shiru Yusuf yayi yana kallon Widad, yayin da yaji gaba ɗaya hantar cikinsa ta kaɗa jin abunda Widad ɗin ta faɗa, ta kalleshi tace
"Ya naji kayi shiru ne? Akwai matsala ne?"
girgiza mata kai yayi yace
"A'a babu komai" Widad tace
"Shikenan, ga Abinci can, kaci seka sha magungunanka ka kwanta"
Kasa motsawa yayi daga inda yake, balle ya aikata ɗaya daga cikin abunda tace, sake kallonsa tayi tace "wai ko dai jikin ne?"
Girgiza mata kai yayi yace "A'a jikina ai na warke"
" to ai gani nai duk ka wani koma so silent, shiyasa nayi zaton ko jikin ne, ka tashi zan kwanta "
Yusuf ya miƙe, ya bata guri ta gyara shimfiɗar ta ta kwanta, yayin da ya koma gefe yayi jugum kamar wanda aka gayawa saƙon mutuwa.
A ƙoƙarinsa na kaucewa zargi daga Widad, ya miƙe ya ɗakko Abincin da niyyar ya fara ci, Amma gaba ɗaya ya ya kasa, tunani burjik a zuciyar sa, ga labarin da Saleh ya gaya masa, ga kuma itama abunda ta faɗa masa yanzu, ashe dai da daru a gaba, ko wane irin hukunci zata yi masa idan ta gano shi jami'in sirrine? Gashi zuciyarsa ta riga ta gama kamuwa da tsananin ƙaunar Widad, yana matuƙar jin sonta a ransa, a yanzu haka dama yana ɗar ɗar, saboda yasan bashi da tabbacin idan suka koma gida Widad ta cigaba da zama da Auren sa, dukda a yanzu yana ƙoƙarinya jarraba Widad yaga ko tana son shi, a ƙaddara ma ta yadda da Auren, su cigaba da zama tare, waye yasan Aure suka yi, Saleh ne kawai sheda ta yaya zasu fuskanci mutane suyi musu bayanin wannan rikita rikita?.
Nan da nan wani irin gumi ya shiga tsasttsafowa Yusuf, lallai akwai ƙura a gaba, kasa cin Abincin yayi, dama gashi bakinsa babu ɗanɗano saboda zazzaɓi, dan haka ya ajiye Abincin a gefe ya nemi guri ya kwanta, sedai kamar yadda beyi tsammani ba, bacci ya ƙauracewa idonsa se tunani, yanzu meye mafita? Ta ina ze tunkari Widad yayi mata bayanin waye shi, dan kamata yayi ace shi ya gaya mata ba wani ba.
Haka nan jiki a sanyaye ya cigaba da tunani, ya daɗe a zaune ba tare da ya kwanta ba, yana ta saƙawa yana warwarewa.
Muryar Widad yaji tace "Tunanin Meka ke hakane wai?"
Da sauri ya dawo daga tunanin da yake yace "Babu komai karki damu"
"Ko kana tunanin gidane, da Ummanka?"
Murmushin dole ya ƙaƙalo yace "A'a"
"Nasani dole zakayi tunanin gida, nasan baka jin daɗin zaman garin nan, ko baka faɗa ba zaman garin nan ba daɗi, Amma ni ta wani ɓangaren rahama ne a gare ni, bana fargaba ko tashin hankali saboda maƙiyana, ina matuƙar jin daɗin karamcin da mutanen gidan nan suke min, dukda yadda zaman garin ke bani wahala, amma karamcin su da goyon bayanka na ƙara bani ƙwarin gwiwa, tabbas duk wani motsi da zanyi ina tunanin Daddy, ina tunanin wani hali yake ciki, me yake yi? Nasan ina ransa, sedai ina masa Addu'a zuwa lokacin da Allah ze kawo ƙarshen wannan abun in koma gida, kaima kayi haƙuri nasan duk nice silar shigar ka wannan halin"
Ta ƙarasa maganar cikin damuwa. Yusuf yace "bana dana sanin kasancewa ta dake anan, saboda karamcin mahaifinki da yadda da yayi dani beci ace na bar 'yarsa ɗaya tilo ta shiga wani hali in kasa temaka mata ba, sedai dole inyi kewar Ummana, bata da kowa seni, mahaifina ya rasu, gata marainiya ni kaɗai ne a kusa da ita muke rayuwar mu tare, Allah kaɗai yasan irin damuwar da take ciki, dan tunda na tashi ban taɓa nesa da ita ba, nasan tana cikin damuwa "
Cikin tausayawa Widad tace
"Allah sarki, dole zukatan makusantan mu su shiga damuwa, har gara kai wataƙila bayan mamanka akwai wanda zasu damu da halin da kake ciki na ɓatan da kayi, nikam daga Daddy na se Bulama nasan sukaɗai zasu damu, duk wanda yake tare dani, yana tare dani ne dan wannan dukiyar, nasan da babu ita da bazasu nunamin so ba, kuma nasan zagina suke a bayan idona, shiyasa nake wa mutane wani kallo na daban, a da na zata duk mutane miyagu ne, kuma talakawa zasu iya komai akan kuɗi basu da kirki, sedai wani darasi da nayi shine, shi rashin kirki ba'a talaka ne ko me kuɗi ba, a mutum ne kawai, na samu misali akanka da kuma mutanen ƙauyen nan, basu san koni wace ba, amma suna ta kyautatamin"
Yusuf yace "hakane kam, naga kin sake dasu sosai kamar bake ba, kamar ba kece me wannan AƘIDAR ta ƙin mutane ba, me yiwa mutane kallon miyagu ba"
"Hmm ina da dalilin yin hakan, ka kwanta dare ya fara yi, kaga baka da lafiya akwai buƙatar ka samu isashen bacci"
Yusuf yace "Hakane, kema ki kwanta my queen"
'ba zaka dena faɗar wannan sunan bako? "
"Dama bakya son sunan ne? "
"ban sani ba, ai kasan nace maka bana so"
Yusuf yace "ni gaskiya daɗin sunan nake ji, My Queen, My life, I love you so much My dearest Queen"
Tsaki tayi, ta canza position ɗin da take kwance ta toshe kunne ta, wai danma karta cigaba da jin meze ce"
Yusuf yayi murmushi, ya kwanta sedai fa bacci yaƙi yuwuwa, saboda saƙawa da warwarewa da yayi tayi, akan ya sanar da Widad gaskiya waye shi, kokuma karya gaya mata?
"Barrister Hafiz, kuyi duba a cikin lamarin nan da kyau, ku tsananta tunani kafin yanke hukunci, akwai gwagwaɓar riba da zaku samu idan akayi wannan harƙallar daku, zaku samu alheri fiye da tunaninku, zaku samu arziƙin da baku samu a harkar aiki bama"
Barrister Hafiz ya gyara zama yace "Abunda nake so ku fahimta anan shine, wannan aikin fa hatsari ne dashi, mu sa hannu a siyar da kadarorin Daula, karkuyi mamaki akwai masu bibiyar al'amuran dukiyarsa bamu sani ba, idan abu yazo ya tonu sunanmu ze ɓaci, kuma mu rasa aikin mu, sannan mu fuskanci fushin hukuma"
Alhaji Musa yace "Barrister, sha'anin ƙasar nan tamu yanzu kowa mafita yake nemawa kansa, da kayi ƙaramin laifi a kaika prison a banza, gara kayi gagarumi wanda zaka samu mafita a al'amuranka, kuɗi zaka samu manya ba ƙanana ba, wanda baku taɓa zaton samu ba, kuma a yanzu waye yasan inda Daula yake? Idan abubuwan nan suka samu zaku iya barin ƙasar ma gaba ɗaya, dan haka ku san dabarun da zakuyi, kuyi mana wata takarda da zata nuna yayi holan wasu daga kadarorinsa, a bisa farashi me sauƙi ".
Ya kice gumi Barrister Hafiz yayi yace" Yallaɓai akwai buƙatar a ɗan bamu lokaci, zamuyi shawara tukuna "
"Shikenan, amma bama buƙatar a ɓata dogon lokaci, muna sauraren ku"
"Shikenan yallaɓai, sekun jimu"
Hajiya Sarah ce zaune gefen Bulama, yana shan tea yana karanta jarida, tace
"Yallaɓai, dan Allah ka tausayawa Hajiya Halima, kasa baki a sakar mata ɗanta, gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, hankalin ta gaba ɗaya baya jikinta saboda damuwa"
Bulama ya nisa yace "banƙi ta taki ba, amma baki fini son Halima ba, da ina da yadda zanyi da zanyi ƙoƙari in saka a fitar da shi, amma wannan case ɗin ba ƙarami bane, idan na matsa sunana ze iya ɓaci"
"Hakane amma ya kamata kayi wani abu, koda ta ɓangaren kwantar mata da hankali ne, Allah kaɗai yasan halin da take ciki, ba ƙaramin abu bane uwa ta iya jure ɗanta a wani yanayi, idan ka bincika babu lallai ko Abincin kirki tana iya ci"
"Eh to banƙi zancen ki ba, amma Halima mace ce me taurin kai da rashin haƙuri, maimakon tayi haƙuri a bi komai a hankali, amma se azalzala ta take, irin wannan lamarin a hankali ake binsa, amma ita ta fiye garaje, case ɗin nan ba ƙaramin case bane ba, karki manta Daula ne fa aka nema aka rasa, kuma shine yake kula dashi, gaba ɗaya ana saurarar hukuma aji me zasu ce, Amma insha Allah ze fita "
Hajiya Sarah tace " shikenan, Allah yasa amma tana cikin damuwa sosai, Allah ya fitar dashi, dan yaron kirki ne sosai "
Bacci be ɗauki Yusuf ba se wajen Asuba, dan haka da Asuba kasa tashi yayi, Widad ce ta fara tashi taje tayi alwala, ta dawo amma be tashi ba.
Hannu tasa tana ɗan dukan ƙafarsa tace " ka tashi ka makara fa yau "
A hankali Yusuf ya motsa yace
"Subhanallah, kuma shine zaki dinga dukana haka da ƙarfi, sekin jimin ciwo?"
"wannan ɗan dukan ne zan ji maka ciwon?"
"Eh mana duba gurin kiga, har yayi ja fa, kin zage ƙarfinki kina ta faman dukana"
Dagewa tayi ta ƙara masa wani dukan tace "wannan kuma se kace na karya ka ko?"
Yusuf yace "kai, tabbas idan na riƙe ki se na rama, zan rama wannan dukan da kika yi min" yai maganar tare da miƙewa ya fita waje domin yin alwala yazo yayi sallar Asuba.
Da gari ya ƙara haske, Gwaggo ta aiko musu da koko da ƙosai, Widad ta zauna ta dinga tsintar ƙosan ta naci, tace bata shan kokon, shikam Yusuf yaji daɗin yadda ta fara sakewa, yanzu tana iya cin Abincin su, dukda a yanzun ma bakomai take iya ciba, amma tana iya cin wasu abubuwan, yanzu wanke wanke ma, ita take abunta ta wanke banɗaki, wataran kuma Hindu ce ke mata.
Yusuf ya kalleta yace "meyasa ba zaki haɗa da kokon ba?"
"nifa ba son wannan kokon nake ba, wataran ji nake kamar zanyi amai idan na sha"
Yusuf yace "Allah yasa Baba Hari ta jiki, Kisha faɗa da baƙar magana"
Dariya Widad tayi tace "Aikuwa dai, ai gaba ɗaya matar nan comedy ce, komai ta gani se tayi magana, wani abun ina sane nake yi, amma bata ganewa taita faɗa"
Yusuf yace "Hmm Allah ya shiryeki to, aini ban san haka kika iya neman magana ba, ganin cewar a baya ko maganar ma bakya son yi, idan anga fara'arki to da magenki ne roux ko kuma Daddy"
"Allah sarki, harka tunamin da sister roux ɗina, nasan tana missing ɗina, maybe ma yanzu sun barta ta mutu saboda yunwa, nasan bame kulamin da ita, nima haushina suke ji balle magena"
Yusuf yace "Eyya Sorry, Insha Allah bata mutu ba zamu koma ki tarar da ita tana nan"
"Hmm is very hard gaskiya, am missing Home Yoseef, ina tunanin dabbobina gaba ɗaya nasan suna missing ɗina"
"wai me yasa kikafi son dabbobinki akan mutane, kina ƙaunar dabbobi sosai"
Widad tayi ajiyar zuciya tace "labarin yana da tsayi sosai, Amma tabbas dabbobi sun fiyemin mutane, except in some circumstances, duk abu indai dabba ta shaƙu da kai, ba zata yadda a haɗa kai da ita a cutar da kai ba, amma dan adam fa yana iya manta dukkan alkhairinka a hada kai dashi a cuceka, shiyasa na zabi rayuwata a cikin dabbobi”
Yusuf yace “hakane maganarki amma sedai ba duka aka zama daya ba, Amma na Allah ai basa karewa sannan ba yadda zaai ace mutum yayi rayuwa ba mutane"
Widad tace "kai ka ga haka, nikam nayi, kuma yafi kwanciyar hankali"
Yusuf yace "Ai ba ƙaramin mamaki nayi ba, ranar dana ga kina sukuwa akan doki"
Widad tayi murmushi tace "i miss that Moment, ko a England ina wasan polo, ina son tseren dokuna sosai"
Yusuf yai murmushi yace "ko tsoro ba kya ji"
Daga nan be kuma cewa komai ba ya maida kai yayi shiru yana da cin abincin a hankali, widad ta kalleshi tace kamar
" akwai Magana abakinka da kake so ka gayamin,naga jiya tun jiya kana ta yawan kallona"
Yusuf yace aini kullum cikin kallonki nake, babu wani abu da nake son gayamiki
"shikenan tunda kace haka,amma gara inda akwai ka gaggauta gayamin, bazan takuraka seka gayamun ba amma nasan akwai abunda yake damunka”
“kinfara samun ido kenan?”
“ba ido nake samka ba, yanayinka ne ya nuna min, amma shikenan ba ina kokarin matsa maka bane, ko son sanin me kake ciki ba, ni bari in tashi in fita in dan sha iska”
Yususf ya kalleta yace “bana son kifita ki barni,ina jin daɗin hirar nan da muke”
Yamutsa fuska tayi tace "ni kuma na gaji da zaman dakin, dan haka waje zan fita”
Yusuf yace “shikenan tunda haka kike so,your wish is mine my queen”
“ka ji dashi dai, inka gama karka manta da shan maganinka" daga nan tai waje abunta
Alhaji Haruna ne shida Alhaji Munir suke cigaba da tattaunawa akan al amuransu.
