Alhaji Musa yace "ke nifa tuni na dawo daga rakiyar mutumin nan, Azzalumi ne kawai, kansa ya sani bashi da imani sam, ni kaina yanzu haka muna Asibiti nida su Nurat, amma gaba ɗaya ko yamin jaje se masifa da tashin hankali da yake min, shiyasa na kwashi kuɗina na saka a siyasa, in samu su bani takara in huta da wannan mulkin mallakar da yake mana, ga uwar dukiyarmu da muke narkawa amma har ynzu babu wani bayani "
Hajiya Halima ta fashe da kuka tace " ni Bulama zeyi wa haka? Anwar kamar ɗa yake a gurinsa amma shine zece a kashemin shi? Baze yuwu ba kuwa "
Ta ajiye wayar, ta miƙe ta shiga ɗakinta ta zura doguwar riga, kusan ƙarfe goma saura na dare, amma tayi waje ta ɗau mota ta fita ta tafi gidan Bulama a daren.
Shikuma Bulama yana zaune yana ta nazari akan yadda ze ɓullowa al'amura da suke neman damalmale masa, ya dinga kiran layin su Me Adda amma shiru babu Labari, waya taƙi shiga sam.
Masu gadi kansu sunyi mamakin ganinta a wannan daren, kamar wata mahaukaciya ko gabanta bata gani sosai saboda tashin hankali, kai tsaye ya shiga falon dake ƙasa tana bala'i "Ina Bulama yake? Ina Bulaman?"
Iman ce zaune a falon tana kallon zee world tace "Mummy lafiya kuwa?"
"ban sani ba, ina uban naku yake tsohon macuci azzalumi?"
Iman ta kalleta da mamaki jin irin furcin da take akan mahaifinsu wanda ya kasance ɗan uwa a gareta, Iman tace "Mummy ya riga ya hau sama, inaga ma ya kwanta fa"
Ai bata tsaya jiran me Imana zata kuma ce mata ba ta haura saman da kanta, ba zato ba tsammani ya ɗaga kai yaci karo da Hajiya Halima a tsaye a kansa.
Ya kalleta yace "Halima, lafiya kuwa zaki zo a daren nan? Bakya jira ayi miki iso kawai ki hauromin ɗaki haka?"
"Dalla rufemin baki, me zaka gayamin har wani iso zan jira ayimin, munafuki azzalumin banza dana wofi, tsawon shekaru ina maka aiki, kana sani duk abunda kaga dama ina maka, dan ka cinma burinka ba tare da na nuna gazawata ba, shine halin naka na baƙin kumurci zaka gwadamin, shine kayi umarni da idan anga Anwar a kasheshi, ɗan nawa za'a kashe? Wallahi baka da imani ba kada Alƙawari tun wuri ka dakatar da wannan maganar idan ba haka ba Wallahi ran ɗana baze tafi a banza ba"
Zazzaro ido Bulama yayi ya dinga ƙifta mata ido akan tayi shiru, amma tace "bazan shirun ba, wallahi babu inda zani se an dawo min da ɗana"
"Halima wai wace irin magana kike hakane? Kamar yaya nace idan anga Anwar a kasheshi? Me Anwar yayi min wanda zesa ince a kashe shi, ni da na kaiwa jam'ian tsaro maganar dan ayi bincike akansa a gano inda yake ya zakice nace a kasheshi? Wani munafukin ne ke neman haɗani da 'yar uwata?"
" Kaga bana son kame kame da ƙaryar banza, wanda ya gayamin baze maka ƙarya ba, macucin banza da na wofi kuma wallahi idan ɗana ya mutu you must pay for it, wallahi aka kashemin Anwar seka fanshi ransa, nima kasan halina ka san abunda zan iya aikatawa "
Gaba ɗaya Bulama ya dirirce ya rasa abunyi, ya shiga tsuma yana fatan Allah yasa wani beji abunda ta faɗa ba.
Ya biyo bayanta ya leƙa, yaga ba kowa a falon ƙasa dukda ɗakin a rufe yake babu wanda ze iya jiyo me sukayi, ya koma bedroom ɗinsa ya tarar da Hajiya Sarah tana ta baccinta hankali kwance, yai ajiyar zuciya tare da tunanin bata jiba, amma ya zauna yai shiru akan gadon yana tunani, tabbas babu wanda ze gayawa Halima wannan maganar idan ba Alhaji Musa ba, tabbas dole yayi maganin Alhaji Musa.
Cikinsa ne ya murɗa ya tashi ya tafi banɗaki, kusan kwana huɗu kenan yana fama da gudawa taƙi tsayawa, dan haka ya sa ransa idan ya gama da wannan matter ɗin zeja yaga likita.
Yusuf se sake juya takaddar nan yake, yana tunanin wani hali Widad ɗin ke ciki, tabbas yasan da tana da dama bazata barshi a gurin nan ba, dole akwai wani abu da yake gudana a ɓoye, idan ya kalli sentence ɗinta na ƙarshe na ba lallai su sake haɗuwa ba se yaji gabansa ya faɗi, lallai ko a ina take tana cikin mawuyacin hali, "Allah ya ƙara haɗa fuskokinmu my wife, Allah yasa kina hannu na gari, i love you too" yai maganar a hankali tare da lumshe idonsa.
Rayuwar da suka yi tare a ƙauye ta dinga dawo masa, koba komai zamansa da ita ba ƙaramin farinciki ya samu ba, zamansu a ƙauye yasa Ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ta samu hutu na wani ɗan lokaci, ya daɗe beji cin zarafi da gorin rashin iyaye daga mutane ba, sedai matukar kewar Ummansa da yayi, be sake zaton ze samu wadda zata aureshi ba saboda rashin nasaba ba, sedai cikin hukuncin Allah ya auri yarinyar da zuciyarsa ta mato a sonta, dukda nisa da ratar dake tsakanin su, yarinyar da manyan wanda suka isa ma basa gabanta, soyayyar ma bata yadda da ita ba, amma Allah ya ƙaddara Aurensu, har suka yi zama cikin farin ciki, ya dinga tuna irin Shagwaɓarta wauta da yarinta wasu lokutan, ya tuna lokacin da take koyar tankaɗe, da sanda take wa Abincin garin kallon banza, da yadda ta dage ita seta samu ciki, da irin kallon da take masa idan ya tsokane ta.
A hankali ya sake lumshe ido yana murmushi, sekuma ya tuna yadda ta shiga damuwa daya bata labarinsa, da yadda ta dinga kururuwa tana kuka tana gaya masa tana sonsa lokacin da aka kama shi a garin, da yadda taje kotu ta bada sheda akansa, ga shekarun da aka yanke masa a gidan yari, ga abunda ta rubuta masa kawai se yaji ya karaya hawaye ya shiga bin gefen idonsa, baya tunanin ze sake wata rayuwa me daɗi a nan gaba, mussman kasancewa da Widad a inuwar Aure.
Da ƙyar likitoci suka samu Nurat ta dawo hayyacinta ta samu bacci, aka sa mata ruwa, sedai harta farfaɗo ɗin numfashinta da vital signs ɗinta suka daidaita bata gane mutane sosai, saboda ta galabaita an samu dai bacci ya ɗauketa cike da fatan idan ta tashi zata iya dawowa hayyacinta gaba ɗaya, mahaifiyarta kuwa gaba ɗaya har yanzu ba'a gano kanta ba, tana kwance ne kawai, numfashi ne kawai a ƙijinta, banda haka babu abunda yake aiki a jikinta, sam bata san abunda ke faruwa ba, shi kansa numfashin nata da ƙyar take yinsa wasu lokutan, saboda ta zubar da jini sosai, kuma ana kyautata zaton ta samu rauni a cikin kanta, sakamakon buguwa da tayi, likitoci sun rubuta mata hoton Ƙwaƙwalwa dan tabattar da abunda yake damunta.
Abu kamar wasa, jini yaƙi tsayawa Amal, se aikin zaryar banɗaki take, jini se zuba yake babu ƙaƙƙautawa, ta rarrafa ta haɗa Abinci tana ci kota samu sauƙin wannan wahalar haka, zuciyarta tana ƙuna akan yadda Alhaji Haruna ya cuce ta, Hajiya Halima ta fito falon ta zauna ta dafe kai ta kalli Amal tace
"wai kuwa lafiyarki ƙalau kuwa? Gaba ɗaya kin wani ɗashe kinyi fari ƙal, kamar baki da jini a jiki, ko baki da lafiya ne?"
Amal tace "lafiyata ƙalau, period kawai nake shiyasa"
Hajiya Halima tai ajiyar zuciya tace "Amal kin kuwa san abunda Bulama yaimin?"
"A'a sekin faɗa"
"wai an gano inda Anwar yake, amma yace wai a kasheshi saboda karya tona Asiri"
Da sauri Amal ta kalleta tace "A kasheshi kuma? Me me kikace masa?"
"Naje har gidansa jiya da daddare, na ƙare masa tatas, nace wallahi aka kashe min ɗana seya fanshi ransa da nasa ran kona 'ya' yansa"
Amal tabi mahaifiyarsu da kallo, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, duk mahaifiyarsu ta ɗaiɗaita rayuwarsu da kanta, kowa yana karɓar nasa kason ɗaya bayan ɗaya.
Ramlah ce ta fito tana tangaɗi, tana magana cike da maye ta tsaya a tsakiyar falon tace "Wai ni.... Waini Fahad baze Aureni bane... Bazaki ce ya aureni ba ko? Wa.. W.. Wallahi kuwa bazan dena shaye2 ba tunda ya lalatani, ku.... Kuma... Kumaaa ai shikenan tunda nasan Na sakawa Bulama cutar tunda shima ya sakamin... Wallahi idan baka Aureni ba sena sakawa Wannan yaron Ramadan ma, idan yaso kow... Ko..... Kowama ya samu ni za'ayiwa hauka? Ya.. Ya ɗauka bani da wayo hmm baka san Rmalha bane" kawai ta faɗi a gurin tana juyi tana ci gaba da sambatu marasa kan gado sam.
Hajiya Halima ta kalleta tace "Ramlah wai wace cutar kike magana akai ne? Wace irin cuta?"
Ramlah bata san me take ba, juyi kawai take yi tana wasu surutan irin na marasa kan gado, Amal kam tasan babu mamaki idan akace Fahad yana ɗauke da wannan cutar me karya garkuwar jiki, amma sedai dagaske Ramlah take tana mu'amala da Bulama ma kenan, gaban Amal ne ya faɗi kardai ace itama tana da wannan cutar, miƙewa tayi da sauri zata tafi ɗakinta, Hajiya Halima tace "Amal ina zaki? Kina jin maganar da gake faɗa? Ko dai duk a cikin maye take ne?"
Amal tace "tunda ki kaji ta faɗa a maye, to ko ba'a mayen bama ya faru, sedai fatan Allah ya kyauta"
Amal ta tafi ɗakinta, dan itama fama take da kanta, wannan azabar ciwon marar da zubar jinin sun isheta haka.
Anty Saddiƙa ƙanwar Maman Nurat itace a gurin Nurat, itakuma maman Nurat ba'a barin kowa ya shiga inda take in ba likitoci ba, saboda tana ƙarƙashin kulawa ta musamman, Anty Saddiƙa taje salla Khalil na zaune a gurin Nurat, ai kuwa ta farka ta zaci zata ganta a ɗakin Dad ɗinta ya kulle ta, sedai tana buɗe ido tai arba da wani gurin daban, ta yunƙura zata tashi zaune, Khalil ya taho da sauri ya riƙeta yace "yi haƙuri, ki kwanta kinji, karki gaggawa jikinki babu ƙwari"
A Shagwaɓe Nurat tace "Brother ruwa zan sha"
Yace "ok bari in baki"
Ya ɗakko ruwam roba, ya buɗe ya bata ta sha, har ze gyara mata kwanciyarta ta kwanta, ta riƙe shi gam tana kallonsa, tana ƙoƙarin tuna meyafaru ihun Mummynta ta tuna, nan da nan ta razana tace masa "Mummy, Khalil Mummy na tana ina?"
Khalil yace "kwantar da hankalinki tana nan lafiya"
"A'a ban yadda ba, naji ihunta fa ranar, ban san meye ya sameta ba, tunda Daddy ya kulleni ban sake ganinta ba, waini ya akayi ma nazo nan ne?"
Khalil ya kalleta yace "kamar yaya ya kulle ki? Ya kulleki a ina?"
Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta gaya masa, yai shiru yana nazarin maganganun Nurat, cikin kuka tace "ina Mummy take? Dan Allah ka kaini in ganta dan Allah"
Khalil yace "ki kwantar da hankalinki, likitoci na can na kula da ita, idan ta farka zata zo ki ganta"
"to wai meyasa meta ne?"
"Bakomai, ta faɗi ne kawai saboda Dad ɗinki ya rufeki, bari Anty Saddiƙa tazo ta temaka miki kiyi wanka"
Bayan Saddiƙa ta shigone, Khalil ya tashi ya fita, a reception yaje ya samu Alhaji Musa a zaune, dan idan yazo Asibitin ya duba su Nurat nan yake dawowa ya zauna, dan gaba ɗaya haushinsa suke ji.
Ya zauna kusa da Alhaji Musa ya kalle shi yace "garin yaya ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene?"
Alhaji Musa yace "wace irin magana ce wannan? Ba a gabanka nayi wannan bayanin ba?"
Khalil ya kalle shi yace "to ya akayi ka kulle Nurat? Laifin me tayi maka"
Da sauri Alhaji Musa yace "tana ina? Nurat ɗin ta farkane?"
Yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, amma Khalil ya tareshi yace "na tambayeka kana ƙoƙarin tashi ina zaka?"
Yace "wai ita Nurat ɗince tace maka kulleta nayi?"
Khalil yace "labari na samu, daga majiya me ƙarfin gaske, dan haka nake tambayarka garin yaya ka kulleta"
"wai Khalil yaushe ka koma haka? Yaushe ka koma mara kunyane?"
"ba rashin kunya bane, gaskiya ce dama ina da ayar tambaya akanka, wallahi muddin na ganoka da wani abu ba dai dai ba, naga wani abun kayiwa ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene, wallahi se nayi shari'a da kai, yanzun ma ba ƙyaleka zan ba, dan ba ƙaramin haushinka nakeji ba"
Alhaji Musa zeyi magana, amma Khalil ya dakatar dashi yace "ba abunda zaka gayamin, bana buƙatar jin komai daga gareka, amma tabbas ina nan ina bincike akanka, kuma wallahi ina daf da tsayawa a kotu a gaban alƙali da kai"
"Da nayi maka me?"
"in mun haɗu a kotu kaji"
Ya miƙe ya bar gurin, Alhaji Musa ya bi shi da kallo, yana tunanin me Khalil yake nufine?
Bayan Ramlah ta tashi daga mayen da take ne, Hajiya Halima tazo ta sata a gaba tana tambayarta "Ramlah wata magana naji kina yi ɗazu cikin maye, wai Fahad yasa miki cuta, kekuma kin sakawa Bulama, wacce magana ce haka?"
Ramlah tace "Eh to, dukda kince a maye nayi maganar kamar yadda kiji maganar haka take, Bulama shiya fara lalatamin rayuwa ta, na kamu da son ɗansa wanda hakan yasa na biye masa, sedai Bulama yaƙi goyon bayan ya aureni, yake ta cusa masa 'yar Daula ya aura saboda ya cika burinsa, soyayyar da nakewa ɗansa tasa na dinga biye masa ya koyamin shaye2, ya koyamin rayuwar banza nida shi ba abunda bama yi, nace ya Aureni amma yaƙi, kuma na gano yana da cuta me karya garkuwar jiki, dan haka na ƙuduri aniyar ramawa na komawa mahaifinsa, kuma da yake ɗan Akuyane ya karɓeni, ba tare da yasan ina mu'amala da ɗansa ba, dan haka shima ya kwasa, zuwa yanzu nasan uwarsa ma ta ɗauka, hakan yasa na ɗan rage abunda ke zuciyata gara muyi jinyar tare hadda ubansa"
Hajiya Halima ta ɗora hannu a ka tace "yanzu Ramlah abunda kikayi kenan? Ramlah gaba ɗaya kika biyewa namiji kika barbaɗar da rayuwarki da mutuncinki? Kin kyautawa kanki kenan?"
Ramlah tace "Mummy, bafa laifina bane wannan lamarin, duk wanda yazo neman Aurena se ki nunamin ai shi ba sa'an aurena bane, ina gidan Attajiri kamar Daula bekamata in Auri wane ba, ƙarewa ɗan uwanki ya biyoni ya lalata, na kamu da son ɗansa amma yai biris dani, kuma akan idinki nake fita ai, kin taɓa tuhumata ina muke zuwa nida Fahad idan mun fita? Me yasa? saboda idonki ya rufe ke burinki ya kawo miki masu siyan kadarori ki tara kuɗi, don't blame me for this please "
Ta tashi tai tafiyar ta ɗaki ta bar mata falon, Hajiya Halima ta dafe kai ta fashe da kuka, Bulama ya riga ya gama cutarta a rayuwa, ba ta san mema za tace a game da shi ba, ya lalata mata rayuwar 'ya, kuma wai yanzu Ramlah na ɗuke da cuta me karya garkuwar jiki, wanda ta samune a sanadin ɗansa, kuma ya dawo yace a kashe mata ɗa, ta rushe da kuka harda sheshsheƙa, gaba ɗaya komai ya rikice mata, tama rasa meye abunyi, wannan wace irin masiface haka take bibiyar ta? Daga wannan se waccan gaba ɗaya 'ya' yanta sun barbaɗe, haka ta dinga gunjin kuka ita ɗaya a falo, Amal ta ƙarawa ƙofar ɗakinta key, dan bata son tashin hankali.
Da safe Fahad ya shiga cikin gida, domin gaida iyayensa, sedai yan zaune a falon Iman nata masa surutu amma sam hankalinsa baya kanta, yayi zurfi a tunani can ya ɗago kai yace "ke wai ina Mummy ne?"
