"Meya gaya maka haka, wanda ya jefa ka cikin wannan dogon tunanin?" yaji muryar Widad.
"Bakomai" ya bata amsa
"Har yanzu fa ban canza daga Widad ɗin daka sani ba, bana son ƙarya bana son ɓoye ɓoye, ka gayamin tun kafin kaima in saka a Jerin wanda nake zargi"
Ya kalle ta yace "zargin me kenan?"
"zargin zaku haɗa kai ku cutar dani, in ba haka ba, meye na ɓoyemin wasu abubuwan da dole nasan sun shafi rayuwata?"
Yusuf ya kalle ta yace "har yanzu kina tunanin zan iya kasancewa cikin masu cutar dake?"
"Yoseef, zuciya bata da ƙashi ya kamata kamin uzuri, musamman a irin rayuwar da na tsinci kaina, amma ya kamata in dinga sanin al'amuran da suka shafeni"
"Ba wani abu bane, dama ya gayamin muƙara haƙuri da zama anan ne, saboda ana can ana nemanmu, maƙiyanki sun baza komar anemomu, tunda tuni labarin guduwarmu ya iskesu, sannan baƙon da suka zo tare, shima ɗan uwansane, soja ne sunzo hutune shida matarsa, shikenan "
Ba tayi magana ba, se riƙe gashin kanta da tayi, sekuma ta shiga jan numfashi tana zazzare ido, ta dunƙule hannunta, tana girgiza kai.
A Rikice Yusuf yace " Subhanallah, lafiyar ki kuwa Widad? Meyafaru? "
Girgiza kai take hawaye na zuba daga idonta tace " almost ten years, good ten years ana cutar dani, bani kaɗaiba har wanda ya raɓeni, yana ɗaya daga abunda ya nesanta ni daga mutane, bana son rayuwar wani ta shiga matsala saboda ni, amma ƙaddara ta haɗa rayuwarka da tawa kana ta faman wahala, an cutar dani an kassara lafiyata, an cigaba da bin diddigina ana son ganin bayana saboda abun duniya, kuma aka jefa ƙiyayyata a zukatan jama'a suka koma gefe suna zagin AƘIDATA, Insha Allah bazan mutu ba sena ga bayan maƙiyana, ko kuma mu yi mutuwar kasko nida su, i can't tolerate it anymore "
Tai maganar tana jifa da kayan gurin, sannan ta yunƙura zata miƙe, Yusuf ya riƙeta gama, fizge fizge ta dingayi tana kai masa duka tana nema ta ƙwace daga hannunsa, ya riƙeta sosai yana mata addu'a, surutai take sosai cikin ɗaga murya, idan Yusuf yasa hannu ya toshe mata baki, se taita kai masa duka, idan ya riƙe hannunta kuma seta hau surutai, yana gudun hankalin mutane ya dawo kansu, dan sam baya son wani yasan tana da larurar taɓin hankali, dan haka kawai ya haɗe bakinsa da nata.
Tun tana mimmiƙewa tana son ta ƙwace, harta gaji jikinta yayi sanyi, Numfashi take saukewa a hankali, hawaye na bin gefen idonta, seda yaga ta dena fizge fizgen sannan ya cire bakinsa daga nata, ta lumshe idonta kamar me bacci, Yusuf ya rungumeta yana cigaba da karanta mata duka Addu'ar da tazo bakinsa.
Widad ya kira sunanta, ɗaga masa hannu tayi alamar ya ƙyaleta, sun daɗe a haka sannan ta tashi zaune, Yusuf ya kalleta yace "Sannu"
Jinjina masa kai kawai tayi ta sunkuyar da kai, ya riƙe hannayenta yace "dan Allah kidena saka damuwa a ranki, kinga hakan yana shafar lafiyarki"
"bazan iya dena damuwa ba, saboda an diga an gama kassara rayuwata, bana jin zan samu nutsuwa har se ranar da na gamsu, na ɗau fansar abunda akayimin"
"Rayuwa ba zata tafi a haka ba, lafiyar ki abun dubawa ce, kalli yadda lokaci ɗaya kika fita hayyacinki fa"
"Ai dama ba lafiyar ce dani ba, dan haka ba wani abu dan na ƙarasa a haka"
Kawai ta rufe bakinta da hannunta tana kuka, Yusuf ya shiga share mata hawayenta, yana cewa "ke lafiyayyiya ce, kuma ina miki fatan samun lafiya me ɗorewa"
Tai murmushi me ciwo tace "wai in warke daga haukan? Ko ciwon zuciya?"
"Nifa ban yadda da wannan ciwon haukan ba"
Widad tace "yakamata ka yadda, ka sawa ranka kana zaune da mahaukaciyane"
Yusuf ya ɗanyi shiru sannan yace "nifa akwai ranar da naga an saka miki wata ƙwaya a cikin tea, amma baki sha ba, shiyasa nake da question mark akan wannan ciwon naki"
Seda tayi shiru na wasu lokuta, sannan ta gyara zamanta tace "Bayan an kashe Ammina, ɗaya daga cikin wannan mutanen, ya ɗakko wayarsa ya fara waya, yayi wayarsa ya gama sannan ya kalli sauran yace, ku cajemin gidan nan, akwai wata yarinya, ku kawomin ita nan, Widad na tsaye tana jinsu, bata ko motsa daga inda take ba, suka fito suka shiga bincike gidan nan, amma basu ga Widad ba, suka dawo sukace "mun caje ko ina a gidan nan bamu ga yarinyar nan ba"
Yace "ta yaya za kuce baku ganta ba, bayan tana cikin gidan nan?"
Suka haɗu har dashi suna dubawa, sun wuce ta inda Widad take yafi sau uku, amma Allah besa sun ganta ba.
Suka sauka ƙasa falo, babban ya sake kiran waya, ya sanar da wani cewar sun duba kaf basu ga Widad ba, kawai Widad ji tayi yace " An gama Oga.... "
Bata iya jin cikakken sunan daya faɗa ba, kamar taji dai dai kamar kuma ba daidai ba.
Babban yace "kai mu tafi, Oga yace yasan yadda zeyi da ita, mu ɓace kafin a gane munzo"
Haka suka rankaya suka fita, cikin sanɗa Widad ta sakko daga kan benen, ta sakko falo taje ta leƙa taga, taga sunyi maganganu da Bala, sannan ya buɗe musu ƙofa suka fita.
Widad ta juya ta koma kan bene, ta koma ɗakin da Amminta take cikin sauri, tana zuwa ta tarar da ita a yadda ta batta.
Widad ta shiga jijjigata tana kiran "Ammi ki tashi mutanen sun tafi, baki ji ciwo bako?"
Ganin Ammin nata bata motasa ba yasa tace "Ammina bacci kikayi ne? Ko kuma sanyi kike ji?"
Nanma bata samu amsa ba, dan haka ta ɗakko bargo ta lulluɓeta, itama ta shiga bargon ta rungume Ammin nata, daga nan bacci yayi awon gaba da ita.
Dukda Kasancewarta yarinya ƙarama, amma da Asuba Amminta ke tashinta salla, Asuba tayi Widad ta tashi taje tayi salla, Amma Amminta bata motsa ba, ta sake zuwa ta kwanta a jikin gawar ta koma bacci, har kusan ƙarfe tara na safe Widad ta farka, ta shiga girgiza gawar Ammin tana "Ammi ki tashi bakiyi salla ba, kuma yunwa nake ji, Ammina ki tashi ina jin yunwa, Ammi Abinci" haka Widad ta cigaba da hayyata irin tasu ta yara, ba tare da tasan Ammin mutuwa tayi ba.
Tana nan zaune, ta gaji ta shiga wasa da gashin kan Ammin nata, tana mata surutu ba tare da tasan mutuwa tayi ba.
Tana nan zaune Bala ya buɗe ɗakin ya shigo, ya kalli Widad yace "ke a ina kika kwana?"
Kallonsa Widad tayi ta ɗauke kai, ya kalli Gawar Huda dake kwance a gurin, ya juya ya fita.
Wajen ƙarfe sha ɗaya sega Bulama da wasu abokan kasuwancin Daula, suka shigo har ɗakin, Bulama ya kalli Huda ya shiga rangaɗa salati, ya kalli Bala yace " kuma ba rashin lafiya ce ta kamata cikin dare ba?"
Bala yace "nima ban sani ba, gani nai shiru banji motsinsu ba, shine na shiga dubawa, nazo na tarar da gawa da yarinya"
Bulama yayi ajiyar zuciya yace "Allah me iko, Allah yayi mata rahama amma abun da mamaki, munyi waya da Daula, lafiya ya tafi ya barsu, amma a wayi gari ta rasu, Allah kenan, yanzu dai a kira motar Asibiti aje da gawar a dubata a Asibiti, ita kuma daughter a tafi da ita gidana, zuwa muga yadda hali zeyi"
Widad ta dinga bin Bala da ido, tamkar bata taɓa ganinsa ba, duk inda ya motsa seta bishi da ido.
Aka ɗauketa aka tafi da ita gidan Bulama, aka tafi da gawar Huda Asibiti.
Tunda aka kai Widad gidan Bulama, ba tace uffan ba se kallonsu da take kamar baƙin halitta, aka bata Abinci harta fara ci, ta ture ta shiga kuka tana kiran Ammina.
Gaba ɗaya tausayinta, ya kama Hajiya Sarah, ta dinga rarrashin Widad amma fafur Widad taƙi yin shiru, Fahad yace "kai wannan wace irin jarabbabiyar yarinya ce, banza kawai ana ta magana ana rarrashin ta se wani iskanci take yi, shegiya kai me kama da Aljanu"
Fahad be rufe baki ba, Widad ta ɗauki wani kofin glass ta jefa masa, gaba ɗaya ta basu mamaki, suka juyo suna kallonta, kofin ya sameshi a ƙafa ya faɗi ya fashe, sannan kuma ta koma gefe tana kallonsa tana huci, kanta yayo ze maketa a zuciye, Hajiya Sarah ta tareshi tace
"yi haƙuri, marainiyar Allah ce, meyasa zaka zageta"
Fizgewa yayi ze daketa, amma Widad ta shammaceshi, ta kafa masa haƙora a hannu, da ƙyar aka ɓanɓareta dan seda gurin ya fashe.
Fahad ya dinga ihu yana "na shiga uku Mayya, 'yar gidan mayu zata shanye min jini"
Tun daga lokacin, ko hanya basa haɗawa da Widad, dan tunda ya zageta ta tsane shi, a wunin ranar nan gaba ɗaya suka rasa yadda za suyi da Widad, suka kasa gane kanta dan bata jin rarrashi, bata sanshi ba ga kafirin taurin kan masifa, taƙi cin Abinci taƙi saurarar kowa, da Hajiya Sarah ta gaji ta kira Bulama ta gaya masa, shi kuma yace ayiwa direbansa magana Fahad ya rako su Asibitin, dan Daula ya iso.
Fahad yace "Allah ya kiyaye in raka Mayya, wannan a binciki danginsu mayune, shegiya kawai"
Ƙarshe direba ne ya kai Widad Asibiti, bata tsaya jiran direban ba, ta shiga cikin Asibitin tana leƙe leƙe, ta buɗa wannan ƙofar ta buɗe waccan.
A saman bene ta buɗe wani ɗaki, taga su Bulama da Bala a ciki da wasu mutane, se Mahaifinta durƙushe a gaban gado an rufe gawa, yana rusar uban kuka kamar ƙaramin yaro, Widad ta tsaya tayi sak tana binsu da kallo, Daula na ɗaga ido yaga Widad ya sake fashewa da kuka, ya miƙowa Widad hannu, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta faɗa jikinsa, cikin kuka Daula yace "Lovely daughter, mun rasa Amminki, ta tafi ta barmu"
"Daddy ina Ammina"
Daula ya buɗe mata fuskar Huda, kamar kace mata tashi ta miƙe zaune.
"Your Mum is dead Daughter" yai maganar cikin kuka.
Zumbur Widad ta miƙe tsaye, tana kallon mahaifinta, idan bata manta ba ko a film da take kallo, when someone is dead, you won't see him again, that's mean her Ammi has gone, she won't see her again.
"Noooo Daddy, she's alive, she's not death!"
Wata irin ƙara tayi tana tirje tirje, ƙarshe se ɗaukarta akayi aka kaita pediatric, aka mata allurai, se bayan an kai Huda nakwancinta sannan Widad ta farka.
Amma tunda ta farka ba ummm ba umm, idonta a buɗe amma sam bata magana, bayan an dawo daga kai Huda, Daula se kuka yake yana sharɓe hawaye, Asibiti ya wuce gurin Widad ya tarar ta farka, su Bulama dai yana biye dashi dasu Bala, ya zauna ya rungume Widad a jikinsa, yana kuka yayin da Widad ta tsaida idonta akan Bala megadi, bata ko ƙyaftawa.
"Daddy, what exactly kills Ammi?" Tayi tambayar a bazata.
Daula yace "i don't actually know daughter, likitoci sunce ta samu cardiac failure ne"
"is a lie Daddy"
"How?"
"someone sponsored her murder, she was killed Daddy"
Daula yace "what are you trying to say?"
Mamaki ya cika su yadda take magana, sekace wata babba, kuma she's very serious about what she says "
Alhaji Munir yace " ranka ya daɗe, yakamata fa muje gida, mutane na jiranka.
Haka suka tafi da gida, Daula na cigaba da kuka wiwi, Bulama da sauran mutane suka raka shi gida, har an kafa manyan rumfuna, manyan mutane gaba ɗaya sun hallara, anata miƙo gaisuwa.
Daula na rungume da Widad a jikinsa, Widad gani take kamar ƙaryane wai Ammi ta mutu.
Seda ta kwana biyu cirr ko gyangyaɗi ba tayi ba, hakan ya firgita Daula kar wani abu ya sameta, ya fara tunanin ko Asibiti ze maida ita, dan seta wuni ba tace uffan ba, sedai lokaci lokaci ta fashe da kuka.
Ranar uku, gidan nan ya cika da ɗan Adam, babu masaka tsinke Kasancewar ita kanta Huda mutuniyar kirki ce ga kyauta.
Ana zauna a nayiwa Daula gaisuwa, ta dubi wani babban ɗan sanda, ta tashi daga jikin Daula ta tafi gaban ɗan sandan ta zauna, ta kalle shi tace "Are you a police?"
Ya amsa mata da 'yes my dear "
" Can i ask you a question? "
" Yes of course "
Widad tace " idan na tambayeka, will you do your best to help me? "
Yace" insha Allah "
Widad tace" karka saɓa Alƙawari fa"
Mamaki ya kama mutanen gurin, yadda take zaro magana haka, daki daki kamar babbar mace.
Yace "insha Allah, i promise you, bazan saɓa ba"
Daula yace "lovely, dawo na kusa dani, karki dameshi"
Widad ta ɗagawa mahaifinta hannu, alamar ya ƙyaleta, ta kalli cikin idon ɗan sandan tace "you promise to help me, tambayar da zan maka itace, idan aka rufe fuskar mutum da pillow ze mutu?"
Yace "kamar yaya?"
"misali, Daddy ya doramin pillow fuskata, inta motsi amma yaƙi ɗagani, kawai se misali Bala megadi ya dawo ya riƙemin ƙafa, in dena motsi, to zan iya mutuwa"
Yace "yes of course dear, it's a murder attack, kisan kai kenan a ina kikaga anyi?"
"Yanzu misali, idan na gaya maka a inda na gani, wani mataki zaka ɗauka?"
Gaba ɗaya rumfar tayi shiru, ana sauraren Widad, Ɗan sandan yace "zamuyi abunda doka tace akai, idan har muka kama mutum da laifi, zamu kashi kotu a yanke masa hukunci"
"Arrest Bala! And the doctor that confirms that my Mum is dead, as a result of cardiac attack" ta faɗa kai tsaye
"Why" ya tambaye ta
Cikin ƙara tace "Bala yasan suwaye suka kashe Ammina, kasheta akayi fa, i use to watch in movies, she was killed not dead as a result of cardiac attack, Ka kama Bala ko in kasheshi, he's responsible for the murder, na ganshi shine ya buɗe wa wasu ƙofa, suka rufe ammina da pillow, Arrest him i said "!
Gaba ɗaya Widad ta hargitsa gurin, ihu take sosai tana nema ta fita daga hayyacinta, se kurma ihu take tana akama Bala.
Alhaji Haruna yace" ya za'a biyewa yarinya ƙarama tana wa mutane shirme, watakila alhinin mutuwane ko mafarki tayi "
Daula ya fashe da kuka yace " Widad mutum ce, kuma yarinya ƙarama, amma idan kaga tayi maka ƙarya ajizanci ne irin na ɗan Adam, dan haka Arrest him, ayi bincike akai "
Yai maganar yana kuka, aikuwa Bala yana ihu haka aka buga masa ankwa akayi gaba dashi, nan wasu suka dinga jinjinawa kaifin basira irin na Widad da ƙarfin hali, yayin da wasubsuke ganin be kamata a kama Bala ba, tunda shirmen yarane.
Nan fa 'yan sanda kuma suka shiga bincike akan Bala, Widad ta fayyace musu yadda abun ya faru, Alhaji Haruna yace "Nasir, bekamata a biyewa yarinya ƙarama ba, ta faɗi magana sannan a yadda"
Daula yace "Tunda Widad ta faɗi haka ba ƙarya take ba, bata taɓa haka ba, kuma akwai ƙamshin gaskiya a lamarin nan, dan haka se abunda hukuma tace, dan nikaina bana ja da ikon Allah, amma tabbas mutuwar Huda, abar a bincika ce, lafiya muka rabu da ita, ba ta da wani ciwo, ace in dawo in tarar ta rasu, Allah na tuba "
Kawai ya fashe da kuka, Bulama yace " Nasir, kayi haƙuri nasan irin mahimmancin Huda a rayuwarka, amma karkayi abunda zaka dawo kana dana sani, kar azo aji kunya "
Widad na kan kujera, tana wasa da yatsunta, tunda suke maganar su bata saka baki ba, se yanzu tace "Daddy, ko nima na mutu kar ka bari a ƙyale Bala, seya faɗi wanda suka kashe Ammina, idan ba hakaba zan faɗa maka ko suwaye"
Zaro ido sukayi, suka juyo da kallonsu kanta, Daula yace "Baby na, dagaske kin san suwaye? Ya akayi kika sani? Gayamin suwaye, meyafaru?"
