Nasir yace "Yayana, tun ɗazu nake gurin nan naji duk hirar da kuke da Anty, sedai bazan bari ka cigaba da wahalar da kanka saboda niba, akwai buƙatar kaima ka gina rayuwar ka data iyalinka ni dai ka ƙyaleni kawai, na haƙura da Huda"
Yusuf yace "ba shawararka nake nema ba, a gurin Allah nake nema, fita ka bani guri"
"Yayana, ka saurareni na haƙura da zancen Huda wallahi, bazan sake zancenta bama"
Yusuf be saurari Nasir ba yai waje abunsa, Nasir ya ƙarasa shiga ya tarar da Nadiya a zaune ya nemi guri ya zauna yace "Anty dan Allah kisa baki, kar Yaya ya ciwo bashi saboda ni, ki gaya masa na haƙura da zancen Hudan nan"
Nadiya tace "kai ina ruwanka, ka zuba ido kawai"
"ba batun in zuba ido bane rayuwarku da cutu saboda ni, dan Allah Anty ki gaya masa na haƙura da Huda"
Ƙyaleshi Anty Nadiya tayi ta shiga ayyukan ta.
Bayan sallar magariba Nasir ya fita.
Nasir ya tafi gidansu Bulama, ya jashi sukaje masallaci sukayi salla.
Nan Nasir ya bawa Bulama labarin abunda yake faruwa, Bulama yace "to ita kaɗaice 'ya, malam ka haƙura mana"
Nasir yace "haba Bulama, ya zakace haka, kasan yadda nake son Huda kuwa?"
Bulama yace "eh mana, kai banda abun soyayya meya haɗo biri da gada dama, ina kai ina Auren balarabiya ko dan kaga kana juya kuɗi a hannunka, malam ka nemi wata me ɗan rangwamen gata in auren kake so kayi"
Nasir yace "ni bama wannan ba Bulama, kasan Yaya Nasir wai bashi ze ciyo a kai kuɗin Auren Huda, sun yanaka mana kuɗi kusan million huɗu"
"Au wai dama sunce zasu baka auren nata?"
"Eh mana, sunce zasu bani, amma baffanta yace kuɗin Auren million huɗu, na rasa yadda zanyi ne, ga Yayana wai ze ciyo bashi akai kuɗin auren"
"bashi kuma? Kawai ka bari idan ya karɓo bashin, kazo muje 'yan mata se wadda kake so, mezesa ka wahalar da kanka akan wannan balarabiyar, hasken fatane fa kawai da gashin'
Nasir yace " A'a gaskiya ni Huda nake sl, kuma bazan ma bari ya karɓo bashin nan ba gaskiya"
Bulama yace "kai meyasa baka da wayo, wallahi garin nan akwa tsula tsulan 'yan mata, duk abunda kake so zasuyi maka indai da uwar kuɗin ka"
Tsaki Nasir yayi, ya tashi ya bar gurin saboda kunna shi da Bulama yayi.
Be zame ko ina ba se gidan Alhaji Abubakar, ya samu Ahmad ɗan gidan Alhaji Abubakar, suka zauna suka gaisa Ahmad yace "Angon Huda ya akayine? Naga baka walwala sam"
"Ahmad ina zanyi wata walwala? An yanka min sadaki fiye da tunani, gashi gaba ɗaya jarin da ribar da nake juyawa basu fi million ɗaya ba, ga Yaya Yusuf duk ya damu, har yana batun ze karɓi loan, gaba ɗaya na damu nina ma haƙura gaba ɗaya, amma yaƙi saurarata"
Ahmad yace "Nasir, ita kanta Huda tana buƙatar taimako, idan ka aureta zata samu sassauci, Allah baze hanaka yadda zakayi ba, Insha Allah, in dai matarka ce seka Aureta"
Nasir yace "Ni dai na haƙura na fidda rai, nasan ina matuƙar son Huda, amma bani da halin Aurenta"
"Ka dena faɗar haka, Insha Allah za'a samo kuɗin nan, kuma zaka auri Huda"
Nasir yace "to idan rabona ce Allah yasa in samu"
Yusuf ya dinga faɗuwa yana tashi, ya fasa karɓar bashin banki saboda haramcin hakan, Amma ya saida abubuwansa ya tattara kuɗin hannunsa da ƙyar sukayi million ɗaya da rabi, Ahmad ya bawa Nasir gudunmuwar dubu ɗari biyu, shima ya tattara ɗan abunda yake dashi, amma kuɗi ko million biyu basu yi ba, saura kwana uku kwanakin su cika, Alhaji Abubakar yazo ya samu Yayan Nasir yace "Malam Yusuf ya ake ciki ne? Kun haɗa kuɗin kuwa?"
Yusuf yace "wallahi kuɗin nan basu kai ba, muna ta faɗi tashine, dan Allah inda hali a basu haƙuri su ɗan ƙaramana lokaci, dan Allah karsu bawa wani, Insha Allah zamu cika a samu Nasir ya aureta"
Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar yayi yace "nikam wani irin so kakewa Nasir haka?"
Yusuf yayi murmushi yace "Nasir ne kaɗai ya ragemin, kuma kaga yarone ƙarami ba wani babba bane, kuma maraya ne, yana buƙatar a jashi a jiki, kuma iyayenmu sun mana wasiyya sosai akan muso juna, inyi haƙuri dashi in kula dashi, kaga dole in kula da marayana"
Alhaji Abubakar yace "Masha Allah, gaskiya na daɗe banga managarcin mutum kamarka ba Yusuf, Allah ya biyaka, kawo abunda ya samun, inje musu dashi inga ya zamuyi"
Yusuf ya dinga murna, kamar Alhaji Abubakar yace an bawa ƙaninsa Hudan, yaje ya kawo masa kuɗin, ya duba ya ƙirga su sannan yace "zanje can marocon, zanga yadda zamuyi, amma da ina da 'ya ko ƙanwa gaskiya dana baka, dan na yaba da amanarka da haƙuri da ɗan uwanka'
Yusuf yayi murmushi yace " rufamin Asiri kar Uwargida ta jimu, kasa ta haɗemin rai yau"
Sukayi dariya gaba ɗaya, daga nan suka yi sallama.
Sam Nasir be san me ake ciki ba, Yusuf yana ta cigaba da fafutuka, yana haɗawa da Addu'a.
Tafiyar Alhaji Abubakar da kwana biyar, ya dawo yai sallama da Yusuf ya sanar masa da an basu Huda.
Yusuf ya gigice yace "ai bamu cika kuɗin ba"
"karka damu, na shawa kan wannan matsalar, nan da sati biyu za'a kawo masa ita"
Yusuf yai godiya kamar ze duƙawa Alhaji Abubakar, har seda yasa Alhaji Abubakar yaji kunya.
Shikam Nasir ya dawo daga kasuwa, yayi sallar isha'i yaje yayi kwanciyarsa, ko abinci be nema ba, babu abunda yake banda begen Huda.
Yusuf ne ya shigo ɗakin da Nasir yake yace "Ango kasha ƙamshi"
Nasir be gane me yayansa yake nufi ba, yayi zaton zolayarsa kawai yake.
Yusuf yace "gobe in Allah ya kaimu, masu aiki zasuzo suyi gyare gyare a gidan nan, ka tattare kayanka ka koma shagon gidana"
Cike da rashin fahimta Nasir yace "gyaran me kuma za'ayi?"
"Amarya za'a gyarawa gida"
"Aure zaka ƙara ne?"
Yusuf yace "Rufamin Asiri, inani ina ƙara Aure, Nadiyata ta isheni matar rufin Asiri, 'yar aljanna insha Allah, har ƙiyama muna tare da ita"
Nasir yace "to gyaran me za' ayi?"
"Huda za'a gyarawa gida"
Zare ido Nasir yayi yace "wace Hudan?"
"Hudanka mana"
'Yayana, yaushe ta zama tawa? "
" Sun baka, nan da sati biyu insha Allah za' a ɗaura Aure"
Ai ba shiri Nasir ya rungume Yusuf ya fashe da kuka yace "Yayana, wallahi na rasa me zance ma gaba ɗaya, yadda kake ƙoƙarin farantamin rai, Allah ya sadaka da Annabin rahama, yasaka a aljanna ma ɗaukakiya"
Yusuf yace 'Ameen ya Allah, tare da kai ƙanina, farincikin ka shine nawa, nima nasan idan nine a halin da kake ciki, ba zaka zuba ido ba, ina me maka nasiha daka kula musu da' ya, ko bayan ba raina ka tuna gwagwarmayar da muka sha kafin ka sameta, ka nunawa duniya mazan hausawa Jarumai ne, kuma sun iya riƙe mace su bata kulawa "
Nasir yace " karka damu Yayana, Insha Allah zanyi iya ƙoƙarina inga na riƙe Huda da Amana"
Haka Yusuf ya ci gaba da yi masa nasiha, da jan kunne akan sha'anin Aure.
Nan da nan magana ta cika unguwa Nasir ze auri Huda, wani abun takaici dangin mahaifinsu sukace bada yawunsu ba, ba zasu yi jagora aje a Aurowa Nasir balarabiya ba, babu hannunsu a ciki, abun nan ya ƙara tsayawa Nasir a rai, ƙiri ƙiri se bare ne yayi jagorancin karɓa masa Auren wato Alhaji Abubakar.
Haka suka tafi maroco, da Alhaji Abubakar, da ɗansa Ahmad, da Yusuf da Nasir da wasu Abokan Alhaji Abubakar suka tafi maroco, Nasir yaso a tafi da Bulama, amma Yusuf ya hana yace ba zasu je da shi ba.
Huda ji take kamar ba itaba, lokacin da aka faɗa mata kuɗin da aka yankewa Nasir ta fidda rai da Aurensa, saboda tasan bashi da wannan kuɗin, ta fidda rai gaba ɗaya ta haƙura, se rashin lafiya take tana rama, babu zato babu tsammani yayarta Islam tazo mata da zancen ai megidanta ya zo da kuɗin Auren Nasir daga Nigeria, Alhaji Abubakar ne ya cika kuɗin, amma babu wanda ya gayawa hakan.
Baffansu Huda be taɓa tsammanin za'a iya biyan kuɗin nan ba, duba da yadda aka gaya masa Nasir marayane, kuma bashi da ƙarfi, ganin haka yasa yace tunda ta dage se bahaushe, bahaushen ma talaka ta dage ita da 'yar uwarta to suje, gasu nan ga bahaushe, kuma ya cire hannunsa daga kansu, kome ze faru ta nemi' yar uwatta da mijinta da suka dage akan se anyi wannan Auren, karsu ƙara nemansa.
Huda ta wani fannin tayi farinciki, yayinda gefe ɗaya kuma hankalinta a tashe, jin cewar jigon da suke tunƙaho da shi yace bashi basu.
Alhaji Abubakar kuma yace yaji ya gani, shi har Abada Aure albarkarsa ake nema ba wai tarin dukiya ba, idan da rabo a gaba Nasir zeyi Arziki, kuma in dai Huda ce kome ze faru ze riƙeta, balle babu abunda ze faru se alkhairi.
Shikuma Habib yace se an biya shi duk abunda ya kashewa Huda, alhalin duk abunda Ake bayarwar ba bata akeyi ba, wanima bata san an bayar ɗinba.
Da kuɗin Auren gurin Nasir, aka tattara abunda ya samu aka biya Habib.
Kamar wasa ranar wata juma'a, bayan sallar juma'a, a masallacin Kairaouine, suka ɗanyi shagalinsu a can, da suka tashi dawowa Nigeria, Alhaji Abubakar ya kasa ya tsare ya karɓi sadakin Huda a hannun ƙanin mahaifinta, sauran 'yan uwa ma suka tattara mata sha tara ta arziki, wani aka bata wani kuma aka ƙwace, suka taho da Amarya Nigeria.
'yan unguwar su Nasir, suka haɗa kuɗi suka shirya musu walima, wani ya bada hall, wani ya bada buhun shinkafa, gaba ɗaya kai baka ce Auren maraya ne ba, abokansu suka dinga basu gudunmuwar kuɗi wasu kaya, saboda duk wanda yasan Nasir da Yusuf yasan iyayensu, yasan mutane ne masu karamci da biyayya.
A lokacin maƙoci yana ganin ya isa da ɗan maƙocinsa, ana zaune lafiya kamar 'yan uwa dan haka Nasir yayi mamakin yadda bare sukayi musu wannan karar amma dangin mahaifinsu suja kasa yi musu.
Duk Wanda yaji yadda akayi auren yasan kawai rabone, dama Allah ya rubuta Huda rabon Nasir ce.
Huda ta tare a gidanta, musamman Yusuf yasa Nasir a gaba sukaje gaban Alhaji Abubakar sukayi masa godiya dashi da Islma amaryarsa.
Nasir baze taɓa manta alherin Ahmad da mahaifinsa ba, da sauran abokansa, amma Bulama babu abunda yayi masa, sema wadaƙa da sata daya dingayiwa Nasir a shago, ganin hankalinsa ya koma kan Auren da zeyi.
Sam Bulama beso Nasir ya auri zuƙeƙiyar balarabiyar yarinya ba, kullum suna tare, amma gaba ɗaya Nasir ya fishi sa'a a rayuwa.
Kuɗaɗen da Nasir ya samu na gudunmuwa, da wanda aka bawa Yusuf ya ɗau abunda ze ɗauka ya bawa Nasir sauran, ya sake zuba dukiyar a harkar kasuwancinsa, duk inda yaji wata harkar samu seya ɗebi kuɗi ya tafi ya jarabba, duk lokacin da yayiwa Yusuf zancen be bashi kuɗin daya ara masa, se yace ya ajiye masa ba yanzu ba, dan gani yake idan ya karɓa hakan ze iya shafar kasuwancin ƙanin nasa, yana nan zaune da matarsa lafiya, yana sonta tana son shi, Arziki se bunƙasa yake a hankali.
Ya ɗaukewa Yusuf ɗawainiyar siyan kayan Abincin gidansa, ya nuna masa baya so amma be bari ba.
Huda ta ɗau kuɗinta na sadaki da abubuwan data samo a can ƙasarsu, ta bawa Nasir tace ya haɗa, da tayi ta ajiyar kuɗin babu abunda zata yi dasu gara ya dinga juya su, ya karɓa ya haɗa yana juyawa, a hankali ya dinga janyo abokansa cikin harkar kasuwancin da yake yi, wasu suzo zuciyarsu ɗaya wasu kuma suzo da niyyar mugunta.
Allah maji roƙon bawa, katsam Nadiya matar Yusuf ta samu juna biyu bayan shafe shekaru uku da Aure, Nasir kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, danma yafi yayansa farinciki da wannan rabo, kullum zancensa Anty Nadiya idan kin haihu ni zanyi kaza.
Tun kafin bikin Nasir ta samu cikin, sam Nasir be saniba saboda yana cikin gararin soyayya, Nadiya ta girni Huda, amma suna mutunci sosai suna ƙaunar juna, Duk inda Ahmad yaji harkar kasuwanci da samu seya janyo Nasir, shikuma Nasir seya janyo Bulama, wani abun Bulama ya ɓata lamarin.
A hankali Abu ya bunƙasa, sanadiyyar Ahmad Nasir ya fara fita ƙasashen ƙetare, yana shigo da kayan ado na mata da turarruka, Ahmad ya koya masa yadda ake siyan Hannun Jari a manyan kamfanunnuka.
Nan da nan Kuɗi suka fara zaunawa Nasir, duk kasuwancin daya shiga seya samu alheri, shine nan shine can.
Ba ƙaramin daɗi Yusuf yaji ba, ganin dukda ƙarancin shekaru na Nasir amma ya fara nutsuwa, dan a lokacin befi shekaru Ashirin da uku ba yayi Auren, a wannan lokacin Auren wuri ba wani abu bane, indai yaro yana da sana'a.
Bulama ya tsani alaƙar Ahmad da Nasir sam, da yana zuwa gidan Nasir, amma fafur Huda ta nuna bata son ya dinga zuwar mata gida.
Kafin Nasir yaje Saudiyya Yayansa ya fara biyawa yaje Umara, Yusuf yace Nasir ya fara zuwa amma yaƙi yace shi yakeso ya tafi.
Ba ƙaramin daɗi da farinciki Yusuf yayi ba, dan badan a wancan lokacin ya haɗa kuɗin Auren Nasir ba, da tuni yaje, aikuwa yayi farinciki sosai.
Bayan dawowar Yusuf daga Saudiyya, lokacin Wata huɗu da Aurensu Nasir, matar Yusuf Nadiya ta haihu, Nasir kamar shi akayiwa haihuwar nan dan murna, kayan jariri kaf dana me jego shiya siya, hatta abun hakika shine yayi.
Tunda akayi haihuwar nan, Huda take zuwa gidan mejegon nan, tana addu'ar itama ubangiji Allah ya bata nata, dan tana matuƙar son yara.
Kwana bakwai da haihuwa akayi suna, yaron yaci sunan Mahaifinsu Nasir wato Umar faruk, ganin Nasir ya fara ajiye abun arziki yasa, da sunan Umar dangin Mahaifinsu suka zo suna.
Anci an sha dai dai gwargwado anyi shagalin sunan daba'a taɓa makamancinsa a unguwar nan ba, nan Sunan Daula ya sake bin Nasir sosai, Suna nunawa junansu ƙauna da sadaukarwa a tsakanin shi da ɗan uwansa.
Gaba ɗaya kusan Wuni Huda take yi a gidan Nadiya, ko taje gurin yayarta Islam taita musu raino saboda son yara da take yi.
Kasuwancin Daula fa ya faɗaɗa, abun har mamaki yake bawa mutane, babban abunda yasa mutane ke ƙara son Nasir shine hannunsa a sake yake, bashi da rowa sam, ga jan yaransu da yake akan harkar sana'a, dukda cutar da suke masa wasu lokutan.
Yusuf yana yawan yi masa faɗa akan watsi da yayi da 'yan uwan mahaifinsa, hakan be kamata ba, dan ko gaishe su baya zuwa yi.
Nadiya na fama da raino, ba damar zuwa Saudiyya, Nasir ya biyawa kansa da Huda suje suyi Umara, lokacin nan Ahmad ma zashi, ana i gobe zasu tafi, suka je gidan Yayansa Yusuf suyi musu sallama.
Suka zauna suka dinga hira kamar bazasu rabu ba, suka dinga tuna lokacin ƙuruciyarsu da gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa, da kuma wahalar maraici.
Har Huda ta dinga kuka, Yusuf yace "haba Huda, ai lokacin ya wuce ba gashi yanzu se labari ba?"
