf, shiyasa kikaga an kasa komai a kai, bakiga inaji ina gani akace wai ba hukumar 'yan sanda ce ta bashi aiki ba, bayan kuma nasan ƙaryane ba, da hannuna na bawa Yusuf aikin nan, amma ina yunƙurin yin wani abu, komai ze kwaɓe "
Umma tai ajiyar zuciya tace" babu wanda ya bani mamaki irin Abbas, har gida yake zuwa ya ɗaukeshi su tafi gidansu yarinyar nan, amma saboda rashin imani, yace wai be san zancen ba"
Suleiman yace "kiyi haƙuri, ki dena kuka haka, dama ai si mutane kullum ƙara koya maka hankali suke, amma ina tabattar miki Yusuf baze zauna a gidan yari ba, gaskiya zata yi halin ta"
Umma tace "Allah yasa, ina fatan haka nima"
Nurat kam kamar ta ɗora hannu aka tai ihu, ta rasa abunda yake mata daɗi, wai ace Widad ya bada wannan shedar aka Yusuf, dukda irin yaddar da tayi dashi, tabbas da Yusuf yana neman wani abu a gurin Widad dabe dinga bata kariya ba, yanzu shikenan saboda shedar Widad, ta tabatta Yusuf yayi abunda ake zarginsa dashi, kamar wadda mintsina, ta tashi da sauri don taje ta sato wayar Mummy tai waya, sedai tana fitowa falo ta tarar daddynta yana kallon labarai, 'yan jarida na bayyana abunda ya faru a kotu, Alhaji Musa yace "Maman Nurat, kinga shari'ar yaron nan ko? Dama na faɗa miki, irinsa ba abun tausayi bane, gashi nan ita kanta yarinyar ta tabattar da abunda ake zarginsa dashi, bari in kira Bulama"
Ya ɗakko wayarsa ya kira Bulama, "Allah ya baka yawan rai, ai yau naga yadda shari'ar nan ta kasance, komai ya tafi daidai, kayi ƙoƙari gaskiya, haka ake son Amini, gashi baya nan amma ka tsaya tsayin daka akan sha'anin iyalinsa, gaskiya kayi namijin ƙoƙari, Allah dai yasaka da alkhairi"
Nurat bata iya jin abunda ake cewa daga ɗaya ɓangaren, amma tana ganin yadda Daddynta ke ƙyaƙyata dariyar mugunta a waya.
A hankali ta juya ta koma ɗakinta, tana hawaye tace "Allah sarki Yusuf, ya za'ayi in fita in gayawa duniya cewar ba kai kayi garkuwa da Widad ba, da saka hannun mahaifina a sace su Yusuf? Ta yaya? Tabbas idan aka rufe Yusuf ba'a masa adalci ba, definitely tasan akwai yadda akayi har suka kuɓuta aka kamasu a ƙauye, amma Yusuf baze garkuwa da Widad ba, ta zauna tai shiru tana tunani, bata san ta ina zata fara temakawa Yusuf ba, amma tabbas ƙarshen zalunci an masa.
Ramlah ce tsaye akan Fahad tana zazzaga masa masifa, "Wallahi Amal baka isa ba, tun wuri ka maida hankalinka, nafi ƙarfin ka wulaƙantani, wato ka gama dani ka kama wasu, to baka isa ba tun wuri kaje ka turo azo ayi maganar Auren nan"
Fahad yai wata irin dariya sannan yace "Ramlah kenan, waye yake yaudarar wani tsakanin nida ke, dama a rashin wannan yarinyar ne, tuntuni tun ina ƙasar waje kin san ita zan aura, kuma gata ta dawo, dan haka me kike so inyi miki kuma? Kawai ki rungumi sorry, in kin samu wani wanda zaku daidaita se ku haɗe, dukda dai bance ke mummuna bacd but gaskiya ga balarabiya ina kallo bazan aureki ba, sorry kawai "
" Ni kake kallo kake gayawa haka? Lallai baka san Ramlah ba, kai ƙaramin ɗan isaka ne, wallahi baka isa ba, zaka ga abunda zan maka "
Fahad ya busa hayaƙin shisha sama sannan yai murmushi yace " Hmm keme baki san waye Fahad ba, karki bari ki gane waye Fahad tabbas "
" Ni kake gayawa haka ko? "
"Na gayamiki ɗin, dama haka bariki ta gada, kuma ki shiga hankalinki tunda wuri, tun ban saɓa miki ba"
Ramlah ta kalleshi tai ƙwafa, tai waje a matuƙar fusace, tana fitowa tai karo da Hajiya Sarah ta fito zata fita, mamaki yakamata ganin Ramlah daga part ɗin Fahad, ta tsaya Ramlah ta ƙaraso, tana ƙoƙarin buɗe motarta, Hajiya Sarah tace "Ramlah, lafiya kuwa? Me kika je yi ɗakin Fahad? Ina fatan lafiya?"
Ramlah ta kalleta tace "ba lafiya ba, kuma wallahi ki gayawa ɗanki ya saurari abunda ze biyo baya"
Hajiya Sarah tace "lafiya kuwa? Meya haɗaki da Fahad ɗinne? Me yayi miki ne?"
"Ki tambaye shi, shi yasan me yayi, kuma ya jira sakamakon abunda yayi min"
Ta bankaɗa ƙofar motarta ta shige ta jata a guje, mamakine ya cika Hajiya Sarah, ta shiga part ɗin Fahad, tana zuwa ta tarar yana shan shisha ta kalle shi tace "Fahad, wato har yanzu baka dena shaye shayen banzan nan bako, kana kawo mana matan banza har cikin gidan nan, kasa ubanka yazo ya kamani da faɗa da masifa, wallahi kaji tsoron Allah, ita kuma Ramlah meye ya haɗaka da ita?"
"wani abun tace miki na mata?"
"Ban sani ba, me take a part ɗinka? Ko itama shashancin kuke yi?"
"Mum dan Allah ki bar wannan maganar, kawai wasu suratanta ne na banza, marasa tushe balle makama, tazo ta nawa mutane Hayaniya a ka"
"wane irin Hayaniya ce? Gayamin kasan halin uwatta sarai, daga ita har yaranta ba mutunci suka cika ba, har gara Anwar ma, amma wannan me soyayyen idon, idan ka sake wani abu mara daɗi ya haɗaku dasu, wallahi duk abunda suka maka kai ka janyowa kanka, kaje ka ƙarata kai da uwarsu, idan yaso ubanka yasan yadda zeyi dasu, tunda 'yan uwansa ne, na gaya maka, tunda wannan rayuwar ka zaɓawa kanka Fahad, gaka nam ga duniyar kaje kayi Allah ya temaka "
Ba ce mata komai ba, ta fito ta baro ɗakin nasa, zuciyarta sam babu daɗi, ace yaronta na farine ke irin wannan mummunar rayuwa haka, ranat baya mata daɗi Sam.
Amal ta rasa yadda zata yi da uban kuɗin data damfari Alhaji Haruna, gashi sam Mummy bata san abunda ya faru da ita ba, balle tasan da wannan uban kuɗin data damfari Alhaji Haruna, sedai Amal ta kasa gane abunda yake damunta, gaba ɗaya yanzu kullum cikin ciwo take, nan ciwo can ciwo, abun ya fara damunta, ta yanke shawarar zata je ganin likita zata je taji meye yake damunta haka.
Ramlah kuwa data bar gidan Bulama kamfaninsa ta tafi, yana tsaka da aiki yana shirin shiga meeting se gata, babu sallama babu komai ta tsaya ta tstsareshi da ido.
"Ke lafiya kuwa? Ni na rasa waye yafi hanki tsakanin ke da babarki, ya zaki zo ki tsaya a kaina haka kina ƙaremin kallo babu ko sallama"
"kaga suararamin kawai, tsason shekaru kana juya mahaifiyarmu, muna abunda kake so, wancan satin har kotu kasa naje na bada sheda akan wannan sharia'r, to nazo da buƙatata guda ɗaya tam, da nake so kamin"
"wace irin buƙatace haka? Bayan seda aka baki wani percentage kema, kuma idan kuɗin nan suka samu hadda ke za'a ci"
"Niba kuɗi zaka bani ba, shekaruna sun na ina zaune a gida na gama karatu bana aimin fari, balle na baƙi, kuma ɗanka Fahad ya taɓa min Alƙawarin Aure, dan haka tunda wuri azo ayi maganar da za'ayi a wuce gurin"
"Nifa ban gane maganar da kike ba"
"Kamar yaya baka gane me nake nufi ba? Wane yaren nakeyi maka? Ɗanka Fahad ya Aureni"
"Haba Ramlah, wacs irin kwaɗon magana ce wannan haka mara daɗin ji? Baki san Widad ze aura ba?"
"ban saniba, kuma matsalar kuce ba ta Ramlah ba, kawai ayi maganar da za'ayi"
Bulama yace "ni kike wa magana a haka? Ƙwarai kuwa waye kai a gudina da bazan maka magana a haka ba, ina ƙarewa 'yar gidan Daula shekaru ta kwashe tana maka wulaƙancin data ga dama, balle kuma ni da kake wa kallon biri ina maka ta ayaba, kawai kayi abunda ya dace, ko kuma komai ya faru "
Bulama yace " Ramlah, ban san meyasa kike haka ba? Kema kin san aurenki da Fahad ba abune me yuwuwa ba ko? "
" Aurena da Fahad, ba abune me yuwuwa ba, ka gayamin shima ya gayamin, nagode nima ku jira matakin da zan iya ɗauka "
Ta bar office ɗin Bulama, zuciyarta na ƙuna da raɗaɗin abunda sukayi mata, Amal na zaune a falo tana kallo, cikinta ss ciwo yake mata, ga wani irin ciwon baya da take fama dashi, gashi lokaci lokaci inda ta karye yana motsa mata.
Ramlah tana parking ta fito, ta buga ƙofar motar da ƙarfin gaske, tai ciki fuuuuu, kamar guguwa, Nura yace "Allah dai ya kwashe ma wannan baiwa Albarka, da ita da duk wanda suka je kotu suka bada shedar ƙarya akan Yusuf"
Murtalah yace "bari Nura, wallahi abun ya bani mamaki sosai, Amma nan aka zo aka taramu aka mana kashedi akan duk wanda yai wani yunƙuri, ze fallasa wani abu se an kasheshi, wayaga ta bakin magana, amma da tabbas nima sena bada sheda"
Isa yace "dan Allah Murtalah kaje ka bada shedar nan a saki Yusuf, wallahi zaluntarsa kawai ake yi"
Nura yace "Allah sarki duniya, kalli Isa wai kaine ke cewa ayi abunda za'a temaki Yusuf, abun da mamaki"
Isa yace "bari Nura, wallahi duk baƙin cikin mutum da iya ƙiyayyarsa, idan dai har mutum ya zauna da wannan bawan Allah, wallahi idan kaji za'a masa haka dole ka tausaya masa, kalli duk irin abunda muka dinga masa baya tanka mana, se azabar miskilancin tsiya a cikinsa kamar Uwarɗakinsa"
Nura yace "kai dai bari Isa"
Isa yace "kun san abunda ya ɗauremin kai kuwa?"
Sukace A'a
"Wai ashe Sani me yankan farce shima ɗan sanda ne, shine fa ya haɗani da Yusuf yace ɗan uwansa ne, dana gayamasa ana neman direba, amma naji wannan lawyern yace wai Abbas be san zancen ba, Amma duniya babu gaskiya, tabbas yanzu nake ganin gimbiyar Daula bata da laifi na ƙin mutane, ka yadda da mutum ya cuce ka a banza, yanzu duk wanda suke jikin Daula suna morarsa sune suke zalintarsa, kalli matar gidan nan ko sau ɗaya ba taje kotun nan ba"
Murtalah yace "iko se Allah, wallahi Isa da zamu samu dama ko iya wannan shedun muka riƙa, aka shiga kotu dasu zasu temakawa Yusuf, amma wallahi ina jin tsoro, kuma wallahi dani akan matar gidan nan zan bada shedata"
Nura yace "kai ita ta dameka, a samu a Yusuf ya kuɓuta, wallahi dukda nima inajin haushinsa yadda ƙirƙiri ya samu fada fiye damu a gidan nan, musamman ni daya nemi ya ƙwacemin aiki na, Amma gaskiya Yusuf baze aikata haka ba, kalli fa ko magana ake, idan aka sakota ko aka zageta seya haɗe rai yana ɓata fuska yana kare ta, wallahi da yayi niyyar sace ta da tuni ya saceta, akwai dai yadda akayi "
Nan suka cigaba da tattaaunawa suna hirar a tsakaninsu.
Ramlah kuwa tana shiga falo, Amal ta kira sunanta, Ramlah ta waigo a fusace tace " lafiya kuwa? "
" Ashe kema kim bada sheda a kotu akan Yusuf "?
" Eh na bayar se yaya? "
" Yakamata kiyiwa kanki adalci Ramlah, a bar bawan Allah nan da wahalar da aka jefa shi a ciki, bakya ganin saboda Alhakinsa ne muma namu ɗan uwan yana nan kwana da kwanaki ba'a ganshi ba, ga mahaifiyarmu se fama take da marurar hawan jini saboda damuwane da ɓacin rai? "
'Ke dalla sauraramin, an bada shedad kiyi abunda zakiyi, da aga Anwar da kar a ganshi be dameni ba, abunda yake gabana shi zanyi, kuma karki ƙara yimin wannan maganar"
Ta nufi ɗakinta, tana jin yadda zuciyarta take tafasa.
Tana zuwa ta jefar da Jakarta akan gado, ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗakko kwalaben syrup, kawai ta kafa kai ta kama tittilawa cikin ta, Hakan yai dai dai da buɗe ƙofar ɗakin da Hajiya Halima tayi, ta tarar Ramlah ya shanye kwalaben syrup ta faɗi a gurin, cikin fitar hayyaci.