"Daddy nima ban san suwaye ba, amma nasan mutum ɗaya, naji sun faɗi sunan wani mutum, amma zanyi tunani in tuna, na manta sunan, amma zan tuna idan be faɗa ba zan faɗa"
Bulama yace "Daula anya yarinyar nan bata samu matsala a ƙwaƙwalwarta ba? Ji wata irin magana da take fa, Anya baza'a kaita Asibiti ba"
Alhaji Haruna yace "gaskiya kam, nima naga kamar alamun haka a tare da ita"
"Niba mahaukaciya bace, karku sake cemin mahaukaciya, ni nasan abunda nake, wasune suka danne Ammina da pillow, ni ina da hankali"
Daula ya rungumeta yace "Sorry my lovely, nima na sani lafiyarki ƙalau ai"
Wasa wasa Widad gaba ɗaya walwalarta ta ɗauke, ta dena walwala ta dena fara'a, ko Abinci bata iya ci saboda kewa dake damunta, wasu lokutan seta wuni akan gadon nan da aka kashe Ammi, ko haka kurum taje ta buɗe wardrobe ɗin Ammin, ta watso kayan Ammin duka ta zauna a cikin kayan tana rusa uban kuka, haka Daula zezo ya na rarrashinta, wani lokacin kuma ya zauna ya tayata kukan.
Sosai Widad kaɗaici yake damunta, dama gata bame son mutane ba, Babu wani dangi da suke dasu da suke zuwa gurin su, dan haka Widad abun ya ƙara nata yawa, haka kurum wani lokacin da daddare seta hau firgita tana cewa "Daddy gasu nan, ka tashi kaima karsu kasheka" ko taita ihu tana ƙoƙarin fita da gudu, se Daula ya riƙeta gam.
Sosai ta dena magana, sedai ta kan zauna taita kallon magunan Ammi da take kiwo, da zomaye da tsuntsaye, da yake Huda mace ce me son dabbobi, sosai take kula dasu tana ciyar dasu, idan Widad tana kallonsu, se taga kamar Amminta tana nan, zata zo ta basu Abinci, haka zata zauna tana musu magana
"Kuma kunyi missing Ammina ko? An kashe ta, amma zata zo ta baku Abinci"
Bulama yace "Daula, nifa na fara jin tsoro da sha'anin yarinyar nan, karfa muna zaune ta haukace, gaba ɗaya ta canza lokaci ɗaya, ta zama wata iri"
Daula yace "nima na gani, abun yana damuna, na rasa ya zanyi bana son in rasa ɗiyata, kota rasa hankalinta, gashi kullum cikin kashedi takemin akan, lallai kar in bari a saki Bala, sannan idan be faɗi waye ba ita zata faɗa, nayi nayi ta faɗa taƙi gayamin, yanzu fa ko Abincin kirki bata ci, se koke koke"
Bulama yace "yanzu ajiyar da ka bata na dukiyar nan, baka tsoron ta samun taɓin Ƙwaƙwalwa, ayi asarar maƙudan kuɗaɗen nan?"
Daula yace "duk me wannan dukiyar, in dai ta sace ko waye, kuma ko a ina yaje, seya karɓi kayarsa dan haka wannan ba abun damuwa bane, ni abunda ya dameni yanzu, shine lafiyar ta"
Bulama yace "karka damu, akwai wani likitan ƙwaƙwalwa da Alhaji Munir ya sani, zan masa magana ya turoshi yazo ya duba ta"
Haka akayi, washegari Bulama yazo da Likitan nan da Alhaji Munir, Widad na ganinsa ta miƙe da gudu ta maƙalƙale Daula, juyin duniya ta sunkuyar da kanta taƙi kallonsu.
Suka gaisa da Daula, Daula yace "lovely ga likita ze dubaki, ki gaishe shi"
Ƙara sunkuyar da kai tayi, taƙi kallonsu, likitan yace "Baby zomu gaisa mana, tambayarki zanyi"
"Niba mahaukaciya bace" ta bashi amsa.
"Ai bance mahaukaciya bace ke, tambayarki kawai zanyi"
Juyin duniya Widad taƙi magana, duk tambayoyin da suke mata taƙi amsawa, likitan nan ya kaɗa ya raya, amma tayi mursisi kamar yana magana da itace.
Daula yasa hannu ya janyo ta daga bayansa data shige, ta sunkuyar da kai kamar sabuwar bokanya.
Ya ɗorata akan cinyarsa yace "Babyna lookup" ta ɗago ta kalli mahaifinta idonta fal hawaye.
Yace "ba cutar dake za suyi ba, tambayarki za'ayi lafiyarki nake son a dubamin, kinji Gimbiyar Daddynta"
"Daddy, idan Bala be faɗi wanda suka kashe Ammina ba, zan faɗi sunan da mutanen suka faɗa idan na tuna, ina kallonsu Bala ne ya rufe Alba Dog, ya buɗe musu ƙofa, shiya rako su har kan bene, ina kitchen ina kallonsu, har akace su nemoni a gidan nan"
Bulama yace "ikon Allah, kalli abunda ake tambayarta daban, abun da take faɗa daban"
Daula ya dafe kai yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ka rufamin Asiri kar Abunda ya ragemin ya kufcemin, Allah ka bawa 'yata lafiya".
Kawai ya fashe da kuka, yana ƙanƙame Widad a ƙirjinsa, aikuwa ta kwanta a jikinsa, tana ajiyar zuciya.
Alhaji Munir yace "dan Allah ka dena kukan nan"
Likitan da suke kira da Hamisu yace "Alhaji ina me sake yi maka ta' aziyyar rashin matarka, sannan kayi haƙuri ka dena kukan nan, ka bani haɗin kai ka amsa tambayoyin da zan maka, saboda alamu sun nuna Ƙwaƙwalwarta ta fara taɓuwa, tana iya bacci, ya yanayin cin Abincin ta?"
Daula yayi masa bayanin duk abunda Widad take yi, nan aka tabattar masa depression ne yake damunta.
"zan mata wata allura guda ɗaya, idan akayi mata insha Allah zata samu sauƙi, za'a samu ƙwaƙwalwarta ta dinga karɓar abunda ake so "
Widad tana zaune, aka haɗa allura aka zuƙa, tana kwance jikin Daula, likitan ya ɗaga hannunta, daidai dantsanta yayi mata allurar, sedai me ko mintuna biyar ba'ayi ba.........
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
78_79
Take Widad taji duniyar tana juya mata, taga abubuwan dake ƙasa sun koma sama, na sama sun dawo ƙasa, ta kasa gane inda kanta yake, ta dinga jin kamar ta tashi ta zura da gudu, ta riƙe kanta gam, kafin can ta kurma wani uba ihu ta miƙe tsaye tana zazzare idi.
Daula a gigice ya riƙeta yace "Subhanallah, doctor meke faruwa ne? Kaga abunda take fa, meya sameta ne? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
Likitan yace "wannan shike tabbatar da ta samu taɓin hankali ne, badan haka ba da babu abunda allurar za tayi mata, dole a cigaba da kula da ita, idan ba hakaba kuma zata zama tuburan, amma zan sake mata wata allaurar zata samu relief tayi bacci"
Widad tana ta gunji, tana fizge fizge haka aka kuma yi mata Allura, wadda seda ta ƙara birkitata ga baki ɗaya, ya zamana bata gane a duniya take ko a ina? Ga mutane tana kallonsu, amma bata gane meke faruwa, a haka har wani irin galabaitaccen bacci ya ɗauketa a wahalce.
Seda bacci ya ɗauketa sannan hankalin Daula ya kwanta, ya kalli likitan yace "yanzu doctor, wannan baccin shine samun relief ɗinta? Sannan kuma ya batun yadda za'a cigaba da kula da ita"
Doctor Hamisu yace "Eh shine samun sauƙinta, tunda kace baccin ma bata yinsa sosai, dan haka karka damu, ko yaushe zata kai tana wannan baccin babu wata matsala ba abun damuwa bane"
Daula ya jinjina kai yace "shikenan, ubangiji Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗunta, Allah ya baki lafiya daughter na"
Alhaji Munir yace "to tunda hakane baka ganin a cikin taɓin hankalin ne yasa tace kashe mahaifiyarta akayi? Tasa aka kama Bala? Kuma ma ai tayi ƙanƙanta ace ta bada irin wannan shedar an yarda an karɓa"
Daula ya haɗe rai yace "bana yadda in zalunci kowa a rayuwa ta, ina taka tsantsan da duk abunda zan aikata da zesa in ɓatawa wani, ko in zalunci wani dukda tarin dukiyar da nake da ita, amma a wannan karon nima zan ɗana izza da amfani da ƙarfin dukiya da Allah ya bani, in dai hakan ze samarwa da 'yata farinciki, bari in gaya maka wani abu, ko nawane zan kashe a cigaba da tsare Bala, har se ya faɗi abunda yasani game da kisan matata, uwar' yata"
Bulama yace "Daula karfa soyayyar 'yarka yasa ka aikata abunda zakazo kana danasani, abi komai a sannu har a gano bakin zaren, kaga yarinyar nan ga abunda aka ce yana damunta, ga kuma ita abunda take faɗa, kar ƙaunar da kake mata yasa ka ɓata sunanka a idon duniya"
Daula ya kalli Widad dake kwance a jikinsa, ya shafi gashin kanta yace "bata taɓa aikata wani abu makamancin haka ba, 'yata ba irin sauran yara bace, Ƙwaƙwalwarta na aiki fiye da shekarunta, tunaninta ya zarta tunani irin na yara, a baya Huda na ɓacin ran irin halayen Widad, tana jin haushin irin kallace kallacen da take yi, sedai me bayan ran Huda wannan hali na Widad yayi rana, saboda ni abunda likita ya faɗa daban abunda kuma ya faru daban, abun da baku sani ba shine, har kitchen inda ta hau kan drower, har garin hawa abunda take ci ya zuba a ƙasa, seda ta nunawa 'yan sanda, kuma ta nuna musu ta ƙofar da Bala ya shiga da mutanen nan, an auna gurin anga zanen yatsunsa a jiki, dan haka bana tantama abunda ta faɗi gaskiya ne"
Munir yace "Amma, baka ganin lokacin da ya shigo duba sune ya kama ƙofar ya shigo, har hoton yatsunsa ya fito"
"Wannan kuma aikin hukuma ne, su zasu tabattar da gaskiyar abunda ya faru, amma wannan karon nima zan ɗana, zanyi Amfani da ƙarfin dukiyata, da kuma alfarma da sanayya da nake da ita a faɗin ƙasar nan, se an nemo wanda suka kashe matata, kuma wallahi ko Arziƙina ze ƙare se na tabattar da anbi mana haƙƙinmu"
Likitan yace "Amma ranka ya daɗe kabi komai a sannu yafi, alamu sun nuna yarinyar ka tun tana ƙarama take da larurar Ƙwaƙwalwa, amma baka ɗau mataki ba"
Daula yace "ni lafiyar 'yata ƙalau, babu abunda ya samu Ƙwaƙwalwarta a wancan lokacin, Allah dai ya bata kaifin basira fiye da shekarunta" yana gama maganar ya miƙe, ya saɓa Widad a kafaɗarsa ya tafi ɗakinsa da ita, yaje ya kwantar da ita, ya koma gefenta ya kwanta ya ƙura mata ido yana jin tausayinta na ratsashi, Widad ta rasa mahaifiya da ƙananan shekaru, yasan rayuwar maraici, yasan yadda take, musamman ga 'ya mace tafi shan wahala, take hawaye suka shiga zarya a fuskarsa yace "insha Allah zanyi iyayina, ba zakiyi kukan maraici ba Widad"
Wasa wasa tunda aka yiwa Widad Allurar nan bata sake farkawa ba, haka ta dinga wannan baccin kamar wata matacciya, abun ya ɗagawa Daula hankali sosai, Amma likita yace masa bakomai samun relief ɗinta kenan.
Seda Widad tayi kwana biyu cir tana wannan baccin, ko motsi ba tayi rana ta biyu da yamma sannan ta farka, tunda ta fara baccin nan Daula baya matsawa ko nan da can, yana kusa da ita, har Allah yasa ta farka.
Koda ta farka ta farka da wata irin matsananciyar yunwa, amma ta kasa cewa tana jin yunwa, maganar duniya Daula yayi amma taƙi bashi amsa, sedai ta bishi da ido.
Ya haɗo Abinci yazo ya zauna yana bata, tana ci tana kallonsa kamar taga sabon abu a tare da shi, yana cikin cin aka zo aka sanar dashi yayi baƙi yace ayi musu iso nan inda yake baze iya tashi ya bar Widad ba.
Aka musu iso suka shiga har inda Daula yake, sedai Widad na ganinsu se taga kamar wannan mutanen da suka kashe Amminta, seta dinga ganinsu da wannan mask ɗin a fuskarsu, abunda ya faru da Amminta ya shiga dawo mata fes a idonta, taga kamar a lokacin abun ke shirin faruwa, aikuwa ta kurma ihu me razanarwa, haka yasa mutanen suka tsaya suna zuba mata ido, ta riƙe Daula gam tana ihu, ta rintse idanunta alamar bata son ganin kowa gaba ɗaya.
Ƙarshe mutanen nan se barin ɗakin nan sukayi gaba ɗaya, suka koma babban falo suka jira shi, abu kamar wasa sosai Widad take gudun mutane bata son kowa a inda take inba Daddynta ko Bulama ba.
Watarana tana zaune a ɗakin Daddynta, tana wasa da magen Amminta data bari, Alhaji Daula yana son ya ɗan fita, amma yana tunanin yadda zeyi da Widad.
Widad da a rana bata fi tayi magana sau a ƙirga ba amma tace "Daddy kaje inda kake son zuwa, ba inda zani"
"A'a lovely, ina tsoron barinki anan ke kaɗai, abubuwa sun fara bani tsoro, ina zaton zan sa a ƙara security"
Widad tace "Daddy har yanzu Bala be magana ba?"
"Eh lovely, Amma a binciken 'yan sanda, security na kan babban titi sunga wucewar mota tsakar darw ta shigo hanyarmu, sedai wai sunyi zaton gurina ko wani suka zo, saboda kin san mukanyi meeting cikin dare, amma har yanzu anata bincike"
Widad ta jinjina kai tace "Daddy kaje kawai, ina nan ba inda zani"
"Babyna ina tsoron barinki, kinga baki da lafiya"
"Lafiyata ƙalau fa"
"ko kuma mu tafi tare da ke?"
"A'a Bazani ba, ka tafi kawai"
Daula yace "nayi murna daughter, yau kina magana sosai da kanki".
Tayi murmushi, Daula ya shirya ya fita.
Bayan fitarsa Widad ta fito ta dinga zagaye gidan, kamar bata saba ganin gidan ba.
Kamar gaske ta fara dawowa daidai, amma dukda haka bata son mutane sam, daga Daddynta bata son kowa ya raɓeta, balle a yimata wani abun, haka Daula yake yawo da ita gurin taro ko harkokin kasuwanci, kamar yadda uwa ke yawo da ɗanta, sam ko makaranta bata zuwa saboda rashin son mutane, indai ba'a gida ba ko tana tare da Daddynta bata zama a ko ina.
Daula Shine wankanta, Abincinta, da dukkan buƙatunta, sam baya gazawa.
Wataran zeje taron kasuwanci Africa ta kudu, nanma ya ɗauki Widad ya tafi da ita, ranar da suka dawo kusan ƙarfe ɗaya na dare, direbansa yaje ya ɗakkosu daga airport suna tafe suna hira, kawai aka tare motar tasu.
Widad na ganin mutanen da suka taresu ta gigice, yanayin jikinsu sak wanda suka kashe Ammi, gasu da mask a fuskarsu.
"Kai buɗe motar nan"! Ɗayan yayiwa direban Daddy tsawo
Widad ba zata taɓa mantawa da wannan muryar ba, tabbas sune wanda sukaje har gida suka danne Umminta da pillow, nan da nan jikin Widad ya ɗau rawa, amma ta dake taƙi nuna alamar Hakan.
Suka bubbuɗe murfin motar, Daula ya rungume Widad a jikinsa yana ta nanata Hasbunalahi wani'imal wakil, suka fizgo direban Daula ƙasa suka saita masa bindiga.
Ɗaya daga cikinsu Wanda Widad bazata manta dashi ba, shine wanda taji yana wayar nan ranar da suka kasje mahaifiyarta, har ya ambaci sunan wani mutum, ya kalli Daula yace "Nasiru Daula, haƙiƙa ina me tabattar maka da zaka bi matarka inda ta tafi idan har ka mana gardama, tambaya ɗaya zan maka kuma amsa nake so ta kai tsaye, ina wannan takaddun da wasiyyar da kayi na cewar akwai wanda yake da kashi bakwai bisa goma na dukiyarka suna ina?"
Daula ya kalleshi cikin mamaki yace
" dama dalilin da yasa kuka taremu kenan? toni babu wannan kayan a hannuna, kamar yadda nayi bayani lokacin da nayi hira da 'yan jarida"
Cikin tsawa yace " kai, karka min wata taƙama da jin kai, babu wani amfani da taurin kai ko tsaurinka ze maka a nan, zan iya fasa maka kaibda harsashen nan"
Ɗauke Daula yayi, yai musu shiru.
"Ina takaddun nan suke?!" sukai masa magana cikin tsawa.
Ko gezau beba balle susa ran ze basu amsa, yunƙurwa sukayi zasu danƙo Daula daga cikin motar, Amma Widad ta buɗe hannayenta ta tare mahaifinta.
Daula yace "lovely, ki bari kar suyi miki wani abun kinji, karsu illatamin ke"
"Am not afraid of anyone, abunda suke nema yana gurina, karsu ƙara yi maka tsawa"
Kallonta suka shigayi, dudu ba zata fi shekaru takwas ba, amma kalli yadda take magana kamar ba yarinya ba.
Hannu babban cikinsu ya saka ze fizgo Widad, amma Daula ya riƙita gam suna janta, shi kuma ya riƙeta gam.
"Idan baka saketa ba zamu fasa kanta da harsashi!"
Daula yace "idan kuka kasheta kun kasheni, kuma kun rasa abunda kuke nema, kuma koda kun barmu a raye shima duk ɗaya zaku rasa abunda kuke nema, dan wallahi kome zakuyi da kaina bazan baku amana ba, bazan baku kayan da ba nawa ba, sedai idan Widad ɗince ta yarda ta baku bani da matsala da duk wanda ta ɗauka ta bawa"
Zuro hannu ya kuma yi ze danƙo Widad, sedai a wannan karon bisa sa'a, Widad ta nuna musu ita mahaukaciya ce, dan kukan kura tayi ta datse yatsan mutumin nan a bakinta, ta kafa masa haƙora kamar yadda ta yiwa Fahad.
Abun mamaki sega Ƙaton da yake ɗauke da bindiga yana kurma ihu, yasa kan bindiga ya daki kan Widad, wanda hakan yasa ta ƙwala ihu ta sake shi, sega jini na zuba ta hancinta ta sume a gurin, ganin Asirinsu na ƙoƙarin tonuwa yasa suka cika wandunansu da iska suka ɓace daga gurin.