Nadiya tace "itafa Huda ko a labari bata son taji abunda ze taɓa wannan mijin nata, jinsa take kamar ranta, dan haka ku dena ma wannan labarim"
Huda ta ƙunshe kanta tana dariya, Nasir yace "Anty ya kika gani, kema fa haka kike son Yayana, laifi ne dan ta so mijin ta, wallahi my Huda kidena jin kunyar Anty Nadiya, naga ta fara damun ki"
Huda ita dai sedai tayi murmushi, Yusuf yace "ɗanuwa babu abunda zan cewa Allah se godiya, kamar yadda Antynka take fata gashi ka bunƙasa kamar wasa, Allah ya ƙara yalwata maka Arzikinka, Allah yasa ku yi ibada karɓaɓiya, ya dawo daku lafiya, sannan yakamata kayi haƙuri ka manta da abunda dangin mahaifinmu sukayi mana, komai ya wuce suma ka dinga kyautata musu "
Nasir yace " Taɓɗijan, wallahi nida su har abada, bazan manta cin zarafi da wulaƙancin da suka yi mana a rayuwa ba"
Yusuf yace 'A' a Nasir, abun da haƙuri be bayar ba, rashin sa baze bayar ba, ka maida komai ba komai ba, se kaga Allah ya daɗa buɗa maka, sannan ina gargaɗinka akan wannan yaron Bulama yake kowa? Ban yarda ka barshi akan kayanka ba, ko harkar kasuwancinka ba, dan bashi da kirki "
Nasir yace " Nikam na rasa me Bulama yayi muku kuka tsane shi, ni tausayi yake bani kaga shima marayane, kuma basu da ƙarfi "
Yusuf yace " banƙi kayi taimako ba, amma ya kamata kasan irin taimakon da zaka dingayi, Ka kiyayi yaron nan"
Nasir yace "to babbn Yaya magajin babanmu, Antyna ta kaina insha Allah baɗi in Allah ya kaimu lokacin aikin hajji, seki barmin babana kema kije ki sauke farali"
Nadiya tace "Allah ya ƙara Arziki ɗan gidan Anty"
Nasir yace "Ameen, ban cika Alƙawari ba, ke nace zan fara kaiwa amma na kai Yaya, nayi son kai ko?"
Nadiya tace "ai duk wanda ya kyautatawa Mijina ni yayiwa, nan duniya in ana son farincikina to a kyautatawa mijin marainiya"
Nasir yace "imra'ati kinji ko? Tana tsokanarki kin fiye sona, amma ji abunda take cewa"
Sukayi dariya, Nasir yace "Yayana, wai yaushe zan dawo muku da kuɗinku ne? Kasan fa yanzu Alhamdilillah, zan iya biyanku hadda riba"
Yusuf yayi dariya yace "Naji, Alhamdilillah haka nake fata, ka ci gaba da juya mana, lokacin karɓar yana nan zuwa, mesu ze karɓa"
Nasir yace "waye me su ɗin dazs karɓ?"
Yusuf yace "kai Baba suda sarki zance, kuje dare ya fara yi, kuje kuyi sallama dasu Antyn Huda, nima jibi in Allah ya kaimu nida su Nadiya zamu tafi Abuja, zamuje wani taro zan wakilci bankinmu, inaga daga nan idan na dawo zasu bani allowances ɗina na siyan gida da mota"
Nasir yace "masha Allah, Allah ya tabattar Yayana, Huda bani babana sanyin idaniyata, in sake ganinsa in sumbaci fararen kumatunsa"
Huda ta miƙa masa Faruk, ya karɓi jaririn ya rungume shi, yana sumbatar fuskarsa.
Yusuf yace "gaskiya Nasir kana ƙaunar wannan ɗan naka, Maman Faruk sekinyi dagaske karsu ƙwace mana ɗa shida matarsa"
Haka suka wanzu suna zolayar juna, suna hira tare sukaci Abincin dare kamar karsu rabu, suka shiga gurin Islam sukayi mata sallama itama, nan mu sun daɗe a can, daga ƙarshe Yusuf da Nadiya seda suka kusa rakasu gida sannan suka juya suka koma.
Washegari Alhaji Abubakar ya aiko da babbar mota, aka ɗauki su Nasir da Huda da matarsa, su Yusuf sukayi musu rakiya har airport, canma seda suka tsaya hira kaman karsu rabu, sannan suka tafi.
Satinsu uku a can sannan suka dawo gida Nigeria, sedai dawowar tasu suka tarar da abu mafi muni a tarihin rayuwarsu, wannan rana ta zamewa Huda da Nasir rana mafi muni da a tashin hankali, tashin hankalin da bazasu taɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwarsu, ranar tazo musu da wani al'amari me taɓa zuciya da girgiza ruhi, basu kaɗai ba hatta Ahmad ɗan gidan Alhaji Abubakar wannan rana tazo masa da baƙin tarihin da baze taɓa goguwa a zuciyarsa ba
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
66_67
Mummunan labari, Islam 'yar uwar Huda, ta bawa me aikinta guga, yana cikin yi, me gidan ya dawo ya aike shi, koda me gugan ya dawo se ya tattare kayan gugar yace da safe ya ƙarasa, ashe ya manta be kashe dutsen gugar ba, cikin tsautsayi cikin dare dutsen ya ɗau zafi wuta ta fara ci, babu wanda ya farga, har wutar ta shiga gidan Yusuf Yayan Nasir, gobara ce ta tashi sosai, daga gidan Alhaji Abubakar, har gidan Yusuf babu wanda aka iya ceta, gaba ɗaya.
tsautsayin wutar nan ya ritsa dasu, suka ƙone ƙurmus a cikin wannan gobarar, 'yan unguwar sun kaɗu sun shiga cikin tashin hankali da wannan ifyila'i ya faru, se yayyafa musu ruwa akayi aka rufesu dan babu ta inda za' a iya sallatarsu.
Nasir ya kaɗu da samun wannan mummunan tashin hankali, dan bashi ba hatta Huda se kwasarsu akayi zuwa Asibiti, dan babu wanda yake cikin hayyacinsa.
Dukda Ahmad ma ya kaɗu ya shiga cikin tashin hankali, da labarin daya tarar na rasuwar mahaifinsa, dama shi mahaifiyarsa itace Uwargidan Alhaji Abubakar, kuma ta rasu yana da wasu matan amma ba a wannan gidan suke ba, da ya Auro Islam ne ya sakata a wannan gidan, ya dawo da Ahmad gidan, shima ya kaɗu ya shiga cikin tashin hankali, shine babba a gurin mahaifinsa gashi yana ji dashi, dukda ya sha wahalar matan uba, amma Auren Islam yasa ya samu sassauci, dan ita sam babu ruwan ta, dukda wannan masifar tashin hankali da yake ciki, amma ya tausayawa Nasir da Huda, dan duk wanda wannan mutuwar zata taɓa a bayansu yake.
Seda Nasir ya kwana biyar besan inda kansa yake ba, numfashi ma baya iyayi seda taimakon Oxygen, ita kuwa Huda tunda ta farka bata magana, sedai hawaye yaita bin fuskarta, ko Abinci bata iyaci balle magana, fuskarta ta kumbura tai jawur, ga rashin 'yar uwatta, ga ɗan uwan mijinta da matarsa, ga babu mijin' yar uwatta, ga mijinta a kwance shima rai a hannun Allah.
Se a kwana na Shida sannan Nasir ya farfaɗo, ya farfaɗo da kalmar la'ilahaillalah Muhammadur rasulillah salallahu alaihi wassalam "
Likitoci suka rufu akansa, suna monitoring ɗin bugun zuciyarsa, salati kawai yake yana faɗin " Yayana, ɗan uwana, shi kaɗai ne ya ragemin, Anty Nadiya da ɗansu duk babu, innalillahi wa inna ialaihi raji'un "
Wani liktane yace " haba ɗan uwa kamar ba musulmi ba, kayi haƙuri kayi tawwakali, idan kaji ƙaddarar wani seka rufe baki, kayi haƙuri mu samu mu ceci rayuwar ka, an san mutuwa da ciwo amma kayi haƙuri "
Nasir yace " likita, ɗan uwana ya mutu, da zan tafi umara ya muka dinga hira, ashe wasiyya ce, nayi rashi likita, banji rasuwar iyayena kamar yadda naji mutuwar Yusuf da Nadiya ba, har ɗan namu ma na rasa, innalillahi wa inna ialaihi raji'un wayyo Allah yayana"
Yai maganar yana fashewa da kuka, kamar ƙaramin yaro.
Likitan ya dafa kafaɗarsa yace "Allah yasan da kai, kayi haƙuri, Allah shike da rayuwar kowane bawa, ka kwantar da hankalinka, matarka mafa tana can munata ƙoƙari akanta, karta rasa hankalin ta, idan taganka a mawiyacin hali to jikinta ze rikice"
Jinina kai Nasir ya shigayi yana "Allah sarki Hudana, Huda munyi rashi, mun rasa 'yan uwa dagani harke, Allah ka zama gatan mu, Allah kayiwa bayinka Rahama"
Likitan ya amsa da Ameen, yana cigaba da kwantarwa da Nasir hankali.
Nasir yace "likita, ku kaini inga matata"
Likitan yace "A' a ka bari za'a kawo ta, har nan inda kake bama son ka dinga wahalar da jikinka"
A wannan kwanaki biyar ɗin Huda tayi ɓari, amma saboda halin da suke ciki ba'a sanar musu ba, dukda alhini da Ahmad ke ciki, amma a haka yake ta sintiri a Asibitin, wata ƙawar mahaifiyar su Nasir ce take sintirin jinyar Huda, yayin da Ahmad ke kula da Nasir, 'yan unguwa nata zuwa yi musu jaje da kuma duba su.
Duk Wanda yaga halin da suke ciki, sya tausaya musu, gaba ɗaya sun rame mussman Huda abun yafi mata yawa, yanzu ta rasa kowa da komai nata, se Allah da kuma mijinta Nasir, shima gashi a kwance se yadda Allah yayi dashi, ga ɗan uwan mahaifinsu ya sallamasu, dan bezo Nigeria gurin ta'aziyya ba, kuma labarin gobarar ya iskeshi, yace suje can su ƙarata ba abunda yayi masa zafi.
Nasir ya takura akan yana son ganin Huda, a haka aka turo Huda a wheel chair tazo duba Nasir.
Tana ganinsa a zaune ta ɗanji sanyi a ranta, ganin nasa jikin da sauƙi, ana ƙarasawa da ita suka rungume juna suna kuka, Kuka me tsuma zuciya, a hankali Huda tace "zaujee, mun rasasu gaba ɗaya babu wanda yayi rai a cikin su '
Nasir yace " Na sani Huda, babu yadda muka iya se mu rungumi ƙaddararmu, sukuma mu cigaba da yi musu Addu'a "
Nan suka dinga kuka, aka rasa me rarrashin wani, Ahmad ne ya shigo ya tarar dasu a wannan yanayi, suna ta kuka.
Ahmad yaja kujera ya zauna, ya dubi su Nasir cike da rauni da karaya shima ya fara magana yace " Nasir, dama itafa duniya munzone tamkar matafiya, dole wataran mu barta, sannan dukkan ɗan Adam dole ne Allah ya jarrabe shi, Allah baya barin mumini babu jarrabawa, dan haka nida ku mu rungumi ƙaddrara mu, mu yi tawwakali mu barwa Allah komai, shi ze bamu mafita, su kuma da muka rasa muyi musu Addu'a "
Ahmad ya ƙarasa maganar, ƙwalla na zuba daga idanunsa, amma ya cigaba da tausarsu yanayi musu Nasiha.
Seda suka shafe sati biyu a Asibiti, saboda jikin Nasir, dan zuciyarsa ta taɓu saboda damuwa, haka likitoci suka gindaya masa sharuɗa da magunguna, sannan aka sanar dashi ɓarin da Huda tayi, sam da gashi har ita basu san da cikin ba, dan koda zasu tafi umara da aka yi gwaji babu, yanzu kuma an tabattar masa da cikin watansa uku ma, Ba laifi Bulama ma yayi zaryar Asibitin nan sosai, saboda Nasir, dan dukda rashin jituwar da yake da Yayan Nasir ya tausaya masa wannan rashin da suka yi lokaci ɗaya, shima ya dinga rarrashin Nasir, akan ya kwantar da hankalinsa ya rungumi ƙaddara.
A haka aka sallamesu suka koma gida, sedai babu me iya rarrashin wani a cikinsu, idan abun ya taɓosu se su wuni kuka ita dashi, dama ga Nasir da raguwar zuciya, su wuni cikin damuwa babu me ko iya cin Abincin, saboda dukkaninsu mutuwar tana dukan su.
Kusan watanni Uku, da mutuwar har ɗan gara Nasir ya fara jarumta yanzu, amma Huda kam babu wannan batun, musamman gari ya waye da ta saba ta tafi gidan Nadiya, ko Yayarta Islam taje taita musu rainon 'ya' ya kasancewar tana matuƙar som yara, amma lokaci ɗaya Allah ya karɓe su gaba ɗaya.
Yanzu Nasir na iya zaman rarrashin ta, yaita bata baki yana tausarata, yace "Huda, ni dake Allah ne gatanmu, shiya haliccemu gaba ɗaya, kuma yafi mu sonsu daya karɓesu, ni dake dole muyi kukan maraici, nasan zakiyi tunanin ya rayuwarki zata kasance a nan gaba? Huda a duniya bayan iyayena ina jin maganar Yayana fiye da tunaninki, kuma nima nasam abunda ya dace, nasan gwagwarmayar da akayi kafin in Aureki, dan haka ko sau ɗaya karki sawa zuciyarki Nasir ze juya miki baya, nida ke yanzu gaba ɗaya muna cikin maraici gaba da baya, dan haka mu rungumi ƙaddararmu mu rayu tare, mu jure duk wani ƙalubale mu kasance a tare har zuwa namu wa'adin, in dai ta ɓangare nane, Insha Allah bazaki zubda hawaye ba"
Huda tayi ajiyar zuciya tace "Zaujee, nima nasan abune mawuyaci in fuskanci ƙalubale ko juya baya daga gareka, ina da kyakkyawan yaƙini akanka, amma dole in koka, munyi rashin da ba zamu mayar da wannan gurbin ba, kamar yadda ka faɗa insha Allah, duk tsanani zan jure duk wata ƙaddara in rayu da kai, bani da kowa se Allah sekuma kai"
Nasir yace "Insha Allah, bazan baki kunya ba Huda, nasan halaccin da kikamin a rayuwa, dan haka insha Allah zan kasance dake, zan kasance me baki kariya, kuma zan zame miki mijin marainiya insha Allah"
Haka su dinga kwantarwa da junansu hankali, suna bawa junansu haƙuri.
Amma duk da haka, Huda ta kasa sakin jiki ta haƙura gaba ɗaya, ƙarshe seda Nasir ya bar unguwar gaba ɗaya ko hankalinta ya kwanta, dan ko fita tayi tazo wucewa ta layin gidajen ƙarshenta idan ta fara kuka hadda suma.
A haka Nasir ya daddafa ya cigaba da kasuwancinsa, kuɗi ko ta ina shigomasa suke, a haka har Ahmad yayi Aure, Bulama ma ya tattago maganar Aure, kusan Nasir ne yayiwa Bulama komai na Auren, dan har gidan daze zauna shiya bashi.
Shikuma Nasir likkafa se ƙara cigaba take, gaba ɗaya ya zama busy man, yawo ƙasa ƙasa kasuwanci kala kala, duk ba wanda ba yayi.
Shine saida kayan sarƙoƙi, motoci, kayan masarufi, ga shaguna da yake dasu a kasuwa, na siye da siyarwa, hannun jari dayake siya a manyan kamfanunnuka.
Nan da nan ya zama kamar bashi ba, gashi dai matashi amma ya tara kuɗi.
Nasir ya ɗauki Huda sukaje ƙasarsu can Maroco, amma baffanta yayi musu wulaƙanci, Kasancewar besan Nasir ya fara arziki ba, yayi musu fata fata yace yadda aka cinye 'yar uwatta itama haka za' a cinyeta, haka suka dawo Nigeria da ɓacin rai.
Ganin Huda ta kasa samun nutsuwa har yanzu, ga tarin damuwa data sa a ranta, hakan yasa ya ɗauketa ya tafi da ita ƙasashen waje, can Dubai inda yafi harkokinsa, ya koma makaranta a can, sedai tun bayan ɓarin nan Huda bata sake samun ciki ba, kullum cikin addu'a take ubangiji Allah ya bata rabo itama.
Ya zamana Huda tana Dubai, kowani abun zezo yi Nigeria, ita tana can duk dan ya samu ta rage damuwa.
Seda suka shekara takwas da Aure bata sake yin ko ɓari ba, abun duniya duk ya addabeta, shikam ko a jikinsa, dukda yana addu'a sosai a ransa a bun yana damunsa, amma sam baya nuna mata, ta takura masa sukaje Asibiti akayi musu gwaje gwaje, amma akace lafiyarsu ƙalau.
Se a shekara ta tara Allah yasa Huda ta samu ciki, aikuwa Nasir yayi murna babu adadi, nan suka shiga rainon cikin nan da tattalinsa, gefe guda kuma ya zama matashin ɗan kasuwa na farko, wanda sunansa yake zagawa a cikin Nigeria, a hankali yasan manyan 'yan siyasa da attajirai, saboda har harkar kwangila yake yi, nan dangin mahifinsa suka shiga ƙoƙarin nuna ai ɗansu ne, amma fafur yaƙi yadda su raɓe shi, a cikin dangi can suka haɗu da wani Musa, sun ɗan haɗa alaƙa amma ba irin ta sosai ɗin nan ba, ɗan unguwarsu ne dai, ya dinga shisshigewa Nasir, tun Nasir na basar dashi, har ya fara sakewa dashi.
Musa ya nuna sha'awarsa ga harkar siyasa, Nasir ya haɗashi da manyan 'yan siyasa, ya goyi bayansa akan harkar siyasar, nan da nan mutane suka karɓi Musa, a dalilin Nasir, kasancewar Nasir mutum ne na mutane, mutane na ƙaunarshi saboda hannunsa a sake yake, ga shaharar da yayi ganin Nasir ne ya talatta Musa da kansa, hakan yasa mutane suka karɓe shi hannu biyu biyu.