"Na shiga uku, Ramlah me zan gani haka? Ramlah dama dagaske shaye2 kike? Me yasa zaki cuci kanki"
Sam Ramlah bata san me ake ba, tuni ta fara maye ta lula gajimare.
"Amal! Amal!" ta shiga ƙwalawa Amal kira.
Amal tazo tace "gani"
"Amal kinga, shaye2 Ramlah take yi, meke damunta haka zata faɗa wannan mummunar hanyar haka?"
Amal ta ɗan taɓe baki, tare da naɗe hannunta tace "Allah ya jiƙan Yaya Anwar, ba dan ya mutu ba, nan ya hukunta ta ya gayamiki ga abunda take yi, amma baki yadda ba, tuntuni take shaye shayenta, kuma wannan Fahad ɗinne ya koyamata, amma ba yau ta fara ba"
Hajiya Halima tace "Na shiga uku ni Halima, wannan wace irin masifa ce haka, Ramlah dama baki dena wannan halin ba, Kisha kwalba huɗu a cikin ki?"
Amal kam taɓe baki tayi tai nata guri ta barsu.
Kamar koda yaushe, yauma zaune suke suna tattaunawa, Bukar yai gyaran murya yace 'ga samu ga rashi, labaran kala biyune, masu daɗi da kuma akasin hakan, wannan yaron munyi magana da A dutse, ya tabbatar min a zama na gaba ze ƙarƙare shari'ar yaron nan, sedai wani hanzari ba gudu ba, ita wannan yarinyar da yake ita uwar Daula ce a jarabar taurin kai, taƙi bayar da abun nan, ba irin azabtarwar da banyi mata ba, amma taƙi ƙarshe ma se cewa tayi ai "Recording ɗin inda dukiyar take Daula yayi, ya bata itama bata san inda dukiyar take ba, kuma wai recoding ɗin yana hannun Wannan yaron Yusuf"
What! Cewar Alhaji Munir "to yanzu meye abunyi?"
Alhaji Musa yace "kawai aje kurkuku ta ƙarfin tsiya ace ya bayar"
Bukar yace "Mhmm, baku san azabar taurin kan mutanen nan ba, ya saka hannu kawai mugani a tabattar idan wannan signing ɗin nasa ne, me kama dana Daula, amma wallahi fafur yaƙi, shima an azabtar dashi kamar kamar me a gidan yarin nan amma yaƙi, na rasa abunyi"
Alhaji Haruna yace "a sake azabtar dashi mana, ya faɗi inda recording ɗin yake, ko kuma aje a ɗauke mahaifiyarsa, ai naga tana zuwa kotun"
Bukar yace "ai abun ya wuce tunaninku, idan mukayi wani yunƙuri zamu iya barin ɓarakar da za'a ganomu, komai a sannu ake samun sa, zan cigaba da bibiyar yadda za'ayi a samu"
Suka gama tattaaunawa suka watse, dama a office ɗin Bukar sukayi meeting ɗin.
Bayan fitowarsu Alhaji Haruna yacewa Alhaji Musa "Waini anya ba raina mana hankali Bujar keyi ba, yarinyar nan tana hannunsa fa, babu wanda yasan inda take, ta yaya za'ace ko yaya bata gaya masa wanj abun ba, nifa kamar mutumin nan raina mana hankali yake"
Alhaji Musa yace "kai dai bari kawai, kallonsa kawai nake yi, gaba ɗaya kuɗaɗenmu sun tafi akan wannan harkar, amma Har yanzu babu wata riba"
"ba gara kaiba akaina, ni kamanta wannan yarinyar ta damfareni, rabin kuɗin account ɗina ta kwashe fa"
"kasa a sato maka ita, kaci ubanta ta mayar maka da kuɗinka, ni yanzu kallon Bukar kawai nake idan be wasa ba, zan ɓallo ruwa...
LITTAFIN KUƊI NE, IDAN KIN SIYA AMANANE, IDAN KIKA FITARMIN KINCI AMANA, KIMIN ADALCI KIYIWA KANKI
AYSHERCOOL
07063065680
11/29/21, 8:55 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
138_139
Alhaji Haruna yace "kamar yaya zaka ɓallo ruwa?"
"Eh zan ɓallo ruwa mana, muddin naga za'a cuceni, zan tads husuma ne, daga fara harƙallar nan zuwa yanzu zunzurutun kuɗi nawa muka kashe? Haka abun yayi yawa, mutumin nan ba imani ne dashi ba, ze iyayin komai dan haka gara mu saka ido yadda yakamata"
Alhaji Haruna yace "hakane kam, shikenan se anjima se yadda ta yuwu"
Daga nan suka watse.
Ramlah har gari ya waye, tana tangaɗi bata san me takeyi ba zabo maye, kwalba huɗu ta shanye babu sirki da komai, tayiwa kanta caji na sosai, yayin da Hajiya Halima ta dinga kuka, ganin yadda shaye2 ya ratsa Ramlah haka, ga ɓatan Anwar yana cin zuciyarta, gashi duk 'yan kuɗaɗen data tara Shu' aibu ya karɓesu, ta rasa inda zata saka kanta.
Amal kam bata tasu takeyi ba, gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta, ta rasa takamaimai meke damunta, tana zaune tana danna wayarta taga wani business, wanda idan kayi investing kuɗinka, zasu nunnuku a lokaci kaɗan, nan da nan ta gyara zama tana sake duba yadda bayanin abun yake, ta shiga link ɗin group ɗin da aka bayar, taga yadda mutane keta comments wai sun sak kuɗinsu an riɓanya musu an basu.
Nan wani tunani yazo mata, dan wannan maƙudan kuɗin da suke account ɗinta bata san ya zata yi dasu ba, dan haka ta jarraba saka naira dubu hamsin, bayan awannin biyar aka turo mata dubu ɗari da biyu, abun ya bata mamaki, nan ta dinga murna akan ta samu sana'a daga kwance zata dinga samun kuɗi.
Widad se kaffakaffa take da Cikinta, kar Bulama ya gane cikin nan yana nan be fita ba, dan ya fara ɗagawa sosai tana jin motsinsa, wasu lokutan yaji yana motsi sosai, wani lokacin kuma yayi dankam motsinma se kaɗan kaɗan, mussman idan bata da lafiya, duk lokacin da taji ya daɗe be motsa ba se tai taɓa cikin tana addu'a Allah yasa ba wani abunne ya sami abunda take ɗauke dashi ɗin ba.
Cuta kuwa kullum a cikinta take, gashi babu me gayamata yi kaza bar kaza, ita dai Sabuwa ta kan tirsasata ne taci Abinci, amma babu magani ga kwanciyar ƙasa da take, da shan abu me sanyi duk se tabi ta kukkumbura, babu hanyar zuwa Asibiti, ga Fahad dayake yawan kawo mata farmaki wasu lokutan, dan haka baccinma ba iya shi take cikin kwanciyar hankali ba, sedai tana yi tama farkawa, gani take da nannauyan bacci ya ɗauketa Fahad ze shigo yai mata wani abun.
Haka rayuwar Widad ke tafiya a wannan gurin da take, gashi dai yafi ɗakinta na ƙauye nesa ba kusa ba, amma ɗakinta na ƙauye ya fiye mata daɗi da kwanciyar hankali akan wannan ɗakin da take ciki haka a cike da wannan damuwar da tashin hanaklin.
Se wajen laa'sar sannan Ramlah ta dawo hayyacinta, daga wannan muguwar buguwar da tayi, taje tayi wanka ta canza kaya, ta nemi abunda zata saka a cikinta, ba tare da ta kula kowa ba, Hajiya Halima ce ta bita ɗakinta, ta sameta tana ƙoƙarin fara cin Abinci.
Ta ƙare mata kallo sannan tace "Ramlah, wannan rayuwar ita kika zaɓawa kanki ko? Rayuwar shaye2, Ramlah kwalba huuɗ fa kika shanye a cikinmi, ke ko tsoron lafiyarki bakya yi, bakya tausayin halin da nake ciki ko? Ban san inda ɗan uwanku yake ba, ga wannan uban naku yana ta min barazana akan ze tonamin Asiri, amma a haka kike ƙara gayyato mana wata matsalar, meyasa haka Ramlah? "
" Dan Allah Mummy ki ƙyaleni injibds abunda ya dameni, ni Fahad ze kalla yace baze Aureni ba, bayan tuntuni yasan zaman jiran sa nakeyi, amma zemin haka"
"to yanzu dan yace naze aureki ba shine zaki kashe kanki? Shine zaki sha wannan maganin haka? Haba Ramlah shikaɗai me namiji ko shine autan maza, kina gani kuɗaɗen hannuna duka babu sun ƙare, shine yake kawo mana wanda suke siyan kadarorin nan fa a ɓoye, ki lallaɓashi ku rabu lafiya mu samu mu sake wawurarar abunda ya samu mu siyar, idan muka siyar seki ƙyaleshi, Allah ya baki wani ki aura"
"Mummy, ni gaba ɗaya ma nakasa gane kan maganganun nan da kikeyi fa, kamar yaya babu kuɗi a hannunki, ina duk kuɗaɗen da kika saida filayen nan? Duk suna ina, kuma ga wannan kuɗaɗen da ake saka rai na gurin Bulama daze samo a hannunta suma basu samu ba, abun yazo da rainin hankali fa"
"wai bana gayamiki ubanku ke tamin barazana ba, kin sam maƙudan kuɗaɗen daya karɓa kuwa hannu na?"
Ramlah tace "wai wannan jakin da yazo harya mareni kike nufi?"
"Eh, shu'aibu dai"
"to meyasa kike bashi?"
"Ramlah idan shu'aibu ya tinamin Asiri na kaɗe, dan na gama yawo, mutumin nan hatsabibin gaske ne, baku da wayo lokacin da muka rabu ai"
"Lallai Mummy, wallahi dana san hakane baza'a bashi ko kobo ba, sedai yaje ya tina karya fasa, yanzu shikenan mun tashi a tutar babu? Duk wannan baƙar wahalar da mukayi? Yana gefe kika dinga tura masa kuɗi, baze yuwu ba Wallahi"
"bazs yuwu ba kamar yaya? Ai tuni ya yuwu, bashi kuɗin nam sune rufin asirinmu, kuma karki kuskura kice zakiyi wani abu, kinji ma gayamiki sannan Ramlaj ki shiga hankalin ki, akan wannan mummunar ɗabi'ar, babu inda zata kaiki shaye2 ba abunyi bame, kuma ba cinyewa bane "
'mhmm Mummy kenan, yadda raina yake a ɓace idan har ba caji nayiwa kaina ba bana jin daɗi, kawai ki ƙyaleni idan kuma kina buƙatar in dema shaye2 to tabbas Fahad ya aureni, idan bahaka ba bakiga komai ba har yanzu"
"Ramlah ni kike gayawa haka?"
"Ai gaskiya na gayamiki ba wani abu bz, idan harya Aureni shikenan an wuce gurin saɓanin haka kuma, komai ma zaki iya gani"
Ta ƙarasa magana, tare da fara cin Abimcinta, bata sake bi ta kan mahaifiyarta dake kallomta da mamaki ba.
Jiki a saɓule Hajiya Halima ta tashi ta fita ta bar ɗakin Ramlah, ranta sam babu daɗi, wai yanzu Ramlah ce a wannan mummunar hanyar.
Alhaji Musa sosai yake jin zuciyarsa tana ɗarsa masa wani abiua ransa, yana zargin Bulama kawai ƙoƙarin kifesu yake yi, yana can yana zare zaren, dan haka dole zeyi wani abu a akai, ta ƙarƙashin ƙasa ze bincika ya hani ko Bulama na karɓar wani abu basi sani ba.
Yauma akazo akace ana son ganin Yusuf, ya zata ma ko Ummace ko Suleiman wani ya kawo masa ziyara, sedai still wannan ɗan sandan ya gani, se wasu gandirobobi, aka saka Yusuf a wani tsukakkaken ɗaki, da gashi sesu a ciki, aka zaunar da Yusuf ɗan sandan ya kalleshi yace "Hmm Nasan kayi mamaki, ganin yarinyar daka ceta ta juya maka baya taje kotu ta bada sheda akanka ko? Dama haka mata suke basu da tabbas, gashi tana can tana hutawa, ranar da za'a yanke maka hukunci, a satin za'a ɗaura mata Aure da Fahad Bukar Bulama.
A razane Yusuf ya kalleshi yace "Bukar Bulama kuma?"
"Au kana mamakine? Ƙwarai Ɗan gidan Bukar Bulama, wato Fahad, yanzu haka ta aiko mune gurinka, akam cewar akwai ajiyar wani recording data baka, ka gaya mana inda recorder ɗin take, zamu je mu ɗauka '
Hankalin Yusuf sam baya kan Ɗan sandan, sedai nanata Bukar Bulama day keyi a zuciyarsa, wato abu biyune ya haɗar masa, ga mamakin Jin an Ambaci Bulama da Bukar, to kenam shine Bukar ɗin da Widad take magana kokuwa? Idan shine ya akayi gake zaune a hannun sa? Idan ya cutar da ita fa? Sannan wani irin azababben kishi ya taso masa, dagaske Widad ɗinsa ce zata Auri Fahad?
'to idan bata aure shi ba me kake so tayi? Kaida rayuwarka zata ƙare a kurkuku, kuma taje har kotu ta bada sheda akan ka' wata zuciyar ta tunasar dashi, amma dukda wannan abun ya kasa jin tsanar Widad a ransa, shi wani irin tausayinta ne yake kama shi ma, kuma gefe guda zuciyarsa ma cigaba da begen sake kasancewa da ita.