Iman tace "tana sama ɗakin Daddy"
Ji yayi kamar ta watsa masa wuta, ta ina ze fara gayamata hakinda ake ciki? Koma ya gayamata ai yasan aikin gama ya riga ya gana zuwa yanzu.
Yana nan zaune Sega Bulama yana Sakkowa, hannunsa ɗauke da jakarsa, Mummy sanye da doguwar rigar baccinta, ta riƙo masa wayarsa suna hira, Fahad yaji kamar yaje ya make Bulama saboda tsabar baƙin ciki da takaici, ga wani irin tausayin mahaifiyarsa ya kama shi.
Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace "yau Allah ya nufe ka da shigowa cikin gidan kenan? Yaushe rabonka da shigowa"
Bulama yace "wai gidan ubanwa kake shigewa ne? Ko haryanzu yawon kake baka kwana a gida?" ga mamakinsa seya ga Fahad ya maka masa wata uwar harara, abun da be taɓa yi masa ba, ya kalli mahaifiyarsa yace "Mummy ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, ka tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau, dama na shigo mu gaisa ne zan karya"
Tace "shi Daddyn naka bazaka gaishe shi ba?"
"Ai na gama gaidashi, ni da sake gaisheshi har abada"
Kallonsa sukayi gaba ɗaya, Hajiya Sarah tace "Fahad, daga kan kayan shaye2 naka ka taso ka shigomin falo ko? Shine har kake gayawa mahaifinka wannan maganar?"
Alhaji Bukar yace "ƙyaleshi, ina daf da maganinsa akan wannan mummunar ɗabi'a ta shaye2, dank yake zancen, ban agogona zan fita ina da ayyuka da yawa a Office "
Yasa hannu ya karɓi agogonsa, yai waje bayan fitarsa Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace " Fahad, meyasa ka gayawa mahaifinka wannan maganar haka? Kai lalacewar taka harta kai kayiaa mahaifinka haka? Me yayi maka? "
Yace " bakomai "
" Bakomai amma ka faɗa masa wannan maganar? Abunda kayi ya dace kenan?"
Ya girgiza kai alamar a'a
"to meyasa kayi, salon mutane suji suce ni nake saku a turbar banza, na ku Wulaƙanta mahaifinku?"
"Nifa Mummy bakomai, kema da kin san me yayi da baki faɗi wannan maganar ba, kawai dai Allah ya kyauta"
Ya mike a fusace ya baf falon, tabi bayansa da kallo, Iman tace "Mummy"
"Na'am"
"wai kuwa idonki biyu, jiya da Maman su Amal tazo gidan nan?"
"haba dai? Gidan nan tazo? Ai ban sani ba"
Iman tace "wallahi tazo, bayan ƙarfe goma se bala'i take tana neman Daddy"
"subhanallah, Allah yasa ba'a akan Ramlah tazo ba, saboda kin san halin ɗan uwanku sarai, ina kyautata zaton akwai alaƙar banza a tsakanin sa da Ramlah"
. "Mummy ya akayi kika sani?"
"last week na ganta ta fito daga sashinsa, na tambaye ta amma bata gayamin komai ba, sema baƙar magana da tayi min"
Iman tace "Umma kiyi ta haƙuri, Yaya Fahad se Addu'a gaba ɗaya zamansa a ƙasar waje ba abunda yasa masa se koyar mugayen halaye"
Hajiya Sarah tace "idan da zaman ƙasar waje dai to harda halinsa, meyasa shi Anwar be lalace ba se shi? Bani da abunyi se dai yi masa addu'a, baya jin faɗa baya jin rarrashi, babu wanda banyi ba, amma duk baya ɗauka"
"Mummy kiyi haƙuri, wataran se labari ze dena insha Allah"
"Mhmm Iman kenan, yaushene watarn ɗin? Mutum ya girma amma kullum ba hankali, Allah ya kyauta dai kawai".
Yanzu ma Bulama yana zaune a Office, kiran wayar Me Adda kawai yaje amma taƙi shiga, yai shiru can wayar ta fara ringing, cikin hanzari ya ɗauka ya zata me Adda ne, sedai yaga baƙuwar lambace, ya ɗaga yai sallama
"justice A dutse ne ke magana '
Bulama yace " ok nagane, ya kake ya aiki? "
" Alhamdilillah, dama na bugo in sanar makane da cewar tawagar lawyoyi da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ɗaukaka ƙarar shari'ar Yusuf da nayi, kuma ina kyautata zaton ƙarƙashin jagorancin shahararren lawayrn nan ɗan gwagwarmaya wato Barrister Adam A Adam, dan haka tun wuri kasan abunyi!!!
(Alhamdilillah masha Allah, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, da addu'oinku da na samu bisa rashin da akayi mana, nagode sosai Allah ya bar zumunci)
AMANA! AMANA! AMANACE!!!
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _
146_147
Cikin Bulama yai wata irin ƙara yace "A dutse garin yaya haka ta faru? Ina tarin kuɗin dana baka kaida lawyoyi, ya za'amin haka?"
'Aini kuɗin daka bani, nayi aikin daya dace da su, na rufe yaron nam amma doka ta bashi damar ɗaukaka ƙara, kuma ya ɗaukaka ni yanzu shawara ɗaya zan baka, karka sake a gane kana da hannu cikin wannan badaƙala dake faruwa, idan da hali ma ka halarci zaman kotu da za'ayi, karka bari wani ya gane da saka hannunka"
Bulama yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, ko dai ƙasar zan bari gaba ɗaya ne? '
" baza' a gane da saka hannunka ba, tunda manyan ƙasar nan da 'aya siyasa dama jam'ian tsaro suna tare da kai, karkaji komai I will give you the necessary support i can, ka kwantar da hankalinka fa"
Bulama kawai ya ajiye wayar, ya dafe kansa Fahad ne ya bankaɗo office ɗin kamar wanda aka jefo, Bulama ya ɗaga kai ya kalleshi, ya mayar ya sunkuyar, Fahad ya ƙaraso gabansa ya tsaya yace "wallahi Daddy ka bani kunya, ka zubar mana da mutunci a idom duniya, ka cucemu ka zaluncemu kuma se Allah ya sakawa Mummy"
Kasa vane inda maganganun Fahad ɗin suka dosa yayi, dan haka yace "kai me kame faɗane haka? Meye hakan?"
"dole ka tambayeni mana, dama Daddy kana alaƙar banza tsakaninka da Ramlah?"
"kai wace irin maganar banzace wannan? Ƙwayar taka bata sakeka a gidan ba shine ka biyoni har nan za kamin hauka? Wacece kuma Ramlah"
Cikin shouting Fahad yace "niba hauka nake ba, dagaske nake, akwai haramtacciyar alaƙa a tsakaninka da Fahad, kuma Asirinka ya tonu"
"wane banzan ne ya gaya maka wannan maganar banzar, mara tushe balle makama? Waye wannan waima wace Ramlah kake nufi ne?"
"Ramlah dai, 'yar gidan Hajiya Halima kumabita ta gayamin, da bakinta ta gayamin"
A fusace Bulama yace "zaka fitarmin daga Office ko sena ci ubanka na tattaka ka, dama akan tsini nake, saboda mahaukaci ne kai kamar ni, ni zan nemi wannan yarinyar? Inyi uwarme da ita? Fitarmin daga Office kobin saka security su casamin kai, kai ko kunya bakajiba, ina ubanka ka tunkareni da wannan maganar ba kai ba ma'ana, kai data gayamaka meyasa baka yi bincike a kai ba? Kawai ta gayamaka maganar banza ka hau kai ka yadda, fitarmin daga Office shashasha kawai "
Sekuma Jikin Fahad yai sanyi, dan ƙarya batawa Ramlab wahala, a ransa ya dinga fatan Allah yasa ƙarya takeyi, yana fita Bulama ya share gumi ya zauna yace
" Jimin tsinanniyar yarinya, ni zata kwaɓawa aiki haka? Waini garin yaya abubuwa suke ta cakuɗewa ne babu mafita sam a cikin lamuran, daga wannan se wancan? Kai baze yuwu ba da sake gaskiya"
Mahaifiyar Nurat fa babu sauƙi a lamarin nata, dan a kwanaki ukun nan ko yatsan ƙafarta bata motsa ba, yadda take a kwance a haka take, sedai a juya ta nan a juyata can, babu wani cigaba kuma a wannan kwanaki ukun still, lokaci lokaci jini na fita ta hancinta da bakinta.
Nurat ta ɗaga hankalinta akan san sanin Halinda mahaifiyarat ke ciki, amma se dai ace mata tana ƙarƙashin kulawa ta musamman ta likitoci, dan haka bazata ganta ba, Bata da aiki se kuka, danta fara zargin ko ta mutune ake ɓoye mata, Khalil neke aikin rarrashi kullum cikin rarrashinta yake akan ta kwantar da hankalinta, Mum ɗinta zata tashi zata warke da yardar Allah.
Sam bata son ganin mahaifinta yazo inda take, data ganshi se taji ranta babu daɗi, mussman idan ta tuna irin muguntarsa da zalumcinsa, da rashin afuwarsa.
Bulama mussman ya shirya ya tafi gidan Justice A dutse da yamma, lokacin yasan ya dawo daga gurin aiki.
Bulama yace "Nifa A dutse na kasa gane bayanin ka, ji naifa kace wai harda wannan barrister me shegen bakin tsiya za'ayi shari'ar nan, yanzu meye abunyi kenan?"
A dutse yace "eh to, kaga dai ko ana hauka kasan A Adam baze karɓi bribe ba, ni dai shawarata da kai shine karka yi wani Yunƙuri da zesa a ganoka, dan ba kaiba harni zamu shiga cikin matsala, saboda irin shari'ar da nayi, musamman idan aka gano na karɓi cin hanci daga hannuka, abun baze mana kyau ba"
Bulama ya dafe kai yace "yanzu shikenan, babu wata mafita kenan?"
"Karfa ka damu, ka kwantar da hankalinka ai su Barrister Sadik suna nan, za suyi iya yinsu akan shari'ar, suma jajirtaccune karka damu koka ɗaga hankalinka, babu abunda ze faru fa"
Bulama yace "to shikenan, dan Allah idan da wani information ka dinga sanar dani"
A Dutse yace "Insha Allah, kar kaji komai, ba zasu yi Nasara ba"
Fahad kuwa yana zuwa gida, ya ɗau waya ya kira Ramlah, yana kira ta ɗaga.
Aikuwa tana ɗagawa yace "munafukar banza da ta wofi, ashe ƙarya kikewa Mahaifina zaki haɗani faɗa da ubana, mara mutunci ƙaramar karuwa"
"Lallai Fahad, Bulama ya maida kai gaula, gashi ka ka raineni ka bani training a harkar karuwanci, amma kuma na shallake tunanink, dan na kai inda baka kaiba, to idan uban naka ya isa, ya kirani a waya a gabanka yace ƙaryane abunda na faɗa mana, ko kuma yaje a binciki lafiyarsa ko yazo har gida ya sameni yace ƙarya nayi mana, ai baka isa ka cuceni a banza ba, gidanku ma kun ƙara yawa masu ciwon, seku dage da shan magani tare "
Ta katse kiran wayar gaba ɗaya, Fahad ya jinjina kai tabbas tunda ta dage babu ko shakka mahaifinsa ya aikata abin da Ramlah ta faɗa, kuma da wuya idan ba'a sameshi da cita me karya garkuwar jiki ba, dan tunda ya iya neman Ramlah to yana biye biyen mata.
A hankali ya furta wayyo Allah Mummyna, ya nufi gida da sauri, yana zuwa ya tarar da mahaifiyarsu Hajiya Sarah ta shirya ta sha gayu zata fita, dama gata mace me iyayi da son kwalliya.
Ya ƙura mata ido, yana jin tausayinta a ransa,
"kai lafiya kuwa? Wannan kallon ƙurillar da kakemin fa? '
Fahad yai murmushin ƙarfin hali yace" kyau kikamin Mummy "
Tai murmushi tace "Allah ya shiryeka, sarkin zolaya"
Tai maganar tare da murmushi, ta shige motarta taja ta fita.
Jiki a sanyaye Fahad ya tafi part ɗinsa, yana zuwa ɗakinsa ya zube akan akan gadonsa yana rusa kuka kamar ransa ze fita "wayyo Allah na, kaicona da irin wannan rayuwar da nayi, a sanadina rayuwar mahaifiyata zata shiga garari, Daddy bakamana Adalci ba, wayyo Allah kaicona"
Jin hargowar kukan Fahad ne yasa Ramadan farkawa daga bacccin da yake yi, ya fito daga ɗakinsa ya shiga ɗakin Fahad, ya tarar da shi a zaune zaman dirshen yana ta gursheƙen kuka.
Jiki a sanyaye Ramadan yace "Fahad lafiya kuwa? Waye ya mutu?"
Fahad ya ɗago ya kalli Ramadan, ya goge hawayensa tare da daidaita nutsuwarsa yace "ba kowa"
"Amma kake wannan kukan? Idan ba mutuwa akayi ba meyafaru? Kukan kane fa ya tasheni daga bacci"
Fahad ya share hawayensa yace "Ramadan Daddy be mana adalci ba, wai ashe Daddy yana da mummunar alaƙa tsakaninsa da Ramlah"
Ramadan yace "wace Ramlan?"
"Ramlah dai, Ƙanwar Anwar"
Ramadan yace "subhanallah, wai kana nufin da Daddynmu take mummunar mu'amala"
Fahad yace "ba wai bane Ramadan, gaskiya ne ita ta gayamin da bakinta"
Ramadan yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, meyasa Daddy ze mana haka? Fahad abunda kake aikatawa ga 'ya' yan wasu ne muma yazo mana har cikin gida, kai kayi Daddy yayi alhalin muna da uwa muna da ƙanwa mace wannan abun dame yai kama?"
Fahad yace "wallahi Ramadan nayi nadama, nadamar da bata da amfani sam, a yanzu haka maganar da nake maka da ƙyar idan Daddy bashi da cuta me karya garkuwar jiki, saboda Ramlah ta tabattar min tana da ita"
A razane Ramadan ya kalli Fahad, "HiV kake nufi fa?"
Fahad ya jinina masa kai alamar eh.
"La'ilahaillalah Muhammadu rasulillah salallahu alaihi wassalam, Fahad HIV? Mummy kenan itama ta ɗauka a jikinsa? Subhanallah kun jawa wadda bata ji ba baya gani ba Fahad, ka ga illar zina da nake ta nuna maka ka kasa ganewa, Anwar ma ya nuna maka ka toshe kunnenka, gashi sanadin zina Daddy ya kwaso mana masifa, illar zina kenan idan kayi kai kaɗai illarta seta shafi al'umma da dama, Daddy be kyauta mana ba"
Fahad a ransa yace "Ramadan idan na gaya maka ni na sakawa Ramlah ciwo ta sakawa mahaifina ban san wani kallo zakamin ba"
Ramadan ya zauna yana share hawaye, tare da baƙincikin abunda mahaifinsu ya aikata, tausayin mahaifiyarsu ya mamayeshi, ya kalli ɗan uwansa yace "yanzu Fahad yaya zamuyi mu gayawa Mummy wannan maganar? Itama taje a binciki lafiyarta tunda wuri?"
Fahad yace "Ramadan abunda nake ta tunani kenan, na rasa abunyi gaba ɗaya, ban san ta inda zan ɓullowa wannan maganar ba, da ƙyar idan Mummy bata ɗauka ba, dan babu wanda yasan tun yaushe yake tare da ita, suke mu'amala"
Ramadan ya dafe kansa, ya dinga jujjuya kansa cike da ƙunar rai, ya fice jiki a sanyaye daga ɗakin Fahad, zuciyarsa na masa wani irin zugi da takaici, gami da tausayin mahaifiyarsu.
Shirye shirye sukayi nisa, akan ɗaukaka ƙarar Yusuf, manyan lawyoyi da masu kare haƙƙin ɗan Adam suka shiga lamarin, suna ta tattar hujjoji da shedu wanda suma zasu gabatar, a sake sharia'r Yusuf.
Yayinda Widad ke zaune a inda take ɓoye, inda Bulama yake ɓoye da ita, take communicating da mutane a waje, ta hanyar Sabuwa me aiki, taita aikenta da takadda ba tare da Sabuwa tasan ma'anar hakan ba, ga cikinta ya ɗan ɗaga sosai ya fito, dan sosai yake motsi yanzu, sedai duk lokacin da cikin ya shiga wani watan, se wata matsala ta taso, kodai yawan amai, ko ciwon kai, ko rashin son Abinci, haka Widad keta wahala tana ƙumbiya ƙumbiya da cikin a hijjabi kar wani ya gani, ga Bulama ya shafe kwanaki bezo ba, tunda yayi mata barazanar kama mahaifiyar Yusuf bata sake ganinsa ba.
Bulama kuma yaga canji a tattare da yaransa, abun da ya bashi mamaki be wuce yadda Ramadan ɗin dayake nutsatse yabi sahun Fahad ba, sam basa gaisheshi ko kallon inda yake basayi, balle ya saka ran wani abu na kirki ya shiga tsakaninsu dashi, suka dena shiga cikin gidan ma sam.
Bulama yace "Sarah, kin lura da yadda yaran nan suka canza gaba ɗaya a gidan nan? Na rasa me nayi musu, sam basa shiga harkata sun dena ko gaishesni, ko wani abun sukace nayi musune?"
Hajiya Sarah tace "ni dai bani da masaniya akan komai, ni Ramadan yafi bani mamaki ma, nasan ba haka yake ba, amma ban san yadda akayi shima ya ɗauki wannan mummunan halin ba, amma dan Allah kayi haƙuri, zanyi magana dasu insha Allah"
Bulama yace "shikenan, yakamata kam"
Daga nan ya kintsa ya fita, bayan fitarsa Hajiya Sarah taje har BQ ta samesu,
'Fahad, wani abu nake gani wanda na kasa gane kansa, meye dalikinku na dena kula mahaifinku ne?'