Bulama kam basa jituwa da Ahmad, dan haka ya dinga shiga yana fita danya raba Ahmad da Daula, gashi kusan duk wani harkar kasuwanci Ahmad ne yake jan Daula, dan tun yana ƙarami Mahaifinsa ɗan kasuwane, dan haka yasan sirrin kasuwanci sosai, Ahmad yana yawan ankarar da Daula akan ya kiyayi Bulama, amma se Nasir yace ai Bulama ya zamani na zama shi, rabuwarmu abune me wahalar gaske.
Bulama ya kunno musu wata rigima akan harkar kasuwancin da suke, ya shiga ya fita seda yasa Daula da Ahmad sukayi baran baran suka rabu, ya zamana shine ma gaban Nasir.
Watan cikin Huda tara cif ta haifo sankaceciyar jariryarta mace, Daula ya rasa inda zesa ransa dan murna, sedai haihuwar ta fama musu mutuwar mutanen da suka taka mahimmiyar rawa a rayuwar su, yau gashi kamar yadda Nadiya ke fata, Nasir ya amsa sunan Daula, ga rabo sun samu, amma babu ɗaya a mutanen nan daze taya su farinciki.
Haihuwar jaririyar nan tasa sun zubda hawaye, har damuwa taso ta maye gurbin farincikin da suke ciki, wani abun mamaki jaririyar nan ta ɗakko kamanin Islam Yayar Huda, dukda Huda da Islam suna kama sosai, amma kamanin Jaririyar nan sunfi karkata ga Islam.
Huda tana zaune rungume da jaririyar nan tace "Duk wanda yake ƙaunata, ya ƙaunaci jaririyar nan, duk wanda yaƙi jaririyar nan to tabbas ni yaƙi, a duniya yanzu banda Allah, se mijina da wannan 'yar, su kaɗai Allah ya mallakamin, inajin son' yar nan a raina, kamar yadda nake son mahaifinta, Allah yasa ta zamo me jinƙi da tausayi kamar mahaifinta "
Nasir ya rungume Huda da jaririyarsu yace" tabbas nima duk me sona, to ya ƙaunaci Huda da jaririyar nan, Allah yasa mun ƙara yawa, ya azurtamu ta samun ƙaruwa, yanzu wani suna kike ganin zamu saka mata? Ko mu mayaf da Sunan Anty Islam '
Girgiza masa kai Huda tayi tace "A' a idan ka mayar min da sunan Islam, bazan iya tsawatar mata ba, kamaninta ɗaya da Islam zan dinga ganin kamad itace, haka idan ka samun sunan Anty Nadiya, nan ma bazan iya tsawatar mata ba, saboda ina girmama Anty Nadiya, tambarin mutjwarsu baze taɓa barin zuciya ta ba, gara mu sa kamata wani sunan daban, mu sama ta Widad, wato soyayya da Abota, na zaɓi sunan ne saboda yana da kyakkyawar ma'ana, Ina sonta kuma itace babbar ƙawata"
Nasir yayi murmushi yace "muna sonta dai'
Haka akayi gagarumin shagalin suna, a Nigeria, nan dangin mahaifin su Nasir suka dinga rige rigen zuwa, saboda Arziki ya samu, Bulama ya taya Nasir murnar haihuwar Widad sosai, duk da saɓanin da suka samu da Ahmad, seda yazo yayiwa Nasir barka, ya bawa Widad kyaututtuka, Bulama ne ya saiwa Widad Haikika, yayi Ƙaton Akwati da kayan jarirai, haka nan yaji yana ƙaunar yarinyar, sanadin abunda yayiwa Widad, yasa mafi yawa na ƙiyayyar da Huda ke masa ta ragu, dan taji haushin rabuwar Nasir da Ahmad, abunka da abun masu Arziki da neman gurin zama, nan masu kuɗi suka dinga bajinta suna gwangwaje jaririyar nan da manyan kyautuka, dan kawai su birge Daula, ko ace wane ya bada kaza.
Kafin su koma Dubai, kusan kullum se Bulama da matarsa sunzo, dan ya ɗauki Widad, ko kuka take ya dinga rarrashinta kenan, Yana matuƙar son yarinyar.
Kwanansu Arba'in Nasir ya ɗauke Huda suka koma, Bulama ma albarkacin Nasir ya fara kama ƙasa, nan da nan ya shiga aure Auren mata, ya auri wannan ya saki, ya Auri waccan ya kora, tun Nasir yana masa faɗa harya ƙyaleshi.
Kadarorin da Aka tarawa Widad na suna, Daula ya haɗa ya siyar bisa shawarar Huda, suka haɗa kuɗi suka buɗe kamfanin sarrafa ƙarafa, manyan mutane har daga ƙasashen ƙetare suka zuba hannayen jarinsu cikin kasuwancin, nan fa Sunan Daula ya ƙara shahara, ya zama babban attajiri, me sana'a goma maganin me gasa.
Widad ta fara wayo a hankali tana girma, ta isa shiga makaranta se Daula ya koma England, saboda mafi akasari yanzu yafi ta'amalli dasu akan harkar kasuwancin motoci, aka saka Widad a makaranta, Huda kuma ta dage da koyar da ita na Addini, dukda akwai wani ustaz dayake koyar da yaran musulmai a ƙasar.
Sedai gaba ɗaya rayuwar Widad da girmanta, ya sha ban ban dana sauran yara, sun raba gari da duk wasu ɗabi'u na yara, duk inda yaro yake an sanshi da son kallon fina finan cartoon, kona dabbobi amma banda Widad, idan za tayi kallon film, daga wrestling, se film wanda ake yaƙe yaƙe ko harbe harben bindiga, kokuma fina finan horo na ban tsoro, kona harkar fashi, suke birgeta, sam bata kallon wani film ɗin Indiya ko soyayya da tausayi, basa gabanta, Huda taita fada tana mita, amma Nasir se yace ta ƙyaleta, nan gaba zata dena.
Huda taita mita tace "yarinya kamar ba mutum ba, ke duk abunda mutane suke yi ko suke so, ke kunyi hannun riga dashi?"
Widad tana da miskilanci, bata magana seta ga dama, idan har kaji ta zage tana surutu, kodai da mahaifintane ko kuma Bulama ne ya kawo musu ziyara, bata wasa da 'yan uwanta yara, sedai taita gwada tsalle tsalle, da harbin bindiga da take gani a film, shine wasanta sosai abun yake damun Huda, Nasir yace tayi haƙuri irin tata ƙuruciyar kenan.
Widad tafi sakewa Da Babanta akan Amminta wato Huda, Huda tana da zafi sosai akan tarbiyyar Widad, yayinda Babanta duk abunda takeso shi yake so, amma duk da haka akwai soyayya da shaƙuwa a tsakanin Widad da Amminta, babban abunda yake haɗasu shine rashin son mutanen Widad da kuma wannan kallon da take yi.
Widad ko ƙawayen kirki bata da su, saboda rashin son maganar ta, sedai tana ji da magenta, tana nuna musu soyayya, sune abokan wasanta, dasu take hirarta.
Tun bayan haihuwar Widad me abun mamaki, Huda bata sake samun haihuwa ba, tana ta Addu'a tana fatan ubangiji Allah yasa ta kuma samun rabo.
A wannan lokacin shaharar Daula ta wuce iya Nigeria, da taimakon Allah Daula ya goyawa Musa baya da maƙudan kuɗaɗe, ya tsaya takara a wata jam'iyar siyayasa a wannan lokacin, a dalilin son da mutane suke wa Nasir Daula suka zaɓi Musa.
Tunda Musa yaci zaɓe nan ya ɓarke da bushasha, bashi da aiki se gantalin ƙasashen duniya, ya manta da al'ummar da suka zaɓeshi, da irin Alƙwarirukan daya ɗaukarwa mutane, Ya kai 'yarsa Nurat makaranta a ƙasar waje, inda Widad take karatu, Nurat tana matuƙar son Widad, Kasancewar Widad ce bahaushiya' yar uwatta a makarantar, duk sauran yaran turawa ne, tun Widad bata damuwa da Nurat harta fara kulata, a hankali suka fara sabawa suna shaƙuwa da juna.
Widad sam tun haihuwarta, rayuwarta tafi a ƙasar waje, idan sunzo Nigeria to hutu sukazo ko kuma ziyara, gashi Huda ba wani Hausa takeji ba, tama jin Husa amma ba sosai ba, dan haka wasu abubuwan duk Widad bata sansu ba.
Nasir ya haɗa kai da wasu 'yan china, suka buɗe wata katafariyar ma' aikatar harkar kwangila, na gine ginen tituna, da shigo da kayan gini, ya jawo matasa sosai cikin harkar, bayan wancan kamfanin ƙarafa da yake dasu, da sauran manyan kadarorinsa na mamaki, dan har rijiyar mai Daula ya mallaka, kullum Arziƙinsa gaba yake, baya baya, gashi ba wani babba ba a a wannan lokacin, amma ya tara Arziki da shahara.
Shekarun Widad bakwai a duniya, har Huda sun fidda ran samun wani ɗan, kawai ta tashi da matsanancin ciwon ciki, tayi zaton ɓacin cikine kawai, amma ta wuni a kwance, hakan yasa Daula ya ɗauketa zuwa Asibiti, a nan aka tabattar masa da tama ɗauke da juna biyu.
Daula ya rasa inda zesa kansa dan farinciki, sunyi murna sosai da samun wannan cikin, nan ya ƙara ririta Huda fiye da yadda yake yi a baya.
Da tayi motsi se yace "me unborn ɗina yake sone, har Widad ta fara kishi tace "Daddy, wai yanzu kafin son unborn ɗin nan ne dani?"
"wane ni, ga gimbiyata ince nafison wani dake, ai you are my forever Queen, babu wanda ze rusamin fadarki, kiyi yadda kike so Gimbiyar Daula'
Ire iren wannan kirarin, da soyayyar da mahaifinta ke mata suke fasa mata kai, Widad bata taɓa kukan babu ba, bata san ta nemi abu ta rasa shi ba, haka ta taso cikin zunzurutun jin daɗi da dukiya ta ban mamaki.
Tun Widad tana ƙarama take bada kyauta, idan Daula ya ga dama, se yace "Ran Gimbiyata ya daɗe, ga wane me kike so a bashi?"
Duk abunda ta faɗa ta zauna, se an bawa mutum, Huda taita mita tama ya fiye sangarta Widad, shi kuma ya kance idan banyiwa Widad abunda takeso ba se yaushe? Idan na mutu bata mori dukiyar mahaifinta bafa?"
Ya sai kadarori da sunayen Widad, kadarorin daya siya da sunanta basu da adadi, Widad komai yi mata akeyi, suna da nanny.
A hankali Huda taga idan ta biyewa Daula, to Widad zata tashi a sangarce, dan haka take ɗan koya mata waus abubuwan, kamar gyaran ɗakin data kwanta, ɗauke kwanon Abinci, da shara daidai wadda zata iya.
Katsam bayan tenure Musa ta farko, yana ƙoƙarin ya koma, labarin irin almundahanar da Musa yayi ta iske Daula, abun yayi masa ciwo, ya goyawa macuci baya ya jagoranci al'umma, amma ƙarshe ya zalunce su, Daula da kansa ya kai Musa EFCC yace su tuhume shi, a bincike shi ya fito da haƙƙin mutane.
Abun ya bawa mutane mamaki, ganin shiya kawo Musa Siyasa, amma da kansa ya kaishi gurin hukuma, sannan yace bashi bashi, kuma duk hukuncin daya dace ayi masa.
Gaba ɗaya siyasar Musa, da mutuncinsa ya zube a idon mutane, dama farin jinin saboda Daula ne, mutane suka juya masa baya.
Ƙarshe da kyar ya sha a hannun EFCC, dan seda aka kaishi prison a ƙasƙance, aka ƙwace wasu daga kadarorin da ya mallaka, a wannan lokacin abubuwa basu taɓarɓare kamar yanzu ba, da ƙyara wasu daga 'yan siyasa suka dinga shiga suna fita, seda Musa yayi watanni shida a prison, sannan aka sako shi da kyar, shima se da aka ƙwace masa passport, dan gwamnatin lokacin ba tasu bace.
Wannan dalilin yasa Musa ƙulattar Daula, ya manta duk alkhairin da Daula yayi masa, ya manta yadda ya tsamoshi daga ƙangin talauci da shaye2, yayi aniyar rama abunda Daula yayi masa kota halin ƙaƙa, yayi Alƙawarin tozarta shi da wulaƙa ta shi, kamar yadda yayi masa, yayi alwashin ɗanɗanawa Daula baƙin ciki mafi muni a rayuwarsa, tunda ya ɓata masa suma ya lalata masa siyasarsa.....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: .LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
68_69
Cikin Huda ya ci gaba da girma, yayin da gefe ɗaya Daula ya fara tara maƙiya da mahassada, danshi duk abunda zeyi be yadda da cuta ko ha'inci ba, komai nasa tsakani da Allah yake yinsa, ga gefe guda mutanen daya ƙwacewa kasuwar wasu abubuwan, suma suka sako shi gaba suna jin haushinsa.
Wata gidan Talabijin yayi hira da Daula, akan yadda akayi ya fara kasuwanci, nasarorin daya samu da kuma ƙalubale, duk ya dinga bada amsa, gashi duk hirar da za'ayi dashi se yayi zancen Yayansa Yusuf, se yayi musu addu'a, duk inda me Suna Yusuf yake Nasir kamar ze duƙa masa saboda girmamawa, komai ƙanƙantar Yaro indai yana da wannan sunan, to tabbas yana da ƙima a idon Nasir.
Babban abunda ya daɗa ja masa baƙin jini shine, yadda yakewa al'umma hidima, yake facaka da dukiyarsa gurin hidimtawa al'umma da addini, wanda sauran abikan kasuwancinsa basa yi, hakan yasa ya ƙara samun masoya ta kowane fanni.
A cikin hirar da'ake dashine ya bayyanawa 'yan jarida cewar, shifa ainihin kuɗin daya fara kasuwanci dasu bashi aka bashi, kuma be biya bashin ba, ya sanar dasu cewa wanda ya bashi bashin ya gaya masa me kuɗin yana nam zuwa ya karɓi wannan kuɗi, dan haka gundarin dukiyar da yake juyawa yana samun riba akwai me ita, kuma duk sanda lokaci yayi indai me dukiyar ya bayyana to tabbas shi keda kaso bakwai cikin goma na dukiyar daya mallaka, ya ƙara da cewa a hirar nan da suke, tuni ya ware wannan dukiyar guri guda, ko bayan ransa duk wanda yasa hannu akan wasiyyar daya bari da takaddun dukiyar daya ware, to tabbas wannan dukiya tasace, ko waye yasa hannu akai tasa ce "
Wannan hira da Daula yayi ba ƙaramin cecekuce ta janyo ba a cikin al'umma, wasu suna jinjinawa amanarsa, wasu suna ganin wautarsa suna inama zasuga inda tajaddun suke su saka hannu su karɓe kuɗaɗen, wanda suke da hannun jari a kamfanunnukansa suka shiga zullumi, akwai dukiyarsu a cikin kuɗaɗen Daula, kuma muddin ya janye daga kasuwancin to tabbas zasu talauce, dan haka suka shiga tunanin nemawa kansu mafita.
Katsam akayiwa Huda scanning, aka tabattaf da cewa tana ɗauke da ɗa namijine a cikin ta, ana gayawa Daula ya zube yayi sujjadar godiya ga Allah, bakinsa yaƙi rufuwa, farincikinsa yakasa ɓuya.
Sunyi murna sosai da wannan kyauta da Allah yayi musu, Kasancewar Daula ya daɗe yana kuma neman haihuwa yasa shi, ya shiga gayawa abokansa ai Madam ta samu rabo, kuma anyi scanning ance zata haifi namiji, zatonsa duk masuyi masa dariyar nan masoyansa ne, zasu taya shi farinciki, ashe abunda be sani ba ta ciki na cikine kawai, dan gaba ɗaya ba ƙaunarsa suke ba, dukda da yawa su, Daula shine silar Arziƙinsu.
Watarana suna zaune suna hira da abokansa, suke bugun cikinsa Haruna yace "Yanzu kai Daula, gashi ga abunda kace akan cewa akwai me kaso bakwai na dukiyarka, yanzu idan ba'a samu wanda yasa hannun bafa? Sannan meyasa me dukiyar baze zo ya karɓa ba"
Daula yace "me kuɗin, yayana ne da matarsa da Allah yayi musu rasuwa, kuma shi ya gayamin akwai wanda ze karɓi wannan kuɗin, dan haka nayi a rubuce ko bayan raina idan mesu bezoba, a rabawa al'umma su, ko kuma a gina abunda al'umma zasu amfana"
Haruna yace "duk wannan uwar dukiyar, kace a rabar?"
Nasir yace "eh mana, haka shine yakamata ai, har wasiyya nayi yadda na kasafta dukiyar"
"to yanzu a ina suke, balle mesu ɗin yasa hannu ya karɓa?"
Daula yace "idan har me dukiyar nan yazo, no matter how hard seya karɓi abarsa, babu wanda yasan inda suke, se Allah seni, nayi bayanin komai a video wasiyyar dana bari, na danƙashi a hannun 'yata Widad"
Munir yace "Widad kuma? Wannan jaririyar yarinyar?"
Daula yai murmushi yace "wannan Yarinyar, yadda kanta yake lissafi naka bayayi, a hakan tayi min alƙawarin zata adana wasiyyata kamar yadda zata adana Ranta daza ta ganshi"
Haka sukayi ta bugun cikin Daula, wani abun ya gaya musu, wani abun ya waske shi duk a ganinsa an zama ɗaya, har yake labarta musu ai matarsa namiji zata haifa.
Cikin Huda yana da watanni bakwai, ta dage tace ita seta koma Nigeria a can take son ta haihu, Daula ya kaɗa ya raya tace ita Nigeria takeson ta koma, yanzu zaman nan ya isheta.
Haka Daula ya tattara ya dawo Nigeria, dama akwai katafaren gidansa me girman gaske, inda suke sauka idan sunzo, akwai ma'aikata a gidan saboda girmansa, dukda babu kowa a gidan akwai megadin gidan Bala, Sojane shiyake kula da shuke shuke da sauran al'amauran gidan idan basa nan, gidane har gida katafaren gaske me matuƙar girma da yalwa.
Suka koma Nigeria suka sauka a wannan gidan, lokacin da cikin Huda ya shiga watanni takwas tafiya ta kama Nasir ta gaggawa, Huda haka nan taji bata son ya tafi, ta dinga masa Shagwaɓa harda kuka ita karya tafi.
