Widad ta tashi tabi Jamila, suka zaga ɓangaren Jamila, ta buɗe ɗakinta tayi mata iso, suka shiga sannan ta kalli Widad tace
"dukda naga baki da sakin jiki da mutane, amma naji ina son in temakeki, kinga nima da a ƙauyen nan nake, da mijina ya aureni muka tafi can barikin sojoji, to a can nima naga abubuwa, duk banyi karatun boko ba, amma na bazama na fara nema, naga yadda mata ke kula da mijk, naga a mugun ƙauye nake bansan komai ba, a tashin da mukayi a garin nan komai iyayen mu basa iya gayamana, mussman da ya shafi ɓangaren Aure ba abunda suke iya gayamana, saboda kunya amma ita rayuwar Aure faɗine da ita, amma a ɗan zaman da nayi zuwan nan nawa na fuskanci abubuwa da dama, ta wasu ɓangaren kina ƙoƙari, amma ta wani ɓangaren kina da rauni, mijinki yana da kyau yana da kirki masha Allah, idan har kikayi sake 'yan matan ƙauyen nan zasu cigaba da bibiyar sane, kiyi ƙoƙari ki riƙeshi sosai saboda mijinki zinare ne, samunsa a cikin maza akwai wahala
Dan haka shi namiji idan yana ta taka, baka wannan dogon jan ajin, ai daya miki laifi idan ya baki haƙuri kawai a wuce gurin, idan ba haka ba ze fara tunanin ko bakya sonshi ne, ya fara leƙe leƙen wasu matan, idan da ba yayi to zaki koya masa da kanki
Sannan wasu lokutan kina gsyamasa baƙar magana, kuma hakan be kamata ba tunda mijin kine, ba kowace magana zaki dinga gaya maaa yadda kike so ba, a koda yaushe mune ƙasa dasu dan haka dole mi bisu, dukda ban san dalilin zamanku a garin nan ba, amm gaki sam babu abunda ya haɗa kalarki da ƙauyen nan, dan baki kama da wadda take a wahala ba, amma ke yanzu dake kaɗai aka bari ki kula da kanki a ƙauyen nan zaki iya? Babu lallai ki iya saboda haka kodan yadda yake tsaye yana kula dake, yake iya ƙoƙarinsa akanki ya cancanci ki girmamashi saboda haka.
Nasan ko ban faɗa miki ba abubuwan da Hanne take kinsan son mijinki take yi, dan haka seki kula sosai bar ganin kima da wannan kyan surar, yanzu se hankalinsa ya ɗauke idan kika gaza sauke haƙƙoƙinsa dake kanki.
Ki kula ki tsare haƙƙinsa, sannan rayuwar Aure duk ta haƙurice, babu yadda za'ayi ace kullum shi ze dinga baki haƙuri, tun yana ta taki zeyi watsi dake wataran, mata na rububin irin mijinki, dan haka dan Allah ki dinga haƙuri dashi, karki ƙara yi masa abunda Gwaggo ta gani ɗazu.
Maza na son a girmamasu, ka basu girmansu tunda Allah ne ya basu.
Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki kula da mijinki, duk abunda baki gane ba ki tambayeni zan gayamiki, dan ita Gwaggo bakomai zata gayamiki ba saboda kunya"
Nan ta cigaba gayawa Widad abubuwa da dama akan sabgar Aure, wanda Widad sam bata sani ba, nan ta dinga koya mata kissa da dabarun zama da miji, wanda ita Widad sam bata taɓa sanin su bama, dan ita rayuwar Auren bata gabanta balle tasan meya ƙunsa.
Abun ya dinga bawa Widad mamaki, lallai wanda ya rasa uwa yayi kuka, ita banda yanzu ma wasu abubuwan bata sansu ba game da Auren, lallai Yusuf yana haƙuri, wata zuciyar ta ta tace 'amma ai Auren bogine bana gaske ba meye na damuwa da ɗaga hankali?'
Wata zuciyar kuma tace 'dukda hakan dai, ai yakamata ko yaya ki kyautata masa, ko bakomai ya cancanci hakan daga gareki, karki zama me butulci mana.
Duk da Jamila ba wata babba bace, amma ta gayawa Widad abubuwa da dama da yakamata ace ta sani, game da rayuwar Aure, wanda yanayin zamansu da Yusuf ita bata saniba.
Widad tayi mata godiya, sannan suka dawo ɓangaren su Gwaggo, koda ta koma Yusuf ya fita bayanan, dan haka ta shiga shagalinta.
Hari na ganin Widad a tsakar gida tace "Mhmm yau ninaga abunda yafi ƙarfina yafi ƙarfin idanuna, wai nikam dama Yaya nace mutane ma na wa junansu ɗura kamar yadda tsuntsaye keyi?"
Gwaggo tace "to ikon Allah, nima ban sani ba gaskiya dan ban taɓa jiba ko gani, se yanzu a bakinki"
Hari tace "hmmm, ai ina ganin tsiyataku kala daban daban, wani abunma idan na gani na dinga Tuba kenan kar inje in fita daga musulunci ban sani ba, banda jaraba ace mutum yasa bakinsa a cikin na ɗan uwansa, saboda tsabar ƙazanta, yo nidai nasam tsuntsaye ne kawai ke yin haka, amma se gashi mutane ma nayi, kai ina ganin masifa ƙuru ƙuru"
Widad ta ƙura mata ido, Ba shiri Hari taja bakinta ta tsuke, tun kan Widad ta gayamata baƙar magana itama.
Widad a ranta tace "ke wannan haƙoran naki, gaftara gaftara koraye wane mijin ze sha'awar sa bakinsa a naki? '
Yusuf ya dawo amma yayi watsi da Widad, yaƙi shiga sabgarta ya cigaba da harkokin gabansa, sam yaƙi kula ta, gaba ɗaya se taji babu daɗi, ta kuma rasa yadda zata yi ya kula ta.
Yusuf ya samu guri yai kwanciyarsa, ba tare da ya tsokane ta ba yau, koya mata hira, ko yazo inda take ya share ta kamar shikaɗaine a ɗakin.
Bacci ma ya nemi ya gagareta, gashi 'yan kwanakin nan ta fara sabawa da kwanciya a jikinsa, amma yaƙi kulata yau, gaba ɗaya taji garin ya mata zafi.
Da safe ma farkawa tayi taga yayi ficewarsa, ta rasa abunda yake mata daɗi haka nan jiki a sanyaye take komai, tayi wanka ta karya.
Hindu ta tsiri yin Faten tsaki, Widad tace suyi a kan risho ɗinta, suka gyara yakuwa tare da kabewa, anan Jamila ta sake lura shikansa aikin Widad bata iya ba, danma ba tun farkon zuwanta taga kwaɓar da Widad take ba.
Akayi fate aka gama, suka zuba suka fara sha, Widad da ƙyar tai spoon biyu tace
"ni gaskiya wannan abun ba daɗi, tayar min da zuciya ma yake, ga tsami ga gishiri ni na kasa gane ma meye taste ɗin Abincin"
Jamila ta dinga tsokanar Widad, wai kodai cikine kuma baya son faten, ita dai Widad har yanzu bata sake da Jamila ba, amma taji daɗin bayanan da tayi mata.
Kuma babban abunda yake burgeta da Jamila, kullum jaririyarta tsaf da ita, kuma idan taje ɗauka bata hanata, tana bata ta ɗauka.
Jamila tace "kun shirya kuwa?"
Widad ta tura baki tace "baya ƙi kulani ba, me zance masa?"
Jamila tace "kinga abunda nake gayamiki ko? Allah yasa ba budurwa yayi ba wadda zata dinga tarairayarsa ba"
Zare ido Widad tayi ta harari Jamila tace "shi ya isa ma?"
"Au haka kika ce?"
"Eh haka nace"
Jamila tayi murmushi tace "ai shikenan, cikin hira ta cigaba da ganar da Widad wasu al'amuran, dukda wani lokacin in anyi gabas se tayi yamma.
Da yamma taga su Gwaggo suna ta shirye shirye, Widad tace" Mama ina zuku ne kuke ta shiri haka? "
Gwaggo tace " bikine zamu wani ƙauye a gabanmu, Yayar Baffa ce zata yi Auren 'ya"
"Mama zan biku nima dan Allah"
"Ahh haka kurum, da mijinki da komai a' a ba ruwana"
Widad ta marairaice tace "dan Allah Mama"
Gwaggo tace "to ki tambayi Yusuf tukuna, danmu kwana uku zamuyi"
"to ai bazece komai ba, dan Allah nidai zan biku zanje nima in haɗa kayana"
"Amarya, babu yadda za'ayi muyi tafiya dake, ba tare da kin nemi izininsa ba, idan ya bari bakomai semu tafi'
Widad tace " bari yazo in tambayeshi to "
Wani wahalallaen bacci ne Nurat take yinsa bayan sallar Azahar, wayarta dake ƙasan pillow ta fara vibrating, a ɗan razane ta farka, tasa hannu a ƙasan pillowa ta ɗakko wayar, ta amsa sannan ta saka a kunnenta "Hello Brother"
"Nurat, kina gida ne zan shigo yanzu?"
Ta miƙe zaune da sauri tace "No karka zo dan Allah, Daddy yana gida yanzu ze iya fara zargin wani abu, kuma kasan ya hanani fita, amma me ake ciki?"
Khalil yace "Aikin da kika bani na fara, amma ko kin san cewa Yusuf ɗin nan ɗan sanda ne?"
"Kamar yaya? Wai dama dagaske ne shi ɗan sanda ne? Naji a labarai na zata ƙaryane ai"
Khalil yace "to gaske ne, ɗan sanda ne na farin kaya, yayi basaja yaje a matsayin direba, kuma yayi garkuwa da yarinyar"
"Kahlil saboda wanke Yusuf yasa na sakoka a cikin wannan lamarin, dan Allah karka ƙara danganta Yusuf da wannan mugun aikin, baze taɓa aikata haka ba na tabatta"
Khalil yace "shikenan naji, karkiyi kuka, ai ina kan yin bincike ne, ban tabattar ba, abun da ake ciki zan miki magana, amma banda kuka kinji ƙanwata"
Nurat ta gyaɗa kai kamar yana ganinta.
Widad da wuri ta sallami ɗalibanta yau, dan wasa wasa da yammar nan cika tsakar gidan Megari akeyi, an samo musu alli da allo na rubutu, sannan kowa da littafinsa da abun rubutu, babban abunda yake burge Widad be wuce yadda suke girmamata ba, suna girmama malami a ƙauyen nan, kuma a hankali tana jansu a jiki yanzu, musamman 'yan ƙananan yaran nan, da sunzo kwanukanta ɗakinta har tsakar gidan duk se subi su gyara, saboda tsabar girmamawa.
Widad nata ɗokin Yusuf ya dawo ta tambaye shi, dan harta manta sunyi faɗa, seda ya dawo taga ba fuska, Yusuf be taɓa mata kwarjinin da yayi mata yau ba, sam ta kasa masa magana sedai kallonsa kawai da take yi.
Koda yayi alwala ya fita sallar magariba, se bayan isha'i sosai sannan ya dawo, ya ɗau Abincinsa ya fara ci, ta zuba masa ido amma ta kasa magana, can dai taita maza tace
"Yoseef dama, su Mama ne zasu je biki, shine tace in tambayeka idan zaka barni in bisu, inje inga yadda akeyi"
Banza Yusuf yayi mata, kamar beji me tace ba, "Yoseef magana fa nake maka"
"Kiyi abunda kika ga dama kawai" ya bata amsa.