Daula gaba ɗaya ya rikice, ƙarshe direban ne yayi dabarar wucewa dasu Asibiti, aka kai Widad emergency gaba ɗaya Daula ya rasa abunda yake masa daɗi, matsala daga wannan se wancan be maganin wannan ba waccan ta kunno kai.
Yai shiru ya dafe kansa ya zubawa Widad ido, wadda ke kwance ruwa na shiga jikinta, ya kifa kai akan gadon da take yai kuka yai kuka, harya gaji yayi shiru, cikin dare Widad ta farka tayi juyi taji kanta yayi mata nauyi, ta juya taga mahaifinta ya kifa kansa a kan gadonta, ya riƙe hannayenta, da alamu yana cikin matsananciyar damuwa, a hankali tayi juyi ta rungumo kan Daddynta ta kwantar da kanta a kan nasa, a haka bacci ya ɗauketa.
Wayewar gari labari ya cika gari, ga abunda ya sami Daula da 'yarsa nanma akayi ta tururwar zuwa Asibiti dubata.
Daula ya tafi masallaci salla sega wasu mutane sun shigo ɗakin nata, wai sunzo dubata, ta dinga binsu da kallo, suka zazzauna, kallo ɗaya ta gane wanda ya buga mata bindiga jiya, wanda suka kashe Amminta ne, bata taɓa ganin fuskarsa ba se yau, bata ƙara tabattarwa ba seda ta kalli inda ta gasa masa cizo jiya, a hankali yace
"ina baban naki?"
Shiru tayi ba tace masa komai ba, yazo gaban gadonta ya durƙusa sannan kalleta yace "Baby girl, tambayarki zanyi kinji ko? Ina abubuwan da Dad ɗinki ya baki ajiya, su nake son ki gayamin inda suke kinji, nima bazan gayawa kowa ba"
Widad ta tsare shi da manya manyan idanunta tana masa wani irin kallo, daya kasa gane na menene?
"Baby ki gayamin kinji"
Still ba amsa, ya ɗakko wata ƙaramar wuƙa yace "idan baki gayamin ba, zan gutsutsura naman jikinki da wuƙar nan, in dafa in cinye, gayamin nace"
Yai maganar yana zare mata ido.
Ya ɗauka Widad irin yaran dazewa barazana ne, amsar data bashi shine "idan ka kasheni bakomai, nasan dai Daddy zeyi kuka, amma nasan wanda ya kashemin Ammina" tai maganar tana kallonsa
A fusace yace "ina ruwana da wanda ya kashe ta? Kema kashe ki zanyi in kashe babanki idan baki faɗan ba"
Maimakon ta bashi amsa, se tace "Na rubutawa DSP wasiƙa, zan gayamasa wanda ya kashe Ammina, yayimin Alƙawarin ze gano suwaye"
"Ke dan ubanki ba wannan muke tambayarki ba, ina kayan nan suke?"
Widad bata nuna ta ganesu ba, ta sake kallon hannunsa tabbas shine babu ko tantama, ga inda ta cijeshi jiya a tsintsiyar hannu, abun da ya faru ranar da aka yi kisan ya sake dawo mata ranta, gani tayi ya miƙe ya ɗakko handkerchief a aljihunsa ze saka mata a hanci, nan experience ɗinta na kallace kallacen films ya dawo mata, bata san ya akayi ba ta fasa ihu, ta ɗakko kwalbar malt zata buga masa, ai kafin tayi wani yunƙuri, sun bar ɗakin nata da sauri, nan ta cigaba da kurma ihu tana jifa da kwalabe a ɗakin.
Da gudu Daula dasu Bulama, da ɗan sandan Da Widad ta saka ya kama Bala, suka ƙaraso ɗakin, dama suna kan hanyar zuwa ɗakinne, Daula yayiwa ɗansandan waya, yayi masa bayani, shine ya taho Asibitin.
Tayi watsi da kwalabe tana kuka, Daula jiki a sanyaye ya karaya, tabbas hauka ya tabatta akan Widad, ta haukace.
Daula yana da matuƙar raunin zuciya, dan haka kuka baya bashi wahala, haka ze zauna idan damuwa tayi masa yawa yaita abunsa.
Yazo kan gadon nata ya zauna, aikuwa nan da nan ta rungume shi, tana ta sauke numfashi kamar wadda tayi dambe.
Ɗansandan yace "Alhaji, wannan harin da aka kai muku jiya, ya tabattar da maganar Widad, kashe matarka akayi muma munata tattara abunda bincike ya nuna mana, Insha Allah kamar yadda nayi Alƙawari, se naga abunda ya turewa buzu naɗi"
Daula yace "nagode sosai ranka ya daɗe"
Bulama yace "Nasiru kaga tashi muje a maida yarinyar nan gurin Likitan nan, ya duba ta asan halin da take ciki, abun nata gaba yake fa"
Babu tunanin komai, Daula ya amince, Bulama ya saɓa Widad a kafaɗarsa, suka fito sedai tasa tafukan hannayenta ta rufe idonta, saboda bata san haske kuma bata son koda wasa ta sake ganin mutanen nan.
Asibitin doctor Hamisu suka wuce, ya karɓesu hannu bibiyu, ya sake ɗurkawa Widad allurai wanda suka sake rikita ta gaba ɗaya, sannan ya ɗirka mata allurar bacci.
Gaba ɗaya seda inspector ya kamu da matsanancin tausyin Widad, yarinya ƙarama amma rayuwarta a garari haka, ya kalli Daula yace
"ranka ya daɗe, yakamata ace an sake tsananta matakan tsaro, a hanyar gidanka saboda kariya ga lafiyarka da kuma ta 'yarka, ina jin tausayin yarinyar nan, kuma nayi mata Alƙawari insha Allah bazan mutu ba zan cika mata, tacemin zata yi magana dani rannan, tace maganar tana da mahimmanci sosai, dan haka insha Allah zan sake zuwa, in duba ta sannan inji maganar da zata yi min"
Daula yace "Nagode DSP da wannan ɗawainiya da kake, Allah yasaka maka da alheri"
"Karka damu, aikina ne yin hakan ai, Allah ya bawa Baby lafiya"
Kwana biyu da tafiyar DSP, lokacin Widad ta farfaɗo, a lokacin aka sanar da rasuwar Wannan DAP Na 'yan sanda da yake faɗi tashi akan case ɗin, ranar da ya bar gurin Widad, akayi masa kiran gaggawa Lagos, akan hanyarsa sukayi artabu da' yan fashi aka kashe shi.
Daula ya kaɗu matuƙar gaske da jin wannan labarin, ya shiga damuwa haka kurum zuciyarsa ke raya masa, ba haka abun ya faru ba, yanzu kenan duk me niyyar taumakonsu se anga bayansa?
Wannan karonma farkawar Widad yazo da sabon salo, bayan rashin magana ma, sam bata son haske sedai a rurrufe ko ina, ko yaya haske yake bata sonsa komai sedai tayi a ɗaki.
Ta ƙara shiga damuwa da taji labarin mutuwar DSP, dukda ba magana take son yi ba amma tayi kuka sosai.
Tace "Daddy"
Daula yace "Na'am lovely na"
"Daddy dan Allah, ko duk kuɗinmu zasu ƙare, karka bari a saki Bala megadi"
"Insha Allah Baby, bazan bari ba amma na fara damuwa, gashi baki da lafiya, gashi an fara kashs duk masu niyyar temakonmu"
Ta kalli Daula tace "idan an kashe masu taimakon mu, Allah ze temake mu, idan kaje gaisuwa kayiwa iyalinsa alheri, ka basu haƙuri"
Daga nam ta kwanta bata sake magana ba.
Gaba ɗaya Daula ya ajiye batun harkar kasuwanci a gefe, ya tattara hankalinsa akan lafiyar 'yarsa.
Suna zaune da Bulama a falon gidansa, Bulama yace "Daula, zamanka fa da Widad a gidan nan baze yuwu ba, zuwa yanzu ya kamata kayi Aure kodan ka samu me ta yaka kula da ita, ga harkokinka suna nema su tsaya, ni da zaka yadda dana ɗauketa, saboda ina son Yarinyar nan"
Daula yace "nasan kana son 'yata Bulama, sedai koms za' ace sedai ace, zan cigaba da kula da ita, ina nema mata lafiya, yanzu abunda ya dameni ina son in samo malamai suzo su raba gadon Huda"
Bulama yace "wane irin gado kuma? Naga dama idan wani abu take dashi kaika bata, tunda ta mutu ai ya zama naka"
Daula ya girgiza kai yace "A'a, akwai kuɗaɗenta masu yawa da bani lokacin da mukayi Aure, ina son a ware natane a cikin dukiyata, idan aka ware zan mallakwa Widad su"
"Kamar yaya? Da can ka ware kashi bakwai, yanzu kuma Allah kaɗai yasan kashi nawa zaka kuma warewa, Widad ɗin da take yarinya me zata yi da dukiya? Kuma yanzu idan duk ka kwashe kuɗaɗen nan, kasan adadin mutanen da zasu durƙushe kuwa? Mutane dayawa da Allah suka dogara, amma suna daga kwamce suke Arziki saboda kasiwancinka"
"Nasani Bulama, amma hakan baya nufin zan janye kuɗaɗen ne, zan cigaba da juyasu, amma zan canza suna na dana 'yata akan abunda yake mallakinta, kuma insha Allah idan naga maganin da ake mata anan beyi ba, zamu dan gana da ƙasashen waje ne kawai"
Widad fa ba zuwa makaranta, kullum se a gida banda zabure zabure da ihun da take yi cikin dare, ga ƙin mutane dan a tsorace take da mutanen nan kar su sake dawowa su cutar da su.
Sedai a hakan an cigaba da yiwa Daula barazana iri iri ta waya, ace za'a kasheshi ko za'a sace Widad idan be faɗi inda takaddun nan suke ba, tun yana zarya hukumar 'yan sanda harya haƙura gaba ɗaya.
Bulama ya saka Daula a gaba da yayi Aure, dan ba mutuncinsa bane babban mutum kamarshk ace bashi da Aure kuma yana zaune da gashi se ƙaramar yarinya a gida ba.
Daula yace "sam baze Aure ba, yazan babu me maye gurbin Huda"
Bulama yace "idan balarabiya kake so, kana da kuɗin da zaka je kowani ƙasa ka auro mace, wadda kake so"
Daula ya kan ce masa "ba balarabiya nake so ba, nagarta nake nema irin ta Huda"
Bulama ya matsa, ya dage ya takurawa Daula, Daula yace "nifa ka ƙyaleni, lafiyar 'yata ta fiyemin wani Aure"
Amma Bulama ya cigaba da matsawa, gefe guda kuma anata bankawa Widad allurai da ƙwayoyi da suke birkita mata lissafi, ƙiri ƙiri ta dena zancen zata faɗi wanda ya kashe Amminta, gaba ɗaya aka tsaya da zancen ma, a haka aka daddafa aka fara shari'a da Bala, anan Daula yayi amfani da tasirin dukiya, shari'a taƙi gaba taƙi baya aka tsare Bala, da rundunar sojoji sunso kawowa Bala ɗauki, Kasancewar nasu ne, sedai Daula yai amfani da kuɗinsa, hakan yaƙi tasiri.
Ganin Daula bashi da niyyar yin Auren nan, gaba ɗaya ya tattara hankakinsa akan 'yarsa yasa Bulama da kansa nemawa Daula matar daze Aura, sedai me.......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
80_81
Daula yace "se Widad ta amince tukuna"
abun ya bawa Bulama Haushi sosai yace "haba Nasir, kaima ka zama ƙaramin yaron kenan? Ya za'ayi kace se Widad ta amince? ita meta sani game da wannan maganar?"
Daula yace "Yarinyar nan itace uwata, itace Ubana itace komaina a yanzu, dan haka duk hukuncin data yanke shikenan"
Bulama yaji kamar yayiwa Daula dukan tsiya ya huce, haka ya ci gaba da cusa masa matar nan, 'yar uwace a gurin Bulama matar, sun rabu da mijinta tana da yara Uku, mijin idan ya shura takalmansa se yayi wattanni ba'asan inda yake ba, ga ba Abinci ya barta da yar taita wahala shine aka raba auren.
Daula fafur yaƙi maganar sam, Ita kam Gimbiyar wato Widad ana cigaba da sake birkita mata tunani, ta hanyar ƙwayoyi da kuma allurai, gaba ɗaya ta koma wata iriya abun tausayi, wani lokacin idan ta rasa me yake damunta sedai tayi ta kuka, takasa banbance a aace duniyar take.
Wani lokacin haka kurum tana zaune, sedai taji ana mata ihu ko ana kuruwa a cikin kunnuwanta, ko taga duniya tana juyawa, ko kuma taji kamar ana buɗe ƙofa za'a shigo kawai se zuciyarta ta bata mutanen nan ne zasu shigo.
Abun duniya ya ishi Daula, ga surutun mutane ya fara masa yawa akan yakamata yayi Aure, bekamata ya cigaba da zama haka ba.
Bulama yace "kaga Daula, tun wuri ya kamata ka nemawa kanka mafita, kai ba dan Allah yasa kana da nasibi akan harkar kasuwanci ba, da tuni kasuwancinka yazo ƙarshe gaba ɗaya, kuma kaɗaici ze iya sawa Widad ta ƙara shiga wani hali, babu yadda za'ayi rayuwar yarinya ƙarama ta yuwu ba tare da mace me kulawa da ita ba, kai a yanzu taurin kai ba naka bane, kaje ka samu kayi Auren nan ko hankalinka yafi kwanciya "
Daula yace " Bulama ba naƙi inyi Auren nan neba, bana son in Auri wadda zata zo takasa jure zama dani, wadda zata ƙarasa kassarani, yanzu duk macen da zan aura, zata aureni ne dan dukiyata, matata ta fari kuwa ta Aureni tun banda komai, shiyasa nake jin tsoron hakan, ko in Auri mace ta haihu dani in kasa daidaita adalci a tsakanin 'ya' yan, dan bazan taɓa kamanta ƙaunar abunda Huda ta bari da wani ba, Allah sarki Huda ba ita ba abunda yake cikinta, Allah ya jiƙanki Huda ya saka miki kissan gillar da akayi miki"
Bulama ya dafa kafaɗarsa yace "Nasir, Kayi haƙuri, zan samo maka mace me hankali, kaga Haliman nan muyuniyar kirkice 'yar uwatace, mijin tane ta Aura Azzalumi, ƙarshe aka raba Auren, nayi imani da Allah zata zauna da kai lafiya, harta kula da Yarinyar nan tunda kaƙi bani ita, da naso ka bani ita kafin kayi Auren se in dawo maka da ita, amma kace kafi son ka kula da ita, tunda hakane gara ka lallaɓa kayi Aure, amma zaman da kake haka be dace sam, kuma kaima ka sani"
Haka Bulama yaita lallaɓa Daula, harya yadda zeje su gaisa da ita matar.
Duk da rashin lafiya na Widad, haka ya shiryata suka tafi tare, gidan da Halima take duk a kwararraɓe ba gyara, aka masa iso sitting room ɗin gidan, tunda sukaje Widad take kallon gidan, ita bata taɓa ganin gida a haka ba, gashi ɗan ƙarami gashi wani irin.
Halima taitawa Widad magana amma taƙi kulata, Alhaji Nasir yace "Halima kinga 'yata Widad, kuma bata da cikakkiyar lafiya tun rasuwar mahaifiyarta ta samu matsalar Ƙwaƙwalwa, bata yadda da kowa ban saniba ko zaki iya zama da ita, danni da banyi niyyar yin Aure ba, amma saboda Bulama ya matsa, kuma ke' yar uwarsa ce yasa nace to shikenan na amince, amma ya kikace? "
Halima tace " insha Allah zan iya zama da ita in kula da ita, tunda kaga nima ina da yara, in Allah ya yarda baze gagara ba"
Daula yace "Masha Allah, idan ba zaki damu ba, mahaifin yaran baze ce komai ba, zaki iya tarewa tare dasu, mu zauna gaba ɗaya"
Nan ta rusuna tace "Masha Allah, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi Alhaji"
Yarane sukayi sallama, suka amsa musu gaba ɗaya, su ukune bini in bika, sanye da uniform ɗin makarantar gwamnati, kowannensu hannusa ɗauke da jakar nan ta da wadda ake cewa Baba nagode, takalmansu Sandal wanda ake cewa ganda, duk sun tsufa sun cinye, sun tsitsinke.
Yaran Biyu mata ne ɗaya namiji, suka gaida Daula, ya amsa musu cikin fara'a, Widad ta dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya, tana kallon suturar jikinsu, duk wani iri haka take ganinsu.
Namijin ne wanda aƙalla ze kai shekaru goma sha huɗu yace "Mama, wannan wacece?"
Yai maganar yana nuna Widad, Halima tace "to sarkin surutu, aje a cire Uniform".
Daula yace "A'a ba'a gwale yaro ai, Ya sunanka ne?"
Yaron yace "Anwar"
Daula yace "Masha Allah, itakuma sunanta Widad ƙanwarka ce"
Anwar yai murmushi yace "Mekyau da ita, Baby zomu gaisa"
Haɗe rai Widad ta ƙarayi ta kwanta a jikin Daula, Daula yace "ai bata da lafiya ne Yaya Anwar"
Anwar yace "Allah ya bata lafiya, ina da sweet bari in baki kina so?"
Yai maganar yana zura hannu a jakar makarantar sa, ya miƙo mata alewa 'yar uku biyar guda biyu, ga mamakin Daula yaga tasa hannu ta karɓa tace "thank you"
Nan Daula ya shiga murmushi, abunka dame ɗa, nan ya fara jin insha Allah a hankali Widad zata ware, ta saki jiki dasu idan ya Auri Halima, Sukam yaran matan kallon Widad kawai sukeyi, kyakkyawa da ita, ga gashi dan kanta ko ɗankwali babu, tana sanye da riga da skirt kamar 'yar turawa, tana kwance a jikin Babanta ta buɗe alawar nan tasa a bakinta, ta buɗe ɗaya tasawa Daula a baki gwanin ban sha' awa.
Suka tashi tafiya Daula ya babbasu kuɗi, babu ko kara suka karɓe, sedai fafur Anwar yaƙi karɓa yace tunda an bawa Su Amal da mamansu baze karɓa ba, juyin duniya yace a'a, Widad ta zura hannu a aljihun mahaifinta ta ɗakko kuɗi taje ta miƙawa Anwar kuma ta tsatstsareshi da ido.
Daula yace "Good, kuma ba'a maida kyautar Gimbiya, ni idan na baka kaƙi karɓa, ita ba'a maida mata da abu idan ta bayar"
Haka Anwar yasa hannu ya karɓa ya dinga godiya.
Nan Daula yaji daɗin ƙauna da karamcin da sukayi musu, dan haka ya amince da Auren Halima, amma yace baze zauna a wannan gidan ba canza gida zeyi.