Widad ganin Mamanta na kuka, hadda shagwaɓa yasa tace "da nice da yanzu Ammi kin koreni kince na fiye takura, shine kikewa Daddy kuka ko? Daddy ka ƙyale Ammi shagwaɓabiya"
Nasir yayi murmushi yace "my princess gayamata dai, kalli tana kuka kaman baby"
Widad suka haɗu ita da Babanta suka dinga tsokanar Huda suna dariya, akwai kyakkyawar fahimta da ƙaunar juna a tsakaninsu, haka yaita rarrashin Huda, harta haƙura ta ƙyaleshi ya tafi, ita dama tsoromta bata son ya tafi daga ita se Widad a gida ga tsohon ciki.
Kwana biyu da tafiyar Daula, cikin dare sun tsaka da bacci, Widad ta tashi ta shiga kiran "Ammi, Ammi ki tashi"
Cikin bacci Ammin Widad ta farka tace "lovely lafiya kuwa?"
"Ammi yunwa nakeji"
"Widad yunwa cikin daren nan kuma?"
Widad ta jinjina mata kai, Huda tace "Widad kin fiye rigima, ko tausayin halin da nake ciki bakya yi, tashi muje in haɗa miki"
Haka ta kama hannun Widad zuwa kitchen, ta haɗa mata Frisco ta samata madara ta bata, Widad ta zauna tana sha, yayin da Huda keta hamma saboda bacci.
Widad ta kalli Amminta tace "Ammina kije ki kwanta, idan na gama nima zanzo in kwanta"
Huda tace "kin tabatta bazaki min fitina ba?"
Widad tace "yes Ammi, i promise you i won't do anything bad"
Huda tace "Yawwa my lovely friend, barakallahu fik"
. Ta sunkuyo ta sumbaci goshin Widad, itama ta sumbaci goshin Amminta, har taje bakin ƙofar kitchen ɗin, Huda ta juyo ta kalli Widad ta ɗaga mata hannu, itama ta ɗaga mata, Huda tace "Babyna, ki zama me riƙon Alƙawari, sannan karki zama me manta alkhairi"
Widad tayi murmushi, ta jinjinawa Amminta kai.
Tafiyar Ammin ɗaki ba daɗewa, Widad taji kamar ana taɓa gate ɗin gidansu, ga Ƙaton karensu yanata zabga haushi, a zatonta ko Daddynta ne ya dawo a daren nan, dan haka ta taka kujera, ta hau kan drower ɗin kitchen, ta leƙa Window, da yake gurin a saman bene ne, hakan ya bata damar ganin abunda ke faruwa a ƙasa harabar gidan.
Ƙaton police dog ɗin nasu yake ta haushi yana zagaye, a harabar gidan, Bala soja ya kama karen ya maida shi ɗakinsa ya rufe, sannan yaje ya zare sakatar dake gate ɗin.
Wasu mutane ne suka shigo cikin gidan, sun kai su biyar fuskarsu ɗauke da mask baƙi, baka gane fuskokin su, ga manyan bindugu a hannunsu.
Tunani Widad tayi, a irin fina finan da take kallo, idan akaga mutane da irin wannan shigar musamman cikin dare, to they are dangerous, tana nan akan drower taga Bala yayi musu jagora har ƙofar da zata sadaka da cikin gidan.
Ya buɗe musu ƙofar suka shiga, Widad ta sakko daga kan drower a hankali, ta leƙa ta ɗaya window, tana gani suka shigo babban falon ƙasan benen, suka shiga haurowa saman benen, komawa tayi ta ɓuya suka buɗe ƙofar ɗakin da Huda take ciki suka shiga.
Suna shiga Widad ta fito daga kitchen ɗin, tana tafiya a hankali tazo ta window dake corridor ta tsaya ta Leƙa window a hankali, cikin sanɗa take komai.
Tana gani ɗaya ya kunna fitila, haske ya gauraye ɗakin, Huda ta buɗe ido tana salati, nan da nan ɗayan ya janyo pillow ya danneta, ta dinga mutsu mutsu tana fizge fizge, Kasancewar ƙaramar rigar bacci ce a jikinta, kana iya ganin yadda cikin dake jikinta ya dunƙule guri ɗaya.
Widad tana tsaye tana kallonsu, ta toshe bakinta da hannunta, tana ta gumi jikinta yana tsuma, ƙafafunta se rawa suke, tun Huda na iya mutsu mutsu da ƙoƙarin ƙwacewa, ɗaya ya zaga ya hau kan gadon ya riƙe hannayenta, tun tana motsa ƙafafunta, har rai yayi halinsa ta dena motsi.
Widad na zuwa nan kawai ta rirriƙe Yusuf ta fashe da wani irin kuka me matuƙar ban tausayi, ba Widad ba shi kansa Yusuf seda jikinsa yai sanyi, labarin ya ratsashi sosai, tun daga rayuwar iyayenta zuwa kanta a cikin ƙaddara take, rungumeta Yusuf yayi yana shafa bayanta da sigar rarrashi, amma ya kasa magana sam se Ajiyar zuciya.
Ganin Widad bata da niyyar sassauta kukan da take yasa Yusuf ya fara magana, cike da rauni da tausayawa yace "Am very sorry dear, ubangiji Allah jiƙansu gaba ɗaya, take heart Widad, Allah ya jiƙan Ammi"
"Yoseef, my Mum was killed before my eyes, a gaban idona aka kashemin ita, bayan an san bani da gata se Allah se ita da Daddy na, amma without fear, she was killed mercilessly, ga tsohon ciki, how can I forget this in my life, how?"
Jikinta har tsuma yake saboda kukan da take, ga wani irin numfashi da take jerawa, Yusuf yace " tabbas an cutar da ahlinku, cutarwa mafi muni Widad, amma kiyi haƙuri ki miƙa lamarinki ga Allah, dama Allah yayi a lokacin mahaifiyarki zata rasu, bawa baya wuce lokacinsa"
Widad tace "na sani, da Ammi mutuwar Allah tayi, bazan cigaba da damuwa tsawon wannan lokacin ba, nasan lokacinta ne yayi, amma aka kasheta da tsohon ciki laifin meta yi? Me tayi musu zasu kashemin ita Yoseef?" ta maganar muryarta na sarƙewa.
Seda Yusuf ya zubda hawayen tausayin Widad, ya shiga share mata hawayenta yana, " kiyi haƙuri, mucigaba da yi musu Addu'a, kidena wannan kukan, Allah yayi mata rahama, take heart "
Shaƙuwa Widad ta dingayi, numfashinta yana sama yana ƙasa, gigicewa Yusuf yayi ya shiga kiran sunanta, tana jinsa amma bata iya magana hannunsa ya ɗora akan ƙirjinta ya shiga karanta mata duk abunda yazo bakinsa, na ayoyin alƙur'ani.
A hankali ta dinga sauke ajiyar zuciya, ta dena shaƙuwar, Yusuf yace mata sannu, jinjina masa kai kawai tayi.
Yace "dare yayi sosai yanzu, ma cigaba wani lokacin, ki kwanta ki huta"
Ta jinjina masa kai, ya gyara mata pillow ya kwantar da ita ze miƙe, ta riƙe hannunsa, ya kalleta yace "ya dai?"
"Akwai hadari a garin, akwai yuwuwar ayi ruwan sama, ka kwanta anan kawai".
Yusuf yace "to ai ba'a fara ruwan ba"
"Eh bakomai ka kwanta, i need a shoulder to cry on, ka kwana a kusa dani"
Har yanzun dai kuka Widad take yi, ya kwanta ya ɗora kanta a Ƙirjinsa, ya dinga sauke ajiyar zuciya, tana cigaba da zubar da hawaye.
Yusuf yaja wata doguwar ajiyar zuciya yace "Gimbiya kina son ki karyamin zuciya ne in cigaba da kukan nima?"
Girgiza masa kai tayi, yace "kinga har shaƙuwa kikeyi, kin kusa shiɗewa ɗazu saboda kuka, kiyi haƙuri dan Allah ki dena haka ya isa, yi shiru muyi musu addu'a"
Widad tace "karka damu da shiɗewar da nayi, bayan ciwon hauka inada ciwon zuciya kamar Daddy na, dan haka ba wani abu bane, nasan idan kwana na ya ƙare zanbi Ammi na ne"
"Widad bakya tausayina ko? Baki damu da ki dinga gayamin zaki mutu ki barni ba ko? Babu ruwanki da halin da zan shiga idan kika mutu kika barni bako?"
Ɗago kanta tayi tana kallon Yusuf, dukda a cikin duhu suke amma ta kai hannunta fuskarsa taji ɗumin hawaye a fuskarsa.
Murmushi tayi tace " Ragon maza kawai, ɗan sanda yana kuka, se kace ba jarumi ba, ni meyasa ka damu dani haka baka son in mutu in barka? Dukda tarin rashin kirki na a gareka"
Tai maganar cike da son bagarar da wancan zancen da suke.
Mirginata yayi ya koma kanta, a hankali ya kai fuskarsa kunnenta yana mata numfashi a kunne sannan yace "saboda ni bana ganin laifinki, kuma ni bana riƙo ina sonki sosai, kuma ba kince ni ɗan uwanki bane?, kuma seki tafi ki bar ɗanuwa haka akeyi? Bakya tunanin halin da ɗan uwa ze shiga? Anya kina 'yan uwantakar dani kuwa?"
Murmushi tayi tace "wani lokacin inayi, wani lokacin kuma ba nayi"
Tai maganar tana dariya, ta rungume Yusuf tace "dare yayi sosai, muyi shiru haka mu kwanta"
Yusuf ya sake gyara kwanciyarsa a jikinta, yayi shiru wani irin matsanancin tausayin ta yana ratsa ransa, daga ita har mahaifinta kowannen su yaga ƙaddarar rayuwa daban daban.
A haka har bacci yayi awon gaba da dukkaninsu.
Alhaji Musa yana zaune yana karyawa da safe a falonsa, wayarsa ta fara ringing, ɗaukar wayarsa yayi ya tafi bedroom, ya rufe ɗakin ya saka key sannan ya ɗaga wayar.
"Ka kasa kunne yau, zakaji matakin dana ɗauka akan Yaron nan, dan haka ka kwantar da hankalinka babu abunda ze faru"
Ajiyar zuciya Musa yayi yace "Alhamdilillah, Insha Allah zan saurara inji wani irin mataki ka ɗauka akan lamarin, amma to batun Daula fa? Har yanzu fa babu wani labari a game da shi, ya muke ciki a wannan ɓangaren?"
"Karka damu, shima ina nan ina tunanin mafita, sannan wannan Likitan shima masa a kau dashi, dan amfaninsa ya ƙare"
Musa yace "doctor Sufyan kake nufi wai?"
Bukar yace "Eh shi, na bada umarnin da ya dace akansa shima, dan haka kowa ya kwantar da hankalinsa"
Alhaji Musa yace "to shikenan, babu laifi godiya muke"
Daga nan ya kashe wayarsa, yana jin wani sanyi a ransa, dan da ba ƙaramin ɗurar ruwa cikinsa yayi ba.
Nura direba ne a cikin lambun Widad yana ta gyarawa, yana cire ciyayin ciki yana gyara flowers ɗin tare da sharewa, yace "Allah sarki, lambun nan kansa yayi babban rashi, da meshi tana nan babu yadda za'ayi a barshi a haka, kai rayuwa ba tabbas"
Kukan mage ya dingaji a tsakanin flowers, har ya tsorata ze ruga da gudu, sekuma yayi ta maza ya dake, leƙawa ya shigayi a hankali, yana duba ciyayin.
Roux ce magen Widad a kwance, gaba ɗaya tayi wani iri abun tsoro, da ƙatuwace magen nan, gata da kyau gwanin ban sha'awa da yake bata Nigeria bace, amma yanzu kamar an jiƙata a ruwan zafi, gaba ɗaya gashin jikinta yayi wani iri, gashi duk ya zube ta koma wata iri abun tsoro.
Nura yasa hannu ya ɗakkota, ya nufi bakin gate da ita, yana zuwa ya ajiye ta, Isa ya kalleshi ya yamutsa fuska yace "meye wannan haka?"
Nura yace "Magem 'yar masu gidace"
Murtalah yace "itace ta koma haka?"
Nura yace "kaima dai ka faɗa, ai maraici yakama magen nan, abun tausayi"
Isa yace "wannan matsiyatan basu kula da mutum bama balle wata mage, duk halin nan da ake ciki na rashin me gidan nan da' yarsa ko a jikin su, sabgarsu kawai suke har gara ma Anwar ɗin nan, shikam akwai kirki sosai"
Nura yace "bari Isa, Allah abun tsoro duniya abun tsoro, kalli da yadda gidan nan kullum cikin shige da ficen mutane ake, amma yanzu tsit kake ji"
Murtalah yace "kai dai bari, bari in jarraba bawa magem nan Abinci ko zata ci"
Isa yace "kaga fa baka da abunda zaka bata, dan Wani Abincin da fake ci kai kanka baka taɓa ciba, ka ƙyaleta kawai ta ƙarasa ta hutawa rayuwarta"
Murtalah yace "A'a ba'ayi haka ba, Yanzu a dalilin taimakon dabbar nan se kaga Allah nima yaji ƙaina, kuma dame ita tana nan kasan bata yarda abar wani da yunwa a gidan nan ba, dan haka zan jarraba bata Abinci ko zata ci"
Isa yace "ai se kai tayi ɗan wahala, ga hanyoyin neman lada nan ba adadi, amma ka tsaya wahalar da kanka akan abar data kusa mutuwa"
Murtalah be kuma kula shi ba, yaje ya siyo biscuit katako, da madara 'yar talatin yazo ya haɗa ya bata, ai nan da nan magen nam ta lamushe, saboda azabar Yunwa da take ji, abunka da dabba da sabo, tana jin ƙwarin jikinta ta koma ɗakin Widad, tana kuka ta hau kan gadonta ta sauka, ta fito falonta zuwa babban falo.
Ramlah tace "wai dama wannan shegiyar halittar tana raye bata mutu ba?"
Amal tace "ni kaina na zata ta mutu fa"
Ramlah tace "aikuwa ƙarasata zanyi, sena kasheta"
Amal tace "ke Ramlah, ina ruwanki da ita? Me tayi miki?"
"ke nifa duk wani abu daya shafi waccan banzar ba sonsa nake ba, tunda Allah yasa ta bar gidan nan mukayi 'yanci, muke warwasawa son ranmu, babu tsawa balle hantara, shiyasa bana son ganin duk wani abu daya shafeta balle raina ya ɓaci"
Amal tace "dukda haka dai karki huce akan magen nan danni tausayinta nake ji, itama magen wata kinibabbiya kamar uwarɗakinta, bata zuwa ko ina se tare da ita, ai gashi yanzu tana wahala"
Ramlah tace "tunda uwaɗakin nata bata nan, ai itama seta ƙara mai"
Da ƙyar Yusuf ya iya tashi sallar Asuba saboda daɗewar da suka yi basu yi bacci ba jiya, hadari yana ta cida, da akama ruwan sama za'ayi.
Ya tashi Widad sannan yaje yayi alwala ya fita salla, sedai harya dawo bata tashi ba, hannunsa yaje ya wanke yazo yana shafa mata ruwan a fuskarta.
A hankali tayi miƙa, ta koma ta kuma lumshe idonta, ɗagota yayi daga kwanciyar gaba ɗaya ya ɗan ƙura mata ido sannan yace "wai wani darem za'a kuma yi miki ne?"
Kasa buɗe idon tayi saboda baccin da take ji, hannayenta ya shiga matsawa yace "kalli gari ya wayefa, buɗe idonki ki gani"
. A hankali ta buɗe idonta, tabbas gari ya fara hasks duhun Asuba ya yaye, ta kalle shi tace "meyasa baka tasheni ba"?
"na tasheki baki tashi bane" a hankali ta zauna sosai, sannan ta miƙe taje tayi alwala tazo ta tada salla, Yusuf yana gefe yana cigaba da lazumi, ya kwaɗaitu da son jin ƙarshen labarin Widad, sedai yasan halinta da rikicin tsiya, idan bata ga dama ba haka zatai ta ja masa rai ba zata gaya masa ba, idan ya takura ta se yaji kuma suyi faɗa.
Data idar da sallar ta fara lazimi ta kife a gurin, yana kallonta da alama bacci ne sosai a kanta, ya tashi a hankali ya ɗagata ya maida ita kan katifar, still yana jin tausayinta yana ratsa ruhinsa da ganganr jikinsa.
Ya kwanta a bayanta cike da fargabar kar ta tashi ta kama masifa, tunda ba ita tace ya kwanta ba, sedai ta ɗanyi juyi taji shi a bayanta, a hankali ta juyo tana fuskantarsa, ba tare da ta buɗe idonta ba, ta zura hannunta ta rungumeshi, ta kwantar da kanta a jikinsa, a haka bacci ya sake yin awon gaba dasu.
Har shaɗaya da rabi na Safe basu farka ba, Hari sunata aikace aikacen su a tsakar gida, ta kalli Gwaggo tace "Yaya, har yanzu fa Wudas basu fito ba, lafiya kuwa?"
Gwaggo tace "lafiya ƙalau insha Allah, ai da Asuba shi yaja salla, dan haka lafiya ƙalau"
"Yaya sha ɗaya da rabi fa"
Hansai tace "A'a haba Yaya Hari, abu na mata da miji ina ruwanki? Ba suyi niyyar fitowa yanzu bane"
Hanne ji tayi kamar ta faɗi ƙasa dan haushi da takaici.
Widad ce ta fara farkawa, ta buɗe idonta taga yadda rana tayi, a hankali ta bar jikin Yusuf ta tashi zaune, garin ta tashin ne shima ya farka, ya kalli garin yadda rana ta buɗe, yace "Subhanallah, rana tayi ma"
Widad tace "Aikam dai, kasan bamuyi bacci da wuri ba, shiyasa"
Yusuf yace "hakane, gashi ko breakfast bakiyi ba, bari in tashi idan akwai Abinci a gurin Gwaggo shikenan, in babu se inzo in dafa"
Widad tace "karka damu ni bana jin Yunwa, wanka nake son inyi amma ina son Ka temakamin in wanke kaina, gani nake kamar baha fita yana damuna sosai saboda babu gyara"
Yusuf yace "to aini ban san yadda ake yi ba, ban san yadda ake wanke gashi ba"
Widad ta kalleshi tace "eh amma ka iya taɓawa ai"
Yusuf yayi murmushi yace "wannan ai me sauƙi ne, dan bana gajiya da taɓawa, amma wankewa ni ban san yadda ake yi ba"
"Yau zaka koya kuwa, zan karɓo ruwa a gurin Gwaggo seka tayani mu wanke"
Yusuf yace "wait, waima a ina zamu wanke kan? Ba dai banɗaki ba"
"Koma a inane" ta bashi amsa
Yusuf yace "kawai se aga mun shiga banɗaki tare? No banda wannan, sannan da kunya aga na taƙarƙare ina tayaki wankin kai a tsakar gida, ki bari seda daddare, muje toilet mu wanke gashin, yadda ba wanda ze ganmu"
Hararar Yusuf tayi tace "ni yanzu nake so, idan aka wanke kafin dare ya sha iska, in aka wanke daddarw na kwanta ai wari zeyi tunda babu shampoo"
Yusuf yace "ni ya zanyi, kawai aga mun shiga banɗaki tare? Da kunya fa"
"Au wai nan kunya kake ji, amma ai baka jin kunyata tunda..