Alhaji Munir yace "‘anya baka ganin ayi kokari a sakarwa matar nan danta, da yasan inda Daula yake iya azabar da aka gana masa ya isa ya fadi inda yake, amma tunda be faɗa ba to tabbas besan inda yake ba, gashi ana batun tafiya kotu, karfa matar nan ta tona mana asiri”
Alhaji Haruna yace “ka kwantar da hankalin ka, hakan ma duk shirine, idan sun tafi kotu, za a dauke hankalin mutane daga wasu abubuwan, da zarar hankali ya dauke ya karkata can, mukuma semu cigaba da barnar mu, kafin a farga mun kwashi abunda muka kwasa koda wancan abubuwan basu samu ba”
“banƙi ta taka ba, amma ka gane wani abu guda daya, mudinga yi muna ankarewa da abunda ze biyo baya, yanzun idan aka shiga kotun nan slide mistake ze iya sakawa asrinmu ya tonu, sannan maganar da muke har yanzu fa babu wanda yasan inda yaran nan suka shiga, tunda suka gudu har yanzu shiru babu labarinsu, babu labarin inda suka tafi, kuma har yanzu basu dawo garin nan ba, gaba daya a tsorace nake, kuma yakamta ace zuwa yanzu shi wannan yaran da muka sa su sace su me adda yake kowa?, yakamata ace basa raye bekamata abarsu suci bulus ba,suma fa hatsarine as garemu”
Alhaji Haruna yayi murmushi yace “Alhaji Munir ikon Allah, kaikam wasu lokutan akwaika da tsoro, munefa masu kasar nan, ko yaya muka ga wani abu na shirin kawo mana tangarda zamuyi maganinsa, mukeda hukumar tsaro kudi da masu mulki, kai a tunnainka har akwai wani wanda ze kawo mana tarnaki ne? ka sha kuruminka, komai a tsare yake, shekara nawa mukayi ana tafiyar nan, ba tare da an samu mtsala ba? Karka manta Alhaji Bukar ma fa namune, kadai mubi komai sannu”
Alhaji Munir yace “ duk nasan da wanan, amma abunda nake so ka sani shine,wannan mahaukaciyar matar fa zata iya komai idan taji za a kaimata danta prison,bafa zata zuba mana ido tana kallo danta ya tafi prison ba”
“karka damu za a san yadda za ayi da ita”
“shikenan, amma nifa kwanan nan na fuskanci wasu halaye da Musa yake yi, sam na kasa gane kansa fa”
“ba kai kadai ba, nima kallonsa kawai nake, kar ace na fiye matsawa ne ko neman rigima shiyasa kawai nake kyleshi”
Alhaji Munir yace “Banda shi mahaukaci ne, wai takara ze fito, ubanwa ze zabeshi bayan bakin tabon da Daula ya goga masa, ai mutane ba mahaukata bane”
Alhaji Haruna yace “kyaleshi ai ya zata mutane basu da hamnkali, a da alokacin da yayi siyasar ma ai farin jinin Daula ne yasa aka zabeshi, ba wai dann ya cancanta ba, mu zuba masa ido ya cigaba da haukansa tunda bashi da hnakali”
“aikam babu alamar hnakli, gara yaje mutane su cinye ɗan abunda ya tara ɗin ai, se sun talauta shi sannan yazo ya fadi zaben, mutum se taurin kan tsiya, baya ɗaukar shawara sam, indai 'yan siysa ne zasu ziga shine, su cinye komai idan ya fadi su gudu su barshi”
Alhaji Musa yace “:ai shiyasa ban damu da in bashi shawara ba gara yaje suma suci rabon su, daga baya yayi hankali ai”
‘shikenan, ni bari in wuce se munyi waya”
“shikenan,semunyi waya”
Daga na sukayi sallama.
Ganin wucewar Hajiya Halima ne yasa Ramlah bin bayanta zuwa dakinta, tana zuwa tace “Mummylafiya kuwa?”
Zama hajiya Halima tayi tace “ina fa lafiya, wai kotu za akai Anwar kotu fa Ranlah”
“mummy wane irin kotu kuma? Ba za bada belin nas ba ?”
“sun hana , sunce ba zasu bada belinsa ba, kuma wadan nan banzayen sunki suyimin komai akai, sun barni se wahala nake nikadai, nikadai na haifeshi nikadai nake wahala ta, dan san abunda ze biyo baya kenan da ban barin Anwar yaje yana wannan wahalar ba, idan yaso ba zagi ba ko tsinewa ce duniiya sumun baze dameni ba,amma ina kallo akaimin da na prison baze yuwu ba, niba abun in tona asiri ba, nima zan kwana a ciki, da sedai ayi duk wadda za ayi”
Ramla tace ” mummy kiyi hakuri, ki kwantar da hankalinki, idan kika fallasa ba iya asirinsu ba hatta namu muma ze tonu ne, dan haka kiyi hakuri mubi a hankali”
“wani irin mubi a hankali komai yana lalacewa, in zuba ido akaimin ɗana prison sam baze yuwu ba wallahi, ana shiga kotu nasan prion ne zasuce zasu kaimin shi”
“babu me kaishi prison, kidena damun kanki, Anwar ze fito”
Haka taita kwantar mata da hankali.
Tunda widad ta fice tsakar gida bata sake komawa ɗaki ba, tana maƙale da Gwaggo da Hindu tana koyo aikin gida, yayinda gefe guda sunayi suna faɗa da Hari, yayinda Hanne keta jifanta da bakaken maganganu, wani abun Widad ta gane wani ba zata gane ba, dan wata hussar ina tayi tsauri bata ganewa sam, ita dai tafi maida hankali akan ta koyi aikin,Gwaggo bata hantarar ta idan tayi ba daidai ba seta gyara mata cikin ruwan sanyi.
Saleh ne ya shigo gidan, ya tarar Widad zatayi tatar gasara, tanata kokowa da abun tatar Gwaggo tana gyara mata, gashi ta maida duk hankalinta so take ta koya, gwanin ban dariya da tausayi.
Saleh yace "Ina kwana ranki ya dade?”
Dagowa widad tayi ta kalleshi cikin basarwa tace “lafiya kalau”
Saleh yace “aiki kike ne?’
Gwaggo tace “aikam aiki muke tayi”
”madallah sannu da kokari Gwaggo, ya me jiki kuma?”
Gwaggo tace “jiki da sauki Alhamdilillah”
“mashaallah, bari inshiga in duba shi”
Widad na jinsu tayi masa banza taki kula shi.
Da sallama Saleh ya shiga dakinsu Widad, ya tarar da Yusuf a zaune yayi shiru yayi zurfi a duniyar tunani, Yusuf ya dago ya amsa.
Saleh yace “ya dai ko jikin ne?”
Yusuf yace “ jiki ai naji sauki Alhamdilillah”
“madallah ai haka ake fata, ai can naga mutuniyar taka a tsakar gida tana ta kokawar yin tatar gasara, se barna take”
Yusuf yayi dariya yace “danma baka ga yadda take tankaɗe ba, bakaga asarar garin da tayiwa Gwaggo ba, ai Gwaggo ba karamin mutunci take man aba, se fatan Allah ya sakamata da alkairi”
Saleh yace “ai abunma da takaici ace yarinya kamar wanna bata iya aikin gida ba,abun da kunya ai”
“yakamata kiyi mata uzuri da an koya mata da zata iya ai”
Saleh yace “waye ze koya mata, ta dinga hantarar mutum tana masa wulakanci”
Yusu yace “adinga kara mana matata ce fa Saleh”
Sale yai murmushi yace “masu mata manya,to Allah ya bada hakuri, na manta ne, Allah yasa in an tashi komawa a tafiwa da Daula jika”
Shiru Yusuf yayi bece komai ba yana tunani, Saleh yace “lafiya kuwa?”
Yusuf yace “Saleh akwai matsala ina cikn damuwa sosai, har yanzu bata san waye niba, bana son taji a wani gurin tayimin kallon makaryaci, yanzu ban san ta in zan faraba bansa n ya zata kalli abunba, zata iyayimin bore ina tsoron darunta”
Saleh yace “hakane amma ai kai namijine, kuma zuwa yanzu duk ta rage wasu abubuwan ai, ba lallai ta maka wulakanci tunda yanzu ba wanda ta sani se kai”
“Saleh anya ba ka manta wacece Widad ba? Jiya ta gama jadaddamin bata yafiya ga wanda yayi mata karya ko yaci amanarta”
Saleh yace "ƙwarai na san wacece ita, yadda ta gaya maka hakane bata yafiya ga wanda yayi mata ƙarya ko yaci amanarta, duk yadda suke da shi kuwa, amma ai kai akwai alaƙa me matuƙar ƙarfi a tsakaninku, zata iya ɗaga maka ƙafa kuma kamata yayi ace kai da kanka ka gaya mata, karka bari taji a waje, idan kuwa ka kuskura ta samu labari a gurin wani akwai matsala, dan bata ƙi ka tafi prison ba kaima, tace an haɗa baki da kai za'a cuce ta, abun da nake ganin dai yafi shine ka sanar da ita kawai, hakan zefi "
"tabbas nasan bata yafiya ga wanda yaci amanarta, nikam Saleh me kayi mata wanda yasa ta kasa duba alkhairin ka se laifukanka? "
Saleh yayi murmushi yace " labari ne me tsawo Yusuf, kuma gaya maka labarin tamkar ƙara wani laifin ne akan laifi, amma ka bari idan tayi niyya zata iya gaya maka komai, nidai shawarata da kai, tun kuna nan ka gayamata waye kai"
Yusuf yaja ajiyar zuciya yace " Inajin tsoro Saleh, harga Allah ni fa ina son Widad ne tsakani da Allah, yanzu idan na gaya mata zata iya ƙina, a yanzu mu tana ƙasa tana dabo ne, dan itafa bata yadda akwai so ba, dan haka bani da tabbacin tana sona, kuma inzo in gaya mata wannan magana, abun ze lalace gaba ɗaya ne fa"
Saleh yace "haba namijin duniya, ai kai kana da jarumrtar da ka cancanci a sara maka, haka nan duka butulcin me butulci dole ya sarawa namijin ƙoƙarin da kayi akan Widad, ni kaina na fuskanci sonta kake, amma dole zata ɗaga maka ƙafa dan baka cancanci ta wulaƙanta ka ba, be cancanci ta manta da alkhairin da kayi maka ba, dukda yarinyar wata irin muguwar bahaguwa ce, amma kayi ƙoƙari kafin ku bar garin nan tasan abunda ake ciki "
Yusuf ya dafe kai yace " Subhanallah, ban san ta ina zan fara ba Saleh, ina tsoron abunda ze biyo baya, ni kome zata yi baze dameni ba, ni fargaba ta karta rabu dani ko tayi min wata mummunar fahimta "
" Yusuf kenan, da alama wannan ne karonka na farko na shiga soyayya ko?"
Yusuf ya girgiza kai yace " Na taɓa soyayya Saleh, har na sawa kaina bazan sake soyayya ba, katsam Widad ta shigo cikin rayuwata ba tare da na warke daga wancan ciwon dake zuciyata ba, kuma har nake jin cewa a yanzu inawa Widad son da banyi wa waccan yarinyar ba"
Saleh yace "lallai kana cikin Jarrabawa Yusuf, ina maka fatan Alkhairi tare da fatan Allah ya fitar da kai"
Sallamar Widad ce a ɗakin ta katsesu, suka amsa mata gaba ɗaya, fuskarta duk bushashiyar gasara, kanta babu ɗankwali goshinta duk gumi.
Ta kalli Saleh ha haɗe rai tace "Excuse us please"
Saleh yace "to" ya tashi ya fita ya bar ɗakin.
Ta kalli Yusuf tace "ka zauna kana ta surutu, baka san lokacin salla yayi bane, har an fara aikowa ana tuna maka, kaje kaja salla"
Yusuf yace "aini yanzu gaba ɗaya kunyar mutanen nake ji".
Widad tace "me kayi musu na kunya?"
Yusuf yace "tunda kika rungume ni a gabansu, indai suka ganni se inga suna wani sunkuyar da kai"
Ɗan guntun tsaki Widad tayi tace "to dana rungumeka a gaban su is it an abomination? Saɓo nayi kome?"
"to ai su basu saba ganin irin haka ba, is against their norms"
Widad tace "to su suka sani, ni wanka zanje inyi, kaje kayi sallar"
Yusuf yace "to bari inje in dawo in rama dukan da kika yi min da Asuba"
"ina nan ina jiranka kuwa, kasan dai na fika ƙarfi yanzu, kai sauro ya zuƙe maka ƙarfi".
"dole kice haka mana, tunda na baki jinina, dole kiyi ƙarfi ai"
Ta kalle shi tace "ji wata magana, jinin naka ma da bashi da kyau, duk ba wasu sinadarai a cikinsa, shine duk ka dameni da ka bani jini, to zan biya ka abunka"
Yusuf yayi dariya yace "kamar gaske"
Yai waje, yana fita ta kintsa ta ɗau bokiti ta tafi taje tayi wanka.
Tana zaune tana shafa man zaitun a jikinta Yusuf ya dawo, ta bawa ƙofa baya, farar fatarta se ƙyalli take da ɗaukar ido, ga baƙin gashinta ya kwanta sosai a bayan ta, ƙasansa ya jiƙe da ruwan wanka, ba taji dawowar Yusuf ba se jinsa tayi zaune a kusa da ita, numfashinsa na sauka a jikinta.
Da sauri ta ɗago ta kalle shi tace "meye haka? Ya zaka zo ba ko sallama, ka zauna kana shinshinani"
Seda tasa Yusuf yayi dariyar dabe shirya yinta ba, yace "niba shinshinaki nake ba, se kace wani kare"
"to baga numfashinka nan inaji a jikina ba"
Beyi magana ba, ya kalli hannun ta data tsiyayo zaitun, ya zura nasa hannun akan nata, zaitun ɗin wani duk ya zube, ya shiga shafa mata a jikinta.
Ji tayi tsaigar jikinta na tashi, ɗan yamutse fuska tayi tace "Yoseef bana so, ka bari in shafa da kaina"
"Ni kuma ina so, ki bari in shafa miki"
Tsaki tayi ta ɗan ɗaga murya tace "nace maka bana so" tai maganar tana ƙoƙarin miƙewa, Amma Yusuf ya riƙeta ya hanata tashi, a hankali yace "yi haƙuri Widad, magana nake so muyi" yai maganar yana sauke numfashi.
Littafin kuɗi ne, kuyi magana ta wannan lambar domin siyan littafin
Nagode
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 48_49
Littafin kuɗi ne pay before you read please 🙏 🙏 🙏
Haɗe rai tayi tace "dan za muyi magana shine zaka dinga yimin wannan abun haka, ni bana so gaskiya karka sake yimin"
Maimakon yayi magana Shiru yayi ya sake ƙanƙameta sosai a jikinsa, ya kwantar da kansa a jikinta, ita kuwa mutsu mustu kawai take, so take taga ta ƙwace daga jikinsa, amma abu ya gagara, ya riƙeta sosai ga ƙarfinsu ba ɗaya ba.
A hasale Widad tace "Wai dan Allah Yoseef meye hakane?, ka cikani towel ɗin jikina ze kwance fa? Nace maka bana so ka cikani dan Allah, wallahi gaba ɗaya ka canza hali, kwanan nan sekai tayi min wasu abubuwa wanda bana so, kuma kana sane"
A hankali ya cika ta, ya kwanta akan katifar yayi shiru tare da lumshe idonsa.
Se kuma ta juya tana kallonsa tace "meye kuma?" ba tare da ya buɗe idonsa ba ya girgiza mata kai.
"to me zaka gayamin?"
"bakomai" ya bata amsa
"wani irin bakomai bayan kace magana zamuyi?"
Gabansa ne ya faɗi, yaga be kyautu yayi mata wannan zancen a wannan gaɓar ba data ɗau zafi, dan haka ya buɗe idonsa ya ɗan tsare ta da ido yace dama ba wata magana bace, ina son in sake gayamiki Ina sonki Widad "
Ha ɗe rai tayi tace " kaga tasarmin daga kan katifa ta, tunda ba zaka dena wannan shirmen ba, kuma daga yau in ka san wannan shiritar zaka gayamin, karka sake cewa zakayi magana dani na gaya maka, dan bazan saurareka ba"
Yusuf yace "Maganar tawace shiririta? Queen ba shirita bace i mean it, kalmar so ba abun wasa bane ko imagination ba, please my Queen ki yarda ina sonki mana"
Banza tayi masa, ta ɗakko kayanta tana ƙoƙarin sakawa, ya juya mata baya don ta sa kayanta.
tayi ƙasa da muryarta cikin ƙunƙuni tace 'kaji da shi dai, kai ta mun wasu abubuwa amma idan zansa kaya seka wani juya, wai kai gaka na Allah, inma baka juya ba niba abunda ya dameni sa ka yana zanyi'
Bece mata komai ba se dai murmushi da yayi, se data gama sa kayan, ta yunƙura zata miƙe ya sake riƙeta, a fusace tayi niyyar yi masa rashin mutunci, amma ya rungumota ta kasa cewa komai jin ya haɗe bakin su.
Gaba ɗaya Yusuf yafi ƙarfinta, ta kasa gane kansa kwata kwata, kwanan nan se wasu ɗabi'u yake mata wanda bata gane kansu, tana ji tana gani seda yayi me isarsa sannan ya cika ta, ba zata iya ƙwace kanta ba.
Yana cikata bata kuma kallonsa ba, ba tace komai ba rai a matuƙar ɓace tayi waje, kallo ɗaya zaka yiwa fuskar ta kasan a fusace take, ta fita tsakar gida rana ta take, kowa yana ɗaki ta fita ta samu guri a ƙasan bishiya tayi zamanta.
Hakanan Yusuf ya dinga jin be kyauta ba abunda yayi, amma ya zeyi shima bayin kansa bane, mutum ne shima kuma me cikakkiyar lafiya, shi kansa yanzu ya fara ɗar ɗar na zama da Widad a guri ɗaya, komai ze iya faruwa.