Jin maganar tayi wani banbarakwai ba tsari, wai tayi abunda taga dama.
"Ka barni inje kenan?"
"Meye na tambayata kuma ne? Nace kiyi abunda kika ga dama, ai damani baki ɗaukeni miji ba, na kan manta in wuce gona da iri wasu lokutan, waini game mata, na kan manta ashe nifa direba ne, iyakaci in miki aiki ki biyani, dan haka idan harni mininki ne, to ban yadda kije ba, sedai nasan ba lallai ki yadda da hukunci na, saboda ban kai a kirani mijinki ba, ban isa komai a gurin kiba, dan haka kiyi abunda kike so, zama ko zuwa ya rage naki"
Yana gama maganar ya tashi ya bar mata ɗakin, wani malolon takaicine ya tokare mata zuciya, dama Wai Yusuf ya iya fushi haka?
Har washegari be kumabi takanta ba, tana ji tana gani su Gwaggo suka shirya yaransu da manyansu suka tafi aka barsu a gida, Jamila na ɓangaren ta nata bisu ba, se abokiyar kishin Widad wato Hanne bata bisu tace bata da lafiya ita bazata ba dan haka tana gida itama.
Da daddare Yusuf ya idar da sallar isha'i yana lazimi, Widad a hankali tace
"Yoseef" ta kira sunansa kusan sau uku, amma yayi shiru, can tace
"Yuzarsef"
Da sauri ya ɗaga ido ya kalleta jin sunan data faɗa, dukda be amsa ba amma taga damuwarsa ta ƙaru, ya kifa goshinsa akan gwiwar ƙafafuwansa daya ɗage.
Sanye da zumbulelen hijjabinta tazo, tasa hannu ta ɗago fuskarsa tace "wani laifin na kuma yi maka dan na kiraka da Yuzarsef?"
Girgiza mata kai yayi, alamar a'a yana ƙoƙarin maida kansa.
Ta sa hannu biyu ta tallafi fuskarsa tace "Yoseef, me nayi maka ne? Dan Allah kayi haƙuri"
Yusuf yace "aini baki min komai ba, sedai yau ina son in san saki nawa kike so in miki?"
Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa, tace "kamar yaya? "
Yace "kamar yadda na tambayeki, saki nawa kike so?"
"Yaushe nace maka haka?"
Yace "kin manta abunda kika gayamin ne? Ina son in koyawa kaina rayuwa ko babu ke ne, kusan koyaushe kina maganar in sakeki, duk ƙoƙarina bakya gani, bakya tausayamin ya zanyi? Gara idan muka rabu inda wani ɗakin duk rashin kyansa a bani, in lallaɓa in fara koyawa kaina zama ko babu ke"
Aikuwa ta fashe da kuka tace "nifa ban san nayi ba, ban san meyasa nake jin haushi idan naga wata ta raɓeka ba, tun jiya nake maka magana, amma kana shareni, se kulaka nake amma kaƙi ko kallona, na tambayeka abu ka hanani, kuma banyi ba, amma ka kama min faɗa, you want turn on me ko, shikenan"
Ta juya zata tashi ya Riƙeta, yace "babu wani dalili da zesa in juya miki baya, sedai nine kin kasamin adalci, bakya iyayi min adalci a wasu lokutan, kiyi ta bani wahala saboda kinga ina sonki ko?"
Share hawaye tayi, ba tare da tace komai ba, Yusuf yace "yanzu me kikeson ayi?"
"Ka dinga kulani, ka dena ɗauremin fuska"
"shikenan za'ayi yadda kike so, amma da bakinki nake son ki faɗi saki nawa kike so?"
Shiru tayi batayi magana ba, sema sunkuyar da kanta da tayi tana kallon wani gurin daban.
"Widad magana fa nake miki"
Ɗison hawayen ta ya gani yana ɗigowa a ƙasa, taƙi ɗaga kanta kuma taƙi magana.
Yace "shikenan, tashi kije ki kwanta"
Ta miƙe sum sum ta tafi katifarta ta kwanta, tai shiru tana tunani, wai yanzu dagaske Yusuf yake sakinta zeyi, se taji gabanta ya faɗi, 'to meye dan ya sakeki, dama ai akan haka kuke' wani sashe na zuciyarta ya gayamata.
'Amma dukda haka nayi sabo dashi, sabo me ƙarfin gaske, yanzu idan ya rabu dani ya zanyi? Zan koma irin rayuwar kaɗaici na ta baya kenan?'
Kawai ta sake fashewa da kuka, yana jinta amma yai shiru kamar be san tana yiba, se can dare bayan ya idar da sallar dare, yayi addu'oin da zeyi sannan ya tao a hankali ya hau kan katifar ya rungume ta a jikinsa, lokacin har riga tayi bacci, wannan fushin da yayi da ita na kwana biyu shikansa yaji a jikinsa, dan ba ƙaramin kewarta yayi ba, a jininsa yake jin soyayyar Widad na ratsashi, shi dai yana matuƙar sonta.
Kamar yadda Suleiman ya buƙata, Abbas yaje office ɗinsa, seda ya ɗan jira ya sallami baƙi sannan ya ganshi.
Bayan sun gaisa ne Suleiman yace "Abbas ashe ka shigo garin nan babu Labari, sekace wanda akayi zaman gaba aika leƙo a gaisa '
Abbas ya ɗan sosa kai yace " Ai Yallaɓai abubuwan ne dama duk se a hankali, kuma ni ɗanje ziyare ziyare ne, shiyasa amma dama can nayi niyyar in ɓullo a gaisa ai, da amana bazan watsar daku ba"
Suleiman yai murmushi yace "shikenan, ya aikin ya hanya?"
"Alhamdilillah, aiki can ai har yafi nan daɗi"
Suleiman yace "madalla ai haka ake so, nace ka kuwa ji abunda ya faru da Yusuf?"
Abbas yace "naji yallaɓai, abun ya bani mamaki, mutum a fuska mumini amma zuciyarsa ba Allah, saboda son zuciya kawai daga aiki seka yi garkuwa da 'yar mutane, gaskiya bewa kansa adalci ba, Yusuf ya bada mamaki"
Suleiman yai ƙuri da ido yana sauraren Abbas, se da ya gama sannan yayi ajiyar zuciya yace "to ai koma menene Allah baya bacci, kuma muna bayan ɗan uwanmu, Insha Allah, sannan bama saka ran Yusuf ze aikata abunda ake tuhhmarsa dashi sam, yanzu ni babban abunda yaaa na kiraka shine, kaga kaine babban Abokinsa, mahaifiyarsa tana cikin damuwa ƙwarai, naje gurinta take cemin taji ance kaje amma ba kaje ka mata jajen abunda ya samu Yusuf ba, dan Allah ka daure ka zagaya kayi mata jaje ko ka ɗebe mata kewar ɗanta"
Abbas yace "shikenan, dan dai wannan insha Allah daga nan ma zanje, Allah sarki insha Allah zan biya in gaisheta"
Suleiman yace "ba laifi hakan yayi kyau"
Abbas na fitowa yace "Aikin banza, ina ruwana uwatace ita, taje duk abunda ze sameta ya sameta, nan aka canza gurin aiki aka bawa ɗanta muƙamina, ba abunda tace se yanzu wani in mata jaje baza'ayi ba ɗin, Allah ya ƙara '
Harze wuce ya hangi Sakina ta taho da files a hannunta, yana ganinta ya fara murmushi yace "budurwar kidnapper, ashe abunda ya faru kenan? Saurayinki yaje ya sace' yar masu kuɗi gaskiya kuna ruwa"
Sakina tace "haba Abbas, yazaka maida abun abun wasa? Wannan maganar be dace a jita daga bakinka ba a matsayinsa na Abokinka, kuma abokin aikin mu, kuma kasan baze aikata hakan ba"
"ke dalla ware, waye yace miki baze aikata ba? Mutum nefa shi, waye baya son kuɗi a rayuwar nan? Kedai Allah ya kyauta kawai ya tona masa Asiri, dama ya daɗe yana naɗe kura da fatar Akuya ne"
Sakina ta dinga bin Abbas da kallon mamaki, wai babban abokine yake faɗar maganganu akan Abokinsa haka, lallai duniyar nan ba abun yadda bace.
Da Asuba Yusuf ya tashi Widad tayi salla, taji daɗi yau ya kulata ya tasheta tayi salla, bayan ta idar ta koma baccin nata na ƙa'ida.
Yusuf yayi komai, har sharar tsakar gida, Hanne a ɓangaren Jamila ta kwana, da safe ta dawo ɓangaren su dan taga Yusuf, aikuwa ta tarar dashi yana shara.
"Ina kwana? '
Yusuf ya kalleta ya amsa mata, ya cigaba da shara," kawo in share gidan "
Yusuf yace ' A'a bakomai zanyi, ai ba wani abu bane"
Duk yadda Hanne taso ko hira su ɗanyi da Yusuf yaƙi yadda, saboda ya gane Lagon Widad yanzu, kishi ne da ita matuƙa, dan haka ya fara ƙoƙarin kiyayewa.
Sam Hanne bata ji daɗin yadda Yusuf yayi mata yau ba.
Ya koma ya ɗora girki a ɗaki, yana yi ya kalli inda Widad ke kwance na bacci, yana zuwa beyi wata wata ba ya ɗagata sama yai waje da ita tsakar gida.
Buɗe baki tayi zata yi ihu, ya rufe mata baki yace "ke nine fa" sannan tai shiru tana ajiyar zuciya tace 'shine zaka tsoratani kuma?'
"Yaushe kika zama matsoraciya ne? Kedai kiyi bacci kiyi bacci, ko gajiya bakya yi? Karɓi brush ɗinki ki wanke baki, muje ki tayani girki"
Yai maganar yana matsa mata toothpaste, "Yayan Daddy ka dena fushin dani ne?"
"A'a har yanzu inayi"
"Meyasa bazaka haƙura ba?"
Yusuf yace "kona haƙura anjima ma, sekin sake abunda zanyi fushi dake"
"to ai nace Kayi haƙuri, kuma ai kai baka fushi fa"
Yace "waya gayamiki bana fushi? Nima mutum ne fa"
"To na dena kaji" tai maganar a sigar Shagwaɓa.
"Idan kika kuma, sedai ki wayi gari kiga na fece na barki"
"Aikuwa inaga da haɗiyar zuciya zanyi in huta"
Murmushi yayi yace "ba wani haɗiyar zuciya, ai bakya sona"
Ba tace komai ba ta fara wanke bakinta, suka gama suka koma ɗaki, can Widad tace "Yoseed, meyasa da nace maka Yuzarsef naga ka shiga damuwa jiya?"
Yace "karki damu ba wani abu bane, kin tunamin da babana ne"
"Allah sarki, Allah yayi musu rahama gaba ɗaya"
Yace "Ameen ya Allah masoyiyyata"
Yai maganar tare da sumbatar kumatunta.
