Yusuf da Nurat duk suka ɗaga kai suna kallon inda Widad ke tsaye a bakin ƙofa, seda ƙirjin Yusuf ya buga da ƙarfi ganinta a tsaye, fuskarta babu Annuri sam, dan kwata kwata be taɓa zatan ganinta ba a wannan lokacin, ba Yusuf kawai ba hatta Nurat seda hanjin cikinta ya kaɗa, ta shiga fargaba saboda yadda Widad ɗin tai kicin kicin da rai.
Yusuf ya tattaro dukkan jarumtarsa, ya dake ya kauda fargabar dake zuciyarsa ya kalli Nurat yace "Light, gaskiya ki sha ko ruwane kafin umma ta dawo, bazanji daɗi kizo gidanmu ki tafi baki ci komai ba"
Fargaba ce lulluɓe a fuskar Nurat, jikinta se tsuma yake kamar taga zakanya.
Yusuf ya ɗakko ruwan roba, ya buɗe ya zuba a cup ya miƙawa Nurat, amma Nurat ta kasa karɓa se kallon Widad kawai da take yi, Widad ɗin dake tsaye tana huci.
Nurat tace "Amm.. Am naga kamar gurinka tazo bari in baku guri"
Yusuf yace "yi zaman ki kawai, idan wani abunne ya kawota ta faɗa a nan ina jinta"
Widad ta kalli Yusuf, taiwa Nurat wani mugun kallo, ai ba shiri Nurat ta miƙe, a ɗarare ta raɓa ta jikin Widad ta fice daga ɗakin, tana fargabar kar Widad ɗin tayi mata wani abun
Yusuf ya yunƙura daga kan kujerar da yake, ze bar mata ɗakin amma ta sha gabansa ta kalle shi tace "Yoseef, Anya kamin adalci kuwa? Na cancanci haka daga gareka? Bani da kowa se Allah, ba uwa, ba uwa, ba dangi ba kowa kasan bani da kowa se Allah, se kuma kai da nake sa rai, amma kamin haka? Yoseef tunda Allah yasa ka kuɓuta baka nemi inda nake ba, ina ta faman wahala da rayuwata babu me temakona se Allah, bani da wani jigo da zan jingina dashi inji farinciki, kawai se inzo in ganka da wata, bayan kasan zuciyata bazata iya jure hakan ba" tai maganar idonta taf ƙwalla.
Yusuf yace "ni bance ba kimin adalci ba seke zaki gayamin haka? Duk tarin wahalar dana sha saboda ke, amma kika kalli duniya kika bada shedar ƙarya a kaina Widad, baki tausayawa halin dana shiga ba, seni zakiwa kallon ban kyauta miki ba?"
"Yoseef, a tunanina ko kowa be fahimceni ba kai zaka fahimceni, na gaya maka komai, kasan komai game dani fiye da kowa, na baka dukkanin yarda wanda har hakan yasa na gaya maka waceceni, da abunda ya faru da rayuwata, kasan bazan taɓa yin haka dan in tozarta ka ba, dukda na ɓoye maka waye Bukar, ba nayi hakan ne dan komai ba se dan tseratar da rayuwarka, da kuɓutar da kai daga sharrinsu, na ɓoye maka Bukar shine Bulama saboda na bar hakan a zuciyata har ranar da zan kama shi red handed, sedai ƙaddara ta riga fata, amma shikenan tunda baka buƙata ta yanzu a rayuwarka, zan rungumi ƙaddara da irin rayuwar da Allah ya ƙaddara zanyi, amma kafin nan "
Ta saka hannu ta cire dogin hijjabin jikinta, wanda ya kasance har ƙasa, ta cire doguwar rigar abayar dake jikinta, ya rage daga ita se gajeran wando, da kuma half vest.
Tozalin da Yusuf yayi da cikin dake jikin Widad ne yasa shi ya ɗan rikice, tabbas idonsa ba gizo yake masa ba, cikine a jikin Widad gashi nan yayi girma sosai ya fito.
Ta ƙaraso gabansa ta kama hannunsa, ta ɗora a kan cikin nata tace "dan Allah Yoseef, koka watsar dani karka watsar da ɗanka, yau idan na mutu bashi da kowa se kai, dan Allah karka bari yayi irin rayuwar dani ko kai mukayi, Yoseef ka tausayamin ko dan ɗanka da nake ɗauke dashi.
Yusuf ya kalli Widad ya kalli cikin jikinta yace "You are pregnant Widad"
Ta jinjina masa kai, Yusuf yai murmushi yace "'yar baiwa, ashe Allah ya amsa Addu'ar ki, ya baki abunda kike nema, hankalinki ya kwanta" yai maganar cikin farin ciki fuskarsa ɗauke da murmushi.
Ya rungumeta a jikinsa hawaye na zuba daga idonsa, Widad ta rirriƙeshi itama tana kukan tana faɗin "We miss you Daddy me and your unborn, munyi missing ɗinka sosai, we really suffered, banyi zaton zan sake ganinka ba, bam zaci zanyi rai zuwa wannan lokacin ba"
Ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka, Yusuf ya sake manneta a jikinsa shima yana zubar da hawaye yace "i miss you too Babyna, i miss you my Queen, I love you"
"I love you too my Husband"
Sosai suke kuka daga shi har ita kamsr ƙananan yara, ya sake ɗagota ya kalli cikin nata, ya rungumota jikinsa ya haɗe bakinsu yana kissing ɗinta, hawayen tausayawa kansu na zuba a idonsa, yayin da itama kukan take.
Ya cire bakinsa daga nata, yana share mata hawaye ya kalleta yace "ɗan sake maimaita min abunda kikace yanzu mana"
Murmushi tai ta miƙa hannunta itama fuskarsa, tana share masa hawaye "tace me kake so in sake faɗa?"
"kin san koda ina prison, kalmomin nan da kika dinga faɗamin ranar da aka kamani sun tsaya a zuciyata sosai my wife"
Fashewa ta sake yi da kuka tace "dan Allah Yoseef ka dena tunamin kayi zaman prison please, zuciyata zata tarwatse, am sorry Yoseef duk sanadina ne ka shiga mummunan yanayi"
Yusuf yace "ni dai a sake cewa ana sona please" yai maganar a Shagwaɓe.
Ta noƙe kafaɗa tace "Anƙi ɗin"
"Ya akayi kika fara so nane?"
"Nima ban sani ba ai, Yoseef dan Allah ka dawo gareni, akwai maganganu dayawa da nakeso muyi, kuma kaga nikaɗai nake rayuwa ina farmhouse, kalli jikina duk ya kumbura, Yoseef zuciyata ciwo take, likitoci sunce idan nazo haihuwa ko dai muyi surviving, ko mu mutu gaba ɗaya ko ɗaya ya mutu ya bar ɗaya"
"Shhhhh hakan baze faru ba insha Allah, zaki haihu lafiya, kinga a yanzu haka ina ta fama da Umma saboda ke, kin san a rayuwa Umma bata son abunda ze taɓani, dan haka abune mawuyaci ta fuskanceni, saboda tana cikin kotu kika bada sheda a kaina, dan haka sena fara shawo kanta tukuna"
"Yoseef, umma bata sona kenan?"
"A'a ba haka nake nufi ba, taji ba daɗine abunda kikayi"
"Dan Allah kayi mata bayani Yoseef, nasan kaika fahimceni kasan komai fa"
"Na sani my wife, kiyi haƙuri, zanyi ƙoƙari inzo har farmhouse ɗin in ganki, yanzu maida rigarki in rakaki mota, nasan Umma na daf da shigowa"
Ai gaba ɗaya sun manga da batun Nurat, dan Widad ta manta ma da taga Nurat tare da Yusuf.
Ta tura baki tace "Nika ɗakko ka samin"
Ya harareta yace "zaki fara sani aiki ko?"
"Eh mana, tunda ka haɗani da aiki ai dole Kayi aiki"
Yusuf yai dariya yace "lallai kinyi baki, mara kunya kawai"
"Ai kaika koyamin rashin kunyar"
"Allah yasa Hari ta jiki, Kisha baƙar magana"
Widad tace "Allah sarki Hari mutuniyata, ina jin bayin Allah nan sosai a raina, ina kewarsu mussman Hinduna da Gwaggo, in komai ya daidaita zamuje insha Allah"
Yusuf yace "kin san kuwa wannan Sunusin, mijin Jamila yaje ya bada sheda a kotu?"
Widad tace "Nasani"
"Ya akayi kika sani?"
Widad tai ajiyar zuciya tace "shiyasa nace maka ina son mu haɗu, ina da magana da kai sosai"
Tai maganar cikin Shagwaɓa tana tura baki.
Yusuf yace "Malama karki sa mu saki layi, matso in saka miki rigarki"
Murmushi tai masa ta ƙara matsowa daf dashi, sedai yaga abu kamar kwanciyar bulala yai duhu akan fatarta, wajen damtsenta.
"Baby meye wannan?"
Yai maganar yana kallon hannun nata.
"Bakomai, samin rigata in tafi"
Shiru yai yana nazarinta, idonsa ya kuma sauka akan gefen fuskarta, nan ma wani tabon ne a gurin, ya sake kallonta zeyi magana tace "waiya kake ƙaremin kallo hakane kamar yauka fara ganina? Bani rigata in saka tunda kallona zakai ba samin ba"
Yusuf ya riƙe rigar yace "bazan taɓa gajiya da kallonki ba" yai maganar yana sake janyota jikinsa, yana sa fuskarsa a wuyanta.
"Naji, amma ka ƙyaleni in tafi, hankalina ya kwanta tunda na ganka"
Haka ya saka mata rigar, ta ɗau hijjabin zata saka, ya dakatar da ita ya ɗaga rigar jikinta, ya sake kallon cikim nata, ya sumbaci cikin ta yace "I love you my unborn, karka waharmin da Mum ɗinka kaji Babyna, i love both of you"
Widad ta dinga masa dariya, wai yana surutu shi kaɗai, kamar zasu cinye juna, ko sababbin masoya.
Nurat kam tana fita daga ɗakin, waje tayi amma bata ga Khalila ba, se motocin 'yan sanda dake gurin, dan haka ta koma tsakar gidan, can nesa da ɗakin da su Yusuf suke, ta zauna akan kujerar tsakar gida.
Sedai tana jiyo dariyar su, ta sunkuyar da kanta a tsakanin cinyoyinta, tai shiru tana tunani, tana son Yusuf so na haƙiƙa, tana sonshi saboda Allah, amma tasan tunda ya auri Widad abune me wahala ya saurareta, kuma ga dukkan Alamu Widad ma tana matuƙar sonshi itama, dan haka Yusuf babu lallai ya saurare ta.
A hankali ta fara hawaye, tana gogewa a hankali, tana addu'a a zuciyarta "Allah ka yaye min son Yusuf, Allah ka zaɓamin abunda yafi Alkhairi a rayuwa ta"
Jin abun nasu bana ƙare bane, yasa ta sake miƙewa ta fita waje, tana fitavtarar da Khalil ya dawo, ya kalleta yace "Ta Yusuf harkin fito ne? Ai bamu gaisa da Umman ba"
Nurat tace "Brother mutafi gida"
Yace "meyasa? Kefa kika damu in kawoki"
Nurat tace "ni dai mutafi gida kawai"
Tai maganar hawaye na ƙoƙarin tona asirin dake zuciyarta, a ɗan dirirce yace "ko wani abun Yusuf ɗin yayi mkki?"
Ta girgiza masa kai ta buɗe mota ta shige, cike da mamaki Khalil ya bita da kallo.
Umma ceta shigo layin hannunta ɗauke da ledoji, sedai ganin motar 'yan sanda a ƙofar gidan yasa gabanta ya faɗi, ta dinga nanata innalillahi wa inna ialaihi raji'un, hankalinta ya ɗan kwanta data hangi Khalil.
Ta ƙaraso inda Khalil ke tsaye, tace "Khalil lafiya kuwa? Naga motar' yan Sanda?"
Khalil yace "lafiya ƙalau Umma, sunce min wani aiki sukeyi, Nurat na kawo ku gaisa kuma bakya nanma ashe"
Umma tace "Ai da kun shiga Yusuf yana nan ai"
Yace "Ai ita ta shiga ɗinma, amma ta fito"
Umma tace "A'a ban yadda ba, Nuratu fitowa zaki mu shiga mu gaisa"
Nurat tace "Umma yamma tayi ai"
Umma tace "a'a, ai ga Khalil nan Tare kuke kuma ga mota fito maza"
Nurat bata son tayi sanadin da zata gusar da farincikin dake zuciyar masoyinta, amma babu yadda ta iya, Umma ta haifeta bekamata ta bijirewa umarninta ba.
Nurat ta fito daga motar, tabi bayan Umma suka shiga gidan, sedai suna shiga suka tarar Yusuf da Widad sun fito, yana riƙe da ƙugun Widad suna murmushi cike da kulawa da juna.
Suna yin tozali da Umma, Yusuf ya saki Widad da sauri, ita kanta seda Widad ta tsorata ganin kallon da Umman take musu.
Umma ta kalli Widad tace "kinzo ki sake kulle shin ne kokuwa? Ko prison ɗin kike son ya koma?"
Widad ta kalli Yusuf, ta sunkuyar da kai.
Umma tace "ya kikayi shiru baki bani amsa ba? Kinzo ki sake maida shi prison ne, bayan duk wahalar da ya sha saboda ke, ki kaje kotu kika bada sheda akansa, banda Allah yasa wannan yarinyar Nurat da ɗan uwanta sunyi masa ƙoƙari suma da yanzu shekaru talatin zeyi a kurkuku "
Widad ta ɗaga ido ta jefi Nurat dake bayan Umma da wani matsiyacin kallo, wanda yasa Nurat jin kayan cikinta kamar sun koma bayan ta, a hankali ta silale ta fice ba tare da Umma ta lura ba.
Umma ta kalli Yusuf tace " kai kuma na dawo kanka, mara zuciya kai har abunda yai saura tsakaninka da wannan yarinyar, saboda rashin zuciya tana mace amma ta biyoka har gida? Idan na ƙara ganinta a gidan nan duk abunda nayi mata ita siya, yakamata ma hukuma tai mana tsakani da ita, tunda Allah yasa dai an gane baka da laifi meye kuma na cigaba da bibiyarka, kowa se yayi hanyarsa Allah ya bada lada "
Yusuf yace 'Umma dan Allah kiyi haƙuri, Widad aurenta nayi mata tace, amma..
Umma ta katse shi tace " kai kasan wannan, ni ban san da haka ba, iya sanin da nayi baka da wata mata, Ni Nuratu nake fatan ka Aura, dan se tafi wannan yarinyar sauƙin kai "
Widad ji tayi zuciyarta ta buga da ƙargi, tankar Umma ta soka mata mashi, take taji ta tsani Nurat, dama ga abunda mahaifinta yai mata, gashi kuma yanzu tana bibiyar mijinta, hawaye ya fara zarya a fuskar Widad, a hankali ta sanya takalmanta tai waje.
Yusuf kamar ya ɗora hannu a ka ya kurma ihu haka yake ji, baya son kukan Widad yana matuƙar ƙaunarta, amma Umma na son datse igiyar farincikin dake tsakanin su.
Umma ta kalle shi tace "wato da Nuratun tazo gidan nan wulaƙanci kai mata saboda wannan yarinyar ko? Farar fatarta na ɗaukar maka ido kana nema ka gayamin magana saboda ita ko Yusuf?"
Yusuf ya girgiza kai, Umma tace "duk abun kaga nayi bazanyi dan in citar da kai ba, wannan yarinyar idan ta ƙara raɓarka za'a iya samun matsala, ka manta da ita kawai ka nemi wannan yarinyar Nurat, dan se tafi waccan tausayi, kuma dama kaga Auren naku mutane na shakku a kai, tunda ba kowane yasan da wani kunyi Aure ba, kayi haƙuri ka rabu da yarinyar nan, Allah ya zaɓa maka mafi Alkhairi kaji yaron kirki, bana son abunda ze sake ɗaga mana hankali tashin hankalin da muka shiga ma ubangiji Allah ya yaye mana ya kiyaye gaba, Allah yabaka mace tagari mafi Alkhairi a rayuwar ka "
Ta miƙa masa wata ƙatuwar leda tace " yawwa ga wannan, yadine guda uku masu kyau da shadda biyu, idan anyi sallar magariba dare yayi ka kaiwa magaji ya ɗinka maka, ga takalma nan ma, hadda sabon agogo na siyo maka, ka ƙara akan kayanka, sonake nan kusa ka koma gurin aikinka"
Jiki a sanyaye yasa hannu ya karɓa yace "Nagode Umma"
Ya juya ya shiga ɗakinsa, yana zuwa ya ajiye kayan ya zauna ya dafe kansa yace "ua zanyi da umarnin Ummana, matar da ta dimga ɗawainiya dani tun a zanin goyo harna zama mutum, bani da uwar data fita, sannan ya zanyi da matatat wadda a yanzu haka nauyin kula da ita a kaina yake, haba Umma ki fuskanceni mana"
Yai maganar yana sake dafe kansa dake sara masa.
Nurat kuwa har sukaje gida, bata ce komai ba, juyin duniya Khalil yai yai ta gaya masa abunda ke faruwa amma fafur taƙi, suna zuwa gida ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa ta shiga aikin kuka, tana jin yadda soyayyar Yusuf ke ƙafa tsuma mata zuciya, tana shiga dukkan wani sashe na jikinta, amma tasan ssamun Yusuf idan ba wani iko na Allah ba, abune da baze taɓa yuwuwa ba, ya riga ya mata nisa tunda ya zama miji ga Widad, ko ba'a gayamata ba Tasan Widad bazata zauna da kishiya ba, kishiyarma ita wadda mahaifinta ke da Mummunan tabo a gurin Widad ɗin.
Khalil duk ya shiga damuwa ganin Halin da Nurat ke ciki, a nan falo mahaifiyarsa ta fito ta sameshi tace "Khalil har kun dawo ne? Ina Autar tawa take ne?"
Khalil yace "Ta shiga ɗakinta"
Tace "yaya, da kuka fitan ta ɗam saki jikinta kuwa? Na fuskanci har yanzu Nurat tana cikin damuwa da alhini, bana son rashin walwalrata, gashi ni bani da 'ya mace balle ta samu' yar uwa, ni kuma ba son yawan hira take dani ba, na rasa ya zanyi, Abbanku ma ya faramin magana akan rashin walwalarta wai kowani abu nake mata? Nace masa ya za'ayi in takuramata tana 'yar ƙanwata? "
Khalil yai ajiyar zuciya yace " Mama akwai abunda yake damunta, kuma baze rasa nasaba da halin data tsinci kanta a ciki ba, dole se an bita a hankali "
Mama tace " to shikenan, naga kai taku tazo ɗaya sosai, dan Allah ka dinga kwantar mata da hankali, kana rarrashinta"
"to Mama Insha Allah, bari in shiga inyi alwala magariba tayi '
Ya tashi ya baf falon, uana jin inama ze iya ɗaukewa Nurat damuwar da take ciki.
Widad kam tasha kuka data koma gida, taji ta tsani Nurat bata ƙaunarta sam, ta barwa ranta sedai ayi duk wadda za' ayi, amma bazata bari Yusuf ya auri Nurat ba.
Yusuf ya fita yai sallar magariba ya kai ɗinkin kayansa, ya dawo yana daf da shiga gida wani yai masa sallama, ya tsaya ya amsa suka gaisa.