Barrister Khalil kam tunda yakoma gida yake tunanin hirar da sukayi da Nurat game da mahaifinta, tabbas mahaifin Nurat ba karamin hatsabibi bane ,ze iya aikata komai muddin burinsa ze cika ,amma yayi mamakin yadda Nurat tace masa da saka hannunsa a sace Daula da akayi,abun da mamaki matuka, nan ya shiga nazarin ta ina yakamata yayi wani abu? Amm muddin ya kuskura Alhaji Musa yasan yana wani yunkuri,ko kuma ya gane ya san wani abu akan abunda yake aiktawa,to tabbas ba abunda ze hanashi daukar mataki akansa,dan bashi da Imani sam.
Barrister Hafiz ma tunda ya koma gida yake tunanin batun da aka bijiro masa da shi akan dukiyar Daula,tabbas kudi abun sone,amma meze biyo baya idan suka amince akayi wann aika aika? Idan sukayi aikin nan tabbas zasu samu kudi,amma hatsarin dake cikin hakan shine abun dubawa, watakila idan shi nya amince ba lallai sauran lawyoyin su yadd ba,amm tabbas yana son kudi shima.
Ya yanke shawarar zefara tuntubarsu daya bayan daya yaji opinion din sauran akan lamarin abunda suka yanke shikenan.
Ya tashi ya dau mukullin motarsa ya fice.
Anwar kuwa gaba daya yayi baki,ya rame saboda zaman gurin nan babu sauki sam, ga sauro ga rahsin kula, ga azabar wahala da ake gana musu akan lallai se sun fadi inda Daula yake, amsar sa dai dayace be san inda yake ba.
Yana zaune a inda suke ajiye yayi shiru yana tunani,s hi babban abunda yake damunsa shine waye ya sace Daula? Wanda ya sace shin yana iya kula dashi?maganinsa ma ko ana kula dashi a bashi oho? Yayi zurfi a duniyar tunani yaji an kira sunansa, a hankali ya daga kai, dan sandan yace
“ka taso kana da bako”
Anwar ya taso ya taho a hankali yana jan kafa,yabiyo bayan dan sandan.
wanda aka nuna masan akace shine me nemansa sam be sanshi ba, dan ko ganinsa be taɓayi ba.
Mutumin ya kalli Anwar yace “kaine Anwar?”
Anwarv yace “Eh nine”
Mutumin ya kalli Anwar yace “ naji ance ranar sha biyar ga wata za a kaiku kotu ko?”
Anwar ya jinjina kai yacec “ eh hakane”
Dukda ban gabatar maka da kaina ba baka san koni waye ba,nima turoni akayi gurinka,kuma ancemin babu bukatar seka san waye ya turoni, yanzua abunda nake so nbda kai shine ina son ka gayamin tsakani da Allah meka sani game da batan Alhaji Nasir”
Anwar ya gaya masa iya abunda ya sani,Mutumin yace "shikenan karka damu ka kwantar da hankalinka,insha Allah komai zezo da sauki”
Anwar yace “shikenan nagode sosai”
Mutumin yace “sannan kuma, bana bukatar kowa yasan nazo gurinka ciki harda mahaifiyarka’
Anwar yace “shikenan,Insha Allah babu meji”
Daga nana sukayi sallama mutumin yatafi.
Widad na zaune a gindin bishiya, tana tunanin abunda ya shiga tsakaninta da Yusuf, tai shiru sosai tana tunani, tama rasa me yakamata tayi, haushi zataji kome?, Ganin Widad zaune ita kaɗai a gindin bishiya yasa Hindu tazo ta Zauna a gurin Widad, tace "Amarya me kike anan ke ka ɗai haka?"
"ina shan iska ne kawai" Widad ta bata amsa
Hindu tace "tunda ba abunda kike, ɗan koyamin turancin mana"
Murmushi Widad tayi tace "to ta ina zamu fara, bansan a inda kika tsaya a turancin ba"
Hindu tace "ni dai kota ina ne mu fara"
Nan Widad ta shiga koya Mata daga ƙananan abubuwa wanda zata iya riƙewa.
Yusuf ya fito ze tafi Sallar la'asar, ya ya kalli su Widad yace "karatu ake ne?"
Widad bata amsa ba, Hindu ce tace "eh wallahi turanci ake koyamin"
Yusuf yace "Masha Allah, Allah ya temaka"
"Ameen" Hindu ta amsa banda Widad data haɗe rai.
Daya dawo ma a gurin bishiyar ya tarar da ita, tana cin Abinci.
Yusuf ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita yace "Shine kike cin Abincin babu ko gayyata? Bari inzo muci tare, kin san cin Abinci tsakanin ma'aurata yana ƙara danƙon soyayya, nikuma ina son Soyayyarmu ta wuce ɗanƙo ta zama kamar ƙarfe"
Banza tayi masa taƙi kula shi.
Ya wanke hannu yazo yasa hannu suna cin Abincin, amma Widad taƙi ce masa komai.
Se yanzu Yusuf ya fuskanci fushi take dashi.
Yusuf yayi ƙasa da muryarsa yace "My Queen me nayi miki ne? Se magana nake am kin basar dani, bana jin daɗin hakan fa"
Ƙara haɗe rai tayi, ba tare da tace masa komai ba.
Yusuf yace "Abunda nayi miki a ɗaki ne yasa kike fushi dani ni ko?"
Cire hannunta tayi daga Abincin, taje ta wanko hannunta ta dawo tai zamanta, shiru yayi yana sake binta da kallo.
Hanne ce ta fito, tana ganin Yusuf ta wangale baki tace "Sannu"
Jiki a sanyaye Yusuf yace "Yawwa Sannunki Hannatu"
Ba ƙaramin daɗi Hanne taji ba jin Yusuf ya kira sunata da Hannatu.
Ta ƙara wani rausayar da kai tana murmushi, ta ƙaraso inda yake zaune kusa da Widad a kan tabarma, tace "bari in ɗauke kwanon, naga kamar ka gama cin Abincin"
Bece mata komai ba, taje ta ɗauke kwanon ta kai gurin wanke wanke, ta kawo masa ruwa a buta tace "ga wannan ka wanke hannu"
Yusuf yace "God bless you, Nagode sosai"
Ta jinjina masa kai tana murmushi, Widad ko kallon inda suke ba tayi ba, ta cigaba da kaɗa ƙafarta.
Tana jin yadda Hanne keta wata kwarkwasa, Hindu dake banɗaki ji take kamar ta fito ta shaƙe Hanne, ta wani ɓangaren kuma tana ganin baiken Widad, data zuba mata ido ta ƙyaleta.
Yusuf ya tashi ya tafi ɗakin su, Hindu na fitowa daga banɗaki a fusace tace "Hanne gaskiya abunda kike bakya kyautawa, ya zaki dinga shigewa mijin mace a gabanta, dan kawai kinga tana ɗaga miki ƙafa, haba Hanne dan Allah ki dimga tunani mana"
Hanne tace "ba zanyi tunanin ba ɗin, ina ruwanki dani? Tunda ita ba zata iya kula dashi ba ai shikenan, mace ba abunda ta iya se girman kai, sam bata da tarbiyya, bata san darajar miji ba"
Widad ta miƙe zata koma ɗaki, sedai babu zato Hanne taji Widad ta shaƙeta da rigar jikin ta, seda idanunta suka yo waje dan azaba, cikin zare ido da ɗaga murya Widad tace
"Am tired, ban taɓa ɗagawa wani mahaluki ƙafar dana ɗaga miki ba, ina ƙyaleki ne saboda Karamcin iyayenki a gare ni, kin san wacece ni? Babu ruwana da alaƙar dake tsakaninki da Yoseef, amma karki sake sakani a irin wannan haukan naki, banda ƙaddara ko a mafarki aka ce ni Widad zan zauna a wannan ƙasƙantaccen gurin zance ƙaryane, saboda kawai ina zaune a cikin wannan jar ƙasar shine zaki dinga gayamin baƙaƙen maganganu? Kin san wace ni, idan kin san wace Widad ko hanya muka haɗa sekin kauce, banda dalilin ƙaddara babu abunda ze haɗanj da daƙiƙiyar baƙauyiya kamarki, hanyar dana sa ƙafata na wuce ma baki isa ki biyo ta ba"
Hanne se kakari takeyi, Su Hari sukazo da gudu amma suka kasa ƙwatar Hanne a hannun Widad, fitowar Yusuf ne yayi daidai da shigowar Saleh, da sauri Yusuf ya ƙarasa inda dramar ke faruwa, idanun Widad sunyi jawur, fuskarta sharkaf hawaye tana masifa.
Yusuf ya ƙarasa yasa hannu ya cire hannun Widad daga wuyan Hanne, Hanne ta shiƙi iskar 'yanci, ta koma gefe tana ta haki tana zare ido, kamar an karɓeta daga hannun zaki.
Saleh yace "Wallahi da ta kasheki ta kashe banza, dan babu wanda ya isa ya ɗaukarr miki mataki, kin san wacece kuwa? Kin san' yar waye ita? Ko dan kawai kin ganta a cikin gidan nan a zaune, ina lura da yadda kike mata wasu abubuwan tana ƙyaleki, tunda kika ga nima tana mun abunda taga dama ina ƙyaleta to tabbas kin san ba a banza ba, ƙaddara ce ta kawota zama daku, amma ke a gidan su ko me goge mata takalmi baza'a ɗauke ki ba"
Gwaggo tana jin duk dramar da'ake yi, amma tai shiru a ɗaki bata ko fito tsakar gidan ba, saboda tasan abunda ke faruwa, tasan yadda Hanne ne ke wuce gona da iri a wasu lokutan.
Shikan sa Yusuf yasan ba ƙaramin ɗaga ƙafa Widad kewa Hanne ba, a yadda Widad keda izza bata ɗauka raini, amma take sharewa idan ta mata wani abun, lallai haƙurinta ne ya ƙare.
Suka shiga ɗaki, Widad se kuka take jikinta na tsuma, ga gumi data haɗa.
Yusuf ya shiga share mata hawayen fuskarta tare da faɗin "is ok, kiyi haƙuri nasan kina haƙuri, Amma ki ƙara insha Allah mun kusa mu koma gida"
Kamar wadda aka mintsina, ta miƙe daga jikinsa a fusace tace "dalla ma ni ƙyaleni, ba kaine kake mata dariya ba, yasa ta rainani takemin wani kallo na daban ba, harni wannan baƙauyiyar yarinyar zata kalla ta dinga zagina? Tunda kana mata dariya dole ta Kalleni ta dinga cewa ban iya kula da miji ba se ita, ai seka Aure ta tazo ta kula da kai, wallahi ta kuma yimin abunda bemin ba, sena ɗau mataki mafi muni a kanta, zan nuna mata wacece Widad "
From no where Yusuf yaji wani farinciki yana ratsa shi, Widad ta fara kishinsa kenan? Murmushi yayi yace
" Ohh yasalam, shikenan tabbas nayi laifi, dukda badan ina mata murmushi ba, da tabbas ba zata rainamin 'ya ƙwalisar mata ta ba, amma ayi haƙuri zan kiyaye insha Allah, na dena mata dariya amma ayi min afuwa".
"Karma ka dena kai tayi mata, wallahi na dena ƙyaleta"
"Ayi haƙuri dai, kar ayi aika aika, ki dena kuka share hawayen ki maza, mijinki baze sake kallonta yayi mata dariya ba"
Shiru tayi masa ta cigaba da ajiyar zuciya. Yusuf a ransa yace 'insha Allah ko baki son meye so ba zaki sanshi a kaina, kuma ina fatan ki furta da bakinki kina son Yusuf, muje zuwa dai'
Shikam Saleh a tsakar gida ya cigaba da zazzaga musu masifa, akan abubuwan da Hanne ke yiwa Widad, sun sha mamaki jin yace ko za'a tattara kaf ƙauyen da kadarorin da mutanen ƙauyen suka mallaka ba zasu sai gidan mahaifin Widad ɗaya wanda take rayuwa a ciki ba.
Hari ta zaro ido tace "Wudas ɗin?"
"ke dalla ware ai kece Wudas ɗin, meye wani Wudas"
Hindu ta yadda da maganar Saleh, saboda sam Widad ba tayi kalar wahala ba.
Ita kuwa Hanne jinsa kawai take badan ta yadda ba, shaƙar da Widad tayi mata tafi komai bata mamaki da ɗaga mata hankali.
Ramlah ce ta shiga falo, ta tarar da Amal a kwance tana kallo, amma hankalin ta sam baya kan tv tunani kawai takeyi, a ɗan gigice tace "Amal wai kinji Anwar kotu za'a kaisu next week"
Da sauri Amal ta tashi zaune tace "kamar yaya kotu?"
"Yanzu Mummy ta dawo take gayamin"
"Dama ana kai mutum kotu, koda ba'a tabattar da laifin da ake tuhumarsa ba?"
Ramah tace "ya za'ayi in sani? Nifa hankalina ya tashi, ashe abun nayi ne"
Amal tace "mun shiga uku Ramla, da ƙyar in aka shiga kotu kiga ba'a kai shi prison ba, yanzu meye abunyi?"
"wallahi nima ban sani ba, gaba ɗaya kaina ya gama kullewa, Ga Mummy ta damu sosai, ko Abinci ma ba ta ci fa"
"Subhanallah, Allah sarki Yaya Anwar, yanzu fa da sunje koti se ace se prison"
Ramlah tace "wallahi nima abunda nake tunani kenan Amal, Allah sarki bawan Allah"
Nan suka yi ta jimantawa juna.
Har dare Widad taƙi walwala, ko kula Yusuf ta ƙiyi, yau ko harar da suke a tsakar gida dasu Hansai bata zauna ba, ta gyara shimfiɗar ta zata kwanta, Yusuf yaje kusa da ita yace
"My Queen dan Allah kidena fushi dani, nasan yau gaba ɗaya ranki a ɓace yake, na farko na sake gangancin sumbatarki, ga kuma wancan laifin shima da kika ce nayi, dan Allah kiyi haƙuri bazan iya jure ganinki cikin ɓacin rai ba"
Cunkusa baki tayi, ta cigaba da ƙoƙarin kwanciya.
"Amma inaga dole mu koma kan shawarata ta farko, na yakamata mu raba ɗaki, kinga ni ba waliyyi bane mutum ne kamar kowa, idan muna tare a guri ɗaya akwai matsala, ina gudun wani abu yazo ya faru, kinga na fara gazawa gurin riƙe Alƙawarin yarjejeniyar dake tsakaninmu"
"wallahi bazan kwana a ɗakin nan nikaɗai ba, duk inda zaka je sena bika"
"to idan na kuma kissing ɗinki kika haɗemin rai se nayi abunda yafi haka, kina bani ciwon kai Widad, komai nayi laifi ne a gurinki, ki dinga sassauta min mana, a dinga jin tausayina"
Kwanciya tayi ta juya masa baya, shima kuwa ya kwanta a bayanta, banza tayi masa taƙi magana, ta lumshe ido da nufin tayi bacci, a kunnenta ya dinga raɗa mata
"I love you My Queen, ina sonki Widad, and I mean it from the bottom of my heart, i love you"
Cike da ƙosawa Widad tace "Naji amma dan Allah ka ƙyaleni inyi bacci"
"to ba kice komai ba, kin haƙura kin dena fushin?"
"eh na haƙura jeka"
"kora ta fa kike Queen"
"Niba korarka nayi ba, bacci nake ji"
Yusuf yace "shikenan, Asuba tagari masoyiyya"
"kaika santa"
Yai murmushi ya koma kan shimfiɗarsa.
Ana ta shirye shirye za'a kai su Anwar kotu domin fara sauraren ƙararsu, akan tuhumarsu da'ake da haɗa baki gurin sace Daula, Anwar ya duƙufa sosai da Addu'oi babu dare babu rana.
Yana zaune da safe wani ɗan sanda yazo ya buɗeshi, aka tasa ƙeyarsa zuwa wani guri, wannan mutumin dai daya zo ya kuma gani, aka bawa Anwar kayansa da aka karɓa.
Mutumin ya miƙawa Anwar hannu suka gaisa yace "masha Allah, you are free now malam Anwar, muje in ajiyeka a gida"
Cikin mamaki Anwar ya kalle shi yace "i am free as how? An game bani da laifi kenan?"
"eh baka da laifi, muje"
Kamar soko haka Anwar yabi mutumin, kuma ya kasa tambayar sa waye shi, ya kai shi restaurant yaci Abinci sannan ya wuce ya kai shi har ƙofar gida.