Tayi murmushi tace "Yayan Daddy, kamin addu'a Allah yasa in samu ciki, so nake in haihu nima ace ina da baby"
Da sauri Yusuf yayi mata wani irin kallo, da ita kanga bata gane ma'anar sa ba....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
90_91
Saroro tayi tana kallonsa ta kasa gane me yake nufi da wannan kallon da yake mata, tace
"ya dai naga kamar ka ɓata rai? Ko na sake faɗan wani abun na dai dai ba"
Girgiza mata kai yayi yace "No bakomai"
"Amma naga kamar ka ɓata rai? Da ba a haka fuskarka take ba fa"
Yusuf yace "A'a ba ɓata rai nayi ba, karki damu zo kici Abincin ki, nasan kina jin yunwa yanzu, dan rana tayi baki karya ba"
Ya zuba mata Abincin, Haka taci Abincin tana lura da yadda Yusuf duk yayi wani iri, kamar wani abu yana ɗan damunsa, amma babu alamar ze faɗa mata meke damun nasa.
Anwar ya shirya yaje gidansu Fahad, domin yana son ganin Bulama suyi magana, sedai be sami Fahad a gida ba, dama ba gurinsa yaje ba dan haka be kula ba ya nemi idan Bulama yana nan a masa iso, Ramadan yayi masa iso zuwa gurin Bulama, Bulama na ganinsa yayi murmushi yace "Anwar, anya in kulaka kwana biyu baka leƙowa mu gaisa"
Anwar yayi murmushi yace "tuba nake, abubuwa ne suka ɗanyi yawa wlh, Daddy ya aiki ya gida? Naji amce zaka Umarah shiyasa nace bari inzo in sameka"
"Alhamdilillah Anwar, eh insha Allah sati ma gaba zan tafi da yardar Allah, ya gidan naku ya babarta ka da ƙannenka?"
Anwar yace "Tana lafiya ƙalau Alhamdilillah"
"Masha Allah, nice to hear that haka akeso ai, naji kana son ganina meyafaru ne?"
Anwar yace "Amm Daddy, dama nazo ne akan inji wai har yanzu babu wani labari game da ɓatan Mariƙinmune? Har yanzu babu shi babu Widad gashi lokaci yana ta ƙara ja, amma shiru babu wani labari akai"
Bulama ya gyara zama sannan yace "Ahh mekuma kake sonji Anwar, bayan wanda yake ta yawo a gari? Widad garin jajibe jajibenta duk wayo da ƙin mutanenta, amma ta yayimo tsiya, wani koɗaɗɗen yaro me kama da sadakar yalla nan, direbanta ta ɗauki duk wata ragamar yaddarta ta bashi, ko gidan nan tazo duk sirrin magana sedai muyi a gabansa, ko nan da cam ba zata je ba seda shi, duk maganar da zamuyi sedai a gabansa, dan haka duk yadda take kaffa kaffa yasan wasu daga cikin sirrinta, gashi ƙarshe 'yan sanda bincikensu ya tabattar musu da cewar, shine yayi garkuwa da ita, ya nemi kuɗin fansa a gurin mahaifinta, dabe samu ba shine yabi Asibitin ya sace mahaifinta, yanzu dai' yan sanda suna nan suna binciken inda zasu gansu, amma shiru babu Labari, sedai a cigaba da Addu'a sannan mu cigaba da sauraren abunda zasu ce, amma abun da ɗaure kai fa sosai"
Anwar yace "nifa Daddy har yanzu ban yadda da wannan sakamakon binciken ba da aka bayyana, babu yadda za'ayi ace shine ya saceta, Daddy kasanta da wayon tsiya, babu yadda za' ayi tana sane ta bari yasan sirrinta, sedai idan akwai wata manufa da take dashi a kanta, sannan daga rundunar 'yan sandan nan a farko an sanar da sace su akayi, har an siyar da motar da aka sace su a ciki an ganta a kasuwa, ba' a kumabi takan zancem ba, basu bincika ya akai motar taje kasuwa ba, kuma azo a sake sanar da cewa wai shine ya saceta, it doesn't make sense, kuma bayan haka ace ya kuma zuwa ya sace mahaifinta, sam beyi kama da criminals ba, ni gaba ɗaya banji ƙamshin gaskiya a lamarin nan ba, akwai wata a ƙasa dai"
Bulama yace "eh to, kaima maganarka abun dubawace, amma ka sani mutum yana iya canzawa a kowane lokaci, kuma ze iya yuwuwa shine ya saida motar, tunda yasan siriikanta dan yasan abunda ban sani ba ni game da ita, sannan kuma duk abunka da ƙwaƙwƙwafinka kasan dai ba zaka gwadawa 'yan sanda aikinsu ba, tunda suka faɗi haka kasan abunda bincikensu ya nuna musu kenan, ba zasu yi ƙarya ba haka kurum, kabar mutum akan aikinsa kawai"
Anwar kamar ze kuka yace "Amma Daddy babu abunda' yan sanda ba zasu iyayi akan kuɗi ba kaima ka sani, idan wasu ba zasu yi ba, wasu zasuyi tunda suma mutane ne, dan haka ba abun mamaki bane suma 'yan sanda suyi komai akan kuɗi ba, dan haka yakamata ta ɓangarenka ma, kasa a sake bincikawa a tabattar da in dagaske binciken nasu haka yake, kasan Alhaji Nasir da' yarsa suna da maƙiya, komai fa ze iya faruwa, zata iya yuwuwa su suke wannan abubuwan haka"
Bulama yayi dariya irin tasu ta tsofaffin manya yace "Yaro yarone dai, Amma kaima kace wani abu me mahimmanci fa, shikenan Anwar tunda haka kace, Insha Allah zanga ƙoƙarin da zanyi ta ɓangarena, tabbas Daula yana da maƙiya kam, kuma komai ze iya faruwa, zanga abunda zan iya, Allah ya wuce mana gaba"
Anwar yace "Ameen Daddy, nagode sosai"
Kasancewar gidan babu kowa yasa Yusuf baya fita ko ina, dan baze iya fita ya barta a gida ba ita kaɗai, yasan ba zata zauna bama, suna zaune tama ta saƙa mafici Ya ɗan kalleta yace "Widad"
Ta ɗago ta kalleshi Tace "Na'am"
Yace "Me kike tunani game da wannan baƙin, ɗan megari da matarsa, bakya ganin Asirinmu ze iya tonuwa zamanmu dasu? Kar muje a samu matsala fa"
Widad ta ajiye abun hannunta jiki a sanyaye tace "To aini gaba ɗaya kaina ya kulle Yoseef, na rasa meye abunyi wallahi, kawai ni yanzu na fawallawa Allah lamarinsa, duk yadda yayi damu shikenan, ni dai babban fatana in cika burina kafin in mutu, nasan ko asirinmu ya tonu, ko be tonu ba dole ɗayanmu zeyi nasara, komu ko maƙiya, dan haka na miƙawa Allah lamarina, Allah ya kiyaye mu gaba ɗaya, amma nima nayi irin wannan tunanin naka, amma ba yadda na iya, in mun bar nan ina zamu?"
Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "da farko ina ɗan jin shakku a raina ne, amma Saleh ya tabattar min da babu komai, ba abunda ze faru yasan matakan daya ɗauka, sedai ina fatan Allah yasa hakan, Allah ya kiyayemu da kiyayewarsa"
Tace "Ameen ya Allah, Amma Yoseef nifa har yanzu baka taɓa gayamin meka gano a naka binciken ba, da kayi a lokacin muna gida"
Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "Anƙi a faɗa ɗin, kema ai jamin rai kika dingayi, kika ƙi gayamin tarihinki"
Cikin Shagwaɓa tace "please"
Yusuf yace "to shagwaɓaɓiya karkimin kuka dai, bincike daga cikin gidanku na fara yi, sedai nayi mamakin ƙiyayyar da matar mahaifin ki ke miki, da farko nayi zaton tana yi ne saboda halayenki, da abunda kikeyi na wulaƙanta ta da 'ya' yanta, sedai daga baya na gane son zuciyarta ne abunda take, akwai ranar da kika rufe ƙofa kika ƙi buɗewa, nasa Amal ta kawo miki tea, sedai kika zubar da tea ɗin, nayi mamakin ganin ƙwaya a ƙasan kofin shayin"
Widad tace "Kasan meyafaru a wannan daren, da na birkice?"
Ya girgiza mata kai alamar a'a.
Tace "samunsu nayi a falo, suna tattauna yadda zata damfari Daddy kuɗi, kasan na kanyi kwanaki a part ɗina ban fito ba, shine suka sakankance suna hirarsu, basu yi tsammani ba kawai suka ganni a ƙofar falo, shine suka shiga kame kame, bance musu komai ba, na fita dama fita zamuyi da kai ranar, bayan mun dawo cikin dare ina bacci, da yake ban rufe ƙofar ɗakina ba, kawai seji nayi cikin bacci ana lalabun hannuna, nayi yinƙuri zan ƙwaci hannuna kawai akayi min Allura, irin Allurar da'ake min a baya a birkita ni, take na fara dena gane abubuwa sosai, ban san wanda yayi min allurar ba, amma a haka bayan ya fita na tashi ina tangaɗi na rufe ƙofata, tun daga nan ban sake sanin abunda ke faruwa ba, se bayan dawowar Daddy, shiyasa a rayuwa na tsani matar nan Yoseef, na tsaneta fiye da yadda kake tunani, ji nake kamar in shaƙeta seta mutu"
"a'a karki kuma cewa zaki kashe mutum, sannan kika sani ko Daddy yana son matarsa? Ki barwa Allah zakiga sakayyar daze miki, amma banda ambaton kisa"
"Rabu dani bazaka gane ba Wallahi, dama muna komawa Seta barmana gida, sannan Aure zan nemawa Daddy da kaina, sannan ko banyi kisa ba idona idon Bukar a zahiri seya tafi lahira da tabom da zanyi masa"
"Kibi komai a hankali Widad, Insha Allah komai zamu bishi a hankali, kuma zamuyi nasara da yardar Allah, Amma karki yinƙurim ɗaukar doka a hannu, dukda bansan waye Bukar ɗinba, kuma bansan meya yi miki ba, amma karkiyi ganganci, muyi komai a dokance"
Ta girgiza kai tace "bazaka gane me nake jiba a Yoseef, idan ban kashe mutumin nan ba kona masa illar da zan nakasta shi ba, to zan mutu ne" tai maganar tana kwanciya a jikinsa.
Yasa hannu ya rungumeta a jikinsa, shiru ya wanzu a tsakanin su.
Yusuf idan suka gaji da zaman ɗaki sesu dawo tsakar gida, suyi shimfiɗa suyi zaman su, sannan gaba ɗaya Yusuf ya shiga kiyaye abunda yasan zai ɓata mata rai.
Lokaci lokaci takan shiga ɓangaren Jamila, dan ta ɗau jaririyarta, dan har goya mata ita take yanzu, idan ta goyamata ita ta zauna guri ɗaya ta nutsu sosai kamar am goyawa yaro, Jamila tace "Widad waike bakya saka Atamfa ne,? Kullum se ƙananan kaya, baki san yawan saka abu ɗaya yana gundurar mijinki ba?zeso yaga kin canza ai"
Widad tace "nifa ban iya saka wata atmfa ba, tun taso wata ni bana saka wata Atamfa fa ko makamancin haka"
Jamila tace "Eh naga alama nima, amma Aikuwa yakamata mu bawa mijinki mamaki, ina da sabuwar atamfa na haihuwar Yusra da aka bani na barka, zan kai a ɗinka miki"
Widad tace "A'a karfa Yoseef yaji haushi, ko yace ban gaya masa ba"
Jamila tace "baze ce komai ba, zeyi mamaki ya ganki acikin Atamfa, karki damu ba abunda zece zeyi murna shima, kim san maza nason a basu mamaki, amma ina fatan kun shirya da shi"?