"Kai Malam magana nake maka fa!"
Ɗan sandam yai maganar cikin tsawa, Yusuf be razana ba ya kalleshi yace "ita Widad ɗince tace maka ta bani wani abu ajiya?"
"zan maka ƙaryane?"
Yusuf yace "to meze hana kayi ƙarya, tunda mutum ne kai ba mala'ika ba, kamar yadda tace muku ta bani ajiya, tazo da kanta ta Karɓa, ta gayamin lokacin data bani, sannan ta karɓa"
Ɗan sandan yai ƙasa da murya yace "ka bani tunda wuri, ko kuma a ran mahaifiyarka"
Yusuf yace "Ran mahaifiyata yana hannun Allah, babu wanda ze iyayi mata abunda Allah be rubuta ze sameta ba, Magana ɗayace, ni bata bani komai ba, idan kuma ta bani ku kawota ta gayamin lokacin data bani ajiyar recording ɗin"
Ɗan sandan nan ya jinjinawa azababben baƙin taurin kai irin na Yusuf, ya kalli gandirobobi yace "ku tambayeshi"
Yusuf be motsa daga inda yake ba, suka dinga buga masa kulki kota ina, sedai yana ƙoƙarin karewa, babu wata gaɓa ta jikinsa da bata masa ciwo saboda azabar dukan da yake sha a kowane lokaci.
Suka farfasa masa jikinsa, banda targaɗe dake yatsunsa saboda duka.
'zaka bamu ko bazaka bamu ba"?
Yusuf yace "ni bata bani komai ba na gaya maka, karka ƙara tambaya ta"
Ya ɗaga hannu ze wanke Yusuf da mari, Amma jarumin ya riƙe hannunsa yace "karka kuskura ka mareni, kuyita dukana har lokacin da zaku ga na dena numfashi, tunda haka kuke so, amma karka kuskura ka sake ɗaga hannu kace zaka mareni"
Suka kum sashi gaba da duka, seda suka ga baya motsi, sannan hankalinsu ya kwanta, suka tafi suka barshi a gurin.
Widad na zaune kawai taji gabanta ya faɗi, hakan yasa kawai ta fashe da kuka, domin ta fuskanci kamar idan Yusuf yana cikin mawuyacin hali se taji wannan faɗuwar gaban, ai kuwa ta hau aikin kuka, tayi ta gaji ta haƙura, ta cigaba da yi masa addu'a, tans tuno irin haƙurin daya dingayi da ita, ga rarrashinta da yake yawan yi, da yadda ta koyi abubuwa da dama a sanadin zama dashi Yusuf mutum ne, wani irin shauƙin soyayarsa ne ke taso mata, ta rintse ido ko zata samu sassauci a zuciyarta, tana jin inama tana buɗe idonta ta ganata a kusa da Yusuf, lallai so ba ƙarya ne ba.
"Allah ya fitomin da kai Yoseef, ka dawo muyi rayuwa tare, mu rainin cikin nan tare da kai, nasan da muna tare zan samu kulawarka" tai maganar tana hawaye.
Can kuma tayi wani tunani a ranta, wani irin kallo Yusuf zeyi mata idan Allah yasa ya fito, bayan taje ta tsaya a gaban mutane ta tabattar da Yusuf saceta yayi.
Cikin kuka tace "wayyo Allah na, Yoseef kayi haƙuri ba laifina bane, nayi hakan ne dan in ceci rayuwarka, karsu kashemin kai, ban manta halaccinka a gareni ba Yoseef, ba yadda zanyi ne"
Sabuwace ta shigo da sauri tana faɗin "lafiya kike kuwa? Kinga ki dinga ramgwatawa kanki wannan kukan da kike yi haka, naji ance kina da ciwon zuciya gashi ba ganin likita ake kaiki ba, karki kashe kanki a banza mana"
"Ni ki ƙyaleni inyi kukana, baki san abunda yake damuna ba, ki rabu dani dan Allah ki ƙyaleni"
Sabuwa tace "A'a Allah ya baki haƙuri, na ƙyeki yi abunki som ranki"
Widad ta cigaba da gunjin kukanta.
"Allah ya isa tsakanina da kai Bulama, Insha Allah se gawar jaki tafi taka daraja, Azzalumi macuci"
Bulama yace "yi addu'arki da kyau, ai ina kusa ba nisa nayi ba, duk abunda zaki faɗa ki faɗa"
"me Yoseef yayi maka? Meye laifin da yayi maka da kake azabtar dashi haka, kake neman cutar da rayuwar sa Kasashi a garari?"
Bulama yace "saboda ya raɓeku, ni kuma duk wanda ze raɓeku, in dai ba dani ze haɗa kai ba in mallaki abunda nakeso to tabbas bashi da wani amfani, shiyasa nake kawar da du wani makusanta a gareku, ko wanda ke shirin sama muku farinciki, kum ɗaukake shi da matsayi me girma, dukda baki yadda da mutane amma naga ya zama wani abun yadda a gareki, nasa an jarabbashi koze aminta damu, ya karɓo abun hannunki ya bamu, sena fuskanci shima irinki ne, me taurin kan tsiya, kuma ya dasa hasashensa da bincikensa a kaina, Allah yasa na farga da suri, da yanzu ya kassarani, dan haka dole in koya masa darasi "
Widad ta ƙure shi da ido tace" Shikenan, ayi dai mu gani, na yadda da rayuwata da Yoseef da Babana jarrabawa ce Allah yake mana, kuma ina fatan muyi nasara, Allah ya nunamin ranar da zata zo ka wulaƙanta, ka tozarta a idon duniya "
Bukar yace " daha baya kenan, bayan ns mallaki wannan dukiyar, sannan Wannan uban masu koɗaɗɗen idon, yaƙi bada recording ɗin, yace shi baki bashi komai ba, dan haka a wannan karonma dole ki san yadda zaki yi, kodai ya bayar kodai yaita shan wahala harya mutu a kurkuku, kamar Yadda nasa a ka kashe Bala a gidan yari "
Widad tai murmushi tace " Yoseef be san na bashi ajiyar nan ba, dan haka Kadena yaudarar kanka da tunanin ko zaka samu abun nan cikin sauƙi "
Bukama ya ƙure ta ido, ta ɗauke kanta daga kallon inda yake, yama rasa me ze mata saboda tsabar wasa da hankali da raina masa hankali da take yi.
Ya kalleta yace " shikenan, a bakin ran mahaifiyar Yoseef "
" itakuma me tayi maka? "
" zaki fanshe ta ne idan kika bada abunda ake nema, dan haka ki zaɓa ko ki bani abunda na nema, ko kuma a bakin ranta"
"Abunda ka nema yana hannun Yoseef, kuma shima besan meye na bashi ba, sedai ka kaini gurinsa in karɓa maka, amma karka cutar da ita dan Allah"
"Se kuma kiyi, ba dai taken ki rainin hankali da iya wasa ba, to zaki gane kurenki"
Widad ta bishi da kallo harya fice, ta kwanta a nan inda take, ta lumshe idonta tana tunani.
Mutane nata sauraren lokaci yayi, suji yadda za'a ƙarƙare shari'ar Yusuf, kullum Gidajen radio da dandalin sada zumunta zancen kawai ake yi, kowa yana tofa albarkacin bakinsa, wani ya tofa na alkhairi wani kuma ya tofa akasin haka.
Suleiman yaje kaiwa Umma ziyara shida matarsa Surayya, sedai kallo ɗaya zakayi mata kasan bayan damuwa harda rashin lafiya take fama.
Surayyah ce ta fara cewa "Umma kodai jikinne ya motsa? Naga kinyi wani iri"
Suleiman yace "nima nagani, ko gurin likita zamu koma ne?"
Umma tace "A'a Suleiman, ɗawainiyar nan tayi yawa, lafiyata ƙalau ai"
Suleiman yace "wace irin ɗawainiya kuma Umma, ai in dai da amana nine yakamata in kula dake, Umma ban san haka abun nan ze kasance ba, Abbas ne yace a bawa Yusuf aikin nam ze iya, na goyi bayan hakan na bashi aikin, dana san haka zata faru da ban bashi ba, kuma ace wannan abu ya faru dashi, in kasa kulawa da mahaifiyarsa, ai da banyi wa kaina adalci ba, ni dai ina baki haƙuri Umma"
Umma tace "haba Suleiman, ai duk wani mumina dole ya yadda da ƙaddara, ba kai ka kama Yusuf ba, kuma ba kai kasa aka kamashi ba, ƙaddararsa ce a haka, duk imani da girma irin na Annabawan Allah, seda ya jarrabesu to waye Yusuf da Allah baze jarrabeshi ba, nasani Allah yana jarrabar bayinsa ne wanda yake so, dan haka inawa Yarona Addu'a, Allah ya bashi mafita ta idan bamu zata ba, sedai babu wanda ya bani mamaki kamar Abbas, ba ƙaramin mamaki ya bani ba, irin yadda yake nunawa Yusuf soyayya, Yusuf bashi da abokin daya wuce shi, da kansa yazo ya ɗau Yusuf ya kai shi gidansu yarinyar nan, amma yace be san zancen ba"
Suleiman yace "Umma kiyi haƙuri, ki dena tunawa kawai, mu barwa Allah mucigaba da Addu'a"
Umma tace "Addu'a kam, na duƙufa ina nan inayi, kuma na saka anata saukar Al'qur'ani, na miƙawa Allah ya isar mana"
Surayyah tace "insha Allah, addu'arki bazata faɗi ƙasa ba Umma, amma Umma akwai Abinci a gidan nan?"
Umma tace "eh ina da Abinci"
Surayyah tace "dafaffe fa"
Umma tace "Aa', sedai in yanzu za'a girka miki, kina jin yunwa ne?"
Surayyah tace "hakan ya nuna bakya cin Abinci Umma, ƙarfe biyu yaci ace ai anyi girkin rana"
Umma tai murmushi tace "wayo kikayi min kenan?"
Surayyah tace "ai ramar taki tayi yawa, dama munyi magana da Abban Nihal ne, muna so ki koma gidanmu zuwa muga yadda hali zeyi"
Umma tace "A'a, hakanma nagode ku barni a nan, bazan ɗora muku wahala ba"
Surayyah tace "Umma ba wahala bace bafa, kinga kaɗaici yana damunki sosai, ga rashin cin Abinci, ga larurar rashin lafiya kina tare da ita"
Umma ta dage ba zata bar gidan nan ba, Suka dinga mata magiya sukace bazat wuce sati ɗaya ba, so suke jikinta ya warware.
Da ƙyar Umma ta yarda, Surayyah ta haɗa mata kayan ta, suka tafi da ita gidan Suleiman.
Yusuf duk iya azabtarwar daya sha, basu samu abunda suke so ba, ƙarshe ma Yusuf ya koma kurman ƙarfi da yaji, juyin duniya baya magana, itama Widad bata da maraba da 'yar prison ɗin itama, tayi wujuga wujuga itama, kamar korarriya ga Duka ga azabtarwa da take sha a hannun Bulama, duk ta fita hayyacinta.
Nurat ma bata da kwanciyar hankali, se fama take da damuwa da tunani, sedai ta rufe ɗakinta tasha kuka, gashi yanzu ta dena samun magana Da Khalil sam.
Haka gidan Hajiya Halima ya rincaɓe, Ramlah shaye2 ba kama hannun yaro, bata ganin kimar Mahaifiyarsu sam, yayin da Amal kuma gaba ɗaya haushinsu takeji, dan haka tai dumping ɗinsu gaba ɗaya a side, ta dena shiga sabgar su, ta kama wayarta take shiga wata caca a online da kuɗin data damfari Alhaji Haruna, sabgar ta kawai take ta dena shiga harkar mamanta da 'yar uwatta, idan taga Mummya zata dameta da koke koke ma, ko zancen Ramlah, se tai waje ta bar musu gidan, ko kuma ta shige ɗaki ta rufe taita danna wayarta, saboda tun kan Ramlah tai nisa da shaye2 Anwar yaso ɗaukar mataki akan lamarin, amma ta nuna bata so taci masa mutunci, dan haka na meye zata takura kanta akansu yanzu?.
Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, yau kotu tafi kullum cika, da mutane daban daban, duk ana jiran jin yadda zata kaya a wannan shari'ar, yadda aka rirriƙo Yusuf aka shigo da shi cikin sarƙa, yana jan ƙafa da ƙyar, saboda wahala.
Aka kammala wasu shari'ar da take kafinta su Yusuf, sannan akazo kan Tasu Yusuf.
Justice Abdullah A Dutse ya gama rubuce rubucensa sannan yace "duba da yadda muka fara wannan shari'ar, da irin shedu da hujjoji a gaban wannan kotu, kuma wanda ake ƙara ya gaza musanta abunda ake tuhumarsa dashi, an samu wanda ake zargi da laifin yin garkuwa da mutum, duba sashi na 273 na kundin penal court, wannan kotu ta yanke wa wanda ake ƙara hukuncin shekaru goma a gidan yari, ba tare da zaɓin tara ba, sekuma laifi na biyu da ake tuhumarsa dashi shine laifin fyaɗe ga ita wadda akai garkuwa da ita, duba da sashin manyan laifuka, ƙarƙashin sashe na 221 wannan kotu ta yanke wa wanda ake zargi hukuncin shekaru goma sha huɗu a gidan yari, tare da aiki me tsanani, sekuma laifi na gaba laifin sata da siyar da abunda ba mallakinsa ba, saida motar ita wannan yarinya wadda kuɗinta yayi naira miliyan talatin, wannan kotu ta yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan yari, da tarar Naira million biyar, wanda ake ƙara idan hukuncin nan be masa ba, yana da damar ɗaukaka ƙara nan da kwanaki talatin masu zuwa "
Alƙali ya buga gudumarsa ta kotu, aka sake taso Yusuf a gaba, sarƙa hannu da ƙafa akayo waje dashi, kamar kullum duk yadda 'yan jarida suka so jin ta bakinsa, yaƙi cewa uffan.