Mutumin ya kalli Anwar yace "Anwar ina maka fatan Alkhairi, ina maka murnar fitowa da kayi da kuma tsallake tarkon azzalumai, seka kula Allah ya kiyaye gaba"
Anwar yace "sedai ni tunda kake zuwa gurina ban gane ka ba"
Mutumin yace "nasan baka sanni ba, kuma bazaka ganeni ba, sedai nima aikoni akayi ba'a bani umarnin sanar da kai wayeni ba, babu buƙatar hakan Daula yana tare da ubangida na, shiyasa aka ɗauke shi a Asibiti, yana gurinsa dan haka ka kwantar da hankalinka"
A firgice Anwar yace "dan Allah waye uban gidan naka? Daula bashi da lafiya, yana buƙatar kulawar likita"
"ɗan samari kai dai ba Ruwanka, koma a wani hali yake ciki tunda dai kai ka fita, maza jeka zan tafi"
Jiki a sanyaye Anwar ya sauka, yana bin motar da kallo kamar wani soko, har motar ta bara layin.
Gate ɗin gjdansu ya nufa, ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin, Isa ne yazo ua buɗe ƙaramar ƙofar, yana ganin Anwar ya shiga mutstsuka ido ko gizo yake masa, Isa yace
"Kamar Yallaɓai Anwar nake gani"
Anwar yace "eh nine Malam Isa"
Buɗe masa ƙofar yayi ya shigo, Isa yace "Yallaɓai an sakoka kenan?"
Anwar yace "Alhamdilillah Isa an sakoni" nan ma'aikatan suka dinga murna suna taya shi farinciki.
Cikin gidan ya ƙarasa, yana shiga ya tarar babu kowa a falo, ɗakin mahaifiyarsa ya nufa, yasa hannu ya murɗa ƙofar ɗakin yayi Sallama, da sauri ta waigo dan mamar Muryar Anwar taji, aikuwa ba kama bane shi ɗinne, ai da hanzari ta miƙe, ta nufe shi da sauri
"Anwar kaine? Garin yaya, ya akayi aka sake ka?"
Rungume ta yayi yace "Mummy ki bari in huta se in gaya miki, duk kin rame Mummy na"
Kuka ta saka tace "ba dole ba Anwar, baka nan na rasa me kemin daɗi, nasan zaman gurin nan sam ba daɗi yake maka ba, nayi zarya harna gaji anƙi a sakeka, ko Abinci bana iya ci, bana baccin kirki"
"shikenan, is over now, ai gani na dawo Alhamdilillah"
Suna nan zaune sega su Amal, dan ta manta ma bata sanar dasu dawowar Anwar ba, nan suka dinga murna suna farinciki da dawowar Anwar, aka shiga yi masa girki, yai wanka ya huta dan ko ina na jikinsa tsami yake masa saboda wahala.
Mummy tace "nikam ka gayamin, ya aka yi aka sako kame?"
Anwar yace "wallahi Mummy ikon Allah kawai, ina zaune akace in fito, wani mutum ya ɗakkoni a motarsa yace bani da laifin komai, ya kawoni har gida ya tafi"
Ɗan yatsine fuska tayi tace "meye haka sekace wata almara?"
"Wallahi Mummy dagaske nake miki, kiyi waya ki tambaya kiji"
"ikon Allah ko wane mutumi ne wannan oho? Ta be gaya maka waye shi ba?"
"nayi nayi ya gayamin, amma yaƙi sam, be gayamin ko waye shi ba"
Amal tace "Mummy koma dai waye, tunda Allah yasa an sako mana shi ai shikenan, mu dama fatanmu ka dawo gida"
Mummy tace "Amma da mamaki, ina mamakin waye haka? Dan na san ba'a cikin waɗan cam tsinannun bane marasa imani"
Anwar yace "Mummy suwaye kenan kkke zagi haka?"
Da sauri ta wayence tace "A'a karka damu, 'yan sanda nake nufi, ba irin zaryar da banyi ba amma suka ƙi bani belinka"
"Allah sarki, ai Abincin su suke karewa suma Mummy, bekamata ki tsine musu ba"
Mummy tace "hakane kam, na dena tsinemusu tunda nidai ɗana ya fito"
Yau Widad har takwas na safe bata tashi ba, tunda tayi sallar Asuba, Yusuf yaje kan shimfiɗarta ya riƙe hannunta a nasa yana ɗan matsawa yace "My heart, ki tashi baccin ya isa haka, ki tashi kici Abinci"
Motsawa tayi a hankali tayi juyi tace "kaci Abincinka, ni bacci nake ji"
"A'a ni gaskiya bazan iya cin Abincin babu ke ba, ki tashi please"
Shiru tayi ta sake lumshe ido, "zanyi miki abunda bakya so yanzun nan fa"
Murmushi tayi tace "banyi brush ba dai" ta ƙarasa tana dariya, Yusuf yace "aini bana ƙyamar ki, kece kike ƙyamata komai naki ni so nake"
Widad tace "naji, ɗakkomin brush ɗin inje in wanke baki"
Ya duba inda take ajiyewa, ya ɗakko ya bata, tana zaune akan katifar bata tashi ba, Yusuf yace "ya dai? Ko sena ɗauke kine?"
Jinjina masa kai tayi alamar eh, aikuwa ya ƙaraso ya ɗauketa cak, dariya take tace "ajiyeni tun kan Baba Hari tamin ba'a ko ace na aikata wani babbam zunubi a koreni daga garin nan"
A tare suka kwashe da dariya, Yusuf yana kallonta cike da farinciki.
Tayi waje, taje tai brush ta dawo suka fara cin ɗumamen tuwo.
Yusuf kallonta yake, da alama tana cikin nishaɗi, yanzu ne lokacin da ya dace ya gaya mata abunda yake son gaya mata, yai shiru yana saƙe saƙen yadda ze ɓullo da zancen yaji tace
"Me kake son gayamin ne da yake razanaka har yanzu ka kasa gayamin? Ka gayamin kawai ina saurarenka"
Littafin kuɗi, dan Allah a biya kafin a karanta badanniba dan girman Allah
A tuntuɓeni ta wannan lambar
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 50_51
NA KUƊI NE, BOOK 1 NE FREE, DAN ALLAH A BIYA KAFIN A KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH 🙏🙏🙏
gaba ɗaya Yusuf ya ɗan ruɗe yace "ba wani abu da nake son gayamiki ba fa, kece kike ganin kamar ina son in faɗi wani abu ne"
Murmushi tayi tace "Hmm Yoseef kenan, a ɗan zaman da nayi da kai daga lokacin da ka fara min aiki, na fuskanci halayenka da yawa, koba haka ba ina iya karantar abunda ke ran mutum ta hanyar fuskarsa, bana son ƙarya, karka ji wani abu, babu abunda zan maka, se abunda Allah yayi nufin ya faru da kai"
Yusuf yace "dama ina son in gaya miki yau nake son na cigaba da fitane, ina son in sai mana wasu abubuwan na buƙatunmu, wasu abubuwan duk sun ƙare"
Widad tace "Yaushe ka warke da har zaka fara zancen fita? Se kaje ka kuma haɗuwa da wata rashin lafiyar ko? toni babu ruwana, tunda dai ban takura maka nace seka saimin abunda baka dashi ba, ka ƙyaleni komai aka bani zanci, in wanda zan iya cine se inci, in bazan iya ciba kuma se in haƙura kawai"
Sosai ta bawa Yusuf tausayi jin abunda ta faɗa, Yusuf yace " duk da haka Yakamata ace nima ina taɓuka wani abun da kaina, in sauke haƙƙinki da yake kaina, in sai miki abubuwan da kike buƙata koba duka ba"
"Shikenan, amma nidai bance kayi abunda zaka cutu ba koka wahala ba, ka kula da lafiyarka"
Yusuf ya gama shirinsa tsaf ze fita, Saleh ya shigo gidan ya kalli Yusuf yace "Ahh Yusuf ina zuwa haka? '
" zani cin kasuwane Saleh " Yusuf ya bashi amsa
Saleh yace " Haba Yusuf, kasan fa baka da lafiya sosai "
Yusuf yace " shima zaman guri ɗayan babu daɗi Saleh "
Harice take a tsugune tana ta tattara ƙwan da kazarta tayi zata bayar akai kasuwa, Yusuf yace " Baba Hari, wannan ƙwan na siyarwa ne?"
Hari tace " Eh za'a akaimin kasuwane"
Yusuf yace "Masha Allah, inba damuwa a zuba na kaji biyar na zabi biyar, a kaiwa Queen idan na dawo insha Allah zan bada kuɗin"
Hari tace "meye kuma Kun?"
Yusuf yayi murmushi yace "A kaiwa Widad nake nufi"
"Awo sekace min Wudas, amma kun ai bazan gane ba idan kace haka"
Saleh yace "Hari baki abun magana, Queen yace ba kun ba, yana nufin sarauniya"
Kwaɓe baki tayi tace "Wace sarauniyar? Sarauniyar fitsararru ba"
Yusuf yace "Ayi haƙuri"
Hari tace "dan dai kaine, kuma ina jin kunyar ka, amma da ita zata siya bazan sayar mata da ƙwan nan ba"
Yusuf yayi dariya yace "ayi haƙuri, A temaka mana"
Saleh yace "kedai kinji kunya, ki rasa da wadda zaki dinga faɗa se wannan Yarinyar"
Widad ta ƙaraso inda suke da kwanukan wanke wankenta a hannu tace
"Idanma baki siyar dan Allah ba, zan buɗe gurin ƙwan ne in kwashi san raina, ko in kama kajin naki in yanka in soye muci nida Yusuf tunda bashi da lafiya dama"
Dariya suka yi, Saleh ya dinga mamaki, dama Widad ta iya magana haka hadda tsokana?
Hari tace tunda Yusuf ne ze sai ƙwan, ya biya kuɗin biyar, ta bashi biyar kyauta, amma bata yarda ya bawa Widad wanda ta bashi ba.
Widad tace "Hari dama kina ɗan dafa ƙwan nan kici, dase kinfi haka ƙiba da kyau, ke kullum cikin neman kuɗi kamar zakiyi ƙwace, kuma na rasa inda kike kai kuɗin"
Hararta Hari tayi taƙi ta kulata, aka ɗakko kwano za'a sakwa Widad ƙwai, Widad tace
"kuma idan kika samun ƙanana bana so, manya za'a bani dan nima ƙatuwa ce"
Haka Widad tasaka Hari a gaba, tana ta zolayarta ita kuwa Hari tunda Widad ta shaƙe Hanne take ɗan shakkarta.
Yusuf yace "Queen zan tafi"
Widad tace "ba zaka soyamin ƙwan ba zaka tafi?" tai maganar kamar wata ƙaramar yarinya tana sa hannu a gashin kanta.
Gwaggo ta sunkuyar da kai tana jin taɓara, Yusuf yace "ki bari in dawo"
Maimakon tayi magana se ta cuna baki tana kallonsa,
Yusuf yace "Shikenan Muje in soyamiki, amma nasan ba iya ci zaki yi yanzu ba, dan yanzu kika gama cin Abinci"
Gwaggo tace "Yusufa jeka abunka, za'a soya a bata kaji"
Widad ta cunkusa baki tace "Ni gaskiya Mama nasa nake so, naga kin fi son Yoseef dani, ni kowa baya sona"
Gwaggo tace "nina isa ince bana sonki, waceni niko nake sonkj, amma ina nema masa Alfarma, a ɗaga masa ƙafa tunda fita zeyi"
Widad tace "shikenan Allah ya temake ka, jeka seka dawo" tai maganar tare da kashe masa ido ɗaya.
Hari tace "A'uzubullahi wannan Yarinyar idan ka zauna a inda take seta karya maka alwala"
Dariya Yusuf yayi sukayi waje shida Saleh, Saleh yace "Salute to you Yusuf, babu wanda ya isa ya biyaka namijin ƙoƙarin nan da kake, kalli yarinyar da take rayuwa kamar wata halitta daban, me gudun jama'a da son rayuwar kaɗaici, amma ita ta sake a ƙauye haka take rayuwarta, cikin farin ciki fjye da wanda take a gidansu da yake da tarin arziki "
" Saleh, ai dama kuɗi dukiya ba sune kwanciyar hankali ba, farinciki zama cikin wanda suka damu da kai shine farinciki, mutanen wannan zamanin muke ganin in kana da kuɗi kana da komai, ka wuce baƙin ciki "
Saleh yace" tabbas hakane maganarka Yusuf, da fa tsakaninta da mutane kallon banza da hantara, amma yanzu kalli yadda ta sake da Gwaggo ta maida ta kamar wata kakarta"
Yusuf yace "sosai makuwa, akwai shaƙuwa a tsakaninsu, Gwaggo nada sauƙin kai, kuma tana janta a jiki, bata hantararta idan tayi mata wauta ko wani abu, shiyasa itama take sonta"
Saleh yace "hakane, amma ya batun ciwon ta kuwa? Na taɓin hankali?"
Yusuf yace "ina doubting akan wannan ciwon da take dashi, ina da question mark akai, amma lokaci nake jira"
"Alhaji Musa, kaji wata maganar banza wai an saki Yaron nan Anwar"?
Alhaji Musa yace "haka nima labari ya isheni, ni kaina abun ya ɗauremjn kai Munir, wane mara mutuncin ne haka, waye yayi wannan karambanin?"
Alhajj Munir yace "munyi waya da Bukar, yace ze bincika nima nasa a bincikamin amma har yanzu babu wani labari, an rasa waye yasa a sake shi, wai daga sama aka bada umarni"
Alhaji Musa yace "waye a saman ya bada umarni damu bamu sani ba? Ta yaya ana tuhumarsa da wannan babban laifin za'a sake shi, idan kuwa hakane to tabbas muna da abokan Adawa wanda suke mana zagon ƙasa akan lamarin nan"
Alhaji Haruna da tun ɗazu bece uffan ba ya nisa yace "ni kaina gaba ɗaya ya kulle, na rasa abunyi semun toshe nan se can ya buɗe, na rasa wane banzan ne yayi wannan aikin"
Alhaji Musa yace "tabbas akwai lauje cikin naɗi, yanzu abunda ze faru shine, zamu saurari Bukar muji me zece, lallai a binciki wanda yayi wannaan aika aikar, sannan a tabattar an kama yaron nan an maida shi"
"haka ma za'ayi, wannan shine abunda ya dace, akama shi harse an ga Daula"
Anwar yana zaune yana cin Abinci yace "Mumsy kin san wani abu kuwa?"
"A'a seka faɗa" ta bashi amsa
"wato bawa baya taɓa gane Allah subhanahu wata'ala yayi masa ni'ima, se yayinda wannan ni'imar ta gushe, kinga ko 'yancin kayi yawonka ɗin nan inda kaga dama, ba ƙaramar ni' ima bace, zama guri ɗaya bala'ine Mum, ga rashin gurin kwanciya me kyau, ba Abinci me kyau, wai danma nine fa wasu haka suke tagayyara a cikin gurin nan "
Hajiya Halima tace " Aini duk zance ya ƙare, tunda Allah ya fito min da kak, Se fatan Allah ya kiyaye gaba"
Anwar yace "Ameen Mummy, ni yanzu fatana ubangiji Allah ya bayyana Daddy, yasa yana hannu nagari, dan na tsorata da abubuwan da suke faruwa"
Mummy tace "kai kam wannan dashi ya haife ka da an shiga uku, kai har yanzu baka shiga hankalinka ba, ba kaga masifar daka shiga saboda temako ba, still kai tunaninsa ka keyi"
. "Mummy ba zan taɓa iya dena tunaninsa ba, saboda gudunmuwarsa a rayuwar mu"
Wayar Anwar ce ta shiga ringing, ya ajiye spoon ɗin da yake cin Abincin ya ɗaga wayar yasa a kunnensa.
Lambar Bulama ce, bayan sun gaisa Bulama yace "Anwar ashe ka fito?"
Cike da ladabi Anwar yace "eh Daddy na fito"
"to Alhamdilillah, Allah ya kiyaye gaba inba damuwa ina son ganinka anan gida, zamuyi magana"
"to shikenan, Insha Allah idan nayi sallar la'asar zanzo"
Bulama yace "to babu laifi"
Anwar Ya ajiye wayar, Hajiya Halima tace "waye haka?"