Fahad yace "babu komai"
"ƙarya kuke yi, akwai dalili idan ba haka ba, meye na wannan shareshin da kuke yi?"
Ramadan zeyi magana, Fahad ya girgiza masa kai yace "Mummy, kin san daddy da yawan faɗa, komai ya gani se yayi magana, se yayi mita da faɗa, shiyasa muke ɗan janyewa kawai"
Tace "Ai ba yanayi ne dan ya takuda muku ba, dole idan kukayi ba daidai ba a tsawatar muku, dan haka bana son wannan abun da kuke, a gyara dan ya fara zargin koni nake saku kuke masa haka"
Fahad yace "to insha Allah, zamu gyara"
Bayan fitarata, Ramadan yace "Fahad meyasa ka hana a gayamata?"
Fahad yace "Ramadan, ba'akowane irin yanayi ake gayawa mutum magana ba, ka bari zamu gayamata '
" Aikuwa bashi da amfani ko mun gaya mata, nasan aikin gama ya gama, ya riga ya cutar da ita "
Fahad yai shiru be kuma cewa komai ba.
Jini fa yaƙi tsayawa Amal, gaba ɗaya ta ɗashe tayi fari, ta kira doctor Hamisu a waya, ya rubuta mata magani, taje ta siya amma idan ta sha wuni take a kwance tana jiri, gaba ɗaya tayi wani iri, tambayar duniya taƙi gayawa Hajiya Halima abunda ke faruwa.
Tana kwance ta lallaɓa, zataje Asibitin da aka cire mata cikin ganin Likitan, se taga message nata shigowa wayarta, tana dubawa me zata gani? Kuɗinta na Account ake ta kwashewa, ta tashi a gigice sedai ba wani abu data iyayi an kwashe kuɗin nan tsaf, sakamakon wani website data shiga, akace ta saka BVN Number ɗinta, kuma ta saka akayi amfani da shi aka kwashe kuɗin nata.
Ta fito falo a gigice tana kuka, Hajiya Halima tace "ke lafiya kuwa?"
"Mummy kuɗina, an kwashemin kuɗina a Account"
Ramlah tace "ke kuwa kina me? Garin yaya?"
"Wani website ne, na shiga na saka BVN ina ga ta nan aka kwashemin kuiɗn, gashi nayi investing kusan million biyar a wani business shima an kwashe ma shiga uku"
Hajiya Halima tace "million goma kuma? A kna kika samu million goma?"
Sekuma ta dawo hayyacinta, ta shiag inda inda, cikin tsawa Hajiya Halima tace "magana nake miki, a ina kika samu million goma?"
Tai shiru tana tura baki, "zakiyi magana ne? Ko kuma sena tashi na tattaka ki?"
"Alhaji Haruna me yamin fyaɗe, ni kuma na sace masa kuɗi a account"
Ramlah ta buɗe baki, Hajiya Halima ta miƙe tsaye "ya miki fyaɗe kamar yaya?"
Nan Amal ya kwashe komai ta gayamata, har jinin da take ta zubarwa tunda aka cire cikin.
Nan da nan jikin Hajiya Halima ya ɗau rawa, ta kasa magana ma gaba ɗaya, ta dinga bin Amal da Ramlah da kallo.
Tunda mutane suka ji batun Yusuf zeyi appeal, suke ta ɗokin sake zaman ganin shari'ar nan, ranar da za'a fara sauraren ƙarar kotu ta cika maƙil, musamman jin labarin a ƙarƙashin jagorancin gogaggaun Matasan lawyoyi dodannin Azzalumai za'ayi shari'ar, kotu tayi maƙil assurance ɗin da Bulama ya samu a gurin Justice A dutse, da kuma su Barrister Sadik yasa ya je kotun da ƙwarin gwiwarsa, sedai duk da haka bashi da wani karsashi, saboda Alƙalin koyun bashi da wasa, balle ka tunkareshi da wata maganar cin hanci Justice Muhammad Mustapha.
Shikansa Yusuf yayi mamakin ganin, manyan lawyoyin da sukazo dan tsaya masa, da yawa a radio yake jin sunayen su, sekuma a dandalin sada zumunta, amma yau gashi gasu wai zasu tsaya masa, a iya saninsa ba kowa ke iya ɗaukarsu shari'a ba, saboda lawyoyine masu tsadar gasme, kuma basa tsayawa shari'ar Azzalumai, to ta yaya akai shi suke son tsaya masa? Bayan ta bayyana ƙarara shi me laifine?.
Barrister Adam A Adam ya fito gaban alƙali ya gabatar da kansa a gaban alƙali, sannan ya kalli kotu yace "sunana Barrister Adam A Adam, ni lawyer ne me zaman kansa, ina daga cikin tawagar lawyoyin da zasu tsayawa wanda ake ƙara, don bashi kariya, a tare dani akwai hujjoji da shedu da zasu tabattarwa da alƙali cewar wanda ake tuhuma, be aijata ɗaya daga laifukan da ake zarginsa dasu ba, idan kotu ta bani dama ina buƙatar ganin Sada, wanda yace Yusuf ya kai masa mota ya siya "
Sada ya fito yana rarraba ido, dan kallo ɗaya zakayiwa Barrister Adam A Adam kasan babu wasa a tare da shi, sannan abune mawuyaci a kada shi a shari'a, saboda gogaggen lawyer ne, kuma ɗan gwagwarmaya.
Barrister ya kalli Sada yace " ko zaka iya gayawa kotu sunanka, da abunda ka sani akan wanda ake zargi?"
Sada ya maimaita abunda ya faɗa a kotun baya, Barrister Adam yace "wow, ko zaka iya gayawa kotu wame irin motoci Yusuf ke kai maka gyara daga gidan Daula?"
Sada yace "motocine dai, kamar su jeep su Honda da sauransu"
Barrister yace "wace irin mota ce Yusuf ya kai maka ta gidan Daula ka siya?"
"Prado ce" ya bada amsa
"wow, kasan irin wannan motocin se gidan attajirai irinsu daula kam, amma ya akayi ka siyi motar da kuɗinta ya haura naira million talatin a matsayinka na bakanike?"
"Amm ai, ai, ai dama bani nake...
Objection ya me shari'a cewar Barrister Sadik, " Barrister Adam yana ƙoƙarin jefa tsoro da razani a zuciyar sheda, kuma ai shi arziki sirrine, dan mutum yana ƙaramar sana'a shikenan baze mallaki dukiya ba? "
Justice Mustapha yace "tambayoyin da Barrister Adam yakewa Sheda, zam basu kauce ba dan haka wannan ƙorafin be karɓu ba, cigaba da aikinka"
"Nagode ya mai girma me shari'a" cewar Adam A Adam.
"Sada, waye megidanka da ya sai motar?"
"Amm, wa.. Wani oganane ubangidanane"
"Amma meyasa kuka sai motar, bayan kun san Yusuf bashi da arzikin daze mallaki wannan motar?"
"Amm, ai, ai dama bece min satota yayi ba, kawai yace in siya nace masa bana siyan mota, na haɗashi da me siya na zata ko bashi motar Alhaji Nasir yayi, kasamcewarsa mutum me kyauta"
Barrister Adam yace "hakane, ina neman alfarma da kotu ta bani dama dan gabatar da wata ƙwaƙwarar sheda da zata tabattar da abunda Sada ya faɗa ba gaskiya bane"
Aka bawa Adam dama, aka shigo da Nura, aka tsayar da Nura a gurin Tsayuwa, Barrister Adam yace "ko zaka gayawa kotu sunanka"
"Sunana Nura Idris"
"Kasan wannan" aka nuna masa Yusuf, Nura ya jinjina kai alamar eh, "wannan fa?" aka nuna masa Sada, Nura yace "A'a"
"toko zaka iya shedawa Kotu, abun da ka sani game da abunda ake tuhumar Yusuf dashi?"
Nura yace "kamar yadda na faɗa sunana Nura, kuma nine direban Alhaji Nasir Daula, kafin zuwan Yusuf ya fifita Yusuf sama da kowane ma'aikaci a gidan, na shekara a ƙalla tara ina aiki a gidansa, a haƙiƙanin gaskiya idan mota ta lalace a gidan Alhaji Nasir, Har gida ake zuwa a gyara ta, kuma Yusuf baya kai gyaran mota iya abunda nasan yanayi, shine tuƙa 'yaf gidan Alhaji Nasir Daula, sekuma shikansa Alhaj Daulan wasu lokutan, kuma idan mota ta lalace ma ba' a fiye barinta a gidan ba, gyara ta ake a bayar da ita, dan haka gaskiya ni ban san wannan bawan Allah ba, kuma a gidan Alhaji Nasir Daula, babu irin motocin daya faɗa, manyan motoci na alfarma su ake hawa a gidan Alhaji Nasir"
Barrister Adam yace "Malam Nura muna godiya, ban sani ba ko Sada yana da abun faɗa?"
Sada ya soma inda inda, yana kallon inda Su Bulama suke, akace ko su Barrister Sadik suna da abun faɗa? Sukace babu.
Barrister Adam yace "sheda ta gaba da zan gabatarwa da kotu itace, shedar da aka bawa Yusuf a hukumance, daga hukumar 'yan sanda, na cewar yaje gidan Alhaji Daula yai bincike sannan ya bawa' yarsa kariya a ɓoye, a matsayinsa na ɗan sandan farin kaya, wanda hukumar ta musanta hakan, Amma akwai takadda da aka samu, wadda da saka hannun hukumar da stamp ɗinta, wanda babu wanda ya isa ya samu wannan stamp ɗin, idan har ba daga ofishin manyan cikin jam'ian tsaron ba " Barrister Adam ya fito da takadda aka karɓa ka miƙawa alƙali, shi dai Yusuf yana tsaye, yana tunanin waye ya masa wannan ƙoƙarin haka?"
"dan haka muna neman jin cikakken bayani daga bakin 'yan sanda, idan har bata hannunsu wannan takadda ta fito ba, ta yaya akayi stamp ɗinsu ya fito a takaddar, idan kuma da saninsu yaje yin aikin, meyasa suka musanta sune suka bashi aikin?"
Nan fa sa'insa ta kaure tsakanin lawyoyin, su Barrister Sadik suna da'awar ai ƙarewa Wadda abun ya faru akanta da kanta ta bada sheda, seda alƙali ya buga guduma, yace ya ɗage shari'ar zuwa sati biyu gaba.
AMANA! AMAA!! AMANACE!!!
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _
150_151
Zare ido Bulama yayi jin an ambace shi haka, abun da be taɓa kawowa ba, yaga dai duk shedun da aka gabatar babu wanda yai wata magana da ta shafe shi, amma yaji an ambaci sunansa.
Ya tsaya yana zazzare ido, ya miƙe cikin fargaba ya fito ya tsaya a inda ake tsayawa, Barrister Khalil yace
"Alhaji Bukar Bulama, duniya tasan kaine babban abokin mahaifin Widad, wato Alhaji Nasir Daula, ko zaka iya gayamana abunda kasani game da ɓatanta?"
Bulama yace "Eh to, kafin ɓatan nata dai, kamar yadda ka faɗa ni ubane a gurinta, dukda rashin yaddarta ga mutane akwai kyakkyawar alaƙa tsakani na da ita, Daula da 'yarsa sun bada amanna sosai ga wannan bawan Allah, sun yadda dashi sosai.
Har nake ja masa kunne akan yayi taka tsan tsan, da wannan yaron saboda be kamata ace yana shishigemasa haka ba, saboda duniya babu gaskiya, wata rana ina bacci cikin dare, sega wayar Daula ina ɗagawa a gigice yake gayamin ai Widad direbanta ya gudu da ita, a daren na tafi gidan gonarsa, yake gayamin ya kira Yusuf akan ze kai Widad Abuja, yana son ya kwana a nan gidan gonar dan suyi tafiyar Asuba suje da wuri, amma cikin dare Yusuf ya sace ta ya gudu da ita"
Barrister Khalil yace "duk ina ma'aikatan gidan, da har ya gudu da ita a mota babu wanda ya sani?"
"Nima ban saniba, tunda seda abun ya faru sannan ya kirani"
Khalil yace "Kasancewar ka Uba ga wannan yarinya, bayan an gano inda take, an karɓota daga hannun masu garkuwa, an kaita Asibiti an gama mata dukkanin wasu gwaje gwaje da yakamata, tana hannunka a zaune kenan?"
"Eh tana gurina"
Bulama ya bada amsa, Khalil yace "tana gurinka, amma ba'a gidanka da kake zaune da iyalinka ba?"
Bulama yace "Eh, tana wani gidan daban sakamakon rashin jituwa dake tsakaninta da ɗana Fahad, da kuma ta samu hutu"
"Amma me yakawo rashin jituwa tsakaninsu, dukda cewar kusan uba kake a gurinsu duka"?
Bulama ya rasa yadda zeyi da tambayoyin Khalil, yace "Eh, nima ban san dalili ba, amma basa jituwa '
Khalil yace "bekamata ace baka sani ba kuwa, sannan duk wanda yasan Alhaji Bukar Bulama a baya bashi da wannan tabon ɗinki a fuskarsa haka? Ko ya akayi ya samu wannan tabon? "
Barrister Saminu yai suka akan abunda Khalil yake yi, amma Justice Mustapha yaƙi saurarrasa, yace Khalil ya cigaba.
Bulama yace "'yan dabane suka yankeni a fuskar"
"meya haɗaka da' yan daba kana babban mutum har suka maka wannan yankan a fuska haka?"
Bulama yace 'kuɗi suka nemi in basu ban bayar ba, shine suka yankeni a fuska da cinya ta "
" ka kai rahoton faruwar hakan ga hukuma? "
' A'a"
Khalil yace "saboda me?"
Bulama kawai yai shiru, yama rasa meze cewa Khalil, saboda yadda ya titsiyeshi da tambayoyi, tabbas da tun a shari'ar farko irin wannan shari' ar akayiwa Yusuf, da baze je prison ba, Umma dake zaune na kallon shari'ar banda tasbihi da hamdala ba abunda take yi a ranta.
Barrister Khalil yace "bayan kai akwai wanda Yasan inda gidan daka ajiye Widad Nasir Daula yake?"
Yace "Eh"
Khalil yace "wakenan?"
"'ya' yana duk sun sani"
'ka bawa' yan jarida damar ganawa da ita? Ko kuma jam'ian tsaro sun san inda take? , ko kuma meyasa iya kaida 'ya' yanka ne suka san inda take, alhalin ana kan shari'a, dole za'a so bincike se anji wani abun ta bakin ta, ka kaita ka ɓoye ta, ka tirsasata ta bada shedar ƙarya a kotu, kai yunƙurin cutar da ita, tai maka rauni da wuƙa, Bulama kaike da alhakin daukkanin abunda ke faruwa a gidan Alhaji Nasir daula, saboda babu wanda yasan sirrinsa sama da kai"
"Objection yame shari'a, wani irin abu Barrister Khalil yakeyi haka? Yana ƙoƙarin liƙa laifi ga wanda be jiba be gani ba, ba tare da wata hujja ko sheda ba, yana ta ƙoƙarin ƙirƙirar labari da hanyar da ze jingina laifi akan wanda bashi da laifi" cewar barrister Sadik.
Alƙaki yace "Barrister Khalil, ko kana da shedar abunda kake faɗa?"
"Ina da ita yame girma me shari'a"
Khalil ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko wata waya, yazo gaban Yusuf ya nuna masa wayar yace "ko za ka iya tuna wannan wayar?".
Yusuf ya karɓa ya jujjuya wayar yace "eh na gane wayar"
"wayar waye?"
Yusuf yace "Wayar Nurat ce, 'yar gidan Alhaji Musa"
Khalil yace "meyasa baka gabatar da wannan wayar a matsayin shedarka ba lokacin da ake maka sharia' ar farko?"
Yusuf yace "saboda an hanani duk wata dama da zan kare kaina"
Khalil yace "ina son ka karɓi wannan wayar, kayiwa kotu bayanin abunda ke ciki"
Yusuf shi gaba ɗaya ya manta ma da batun wayar Nurat, ko ya akayi Khalil ya gano da wani abu a wayar harya ksrɓota oho, saboda Yusuf besan akwai alaƙa a tsakanin Nurat da Khalil ba.
Yusuf ya riƙe wayar yace
"Kamar yadda nake gudanar da bincike na a ɓoye, a gidan Alhaji Nasir Daula, katsam watarana nayi dare a gidan na fito zan tafi gida wasu mutane suka tareni, sunamin kashedi akan lallai suna daga cikin masu bibiyar Alhaji Nasir da 'yarsa, kuma nima zasu dinga bibiyata akan lallai sena samo musu wani abu a hannun Widad, har mukayi sa' insa dasu suka dakeni, still bayan wani lokaci suka sake biyoni, nan ma suka dakeni sedai na ɗau lambar motar tasu, naje na kai Office muka bibiyi lambar, a nan na gano lambar motar gidan Alhaji Musa ce, wato mahaifin Nurat.
sannan na taɓa kai Widad wani hotel, na jirata a waje, ta shiga ta fito tana kuka, bayan mun koma gida, na maida ita naji lallai ina son sanin me taje yi a Hotel ɗin nan, bayan na koma na kasa gane komai, sena nemi manager nace ina buƙatar ya bani record na wanda suka kama ɗaki a hotel ɗinsu, mun kai ruwa rana kafin ya bani, dan seda na biya shi, aka bani Jerin record na wanda suka kama ɗaki na kusan watanni huɗu, a nan naga Alhaji Bulama yafi kowa kama ɗaki, dan yakan kama na wata guda, kuma da na ƙara bincike sena gano suna yawan zama dashi Alhaji Bulama, da Alhaji Musa, da Alhaji Munir da kuma matar Alhaji Nasir Daula, yanayin yadda Widad ke matuƙar tsoron mutane da kuma nima yadda akace za'a dinga bibiyata, yasa naji cewar lallai ya kamata inyiwa binciken da nake kyakkyawan ɓoyo, bayan na system ɗina na wayata, da wanda nake haɗa report a takadda, dan haka na yanke shawarar zuwa gidan Alhaji Musa, Na samu Nurat, na samu bayanai daga bakinta na yadda rashin jituwar mahaifinta da Alhaji Nasir ya samo Asali.
nai amfani da wannan damar, na karɓi wayarta na buɗe wani website nai hiding ɗinsa, na tura mata duk wani sakamakon binciken da nayi, sannan nai linking ɗinsa da wayata duka lokacin dana tura wani abu website ɗin ze shiga wayarta, kuma ze zauna akan wayata, nasan babu wanda zeyi tunanin da wani abu a wayarta, ko da na rasa na gurina"
Aiba Khalil ba hatta jama'ar kotun, sun jinjinawa Yusuf wannan basira tasa, Khalil yace "Amma ya akayi kai garkuwa da 'yar Alhaji Nasir Daula?"