Suleiman kuwa dama hana Umman Yusuf yayi zuwa ganin shari'ar gaba ɗaya.
Ramlah kuwa ta sake bin Fahad ɗakin Hotel, tana ta zazzaga masa bala' i akan lallai seya aure ta, Fahad yace "asje ke ƙwayar da kike sha, hauka ta saka miki ban sani ba, ko matan duniya sun ƙare bazan aure ki ba, kin zama second hand, kije ki samu wani ajawon daze iya rufamiki asiri".
Cikin ɓacin rai tace "ita wadda kake harin, itama ba second hand ɗin bace?"
'ai gara ita dake, koba komai ko second hand ce ai akwai kyau, dujda kema ba munine dake ba, amma ai kowa yana son canji, kuma itama da manufa zan aure ta "
" wallahi baka isa ba, kayi kaɗan Fahad, zan gwada maka Rashin mutunci, jaki macuci kawai wallahi bazan yafe maka ba"
"Ai babarki ce macuciya, itace babbar macuciya, kuma ina baki shawarar kije Asibiti a tabattar da lafiyarki, saboda akwai matsala a lafiya ta"
Maimakon hankalin Ramlah ya tashi, kawai se yaga ta ƙyalƙyale da dariya irin ta mugwayen nan.....
AMANA! AMANA!! AMANA!!!
Ayshercool
07063065680
11/29/21, 8:55 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
140_141
Seda Ramlah tai dariya me isarta, yayimda Fahad ya bita da kallon mamaki irin dariyar da take ƙyaƙyatawa, tace "Fahad ai duk yadda kake tunanina na wuce nan in gaya maka, shiyasa nake ta binka Allah ma'aiki ka aureni, ban nuna maka nasan kana ɗauke da cutar HiV ba harka samin ba, nake ta lallaɓaka amma baka gane ba, to na ɗau matakin daya dace, dan haka zan maka Albishir, Danni agurin Albishir ne, ina me farincikin sanar da kai cewa Ubanka Bulama ma yana ɗauke da wannan ƙwayar cuta "
Ai a razane besan ya miƙe tsaye ba akan ƙafafunsa, ya dinga binta da wani ƙasƙantaccen kallo, yace " mekike nufi? "
" Kurma ne kai? Ko yaren da nayi magana dashi ne baka ji, nace ubanka mahaifi wato Bulama, shima yana da cutar, na saka masa dan haka seka hanzarta kaje kasa shi ya fara shan magani akan lokaci, tun kan ciwon ya huda shi sosai, sannan yama da kyau ka binciki babarkama, ko itama ta rabauat seku duƙufa shan magani, kaga rabajau daku idan wannan ya manta lokacin sham magani yayi, se wannan ya tuna muku "
Kamar Fahad ze fashe da kuka yace" kina nufin, Dad ɗina yana ɗauke da wannan cutar ne? "
" babu ko shakka " ta bashi amsa
" Amma wace irin tinkiyace ke Ramlah, yanzu sekiyi mu'amala dani ki koma kiyi da mahaifina saboda mugun abu? "
Ramlah tace " duk cikin iya takune, da farko shiya fara ɓatamin rayuwa, na rufa masa Asiri, har na fara sonka, tun a wancan lokacin ya fara take taken baya goyon bayan soyayyar, kaima kazo ka nemeni na bada ksi bori ya hau ina zaton zaka Aureni, amma kaƙi kuma na kasa rabuwa da kai, duk da yadda Anwar ya dinga nusar dani, kawai naga magani a jakarka, na tambayeka na mene kace min na gyaran jiki ne, nai nai ka bani ka hanani, shine nai snapping nace a samomin maganin, aka gayamin na meye, nayi kuka na shiga damuwa amma nakasa gayawa mowa damuwata, na cigaba da shaye2 daka koyamin dan ragewa kaina tension, naga babu hanyar da zanbi in huce takaicin nan daka ƙunsami , seta hanyar sanyawa Ubanka wannan ciwon, se duk muyi jinyar tare, nake ta binka ka aureni kana rainamin hankali kana ganin ka cuceni, kuma ina me tabattar maka da cewa dukda kamilewa irin ta ƙaninka Ramadan, shima zan iya bashi nasa rabon, dan haka seka san abunyi tun dare be maka ba ".
Ta ƙarasa maganar tana hararasa, ta bar ɗakin.
Ya dafe kai ya zauna yana faɗin" Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ya isa tsakanina dake, kin cuceni, ba kowa aka cuta ba se Mother, tana gefe ta kawamme kanta ta riƙe Aurenta an kwasa mata masifa, Daddy why? "
(dama ita zina haka take, idan ka yi da ɗan wani za'ai da naka, idan ba ayi da naka ba in one way or another, dole se wannan illar zinar ya shafi wani naka, zina bata da wata riba sam, ga zunubi, ga cuta ga ɗaukar alhakin wanda basuji ba basu gani ba, Allah ya shirya al'ummar musulmi baki ɗaya)
Fahad ya cigaba da kuka yana tunanin, ta yaya ze fara gayawa Mummy abunda ya faru, wama ze tunkara da wannan Mummunan labari haka?
Babu wanda aka cuta sama da Mummyn mu, dama har yanzu Daddy yana biye biyen mata? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un.
"Ramlah kin cuceni, tsakanina dake Allah ya isa kawai ban yafe ba Wallahi, wayyo Allah na, ban taɓa dana sanin irin rayuwar da nayi ba se yau, ubangiji Allah yasa Mummy bata ɗauka ba, saboda abun kunya da Allah wadai, ace inbi yarinya mahaifina ma yayi, wace irin rayuwa ce haka? Ta yaya zan tun kari Mummy in sanar da ita ta binciki lafiyarta?
Fahad ya zauna zaman dirshan a ƙasa yana kuka, sekace ɗan yaye kuka harda majina, ya rasa inda ze saka kansa dan baƙin ciki da takaici, yau a dalilinsa za'a sakawa mahaifiyarsa wannan larura, koma an riga an saka mata, yanzu ta yaya ze tun kare ta da wannan maganar?
Seda aka watse daga kotu sannan Bulama yabi Justice A duste chamber, A dutse yai murmushi yace "ya kaga shari'ar tamu? Naga tunda muka fa fara shari'ar baka zuwa"
Bulama yace "ya za'ayi inzo, sannan shari'a tayi dan yi, shekaru talatin ai kan nan komai yayi dai dai , amma abunda ya bani mamaki shine meyasa zaka ce wai yana da damar daze ɗaukaka ƙara, ɗaukaka ƙarar na mene kuma? Tunda ka yanke hukunci, meye kuma na wani ze iya ɗaukaka ƙara kuma? "
" Bulama kenan, har yanzu baka san meye shari'a ba, babu yadda za'ayi aiwa mutum hukunci a irin kotunanmu sannan ka hanashi ɗaukaka ƙara idan hukuncin be masa ba, ba'ai haka ba haka ƙa'idar aikin take ba, nan da kwanaki talatin yana da damar daze je ya ɗaukaka ƙara "
Bulama ya ɗanyi ƙaramin tsaki yace " to yanzu meye abunyi? "
" Eh to, iyakaci kuyi ƙoƙarin toshe duk wata dama da zata saka ya ɗaukaka ƙararar, idan kuma ya ɗaukaka ƙararar, to se ka faɗi ka tashi suma ka siye su "
Bulama yai tsaki yace " Aini daya ɗaukaka ƙarar da kar ya ɗaukaka idan na samu abunda nakeso, can ta matse musu, ni yanzu zanje in maida hankali in samu abunda nake so "
A dutse yace "Shikenan, as you wish"
Bulama yace "Nagode sosai da gudunmuwar ka"
Suka musabaha, ya bar chamber.
Bulama kai tsaye gidan da Widad take ya nufa, yana zuwa ya tarar da ita a zaune cikin zumbulelen hijjabinta, ta ƙara zabgewa, duk babu ƙibar nan, Widad lazumi kawai take a zuciyarta, dan tasan yaune ranar daza'a yankewa Yusuf hukunci a kotu, sedai zuwa yanzu bata san wani hukuncin za'a yanke masa ba.
Bulama yazo ya sakata a gaba yana ƙare mata kallo, shikansa yaga yadda duk ta rame ta fita hayyacinta, mutum baya ce ita ce Widad Nasir Daula ba.
Tunda ya shigo bata motsa ba, balle ta ɗaga kai ta kalle shi, ta zuba guri ɗaya ido ko motsi ba tayi.
"Ina fatan kinji hukuncin da aka yankewa wannan sakaran xa kike iƙrarin mijinki ne? Koda yake ba lallai ki sani ba, amma shekarun babu yawa, shekaru talatin da ɗaya ne, se tarar miliyan biyar, sakamakon kama shi da laifin garkuwa da mutum, laifin fyaɗe da kuma sata, ina fatan yanzu kin san me Bulama ze iya aikatawa? Koda yake tun ba yau ba kin san irin abunda nake iya aikatawa idan ina buƙatar abu"
Widad bata motsa ba bata kalle shi ba, tai shiru abunta tana cigabs da ƙurawa guri ɗaya ido.
"Yanzu kin shirya gayamin inda abubuwan nan suke ko sena je nasa an kashe Uwar Yusuf"?
A hankali ta ɗaga kai ta dube shi, tace "kai a tunanin ka zan bar mijina ya shekara talatin da ɗaya a gidan yarine? Lallai baka da hankali, kuma ga dukkanin alamu ka manta wacece Widad ko? Zan baka mamaki kuwa, Yoseef baze zaman gidan yari ba, kuma bazaka samu abunda kake so ba"
"Kin zaɓi mahaifiyarsa ta mutu kenan?"
"Ba zata mutu ba se lokacinta yayi"
"Shikenan, tunda haka kika zaɓa, zaki gani kuwa"
Widad tace "meye ban gani ba Bukar, zalunci da mugunta wanne ne bakamana ba? Kasa aka kashe mahaifiyata, kasa aka haukatani, kai kutungwila ka aurawa mahaifina matar da ta dinga azabtar da shi tsawon lokaci, yana bauta ita da 'ya' yanta amma suna azabtar dashi, hakan be isheka ba kasa aka dinga kaimin farmaki dan a kasheni akan dukiyar nan, banda message na razanarwa da tashin hankali da kake turomana, ƙiri ƙiri ka rabani da ƙasata ta haihuwa saboda mugun zaluncinka, kasa nayi rayuwa kamar matacciya, babu me raɓata ka jefa tsoron mutane a zuciyata, kasa aka dinga farautata kamar dabbar daji, Allah ya kawo Yoseef na fara samun sassauci, nan ma akasa akayi garkuwa damu, muka kuɓuta ya dinga wahala dani, amma a ƙarshe kalli sanadin zaluncinka abunda aka masa, nida abun a kaina ya ƙare da sauƙi, shi meye nasa a cikin lamarin nan? Wallahi wata shari'ar se a lahira shi kaɗai ze sakamin wannan zalunci da kamin "
Bulama ya ƙyaƙyace da dariya yace " ke yanzu da duk kin san ni nake shirya wannan abubuwan amma kika ƙyaleni nake cin karena ba babbaka? Lallai kin iya wauta, meyasa kika ƙyaleni kikemin kallon uba bayan kin san ni maƙiyinki ne "
Widad tace " talala na maka, tun ranar da aka kashe mahaifiyata aka ambaci sunanka, bazan taɓa manatawa ba, sedai na ƙyaleka ne saboda muddin nai wani yunƙuri zaka kashe min mahaifi, shiyasa na ƙyeleka, amma a yanzu inaji a jikina kana daf da yin faɗuwar baƙar tasa"
"Hmm, lallai yarinya dole a sarawa ƙoƙarinki, da iya takunki tun kina ƙarama kanki yake kawo wuta sosai, kin iya lissafi sosai, Amma ki sani ni tsohon hannune a duniyanci, tunda hukuncin da akayiwa mijinki be zama izina a gareki ba, zan sa a kamo min uwarsa, inzo in yankata a gabanki tunda ke taurin kai baze barki ki ƙwaci kanki ba"
Wani mugun kallo tayi masa, ya tashi ya fita daga ɗakin nata, bayan tafiyarsa Sabuwa ta shigo ɗakin Widad tana dube dube tace "dan Allah ban yarda memory ɗina a ɗakin nan ba, tun jiya nake nemansa ban ganshi ba sam"
Widad tace "nima ban ganshi ba gaskiya, dan Allah Al'ada ne yazomin, tunda aka ciremin cikin nan ban ƙarayi ba se yanzu, dan Allah ki aramin dubu ɗaya, in rubuta miki irin wadda nakeso ki kai kowane shago a baki, idan Allah ya fitar dani zan bi yaki"
Sabuwa tace "to shikenan" taje ta samo biro da takadda ta bawa Widad ta raba takaddar biyu, Widad tai rubutu akan kowacce takaddar, da yake Sabuwa bata iya karatu ba, Widad ta rubuta ta bata ta ɗakko wata leda tace "dan Allah karki gayawa kowa na aike ki, ki kai shago kice a bani abunda na rubuta a jiki, ki haɗa musu da wannan ledar ki basu"
Sabuwa ta karɓa tace "shikenan, zan sawo maki insha Allah"
Widad tace "nagode sosai"
Mum Nurat taga sam bata ga gilmawar 'yarta ba, dan haka ta tafi ɗakin Nurat ɗin, tana zuwa ta tarar tayi wujuga wujuga saboda kuka, se rusa uban kuka take kamar ubanta ya mutu.