"babansu Fahad ne, yace inaje yana son ganina"
"ba zaka ba" ta faɗa kanta tsaye.
"Mummy meyasa?"
"saboda haka naga dama, akanme zece kaje bayan ba irin sintirim da ba ba akan yasa baki a sake ka yaƙi"
Anwar yace "haba Mummy, kidinga yiwa mutane uzuri mana, a baya kinsha neman Alfarma yayi miki, dan wannan karon be miki ba be kamata ki manta baya ba, kiyi haƙuri i je i ji meze ce"
"shikenan tunda kace haka, amma ba dan haka ba Wallahi da bazaka ba"
"kiyi haƙuri, kar hakan yayi sanadiyyar lalacewar zumjncinku"
Da yamma Hindu tayi kwalliya itada su Hanne da ƙannensu zeuje biki, Widad na ganin Hindu tace "Masha Allah, you look so beautiful Hindatu, kina da kyau masha Allah"
Hindu tace "Rufani ki saya Amarya, ai daga kanku kyau ya ƙare, kina ganina baƙa kirin ina wani kyau yake?"
Widad tace "waye yace miki baki da kyau? Ke nima fa ba wata kyakkyawa bace, dan dai ina da haske ne, amma baki ganki ba, kinyi kyau Allah ya baki miji nagari ɗan birni"
"hmm Amarya kenan, ni da ban taɓa zuwa birni ba, banyi boko ba ta ina ɗan birni ze ganni ya aura"
Widad tace "da ina da Yaya namiji zance ya aure ki Hindu, kina da kirki kaman Mama, wai ina zakune?"
"biki ne zamuje, a gangare"
Widad tace "laaa shine babu gayyata, ku jirani zan biku, dama ban taɓa fita waje ba"
Hindu tace "to ai Amarya baki da kaya irin Atamfa, duk kayanki ba irin namu bane, idan muka je seki zama abin kallo, kuma dama gaki ba kalarmu ba"
"se in saka hijjabi"
Gwaggo tace "A'a amarya bekamata ki fita ba, baki tambayi mijinki ba, se da yaddar sa sannan zaki fita"
"Mama baze ce komai bafa"
"dukda haka, kuda kukayi ilimi ma Amarya, ai kunfi mu sanin hukuncin hakan"
Hak Widad tana ji tana gani aka tafi biki aka barta a gidan.
Bata ji daɗin hanatan da Gwaggo tayi ba, sedai bata son yi mata musune.
Daf da la'asar Yusuf ya dawo, ya taho da kayan da Saleh ya bayar a siyo musu, seda Gwaggo ta kalli Widad sannan ta tashi, ta taya shi kai kayan ɗaki.
Ya fito ya ɗauki buta yana alwala, yace "Mama yau naga gidan shiru, ina mutan gidan ne?"
Gwaggo tace "sun tafi biki, tace zata bisu nace karta je seta tambayeka, shine taƙi kulani"
Yusuf yayi dariya yace "babbar magana, faɗa tsakanin 'ya da uwa yau"
Widad tace "tunda nazo fa ban taɓa fita ba, kullum ina gida"
Yusuf yace "idan kin fita Meza kiyi? Sarkin rigima"
"kaikuma kaji ka, Yoseef ka kiyayeni nice sarkin rigimar?"
Gwaggo tace "ɗiyar albarka a dinga saya masa sunan mana, idan daga ke se shine seki faɗa, amma a gaban mutane mu nan abun kunyane mace ta dinga faɗan sunan mijinta kai tsaye"
Yusuf yace "yawwa gaya mata dai Gwaggo"
Cikin Shagwaɓa tace "to me zance masa?"
Gwaggo tace "ki dai samo wani sunan mi dinga gaya masa, kafin Allah ya baku rabo, in kin haihu seki dinga cewa baban wane ko wance"
Haɗa ido sukayi da Yusuf, ga mamakinsa se yaga ta kwashe da dariya tace "taɓ sedai inya Auri Hanne ta haifa masa, amma ni babu wannan Kalamin, ai Yayana ne kai ko Yoseef?"
Tai maganar cikin sigar zolaya, tayi gaba ta bar tsakar gidan, Gwaggo ta zata kishine yake damunta, saboda tasan yadda basa shiri da Hanne, shi kuwa Yusuf, a wata cakwalkwalin cakwakiyar tunani ta kuma sashi, duk jikinsa yayi sanyi.
Bayan yayi sallar la'asar ya koma gida, ya tarar da Widad tana gyaran Akwati, ya kalleta yace "Queen waye yace miki zan Auri Hanne? Idan kuma Gwaggo ba taji daɗin abunda kika faɗa bafa?"
"Ai naga ita Hanne kaman she's having the same feelings on you, she also believes in love"
"Se kuma akace miki ni Aurenta zanyi?"
"to waye yasan muku? Ranar da zamu koma gida, idan ka sake ni base ka Aure ta ba, ka tafi da sabuwar Amaryarka ba"
Tsaki Yusuf yayi, saboda yaji haushi sosai, ya miƙe ya bar ɗakin, bin bayansa Widad tayi da kallo, ta taɓe baki ta cigaba da aiki ta.
Tunda ya fita be dawo gida ba se bayan sallar isha'i, sannan yaƙi kulata kwata kwata, dukda taji ba daɗin dena kulatan da yayi da yawan tsokanar ta da yake, yaji ba daɗi amma ta maze ta basar dashi itama, haka kowa ya kwanta be kula kowa ba.
Da Asuba ma da yayi salla, suka zauna zaman karatu seda gari ya fara haske sannan ya taho gidan, tun bayan da aka idar da sallar Asuba kafin a fara karatu, Saleh ya janyo Yusuf waje yace "Nifa zan koma, sammako zanyi in tafi tunda kaji sauƙi" .
Yusuf yace "da wuri haka Saleh?"
Saleh yace "eh mana dole, in tafi bana son mutanen nan su farga su fara zargin wani abu"
Yusuf yace "hakane, mungode Saleh Allah yasaka maka da alheri"
"Ameen ya Allah, nace ka gaya mata kuwa?"
Yusuf ya ɗanyi shiru sannan ya girgiza kai yace "A'a amma zan gayamata insha Allah"
Saleh yace "gara ka gaya mata, tayi duk borin da zata yi ta gama a nan, sedai Kayi haƙuri, ina son insha Allah idan na koma zanje in gaida Ummanka, in gaya mata kana cikin ƙoshin lafiya"
Yusuf yayi murmushi yace "ka gaya mata ina lafiya, kuma ina kewarta, sannan ta kwantar da hankalinta"
Saleh yace "zan gaya mata insha Allah, sena sake dawowa"
Sukayi Sallama Saleh ya tafi.
Widad kam wanke wanke suke ita da Hindu, Hindu tace "Amarya ban taɓa tsammanin kin iya faɗa haka ba, ashe kina sane kike ƙyale Hanne se kace bakya kishin mijinki"
Widad tace "Meye kishi?"
Buɗe baki Hindu tayi tace "baki san meye kishi ba?"
Widad ta jinjina mata kai tace "ni ban san wani kishi ba, banajin komai ina dai ji ana faɗa amma ban san me ake jiba"
"Lallai Amarya abun mamakin ki da yawa yake, se kace wadda akayiwa Auren dole? Zakice ba kya kishinsa, Amma dai ai kina sonshi ko?"
Taɓe baki Widad tayi tace "Nifa ban san me ake ji ba a son nan, nifa kawai gani nake wannan son shirme ne, babu wani so mutanene kawai ke abunsu"
Dariya Hindu tayi tace "Yanzu dai bakya son Yusuf ɗin kenan?"
"To base na yadda akwai son sannan zan iya banbance idan ina sonshi ko bana sonshi ba?"
Hindu tace "ina mamakin kalar taki rayuwar Amarya, gaba ɗaya abubuwan ki wani lokacin sun saɓa da na sauran mutane, anya gidan ku akwai mutane kuwa?"
Widad tayi dariya tace "eh mana, akwai mutane, sedai nikaɗai nake rayuwata"
"Amma meyasa kika dinga kuka, kika kasa cin Abinci da mijinki bashi da lafiya?"
Ɗan shiru Widad tayi tace "Saboda idan Yoseef ya mutu, nima tamkar matacciya nake, ban san kowa anan ba se Allah se shi, sannan ya sha wahala sosai sabodani, yana shiga damuwa idan bani da lafiya ko ina cikin damuwa, shiyasa naji rashin lafiyarsa har cikin raina, kuma kinga ni bani da wa ko ƙani, Mamana ta rasu ina Yarinya Babana kawai nasani, Yanzu Yusuf shine yaya na, shine ƙanina shine ɗan uwana, shine komai nawa anan"
Hindu tace "Allah sarki Amarya, kin bani tausayi wallahi, amma Saleh yace mana ɗan uwanki ne Yusuf"
Widad tace "ɗan uwana ne mana, Allah ne ya bawa Babana shi, ya zama garkuwa a gareni, Hindu kina da kirki sosai naga garin nan kun ɗau Aure da mahimmanci sosai, Allah ba yadda be iya ba, na dage ba zanyi Aure a rayuwa ta ba, babu Aure a gabana saboda wani ƙuduri da nake dashi a raina, babu zato ƙaddara tasa na Auri Yusuf, ina yiwa mazanmu na Hausawa kallon wanda basu san darajar Aure ba, gaba ɗaya ina yiwa Aure kallon rayuwar muzgunawa, Amma ina miki fatan ki Auri Namji kamar Yoseef, idan akace akwai mutum me haƙuri kamarsa zance ƙaryane, Amma yana da haƙuri sosai, nasan yana haƙuri dani, ni gaba ɗaya tausayinsa nake ji Hindu saboda.....
Ta kasa ƙare maganar se Hawaye dake bin idonta, Yusuf yana tsaye a soro yana jin duk hirar da sukeyi, a hankali Yusuf yayi gyaran murya tare da yin sallama.
Da sauri Widad ta basar ta share hawayenta, Yusuf yace "Sannunku da aiki"
Hindu tace "Yawwa ina kwana"
"lafiya ƙalau Alhamdilillah"
Ya kalli Widad yace "My Queen, let's go inside"
Ta kalle shi tace "ka gama fushin?"
"ni dama nace ina fushi da ke ne?"
"ni dai ka bari in gama wanke wanke na"
Hindu tace "kije zan ƙarasa"
Yusuf yace "ƙyaleta, idan bata tashi ba, zan ɗauketa ne cak in kaita"
Hindu ta sunkuyar da kai, dan abun nasu Yusuf wani lokacin basa jin kunya.
Ɗaki suka shiga, ta kalle shi tace "gani meye?"
"Ƙwanki dama zan soya miki, tunda bakya so shikenan"
Murmushi tayi tace "Au ai na manta, soyamin inci"
Murmushi Yusuf yayi, ta zauna ta zuba masa ido, ya fasa ƙwan ya kaɗa yasa gishiri, dan su nan babu Seasoning.
"Wai dan Allah Mamanka ce duk ta koya maka wannan aikin?"
"Eh mana gashi kuwa kina gani"
"taɓ gaskiya kaji daɗi, ina Baban ka, baka maganarsa kullum se Ummanka kake faɗa"
Yusuf yace "Allah yayi masa rasuwa"
"Eyya Allah ya jiƙansa, yayi masa rahama"
"Ameen"
Ya miƙo mata ƙwan a plate, ya dafa mata tea ya haɗa mata, Widad tace "Allah sarki rayuwa, yau ni nake murna zan ci ƙwai, alhalin har kamfanine dani da'ake fitar da ƙwai har wajen Nigeria"
Yusuf yace "haka lamarin ubangiji yake, sedai dama da bredi se yafi daɗi"
"hakan ma nagode, zama da kai ka koyamin ci kuma da ni ba haka nake ba"
"Eh mana, so nake idan muka koma gida kar aga rama a tare da ke"
Dariya tayi tace "matso muci"
"A'a ci abinki, dama ke na saiwa, ni in aka ɗumama tuwo se inci"
"Aikuwa ba zance kaci dole ba, cikinka ni ci zan in ƙoshi, kaita jin ƙamshinsa"
Ta soma cin ƙwan nan, kawai yaga tayi murmushi tace
"ban taɓa cin ƙwai mara daɗin wannan ba"
Yusuf yace "to mutum ya soya wanda yafi wannan in an isa"
Tai murmushi tace "Gwaggo tana koyamin ai, zakayi mamakin yadda zan iya girki, inyi girki me daɗin da baka taɓa cin irinsa ba"
Ta cigaba da cin Abincinta, ƙura mata ido yayi yaga yadda take nishaɗi, tana cin Abincinta cikin nishaɗi, tunani yake ko ya gayamata yanzu? Tunda tana cikin nishaɗi, to idan kuma ya ɓata mata nishaɗin da take fa?.
Ba tare da ta kalli Yusuf ba tace "gayamin abunda kake son gayamin ka dena kallona kar in ƙware"
Jin maganar tata yayi a bazata, dan be zaci tana kallonsa ba, kuma yaji muryarta ta a asalin Widad ɗinta me cike da izza da jin kai.
Cikin kame kame Yusuf yace "Amm. Bakomai dama....
" bana son ƙarya, kuma bana son wasa da hankali Yoseef, ina jinka ka gayamin abunda kake son faɗa "
Gaban Yusuf ya faɗi, yace " dan Allah ina son ki fahimceni dama... "
"ni mutum ce kamarka, ban isa inyi maka abunda Allah be maka ba, sedai kome bakinka ze furta, karka kuskura kayi min ƙarya"
"to ai ƙaryar ma nayi miki Widad, shiyasa nake fargabar ta ina zan fara miki maganar ban san yanda zaki fahimci abun ba"
Wani irin sheɗanin kallo ta ɗago idonta tayi masa, me cike da tarin tuhuma, da gargaɗi gami da kashedi.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA, BA DANNI BA DA GIRMAN ALLAH.
A TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 52_53
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH
07063065680
Gaba ɗaya Yusuf ya shiga taradaddi, gumi ya tsasttsafo masa a goshi, saboda irin kallon da take masa, dan tun a nan yaga alamar rashin nasara.
Ɗauke idonta tayi daga kallonsa tace "ina jinka" tai maganar tana zuƙar tea ɗinta, Yusuf yace
"Da farko zan fara da baki haƙuri dan Allah... "
Katseshi tayi ta hanyar cewa "bana son wani ban haƙuri, ka tafi kai tsaye kawai ina jinka"
Cikin damuwa yace "dole in baki haƙuri, saboda a karon farko da ƙarya na fara miki, tun a zuwana akan ƙarya nazo miki, saboda nima ban san ya akai hakan ta faru ba, saboda" Se kuma yayi shiru.
Ba tare da ta kalle shi ba tace
"to tunda ka kasa gayamin ni bari in gaya maka abunda kake son faɗa ɗin ka kasa, na farko kai jam'in ɗan sanda ne na sirri ko ba haka ba?"
Ƙuuuu cikin Yusuf ya kaɗa, ya kalle ta a razane, ta ci gaba da cin Abincinta tace "cigaba na fara maka, ƙarasa ina jinka, saura me kuma?"
Kasa magana yayi, ya dinga binta da kallo cike da ban al'ajabi, kamar yaga wata halitta daban.
"yanzun ma zaka cigaba ne ko in cigaba da gaya maka"? Tai maganar tana kallonsa
"Amma ya akayi kika sani?"
Cikin isa da taƙama tace "An turo ka ne a matsayin jami'in sirri, da sunan wai ka bani kariya ko?"
Buɗe baki Yusuf yayi yana kallonta, amma ya kasa cewa komai dama tasan waye shi?
Ta kalle shi tace "shikenan ko akwai saura?"
Wani irin yawu Yusuf ya haɗiye da ƙyar, kai da ka ganshi kaga mara gaskiya, yadda yake ta gumi kuma ya kasa cewa komai.