Mutumin yace "matarka ce ta aikoni, tace ga wannan in baka"
Yusuf ya karɓi ledar daya bashi, mutumin ya tafi, Yusuf ya shiga gida ya wuce ɗakinsa, yana zuwa ya buɗe ledar, sabuwar wayace kar a ciki da layi, tai rubutu a jikin kwalin wayar"
"switch on the phone, and call me Baby, Your wife"
Murmushi yayi cikin rawar jiki ya kunna wayar, ya duba yaga lamba ɗayace a ciki, maimakon ya kirata da wayar, seya kwafa a ƙaramar wayar dake hannunsa ya kirata.
Tana kwance akan gado, tayi rigingine wayar ta fara ringing, ai da sauri ta ɗakko wayar ta ɗaga.
"Hello My Queen"
"meyasa baka kirani da layin dana baka ba?"
"so kike Umma ta tambayeni ina na samo waya?"
"Shikenan, ya kake?"
Yace "lafiya ƙalau, ya ki kaje gida?"
Tai ajiyar zuciya sannan tace "Alhamdilillah"
Yace "Widad dan Allah kiyi haƙuri da abunda ya faru yau kin san"
"I understand, just forget sonake kawai muyi hira da kai, inji daɗi a raina, kaɗaici ya dameni ko Abinci bana iyaci Yoseef, ga bani da lafiya I need you Yoseef, i need your help"
Jiki a sanyaye Yusuf yace 'ki kwantar da hankalinki my wife, Insha Allah inaji a jikina komai ya kusa zuwa ƙarshe insha Allah, kiyi haƙuri karki cutarmin da kanki da Babyna, ki dinga cin Abinci please, karki mana illa "
" toni ya zanyi inci, babu me rarrashina ya bani a baki? Gashi bana samin irin Abincin da nake so, Yoseef dan Allah ka bawa Umma haƙuri ka dawo gare ni please "
" karki damu, Umma zata soki tana da sauƙin kai sosai, Insha Allah zam sam abunyi, amma dan Allah kici Abinci kinji Wudas ɗina "
" Wudas ko? " tai maganar a Shagwaɓe.
Yusuf yai dariya yace " ba haka Hari take ce miki ba? "
" to kai ita ne? Kasan meze faru kashe wayar, zanje inyi wanka video call nake son muyi in ganka "
Yace" shikenan, as you wish Babyna"
Yusuf ya rungume wayar nan.
Ko takan Abincin dare Yusuf bebi ba, Widad ta sake kiransa video call, ta saki dogon gashin nan nata, tana shafa mai.
Yusuf yace "Cikin nan ba ƙaramin kyau ya miki ba fa"
"Allah ne yayi cikin nan baze fita ba, amma allurar zubar da ciki Bulama yasa ayimin"
"cikin nawa aka so zubarwa?"
"Eh mana, sun kusa kasheni fa, akwai labari idan mun haɗu fa"
Yusuf yace "Allah sarki babyna, mun sha wuya sosai, ko da kikazo kotu kallo ɗaya nai miki na gane ba'a kwanciyar hankali kike ba"
Widad tace "bar wannan zancen kawai, kar ka ɓatamin rai ka rusa mana farinciki"
Yai murmushi yace "to shikenan, kina min ƙwalele da gashin nan fa"
Tai murmushi tana masa gwalo ta waya, tace "ziro hannu ka taɓa mana"
"Inama in rufe idona in buɗe in ganni a kusa dake, in tayaki shafa man nan"
"Harka tunamin lokacin da muna ƙauye, gaskiya Yoseef kana da haƙuri kayi haƙuri dani sosai, shiyasa ka taka wani gagarumin matsayi a zuciyata my love"
Har tagama shirin kwanciya, ta kwanga video call suke, ba tare da sun sam dare yayi ba.
Ƙarfe biyu da rabi lokacin ne Umma take sallar dare, ta fita alwala ta dinga jin maganar Yusuf ƙasa ƙasa, ta leƙa tagarsa ta hangoshi akan gadonsa ya tasa screen ɗin waya a gaba yana murmushi.
"Ki kwantar da hankalinki, Insha Allah zuwa jibi zanzo in ganki masoyiyata"
"Allah ya kawo ka lafiya, zaman kaɗaici ya isheni Yoseef, babu kowa a kusa dani fa"
"Ai mace miki zanzo insha Allah, inzo in ganki inji labarin da kike son gayamin, inji yadda akayi kika samu wannan tabon haka a jikin ki, ki kwanta kiyi bacci dare yayi fa"
Tace "ok come closer, hug me and kiss me, then we sleep together"
Yusuf yai murmushi yace "nayi missing ɗinki Widad, yai kissing ɗin screen ɗin wayar yana lumshe ido, ƙarshe ya kashe wayar ya ajiye, ya rungume pillow sosai a jikinsa yana lumshe ido.
Umma ta jinjina kai ga wuce banɗaki domin yin alwala.
Da safe Yusuf ya tashi yana ta nishaɗi kamar bashi ba, Umma tana kallonsa amma ba tace masa komai ba.
Ranar da yayiwa Widad alƙawarin ze je yana ta kallon agogo, yana zaune Umma ta sashi a gaba yaci Abinci, ya gama ci wayarsa ta fara ringing, sedai ba suna amma yaƙi ɗagawa, Umma tana kallonsa.
Can yace "Umma bari inje ɗaki zan kwanta bacci"
Umma tace "ɗakko pillow ka kwanta a nan"
Ba haka yaso ba, amma haka nan ya haƙura, ya ɗakko pillow ya kwanta a ɗakin Umman.
Aikuwa babu daɗewa bacci ya ɗaukeshi, saboda dama dare yake rabawa yana soyayya.
Umma ta ɗakko mafici tana masa fifita, Kasancewar an ɗauke wuta gashi ya fara gumi.
Sedai tun ba'aje ko'ina ba Yusuf ya fara surutan bacci.
"My Wife, kiyi murmushi mana yarinya fushi baya miki kyau fa"
Umma ta juya tana kallonsa, iya saninta dashi tun yana yaro ƙarami, baya surutan bacci, amma yau da ranar Allah yana bacci yana surutu akan wata.
Bata gama mamakin ba ya cigaba
"Baby ki dena kuka, bana so fa, kinga baki da lafiya, kuma Gwaggo yau zata kawo mana kunun tsamiya, ai zaki sha ko?"
Suleiman ne yai sallama a gidan, Umma ta amsa masa, ya shigo ya zauna yana faɗin "Lallai ɗan gata, yana bacci Umma na masa fifita, tashi c
Yai maganar yana taɓa Yusuf, Umma tace " ze tashi kuwa, yana mafarkin soyayya "
Suleiman yace " Soyayya kuma? "
" Eh mana, se surutai yake shikaɗai"
Suleiman ya daddaki Yusuf, Yusuf ya buɗe ido a hankali, ya tashi zaune yace "Yallaɓai dama kaine?"
"Eh nine, ka tashi ka shirya mutafi"
Yusuf yace "mutafi ina?"
Umma tace "gidansu Nurat zaka je, Munyi waya da Khalil bata da lafiya!!!"
Wayat Yusuf ta shiga ringing, ya kalli wayar lambar Widad ce, tana can tana jiransa
AMANA! AMANA! AMANACE!!!
DUK WANDA YACI AMANA, AMANA ZATA CISHI
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
158_159
Yusuf yace "Amma Umma, da wani guri nake son zuwa"
"zaka bijirewa umarnina ne?"
Yusuf ya girgiza kai, Umma tace "to tashi maza, jeka kintsa kazo ku tafi"
Jikin Yusuf babu daɗi, ransa sam ba daɗi yaje yai wanka ya shirya ya fito.
Umma tace "Suleiman, dan Allah ga Shi nan, ka tabattar yaje dan Allah ga kuɗi ku sai mata ko kayan marmari ne, aje a duba ta, gaida mai gaisheka ko baze amsa ba"
Yusuf dai bece komai ba yai waje, wayarsa na cigaba da ringing.
Suleiman ya fito ya shiga motar suka tafi, Umma ta maida Suleiman kamar ɗanta Yaya a gurin Yusuf, dan shima tana masa hidima shida iyalinsa, tunda yaita faɗi tashi akan case ɗin Yusuf.
Yusuf be kula Suleiman ba, gaba ɗaya ransa a ɓace yake, ya ɗakko wayarsa ya kira Widad, tana ɗagwa ta fara mita "Haba Yoseef, inata kiran wayarka kaƙi ɗagawa, na shirya ina ta jiranka fa"
Tai maganar cikin Shagwaɓa.
Yusuf yace "Am sorry, wata fitace ta gaggawa ta kama ni, amma idan na kammala zanzo insha Allah, ki kwantar da hankalin ki kinji my Wife"
Tace "to naji, ka siyomin abu me daɗi, ina jin kwaɗayi"
"To shikenan, zanje ƙauye in Hari tayi girki ta zubo in kawo miki"
A tare sukayi dariya, yace "shikenan sena zo"
Ya maida wayarsa ya ajiye, Suleiman yace "Yusuf zaka karya maganar Ummanka kaje inda Widad take kenan?"
Yusuf yace "yallaɓi, yakamata ka fahimceni Widad fa ita kaɗai take zaune a gidan nan, babu kowa kuma ina tare da Aurenta, duk haƙƙoƙinta suna kaina, Umma taƙi bani dama in mata bayani, bayan haka Widad tana buƙatar kulawa, duk ta kumbura saboda ciwon zuciya da hawan jini, kuma.. Kuma tana ɗauke da tsohon ciki fa" Yusuf ya ƙarasa magaanar cike da jin kunya da kuma damuwa.
Suleiman yace "hakane, yakamata ace Umma ta fuskance ka, amma tanaa gudun abunda ze sake kawo barazana ga rayuwarka ne, amma kabi a hankali, zata fahimta Insha Allah"
Yusuf yace "Allah yasa, amma ni batun Auren nam da Umma ta bijiro dashi, dan Allah Yallaɓi kasa baki, idan har nace zan Auri Nurat Widad zata rabu dani, kuma ina matuƙar son mata ta"
"Shikenan nagane halinda kake ciki, amma Nurat ma abun tausayi ce"
Yusuf yace "Nasani, badan kishi irin na Widad ba da zan iya auren Nurat, saboda tana sona sannan bata da wani aibu, sema nine nake da aibun da za'a gujeni saboda shi"
Suleiman yace " aibun me kenan?"
Yusuf yace "bakomai, manta kawai"
Suka cigaba da hirarsu, har zuwa gidan su Nurat.
Koda dukaje Khalil baya gida, megadi yaje ya sanar da zuwansu, aka musu iso.
Sedai Suleiman yace baze shiga ba sedai Yusuf yaje, haka kuwa akayi aka masa jagora har falon da aka saukesu wancan zuwa.
Yayar maman Nurat ce ta fara zuwa, Yusuf ya gaisheta cikin girmamawa, sannan ta koma ta turo masa Nurat.
Yusuf yana nan zaune yana sake kallon wayarsa, yana addu'a Allah yasa kar Widad tayi fushi, yaji ƙamshin turaren Nurat, ya ɗaga kai ya kalli Nurat, duk ta rame kallo ɗaya zaka mata kasan bata da lafiya, a hankali take tafiya tana ɗan lumshe ido irin na marasa lafiya, ta ƙaraso ta zauna a kan carfet.
Yusuf ya dawo kujerar da Nurat ke zaune a ƙasa, ya kalleta yace "Light Dama baki da lafiya?"
Maimakon ta bashi amsa se cewa tayi "ina wuni"
Yusuf yace "lafiya ƙalau, ya jiki ɗazu Umma ke gayamin ban sani bane"
"Jiki da sauƙi Alhamdilillah" ta faɗa tana rausayar da kanta ƙasa.
"Amma kin daɗe kina rashin lafiyar nan, meke damunki haka?"
Girgiza masa kai tayi tace "bakomai"
"ban yadda bakomai ba, ki gayamin meke faruwa ne?"
Kasa magana tayi, se hawaye da suka shiga zarya a fuskarta, ba tare da ta shirya zubarsu ba, dan tayi duk me yuwuwa ganin basu zuba ba, amma abun ya gagara.
Yusuf ya sakko daga kan kujerar, ya zauna a kan carfet ɗin yana kallonta, a hankali yace "Nurat, dan Allah kiyi magana mana, meyafaru?"
Shiru tayi ta ɗauke kai daga kallon inda yake, dan data kalle shi sonshi ƙara shigarta yake, da kuma kishinsa.
"Nur ko nine nayi miki laifi?"
Ta ɗago idanunta ta kalleshi na wani ɗan lokaci, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta, a hankali tace "Nagode sosai kazo ka dubani, nagode ka gaida Umma"
Ta yunƙura ta miƙe zata tafi, cikin zafin nama Yusuf ya miƙe ya riƙo hannunta, ta juyo tana fuskantarsa, ta kalli inda ya riƙe hannunta ta kalli Fuskarsa taji tamkar ta rungumeshi tayi kuka, ita dai a rayuwarta maza dayawa sun nuna suna sonta, amma bata taɓa jin ƙauna da soyayyar wani a ranta kamar Yusuf ba, zata iya cewa akansa ta fara Soyayya.
Yusuf yace "Nurat bana so in zama butulu, bana son zama ɗaya daga cikin masu butulci, ki gayamin me kike so? Meke saki kuka haka?"
Cikin sassanyar muryarta, me cike da karaya tace "bazan samu abunda nake so ɗin ba ai, dan haka babu buƙatar cigaba da ɓata lokaci gurin faɗa"
Yusuf yace "gayamin, ko mene ki faɗamin, me kike so?"
"Yusuf kai nake so, kaine Yusuf, ban taɓa so ba se akanka, ban san haka ake ji ba, sedai nasan bazan sameka ba, kamin nisa na har abada, nasan ko a mafarki Widad bazata yadda ka auri wata bayan ita ba, bayan haka ta fini komai, sannan ga abunda ke tsakaninta da mahaifina, ina ganin ƙiyayyata ƙarara a idonta, ga kuma bazan so ka dinga samun saɓani da mahaifiyarka saboda ni ba, dan haka ina muku fatan Alkhairi a rayuwar Aurenku me cike da alkhairi, Allah ya ƙara tsareku daga sharrin maƙiya, da mahassada nagode sosai Yusuf "
Gaba ɗaya jikinsa yai sanyi, sosai ta bawa Yusuf tausayi, tabbas Nurat ta cancanci a tausaya mata, da tausayi halin da take ciki a yanzu, amma yasan ko wace kalar wiwi yake sha, baze haɗa Widad da wata ba, saboda yasan azabar kishi irin na Widad, Nurat ta zare hannunta daga nasa ta koma ciki da sauri.
Jiki ba ƙwari Yusuf ya fito daga falon, ya nufi waje, Suleiman ya kalleshi yace "lafiya kuwa?"
Yusuf yace "Yallaɓai akwai damuwa"
"meyafaru"?
"Nurat sona take dagaske fa"
Suleiman yace "Au kaida baka san son naka take ba?"
Yusuf ya dafe kai yace "Yallaɓai, dan Allah kamin alfarma ka kaini in ga Widad, dan Allah bazan daɗe ba insha Allah"
Sulaiman yace "Shikenan, bakomai mije ina ne?"
Yusuf yai masa kwatance suka tafi, a bakin gate wani ɗan sanda ya taresu yace "ya akayi?"
Yusuf yace "a gayawa Widad Yusuf ne"
Ɗan sandan yai murmushi yace "Ohhh ashe megidane, ai tun ɗazu take jiranka"
Aka buɗe musu gate, Suleiman ya shiga da motar yana mamakin haɗuwa da tsaruwa gami da girman gidan.
Yai parking Yusuf ya fito daga motar, yace "Yallaɓai zo mu shiga mana"
Suleiman yace "Gurin budurwa ma ban bika ba se gurin matarka, a'a ina nan"
Yusuf kawai yai murmushi ya girgiza kai, ya shiga ya dinga duba falukan dake gidan, Kasancewar ya kirata bata ɗaga ba, can ya hangota a wani falo, tana zaune akan 3 seater, ta haɗe rai sosai, sanye take da dogon wando, da 'yar riga ƙarama, ta gyara gashin kanta ta saka ribbon saki ƙarshensa a bayan ta, hakan ya bawa cikinta damar fitowa sosai, abun mamaki ta saka jambaki da kwalli a idonta, abun da Yusuf be taɓa gani ba, sedai ta haɗe rai.
Yusuf ya ƙaraso inda take yana murmushi yace "farar mace alkyabbar mata, why are you sad? Ba gani nazo ba"
Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta mayar ta sunkuyar da kanta tana danna wayarta.
Yusuf ya ƙaraso ya zauna kusa da ita yace "bazaki ɗago in ƙare miki kallo ba?"
Matsawa tayi daga kusa dashi, ya kalleta cike da mamaki yace "lafiya kuwa?"
Ta ɗago tace "Daga ina kake?"
Yusuf yace "naje wani gurine shiyasa..
" Yoseef kasan bana son ƙarya fa, ina kaje? "
Maimakon yai mata magana, seya ƙura mata ido, ta saka idonta a nasa tace " Yoseef gurin Nurat kaje "
" waye ya gayamiki gurinta naje? "
" tunda ka cemin zaka wani guri, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, naji a jikina gurinta zaka je, kuma kana shigowa naji kana ƙamshin turarenta, Yoseef wallahi gurinta kaje"
Yusuf yace "lallai zuciyarki tana tare dani, dan ba tayi miki ƙarya ba, tabbas naje gurin Nurat bisa ga Umarnin Umma, naje na duba Nurat bata da lafiya, Widad, Nurat bata cancanci wulaƙanci ko banzatarwata ba, dukda abunda mahaifinta yayi, amma ta taka mshimmiyar rawa a gurin kuɓutata, kalli ta rasa mahaifiyarta, mahaifinta ya tafi prison, kuma a yau take gayamin tana sona, be cancanci in wulaƙatanta ba"
"Yanzu me kake so ka gayamin? Zaka Auri Nurat ne kokuwa?"
Tai maganar tana tsststare shi da ido, Yusuf yace "ni bahaka nske nufi ba, itama tasan hakan bame yuwuwa bane, amma yakamata itama a dubata, a tausaya mata, ta rasa kowa Widad ko ban Aureta ba bata cancanci wulaƙanci ba, ta temakeni kuma kin.....
Cikin faɗa Widad ta dakatar da shi, ta hanyar cewa " ni ka cikamin kunne da ta temakeka, ni wulaƙanta ka nayi? Ko kana zaton Nurat tana da abunda zata ja da Bukar Bulama ne? Kasan waye Bulama kuwa? Aiko mahaifinta da suke tare da Bulama, wallahi bashi da ƙarfin ja da shi, yana da arziki kuma goyon bayan manyan mutane a duniya ba ƙasa ba kawai, Yoseef Bukar yamin barazana ko inje kotu in bada sheda ko ya kashe Ummanka, ko kasan ba Nurat ce tai sanadin kuɓitarka ba Allah ne ya kuɓutar da kai, amma se da na bada kadarorina na miliyoyin nairori, aka siye mutanen Da Bulama ya siye, nasa aka ninka musu abunda ya basu, na ɗaukar maka babban lawyer wanda shine ya tsara komai? "
Ta ɗanyi shiru sannan ta kalli Yusuf, daya zuba mata ido tace "inda Bulama ya kaini ya ɓoye, akwai wata mata da take kula dani a gidan, wayarta nake karɓa inyi browsing inga yadda shari'arka ke gudana, katsam ta bar wayar a hannuna, ta tafi aikace aikacenta, ni kuma nayi recording a wayar, na cire memory card ɗin bata sani ba, na bata wayarta, na rubuta takadda na bata na nannaɗe memory card ɗin a leda, a cikin takadda, nace ta aramin dubu ɗaya taje ta samu shagon masu saida abubuwa ta basu, na bata ina addu'a Allah yasa saƙona yaje inda na tura shi.