Widad tace "eh mun shirya, tun jiya amma da ƙyar yayi fushi dani sosai"
Jamila tayi murmushi tace "Yawwa tawan, karki ƙara bari ya kwana yana fushi dake kinji ko, sannan ke zakiyi dabarun daze dena daɗewa yana fushi dake"
Widad tace "to ni ya zanyi?, yana daɗewa beyi ba, amma idan yayi fushi da ƙyar yake sauka fa"
Tace "to kidena yin abunda ze sashi fushin mana, kuma Kinga yadda kike da kyan nan masha Allah, gaki da manyan idanu masu ɗaukar hankali masha Allah, ki dena kallonsa kamar yadda kike kallon sauran mutane, ki nuna masa Wata kissar sai mata (wanda be karanta littafin wata kissar sai mata ba na Ammar da Mufeeda, ya garzaya ya nemi nashi, akwai darasi a ciki 😍 da Nishaɗantarwa)
Idan zaki masa magana, ki dinga kashe masa ido, ko ɗan shanye idanunki kamar kina maye, dama na ganki masha Allah, shagwaɓaɓiya ce duk kidinga masa, ko yayi fushinma da kansa ze sakko, saboda karya yi missing wannan kallon"
Widad kawai ta kwashe da dariya, "Au dariya ma na baki? Aiko ki gwada zaki bani labari, ki dinga zuwar masa da abubuwan da bakya masa a baya, hakan zesa ya ƙara sonki, kin san mazan ne seda lallaɓawa, amma dukda haka suna mana ƙoƙari kuma suna haƙuri damu, sedai duk Allah ya bamu haƙurin zama da juna"
Hanne ce ta shigo, ta dinga jiyo dariyar Widad da Jamila, ta ƙaraso ta ɗaga labule, taga Widad a zaune da goyon 'ya suna hira da Jamila, ai shigowar da ba tayi ba kenan ta koma, tana tsaki.
Sunusi ne mijin Jamila ya dawo, dan haka Widad ta bawa Jamila' yarta ta fice, dama ba gaisawa suke ba da Widad, dan haka ne kulata ba bata kula shi ba ta fito ta tafi ɓangarensu, ta tarar Yusuf ya shimfiɗa tabarma a tsakar gida yayi ruf da ciki, yana karanta azkar.
Tana zuwa ta cire hijjabinta, ta hau kan bayansa.
Yace "ya hakane? sekin karyamin baya ne? So kike ki maidani gurgu?"
"Idan na maida kai gurgu ai dai mijinane bana wata ba ko?"
Yusuf yace "Allah? waye mijin naki, gayamin"
Tace "Yoseef ne mana"
Yace "to naji ɗagani, dan kin ƙara nauyi, matar ƙauye kawai kina ƙauye amma ƙiba kike"
"kaima Mijin ƙauye, kuma bazan tashi ba, idan ka takuramin kuma ka sha cizo ba"
Yusuf yace "hmm aikin taɓa cizona fa, akwai tabon a jikina"
Ta zare ido tace "yaushe na cijeka?"
"Ranar da aka yi ruwan sama mana da daddare"
Tace "wane ruwan saman akayi?"
Yasa hannu ya janyota daga bayansa, ya kwantar da ita a jikin bango yana kallonta, sannan yace
"Ranar da kika kusa taramin jama'ar garin nan, kalli inda kika cijeni, banda duka dana sha a gurinki"
Tura baki tayi tace "Eh anyi ɗin ba kaine ka... Se tai shiru
Yace " ƙarasa mana"
"Anƙi a ƙarasa ɗin" tai maganar tana dariya.
Yusuf ma dariya yayi ya juya yayi rigingine, ta kwanta a ƙirjinsa tace "Yayan Daddy, a rayuwa yadda da farinciki sune gaba gurin sada mutum da walwala, kalleni a garin da babu wauti, ba ruwa, ba waya, ba system, ba motoci babu duk wani abu na more rayuwa, amma gashi kai kaɗai kana bani farincikin da duk wannan abubuwan dana rayu dasu basu bani ba, dukda na sha wahala kafin sabawa da wasu abubuwan a garin nan, amma bayan na saba sena gane ita rayuwa a bace me sauƙi, yadda ka ɗauketa haka take zuwar maka Nagode sosai Ɗan uwana, kayi rawar gani a rayuwar Yarinyar da baka haɗa komai da ita ba"
Rungumeta yayi yace "ina fatan kasancewa dake har ƙarshen rayuwa ta Widad, dukda bani da tabaccin ina da mahalli a zuciyarki, kuma ban san yadda al'umma zasu karɓi Auren nan namu ba, amma nidai nasan ina sonki Widad, ban san yadda hali zeyi ba a nan gaba, ko dai mu kasance tare, kokuma mu rabu, amma ni dai nasan ina sonki, Dukda soyayya ta ta baya, banji naso wata kamarki ba, I love you Widad "
Ƙanƙame Yusuf tayi, tana jin wani irin shauƙi yana ɗibarta, a koda yaushe ta kanji farinciki idan yana tare da ita, koda suna gida yana a matsayin direbanta, ko tana cikin ɓacin rai idan taga yazo se taji damuwarta ta ragu, tana jinsa sosai a ranta amma ta kasa danganta hakan da Soyayya, a duk lokacin da taji damuwa ta mata yawa, tana haɗa ƙirjinta da nasa zataji bugun zuciyarta na daidaituwa, da zarar ya fara rarrashinta ta kan manta ɗinbin damuwarta, tayi wani irin sabo na bazata da Yusuf, wanda har take jin ya zata kasance idan ta koma gida, Yusuf ya nesanta ida?.
"Yayana, zaka dawo gidanmu da zama dan Allah"
"meyasa kika dage sena koma gidanku da zama?"
"Saboda Halima zata bar mana gida, da kaina zan samowa Daddy mata ya aura, zaka dawo gidanmu ko?"
"Meyasa kika damu sena dawo gidanku bayan bakya sona?"
"Nima ban san dalili ba, sedai ina jin a jikina, rasa ka a rayuwata babban giɓine, kuma tamkar rasa garkuwa ne a gareni"
"Nima rashinki a gareni babban giɓine, saboda na kamu da makauniyar soyayya cikin bazata, amma ban saniba ko zaki iya cigaba da zama dani idan kika san wani abu game da rayuwata"
"Ni dai koma meye, dan Allah ka zauna a gidanmu idan mun koma kaji"
Ta maganar cikin Shagwaɓa tana kallonsa, "Babyna wannan wane irin kallone haka kikemin? You look so cute da kika juya idonki"
Kamar ƙaramar yarinya ta kuma cewa "dan Allah kec zaka dawo mana"
Yace "sedai in dawo im cigaba da kaiki unguwa, ni nafi son aikina"
"Aikuwa demotion zan maka, ka koma gadin ɗakina"
"Bakomai in dai hakan zesa in dinga ganinki"
Yai maganar yana saka hancinsa a wuyanta.
Ji suke tamkar suka ɗaine a duniyar, Kasancewar gidan ba kowa dan haka hankali kwance suke soyayyarsu a tsakar gida, basu san Hanne tana ɗaki tana jiyo dariyarsu ba, dan har leƙsensu take ta taga tana share hawaye.
Anwar yayi tunanin bari ya tsaya a gidansu Nurat su gaisa, kwana biyu kota waya basa haɗuwa dan bama hawa yake social media ba sosai balle su gaisa, sannan su jajantawa juna abubuwan da suke wakana, sedai a bakin gate megadi ya tareshi yace "wa kake nema ne?"
Anwar yace "gurin Nurat nazo"
Megadin yace "baka da labarin abunda ya sameta wancan zuwan naka ne? Mahaifinta seda ya kusa halakata, ni ban san hali irin na mutumin nan ba, dan haka yun wuri kabar gurin nan tun kafin kaja mata wata wahalar"
Mamakine ya cika Anwar sosai da jin abunda megadin yace, amma yace "Shikenan, nagode sosai, dan Allah ka gayamata nazo mu gaisa ne kawai, kace ina gaishe ta sosai, sannan idan ta samu lokaci ta taɓani a waya se in kirata"
Megadin yace "Shikenan, zan gayamata wannan karka damu kanka dan dai saƙo"
Anwar ya cika da mamakin me zesa a hukunta Nurat dan yaje gurinta, alhalin mahaifinta be nuna masa komai ba har gaisawa sukayi dashi, amma ace an hukunta ta kuma bata gaya masa ga abunda ya faru ba.
Haka yakama hanyar gida, yanata zancen zuci, yana danja a tsaye yana ta tunani a ransa kamar ance ya ɗaga kansa, ya hango Ramlah a farajiyar wata plaza, da Fahad da wasu maza suna ta shan shisha, kayan jikinta sun Matseta sosai kamar ba 'yar musulmi ba, abun ya ɗaure masa kai ya sake mustsustuke idonsa ya kalli gurin, babu ko tantama itace, ya dafe kai yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Mummy kina me Ramlah ta lalace haka? Kalli yadda ta koma"
Motarsa ya fizga a guje yai gida, zuciyarsa na wani irin tafasa kamar ta tsaga ƙirjinsa ta fito dan baƙin ciki.
Sedi yana zuwa gidan, ita kanta Mummyn bata nan gidan babu kowa se masu aiki.
Ya zauna a falo yana jin zafi akan sakaci irin na mahaifiyarsu, kuma da yayi magana taji haushinsa, amma yau kome ze faru seya ɗau mataki akan Ramlah.
Tun la'asar yaga Ramlah, amma har bayan isha'i babu wanda ya dawo gidan, yana nan zaune Yaji ƙararar mota ya leƙa, ya hango Ramla ta fito da ƙyar take iya buɗe idoma, saboda azabar buguwar da tayi, amma a haka ta tuƙo mota zuwa gida.
Ta riƙo takalmanta a hannu da jakarta, tana tafe tana gware da bango harta shigo falon.
A zafafe Anwar ya kalleta yace "daga ina kike?"
Cikin maye tace "Ni.. Ni...... Ni....... Fa na inda naje, kawai naje cin... Cin Abinci ne a w. Wa. Wani restaurants that's all"
Kwaɗamata mari yayi, wanda seda ta dawo hayyacinta na 'yan sakanni, ya zare beilt ya dinga dukanta yana ƙwallo da ita, seda yayi mata kaca kaca ya tabattar ta daku sannan
yace "kaiconki Ramlah, kin biyewa wannan ɗan iskan kina lalacewa, dama Aurenki zeyi da sauƙi wataƙila ya shiryu a sanadin ki, amma kawai kin biye masa kin ɓata rayuwarki a banza a wofi kaiconki Ramlah, yanzu kin riga kin ɓata rayuwarki, ke ba aurenki zeyi ba kuma babu wani mutumin kirki daze yadda ya haɗa zuriya dake, tunda kika zaɓi rayuwar shaye shaye da lalacewa"
Hajiya Halima ce ta buɗe ƙofar falon, ta shigo ita da Amal, sedai tayi tozali da Ramlah a baje a gurin fuskarta duk a kumbure, saboda dukan da ta sha, gashi a hakanma maye take yi.