"tunda ka kasa magana bari in ƙarasa maka, bayan bani kariya da kake, kuma kana yin bincike akan maƙiyan mahaifina, da wanda suke bibiya ta, ka maida hankali sosai akan aikinka, sannan kana taka tsan tsan dan kar in san ko kai waye"
Ta ɗanyi shiru tana nazarinsa sannan tace "Sannu Yoseef amma meyasa kasa hannu akan contract ɗina, bayan na gaya maka bana yafewa maƙaryaci?, saboda tsabar taurin kai, son aiki da rashin nuna gazawa ka saka hannu, dukda baka san wane irin hukunci zan ɗauka akanka ba idan na ganoka, idan ban manta ba a lokacin nace if you know you are here to spy don't sign the contract, but you feel like to sign it, saboda ba zaka iya komawa Office ba tare da kayi aikin da'aka turoka ba right? Yoseef meyasa kayimin ƙarya? "
Jiki a sanyaye Yusuf yace " ai kin bawa kanki wannan amsar Widad, bazan iya komawa ince ba zanyi aikin ba, saboda Alƙawari nayi kafin in fara aiki zan kare rayuka da dukiyoyin jama'a, kuma tunda na fara aikin, dagaske har cikin zuciyata naji ina son in baki kariya, musamman ranar da mukaje gurin birthday Nurat akayi yunƙurin saceki, tun anan na fara karaya, na ƙara tabattarwa lallai rayuwarki a hatsari take, dan haka nayi ɗamarar baki kariya iya iyawata, amma dan Allah ya akayi kika san wannan abubuwan haka?"
Ta ɗan jinjina kai tace " lallai biri yayi kama da mutum, ranar ba yadda banyi da kai ka gayamin meyafaru ba, amma kaƙi ka gayamin, nima nasan nayi ganganci a wannan ranar, na zuwa gidan Alhaji Musa, sedai ina ƙoƙarin cire kaina a cikin rigimarsa da mahaifina, shine dalilina na zuwa gidans, amma shima ka ɓoyemin baka gayamin meyafaru ba ranar, meyasa? "
Yusuf yace " saboda muddin na gaya miki zakiyi yunƙurin ɗaukar mataki ne, da kinyi yinƙurin yin haka nikuma Asiri naa ze iya tonuwa, kuma zaki ɓata komai ne, Amma dan Allah ya akayi kika sani? "
Cikin isa tace "Lallai ka raina Wacece Widad da kuma AƘIDARTA, in dai nice har yanzu bakaga komai ba, Tunda kazo gidanmu, jikina ya bani akwai something different with you, either good or bad, na kasa nutsuwa, na dinga ɓullo da abubuwa daban daban amma na kasa gane komai na cutarwa a tare da kai, ranar da 'yan sanda suka kama ka da bindiga, ni na fara ganin bindigar a jikinka kafin mu fita daga gida, kazo shiga mota ka ɗaga rigarka naga bindigar, nai shiru ban nuna na gani ba, dan ina son sanin da wacce kazo, sannan inga wani hukunci ne ya dace da kai, bayan mun fita a ranar aka kamaka da bindiga ka bawa 'yan sanda id card, sukayi ƙoƙarin saluting ɗinka amma ka hanasu, tun daga nan nabi diddigi da ƙwaƙƙwafinka na gane waye kai, har headquarter ɗinku naje aka bincikomin waye kai, sedai abu ɗaya ne ban gano ba har yanzu, waye yasa a baka aikin nan?!"
Yusuf yayi ajiyar zuciya, cikin damuwa yace " Nima ban sani ba, da bani za'a bawa aikin ba, amma abokin aikina yace a bani na fishi haƙuri, ban san waye ya bada aikinba nima"
Widad tace "Abokin aikinka Sani me zuwa gurin Isa megadi ko? Wato Abbas"
Gaba ɗaya Yusuf ya rasa meze ce saboda tsananin mamaki.
"Ni na saka aka ɗauke shi daga kano, aka kai shi kudancin Nigeria saboda ban yadda dashi ba, yayi ruwan Azzalumai da yawa"
Yusuf yace "Dama kece kika saka aka ɗauke shi? Ba mugu bane aminina ne, bani da aboki sama dashi"
"Yana ɗaya daga abunda yake cutar da mutane, shine saurin yadda, waye ya gaya maka duk memaka dariya sonka yake yi? Kayi kuskure ni bemin ba, shiyasa nasa aka rabashi da garin nan, sannan ina cike da son sanin waye ya bada wannan aikin"
Yusuf kam rasa bakin magana yayi, se kallonta kawai da yake yi.
Widad tace "shikenan" ta miƙe tsaye ta ɗau kwanukanta, yaji taja sumar kansa tace "matsoraci kawai, ashe haka kake da tsoro, i wish kaga idonka yadda suka sauya, kaine mutum na farko da na yafewa wanda yai min laifi mafi muni, saboda kaima hanyar da akabi aka baka aikin dan a cutar da kaine"
Yusuf yace "kamar yaya?"
"Bazan faɗa ba, ban yadda da kai ba" tai waje abunta tana dariya.
Mamaki ya cika Yusuf tatil, yanzu dama kallon biri yake mata take masa na Ayaba, tasan waye shi tsawon lokacin nan, be taɓa zaton zata gane ba yadda ya dinga taka tsan tsan, lallai Widad ba ƙaramin wayone da ita ba, amma kuma yana da tarin tambayoyi daze mata, amma taƙi bashi damar yin hakan.
Anwar ne ya shigo falon mahaifiyarsa yace "Mummy zanje kiran da Babansu Fahad yake min ne"
Ta kalle shi tace "Naji amma tare da Amal zaku tafi"
Anwar yace "Amma Mummy meyasa?"
"Saboda haka naga dama" ta bashi amsa, ta ɗau wayarta ta kira Amal tace tazo.
Befi mintuna biyar ba sega Amal ta shigo tace "Mummy gani"
"Jeki shirya maza kizo kuje gidan Bulsma keda yayanku"
Amal tace to, Hajiya Halima ta kalle shi tace "jeka mota ka jira ta"
Anwar ya fita kamar yadda aka bashi umarni, Amal ta shirya ta koma ɗakin mahaifiyarta, tace "Mummy gani na shirya"
"Yawwa ki buɗe kunnenki ki jini, wannan yayan naku wani lokacin sakaraine, ba hankali ya cika ba, ina son ki saka min ido akansa, duk abunda ya faru ko abunda Bulama yace idan kun dawo ki gayamin"
Amal tace "shikenan Mummy, Insha Allah zan gaya miki"
Ta juya ta fita, ta samu Anwar a mota suka tafi.
Suna zuwa gidan Bulama, Ramadan da Iman suka shiga murna Ramadan yace "Sannu Anwar, barka da Arziki Allah ya kiyaye gaba ya bayyana Daddy"
Anwar yace "Ameen Ramadan"
Iman tace "Sannu Yaya Anwar, Allah ya tsare"
Nan suka tsaya suna hira, Hajiya Sarah ta fito daga ɓangaren ta, itama tana ganin Anwar ta faɗaɗa murmushinta tace "Anwar, sannu Anwar ashe ka fito da yau naso inzo har gida in maka jaje, Amma naji alamun hawan jinina ya tashi, shiyasa na fasa fitar"
"Allah sarki, bakomai Mummy Allah ya baki lafiya"
"Ameen Anwar, Amal sarkin zumunci ya Maman naku? '
Amal tayi murmushi tace " Mummy kenan tana lafiya "
Bulama ne ya sakko daga kan benensa, bayan ya sakko Anwar cikin girmamawa ya rusina yace " barka da Yamma Daddy "
Bulama yace " Yawwa barka Anwar, ya kake ashe ka fito?"
"Eh Daddy Alhamdilillah, Allah yayi na fito"
Amal cike da basarwa tace "Ina wuni"
Bulama yace "lafiya ƙalau Autar mamanta, ya gidan naku?"
"Lafiya ƙalau" ta bashi amsa.
Yazo ya zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun falon.
Ya kalli Anwar yace "barka da Arziki Anwar, ba irin sintiri da shiga ficen da ba'ayi ba akan aga an samu ka kuɓuta amma Allah be nufa ba, amma ya akayi suka sakoka ne suka bar Sufyan?"
Anwar yace "to nima dai wani mutum ne yazo ya taho dani, bemin wani gamshashen bayani akai ba, ya cemin shima wanine ya turoshi"
"Allah sarki, haka lamarin ubangiji yake ai, kaga mu ba yadda bamuyi ba amma abu ya gagara, mahaifiyarka ta ɗaga hankalinta ta dinga ganin kamar bama wani ƙoƙari akai, se gashi Allah yayi an sako ka, to ubangiji Allah ya kiyaye gaba"
"Ameen ya Allah Daddy, Daddy nace to har yanzu babu wani labari akan ɓatan Daddy, har yanzu ba'a san inda yake ba?"
Bulama cikin damuwa yace "Anwar da akwai wani labari ai da kaji, babu wani labari har yanzu, binciken ake amma kamar ba'ayi"
"ubangiji Allah ya bayyana shi, ni fatana Allah yasa yana hannu nagari, tunda bashi da lafiya"
Hajiya Sarah tace "sha'anin ƙasarmu ai se Addu'a, banda haka ace an sace mutum kamar Alhaji Daula, abun da mamaki kuma har yanzu ko a jita jita babu wanda yaji inda yake, bawan Allah nan ba lafiya ba, yana fama da kansa ga tashin hankalin an sace masa 'ya, Amma a bishi har gadon Asibiti a sace, ga' yar tasa har yanzu babu wanda yasan inda take, abun akwai ban tausayi, Daula yana ganin Jarrabawa "
Bulama yace " tabbas, yana ganin jarrabawa, na rasa wani irin abune wannan ita kanta Widad wata na biyu zuwa uku kenan da ɓatan tal, amma babu labarin inda take, ni abun har tsoro yake bani"
Anwar yace "gaskiya ne, abun da tsoro kam, kamar Widad tasan meze faru ranar da zasu tafi farm house, tana kuka tacemin ga Amanar Daddy nan in kula dashi, nace mata zanyi iya ƙoƙarina, Amma ga abunda ya faru, i don't even know how to explain this incident to her when she's back "
Ramadan dake gefe yace " Allah sarki, karka damu ai duk wanda yaji abunda ya faru yasan ƙaddara ce, Amma ni wani lokacin har mamakin Widad nake, yarinyar nan 'yar baiwace akwai ta da kai"
Anwar yace "sosai makuwa, ina fatan Allah ya bayyana mana su gaba ɗaya"
Suka amsa da Ameen.
Haka suka cigaba da hira, sannan suka fito zasu tafi.
A harabar gidan suka haɗu da Fahad, Fahad yana ganinsa cike da borin kumya ya rungume Anwar yana faɗin "Ohh God, so you are free now, Alhamdilillah na ta yaka murna, Allah ya kiyaye gaba, nace zanje in duba ka akace ba'a bari a ganku"
Anwar yace "Haba kamar kai kaje inda nake ace bazaka ganni ba, da kazo da zamu iya haɗuwa ai"
Fahad yace "kasan bana son disgracing, and those people are good in that, but da naji ance court za'a kaiku ya akayi ka fito?"
Anwar yace "Al'amarin ubangiji ne kawai, shiya dubeni ya fitar dani"
Fahad yace "hakane, that's good ubangiji Allah ya ƙara karewa" ya kalli Amal yace "ke bakya kula mutane ne?"
Tsaki tayi tai masa wani irin kallon banza, ta buɗe mota ta shige.
Anwar ya girgiza kai yace "Fahad bari inje, akwai inda nake son zuwa daga nan".
"Ok, shikenan my regards to Mummy and lovely Ramla please"
Anwar yayi murmushin yaƙe yace "Fahad kenan, za suji insha Allah"
Daga nan shima ya juya ya shiga motar.
Suna cikin tafiya Anwar yace "wai Amal meyasa kuke yawan faɗa da Fahad ne? Banji daɗin abun kikayi masa ba, ya yanki ne fa"
Amal ta kwaɓe baki tace "nifa wallahi Yaya Anwar na tsani Fahad ɗin nan, nifa tun asali bemin ba, mugun maƙaryaci ne munafuki duk yadda kuke dashi ya kasa zuwa ya jajanta maka abunda ya same ka"
Anwar yace "to meye a ciki? Koma menene ba gashi Allah ya fito dani ba, idan kace zaka dinga biye wa mutane ranka ne kawai ze ta ɓaci"
Amal tace "taɓ ai kai zuciyar ka daban Yaya, ba kowa ze iya wannan abun naka ba"
Da suka je gida a waje yayi parking, ya kalli Amal yace "sauka ki shiga gida, ina son zani wani guri ne"
Ba musu ta sauka daga motar ta shige gida, shi kuma Anwar ya tafi.
Shiru shiru Yusuf be fito daga ɗaki ba, har Widad taje tayi wanke wanke ta dawo yana zaune a inda ta barshi, ta kalle shi tace "wai yau bazaka fitan bane?"
Jiki a sanyaye yace "zan fita mana"
"to ai naga ko wanka ba kayi ba, ko har yanzu tunanin kake ne?"
Ɗan murmushin yaƙe yayi, yana sake mamakin Widad, ya miƙe yaje yayi wanka ya shirya, yana yi yana kallonta yaga ko zata canza masa, amma yaga babu wata alama ta damuwa a tare da ita.
"zan tafi"
"Wai naga se wani sunkuyar da kai kake, kana komai a sanyaye meyafaru ne"
Cikin damuwa ya kalleta yace "bakomai"
"to seka dawo" yasa kai ya fita.
A hankali Widad tana ta koyon abubuwa, dan yanzu ta fara iya saƙa mafici da Hindu ke koya mata, tana gane abubuwa duk aikin da zasuyi seta shiga cikin su tana ƙoƙari.
Yanzu indai Widad zasu gaisa da Hindu da turanci suke yi, Hindu na da matuƙar ƙoƙarin riƙe abubuwa, gashi ta sawa zuciyar ta zata iya, tana son karatun sosai, Widad ta koya mata na boko sannan tana mata bayani akan litattafan addini, sega Hindu ta iya gaisuwa da turanci, tasan sunan abubuwa, Widad tana yawan yi mata magana da turanci dan wasu lokutan hausar ma wahala take mata, dan haka Hindu take kama wasu abubuwan.
Nan fa Hindu ta fara birge wasu daga cikin ƙawayenta, suke cewa itama ta koya musu.
Hindu suna ɗaki tana yiwa Gwaggo tsifa tace "Gwaggo, kinga laraban gidan me tabarma, da su Ishalle ne wai suma suke son a dinga koya musu karatu, nace zan tambayi Amarya amma nauyinta nake ji, kar taga kamar na takura mata"
Gwaggo tace "kunfi kusa keda ita ai, Amma na lura kamar bata son mutane fa, kina ganin ko baƙi akayi ɗaki take komawa bata son mutane, amma ki tambaye ta idan zata dinga yi muku taren"
Hindu tace "to shikenan zan tambayeta insha Allah, Amma nikam Gwaggo Amarya ba ƙaramin mamaki take bani ba, wai bata son meye kishi ba, kuma wai ita gani take Soyayya ƙaryace da ɓata lokaci, na tambayeta to bata son mijin nata? Wai wallahi itama bata sani ba ko tana sonshi ko bata sonshi "
Gwaggo tayi murmushi tace " Amarya 'yata ta kaina, yarinyar kam tabbas yarinta ce ke damunta, kuma kinga karta kamar shagwaɓaɓiya ce, bata san abubuwa da dama na rayuwa ba, shi kansa zaman Auren da alama bata san meye ba, Amma insha Allah ina son in zauna da ita, in dinga yi mata nasiha, naga tana jin faɗa, dan Hindu ina jin takaicin Abunda Hanne ke aikatawa a gidan nan, yadda take shigewa Yaron nan, dan ina daf da kai ƙararta gurin mahaifinku"
Hindu tace "A'a Gwaggo dan Allah kiyi hakuri, idan kika gaya masa ze ɓata mata rai sosai, ni mamakin da ta ke bani da kuɗin Aurenta a ka fa, amma take haka, ki dai cigaba da ja mata kunne zata dena"
"Ai banga alamar hakan ba"
Har Yusuf ya dawo a cikin damuwa yake, saboda ya fuskanci kwata kwata gane kan Widad se Allah, yanzu zaku zauna lafiya ana jimawa ta canza gaba ɗaya.
Widad bata san ya dawo ba, ta fito daga wanka tana zuwa ta tarar da Yusuf ya kwanta a ƙasa, ya lumshe ido.
Widad tace "ya dai harka dawo ne? Ya naga ka kwanta haka a ƙasa, ko jikinne?"
Ya buɗe idonsa ya kalleta yace "Eh na dawo, na gajine sosai bayana da ƙafafuna ciwo suke min"
Ajiye bokitin tayi ta zauna kusa dashi tace "me kaje kayi a wajen bayanka yake ciwo sekace tsoho?"