" tunda me? "
" ban sani ba"
Murmushi yayi yace "Allah ya barni da abar sona, ina sonki Habibty na, kura kike ga tsoro ga ban tsoro"
Suleiman ne tafe yana driving a motarsa, yana sauraren radio yana jiran ƙarfe huɗu ta cika ya saurari labaran yamma, kanin labaran ne suka ɗauki hankalinsa, hakan yasa shi maida hankali don jin cikakkun labaran.
Labarin farko da aka sanarne ya ɗau hankalinsa, ya kaɗashi matuƙa ya tayar masa da hankali, be gama tsinkewa da lamarin ba, seda ya ƙarasa traffic ta tsaida hannun da yake, wani yaro yazo ya tsaya a window motarsa yana masa tallan jarida, shafin farko ya kalla yaji gabansa yayi mummunar faɗuwa.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
MASU FITARMIN DA LITTAFI KUMA, IN DAI DAI KUKE KUN SANI IDAN AKASIN HAKANE MA KUN SANI
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
70_71
Da rawar jiki Suleiman ya sayi jaridar nan yayi parking a gefen titi, hoton Yusuf ne a bangon jaridar an rubuta wanted, ya buɗe cikin jaridar ya shiga duba shafin da labarin yake, wai 'yan sanda sun fitar da sakamakon binciken da suka yi akan ɓatan 'yar gidan Daula, bincike ya tabattar musu da direban Widad Nasir Daula wanda aka sani da Yusuf, shine ya sace Widad yayi garkuwa da ita, ba sace su akayi tare ba, dan haka jam'ian tsaro suna nan suna binciken inda suke, sannan duk wanda ya gano inda suke ya faɗa akwai kyauta me tsoka.
Gaba ɗaya jikin Sulaiman yayi sanyi, akanme za'a fitar da wannan sakamakon binciken? Meye dalili? Cikin hanzari ya juya sitiyarin motarsa zuwa wani gurin, tuƙin kawai yake amma hankalinsa sam baya kan abunda yake yi, Allah ne ya kaishi inda yake son zuwa.
Harabar headquarter 'yan sanda yaje yayi parking ɗin motarsa, ya fita da sauri daga cikin motar, yana shiga harabar gurin ƙananan' yan sanda sunata sara masa, cikin gaggawa ya nufi wani office, ya buɗe ya shiga suka gaisa da ma mallakin Office ɗin, Suleiman ya zauna ya miƙa masa jaridar hannunsa sannan yace "SP waye ya fitar da sakamakon wannan binciken haka? Har aka sanar da 'yan jarida?"
SP yace "kamar yaya kenan? Sakamakon binciken da akayi kenan, kuma aka bada umarni mu sanar"
Suleiman yace "haba SP, wannan yaron fa jami' inmu ne, ta yaya kake tunanin ze iya aikata wannan mummunan aikin haka, sam ba haka abun ya faru ba, ta yaya za'ace Yusuf ne yayi garkuwa da 'yar gidan Daula? Ta yaya?"
"Kaga karka zo ka ɗagamin hankali mana, nima umarni aka bani inyi wannan Sanarwar kuma nayi, meye nawa a ciki?"
"An gabatar maka da sakamakon binciken da akayi kafin kayi wannan Sanarwar, wannan fa tamkar ɓatawa hukumar' yan sanda sunane, ta yaya wasu tsirarin mutane zasu sa ku saɓa dokar aikinmu saboda biyan buƙatarsu?"
SP ya kalli Suleiman yace "ya akayi kasan wasu tsirarin mutane ne suka sa ayi hakan?"
Nan da nan Suleiman ya dawo hayyacinsa ya daidaita nutsuwarsa yace "to koma dai a cikinmu ne mukayi hakan ai munsan mun saɓa dokar aiki, yaron nan abokin aikinmu ne, jajirtaccen ma'aikaci ne mara ƙyuya, ga gaskiya a harkar aikinsa, ya dace ayi masa haka, zan iya rantse maka ko a wasa Yusuf baze aikata haka ba"
SP yace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, kai kake zaune dashi kasan halinsa, ni babu ruwana sakamakon da aka gabatarmin shi zan bayyanawa al'umma, dan haka in baka da abunyi zaka iya bani guri, ina da baƙi"
Cike da baƙin ciki da ɓacin rai, Suleiman ya baro office ɗin nan, gaba ɗaya tausayin Yusuf da mamaki suka cika zuciyarsa, tabbas idan akayiwa Yusuf haka an zalunce shi, kuma an zubar da kimar aikin ɗan sanda a idon duniya.
Saleh ne yayi jifa da jaridar hannunsa yace "Impossible, Alhaji Musa anya kanaso mu gama da duniya lafiya kuwa? Ta yaya za'ace anyi masa wannan ƙazafin haka? Abun yayi yawa, yakamata mudinga yi muna jin tsoron Allah"
Alhaji Musa yace "kai dakata! Meyasa ba zamu nemawa kanmu mafita ba? Ina ruwanmu da koma wani hali ze shiga, ai ba ƙarya akayi masa ba, in ba hakaba meyasa da suka gudu basu dawo ba, waye yasan inda suke? Dan haka shiya saceta yayi garkuwa da ita, kuma ya koma yayi garkuwa da mahaifinta, ai mafita muke nemawa kanmu, ɗan sanda nefa, yanzu idan ya dawo asirinmu ne ze tonu, dan haka gara da mukayi masa haka, idan kuma baka cikinmu ne zaka iya ƙarawa gaba"
Saleh yayi shiru cike da takaici da baƙin ciki, ya rasa mema yakamata yayi, idan aka yi haka an cutar da rayuwar Yusuf ba kaɗan ba, rasa abunyi yayi kawai ya juya ya fice a matuƙar fusace.
Hari tana ta fifitar Wuta, ta kuma kallon ƙofar ɗakinsu Widad tace "taɓ amma wannan abu yayi yawa haka, ai kome suke yaci ace sun fito haka, sha biyun rana fa wane irin abune haka?"
Banza Gwaggo tayi da ita, yayin da Hansai tace "ke kuma sa idonki yayi yawa, ina ruwanki da koma me suke yi ina ruwanki? Kedai bakya rasa abun faɗa shiyasa duk tabi ta raina ki"
"to naga abun magana bazan magana ba? Ai abun da damu ace garin Allah ya waye, har wannan lokaci suna ƙule a ɗaka, idan wani abun ya samesu fa"
Widad ce ta fito hannunta ɗauke da bokiti, ta ƙaraso inda Gwaggo take ta gaisheta, tace "A temakamin da ruwa, ina so da ɗan yawa zan wanke gashina ne"
Gwaggo ta karɓi bokitin, taje rumfar da suke girki ta Ɗebo mata ruwan, Yusuf a kunyace ya fito suka gaisa da mutanen gidan, yaje ya Ɗebo ruwa a rijiya ya sirka ya kai banɗaki.
Widad ta ɗakko abun wanka, tazo ta shige banɗaki, Yusuf ya rasa yadda zeyi ya bita toilet ɗin nan saboda kunya, leƙowa tayi tace "Yoseef ka shigo mana, kose ruwan yayi sanyi?"
Hari ta tsaya tana kallon ikon Allah, haka Yusuf ya shiga banɗakin nan, ta cire hijjabin jikinta daga ita se towel, ta cire ribbon ɗinta, ta zauna akan kujera, Nan Yusuf ya shiga tayata wanke gashin nan me matuƙar tsawo da yawa.
Hansai kam burgeta sukayi, yayin da Hari ta taɓe baki tace "ni tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin baɗalar da nake gani a gurin bayin Allah nan ba"
Hansai tace "taɓ wallahi nikam birgeni sukeyi, yanzu kai anan ka isa miji ya wani ta yaka wanke kai, yadda yake ɗawainiya da ita ba ƙaramin birgeni yake ba"
Hari tace "mhmm, ai ko sharar ɗaki baki isa miji anan ya tayaki ba, balle wani wanke kai, ai maza suna birni, mu nan se godiyar Allah kawai"
Hansai tace "me kike nufi to?"
"Ni ba abunda nake nufi, karki ƙullamin sharri"
Haka suka cigaba da maganganunsu.
Yusuf dai bega wani datti da kan Widad yayi ba, ta dai damune kawai ta wanke kan nata, tunda ta saba wanke shi akai akai.
Seda ta gama ya bata guri tayi wanka, duk ya jiƙa kayansa da ruwa, Widad tayi wankanta ta kammala sannan ta fito, Towel ɗin nan kawai ta ɗauro ta fito, gashin nan ya baje a bayanta se ɗigar da ruwa yake.
Ai gaba ɗaya sukabi Widad da kallo, tubarkallah Allah yayi mata kyau da halitta me ɗaukar hankali, ta kama ƙasan gashinta tana yarfewa, ga towel ɗin iyakacinsa gwiwarta, fatarta se sheƙi take.
Hanne tabi Widad da kallo, tana tunanin me zata yi mata ta huce wannan baƙincikin, Widad kamar da gayya take juya jikinta har ta shiga ɗakinsu.
Hindu ta lura da irin kallon da Hanne ke yiwa Widad, dan haka tace "Masha Allah, Allah me halitta duk mutumin da yake da mace kamar Amarya, wallahi babu me kama da bayan tukunyar daze kalla balle yayi sha" War Aurenta, kamar ita tayi kanta masha Allah "
Hanne ta kalli Hindu, taja tsaki tayi tafiyar ta abunta.
Yusuf ya kalli Widad yace " Masoyiyya ba dai a haka kika fito ba? "
" A haka na fito menene? Ai dai naga ba maza"
"Anya kin san irin kyawun halittar da Allah yayi miki, koda ba maza baki abun gudu ne, dan Allah karki kuma fita a haka"
"Kaga nifa na fara jin yunwa"
Yusuf yace "maganar tawa ce bata da amfani ko? Shine kike sharewa"
Shiru tayi masa ta nemi guri tayi zamanta.
Hindu tayi sallama ƙofar ɗakinsu, ta kawo musu Abinci, Yusuf ne yaje ya karɓo ya dawo ya zauna, Widad bata da niyyar saka kaya, a haka take zaune abunta, Yusuf kam se ƙureta yake da ido, gaba ɗaya ya rasa sukuni har suka kammala cin Abincin idonsa a kanta.
Bayan sun gama yace "yau kuma baza'a sa kaya bane?"
"zan saka ban shafa mai bane"
Yace "Kawo in shafa miki"
Ɗakko zaitun tayi ta miƙa masa, ta koma ta zauna tana cin jiƙaƙiyar aya da Hindu ta koya mata ci.
Yana shafa mata man yanajin fatarta kamar ze ji mata rauni idan beyi a hankali ba, Yusuf yace "me kike cine haka?"
Tace "Hindu ce ta bani, ina son wannan abubuwan da Aya, da wata baƙar aba mulmulmulalliya, da yama sunanta wani abu baƙa cikinsa ja ƙanana me ɗan tsami tsami"
Yusuf ya jinjina kai yace sannu bagwariya, ɗinya da tsamiyar biri dai ko? "
Widad tai murmushi tace " what ever dai "
Haka ya kammala shafa mata mai, se sheƙi fatar take saboda man zaitun daya shafa mata, yaje ya buɗe Akwatinta ya ɗakko mata kaya, Ya kalleta yace " bari in samiki "
Tura baki tayi tace "A'a bana so"
Yusuf yace "Meyasa ba kyaso? Ai tunda na shafa miki mai saura sa kaya kuma"
Tace "A'a ni gaskiya bana so, ka ƙyaleni kawai in saka abuna"
Kokawa suka shigayi ita da Yusuf, aikuwa ta buɗe baki ta shiga kiran sunan Gwaggo da ƙarfi, ba shiri ya cikata ya ƙyaleta, dan a wautar Widad ba taƙi azo a tarar dasu a haka ba in be ƙyaleta ba, ta koma gefe tana harararsa hadda murguɗa baki.
Yusuf yace "Ni kikewa wannan ihun Masoyiyya?"
"An maka ɗin, waye yace kamin abunda zanyi ihun?"
Murmushi yayi yace "Shikenan Allah ya baki haƙuri"
Zumɓura masa baki tayi, ba tare da tace komai ba.
Labari ya game gari a game da Yusuf, Nurat tana kwance tana kallon labaran dare a TV aka nuno zancen Yusuf, ta kaɗu matuƙa da ganin labarin da gudu ta tafi ɗakin mahaifiyarta tana ƙwala mata kira.
"Ke lafiya kike ƙwalamin kira hak?"
"Mummy kinga abunda na gani kuwa?"
"Ta yaya zanga abunda kika gani? Ina nan kina can"
"Mummy an buga fastocin Yusuf, wai he is wanted shine yayi garkuwa da Widad sannan yayi da mahaifinta"
Tace "wai waye Yusuf ne?"
Nurat tace "Mummy direban Widad ne fa"
Tace "Allah sarki, dama duk abun nan shine ya sacesu aketeta nemansu?"
Nurat kamar ta fashe da kuka tace "Mummy, ki gane me nake nufi mana, wannan abun duk shirin su Daddy ne, Daddy ne suke ƙulla wannan abubuwan, Yusuf bashi da laifin komai fa"
Da sauri Mahaifiyarta ta riƙota, ta rufe mata baki tana waige waige, a fusace ta kalli Nurat tace "waike yaushe zakiyi hankali ne? Kina kallo kwanan nan ya kusa halakaki, shine kike wannan maganar, maza ki bari ya jiki idan ya ƙarasaki shikenan"
Cire hannun Mahaifiyarta tayi daga bakin ta ta kalle ta tace "haba Mummy, yanzu shikenan mu zuba ido babu wani abu da zamuyi, wallahi Umma Yusuf baze sace Widad ba, ina yaga yadda ze iya sace Daula a gadon Asibiti, shikenan idan baka da kuɗi baka da gata a garin nan?"
"to dan ubanki kije kiyi tayi, ina gargaɗinkibakan shiga wannan sabgar tasa, akan ya hana ki fita kawai ya kusa aikaki lahira, amma se sake cusa kanki kike kina bin diddiginsa, ki cigaba karki fasa, inya kasheki ya kashe banza dukda shiya haifeki, kinfi kowa sanin takun saƙar dake tsakaninsa da Daula, kuma kin san alwashin da yayi, ki cigaba da sa kanki a lamuransa, inkin ƙiji ba zaki ƙi gani ba"
"Amma Mummy......"
A fusace tace "Amma me? Kije kiyi dan ubanki karki fasa, fita ki barmin ɗaki"
Jiki a sanyaye ta fito daga ɗakin, tana jin wani irin jiri yana kwasarta, tana fitowa falo taci karo da mahaifinta, yana shirin fita, suka haɗa ido ya ganta kamar wata mara gaskiya, tana tafiya a hankali, ya kalle ta yace "ke lafiya kuwa?"
Ba tace masa komai ba, se binsa da tayi da ido.
Yace "jeki ki kiramin mahaifiyar ki" ko kallon inda yake ba tayi ba, ta shige ɗakinta ta kulle ƙofa, ta faɗa kan gadonta ta fashe da kuka.
Mamaki ne ya kama Alhaji Musa, ya nufi ɗakin Maman Nurat, yaje ya tarar da ita tana gyara kan mudubinta, ya kalleta yace "to uwar masifa, hala wani abun kikayiwa yarinyar nan, na ganta a waje na mata magana taƙi kulani"
Wata uwar harara maman Nurat tayi masa tace "masifa harna kaika, daka kusa hallakata saboda tsabar masifarka da son zuciya, niba wani abun nayi mata ba, halayenka ne suke baƙanta mata zuciya"
"Halayena kamar yaya?"
Tace "Ahh gaba ɗaya ka canza mana, kana treating ɗinta kamar ba kai ka haifeta ba, dole ranta ya dinga ɓaci"
A fusace yace "ƙarya kike munafuka, kece kike zigata, idan ba haka ba ya za'ai in haifi 'ya sannan kikama kawomin ƙabali da ba' adi, babu yadda za'ayi 'yata ta dinga min wannan halin na taurin kai, in bake kike zigata ba"
Ta Harare shi tace "au har kamanta tantama kakeyi akan ko kai ka haifeta? Ai baka da tabbacin kaika haifeta ko ba kai ka haifeta ba"
"Malama karki gayamin maganar banza, Nurat' ya tace nina haifeta, kuma ina son abata"
Tsaki tayi ta miƙe tace "ƙaryar banza kawai, ji wata fuffuka kake 'yarka ce, bayan da hannunka ka kusa kasheta"
"Muka kusa kasheta dai, waye sila?"
Banza tayi masa ta shige banɗakinta, ta rufe ƙofa ta barshi a gurin a tsaye.
Juyawa yayi ya fito daga ɗakin, ya kuma kallon ƙofar Nurat, still a rufe take bata buɗe ba, girgiza kai kawai yayi ya fice abunsa.
Ita kuwa Nurat tana cikin ɗakin, se rusa uban kuka take, tana jinjina zalunci irin na Mahaifinta, sun haɗa kai sun sace 'yar Daula tare da Yusuf, kuma ya koma sunsa ace shine yayi garkuwa da mahaifinta, tuna tana iya kukan hawaye na zuba, har tayi shiru se ajiyar zuciya da take yi.
Da Yamma Widad suna zaune dasu Hindu, kowacce da littafinta tana koya musu karatu, cikin ikon Allah da yake sunsa kansu, suna fahimtar karatun sosai, duk me tambaya ta bashi damar ya tambaye ta, dukda idan tare da su Indo take koyawa Hindu karatu bata wani sakar musu fuska, amma a hakan girmamata sukeyi sosai, saboda bata hantararsu sam, bayan sun kammala karatun ne kuma ta shiga yi musu bayani akan tsafta da mahimmancinta, ta shiga ɗakinta ta ɗakko musu pad a cikin wadda Yusuf ya siyo mata, ta bawa kowa ɗaya, tayi musu bayanin yadda ake amfani da ita, da kuma yadda zasu dinga kula da kansu lokacin al'ada, kunya suka dingaji suna wani sinne kai, hakan seda ya kusa bawa Widad dariya, dan sam ba taga abun jin kunya a bayanin nata ba, suka karɓa suka dinga yi mata godiya, suna nan zaune suna bitar karatun da tayi musu, ita kuma tana ta faman saƙar mafici da Hindu ta koya mata.