"Lafiya mezan gani haka Anwar?"
Cikin ɓacin rai Anwar yace "Mummy ɗazu a danja, na hangeta a harabar wata plaza suna shna shishsa ita da maza, da wannan sakaran Fahad ɗin mara tarbiyya, kuma ta dawo gidan nan tana maye"
"Kuma shine zaka mata wannan dukan, idan ka kashe ta kuma fa kalli yadda ka daketa, idan kaji mata rauni kace baka san yadda akayi ba?"
"Mummy, amma yanzu laifin Ramlah bekai a hukunta ta ba? Shaye2 tana mace, kallifa a hakan ma maye take yi, bata san meke faruwa ba, kuma amma a haka kike cewa meyasa na daketa?"
"Rufemin baki ko in tsinkeka da mari, baiwar ubankace ita da zaka mata wannan dukan? Kai duk laifin da kake yi haka nake kamaka in jibga kamar jaki? Ka ɓatawa yarinya halittun fuska, kuma kana cemin maye take, haka ake mayen zafin duka dai yasa take surutai, dalla wuce ka bani guri babban banza kawai "
Anwar yace" Amma Mummy kina gani......
A fusace tace "fitarmin daga falo tun ban rama mata abunda kayi mata ba, ɗan banza me baƙin hali kamar ubansa, yadda halinka yake haka na matsiyacin ubanku yake, baƙin hali dai akwai shi hadda na masifa da jaraba ka gado shi a gurinsa, fice ka bani guri me zuciyar banza data wofi "
Anwar yasha mamakin zagi da cin zarafin da mahaifiyarsu tayi masa, alhalin ga gaskiya tana gani ƙurƙuru, amma ta rintse ido ta masa wannan mummunan cin fuska haka.
Hajiya Halima ta ƙarasa gaban Ramlah tana ɗagota tace " Sannu Ramlah, Allah ya haɗaku da jarababbem ɗan uwa yana nema yaga bayanki, ni na rasa wannan mummunaan hali daya kwaso a gurin ubanku, Amal kawomin ruwan sanyi a fridge in shafa mata ko zata farka daga suman da tayi, da wannan surutan da take yi"
Amal tace "Mummy, maganar gaskiya fa Yaya Anwar yana da gaskiya, Ramlah fa maye take yi, kuma ba yau ta fara shan kayan maye ba"
Hajiya Halima tace "kamar yaya kenan?"
"Kamar yadda na gaya miki mana, wallahi tana shaye2 ne, wannan cocacolan da take sha, syrup take juyewa a ciki ta sha abunta, shine zakiga tana ta faman bacci, nayi mata magana amma kin san halinta baji take ba, wannan Fahad ɗin kuma shine silar komai"
"Ke Rufemin baki, idan har dagaske ne tana shaye2 da tuni na sani, ko kuma wani abune yake damunta yasa tayi shaye2, amma idan ta tashi zamuyi magana, sannan daga nan kar in sake jin maganar nan kinji na gayamiki"
Amal ta jinjina kai tace "to"
Da daddare Yusuf yana kusa da Widad akan katifarta suna bacci tare, wani mummunan mafarki Widad tayi, suna tafiya ita da Yusuf a wani guri me kyau, suna sanye da kaya masu kyau sosai, yana riƙe da hannunta yana mata hira tana ta dariya, shima fuskarsa ɗauke da murmushi.
Babu zato wata mata ta ɓullo a fusace, ta riƙe hannun Yusuf tana jansa, Widad ta fashe da kuka ta riƙe Yusuf gam tana
"dan Allah Yoseef karka tafi ka barni, dan Allah ki ƙyalemin shi nawane ba naki bane, na fiki buƙatarsa, nafi ki kusanci dashi, dan Allah kiji tausayina ki barmin shi, dan Yoseef karka barni"
Yusuf kuma ya fara ƙoƙarin bin matar nan su tafi, yana kallon Widad fuskarsa ɗauke da damuwa, da alama shima yafi son zama a gurin Widad.
Hannunsa ya fara zamewa daga na Widad, ta fara dena ganin fuskar Yusuf se dishi dishi.
A firgice ta farka daga baccin tana haki, tana ambaton sunan Allah, a gigice ta ɗakko fitila tana haska inda Yusuf yake sedai me......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/15/21, 4:52 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
94_95
Haska inda Yusuf ke kwance tayi tana sauke numfashi, gani tayi ya haɗa gumi yana bacci, daga shi se dogon wando da alama zafine ya isheshi, shine ya cire rigar ya kwanta haka, ta hasakashi sosai taga kamar baya numfashi, ta kai hannunta da sauri Ƙirjinsa saitin zuciyarsa, taji zuciyarsa tana bugawa a hankali, bacci yake yi sosai sedai yayi gumi sharkaf a jikinsa.
Tashi tayi a hankali ta tafi ta lalubo mafici, tazo ta zauna ta ɗaga kansa ta ɗora a kan cinyarta, ta shiga yi masa fifita, tana goge hawayen da bata san dalilinsu ba, tama jin yadda ƙirjinta ke cigaba da bugawa saboda mafarkin nan da tayi, tana kuma godewa Allah da yasa ba gaske bane mafarki ne.
Yusuf ne yayi ƙoƙarin yin juyi, yaji shi a jikin mutum, ya kai hannu ya tattaɓata, ga ƙaramar fitilarsu ta kunna wadda haskenta yayi ƙasa sosai saboda rashin batir.
"Widad lafiya kuwa?"
Ta jinjina masa kai alamar eh, "to meyasa kawai zaki katse baccinki ki tashi kina min fifita?"
Tace "kasa bacci nayi, kuma naga kayi gumi dayawa, ka kwanta kawai ka cigaba da baccinka"
Yai murmushi yace "Allah sarki my Widad, nagode sosai Allah yayi miki albarka, amma Kasancewar ina mijinki kina mata ta bashi ke nufin, in cutar dake ba dare lokaci ne da Allah ya bawa bayinsa, dan su huta ko suyi ibada, amma in hanaki naki baccin dan nawa no baze yuwu ba, kece yakamata in miki fifita kiyi bacci saboda nasan wata ƙila zafine ya hanaki baccin, kuma nine gaba dake akwai buƙatar in tausaya miki "
Girgiza masa kai ta kuma yi tace " A'a kabari, kwanta kayi bacci kawai "
Tashi zaune yayi, ya karɓe maficin hannunta sannan ya kwantar da ita, yana mata fifita yace " wai na ganki some how looking disturbed, menene meya hanaki bacci ne matar? "
"Yoseef i have a bad dreams"
"On what?" ya tambaye ta.
Nan ta gaya masa abunda ta gani a mafarkin, ta ƙarashe zancen da kuka.
Murmushi yayi yace "Ohh My God, ya ilahil alamina Widad dreams are not true, mafarkine fa kawai meye na ɗaga hankalinki, ba gani a tare da ke ba, dena kuka haba babyna"
Kukan ta sake fashewa dashi tace "i don't want to lose you, Ina tsoron ya zama gaske mafarkin, sometimes our dreams come true, ina jin tsoro sosai, and am still having palpitation, ina jin kamar ze faru ne a gaske"
Yusuf yace "No my dear, kawai dai kin tsorata ne, kuma zuciyar ki ta fara jin abunda Yusuf yake ji game dake, amma in dai nine bazan gujeki ba ko in juya miki baya, sedai in daga ɓangaren ki a samu akasi, amma nikam nasan ina son matata"
Yai maganar yana saka hancinsa a wuyanta, shiru ta ɗanyi tana ƙara so ta tabbatarwa da zuciyarta kalaman Yoseef ɗin, na mafarkine kawai baze zama gaskiya ba, amma dagaske kenan Ta kamu da soyayya?
Tana cikin tunanin taji Yusuf yace "Wife, ina kika samu wannan turaren ne, tun rana yake tashi a jikinki, ina ta ƙoƙarin riƙe kaina, tauraren nan yayi daɗi a jikinki sosai"
Cikin cuna baki irin na wanda ya gama kuka tace "Jamila ce tabani"
"Wow, kince mata kin gode dai ko?"
Ta gyɗa masa kai, yace "good, ki tambayeta kuɗin turaren nan, zan bayar a ƙara mana"
"Dayawa fa ta bani, wai itama maƙociyarta ce a barrack ɗim da take ta bata dayawa da ta haihu, shine nima ta zubamin kuma da yawa fa ta bani"
Cikin nishaɗi yace "dukda haka i suppose to pay for it, naji daɗi Sosai, bazan manta kyautar turaren da kika bani ba, kyauta ta farko da kika bani, kyauta daga hannun masoyiyya, amma sedai naji kamar wari nake shiyasa kika bani turare"
Duk da a damuwa take, amma seda tayi dariya tace "taɓ duk wannan gayun naka, dukda basajar da kake yi amma abunda ya fara birgeni da kai ashine tsaftarka, dan wasu dan suna irin wannan aikin se suyita ƙazanta, su a dole se sun nuna talaucinsu, abun da yasa na baka turaren nan, duk lokacin da naji turare na tashi a jikinka, se naji wata kasala ta kamani, ko laifi kayi min seka rage ƙarfin fushin da nake ɗauke dashi, shiyasa nace bari in canza maka turare ko zan dena jin hakan, wataƙila daga turaren naka ne "
Yusuf yayi murmushi yace 'to daga baya mekika fuskanta?"
"Nagane cewar kwarjini kakemin, kuma abun ba daga turarenka bane daga kai ɗinne"
Yusuf yace "Ahse dai an daɗe ana so"
Tace "Ana son me?"
Yace "bakomai, just forget, ni dai ki bari kawai in shaƙi wannan ƙamshin me daɗin gaske"
Shiru tayi tana saurarensa ba tare da ta sake cewa uffan ba, aikuwa Yusuf ya wuce makaɗi da rawa, yau dai be sha cizo ba🤭🤭, sema wani farinciki mara misaltuwa da suka tsinci kansu a ciki.
A hankali a kunnenta yace "God bless you my Wife, thank you very much"
Ƙin magana tayi, sema lafewa data sake yi a jikinsa, yace "tashi in ɗora mana ruwa, naga akwai sauran kalanzir ko?"
Widad tace "eh akwai, amma shekaranjiya Hindu tayi girki a kai, idan babu se muyi dana sanyi"
"No akanme? Haka kurum in baki ruwan sanyi kiyi wanka inje ki shiɗemin, abunda baki saba ba, bakomai zan dafa mana, inma babu naje in tada murhu yanzun nan"
Widad tace "Murhu kuma a daren nan?"
"Eh mana, meye a ciki, muna cikin baccin mu kin tasheni kin janyo mana aiki"
"Au hakama zakace ko?"
"A'a tuba nake, wane ni" yai maganar cikin murmushi.
Akayi sa'a da kalanzir ɗin, ya fito da rishon tsakar gida ya ɗora musu ruwa, saboda yanayi na zafi kae ɗakin ya ƙara ɗaukar zafi, kafin ruwan yayi zafi, Yusuf ya ɗakko musu gashashiyar gujjiya suka zauna suka kama cin abarsu suna hira a wannan daren, se kace aljanu.