Nayi rubutu ne, nace 'zuwa ga wannan takaddar taje gareshi, dan Allah ina neman Alfarma, ina son duk yadda za' ayi ledar dana aiko da ita, da abunda ke cikin ledar, a kaiwa Barrister Hafiz Mubi, ace masa inji Widad, sannan a karɓi dubu ɗayan hannun matar a bawa wanda ze kai yayi kuɗin mota, itakuma ace maya babu abunda na aikota ta saimin.
Shine aka karɓi saƙon, akace mata babu aiken da na mata, ta dawo ba tare da tasan mena aiketa ba.
Barrister Hafiz, ɗahane daga cikin lawyoyin Daddy, saƙon ya isheshi ya duba, shima na rubuta masa wasiƙa, nace ya duba cikin memory card ɗin, akwai saƙo ya duba.
A cikin audio na gaya masa yadda ze saida wasu daga kadarorina, ya ɗaukar maka lawyer, Kasancewarsa abokin Khalil ɗan uwan Nurat, a nan ya samu dama shima suka haɗu da wasu lawyoyin aka tsaya maka a shari'ar, badan kuɗin da na saki ba, da har yanzu ba'a ƙare shari'ar a haka ba, da kotu bazata wanke ka ba, harse an kammala shari'a dasu Bulama, sedai a bada belinka, amma daka motsa sekace Nurat ta maka halacci, kaje ka ƙarat kai da ita, kaje ka Auri Nurat"
Ta ƙarasa maganar tana kuka, ta tashi zata tafi, Yusuf ya riƙeta gam ya zuba mata idanunsa, taƙi kallonsa ta cigaba da kukanta, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nasa.
"Kinji nace miki zan auri Nurat ne?"
"Idan ma baka faɗa ba alamu sun nuna ai"
"kina so in saɓawa Umma, dukda tarin alkhairinta a gareni saboda ke? Idan nayi haka na kyauta? Kina ganin raguwar auren namu zata yi albarka ne?"
Widad ta girgiza kai alamar a'a.
Yusuf yace "ki bani lokaci, ina son in daidiata komai ne, amma sekin dena wannan koke koken, da tayarmin da hankalin sonake mubi komai a sannu, kinga ni duk ban san wannan ba se yanzu da kika gayamin, kiyi haƙuri kinji"
Ta zumɓura baki taƙi magana, hawaye na cigaba da fita daga idonta.
"bazaki dena kukan bane?"
"Nika ƙyaleni inyi dan haushinka nake ji" tai maganar tana basarwa
Yusuf yace "to shikenan, bari in tashi in tafi"
Sauri tayi ta riƙe shi tace "wallahi ka tafi sena bika"
"to goge hawayen nan maza"
Bata goge hawayen ba, ta kwanta a jikinsa tana sake tura baki gaba, kamar yarinya ƙarama.
Ya shafa gashin kanta yace "dama haka kike sona? Bani da bakin yi miki godiya, nagode sosai Babyna, Allah ya bani abunda zan mayar miki da kadarorinki bazan so ace kin rasa wani abu da kika mallaka saboda ni ba"
Widad tace "Dukiya ɗazu ce, ni kai ne a gabana Yoseef, bana kallon dukiya ni kai nake kallo kawai, zuciyata kai kawai take kallo, ni kai nake so fa, ni banyi dan ka biyani ba, ni tukucin zuciyarka nakeso kawai"
Tai maganar tana sake kwanciya a jikinsa tana kuka.
Ya rungumeta sosai a jikinsa yace "is ok my love, ki dena kuka na fahimce ki, in dai zuciyata ce kin samu I love you my wife"
Tace "I love you too Yoseef"
Ta maƙalƙaleshi tana lumshe ido, tana shaƙar ƙamshin turarensa daya kashe mata jiki sosai.
Yusuf ya shafa gashin kanta yace "kinyi kyau sosai masoyiyata, kamar in sace ki in gudu haka nakeji"
Widad tace "dan Allah mijina ka fahimtar da Umma, mu samu ta yadda mu rayu tare, Yoseef na yadda in rasa komai nawa in kasance da kai har abada, you are my world and happiness Yoseef"
Yusuf kasa magana yayi, se ajiyar zuciya da yake tayi, saboda yadda jikinsa ya mutu gaba ɗaya, ya dinga sauke ajiyar zuciya, can yace "My love ya babyna yake? Fatan baya wahalar min dake dai?"
Ta tura baki tace "gaskiya yana bani wahala, yaita kicking cikina, ko ya hanani cin Abinci"
"ki kwantar da hankalinki, lokacine ze dena insha Allah, zan masa faɗa ya dena wahalar min da babyna, ke dashi duk ina sonku sosai"
Widad ta tashi daga jikin Yusuf, ta kalli cikinta tana murmushi tace "kaji dai Abunda Dad ɗinka yace ko? Ka dena takuramin"
Yusuf ya ƙura mata ido sosai, ta ɗago ta kalle shi tace "lafiya kuwa? Wannan kallon fa? Ga fruit can a dining tashi muje ka bani abaki, nima in baka"
Yusuf ya girgiza mata kai alamar a'a, tace masa "why?"
Yace "that's not what I want"
'So what do you want? " tai maganar tana kallonsa.
" I want to kiss you, lips ɗinki sunyi kyau sosai da kika sa jambaki "
Murmushi kawai tayi ta ɗauke kai daga kallonsa, a hankali ya sunkuyo da fuskarsa dai dai tata yana mata wani irin kallo me wuyar fassara, a hankali yake mata numfashi a fuska, Widad kamar an sassaƙata ta kasa ko motsi daga inda take zaune, tana jin saukar numfashinsa a fuskar ta.
Rungumeta yayi yana kissing ɗinta, to show her how he misses her, and she responds to his message to show him that she also miss him, wayar Yusuf data fara ringing ce ta dakatar dashi daga abunda yake yunƙurin yi.
Sunan Umma ya gani akan screen ɗinsa, yaiwa Widad alama da tayi shiru, ya daidaita nutsuwar sa ya ɗaga wayar yace "hello Umman Yusuf"
Umma tace "kuna inane?"
"muna gidansu Nurat ne"
"bata wayar mu gaisa"
"Umma ai ta koma cikin gida, kin ganni a harabar gidansu, yanzu zamu taho da Yallaɓai"
Umma tace "to shikenan, ka hanzarta ka dawo, bana son ka dinga nisa sosai"
Yusuf yace "to Umma, Insha Allah gani nan dawowa"
Ya kashe wayar yasa a aljihunsa, ya kalli Widad dake kwance, ta ɗauke daga kallonsa yace "sweetheart am sorry, kiyi haƙuri zan tafi kar Umma ta gane nazo gurinki kinji"
Bata ce masa komai ba se binsa da kallo da tayi, ya saita nutsuwarsa ya miƙe ze fita, ya waigo ya kalleta yaga tana hawaye, ya dawo ya durƙusa ya riƙe hannayenta yace "kiyi haƙuri matata, Insha Allah na kusa dawowa gareki kinji, karki damu dan Allah kidena kukan nan haka, nafi ki buƙatar ganinki a kusa dani"
Ya share mata hawayen fuskarta, ya sunkuya ya sumbaci goshinta, sannan ya bar falon cikin hanzari.
Suleiman na ganinsa yace "kai haka mukayi da kai, daga zuwa ka ganta seka shige kayi zamanka kana soyayya ka shanyani, har Umma ta kirani a waya, na mata ƙarya ai muna tare a gidansu Nurat"
Yusuf yace "muje kawai, nima ta kirani karta gane naje gurin Widad"
Sulaiman yace "shikenan muje"
Tunda suka tafi Yusuf hankalinsa baya jikinsa, ya baro shi can a tare da matarsa, gashi yayi mamakin jin itace tayi me yuwuwa, da dukiyarta dan ganin shiya kuɓuta daga halin daya shiga.
Tunani kawai yake yi, Suleiman ya fuskanci hakan, dan haka yaita masa nasiha yana kwantar masa da hankali, amma sam Yusuf baya gane me Suleiman ke cewa.
A waje Suleiman ya ajiye Yusuf, shi kuma ya tafi, Yusuf ya shiga cikin gidan.
Ya shiga tare da sallama, Umma ta amsa masa tace "Yusuf kun daɗe fa, ya jikin Nuratun"?
Yusuf yace "da sauƙi, suna gaisheki?"
Umma tace "to Allah ya ƙara afuwa, amma ya na ganka wani iri? Akwai matsala ne?"
"A'a Umma, bakomai fa"
Umma tace "shikenan, ana daf da shiga sallar magariba, kai alwala ka tafi masallaci"
Yusuf yace "to Umma"
Ya shiga ɗakinsa, cike da tunani fal a zuciyarsa.
Dan kar Umma ta gane yana cikin damuwa, yasa yaje ya ɗauki Abincin dare yaci, Umma nata masa hira amma baya ganewa, se amsa mata yake da ummmm.
Ya tashi ya tafi ɗakinsa, yana zuwa beyi wata wata ba ya ɗakko waya ya kira Widad, sedai muryarta ƙasa ƙasa kamar bata da lafiya.
Yusuf yace "lafiya kuwa wife?"
"bakomai" ta bashi amsa
"Kiranki nayi muyi hira, kuma naji kamar ba lafiya"
"hirar da zata fi kowacce a gurina, itace ganinka a kusa dani, amma kamin nisa, ina ji ina gani ba yadda na iya, dukda son da nake maka"
Nan Yusuf ya kwantar da murya ya shiga aikin rarrashi, harta saki jikinta dashi, ta dena fushin suka koma soyayya, yauma seda suka sha soyayyar su, seda dare yayi sosai sannan suka kwanta bacci cike da begen junansu.
Umma tana monitoring ɗin Yusuf, ya dena zaman tsakar gida ko kuma hira da ita, kullum yana ɗaki riƙe da waya, da tayi zancen Nurat seya dinga basarwa, saboda haka ta zuba masa ido, sedai ta toshe duk wata hanya daze fita yaje yaga Widad, dan bata son ya kuma raɓar Widad yaja musu matsala.
Sosai fa Suke kewar juna shida matarsa, gashi baze iya bijirewa Umma ba, yana matuƙar tausayin Widad sosai, dan yadda suka yi waya yau ya gane bata da lafiya tana jin jiki sosai, ga babu hanyar fita, dan idan harze fita se Umma ta tambayi ina zashi.
Da Yamma Umma ta hanshi zaune yayi jugum, yayi shiru kamar wanda akayiwa mutuwa.
Ta kalle shi tace "Yusuf zo kaje ka siyo kayan miya, zanyi girki naga yamma tayi"
Yace "to"
Ta bashi kuɗi ta lissafa masa abunda ze siyo mata, sannan ta bashi dubu biyu tace "ga wannan ka riƙe a hannunka, kafin ka koma gurin aikin"
Yusuf ya karɓa yace ya gode, ya fita yin cefanen.
Umma tana ta aikinta a tsakar gida, taji anyi sallama, ta amsa tare da waigowa wanda ta gani ne yasata sakin tsintsiyar hannuta ta saki baki, tana kallonsa..
AMANA! AMANA!! AMANACE!!!
IDAN KIKA FITAR BADA IZININA BA, ALLAH YANA KALLONKI, KUMA KINCI AMANA
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
160_161
Umma ta bi mutumin da kallo kamar taga baƙuwar halitta, mutumin yace "Madam a bamu guri mu zauna mana, an tsaya ana bina da ido"
Jin yace a basu gurin zamane yasa Umma leƙa bayansa, taga mutumin tare da Widad a bayansa, take Umma ta ɗan tsuke rai.
Mutumin yace "Jidda wannan kallon fa? Ki bamu gurin zama mana"
Umma tai musu jagora zuwa falonta, taje fridge ta kawo musu ruwa da lemo, Widad tace "Umma ina wuni"
Umma ta amsa sama sama, Mutumin yace "Jidda dama rai kanga rai? Rabona dake tun kina budurwa, ban sake sanin inda kike ba, se kwanan nan naji ashe Bashir Maitama ne mijinki, Allah ya jiƙansa da Rahama"
Umma tace "Ameen ya Allah, kwana ba adadi Alhaji Ahmad, dan yanzu sedai ince Alhaji ka ƙara ƙiba, kamar ba kaiba kamaninka sun canza saboda kuɗi sun zauna"
Alhaji Ahmad yace "bari Jidda, abubuwa duk se godiyar Allah kawai"
Ya juya ya kalli Widad yace "daughter na, wannan ce sirikar taki"
Widad ta jinjina kai, Ya kalli Umma yace "dama kece sirikar tamu kike wahalar min da 'ya?"
Umma tace "kamar yaya kenan?"
Alhaji Ahmad yace "to a al' adar Hausawa dai, namiji ke zuwa biko, to hula taja ɗankwali, munzo muyi bikone, dan Allah a temake mu a bamu mijin mu mana, ayi mana afuwa"
Umma tace "wai ya akayi ta zama 'yarka kuma? Kuma ni gaskiya ina tsoron abunda ze biyo bayane, ni inajin tsoron ɗana ya sake shiga matsala gaskiya"
Alhaji Ahmad yace "labarin dogone, amma dan Allah ayi haƙuri a bamu mijinmu, zamuyi miki bayanin komai, amma waini ina sirikin nawa yake nema? A nunamin shi in ganshi, inga ya yake a yanƙwanamu akansa haka?"
Umma tace "A'a ba wani na musamman bane, kawai ni bana son ɗana ya sake shiga matsala saboda itane, ya wahala fiye da tunaninka, duk saboda ita, wahalar da akayi a baya Allah ya amfana"
Yusuf ne yayi sallama, hannunsa ɗauke da ledar aiken da Umma tayi masa, ya shigo falon cikin nutsuwa da sallama, sedai yana ganin Widad a zaune gabansa ya faɗi, ya ɗan tsaya yana kallonta, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
Yusuf ya durƙusa ya gaida Alhaji Ahmad, Alhaji Ahmad ya amsa yana ƙarewa Yusuf kallo, yace "iko se Allah, lallai dole a mana jan aji akan wannan zuƙeƙen matashin, Widad banga laifinki ba da kikabi kika ɗaga hankalinki akan mijinki, dan an ganshi kyakkyawa shine ake wani jamana Aji"
Yusuf ya ɗanyi murmushi, yana son sanin waye wannan mutumin da suka zo tare da Widad?
Yusuf ya maida kallonsa ga Widad, ya ɗan kashe mata ido, amma ta haɗe rai tana ƙoƙarin maida ƙwallar idonta, girgiza mata kai Yusuf yayi, ya ɗakko handkerchief ɗinsa, ya faki idon Umma, ya miƙawa Widad, Alhaji Ahmad suna magana da Umma, amma hankalinsa yana kansu Yusuf.
Yusuf ya miƙe ze bar falon, Widad tabi Yusuf da kallo, kamar zata cinye shi.
Alhaji Ahmad ya kalleta yace "Widad ɗan bamu guri, maza tashi ki bishi, ai tunda Allah yasa munzo se Jidda ta bamu mijinmu, an dena wahalar min da 'ya dan anga yana da kyau, nasan dai' yata tafi shi kyau"
Umma tayi murmushi, Widad kam cikin hanzari ba kara ba kunya, ta miƙe yabi bayan Yusuf, yayin da Umma ta jinjina rashin ta ido irin na Widad "
Suna fita Yusuf ya janyota gefe yace " sweetheart, waye wannan mutumin ne? "
" Nima ban sanshi ba"
"Are you serious?"
"dagaske nake" ta bashi amsa
"Amma ya akayi kuka zo tare?"
"Nifa ban sanshi ba, ya cemin yasan Ummane, nazo mu bada haƙuri"
Yai murmushi yace "shikenan naji, zomuje ɗakina muyi hira kafin su gama maganar"
Widad ta zaro ido tace "haka kurum, Umma tace bani da kunya, ni a nan zan zauna"
Ya shimfiɗa musu dadduma, suka zauna hirarsu suke kawai kamar babu abunda yake damunsu, Umma ta fito ita da Alhaji Ahmad, Alhaji Ahmad yace "Widad taso mutafi, se Allah ya kaimu weekends ɗin"
Widad ta tsaya tana kallonsa, kamar bata gane me yake faɗa ba.
Ya sake maimaita masa maganar, amma Widad taƙi motsawa.
Yusuf yace "ki tashi ku tafi mana"
Aiba kunya Widad ta noƙe kafaɗa, alamar ba inda zata je.
Alhaji Ahmad yace "iko se Allah, kiyi haƙuri kizo mutafi, idan Allah ya kaimu Weekend zamuyi tafiyar nan, kuma ina lallaɓa sirikata mu, dan haka kiyi haƙuri za'a baki mijinki"
Widad tace "dan Allah ni ka ƙyaleni a nan, wallahi bana son zaman gidan nan nika ɗai, damuwa damuna take, dan Allah ka barni a nan zuwa weekends ɗin mu tafi ta nan gaba ɗaya"
Alhaji Ahmad yace "Ikon Allah to sirkarmu kinji abunda tace, bakomai ta zauna ɗin a nan, zuwa Allah ya kaimu weekends ɗin?"
Umma tace "toni me zance, in dai gidane gashi nan ta zauna, sedai mu bamu da Arziki ba lallai muna da abubuwan da take buƙata ba"
Yusuf a ransa yace "Umma da kin san a ƙungurmin ƙauyen da muka zauna, da baki faɗi haka ba"
Widad kam cewa tayi "Ni dai zan zauna a nan"
Alhaji Ahmad yace "toke yanzu gashi baki ɗakko kayanki ba, a haka zaki zauna ɗin?"
Widad tace "zamuje da Yoseef in ɗakko"
Alhaji Ahmad yace "ina ganin ƙauna, ikon Allah dan Allah Jidda ayi haƙuri idan muka dawo daga tafiya Yusuf ya koma ɗakinsa"
Seda Umma tayi dariya, jin abunda Alhaji Ahmad ya faɗa, gaba ɗaya suka raka shi har bakin mota ya tafi, sedai tafiyarsa babu wuya aka girke 'yan sanda a bakin layin su Yusuf dan basu tsaro.
Mutanen layin sunata gulma dan sunga an kawo' yan sanda layin, wataƙila Yusuf aka kuma zuwa kamawa, tunda yai wannan laifin unguwarsu bata rabo da 'yan sanda.
Yusuf yana son ya keɓe da Widad suyi hira sosai, amma kunyar Umma yake ji sosai, Umma kam basar dasu tayi kamar bata san da zamansu ba, sabgogin gabanta kawai take yi.
Bayan sallar magariba Yusuf ya dawo daga masallaci, Widad tace "Yoseef nayi waya gida, Nura zezo da mota muje farm House mu ɗakko kayan.
Yusuf ya kalli Umma, amma yaga basu take kallo ba.