Yusuf ne yayi Sallama, suka amsa gaba ɗaya suna gaishe shi, hannunsa ɗauke da ledoji, Widad ta kalle shi ta basar tana zumɓura baki, Gwaggo ta harareta, ta gane kallon da Gwaggon take mata, taje ta karɓi kayan hannun Yusuf ne, aikuwa ta tura baki tace "mhmm Mama kayanfa da nauyi, kuma ze iya kaiwa ɗakin"
Dariya ta bawa su Indo, dan yadda take haɗe rai tana koya musu karatu, bazaka ce tana dariya ba, Gwaggo tace "haba yarinyar kirki, aikin ladane fa duk abunda kika masa yaji daɗi lada zaki samu, ko ba kyason ladan ne?"
"Ina so mana"
Gwaggo tace "Yawwa 'yar Albarka, aje a karɓi kayan hannunsa"
Widad ta miƙe ta ƙarasa inda Yusuf yake yana kallonta, tana zuwa ta karɓi leda ɗaya tana harararsa, Yusuf yace "to mara kunya, ni kike harara ko?"
"Mama kinga yana cemin mara kunya ko?"
Gwaggo tace "Allah ya huci zuciyarki, tuba muke, kai kuma haka akeyi, ka samu za'a karɓi kayan naka shine za kace mata mara kunya?"
Yusuf yayi dariya suka wuce ɗaki, Hari tace "wallahi Wudas ɗin nan ba ƙaramar taɓararriya bace, gaba ɗayanta gaɓuwa ce"
Hansai tace "Allah yasa ta jiki, ta ƙare miki tatas ai"
Me gari kam yana ɗaki yana jin dramarsu, koda ya fito ya kalli Gwaggo yace "Allah ya saka miki da Alkhairi Hasana, kina ƙoƙari da wannan 'yar taki"
Sukayi dariya, ya koma kan ɗaliban Widad yana cewa "masha Allah, kuna gane karatun dai ko?"
Hindu tace "muna ganewa sosai"
Ya kalli inda Hanne take zaune, yace "ke ina naki littafin?"
Hindu tace "ai banda ita ake koyamana"
Me gari yace "saboda me banda ita? Ke meyasa ba zaki koya ba? '
" Baffa ni bana so" Hanne ta bashi amsa.
"ba kyason ƙaniyarki, kije ki samu Ila, ki gaya masa nace idan yaje kasuwa ya taho miki da kayan rubutu kema, idan na kuma zuwa na tarar ana karatu bake senaci mutuncinki"
Kallon me gari tayi, ta yaya ma zata fara zama wannan mara mutuncin, 'yar wulaƙancin ta koyar da ita? Shiru tayi masa taƙi kula shi, dan ba zata taɓa zama wannan banzar ta koya mata karatu ba.
Gaba ɗaya Anwar a rikice ya shigo babban falon gidan, ya tarar da Amal da Hajiya Halima na shirin fita, yayin da Ramlah ke zaune tana zuba Coca-Cola a kofi tana sha a hankali.
"kai lafiya kuwa na gankaba haka? Kamar wani korarre?"
"Mummy, kin saurari labarai ne yau? Ko kuma kin kalla?"
"A'a ni kasan ba wani shiri nake da radio ba, dama da Daula yana nan ne, shine sarkin labarai da radio saboda kasuwanci"
Anwar ya girgiza kai yace "Mummy, na rasa mema zance miki, yanzun nan naji a labarai, wai hukumar 'yan sanda sun fitar da sakamakon binciken ɓatan Widad"
Cikin Hajiya Halima yayi wata ƙara, ta dake tace "me sukace, ni sam banji labarai ba, am ganta ne?"
"Mummy wai ana zargin Yusuf ne yayi garkuwa da ita, ya nemi maƙudan kuɗaɗe da aka hana shi, shine yayi garkuwa da Daddy"
Wani sanyi ne ya ratsa Hajiya Halima, dan ba ƙaramin daɗi labarin yayi mata ba, amma ta nuna kaɗuwarta a fili tace "to yanzu ya ake ciki? An kama shi ne?"
"Mummy ba'a kama shi ba, amma ance duk inda aka ganshi ko a mace ko a raye a kamo shi, Amma ni sam banji na yadda da wannan labarin ba Mummy, ya za'ayi Yusuf ya iya aikata haka? Yusuf baze wannan abunba, dukda ban daɗe tare da shiba, amma beyi siffar miyagu ba, ni ban yadda da wannan labarin ba"
"to kar Allah yasa ka yadda mana, ubankane shi, ai a rayuwar nan kai dai kaga mutum kawai, yana ta shisshigi a gurin me gidan nan da Widad, ashe macuci ne Azzalumi, ai ba'a gane mugu a fuska tunda kaji an faɗi haka to tabbas ya aikata ne"
Anwar ya girgiza kai yace "gaskiya bazan taɓa yadda ba Mummy, dan yadda akayi aka sace Alhaji Nasir ba ƙaramin me hikima ne ya shirya faruwar hakan ba, kuma shida aka sace su ta yaya harya iya dawowa ya sace mahaifin Widad, nifa ina da shakku akan wannan sakamakon fa"
Ramlah ta taɓe baki tace "ni dama wannan da ganinsa ya saba aikata laifi, kuma zata iya yuwuwa da wasu ya haɗa kai bashi kaɗai yayi ba, tunda ɗansanda ne yasan duk wasu hanyoyi na aikata laifi, kuma ba abun mamaki bane dan yayi garkuwa da ita, tunda yasan da yawa daga sirrikanta, har ATM ɗinta tama bashi, ba inda be sani ba a ɗakinta, duk wani gantali da zata tare suke zuwa, Allah kaɗai yasan iya abunda suke yi kaga kuwa ba abun mamaki bane dan ya sace ta"
"ƙarya kikeyi Ramlah!!! Nasani kin sani Wallahi Yusuf baze taɓa iya sace Widad ba, a gaskiya abun nan ya isa haka, haba dan Allah shikenan a dinga rayuwa babu tausayi ba imani, mutum beji ba be gani ba a ɗora masa wannan masifar, kun san hkuncin duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane kuwa? "
A fusace Hajiya Halima tace " Ke Amal rufemin baki, ya isheki haka, koma meye hukuncin ina ruwan wani tunda harya iya aikata laifi mummuna irin wannan, yaje ayi masa duk hukuncin daya dace dashi, ina ruwan wani can ta Matse masa"
Ƙurawa mahaifiyarta ido tayi na wani ɗan lokaci, kawai tayi ƙwafa ta juya da gudu ta koma ɓangaren su tana kuka.
Kame kame Hajiya Halims ta shigayi "Amm gaskiya Amal yarinyar nan bata da hankali, tunda ta ƙyalla ido akan yaron nan ta fara sonshi shikenan ta susuce, bata taɓa yadda ace ga abunda yayi, yaro sekace iblishi, duk yabi ya saye zuciyar mutane da halin kirki amma yana zagayewa yana cutar da mutane, me siffar munafukai.
Wani irin kallo Anwar yabi mahaifiyarsa dashi, kallon data kasan tantance kallon meya ke mata, cam yace "koma meye dai, shi Allah ya haramtawa kansa zalunci sannan hmya haramtashi a tsakanin mu, dan haka yana kallon komai, Mummy be halatta kidinga saurin yanke hukunci akan abubuwa ba, baki da tabbas akan shiya aikata dagaske ko kuma bashi bane, amma kin zauna kina ta tsine masa kin aibata shi, nan akamin ƙazafi aka ɗaureni kika kasa samun sukuni sam, bakya tunanin shima uwace ta haife shi? Bakya tunanin wani hali take ciki itama a yanzu, kefa uwace Mummy, duk abunda zakiyi you need to have that feeling as a mother, saboda kema kin haifa, kuma kome ka shuka duk daɗewa zeyi tsuro ka girbi abunka da hannunka....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
MASU FITARMIN DA LITTAFI KUJI TSORON ALLAH, AMANACE TSAKANIN NI DAKU, IDAN KUKA FITAR BAKUMIN ADALCI BA
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
72_73
Saroro Hajiya Halima tayi tana kallon Anwar, har yayi ya gama ya juya ya bar ɗakin.
Hajiya Halima tace "ke me yaron nan yake nufi ne? Naji yana wasu maganganu, kamar jurwaye me kama da wanka"
Taɓe baki Ramlah tayi tace "dan Allah ƙyaleshi Mummy, kin sanshi da sanyin haki da kuma tausayi, shi gaba ɗaya kamar bake kika haife shi ba saboda sakalancinsa, kawai dai surutu ne irin nasa, manta da shi kawai"
Hajiya Halima tayi ajiyar zuciya tace "Saura waccan makirar, bari inje inci ubanta, tana nema ta tonamin Asiri, 'yar banza mara mutunci"
Ramlah tace "A' a Mummy karki kuskura, kin san haukan Son Guy ɗin nan da take, kina matsawa ba taƙi ta ɓata komai ba, ki bita a sannu".
Tai ƙwafa tace "yarinya se kace yayi mata Asiri, duk zancen da za'ayi akan yaron nan seta kawo cikas, dani take zancen dan ƙaniyarta"
"ki daibi a hankali Mummy, dan ba taƙi ta zama rival ɗinki ba, kin san halin Amal sarai"
"Aikuwa da nayi maganinta, ina uwatta ta zama rival ɗina, amma nikam ba ƙaramin daɗi matakin nan yayi min ba, gaskiya mutanen nan basu da dama, kinga tunda akayi wannan sanarwar da an gano shi shikenan, a yanke masa hukunci kowama ya huta"
Ramlah tace "hakane, sedai ita uwar gayyar wani mataki zaku ɗauka akanta, dan bana tunanin zata bari a rufe shi, ƙaddara ma an rufesh ta yaya za'a karɓi abun hannunta, dan ba ƙaramar gaddamamiya bace"
"Allah masani, su suka san yadda za suyi da ita, nidai fatana ayi abani kasona kawai".. Suka kawashe da dariya kamar wasu ƙawaye.
Widad kam suna shiga ɗakin ta ajiye ledar data karɓa a hannunsa, ya zagaya gefenta ya ajiye na hannunsa ya kalleta yace
"Sannu da gida rigimammiya, tunda baki iya cewa miji sannu da zuwa ba, se tura baki kika iya"
Kallonsa tayi ba tace komai ba ta sake tura baki, ta nemi guri ta zauna, Yusuf yace "kin gama da ɗaliban naki ne? Naga kin zauna"
Tace "eh mun gama, na basu assignment ma, sannan nifa na bada kyautar pad ɗin nan, na basu suma su dinga amfani da su, zan baka kuɗi ka siyo musu brush da toothpaste, da shaver they need a lot counseling on personal hygiene, naga abubuwan nasu duk se a hankali"
Yusuf yayi murmushi yace "kaga malama ta gari me son ɗalibanta, naji daɗin hakan da kika yi dan kin temake su sosai kam, Allah ya baki lada amma a ina kika samu kuɗi?"
Widad tace "kuɗin sadakina mana, kuma yanzu na iya wannan maficin, Hindu kuma zata koyamin saƙa ksya, Mama tace idan nayi aka siyar na tara kuɗina, nikuma nace mata zomaye zan siya nima in dinga ganinsu"
Murmushi kawai Yusuf yayi, Widad akwaita da Wauta wasu lokutan, yace "Sannu sarkin son dabbobi, gashi nan Na auno mana shinkafa, na siyo mana kifi da gurji da albasa, zaki ci Abinci me daɗi yau, bari inzo in tsince shinkafar kafin magariba tayi"
"Yoseef wai me kake tsinta a cikin shinkafar ne?"
Yusuf yace "tsakuwa ce da sauran dattin dake ciki"
Widad tace "tsakuwa kuma? A cikin Abincin ake ganin tsakuwa kuma a ci?waye yake zubawa"
Yusuf yayi murmushi yace "Eh mana, ke kinma samu me tsakuwar, idan na gaya miki a inda nake samo me tsakuwar zakiyi mamakin nisan gurin, ko kinga gidan nan ana dafa shinkafa dukda a haka wai gidan megarine?"
Shiru tayi, tabbas tunda sukazo bata taɓa ganin an dafa shinkafa ba, babban abunda suka fi ci shine, dankali, rogo, kunu, se kayan rama, zogale da sauran kayan gargajiya.
Amma abun ya ɗaurewa Widad kai, wai tsakuwa a cikin Abinci, ta kalli Yusuf jiki a saɓule tace "Sannu da ƙoƙari, Allah ya saka maka da alheri, na tambayi Mama meye faskare, ta gayamin dama ina son in gaya maka, yakamata Kadena wannan aikin, kaga jikinka be saba ba"
Yusuf yai murmushi yace "eh jikina yafi saba wa da tuƙa motocinki manya masu AC, sanyi na ratsani ƙamshin turarenki ya hanani sukuni, shauƙin soyayyarki yaita ɗibata, gefe kuma anamin tsiwa ana dakamin tsawa, i miss that moment fa"
Dariya ya bata tace "hakama zakace?"
Yace "eh mana, sedai duk da haka nauyin ciyar dake a wuyana yake, dan haka zan iya kowane aikine muddin be saɓa dokar addini ba dan in ciyar dake, bani da hujjar da zan tsaya gaban Allah in faɗa na kasa ciyar da ke alhalin inada rai da lafiya, dan haka karki damu kinji beb" yai maganar yana kashe mata ido ɗaya.
Ta ƙara tabattarwa da kanta da lallai Yusuf na daban ne, shi dai akwai sanyin hali, ta tuna labarin da Daddynta yake bata akan Yayansa, hakan yana nuna duk masu sunan haka suke kenan.
Zuwa isha'i ya kammala girkin, ya haɗa shinkafa da manja da gishiri da tumatir da albasa, ga gurji ya marmasa musu kifi, ba ƙaramin daɗi Abincin nan yayiwa Widad ba, dan ko ba'a gaya mata ba tasan wannan Abincin da take ci yafi wanda take ci a gida lafiya, duk gayyar iyayi ga ba ƙoshi ake ba, ga kayan cutarwa.
Suka gama ci, ya ɗakko rake a leda, yace mata "ga tsaraba na kawo miki, ko shima baki sanshi ba"
Ta kalli raken ta harareshi tace "sugar cane ɗinne ban sani ba, amma bazan iya sha a haka ba, yayi min gjrma a baki"
Yusuf yace "toni ba abun in dinga gutsuro miki ina baki ba, kar in sa yawu kiƙi sha"
Hararasa tayi tace "yawu kuma na nawa, sedai kuma kar a ƙara, ka koyamin ƙazanta kawai"
"dama can kin iya a barki, bani na koyamiki ba"
"wallahi ban iyaba, dan ban taɓayi ba, kaika fara Yimin"
"Nayi miki me?"
"Kiss mana" Yusuf yayi dariya sosai, ba ruwanta wasu lokutan sosai yake ganin ƙuruciya da kuma wautar Widad.
Yusuf yace "Nima a nan na koya, ai"
Tace "Kai dai ka sani"
Murmushi yayi, ya samo wuƙa ya dinga sara mata raken ƙanana, tana ɗauka tana sha, seda suka gama shan rakensu tare, sunayi suna hira,
Yusuf yace "gaba ɗaya kayan ƙwalamar nan na gargajiya sunfi lafiya da inganta jikin ɗan adam, saɓanin artificial ones ɗin nan, suyi ta haddasa ciwo kala kala"
Widad tace "aikam dai suna da daɗi Sosai, dan bana missing chocolates da ice cream yanzu tunda ina cin waɗan nan"
Suka cigaba da hira, ba tare da sun yi faɗan da suka saba ba, bayan sun kammala Yusuf ya gyara gurin, yaje yayi wanka sannan itama ta ɗau bokiti taje ta karɓi ruwan wanka, Hari taita mita wai zuwa yanzu yaci ace Widad tana wanka da ruwan sanyi, amma dan gajeren fi'ili kullum se an bata ruwan ɗumi.
Widad bata saurareta ba ta tafi wankanta, bayan ta fito ta shiga ɗaki, ta ajiye bokitin ta nufi shimfiɗar ta domin sa kaya, tana hasakawa da fitila taga Yusuf kwance akan katifarta, daga shi se gajeren wando, ya lumshe ido da alama bacci nema ya ɗauke shi, da farko seda ta firgita ganin sankacecen mutum dogo kwance a gurin, daga baya kuma taga Yusuf ne.
Ƙafarsa ta haska taga ciwon da yaji yana warkewa a hankali, sannan ta hasak jikinsa, tun daga kansa har fuskarsa zuwa ƙirjinsa da ƙafafunsa, lulkuɓe suje da dogayen gashi.
Inda akwatinta suke a gefen Yusuf ne, gashi ya kwanta a gurin, kuma bata son ta tasheshi dan da alama a gajiye yake, ta zarwle hijjabin jikin ta ta shanya saboda a jiƙe yake da ruwan wanka, tazo ta zauna kusa da Yusuf tana son ta ɗakko Akwatin, amma se taga kamar ze tashi, ta ɗan ƙura masa ido, duk ya rame se dogon hancinsa da yake tsaye kyam, ga ƙasumba data fara fito masa wadda da bashi da ita (kasancwarsa jam'in tsaro, basa tara gemu) .
A hankali hannunta yana rawa, ta kai hannunta kan sajensa, wanda yake a kwance kamar na Fulani, a hankali ta dinga shafa gashin ta gangaro har ƙirjinsa inda gashin yafi yawa, ta dinga wasa da gashin a hankali, tana yi tana zancen zuci, yunƙurawa tayi zata ɗauke hannunta taji ya riƙe hannunta, zaro ido tayi a firgice tace "dama idonka biyu?"
Gaba ɗaya ya janyo ta jikinsa, ya kwantar da ita akan katifar, yace "me kike yi ne tun ɗazu? Duk abunda kike ina jinki fa"
Haɗe rai tayi tace "ɗagani Malam, wai baka san kana da nauyi bane?"