A ɗan gigice tace "ke lafiya kuwa? Meye ya faru dake haka? Me akayi miki ne?"
Maimakon ta bata amsa, sema sake rushewa da kukada tayi, "ke bana son sakarci fa, menene haka? Meya sameki kike rusa wannan uban kukan haka?"
"Mummy baki ga hukuncin da aka yankewa Yusuf bane?"
"To idanma na gani me zanyi, ko kuma me zance? Allah ya bayyana gaskiya kawai, amma shine zakizo kina wannan uban kukan haka? Ai koni na mutu iyakar wannan kukan kenan"
"Mummy wai meyasa kike basarwa ne, baki san menene yake wakana ba? Kin san fa komai Mummy? Daga gidan nan fa ake shirya maƙarƙashiya fa kin sani fa"
Da sauri Mummy ta ƙarasa, ta tishe mata baki tace "dan ubanki yana cikin gidan nan, so kike ya jiyo yazo yai miki wani abun?"
Nurat ta fizge tace "Haba Mummy, meyasa zamu ɗauke ido akan gaskiya Mummy? Wallahi ranar lahira muma harda mu a cikin wannan zaluncin da akayi, Mummy da saka hannun Daddy fa aka sace su Widad, Mummy da kunnena fa naji shi"
Maman Nurat na juyawa taga Alhaji Musa a ƙofar ɗakin, yana kallon su.
Nurat taƙi yin shiru tace "gaskiya Mummy idan mukayi shiru bamu da adalci, wallahi da saka hannun Daddy akan abunda ya faru, kuma kema kin sani, Wallahi da Daddy ake shirya komai, Mummy ya zakiji idan ɗankibaka yankewa hukuncin shekaru talatin da ɗaya a gidan yari? Kefa uwa ce Umma, bakya tunanin me mahaifiyarsa zataji a ranta a yanzu haka? Ancd shikaɗaine ɗanta amma an yanke masa hukuncin shekaru talatin da ɗaya a gidan yari "
Cikin tsawa Mummy tace " dan ubanki bazaki min shiru ba, seya miki wani abun tukuna? "
Nurat tace" Mummy nifa gaskiya nake faɗa, kuma ni zanje in bayar da shedar abunda ya faru, mahaifina yasan komai fa"
Alhaji Musa ya tako a hankali, yana zuwa bece komai ba ya danƙi hannun Nurat ya fara jan ta, a gigice Mummy tace "ya haka? Ina zaka kaimin 'yata? Ina zaka kaita? Karka cutarmin da ita dan Allah, ita kaɗaice' yata karka cutar da ita na gaya maka"
Be tankamata ba, ya dinga jan Nurat, Nurat tana faɗin "Daddy kaji tsoron Allah, a wannan shekarun naka me kakae nema a duniya haka, wanda zesa kasa hannu a zalunci wani, da Alhaji Nasir kake da matsala bada 'yarsa ko wanda beji ba be gani ba, dan Allah Daddy ku ƙyale Daula ya huta, da kunnena naji kana magana kune kuka saka aka sace Widad da direbanta, kuma yanzu kun sauya maganar kuna gabi aka kaishi kotu aka yanke masa hukunci akan abunda bejiba be gani ba"
Yana jan Nurat, tana biye dashi yayin da mahaifiyarta ke binsu tana masa magiya, wani ɗaki yaja Nurat can bayan ɗakinsa a ƙarshen bene, ya jefa ta ciki yasa mukulli ya kulle ta, ya juya ze tafi, Maman Nurat ta sha gabansa tace "meyasa zaka kullemin yarinya a wannan ɗakin ita kaɗai? Me yasa haka? Dan Allah ka buɗe mata ƙofar nan ta fito, karta cutu dan Allah"
Alhaji Musa yace "wallahi bazan buɗe ta ba, ashe kune manyan maƙiyanaba gidan nan? Dole ta bar ƙasar nan ko tana so ko bata so, kuma kema daga yau, bake ba fita ko ina, kuma duk sena karɓe wayoyin ki, munafukar banza da ta wofi"
"Niba munafuka bace, karka ƙara kirana da munafuka, halin rashin gaskiya 'yarka ce ta fara gano kana yi, dan haka babu laifina a cikin wannan batun? Dan Allah ka buɗemin' yata dan Allah ka barta ta fito, wallahi bazan bari tayi komai ba, dan Allah kayi haƙuri "
Tsaki yayi, ya raɓa ze wuce ta, amma ta sha gabansa tana kuka akan ya buɗe Nurat, aikuwa ya Tureta ze wuce bisa ga tsautsayi ta gangaro daga kan benen nan, ta ƙwala ihu da ƙarfin gaske, tun daga ƙafar farko har ƙasa, da sauri ya bita sedai kan ya ƙaraso tuni ta ƙarasa, ta faɗa da fuska aikuwa tuni jini ya wanke gurin, jikinsa yana rawa yazo ya ɗagota, fuskarta ta wanke tsaf da jini, gashi ko motsi ba tayi, akan idon me gadinsa ta faɗo daga kan benen.
Nurat ta jiyo ihun mahaifiyarta, amma bata san meyafaru ba, dan haka hankakinta ya tashi, ta shiga dukan ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske tans kuka, tana kiran sunan Mummy.
Aka ɗauki Maman Nurat, zuwa Asibiti cikin gaggawa, ana zuwa aka karɓeta a Asibitin, da gaggawa aka shiga da ita emergency.
Sabuwa ta dawo gidan da Widad take, ta shiga gurin Widad tace "Nifa naje na kai musu, amma basu bani komai ba, sun karɓi takardar sun karanta, sun bani wata takardar, sun karɓi ledar sunce in tafi kawai, hadda tambayata wai waye ya aikoni?"
Widad tayi murmushi tace "inaga basu da ita ne, bani takardar da suka baki"
Ta miƙawa Widad takardar da suka bata, ta karɓa ta karanta, tai ajiyar zuciya tace "nagode sosai Sabuwa, sunce basu da irin wadda nake so, se Allah ya kaimu jibi kije ki karɓa"
Sabuwa tace "to yanzu ya zakiyi? Ga jini na zuba?"
"no karki damu, zan iya maleji zuwa lokacin da zasu kawo ɗin, bana iya amfani da kowacce se ita ne"
Sabuwa tace "to shikenan, Allah sarki ashe cikin ya fita dagaske?"
Widad tace "eh ya fita, ina son zan ɗan kwanta"
Sabuwa tace "to shikenan, se anjima"
Fahad fa ya rasa inda zesa kansa, da yaga mamansa, se yaji tausayinta ya kama shi, se yaji ƙwalla ta tarar masa, maimakon yaji haushin kansa, haushin mahaifinsa ya dinga ji, dan dabe nemi mata ba da babu abunda zesa mahaifiyarsa ta samu, gashi ya rasa ta inda ze mata wannan baƙin bayanin mara daɗin ji.
Gidansu Amal ma gidan sam babu daɗi, idan Ramlah taga dama a falo, haka take zuwa ta kama shan shisharta, kota kunna sigari tana busawa, ta baje kayan coadine ɗinta taita yiwa kanta caji, Hajiya Halima yanzu kam tsaro Ramlah take bata, sam bata iyayi mata magana, tana kallon ta, tana yi amma bazata iya cenata bari ba, Amal kuwa dama tuni ta fita daga harkar su.
Hajiya Halima na ɗakinta, ko izininta bata tambaya ba ta fice ta tafi Asibiti dan a dubata, sedai ta razana da sakamako ya fito aka tabattar mata da tana ɗauke da juna biyu, ta shiga ɗimuwa da tashin hankali, tun a Asibitin ta lalubi lambar Alhaji Haruna ta sanar masa da tana ɗauke da juna biyu, kuma ko yasan yadda zeyi da ita ko kuma tayiwa duniya Albishir da tana ɗauke da cikinsa.
Abubuwa fa suka rincaɓe sosai, Wata Nurse inyamuda ta jata gefe tace mata tasan inda zata kaita a zubar da cikin, in dai bata son cikin, ba musu ko tunanin komai Amal ta amince da a zubar da cikin.
Yusuf yana cikin fursunoni, yana zaund shiru kamar yadda ya saba zama, akace yayi baƙi ya kalli gandiroban ya ɗauke kai kamar beji ba, "Malam da kaifa neka" gandiroban yai maganar a ɗan hasale"
Yusuf yace "bazani ba"
"Kamar yaya bazaka ba?"
'me zanje inyi? An riga an yanke min hukunci, burinku ya cika kuda iyayen gidanku, me kuke nema a gurina kuma? Ko waye bazani ba"
Gandiroban yace "koda mahaifiyarka ce kuwa?"
Da jin haka Yusuf ya miƙe da sauri, se kuma yaji bashi da karsashin tunkararta ya kalleta, dan yasan abune mawuyaci sukuma rayuwa da Ummansa kamar da.
Yusuf yabi bayan gandiroban jiki a saɓule, yana dogara ƙarafarsa da kyar saboda ciwo da take masa.
Yana zuwa yaga wasu mutane a zazzaune, wanda be sansu ba sam, aka bashi guri ya zauna yana ƙare musu kallo.
Ɗayan ya kalle shi yace "sannu Malam Yusuf, sunana Barrister Hafiz wannan abokan aikinane" yai maganar yana miƙawa Yusuf hannu.
Amma Yusuf ya ƙeƙashe ƙasa yaƙi bashi hannu, ya kalle shi yace "me kuke nema a gurina? Bayan shari'a tazo ƙarshe an yankemin hukunci, me yayi saura kuma me kuke so inyu muku"
Yai maganar cike da karaya, ƙwalla na taruwa a idon sa.
Hafiz jiya yi kamar yayi kuka shima, ya maze yace "haba Yusuf, ai ka tsaya kaji meke tafe damu ai, Barrister miƙo takaddar nan"
Barristern dake gefensa ya ɗakko takadda ya miƙawa Hafiz, Hafiz ya karɓa ya miƙa masa yace "ga saƙo inji matarka"
Jikin Yusuf na tsuma ya karɓi takaddar yana buɗewa yaga rubutun Widad "
_Bani da abunda zan iyayi maka a halin da nake ciki I love you My Yoseef, but I will do my best to see what I can do for you, please pray for me, is either we should meet again or the time you will be free i pass away_
Yusuf yace " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
AMANA! AMANA!! AMANA!!!
AYSHERCOOL
07063065680
11/30/21, 8:20 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _
Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)
Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji
Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata
Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219
Chat 08063114606
144_145
Ai zumbur ta miƙe zaune tace "ban gane a kasheshi ba? Anwar ɗin nawa za'a kashe? Me yayi masa haka?"
Alhaji Musa yace "ke nifa tuni na dawo daga rakiyar mutumin nan, Azzalumi ne kawai, kansa ya sani bashi da imani sam, ni kaina yanzu haka muna Asibiti nida su Nurat, amma gaba ɗaya ko yamin jaje se masifa da tashin hankali da yake min, shiyasa na kwashi kuɗina na saka a siyasa, in samu su bani takara in huta da wannan mulkin mallakar da yake mana, ga uwar dukiyarmu da muke narkawa amma har ynzu babu wani bayani "
Hajiya Halima ta fashe da kuka tace " ni Bulama zeyi wa haka? Anwar kamar ɗa yake a gurinsa amma shine zece a kashemin shi? Baze yuwu ba kuwa "
Ta ajiye wayar, ta miƙe ta shiga ɗakinta ta zura doguwar riga, kusan ƙarfe goma saura na dare, amma tayi waje ta ɗau mota ta fita ta tafi gidan Bulama a daren.
Shikuma Bulama yana zaune yana ta nazari akan yadda ze ɓullowa al'amura da suke neman damalmale masa, ya dinga kiran layin su Me Adda amma shiru babu Labari, waya taƙi shiga sam.
Masu gadi kansu sunyi mamakin ganinta a wannan daren, kamar wata mahaukaciya ko gabanta bata gani sosai saboda tashin hankali, kai tsaye ya shiga falon dake ƙasa tana bala'i "Ina Bulama yake? Ina Bulaman?"
Iman ce zaune a falon tana kallon zee world tace "Mummy lafiya kuwa?"
"ban sani ba, ina uban naku yake tsohon macuci azzalumi?"
Iman ta kalleta da mamaki jin irin furcin da take akan mahaifinsu wanda ya kasance ɗan uwa a gareta, Iman tace "Mummy ya riga ya hau sama, inaga ma ya kwanta fa"
Ai bata tsaya jiran me Imana zata kuma ce mata ba ta haura saman da kanta, ba zato ba tsammani ya ɗaga kai yaci karo da Hajiya Halima a tsaye a kansa.
Ya kalleta yace "Halima, lafiya kuwa zaki zo a daren nan? Bakya jira ayi miki iso kawai ki hauromin ɗaki haka?"
"Dalla rufemin baki, me zaka gayamin har wani iso zan jira ayimin, munafuki azzalumin banza dana wofi, tsawon shekaru ina maka aiki, kana sani duk abunda kaga dama ina maka, dan ka cinma burinka ba tare da na nuna gazawata ba, shine halin naka na baƙin kumurci zaka gwadamin, shine kayi umarni da idan anga Anwar a kasheshi, ɗan nawa za'a kashe? Wallahi baka da imani ba kada Alƙawari tun wuri ka dakatar da wannan maganar idan ba haka ba Wallahi ran ɗana baze tafi a banza ba"
Zazzaro ido Bulama yayi ya dinga ƙifta mata ido akan tayi shiru, amma tace "bazan shirun ba, wallahi babu inda zani se an dawo min da ɗana"
"Halima wai wace irin magana kike hakane? Kamar yaya nace idan anga Anwar a kasheshi? Me Anwar yayi min wanda zesa ince a kashe shi, ni da na kaiwa jam'ian tsaro maganar dan ayi bincike akansa a gano inda yake ya zakice nace a kasheshi? Wani munafukin ne ke neman haɗani da 'yar uwata?"