Jin ana ɓuruntu, yasa Hanne ta miƙe cikin tsoro ta leƙa taga dan ganin meke faruwa, ta hangesu zaune a cikin farin wata, suna ciue ciyensu suna hira.
Ta jinjina kai tace "lallai wannan kinyi dacen miji, yana sakar mata fuska sosai saɓanin mazan garin nan, wanima murmushi baze iyayiwa mace na wai karta raina shi.
Ƙarshe ma tare sukayi wankansu, Yusuf jinsa yake kamar wani sabon mutum, wani irin farinciki ya mamaye zuciyarsa, sedai duk da ɓangaren Widad ma hakan take, amma ta kasa manta mafarkin da tayi akan Yusuf, haka kurum abun ya tsaye mata a rai.
Anwar gaba ɗaya abunda ya faru yau a gidansu ya tsaye masa a rai, muraran mahaifiyarsu ta tabattar maaa da tafi ƙaunar Ramlah akansa, kuma bata son ace ga laifin da tayi, balle a saka rana zata mata hukunci, ransa ya ɓaci sosai dan haka ya fara tunanin, wane mataki yakamata ya ɗauka, dan janye jikinsa daga harkokin gidanma gaba ɗaya?.
Yana kwance yana tunanin meye mafita, yaji wayarsa tana ringing, da kamar baze ɗaga ba amma ya janyo wayar ya ɗaga.
Jin muryar Nurat ce tayi masa sallama yasa ya ɗan saki ransa ya amsa, Nurat tace "Yaya Anwar, ɗazu kazo baka samu ganina ba"
Anwar yace 'eh, nazo mu gaisa amma megadi yacemin zan ja miki matsala, wancan zuwan da nayi ma na jamiki matsala amma baki gayamin ba"
Ajiyar zuciya Nurat tayi tace "hmm kai dai bari kawai Yaya Anwar, abunne duk se a hankali, na kasa gane kan mahaifina gaba ɗaya, ya hanani fita zuwa ko ina, sannan ya hana kowa yazo inda nake, na kasa gane manufarsa, sam ban gane inda ya dosa ba"
Anwar yace "Amma kuma lokacin da yazo ya samemu tare be nunamin komai ba"
"Ai haka yake yi, baya taɓa nunawa a gaban mutane, amma bayan tafiyar ka har dukana yayi"
"Subhanallah, kiyi haƙuri wallahi ban zan zuwana ze kawo miki matsala a gurin mahaifinki ba"
Nurat tace "bakomai karka damu Yaya Anwar, ba laifinka bane, sannan kayi haƙuri rashin haɗuwar da mukayi"
"A'a bakomai Nurat, ina fatan ubangiji Allah ya daidaita tsakanin ku, dama biyowa nayi mu gaisa, wallahi nima kusan a cikin damuwa nake Nurat"
"Subhanallah, meyafaru?"
"Wallahi Nurat abubuwan nan da suke faruwa gaba ɗaya na rasa abunyi ma, jiya Ramlah a buge ta dawo tayi mankas da ƙwaya, amma ƙiri ƙiri dan na hukuntata Mummy ta fituttuke tace ƙaryane, taita faman Yimin faɗa, ban san meyasa take haka ba, abu in dak Ramlah ce bazata taɓa ganin laifinta ba, ƙarara take nuna banbanci a tsakaninmu"
Nurat tace "se haƙuri ai, lamarin iyayen nan namu sedai addu'a, ni gashi nikaɗaice a gurin iyayena, amma wasu lokutan idan Daddy yayi min wani abun, se inga kamsr bashi ya haifeni ba, yaita treating ɗina a hagunce, abun yana damuna sosai"
Anwar yace "kin san kowane bawa da irin tasa jarabbawar, kowa akwai ta ɓangaren da Allah yake jarabtarsa, sedai fatan Allah ya bamu ikon cin jarrabawa"
"Ameen Yaya Anwar"
"to akwai wani news ne daga gareki?"
Ajiyar zuciya tayi tace "News kam baza'a rasa ba, amma kasan wai Yusuf ɗan sanda ne ashe?"
'Eh nasani, amma da farko nima ban saniba, se daga bayan nan, da aka fitar da wannan Sanarwar"
Nurat tace "Amma Anwar meka fuskanta game da wannan Sanarwar"
"To ni dai abunda nake gani, wata maƙarƙashiyar ce aka shirya domin ɓatawa Yusuf suna, turoshi akayi domin bincike akan maƙiyan Daula, amma kuma daga baya ake nema a ɗora masa sharri, ni yadda naji ma sunce wai babu wanda ya turoshi aiki gidan"
Nurat tayi ajiyar zuciya tace "Yaya Anwar, wannan abubuwan duk shirine akayi shi domin a ci mutuncin Yusuf, kuma shiryayiya ce aka shirya wannan lamarin, ni ban san yadda za'ayi Yusuf ya ƙuɓuta ba, yana cikin matsala"
Anwar yace "hakane, nima naje na samu Alhaji Bulama, tunda yana da alfarma a ƙasar nan, ayi bincike yadda yakamata"
Nurat tace "Yaya Anwar, tayasu da Addu'a shine abunda yakamata, amma harkar ƙasar nan se godiyar Allah, gashi haryanzu babu labarin Mahaifin Widad"
Anwar yace "wallahi kuwa, to Allah ya wuce mana gaba, Allah ya kawo mafita gaba ɗaya"
"Ameen ya Allah, nagode sosai Yaya Anwar"
"Bakomai, nima nagode"
Washegari da safe, Widad ta riga Yusuf tashi, yau da kanta ta dafa ruwa tayi wanka, ta gyara tsakar gidan nan fes tayi wanke wanke, ta zuba shinkafa ta fara tsincewa, ta tsince shinkafar nan iya yadda zata iya, amma Yusuf be tashi daga bacci ba,
Taje inda yake kwance ta zauna ya gama ƙare masa kallo, sannan ta shiga tashinsa kamar zata tashi jariri.
A hankali ya buɗe ido, yanayi yana lumshewa alamar bacci be isheshi ba tace "wai yau da Yunwa zaka barni?"
Murmushi yayi ya sake lumshe idonsa, cikin Shagwaɓa tace "tashi Yunwa nakeji fa"
'Nikuma bacci nakeji "
"to bari inje in dafa da kaina, tunda ba zaka tashi ba"
"No sorry, bari in tashi in dafa miki'
"kaga harna dafa ruwa nayi wanka, na tsince shinkafan ma"
"Haba dai?"
'dagaske nake fa"
Ya miƙe ya duba ta share ko ina, tayi wanka har shinkafa ta gyara ta wanke, murmushi yayi yace "Alhamdilillah, mutuniyar ta fara zama mace"
"Dama ni namijice?"
"A:a ni bance ba, amma mace ai seda aikin gida, kice zamuyi surprising Daddy '
" Sosai makuwa "
Ya ƙarasa musu girkin, suka zauna sukaci Abincin su.
lokaci lokaci Widad se taji gabanta ya faɗi, amma ta dake da dinga ɓoyewa, dan karya gane tana cikin damuwa.
Widad tace "Yoseef ina kewar su Mama sosai da Hindu, mutum rahama ne"
'Ni Aljani ne kenan? "
" A' a ni ba haka nace ba, na saba ganinsu ne, ina ganin mostinsu da giftawarsu, amma kwana biyun nan shiru bana ganinsu"
Yusuf yace "yanzu kin gane amfanin mutum a rayuwar ɗan adam kenan? Babu yadda za'ayi mutum yayi rayuwa shi kaɗai babu mutane kuma yace hakan yafi daɗi"
'hakane, dan ina gudun a cutar dani ne, shiyasa nake gudun mutane, amma yanzu nasan wannan mutanen da muke tare dasu bazasu cutar dani ba, shiyasa nake kewarsu"
"hakane, naga taku tazo ɗaya dasu sosai, Amma naji anjima zasu dawo ai ko?"
"Eh anjima zasu dawo insha Allah"
"to Allah ya dawo dasu lafiya"
Ta amsa da Ameen.
Anwar sosai yake tunanin samawa kansa mafita, akan lamarin gidansu dan duk se yaji zaman gidan baya kansa ya fita a ransa.
Shiga yayi gidan da nufin gaida mahaifiyar su da safe kamar yadda ya saba, sedai ta window ɗin ɗakinta yaji suna magana ita da Ramlah, seya tsaya be ƙarasa ba.
"Ramlah wannan rayuwar da kika ɗauka ba inda zata kai miki, ki kiyayi kanki da shaye shaye nan, kinga na gwale 'yan uwanki jiya amma tabbas maye kikeyi, dan dai inajin daɗin shawara dake ne da fushi zanyi dake"
'Mummy na dena fa"
"Shikenan, ai dama nasan zaki dena, nace ya kukayi da Fahad ɗinne, ina fatan dai baze tona mana asiri ko gurin babansa ba"?
' Haba Mummy, shiya fara ma tunda abun nan harda shi ake ƙaruwa "
"Yawwa haka nake son ji, yanzu wannan manyan filayen nasa nake so in sa a kasuwa na GRA, dan haka kiyi masa magana, kamar yadda akayiwa Gidajen layout ɗin nan takadda, suma wannan ayi musu takaddu mu siyar, ke ni ko miliyan sha biyar biyar, a siye su"
Ramlah ta ɗan zaro ido tace "Mummy million sha biyar kima, a filayen miliyan kusan arba'in ɗin za" a siya a haka? "
" Eh to seme? Da gumunmu muka tara? Nifa sonake ayi yadda za'ayi mu ɗan tara daga nan mu san nayi, dan haka ki masa magana, ke har gidan nan ma sena siyar dashi, ai in sun san wata basu san wata ba"
"hakane Mummy, amma gaskiya baza'a siyar da filayen nan a haka ba se an ƙafa, in ba haka ba mume zamu ci?"
"to koma dai yane, kiyi masa magana ayo takaddun daga nan musasu a kasuwa"
"Shikenan zamuyi waya dashi, kokuma inaga anjima ma zezo, se muyi maganar gaba ɗaya"
Hajiya Halima tace "ainaji daɗin harkar nan da yaron nan, motocin nan na farmhouse ma ai duk shi yayi mana hanya aka siyar dasu, banda sauran abubuwa, aini wannan lamarin ma gaba ta kaimu"
"Wallahi kuwa Mummy, semunci rabon mu tukuna"
Anwar ji yayi kamar ƙasa ta buɗe ya nutse a ciki, dama kadarorin Daula mahaifiyar sa ke siyarwa yana wadaƙa da kuɗin? Lallai ɗan Adam butulu ne, idan ya tambayeta ina motocin gidan se tace tasa an kaisu Farm House, dama abunda take yi kenan? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un'
Jiki a sanyaye yaje ya ɗau motarsa ya tafi gidan gonar Alhaji Daula wanda aka riga aka mallakawa Widad, yaje da niyyar zagaye yake ya biya dan yaga gidan, ya tarar fiye da rabin motocin nan idan ya tambaya se ace Hajiya ta turo a ɗauka, hatta dabbobin Widad tana ta musu ɗuki ɗai ɗai, dan akwai da yawa wanda bana ƙasar nan ba a ciki, dan haka ana siyansu da tsada.