Ya sanar da Bulama sun amince, haka Bulama ya wuce gaba Daula ya auri Halima, sannan yace ta taho da 'ya' yanta ze riƙe mata.
Suka tare a sabon gidan Daula, sedai fa wannan rashin yaddar na Widad yana nan, sam basa gabanta bata damu dasu ba, har gara Anwar shima wani lokacin take ɗan yadda dashi, amma Ramlah da Amal kam bata ɗaukesu wasu mutane bama.
Part ɗinta daban a cikin gidan, dan karma wani ya takura mata.
Halima kam tana Auren Daula nan da nan 'ya' yanta suka koma ce mata Mummy daga Mama, nan da nan sukayi shar, Daula ya sauya musu makaranta zuwa ta 'ya' yan masu kuɗi, ha ajiye musu direba da yake kaisu yana dawo dasu, komai shar dasu nan da nan suka fara canzawa, sedai babban abunda yake tsayewa Halima shine, Daula ya fifita 'yarsa akanta, ko magana tayi idan Widad ta rusheta ta zauna a gurin Daula, idan wani abu kake so a hannun Daula muddin Widad ta amince ka samu, wani lokacin ma itace zata baka, dan haka ta ɗorawa Widad karan tsana.
Ƙwayoyi da Alluran da akewa Widad sunyi tasiri a jikinta, ya zamana ko ba abata ba, haka kurum zata fara wannan fizge fizgen da iface ifacen, idan har Daula baya nan haka zata yi ta faman wannan kuruwar, suna jinta babu me kawo mata agaji, haka wasu lokutan zata jiyawa kanta rauni, ta gama ihun harta gaji ta faɗi, Anwar ne kawai idan yana nan yake iya taimakonta, Abinci idan anyi se anga dama za'a bata, ita kuma baza tace a bata ba, amma a gaban Daula Suyita nan nan da ita suna bata kulawa da nuna mata soyayya, baya kaso komai a ransa saboda halin ko in kular da take wa su Halima, saboda yana tunanin yanayin ciwon nata ne.
Tun daga nan Widad ta ƙara tsinkewa da lamarin mutanen nan, suyita nuna mata kulawa a gaban mahaifinta, amma daga ita sesu suyi ta zaginta, suna ce mata mahaukaciya.
Hakan yasa ta ƙara zame jikinta daga garesu, sam bata iya fitowa tayi karo dasu, babban abunda ya ɗaure mata kai, be wuce yadda taga mutumin da taji an ambaci sunansa ranar da aka kashe Amminta, yazo gidanba a lokacin Daddynta baya gari, abun ya ɗaure mata kai sosai, ya daɗe a gidan sannan ya tafi, kafin ya tafi zuciya ta dinga azalzalar Widad taje tai masa wani abu daze illatashi, amma ta gagara aikata komai.
Jikintane ya fara tsuma, ta dinga tuna abunda ya faru, nan ta faɗi tana wannan ihun da take yi idan abun ya motsa, suna jiyo kururuwar Widad amma kota kanta basu biba, haka ta dinga gurnani ita kaɗai.
Anwar ne ya shigo, yace "Mummy ina Widad ne?"
"Kaje ka duba mana"
Anwar ya tafi ɓangarenta, yaje ya tarar da ita a zube a ƙasa a falonta, gaba ɗaya bata hayyacinta, a gigice Anwar ya fito falo yace "Mummy, Widad fa ba lafiya, tana sume a ɗakinta"
Halima ta lura da yadda Anwar yake nan nan da Widad, taga alamun bazata samu goyon bayansa ba, dan haka ta maze sukaje kan Widad, ya kwantar da ita akan kujera, aka kira likita, yace akaita can Asibitinsa, nan fa ya kuma ɗura mata wannan allura me kama da ta doki, wadda ke gigita Widad.
Cikin tangaɗin wahalarwa da allurar ke mata, bata gane komai ga idonta a buɗe amma sam bata cikin hankalinta, Wannan mutumin da aka ambaci sunansa ne yazo kanta, ya ƙura mata ido sannan yace
"Ke ki gayamin inda kayan nan suke, takaddun nan da ubanki ya baki ayce akwai mesu, suna ina?"
Kallonsa Widad take, bata gane gaskene abun yake faruwa ko kuma mafarkin ne, ta kai idonta gefe taga Halima a zaune a gurin, lumshe idonta tayi taƙi magana.
Cikin tsawa yace " zakiyi magana ko sena miki azaba, irin wadda ba'a taɓa miki makamanciyarta ba"?
Ko gezau ba tayi ba daga inda take, ta lumshe idonta tamkar bacci ya ɗauketa
Halima tace "bafa a hayyacinta take ba"
Mutumin yace "Aikuwa zata dawwama a haka muddin ba zata faɗa ba, semun kashe Uban nata, an dinga ɗirka mata allurar nan kenan, da ƙwayoyi seta zama mahaukaciya tuburan ta girma tana yawo tsirara tana bin bola saboda rashin gata"
Widad najinsa, wani irin ƙuna ranta ya shiga yi, yasa an kashe mata mahaifiya, kuma yazo kanta yana gayamata maganar banza, sam takasa gane ko mafarki take ko a zahiri abun ya faru, ganin haka yasa hawaye ya fara bin gefen idonta, ta tabattar da ta haukace.
Can bayan wasu awanni, taji an taɓata ai wani kukan kura tayi dan a zatonta wannan mutumin ne, ta kai masa wata irin mahaukaciyar shaƙa tana zazzare ido, sedai kuma se taga ashe mahaifinta ne, da farko fuskar wancan ta gani, daga baya kuma taga ashe Daddynta ne, ba ƙaramin tsorata Daula yayi ba, tunda har Widad ta fara ƙoƙarin shaƙeshi to tabbas hauka ya tabatta, a hankali ta ajiye hannunta ta kwanta a jikin Daddynta.
Ko mintuna biyu ba'ayi ba kuma se bacci, amma cikin baccin banda mafarke mafarke ba abunda take yi, seta dinga ganin mafarkan kamar gaske, dan haka seta ƙwala ihu.
Sosai fa Daula ya shiga damuwa, Doctor Hamisu yace "Ranka ya daɗe, kaga ana treatment ɗin nan but her body is not responding to the treatment, dan haka she needs to be admitted to psychiatric Hospital, yadda za'afi kula da ita"
Hawaye ne ya ƙwacewa Daula yace "Over my death body, in ɗau 'yata da hannuna in kai psychiatric, bazan iya ba, zan cigaba da kula da ita, idan yaso a cigaba da mata treatment"
Bayan ta ɗan farfaɗo, ya ɗau' yarsa yayi gida, kwana biyu ta ɗanji sauƙi amma lokaci lokaci takan yi ihun nan na dare.
Daula yana zaune da Halima da yaranta a falo suna hira, harda yaranta da jansu yake kamar 'ya' yansa, Widad ta fito tana taku ɗai ɗai tana kallonsu, Babban abunda ya ƙular da Halima be wuce yadda Daula ya miƙe tsaye ba domin tarar Widad, sekace yaga wa shugabarsa, gata gwansamemiya da ita, kusan shekara tara amma haka yake ɗorata a cinya kokuma ya goya ta a bayansa, ta zauna a cinyar Daula tace
"Daddy, tunda babu me dubamin wanda ya kashe Ammina, ina son gidan nan da Ammi ta rasu ka siyomin su zomo, su mage da duk domestic Animals, ka haɗa dana Ammi in dinga ganinsu"
Daula yace "considered it done your majesty, yadda kike so haka za'ayi, kwanan nan ina son in buɗe miki Account mu dinga tara ribarmu ta kasuwanci nida ke"
Murmushi kawai Widad tayi ba tace komai ba, se can tace "Daddy wai na dena zuwa makaranta ne?"
Daula yace "ina so ki warke ne tukuna, bana son a kaiki makaranta ki cigaba da rashin lafiya"
Widad tace "Daddy bana son zaman gidan nan kwata kwata"
Cikin Halima ya ɗuri ruwa, ta zata Widad zata tona mata Asiri, amma se tace "idan ina nan ina tunanin Ammine sosai"
"Babyna, shiyasa muka taso daga wancan gidan fa, saboda ki dena ganin abunda ze ɗaga miki hankali"
"Nan ma akwai wanda yake ɗagamin hankali, kuma ni makaranta nakeso in koma, ka maidani gidanmu na England seka kaini boarding school"
Shiru Daula yayi yace "lovely, zaki tafi kibar Daddynki?"
"No Daddy, kaga nan kullum kana cikin damuwa saboda ni, ni kuma ina tsorata sosai anan, dan Allah ka kaini can bana son zaman nan, please Daddy"
Daula yace "Shikenan, zan duba wace makarantar yakamata in kaiki"
Anwar yace "banji Daɗi ba, bazan ji daɗi ba idan kika tafi Widad"
Widad ɗin dako fara'ar kirki ba tayi amma tai murmushi, dan Anwar yana nuna mata tausayi, ko Daddy baya nan idan shi yana nan suna sassauta mata, Widad tace "ko zaka bini ne, mu tafi tare?"
Anwar yace "Ƙwarai kuwa, daga nan har birnin sin, idan zaki dani zan biki"
Murmushi tayi tace "aini makarantar mahaukata za'a kaini, kai kuma kana da hankali ai"
Sosai Anwar yaji tausayinta yace "Ai zakiji sauƙi insha Allah, zaki warke ki dena cewa kanki mahaukaciya"
Girgiza kai kawai tayi tace "Daddy, zanje in kwanta, ka rakani"
"Shikenan muje gimbiyata"
Halima da tun ɗazu ba tace uffan ba, dan wani mugun haushinsu take ji, da gashi har 'yar tasa.
Kwana biyu da yin wannan maganar, cikin dare suna bacci aka kuma shigowa gidan, dukda tarin security dake layin gidan, still dai wannan takaddu suka sake biyowa, aka rufe ɓangaren Halima da' ya'yanta suka shiga na Daula suka tarar dashi yana bacci, Widad na bayansa tana bacci itama.
Haka suka tashesu, Amma saboda gaddama da taurin kai irin na Daula daga shi har Widad suka ƙi magana, a gabansa suka dinga solata suna bugawa da ƙasa dan tayi magana amma taƙi, ba abunda Daula ze iya saboda kashedin da suka yi masa na zasu kashe Widad idan yayi wani yunƙuri.
Wani daga cikinsu yakama kumatun Widad, da suke ɓulɓul jajawur saboda hutu, yasa Ƙaton hannunsa ya matse da ƙarfi seda tayi wani uban zillo dan azaba ta saki fitsari, amma taƙi magana se kace wata itace.
Ƙarshe haka suka yi jifa da ita a galabaice, suka zuba mata ido, tana kallon Daula yana kallonta yana hawaye itama tana yi.
Ɗayan yace "Wallahi ban taɓa ganin halitta me taurin kan mutumin nan da 'ya' yansa ba, ba dan ba abamu umarnin kisa ba, da wallahi sena musu kisan wulaƙanci mafi azabtarwa"
Ƙarshe haka suka haƙura suka tafi, Widad ta shiga tunanin ya akayi aka kuma shigowa gidan duk da tarin security ɗin nan?
Ɓangaren Daula ma yanzu ya amince dole Widad ta bar ƙasar nan dan tseratar da rayuwarta, kusan kullum cikin turo masa saƙo ake akan idan be bayarba za'a kashe shi, ko a sace 'yarsa, tun yana damuwa harya fara sabawa.
Ya nemi shawarar Bulama, Bulama ya goya masa baya akan ya fita da Widad ƙasar waje, hakan tamkar tseratar da ita ne.
Haka kuwa akayi, Daula ya nemawa Widad makaranta a makarantar masu fama da larura ta musamman a ƙasar England, Anwar kamar yayi kuka, Widad tace tana son ya rakata makarantar, karon farko da Anwar ya hau jirgi.
Daula yace "Mummynki fa bazata rakaki ba?"
Cikin harshen larabci Widad tace "ni ba uwata bace, uwata ta mutu bani da uwa a yanzu, kuma ni mahaukaciyace, babu wanda zeso ya zama maman mahaukaci"
Daddy yai shiru yana kallonta, bece komai ba suka tafi airport, da ita da Daddynta, da Bulama da Anwar suka tafi, tana tunanin irin zaman da Daddynta zeyi da wannan matar me fuska biyu, dan ko a yanzu ta lura da tana wulaƙanta mata mahaifi wani lokacin, kuma baya iyayi mata magana.
Haka aka kai Widad wannan makaranta, aka danƙata a hannun likitocin can ƙasar, Daula yana kuka itama tana kuka suka rabu.
Tun a hanya kewar Widad ta damu Daula, Anwar ne yaita bashi haƙuri, dan Bulama ya gaji da rarrashin Daula.
Haka ya dawo gida zuciyarsa fal tunanin Tilon 'yarsa, yanzu bashi da kowa se Allah se' yar nan, yana mata son da shi kansa be san kansa ba, dan duk ƙaunar da yakewa mahaifiyarta ta koma kanta.
Kamar yadda Widad ta buƙata, wannan Ƙaton gidan nasu na farko, haka ya zuba dabbobin nan a gidan nan, dukda Widad ɗin bata nan.
Kullum cikin hirarta yake da begenta, abun fa ba sauƙi, dan ba'a fasa masa barazana ba iri iri, ta waya akan dukiyar nan, ƙarshe ya ware kason Widad a dukiyarsa, itama yasa mata a kasuwanci aka cigaba da juyawa, haka rayuwa ta cigaba da tafiya.
Da Anwar yayi candy, Daula ya ɗauke shi dashi da Fahad ya kaisu ƙasashen waje yayi sponsoring ɗin karatunsu, da komai da komai.
Amal da Ramlah kuwa manyan makaratun yaran masu kuɗi suke yi, ya mallakawa Halima kadarori da dama, taje Saudiyya ita da yaranta, duk ƙasar da suke so sunje, an kai waninta ma, amma gaba ɗaya bata gani ba, wannan dukiyar ce take hari itama, ga baƙinciki da kishin da take da Widad da Huda wadda ta riga ta rasu, jin maƙudan kuɗin da suke Asusun Widad kawai ba ƙaramin firgita ta sukayi ba.
Saleh kuwa bayan an kama Bala ɗanuwansa, maƙiyan Daula sukayi amfani da shi suka sa aka kai shi gidan Daula yin aiki, dan ya zame musu CID, suka cusa masa aƙidar lallai yaɗau fansar abunda akayiwa ɗan uwansa Bala.
Haka Widad ta cigaba da rayuwa, a cikin mahaukata iri iri, ana cigaba da bata kulawa a can, komai yi musu akeyi, Daula na yawan zuwa ganinta, dan wasu lokutan har gidansa na can yake tafiya da ita, suyi kwanaki su sha hira sannan in ze tafi ya maida ita, lokaci lokaci Bulama ma yakan kai mata ziyara, a bayan gidansu gidan Alhaji Musa yake, dan haka sukan haɗu da juna.
Lokacin da zata shiga high school (secondary school) tace lallai se an cire ta daga makarantar mahaukata, dan ita ta warke, da yake Daula baya son ɓacin ranta haka ya cireta, da yake dama Asibiti ne haɗe da makarantar masu buƙata ta musamman.
Daula ya taho da Hajiya Halima da yaranta, amma a ranar seda jikin Widad ya kusa motsawa, ta birkice masa sosai, tace "kodai su bar mata gidan nan, ko ita ta bar musu"
Daula yace "daughter, Mummy cefa kuma dan su ganki suka zo"
'Daddy karka ƙara ce mata Mummy na, kuma ina neman alfarmarka, idan har ina England karsu ƙara sa ƙafa a ƙasar nan, nan gidan Ammi ne da ita muka rayu a cikinsa, dan haka bana buƙatarsu anan "
Aikuwa jikin Daula yana rawa, aka maida su Hajiya Halima Hotel, abun nan ya baƙantawa Hajiya Halima rai fiye da tunani.
Tun daga nan suka fara takun saƙa, duk isa da hura hancin da Halima take yi se Widad tayi abunda zata nuna mata bata isa ba.
Widad ta shiga high school, itama boarding ce, amma bata mahaukata ba.
Daga ƙasar da take idan taso se tayo waya, ta bada umarni a Nigeria kuma abunda tace shi za'ayi, duk azabar bin malaman Halima, amma ta kasa raba Daula da Widad.
Wataran Widad tazo hutu Nigeria....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: .LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
82_83
Lokacin da tazo Nigeria, maƙerin budurci ya fara ƙera Widad, ta fara zama budurwa me ji da kyau, zamanta a Turai sam bata san saka wata Atamfa ko makamancin kayan al'ada ba, da Amminta na da rai ma mafi yawan rayuwar su tana Turaine, dan haka sedai a saka mata blouse, yanzu kuma babu ran mahaifiyarta, gashi a tsakiyar turawa take, dan haka duk shigar da taga dama yi take ba wanda ya damu, Daula ya ɗaukar mata Nanny, idan anyi hutu tana gidansu na can, ita da Nannynta wata 'yar Nigeria ce amma bayerabiya, sedai a dafa taci, hatta gadonta da zata kwanta ta tashi sedai a gyara mata, saboda haka bata iya komai ba.
Itama Nannyn Widad ba wani yadda take da ita ba, gani take duk wanda ta yadda dashi ze iya cutar ta, ba abunda Widad ta iya na aiki, duk wani abu yi mata ake, ba wata wahala data sani a rayuwar ta, komai ta nema akwai available, kuɗi ko nawa take buƙata akwai shi available.
Widad tazo Nigeria, Daula ya dinga murna dan kusan shekararta Biyar bata taka Nigeria ba, sedai tunda ta dawo babu ragayya ko sassauci tsakaninta dasu Amal da babarsu, sam basa gabanta idan tana rayuwa a part ɗinta mantawa take dasu, Daula ya dinga zagayawa da ita guraren kasuwancin sa, da wanda yasa aka buɗe mata, taje har tsohon gidansu data sa aka maida shi na gona, gurin yayi mata kyau, tasa aka gyara mata wasu abubuwan aka canza mata wasu, ta cewa mahaifinta wato Daula tana son a siya mata dokuna biyu irin na wasan polo a saka mata a gidan, sannan aka kawo wani kare nasu, wanda yake a ƙasar waje, tasa aka kawo shi gidan aka ajiye.
Cikin hira Daula yake gayawa Hajiya Halima batun siyan doki, yace
"kinga rigima irin ta 'yarki ko? Saboda rigima wai dokin polo takeso a siyo a samata a wancan gidan namu, nasa ayo mata order su"
Dama Hajiya Halima tayi tayi su koma wancan gidan, dan yafi haɗuwa da girma amma Widad tace baza"a koma ba, ƙarshe ma tasa aka zuba mata kiwon dabbobi a ciki, wani ɓangaren gida sosai, wani ɓangaren gidan gona.