Ba daɗewa sega Nura direban Daddy ya ƙaraso, Yusuf yaje ya samu Umma yace " Umma zan raka Widad ta ɗakko kayan ta "
Umma tace "sekun dawo"
Sam Yusuf baya jin daɗin yadda Umman keyi, duk se yaji ya damu ya tsargu sosai, baya jin daɗin hakan sam.
Widad ta saka takalmanta tayi waje, Yusuf yabi bayan ta, suna zuwa Nura ya buɗe mota ya fito yana, jinjinawa Yusuf hadda duƙawa yana "Allah ya temaki me gida, Allah ya tsare gabanka da bayanka mijin Hajiya Widad, siriki ga Alhaji Nasir Daula"
Yusuf yai murmushi yace "Nura karka bani kunya mana dan Allah, ni nayi laifi ma, tunda aka sakeni, ban samu nazo mun gaisa na muku godiya ba, saboda bana son sake zuwa gidan nan ne, amma ina godiya Nura"
Yai maganar yana miƙawa Nura hannu su gaisa, Nura ya zare ido yace "wane talaka haɗa hannu da kai yanzu? Ai sedai ai muku gaisuwa irin taku ta manya"
Yusuf yace "dan Allah Nura ka bari, bazanji daɗin haka ba, ka barni a Yusuf direba na kawai"
Widad tace "aikuwa naga wanda ze kiramin miji da direba, yaga yadda zanyi dashi, koda yake ni kaɗai zan dinga ce masa direbana"
Sukayi dariya gaba ɗaya, Widad ta ɗakko ƙaramar jakarta, ta ɗebo kuɗi ta miƙawa Nura tace "gashi nan, ka hau mota ka koma gida, bawa Direbana mukullin, zamuje yawo tare"
Yusuf yai murmushi yace "Yarinya ki cigaba da cemin direba, idan na kaiki bazan dawo dake ba"
"kai ka isa"? Tai maganar tana kaimasa dukan wasa a ƙirjinsa, Yusuf ya karɓi mukullin motar suka shiga suka tafi.
Nura kuma yai ram da kuɗin da Widad ta bashi, dan kuɗin yafi ƙarfin dubu Ashirin, yana tafe yana mamakin yadda Widad ta canza gaba ɗaya, ga kuma ga dukkan alamu ba ƙaramin so takewa Yusuf ba.
Haka ya isa gida yana wannan mamakin da tunani, Isa yace "ha na ganka kao kaɗai? Ina motar da kuma gimbiyar Daula?"
Nura yace "barni inyi mamaki Isa, gaskiya gimbiyar Daula ta canza, kaga wasa da dariya?"
Isa yace "na gani ranar data zo nan kam"
Nura yace "mhmmm, na yadda dare ɗaya Allah kanyi bature, nikam dama can Gimbiya bata son Yusuf kuwa, tunani nake yadda ko a baya da yana direbanta, tana masa wulaƙanci son ranta amma bata yadda wani ya taɓashi ba, kai kaga soyayya, motar suka karɓa wai zasu unguwa, Allah sarki dafa a cikinmu yake, amma Allah ya tsame shi ya auri 'yar masu gida, shikenan Allah ya masa sitirar arziki, dan ynzu yayi hannun riga shida talauci, da Daula yana da wata' yar nima se ince inama inama"
Isa yace "Inama me? Kana ganin baƙar azabar da ya sha, kafin ya kuɓuta, ni mamakin da nake ya akayi sukayi auren ne?"
Nura yace "kanaji ana gayamaka, Saleh ne ya kuɓutara dasu, ya kaisu wani ƙauye aka ɓoyesu, kasan ta bata da yadda sam, taƙi yadda da kowa seshi, kuma ance lokacin bata da lafiya sosai, tace bame kula da ita seshi, shine fa sukayi Aure a can, daga nan kuma abu ya zame masa silar Arziki, dan nasan yanzu ita da abunda ta mallaka yana da iko dasu, dama ka santa ga kyauta, gaskiya ze warwasa, inama inama nima ace in samu dama haka ko bata kai kamar tasa ba"
Isa yace "ga Amal, ka lallaɓa da ita mana"
Nura ya haɗe rai yace "Agolar? Uwar me taci balle ta bani, suma yanzu suna fama da kansu, sun saida koma, komai ya ƙare musu, an kashe babban ɗa, uwa ta tafi hannun hukuma, ita wannan ga rashin lafiya, waccan ga shaye2, komai ya ƙare, ni nayi mamaki ma da Gimbiya ta ƙyalesu har yanzu zaune a cikin gidan nan, ai dama shi ramin mugunta idan zaka ginashi, seka gina shi gajere, dan wataƙila kai zaka faɗa "
Isa yace " babu wanda yafi bani mamaki, se Alhaji Bulama ubangiji Allah yayi mana tsari da azzalumai kamarsa, yanzu duk yada yake da Daula, da soyayyar da yake nunawa Daula, ashe azzalumi ne mufuki, na ƙaryane zagon ƙasa yake masa, gaskiya mun shiga haƙƙin Widad na ganin aibunta, ashe tana da dalili akan ƙin mutane, ji wannan asara fisabilillahi "
Nura yace " bari kawai Isa, duniya babu gaskiya, mutane mun lalace se fatan shiriya, amma tabbas gaba ɗaya mutanen nan sunyi tarayya a cikin ƙaddarorinsu, Alhaji Daula, 'yarsa da kuma Yusuf daya shiga rayuwarsu daga baya, sedai fatan Allah yasa bakin wahalrsu kenan, kuma Allah ya bayyana Alhaji Daula "
Isa yace " Ameen ya Allah "
Yusuf da Widad kuwa, seda suka sha yawonsu a gari, sannan ya kaita suka ɗakko kayanta suka dawo gida.
Ɗakin Umma ya kai akwatin kayan nata ya ajiye, ita dai UMMA bata tanka musu ba, tana ganin Yadda suke rawar kai akan junansu, da nan nan da juna cike da tsantsar kulawa da soyayya.
Yusuf yace "Umma kinci Abincin dare ne?"
Umma tace "eh naci, ga naku can a flask"
Yusuf ya ɗakko flask ɗinAbinci ya kawo, tuwon Alkama ne miyar kuɓewa Umma dafa, Yusuf yana zubawa Widad kamar zata shiga cikin kwanon, saboda yadda yawunta ya tsinke.
"Yoseef dan Allah ka zuba da sauri mana, kana yi a hankali fa, kuma ni sonake inci"
Tai maganar a ɗan Shagwaɓe, Yusuf ya kalli Umma, amma yaga hankalinta baya kansu, kuma tana jin taɓarar da Widad ɗin keyi.
Yusuf a hankali yace "bazanyi saurin ba"
Ta harari Yusuf tana tura baki, ya zuba mata tuwon nan, miyar ta sha kifi, ya samat man shanu, yadda Widad ta duƙa tana zuba tuwon nan yafi komai bawa Yusuf mamaki, ci take kawai ko magana ba tayi.
Yusuf yace "wai baki ƙoshi bane har yanzu?"
Widad tace "wallahi ban ƙoshi ba, rabona da Abinci inci cikakken Abinci cikin kwanciyar hankali, tun ranar da muka baro ƙauyen nan, bana samun Abinci inci, ga Abincin yayi daɗi Sosai"
Yusuf yace "ikon Allah, yanzu ke tunda kike gurin Bulaman bakya cin Abinci?"
Widad tai murmushi me ciwo tace "Yoseef, bana son tuna abunda ya riga ya wuce, ban zaci zan kuɓuta ba, na sha wahala fiye da tunaninka, banda duka da baƙar azabtarwa ba abunda nake sha a hannunsa, ga ɗansa kuma Fahad, daya dinga nema yaci zarafina, bana samun abunda nake so inci, komai bayamin daɗi, shiyasa na masa wannan tabon da wuƙa a fuskarsa, ko zan rage raɗaɗin abunda yayi min"
Gaba ɗaya jikin Widad yai sanyi tace "ƙaramin tuwon nan, yunwa nakeji ban ƙoshi ba"
Ya sake zuba mata, ta dinga cin abunta, ba wata kunya ko kara seda taji tayi ƙyat babu sauran gurin zubawa sannan ta haƙura, ta tashi taje fridge ta samo ruwa me sanyin gaske, ta zauna ta sha abunta ta wanko hannunta tazo ta zauna tana hutawa.
Yusuf yace "Sannu da aiki"
Widad tai murmushi ba tace komai ba.
Abincin data cine ya fara taso mata, tai shiru ta kasa magana, Yusuf ya zuba abunda ta rage yana ci.
Cikin hanzari Widad ta tashi ta fita, ta dinga amai, seda ta amayar da duk abunda taci, Yusuf yabi bayan ta da sauri.
Tayi amai sosai, Yusuf ya temaka mata, ta gyara jikinta ta kuskure bakinta.
Umma ta fito daga ɗaki tace "garin yaya take amai haka? Ko bata da lafiya ne?"
Widad tace "A'a Umma, lafiyata ƙalau"
Yusuf yace "inaga ko over feeding ne da tayi"
Umma tace "in ba hali, ko Asibiti zaka kaita saboda dare"
Widad tace "A'a, base munje Asibiti ba, ya lafamin ma"
Umma tace "shikenan, kije kwanta ki huta"
Widad taje ta canza kayanta, zuwa na bacci ta sake burma ƙaton hijjabinta, ta nemi guri ta kwanta a ƙasan carfet.
Umma ta shigo ɗakin ta ga Widad a kwance a ƙasa tace "tashi ki hau kan gadon mana"
Widad tace "A'a Umma, bana jin daɗin kwanciyar kan katifa, bayana ciwo yake nafison kwanan ƙasa"
Umma tace "shikenan"
Widad dukda basar da ita da Umma take, amma taji daɗin ganin yadda Umman, ta nuna mata kulawa.
Umma taje ɗakin Yusuf tace "bani bargonka guda ɗaya, a shimfiɗa nata tace bata son kwanciyar kan gado"
Yusuf yace "yawwa Umma, naji ana cewa za" ayi tafiya da weekend, amma ina za'aje ne? "
" ban sani ba, meya hana ka tambayi matarka? Bani bargo ni"
Yusuf ya miƙa mata bargon, ya ja bakinsa ya tsuke.
Umma ta gyarwa Widad gurin kwanciya, ta kwanta.
Nurat kam gaba ɗaya damuwa ta addabeta sosai da sosai, bata jin daɗin zaman gidan gaba ɗaya, gashi ta saka duk mutan gidan a damuwa, ganin yadda taƙi sakin jikinta, Nurat tai tunani taga damuwa bazata maganta mata abunda ke damunta ba, ta tashi ta fito falon gidan.
Ba kowa a gidan, duk ma'aikata ne sun tafi gurin aiki, ƙannen Khalil kuma duk suna kudancin Nigeria suna karatu.
Nurat ta gyara ko'ina na gidan, tayi girki yaje tai wanka ta dawo falo tana kallo, duk a ƙoƙarin ta na kauda damuwar dake ranta.
Wajen ƙarfe biyu Khalil ya dawo gida, ganin Nurat a falo tana kallo yasa yaji daɗi, ba kamar da ba da kullum tana ɗaki, ya ƙaraso yana mata murmushi yace "Sisyna, masha Allah, wannan kyau haka"
Tai murmushi taje ta karɓo kayan hannunsa, tana masa sannu da zuwa tana masa murmushin nan nata me ɗaukar hankali.
Yaji inama ace matarsa ce.
Nurat tace "Sannu da zuwa, kaje kai wanka kazo yau nina yi girki kaci Abinci"
Khalil yace "ashe yau da shagali, zanci Abincin 'yar auta"
Nurat tai murmushi, taje ta kai masa kayan ɗakinsa, dake kusa da falon.
Bayan yayi wanka yai salla, ya fito ya zauna a falo yana jiranta, ta shigo da sallama hannunta ɗauke da kulolin Abinci, ta tarar da Khalil ya zubawa wayarsa ido.
Nurat tace "inyee, da alama wannan matashin barrister ya shiga soyayya, hoton wa ake kallo haka?"
Ya ɗago ya kalleta yace "kalleki, wai hoton wa nake kallo, niwa zan kalla"
"Nifa dama baka taɓa nunamin budurwarka ba, gaskiya yakamata kayi aure haka, haba seka zama tuzuru tukuna, dan kaga Mama ta shagwaɓaka ne, da Abincin ta, ta koraka bakin gate a maka ɗaki, sannan a dena baka abinci zakayi aure"
Khalil yace "kice azabtar dani za'ayi kenan? Hmm ni tsoron matan yanzu nake Nurat, soyayyar gaskiya tana wahala, shiyasa ni ban taɓa budurwa ba"
Nurat tace "No akwai soyayyar gaskiya mana, kai dai kawai kace tsoron 'yan mata kake yi, you can't toast a lady"
Tai maganar tana dariya, Khalil ya girgiza kai yace "Eh naji ɗin, yanzu dai in kin matsu inyi Aure ki samo min budurwa, sannan ki dinga rakani zance"
Nurat tai murmushi, seda fararen haƙoranta suka bayyana tace "ba budurwar da zata aureka kuwa a haka, in dai sena raka ka zance"
Ta zuba masa Abinci, yanaci yana kallonta, yana jin kamar ya gayamata yana Sonta, sedai yasan zuciyarta tana tare da Yusuf.
Da Safe Widad ta tashi, Umma tana bacci ta tafi ɗakin Yusuf, yana kwance yayi ɗai ɗai akan gado, yana baccinsa.
Ta kalli ɗakinsa, ɗakin tsaf dashi, kamar ɗakin wata matar ga Mirror, da gado wardrobe komai tsaf dashi.
Ta ƙarasa kan gadon nasa, ta zauna ta ƙura masa ido, Wani murmushi take ganin yadda yake baccinsa hankali kwance, kamar wani jariri ya ɗan ciko daga ramar da yayi, sedai shima jikinsa duk tabon duka daya sha a prison.
Hannu ta kai tana shafa gefen fuskarsa, tai ƙasa sa muryarta tace "Hubbyna ka tashi muna jin yunwa fa"
A hankali ya buɗe ido ya kalleta yace "ke kin fiye takura, haba Babyna wace irin yunwa ƙarfe shida na safe?"
Cikin shagwaɓa tace "ni dagaske yunwa nakeji, ka tashi yunwa nakeji"
Yusuf ya noƙe kafaɗa, yana ɗora kansa akan cinyarta yana lumshe ido.
"Wallahi idan baka tashi ba, zan zauna se Umma tazo ta gamu a nan tare"
Ba shiri Yusuf ya miƙe zaune, yace "rufamin Asiri, tashi muje"
Widad ta dinga dariya, har sunje bakin ƙofa, ya juyo ya kalleta ya rungumota jikinsa yai kissing ɗinta yace "good morning"
"Morning, ka tashi lafiya?"
"Alhamdilillah, ya babyna?"
Tace "yana nan yana jinka"
Yai murmushi, suka fito tare suka shiga kitchen.
Suka feraye dankalin hausa tare, suka dafa tea, suka shiga suya Tare, hirarsu kawai suke kamar suka ɗaine a gidan.
Yusuf so yake ya saki layi, amma Widad na kakkarewa tana hanashi.
Umma kuwa tuni motsinsu ya tashe ta, amma bata fito ba karta takurasu, suka gama sukayi wanke wanke suka gyara komai tsaf.
Widad na shiga ɗakin ta tarar Umma ta tashi, Widad tace "Umma ina kwana"
Umma tace "lafiya ƙalau, ya jikin naki?"
Widad tace "naji sauƙi"
Umma tace "Allah ya ƙara sauƙi"
Duk yadda Umma take basar da Widad, Widad bata nuna mata taji haushi ba sam, tana girmamata sosai, sedai bata iya kara ta ɓoye soyayyarta ga Yusuf ko a gaban Umma ne
Wajen ƙarfe goma na safe, ciwon ciki ya kama Widad, tun tana mazewa seds Umma ta gane.
Lokacin Umma ta aiki Yusuf, baya gidan amma ganin Yadda Widad ke murƙusus yasa Umma ta kira shi a waya.
Da hanzari ya dawo gida, ya tarar Da Widad ta durƙusa tana kuka, se numfashi take da ƙyar.
Yusuf ya ɗagota yace "Widad, lafiya kuwa?"
"Yoseef cikina, ciwo yakemin"
"Wai anya ma kina zuwa Asibiti awo?"
Umma tace "Awon me kuma?"
Ɗan dirircewa Yusuf yayi, dan Umma bata san da ciki a jikin Widad ba, saboda kullum cikin zumbulelen hijjabi take.
Yusuf yace "ina nufin, taje likita ya ganta"
Umma ta tashi, taje ta ɗaga Widad daga jikin Yusuf, ta kwantar da ita akan pillow, tace "naga da mota a hannun ka, jeka ɗakko kazo a kaita Asibiti ko ɓarine"
Yusuf yace "Umma ba ɓari bane"
Umma tace "kamar yaya?"
Widad cikin kuka take cewa "Umma cikina, zan mutu"
Widad ta haɗa gumi sosai Umma tace "kiyi ta ambaton Allah, kidena kuka"
Widad ta kwanta rigingine, tana jujjuya kai, hakan ya bawa cikin nata damar fitowa sosai, Umma tayi mamakin ganin cikn nan, kenan dama da cikin aka kamosu?
Umma tace "to ko haihuwa ce?"
Widad ta girgiza kai tace "beyi wata shida ba, Allah yasa ba zubewa zeyi ba"
Yusuf dai haka ya ɗakko mota, suka sa Widad a ciki zuwa Asibiti.
Ta sha wahala sosai, seda suka wuni a Asibiti, likita ya tabattar musu da cewa allurar zubar da ciki da aka dinga mata ce take bata wahala haka.
Yusuf yace "Widad meye ya haɗaki da allurar zubar da ciki?"
Widad tace "Bulama, shine yasa aka dingayi min tunda akace masa ina da ciki, Amma dai cikin yana nan ko likita? Bana son in rasa shi dan Allah"
Likitan yace "ki kwantar da hankalinki, bakomai cikinki yana nan lafiya"
Haka nan Umma taji Widad tana bata tausayi sosai, mussman da taji tace allurar zubar da ciki aka dinga mata.
Se bayan ƙarfe goma na dare suka koma gida.
Bulama yasha matsa sosai, dan gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, a hankali yake ta faɗar da wanda yake haɗa baki ana cutar Daula, ga HIV ta fara nunawa a jikinsa, gudawa yake ba ƙaƙƙautawa, ga zazzaɓi me zafin gaske da yake fama.
Ya kalli 'yan sandan dayake hannunsu yace "Ranka ya daɗe, yakamata fa ace an barni naga lawayerna, dan har yanzu ba' a tabattar da laifin da ake zargina dashi ba"
Ɗan sandan yace "ka makara, dan baka da wannan damar kaima, kamar yadda ka siye wasu daga cikin hukumomin tsaro akayi maka yadda kake so a wancan karon, to yanzu an siyesu, ninkin yadda ka siyesu, kuma anace kar a sake a baka duk wata dama ko kwatankwacin ƙofar Allura ce, dan haka karka yi zaton zakayi free, kaida 'yanci har abada daga kai har muƙarrabanka!!!
AMANA! AMANA!! AMANACE!!!