Yusuf yace "banyi garkuwa da itaba, Alhaji Nasir ya nemi da inje gidan gonarsa in kwana, zan kai Widad Abuja dan ganin wani likitan Ƙwaƙwalwa, cikin dare aka turo masa saƙo a wayarsa, ina kwance ina bacci yazo tasoni nida Widad, ya nunamin saƙon yace maza maza in ɗau Widad mu bar gidan, na tsaya ina tambayarsa ina zamuje, yace maza maza in bar gidan da Widad, saboda saƙon da aka tura masa ana barazana ne ga kodai ya bada abunda akeso, ko kuma a hallaka 'yarsa, nace masa mu kira' yan sanda amma yace aa', in kula da Widad, na ɗauketa muka fita ba tare da nasan inda zamuba, munyi tafiya me nisa ga dare, kawai aka zagaye motarmu, da Widad kawai suka so su ɗauka, ta riƙeni tana kuka na hana su tafi da ita, shune suka haɗa dani, kwananmu biyar a hannunsu, Saleh ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan gonar Alhaji Nasir, yaje ya kuɓutar damu, an harbi Widad a hannu ya kaimu Asibiti, aka cire mata bullet, sannan ya bamu mafaka a wannan ƙauyen, ya cemin idan har muka dawo za'a hallaka Widad dani kaina, dan haka mu zauna zuwa lokacin da komai ze lafa, amma bani na sace ta ba"
Barrister Saminu ya mike yace "meyasa baku shigar da ƙara ga hukumar 'yan sanda ba? Ka cigaba da zama da ita a inda babu wanda yasani tsawon lokaci?"
Yusuf zeyi magana Barrister Khalil yace "zan gabatarwa da kotu, wata shedar wadda take nuna wanda ake zargi bashi da laifi a zaman kotu na gaba"
Nan kotu ta hargitse da Hayaniya, kowa yana tofa albarkacin bakinsa, Alƙali ya buga gudumarsa, akayi shiru, yai rubuce rubuce sannan yace
Duba da yadda lawyoyi suka gabatar da shedu da hujjoji, wannan kotu me albarka zata ɗage cigaban wannan sharia'r zuwa nan da sati biyu masu zuwa, dan yin zama na ƙarshe da yanke hukuncin daya dace akan wannan shari'a, sannan kotu tana umarni da hukumar 'yan sanda su binciki Alhaji Bulama da tawagarsa"
Kotu ta ɗau hargowa da sowa, 'yan sanda suka tafi da Yusuf gidan yari, Umma ta kalli Suleiman tace " Suleiman ya haka? Naga za' a maida shi"
Suleiman yace "ki kwantar da hankalinki, kin san shari'a komai a hankali a binsa ki kwantar da hankalinki"
Suleiman yaita kwantar mata da hankali, yana bata baki.
Hajiya Halima ganin ba'a kama da ita ba, yasa ta silale tai gida, zuciyarta cike da fargaba da kuma tsoro, tana tunanin meye mafitarta ta ƙarshe? Tasan tunda Bulama yaje hannu itama tata ta ƙare, sedai tana zuwa gidan ta tarar da gate ɗin gidan hanhai a buɗe, ga motar 'yansanda, ga mutane sun cika gidan, kamar ta juya ta gudu, amma ta fasa ta ƙarasa, tana zuwa me zata gani, an rufe mutum da zani alamar ya mutu, Ramlah se uban kuka take, ga Amal a sume a gefe ana ta mata fifita, jiki na rawa ta ƙarasa gaban gawar, tasa hannu ta yaye zanin, Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!!!
Gawar Anwar ce ɗanta, gawar se zubar da jini take, idonsa a rufe kamar me bacci, kamar kace tashi ya tashi a nutsensa yake, amma ya mutu.
Ta ɗora hannu a ka tana kurma ihu "Wayyo Allah na shiga uku ni Halima, Bulama ka cuceni ka tarwatsa rayuwata, Allah ya isa tsakanina da kai Bulama, Bulama seda kasa aka kashemin Anwar? Nayi dana sanin saninka, da farko ka rabani da gidan uban Anwar, na Auri Shu'aibu shima ka kashemin Auren, ka haɗa kai da Shu'aibu kuka kashe matarsa ya sakeni dan Daula ya aureni, duk biyayyar da na maka, amma ka kashemin ɗana Me ƙaunata da gayamin gaskiya, wayyo Allah Anwar ɗina, wayyo Anwar ka tashi dan Allah, na shiga uku "
Tana wannan ihun, tana maganganun nan ana mata video, ita dai Ramlah kasa cewa komai tayi, se bin mahaifiyarsu da ido, ga Amal wadda babu tabaccin tana da rai itama, dan abun yazo mata akan gaɓa, dama ta gama galabaita babu jini a jikinta, kuma ga wannan mutuwar ta Anwar, ƙarseh wannan kururwar da Hajiya Halima keyi, se rufeta akayi a ɗaki akayiwa Anwar sutura.
Khalil kuwa yana ta rawar jiki yaje ya bawa Nurat labarin yadda shari'a ta kaya, akwai alamun nasara akan shari'ar Yusuf sedai yana zuwa gida ya tarar da fuskaokinsu wani iri, Nurat a zube a ƙasa ana ta fama numfashinta ya tsaya.
Khalil yace "lafiya kuwa?"
"Allah yayiwa mahaifiyar Nurat rasuwa, yanzun nan an tafi ɗakko gawarta daga Asibiti" Anty Saddiƙa tai maganar tana kuka.
Khalil yace "la'ilahaillalah Muhammadu rasulillah salallahu alaihi wassalam, Antyna ta rasu kenan?wallahi Musane ya kasheta, shine ya kasheta"
Yai maganar yana zubar da hawaye.
Haka itama akayi mata sutura aka sallaceta, aka kaita makwancinta na gaskiya, Nurat kam tasha kuka kamar ranta ze fita, gaba ɗaya ta birkice an kasa gane kanta ma gaba ɗaya, se da aka samo likita yai mata alluarar bacci dan ta samu relief.
Amal kuwa har aka kai Anwar bata dawo hayyacinta ba, gawar Anwar ya tara mutane sosai kasancewarsa mutum ne na mutane, ga sauƙin kai da girmama jama'a.
Fahad ya kaɗu da jin labarin an kama mahaifinsa, da kuma harƙallar da suka ƙulla da shi da Hajiya Halima, suka dinga siyar da dukiyarsa ba bisa ƙa'ida ba, ga mutuwar Anwar data dake shi, ya kaɗu matuƙa da jin Anwar ya mutu, ya lallaɓa komtsan sa ya ɗau mota ya gudu.
Haka Bulama ya kasance a hannun 'yan sanda shima, Aka kama Alhaji Musa, shi laifuka biyuma aka kama shi dasu, ga laifin hankaɗo matarsa daga bene, gana wanda suka aikata da Bulama.
Tunda Amal ta farka ta farka ba a daidai ba, tunda ta buɗe idonta bata magana kwata kwata, sedai taita bin mutane da kallo, kamar bata sansu ba, Hajiya Halima kuwa kamar wadda ta shekara a daji, tai wujiga wujiga ko tayi shiru idan aka jima se surutai, taita tonawa kansu Asiri ita da su Bulama, itama ƙarshe ana cikin makoki 'yan sanda suka zo suka yi gaba da ita.
Nurat tana cikin tashin hankali, na rashin mahaifiyarta, ga kama mahaifinta anyi da wannan manya manyan laifuka haka, dukda tarin abunda yai mata na laifuka, amma ya haifeta, gaba ɗaya ta rame tai wani iri, ga labarin mutuwar Anwar ya risketa, mutuwar ta girgiza ta ƙwarai, ba zata manta halacci da kara irin na Anwar ba, Anwar mutum ne nagari me haƙuri da nagarta gaske.
Bulama a hannun Hukumar 'yasanda ɓangaren SWAT aka danƙasu, domin tuhumarsu, dama kuwa masu fushi da fushin wani, dan haka ba'a ragawa su Bulama ba sam, kamar yadda suke sawa a azabtar da wasu, haka suma suka shiga hannu aka dinga azabtar dasu.
Ana wannan halin, a haka sati biyu ta cika, aka koma kotu ranar da aka koma kotu kallo ɗaya zakayiwa Khalil kasan yana cikin alhini sosai.
Kamar kullum an cika kotun nan maƙil, haka aka shigo dasu Bulama, wujiga wujiga.
Khalil ya fito gaban kotu, ya gabatar da shedarsa da suke dashi akan Bulama.
Babban abunda ya bawa Yusuf mamaki, be wuce yadda yaga Sunusi ya shigo ba, ya buɗe baki yana kallon Sunusi.
Sunusi yazo ya tsaya, Khalil ya masa umarni ya gabatar da kansa, Sunusi ya gabatar da kansa sannan yace "tabbas wanda ake zargi bashi da laifi, Saleh ɗan uwanane, kuma akwai Bala Yayansa, Saleh ya haɗa kai da Alhaji Bulama da niyyar ya ɗau fansa akan Alhaji Daula na sakawa da 'yarsa tayi aka tsare ɗanuwansa, dan tana zargin da hannunsa a kashe mahaifinta, sedai Bulama ya gaza cika Alƙawarin da yaiwa Saleh ma ze saka a saki ɗan uwansa, su ɗau fansa akan Daula, ganin haka yasa ya koma taimakon' yar gidan Daula, ya kuɓitar dasu daga hannun masu garkuwar, sannan ya kaisu ƙauyenmu gurin mahaaifina, saboda muddin suka dawo za'a kashe yarinyar, kuma shima Saleh ze shiga matsala, lokacin da sukaje ƙauyen bata yadda da kowa se Yusuf, ga jikinta duk rauni se anyi jinyarta, shi kuma yace ita ba muharramarsa bace, babu yadda zeyi jinyarta wannan dalilin ne yasa Saleh ya shige gaba aka ɗaura musu Aure bisa amincewarta, shedar da aka saka ya bayar a kotu shedar ƙarya ce, tursasashi akayi kuma aka masa rauni a cikinsa saboda duka, akace za'a kasheshi in be bada shedar ba, shine aka kawo shi kotu ya faɗi wannan shedar, sannan lokacin da suke ƙauye ya gayamin idan har aka kama Yusuf za'a kasheshi dashi da Widad baki ɗaya, tunda Daula ma ba'asan inda yake ba, nace masa ya gayawa 'yan sanda, amma yace a"a akwai haɗaka me ƙarfin gaske tsakanin Alhaji Bulama da Hukumomin tsaro, dan haka yana da ɗaurin gindi, idan ya faɗa tamkar ya sake jefasu a garari ne"
Nan kotu ta ɗau salallami, Barrister Khalil yace " Alhaji Bukar Bulama, kaine mutum na farko da Alhaji Nasir ya kira bayan an sace 'yarsa, ya akayi wanda suke turo masa saƙo suka san inda suka tafi idan ba kai ka gaya musu ba? "
Bulama yace " ni.. Ni bani bane ba, ya za' ayi in saka a sace yarinyar da takemin kallon uba? "
Khalil yace " Akwai sheda, ina son kotu ta bani dama, in gabatar da sheda ta ta ƙarshe wanda zata tabattar da Alhaji Bulama shike da alhakin dukkan wannan abubuwan da suke faruwa, yasa akayi garkuwa da 'yar Amininsa, kuma yake bibiyar yadda ze mallake dukiyar Aminin nasa"
Aka bashi dama, wa Bulama ze gani? Su me Adda aka jero a layi, akaje aka tsaidasu, nan da nan Bulama ya sadaƙar yasan ƙarshensa yazo.
Aka tsaida me Adda, Khalil yace "gayawa kotu sunanka"
"Sunana Hashimu, amma ana cemin me Adda"
"meka sani game da garkuwar da akayi da 'yar Nasir Daula?"
Me Adda ya kalli Bulama yace "eh, Alhaji Musane da farko ubangidana, dashi da Alhaji Musa da Haruna da Munir suke sa kamu aiki, nine na dinga bibiyar Yusuf nida yarana, Bulama ne ya kiramu a waya, yace mana ga inda zamuje, motar gidan Daula zata zo da Widad a ciki da direbanta, mu kama Widad, muka je kamata amma shi Yusuf yai ƙoƙarin hanamu, yace mu haɗa dashi, kwananmu biyar muna basu wahala, akan ta faɗi inda dukiyar nan take, amma taƙi, shine yace mu kasheta, dan har mun harbeta ma a hannu, kuma mun musu horon Yunwa da duka, bayan yace a kashesu muna zuwa muka tarar sun gudu, tsawon watanni ba'a gansu ba, seya gano Saleh yana mufuntarsa, shine yace mu kamo Saleh, bayan mun kamk Saleh ne shima muka dinga dukansa muna bashi wahala, daga baya ya bawa 'yansanda shi yace a tuhumeshi ya faɗi inda ya ɓoyesu, bayan wannan kuma yace muje gidansu Yusuf da daddre mu ɗakko masa babarsa, ashe akwai' yan sanda a kewaye da gidan bamu sani ba, muna zuwa suka kama mu "
Khalil yace " tsawon wane lokaci ka ɗauka kana masa aiki? "
Me Adda yace " gaskiya an daɗe, muna masa aiki yana biyan mu, yana bamu kuɗi sosai, a haƙiƙanin gaskiya mune mukayi garkuwa dasu, 'yan sanda sun tambayemu kuma mun faɗa musu gaskiya"
Barrister Khalil yace "Ya me girma me shari'a, duba da tarin hujjoji da shedu da kuma sakamakon' yan sanda, da muka gabatarwa wannan kotu, muna neman wannan kotu me albarka ta wanke wanda ake ƙara daga wannan tuhuma da 'ake masa
Justice Mustapha Yace " duba ga yadda shari'a ta kasance, da tarin hujjoji da shedu da aka gabatar, wannan kotu da dogon Nazari da duba ga kudin shari'a wannan kotu ta wanke wanda ake zargi, wato Yusuf Bashir Maitama, sannan wannan kotu me albarka tayi umarni da hukumar 'yan sanda su kama Alhaji Bukar Bulama, da muƙarabbansa don zurafafa bincike a sake gurfanar dasu, sannan hukumar' yan sanda zata biya wanda ake ƙara Wato Yusuf Naira million goma, sakamakon ɓata masa suna, da tauye masa haƙƙinsa a matsayinsa na ɗan ƙasa dukda dama da kundin tsarin mulki ya bashi, sannan kotu tana umarni a maida shi bakin aikin sa "
Yusuf yana jin haka ya fashe da Kuka, ya zube a gurin yana sujudu shukur ga ubangiji subhanahu wata'ala, kuka sosai kamar wani ƙaramin yaro, Umma ta taho da gudu, ta rungume shi itama tana zubar da hawaye, tawagar 'yan sanda suka rako Yusuf wajen kotu, yayin da akayi Ram da Bulama da Alhaji Haruna dake gurin, sannan aka bazama nemo sauran.
Yusuf na fitowa jama'a suka baibaiyeshi, sedai ya kasa magana se hawaye, Suleiman ya rungume Yusuf yana faɗin "barka da Arziki abokin aiki, barka da Arziki Yusuf"
Yusuf ya rungume Sulaiman shima, sedai ba bakin magana se hawaye dake fita daga idonsa, tawagar lawyoyin nan suka zo gaban Yusuf suka dinga miƙa masa hannu suna gaisawa, Cikin kuka Yusuf yake faɗin "Nagode, Nagode, Nagode" yana maganar yana kuka dan yama rasa meze ce musu.
Umma ta rirriƙe Yusuf, kamar za'a sake ƙwace mata shi, itama kuka kawai take yi.
Khalil yace "yau na sauke babban nauyin dana ɗauka, na Alƙawari ga Nurat, da nace zanyi iyayina inga ka kuɓuta"
Yusuf yace "Nurat kuma?"
Khalil ya jinjina kai, yace "Eh Nurat, sannan Yakamata a wuce dashi Asibiti, a duba lafiyarsa.
Bulama kuwa aka fito da shi, da Alhaji Haruna, dasu Musa a ƙasƙance, mutane nata tsine musu, 'yan jarida suka sa kasu a gaba, amma sukaƙi magana sam, suka duƙufar da kai kamar munafukai.
Bisa rakiyar' yan sanda, aka tafi da Yusuf Asibiti.
Yusuf kuwa ya galabaita, dan admitting ɗinsa akayi, yana buƙatar agajin gaggawa, saboda tarin raunuka dake jikinsa, gashi ya kasa dena kukan da yake yi, Suleiman cewa yake "Yusuf, kukan nan ya isa haka, ka godewa Allah, dan shine ya dubi halin da kake ciki ya fitar mana da kai, amma mun shiga cikin damuwa muma lokacin da ka shiga mawuyacin hali"
Cikin kuka Yusuf yace "Yallaɓai, yanzu kenan harda Abbas aka haɗa kai dan cutar dani? Yace be san da an bani aikin nan ba? Abbas fa? Aminina Abbas fa?"