Abun ya bawa Anwar mamaki, ya tuna irin gwagwarmaya da ɗawainiya da Daula yayi dasu, amma mahaifiyar su ta rasa dame zata saka masa se wannan zalunci da tsantsar butulci, lallai ɗan Adam butulu.
Da ƙyar ya kai kansa gida, saboda azabar ɓacin ran da yake ciki, ta haɗa kai da 'ya' yanta suna ta wadaƙa da dukiyar marainiya data mahaifinta, se yanzu yake jin Widad bata da laifi da suke iƙrarin tana Wulaƙantasu.
Da yamma Widad taita zuba ido a hanya taga ta ina su Gwaggo zasu dawo, se bayan ƙarfe biyar se gasu sunyi sallama sun dawo, Widad ta dinga murna, tace "Sannunku da zuwa na zaci ma kum fasa dawowa yau"
Gwaggo tace "aiko kowa be dawo hau ba dole in dawo saboda ke, muna can amma hankalina yana nan"
Widad tace "Hindu 'yan biki, a huta azo a bani labarin abunda ya faru"
Hindu tace "ni wallahi muna gurin biki, hankalina yana kan makaranta"
"to aini tunda kuka tafi, nace a bari sekun dawo a cigaba'
Suka baje a tsakar gida, Yusuf ya fito yayi musu sannu da zuwa sannan ya fita.
Saboda ɗaurin Aure, megari ma yaje gurin bikin, da shi da Sunusi Kasancewar Yayar megari ce ta aurar da 'ya, nan ma Yusuf ya shiga yayi musu sannu da zuwa, daga nan megari yaja shi da hira suka shantake a gurin.
Gwaggo ta baje kayan biki da suka zo dasu, ƙulli daban tayiwa Widad na kayan gara kuma fal da yawa, kayan zaƙin nan.
Gasu wainar masa da ƙuli, Widad tana son kayan zaƙi dama, ta zauna ta cicci abunta tana lashe baki.
Ana idar da sallar magariba ta tura yaro ya kira mata Yusuf a waje, Yusuf ya shigo gidan ya shiga ɗaki ya sameta yace
"lafiya kika aika a kirani? Me zaki ban?"
"To ai kaine kaƙi dawowa tun ɗazu"
"to ai bamuyi sallar isha'i ba, kuma zamuyi karatu"
Ta miƙe ta ɗakko masa kayan da Gwaggo ta bata, Yusuf yace "masha Allah, 'yar gatan Gwaggo wannan duk namu ne?"
"Eh mana shiyasa nace kazo kaci naka, gashi nan kaci iya cinka, ni na tafi tsakar gida"
Tana gama maganar ta miƙe ta fita.
Yusuf ya zauna yana cin kayan gara, Widad tayi waje, Hindu tana ta bata labarin yadda bikin ya gudana, Hanne kuwa se cika take tana batsewa, ba wanda yabi ta kanta suka ƙyaleta da ƙuncin ran da take yi.
Bayan Yusuf ya gama ya fito tsakar gida yana alwala, Widad tace "Mama waiya mutum ze gane idan yana da cikine?"
Gwaggo tace "to babbar magana"
Jamila tace "karki damu, ni zan gaya miki in munfi haka yawa"
Widad tace "ai yanzu ma muna da yawa ki gayamin mana"
Hari tace "to bahaushiya, tana nufin se daga ke se ita tukuna"
Widad tace "koma yane, ni dai dan Allah Mama ki dingamin Addu'a, Allah yasa in samu ciki"
Hari tace "Ai himma kawai zaki ƙara, idan kika shiga ɗaki tun magariba, se wata magaribar"
Sam Widad bata gane me Hari ke nufi ba, Yusuf shi kunya cema duk ta kama shi, ya tashi ya fice waje.
Jamila tace "Widad zomu je ɓangarena, in baki tawa tsarabar"
Widad ta tashi ta bita, Jamila tace "Widad nace miki irin wannan tambayoyin, ni zaki dinga yiwa ba Gwaggo ba, kunyace dasu, kinga baki taɓa haihuwa ba balle ace kin san alamomin, dan haka ba lallai alamomin da zan gaya miki su zamana ciki bane, amma mafi akasari dai cikinne ke sawa, Alamomin da zaki gane kina da ciki sun haɗa da, ɗaukewar Jinin al'ada, zazzaɓi, ciwon kai, jiri, Mamanki zasu danyi miki nauyi, koma su dinga zafi, yawan tashin zuciya, koma amai, yawan san ki kasance da mijinki a shimfiɗar Aure, ko jin haushin hakan, yawan som cin wani abu ko ƙin wani kalar Abincin, da sauransu amma alamomin ba lallai kiji su duka ba"
Widad tace "wanne ne babban alama to?"
Jamila tace "Ɗaukewar Al'ada, ko kuma laulayi idan cikin me laulayi ne"
Widad tace "shikenan nagode sosai"
Jamila tace "abubuwan duk da nake gayamiki, kina ganewa kuma kina aikatawa dai ko?"
Widad ta jinjina mata kai.
Suka cigaba da hirarsu, tana ci gaba dayi mata lectures akan Rayuwar Aure.
Da daddare Yusuf ya dawo Widad tayi masa sannu da zuwa, ya lura da ta canza akan abubuwa da dama, wanda da a baya ba tayi.
Ba zato Yusuf yaji Widad tace "Yayan Daddy dan Allah meye maganin mata?"
Yusuf ya kalle ta yace "ke a ina kikaji hakan?"
Tace "A gurin Jamila"
'Sha kika yi kenan? Ya tambaye ta
Widad tayi shiru ba tace komai ba, kawai taga Yusuf ya kwashe da dariya yace "lallai yarinya kina ruwa"
Kamar zata yi kuka tace "wani abu ne ze sameni?'"
"A'a ni bance wani abu ze same ki ba"
Gaba ɗaya bata gane me Yusuf yake nufi ba, taga ya ɗauki kayan shimfiɗarsa yayi wajen kwanan sa.
' Yusuf meye haka wai? "
Yusuf yace " A ina? "
" Naga ka ɗauki kayan shimfiɗarka, yau bazaka kwana a gurina ba?'
"Eh yau a gurin kwanciyata zan kwanta"
Kamar zata yi kuka tace "Amma naga yaushe rabon daka kwana anan gurin, kawai se yau zaka wani ce a can zaka kwanta?'"
Kamar Yusuf zeyi dariya ya maze yace "A'a ni gaskiya sha'awar kwanan kam bargona nake, kowa ya kwanta a inda ya saba kwana"
Kawai ta zauna tana kuka, Yusuf ya sha dariya sosai, dan Widad ta iya gaɓunta wasu lokutan, seda yaga dagaske take sannan ya koma inda suke kwana yana mata dariya.
Da gari ya waye, idan Widad ta tuna abunda tayi jiya kawai se wani irin haushi yakamata taita tsaki, Yusuf yace "uwar kwaɗayi, gobema kije a kuma baki abunda baki sani ba kici"
"Bazan ƙara ba har abada"
Yusuf yaita dariya yace "A'a gaskiya ki ƙara, ni zan bada kuɗi ma ki ƙara"
Ya dinga mata dariya, taga idan ta biyewa dariyar da Yusuf ke mata se tayi kuka, dan haka ta biye masa suka dinga dariyar tare.
Cam tace "Yoseef, dan Allah ka dinga min addu'a, Allah yasa in samu ciki, haihuwa nake so nayi nima"
Maimakon yayi magana, kawai seya janye ta daga jikinsa ya bar mata ɗakin.
Mamaki ne ya cika Widad ta bishi da kallo, tana tunanin me yake nufi da wannan abunda yake yi, duk lokacin da tayi zancen tana son samu ciki, seya canza mata meye Nufinsa nayin haka?......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/15/21, 4:52 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
96_97
Widad taje ta samu guri tayi zamanta a tsakar gida tana kuka, saboda tayi mamakin abunda Yusuf yayi, idan wanine yace ze mata haka tabbas zata ƙaryata, amma se gashi Yusuf ke ƙyamar haihuwa ko meye dalilinsa oho, to koma dai wani daliline ai bashi da ƙarfin da zesa ace yana gudun haihuwa haka, idanma tunanin sa yadda zasu yi idan sun koma gida, ai suna da hujjar da zata nuna aure sukayi ba zaman kansu ba, kuma tasan Daddy zeyi farinciki da hakan, abun da yake ta buri yaga 'ya' yan Widad a rayuwarsa.
Kusan kwana biyu babu Anwar, an kai har gurin 'yan sanda amma babu Labari.
Hajiya Halima ta tafi gurin Alhaji Munir, yana ganinta ya ɗan ɓata rai yace "to uwar matsala, ke duk inda aka ganki ba alkhairi se tarin matsala da damuwa"
Haɗe rai tayi sosai tace "nice ma kake gayawa haka? Dole kace ganina ba alkhairi bane, kuma ai ganin naku ba alkhairi bane ba, malam ɗana ya ɓata Anwar, tun jiya ban san inda yake ba, idan wata ƙulla ƙullar kuka haɗa, kowani makircin to kufito min da ɗana, dan babu ruwansa a harƙallar da mukeyi "
Alhaji Munir yace " to akama ɗanki ayi masa me? Har akwai abunda za'ayi aji tsoron gayamiki ne? Kije can kineme shi, idanma a cikin namu ne toni dai bada yawuna ba, dan ban san anyi ba, sedai ko Musa kowani amma ni ban san komai ba kam"
"to bari kaji in gaya maka, idan ma ka sani ka rainamin hankali wallahi duk abunda nayi maka kai ka ja, dan wallahi sena saka mutum dana sani da cizon yatsa"
Alhaji Munir ya taɓe baki yace "a banza ƙiba a kunne, ƙarewa 'yar gidan Daulama duk zare idonta da hura hanci shekaru kusan Goma sha biyu ta kasa gano mu balle ta ɗau mataki, se wata ke zakizo min da wannan ƙaramar barazanar taki dan ki firgitani, kije kiyi duk abunda zakiyi karki fasa, tunda naga alama daga ke har Musa kun fara hauka"
"Shikenan, zakaga hauka ganin idonka, wallahi idan da saka hannunku kika sacemin yaro wallahi se kunyi danasani, zan nuna muku masifa da kaidin mace, shima Musan zanje in kasa masa warning, tun wuri ka kiyaye ni, ku fita daga idona kallon ku kawai nake yi"
Ta juya a fusace ta koma inda motarta take, Alhaji Munir ya bita da ido, yayi tsaki ya koma ciki yana jinjina hauka da rashin hankali na mata.
Daga nan gurin Alhaji Musa taje a Office ɗinsa na neman zaɓe, nan ma suka fafata, sukayiwa juna kaca kaca shi da ita, sannan ta bar gurin rai a ɓace.
Murtalane yake gyarawa Anwar ɗakinsa wasu lokutan, wani lokacin kuma da kansa yake gyara abunsa dan shi babu ruwansa, be ɗau duniyar da zafi ba sam kamar yadda mahaifiyarsa da' yan uwansa suka ɗauka, Nura ya shiga yana gyara ɗakin Anwar, yaga takadda a ƙarƙashin fulon Anwar ya ɗakko tajadar ya buɗe yakaranta ta tsaf sannan ya ɗauka ya nufi cikin gidan.