" Kaga bana son kame kame da ƙaryar banza, wanda ya gayamin baze maka ƙarya ba, macucin banza da na wofi kuma wallahi idan ɗana ya mutu you must pay for it, wallahi aka kashemin Anwar seka fanshi ransa, nima kasan halina ka san abunda zan iya aikatawa "
Gaba ɗaya Bulama ya dirirce ya rasa abunyi, ya shiga tsuma yana fatan Allah yasa wani beji abunda ta faɗa ba.
Ya biyo bayanta ya leƙa, yaga ba kowa a falon ƙasa dukda ɗakin a rufe yake babu wanda ze iya jiyo me sukayi, ya koma bedroom ɗinsa ya tarar da Hajiya Sarah tana ta baccinta hankali kwance, yai ajiyar zuciya tare da tunanin bata jiba, amma ya zauna yai shiru akan gadon yana tunani, tabbas babu wanda ze gayawa Halima wannan maganar idan ba Alhaji Musa ba, tabbas dole yayi maganin Alhaji Musa.
Cikinsa ne ya murɗa ya tashi ya tafi banɗaki, kusan kwana huɗu kenan yana fama da gudawa taƙi tsayawa, dan haka ya sa ransa idan ya gama da wannan matter ɗin zeja yaga likita.
Yusuf se sake juya takaddar nan yake, yana tunanin wani hali Widad ɗin ke ciki, tabbas yasan da tana da dama bazata barshi a gurin nan ba, dole akwai wani abu da yake gudana a ɓoye, idan ya kalli sentence ɗinta na ƙarshe na ba lallai su sake haɗuwa ba se yaji gabansa ya faɗi, lallai ko a ina take tana cikin mawuyacin hali, "Allah ya ƙara haɗa fuskokinmu my wife, Allah yasa kina hannu na gari, i love you too" yai maganar a hankali tare da lumshe idonsa.
Rayuwar da suka yi tare a ƙauye ta dinga dawo masa, koba komai zamansa da ita ba ƙaramin farinciki ya samu ba, zamansu a ƙauye yasa Ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ta samu hutu na wani ɗan lokaci, ya daɗe beji cin zarafi da gorin rashin iyaye daga mutane ba, sedai matukar kewar Ummansa da yayi, be sake zaton ze samu wadda zata aureshi ba saboda rashin nasaba ba, sedai cikin hukuncin Allah ya auri yarinyar da zuciyarsa ta mato a sonta, dukda nisa da ratar dake tsakanin su, yarinyar da manyan wanda suka isa ma basa gabanta, soyayyar ma bata yadda da ita ba, amma Allah ya ƙaddara Aurensu, har suka yi zama cikin farin ciki, ya dinga tuna irin Shagwaɓarta wauta da yarinta wasu lokutan, ya tuna lokacin da take koyar tankaɗe, da sanda take wa Abincin garin kallon banza, da yadda ta dage ita seta samu ciki, da irin kallon da take masa idan ya tsokane ta.
A hankali ya sake lumshe ido yana murmushi, sekuma ya tuna yadda ta shiga damuwa daya bata labarinsa, da yadda ta dinga kururuwa tana kuka tana gaya masa tana sonsa lokacin da aka kama shi a garin, da yadda taje kotu ta bada sheda akansa, ga shekarun da aka yanke masa a gidan yari, ga abunda ta rubuta masa kawai se yaji ya karaya hawaye ya shiga bin gefen idonsa, baya tunanin ze sake wata rayuwa me daɗi a nan gaba, mussman kasancewa da Widad a inuwar Aure.
Da ƙyar likitoci suka samu Nurat ta dawo hayyacinta ta samu bacci, aka sa mata ruwa, sedai harta farfaɗo ɗin numfashinta da vital signs ɗinta suka daidaita bata gane mutane sosai, saboda ta galabaita an samu dai bacci ya ɗauketa cike da fatan idan ta tashi zata iya dawowa hayyacinta gaba ɗaya, mahaifiyarta kuwa gaba ɗaya har yanzu ba'a gano kanta ba, tana kwance ne kawai, numfashi ne kawai a ƙijinta, banda haka babu abunda yake aiki a jikinta, sam bata san abunda ke faruwa ba, shi kansa numfashin nata da ƙyar take yinsa wasu lokutan, saboda ta zubar da jini sosai, kuma ana kyautata zaton ta samu rauni a cikin kanta, sakamakon buguwa da tayi, likitoci sun rubuta mata hoton Ƙwaƙwalwa dan tabattar da abunda yake damunta.
Abu kamar wasa, jini yaƙi tsayawa Amal, se aikin zaryar banɗaki take, jini se zuba yake babu ƙaƙƙautawa, ta rarrafa ta haɗa Abinci tana ci kota samu sauƙin wannan wahalar haka, zuciyarta tana ƙuna akan yadda Alhaji Haruna ya cuce ta, Hajiya Halima ta fito falon ta zauna ta dafe kai ta kalli Amal tace
"wai kuwa lafiyarki ƙalau kuwa? Gaba ɗaya kin wani ɗashe kinyi fari ƙal, kamar baki da jini a jiki, ko baki da lafiya ne?"
Amal tace "lafiyata ƙalau, period kawai nake shiyasa"
Hajiya Halima tai ajiyar zuciya tace "Amal kin kuwa san abunda Bulama yaimin?"
"A'a sekin faɗa"
"wai an gano inda Anwar yake, amma yace wai a kasheshi saboda karya tona Asiri"
Da sauri Amal ta kalleta tace "A kasheshi kuma? Me me kikace masa?"
"Naje har gidansa jiya da daddare, na ƙare masa tatas, nace wallahi aka kashe min ɗana seya fanshi ransa da nasa ran kona 'ya' yansa"
Amal tabi mahaifiyarsu da kallo, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, duk mahaifiyarsu ta ɗaiɗaita rayuwarsu da kanta, kowa yana karɓar nasa kason ɗaya bayan ɗaya.
Ramlah ce ta fito tana tangaɗi, tana magana cike da maye ta tsaya a tsakiyar falon tace "Wai ni.... Waini Fahad baze Aureni bane... Bazaki ce ya aureni ba ko? Wa.. W.. Wallahi kuwa bazan dena shaye2 ba tunda ya lalatani, ku.... Kuma... Kumaaa ai shikenan tunda nasan Na sakawa Bulama cutar tunda shima ya sakamin... Wallahi idan baka Aureni ba sena sakawa Wannan yaron Ramadan ma, idan yaso kow... Ko..... Kowama ya samu ni za'ayiwa hauka? Ya.. Ya ɗauka bani da wayo hmm baka san Rmalha bane" kawai ta faɗi a gurin tana juyi tana ci gaba da sambatu marasa kan gado sam.
Hajiya Halima ta kalleta tace "Ramlah wai wace cutar kike magana akai ne? Wace irin cuta?"
Ramlah bata san me take ba, juyi kawai take yi tana wasu surutan irin na marasa kan gado, Amal kam tasan babu mamaki idan akace Fahad yana ɗauke da wannan cutar me karya garkuwar jiki, amma sedai dagaske Ramlah take tana mu'amala da Bulama ma kenan, gaban Amal ne ya faɗi kardai ace itama tana da wannan cutar, miƙewa tayi da sauri zata tafi ɗakinta, Hajiya Halima tace "Amal ina zaki? Kina jin maganar da gake faɗa? Ko dai duk a cikin maye take ne?"
Amal tace "tunda ki kaji ta faɗa a maye, to ko ba'a mayen bama ya faru, sedai fatan Allah ya kyauta"
Amal ta tafi ɗakinta, dan itama fama take da kanta, wannan azabar ciwon marar da zubar jinin sun isheta haka.
Anty Saddiƙa ƙanwar Maman Nurat itace a gurin Nurat, itakuma maman Nurat ba'a barin kowa ya shiga inda take in ba likitoci ba, saboda tana ƙarƙashin kulawa ta musamman, Anty Saddiƙa taje salla Khalil na zaune a gurin Nurat, ai kuwa ta farka ta zaci zata ganta a ɗakin Dad ɗinta ya kulle ta, sedai tana buɗe ido tai arba da wani gurin daban, ta yunƙura zata tashi zaune, Khalil ya taho da sauri ya riƙeta yace "yi haƙuri, ki kwanta kinji, karki gaggawa jikinki babu ƙwari"
A Shagwaɓe Nurat tace "Brother ruwa zan sha"
Yace "ok bari in baki"
Ya ɗakko ruwam roba, ya buɗe ya bata ta sha, har ze gyara mata kwanciyarta ta kwanta, ta riƙe shi gam tana kallonsa, tana ƙoƙarin tuna meyafaru ihun Mummynta ta tuna, nan da nan ta razana tace masa "Mummy, Khalil Mummy na tana ina?"
Khalil yace "kwantar da hankalinki tana nan lafiya"
"A'a ban yadda ba, naji ihunta fa ranar, ban san meye ya sameta ba, tunda Daddy ya kulleni ban sake ganinta ba, waini ya akayi ma nazo nan ne?"
Khalil ya kalleta yace "kamar yaya ya kulle ki? Ya kulleki a ina?"
Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta gaya masa, yai shiru yana nazarin maganganun Nurat, cikin kuka tace "ina Mummy take? Dan Allah ka kaini in ganta dan Allah"
Khalil yace "ki kwantar da hankalinki, likitoci na can na kula da ita, idan ta farka zata zo ki ganta"
"to wai meyasa meta ne?"
"Bakomai, ta faɗi ne kawai saboda Dad ɗinki ya rufeki, bari Anty Saddiƙa tazo ta temaka miki kiyi wanka"
Bayan Saddiƙa ta shigone, Khalil ya tashi ya fita, a reception yaje ya samu Alhaji Musa a zaune, dan idan yazo Asibitin ya duba su Nurat nan yake dawowa ya zauna, dan gaba ɗaya haushinsa suke ji.
Ya zauna kusa da Alhaji Musa ya kalle shi yace "garin yaya ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene?"
Alhaji Musa yace "wace irin magana ce wannan? Ba a gabanka nayi wannan bayanin ba?"
Khalil ya kalle shi yace "to ya akayi ka kulle Nurat? Laifin me tayi maka"
Da sauri Alhaji Musa yace "tana ina? Nurat ɗin ta farkane?"
Yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, amma Khalil ya tareshi yace "na tambayeka kana ƙoƙarin tashi ina zaka?"
Yace "wai ita Nurat ɗince tace maka kulleta nayi?"
Khalil yace "labari na samu, daga majiya me ƙarfin gaske, dan haka nake tambayarka garin yaya ka kulleta"
"wai Khalil yaushe ka koma haka? Yaushe ka koma mara kunyane?"
"ba rashin kunya bane, gaskiya ce dama ina da ayar tambaya akanka, wallahi muddin na ganoka da wani abu ba dai dai ba, naga wani abun kayiwa ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene, wallahi se nayi shari'a da kai, yanzun ma ba ƙyaleka zan ba, dan ba ƙaramin haushinka nakeji ba"
Alhaji Musa zeyi magana, amma Khalil ya dakatar dashi yace "ba abunda zaka gayamin, bana buƙatar jin komai daga gareka, amma tabbas ina nan ina bincike akanka, kuma wallahi ina daf da tsayawa a kotu a gaban alƙali da kai"
"Da nayi maka me?"
"in mun haɗu a kotu kaji"
Ya miƙe ya bar gurin, Alhaji Musa ya bi shi da kallo, yana tunanin me Khalil yake nufine?
Bayan Ramlah ta tashi daga mayen da take ne, Hajiya Halima tazo ta sata a gaba tana tambayarta "Ramlah wata magana naji kina yi ɗazu cikin maye, wai Fahad yasa miki cuta, kekuma kin sakawa Bulama, wacce magana ce haka?"
Ramlah tace "Eh to, dukda kince a maye nayi maganar kamar yadda kiji maganar haka take, Bulama shiya fara lalatamin rayuwa ta, na kamu da son ɗansa wanda hakan yasa na biye masa, sedai Bulama yaƙi goyon bayan ya aureni, yake ta cusa masa 'yar Daula ya aura saboda ya cika burinsa, soyayyar da nakewa ɗansa tasa na dinga biye masa ya koyamin shaye2, ya koyamin rayuwar banza nida shi ba abunda bama yi, nace ya Aureni amma yaƙi, kuma na gano yana da cuta me karya garkuwar jiki, dan haka na ƙuduri aniyar ramawa na komawa mahaifinsa, kuma da yake ɗan Akuyane ya karɓeni, ba tare da yasan ina mu'amala da ɗansa ba, dan haka shima ya kwasa, zuwa yanzu nasan uwarsa ma ta ɗauka, hakan yasa na ɗan rage abunda ke zuciyata gara muyi jinyar tare hadda ubansa"
Hajiya Halima ta ɗora hannu a ka tace "yanzu Ramlah abunda kikayi kenan? Ramlah gaba ɗaya kika biyewa namiji kika barbaɗar da rayuwarki da mutuncinki? Kin kyautawa kanki kenan?"