Suleiman yace "koma dai menene, ba gashi kai ka kuɓuta ba, kuma nasan shima dole kotu ta neme shi ai"
Wayar Suleiman ta fara ringing, ya ɗakkota a aljihunsa ya saka a kunnensa, "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, ubangiji Allah yai musu rahama, Allah ya jiƙan su"
Umma tace "Sulaiman waye ya mutu?"
Suleiman yace "Ina Barrister Khalil? Lawyern daya dinga magana daga ƙarshe"
Umma tace "eh nagane meya sameshi?"
"Ai ɗan uwan Nurat ne, kuma itace ta tsaya kai da fata akan ganin an kuɓutar da Yusuf, Mahaifiyarta ce ta rasu, kuma mahaifintane ya turo uwar daga kan bene, dan ta masa magana ya kulle Nurat ɗin, ashe duk saboda shari'ar kane akan ta dage ayi maka adalci, ya gano ta san sirrinsa shine yai dalilin rasuwar mahaifiyarta"
Umma ta dafe ƙirji tace "subhanallah" , Yusuf ya girgiza kai hawaye na bin idonsa yace
"Allah sarki Nurat, Allah ya jiƙan Mummynki, nayi silar shigarki matsala kema Allah sarki Nurat"
(INA JIRAN TUKUCINA NA WANNAN OAGE ƊIN, TUNDA AN SAKAR MUKU YUSUF 😎😂😂)
Ayshercool
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _
148_149
Gaba ɗaya Bulama bega alamar Nasara a tattare da wannan shari'ar ba, wata zuciyar ta dinga rayamasa kawai yaje ya kashe Widad ya huta, wani sashin ya gargaɗeshi akan aikata hakan.
Haka ya koma gida jikinsa a sanyaye, babu alamar Nasara sam, yana zuwa ya tarar da Hajiya Sarah da Ramadan suna hira a falo, sedai da yayi sallama maimakon Ramadan ya amsa sema tsaki daya ja, suka kalleshi gaba ɗaya tace "Ramadan, are you out of your sense? Mahaifin naka kakewa haka? Ina yabo ka salla zaka kasa alwala?"
Nan da nan Ramadan ya shiga hawaye, "Mummy nayi dana sanin kasamcewarsa mahaifina wallahi, baki san halin mutumin nan ba mugune azzalumi macuci"
Buɗe baki sukayi suna kallon Ramadan, Yace "Mummy ina abun kunya ina abunda Daddy ya aikata? Saboda tsabar abun kunya wai 'yar' yar uwarsa, wadda take kamar a gareshi yake bi, Mummy Ramlah fa kuma ta tabattarwa da Fahad tana ɗauke da cuta me garkuwar jiki"
Gab ɗaya suka kalleshi a razane, Bulama yace "waye ya gaya maka wannan maganar banzar?"
"Karka ƙara kiran ta da maganar banza, dan ba ƙarya akayi maka ba, ko basu sani ba dama yau nayi niyyar zuwa in fayyace musu komai, ɗanka Fahad shine ya shafamin wannan ciwon, ni kuma nai alwashin shafa maka, dan haka ka bimciki lafiyarka, daga kai har matarka, daga yau kaida ɗanka seku shiga taitayinku ku kiyayi yaran mutane"
Kuka Hajiya Sarah ke ƙoƙarin yi, amma ta kasa ta dinga binsu da kallo, yayinda Ramadan ya daskare dan mamaki, Bulama yace "wallahi ƙarya kikemin, ni ban aikata haka ba, wallahi ƙaryane"
Ramlah tace "wannan kuma ya rage naka Bulama, nayi hakane dama dan tarwatsa kan iyalinka kamar yadda a sanadinka duk mun ɗaiɗaice babu wanda be abun kunya ba, gara a raba ai, ace kowama yayi"
Ta kalli Hajiya Sarah tace "Hajiya Sarah kece abar tausayi, Kasancewar kin zauna da baƙin kumurci tsayin shekaru baki san waye ba, ki gaggauta bincika lafiyarki, idan baki kamu ba shikenan, idan kuma kin kamu se ince Allah ya bamu lafiya baki ɗaya"
Ta juya ta bar musu falonsj, ta fics tana fita kuwa Hajiya Sarah ta yanke jiki ta faɗi cike da ɗimuwa Ramadan da Bulama sukayi kanta, sedai Ramadan yace "karka sake ka taɓamin uwa, Kuma insha Allah zaka ga sakamakonka tun a nan duniya, macuci mara imani kawai"
Ramadan ya shiga kiciniyar ɗagota, Fahad kuwa yana ta bayan ɗakin, yana laɓe yaji komai ya zame ƙasa ya zauna yana kuka, tabbas Ramlah ta rusa musu farinciki gaba ɗaya, farinciki na har Abada makuwa, ya shiga tunanin me zeyi wanda ze fanshe wannan cin mutunci da tayi musu?.
Hajiya Halima ma gidan Alhaji Haruna ta tafi, bayan jin irin katoɓarar da yayi mata akan Amal, taje ta sameshi shida Salma da uwargidansa a falo, da gani wata matsalar ce na family issues suke solving, taje musu afujajan kamar wadda tayi gobara a ka, tana zuwa ba sallama ba gaisuwa bakomai ta haushi da bala'i.
"Wallahi Haruna ka bani mamaki, nayi mamakin abunda ka aikatamin, ashe fyaɗe kayiwa Amal? Daga aikota ta kawo maka takadda dan baƙin zalunci, wallahi baka isa ba zakaga matakin da zan ɗauka akanka"
Uwargidansa ta bisu da ido, dan ita bata da wani baki sosai, Salma kuwa tace "ba shakka, biri yayi kama da mutum, shiyasa yarinyar nan ta dinga bibiyar ka? Tana turon saƙonni da ɓoyayyiyar lamba ashe dagaske ne abuika aikata? Ko kunya ba kaji ba gaka da yara mata, amma kayiwa wata fyaɗe?"
Cikin inda inda Alhaji Haruna yace "Ni, Ni wallahi ƙarya takemin ita ta kawo kanta"
Salma tace "kai ko kunya bakaji ba kake cewa ifa ga kawo maka kanta? Allah wadaran halinka nayi dana sanin Aurenk, Wallahi da in Auenka gara ace Yusuf ɗina na Aura dukda rashin asalinsa, dan nasan baze taɓa wannan akuyancin ba"
Hajiya Halima tace "Haruna ka bani kunya, ka bani mamaki ka cutar min da yarinya, gaba ɗaya kun kassaramin rayuwata data yarana, wancan ya ɓata kunce a kasheshi, wannan kai ka lalata ta, waccan kuma Bulama ya lalata ta ɗansa ma yayi, sun saka mata HIV, na rasa dame ma zan kiraku, kun cuceni kai da Bulama dukda kasancewarsa ɗan uwana Allah ya isa wallahi "
Tai maganar tana kuka, Alhaji Haruna ya saki tumbi yana kallonta, duk damfara da satar da 'yarta tayi masa bata gani ba se shi zata kalli abunda yayi mata.
Ya kalleta sama da ƙasa yace "Malama ki fita ki barmin gidana, kije can ku ƙarata, ita bata gayamiki abunda tayimin ba, se wanda nai mata, kije kiyi duk abunda zakiyi, kinzo kin ɗagamin hankali a cikin iyalina"
Hajiya Sarah ta kalleshi tace "ni kakewa haka? Ni kake kora daga gidanka? Kamin wannan mummunan abu sannan ka Kalleni kace in bar maka gida?"
fice daga gidan, zuciyarta na ƙuna gaba ɗaya yaranta sun lalace gaba ɗaya.
Salma taje gabansa ta tsaya tace "wallahi banga amfanin zama da fasiƙin mutum irinka ba, dan haka ka sakeni malam"
Alhaji Haruna yace "Ai Aurena dake har abada tunda iyayenki kwaɗayayyune, sunga kuɗi sun auramin ke wallahi bazan sakeki ba dan ina sonki"
"karka sake ka zagarmin iyaye, kuma wallahi seka sakeni tunda ba tare aka haifemu ba, macuci me abun kunya kawai"
Ya tureta yai wucewarsa yace "kanki ake ji, wadda taga zata zauna shikenan, wadda bzata iya ba ta ƙara gaba, amma saki kam babu shi"
Cikin kuka Salma tace "wallahi ƙarya kake seka sakeni, wallahi bazan cigaba da zama sa fasiƙi ba"
Uwargidan kam bata iya magana, sedai kuka dayake irin ta da ɗin nan ce, tun auren ƙuruciya gashi babu wani isashen ilimi a tare da ita.
Lamarin mahaifiyar Nurat fa sam babu sauƙi a lamarin, dan sati guda kenan babu wani cigaba, gaba ɗaya Nurat ta ɗaga hankalinta akan halinda mahaifiyarta ke ciki, jin mahaifintane yai sanadiyar faɗowar mahaifiyarta daga bene yasa taji gaba ɗaya ya fita daga ranta, ko san ganinsa ma batayi, gashi idan yazo Asibiti dubata 'yan uwanta suyi ta haɗe masa rai, ko sabgarsa basa shiga, Nurat kam an sallameta tuni amma taƙi barin Asibitin, idan tana buƙatar wani abuma gidan su Khalil take tafiya, gidan yayar mahaifiyarata kenan.
Ramadan kam Asibiti ya kai mahaifiyarsu, ya kira Iman dake makaranta suka zauna a gurinta dan kula da ita, dan ta samu shock ne a wannan lokacin.
Bulama kuwa bayan tafiyar Ramlah ya bita har gida, yana zuwa lokacin Hajiya Halima ta dawo da baƙincikin gidan Alhaji Haruna, yazo yana wani muzurai yace "Ina Ramlah take?"
Hajiya Halima ta kalleshi tace 'ban sani na, azzalumi ma cuci burinka ya cika, gaba ɗaya yaran sun watse Bukar saboda muguntarka da rashin imani"
Bukar yace "saboda son zuciyarki dai, da son Abun duniya"
"Ni kake gayawa haka?"
"Na gayamiki ɗin, ai ba ƙarya nayi miki ba, mugun son Abun duniyarkine ya janyo miki da kwaɗayi"
"Lallai Bulama ka cika butulu azzalumi, to wallahi zan taka bakin faranti komai ya watse"
"kar Allah yasa ki fasa takawar, kije kiyi duk abunda zakiyi, ai idan ta tashi watsewa tare zata watse mana, kuma ki sani idona idon Ramlah sena saka an kashe ta"
"ka daɗe baka sa an kasheta ba, kayi maza karka fasa"
Ramlah ta fito daga sashensu tana tauna cingan, kallo ɗaya za kamata kasan 'yar wisi ce, ta kalli Bulama tace "kai ka isa kasa a kasheni, ai base kunyi barazanar taka bakim faranti ba, kuji da abunda ke tunakaroku, Asirinku na daf da tonuwa a kotu, a nan yakamata ku maida kai mussman ma kai, ba wai zaka kasheni ba, dan ni na diha na kasheka da ranka tuni"
Ta ƙarasa maganar tana ɗura ruwan roba a cikinta, ta juya ta wuce dining dan cin Abinci, Hajiya Halima ji take tamkar tayi hauka, komai ya dagule mata, ta rasa meke mata daɗi.
Bulama ya fita da sacacciyar gwiwa jiki ba ƙwari, yanzu duk wannan barazanar da kwarinin dayake ana tsoronsa duk babu.
Tunda Ramadan ya ɗau mahaifiyarsa daga gidan basu sake komawa ba, har Allah yasa ta farfaɗo, aka ɗibi jininta aka gwada amma ba'aga ƙwayar cutar ba, akace bayan watanni uku zasu dawo sake yi, se kuka take tana tunanin wans irin lamarine wannan, ɗa ya nemi mace ta bashi kanta, kuma ta koma tabi mahaifinsa saboda Taɓarɓarewar ƙarshen zamani.
Daga Asibiti kai tsaye, Adamawa Ramadan ya tafi da Mummyn, saboda can ne ainihin garinsu.
Bulama yaje Asibiti aka ɗibi jininsa, da niyyar yasan a wani mataki yake, yana da cutar ko babu? Amma yakasa tsayawa a gaya masa sakamakon saboda fargaba ya gudu.
Haka abubuwa suka cigaba da damalmalewa azzalumai, basu fargaba lokacin komawa kotu yayi, ga kawunansu a rarrabe, kowa yana kallon kowa a banza, ga yadda suka dinga zaluntar junansu.
Yau kuma Barrister Hafiz ne ya fito ya gabatar da kansa, tunda Bulama ya ga Barrister Hafiz cikinsa ya ɗuri ruwa ya zuba ido yaga meze faru.
Barrister Hafiz ya fito ya gabatar da kansa, yace "Sunana Barrister Hafiz, lawyer me zaman kansa, ina ɗaya daga cikin lawyoyi gidan Alhaji Nasir Daula, kuma ina ɗaya daga cikin lawyoyin da zasu bawa wanda ake ƙara kariya, kimanin shekaru goma sha biyu baya, tun bayan da ayyana cewar kaso bakwai na dukiyarsa akwai me ita, yasa aka dinga bibiyarsa da 'yarsa akan lallai a karɓi wannan dukiya, har kawo ga kashe matarsa da akayi, wanda ba' a ƙarabi ta kan case ɗinba tsawon shekaru, a tare dani akwai shedu da hujjoji da zasu tabattarwa da kotu wanda ake ƙara bashi da hannu gurin yin garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula, ko kuma shi Daula kansa "
Ya ƙarasa inda Yusuf yake tsaye, ya kalli Yusuf yace " Malam Yusuf, ko zaka iya gayamana yadda akayi ka fara aiki a gidan Alhaji Nasir Daula? "
Yusuf ya ɗanyi shiru yana kallon Barrister Hafiz, Barrister Hafiz ya jinjina masa kai alamar ƙwarin gwiwa.
Yusuf yace "Abokin aikina Abbas, shine yazo ya sameni da maganar ga aikin da ake so inyi, shugabanmu yace a bani umarnin yin wannan bincike, da farko naƙi amsawa, daga baya naga tunda aikinane bazan iya cewa a'a ba, tunda ni na ɗau alƙawarin aiki, Abbas shine ya kaini gidan Alhaji Nasir Daula da kansa, yana zuwar musu gidan a matsayin Sani me yankan farce, kuma yana mutunci dame gadin gidan "
" waye me gadin gidan? " cewar Barrister Hafiz.
Yusuf yace " Isa ne"
"muje kotu na saurarenka"
"Bayan an kaini gurin 'yar gidan Daula, tace min sena saka hannu akan wata takadda kafin in fara aiki da ita, na karɓa na saka, tace min saka hannun da nayi tamkar na saka hannu a contract ɗin mutuwana ne, da farko naji tsoro se ban nuna ba saboda tunda aiki najeyi, bazan janye ba saboda abunda ta faɗa "
Barrister Hafiz ya jinjina kai yace " ko Isa megadi yana gurin nan? "
Isa megadi ya miƙe, aka masa umarni daya fito, ai kuwa ya fito yazo ya tsaya.
Barrister ya kalle shi yace " me zaki iya cewa akan abunda Yusuf ya faɗa "
Isa megadi yace" tabbas lokacin da ake neman direban da ze dinga jan 'yar Alhaji Daula a mota, Sani me yankan farce, wanda se da aka fara shari'a naji sunansa Abbas kuma ɗan sandane, shine ya kawo Yusuf gidan nan, kuma daya kawo shi me gidan yana matuƙar ƙaunarsa saboda haƙurinsa, kuma duk rashin yaddarta ita uwarɗakin nasa tana yadda dashi sosai"
Barrister Hafiz yace "Isa megadi zaka iya komawa"
Kafin Barrister Hafiz ya kuma gabatar da sheda, Barrister Sadik yace yana da tambayoyin da zewa Yusuf, Alƙali ya bashi dama, yaje gaban Yusuf ya tsaya yace "Kamar yadda ka bayyanawa kotu cewa, 'yar gidan Nasir Daula tace maka aiki da ita tamkar signing ne akan contract ɗin mutuwarka, meyasa ka amince kayi aiki da ita, ko duk cikin shirinka ne na saceta"?
"Objection ya megirma me shari'a, Barrister yana ƙoƙarin saka wanda ake zargi yayi confessing ne ko kuma tambayarsa yake?"
Alƙali ya buga guduma yace "Order, Barrister Sadik cigaba da tambayoyinka"
Yusuf yace "Ni ɗan sanda ne, kuma dama rayuwar ɗan sanda na tsakanin rayuwa da mutuwane dan kare rayuwa da dukiyar wasu, shiyasa ban razana na janye ba, saboda aiki nake"
Barrister Sadik yace "kace bincike kaje yi gidan Alhaji Nasir da kuma bawa 'yarsa kariya, wane irin bincike?"
"Kamar yadda Barrister ya faɗa ɗazu, ana kai musu farmaki, saboda dukiyar da yace batasa bace, an bani aikinne dan gano suwaye da kuma bawa Widad kariya"
Barrister Sadik yaga idan ya cigaba da tambayoyin nan, tabbas Yusuf ze ɓallo ruwa, dan haka ya koma ya zauna.
Barrister Khalil ne ya shigo cikin kotun da hanzari, fuskarsa babu annuri idonsa jajawur, ya tsaya yace "ina me neman afuwar kotu, na gaza halartar kotu da wuri, hakan ya biyo bayan neman wata sheda da bata zo hannunmu akan lokaci ba, sunana Barrister Ibrahim Khalil, lawyer me zaman kansa ina cikin tawagar lawyoyi dake bawa wanda ake tuhuma kariya, idan kotu ta bani dama, zan fara gabatar da shedu da hujjoji, amma kafin nan ina son yiwa wanda ake ƙara tambayoyi"
Aka bawa Khalil dama, Khalil yaje gaban Yusuf ya kalleshi, dukda Yusuf a wahale yake amma hakan be hana Khalil ganin kyau da Yusuf yake dashi ba, yace "Malam Yusuf, kamar yadda kayi iƙrarin bincike kaje yi gidan Alhaji Nasir Daula, kotu zata so ta san wane sakamako ka samu na binciken? Sannan ina kudin binciken da kayi?"