Hajiya Halima tace "Yanzu kai Alhaji saboda ka rasa abunda zakayi da kuɗi, seka sai wannan dokunan? Suna fa da tsada, kuma me zata yi da wasu dokuna tana mace"
Daula yace "Ai babu itace damuwa, amma tunda akwai za'a sai mata, ian son abunda takeso, kin san ba wata lafiya ce sa ita ba, shiyasa nake son yi mata abunda takeso, kodan ta samu farinciki, na rasa me zanyi wanda ze dinga ɗebe mata kewa, yasa ta sake da kowa"
Widad data kawo kai zata shigo falon Daddy taji wannan maganar da suka yi, da yadda Halima take kushe a sai mata abunda takeso, Widad ta maze ta shiga falon ta kalli Daula tace
"Weldone Dad"
"Weldone my Queen, how are you?"
"Fine Daddy"
Yace "Masha Allah, Alhamdilillah, ya akayi ne, ko zuwa zanyi?"
Widad tace "No but Daddy, i see over twelve cars in the parking space, what are they used for?"
Daula yayi murmushi yace "na gidane, wanda muke hawa, ni nawa biyune kawai sauran na mamanki ne da Yayyaenki, tunda kinzo kema se ki sai wanda kike so"
Widad ta haɗe rai cikin hura hanci tace "Niba uwata bace, bani da uwa dan haka bata haifeni ba, , and na saka a kwashe motocin a kaimin su farmhouse a ajiye, na barwa kowa mota ɗaya yayi amfani da ita ta isa, kai kuma an bar maka naka my king" ta ƙarasa maganar tana murmushi.
Daula yace "to babu laifi, godiya muke gimbiyar Daula, yadda kikace ai haka za'ayi"
Tayi wa Hajiya Halima wani kallon tsana na baki isa ba sannan ta fice, tana fita Halima zata fara complain, amma Daula ya dakatar da ita yace "itama dukiyarta ce, duk yadda tayi daidai ne"
Halima taji kamar ta samo abu ta kashe Widad dan baƙin ciki, tun daga Nan fa suka dinga takun saƙa da Widad da matar babanta, bata ganin mutuncinsu sam, sannan bata yadda da kowa ba, sakamakon duk wanda suke cutar da Mahaifinta Yaran talakawane daya janyo a jikinsa sukayi Arziki sanadinsa, wanda ya yarda dasu sune suke cutar dashi.
A wannan zuwan ma, seda akai kaiwa Widad Mummunan Hari, akaso a sace ta amma Allah ya kuɓutar da ita, daga nan ta tattara komatsanta ta koma England ta cigaba da zuwa makaranta.
Daula ya bubuɗe guraren kasuwanci da kuɗinta, ciki hadda manyan gidajen gona, shagunan kasuwa da sauransu, dan haka Widad ma ta kasance 'yace me arziki a ƙashin kanta.
Gaba ɗaya a rayuwarta batayi zaman shekara shida a Nigeria ba, shiyasa abubuwa da dama ita bata sansu ba, ko in anyi take mamaki.
Wannan hali da ta tsinci kanta a ciki a rayuwarta yasa, ta yanke ƙauna da samun mutanen kirki, wanda ze zauna da kai a halin akwai ko babu, kuma ta yadda cewa duk talaka ze iyayin komai akan kuɗi, ta yadda idan har ka amince da mutum ya shiga jikinka, shine na farko daze fara cutar ka, ta lura mutane da yawa suna nuna mata kulawa ita da mahaifinta ne saboda wannan dukiyar da suke da ita, da babu wannan dukiyar da ba zasu dinga mutuntasu haka ba, dan haka itakuma take taka duk wanda taso.
Tun data bar Nigeria a wannan lokacin bata kuma dawowa ba, seda ta cika shekaru goma sha takwas, bayan shekara huɗu kenan, lokacin ta zama cikakkiyar budurwa, yanayin tsarin rayuwarta duk na turawa ne, dukda hali na rashin sakewa da mutane da take dashi, amma tana zuwa gurin shaƙatawa da buɗe ido.
Bayan gama high school ɗinta tace a Nigeria zata zo tayi karatun Jami'a, saboda kawai ta ƙallafa ran seta ta gano suwaye kuma suke da sa hannu akan kisan mahaifiyarta, suke cigaba da bibiyarta da mahaifinta akan dukiyar nan? Kuma tana son nunawa Hajiya Halima iyakarta saboda zaƙewar da take tayi yawa, da yadda take juya Daula yadda take so.
A wannan dawowartata ne aka kawo mata kusan direbobi uku, amma da sun fara aiki se taga kamar an haɗa baki dasu zasu cutar da ita, dan laifi ƙalilan seta kori mutum, bata ragayya bata sassauci bata afuwa ga ƙarya ko yaudara.
Dukda wannan tsawon shekaru, Magungunan nan basu dena aiki a jikin Widad ba, sakamakon ƙarfinsu ne da pressure da suke bawa jikinta yasa ta kamu da ciwon zuciya, ko kuma haka nan jikinta ya rikice ta fara wannan tsoron.
Widad ta ɗanyi shiru sannan tace "Nasan akwai abubuwa da nayi da kake buƙatar sanin dalilina na yinsu, akwai ranar da mukaje Hotel nace maka ni karuwa ce, naje wannan Hotel ɗinne, dan ganewa idona wani abu kuma na gani, wasu mutane ne da nake zargi da sa hannunsu, na gansu tare da matar Daddy, da alama sunyi meeting ne, kuma nasan akan Daddy ne, munje Club tare ranar harka hanani shiga, naje ne domin in kama Fahad red handed ta yadda maganar Aure tsakanina da shi zata rushe, haka nan tun zuwanka naji wani sashi na zuciyata nason Amincewa da kai, dukda wani ɓangaren yana gargaɗina, nace bari in jarrabaka tukuna, duk inda zanje nake tafiya da kai, sannan na maka umarnin cewa ban yadda kayi magana da kowa ba duk inda zamuje, saboda ina tsoron a haɗa baki da kai, watarana kana zaune a gidanmu inda ka saba zama, ina kan varrendar na saman bene, kawai na hango Amal taje inda kake, ka taso kuka taho tare, na fito falo inga meze faru, za kayo hanyar part ɗina, se tace maka ai bana nan ina part ɗinsu, ka bita zuwa ɓangaren su, ni kuma na bi bayanku, nasan zakayi mamaki daka fito ka ganni a tsaye a gurin amma ban ce maka komai ba, haka kurum na fara sakewa da kai bayan na gano waye kai, ganin bibiyata da ake ya fara yawa yasa na ƙara jarrabaka, na baka ATM ɗina, ka tafi dashi tsawon sati biyu, a gaban mutanen gidanmu, wanda nasan dole su bibiyeka a kai, amma ga mamakina bayan sati biyu, se gashi ka dawomin da shi, ba tare da ko ƙwandala ta ɓata ba, kuma yana daga abunda ya ƙara nesantani da mutane shine, duk wanda ya raɓeni shima cikin matsala yake shiga, an dinga bibiyarsa kenan dan a samu wannan takaddun, shiyasa nake sake yin baya baya da kowa, sedai kai ka riga ka shigo rayuwata gaba ɗaya, ban iya kareka da shiga hatsarin da nake ciki ba, seda aka ritsa da kai, sannan ƙiyayyata ga Aure kuma ya samo asaline ga yadda naga Bulama ya maida Aure da saki tamkar shan ruwa, nakan bibiyi shafukan sada zumunta na kanga irin complains akan Aure, kuma ga mahaifina yayi Aure, Amma matarsa sam baya gabanta abunda yake hannunsa shi takeso, se nake ganin muddin nayi Aure tamkar na shiga matsala ne, kuma komai ze iya faruwa dank, kuma a yadda nake jina bazan zauna ƙarƙashin wani yayi amfani da ikonsa a kaina ya wulaƙantani ba, shine abunda ya faru har zuwa ɗaukemu sa akayi tare, Yoseef wannan shine ƙarshen labarina dana mahaifina, kaga laifina akan AƘIDATA? Ban cancanci in guji mutane ba? Ko kuma rayuwar kaɗaici zata zama laifi idan har nayi hakan ne dan kaucewa tarayya da azzalumai masu biyu? Mutane dayawa basu san meyafaru dani ba, abu ɗaya kullum suke kallo shine AƘIDATA "
Shiru Yusuf yayi, yasa hannayensa biyu ya dafe kansa, Widad tasa hannu ta janye nasa, tace " Kana jina kuwa?"
Wata irin ajiyar zuciya yaja, wadda seda Widad ta ɗan razana, ta ɗau fitila ta haskashi, sedai taga Hawaye a Fuskar Yusuf, jijiyon kansa duk sun ɗaga ya ƙara wani kwarjini, ga ja da idanunsa sukayi, saboda labarin Widad ya kaɗashi matuƙar gaske, gaba ɗayanta abun tausayi ce, taga jalala da iftila'i me ban tausayi, a kashe maka mahaifiya a haukata maka tunani, sannan a cigaba da bibiyar rayuwarka da barazana da tsoratarwa iri iri.
"Shiyasa na dinga ja maka rai fa akan baka labarin nan, kalli yadda ka ɗaga hankalinka hadda kuka, dan Allah kabari Yoseef, ni yanzu na fara mantawa da wasu abubuwan saboda sadaukarwarka a gareni, baka yi sallar isha'i bama, gashi yauma munyi dare, kayi salla kaci Abincinka seka kwanta "
Bece mata komai ba ya miƙe, sosai yake jin tausayin Widad, gaba ɗaya labarin nan ya tsaye masa a ransa, Widad ta koma kan shimfiɗarta, sannan ta fara zubda nata hawayen dan bata son ta sake ɗaga masa hankali, tana kallonsa sau biyu yana sake sallame salla, yayi ya idar nan ma ya daɗe sosai akan sallayar sannan ya tashi, be ko kula Abincin ba, shimfiɗar ma beyi ba a ƙasa yaje ya kwanta a rigingine.
Nanfa Ƙwaƙwalwarsa ta shiga kaiwa tana komowa akan abubuwa da dama, da irin binciken da yayi, lokaci lokaci idan ya tuna labarin Widad se yaja tsaki, dan ya rasa a inda yakamata ya ajiye wannan tsagwaron zalunci haka.
Ƙarshe ma tashi yayi zaune ya sake dafe kansa, sedai Duk abun nan Widad tana kallonsa, tana tunanin yanzu akwai wanda zeji labarin abunda ya sameta ya tausaya mata haka, harya shiga wannan irin damuwar? Dukda tarin wulaƙanci da isa data dinga nuna masa, amma ya dake ya shanye har yake jin tausayinta haka, bayan ɗawainiyar da yayi da ita, da ƙoƙarin kareta daya dingayi, lokacin da akazo sace ta ba dashi sukayi niyyar ɗauka ba, ya dage ba zasu tafi da ita ba, shine suka haɗa dashi, ga wahala da azaba da ya sha gurin kuɓutarsu, gashi har yanzu a kan shan wahala yake, a rayuwar da tayi idan akace mata akwai mutum me irin zuciyar Yusuf a zamanin nan to tabbas za tace ƙaryane, ita kam me zata yiwa Yoseef, ta saka masa tasan ko duk abunda ta mallaka zata bashi bata isa ta biya shi ba.
A hankali ta tashi ta tafi inda yake zaune ya rafka tagumi, ta janye hannun tace "wai bazaka kwanta bane? Kuma ina shimfiɗar kake zaune a ƙasa haka?"
"Bana jin bacci" ya bata amsa
"ko Abinci ma fa baka ciba, ga yunwa ga rashin bacci? Gaskiya ban yadda ba"
Yusuf yace "kije ki kwanta kawai, ni bana jin bacci"
Tace "Shikenan nima bana ji, bari mu zauna kawai"
"A'a, kije ki kwanta kinji nasan zaki bacci idan kika kwanta"
Tace "shikenan, kwanta se in kwanta a jikinka"
Yusuf yace "No jikinki ze ciwo, ki kwanta akan katifarki"
Tai murmushin ƙarfin hali tace "baka san jikinka yafi katifar nan daɗin bacci ba, kwanta se in kwanta"
Haka Yusuf ya kwanta, ita kuma ta kwanta a jikinsa, tasa hannu ta zare ribbon ɗin kanta, ta kamo hannunsa ta ɗora a kan gashin ta, a hankali ya rungumeta da hannu ɗaya, yasa hannu ɗaya yana wasa da gashin nata.
Tana jin yadda zuciyarsa ke lugude da ƙarfin gaske, ya zamana ma taji kamar baya numfashi daidai, dukda a duhu ne amma Widad ta gane har yanzu Yusuf kuka yake, yana da matuƙar dauriya da juriya, amma wannan karon ya kasa jurewar, saboda jin Widad yake tamkar wani sashine na tsoka a zuciyarsa, haka kurum yake jin kamar shi akayiwa laifin ma ba ita ba.
Ƙanƙame Yusuf tayi ta fashe da kuka, Cikin jan numfashi Yusuf yace "Widad lafiya, kukan me kike kuma?"
"Dan Allah Yoseef kamanta da labarin nan da na gaya maka, karkasa shi a ranka dan Allah, kar wani abu ya same ka ji yadda kake numfashi fa"
Sosai ya sake rungumeta yace "Never mind dear, ba abunda ze sameni insha Allah, ina tunanin meye mafita ne kawai, a shirye nake da in baki gudunmuwa kota wani ɓangare dan tina Asirin wanda suke aikata muku wannan zalunci haka, amma kafin nan nasan koba duka ba kin san wasu daga cikin mutanen nan, meyasa kika ƙyalesu baki tona musu Asiri ba? "
" Yossef yadda nake shiri akansu haka suke yi a kaina, sun fini iya mugunta da zalunci, na haskawa mahaifina wasu daga cikin su, hakan yasa ya yanke hulɗar kasuwanci da wasunsu, sannan wace hujja nake dashi daze tabattar da abunda nake zarginsu? Bani da sheda se Allah"
Cikin raɗa Yusuf yaje dai dai kunnenta yace "meyasa kika ƙyale Bulama, bayan ko a binciken da nake, ina sanya babbar alamar tambaya a gareshi, dan sam ban yadda da shiba, amma naga kina masa kallon uba, kuma ni shine babban suspect ɗina"
Widad tace "saboda ko yana ciki ni ba ta tashi nake ba"
"Meyasa?" Yusuf ya tambaye ta.
"Saboda bashi nake hari ba, Bukar nake hari, na barwa zuciyata insha Allah koni ko shi, ko kuma muyi mutuwar kasko dashi, Insha Allah se Bukar yaje ƙiyama da tabon da zan masa, ya azabtar da rayuwata, yaso kassarani da mahaifina yamin zalunci mafi muni, wannan abunda akayi mana nasan da sa hannunsa, da Bukar da Baban Nurat sesun wulaƙanta a rayuwa, sun cutar dani Yoseef " tai maganar tana fashewa da kuka, rarrashinta ya dingayi sannan yace
"Waye kuma Bukar? Banji kin faɗe shi a labarin da kika bani ba"
Ta gyara kwanciyarta sannan tace "Bukar! Bukar! Alhaji Bukar! Tabbas ban faɗeshi a labarin da na baka ba, saboda labarin ma wani sashe na baka, na ɓoye maka wani, na kuma canza inda faɗa maka bashi da amfani, saboda jin wani sashin na labarina a gareka tamkar tarwatsa shirin sa nake ne, amma ina fatan ubangiji, Allah ya maida mu gida lafiya, zan baka sauran ɓangaren dana cire maka a labarin, dan se mun koma gida jin ɓangaren zeyi amfani, har in cika dukkan burikana, sannan a lokacin zan baka labarin waye Bukar "
Yusuf yace " Shikenan, ubangiji Allah ya kawo lokacin da zamu koma, Insha Allah se inda ƙarfina ya ƙare Widad, zan baki goyon baya ɗari bisa ɗari mu shiga kowane irin ƙalubale dan cikar burinki"
"Thank you Yoseef, Allah ya jiƙan magabatanka, nagode sosai"
Tai maganar tana Ƙanƙame shi sosai.
Haka suka kwana a ƙasa shida ita, a gurin nan ga sanyi cikin dare amma basu iya tashi daga gurin ba, saboda damuwar da zukatansu suke ciki.
Umman Yusuf se fama take da hawan jini saboda damuwa da tunani, ga rashin cin Abinci da bata iya ci balle bacci, gaba ɗaya ta rame tayi wani iri saboda tunanin halin da ɗanta Yusuf ke ciki, ga kuma wannan labari daya cika gari, ita dai tasan ɗanta ba mutumin banza bane, dan tasan tabbas wannan zance ƙaryace akayi masa.
Tana nan kwance bayan la'asar a inda tayi salla, tana jan carbi tana ta kai kukanta ga Allah akan Allah ya kuɓutar mata da ɗanta, yasa yana cikin ƙoshin lafiya.
Sallama Suleiman yayi, taja jiki da ƙyar ta tashi zaune da ƙyar ta amsa masa, ya tsorata ganin halin da take ciki, a ɗan firgice Suleiman yace "Umma meyasameki haka?"
Take ta fashe da kuka tace "baka ga Sanarwar da akayi a kafafen yaɗa labarai bane? Wai Yusufana ake nema ido rufe wai ya sace 'ya, haɗuwar Ɗana da wannan alhali ba alheri bane, tunda ya fara aiki da yarinyar nan walwalarsa ta ragu kullum cikin tunani yake, kullum cikin damuwa yake banda sintirin fita da wuri baze dawo ba se dare amma ƙarshe abunda za'a sakamana da shi kenan, bakomai akwai Allah, Allah ya bimana haƙƙinmu"
Suleiman yace "Umma kiyi haƙuri, yanzun ma abunda ya kawoni kenan, amma yanzu zan fara kaiki Asibiti tukuna, a duba ki kamar baki da lafiya"
Umman Yusuf tace "Ni ba inda zani, lafiya ta ƙalau ɗana nake tunani kawai, shiyasa ake ganin kamar bani da lafiya"
Da ƙyar Suleiman ya lallaɓata ta yadda ya kaita Asibiti, sukaje akayi mata gwaje gwaje, akace hawan jinine ga ulcer, aka rubuta mata magunguna sannan ya ɗauketa zuwa gida.