"Faskare nayi" ya bata amsa
'meye kuma Faskare? " ta tambaye shi, kallonta yayi yace " Faskaren ne baki sani ba? "
" Wallahi ban sani ba, kaima kana ganin wani abun idam nace ban sani ba ƙarya nake ko? "
" A' a ni bance ƙarya kike ba, nasan baki sani bane, kuma daɗina dake idan baki sani ba kina tambaya"
Widad tace "to ai ba wani abu bane, idan mutum be sani ba gara ya tambaya, ka tashi kaci Abinci seka yi wanka mana"
"bari in huta tukuna"
"Shikenan bari in sa kaya" har taje ta shirya Yusuf yana kwance, a hankali yaji tana danna masa bayan tace "wajen inane yake maka ciwon?"
"duka bayan Queen"
"bance bana son Queen ɗin nan ba?"
"Ai sunan naki ne bana son faɗa, kuma Daddy ma Gimbiya yake ce miki, ko in koma ce miki lovely kamar yadda yake faɗa?"
Dundu tayi masa tace "A'a Widad zaka dinga cemin, niba lovely kowa bace ta Daddy ce"
Yusuf yace "so kike Gwaggo tayi min faɗa? Tace ina faɗar sunan ki"?
Dariya Widad tayi tace "Hajiya Mama manya, tace in dena kiran sunan ka fa ko?"
"Eh amma baki dena ba kuma, ga sunan nawa ma baki iya faɗa ba, ana Yusuf kina Yoseef amma fa suman yana min daɗi in kin faɗa"
Murmushi tayi tana danna masa baya tace "shikenan zan dinga cewa Yayana, kamar yadda Daddy yake ce maka"
Yusuf yace "A'a nifa mijinki ne ba Yayan ki ba, call me with romantic names mana, haba ke kuwa"
"Kaine romantic ɗin ai, kai ka sansu ni ban sansu ba"
"Tabbas na sansu, kuma ni zan dinga kiranki dasu"
Shiru tayi masa, a hankali ya juyo daga ruf da cikin da yayi yace "Nagode sosai My wife, Allah yasa ki a Aljanna, naji daɗin tausar nan kamar karki dena, dama kin iya kula da miji haka?"
"A'a zomaye na iya kulawa da, ai koma meye kaika koyamin, idan bani da lafiya kayimin ina jin daɗi, shiyasa nayi maka"
Shiru ya ɗanyi sannan yace "Widad, meyasa kika ƙyaleni dukda girman laifin da nayi miki, baki hukunta ni ba?"
Widad tace "Saboda Widad ba azzaluma bace, babu zalunci a AƘIDATA, duk wanda na kasa yafewa abunda yayi min to tabbas girman laifinsa ya wuce tunani, ya wuce laifin da zan iya yafewane"
"Yanzu ni laifina be kai a hukuntani ba?" ya tambayeta
"tabbas laifinka ya kai girman a hukunta ka, sedai kash akwai wani dalili me ƙarfin gaske daze hana ka karɓi hukunci, akwai wata ƙaddara da ta ratsa, ita ce zata hana ka karɓi hukunci, sannan idan nace zan hukunta ka Yoseef banwa kaina adalci ba, dan ka bani kariya ka bawa rayuwata kariya sosai, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana ai, matsoraci kaga gumin da ka dingayi ɗazu kamar ba kaine Jarumin ɗan sanda ba me gwagwarmaya kamar yadda aka bani labari, amma se gashi ina baka tsoro"
"Wudas babu Jarumi a soyayya, ba hukuncin da za kimin ne damuwata ba, kice zaki rabu dani shine damuwata"
Haɗe rai tayi tace "me kace?"
"A ina?"
"da wani sunan ka kirani?"
Dariya Yusuf yayi yace "wai Wudas"?
"kaima ko? Zanyi maganinka da kai da Harin da kuke ɓatamin suna, ni ba haka aka samin ba"
"niba ruwana, ɗanawa kawai nayi ai, kuma sunan naki ne na Larabawa, ba kowa ze iya faɗa ba"
Jikinta ne ya ɗanyi sanyi, tai shiru, Yusuf yace "meyafaru kuma?"
"Yoseef ina missing ɗin Daddy sosai, zuciya ta na kwaɗayin in ganshi, i missed a lot from him, ina kewar babana, dashi na rayu na buɗi ido, amma yanzu muna duniya ɗaya amma munyiwa juna nisan gaske, a dalilin wasu tsirarin mutane da suka saka rayuwarmu a gaba "
Hawaye ne ya fara bin idonta, janyota jikinsa yayi ya shiga share mata hawayen cikin tausayawa yace " tabbas yin nesa da wanda muke so ba abune me sauƙi ba, kin ganni nima ban taɓa nisa da mahaifiyata haka ba, amma mu ɗau wannan a matsayin wata ƙaddara ta darasin rayuwa, kiyi hakuri insha Allah zamu koma kiga Daddy, nasan zaman ƙauyen nan tamakar zaman prison ne a gurinki amma ki daure mu cinye jarrabawar mu"
Ajiyar zuciya ta sauke, ta sake kwanciya a jikinsa tace "zamana a ƙauyen nan baya damuna, na ɗau hakan tamkar wani darasine na rayuwa, Allah ya na nunamin ishara, na koyi abubuwa da dama na rayuwa wanda bam sansu ba da, kuma a nan ina zaune hankalina a kwance babu tashin hankali, babu fargabar komai saɓanin a gida, ga dukiyar ga komai hankalina kullum a tashe ina tunanin ta inda maƙiya zasu farmin, nidai tun taso wata rayuwata a cikin ƙaddara take, ina fatan Allah ya kawomin ƙarshen abun nan haka, ya kawo kwanciyar hankali a gareni da mahaifina"
Tai maganar tana ci gaba da zubar da hawaye, sosai tausayinta ke ratsa ilahirin jikin Yusuf, ya dinga shfa gashin kanta cikin sigar rarrashi zuwa gefen fuskarta, yana tunanin anya duk ƙaddarar da Widad ta tashi a ciki takai a misalta ta dashi wadda ya tashi a cikinta?......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH
NA ƊAYA KYAUTA NE, WANNAN NA SIYARWA NE
₦300 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 54_55
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
Shiri ne ya wanzu a tsakaninsu, na wani ɗan lokaci, har bacci yayi awon gaba da Widad, Yusuf ya ƙurawa fuskarta ido, yana jin wani abu na fizgarsa game da ita, wani irin sonta na ƙara ratsa ilahirin jikinsa.
Wai yau Widad ce kwance a hannunsa, har take masa kuka yana rarrashinta, kamar ba itace wannan me tsawa da muzuran ba, ya kwaɗaitu da son jin meyafaru da ita a rayuwa, meyafaru a rayuwarta haka? Amma yasan idan ya takura seya sani, to tsaf ze rusa duk wata alaƙa da yadda da take tsakaninsu
Anwar kuwa gidan su Nurat ya tafi, seda yaje ƙofar gidansu sannan ya ɗakko wayarsa ya kirata, tana kwance tana kallon TV sedai idonta ce kawai akan tv, yayinda zuciyar ta tana can tana fama da tunani, se da wayar ta katse ya kuma kira sannan ta faraga, tasa hannu ta ɗaga wayar sedai tayi mamakin ganin sunan wanda yake kan wayar, Sunan Anwar ne a jiki.
Da hanzari ta miƙe zaune ta ɗaga wayar tasa a kunnen ta.
Anwar yace "ko bacci kike ne na tashe ki"
Zumbur ta miƙe zaune tace "muryar wa nakeji ne haka?"
"Muryar Anwar mana"
Cikin farin ciki Nurat tace "innalillahi, i don't even know what to say, I pray that am not dreaming"
Anwar yayi murmushi yace "you are not dreaming dear, ina harabar gidanku"
"dan Allah dagaske?" ta faɗa cikin tsananin farinciki
Anwar yace "leƙo ki gani"
Mayafin doguwar rigar jikinta ta ɗauka ta yafa, ta ruga da gudu tayi waje, aikuwa tana zuwa ta tarar da Anwar zaune a cikin mota, da sauri ta ƙarasa gaban motar, tana ganin Anwar ɗinne kuwa kawai ta tsaya tana murmushi a lokaci ɗaya hawayen tausayinsa da farinciki ya shiga bin fuskarta.
Ya rame sosai, se dogon hanci da manyan idanunsa da suka sake yin zuru zuru, ga duhu da yaya, koba a gaya maka ba akasan inda yaje babu komai se zunzurutun wahala.
Ya kalleta fuskarsa ɗauke da damuwa yace "ya da kuka kuma?"
"Yaya Anwar dole inyi kuka, baka ji ba baka gani ba daga abun alkhairi aka kama ka, kaje kasha wahala ba yadda banyi ba a ɓoye a samu a sakeka amma abu ya gagara, ƙarewa ma akace kotu za'a kaika na shiga damuwa sosai hankalina ya tashi, se gashi Allah yasa ka fito Alhamdilillah, ban taɓa zaton zaka fito ba"
Anwar yayi murmushi yace "hakane, amma yanzu dena kukan mana"
Murmushi tayi tace "ƙyaleni na farinciki ne, taso muje Mummy ma na ciki seku gaisa, amma dan Allah karka nuna muna wani abu tarene, kawai dai ka nuna ka biyo a gaisa ne please"
Anwar yace "karki damu, ba abunda zan nuna insha Allah"
Ya miƙe ya bita zuwa cikin gidan, a falo ya zauna yayin da Nurat ta shiga ɗakin mahaifiyarta "Mummy kizo ga Anwar yazo ku gaisa"
Da ɗan mamaki ta kalli Nurat tace "Wane Anwar ɗin?"
"ɗan gidan Hajiya Halima mana, yazo wucewa ne yace bari ya tsaya a gaisa ai an sako shi shekaranjiya"
Mummy tace "Allah sarki, yaron kirki ashe an sake shi, bari gani nan bari inzo mugaisa"
Ta sako mayafi ta fito, Anwar ya risina ya gaishe ta tace "Anwar ashe an sako ka? To Ubangiji Allah ya tsare gaba"
"Ameen ya Allah Mummy nagode sosai"
"bakomai Anwar, dan Allah ka gaisarmin da maman naka idan ka koma"
"zataji insha Allah Mummy, nagode sosai"
"Yawwa Allah ya tsare"
Suka amsa da Ameen, ita kuma ta koma ɗakinta.
Nurat ta jashi suka koma harabar gidan, ta kalle shi tace "Yaya Anwar, ya akayi ka fito ne?"
Ya ɗanyi ajiyar zuciya yace "kowa tambayar da yake min kenan, wallahi ban sam waye ya fito dani ba, ban san mutumin ba, na tambaye shi waye shi, yace wai ba'a bashi damar ya sanar dani waye shi ba, amma kin san wani abu?"
Tace "A'a seka faɗa"
Anwar ya ɗan ƙara ƙasa da muryarsa yace "ya cemin Daddy yana gurinsu, shiyasa ma suka sa aka sakeni, amma ban san dalilin da yasa suka sa aka sakeni aka bar Doctor Sufyan ba"
Zaro ido tayi tace "yana gurinsu kuma? To suwaye su? Meyasa suka ɗauke shi?"
"Nima be bani amsa ba Nurat, abun da ya cemin kawai kenan, wallahi gaba ɗaya a cikin damuwa nake, babu Widad babu Daddynta, gashi ranar daza'a ɗauketa kamar tasan abunda ze faru tacemin Anwar ga Amanar Daddy na nan ka kulamin dashi"
Cikin damuwa Nurat tace "kayi haƙuri Yaya Anwar, Allah ya gani kayi iya ƙoƙarinka, amma ƙaddara fa ta riga fata, babu yadda muka iya, sedai muyi ta musu Addu'a Allah yasa suna hannu nagari"
Anwar yace "Ameen, Amma abun da damuwa ace mace kamar Widad a hannun wanda ba'a san ko suwaye ba, akwai tashin hankali sosai Nurat, kin san ku mata kusa a cikin hatsari kuke, daɗina ɗaya tana tare da Yusuf, amma dukda haka abun ba daɗi, mussman shi ƙaddara ta faɗa masa beji ba be gani ba"
Nurat ta ɗanyi shiru tace "hakane kam, ni kaina ina tausayin Yusuf Anwar, amma dan Allah dagaske direban Widad ne?"
Anwar yace "meyasa kika tambaya?"
"bakomai kawai na tambaya ne"
Yace "eh direbanta ne, me kika gani?"
Ɗan girgiza kai tayi tace "yana da kirki sosai, kuma da alama ta yadda dashi sosai, na zata ɗan uwantane"
"Nima na gani, kuma yana ƙoƙari sosai akanta, yana mata biyayya ne sosai, kuma yana da haƙuri shiyasa suke shiri wasu lokutan"
Nurat tace "hakane kam, amma kuwa anje gidan su Yusuf ɗin, 'yan uwansa sun san halin da yake ciki?"
"Aini kinga ban daɗe da dawowa ba, wasu abubuwan duk ban san me ake ciki ba, ban san daga ina yake zuwa ba, sedai zan bincika inji ubangiji Allah ya bayyana mana su gaba ɗaya, amma ina cikin damuwa sosai Nurat, tun Widad na ƙarama nake sonta, ban taɓa furtawa ba, saboda sanin halinta, katsan bayan na dawo naji ance Fahad ɗan gidan Alhaji Bulama zata aura, naita ƙoƙarin in cireta daga raina, sedai ashe ita gaba ɗaya bata da babban maƙiyi a duniyar nan sama da Aure, tana yiwa Aure wani bahagon kallo ne, har a yanzu haka na kasa cireta daga raina, ina jin sonta a zuciyata, ko bacci bana iyayi yadda yakamata, gashi ban san inda take ba gashi na kasa riƙe amanar data barmin"
Wani irin tausayin Anwar ne ya kamata, a ranta tace 'ashe kaima kana cikin damuwar da nake ta soyayya'
A zahiri kuma tace "na tausaya maka Yaya Anwar, ka sawa ranka wannan ɗin Jarrabawa ce, ubangiji Allah yasa mu cinye jarrabawar nan, kasha Lemom mana"
Girgiza mata kai yayi yace "A'a tafiya zanyi nagode sosai Nurat"
Ɓata rai tayi tace "gaskiya idan baka sha ba bazan ji daɗi ba, sekace na baka wani guba, ko kaima Widad ɗinne?"
Murmushi yayi yace "wane ni in zama kamar Gimbiya"
Nan ya buɗe lenon ya tsiyayya yana sha suna cigaba da hira.
Mahaifin Nurat ne ya dawo suna tsaka da hira, ya shigo da motarsa gidan yayi parking, ya fito daga motar yazo ze raɓa su ya wuce, Anwar yace "barka da Rana Yallaɓai"
Ɗan tsayawa yayi ya kalli Anwar yace "wa nake gani haka kamar Anwar?"
"eh nine ranka ya daɗe"
"Allah sarki, ashe ka fito?"
"Eh wallahi Na fito Alhamdilillah"
"to yayi kyau haka ake so ai, har yanzu kuma babu wani labari akan ɓatan Daula ko?"
"Babu har yanzu dai muna sauraren hukuma ne dai"
"Allah sarki, yanzu an fasa kaika kotun kenan?"
"Eh an wankeni, ance bani da laifi shine suka ƙyaleni"
Alhaji Musa yace "gaskiya ne, ai dama bekamata a tsare wanda bashi da laifi ba, hakan ba daidai bane, kuma lawyoyin naku ne suka fitar da kai?"
"A'a su hana su belina akayi, daga baya ma in sunzo hana su ganina ake, wani mutum ne yazo aka fitar dani"
"ikon Allah, shima lawyer ne kokuwa?"
Anwar yace "a'a ban san waye ba gaskiya, dan nima be gayamin ko shi waye ba"
Alhaji Musa yace "Allah sarki, to ubangiji Allah ya tsare"
"Ameen yallaɓai nagode"
Alhaji Musa ya shige cikin gida.
Duk a aikin gida da Widad ke koya bata taɓa attempting zuwa gaban murhu ba, saboda bata son hayaƙi sam, ko menene tana daga gefe.