Yusuf ya ɗaga ido yai ido huɗu da Hajiya Halima, ya kalli inda Bulama ke zaune, ya ɗauke kai yace "An karɓi kundin binciken, lokacin da aka kamoni ina hannun 'yan sanda, sannan a bincikema na farko, akwai yunƙuri da akayi na sace' yar gidan Daula, a gidan wani tsohon ɗan majalisa da taje taya 'yarsa murnar zagayowar haihuwarta"
Khalil yace "ko kana da sheda?"
Yusuf ya girgiza kai, alamar a' a.
Khalil yace "cigaba ina jinka"
"Matar Alhaji Nasir, tana da wani ɓoyayyen nufi akan Widad, suna bata maganin gusar da hankali, sannan suna da wani nufi akan dukiyar Alhaji Nasir, dan akwai babbar 'yarta data taɓa cemin in bata password ɗin Banki na' yar Alhaji Nasir"
"ya akayi kasan password ɗin nata kai?"
"Saboda tana aikena, Na kanyi kwanaki da ATM ɗinta a hannuna"
Barrister Saminu ya mike yace "Objections sir, wannan tambayoyin da Barrister kewa wanda ake ƙara, basu da tushe balle makama kame kame ne kawai sukeyi, dan haka ina Roƙon wannan kotu me Alfarma, da tayi watsi da wannan magana da wanda ake ƙara yake faɗa"
Cikin zafi Khalil yace "ina da tabacci da ƙwararan shedu akan abunda wanda ake ƙara gaskiya yake faɗa, idan kotu ta bani dama ina son ganin Hajiya Halima, matar Alhaji Nasir Daula, don gabatar mata da wasu tambayoyi"
Aka bashi dama, Hajiya Halima ta fito, gaba ɗaya ta tsoste tsufanta ya fito jikinta se rawa take yi, bayan ta tsaya Barrister Khalil ya nemi ta gabatar da kanta, ta gabatar da kanta a gaban kotu, Khalil yaje gabanta ya ɗakko wata takadda a aljihunsa, ya ajiye a gabanta yace "kin san rubutun waye wannan?"
Jikinta ne ya hau rawa, wasiƙar da Anwar ya bari ce, ta kalli Khalil a razane ta girgiza kai tace "A'a ban sani ba"
Yace "waye Anwar a gurinki? '
Tace " ɗana ne"
"kina nufin bashi ya rubuta wannan takaddar ba?"
Ta jinjina kai alamar eh, Khalil ya juya ya kira Murtalah, Murtalah ya fito ya tsaya, Khalil yace "kotu na buƙatar ka gabatar da kanka, sannan ka faɗi abunda ka sani"
Murtalah yace "Sunana Murtalah, kuma ɗaya daga masu aiki a gidan Alhaji Nasir Daula, wata ɗaya zuwa biyu baya, naje ɗakin Anwar zan gyara masa, na ga ya bar wannan takaddar, na ɗauka na karanta na kaiwa mahaifiyarsa ba tare da na nuna mata na karanta ba, bayan na kai mata da yamma 'yarta Amal tazo zata fita tana ga sauri, bata sani ba seta yarda takaddar, nikuma na tsinta, kamar yadda ya rubuta a takaddar, tun daga wannan lokacin ba' a ƙara ganin inda yake ba ya bar gidan gaba ɗaya "
Barrister Khalil yace "zaka iya komawa ka zauna"
Yaje ya dudduba cikin takaddunsa ya ɗakko wani littafi, ya dawo gaban Hajiya Halima ya miƙa mata littafin yace "wannan kamar littafin ɗanki me Anwar, na Jami'a ko?"
Ta karɓa ta duba, ta jinjina kai, Khalil yace "ki dubamin ko akwai bambanci tsakanin rubutun cikin wannan littafin dana takaddar gabanki?"
Take ƙafafunta suka hau rawa, taji tana numfashi sama sama, ta tsaya tana rarraba ido.
Khalil ya ɗau takaddar da littafin da takaddar, ya miƙawa Alƙali.
Alƙali ya karɓi takadda da littafi, Khalil ya kalli Hajiya Halima yace " wane irin rashin gaskiya ne haka ɗanki yake tuhumarki dashi? Wanda yasa har ya bar gida?"
Hajiya Halima tace
"Ni babu wani rashin gaskiya da nake aikatawa fa, kawai maganace tsakaninsa da 'yar uwarsa akan abunda take aikatawa, da kuma zargin nafi fifita' yan uwansa akansa"
Barrister Khalil ya jinjina kai yace "shikenan zamu gani"
Akace taje ta zauna, ta koma inda ta taso tana godewa Allah.
Barrister Khalil yace "ina neman wannan kotu ta bani dama, domin yiwa Babban Amini ga Alhaji Nasir wasu tambayoyi wato Alhaji Bukar Bulama!!!"
Ayshercool
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
152_153
Suleiman yace "Yusuf ka kwantar da hankalinka, dama Allah ya ƙaddara hakan seta faru, ta wannan dalili naka, mudai fatanmu Allah ya baka lafiya ka warware"
Yusuf yace "Ameen, nagode sosai Yallaɓai"
Suleiman yace "bakomai Yusuf, Allah dai ya baka lafiya ya ƙara wanke mana kai daga sharrin maƙiya"
Yusuf yace "Ameen ya Allah, to su lawyoyin da suka tsayamin sun sanni ne? Meyasa suka tsaya min, kuma meyasa basu taimakeni da farko ba?"
"Yusuf, lokacin da ake maka shari'a ta farko, su Bulama sunyi mamaya ga wannan shari'a fiye da tunaninka, ta ƙarƙashin ƙasa aka bi aka dinga samo shedun nan fa, a yadda Khalil yake gayamin, Nurat ce ta takurashi akan lallai ya tsaya a fitar da kai, saboda tasan wasu daga abubuwan da mahaifinta ke aikatawa, to yazo dai ya kawomin ziyara, muka tattauna na gaya masa abunda nasani daga abunda Saleh yake zuwa yana gayamin, yayi duk binciken su daya dace na tallafa masa da abunda nasani, to su dai sauran lawyoyin bansan yadda akai ya samosu ba, nidai ya sanarmin zasu ɗaukaka ƙara, shikenan se ranar shari'a nima na gansu "
Yusuf ya jinjina kai yace " Alhamdilillah, Allah nagode maka "
Suleiman yace" An gode Allah kam, ka kwantar da hankalinka, komai ze wuce insha Allah "
Umma tace " dan Allah ka kwantar da hankalinka, sannan kai shiru da wannan surutun ka samu isashen bacci "
Yusuf yace " to Umma "
Har Yusuf yayi shiru, ya kuma cewa " Yallaɓai ya Widad fa? A wani hali take ciki? "
Umma tace " Meka ce? "
Yusuf yace " cewa nayi a wani hali Widad take ciki? "
A fusace Umma tace " waya san mata, baka da zuciya Yusuf, yarinyar tazo ta bada sheda akanka, bayan a dalilinta ka shiga halin da kake ciki, amma kana wani maganar tana ina, in sake jin kayi maganarta sena saɓa maka"
Yusuf yai shiru, Amma yana tunanin shiya kuɓuta, to matarsa fa?.
Widad kuwa tuni 'yan sanda sukaje suka ɗakko ta a gidan nan bayan an kama Bulama yaji matsa ya faɗi inda take, tana zaune a ɗakin da take, taji ana guje guje, ba inda ta iya motsawa daga inda take zaune, Sega' yan sanda sun shigo, suka ɗakko ta suka tafi da ita Asibiti, tayi baƙi duk ta kukkumbura, haka suka ɗakkota a gakabaice ga babu isashen Abinci da kulawa.
'yan sanda suka kama har wannan Sabuwar, wadda take kuka da Widad a gidan.
Da aka kaita Asibiti ma, a emergency aka ajiye ta, saboda ciwon zuciya da jininta daya hau fiye da kima, ga dislocation data samu a hannunta saboda ball da Bulama yake da ita.
Likitoci sun fara tunanin ko a cire mata cikin, saboda kar yai sanadiyyar rasa ranta, Amma Widad a wahal ce tace "likita, dan Allah ka barmin cikina, gara in mutu dashi a jikina, dan Allah a bawa Yoseef haƙuri, na bada sheda ne dan in ceci rayuwarsa, amma nasan ya bani gudunmuwa, dan Allah ya yafemin, nagode Allah tunda ya kuɓuta"
Haka taita surutai, seda aka mata Allura sannan bacci ya ɗauketa, ta ɗau tsawon lokaci tana wannan baccin, kafin ta farka sedai ga mamakin su, bayan ta farko jininta ya sauka ba kamar da ba, suna yi suna monitoring ɗin yanayin jikinta, da kuma probability na surviving ɗinta da wannan cikin.
Sedai babu kowa a gurin Widad, musamman mace wadda zata dinga kula da ita, Nurses ne suke mata komai, nan ta sake kukan rashin dangi, da tana da dangi da an samu me kula da ita.
Ramlah gaba ɗaya itama a zabure take, mutuwar Anwar ta da keta, bata taɓa zaton dagaske Bulama yasaka a kashe Anwar ba, gashi 'yan sanda suna kama mahaifiyarsu, ga Amal ita bame hankali ba ita ba mara hankali ba, haka suke zaune gaba ɗaya rayuwa ta juya musu baya.
Seda Yusuf ya kwan tara a Asibiti, ana masa screening daban daban dan tabattar da ingancin lafiyarsa, Yusuf ya ɗan murmure sakamakon Abinci da kulawa da yake samu, kullum se an dafo Abinci daga gidan Suleiman an kawowa Yusuf, ya ɗan farfaɗo sedai uwar rama da yayi.
Aka sallameshi daga Asibiti, tare da magunguna zuwa gida, tunda suka koma gida 'yan jaje ke sintirin zuwa gidan nan, wasu dan suyi jaje wasu dan suyi kallo, sedai Yusuf ko tsakar gida baya fitowa saboda baya san Hayaniya.
Abokan Aikinsa suka yi tawaga guda sukazo duba Yusuf, seda wasu suka yi kukan farinciki, dukda miskilancin Yusuf, amma akwai kirki da girmama mutane, duk wanda ya ganshi se yayi mamakin ramar da yayi.
Ɓangare guda kuma, hankalin Yusuf yana kan ta ina zega Widad, a wani hali take ciki?
Seda Widad tai sati biyu a Asibiti, cikin ikon Allah ta murmure, jininta ya sauka amma an kafa mata sharaɗin idan ta tashi haihuwa ta taho Asibiti, saboda tana cikin hatsari karta ce zata haihu a gida, dama tunda aka kai Widad Asibitin kullum 'yan sanda cikin patrol suke a Asibitin, har zuwa sallamarta da akayi.
Da aka sallameta ma headquarter na' yan sanda aka tafi da ita, domin amsa wasu tambayoyi da za'a mata, gaba ɗaya saboda yadda akayi shari'ar Yusuf da yadda abubuwa suka wakana, an sauya manyan shugabbani dake riƙe da manyan muƙamai a hukumar, duk an canza wanda Bulama ya siye da wasu.
Widad ta faɗi yadda komai ya faru, tun daga kan kisan mahaifiyarta, da irin Abubuwan da Bulama ya dingayi, ba tare da yasan tasan shine Bukar ba, har sace ta da akayi tare da Yusuf, ta nuna musu inda aka harbeta a hannu, da yadda Yusuf ya dinga wahala da ita, ƙarshe seda aka kamo doctor Hamisu wanda yake mata allurar hauka, da sauran wanda suke da hannu a miyagun laifukan ta'addanci da aka dinga aikatawa Daula da iyslinsa, Shima Saleh can aka samoshi a wani Asibitin gwamnati babu kulawa, saboda garin dukan daya dinga sha ya samu rauni a hantarsa.
Widad bata da gurin wanda zata ta zauna, Akace a kaita gidan gwamnati fa zauna, kafin Allah ya bayyana mahaifinta, tace ita gidan gonar nan zata je ta zauna, akace baze yuwu ta zauna ita kaɗai ba, Amma Widad ta dage ita babu gidan wanda zata ta zauna, aka ajiye jami'an tsaro a layi da kuma cikin gidan dan tsaron lafiyarta aka barta ta zauna ɗi .
Widad Ta dinga tunanin ya akayi Yusuf be nemeta ba, dukda yayi free yanzu, sedai tayi tunani babu lallai Yusuf ya sake karɓarta, bayan ta gaza taimakonsa a lokacin da yake buƙatar hakan.
Gaba ɗaya gidan ya canza, babu manyan dawakan nan nata, da wasu daga dabbobinta duk babu su, haka manyan motocin dake gidan duk babu, an kwakwance wasu abubuwan masu mahimmanci daga gidan, taga gidan ya mata faɗi, babu Daddy babu kowa a tare da ita yanzu.
Ta zauna tai shiru tana tunani, ta fito harabar gidan tana zagaye, ma'aikatan se zuwa suke suna mata fadanci, suna mata jaje tare da barka da Arziki, ta kira wani daga cikin ma'aikatan gidan Imrana, yazo gabanta ya durƙusa tace "naga gaba ɗaya gidan nan ya canza, ina wasu daga cikin dabbobina da motocin duk da suke cikin gidan nan?"
Imrana yace "ranki ya daɗe, Hajiya ce take turowa a ɗiba a fita dasu, kuma bamu da ta cewa"
Widad ta jinjina kai tace "shikenan jeka"
Haka ta dinga zaga gidan, tana tuna abubuwa da suke shuɗe, da abubuwan da suka faru daren da akayi garkuwa dasu, ta shiga ɗakin data kwanta a ranar, tana dube dube, can ta hango wayarta guda ɗaya a ƙasan gado, Da daddy yazo ya azalzaleta ta tashi ta fito wayar ta faɗa ƙasan gado, ta ɗau waya ɗaya ta fita, waya ɗayan da yanzu bata san a inda take ba, ta ɗakko wayar ta ganta a kashe, ta jona a jikin caji aikuwa ta kama.
Ta jona wayar ta koma ta zauna, a hankali tace "Yoseef am missing you, i have no one, help me to relay on you, ka yafeni ka dawo gare ni mana"
Ta yanke shawarar komawa tayi zamanta ita kaɗai, ta cigaba da Addu'a Allah ya bayyana mata mahaifinta, kota rage wata damuwar, amma da kunya a gareta ta tinkari Yusuf a yanzu.
Gaba ɗaya damuwa da kaɗaici suka baibayeta, ta fito ta ɗau mota zata fita ɗaya daga cikin 'yan sandan dame gadinta yazo yace "ranki ya daɗe, ina zakije ne haka?"
"Fita zanyi" ta bashi amsa
Yace "ranki ya daɗe har yanzu kina ƙarƙashin kulawar' yan sanda ne, idan kika fita ke kaɗai hakan ze iya zame mana laifi a sama"
Widad tace "shikenan, dan kuna gadina bazan fita ba? Da can wake kula dani idan ba Allah ba? Ina kuna garin nan da saninku aka siye wasu daga cikinku akaci zarafin mijina, aka sacemu babu wanda yai yunƙurin kawo mana ɗauki, se yanzu zaka zo kana gayamin zancen banza? Ban fidda ran a sake dawowa a haɗa baki daku a cuceni ba"
Ɗan sandan yace " Allah ya temakeki, kiyi haƙuri kin san duk yadda kaso ga kamanta gaskiya, se an baka umarnin aimata wani abun daga sama kafin kayi, amma dan Allah kiyi haƙuri karki fita ke kaɗai, dan Allah ki rufamana Asiri, za'a iya ladabatar damu idan mukayi sakaci wani abun ya same ki, har yanzu kina ƙarƙashin kulawar jami'an tsaro ne"
Ta jefa masa key ɗin mota tace "kaini gidanmu, inda muke zaune"
Ɗan sandan ya ɗauki key ɗin, yana mamakin wannan izza ta Widad, ta shiga bayan mota ta zauna, ta tuna idan Yusuf ze fita da ita, a gaban mota take zama, suna tafe wataran tana zazzaga masa masifa, ko kuma yana wani abun da ze bata haushi suyita faɗa.
Ta lumshe idonta tana jin yadda sonsa ke ƙara ratsa ilahirin gaɓoɓin jikinta, se yanzu ta yadda so babbar cutane, bata taɓa tunanin haka yake ba, bata zaci tayi sabo da Yusuf haka ba, tana jin ya zama wani ɓangare na rayuwarta gaba ɗaya, kobe nemeta ba doke ita ta nemeshi.
Suna zuwa ƙofar gidan, tace ya tsaya yayi horn, yai horn aikuwa Isa yaeƙo yaga waye, kawai ya hangi Widad a bayan motar, aikuwa ya gigice ya tafi da gudu ze buɗe Gate, ya dawo ya kuma komawa ya rasa mema zeyi.
Widad ta sauke gkass ɗin motarta tai masa nuni da yazo, ya taho da sauri jiki na ɓari yazo ya durƙusa yana faɗin "Allah ya temakeki, Allah ya tsare ki sharrin maƙiya" kawai ya fashe da kuka ya kasa cigaba da maganar.
Widad tace "Lafiya kuwa? Me yasaka kuka kuma?"