Ramlah tace "Mummy, bafa laifina bane wannan lamarin, duk wanda yazo neman Aurena se ki nunamin ai shi ba sa'an aurena bane, ina gidan Attajiri kamar Daula bekamata in Auri wane ba, ƙarewa ɗan uwanki ya biyoni ya lalata, na kamu da son ɗansa amma yai biris dani, kuma akan idinki nake fita ai, kin taɓa tuhumata ina muke zuwa nida Fahad idan mun fita? Me yasa? saboda idonki ya rufe ke burinki ya kawo miki masu siyan kadarori ki tara kuɗi, don't blame me for this please "
Ta tashi tai tafiyar ta ɗaki ta bar mata falon, Hajiya Halima ta dafe kai ta fashe da kuka, Bulama ya riga ya gama cutarta a rayuwa, ba ta san mema za tace a game da shi ba, ya lalata mata rayuwar 'ya, kuma wai yanzu Ramlah na ɗuke da cuta me karya garkuwar jiki, wanda ta samune a sanadin ɗansa, kuma ya dawo yace a kashe mata ɗa, ta rushe da kuka harda sheshsheƙa, gaba ɗaya komai ya rikice mata, tama rasa meye abunyi, wannan wace irin masiface haka take bibiyar ta? Daga wannan se waccan gaba ɗaya 'ya' yanta sun barbaɗe, haka ta dinga gunjin kuka ita ɗaya a falo, Amal ta ƙarawa ƙofar ɗakinta key, dan bata son tashin hankali.
Da safe Fahad ya shiga cikin gida, domin gaida iyayensa, sedai yan zaune a falon Iman nata masa surutu amma sam hankalinsa baya kanta, yayi zurfi a tunani can ya ɗago kai yace "ke wai ina Mummy ne?"
Iman tace "tana sama ɗakin Daddy"
Ji yayi kamar ta watsa masa wuta, ta ina ze fara gayamata hakinda ake ciki? Koma ya gayamata ai yasan aikin gama ya riga ya gana zuwa yanzu.
Yana nan zaune Sega Bulama yana Sakkowa, hannunsa ɗauke da jakarsa, Mummy sanye da doguwar rigar baccinta, ta riƙo masa wayarsa suna hira, Fahad yaji kamar yaje ya make Bulama saboda tsabar baƙin ciki da takaici, ga wani irin tausayin mahaifiyarsa ya kama shi.
Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace "yau Allah ya nufe ka da shigowa cikin gidan kenan? Yaushe rabonka da shigowa"
Bulama yace "wai gidan ubanwa kake shigewa ne? Ko haryanzu yawon kake baka kwana a gida?" ga mamakinsa seya ga Fahad ya maka masa wata uwar harara, abun da be taɓa yi masa ba, ya kalli mahaifiyarsa yace "Mummy ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, ka tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau, dama na shigo mu gaisa ne zan karya"
Tace "shi Daddyn naka bazaka gaishe shi ba?"
"Ai na gama gaidashi, ni da sake gaisheshi har abada"
Kallonsa sukayi gaba ɗaya, Hajiya Sarah tace "Fahad, daga kan kayan shaye2 naka ka taso ka shigomin falo ko? Shine har kake gayawa mahaifinka wannan maganar?"
Alhaji Bukar yace "ƙyaleshi, ina daf da maganinsa akan wannan mummunar ɗabi'a ta shaye2, dank yake zancen, ban agogona zan fita ina da ayyuka da yawa a Office "
Yasa hannu ya karɓi agogonsa, yai waje bayan fitarsa Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace " Fahad, meyasa ka gayawa mahaifinka wannan maganar haka? Kai lalacewar taka harta kai kayiaa mahaifinka haka? Me yayi maka? "
Yace " bakomai "
" Bakomai amma ka faɗa masa wannan maganar? Abunda kayi ya dace kenan?"
Ya girgiza kai alamar a'a
"to meyasa kayi, salon mutane suji suce ni nake saku a turbar banza, na ku Wulaƙanta mahaifinku?"
"Nifa Mummy bakomai, kema da kin san me yayi da baki faɗi wannan maganar ba, kawai dai Allah ya kyauta"
Ya mike a fusace ya baf falon, tabi bayansa da kallo, Iman tace "Mummy"
"Na'am"
"wai kuwa idonki biyu, jiya da Maman su Amal tazo gidan nan?"
"haba dai? Gidan nan tazo? Ai ban sani ba"
Iman tace "wallahi tazo, bayan ƙarfe goma se bala'i take tana neman Daddy"
"subhanallah, Allah yasa ba'a akan Ramlah tazo ba, saboda kin san halin ɗan uwanku sarai, ina kyautata zaton akwai alaƙar banza a tsakanin sa da Ramlah"
. "Mummy ya akayi kika sani?"
"last week na ganta ta fito daga sashinsa, na tambaye ta amma bata gayamin komai ba, sema baƙar magana da tayi min"
Iman tace "Umma kiyi ta haƙuri, Yaya Fahad se Addu'a gaba ɗaya zamansa a ƙasar waje ba abunda yasa masa se koyar mugayen halaye"
Hajiya Sarah tace "idan da zaman ƙasar waje dai to harda halinsa, meyasa shi Anwar be lalace ba se shi? Bani da abunyi se dai yi masa addu'a, baya jin faɗa baya jin rarrashi, babu wanda banyi ba, amma duk baya ɗauka"
"Mummy kiyi haƙuri, wataran se labari ze dena insha Allah"
"Mhmm Iman kenan, yaushene watarn ɗin? Mutum ya girma amma kullum ba hankali, Allah ya kyauta dai kawai".
Yanzu ma Bulama yana zaune a Office, kiran wayar Me Adda kawai yaje amma taƙi shiga, yai shiru can wayar ta fara ringing, cikin hanzari ya ɗauka ya zata me Adda ne, sedai yaga baƙuwar lambace, ya ɗaga yai sallama
"justice A dutse ne ke magana '
Bulama yace " ok nagane, ya kake ya aiki? "
" Alhamdilillah, dama na bugo in sanar makane da cewar tawagar lawyoyi da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ɗaukaka ƙarar shari'ar Yusuf da nayi, kuma ina kyautata zaton ƙarƙashin jagorancin shahararren lawayrn nan ɗan gwagwarmaya wato Barrister Adam A Adam, dan haka tun wuri kasan abunyi!!!
(Alhamdilillah masha Allah, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, da addu'oinku da na samu bisa rashin da akayi mana, nagode sosai Allah ya bar zumunci)
AMANA! AMANA! AMANACE!!!
AYSHERCOOL
07063065680
11/30/21, 8:20 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _
142_143
Yusuf ya dinga jujjuya takardar nan, ya kalli Barrister Hafiz yace "Ya akayi ta rubuta takadda a bani?"
Barrister Hafiz ya matso daf da Yusuf, ya shiga yi masa magana ƙasa ƙasa (ni kaina da nake ɗakko rahoton banji me yace masa ba)
Yusuf ya sunkuyar da kai yana sauraren Hafiz, Hafiz ya gama gaya masa abunda ze gaya masa, Yusuf ya dinga jinjina kai, Hafiz yace "ka sairaremu nan da wani ɗan lokaci, mungode sosai"
Sukayi musabiha da Yusuf, suka miƙe suk tafi, Yusuf kuma aka maida shi inda yake, hannunsa ɗauke da takaddar da'akace Widad ce ta bayar a bashi, yaje ya samu guri ya zauna yana jujjuya takaddar da'aka bashi yana sake karantawa.
A hankali ya furta "Allah yasa kina lafiya Widad, koba wane hali kike Allah ya kuɓutar dake, ya sake ƙaddara saduwarmu dake"
Widad tana nan a tunanin Allah yasa saƙonta ya isa inda ta aika shi, dan zuwa yanzu ta sare da zata bar gurin nan, dan bata ga hanyar barin gidan nan ba, Amma Allah yasa kafin ta mutu Yusuf ya yafe mata, karta mutu yama ɗauke da pain ɗin bada shedar ƙarya da tayi akansa.
Da ta lumshe ido se hawaye, wani na bin wani, tana tunanin anya zata samu sassauci game da wannan halin ni 'yasu da take ciki? Ita dai fatan ta Allah ya haɗa ta da Yusuf ta nemi afuwarsa.
Ganin Widad dagaske ba zata bashi inda dukiyar take ba, tana ta faman raina masa hankali, ya ƙudurce tabbas ze ɗakko mahaifiyar Yusuf yayi garkuwa da ita, ko ta bashi, ko kuma ya illata ta a gabanta, tunda ya fuskanci bata son duk wani abu daze saka Yusuf da ahalinsa su shiga damuwa.
Dan haka ya ɗakko wayarsa, ya kira me Adda "Allah ya temaki Oga, in ba kai waza mu duƙawa muci?"
Bulama yace "kai kana inane? Kana cikin garin nan ne?"
"A'a, na ɗan baza yin wata harƙalla, duk cikin iya taku da ɓoyewa masu saka na mujiya"
"ina son ganinka a yau ba se gobe ba, a cikin daren yau nake so kaje ka ɗakkomin tsohuwar wancan sakaram yaron"
Me Adda yace "sa hankalinka a inuwa, turo adreshinta, zamuyi ram da ita mu kawo maka"
Bulama yace "Good, zan turo maka adreshin, a daren yau nake son a gama komai, ku ɗakkota ka kawomin ita"
"An gama yallaɓai" me Adda yai maganar kamar yana maye.
Likitoci suka yi iya abunda zasu iya akan Mahaifiyar Nurat, amma babu wani cigaba, ta gaza farfaɗowa gashi jini yaƙi tsayawa, numfashi kawai take amma sam zuciyarta bata harbawa yadda yakamata, tuni danginta da 'yan uwanta suka cika Asibitin, Alhaji Musa yayi mamakin yadda akayi suka ji, bayan shi dai be kira kowa ya gaya masa ba.
Nan suka shiga tambayar ba'asi, akan yadda akayi' yar uwarsu ta faɗo daga kan bene?
Alhaji Musa yace "Wallahi ta fito ne daga ɗaƙi, zata sakko daga kan bene kawai ta zamo ta gangaro, dama tun safe take cemin tana jiri, nace mata ko Asibiti zamuje tace in bari seda yamma, ina ga harda jirine ma ya ɗebe ta yasa ta faɗo"
Barrister Khalil kallon Alhaji Musa kawai yake, ji yake tamkar ya danƙo wiyansa ya rufe shi da duka, dan sam beji ya gamsu da maganar da ya faɗa ba.
Amal ta shirya tsaf, dan taje a zubar mata da ciji ba tare da mahaifiyarta ta san halin da take ciki ba, gaba ɗaya ta tattara ta zuba musu ido, dan itama fama take da kanta, ko gani bata iyayi sosai sedai dususu saboda tsabar ɓacin rai da damuwa da yake ta'azzara mata hawan jini, gaba ɗaya ta koma kamar wata zararriya, yauma ta tashi tana ta fama da kanta, jiri da ciwon kai jininta ya hau, tana kwance a falo tana fama da kanta, Amal tazo zata fice.
"Amal ina Ramlah ne?"
Amal tace "tana ɗakinta, inaga yauma tayi shaye2 tana can tana bacci"
. Hajiya Halima tai ajiyar zuciya, tace "kekuma ina zaki? Naga kamar fita zakiyi"
"Eh zan ɗan fitane, ba nisa zanyi ba"
"Amma kina kallon yadda nake fama, ina kwance ina fama da kaina, amma zaki saka kai ki fice ki barni a haka?"
Amal tace "Mummy, na matsu in fitane ina da wani uzuri na gaggawa, ba daɗewa zanyi ba, ga Ramlah can kuma tana nan ai, ba daɗewa zanyi ba"
Tai maganar tana tafiya, a haka harta bar falon ta fice abunta.
Tana zaune a mota ta kira Alhaji Haruna, ya ɗaga ba tare da yasan wanda ya kira shi ba, "na gaya maka ina ɗauke da juna biyu, Amma kaƙi ɗaukar kowane mataki ko? To ka saurareni wallahi zan tona maka Asiri, duniya taji abunda ka aikata"
"wai ke ni dan Allah ya kike son inyi ne? Har yanzu baki fanshe bane? Me kike so inyi miki?"
'haka ma zaka ce? To shikenan, ciki dai nakane, kai kayi shi, wallahi ba zanyi abun kunya ni kaɗai ba, na gaya maka'
Ta ajiye wayar, tare da yin ajiyar zuciya, ta kunna motar ta ta fita.
Suka yi waya da wannan Nurse ɗin, wadda tace zata taimaka mata ta zubar da cikin nan, ta gaya mata a dai dai inda zasu haɗu.
Aikuwa tana zuwa suka haɗu, ta ɗau Nurse ɗin a motarta, ta fara nunawa Amal hanyar zuwa Gurin, Amal tace "nifa gaskiya tsoro nakeji, wallahi ji nake kamar wani abu ze faru"
Nurse ɗin tace "haba ke kuwa, amma dai wannan ne karon farko da zakiyi abortion ko?"
Amal ta jinjina kai alamar eh, Nurse ɗin tace "karki damu mana, ai ke naki cikinma ƙaramine, nan da nan za'a cire shi babu wani tashin hankali, ɗan pain ɗin kaɗanne, ke ciki koya kai 9 months Doctor Hamisu ze jajjageshi ya cire shi tsaf, dan haka ki kwantar da hankalinki, komai ze tafi normal"
Sukaje Asibitin, Nurse ɗin ta jata har office ɗin doctor Hamisu, suka tarar yana aiki a system, Nurse ɗin ta gaisheshi tace "Doctor, ga customer fa cikine take son a cire mata"
Ya ɗago ya kalli Amal sannan yace "cikin wata nawane?"
Amal tace "nima ban sani ba, amma naji da akamin test ance watansa ɗaya be cika biyu ba"
Doctor Hamisu yace "ai wannan ba abun damuwa bane ba, za'a cire shi ba wata wahala, an gayamiki kuɗin aikin?"
Tace "eh an gayamin, zanyi transfer ɗin kuɗin".
Ya ɗago ya sake kallon ta yace "you look familiar to me, is like I know you somewhere"
Amal tace "eh nima ina ganin kamar na sanka fa, kamar likitan dake duba Widad shekarun baya"
Yace "exactly, that's where I know you, ya maman naki?"