DUK WANDA YA FITARMIN YACI AMANA
AYSHERCOOL
07063065680
12/9/21, 2:40 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
166__167
Gaba ɗaya a razane suka kalli Bulama, ya cigaba da cewa "bayan ya kashe Huda, shine ya ambaci sunana har Widad taji, da niyyata har ita a kashe, bayan ya kasheta ne, a gurin zaman makoki Widad ta tonawa Bala asiri a gaban Wannan ɗan sandan, shima na faɗi na tashi na saka aka kashe shi!"
Yusuf ya rintse ido, yana jin kamar Bulama yana rura wuta a zuciyarsa.
Bulama ya cigaba da cewa," daga nan na lallaɓ Saleh, akan ya saki Halima, akwai kaso me tsoka daze samu idan harya sake ta ta aureka, dama ba iya kula dasu yake ba, dan haka ya amince dan yaji batun kuɗi, ya sake ta ko idda batayi ba, na dinga tura ta a gurinka, har seda ka amince da Aurenta, ka kuma ɗauki ɗawainiyar yaranta, ta aureka dan ta dinga tatsar mana kuɗi a gurinka.
Da kuma saka ido, domin mu samu ta karɓo mana wannan dukiyar daga hannunka, na saka aka dingayi wa 'yarka Allurar mahaaukata, saboda kar ta tona min Asiri, kuma inyi amfani da damar idan ta haukace ko Allah zesa in samu inda dumiyar nan taje, amma a banza, na dinga tura maka saƙonni kala kala, na razanarwa akan dukiyar nan, na dinga farmakar ka kaida' yarka da barazanar kisan kai, sannan duk wanda yai yunƙurin raɓarku koku raɓeshi, se shime in farmake shi, na taka rawar gani akan AƘIDAR 'yarka, dana ga hakan bzata yuwu ba, na koma ma baka shawarar ka aurar da ita ga ɗana Fahad, hakan zesa ta canza halaye, amma a zuciyata ina son ta auri Fahad ne dan idan bamu samu waccan dukiyarba, mu gane zunzurutun dukiyar da ka malllaka mata, duk wani meeting da yadda za'a karɓi dukiyarka da matarka mukeyi, watarnma se cikin dare a hotel haka muke meetings ɗin, bazan ɓoye maka ba Daula, tunda komai yazo ƙarshe wallahi ban taɓa sonka ba, na tsaneka ko ganinka nayi cikin walwala se inji kamar in kasheka in huta, kafini komai bana appreciating duk wani goodness ɗinka, burina kawai inga bayanka hankalina ya kwanta, saboda ganinka a raye ma bana ƙaunar yi "
Daula ya sunkuyar da kai, hawaye na bin idonsa, Alhaji Ahmad yace" kaiconka Bulama, kayi asara Nasir da dukiyarsa, da ƙarfinsa haka ya dinga maka wahala kai da iyalinka, ka kawo wasu ma cin arziki, kuma ya musu, amma ƙarshe ga inda ciwon hassada ya kawoka, to ina maka Albishir dukiyar da kake hari, ga me ita nan"
Ya nuna Yusuf, sannan ya ci gaba da cewa "dukiyarsa ce, shine ɗan Yusuf yayan Nasir, wanda kasa rai akan lallai seka karɓi dukiyar, ka azabtar dashi da ahalinsa saboda abun duniya, yadda kazo a banza haka zaka koma a wofi, sannan duk wata kadara indai ta Nasir ce, zamu karɓeta har gidan da kake ciki da motoci, da kamfanin daya ɗora kka akai ka maida shi naka, sannan kema Halima da kika dinga siyar da kadarorinsa, bayan wanda kika ci a baya, da wanda kika dinga sata, duk wanda kika siyarwa da wani abu ya sai aikin banza, zasu iya yin shari'a daku ku biyasu dukiyarsu, sannan bisa ga adalci na Nasir, yace "ze baku duk wata dama a shari'a, baze amfani da dukiya ba ai muku hukuncin daya dace daku akan kisan kai na matarsa, da kuma garkuwa da kuka yi masa da yaransa"
Widad fuskarta sharkaf hawaye tace "Nikuma zanyi Amfani da ƙarfin dukiya, ayi masa irin shari'ar da yai amfani da kuɗi akayiwa mijina, kaiconka Bulama daga kai har 'yar uwarka da sauran mutanen da suka zaluncemu, kuda Allah"
Ana cikin haka aka tankaɗo Abbas ma, Ya kalli Yusuf, Yusuf ya kalle shi, Abbas ya fashe da kuka yana faɗin "dan Allah Yusuf ka yafemin, na biyewa Zuciya da son abun duniya na aka haɗa kai dani aka cutar da kai, dan Allah Yusuf ka yafemin"
Yusuf ko kallonsa beyi ba, yai waje da sauri, yana tuna shima irin yadda ya amince da Abbas, be taɓa aboki kamarsa ba, amma yai masa wannan muguntar.
Su Alhaji Ahmad ma sukayi waje, daga gurin, su Alhaji Musa suna ta salalami dan sun san tasu ta ƙare, ga jikin girma dama kuɗine yasa ba'a gane tsufan nasu sosai, yanzu kuwa kam se cituttukane ke kunno musu kai kala kala.
Wani ɗan sanda ya biyo bayansu Daula yana musu bayani "To yallaɓai har yanzu muna nan munata tattara bayanai, da bincike akan wannan baƙin azzalumi da duk wanda ya haɗa kai dasu, kama daga yadda suka haɗa baki da megadinka, wani Bala zuwa yadda yasa aka kashe shi a gidan yari, da duk wani wanda yake da hannu muna ta kama mutane ɗaya bayan ɗaya, kuma ba da daɗewa ba zamu gurfanar dasu a gaban kotu insha Allah "
Alhaji Ahmad yace " Masha Allah, yayi kyau sosai wannan shine wanda aka bawa aikin dana bayar, Bulama sukayi amfani da wannan damar wajen cinma burinsu"
Widad ta kalli Alhaji Ahmad tace "wane aiki kenan?"
Alhaji Ahmad yace "Aini koda bama tare da Daula, ina bibiyar al'amarunsa, kuma haka nan nake zargin Bulama zata iya kasancewa da hannunsa a masu yiwa Daula barazana, dan tuni ns gane dukiyarsa yakewa, sedai a lokacin son Bulama ya rufewa Daula ido, baya ganewa, ina jin duk labarin yadda kike bakya sakewa da mutane, da larurar taɓin hankali da kuma bibiyarki da ake akan wannan dukiyar, ni kuma na saka ayi bincike akan me bibiyar taku, sannan a baki tsaro ba tare dake ko mahaifinki wani ya sani ba, sedai ban san yadda akayi Bulama yasan an bada wannan aikin ba, har ya shiga ƙoƙarin karɓar file ɗin idan an gama binciken, dan ɓatar da duk wata hujja da zata saka a gane shi "
Widad ta sauke ajiyar zuciya tace " kowa yayi nagari kansa, a duniya babu abunda za ayiwa Bulama wanda zesa mu huce takaicin abunda yai mana, sedai ai masa hukuncin daya dace duniya sauran a barshi se a lahira "
Haka suka shiga mota suka tafi gida, suna jinjinawa azabara zalunci da baƙar mugunta na Bulama, tunda ya kashe ɗan 'yar uwarsa waye baze kashe ba, duk saboda abun duniya.
Da suka koma gida, fuskonkinsu kawai Umma ta kalla tasan wani abun takaicin suka kuma zuwa suka jiyo, a gurin' yan sanda shiyasa tun farko tace bazata bisu ba.
Umma tai musu sannu da zuwa, Daula ya wuce ɗakin hutawarsa, saboda yana buƙatar ya ɗan huta yayi tunani.
Widad ma ta janye mijinta, zuwa wani ɗakin daban, Alhaji Ahmad ya zauna a kujerar dake kusa da ta Umma yace "Hajiya Jidda"
Umma tace "Jiddan dai banda Hajiyar"
"Dole ace miki Hajiya mana, tunda kika riƙe ɗan Daula, kika riƙe babban attajiri haka"
Umma tace 'mhmm, ni tsoro nake ma kar yace ze ƙwacemin ɗana, bana son sunana ya canza daga Umman Yusuf, dan bana tunanin ko da Allah ya bani haihuwa, zanso ɗan nan kamar yadda nake son Yusuf'
'tabbas nima nagani, kuma Wallahi Daula ua jinjinawa ƙoƙarin ki, yace idan ya kalli abunda Bulama ya masa, se yace "Anya kuwa akwai ragowar mutanen kirki a duniya? Idan ya duba irin riƙo da wahalar da kika sha da Yusuf se yace duk lalacewar zamani akwai na Allah, wallahi kin ciri tuta Jidda, kuma abunda kikayi Jihadi ne, riƙon maraya da zuciya ɗaya tamkar ɗan da kika haifa "
Jidda tace " gashi nan ina morarsa, wataƙila da ban riƙe Yusuf ba haka tsufa ze riskeni babu me jin ƙaina, 'yan uwana bama su ƙarfi bane, hasalima a gurina suke nema, bani da wanda muke uwa ɗaya uba ɗaya sedai' yan uba, amma Yusuf ya riƙeni Uwa, yanamin biyayya fiye da yadda kake zato, ƙare magana ko ɗan dana haifa banajin zemin biyayyar da Yusuf yayi min, koda ban taɓa haihuwa ba, amma ni riƙon Yusuf yamin rana, ko be zama komai ba, tausayinsa da jin ƙansa ya gamamin komai "
Alhaji Ahmad yace" hakane, tabbas yana da haƙuri da biyayya, kuma bayan wannan dukiyar dai Allah yayi tasa ce, da ba lallai ya iya jure wannan tsananin da wahlar ba, amma da yake tasace kuma Jininsa ne Daula, kinga ya jure duk gwagwarmaya, an gaisheki Jidda kin cika Uwa tagari "
Jidda tai murmushi tace 'Nikam Ahmad, ina naka iyalin ne?"
"Meyasa kike tambayata?"
"gani nayi tunda mu kazo banga ka koma gidanka ba, ko ka yi zancen su ba"
Yai murmushi yace "iyali suna nan a kano, da ina nan zaune tare dasu ne a nan Abuja, tace ita dai tafison zaman kano, shine suka koma suka barni sedai in dinga zuwar musu"
Umma tace "Allah sarki, Allah ya raya zuriya"
Yace "ameen ya Allah, Jidda nayi mamaki har yanzu kina nan da kyanki baki canza ba gs gayu"
"kajika da wani zance, ina wani kyau da gayu bayan na tsufa"
"wallahi baki tsufa ba, kalleki fa ras dske, amma meyasa baki sake aure ba bayan mijinki ya rasu?"
Umma tai ajiyar zuciya tace "saboda ina son in kula da yarona, idan na auri wani waze yadda ya riƙemin shi, mussman da bani na haife shi ba, shiyasa na zaɓi in zauna ba Aure in riƙeshi"
Alhaji Ahmad yace "to amma ai yanzu ya girma, shima me riƙe wasu ne mussman wannan sitira da Allah yayi masa yanzu, saboda haka yakamata kiyi aure ai"
Umma tace "tsofaitsofai dani se in kama yin wani aure, a'a ai na girma Aure mun barwa yara"
"kece kika tsufan kokuma wa?"
"Eh mana, na tsufa"
"yanzu fa da wanine ya gaya miki seki ji haushi ko?"
Umma tace "akanme zanji haushi, ai nasan na tsufan ne"
Alhaji Ahmad yace "ba wani nan, ni dai ina zawarci har yanzu, ina so"
Umma ta kalli Alhaji Ahmad tace "dan Allah ka dena wannan zamcen haka, haba Ahmad"
"kinga dole inyi wannan zancen, haba Jidda me zesa ki haramtawa kanki Abunda Allah ya halatta, haka zaki cigaba da zama babu Aure kenan?"
Tace "eh mana, har zuwa lokacin da Allah ze karɓi rayuwata"
Alhaji Ahmad yace "No, gaskiya bazaki zauna haka ba, kawai ki tsaya mu sasanta"
Umma ta miƙe tace "kai dai bazaka canza hali ba, ka girma kana abun yara"
Yai murmushi yace "Au hakama zakice? Aini bazaki girman a idona ba, tunda.. Bari dai in shiru"
Umma ta bar falon tana dariya.
Yusuf kam salla yayi a ɗakin da suke, Widad tasa aka kawo fruit da madara me sanyi, amma Yusuf yaƙi sha.
Widad tace "haba my Fluid of life, wai baka murna da kasancewat ƙanwa a gareka ne? Naga baka walwala sam duk kana cikin damuwa"
Yusuf yai murmushin ƙarfin hali yace "yama za'ayi ince bana farinciki da Kasancewar ki ƙanwata, na daɗe ina miki so mai tsanani da takurawa ruhi, se yanzu na tabattar da ashe son ne ya haɗemin dana 'yan uwantaka, tsabar farinciki ne yasa na rasa ta ina zan nuna tsantsan farinciki danake ciki, ashe tun tuni da' yar uwata nake tare, shiyasa nake jin zan iya yin komai ko in bada komai nawa, gurin baki kariya koda kuwa raina ne, nayi farinciki da haka, kuma gefe guda ina jimanta irin wahalar da muka sha, da mamakin cin amanar yadda na mutanen wannan zamani, dukda abunda akayimin be kai na Daddy ba, Amma Widad ko a tatsuniya akacemin Abbas zemin haka bazan yadda ba, ashe haɗa baki akayi dashi akamin gadar zare, yazo ya lallaɓani aka bani aiki, shi yayi dan cutar dani, ashe hakan Silar taradda farinciki nane, kai Widad mutane abun tsorone, banga laifin AƘIDARKI ba baby, kaso mutum dan Allah shikuma bashi da maƙiyi kamarka"
Ya ƙarasa maganar muryarsa na rawa, alamun karaya Widad ta rungume Yusuf tana shafa sumar kansa ta sigar rarrashi tace "tabbas haɗuwarmu da wasu mutanen a rayuwarmu darasi yake bamu, da mutane sunyiwa AƘIDATA mummunara fahimta, amma ba haka kurum nake abubuwan da nake ba a baya, dukda daga baya na gane a AƘIDATA akwai wadda bata kamaceni ba, amma a hankali duniya ta ladabtar dani ns gane rayuwa sosai, sannan nayi farinciki na kasancewarka ɗaya daga ahalina managarcin mutum me matuƙar kamala, ina sonka Yusuf "
Yusuf ya kalleta dukda gefen idonsa hawayene ke zuba, amma yai murmushi har seda haƙoransa suka fito yace " waye ya koya miki yadda ake faɗar sunana? In kikace Yoseef yafimin daɗi, saboda nasan ba wanda yake faɗar sunana a haka se Gimbiyar Yusuf "
Widad tai murmushi tana sake rungume Yusuf a jikinta, Widad tace "Alhaji Yoseef Nasir Daula, seka dena bearing wancan sunan, tunda har gida akazo ama kashedi akan ka dena amfani da sunan saboda tsabar jaraba irin ta mutanen nan"
Yusuf yace "am sorry to say, Baby bazan iya dena amfani da sunan Bashir maitama ba, saboda shina saniba ubana, shina buɗe ido dashi yana ɗawainiya dani"
Widad tace "hakane, babu laifi Mijina"
Yace "Amma ni gaskiya, wannan kuɗin da ake shirin bani, nifa ban san yadda zanyi dasu ba"
"Yoseef, wannan kuɗinfa na mahaifinka ne da mahaifiyarka, wakake so a bawa idan ba kaai ba?"
Yusuf yai shiru yana zancen zuci, Widad tace "mu bar maganar nan, zamuje ƙauye a satin nan yaushe zamu tare ne, nina gaji gaskiya"
"to mara kunya, kije ki tambayi Daddy, wace tarewa kike nema, banda wannan tarewar na cikinki"
Sosai Yusuf ya bata dariya tace "ai shikenan, bama semun wani tare ba, ɗaki ɗaya zamu koma kwana, ai akwai ɗakuna dayawa a gidan nan"
Yusuf yace "Allah ya baki haƙuri, kiyi haƙuri mu koma kano kinji ƙanwata"
Tai murmushi tace "naji, tashi muci Abinci ko?"
Haka suka wanzu suna farinciki da annashuwa a tsakaninsu.
Nuray kama tunda ta gano Khalil sonta yake, take jin tausayinsa, be taɓa gayamata ba, amma idan tana tuna kyautatawarsa, da kulawarsa a gareta, tabbas idan ba so babu abunda ze kawo hakan.
Tana kitchen tana aikace aikace tana tunanin yai sallama ya shigo, ta amsa masa tana binsa da kallo.
Yace "Nurun, me kike soya mana ne?"
Tai murmushi tace "kwaɗayi nake ji, ma rasa me zanci na tsiri yin cake"
"kwaɗayayyiya kawai, amma dai ɗan sanmun"
Tai dariya tace "mun zama kwaɗayayyu kenan"
Ya ɗauka yana ci yana faɗin, "kai Komai naki na dabanne, ban taɓa cin Abinci me daɗin wannan ba fa, Allah ya bani mace tagari wadda ta iya girki kamarki"
Nurat ta kasa ce masa komai se kallonsa kawai da take yi, jiki a sanyaye yace "lafiya kuwa?"
"Lafiya ƙalau Yayana"
"to ai gani nai kamar jikinka ba ƙwari fa, ko akwai matsala ne?"
Ta girgiza masa kai alamar aa' "ko Yusuf ɗinne dai ya kuma yi miki wani abu?"
"Brother, Yusuf yafi ƙarfina na haƙura dashi"
Cikin damuwa yace "saboda me? Ya da karaya haka Nurat"
"Khalil, Ka sani an tabattar da Widad matarsa ce, aure sukayi Dan harda tsohon ciki ma, kasan a ynzu na shiga sahun maƙiyan Widad, nasan bata ƙaunata yanzu haka, Yusuf yana son matarsa sosai cigaba da musu shisshigi a rayuwar su ze iya basu matsala, musamman da Ummansa da take son lallai ya aureni, Yusuf mutum ne me nagarta da haƙuri ba dan Widad ba ze iya aurena, amma ga laifin da mahaifina yai musu, ga Widad nasan dukda a baya bata soyayya amma yanzu na fuskanci akan Yusuf ba abunda bazata iya ba, gara in ƙyalesu bana som zama silar rasa farincikin kowa a rayuwa, ina wa Widad murnar samin nagartaccen abokin rayuwa, nima Allah ya bani miji nagari wanda ze soni, me kyawawan halaye kamar Yusuf "
Ta ƙarasa maganar, tana zubar da hawaye sosai, Khalil ya ƙarasa gabanat, wani irin matsanancin tausayinta ya kama shi, he feels her pain, yasan yadda raɗaɗin son maso wani yake, Nurat ta so Yusuf sosai yana zuwa inda take tsaye, ta faɗa jikinsa tana kuka, ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta, da alama abun yana cim zuciyarta bata samu damar yin kukan bane ba.
"kiyi haƙuri, Allah ze miki musaya mafi Alkhairi, kin san da yawa a rayuwa, mu kanso abunda ba alkhairi bane a rayuwarmu, Allah ya zaɓa miki mafi Alkhairi Ƙanwata"
Ta dinga jinjina masa kai, amma ta kasa magana, saitin kunneta yace "koda kuwa nine, idan Allah ya musanya miki kina so?"