Suna tafe tana share hawaye, bayan ya kaita gida yace "Umma ki kula da magungunanki, kidinga shansu akan lokaci, sannan shi lamari irin wannan Addu'ar ku muke nema, idan harda Addu'ar ku, babu wani abu daze same mu insha Allah, Yusuf Addu'ar ki yake nema kiyi haƙuri, komai ze daidaita insha Allah"
"Amma Suleiman, kana ganin yau watanni huɗu kenan, ban saka Yusuf a idona ba, baya nan ban san idan yake ba katsam kuma inga wannan al'amari haka, kuma naji labarin Abokinsa Abbas yazo, amma ko jaje bezo yamin ba"
Suleiman yace "ki kwantar hankalinki Umma, Abbas baze dawo miki da Yusuf ba, ki manta dashi, Insha Allah muna nan muna ƙoƙari akai, sannan insha Allah zan kawo miki kayan Abinci dana buƙata, amma kisa haƙuri a ranki"
Umma tace "shikenan, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah yayi maka albarka ya raba ka da duniya lafiya"
Suleiman yace "Ameen" sannan ya tafi.
Aka cigaba da yamaɗiɗi da zancen Yusuf, akan ya sace Widad ya gudu da ita, fastocinsa suka cigaba da yawo, dayake in Allah yasa kana zaman lafiya da kowa, baka rasa masoya, wanda suka san Yusuf suka san halinsa suka dinga ƙaryatawa, suna taya shi da Addu'a.
Ramlah na kwance akan gadon ɗakin Hotel, Fahad yana tsaye yana taje kansa a gaban mudubi, Ramlah tace "Fahad, lokaci fa yana ƙurewa, zuwa yanzu yakamata ace an fara maganar aurenmu, amma naga kamar baka damu ba ko zancem baka yi"
Fahad cikin salonsa na yaudara yace "Beb kin fiye garaje fa, mubi komai a hankali mana, nida nake so ayi classic wedding, so nake bikinmu ya zama the expensive wedding of the year, wasu kuɗi nake jira a hannun Dad, shiyasa amma kiyi haƙuri, soon za'ayi komai insha Allah"
Ta ɗan kwaɓe baki tace "Allah yasa, danni ina ma tantama akanka, kar inje Widad ta dawo kaƙi Aurena kace se ita, dan haka kayi min wancan karon"
"No karki damu, ai abunda yaaa nace zan Aureta, saboda in karɓo mana kuɗaɗen hannunta ne, in rabata da komai im azabtar da ita, sannan in sake ta, that's my plan, but unfortunately it's fails, ni yanzu wannan jakin daya gudu da ita, Allah yasa karya karɓe abun ya barmu "
Ramlah tace 'kamar kuwa ka sani, dan wallahi zata iya bashi, can you imagine ATM ɗinta yayi over 1 week a gurinsa, naje masa mu haɗa kai a samu wani abu amma fafur yaƙi, munafuki se gashi yayi awon gaba da ita"
Fahad yace "suje su ƙarata, ai tunda ba' a san inda Dad ɗinta yake ba, zan cigaba da kawo masu siyan kadarorim nan, a rage wani abun"
Ramlah tace "hakane kam, nidai so nake ayi muyi Auren nan, kaga sau biyu ina abortion fa"
"Ai kece, nace miki kije kiyi planning, amma kinƙi"
"Aini kasan abun planning ɗin nan, suna da nasu matsalolin, ɗan bani tablet biyu in saka a coc, i want doze up"
Ya miƙo mata magani, ta zuba a lemo ta girgiza tasha, sannan ta kwanta bacci.
Ya kalleta a ransa yace "baki da hankali, uban waye ze Aureki ashe ma bani da hankali, zanta lallaɓaki ina morewa, gefe guda kuma in cigaba da damfararku"
Yauma Yusuf se a ɗaki sukayi salla, dan bacci be ɗauke shi ba, se daf da Asuba.
Bayan sunyi salla, suka koma suka kwanta bacci, sedai shi Yusuf baccin ya gagareshi sam, a cikin tunanin ma ya raaa wanne zeyi, se kusa ƙarfe goma sannan ya kwantar da Widad ya tashi ya shiga gyaran ɗaki, ya shaee ɗakin ya haɗo kwanukan wanke wanke ya fito tsakar gida.
Da Hanne yayi karo tana shara, tana ganinsa ta zuba masa ido tana murmushi, Yusuf yace mata "Ina kwana"
Cikin yashe baki tace "ina kwana"
Yusuf yace "lafiya ƙalau kina lafiya"
"Lafiya ƙalau, kawo in wanke maka kwanukan"
Yusuf yace "A'a, yi shararki kawai"
"bakomai kiyi aikinki kawai"
"A'a dan Allah ka kawao"
Tasa hannu ta karɓa, Yusuf ya koma ɗaki ya dafawa Widad ruwan wanka, sannan yaje ze tasheta.
Zama yayi ya zuba mata ido, yana jin ƙaunarta da wani irin tausayinta yana ratsa ko ina na jikinsa
Numfashin da yake mata a fuskane yasa ta buɗe ido tana kallonsa, har yanzu idon Yusuf ja, ga alamun damuwa nan ƙarara a fuskarsa.
Yusuf yace "tashi ga ruwan wanka nan, kiyi wanka ki karya"
Miƙa tayi tana ɗan lumshe ido, Yusuf se binta da kallo yake.
"To ka matsa in tashi mana, ka danne ni kuma kana ina tashi"
"Widad bana gajiya da kallon ki, nidai ina sonki Widad"
Ajiyar zuciya tayi, ta shafi sajensa a hankali tace "naji ɗagani in cire kaya inje inyi wanka"
Maimakon ya ɗaga ta seya sake gyara kwanciya a jikinta, yana kuma nanata mata "ina sonki Matata, ina sonki Widad"
Gaba ɗaya taji wata kasala na saukar mata, batayi magana ba sedai tasa hannu ta rungumeshi itama.
Hanne cw ta bankaɗo ɗakin sannan zata yi sallama.....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
84_85
Yusuf ya ɗago da sauri, yayin da jikin Hanne ya ɗau rawa, ba tare da tace uffan ba ta ajiye kwanukan da ta wanke, jikinta na rawa ta fice waje, yayin da wani abu kamar dutse yazo ya daskare mata a ƙirjinta, tana tafe amma kamar ta kifa, danko gabanta bata gani, maimakon taji haushin Yusuf, se wani tuƙuƙin tsanar Widad da taji a ranta, kamar ta janyo ta ta shaƙe haka take ji.
Widad kuwa tsaki tayi, ta haɗe rai tace "kaga malam ɗagani mana"
Yusuf yace "to nikuma meye laifina da zaki wani haɗemin rai haka?"
Ta ƙara haɗe rai tace "kaika sani dan Allah nika ɗagani, ina da abunyi fa"
Yai ƙasa da murya yace "My queen..
Ta katse shi ta hanyar cewa" dan Allah malam ka ɗagani nace, bana son jin komai daga bakinka, kuma karka ƙara bawa wata 'yar ƙauye kwanukana ta wanke min na gaya maka, in bahaka ba nika ajiyemin abuna zan wanke, idan kuwa ta sake wanken kwanuka na, wallahi sena zuba su gaba ɗaya a wannan rijiyar ta gidan nan, kuma idan na kuma ganinta a ɗakina duk abunda nayi mata ita ta janyowa kanta na gaya maka "
Yusuf ya ƙura mata ido, yana kallon yadda take masifa fuskarta na bayyanar da matsanancin kishin dake zuciyarta, amma yanzu daze ce tana sonshi seta fara masa iyayi, tana ita bata san so ba, kawai dai danya temake ta ne.
Ta ture shi daga jikinta, ta miƙe tana kumbure kumbure ta cire kayanta ta tafi wanka.
Bayan fitarta ya miƙe, ya gyara mata shimfiɗarta, Gwaggo ta aiko musu da Abun karin kumallo.
Koda Widad ta fita tsakar gida, tana kallon mugun Kallon da Hanne ke mata, banda Widad na ganin darajar Gwaggo, da ba abunda ze hana tayiwa Hanne rashin mutunci me wuyar mantawa, amma ta ƙyaleta taje tayi wankanta.
Data dawo ɗakima Yusuf yana ta ƙoƙarin rarrashinta, amma ta basar dashi taƙi kula shi, ta barshi yaita ɓaɓatunsa shikaɗai, ta ɗakko kaya zata saka yazo ya karɓi kayan daga hannunta, amma tasa hannu fizge abunta, sosai kishi me zafi ya bayyana a fuskarta, Yusuf yace bari yayi amfani da wannan damar gurin jarraba Widad, bari yaga idan dagaske kishinsa take ko kuwa?.
Ya koma gefe ya zuba mata ido, tasa kayanta, ta koma gefe tana shafa mai tai kicin kicin da fuskarta, kamar ba itace suke tare ɗazu ba cikin farin ciki.
Yusuf yace "Allah sarki rayuwa, Ohh koya Amal ɗina tayi da taji an sace mata ni, Amal ta gama matowa a sona, she really loves me, ga Nurat ma light, ga fara'a ga kirki she also loves me, itama ban san ya zataji ba, ga Sakina abokiyar aikina, abunda ya hana in bawa Sakina fuska shine shigar matsatsun kaya, da yawan kule kulen maza, se gashi Allah yasa na Auri me sa matsatsun kayan, ga tsiwa gashi sam bata sona, taita bani wahala, gashi ina matuƙar sonta, kissing ɗinta in nayi ta dingamin faɗa kenan tanamin tsiwa, laifi koni nayi ko bani nayi ba taita fushi dani, bata tausayina sam, nikaɗai nake sonta, Nasan da Nurat na Aura dana huta, zan sha soyayya dan akwaita da tausayi da sanyin hali, sannan masha Allah, gata da lips masu kyau, nasan ita ba zata dinga ƙyamata ba, ko kissing ɗinta na....
Aibe ƙarasa ba yaji saukar ludayin roba a ƙeyarsa, seda ya razana ya kalli inda Widad take, kawai ta fashe da kuka harda hawaye.
Yusuf yace "Ke lafiya Mena yi miki kuma? Kinƙi kulani nazo ina hirata kuma seki jefe ni, sekin jimin rauni tukuna, mu koma gida 'yan matan nawa duk su gujeni?ko kuma su kasa ganeni?"
Aikuwa ta ƙara sautin kukan nata sosai, harda sheshsehseƙa, wani guntun murmushi yayi a ransa yace' yarinya kin faller '
Amma a zahiri seya miƙe, yazo inda take yace " Widad, meyasa ki kuka ne? Kowani abun nayi miki ne?"
Cikin shagwaɓa Tace" Nima ban sani ba"
Yusuf yace "to meyasa kika jefeni da ludayi? Baki san naji zafi ba?"
"Ni bana son zancen da kake ne, raina ɓaci yake ni karka ƙaramin zancen wata a gabana, bana so am feeling bad, ni gaba ɗaya ma zuciyata haushi nake ji"
Yusuf ji yayi kamar ya ƙyalƙyale da dariya, amma yasan yana yin hakan, sabuwar rigima zata saka masa, dan haka yace
"Ohhh shikenan ya isa haka, am very sorry bazan sake ba, dena kukan kinji abar sona, na dena insha Allah dena kukan haka kinji gimbiyar"
Ya dinga share mata hawayen da yake ta binta fuskarta.
Widad ta ture hannusa cikin zumɓira baki tace "ni rabu dani, tunda ka sani kuka"
"Yi haƙuri I don't mean to hurt you Baby, ban zaci ranki ze ɓaci ba, kinga se binki nake ina magana amma kika shareni, se da ki kaji nafara lissafin 'yan matama sannan kika hau kuka"
Widad tace "to waima meyasa nayi kuka ne?"
Yusuf yace "Oho nima ban sani ba, aike zan tambaya" Yusuf ya bata amsa ɗan taɓa baki tayi ta ɗanyi tsaki sannan tace
"wai dagaske Nurat ma budurwarka ce?"
Yusuf yace "A' a naje gidansu dai, bayan mahaifinta yayi yunƙurin sawa a sace ki, ita na ritsa da bindiga ta gayamin inda kike, bayan nan na koma gidansu, dan inyi mata wasu tambayoyi, da farko ta tsorata daga baya kuma ta saki jiki, muka dinga hira a haka na samu abunda nake son ji daga gare ta, har mukayi exchange na lamba, akwai ranar da muka fita dake, nakw waya nace ina tare da matata ne, ai da ita muke waya, sedai daga baya na fuskanci Nurat ta kamu da sona ne "
Widad tace "kuma kaima kana son ta"?
"To waike meye naki na tambaya ne? Bayan kince bakya sona, ina ruwanki ki ƙyaleni in samo mesona, wanda bazata gujeni ba kota dinga min tsiwa ba"
Ɗan guntun tsaki tayi, tare da jin haushin kanta ko meye na damuwa ma oho, ta janyo kwanon Abinci ta buɗe, kofin an zuba kunun tsamiya, kwanon kuma wainar gero ce an barbaɗeta da ƙuli ƙuli, Widad tace "wannan wane irin Abinci ne kuma, shima wani baƙi dashi??"
Yusuf yace "wainar gero ce"
Tace "Meye kuma wainar gero, mutanen nan suna son yin Abinci baƙi" tai maganar Tare da saka hannu ta fara yashe ƙulin kai tana lashewa, Yusuf ya kalle ta yace "bismillahi, kwaɗayayyiya zaki cinye ƙuli ƙulin ki barmin gaya ko? Dama kin saba"
Hararsa tayi ta cigaba da lasar ƙuli ƙulinta, Yusuf yace "baze fa yuwu ba, se saka yawu kike a jiki, idan muka koma gida sena gayawa Daddy yadda kike bani wahala, duk na rame kekuma ƙibarki kawai kikeyi"
Duk da a fusace take amma murmushi ya suɓucemata tace 'kamar kasan akanka Daddy ze iya zaneni ma inaga, dan yana matuƙar sonka sosai"
Yusuf yace "nima ina sonshi sosai"
Widad ta kalle shi da sauri tace "dagaske? Kana son Daddyna?"
Yusuf yace "sosai makuwa, ai bazan manta alkhairinsa a gareni ba, kuma koba komai ko bama tare, yana da matsayi a gurina saboda na taɓa Auren 'yarsa, dan haka inajinsa kamar mahaifina mussman yadda yake girmamani"
Widad ta jinjina kai, har cikin ranta taji daɗin yadda Yusuf yace yana son mahaifinta harya ya beshi haka.
wainar geron nan ba ƙaramin daɗi tayiwa Widad ba, ta saki jiki taci sosai, sed suka gama faɗansu da Yusuf sannan ya fita.
Widad ta fito tsakar gida, amma bata ga Hindu ba, ta kalli Hansai tace "wai ina Hinduna ne yau ban ganta ba fa"?
"Hindunki a ina?" Hari ta faɗa tana yatsune fuska.
Banza Widad tayi mata, ta kafe Hansai da ido tana jiran amsar tambayarta, Hansai tace "Zazzaɓi take yi, tana ɗakin Gwaggo a kwance"
Widad tace "subhanallah garin yaya?"
Hansai tace "larura daga Allah mana"
Widad ta tafi ɗakin Gwaggo, ta tsaya a bakin ƙofa tayi sallama, Aka amsa ta nemi izinin shiga, sannan ta shiga.
Jamila na zaune a gefe tana shayar da jaririyarta, yayin da Hanne keta ƙoƙarin gyara ɗakin Gwaggo, Gwaggo kuma tana ta rarrashin Hindu taci Abinci amma taƙi.
Gaba ɗaya damuwa ta bayyana a fuskar Widad.
Jamila ta kalli Widad tace "ina kwana?"
Widad ta kalli Jamila ta ɗauke kai, tazo ta nemi guri ta zauna a gaban Gwaggo tace "Mama, meyasa ba'a gayamin Hindu ba lafiya ba?"
Gwaggo tace "ahh haba, ya za'ai a takura miki, amma yanzu ai gashi da kika fito kinji"
Jamila taji haushin sharetan da Widad tayi a karo na biyu, kuma tana ji tana mata magana.
Cike da tausayawa Widad tace "sannu Hindu, Allah ya baki lafiya"
Hindu tayi murmushi tana gyɗa kai, yayin da Hanne se cika take tana batsewa, tana faman jan tsaki kamar wadda akayiwa wani abu, dan data tuna a yadda ta gansu itada Yusuf se taji kamar ta fashe da kuka.
Widad ta kai Hannu ta taɓa Hindu, jikinta zafi sosai Widad tace "Gwaggo, baza'a kaita Asibiti ba? A kaita a duba ta mana"
Gwaggo tace "hmm Amarya kenan, da kinsan azabar tazarar dake tsakaninmu da Asibiti da baki ce a kaita ba, bamu da Asibiti a garin nan, ƙauye uku zuwa huɗune tsakaninmu da Asibitin shaka tafi, yanzu kafin a kaita ma wani wahalar ne, duk seta galabaita"
Widad ta girgiza kai tace "ni wallahi ina mamakin yadda za'ace mutane suna rayuwa babu Asibiti a guri, ai wannan se mutum ya rasa ransa ma ba'a bashi wani agaji ba, haba dan Allah to yanzu ba abunda za'a bata"?
"A'a na ɗan jiƙa kayan magungunanmu na gargajiya, na ɗan bata shima kuma tayi amansa"
Widad tace "Mama nifa bana son wannan kayan jiƙe jiƙen, su ba ƙa'ida ne dashi ba kawai sha akeyi, kuma kayan ciki basa san wannan jiƙe jiƙen, yanzu se wani abun ya taɓu, bari Yoseef ya dawo, in da sauran nasa magungunan se a bata"
Hindu tace "Nagode Amarya"
"Ba godiya tsakaninmu Hindu"
Jamila abun ya bata mamaki taji Widad na hira haka, kuma ta iya hausa amma tayi mata magana taƙi kulata.
Bayan Widad ta gama duba Hindu, ta tashi ta fita, Gwaggo ma ta fito tsakar gida, Jamila tace "wai nikam wacece wannan? Tana ji ana mata magana amma tana wani jin kanta tana share mutane"
Hanne tayi tsaki tace "bar shegiya, haka take wannan wulaƙancin dan tama ganinta a koɗe kamar an wanke karas, taita wa mutane wani iskancin banza da taƙama, se tsabar rashin kunya da rashin tarbiyya, ko magana bata iyaba ga ƙaryar masifa, komai seta dinga nuna bata sanshi ba, saboda gogewa mutane hadda "
Hindu dukda jin jikin da take, ba zata iya jure jin ana cin zarafin Widad ba, Hindu taja tsaki tace " Wallahi Jamila ba bata da mutunci bane, ni baki ga yadda tamin ba, bata da wata matsala, sedai bata sakin jiki da mutane, seta daɗe tukuna, bata fiye son mutane bane, amma Hanne san zuciya ne yasa kike cewa bata da mutunci"
A fusace Hanne tace "dalla malama yiwa mutane shiru, aikin banza uwar shisshigi se wani naniƙe mata kike kina cusa kai ba kwarjini, aikin banza dana wofi kawai"
Jamila tace "ya isa haka, ke Hanne abun faɗa baya miki wuya yaseen, har yanzu kina nan da tijararki baki dena ba"
Hanne ta riƙe ƙugu tana harare harae tace "ƙwarai kuwa, wallahi anamin nake ramawa ehee, babu 'yar masu baƙin jinin da zan saurarawa"
Shiru Hindu tayi, jin Hanne na ƙoƙarin fara ci mata fuska, Jamila tace "Hanne meye hakane? Nace ya isafa"
Hanne ta zumɓura baki tai waje, yinin yau Widad kanta bata da sakewa, ji take kamar itama bata da lafiya, Hindu tana matuƙar birgeta saboda biyayyarta da haƙurinta, shiyasa idan bata nan ko bata walwala Widad ma take shiga damuwa.