"Ya za'ayi in sani, kin zauna tun ɗazu se taɓani kike"
"jika wai se taɓaka nake, me zan taɓa wannan gashin daka tara duk abun ƙyama ma, abun amai shine ɗin zan taɓa, ni cikani in sa kaya, kar towel ɗina ya cire"
Dariya yayi, ya haska fuskarta da fitila yace "meye abun ƙyamar? Gashin jikin nawane abun ƙyama ko kume me?"
Rufe idonta tayi tana tura baki, ya kama hannuta ya ɗora akan Ƙirjinsa, yace "da abun ƙyamane dabe burgeki kin taɓa ba"
Tace "meye abun burgewa anan, sakarmin hannuna ko in tsige gashin nan ɗaya bayan ɗaya"
"gaki na gashi ai, yi yadda kike so dashi my Queen naki ne ai"
"Sarkin daɗin baki, da zakayi politics se an zaɓeka saboda wannan daɗin bakin naka"
A kunnenta yace "ko banyi politics ba, dama ban iyaba amma ina fatan ki zaɓeni a matsayin abokin rayuwarki Weeeedaat, ina sonki masoyiyya ta, na taɓa soyayya a baya amma yanzu nake gane a baya shirme nayi, yanzu ne nake Soyayya, saboda ban san takamaimai a ina nake jin sonki a cikin zuciya ta ba"
Shiru tayi ta ƙanƙame Yusuf tana saurare kalaman da yake gayamata, sedai tun ba'aje ko ina ba, al'amarin ya fara canza salo zuwa wani abu daban, da fari kamar Widad zata dake daga baya kuma tace bata san zance ba, ta tubure masa gaba ɗaya, but Yusuf he shows her the superiority of a Man.
Tashi tayi zaune, ta janyo bargo ta rufe jikinta, tana neman towel ɗinta, yana daga kwance ya kai hannu ze taɓa ta Amma ta bige hnnunsa, tana ta faman zumɓura baki, zaune ya tashi shima zeyi magana, amma ta fashe da kuka.
yace "Am sorry please, dan Allah kiyi haƙuri, is not intentionally kuskurene mun riga munyi shi sedai.. "
Katseshi tayi ta hanyar cewa "eh dama is not intentionally mana, tunda maye kake, kullum haka kake cemin is wasn't intentionally kuma bayan kana sane, kuma karka sake cewa munyi kuskure kayi dai"
Yusuf yace "jimin mara kunya, amma ina kwance kika zo inda nake ai"
"kazo inda nake dai, waye yace kazo ka kwantamin akan katifata?"
"Amma dana kwanta akan katifarki, shine akace ki zauna kina taɓani?"
Rasa me zata ce tayi, kawai ta fashe da kuka Yusuf ya lura kukan Shagwaɓa ne kawai takeji, amma yace "shikenan am sorry, ya isa haka kukan, ba zata sake faruwa ba, semu kiyaye gaba"
Ƙwacewa tayi daga jikinsa tace "ka kiyaye gaba dai, kawai nayi wanka na zan kwanta, kawai ka ɓatamin"
Ta cigaba da ƙunƙuninta, ta miƙe ta sake zura hijjabi tayi waje, yayin da Yusuf ya koma ya kwanta yana murmushi, dan shi wasu lokutan wannan rigimar tata birge shi take.
Taje bakin rumfar da ake girki ta tsaya daga baya, Hari tayi daren Abinci tana ta tankaɗe zata tuƙa tuwo, Widad tace "a zubamun ruwa zan wanka"
Ta ɗago ta kalli Widad tace "sannu Agwagwa, ko kuma ince tarwaɗa sarkin wanka, ba ɗazu Yaya ta zuba miki ruwan kikayi wanka ba?"
"Eh wani zan kumayi" Widad ta bata amsa
"waike sau nawa kike wanka a rana ne? Ke ko ɗan tsallaken nan bakya yi, kullum se kinyi wanka, ni a rana ma bansan sau nawa kike wankan ba, kuma yanzu ko Awa biyu ba'ayi da wankan naki ba kin kuma ɗakko bokiti kin dawo"
Widad tace "Allah ya kiyaye inyi fashin wanka, an gayamiki kowa irinki ne? Kawai mutum ya zauna be wanka ba har ya kwana ya tashi, ni ki zubamin dan Allah"
Hari tace "ko dame kike yawo bazan baki ruwan nan ba, wannan wane irin wanka ne sekace me iskokai?"
"Zaki zubamin ruwan ko sena gayamiki abunda yasa zan kuma wankan?"
"Ina ruwana da abunda yasa zaki sake wanka, keta shafa mace sekace wata kifi kullum cikin ta'annati da ruwa, ba dare ba rana, haba ni matsa ki bani guri"
"Hari za'aji kanmu dake a daren nan fa, kin fiye samun ido da shisshigi gaskiya, zuciya ta na gaya min in faɗi wani abu"
Hari tace "aike in mutum ya biye miki yana tsaye ze bar musulunci seya sake wankan shiga musulunci"
Widad ta nemi guri ta zauna a tsakar gidan, Hari ta tashi taje ɗaki ɗakko abu, dukda Widad bata san hayaƙi haka ta toshe hanci, taje gaban murhun ta ɗebi ruwanta ta ƙara gaba.
Hari na fitowa taga Widad ta kwashe ruwa fiye da rabi, nan ta tsaya ta dinga zazzaga masifa, Widad ta fito ko takanta bata bi ba tai wucewarta ɗakinsu.
Gwaggo ce taita bawa Hari haƙuri, saboda yadda ta wage maƙogoro tana ta zazzaga bala'i a daren nan, kuma Widad ta shareta tana ta surutu.
Wani daddaɗan bacci ne yayi awon gaba da Yusuf, dan duk neman maganar data fita tayi be sani ba, kallonsa tayi taga baccinsa ma yake yi.
"Tasarmin daga kan katifa, zan saka kaya in kwanta" tai maganar tana dukan filon da yake kai, a hankali ya motsa, ba tare da yace komai ba ya miƙe ya bata guri, shima ya fita dan yin wankan, ba tare da yasan me Widad ɗin taje ta aikata ba.
Umman Yusuf tana zaune tana lazimi, ta kunna radio, dan gaba ɗaya ji take duniyar ta mata faɗi saboda rashin Yusuf a gidan, ba ta jin daɗin komai, ji take ta rasa wani sashi me girma, Tana ta laziminta hankalinta ya ɗauke, jin an ambaci cikakken Sunan Yusuf a radio yasa ta dawo daga tunanin da take yi, ta maida hankalinta kan radion ta ɗakkota ta ƙaro sautin.
Rahoton da aka faɗane na bincike ya tabattar da Yusuf ne yai garkuwa da Widad dan ya karɓi kuɗin fansa yasa tayi jifa da radion a gigice, jikinta ya hau rawa, take ta fashe da kuka tana girgiza kai, cikin kuka tace
"baze yuwu ba, Yusuf ɗina ba haka yake ba, ni ɗana baze taɓa aikata wannan mummunan aikin ba, innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wayyo Allah ɗana, wayyo Yusuf aikin ɗan sand be maka rana ba, wannan aiki da kayi yayi silar rushewar farincikinmh, yau nayi baƙinciki fiye da wanda muka rayu a ciki ni da kai, wayyo Allah ɗana, Allah ka kuɓutarmin da Yusuf "
Sosai take kuka, kamar zata shiɗe haka tayi zaman daɓaro tana ta rusa uban kuka babu me rarrashinta, gwanin ban tausayi.
Amal idanunta har sun kumbura saboda kukan da tayi, Hajiya Halima ta shigo ɗakin ta tarar da ita tace " Haba Autan Mummy, kukan ne har yanzu baki dena ba, haba Amal ɗina"
Tai maganar tana rungume Amal a jikinta, ta cigaba da cewa "haba Amal, meye abun kuka, dan Allah ki cire yaron nan daga ranki, kinfi son Asirin Mummy ya tonu a idon duniya? Kin san bani kaɗai ba har ku ta shafa, duk fafatukar nan da nake danku nake yi"
Amal tace "Mummy, nasani amma abun yayi yawane, haba Mummy ki duba lamarin nan fa ki gani, Abunda akayiwa Yusuf yayi yawa Mummy"
Hajiya Halima tace "ke bafa sharri akayi masa ba, tunda akace ya gudu daga hannun wancan mutanen meyasa basu dawo ba? Kina ta kuka akansa, shi kuma ba kya gabansa sam, kina kallon yadda ya dinga yanƙwanaki, yana wulaƙantaki shida waccan fitsararriyar mara mutuncin, suka dinga wulaƙantaki bama ke kaɗaiba harni ba kunya ba tsoron Allah suka dinga cin mutuncinmu, dan haka meye a ciki dan suma an musu? Ki dena kukan nan kinji, ki share hawayenki, danku nake wannan faɗi tashin, ki dena kuka kina ɗagamin hankali kinji"
Amal ta jinjina kai, tana share hawayen Fuskarta.
Haka nan Yusuf yaji jikinsa yayi sanyi, kamar wani abu yana faruwa, jiki a sanyaye yaje yayi wanka ya dawo ɗaki, Hari tana ganin ya shiga banɗaki da bokiti tace
"la'ilahaillalah, ta tabatta Wudas bata da kunya yarinyar nan, innalillahi kai Allah yayi mana maganin wannan zamani, Taɓɗijan ashe abunda yasa ba yau gobe cikin sintirin banɗaki take yin wanka, to Allah ya maganta"
Babban abun takaicin, Hari ba a hankali take magana ba, Yusuf ji yayi kamar karya fito daga banɗakin nan saboda nauyin maganganun Hari, a matuƙar kunyace ya fito ya wuce ɗakinsu, Widad ta lura kamar jikin Yusuf a sanyaye yake, kamar wani abu yana damunsa.
Yazo ze ɗauki kayan shimfiɗarsa, yaji ta kira sunansa "Yoseef"
Ya amsa da "Na'am"
Widad ta tashi zaune tace "meyafaru ne?"
"Me kika gani?"
"Naga kamar kana da damuwa ne, wani abu yana damunka"
Murmushi yayi yace "bakomai, yi kwanciyarki kawai"
"Yoseef" ta kuma kiran sunansa
Ya sake amsa mata kamar ɗazu.
"Dan Allah ka gayamin abunda yake damunka, zaka sani a damuwa fa"
Yaji daɗi a ransa, da yaga ta damu da damuwarsa, "kece kike ganin wani abu yana damuna, ni lafiya ƙalau nake"
Harya juya ze tafi inda yake kwanciya, yaji ta riƙe rigarsa, tsayawa yayi ya juyo yaga ta zuba masa ido.
Zama yayi akan katifar yace "ya akayi kuma?"
"Yoseef, ba yau nafara ganinka ba, ina gane fushinka ko damuwa, just recently kake walawala, suddenly kuma mood ɗinka ya canza, me nayi maka?"
"Ni ba abunda kikamin banda bani joy da happiness i ever expected to get"
Yai maganar yana jan hancinta, "kana son ka koma gida ko? Nima na damu mu koma dukda ina jin daɗin zaman gurin yanzu, amma ina kewar Daddy sosai"
Gyara zamansa yayi yace "Dole ne muyi kewar iyayenmu da masoya Widad, kasancewar ƙaddararki na kamanceceniya da tawa, sedai sun sha banban, Akwai dalilin da yasa Allah ya haɗamu a nan, se mucigaba da haƙuri muga hukuncin da Allah zeyi, amma ni ba abunda kika yi min kinji masoyiyya, ni farinciki kika bani ma, wanda baze taɓa gogewa a zuciyata ba, I love you so much Baby "
Yai maganar yana rungumeta, ba tace komai ba se murmushi da tayi, Yusuf yana daga cikin mutanen da bazata manta dasu ba a rayuwarta, dan Ya canza mata gurɓataccen tunaninta, yayi sadaukarwar da bata taɓa tunanin wani zeyi akanta ba, yana haƙuri da dukkan halinta me kyau ko akasin haka.
Ya nisa yace "bari in baki guri ki kwanta, nasan lokacin baccinki yayi"
Dukda a cikin duhu ne, amma ta niƙe kafaɗa tace "mu kwana anan tare mana"
Murmushi yayi yai ƙasa da muryarsa dai dai kunnenta yace "haka kawai inje wani abu yafaru, kiyi ta haɗemin rai kina hararata, yanzu ma ban san yadda akayi ba naga an ƙyaleni, dukda haka ban fidda ran da safe inga an ɗauremin fuska ba"
"Kai kuma abunda ke ranka kenan, nidai mu kwana tare kawai"
Yusuf ya gyara kwanciyarsa yace "as you wish your majesty, ni dama haka nakeso, saboda hakan yana ƙara danƙon soyayya a tsakanin ma'aurata"
Bata kula shi ba, sedai sake shigewa da tayi jikinsa sosai tana lumshe ido.
Yusuf yace "Babyna, baki ƙarasamun labarin nan bafa"
"shhh, lokacin bacci yayi kayi bacci kawai, bana son in ƙara maka damuwa"
"wai waye yace miki ina cikin damuwa ne?"
"Hmm Yoseef kenan, tunda kaƙi yadda ai shikenan"
Haka suka wanzu a haka, bacci ya ɗauke Widad yayin da Yusuf ya kasa samun nutsuwa, yana sake ji a jikinsa akwai wani abu mara daɗi dake faruwa a wani guri, wanda hakan ya shafeshi ko kuma ya shafi Widad.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
74_75
Yadda Uman Yusuf taga rana haka taga dare, gaba ɗaya ta rasa wanda zata kira ta gayawa halin da take ciki, unguwarsu kuwa tuni labari ya cikata, akan ga abunda Yusuf ya aikata, beji ba be gani ba an ɗaura masa mugun sharri, wasu suna ƙaryene, wasu suna ba'a shedar mutum.
Mata suka dinga shiga da nufin suyi mata jaje, hadda wanda tun ɓatan Yusuf basu yi mata jaje ba, se yanzu da wannan labarin ya fasu.
Saleh ne a office ɗin Suleiman, ya kai gwauro ya kai mari, ya kalli Suleiman yace "ni gaba ɗaya kaina ya rufe ruf, na rasa me yakamata inyi, gaba ɗaya mutanen nan sun shammaceni, banyi zaton ta nan zasu ɓullo ba, duk yadda nake tunanin zaluncinsu sun wuce nan, na rasa mema zanyi ko me zance"
Suleiman dake zaune akan kujera yai shiru, ya nisa ya ɗago daga jinginar da yayi yace "ni kaina bansan me zan iyayi ba, naje na samu Sp amma yaƙi saurarata, wai sakamakon da aka bashi shiya sanar, nabi duk nayi ƙoƙarin da zan iya, na tuntuɓi masu ruwa da tsaki akan abun, amma kowa ya nunamin ba ruwansa, ma'aikatan gidan nan gaba ɗaya hankalin mu a tashe yake, kuma nasan muddin mukayi wani yunƙuri, to muma baza'a barmu ba, zasu ɗau mataki akanmu ne, amma yanzu meye abunyi? "
Saleh yace " Abunyi be wuce inje in ƙara tabattar da na toshe duk wata kafa, wadda zata sa a gane inda suke ba, sannan in ja masa kunne da wannan uwar taurin kan yarinyar, akan duk tsanani karsu sake su bar gurin nan, idan har bani ne naje nace su baro gurin ba"
Suleiman yace "gaskiya, ka gaggauta zuwa ka same su kam, sannan ni gaba ɗaya kunyar mahaifiyar Yusuf nake ji, ban san me zance mata akan wannan al'amarin ba, ni nake bata ƙwarin gwiwa akan ɓatan nan nasa, akazo kazo da labarin sun kuɓuta, amma still hankakinta a tashe yake, ban san ya zata yi ba idan ta samu wannan Mummunan labarin "
Saleh yace " dole zata damu sosai, Amma haka nan za'ayi ƙoƙari a kwantar mata da hankali, dan barinta haka babu me rareshinta shima wata babbar matsala ne"
Suleiman yace "hakane, ubangiji Allah ya shiga lamarin bayinsa, bari in tashi insha Allah zanje in gaisheta, a sake bata haƙuri da kwantar mata da hankali"
Daren Yau kusan kwana su Alhaji Haruna sukayi suna meeting, sunyi farincikin da jin mafitar da Bukar ya samo musu, dan ba suyi zaton irin wannan mafitar ze kawo musu ba, dan haka yanzu kallo ze koma ga sauraren 'yan sanda aga ta inda zasu fara kamo Yusuf.
Alhaji Musa yace "yanzu idan aka gano su, yaya zamuyi da wannan shu' umar yarinyar me jarababben taurin kan bala'i"
Alhaji Munir yace "kai dai bari, yau shekaru kusan goma muna bibiyar abun nan, amma 'yar masu baƙin halin yarinyar nan ta hana, ba abun mu kashe ta ba kuma muzo muyi biyu babu"
Alhaji Haruna yace "idan muka kashe ta ai kuma zamu tashi a tutar babu ne gaba ɗaya, ya zamana duk wannan wahalar ta tashi a banza, ai yadda naji Bukar yace, shi wannan ɗan sandan yaron da an kamosu shi zamu fara kawarwa, saboda Kasancewar sa tare da ita matsala ne a gare mu, idan aka kauda shi, itakuma tunda babu wanda yasan inda ubanta yake, zamuyi poisoning ɗinta ne, a fita da ita waje neman lafiya, idan yaso kodai ta faɗi inda suke kokuma a aikata"
Alhaji Munir yace "Amma fa kun san rashin sanin inda Daula yake, itama wata babbar barazana ce me zaman kanta, muna ruwa fa idan Daula ya bayyana bamu samu abun nan ba, yakamata ace mun san inda yake a hallaka shi tunda wuri"
Alhaji Musa yace "Ai ana nan kan bincike, an duƙufa sosai gurin gano inda yake, kuma akwai alamun nasara, sannan idan aka gano shi kasheshi kawai za'ayi, karma a ɓata lokaci, tunda dama an bada sanarwar duk wannan yaron shine yayi garkuwa dasu"
Alhaji Haruna yace "nifa a gurin nan kamar anyi wauta, in ba hakaba ta yaya za'ace waishi ne ya sace Daula, duk tsaron dake Asibitin nan"
Alhaji Musa yace "nima da nayi wannan tunanin, amma Bukar yace ya san abunda yasa yayi hakan, ni wai ya maganar wannan yaron da muka yi magana, Barrister Hafiz, har yanzu bece mana komai game da abunda suka yanke ba"
Alhaji Munir yace "Aishine, yau kusan sati biyu amma babu wani feedback, idan ba zasuyi ba kawai muje mu haɗo kai da banki, mu kunno wata wutar"
Alhaji Haruna yace "kamar yaya kenan?"