Tashi tayi daga jikinsa ta goge hawauenta tace "cake ɗina ze ƙone, bani guri in duba"
Tai maganar tana basar da abunda yace kamar bata ji ba, ya dinga bimta da kallo yana tunanin she didn't accept his proposals.
Su Widad sun shirya tsaf, domin zuwa ƙauye, Widad se murna take, Amma daga baya se jikinta yai sanyi tace "Daddy, wai ina Saleh ne? Zamuje garin su gurin 'yan uwansa, me zamuce musu idan suka tambayemu shi?"
Daula yace "ai kema kin san Daula baya manta alkhairi, Saleh yayi sintiri a Asibiti saboda ni, kuma shiyafara gayamin kuna hannunsa, sannan kunyi Aure, saboda alkhairin da yayi muku nakejin zan iya yafe masa, na karɓeshi a hannun 'yan sanda, an kai shi Egypt saboda anma rauni da duka a hantarsa, za' a masa aiki "
Widad tace" Daddy hanta kuma? "
Daula yace "Eh, saboda dukansa da aka dingayi a ciki ya samu matsala"
Widad tace "Allah ya bashi lafiya, amma yayi ɗawainiya damu sosai"
Yusuf ne ya fito Umma da Alhaji Ahmad suna bayansa, seda suka fara shirin shiga motar sannan Yusuf yace "nifa Umma har yanzu banji yadda akayi kika san Alhaji Ahmad ba?"
Daula yai murmushi yace "Budurwarsa ce ta farko tun zamanin ƙuruciya, a gidansu akaga be shirya ba Abbanka ya aureta ya barshi'
Kunya ta kama Umma, kamar ta nitse a ƙasa dan kunya, Widad da Yusuf suka shiga yimata dariya.
Alhaji Ahmad yace" kuma har yanzu ina so ba, amma tace min se ɗanta ya yadda, dan haka Yusuf nidai ina so har yanzu "
Yusuf yai dariya ya buɗe mota yana faɗin, ni dai ba ruwana".
Suka shiga mota suka ɗau hanyar garin Bauchi, bisa rakiyar 'yan sanda.
Tun su Alhaji Daula suna sa ran ƙarewar tafiyar, har suka zuba ido nausawa kawai ake cikin ƙauyuka, sannan aka bar kan titi aka saki hanya aka nausa wani surƙuƙin ƙaiye, tun daga nan Daula yake tasibihi, da mamakin azabar surƙuƙin gurin nan.
Nanam sukayi tafiya me nisa akan burji, babu kwalta ba zaka taɓa cewa zaka tarar da gida ba, se sama da ƙasa sukeyi danma a manyan motoci suke, amma hakan be hanasu jin jiki ba, idan aka shiga wani ramin, se Yusuf ya riƙe Widad gam saboda kar abunda ke cikinta ya wahala, a haka suka ƙaraso ƙauyen nan.
Suka fir fito yayinda 'yan garin sukayi dandazo suna kallon motocin, yayin da wasu suke gudu saboda ganin motar' yan sanda.
Daula ya kalli ƙauyen, ya sake kallo yace "yanzu Baby, a nan kuka rayu?"
Widad tace "ƙwarai kuwa Daddy"
Ita kanta Umma daba wani kuɗine da itaba, tunani take ta yadda zata yi rayuwa a wannan ƙauyen.
Widad ta raɗawa Yusuf a kunne "Allah sarki, yau zanje inga ɗakin amarcinmu"
Suka ƙunshe baki suna dariya
Tuni labari yajewa megari, ga wasu nan sunzo a jibga jibgan motoci irin na masi sace mutane, da 'yan sanda, ya fito a ruɗe, dan baya son abunda ze tayarwa da mutanensa hankali.
Sam be gane Yusuf ba balle Widad, Yusuf ya ƙarasa gaban sa ya zube yana gaisheshi, seda ya tsurawa Yusuf ido sannan ya gane shi, yace "innalillahi, Malam Yusuf kaine? Dama zan sake ganinka Yusufa?"
Yusuf yace "Alhamdilillah, gani ai tare muke da iyayen namu ai"
Widad ta ƙaraso itama tana gaida megari, yace "Allahu Akbar, Amarya 'yar gwaggonta"
Widad tace "aikam bari in ƙarasa in ganta kuwa"
Ta shiga da sallama, Hindu na zaune tana tankaɗen garin dawa, taji wani irin ƙamshin turare ya gaauraye gidan, ta ɗaga kai zata amsa sallama tayi tozali da Widad, aiba shiri tayi wani uban tsalle tai fatali da ƙwaryar garin, tai gurin Widad tace "Allah yasa ba mafarki nake ba?"
Widad tace "idonki biyu Hindu, nice Widad ce"
Suka rungume juna suna kuka, Gwaggo ta fito da sauri jin kamar muryar Widad, aikuwa itace ba wata ba, nan gida ya hargitse da murna da koke koke, Widad tace "ina aminiyata abikiyar faɗana Hari"
Hansai tace "taje barka bayan layi ita da Hanne, amma yanzu zasu shigo"
Tana gama rufe bakinta, sega Hari da gudu kamar ƙaramar yarinya "wayyo Allah na, jama'a dagaske Wudas ce? Wai Wudas ce tazo garin nan?"
Widad tace "nice Hari"
Widad ta rungume Hari, Hari ta shiga kuka tace "ban taɓa zaton na saba dake haka ba, seda kuka bar garin nan"
Umma tai sallama itama ta shigo, nan aka shimfiɗa musu tabarma, suka karɓsu hannu bibbiyu Widad tace "Mama ga Wannan itace Umma mamanmu nida Yoseef"
Hari tace "kamar yaya kenan? Ya za'ayi ku zama uwa ɗaya? '
Widad tace " zaki fara ko? Tunda na gayamiki ki barshi a haka mana"
Hari tace "naji an barshi a hakan"
Hanne tai sallama ta shigo, ta kalli inda Widad take, ta ganta a balarabiyarta, fatarta ta sake ja tayi kyau sosai, Kallo ɗaya Widad tayi mata ta ɗauke kai daga kanta.
Tuni aka fara kiciniyar ɗora girki, Widad tace base an ɗora komai ba, sunabda abinci a mota, amma ita dai idan an gama tuwo a bata zata ci.
Aka karɓo mukulli aka buɗe ɗakinsu da suka zauna, Widad cikin hawaye tace Allah sarki ɗakin mijina, wayyo rayuwa, a lokacin da nake shan baƙar azaba a hannun Bulama ji nake tamkar in dawo ƙauyen nan da zama in huta"
Ita kanta Umma tayi mamakin yadda suka rayu a gurin nan, megari yayiwa Su Daddy jagora har ɗakinsu Widad, nan suka tsaya suma suna mamaki.
Hindu har ƙasa ta durƙusa ta gaishesu, Yusuf yace "Hindu amma dake zamu tafi kano ko?"
Hindu tai murmushi tace "waceni"
"yakamata, kinga yayartaki ta kusa haihuwa, seki tayata zama"
Hindu tai murmushi tace "Allah ya sauketa lafiya"
Yace "Ameen"
Daddy ya kalli ɗakin nan nasu yace "yanzu Widad ce ta rayu a ɗakin nan? Allah me yadda yaso sannu Yusuf nasan ka sha gwagwarmaya"
Yusuf sedai yai murmushi.
Hari yazo kusa da Widad ta zauna tace "abun mamaki, Wudas da ciki ana shan taɓara nasan"
Widad tace "ko in kira miki Yusuf ki tambaye shi idan ina taɓarar ko ba nayi?"
"kefa matsala ce dake, baki san wasa ba"
Hari ta shiga halin nata na ɓare ɓaren zance, aka shiga shigo da kayan Abinci gidan nan kamar ba gobe, wanima basu san meye ba.
Nan jikinsu ya hau rawa, suka tabattar da lallai Widad 'yaf ga tace gaba da baya.
Widad taja hannun Hindu gefe, tace "Hindu kinga babana?"
Tace "Na ganshi mana"
Widad tace "tsoho ne sosai ko?"
"A' a wallahi ba tshoho bane, gashi me kyau wallahi yana kama da mijinki sosai, dake dashi da Yusuf duk kuna kama, irin idanunku ɗaya sak"
Widad tai murmushi tace "zaki iya auren Babana?"
A razane Hindu ta kalleta tace "Kamar yaya, ta yaya babanki ze auri 'yar ƙauye kamarni, gashi babban mutum"
"Hindu ki dena duba wannan, dan Allah ki aure shi, nasan zaki kulamin dashi dan Allah Hindu ki auri babana"
Jikin Hindu ya hau rawa, zata yi magana amma Widad tace "yi shiru, karkice komai ina zuwa, kuma karki gayawa kowa wannan maganar"
Widad taje ɗakinsu, inda su Daddy ke zazzaune tace "Daddy, i want to talk to you"
Ba musu ya miƙe ya biyo bayan ta, ta ja shi can waje a wani soro tace "Daddy nifa nayi maka mata a garin nan"
"mata kuma kamar yaya?"
"Daddy, matar Aure dai nayi maka, dan Allah karka bani kunya kaji Daddy"
"Widad, nifa na haƙura da Auren nan"
"A'a Daddy, dan Allah ka tsaya ka ganta mana"
Yace "shikenan"
Ta shiga cikin gidan da sauri, ta tarar da Hindu a inda ta barta, jikinta a sanyaye tace "saka hijjabinki kizo muje"
Hindu ta saka hijjabi, ta biyo bayan Widad, ta mata jagora zuwa inda Daddy yake zaune, gaba ɗaya yaiwa Hindu wani irin kwarjini, da bata taɓa gani a gurin wani ba.
Suka ƙarasa Widad tace "Daddy, ga amaryar da nayi maka, ina fatan bazaka ƙi karɓa ba"
Daddy ya kalli Hindj, yarinya ce ƙarama, yace "Amma daughter, naganta yarinya ce sosai fa, kamar zaki girme mata ma"
Cikin harshen larabci Widad tace "Daddy aiba haramun bane, wallahi yarinyace tagari me nutsuwa, zakayi alfahari da ita"
Yace "to ita kin tabatta tana sona? Karki ƙwareta dan son kai kinga na girma dayawa"
"Daddy Hindu bazata ƙika bafa" tai magana kamar zata yi kuka.
Daddy ya kalli Hindu yace "ya sunan ki ne?"
Hindu dake gefe ta takure kamar bokanya tace "Sunana Hindu"
"masha Allah, Hindu kinji rigimar da wannan matar ta tattago, ban miki tsufa ba?"
Hindu ta kasa cewa komai, se jikinta dake ta tsuma, tana rarraba ido.
Widad tace "Daddy ai mun gama magana da ita, yanzu megari zakayi wa magana, kaga se a bada kuɗin aure ma kafin mutafi.
AMANACE!!!
Ayshercool
07063065680
12/10/21, 1:36 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
168_169
Daula yace 'Widad mubi komai a sannu, ki bari muji ta bakinta, karki mata dole mana, kuma maganar aure ai ba' a gaggawa "
Widad tace " Daddy, nasan irin zaɓen da na maka ne, ni dai ka amince kawai please "
Daula ya lura da yadda jikin Hindu keta tsuma, ko idonta bata iya ɗagawa ta kalle shi, ta sunkuyar da kai tanata cimimiyewa a hijjabinta.
Daula yace " Hindatu, tashi ki koma gida, Widad zata sa ki auri tsoho "
Cikin hanzari Hindu ta miƙe, ta shige cikin gida tana haɗa hanya, Daula ya kalli Widad yace "Widad, wannan haɗin naki beyi ba, kowa zega kamar an ƙwareta ne, tayi yarinta dayawa kuma kinga ba ita tace miki tana sona ba, gashi ni na riga na fidda rai da Aure"
Widad tace "Daddy, na zauna a garin nan na zauna dasu, nasan halin yarinyar nan, Daddy karka duba ƙauyanci ko ƙuruciyarta, ni dai tukuicin dazakamin shine ka Auri Hindu, sannan akawo musu cigaba a garin nan, shine zaka biyani ɗawainiyar sa sukayi damu, dan Allah Daddyna "
Daula yace " Naji, zanyi shawara kafin mutafi "
Da ƙyar ya lallaɓa Widad ta tafi, ta koma gurin Alhaji Ahmad da Yusuf ta dinga musu magiya akan lallai su saka baki, Daddynta ya auri Hindu, Alhaji Ahmad yace "to muyi musaay, kice mijinki ya bani ummansa nima"
Widad tai dariya tace "ka samu, nidai fatana Daddy ya amince da Auren Hindu, sonake kafin mutafi ya bada kuɗin Aurenta"
Umma tace "Widad, ba'a gaggawa a harkar Aure, karki takuramasa ko ita yarinyar ki takura ta fa"
Yusuf yace "Umma Hindu bata da matsala, and she deserves to marry a descent person like him, idan harya yarda ya aureta ze sha biyayya"
Widad tace "Yoseef, dan Allah zomuje ka gayawa Megari, bana son Daddy yayi missing wannan opportunity ɗin"
Daula yai shiru yana tunanin maganar da Widad tazo masa da ita, yadda yaga suna nan nan da su Widad, da yadda suka sake dasu, suma hira ama wasa ana dariya, da yadda mutane keta shiga suna fita a gidan, ya tabattar masa da cewa sun riƙe su Yusuf da Amana, dan haka duk wanda ya shigo gidan seya fita da kuɗi ko Abinci, Daula ya dinga basu kyautar kuɗi da Abinci, da wannan ya shigo se Widad tace Daddy ga wane a bashi kaza, ko kuma ai masa kyautar kaza.
Widad sun sha hira da Gwaggo, seda aka tuƙa tuwon nan taci, suna ta faɗa ita Hari, Hari tace "Ohh ni Hari, wai Wudas ce sa ciki, ranar haihuwa akwai kallo"
Widad tace "me za'a kalla?"
"raki da rashin haƙuri mana"
"Hari kema fa Allah kaɗai yasan abunda kika yi haihuwar fari"
Umma sunyi hira sosai da Gwaggo, ta dinga bata labarin yanayin zaman da suka yi dasu Yusuf a gidan, Hanne kam ta kasa yadda ace wannan ne mahaifin Widad, iya motocin da suka cika ƙofar gidansu ma 'yan rakiya kawai abun kallone, banda rakiyar motar' yan sanda, wai ashe dagaske dai Daula ne baban Widad, lallai yaci sunansa Daula.
Ɗaliban Widad suka dinga zarya suma, suma zuwa gaishe ta da ɗaliban Yusuf, magidantan da yai ta koyarwa, sedai dukda wannan tarin kaɓakin kayan Abincin da aka rarrabawa 'yan ƙauyen, wannan yazo ya bawa Widad kyautar kuka, wannan ya kawo tsintsiya, wannan ya kawo Nono, ƙwan zabi zuma, haka suka dinga kawo musu wai suyi tsaraba, Daddy yai farinciki da karamcin mutanen garin, da yadda suka riƙe' ya'yansa suka zauna lafiya, gefe guda kuma ya tausaya musu yadda suke rayuwa ba makaranta, ba wutar lantarki ba kwalta bare Asibiti.
Kafin su bar garin, Daddy ya sanar da me gari cewa za'azo a gina musu makaranta ta boko da islamiyya a saka gwamnati ta kawo musu malamai, Widad kuma tace zata gina musu Asibiti, a kawo musu ma'aikatan lafiya, Daddy yace "Alhaji Yusuf baka yi magana ba"
Yusuf yai murmushi yace "Aini tunda aka musu makaranta da Asibiti, an gama min komai, fatana kuma ai musu boreholes na ruwan sha, saboda babu ruwa a garin nan, a saka gwamnati ta samar musu da wutar lantarki, saboda Asibiti baze yuwu babu wuta ba.
Nan jama'ar suka dinga murna suna Allah ya Sanya alkhairi, suna saka musu albarka.
Hindu kam ta ƙuke a ɗaki, tana tunanin abunda Widad ke shirin yi, banda abun Widad ina ita ina wannan hamshaƙin attajiri, ɗan gayu me ilimi ga kyau da dukiya, ita kuwa ga ƙauyanci da rashin wayewa, amma ta dage seta aure shi, ita gani take kawai ze aureta ne saboda 'yarsa, amma tabbas ba sa' ar Aurensa bace.
Tana cikin tunanin taji ana guɗa da shela a tsakar gida
"Alhaji Daula, yaga 'yarmu yana so, kuma harya bada kuɗin Aurenta naira dubu ɗari biyar, mudai zaman Yusuf da matarsa a garin nan namu alkhairi ne, yace ya gani yana so, kuma me gari ya amsa, yace ya bashi, watan arzikinmu a ƙauyen nan ya tsaya,' yarmu zata auri attajiri, ko iya Asibiti da makarnta da akace za' a mana aimu am biyamu, 'yarmu Hindu Tayi goshi, zungureren goshima kuwa "
Gaban Hindu ya faɗi, kenan dagaske dai ta tabatta Widad za tayiwa Babanta Auren dole da' yar ƙauye?
Hanne kuwa gigicewa tayi, dan a ganinta tafi Hindu komai, dan meyasa ba'ace itaba se wata Hindu, Hindun daba wani kyaune da ita ba ga baƙin jimi, amma ace zata auri attajiri haka.
Da zasu tafi Widad ji tayi kamar karsu tafi, dan sosai takejin kewa da ƙaunar mutanen garin, saboda karamcinsu da girmamawa, Ta shiga ɗakin Gwaggo ta sami Hindu a ƙarshen gado tayi shiru tana tunani.
Widad tace "Hindu, karki ɗaga hankalin ki, babana bashi da matsala ko damuwa, mutumin kirki ne zaku zauna lafiya ƙalau dashi, sannan an saka wata biyu, saboda kafin ɗaurin Aure a kawo muku cigaba garin nan, saboda manyan mutane ne zasu garin nan, munyi magana za'a aiko da mota tun saura sati biyu biki a ɗauke ki a kaimin ke can kano, mu fara shirye shirye "
Hindu kawai jinjina mata kai tayi, daga nan suka yi sallama suka tafi, a hanya sunata jinjina karamci da mutuntawa na wannan al'ummar gari.
Gaba ɗaya ƙauyen nan ya ɗauka, Daula ze auri Hindu, ga kuma kaɓakin arzikin da aka sauke musj, sunata rawa da murna ga alƙawarurrukan da aka musu na kawo musu cigaba a garin.
Su Widad kuwa garin kanon dabo suka wuce kai tsaye, suka sauka a farmhouse, Bayan sun huta Alhaji Ahmad ya wuce gidansa, Umma tace ba zata zauna a nan gidan ba, gidanta zata tafi, shi kuma Yusuf nauyi yake ji, koba komai Daddy sirikinsa ne, ace suna gida ɗaya su kwana ɗaki ɗaya da Widad, haka ya basar Widad kuma ta dage se Umma ta kwana a gidan ba zata tafi can gidanta ba, da ƙyar Umma ta yadda ta amince.
Wasa2 Seda suka kwana biyu da dawowa, amma suna farmhouse tare da Umma, kullum se Alhaji Ahmad yazo, Umma ta takura akan cewa lallai seta bar gidan, dan ita gaba ɗaya jinta take a takure.
Daddy yace zasu rakata gida, kafin nan ze kaisu gidan daya saiwa su Yusuf, kuma ranar nan da sati biyu Yusuf ze tafi Lagos, inda babban kamfanin shige da ficen ƙarafa yake, wanda yake mallakinsane, shi dai Yusuf jin abun yake banbarakwai, kamar bashi ba.