"ranki ya daɗe dole inyi kuka, tunda kika tafi babu ke babu Yallaɓai, gaba ɗaya gidan annurinsa ya ɗauke, muka shiga mummunan yanayi, katsam kuma se gashi kun dawo amma ba'a yadda akeso ba, a wani yanayi na daban abubuwa sun faru marasa daɗi ranki ya daɗe Alhamdilillah tunda dai kin dawo kuma kin kuɓuta "
Widad tace " Isa dukda mugayen halayena da kuke faɗa, dama zaku iya shiga damuwa dan na bar gida? "
Isa yace " A'a a'aha, ai ranki ya daɗe Hausawa sukace kada Allah ya kawo ranar yabo, amma wallahi zamanki a gidan nan ba ƙaramin haske bane, mungode Allah"
Widad tace "shikenan, kiramin su Nura da Murtalah"
Yace "ranki ya daɗe, bazaki shiga gidan bane?"
Tace "Eh, kiramin su"
Isa ya zabura da sauri hadda gudu, ya shiga gidan yana ƙwalawa Su Nura kira.
Aikuwa gaba ɗaya suka rankayo suka biyo shi, suna zuwa suka ga Widad bakinsu yaƙi rufuwa, suka zube a gabanta suna surutai kowa da abunda yake faɗa.
Haka nan Widad taji ƙwalla ta rasa ta mecece? Tai murmushi tace "Nagode Allah, tunda duk kun tsallake tarko da sharri na Bulama, naji daɗi Sosai da gudunmuwar da kuka bayar a kotu, gurin kuɓutar da mijina, nagode muku sosai Allah yasaka da alkhairi"
Murtalah yace "wai dagaske ranki ya daɗe Yusuf mijinki ne?"
Abun mamaki wai yau Widad na hira da maa'ikatan gidansu, matar da ko murmushinta ba'a gani idan ba na mugunta ba, ko tana gaban mahaifinta ba.
Widad tace "Eh mijina ne, ko akwai magana ne?"
Murtalah yace "A'a, abunne da mamaki sosai ranki ya daɗe"
Widad tace "IKone na Allah kawai, naji daɗi Sosai da kuka temaka da sheda a kotu"
Murtalah yace "Ai bakomai ranki ya daɗe, Yusuf mutum ne ya cancanci a temaka masa, tunda na tsinci takaddar nan na rasa ina zan kaita, saboda barazana da akewa duk wanda yai yunƙurin temakawa Yusuf, katsam sega lawyern Yallaɓai, ya gayyacemu gidansa a ɓoye yai tattaunawar sirri damu, a nan na bada wannan takaddar "
Widad ta jinjina kai tace " Masha Allah, ina godiya sosai da gudunmuwar ka, kuma insha Allah kuna da tukuici akan wannan gudunmuwar da kuka bamu "
Nura yace " Allah ya temakeki, wai yanzu dama duk abubuwan nan Alhaji Bulama ke shirya su, tabbas banga laifinki ba na ƙin mutane da kike, amma abun ya bamu mamaki sosai "
Widad tai murmushin takaici, har bata son yuna irin azabar da suka sha, tace " ya ake cikine? Me gidan namu yake ciki dan bazan shiga ba"
Nura yace "ranki ya daɗe, gida babu daɗi dan ya watse gaba ɗaya, bayan ɓatanku, Yallaɓai ya faɗi yai wata rashin lafiya, babu me zuwa gurinsa ko kula dashi se Anwar, shine yake masa komai yake jinyarsa, da aka sace Yallaɓai a gadon Asibiti ma aka kama shi, akace da saka hannunsa ya sha wahala sosai, Amma ya kula da Yallaɓai "
Jiki a sanyaye Widad tace " Allah sarki Anwar, yana gidan ne yanzu haka? "
Su Isa suka kalli Juna, jin bata san meyafaru ba.
Isa yace " ranki ya daɗe, Amma kin san an kama Hajiya ko? "
Tace" Eh na sani "
Yace" to dama ya bar gida ai tuntuni, takaddar daya bari ai ita Murtalah ya tsinta, ranar da aka yi zaman ƙarshe a kotu, muna nan 'yan sanda suka zo a motoci suna ta jini ya, na buɗe musu gate sukazo suka shimfiɗe Anwar, an gano shi a wani gida yake rayuwarsa yana kasuwanci a can cikin Jos, aka kawo shi an kasheshi ta hanyar caka masa makami a gefen cikinsa, sedai babu wanda yasan wanda ya kasheshi, amma a ranar kukan da Hajiya Halima take kamar dasa hannun shi Bulaman dai a kisan"
Ai tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta dinga jujjuya kai tana maimaita innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Ya Allah, Yaya Anwar ubangiji Allah ya jiƙanka, naso na sameka a raye in maka godiya riƙemin amana da kai, amma zan dawwama yi maka Addu'ar samun salama a kabarinka, kana daga cikin mutanen da bazan manta dasu ba a rayuwata, Allah ya yafe maka Yaya Anwar"
Kuka yaci ƙarfin Widad, yayin da suma duka jikinsu yayi sanyi sukaji mutuwar tamkar yanzu akayi ta.
Widad cikin kuka tace "Murtalah ka sameni a farm House gobe in Allah ya kaimu da yamma, nagode muku Allah yasaka da alkhairi nagode sosai"
Ta kasa ko rufe ƙofar motar, se kuka da take yi, Isa ya rufe mata ƙofar motar, ɗan sandan nan ya ja suka tafi, suna tafe tana kuka, dan Mutuwar Anwar ta da keta fiye da tunani.
Yusuf ya ɗan warware, Suleiman ya kwashe su a mota domin sujewa Nurat gaisuwa, da yake an kwana biyu da rasuwar mutane duk sun watse se tsilla tsilla.
Kahlil yai musu iso har wani katafaren falo, aka kira Nurat, Nurat ta fito cikin Ƙaton hijjabi, tana ganin Yusuf ta kasa magana se hawaye haɗe da murmushi daya ƙwace mata.
Ta durƙusa har ƙasa ta gaida Umman Yusuf, Yusuf yace "Nurat ya ƙarin haƙuri kuma?"
Nurat tace "Alhamdilillah"
"Allah ya jiƙanta yasa ta huta"
Nurat tace "Ameen"
Nan duk sukayi mata gaisuwa, Umma tace "dama munzo muyi miki gaisuwa ne, kuma zamuyi zuwa na mussman muyi miki godiya '
Yusuf yace " Nurat, ban san me zance miki ba, wanda ze nuna irin tarin godiyar dake bakina ba, a sanadiyata ga abubuwa marasa daɗi sun faru dake, Nurat dan Allah kiyi haƙuri, ban san mema zance ba"
Khalil yace "karka damu Yusuf, dama haka Allah ya ƙaddara seya faru, ba kaine sila ba, Allah ya riga ya rubuta hakan dama, sedai kam tabbas tayi faɗi tashi a kanka sosai, tun daga ɓatanku har wannan lokacin"
Umma tace "mungode, mungode Allah ya saka miki da alkhairi, Allah yayi miki Albarka ya jiƙan mahaifiyarki"
Nurat ta dinga jinjina kai, tana tuno Mummynta, ta kalli Yusuf tace "Kasan kuwa an kashe Yaya Anwar?"
A razane Yusuf ya kalleta yace "wane Anwar ɗin wai?"
Ta goge Hawaye tace "Bayan ɓatanku, Daddyn Widad faɗuwa yayi, ya fara rashin lafiya babu kowa a gurinsa babu me zuwa gurinsa , Anwar ne kawai yake gurinsa, ya dinga jinyarsa tsawon lokaci, bayan wani lokaci aka sace Daddyn Widad a Asibiti, aka kama Anwar ya daɗe a tsare ya sha wahala sosai kafin ya kuɓuta, to kwanan nan dai Brother ya cemin ai Ya bar letter a gida, ya bar gidan gaba ɗaya ba'asan inda yake ba, ranar da aka gama shari'arka akace an kashe shi kuma ana zargin Bulama ne yasaka "
. Umma ta dafe kai tana faɗin innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yayin da Nurat ta sake fashewa da kuka.
Khalil yace "se haƙuri, da kuma mu taya su da Addu'a, Wannan me aikin gidan ne Murtalah, ya tsinto takaddar, ban san ya'akayi yai kyan kai ya kaiwa Barrister Hafiz ba, dan abun zamana yayi duk wanda yai wani yinƙuri na temakawa a gano gaskiyar lamarin, se an bishi da mummunar barazana, mutumin nan maƙurane gurin zalunci"
Umma tai shiru tana hawaye, tana jinjinawa zaluncin Bukar, musamman Da taji wai ashe Anwar ɗane a gurinsa.
Nurat ta kira Yayar mahaifiyarta suka gaisa da Umma, sun daɗe suna hira suna jajantawa juna, yayin da Suleiman da Khalil ke hira.
Nurat tai shiru a gefe, tana kuka Yusuf yai ƙasa da muryarsa cike da tausayinta yace "Light am very sorry, kiyi haƙuri da ƙaddarar data same ki a sanadina dan Allah"
'Nifa ba kaine silar faruwar haka a gareni ba, dama Allah ya ƙaddaramin haka zata faru dani ne "
" Bazaki dinga kallona da abunda ya faru ba, koki zargi saboda ni haka ta sameki ba? "
Ta jinjina masa kai alamar eh, Yusuf yace " Nagode sosai, Allah ya jiƙan Mummy ".
Nurat tace " Ameen, naji ance an kaika Asibiti ya jiki kuma? "
Yusuf yace " jiki Alhamdilillah, mungode Allah "
" Allah ya kiyaye gaba, se nazo maka jaje "
Yusuf yace "A'a ni yakamata in sake dawowa in dubaki in sake miki ta'aziyya, Allah ya baki haƙurin jure rashin Mahaifiyarki"
Ta jinjina masa kai tana kuka, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi sosai, ya cigaba da rarrashinta, Umma ta fito ta tarar dasu tace "mu tafi ne ka taho kokuwa?"
Yusuf yace "A'a tare zamu tafi"
Ya miƙe Nurat ta rakosu har bakin mota, Yusuf yana ta sake bata haƙuri yana mata gaisuwa.
Suna tafe a motar, Yusuf yayi shiru yana tausayin Nurat, ga mutuwar Anwar data gigita shi, ga yana son ganin Widad.
Can yaji Umma tace "gaskiya Yarinyar nan tana da nutsuwa da tarbiyya, na yaba da hankalinta gashi ta bani tausayi Yusuf, nikam ko zaka nemi Aurenta idan zasu baka?"
AMANA! AMANA! AMANACE!!! IDAN KIN FITAR ALLAH NA KALLONKI
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
154_155
Gaban Yusuf yai mummunar faɗuwa jin abunda Umma tace, ya kalli Ummansa ta Mirror, amma yai shiru yaƙi cewa komai sema ɗauke kansa da yayi yana kallon waje.
Umma tace "ya Kay shiru ba kace komai ba?"
Ƙin magana yayi, dan bayama son zancen, Umma tace "Suleiman, dan Allah baka yaba da hankalin Nurat ba? Yarinyar tana da nutsuwa da kuma kirki sosai"
Suleiman yace "tabbas hakane Umma, ni kaina na yaba da nutsuwar ta, kuma da alama dai Yusuf akwai dalilin da yasa ta dage ta temake ka"
Umma tace "jimin yaro da wulaƙanci, ana masa magana yayi shiru, kamar ba dashi ake ba"
Yusuf yace "Umma me zance ne? Nifa ina da Aure ya zanyi da Widad kuma?"
"Karka ƙaramin zancen wannan yarinyar, wadda bata san halcci ba bata san abun alkhairi ba, kai ko zuciya baka da ita, duk wannan abunda ya sameka sanadinka baze zame maka darasi ba Yusuf, irin wahalar da ka sha, ba kai kaɗai ba harni kaina da sauran mutane, amma kake ƙara nanata wai kana da Aure, toni ban san da wannan Auren ba, ba wani Aure da kake da shi, ni dai ga yarinyar da ta kwantamin"
Yusuf yace "Umma, Widad bazata bada sheda haka kurum ba, akwai wani dal.....
" Rufemin baki, bana son jin zancen yarinyar nan gaba ɗaya, na gaya maka "
Yusuf yai shiru, ya maida idonsa wajen window, yana tunanin yaze da Umma akan Widad, gashi yana son ya haɗu da ita yana son su gana, amma Umma tana nema ta ɓata komai, kuma yaga alamar idan ya matsa, ze ɓata mata rai, shi kuma babban abunda baya so kenan, ɓacin ranta.
Haka Umma da Suleiman suka cigaba da hira har sukaje gida, ba tare da Yusuf ya tofa ta bakinsa ba, yai shiru dan bema san me suke cewa ba.
Suna zuwa gida Yusuf yaiwa Suleiman sallama ya shige gida abunsa, Umma kuma seda tayi sallama da Suleiman sannan ta shiga gida.
Widad kam sosai take jin mutuwar Anwar, ji take kamar mutuwar Anwar wani babban giɓine a gareta, dukda ba ɗan uwanta ne na jini ba, amma Anwar zuciyarsa ba irin ta mahaifiyarsa bace ba.
Tai kuka, tai kuka ƙarshe taje tai alwala ta tada salla mussman dan taiwa wanda ta rasa addu'a, ƙarshe ta ɗaga hannu zata yi Addu'a, ta kasa roƙar komai kawai ta fashe da kuka, "Allah ka yafemin laifukana, Allah na tuba ka yafeni, Ba Ammina, ba Daddyna, Ba Yaya Anwar, wanda nake sa ran zeji ƙaina maƙiya sun sa na masa abunda bazan sake kima a idonsa ba, ban san dangin mahaifina ba ban san na mahaifiyata ba, bani da wanda zan kalla a rayuwata inji sanyi, babu me raɓata babu wanda zan raɓa, Allah ka kawomin ɗauki "
Ta ƙarasa maganar tana rirriƙe gado da gefenta tana wani irin kuka me raunata zuciya, idanunta sukayi jawur ta fita hayyacin ta, ta rasa abunda yake mata daɗi, gashi har yanzu da tsoron mutane a ranta, tana jin tsoron raɓar wani, bata san meza'a kuma yi mata na cutarwa ba, ta fara tunanin ko ƙauye zata koma gurin Gwaggo?
Wata zuciya tace "suwaye a gareki? Suba danginki ba, wane karɓa zasuyi miki bayan suna zaune an tayar musu da hankali, hadda 'yan sanda ta yaya zasu sake karɓarki? Idanma zasu karɓekin kin san hanyar da za' abi aje a garin? '
Lumshe idinta tayi, hawaye na zuba daga idonta, tana jin yadda take sauke numfashi da ƙyar, alamun zuciyarta bata aiki yadda yakamata.
Ta takure a jikin bango, ta haɗa kai da gwiwarta, tana ci gaba da kuka, sanyin AC dake ratsata taji sanyin da take ji yayi mata yawa, nan da nan jikinta ya ɗau rawa, ta dinga rawar sanyi, kanta na wani irin sarawa amma ta kasa motsawa daga inda takey, ƙarshe ma ta haka ta kwanta a gurin, tana jin cikinta na motsawa, ta tuna Yusuf be san da cikin bama, ta shafa cikin a hankali tana tausayawa abunda ke cikin nata.
Amal ta ɗan farfaɗo, sedai befi tayi magana kaɗan a rana ba, bata magana sam seda ƙyar, gaba ɗaya ta ɗashe ta bushe saboda azabar bleeding da tayi, ga fargaba da tashin hankali da take ciki na kama Mummynsu, ga mutuwar Anwar da damfarar ta kuɗin nan da akayi, gashi har yanzu raɗaɗin fyaɗen da Alhaji Haruna ya mata yakasa barin Ƙwaƙwalwarta, dan haka abun ya mata yawa, ta samu depression, Ramlah ce ke kula da Ita take jinyarta, taga abun nata bana ƙare bane, ta ɗauketa ta kaita Asibiti.
Likita ya dubata, ya rubuta musu teses, ta kaita lap akayimata, suka kaiwa Likitan, ya karɓa ya duba ya kalli Amal yace "ƙanwata, gayamin tsakaninki da Allah ƙanwata meyasameki kike bleeding haka?"
Amal ta kalli Likitan, ta sunkuyar da kai se hawaye, Ramlah tace "doctor, ba lallai tayi maka magana ba, saboda tunda akayi mana rasuwa batavda sukuni, bata magana se kaɗan kaɗan, Fyaɗe akayi mata, harta samu ciki, shine taje ta zubar da cikin jini ya ɓalle mata yaƙi tsayawa"
Likitan yace "waye yayi mata fyaɗen?"
"Wani mutum ne" Ramlaj ta bashi amsa.
Yace "kuma an kai shi gaban hukuma da yayi mata fyaɗen?"
Ramlah tace "doctor, bamu da wannan lokacin yanzu ma baka san da yadda na kawota ba, kawai ai mata abunda ya dace"
"Amma kun san illar dake tattare da ayiwa mace fyaɗe aja baki ayi shiru ba tare da ɗaukaf mataki ba, ba hujja bace a ɓoye irin wannan lamarin dan gudun jin kunyar mutane, ki tsaya ki ƙwaci haƙƙinki shine yakamata, yanzu yaushe abun ya faru? Kuma da ya faru an kaita Asibiti an mata gwaje gwaje ne? "
Ramlah tace " dan Allah ke dena wannan tambayoyin, kawai ka rubuta mata magani a wuce gurin "
Ya ɗan taɓe baki yace " Any way, tunda haka kuka zaɓa zan miki bayanin sakamakon gwaje gwajen da mukayi, wannan abortion ɗin da tayi, an mata amfani da pills me ƙarfi wanda yafi ƙarfinta sosai, musamman duba da yanayin rukunin jininta, hakan ya samar da gagarumin rauni a mahaifarta, wanda yasa take ta zubar da jini, mahaifarta tayi raunin xa abune mawuyaci ta sake ɗaukar ciki, sedai idan an kaita India anyi mata aiki, akwai wani ƙwararren gynecologist dayake aikin, sannan a shawarce yana da kyau a dinga kaita tana ganin Likitan Ƙwaƙwalwa, saboda wannan depression ɗin ze iya zame mata hauka tuburan, duba da yadda matakin depression ɗin nata yayi worst "
Ramlah tace " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yanzu nawane kuɗin aikin zeci? "
Ya kashingiɗa a kan kujerarsa yace " idan kun shirya kumin magana, baya cin fiye da naira miliyan uku haka, ko yanzu idan a shirye kuke, za'a iya booking na jirgi ku tafi"
Ramlah ta dafe kai, dan babu inda zata samo wannan kuɗaɗen, komai ya ƙare musu, basu da komai yanzu a kangon gidan kawai suke, gashi taji labarin Widad na Farm House dan haka a tsorace take, kar Widad tazo ta fatattake su koma tace a kamasu.