Saleh kam kwana biyu yayi ya koma kano, yaje ya tarar abubuwa nata sake rikicewa, dan ya fara karaya ya zubawa sarautar Allah ido, saboda tarakun da'aka kafawa Yusuf, ubangiji Allah ne kaɗai ze iya fidda shi, dan babu imani babu tsoron Allah ko tausayi a tare da su Alhaji Musa.
Saleh yana gidan da yake zaune, yaji ana buga ƙofa yana zuwa ya buɗe yaga Abbas, Saleh yayi murmushi yace "Ahh saukar yaushe haka? Shigo daga ciki mana"
Abbas yabi bayan Saleh suka shiga, har falon Saleh, Abbas yace "ai yau sati na guda a garin nan, nazo in ɗan huta ba inda nake zuwa shiyasa baka ganni ba se yau"
Saleh yace "Allah sarki, to ya Hanya?"
"Hanya Alhamdilillah, dan mun shata kam"
"to masha Allah"
Saleh yace "wai ni kuwa nace ya ake ciki ne? Har yanzu babu wani labari ne? Tun tafiyata banji wani motsi ba har yanzu ba'a samu komai bane?"
Saleh yace "haryanzu ba wani abu fa, ana ta fama ne abun duk se a hankali, shi can ya gudu ba'a san inda suke ba, shima kuma an sace shi, shi Daula babu wanda yasan inda yake haryanzu, anata fama ne"
Abbas yace "Ai naga sanarwar da aka yi akan Yusuf ne ya sace Ita 'yar Daula, hakan yayi ai hakan shine zesa hankalin mutane ya ɗauke daga yin zargi, se a koma sauraren ta inda za' a gano su, ni babban abunda yake damuna ma kar muje ta bashi takaddun mu muna nan, dan wallahi ba kaga alherin da take masa ba"
Saleh kallon Abbas kawai yake harya kai aya, sannan ya numfasa yace "insha Allah, babu abunda ze faru, kota bashi takaddun babu yadda zeyi dasu, su Munir su suka san kan dukiyar, su suka san yadda za'ayi lamarin ya wakana, karka damu komai ze tafi daidai, sedai kamar yadda na gaya maka kansu suma a rarrabe yake yanzu haka, karka yadda wani ɓangare yazo ya nemi wani abu a gurinka, ka yadda ka bayar, karmu ɗau side mu zama a tsakiya, tunda bamu san ɓangaren da zasu yi nasara ba"
Abbas yace "dan wannan, ai karka damu tuntuni kamin wannan kashedin, kuma naji na ɗauka, dan haka ka kwantar da hankalinka, sedai muna biue dasu, zuwa lokacin daza'a samu ɗin"
Saleh yace "hakanma dai dai ne"
Daga nan suka cigaba da hirarrakinsu.
Daga baya kuma suka yi Sallama, Abbas ya shig motarsa sega kiran Suleiman, ya ɗaga yana faɗin "Allah ya temaki Oga, barka da yamma"
Suleiman yace "Yawwa barka Abbas, ya kake ya aikin?"
"Alhamdilillah Oga"
"Good, naji ance ka shigo garin nan, inba damuwa ina son mu haɗu gobe in Allah ya kaimu"
Abbas ya ɗanyi Jim sannan yace "shikenan Oga, yadda kace kaman da ƙarfe nawa?"
"Kamar goma na safe, muhaɗu a office"
"Shikenan, Insha Allah zan shigo"
Yana kashe wayar, Saleh yaja tsaki yace "Aikin banza munafukan banza, da kai aka haɗa baki aka canzamin gurin aiki, aka maida Yusuf kan kujerata, aiga abunda ya sameshi nan, Allah ya ƙara masa saura kaima"
Ya ajiye wayar yana ƙwafa, ya kunna motarsa sannan ya tafi.
Nurat ta rame tayi duhu, gaba ɗaya bata jin daɗin komai, tun mahaifiyarta tana rarrashinta harta haƙura, ita zatonta halayen mahaifinta ne suka sa tashi ga wani hali, bata san me yake damunta ba, ko Abincin kirki bata iyaci, ga wunin ɗaki data tsira, seta wuni cur bata fito ko falo ba tana ɗaki, Abinci in an kaimata ba zata ciba, sedai idan Mahaifiyar tace ta shiga ta sata a gaba shine zata ɗanci kaɗan, fuskar nan tayi fayau bakoma se dogon hancinta da idanuwa saboda damuwa.
Shikuwa mahaifinta sabgar gabansa kawai yake, yana ta faɗi tashi yana kashe kuɗi gurin malamai da 'yan tsibbu, da gurin manyan' yan siyasa domin ya samu ya koma takarar ɗan majalissa da Daula ya tsaya masa yayi, gefe guda kuma sunata cigaba da ƙulle ƙullen yadda ko sun rasa wanccan kuɗin, su samu wani kason ta ɓarauniyar hanya.
Yanzumu shiryawa yayi tsaf, ya tafi gidan Barrister Hafiz da kansa, domin jin inda maganarsu ta kwana akan batun ayi takaddar boge, ayi gwanjon wasu daga kadarorin Daula.
Barrister Hafiz ya karɓi Alhaj Musa hannu biyu, ya masa iso har falo aka gabatar masa da Kayan ciye2, Alhaj Musa ya ture farantin fruit ɗin yace "kafin wannan, dama zuwa nayi inji inda maganar da mukayi ta kwana? Yau kimanin wata guda kenan da yin maganarmu, amma shiru ba amo ba labari bakace mana komai ba, bamu san a ina aka kwana ba"
Barrister Hafiz ya ɗanyi shiru sannan yace "Yallaɓai kamar yadda a wancan lokacin muka rabu akan cewar, zan tattauna da sauran abokan aikin da muka kasance lawyoyin Alhaji Nasir Daula, na bisu ɗaya bayan ɗaya kowa naji ra'ayinsa, na zaɓe wanda nake ganin zasu iya yadda ayi harkar nan dasu, sedai me nazarin da mukayi, da binciken da muka sake yi shine, duk wata kadara da Daula ze siya muna sani, ko ince wasu daga kadarorin daze siya, a gabanmu akeyi da komai da komai, sedai fa takaddun Kadarorinsa babu ɗaya daga cikinmu daya san inda yake ajiye takaddunsa, dukda kasancewar mu lawyoyinsa, 'yar nan tasa dai ita kaɗai ce tasan inda kayansa suke, bakomai muka saniba, munyi tunanin yin takaddar boge kamar yadda kuka ce sedai babu wanda ze iya kwafar sa hannun sa, wataƙila se wannan yarinyar tasa"
Alhaji Musa yai shiru sannan yace, "shikenan ba damuwa, zamuje a bincika dole za'a samu wanda ze iya kwafa, nagode sosai idan akwai buƙatar sake nemanka, zaka jimu nan gaba nagode"
Ya miƙa masa hannu suka gaisa, ya tashi fita.
Nurat ce zaune a bakin gadonta tana ta sharɓe hawaye, wanda ya zamar mata jiki a 'yan kwanakin nan, tayi zurfi sosai a tunani, taji sallama a hankali ta ɗaga kai domin ganin me sallamar barrister Khalil ne, bayansa kuma mahaifiyarta ce, Amsa masa tayi cikin sanyin jiki.
A ɗan razane ya kalleta yace "Subhanallah Anty Sauda dama haka Nurat ta koma?"
"to gata nan dai, shiyasa na kiraka ai, ban sani ba kokai idan kayi mata faɗa taji"
Khalil yace "sistona, meke damunki haka kinga yadda kika rame kuwa?"
Shiru Nurat tayi ba tace komai ba, Khalil yace "gayamin meke faruwa ne?"
Ɗaga kai tayi ta kalli mahaifiyarta ta sunkuyar da kai, Khalil yace "Anty Sauda bamu guri muyi magana"
Ba musu ta juya ta fice ta basu guri, Khalil ya rufe ƙofae, sannan ya ɗakko kujerar gaban dressing mirror ɗinta ya ajiye ya zauna, ya kalleta yace "Nurat, tsakanina dake kin san babu ɓoye ɓoye ko? Bama ɓoyewa juna komai ki gayamin meke faruwa, kin san bazan fallasa sirrinki ba, sirrinki nawane ki gayamin koda taimakon da zan iyayi miki"
Aikuwa ta sake fashewa da kuka, seda tayi me isarta sannan tace "Brother meyasa wayarka bata shiga, na kira layinka babu adadi amma taƙi shiga?"
Khalil yace "wayar aka sa emin a gurin ɗaurin Aure, se yau naje nayi swapping ɗin layin, amma meyasa baki kira ko Mama ba muyi magana?"
Nurat ta goge hawayenta tace "bana son kowa yasan meke faruwa ne, bana son wani yaji shiyasa ban kira kowa ba".
"Shikenan naji, gayamin meke faruwa na ƙagu inji meyasameki haka?"
ɗakko wayarta tayi, ta buɗe labaran da ake yaɗawa akan ɓatan Widad, labarin me ɗauke da hoton Yusuf.
Ta miƙa masa wayar tace "Brother kaga wannan labarin?"
Khalil ya kalli wayar yace "eh naga labarin yana ta zaga gari"
Nurat tace "Allah ya jarrabeni da son wannan bawan Allah brother, kuma wannan shine wanda Daddy na yasaka a gaba, wallahi brother ina tabattar maka da dasa hannun Daddy na aka sacesu, kuma yanzu anyi sanarwa wai shi ya sace Daula da 'yarsa, wallahi baze aikata haka ba brother, dan Allah ka temakeni ka temaki Yusuf "
Khalil yace " yi shiru dena kukan, tsaya yanzu kin zaɓi soyayyarki akan mahaifinki"?
"Brother ba soyayya na zaɓa ba, gaskiya na zaɓa na fifita, na gaya maka komai fa a baya, koka manta?"
Khalil yace "ya za'ayi in manta, ban manta ba kuma indai abunda kika faɗa hakane, to tabbas mahaifinki bashi da imani, yanzu me kike ganin za'ayi? Tukuna ma waishi wannan ɗin waye? "
Nurat tace "direban gidan Daula ne"
"Direba kuma Nurat, to yanzu ya kike son ayi?"
Nurat tace "Sonake a ɓoye, ka bincika waye Yusuf da kuma inda yake, sannan ina son a ɓoye ka cigaba da bin diddigin mahaifina ko zaka samu wani bayanin, wanda ze wanke Yusuf"
Khalil yace "kin haɗani da aiki me hatsarin gaske, amma indai hakan ze sama miki farinciki to zanyi insha Allah"
Ai bata san lokacin da ta faɗa jikin Khalil tana masa godiya ba, kallonta yake yi yana tunani a ransa yace "insha Allah, zan sadaukar da tawa soyayyar dan ganin kin samu taki Nurat"
Zuwa yamma Hindu ta ɗanji sauƙin jikinta, dan harta fito tsakar gidama, Widad tana ta murna, Jamila na jikin ɗakin Hansai, tana wasa da jaririyarta, Widad ta ƙura mata ido kamar tace ta bata jaririyar ta ɗauka, dan ita dai da wayonta bata taɓa ɗaukar jariri ba.
Yusuf yayi Sallama ya shigo, sedai abunda ya ganine yasa ya rikice cikin ɗaga murya yace "Subhanallah......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
86_87
Wato bakomai Yusuf ya gani ba, illa Widad bata taɓa kula Jamila ba, amma taji tana son taje ta ɗau jaririyar nan dako arba'in ba tayi ba, gashi baya tunanin ta taɓa ɗaukar jaririn, Jamila na ƙoƙarin bata 'yar, idan ba'ayi wasa ba tsaf Widad inta ɗauki 'yar nan zata iya jimata rauni saboda yanayin ɗaukar da take shirin yiwa jaririyar.
Yusuf ya ƙaraso da sauri yace "karki bata, bata iya ɗauka ba karta jiwa Babyn ciwo"
Widad ta juyo ta kalleshi, aikuwa ta haɗe rai sosai tace "kamar yaya ban iya ɗauka ba?"
Yusuf yace "eh baki iya ɗauka ba, sekin jima ta ciwo tukuna?"
"wai kai komai ban iya ba, ba a haka zan koya ba, ni gaskiya kabari a bani in ɗauka" tai maganar tana ƙoƙarin cicciɓar ƙafafuwan jaririyar"
Yusuf yace "yi haƙuri tsaya kiga yadda za'ayi, bari in ɗauka ni se in baki"
Yusuf ya karɓi jaririyar, dake ta bacci, yayin da Jamila kuma rigimar Yusuf da Widad suka burgeta matuƙa suka bata dariya.
Yusuf yace "muje ɗaki in baki ki ɗauka"
Yana tafe tana biye dashi har ɗakinsu, suna zuwa ta zauna tace "to zauna ka bani"
"Kedai akwai garaje"
Yusuf ya zauna ya nuna mata yadda zata yi da hannunta, sannan ya ɗora mata Jaririyar a hannu, jaririyar dai baƙace sedai fes da ita, an mata wanka an samata riga me kyau, rigar nata ƙamshin miski, da alama Jamila tana da tsafta.
Widad ta ƙurawa Jaririyar ido, ta dinga jin ina ma tatace, ace wannan 'yarta ce, a ranta tace "da ina zan sa kaina dan daɗi'
" Yoseef so nake in ɗaga ta "
" ki ɗaga ta ki kaita ina? "
" Sonake ta buɗe ido in ganta, se kuma in mata wasa"
Yusuf yace "ikon Allah, ina wannan yarinyar tasan wani wasa? Jaririya cefa dan Allah ki ƙyaleta tayi baccinta, idan kika tasheta kuma kuka za taitayi, mamanta ta karɓeta daga hannunki"
Widad tace "to bazan tashe ta ba, amma sonake ta buɗe idonta"
"zata buɗe ne, amma ki ƙyaleta mana tayi baccinta"
"to na ƙyaleta"
Widad ta cigaba da kallonta, tana ta sake ayyana ina ma ace wannan 'yarta ce.
Yusuf yana canza kaya, yana yi yana kallon Widad, dan karya ɗauke ido Widad tayi wani abu daze cutar da jaririyar, Widad ta nutsu sosai danko ƙwaƙwƙwaran motsin kirki ba tayi, ta riƙe jaririyar sosai.
Widad tace ' Yoseef ka samin ita a bayana, irin yadda akeyi ɗin nan"
Yusuf yace "yau naga ta kaina ni Yusuf, Allah ya haɗani da rigimammiyar mace, keda kike koyon ɗaukar jaririyar ma yanzu, shine zaki wani ce a goya miki ita? Zan ƙwaceta in kaiwa mamanta, ki cigaba damin rikici"
Zumɓura masa baki tayi, tana sake gyara zamanta, ya ɗakko Abincinsa ya zauna ya fara ci, Amma Widad ta hau kici kicin ɗaga jaririyar nan wai zata saka a kafaɗarta, Yusuf ya miƙe da sauri yaje ya karɓe yarinyar nan, danma jaririyar me haƙuri ce, ba tayi kuka ba se buɗe ido da tayi tana miƙa.
Yusuf ya fito tsakar gida yace "Mama ungo Jaririyar nan, bawa mamanta ita tun kan Widad tayi aika aika"
Widad kamar zata yi kuka ta biyoshi da sauri tace "Mama dan Allah ki bani, kawaifa dan nace ina son inga ta buɗe ido, shine se cewa yake ban iya ɗauka ba"
Yusuf yace "karki bata, wai sena goya mata ita, ko ɗaukar jaririyar bata iya ba ta ina za'ayi goyo?"
Jamila dai banda dariya ba abunda take yi, Widad tayi kicin kicin ita a dole anyi mata laifi.
Megari dake ɗakin Hansai yana jinsu ya fito yana cewa "haba Malam Yusufa, yama za'ayi kace bata iya ɗaukar jariri ba, Rabu dashi yarinyar kirki Allah ya baki naki kema"
Widad tace "Ameen"
Hari tace "jimin mara kunya, kikace Ameen a gaban mutane, kai Wudas baki da kunya Al'qur'an"
"baza'aji kunyar ba ɗin, meye abun kunya kuma dan nace Ameen"
Jamila taji daɗin yadda dukda Widad bata kula ta amma ta nuna tana son 'yarta.
Bayan sun koma ɗaki Yusuf ya kalleta yace "Sannu uwar rikici"
Murguɗa masa baki tayi, ta tafi kan katifarta tai zamanta.
Yusuf kamar yayi dariya, haka ya dinga dariyarsa ƙasa ƙasa yana cin Abincinsa, har akayi sallar magariba bata kula Yusuf.
Ta fito tsakar gida zata yi alwala, taga Gwaggo tana aikinta a tsakar gida, Widad tace "Mama wai nan garin ba'a samun Irish potato ne?"
Gwaggo tace "meke nan?"
Tace "dankali"
Gwaggo tace "Auho, ai da kiyiwa Yusuf magana, ko kuma Ila idan sunje kasuwa su samo miki"
Widad tace "bafa wannan ba Mama, dankalin nan 'yan ƙanana, ba masu zaƙin ba su nake sha' awa fa"
Gwaggo tace "au dankalin turawa zakice min"
Widad tace "eh shi nake nufi"
Gwaggo tace "taɓ aikuwa yana ɗan wahala, dan se anje can birni ake samu"
Widad tace "shi nake sonci fa"
Gwaggo tace "Amarya ko an gamu ne?"
Widad tace "aka gamu dame?"
"Ahh nasani ko addu'ar Baffa ta karɓu an samu rabo"
Widad tace "wai kina nufin ina da ciki?"
Gwaggo kawai tayi murmushi, ana ɗan sayewa kar a faɗa kai tsaye amma ita ta faɗa, Gwaggo ta ƙyaleta ta cigaba da aikinta, Widad taje tayi sallarta, ta zauna akan dadduma tayi shiru, kawai taji har cikin ranta tana son ta samu ciki, ace yau gata ɗauke da ɗanta na kanta a jikin ta, idan ta haihu ta samu ɗa da zata dinga gani tana jin daɗi.
Tana zaune tana ta karanta wasiƙar jaki, Yusuf yayi sallama tana jinsa tai masa banza, ta miƙe ta fara shirin kwanciya.