Koda suka fita seda suka fara zuwa ainihin gidansu da suke zaune, suna zuwa ma'aikatan nan suka dinga rige rige zuwa gurin Daula, ganin ya bayyana ashe yana raye, sedai gidan kamar kango, ba shige da ficen mutane, ba manyan motocim dake harabar gidan, abun duk se a hankali.
Nan su Murtalah, Nura da sauran ma'aikatan gidan suka dinga tururuwar zuwa gaban Daula, masu kuka nayi masu murna nayi, ai nan da nan labarin bayyanar Daula ya karaɗa gari, da jaridu Widad kam cikin gidan ta wuce, tana ganin gidan ya koma kamar wani kango.
Alhaji Daula yace "ina sauran mutanen gidan?"
Nura yace "ai ranka ya daɗe ai an kama Hajiyar"
Daula yace "nasani"
Nura yace "to yanzu dai, 'yan sanda sunzo sun kama Ramlah jiya, se Amal ce kawai a cikin gidan"
Daddy ya jinjina kai, ya shiga cikin gidan, yana shiga ya tarar Widad ta wuce ɗakinta, Amal tana zaune a falon tana ta kuka kamar an mata mutuwa, ta rame sosai kamar wadda aka zuƙewa jini, tayi baƙi sosai duk ta canza kamanni gwanin ban tausayi.
Maimakon Daddy yaji haushinta sema wani tausayinta daya kama shi, kafin yai magana Widad ta fito, Umma tace "Yusuf wannan kuma wacece?"
Yusuf yace "Umma wannan itace Amal, 'yar matar gidan nan ce"
"Amma ya naganta kamar mara lafiya?"
Yusuf yace "nima ban san abunda ya sameta ba"
Widad ta kalli Amal tace "Malama You have to leave this house, within some minutes, azzalumai kawai marasa tsoron Allah, masu butulci"
Amal ta shiga girgiza kai tana cigaba da kuka, dan idan ta fita bata san ina zata ba, dan bayan mamansu ta auri Daula, a dangima ba kowa take gani da gashi ba, yanzu idan ta fita ina zata?
Cikin tsawa Widad tace "Am talking to you"
Daddy yace "No Widad, ɗan dakata tukuna"
Ya ƙarasa gaban Amal ya durƙusa, yace "Amal ɗin Daddy, baki da lafiya ne? Kikayi wannan ramar haka?"
Amal cikin kuka tace "Dan Allah kuyi haƙuri, kuyafemin, dan Allah, dan Allah kuyi haƙuri"
Tai maganar tana haɗa hannayenta alamar neman afuwa 🙏
"Daddy, waiya kake wani lallaɓatane? Do you want give them another chance to finish us?"
Daddy ya girgiza mata kai, ya sake kallon Amal yace "yanzu meke damunki kika rame haka?"
Nan ta gaya musu yadda akayi mata fyaɗe, Alhaji Haruna ya keta mata mutunci da abunda likita yace, a maganartata zaka fuskanci ta samu taɓin hankali.
Yusuf kansa seda tausayinta ya kama shi, duk rashin mutuncinsu, Amal ta ɗanfi sauƙin kai, dama Ramlah tafi zaƙewa da wulaƙanci.
Daddy yace "ki kwantar da hankalinki, nasan yanzu dole zaki shiga damuwa sosai, saboda gaba ɗaya 'yan uwanki da iyayenki suna hannu, ina fatan ze zame miki izina akan abunda ya faru, ban miki Alƙawarin saka baki akan taimakon mahaifiyarki da yayarki ba, saboda sun cutar dani a rayuwa, amma daga nan ko zuwa wace ƙasane, daga naira ɗaya zuwa miliyoyi, zan kashe a nema miki lafiya, kidena kuka kiyi musu fatan Allah ya shiryesu, sannan ki dimga musu Addu'a "
Aikuwa a hasale Widad tace " Daddy, why? Me yasa zakayi wannan hukuncin, dukda tarin laifukan da suka aikata mana? "
Yusuf ma cikin tsawa yace " Widad, Daddy kikewa magana fa, talk to him with respect "
" Haba Yoseef, a gabanka akace Mahaifimsu aka saka ya kashe min Ammina, yanzu meze sa Daddy ya temake ta? Bayan yadda suka so ganin bayana, da ganin ma zama mahaukaciya tuburan?"
Daula yace "Widad, ɗan halak baya manta alkhairi, ko bakomai ɗan uwanta yamin wahala, yayi ɗawainiya dani a Asibiti, yamin biyayya, kuma itama ba laifi tana girmamani, albarkacin Anwar nakeso Amal taci, ba ita tayi miki laifin ba, dan haka kiyi haƙuri, kiyi haƙuri ba danni ba dan Allah "
Daddy ya riga ya ɗaureta da jijiyoyinta, dan haka dole tayi shiru.
Daga gidan suka wuce inda nan ne gidan da Daddy yace nasu Yusuf ne, a unguwar lamiɗo crescent, gida ne hargida ya haɗu ya tsaru iya tsaruwa, kamar ba'a Nigeria ba, Widad nata murna yayinda Yusuf ke jinjina abun, waishine da wannan gidan haka?
Amma Babban abunda Widad bata ji daɗinsa ba, be wuce yadda Daddy yace " wai anyi bookin ɗin jirgi shida Yusuf a ranar zasu tafi lagos da yamma, dan canne inda kamfanin Yusuf yake, zeje a nuna masa abubuwa tun yanzu, Widad taji haushi sosai, dan harga Allah tana kewar mijinta sosai, kusan watanni shida ana neman na bakwai basa tare, amma haryanzu sun kasa samun dama su kasance tare, shikansa Yusuf mazewa yake dan yana da kunya sosai amma yana kewar matarsa sosai, Widad ce dai wani lokacin se a hankali bata fiye jin kunya sosai ba, duna da yanayin rayuwarta.
Amal kuwa a ranar Daula yasa aka ɗauketa aka kaita Asibiti, dan a dubata a ga idan aikin ze yuwu a nan Nigeria.
Haka Widad tana ji tana gani, da yamma su Yusuf suka tafi Lagos, ta koma gidan Umma tai zamanta, kwana ɗaya da tafiyarsu Lagos, Daula yai hira a kafafen watsa labarai a can Lagos, ya sake bayyana kansa, ya bayyana dukiya ta Yusuf ce, da irin wahala da azabtarwar da Bulama yayi masa, ƙarshe yai jan hankali da nasiha me ratsa jiki, akan mutane su lura da suwaye masoyansu na gaskiya.
Umma da Widad basu san anyi hirar ba, se gani sukai mutane na zuwa gidan, wai sunzo yiwa Umma murna,ashe Yusuf ɗan Daula ne, babu kunya ciki hardasu Yaya ɗanllami masu yi masa gori, Sunga Arziki ya sameshi, Widad ta dinga mamaki wato a rayuwa idan kaga ana nan nan da kai, wata damace Allah ya baka, ko kuma kuɗine da kai.
Garin su Hindu kuwa, tuni aka kai kayan aiki dan cika alƙawarin da Daddy ya ɗauka, da yake akwai kuɗi, nan da nan aka fara aiki, kuma yace a ɗau leburori a garin dan su samu wani abu suma, gefe guda sunata shiri suma murna akan Hindu zata Auri Daula, yayin da ita Hindu gaba ɗaya yake mata kwarjini, take tunanin taya zatai zaman aure dashi, mutumin daya girmeta nesa ba kusa ba, yama haifeta? "
Nurat kam ta riga ta haƙura da batun Yusuf, tayi murna sosai jin labarin ashe yana da alƙa da Widad, itama in akabi nasaba ɗan uwantane.
Ta samu Khalil a falo tace masa" brother, kaga wani iko na Allah ko? Duk wannan wahalar ashe dai ɗan uwan Widad ne Yusuf, kuma akan dukiyarsa aketa wannan abun "
Khalil yace " hakane kam, Allah babu yadda be iya ba, Sakamakon haƙuri da juriya ga abunda Allah yayi masa, haƙuri me tadda rabo, kema Allah ya baki miji nagari wanda yake sonki"
Nurat tace "Aima ya bani"
"A ina yake? Baki gayamin ba"
"Sunanshi Barrister Ibrahim Khalil gora"
Da sauri ya kalleta yace "Are you serious?"
Ta jinjina masa kai tana murmushi, "yanzu kin yarda kima sona zaki aureni Nur?"
Ta jinjina masa kai alamar eh, murmushi ya shiga yi yana faɗin Alhamdilillah, Alhaji na dawowa zan sanar masa "
" Haba brother, meye na gaggawa kuma? "
" kar inje wani yayi min ba daidai ba, gara in hanzarta inyi wuf dake"
Nurat ta rufe fuskarta tana murmushi.
Wasa wasa, seda Yusuf sukayi Sati biyu sannan suka dawo Kano, kuma da suka dawo ɗinma seda Daula yaje har gidansu Nurat domin yi mata ta'aziyyar mahaifiyarta, abunda bata taɓa zaton Daula zeyi ba, tana ganinsa ta tsaya tana mamaki.
Daula yace "Nurat, ƙaraso mana"
Ta ƙarasa ta zibe ƙasa tana gaishe shi"
Ua amsa tare da faɗin "ya ƙarin haƙuri kuma?"
"Alhamdilillah Daddy"
"ubangiji Allah ya jiƙan ummanki, yai mata rahama"
Nurat tace "Ameen"
Nanma Yusuf ya sake yi mata gaisuwa, Daula yace "Nurat, idan akabi nasaba ina da alaƙa ta jini da mahaifinki, dan haka ki ɗaukeni Uba, duk abunda ya taso miki kike buƙatarsa, ki nemeni ko menene insha Allah, zanyi iya ƙoƙarina imga na miki, am your father now, kinji Nurat"
Nurat tace "to Daddy nagode sosai"
Seda Daula ya tsaya suka gaisa da mariƙin nata, sannan suka tafi.
Yallaɓai Suleiman kansa, seda ya samu tagomashin katafaren gida, da kuma kuɗi masu yawa a gurin Yusuf, saboda irin jajircewa da taimakon da yayi masa.
Kwanansu Uku da dawowa suka tare shida Widad a sabon gidansu, ya samu rakiyar abokan aikinsa gidan, Kasancewar bashi da wasu abokan kirki, Widad kamar tayi tsalle dan murna da farinciki.
Bayan kowa ya watse, gajiya duk ta damu Yusuf, saboda hada hada da mutane, dan har walima akayi na tariyar a event center, Daddy ya gayyato manyan abokansa, Yusuf duk ya gaji dan be saba da hada hadar mutane haka ba, ya shiga yai wanka, lokacin tuni Widad ta shiga ɗaya ɗakim tayi nata wankan, dan itama a gajiue take sosai, ta fito cikin riga da wando na bacci masu jikin bargo pink, ta kashe fitilar ɗakin ta bar dump side lamp, ta ƙaraso inda Yusuf ke zaune yana taje sumar kansa, Yusuf yace "malama ce miki akayi na gama kika kashemin fitila?"
Tace "kai ba mace na amma se ƙaƙale, da mace ne Allah kaɗai yasan me zakayi"
"Shi namiji baze gyara ba kenan, se kincemin ƙazami?"
Widad tace "kuma mayukana zaka dimga shafawa, na bleaching ne dai ba ruwana in ka zama fari"
Yusuf yai dariya yace "dan dai bleaching ai ba damuwa ranki ya daɗe, ince mata tace takemin"
Sukayi dariya tare, ta ƙaraso ta rumgumeshi ta bayansa, tana numfashi a hankali, kwararar hawayenta yaji a Ƙirjinsa da sauri yace "lafiya kuwa Widad?"
Kasa magana tayi, ta cigaba da kukan, ya janyota gabansa yana sake tambayarta, amma sema ƙara saugin kukan da tayi, yace "haba Babyna, mena yi miki kuma? Kodai shagwaɓarce?"
Still bata amsa masa ba, dan haka ya jata zuwa kan katafaren gadon su, ƙato ya zaunar da ita sannan ya zauna yace "gayamin, menene? Ko laifi nayi miki"
Rumgumeshi tayi tana kuka take faɗin "thank you very much Yoseef, thank you very much for your love, caring the sacrifice and all you have done for me, you change my life Yoseef, i love you"
"I love you too my wife, you also done a lot of things for me, bani da bakin godiya se dai zuciyata taki ce mata ta"
Haka suka cigaba da gayawa jinansu kalamai masu daɗi, masu cike da nuna kewar juna, daga nan kuma suka wula wani gurin.
🚶 🚶 🚶 🚶
Ji suke tankar lokacin suka yi aure, dan a wannan lokacin suke cin nasu amarcin a nutse, ba inda Yusuf yake fita, kullum yana gida tare da Widad, yana bata kulawa ta musamman.
Alhaji Ahmad ma ya nemi Auren Umman Yusuf, akasaka lokacin daidai lokacin bikin Daula, ayi biki gaba ɗaya
Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, tun saura sati biyu biki, Widad taje ƙauye ta ɗakko Hindu daga ƙauye zuwa kano domin shirin biki sosai, motar da aka kawo Hindu Tint glass ne da ita, dan haka bata samu damar ƙarewa garin kallo ba, seda suka shiga gidan Widad, data fito daga motar cak ta tsaya tana ƙarewa harabar gidan kawai kallo.
Widad ce ta fito tana murmushi ta ƙaraso tana faɗin "oyoyo amaryar mu, sannu da zuwa Anty Hindu"
Hindu ta sunkuyar da kai cikin jin kunya.
Widad taja Hindu zuwa cikin gidan, yayin da Hindu ta kasa magana saboda tsantsar mamaki, ace a duniya akwai irin wannan gidan lallai jin daɗi yana birni, suna shiga falon Widad taji wani irin sanyi ya ratsata wanda babu shi a waje, tun Hindu na mamaki harta zubawa sarautar Allah ido, dan abun ya shallake hankalinta.
Widad ta dinga koyamata yadda ake amfani da wasu abubuwan, ta dinga kaita gurin gyaran jiki kafin lokacin biki.
Hindu tayi shar da ita, tayi kyau sosai sedai tana jin kunyar Widad sosai, saura kwana huɗu biki sannan Widad ta kira Daddynta a waya tace masa yazo ga amaryarsa a gidan ta.
Ba musu kuwa sega Daddyn a gidan, Hindu na jinjina rashin girman kai na mutumin nan, yana da matukar sauƙin kai da sanyin hali, dukda kuɗin da yake dashi, da kuma shekarunsa.
Yana zaune a falo, Hindu suka fito ita da Widad tayi kyau sosai, Widad tana ja da kyar saboda nauyin cikinta, Widad tace "Daddy ga amaryarka nan, bari in kawo muku abin sha" ta juya ta koma ciki.
Ƙafar Hindu na rawa ta ƙarasa gaban Dula, ta tsuguna tace "ina wuni"
Daddy yace "lafiya ƙalau Hindatu, ya baƙunta? Ina fatan dai Widad bata takuramiki?"
Hindu ta girgiza kai alamar a'a, yace "to in dai tana matsa miki, ki gayamin nida ita ne" yai maganar yana murmushi ƙarshe shikaɗai yai taɗin ya gama bata iya cewa komai, saboda kunya da kwarjinin sa.
Lokacin biki Aka aika da motoci ƙauyen su Hindu, aka kwaso su zuwa birni dan bikin 'yarsu, a tsohon gidansu Widad aka sauke su, sedai Hari tafi kowa rikicewa da ganin gidan nan, tun daga gate motocin dake harabar gidan suka rikita ta, suka shiga katafaren falon gidan, Hari ta rasa a ina zata zauna, tace "ohh ni Hari, yanzu wannan ko' a aljanna ka samu wannan ai ka more"
Hansai tace "ke Hari, ance talaka a gidan aljanna shine gidansa kamar girman duniya, kike cewa ki samu kamar wannan"
"Ke bari Hansai, ke kina tunanin kin aikata abin da da zaki samu wannan ne? Ai ni indai irin wannan ne yaseen ya isheni, kai jama'a kun lura da wani abun mamaki kuwa? Waje lafiya ƙalau amma ɗakin nan hunturu Aradu, sanyi ake sosai a cikin ɗaki ikon Allah"
Widad tasa aka dinga sauke musu Abinci, Abinci kala kala Gwaggo tace "Amarya wai ina 'yar tawa ne?"
Widad tace "wace' yar bayan nikuma?"
Gwaggo tai murmushi, Widad tace "zasu taho tare da Daddy, da kuma Umma"
Gida ya ɗau harama, aka kawo Hindu, suka dinga zuba guɗa, gaba ɗaya Hindu ta canza a sati biyun nan, tayi kyau sosai kamar ba ita ba.
Aka dinga ɗorawa ana sauke musu Abinci, aka ɗakko masu aiki da an ɓata guri su gyara, Da Yamma aka ɗauki Hindu aka tafi reception, na Daddy da abokansa da kuma Ahmad, dama umma cewa tayi ba zata ba.
Hanne kam ji take kamar tayi kuka, tafi Hindu kyau da haske amma zata auri wannan haɗaɗɗen mutum a birni, amma ita zata auri ɗan ƙauye, tunda suka zo Widad ko kallon inda Hanne take ba tayi balle tayi mata magana.
Washegari juma'a, aka ɗaura Auren Umma, da kuma na Hindu da Daula, anyi shagali sosai a gidan nan, dukda ba wani gagarumin taro suka yi ba, amma anci an sha sosai kowa yasan anyi biki, akaita yiwa Hindu Nasiha, akam haƙuri da tsoron Allah, Widad tace Gwaggo, da Hari suzo a raka Hindu gidan ta "
Hari tace" au wai dama nan ba'a gidanta muke ba? "
" Gidan Amaryar za'a sauke ku? Sannu Hajiya Hari me taɓargaza"
Haka suka cigaba da faɗansu da suka saba ita da Hari, Farm House aka sake gyarawa, aka canza furnitures wanda ya tattaka gidan da aka sauki su Hari, Hari se salati take da salallami wai "Nidai Hindu, idan ana neman 'yar wanke wanke dan Allah zanyi"
Widad tace "Kina uwatta zaki zo wanke2"?
"eh wallahi zanyi"
Tun Widad na biyewa ƙauyancin Hari harta ƙyaleta, saboda abun nata bana ƙare bane.
Bayan sun rakata, sun mata addu'a Gwaggo tace "to Hindu, mu daga nan gobe in Allah ya kaimu zamu wuce gida, ki zauna lafiya da mijinki da kowa ma, nasan dai baki da matsala amma dai ayi haƙuri"
Hindu ta rirriƙe Gwaggo tana kuka, da ƙyar ta cikata suka tafi, suna tafiya tsoro ya cika Hindu, saboda ita girman gidan ma abun tsorone, gashi tana jiyo kukan dabbobi kaɗan kaɗan a falon, tana cikin zare idone sega Daula ya shigo da abokansa.
Ta cukuikuye a cikin lifaya taƙi ɗago kanta balle ta kalli wanima, nan suka musu fatan Alkhairi sannan suka tafi.