"Ahh ayi takkaddun boge mana, ace ana bin kasuwancinsa wasu mahaukatan kuɗi mana, idan yaso se muyi agreement da bankin, mu basu wani percentage"
Alhaji Musa yace "amma fa kasan Daula baya cin bashin banki?"
Munir yace "Nida kai muka san wannan, sauran mutane basu sani ba, dan haka muyi tunani akai, idan can baze samu ba se mubi nan, kasan na san Ambassador Auwal Inuwa, kuma kunsan suna da banki, komai zezo da sauƙi"
Haka suka cigaba da ƙulla tsiyatakunsu, kala kala babu ko tsoron Allah a ransu.
Nurat a wuni ɗaya amma gaba ɗaya ta zube ta rame saboda zunzurutun damuwa da tunani, tana tunanin irin hukuncin da za'ayiwa Yusuf idan har aka gabatar da shi a gaban kotu, tana tunanin wannan zalunci ace an sace mutum, kuma a koma da baya a ɗora masa laifin da hukuncunsa daze iya sanadiyyar ɓata feature ɗinsa, tunani ta shiga yi, me za tayi wanda zesa ta samu abunda zata taimaki Yusuf dashi idan buƙatar hakan ta taso?
Ta ɗakko wayarta ta kira Anwar, sedai wayarsa bata shiga sam, ta kuma jarraba layin Khalil amma shima se ace mata busy, ƙarshe dai se haƙura tayi ta ajiye wayar ta maida kai ta kwanta.
Yanzu ɗaliban Widad in sunzo, suke mata wanke wanke da shara, dukda ta nuna bata so amma sesu dage se sunyi, suna matuƙar sonta, dukda bata da fuska amma tana jansu a jiki tana koya musu abubuwa da dama.
Yau Habi ce ta taho mata da soyayyiyar gyɗa me ɓawo, kusan kwano guda tace babarta ce ta kawo mata, Widad tace "Aini dan Allah nake koyar daku, ba dan ku bani wani abuba, ina dai roƙonku ku dingamin addu'a, amma ni base kun biyani ba, kuma duk wanda yake sha'awar koyar wani abu, ko abunda nake koya muku ƙofata a buɗe yake yazo ya koya"
Gwaggo tace "Amarya ba kyau maida hannun kyauta, ai basu isa sun biyaki abunda kike koyar dasu ba, jin daɗin abunda kike musu ne yasa suka baki, ki karɓa kawai"
Habi tace "yawwa Gwaggo, wallahi ba zamu biyata ba kam, amma dan Allah malama ki karɓa"
Da ƙyar dan Gwaggo tasa baki sannan ta karɓa, bayan tafiyar su Gwaggo ta cigaba dayi mata nasiha, na cewar zasu ga kamar wulaƙanci ne yasa bata karɓar abu idan sun bata.
Tafiyarsu keda Wuya kuma, megari ya shigo, yanzu Widad tana sakin jiki ta gaisheshi, harma wasu lokutan ya dinga tsokanar ta, ya shigo yara suka biyoshi da manyan ƙwarya, ɗaya an shaƙeta da ƙwan zabo, ɗaya kuma Nono ne a ciki, megari yasa Hindu ta kira Widad, ta fito suka gaisa yace "Nasan Malam Yusuf be dawo ba, ga wannan inji ɗalibansa suka ce a bashi"
Abun ya bawa Widad mamaki, mutanen ƙauyen nan sudai suna girmama malamai, kuma suna da rige rigen son suga sun kyautatawa mutane, saɓanin irin rayuwar da ake a birni, mutum yana ganin ɗanuwansa a matsala amma ya share, koma a haɗa kai dashi a cutar da mutum.
Widad ta karɓi kayan tace "to Baba, Yoseef ya gode sosai zan gaya masa idan ya dawo"
Megari yayi murmushi yace "bagwariyar 'yata, Yusuf ake cewa ba Yoseefa ba"
Widad tayi murmushi tace "na kasa gyarawa, kuma shima ai yafison in ce masa Yoseef ɗin, kona fara cewa Yusuf se in manta"
Megari yace "Ahh masha Allah, tunda me gidan da kansa haka yakeso gara a kira shi da hakan"
Widad ta ɗau kayan zuwa ɗakinsu, Hari tace "wai me gida duk kayan nasu ne gaba ɗaya mu kuma fa?"
Yace "ke dai Allah ya shiryeki, nan har siyar da ƙwan zabo kike a gidan nan dana kaji, baki taɓa dafawa kin bawa kowa ɗaya a gidan nan ba, a gabanki dai na faɗa nace ɗalibai da yake koyar damu a masallaci sune sukace a bashi, zalamammiya kawai"
Ya wuce ɗakinsa yana cigaba da mita, Widad taje ta samu guri a ɗakinta ta ɗauki gyaɗar da aka bata tana ci, Yusuf ya dawo ya tarar da ita.
"Gimbiya yau kuma me aka samu haka?"
"Gyaɗa aka bani"
"kuma haka ake cin gyaɗar?"
Raba gyaɗar take biyu da bakinta, idan ta fito shikenan, idan bata fito ba ta haɗa da ɓawaonta ta cinye kayarta.
Seda Yusuf yaci dariya sannan ya nuna mata yadda ake ci, tace "ga wannan kayan, Megari ya bani yace a baka inji ɗaliban ka"
Yusuf ya kalli yawan Nonon nan da ƙwan zabi aƙall zeyi guda hamsin, yanzu ma a hanya wani ya tareshi ya bashi Albasa.
Yusuf ya jinjina kai yace "Ni wallahi kunyar karɓar kayan nan nakeji Widad, nifa saboda Allah nake koyar dasu"
Widad tace "nima kaga duk yawan gyaɗar nan haka suka bani, nace bazan karɓa ba Mama taitamin faɗa"
Yusuf yace "gaskiya zan mayar, abun yayi yawa ai"
Widad ta Harare shi tace "ai sedai ka maida wannan albasar, amma baza'a maida wannan ƙwan da madarar nan ba"
Yusuf yace "kaga kwaɗayayyiya"
"Eh naji, kawai kaje kace mungode"
Yusuf yayi murmushi yace "wai yau uwa ɗakina aka bawa kyauta ta karɓa, har take baza'a mayar ba, saɓanin da kana bata abu zata ce ka rainata, ko zaka cutar da ita"
Widad ta ɗan ja ajiyar zuciya tace "baka manta faɗanmu akan kayan daka bani ba ko?"
Yusuf yace "ya za'ayi in manta? Sedai ya wuce a ai"
"daka san faɗan da Daddy yayi min akan abun da nayi seka yi mamaki, kamar ze dakeni, shi dai Daddy a rayuwar sa kar a wulaƙanta Yusuf, kar a ɓatawa me suna Yusuf rai, ya ƙwace kayan yace shi yana so, bayan ya fita naje na ɗauke abuna, na saka rigar saboda hankalinsa ya kwanta ya dena fushi dani, sedai daya ganni a cikin kayan seda yayi kuka, kasancewar Ammi na matuƙar son irin wannan shigar tasu ta dogayen riguna"
Yusuf yace "Allah sarki, ubangiji Allah yayi mata rahama"
Widad tace "Ameen"
"Amma yaushe zaki ƙarasamin labarin ne?"
"ba rana ba wata" tai maganar tana miƙewa.
Yusuf yaje yayi musu godiya da karamcin nan da suka yi masa, suka ce yafi ƙarfin haka a gurinsu, tunda yake koya musu karatu ai ya gama musu komai.
Yusuf haka ya karkasa kayan nan, yayi rabonsu a cikin gidan nan, Widad kam taji daɗin ƙwan nan da Nono, dan Abinci ma seta ga dama take ci.
A hankali ɗaliban Widad suka ƙara yawa, harda ƙana nan yara, ta koya musu na boko ta koya musu na Addini.
Yauma wajen ƙarfe biyar na Yamma, tana ƙoƙarin sallamar ɗalibanta ƙananan yara, sega Saleh yazo, Kallo ɗaya Widad tayi masa ta ɗauke kanta, jin Sallamar wasu ne yasa ta sake ɗaga kai ta kalle su, Saleh ne shida wani mutum, da wata mace da manyan Akwatunan su.
Mutan gidan ne suka ruɗe da shewa ganin mutanen da suka shigo tare da Saleh, da alama dai sun san mutanen, Maida kai Widad tayi ta cigaba da abunda take.
Matar ba zata wuce shekaru Ashirin ba, ta kalli Widad tace "Gwaggo ina muka samu balarabiya ne?"
Gwaggo tace "'yata ce itama, Allah ya bani"
Wadda suka kira da Jamila tun shigowarta, yara suka karɓi jaririyar bayan ta, ta kalli Widad tace "Sannunki" kallonta kawai Widad tayi tai shiru.
Jamila tace "ko bata jin Hausa ne?"
Hari tace "iya shege ne, tana ji sarai kulaki ne da ba zata yi ba, haka take wannan wulaƙancin"
Saleh ya kalli Widad yace "Barka da yammaci ranki ya daɗe"
Yanzu ma kallon Saleh tayi ta ɗauke kai, yai murmushi yace "Ina Yusuf ɗin yake ne?"
Ai kamar da yana magana da dutse, wanda suka shigo tare da Saleh yace "to wannan da alama 'yar Mulki ce dai"
Ƙarshe da Widad taga zasu takura mata gaba ɗaya seta bar musu tsakargidan ma, ta koma ɗaki.
Baƙin nan suka shiga ɗakin Gwaggo, suka ajijiye kayansu, mutan gidan sunata farincikin ganin Jamila, da mijinta da kuma jaririyarsu.
Saleh da mijin Jamila wato Sunusi, suka shiga turakar megari, bayan ya sallami baƙinsa ya shigo ya tarar dasu, megari yayi murmushi yace "Soja marmari daga nesa, ya akayi kuka haɗu?"
Saleh yace "A tasha na gano su sunzo hutu, muka hawo akorikurar shu'aibu tare ya kawomu gida"
Megari yace "Madalla, ya Jamilar ya meɗakin nawa?"
Sunusi yace "duk muna lafiya, gamu munzo muyi muku hutu"
"eh babu laifi, amma Nasan kun kwasarwa yarinyar nan iskar hanya, dan ko Arba'in basu rufa ba"
Sunusi yace "Baffa ya za'ayi, ta matsa ita dai tazo gida, kasan can inda muke babu hausawa sosai, zaman se a hankali gaba ɗaya"
Megari yace "hakane, Allah yayi mana jagora gaba ɗaya, Saleh ya ka baro binni, da mutan kanon Dabo?"
"kowa lafiya ƙalau, na shigo ma ban tarar da Yusuf ba, se ita matar tasa, nayi magana kuma ta shareni"
Megari yace "Malam Yusufa be dawo ba ai, aini tunda nake ban taɓa ganin Yarinya meji da isa kamarta ba, akwai mulki kam, ni kaina na daɗe bata saba dani ba, ko gaisheni ba tayi, ba ruwanta da kowa daga mijinta se Hassana (Gwaggo), se a hankali kuma ta fara sabawa dasu Hindu, se daga baya kuma na gane ɗabi'arta ce rashin yadda da saurin sabo, amma tana da kirki sosai "
Saleh yace " Ai Baffa baka ga komai ba, in dai mulki da ji da kaine, ba abunda ka gani, yanzu ai ta sakko ta saki jiki daku sosai, Amma ai bata da yadda sam"
Sunusi yace "to meyasa, nima daga zuwana na gani, Jamila na mata magana tayi banza da ita, kaima kayi mata ta share"
Saleh yace "idan na gaya maka wacece ita, seka riƙe baki abar maganar kawai"
Megari yace "waini yaushe zasu tafi ne?"
"Ka gaji da zama da sune?"
"Haba wane mutum, aini zuwansu garina Alkhairi ne wallahi, basu takurani ba sam, sedai ina tunanin kana ganin babu wata matsala zamansu anan ɗin, nifa matsala ce bana so"
Saleh ya nisa yace "babu wata matsala Insha Allah Baffa, amma zamansu anan shine tsira da rayuwarsu, zuwa wani ɗan lokaci insha Allah zasu bar nan, ni dai fatana a cigaba da haƙuri dasu"
"Saleh aini zuwansu nan alkhairi ne, baka tarar da yara gidan nan ba? Da Asuba ko magariba shi Yusuf ya koyar da karatun Addini, gashi da ladabi, ba hantara ba cin mutunci yake gyaramana kwaɓar da mukeyi, da Yamma kuma ita ke koyar da yaranmu darussan boko, da Addini, kasan mu babu makarantu haka na muke zaune da jahilci se ɗan abunda ba'a rasa ba"
Saleh ya jinjina kai yace "Yanzu, ita ke koyar da yara karatun?"
"daka shigo ba kaga yara da 'yan mata a gidan nan ba, dukda gidan nan na mutane ne amma karatu take koya musu"
Saleh yace "Allah sarki rayuwa"
Se daf da magariba sannan Yusuf ya dawo, Yusuf be tarar da Saleh ba dan haka ya gaisa da su Hari ya wuce ɗaki, yana zuwa ya tarar da gimbiyar ta cika tayi fam, kallo ɗaya yayi mata yace "Subhanallah, me kuma ya faru? Ko nine na miki wani abu?"
Girgiza masa kai tayi tace "A'a, Saleh ne yazo na ganshi shi da wasu, na kasa yadda hankalina yaƙi kwanciya, ban san suwaye ba"
"To shine zaki ɗaga hankalin ki haka? Ki bari muji ta bakinsa mana"
"A'a, nifa bana son irin wannan abun, ko dai musan suwaye, ko kuma wallahi bazan kuma kwana a garin nan ba, komai dare sena bar garin nan"
Yusuf yace "yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, zan masa magana idan mun haɗu a gurin salla"
Bata son tayarwa da Yusuf hankali, shiyasa ta ƙyaleshi, kamar yadda ya zata sun haɗu da Saleh a masallaci, bayan sun idar da salla, suka gaisa Yusuf yace "kwana biyu, yau kusan watanka guda rabonka damu"
Saleh yace "wallahi kuwa, abubuwa ne sun ɗanmin yawa, ai ɗazu naga gimbiyar taka, na mata magana juyin duniya taƙi kulani, a gaban mutane"
Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "kasan dama kuna takun saƙa da ita, kuma ta ganka da baƙi bata san kosu waye ba, dole ba zata kulaka ba"
Yace "hakane, amma duk da haka yakamata ko gaisawa muyi, ina gaisheta amma ko kallo ban isheta ba"
Yusuf yace "Allah ya baka haƙuri, zata gyara insha Allah"
'hmmm Yusuf kenan, in dai wannan ce babu ranar gyarawa, baƙin da take magana kuma ba wasu bane, mata da miji ne, namijin shima ɗan megarine, matar ma kusan haka, ya tashi da' yan fitintunu ne baya ji, ga yawon tsiya se a shafe watanni uku huɗu, ba a ganshi ba, shine na ɗauke shi na kai shi makarantar horar da sojoji, to beyi karatun boko ba, dan haka kurtu ne yana barrack suna gadin gidan wani babban hafsin soja, shine yayi Aure ya tafi da matar, yanzuma ya samu hutun ƙarshen shekara ne, ga matar ta haihu shine muka haɗu a tasha sunzo gida, suyi hutunsu a nan amma banda haka babu wani abu, amma kai ɗan sanda ne ai, zaka iya bincikawa"
Yusuf yace "A'a babu buƙatar hakan, gara ta sanine ai, kasan bata da yadda"
"hakane amma ita nata yayi yawa ne"
"Hakane, amma ayi haƙuri dai, yanzu meye labari? Ya ake ciki a gida?"
Saleh ya ɗanyi shiru sannan yace "Yusuf labari ba daɗi kama, sedai fatan ubangiji Allah ya shiga lamarin"
"Saleh, dan Allah kamin bayani gwari gwari mana, ban gane labari babu daɗi ba, aani abune ya samu Ummana? Ko mahaifin Widad? Ko kuma wata matsalarce ka gayamin mana"
Saleh yace "kwantar da hankalinka babu ɗaya, mahaifin Widad dai kamar yadda ka sani, har yanzun babu wanda yasan inda yake se Allah, ana ta bincike amma shiru, ko yana hannunsu, ko yana wani gurin Allah ne mafi sanin wannan, sannan mahaifiyarka tana lafiya, mun rabu da Suleiman akan zeje ya gaishe ta ma, sedai....... " Se kuma yayi shiru.
" Se kuma me? Dan Allah ka gayamin kana ɗagamin hankali fa"
"Yusuf jin meke faruwa bashi da wani amfani a gareka, abun da nake so da kai shine, kayi taka tsantsan gurin zuwa cin kasuwar nan da kake yi, sannan ka ƙara tsananta Addu'a, kuyi haƙuri kunci gaba da zama anan, dan sun saka a nemoku duk inda kuke"
Yusuf ya dafe kai yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yanzu meye abunyi? Zuwa yaushe ne zamanmu ze ƙare anan, kar mu takurawa mutan gidan, sannan kuma cigaban zamana da Widad a inuwar Aure shima matsala ne babba, babu wanda yasan batun Aure mukayi se kai"
Saleh yace "batun takura, baku takura musu ba, dan munyi magana da megari, sannan Aurenku aini na san anyi, ina da sheda, kawai Allah yasa ku kawai Daula jika"
"Saleh, why are you not serious about this issue? Bafa abun wasa bane, wani irin kallo mahaifinta zemin, wani suna ze kirani dashi idan har muka koma gida da ɗa?"
"Ahh kallon siriki ze maka mana, karka damu Daula ba baƙon zafi bane, idan har 'yarsa tana ƙaunarka, kaje ka tabattar da irin son da take maka tukuna, nidai fatana iya wuya, idan bani nazo nace kubar gurin nan ba, kuyi zamanku anan, ka koma maza karta fara zargin wani abu "
Har Yusuf ya shiga cikin gidan jikinsa a mace yake, gaba ɗaya ya easa meye yake masa daɗi, Saleh ya sake dagula masa lissafi, yanzu idan aka gano inda suke shida Widad meye sunansa? Idan ya kasance Widad ta samu juna biyu meye makomar yaron, sannan yayi mata adalci makuwa, idan har ya bari suka haɗa zuriya da ita, bayan bata san shi waye ba, ba tasan mecece tasa ƙaddarar ba balle yaji hukuncin da zata ɗauka akansa? Baya tunanin ɗorewar Alaƙa a tsakaninsu muddin taji waye shi, ba ita ba hatta mahaifinta baze farinciki ya zamo siriki a gareshi ba.
0 comments:
Post a Comment