Seda ya bari ta kwanta sannan ya tafi rarrashi, tana jinsa ya hawo katifar yana lalubenta amma ta shareshi.
"Kina jina amma kika shareni ko Queen, laifin me nayi miki ne?"
"ni ƙyaleni bacci zanyi"
"Naƙi in ƙyalekin, ni kike sharewa ko?bafa na son haka"
Cikin Shagwaɓa tace "to ba kaine komai nayi kake cewa ban iya ba"
"To kin iya ɗinne? Matar ƙauye kawai sarkin rigima"
"Kai kuma mijin ƙauye ba"
"Eh naji na yadda, ni mijin ƙauyene kuma mijin matar ƙauye, karki damu zan siyo miki teddy ki dinga wasa dashi, shima kamar baby ne seki koyi goyon a jiki"
"bawani nan teddy daban, teddy mutum ne? Toni mutum nake so"
Yusuf yace "Eh tunda baki da mutum, seki rainon teddy da haka zaki koyi rainon jaririn gaske"
"Bana son teddyn, ni mutum nake so"
Sosai Widad ke bawa Yusuf dariya wasu lokutan, Yace "idan mutum yana yaro idan yayi wasa da dolls 'yar tsana, yana iya raino koba jariri a gidansu, amma ke baki iya ba '
Widad tace" waye ya gaya maka da ina yarinya ina wani wasa ni? Nifa kamar boss nake da ina yarinya, ba ruwana da wani wasa irin na yara"
Yusuf yayi murmushi yace " Yanzun ma ai boss ɗince"
Kawai tayi murmushi tace "nice boss ko, zan ramane"
A haka suna taɓa hirarsu har bacci yayi awon gaba dasu gaba ɗaya.
Da gari ya waye, Widad tana fitowa taga Hindu na tattare tsakar gida tana shara, Widad tace "Hindu kin warke ne kike aiki?"
Hindu tace "jikina da sauƙi Amarya, gani nayi tsakar gidan yayi wani iri, duk ganyen bishiya ya faɗo, shiyasa nace bari in gyara kafin a firfito"
"Kai Hindu, kina fama da kanki ki bari a share mana gaskiya bari"
Widad ta ƙwace tsintsiyar ta hana Hindu sharar, ta gama abunda zata yi ita ta share, sannan ɗakinta koma ɗakinta tayi kwanciyarta.
Wajejen takwas da rabi Widad ta farka, ta hangi Yusuf a zaune da gashi se gajeren wando yana buɗe kwanon Abinci, da alama har yayi wanka ma, dan jikinsa se ƙyallin mai yake.
Ƙura masa ido tayi tana kallonsa, sam Yusuf bashi da makusa gashi da ƙira me kyau, gashi shikansa me kyau ne, ga kuma uwa uba zuciya me kyau.
Tasowa tayi tazo inda yake ta zauna, ta kwanta a jikinsa hannunta kuma tana shafa gadon bayansa.
Yace "Kin tashi kenan? Fatan kin tashi lafiya?"
Maimakon tayi magana sema wani sake lafewa da tayi a jikinsa, tana sake shafa bayansa.
Yusuf yayi murmushi ya cigaba da abunda yake, can yace "in kin gama shafanin seki ɗagani zanci Abinci, tunda naga kamar ke bakya jin yunwa"
Yanzunma shirun ta kuma yi, ta cigaba da abunda take, janyota yayi gaba ɗaya ya ɗorata akan cinyarsa, yana ƙaremata kallo yace "ƙalau kuwa? Ko yau da son jiki kika farkane?"
Murmushi tayi masa, ta kwanta sosai a jikin nasa, tana ƙare masa kallo tun daga fuskarsa har ƙirjinsa, ta kai hannu tana wasa da gashin nasa.
Buge hannunta yayi yace "mara kunya nan kika gama cewa abun ƙyamane, amma indai kika gani sekin taɓa"
Murguɗa baki tayi tace "ai idan baka yi wasa ba, da fork zan maka shaving, duk in cire shi"
Yai dariya yace "Kin fasa tsigeshi ɗaya bayan ɗayan?"
"Duk wanda ya samu zanyi ai"
Yai murmushi yana cigaba da cin Abincin sa, still kallon Yusuf take yadda yake komai a nutse, Yusuf yace "Malama karfa ki cijeni"
Bata san lokacin da dariya ta ƙwace mata ba, tace "aikuwa dan kasan na saba ba, da an takurani idan naga bani da mafita, se cizo kuma haƙorana dafi garesu, duk abunda na kama sena fasa shi, shiyasa Fahad ɗin Bulama yake cemin Mayya, tunda na huda shi da haƙorana"
Jiki a sanyaye Yusuf yace "yanzu idan muka rabu, muka koma gida Fahad zaki aura ko?"
Da sauri tace "Allah ya kiyaye, wallahi ko maza sun ƙare bazan auri wannan ba, mashayin giyane fa, ga neman mata kai zaka so in Auri wannan?"
Yusuf ya girgiza mata kai, ya ɗan tsura mata ido yace "I can't imagine my life without you Widad, ko mu koma idan zaki Auri wani bazan iya jurewa ba, ban san ya zanyi ba"
"waye yace maka zanyi Aureni? Ni ba zanyi Aure ba, bani Abincin nima inci, amma a baki zaka bani yau" tai maganar cike da son da basar da wancan zancen da suke yi.
Haka ya dinga bata Abincin tana karɓa, kamar 'yar yaye suka gama sannan yayi shirin fita, yau da kanta har soro ta raka shi, ta tsaya ta kalle shi tace "bana son ka fita Yoseef, kamar kazo mu koma ɗaki"
"Yau kuma? To idan ma dawo me zaki ban?"
"Kawai inta kallonka, kana bani nishaɗi, da jokes ɗinka da halayenka masu kyau"
Yai murmushi yace "nima idan na fita, duk damuwa nake in dawo, saboda inzo inga abar sona, am missing you fa idan na fita".
Tace "nima haka, keep missing me harkaje ka dawo kaji"
Yusuf yace "yanzu abunda za'ayi shine, Yimin wani abu da in na fita har in dawo bazan manta ba"
Tace "kamar me kenan?"
Yusuf yace "just kiss me here 'yai maganar yana nuna mata kumatunsa na dama.
Ganin tsakar gidan ba kowa yasa Widad, ta rungume Yusuf ta fara kissing ɗinsa a baki, he was so much surprise da abunda Widad ɗin tayi, dan haka yasa hannu biyu ya rungumeta yana murmushi.
Hari ta bankaɗo labule zata fito daga ɗaki, hannunta da kofin da' aka karya, kawai tai gamo da Yusuf da Widad a bakin zaure, Yusuf ya bawa Hari baya dan haka be ganta ba sam, Widad kuwa ta ganta, amma tana sane ta basar ta ƙara maƙalƙale Yusuf ta cigaba da abunda take.
Da gudu Hari ta koma ɗaki, ta bankaɗo labule ta rufo ƙofa, Widad ta zame bakinta ta hau dariya, Yusuf yace "ya dai?"
Tace "bakomai, muje hanyar waje in raka ka"
Yusuf yace "rana me matuƙar tarihi a gurina, ba iya yau zan cigaba da tunanin ki ba har abada zanyi tunanin ki My Queen"
Murmushinta me ƙayatarwa ta cigaba dayi masa, da sukaje soronma soyayyarsu suka cigaba dayi, dukda Yusuf ne kawai ke furta mata yadda yake sonta, Widad kam ta kasa ce masa uffan.
Ya riƙo ƙugunta yana kallon ƙwayar idonta, Widad tace "Idan ma makara baka fita da wuri baf ba ruwana"
"Aiko ke kike da ruwa, dan ke kika hanani fita, ɗan ƙara min kiss ɗin mana kona 10 seconda ne"
Tureshi ta shiga yi tana dariya, tim suka ji an saki kwano, Hanne ta taho da fantekarta cike da Albasa, tayi karo dasu Yusuf, take taji ganinta ya ɗauke ta saki fantekar albasar, Yusuf yace "Subhanallah garin yaya kika zubar? '
Yai maganar yana sakin Widad, ya yunƙura da nufin ya durƙusa ya tayata tsince albasar, amma Widad ta riƙe shi ta tsatstsare shi da ido tace " meye naka a ciki? Ko kai ka zubar mata? "
Yusuf yace "A' a amma kinga mu muka tsoratata ta zubar da albasar, yakamata a tayata kwashewa"
Wani mugun kallo tayi wa Yusuf, taja tsaki ta koma cikin gida, Yusuf ya durƙusa ya taya Hanne suka tsince Albasar, yace "ki dinga kula sosai, ki dena yawan tsorata kinji?"
Hanne ta jinjina kai tace "to nagode"
Ta ɗau fantekarta tai waje, tana kuka tana tunanin me zata yiwa Widad yadda zata ɗan ɗana mata taji abunda take ji.
Alhaji Musane yace "Nifa gaba ɗaya na fara gajiya da wannan wahalar, daga wannan se wannan abu sekace jaraba? Abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, shi ya ɓace ɓat kamar kuɗi an neme shi an rasa, shima wannan ɓangaren yarinyar har yanzu babu wanda ya ganosu, suma lawyoyin nasa sun kawowa mutane wasu surutansu na banza "
Alhaji Haruna yace "haba Alhaji Musa, ni ban taɓa ganin ka karaya ba akan abu se yau, duk abunda aka fiye shan wuya akansa za'a samu ne, yanzu mafita yakamata mu nema amma dole mu kassara Daula, mu kassara wannan dukiyar dayake taƙama da ita"
Alhaji Musa yace "to meye mafitar, nagaji wallahi haba, ni zuwa zanyi in maida hankali akan harkar takarata kawai"
Alhaji Munir yace "kaga dan Allah Kadena mana zancen wata takara please, zancen takararka kai kaɗai ta shafa, mu muyi abunda ya dame mu kawai, Alhaji Haruna meye mafita"
"na saka a duba mana, wanda ze iya kwafar mana saka hannun Daula, sannan kafin a samu me saka hannun ayi fafutuka a bincika mana bankin nan, shima mu gwada muji ta ina zamu dace"
Alhaji Musa yace "to ai shikenan, Allah yasa mu dace, amma ni na fara gajiya wallahi, gashi shima wancan banzan yaron har yanzu ba'a gano shi ba, nifa sonake a kamashi kafin su shigo garin nan"
Haruna yace "karka damu, ai matakan da muka saka baze tsallake tarkonmu ba, ka kwantar da hankalinka komai ze tafi dai dai"
Alhaji Musa yace "shikenan Allah yasa hakan, ynzu a duba mana me iya kwafar signing ɗin nan"
Gidan Alhaji Daula kuwa, Hajiya Halima se shagalinsu suke da dukiya suna facaka, A ɓoye Ramlah take satar wasu abubuwan ba tare da mahaifiyarta ta sani ba ta kaiwa Fahad ya sayar ya kawo mata abunda yaga dama, sannan kuma su raba abunda ya kawo mata ɗin, Amal kam gaba ɗaya a cikin damuwa taje, dukda irin romon bakan da Mahaifiyar su take mata, akan cewar ai bakomai dan an kama Yusuf, amma hankalinta yaƙi kwanciya, sam bata da nutsuwa sosai take jin Yusuf a ranta, take tausayin halin da ze shiga idan aka kamashi da laifin ya sace Widad.
Anwar kam kasuwarsa ya koma zuwa, sam baya zaman gidan nan saboda irin takaicin da yake ƙunsa a cikin gidan, a kan idonsa yana ji yana gani haka Fahad yake zuwa ya ɗauki Ramlah a mota su fita, kuma mahaifiyarsu na gani bazata ce komai ba, shikansa ya fara lura da sauyin ɗabi'a na Ramlah, ya fara zargin ko ta fara shaye shayey, amma yasan da yayi magana mahaifiyarsu zata ƙarhata shi ƙarshe ma su ƙareta babu daɗi dan haka ya zuba musu ido.
Ma'aikatan gidan kuwa, su Isa se yanzu suka gane zaman Widad a gidan nan Rahama ne a garesu, saboda tsagwaron wulaƙanci da cin mutunci da suke fuskanta daga gurin Hajiya Halima da 'ya' yanta, zagi da cin zarafi gami da wulaƙanci ba irin wanda ba'a musu, Albashinsu kuma duk Hajiya Halima tabi zaftare musu, shima se sufi wata ba'a basu ba, zaman haƙuri kawai sukeyi a gidan nan, duk inda suka zauna banda tsinewa Hajiya Halima da 'ya' yanta babu abunda sukeyi, suna shiwa Widad da Alhaji Nasir Albarka, saboda kaɓakin arzikin da suke basu shida 'yarsa se yanzu suke ganin duk izzar Widad a cikin gata suke, dan gashi a yanzu an maidasu kamar bayi a gidan haka suke zaune.
Saleh ma yana ji yana gani, a gidan gonar nan haka Hajiya Halima ke zuwa ta ɗau abunda takeso ta fito dashi daga gidan ta siyar, ba yadda ya iya dan idan ya zaƙe su Alhaji Musa zasu iya gano shi, balli ya tashi dan haka se dai ya zura ido.
Hanne bayan ta dawo daga kai albasarta kuwa, ɓangaren Jamila ta wuce taje tayi jifa da fantekar albasar, Jamila tace "ke lafiya kuwa, ke da yayanki yana nan kikazo kika mana jifa da kwanon nan da yaci ƙaniyarki ai"
Hanne tayi tsaki tace "wallahi Jamila na tsani wannan koɗaɗiyyar bayahudiyar, na rasa me zan mata in huce"
Jamila tace "wace bayahudiyar?"
"wannan farar banzar ta gidanmu mana"
Jamila tace "dama ba musulma bace?"
"Musulma ce mana, sedai shegiya ce, bata da mutunci"
Jamila tace "wai meye tsakanin kune? Me tayi miki haka kuke takun saƙa"
"Wai ba damar magana ta haɗani da mijin ta, seta hau gayan magana, kokuma seta ganni se ta hau wani rungumeshi"
Jamila tace "ikon Allah, toke meye naki a ciki, ba mijin ta bane ba?"
"to dan mijin ta ne seta dinga min haka? Naga dai namiji na maya huɗune, shikenan kuma baza'a kula shi ba?"
Jamila tace "Auho, yanzu na gane inda kika dosa, to tun wuri ki kiyayi kanki, ina ruwanki da mijin ta? Ke ke inake ina wannan bawan Allah, yana da wannan mace kamar ita tayi kanta, ki taba kanki da wahala ki lallaɓa da wanda aka sa miki rana"
Ji tayi wani mugun haushi ya kuma kamata, ta ja tsaki ta ɗau fantekarta tayi waje.
Saboda tsabar takaici Widad kam a ɗaki ta wuni, tunda ta fito ta gaida Gwaggo ta koma ɗakinsu, dan ta riga ta gama kawowa iya wuya akan abunda yake faruwa, so take tayiwa Hannne abunda idan ta taho suka haɗu seta canza hanya, ace yarinya 'yar ƙauye kamar wannan ta dinga shigar mata hanci, wata zuciyar tace ' me zakiytsaya tankawa waccan kucakar, shi Yusuf ɗin zaki yiwa' haka ta wuni tana ƙunci da ɓacin rai, Abincin rana ma ta fara ci ta kasa ta ajiye, ta nemi guri ta kwanta.
Koda Yusuf ya dawo gida da yamma, yama manta da abunda ya faru da Safe, ya dawo ya tarar se cika take tana bastewa, Yusuf yace "Babyna wai meya farune kike wani haɗemin rai?"
Shiru tayi masa ko inda yake taƙi kallo, ƙarshema ta miƙe zata fice, Yusuf yay Wuf ya riƙota yace "haba gimbiyata, me nayi miki ne, bana jin daɗin irin wannan hukuncin da kikemin, ki hukunta ni ban san laifina ba"
Ƙwacewa tayi tace "ka ƙyaleni, ka koma gurin waccan 'yar ƙauyen daƙiƙiya ka Aureta, kuma kazo ka sakeni na gaya maka, nika ƙyaleni ita kaje ka aureta ka rabu dani, tunda itace mace"
Wai yau yake ganin kishi gangariyarsa, dan shaf ya manta da wani abu ya faru yau da safe, ashe abun yana ranta tun safen nan.
"Widad meye ya kawo wannan maganar kuma, ni nace miki ina son watane, ni ban gayamiki haka ba, meyasa kikemin hakane,? Haba Widad ki dinga jin tausayina inje in dawo a wahale, kekuma ki ƙaramin pressure"
Tsaki tayi, tai waje zata bar ɗakin, ya biyota yana cewa "naji na karɓi laifina, kiyi haƙuri dan Allah '
Amma Widad tayi fafur, fuuu tayo waje abunta.
Gwaggo ta kawo kai zata fito daga banɗaki, taga suna rigima seta koma bata fito ba.
Widad ta samu kujera ta zauna kawai ta fashe da kuka, tama rasa kukan me take yi ne.
Yusuf kuma ya koma ɗaki, ya rasa abunda ma zeyi.
Gwaggo ta fito ta kalli Widad tace "Amarya lafiya kuwa?"
Widad ta goge idonta da sauri tace "bakomai"
Gwaggo ta kamo hannunta ta janyota zuwa ɗakinta, ta zaunar da ita akan gado.
Jamila na nan zaune a ɗakin, da yake da ta gama aikin da zata yi a ɓangarenta nan take tahowa.
Gwaggo ta kalleta tace "Amarya, meyasa kike haka? Meyafaru ne ba wai sa miki ido nake ba, na kawo kai naga kina rigima da mijinki, yana baki haƙuri, ba wai ina son jin lallai meya haɗaku bane, a'a yakamata ki gyara mu'amalar Aurenki 'yata, ki samu namiji ya damu dake haka, ga mijinki yaron kirki me haƙuri, amma ki dinga masa haka, anya kuwa namiji ya miki laifi ya baki haƙuri amma kiƙi saurararsa ba' a haka 'yata"
Jamila dake zaune tace "Taɓɗijan lallai ke' yar gata ce, har ana baki haƙuri, lallai kinyi dace ai wani namijim shi ze miki laifi, kuma ya dinga fushi sekin bashi haƙuri, ai kekam kinyi dace"
Nan suka dinga yiwa Widad faɗa, suna mata nasiha akan yadda ake kula da miji, Gwaggo tace "Amarya mahaifiyarki na da rai kuwa?"
Widad ta girgiza kai alamar a'a, "mariƙiyarki bata gayamiki yadda rayuwa take ne?"
Widad tayi shiru ba tace komai ba, nan suka zage suna mata nasiha, se kuma jikin ta yayi sanyi, tabbas Yusuf yana matuƙar haƙuri da ita, sekuma taji sam bata kyauta ba abunda tayi.
Jamila ta tashi ta goya 'yarta tace' zomu je ɗakina kiji wani abu".......
0 comments:
Post a Comment