"tana lafiya ƙalau"
"masha Allah, amma ya akayi ke kuwa wannan abun ya faru haka?"
Amal ta ɗan ɓata fuska tace "wallahi wanine yamin Akuya, daga zuwa kai masa saƙo, shiyasa nake son inyi acire kafin ta gane"
"ba matsala, karki damu kinji yanzu za'a cireshi insha Allah, Nurse maza kaita ɗakin da ake aiki ta kwanta ta jirani".
Aka kai Amal ɗakin, ta kwanta tana jiransa, gabatan se faɗuwa yake, tana tunanin kar wani abu ya faru, bayan an cire cikin "
Tana nan kwance, yazo ya ɗaura mata ruwa, ya bata wani magani ta sha, ko mintuna goma ba'ayi ba da saka mata ruwan, da bata maganin ta fara wani irin ciwon mara kamar zata mutu, ta dinga murƙususu, kafin kace meye wannan tuni jini ya fara malala daga jikinta, bayanta kamar ze ɓalle da ƙugunta, ta dinga antayar da jini, Nurse ɗin nan ta dinga temaka mata, yazo ya sake mata wasu allauran, yace
"Sister, maza idan ta ɗan huta ki kaita gida ta samu rest, jinin ze tsaya insha Allah"
Haka kuwa akayi, Ta kai Amal har gida, Amal ta shiga da motar, a dudduƙe ta tafi ɗakinta ba tare da kowa ya ganta ba, taje ta baje akan gadonta, dan wani irin sanyi take ji da jiri a lokaci ɗaya.
Duk yadda Suleiman yaso ɓoyewa Umma yadda shari'ar Yusuf ta kaya seda taji a radio, kasancewarta mace ms son jin radio, da farko zamanta a gidan tare da Surayyah ta ɗanji daɗi, dan koba komai motsin mutum rahama ne, tana ɗebe mata kewa ita da yaran ta, kuma ta kan sakata a gaba lallai se taci Abinci, ta sha magani amma tunda taji hukuncin da akayiwa Yusuf ta kasa zaune ta kasa tsaye, se kuka nan da nan jikinta ya nemi ya rikice saboda tashin hankali da damuwa.
Suleiman yaje ya sameta a ɗakin da take, yace "Umma, babu yadda za'ayi Yusuf yayi wannan shekarun haka a gidan yari, ai kowa yaga irin shari'ar da akai, ana nan ana wani ƙoƙari, sedai cikin sirri ake komai, ki kwantar da hankalinki, nina gayamiki da yardar ubangiji se Yusuf ya kuɓuta, amma kidena wannan kukan haka da damuwa dan Allah "
Umma tace " Haba Suleiman, kaifa ka cemin duk wanda yai yunƙurin taimakonsa barazana ake masa, taya ya za'a samu wanda zasu taimaka masa alhalin kowa yana kallon yadda akai shari'ar, kuma babu wani taimako da aka masa? Ni na karaya kawai, haka Allah ya ƙaddara masa rayuwarsa, ƙaddara babi babi, daga wannan se waccan " tai maganar tana kuka me taɓa zuciya.
Sulaiman yace" Umma, kece fa kike bani misali da Annabawan Allah, da irin jarabtar da Allah yayi masa, dan haka mu ɗauka jarrabawar sa ce a haka, kuma Allah yasa sanadin ɗaukakarsa ne yazo a haka, duk yadda Allah ya kai ga jarabtar bawansa, se kinga ta wani ɓangaren Allah ya masa wata ni'ima wadda ba kowa yayi wa ba, ki kwantar da hankinki Umma, shirye shirye sunyi nisa ta ƙarƙashin ƙasa, kuma insha Allah zamu bawa maƙiya kunya "
Umma ta gyɗa kai tace " to Allah yasa"
"Ameen ya Allah, ki cigaba da Addu'a Umma, ubangiji Allah ya bamu nasara"
"Addu'a ina nan ina yi, Allah yayi maka albarka da kai da iyalanka, ubangiji Allah ya jiƙan magabatanka ya rahamshesu, ubangiji Allah ya raya maka zuriyar ka akan tafarki madaidaici, yasa su zamo masu jin ƙai kamar kai, Matarka Allah yayi mata albarka ya sake haɗa kanku, tunda abun nan ya samu ɗana kake tsaye a kaina, kana bani gudunmuwa iyayinka, kaine dana ganka nake jin daɗi, nake jin daɗin yadda kake tausata nagode nagode "
Suleiman yace " bakomai umman Yusuf, karki damu duk yiwa kaine, ni ban rayu da mahaiyata ba, marayane ni tun ina yaro ƙarami, ina jinjina soyayyar uwa ga ɗanta, shiyasa nasan kina cikin damuwa rashin Yusuf da dole kina buƙatar a tausasa miki, ga Ɗanki mutum ne nagari kamili, wani abu da Yusuf ya taɓa yimin da bazan manta ba, lokacin mahaifina yana ciwon ajali sunje duba shi, baya iya cin Abinci sam, Yusuf ya kai masa dafaffen ƙwai da kayan marmari, naje siyo masa magani Yusuf ya zauna yana bashi ƙwan nan a baki, bayan ya gama bashi Baba yayi amai, ya ɓatawa Yusuf jiki, kayansa masu kyau a jikinsa suka ɓaci, amma be nuna damuwarsa ba ya ɗaga shi ya gyara masa jiki, kullum aka tashi daga gurin aiki se yaje ya duba mahaifina, har suyi hira, alhalin ni a lokacin ko kulani bayayi sosai, dukda ina shugabansa a gurin aiki, duk ranar da beje ba Baba ya dinga tambayar ina yaron nan me fararen idanuwa kuwa? Ranar da Baba ze bar duniya seda yayi masa addu'a sosai, bazan manta ba, naji daɗin yadda ya nuna damuwa akan mahaifina fiye da tunani, dukda wannan abun alkhairi da yayi min ba fiye shiga sabgata ba sedai in sha'anin aiki ya haɗamu, hakan ya tabattar min halinsa ne a haka, halin taimako da tausayi ga mutane, shiyasa bazan taɓa bari inga wani mummunan abu ya samu iyayen Yusuf ba"
Umma tai ajiyar zuciya tace "Kaga ni be taɓamin wannan hirar ba"
Suleiman yace "Ai Umma wannan ɗan naki halinsa se shi, miskiline ajin farko sedai akwai tausayi da jin ƙai, ni dai fatana kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki"
(Wato shi alkhairi a rayuwa, idan har zaka aikata shi ko bayan ranka waninka ze mora, Kayi ƙoƙari kayi abunda mutane zasu dinga tunaka da alkhairin ka, ba da mugun aiki ba)
Nan Sulaiman yaita kwantarwa da Umman Yusuf hankali, shida matarsa.
Kamar yadda Bulama yai umarni, cikin dare su me Adda suka bazama gidansu Yusuf, inda suke kyautata zaton Umman Yusuf tana nan.
Amal har dare yayi tana fama da matsanancin ciwon mara kamar zata yi hauka, gashi ta kasa cin komai, se uban amai da take faman yi, ga jini se zuba yake yaƙi tsayawa ita kaɗai a ɗaki babu wanda yasan halin da take ciki sam.
Gaba ɗaya babu wanda hankalinsa ya kai kan cewar Nurat bata nan se bayan kwana ɗaya, tai ihun tayi bugun ƙofar babu wanda ya ji balle ya buɗe ta, gashi bata san halin da mahaifiyarta ke ciki ba, sakamakon taji ihutmnta amma bata da tabbas ɗin abunda ya faru da ita.
Khalil ne ya kalli Alhaji Musa yace "wai ina Nurat ne? Tunda mu kazo Asibitin nan ban ganta ba fa"
Cikin inda inda Alhaji Musa yace "Amm da yake itama bata da lafiyar ne, ban san ya nata jikin ba, bana son hankalin ta ya tashi ne, bari inje gidan in taho da ita"
Khalil yace "kace duk gidan ma basu da lafiya?"
"wallahi kuwa, Nurat ɗince ma ta fara sannan uwar"
"Amma an kaita Asibiti kuwa? Meke damun Nurat ɗin"
. "A'a ba wani abu bane dama, dama nace zata koma karatu ne itakuma bata so, shiyasa take ta damun kanta dai, kusan damuwace ta saka take rashin lafiya"
"Amma meyasa baka ƙyaleta ba, tunda bata so ba? Ka takura se taje kaga gashi ta shiga wani hali"
Maman Khalil tace "kai Khalil, wai nan a kotu muke ne? Jimin ja'irin yaro ka tasa mutum a gaba da tambayoyi".
Khalil yace "Allah ya bada haƙuri, muje semu taho nida Nurat ɗin kai seka huta kawai".
Alhaji Musa yace "No, bakomai ai ka bari zan kawota da kaina"
Maman Khalil tace "kuje tare mana, ai bakomai se su taho taho shida ita"
Khalil ya saka Alhaji Musa a gaba, da wani irin kallo wanda ya kasa tantance na menene.
Haka suka tafi kowa a motar Alhaji Musa, koda sukaje gidan Alhaji Musa yace "bari in kirata tana saman bene"
Khalil yace "shikenan babu laifi, bari in jira a nan" ya zauna a falo.
Alhaji Musa ya hau sama da sauri, danshi gaba ɗaya ya manta daya kulle Nurat a ɗaki, yana zuwa ya buɗe ya tarar da ita a baje a sume a ɗakin, a gigice ya ƙarasa yana kiran sunanta amma bata motsi, da sauri ya ɗakkota ya sakko daga benen, hannunsa riƙe da ita.
Khalil ya miƙe tsaye yace "lafiya kuwa?"
Alhaji Musa yace "a sume na tarar da ita"
Basu tsaya ba sukayi waje gurin mota, aka saka Nurat a ciki suka nufi Asibiti cikin gaggawa.
Itama a emergency ɗin aka karɓeta, aka rufu akanta don ceto rayuwarta itama, rufetan da yayi dama bata karya ba, ga kuka ga damuwa ga tashin hankalin da ta shiga jin ihun mahaifiyarta, hakan yasa ta shiga tashin hankali, garin kuka tai shaƙuwa numfashinta ya sarƙe ta faɗi, ga yunwa dan haka abun ya tarar mata, daya buɗe ɗakinma ya ɗakkota numfashinta iya ƙirjinta ne kawai, babu inda yake motsi a jikinta.
Alhaji Musa ya koma reception ya zauna ya dafe kai, yana tunanin wannan wace irin masifa ce haka kashi kashi? Ze kashe iyalansa ɗaya bayan ɗaya da kansa, da hannunsa duk a dalilin aikin banza, dalilin neman kare a Karofi, Bulama nata musu gafara sa amma babu ƙaho tsayin shekaru.
Bulama yana ta jiran yaji su me Adda sun bashi feedback akan aikin daya sa kasu, amma shiru ba suyi magana ba, ya kira layin me Adda babu adadi amma tun tana shiga ta dawo bata shiga, sema ace masa line busy, daga ƙarshema aka kashe wayar gaba ɗaya.
Alhaji Musa yana nan zaune, aka kira shi a waya aka sanar masa da an gano inda Anwar yake, yayiwa Bulama magana, akan me yakamata ayi? An kira wayarsa bata shiga se ace busy.
Kamar ya share ya basar, amma dai ya kira Bulama, Bulama ya ɗaga yace "ya naji muryarka a hakane? Baka da lafiya ne?"
"A'a lafiyata ƙalau, amma ina Asibiti"
"me kake a Asibiti kuma?"
"Wallahi abubuwa sun damalmalemin gaba ɗaya, bisa tsautsayi daga zan ture Maman Nurat daga bene in sakko, bisa tsautsayi ta faɗo kwananta biyu a Asibiti har yanzu bata hayyacinta, na rufe Nurat a ɗaki saboda ta gano halin da ake ciki, ta gano da saka hannuna a abunda ke faruwa a gidan Daula, itama gata can a emergency bata san wake kanta ba, gaba ɗaya na rasa abunyi ma"
Maimakon Bulama ya tausayawa Alhaji Musa halin da yake ciki, seya haushi da faɗa "wai kai wand irin mutum ne haka Musa? Ya za'ayi kabari yarinyar ka ta gano? Gaskiya baze yuwu ba sam, wancan karon dana maka magana ashe baka ɗau mataki ba? To dole kasan yadda zakayi tun wuri dole a ɗau matakin daya dace akanta, bazs yuwu ta tona mana Asiri ba"
Ran Alhaji Musa yai matuƙar ɓaci da jin Kalaman Bulama, bs tausaya masa halin dayake ciki ba, amma ya haushi da faɗa, dan haka a hasale yace "kaga ya isa naji, ance in gaya maka an gano inda Anwar yake, ɗan gidan Hajiya Halima"
Bulama yace 'to me kace musu? "
" me kuwa zance musu? Umarninka suke jira"
"Aina riga na gama bada umarni, a kasheshi kawai dan baze yuwu a ƙyaleshi ba"
Alhaji Musa yace "seka kirasu ka gaya musu, ni yanzu ina cikin wata matsalar ne"
Yana gama faɗin hakan ya katse kiran, tunani ya fara yi, Hajiya Halima tana da Alaƙa da Bulama 'ya' yanta kamar nasane, amma yace a kashe ɗanta dan kar Asirinsa ya tonu, dan haka babu shakka idan ya gama da Anwar kan Nurat ze dawo.
Ai nan da nan ya ɗau wayarsa ya kira Hajiya Halima, ta ɗaga wayar da ƙyar alamar tana jin jiki, tai sallama a hankali
Alhaji Musa yace "malama idan zaki ware muryar ki ki ware, an gano inda ɗanki yake Anwar, amma Bulama yace A kasheshi dan karya tona masa Asiri....
0 comments:
Post a Comment