Ayshercool
07063065680
12/22/21, 11:07 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
170
Bayan fitarsu Daula ya kalleta yace "taso mu tafi"
Ta ɗago a hankali ta kalleshi, sannan ta miƙe tana waige waige, ya miƙe yai gaba tana binsa a baya, wani gurin seta tsaya kallo, seta ɗago taga ya tsaya jiranta setai maza ta taho, ya dinga ratsawa da ita faluka, wai nan duk dan zaman mutum ɗaya akayi shi, suka zo ƙafar bene ya fara hawa tana binsa, sedai ta zame ta faɗi, saboda matattakalr benen kanta wata iri take ganinta, ga ƙananan fitilu a jiki, gata kamar ta glass ta tsaya kallo shine ta faɗi, a ɗan gigice ya waigo yna faɗin "subhanallah, garin yaya? Kodai ɗaukarki zanyi ne?"
Da sauri ta girgiza kai yace "sannu, miƙomin hannunki in riƙeki"
Ta miƙa masa hannu, ya riƙe hannunsa kamar bana namiji ba saboda laushi.
Haka suka ƙarasa saman bene, cikin katafaren falonsa, ji tayi sanyin data keji ya ƙaru, hartana nema ta fara rawar sanyi, yaje ya rage AC suka shiga bedroom, ai a jikin ƙofa ta tsaya tana kallon ikon Allah, lallai gaskiyar Saleh, da yace ko za'a saida duk kadarar da 'yan ƙauyensu suka mallaka baza su siyi ko da motar hawan Widad ba, balle wannan uban gidaje haka.
Ya bata gurin zama, ta zauna already kaji da kayan shaye2 suna ɗakin da plate da komai, amma juyin duniya Hindu taƙi ci, ba yadda beyi da ita ba, amma taƙi ci, se ƙyaleta yayi, sukayi alwala sukayi salla, bisa ga koyi ga sunnar ma'aiki salallahu alaihi wassalam, tare da yin addu'oi, ya miƙe yace mata ga gado cam taje ta kwanta, shi kansa gadon abun kallo ne, lallai Su Widad sun tara abun duniya.
Shima da ƙyar ta hau ta kwanta, ta dunƙule a guri ɗaya, ya ɗakko ƙaton bargo ya lulluɓa mata, ya cire babbar rigarsa taga ya sake tada salla, sannan hankalinta ya kwanta ta shiga baccin ta.
Wani irin laushine da katifar, ga bargon ma laushi se ƙamshine ke tashi a jikin bargon, cikin dare ta tashi a firgice saboda tsoro, Daula yace "lafiya kuwa?"
"tsoro nakeji"
Yai murmushi yace "aiba abunda ze sameki, ki rage yawan tsoro dan wataran ke kaɗai zaki kwana a gidan nan, ki kwanta kiyi addu'a, ba abin da ze sameki"
Haka ta kwanta tana cigaba da rarraba ido.
Sedai a yau ɗinne dai Hindu ta zama cikakkiyar matar aure, dukda tsoro da razanin data tsinci kanta a ciki.
Su Hari kuwa haka suka koma ƙauye, suna zuzuta haɗuwar gidajen da suka je, Abinci kam wannan duk azabar cin mugunta da suka yi seda suka barshi, akayi musu rakiya da sha tara ta arziki, yayin da ayyukan da ake musu sunyi nisa sosai, dan har an kai musu wutar lantarki ma.
Washegari Widad ta aika direba da Abinci ya kai gidansu, sedai ita amaryar ce taƙi sakin jiki sam, lokaci lokaci se Daula ya kalleta yayi murmushi, yarinya ce sosai sedai akwai kunya sosai.
Yace "ga Abinci Widad ta aiko, kizo kici ko in kirata in gayamata kinƙi cin komai"
"Aa' dan Allah karka gayamata"
"to zokici Abincin nan"
Ta sakko ta zauna, ya zuba abincin a plate, ya haɗa mata da tea ya bata, sedai kunyar ci take a gabansa, ta ɗan dinga cakala, ya karɓi plate ɗin, ya ɗebo a spoon ya kai bakin ta, kunya takeji sosai, ta sunkuyar da kai yace "haka zamuyi dake? In gayamata kina gaddama ko?"
Ta girgiza kai, yace "in bakya so in gayamata, maza karɓi kici"
Abun har mamaki yake bata, babban mutum haka amma ya zauna yana lallaɓata, seda taci ta ƙoshi ya jata zuwa wani ɗaki ya nuna mata kayan lefenta.
Banda wanda aka shirya mata a drower.
Umman Yusuf, kwana uku da ɗaurin Aure ta tare a babban birnin tarayya, Widad taso zuwa sedai tana daf da shiga watan haihuwarta, dan haka akace ta haƙura.
Bulama kuma tuni aka shiga zaman kotu, aka dinga shari'a ana warware duk wata ƙulalliya da makirci daya aikata, laifukan nasa da yawa danshi ƙarshe se hukuncin rai da rai aka masa, sauran kuma daga me shekaru Ashirin da wani abu seme talatin, Hajiya Halima kuma shekaru Ashirin da takwas itama, Ramlah kuwa hauka ta dingayi tuburan saboda azabar shaye2, ƙarshe se gidan mahaukata aka maida ita.
Bulama kuma ya dinga larura, ciwo bayan na ƙanjamau ya din rashin lafiya, aka kai shi Asibitin gidan yari ashe cancer ce ta kama masa hanji zuwa duburarsa, ga kotu dukata ƙwace kadsrorinsa ta mayarwa da Daula, bashi da komai ba shi da kuɗin daza'a masa aiki, ƙarshe haka gurin bayan gidansa ya dinga tsutsa, ga wani irin wari yanayi, shima Fahad ya samu shekaru sha biyu a gidan yari, gashi ga ubansa Alhaji Musa kuwa shima rai da rai ne hukuncinsa, saboda hadda laifin kashe matarsa, ga sugar ya fito masa a ƙafa, shima ƙafa ta dinga ruɓewa kamar bata ɗan Adam ba.
A hankali Hindu take ɗan sakin jiki da Daula, babban abunda yake burgeshi da ita shine, tsananin biyayya kamar zata shige cikinsa, ko magana yake mata kanta a ƙasa, wanda rabonsa da samun farinciki tunda Huda ta rasu.
Satinta biyu yasa ta a makaranta, ya ɗaukar mata me zuwa gida yai mata lesson, na ilimin addini dana zamani, kuma gata da saurin ganewa.
Yanzuma yana zaune ta ɗora kanta akan cinyar sa, yana nuna mata hotunan maman Widad daya ɗauka a wayarsa, Hindu ta zuba musu ido tace "masha Allah, tana da kyau sosai gata kamarta ɗaya da Widad"
Sam bata nuna masa kishi ba, sema addu'a data dinga yi mata.
Daula ya bata wani littafin turanci, yace ta karanta yaji, aikuwa ta dinga karanta masa, gashi makarantar da yasa ta, malaman su turawa ne, tana yi yana tafa mata yana murmushi.
Jin sallamar su Widad a falon, yasa cikin hanzari ta tashi daga kan cinyar Daula, tana neman ɗankwali, wai kar Widad taga kamar ta raina shi.
Widad tai murmushi tace "kekam Allah ya shiryeki, ni idan nice ba kunyarki zanji ba, mijin nakima da yake tsoho"
Hindu ta duƙunƙune fuska tana jin kunya.
Yusuf dai sedai ya kallesu yayi murmushi, sun daɗe a gidan se bayan goma sannan suka tafi gida.
A satin Saleh ya dawo, an masa aiki ya warke tsaf dashi, yayi murna da jin Daula ya Auri Hindu, shima an masa halacci sosai, sannan Daula ya canza masa aiki, aka maida shi Lagos.
Amal ma a nan Nigeria aka mata aiki, sedai taji sauƙi sosai anata ƙoƙari karta rasa hankalinta, likitan da yayi mata aiki ya nuna yana sonta ze Aure ta, Daula be ɓoye masa ba ya gaya masa komai game da Amal yace "Amma itama 'ya tace, idan kasan zaka aure ta ka wulaƙantata ka ƙyalemin' yata"
Yace "shi tsakani da Allah yake sonta"
Daula ya shige gaba ya karɓi kuɗin Aurenta, sedai ita tana Asibiti har yanzu.
Wataran da Safe, Hindu ta tashi daga bacci, sega kiran Widad, ta ɗaga wayar tana cewa "Maman biyu kin haihune?"
Widad tace "kedai bari, ina nan ina ja, ima wannan dattijon yake? Zanyi magana da shi"
"Hindu tace " waye kuma dattijon? "
" Mijinki mana "
" gaskiya kidena ce masa dattijo "
Widad ta dinga dariya tace" lallai Hindu, Allah ya baki haƙuri yana ina? "
Hindu tace "bacci yake yi"
"idan ya tashi kice masa, zan tafi Asibiti na fara jin ciwo, yayi min addu'a zanje inji abunda zasu ce, zan iya haihuwa ko kuma aikin za'ayi"
Jikiua sanyaye Hindu tace "insha Allah zaki haihu lafiya, ki kwantar da hankalinki"
Widad tace 'to Allah yasa"
Hindu ta ajiye wayar tai shiru, Daula ya tashi zaune yana cewa matar dattijo ha dai.?
Kallonsa tai tayi murmushi tace "lafiya, Widad ce tace zata Asibiti a duba, idan zata iya haihuwa ko kuma aiki za' a mata"
Da sauri ya karɓi wayar, ya sake kira Yusuf ya ɗaga yace "Daddy mina Asibiti, daga zuwanmu suka riƙe ta sukace haihuwa zata yi"
Daddy yace 'wani Asibitin ne? Gani nan zuwa "
Ya gayamasa, aikuwa anan da nan suka shirya shida Hindu suka tafi Asibitin.
Ansha daru da Widad kafin ta haihu, Allah ya temake ta ta haihu da kanta, sedai Yusuf ya sha kira sosai da Daddy.
Aka fito aka miƙo musu, santalelen jariri me kama da Yusuf sak, Daula ya karɓi Jaririn yana faɗin masha Allah, Alhamdilillah.
Nan ya shiga bige bigen waya, yana sanar da haihuwar ta Widad, nan da nan aka cika Asibitin 'yan barka, se bayan awanni huɗu sannan aka sallameta, suka tafi gida.
Daddy ya rasa inda ze saka ransa da murna, a ranar Umma ta dawo kano, Umma kamar ita akayiwa haihuwar, ta dinga murna tana farinciki ta ɗau jika.
Saura kwana biyu Suna su Hari suka zo daga ƙauye, da abun arzikinsu, megari yabada raguna biyu manya yace a yankawa jaririn nan, Yusuf yai masa huɗuba da Muhammad Bashir sunan mariƙinsa, anyi shagali sosai a sunan nan, jariri ya samu kyaututtuka daban daban daga gurin mutane.
Ana zaune a falon Widad, bayan an dawo daga event ɗin da akayi sunan, ba zato ba tsammani Widad tace "wai yaushe ne bikin Hanne"
Hari tace "to ai mijin natane har ynzu be shirya ba, lega yake tafiya neman kuɗi, amma dai abun dai duk se a hankali ba wata Ƙwaƙwaƙwarar sana'a da yake yi"
Widad tace "aiga 'yar uwatta nan Hindu, ta tambayar mata mijinta a sama masa abunyi shima"
Hindu ta kalli Widad, dan ita harga Allah bata iya tambayar Daula komai, to mema zata tambayeshi bayan komai ya ajiye mata.
Hindu tayi fuska ba tace komai ba, da daddare Daddy da kansa yaje ya ɗakko Hindu, bayan sunje gida har sun kwanta yace "Hindatu Widad tacemin zakiyi magana dani ko?"
Hindu ta girgiza kai tace "A'a"
"gayamin, nasan bazata miki ƙarya ba"
"Bafa nice ba, cewa tai wai ince maka a samawa wanda ze auri Hanne aiki"
Yai murmushi yace 'ta gayamin, ina son ji daga bakinki ne, daga yau kome kike buƙata kowa kike so ayiwa alfarma ki faɗa kanki tsaye zan masa, ance ya iya tuƙin mota, zamu bashi jan manyan motocinmu, sannan zan basu gida a nan garin, itama ta dawo ta zauna a nan ta shiga makaranta "
Hindu harda kukan murna, ta durƙusa har ƙasa tana masa godiya, ya girgiza kai yace" meye abun damuwa haka kuma? Karki damu kinji"
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, lokaci ɗaya akayi bikin Nurat da kuma Amal, kuma duk Daulane yayi musu walicci, da kayan ɗaki da manyan kyautuka ga kowaccensu.
Muhammad Bashir wanda suke cewa Aryan yayi wayo, kusan koda yaushe Daula ya kan je gidan Widad saboda Aryan, yana matuƙar ƙaunar Yaron.
Wataran da daddare Daula ya shigo yace "Hindatu, kisa hijjabinki zamuje muyiwa su Widad sallama, gobe in Allah ya kaimu zamuje Abuja, daga nan zamuje Dubai ki rakani taron kasuwanci"
Hindu tace "sekaje dani taron kasuwanci har wata ƙasar, abokanka za suyi maka dariya ka auri 'yar ƙauye"
"Ni matata ba' yar ƙauye bace, kuma ba inda zanji shakkar shiga da ita, in nunata ince wannan matata ce, saboda ina sonta a haka"
Hindu ta rufe fuska tana murmushi.
A daren suka tafi gidansu Widad, Hindu ta kama Aryan ta rungume tana ta masa wasa, Widad ta karɓi Aryan ta bawa Daddy, taja Hindu ɗakinta, ta bata wata riga tace ta gwada, Hindu ta cire hijjabinta ta gwada rigar, abun da Widad ke son gani, kuma ta gani ciki ne a jikin Hindu.
Widad tai kamar bata gani ba, ta bata kyautar riga, a ranta tace "shine Daddy bemin Albishir ba.
Widad tana jin daɗin yadda mahaifinta ya samu nutsuwa, Dan ita kanta ta lura da yadda Daddy ya samu nutsuwa, da biyayya da take masa, daga ita har Daddy sunyi tsaf dasu sunyi ƙiba, watan Aryan biyar Widad tabi Yusuf Lagos, ya kama harkar kasuwancinsa sosai.
Watannin cikin Hindu tara ta haihu, amma seda aka mata CS aka cire yaron daga cikinta, saboda yai girma da yawa, kwana biyu tana labor, sannan aka mata cs ɗin aka cire yaron.
Widad kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murna, an yi mata ƙani, yaron kamarsa ɗaya da Yusuf sak, kamar shiya haife shi, kuma kusan duk kamaninsu ɗayane dai da Daula.
Daula be taɓa saka ran ze sake haihuwa ba, lokacin da aka gayamasa Hindu na da ciki ma, shiru yayi da bakinsa yaita Addu'a, da cikin ya fara girma kuma ya dena zuwa ko ina da ita, saboda kar itama ayi mata yadda akayiwa Huda, se yanzu data haihu sannan kowa yaji, an taya Daula murna sosai, da kyautar da Allah ya bashi na ɗa namiji.
Widad anyi ƙani, ga kuma ɗa da miji, murna ba kama hannun yaro, se bayan sati biyu akayi gagarumin shagalin suna, a garin kano, har Nurat da 'yan gidsnsu sunje barka, sedai Widad sam bata shiga sabgar Nurat sosai, seda Daddy ya zauna ya sata a gaba, yaita mata faɗa da Nasiha, sannan take ɗan sakin jiki da ita kaɗan.
Duniya ta dawo sabuwa ga wannan ahali, suka dinga tara zuriya, dukda Daddy ya manyanta amma seda Hindu ta haifi yara huɗu dashi, Widad ma ya haifawa Yusuf yara uku.
Bulama kuwa bayan shekara shida a haka ya mutu a gidan yari, yana wannan tsutsar da zubar da ruwan, babu wanda yake iya zuwa inda yake saboda wari da ɗoyi, haka aka yasar dashi a gadon Asibiti, harya mutu babu wata cikakkiyar kulawa haka ya mutu a wulaƙance.
Lokaci lokaci Amal ta kanje ta kaiwa mahaifiyarta ziyara a gidan yari, sannan tana zuwa gidan masu rangwamen hankali, Ramlah ta zama mahaukaciya tuburan, se an ɗaɗɗaureta haka zatai ta ihu tana fizgar gashin kanta, idan bayan gidane a nan za tayi, komai a gurin take yi, ta zama mahaukaciya tuburan, abun da Hajiya Halima taso Widad tayi, shine ya faru a kanta.
Duk wanda ya zamana da sa hannunsa a badaƙalar da Bulama yayi, seda aka masa hukunci daidai da shi, daya mutu ma ds ƙyar aka samu masu masa jana'iza, sedai kowa yana toshe hanci saboda yadda jikinsa ya dinga ruɓewa tun yana raye, ga kowa baya faɗan alkhairi akansa, sedai sharrinsa da Allah wadaran.
Daula baya ƙasar lokacin daya samu labarin rasuwar Bulama, amma seda ya zubda hawaye jin irin mutuwar da Abokin nasa yayi, tabbas da yana Nigeria dashi za'a sallaci Bulama, ya dinga kuka yana "Allah ya jiƙanka Abubakar, Allah ya maka rahama ya yafe maka, yasa jinyar da kayi kaffara ce, ni dai na yafe maka abubuwan da kamin, Allah ya yafe maka"
Seda Widad taji haushin yadda Daddy ya damu saboda mutuwar Bulama.
Daula a haka ya dinga sawa ana kai kayan Abinci gidan yari, da gidan mahaukata, Arziki ya cigaba da bunƙasa, Hindu ta zama hamshaƙiyar mace itama, Daula ya ɗau nauyinta taita karatu na addini dana zamani.
Umma dai Allah be bata haihuwa ba, amma bata sa hakan a ranta, saboda tana da Yusuf ga sirikata ta ɗaiketa uwa, ga yara sun haifa suna da jikoki, gashi tana zaune da mijinta da matarsa lafiya, yaransa suna matuƙar girmama ta.
Yusuf ma suka samu kyakkyawar rayuwa, suna zaune abunsu a garin Lagos da yaransu, ƙauyen su Hindu kuwa, banda wanda yasan ƙauyen ƙayaune a baya ba zakace shine a yanzu ba, saboda cigaban da suka samu ta kowane fanni, bazasu taɓa mantawa dasu Widad ba, saboda a sanadinsu ne Allah yasa suka samu wannan cigaban wanda basu samu ba a baya.
TAMMAT BI HAMDILLAH
9/12/2021
ALHAMDILILLAH ALA KULLI HALIN, ALLAH YA NUFA NA KAMMALA WANNAN LITTAFIN NA AƘIDATA, INA FATAN DARUSSAN DAKE CIKI ALLAH YA BAMU LADA, AKASIN HAKA UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA.
A TARA NAN GABA KAƊAN DOMIN JIM LITTAFIN DA ZANZO MUKU DASHI, AKWAI LITATTAAFAI JINGIM A TASKAR COOL, WASU NA KUƊI WASU NA KYAUTA, INA FATAN DUK WANDA NAZO MUKU DASHI, ZAKU KARƁA HANNU BIYU, NAGODE SOSAI DA KULAWARKU DA KUMA ƘAUNARKU A GARENI
SANNAN INA SON JIN RA'AYOYINKU AKAN WANNAN LABARIN DA KUKA KARANTA
NAGODE SOSAI, A KODA YAUSHE INA MATUKAR ALFAHARI DAKU MASOYA.
ƘOFATA A BUƊE TAKE, DAN GYARA, SHARHI KOKUMA SHAWARA
AYSHERCOOL
07063065680
0 comments:
Post a Comment