Ramlah tace "thank you very much doctor, when we are ready, we will let you know"
Likitan yace "shikenan, ba damuwa Allah ya bata lafiya"
Ramlah ta kama hannun Widad, suka fito suka hau motar da ta rage musu zuwa gida, haka suka koma Ramlah ta saka Amal a gaba tana kallonta, yanzu ita kaɗai ta rage mata, ba Mummy, ba Anwar, ita kanta bata da tabbacin zata tsira, har gara Amal ita ba lallai a sameta da wani laifi ba, gashi itama Amal ɗin ta zama shiri shiri, Ramlah ta rasa abunyi, taje ta ɗakko kayan shaye2 ta ɗurawa cikinta, seda taji tayi dam sannan ta baje tana bacci a gurin.
Kamar yadda Widad tace wa Murtalah tana son ganinsa, haka akayi yaje gidan gona dan ya sameta, amma 'yan sandan da suke gadinta suka hanashi shiga, seda sukaje suka sameta suka gayamata zuwansa, sannan tace a barshi ya shigo tasan da zuwansa.
Har falon ya shiga ya zauna, ta fito cikin dogon hijjabinta, Murtalah a ransa yace "iko se Allah, wai yanzu Widad uwar tsiwa, gadara ganioda izza itace a haka? Itace yanzu take komai sanyi sanyi, harda shigar zumbulelen hijjabi haka, lallai tayi darasi na rayuwa a makarantar duny, me cike da ƙalubale da tarin matsaloli, ya ga yadda ta sake ramewa, se kumburi a fuskarta, duk ƙibar nan babu da da aukinta, amma yanzu kamar sillen kara haka ta koma.
Ta ƙaraso ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon, gaba ɗaya a takude take saboda zazzaɓine ma a jikinta, ga jira dake kwasarta dan tun safe tea ne kawai a cikinta se biscuit, bata da appetite na cin komai sam..
Murtalah ya zube a ƙasa yana "barka da yamma ranki ya daɗe"
Tace "yawwa kana lafiya?"
"lafiya ƙalau Alhamdilillah ranki ya daɗe"
Widad tace "masha Allah, na kiraka ne nan dan muyi magana, zan saka wani aiki ne, amma kafin nan bani labari, wane hali gidan mahaifina ke ciki?"
Murtalah yace "eh to, kamar dai yadda kika sani, an kama matar gidan saboda da haɗin bakinta Alhaji Bulama yake gudanar da wasu abubuwan, ita kuma Amal mamar hankalinta ya gushe, tunda aka kawo gawar Anwar, aka kama mahaifiyarsu ta faɗi shikenan, ko magana bata son yi, kamar dai ta samu matsala a Ƙwaƙwalwarta ne, ita kuma babbar dama tun bayan ɓacewarki take bin wannan ɗan gidan Bulaman, to a yadda muke ganin abubuwa na gudana ma dai, shaye2 take yi dan wataran mankas haka take dawo mana gidan nan, yanzu dai su biyune kawai a gidan ba kowa "
Widad ta jinjina kai tace " Allah sarki, Allah me yadda yaso, anyi ƙoƙarin ƙaƙabamin hauka tuburan ga haauka ya fara bibiyar 'ya' yanta, an haɗa kai an kashemin mahaifiyata, se gashi itama an sa an kashe ɗanta, shi kuma wancan ya kashe matarsa da hannunsa, haƙƙinmu baze taɓa barinsu jin daɗin duniya ba"
Widad tai maganar tana share hawaye, Murtalah yace "ayi haƙuri ranki ya daɗe, ai an gode Allah an auna Arziki sosai, Amma dama ita tasa aka kashe mahaifiyarki?"
"karka shiga hurumin da ba naka ba, ka tsaya iya matsayinka, ina son in dinga sanin duk wani motsinsu, da duk wani abu dayake kaiwa yana komowa a gidan ka dinga sanarmin, tashi ka tafi"
Murtalah ya miƙe yana godiya, harze fita tace "ya batun salary ɗinku? Ana biyanku kuwa?"
Yace "ranki ya daɗe, ai se muyi wata biyu kafin a bamu albashin ma, kuma duk anbi an rarrage mana albashin"
"Kuyi lissafin abunda kuke bi na bashi, zan biya ku ruɓinsu biyu insha Allah"
Murtalah ya zube a gurin yana "Allah ya temakeki, Allah ya baki yawan rai yasa kifi ƙarfin maƙiyanki"
Widad tace "Ameen"
Yana fita itama ta fito, ta kira ɗan sandan nan daya kaita gidansu jiya, ya taho jikinsa na tsuma ya gurfana a gabanta, ta kalleshi tace "kasan gidansu Yoseef?"
Yace "A'a ranki ya daɗe"
Tace "ina son saka ka aikine, kaje ka bincikamin inane gidansu, ina son in dinga sanin duk wani moves ɗinsa ne, ina son dinga sanin halin dayake ciki"
Yace "to ranki ya daɗe, zan ƙoƙari in gano gidan nasu, amma kin san bani da damar da zan bari gidan nan, in koma unguwarsu saboda a nan aka ajiyeni inyi aiki"
"karka damu, akwai tukuici me kyau, sannan babu wanda ze zargeka akan hakan, zan baka kariya ince nine na saka aikin"
Yace "shikenan ranki ya daɗe, amma ki sanar da shugaban mu"
"baka da matsala"
Yusuf jikinsa yayi kyau sosai, ya farfaɗo daga wannan uban baƙin da yayi kamar bashi ba, saboda samun sassauci da yayi daga ƙangin zaman gidan kurkuku, sedai Umma na cigaba da damunsa akan lallai yaje ya nemi Auren Nurat, yace "Umma, kina cewa inje in nemi Auren Nurat, idan fa na nemi Aurenta dole za'azo bincike wataran, bana son abunda ya faru dani akan Salma ya sake faruwa, ga kuma abunda ya faru da iyayenta saboda ni, ina jin tsoro Umma, amma kinga Widad tasan koni wayey, tasan Halinda nake ciki amma muka zauna tare a haka, ba tare da ta nuna ƙyamarta a gareni ba"
Umma tace "kaga sauraramin, Itama Nurat ɗin zata iya aurenka ai, yarinyar bata da matsala kuma banga alamar wulaƙanci a tare da danginsu ba, nifa wannan Widad ɗince bana so, abun da ya samemu saboda ita bazan taɓa mantawa ba, duk wannan baƙar azabar ka shata ne saboda ita fa, amma baka gani "
Yusuf yace " Umma, Widad abun tausayi ce, baki san abunda ya faru da ita bane, ni kaina nasa....
Umma ta katseshi ta hanyar cewa "ban san abunda ya faru da ita ba, kuma bana buƙatar in sani, tun wuri ka kiyayeni akan wannan yarinyar, ita 'yar masu kuɗice ka barta taje, taimakon daka mata Allah ya amfana, kaima ka rungumi talaucinka, kuma idan ka sake ka taka kaje inda take zakaga yadda zanyi da kai, kalli dukda kayi free ai yakamata ko dubaka tazo tayi amma ba ita babu dalilinta"
Yusuf ya rasa yazewa Umma ta fuskance shi, Yasan dole Umma zataji babu daɗi saboda yadda take ƙaunarsa, amma Widad taje ta bada wannan shedar, amma taƙi bari ya gayamata abunda yake faruwa, wanda ita bata sani ba.
Babban abunda ya bawa Umma mamaki, be wuce yadda Yusuf ya ɓata rai ba, duk laifin da zeyi tai masa faɗa baya fushi, amma ƙarara a fusakrsa wannan karon, ya nuna beji daɗin hukuncin data yanke ba, ta dinga binsa da kallo, yai shiru bece komai ba.
Umma tace "yakamata kuma kaje ka sake yiwa Nurat gaisuwa"
Yusuf yace 'to, zanje insha Allah "
Ramadan yaji takaici jin labarin mahaifinsi ne ya dinga shirya duk wata manaƙisa akan Daula, dukda tarin alkhairansa a gareshi, babban abunda ya daɗaɗa masa rai kuma shine ba' a samu mahaifiyarsu da cutar HIV ba, amma yana ta sake zullumi akan ance su koma bayan watanni uku a sake yi.
Ramadan yace "Umma, yanzu shikenan Daddy ya lalata rayuwarsa, mu kuma ya bar mana abh mafi muni da abun kunya, ban taɓa jin labarin mutum me butulci kamar mahaifinmu ba"
Hajiya Sarah tace "bari kawai Ramadan, ni kaina nayi haƙuri da shi tsawo shekaru na masa biyayya iyayi na, amma ban taɓa zaton yanawa Daula zagon ƙasa haka ba, dukda wasu lokutan inajin haushin Widad, amma tabbas mahaifinku ya zalunceta, zalunci me muni ina fatan Allah yasa bani da wannan cutar, shi kuma yaje can yaƙarata, ya girbi abunda ya shuka '
Iman tace "waini Mummy, Yaya Fahad baze zo ya duba ki bane? Tunda muka taho Adamawa be neme mu ba, kuma a waya ba wanda ya kira fa"
Hajiya Sarah tace "ƙyaleshi kawai, ki rabu da shi, aini Na zubawa sarautar Allah ido kawai, nasan zaluncin da mahaifinku ya aikata muma se hakkin ya shafemu"
Ramadan yace "karkice haka Mummy, ai Allah baya kama wani da laifin wani, dan haka kiyi hakuri Allah ya yafe mana kurakuranmu"
Suka amsa da Ameen gaba ɗaya.
Ramlah ta farka daga uban baccin da take n shaye2 da tayi, lokaci ya ƙure tana wannan baccin, amma still damuwar dake tattare da ita bata sake ta ba, ji tayi ma kamar an ƙara mata wata damuwarne, akan wadda take ciki.
Ta miƙe a hankali amma bata ga Amal ba, tayi zaton ko tana ɗakinta ne, ta tafi ɗakin nata, ta duba amma nan ma bata ciki sam, ta sakko ta fito harabar gidan ta tarar masu aiki suna wa Amal fifita.
Ta taho da sauri tace "lafiya kuwa?"
Isa yace "wuƙa ta ɗakko ta fito da ita, tana yunƙurin kashe kanta, da ƙyar muka ƙwace wuƙar, shine ta faɗi ta suma"
Ramlah ta ƙarasa ta ɗago Amal tace "why Amal Why? Why will you attempt to kill yourself, why do you attempt to murder yourself? Haba Amal"
Ta kalli Nura tace ya kawo mata ruwa, ya kawo ruwa aka dinga shafawa Amal ɗin, can taja ajiyar zuciya ta buɗe ido, Ramlah tace "Amal meyasa zaki yunƙurin kashe kanki? Komai yai zafi maganinsa Allah"
Cikin kuka Amal tace "Mummy, Mummy na, Yaya Anwar, dan a kainin inga Mummy i love hery, she's my Mum, dan Allah kice ayi haƙuri bazata sake ba, ina son in ganta"
Ramlah ta rungumeta tana rarrashinta, tace "kiyi haƙy, za'a kaiki ki ganta insha Allah, amma karki ƙara yunƙurin kashe kanki, kinji ko?"
Amal ta jinjina mata, ta kama hannunta zuwa cikin gidan, yayin da masu aikknysuka shiga gulmarsu.
Gabaɗaya walwalar Yusuf ta ɗauke, ko Abinci baya iya ci, idan ya kwanta tunanin Widad kawai yake yi, yana son ya ganta sosai, Amma Umma taƙi.
Ya zauna yai shiru a tsakar gida, Umma ta fito da gyalenta a hannu tace "Yusuf bari zan ɗan shiga kasuwa, ba daɗeaayzan ba yanzu zan dawo"
Yusuf yace "to A dawo lafiya"
Tace "Allah yasa" ta sa kai ta fice.
Widad tana zaune ta tasa 'ya' yan itatuwa a gabanta, ta kasa ci ta zuba musu ido, tana kallonsu kamar ranar ta fara ganinsu, kamar an tsunkuleta ta tashi da hanzari, tai waje ta samu ɗaya daga 'yan sanda dake bata tsaro, ta tambayeshi ina wannan ɗan sandan da suka fita tare, yace mata "Ai ya tafi aikin da kika sashi ranki ya daɗe"
Tace "maza kiramin shi a waya"
Ba musu, ya kira shi a waya, aikuwa ya ɗaga ya miƙa mata wayar, Widad tace "ka gano min gidan nasu?"
Yace "eh na gano, naje na tambayi abokan aikina da suka kaishi Asibiti"
"a cikin ƙasa da mintuna uku, ka hanzarta ka turomin Adress ɗin"
Yace an gama ranki ya daɗe, aikuwa ya tura mata, ta karɓa ta duba ta shiga cikin gidan da sauri, taje ta shirya tsaf ta fito, bata sairari kowa ba, ta buɗe wata mota ta shiga, 'yan sandan suka taho kanta suna tambayar ina zata?
Babu wanda ta saurara a cikin su, ta fafari motar tana wani irin mahaukacin horn, wanda ya tilastawa masu gadin buɗe mata, saboda gudun ɓacin ranta, tai waje da motar a guje.
Nan da nan' yan sandan suka ɗau mota suka rufa mata baya.
Yusuf yana nan zaune, ya gaji da zaman tsakar gidan, ya tashi ya koma ɗaki, Sallama yaji a tsakar gida, ya amsa Sallamar daga ɗaki yace "Umman bata nan"
Me Sallamar tace "dan Allah zan sha ruwa"
Haushine ya kama Yusuf, shi ga abunda ya dameshi amma baƙuwa zata addabeshi, ya fito ransa a ɓace kawai yaci karo da Nurat, tai masa murmushi, gaba ɗaya ya ɗan ruɗe yace "dama kece?"
Nurat tace "Nice ko in koma ne?"
"Ni na isa ince ki koma, ɗazu Umma ta fita nasan zuwa yanzu tana hanya, shigo bismillah"
Nurat tace "Yaya Khalil yana waje, tare muka zo"
Yace "bari inje mu gaisa da shi"
Yusuf ya bata gurin zama a falo, shikuma ya fita waje, yana fita suka gaisa da Khalil, Yusuf yace "shigo daga ciki mana, ka tsaya a waje"
Khalil yace "A'a bazan shiga ba, Naga ta gaji da zaman kaɗaicine damuwa tana damunta, nace bari mu fito tazo ta dubaka ta gaida Umman kota samu relief"
Jiki a sanyaye Yusuf yace "Barrister ina matuƙar jin tausayin Nurat, ga kunyarta nakeji gani nake duk nine sanadin shigarta matsala"
"ka dena faɗar haka Yusuf, ai duk mumini dole ze yadda da ƙaddara me kyau ko mara kyau"
Yusuf yace "hakane, shigo mana"
Khalil yace "zan shigo, bari inje in ga abokina a nan ƙasan layin ku"
Yusuf yace "to shikenan" ya koma cikin gidan.
Nurat tana zaune a guri ɗaya, tai shiru Yusuf ya shigo ta ɗaga kai ta kalle shi tana wannan murmushin nata daya zama nature ɗinta.
Yusuf mabya mayar mata da murmushin, yaje ya ɗakko mata ruwa a fridge da lemo ya kawo mata, yace " Sannu da zuwa light, ga ruwa Kisha umma tana daf da shigowa"
Shiru tai tana sunkuyar da kai yace "ikon Allah, kunyata kuma kike ji? Ko kuma ba kya shan irin wannan?"
Ta girgiza kai tace "ni kowanne ina sha"
"Na gidanmu ne bazaki sha ba kenan"
Ta girgiza masa kai tana murmushi yace "idan Umma ta dawo kuwa sekin sha, Umma ba'a zuwa gidanta a ƙi karɓar abunda ta bawa mutum"
Ita dai sedai murmushin, amma ta kasa cewa komai.
Can Yusuf yace "light, wai nikam dan Allah ya akayi kika san da abunda na ajiye a wayarki?"
Cikin sanyin muryarta tace "ai ka taɓa cemin kayi ajiya a wayata, amma baka gayamin meye ba, lokacin da aka kama ka sena gayawa brother, harda ajiyar da kace kayi a wayar, shine yace in bashi wayar, ya dinga bincike a kai, daga nan ya kaiwa wani Abokinsa, ban san yadda akayi suka gano ba "
Yusuf yace " Aini bani da bakin da zan miki godiya Nurat, Allah jiƙan Mummy, Allah yasaka da alkhairi "
Tace " Ameen "
Can kuma tace " dan Allah dagaske kana da Aure? "
Yusuf yai murmushi yace " Waye ya gayamiki? "
" Kai ka taɓa gayamin, da na kiraka a waya, ka cemin kana tare da matarka "
Yusuf yace " A lokacin tsokanar ki nakeyi, bani da Aure amma a yanzu ina da Aure, Widad mata tace "
Ƙirjin Nurat ya buga da wani irin ƙarfi, take annurin fuskarta ya ɗauke gaba ɗaya.
Yusuf yace " ya dai? Ko kina sona ne, kamar kishi fa nake gani a fuskarki"
Ta ɗago manyan idanunta farare ƙal, ta sauke akan Yusuf, take taji ta karaya gaba ɗaya ƙwalla na neman cika mata ido.
"Yoseef!!!"
Yaji an kira sunansa, kuma babu me ambatar sunansa a haka idan ba gimbiyar Daula ba.
0 comments:
Post a Comment