Tana zaune a ƙarƙashin bishiya tana gyaran wake, Hindu tace "Amarya dan Allah ƙawayena ne suke so suma a dinga koya musu karatu, in basu dameki ba, in baza'a takura miki ba"
Widad ta ɗanyi shiru sannan tace "shikenan tunda ta hanyar ki ne, aini ban isa ince a'a ba, su samo abun rubutu da littafi se mucigaba insha Allah"
Gwaggo tace "Amarya idan da takura fa karkiyi kara, kice musu a'a kawai su haƙura"
"A'a Mama babu takura, bana son mutane ne dai su fiye zuwa inda nake, amma ai bakomai shi ilimin 'ya mace ai abun sone, koba komai zasu amfani al' ummar da suke ciki, suzo zan koya musu Insha Allah"
Gwaggo tace "to Allah ya saka miki da Alkhairi, mu zuwanki garin nan alkhairi ne ai a wajenmu"
Widad tai murmushi tace "bakomai Mama, nima haɗuwata daku alkhairi ne ai".
Hindu tace "lallai su Indo zasuji daɗi, bari inyi sharar nan inje in gaya musu"
Hari tace "wudas dan Allah nima gasu abu na nan a haɗamin dasu dan Allah"
Hararta Widad tayi tace "baza'a koya musu ba ɗin, yaren yahudawan zan koya musu?"
Hari ta wangale baki tace "haba Wudas, dan Allah kiyi haƙuri ki koya musu"
"Anƙi a koya musun" Widad ta bata amsa tare da haɗe rai.
Hari bata kuma yin magana ba, tayi shiru ganin yadda Widad ta haɗe rai, Hanne ce ta fito tana wani yatsine fuska tana harare harare, Hindu ta kalle ta tace "Hanne ke zakiyi wanke wanke fa yau, kin bari ƙudaje se bin kwanukan suke"
Hanne ta galla mata harara tace "bazan ba, inda can ke kike sani inyi, banza uwar shisshigi da sa ido"
Hindu tace "ke kika sani, haka za'a miki auren kije kina ƙazanta, ki bar kwanuka ƙudaje nabi"
"Eh naji gara ni inada mashinshini ma, kefa ba uban wanda yake zuwa gjrinki, aba kamar mujiya aikin banza kawai"
Jikin Hindu ne yayi sanyi, tai shiru gwanin ban tausayi.
Hari se cewa tayi "ni kaina ina mamakin baƙin jini irin na Hindu, ba wanda yake zuwa inda take saboda tsabar girman kanta da baƙin jini"
Shiru Hindu tayi tana goge Hawaye, Gwaggo ce ta janyo Hanne ta dinga kifa mata mari a zuciye.
Widad tace "wai Auren nan dolene? Meye dan mutum bashi da saurayi? Saurayin banza dana wofi, Auren dole ne, itama wannan banzar mata hankali se kace ba sister ɗinki ba, kuna uwa ɗaya kina cin zarafinta"
Hansai tace "ba uwarsu ɗaya ba, Hindu ita kaɗai babarta ta haifa ta rasu, Gwaggo ce ta Riƙeta"
Widad tayi mamaki sosai, dan yadda Gwaggo ke son Hindu seka zata ita ta haife ta.
Widad ta ƙarasa inda Hindu ke tsugune tana kuka, Widad taje ta rugumo Hindu ta dinga rarrashinta tace "kiyi haƙuri kinji Hindu, Allah has a better plan for you kinji Hindu, kiyi haƙuri ki ƙyalesu, ai Aurem ba dole bane"
Gwaggo seda tayiwa Hanne tatas da zagi, ta tsitsstinka mata mari, tazo ta kama hannun Hindu tace "dan Allah kiyi haƙuri kinji Hinduna, muna nan insha Allah miji nagari zezo miki insha Allah"
Ita dai Hindu ba tace komai ba, se goge hawayenta da yake faman yi, tana jin zafin Gorin da akan mata na cewa bata da saurayi, Widad ma abun ba ƙaramin baƙantawa Widad rai yayi ba, dan bata son taga abunda ze taɓa mata Hindu, Allah ya haɗa jininsu sosai.
Widad ta kalli Hari tace "kekam abunda kika yi baki kyauta ba Hari, ke kanki aka bibiya sadakarki aka bawa megari ba dan kina da wani abu da namiji ze kalla ya aureki ba, dan ba kyau kika fi Hindu ba, yakamata ki dinga jan girmanki kema kin haifi mata"
Shiru Hari tayi da yake tasan bata da gaskiya.
Gaba ɗaya ƙarashen wunin nan haka Hindu tayi shi ba walwala, hakan ya shafi Walwalar Widad itama, seta kasa sakewa sukayi jugum jugum.
Nurat suka gama hirarsu da Anwar, tai masa rakiya har mota ya tafi, sannan ta dawo, tana shiga falo ta tarar da mahaifinta a tsaye yana huci, ya kalleta yace "dan ubanki meya haɗaki da wannan yaron?"
Cikin rashin fahimta Nurat tace "Daddy Anwar nefa"
"ina ruwana koma uban waye? Ke yanzu shikenan ban isa in gayamiki kiji ba? Meye haɗinki dashi nace?"
Mahaifiyar Nurat ce ta fito da sauri tace "dan Allah ka saurarawa yarinyar nan, wucewa yazo yi ya tsaya suka gaisa meye abun ɗaga hankali kuma? '
" ke dama ke kike goya mata baya take karyamin doka, ni anya ma kuwa wannan' yata ce"
Cikin mamaki tace "Meka ke nufi da anya kuwa 'yarka ce? Zargina kake kome? Kokuma dan kana abu zata kake kowama haka yake?"
A fusace yace "ni kike gayawa haka?"
"na gaya maka ɗin, ashe ba daɗi nida ka gayamin"
"A gaban' yata kike cewa ina biye biye?"
"to kace ƙaryane mana? Ni zaka kalla kace anya 'yarka ce?"
Aikuwa cike da zuciya yayi kan mahaifiyar Nurat, sedai cikin gaggawa Nurat ta shiga tsakani tana kuka, aikuwa yasa hannu ya shaƙota yayi wurgi gefe ɗaya, bisa tsautsayi tai gware da center table, take ta zube a gurin jini ya shiga zuba a goshinta kamar an buɗe famfo, take suka yi kanta da gudu, sedai ko motsi ba tayi.
Mahaifiyarta ce ta ɗagota a gigice tana kiran sunanta, Alhaji Musa yasa hannu yana ƙoƙarin karɓar Nurat a hannunta amma ta riƙeta gama taƙi sakarmasa ita, cikin kuka tace "ka ƙyalemin 'yata, ai dama kace ba' yarka bace, tunda ka kashemin ita se hankalinka ya kwanta"
Be saurareta ba ya suri Nurat da sauri yayi waje da ita jini yana zuba a goshinta.
Amal kuwa bayan ta shiga gida, Hajiya Halima tace "ina Anwar ɗin?"
"Ya ajiueni ya tafi, wai zashi wani guri ne"
"Nifa bana son yawan yawon nan da yake tafiya, se wani abun ya sameshi tukuna ko? Ze dawo ya sameni ne, ina jinki meyafaru da kukaje gurin Bulama"
Amal tace "ba wani abu bane, dama kawai tambayarsa yayi ya akayi yayi free? Se kuma jaje da yayi masa"
Hajiya Halima tayi tsaki tace "Aikin banza, dana san hakane wallahi ba zashi ba, mutumin banza kawai"
"Mummy kenan ɗan uwankine dai"
"dalla rabu dani, ɗan uwana mara amfani ba"
Amal tai murmushi tace "in an jima zamuga kun jone ai, ba'a shiga faɗanku"
Widad bata wani iya rarrashi ba, dan haka ta kasa saka Hindu farinciki, haka kurum idan ta tuna Gorin da'akayiwa Hindu se taji ta ƙara tsanar Hanne, sam Hanne bata ɗakko halin Gwaggo ba, Gwaggo mace ce me kirki da kawaici, ba zaka taɓa cewa ba ita ta haifi Hindu ba, saboda yadda take nunawa kamar tafi son Hindu ma aka Hanne kai kace gaba ɗaya ita ta haife su, bautar da Hindu take wa Gwaggo Hanne ba tayi, ga shegen som jikin tsiya, shiyasa basa shiri da Gwaggo.
Gwaggo se jan Hindu take da hira, amma taƙi sakin jiki, saboda gaba ɗaya ranta a ɓace yake, haka suka haƙura suka ƙyaleta, sedai hakan ba ƙaramin damun Widad yayi ba.
Yau shiru shiru Yusuf be dawo ba, gashi tun la'asar hadari yake haɗuwa a garin, se cida ake me ƙarfin gaske, kowa ya shige ɗaki ga iska da'ake yi, gaba ɗaya hankalin Widad yaƙi kwanciya, Yusuf be dawo ba ga hadari se cida yake, ga wani irin tsoro da ya baibayeta, lungun kan katifa ta koma tayi shiru tana ta addu'a a ranta.
Har magariba Yusuf be dawo ba, daga bakin ƙofar ɗakinsu tayi alwala, ta rufe ƙofar ta dawo tayi salla, se wata irin walƙiya ake.
Ana idar da la'asar aka kece da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, babu Yusuf babu labarinsa, hakan ba ƙaramin ɗagawa Widad hankali yayi ba, be taɓa yin haka ba se yau.
Tun Widad na tsumayin dawowar Yusuf harta fara cire rai, ga tsoro da ya bai baye ta, take ta fashe da kuka, ta dinga kuka kamar wata ƙaramar yarinya, ga tsoro ga gefe guda tana tunanin ko wani abu ya samu Yusuf ne.
Har wajen ƙarfe goma da rabi na dare, gashi babu alamar za'a tsagaita da ruwan nan, ta dunƙule guri ɗaya tana kuka, ji take tamkar ɗakin nan ze ruso a kanta, dan in akayi cida ji take tamkar ɗakin yana vibrating.
Babu zato ba tsammani taga An turo ƙofar ɗakin, Yusuf ne ya shigo ya jiƙe sharkaf da ruwa se ɗiga yake, jikinsa yana rawar sanyi.
Tana ganinsa maimakon ta tausayawa a halin daya dawo, kawai ta fashe da kuka ta haushi da faɗa
"Ina kaje ka tsaya, kalli agogo ƙarfe nawa? Kawai ka kama ka ɗagamin hankali ga tsoro inaji, ka fita kaje kayi zamanka baka damu da halin da zan shiga ba, wannan wane irin abu ne haka?"
Aikuwa Yusuf ya ƙule, akanta yaje yasha wannan uwar baƙar wahalar, ga ruwan sama yayi masa duka, bata tausaya masa ba se masifa da ta haushi da ita daga shigowarsa, aikuwa ya ajiye kayan hannunsa, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko wata leda ya jefo mata, ya juya ya shiga kokawar canza kayan jikinsa.
Ledar ta ɗauka, taji an nannaɗe leda cikin leda, ga ɗumi a jikin Ledar, se ƙarnin kifi da yake tashi a jiki.
Yadda ya haɗe rai ne yai mata banza yasa ta gane haushi yaji, ya canza kayan jikinsa ya ɗau abun shimfiɗarsa ya shimfiɗa a bakin ƙofa inda yake kwanciya, ga babu abun rufa ga iska da feshin ruwa a gurin.
Gaba ɗaya taji tausayinsa ya kamata, ta ƙarasa kan bargon da yake kwana ta zauna tace
"ka taso mu kwanta akan shimfiɗata, kaga nan ruwa yana jiƙaka"
Banza yayi mata, yaƙi ko motsawa daga inda yake, balle tasa ran ze kulata.
"Yoseef magana fa nake maka" still dai bece komai ba yayi mata banza.
Ta Kai hannunta ta shiga ɗan girgiza shi tana faɗin "dan Allah ka tashi, muje mu kwanta nan akwai sanyi"
A ɗan kausashe yace "malama ki ƙyaleni, tunda bakya tausayina komai nayi abun faɗa ne a gurinki, bana taɓa yi miki abu ki yaba, sedai ki ɓata mini rai, maimakon ki tambayi ya akayi na daɗe haka meya sameni kawai kin hauni da masifa, ni matsa ki ban guri ki dena taɓani"
Se kuma taga tabbas abunda tayi bata kyauta ba.
"Am sorry, ka tashi daga nan karka yi zazzabi"
"ina ruwanki idan nayi, ai ba damuwa kika yi dani ba, ki rabu dani kawai"
Taga dai alamar Yusuf bashi da niyyar tashi, dan haka kawai tayi kwanciyarta a bayansa, sosai ruwa yake feshi yana jiƙasu.
Yusuf yace "ke ki tashi daga gurin nan, wannan ruwan da yake taɓaki ze iya saki mura ko zazzaɓi"
"gara ya samu tare, tunda bazaka tashi ba" tai maganar tana sake maƙalƙaleshi ta baya, Yusuf jiya yi yana nema ya dena fushin da yake, ya maze ya kunna fitilar torchlight ya haskata yace "malama ki cikani kije ki kwanta"
Noƙe masa kafaɗa tayi, Yusuf yace "Shikenan naji, tashi muje mu kwanta a taki shimfiɗar"
Tana jin haka ta miƙe suka nufi katifar, ta gyara musu ita Yusuf ya zauna yace "miƙomin ledar nan" ta juya zata ɗakko akayi wata walƙiya data haske ɗakin gaba ɗaya.
Gaba ɗaya ta afko kan Yusuf, ta riƙe shi gam jikinta yana tsuma, ta runtse ido sosai tana ajiyar zuciya.
Aikuwa akayi wata tsawa me ƙarfin gaske, ruwa ya sake ɓallewa, haska fuskarta yayi yaga yadda jikinta yake tsuma tayi wiƙi wiƙi da ido kamar Agola a rabon gado, yai dariya yace "wai baki iya addu'a bane, se tsoro da kuka?"
Tashi tayi daga jikinsa tana cuna baki gaba, ta miƙo masa ledar kifine a ciki, ya kalle ta yace "wani guri aka kwatantamin, nace bari inje in siyo miki kifi, gurin da nisa ga babu abun hawa a kusa, nayi tafiyar ƙafa sosai, shiyasa kiga na daɗe fa"
Shiru tayi tana kallonsa kamar taga wani sabon abu, ya buɗe ledar kifin, manya manyan gashashiyar tarwaɗa ce da karfashe.
Ya zauna ya dinga cire ƙayar ya ɗakko ya kai bakinta, tasa hannu zata karɓa ya girgiza mata kai yace "karki ɓata hannunki da ƙarni"
Haka ya dinga bata tana ci, can kawai yaga tana hawaye, ya kalleta yace "meyafaru kuma? Yanzu kuma me nayi miki"
Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.
"kifin ne ba daɗi" ya kuma tambayarta, nan ma ta girgiza masa kai
"to faɗan da nayi mikine ya saki kuka?"
Nan ma ta girgiza kai, ƙarshe tace "Nagode"
Yusuf yace "da akayi me?"
"Ka siyomin kifi"
"Haba Queen, meye abun kukan kuma? Kukan ki yana ɗagamin hankali sosai, dan Allah kidena kinji, bakomai is my responsibility to make you happy Baby"
Yai maganar yana ɗago haɓarta da hannu ɗaya.
Shiru tayi tana ci gaba da share hawaye, seda ta ƙoshi sannan Yusuf yaje ya wanke hannunsa, ya dawo ya tarar da ita a zaune.
Yazo ya zauna a kusa da ita yace "oya kwanta"
A hankali ta zame jikinta ta kwanta tayi shiru, kamar wadda ruwa ya cinye, shima ya kwanta sedai ko mintuna biyar ba'ayi ba aka sake ƙyallo walƙiya, aikuwa ta kuma cakumo Yusuf kamar jikinsa ya tsage ta shige.
Yusuf yace "Gimbiya addu'a zaki dingayi, kidena tsoro haka"
Ba tace masa komai ba se sake lafewa da tayi a jikinsa, taƙi ko motsawa.
Haka aka cigaba da tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
Shima Yusuf ya rungumeta gam a jikinsa, yana wasa da saman gashinta data ɗaure da ribbon.
A hankali ya kai hannunsa kan ribbon ɗin, saitin kunneta yace "in cire?"
"inka cire min seka gyaramin"
Murmushi yayi, ya zare ribbon ɗin dogon Gashin kanta ya baje akan katifar.
Yusuf ya dinga wasa da gashin, yana ɗaga shi yana wasa dashi, can Widad tace
"Yoseef wai dan Allah Aure dolene? Sannan meyasa ake Aure ne?"
0 comments:
Post a Comment