Suna zazzaune a falo sunyi jugum jugum, suna jimami da tunanin inda za'a ga Anwar Murtalah yayi sallama.
Suna kallonsa amma ba wanda ya amsa masa, a fusace Hajiya Halima tace "dalla malami meyene, kamar baka san a halin da muke ciki ba, kazo ka samu a gaba da sallama, meyene jarababbu kawai?"
Murtalah yaji haushin abunda Hajiya Halima tayi masa, koda yake imda sabo sun saba, hantara da Wulakan da cin mutunci, sun saba ganinsa dan abunda wanda ya ɗaukesu aikin baya musuma yanzu yi musu ake sedai haƙuri, amma ya dake yace "Dama ba wani abu bane, ina gyara ɗakin Anwar ne na tsinci takadda a ƙarƙashin fulonsa, shine nace bari in kawo miki"
Tasa hannu ta karɓi takaddar sannan tace "to ai seka tafi ko? Ko a gabanka zan duba kaga reaction ɗina, aji daɗin gulma, munafukai kawai 'yan sa ido"
Sum sum Murtalah ya fice yana ƙunƙuni, a ransa yace "Ubangiji Allah ya kawo mana ƙarshenku, jarababbiya dake da wannan matsiyatan' ya'yan naki masu kama da jakuna, da bakinsu kaman na yaran hankaka'
Nurane yaji Murtala na zage zage da tsine tsine, yace " kai kuma kai dawa? "
Murtalah yace "nida wannan balamar matar mana, daga zuwa na tsinci takadda a ɗakin ɗanta naje kaimata, ta kama zagina tana cemin munafuki, ni dana san hakane ma da wallahi ban kai mata takaddar ba, inga ta tsiya"
Nura yace "kaima meya kaika? Jiya Daga Isa ya ɗanyi mata tunanin albashi, ta zage shi tsaf taci masa mutunci, hadda wai tunda ba gidan ubanmu bane, wanda ya gaji yaga baze iya ba ƙofa a bude take ya ƙara gaba, kajifa se kace ita nata gidan ubanne, ko daga gidansu tayi gammo tazo dashi, aimu tsakanin mu da wannan matar sedai Allah ya isa wallahi "
Murtalah yace " Allah ya isa me 'yanci makuwa wallahi, dan koni na mata ba adadi banza tana tafiya a karkace, ita ba ɗa' a 'ya' ya babu tarbiyya, se kayan ɗuwawu kamar zata kai kayan tusa birni"
Sosai Nura ya dinga dariya yace "Wallahi idan ta jika seka bar gidan nan, kaima ka sani yaseen, amma fa ka iya ba'a da cin mutunci"
Murtalah yace "to takorenin mana, ai yanzu gidan Daula sunan ne kawai, amma babu komai a ciki duk a bushe muke, saboda wannan iblishiyar matar, kana gani yanzu duk tarin jama'ar dake zuwa gidan nan yanzu babu kowa saboda baƙin halinta, wannan da a aljanu tazo ba shakka se ace itace babar sheɗan"
Nura yai dariya kamar cikinsa zs ciwo, ganin yadda Murtalah ya harzuƙa sosai se bala'i yake yana zage zage da rashin mutunci da gani kasan an kai shi maƙurar bangone.
Nura yace "malam kar dai kayi saɓo, a gidan ubanwa ka taɓa jin ance sheɗam yana da uwa, hattara dai"
"Bari Nura rainane ya ɓaci wallahi, Allah yasaka mana wallahi, Allah ya nuna mana ranar da dubunta zata cika a tarkatata a koreta da wannan iblisan 'ya' yan nata"
Nura yace "Ameen dai, manyan iblisai makuwa, dan wannan babbar me soyayyen ido shaye2 take yanzu, saura ƙiris shekaranjiya tabi ta kan ƙafar Isa da tayoyin mota, Allah ya temake shi yai saurin matsawa kuma ta fito daga motar, ta zage iyayi da kakaninsa tsaf sannan tabar gurin nan tana maye "
Murtalah yace " haka zasu ƙare, saura kuma hauka da tamɓele, tunda haƙƙin mutane suka san susa a gaba suci babu imani babu tausayi "
Hajiya Halima kuwa tana buɗe takaddar, taci karo da rubutun Anwar kamar haka
" *_Asslam Alaikum warahmatullah zuwa ga mahaifiyata, nasan lokacin da zaki riski saƙona nayi nisa da gida, nisam da bana tunanin zan iya waiwayar gida a kwanan nan, na bar gidane saboda faɗar ma'aiki salallahu alaihi wassalam, babu biyayya ga abun halitta gurin saɓawa Mahalicci, dan haka bazan iya jure cigaba da zama daku ba ana aiakta abunda be kamata ba, nasan idan nayi Yunƙurin yi miki nasiha ba zaki saurareni ba, kin zaɓi lalacewar 'yarki saboda tana miki hanya gurin tara dukiyar Haram, kin fifita akanmu wanda kema kin san hakan ba dai dai bane, kuma kina ɗauki ɗai ɗai ga kayan mutumin daya yayi sanadiyar fitarmu daga masifar talauci zuwa arziki, kin haɗa kai da maƙiyansa ana cutar dashi, nayi dana sani nayi kuka da bincike na ya tabattar min da dake aka haɗa baki komai yake gudana tsakaninsa da maƙiyansa, kaicon wannan butulci naki Mummy, ni bazan iya cigaba da zama daku ba dan haka na bar muku gidan, dama bana ubana bane ba, ina miki fatan Alkhairi dake da ƙannena a duk inda kuke, Allah ya sadamu da alkhairi, ɗanki me ƙaunarki har kullum ANWAR *_
Jikintane ya hau tsuma tana rarraba ido, yayin da wani irin gumi from no where ya shiga tsatsafo mata, ta dinga rarraba ido kamar shege a rabon gado.
Ramlah tace "Mummy lafiya kuwa, wetin inside that later?"
Miƙo mata tayi, domin idinta ya gane mata, Ramlah ta karɓa ta shiga karantowa a fili, tana zuwa ƙarshe ta yarda takaddar tace "shikenan munshiga uku Mummy, wallahi tonon asirinmu yazo, dan abune me sauƙi a gurin Anwar ya tona mana Asiri, kin san halinsa Mummy, yau munshiga uku, wayyo wallahi har cikina ya fara ciwo"
Amal tace "wannan shi ake kira tashin hankali wanda ba'a samasa rana, ina muka kama tunda wannan me iƙrarin ustazancin ya san abunda ake ciki"
Hajiya Halima ta goge fuskarta tace "ni tunanina a gidan ubanwa yasan wannan maganar? Waye ya gaya masa? Tsawon shekaru goma sha ɗaya ana abun nan a sirrance cikin rufin Asiri, waye ya tina min wannan Asirin haka ni Halima?"
Ramlah tace "Mummy ba wannan tunanin ya kamata kiyi ba, tunanin meye mafita yakamata ayai, tunda sanin inda ya samu labarin bashi da amfani"
Hajiya Halima tace "toni ta ina zan fara ne? Ta ina yakamata infara neman mafitar? Na farko ban san inda ya tafi ba, kuma tabbas abune mawuyaci ya iya ɓoye abun nan yakasa gayawa wani, ke ni gaba ɗaya na rasa abunyi wallahi, kuma ɗazun nan naje mukayi kaca kaca dasu Alhaji Munir, da Alhaji Musa na zata su suka sace shi, ni wallahi da iya tafiyar yayi da sauƙi, amma sanin wannan abubuwan yafi komai masifar ɗagamin hankali, kar Anwar ya tona min Asiri in lalace a bakin duniya"
Ramlah tace "aida iya lalacewa a bakin duniya ne da sauƙi Mummy, idan Asiri ya tonufa se komai ya watse ya lalace manya manya abubuwa ne zasu tonu, wanda baki isa kici bulus ba"
Cikin tashin hankali Hajiya Halima tace "Au nikaɗai ma banda ku?"
Ramlah tace "Mummy koda mu koba mu, ai laifinki yafi namu yawa, duk abunda mukayi kece kika samu a hanya, yanzu mafita ɗaya ce, kije ki samu su su Alhaji Harunan, ku sake sasantawa dama kun saba faɗa ku shirya ai, kuje ku sasanta kunemi mafita, dan wallahi Asirin ki ya tonu nasu ya tonu dan se mun faɗi komai "
" Kai Amma wannan yaro akwai shege me baƙin hali, kamar duk fafatukar nan ba danku nakeyi ba? "
Amal tace " Mummy amma kin san halinsa, dama da kuɗin nan sun samu ban san yadda za'ayi dashi ba, dan kema kanki kin san baze cisu ba"
Halima ta zauna kawai murza goshi take yi, saboda tashin hankali da damuwa.
Widad fafur taƙi Yusuf, zaman ɗakinma ta ƙiyi, ya dafa Abinci da safe amma taƙici, ƙarshe ma ta koma ɗakin Gwaggo, ta hau gadon Gwaggo tayi kwanciyar ta, Yusuf ya rasa ta ina ze fara yiwa Widad bayani, ta ina ze fara nuna mata yana mata son da baze taɓa juya mata baya akan wani abu da takeso ba muddin be saɓawa ubangiji ba? Yana da dalilinsa me ƙarfi ya zeyi tagane gaba ɗaya ta fututtuke taƙi saurarensa.
Haka ya shirya ya fita, se bayan ya fita ta koma ɗakin ta gyara, ta barmasa Abincinsa taƙi ci, da yamma ɗalibai suka shigo karatu gurinta, sukayi karatunsu har kusan magariba sannan ta sallamesu.
Gwaggo ta fuskanci kamar sun kuma samun saɓani tsakanin ta da Yusuf, amma bata son taita mata shisshigi, dan haka ta ƙyaleta, dan gaba ɗaya walwalarta ta ragu, kusan ko san magana ma ba tayi, ko kayi maganar ma bata san abunda kake faɗa ba tana tunani.
Dan mamaki yakasa barin zuciyarta wai Yusuf ne yake gudun ta haihu dashi, ita iya tunaninta babu wani dalili daze sa yayi hakan sedai son zuciyarsa kawai.
Da daddare ya dawo tana kallonsa, bata kulashi ba dan ko sallamarsa ƙin Amsawa tayi, ta barmasa ɗakin gaba ɗaya ta koma tsakar gida inda aka baje tabarma ana hira.
Haka ya fito kamar maraya, yayi alwala ya tafi salla, ya dawo shiru shiru taƙi komawa ɗakin, har kusan ƙarfe goma na dare, ya fito yazo inda take dayake duk hirar nan ma da ake yi, ita ba wani magana take ba, sedai in anyi abun dariya ta ɗanyi murmushi, sam hankalinta baya kan hirar ta fitone kawai dan karma Yusuf yayi mata magana.
Tana jikin bango, babu haske a inda take zaune, yazo ya zauna a kusa da ita yayi ƙasa da muryarsa yace "My love, dan Allah kizo muje ɗaki mana, kin barni kamar maraya kin dawo nan kin zauna, dan Allah kiyi haƙuri kizo mu koma mana, kina da miji amma kizo zaman hira"
"Yoseef bana son sake jin kalamn nan naka na yaudara, wanda naji a bayama sun isa Allah ya amfana, kaje da can ai ba tare muke hirar ba"
"Widad kalaman nawane na yaudara?"
"bakaji bane in sake maimaitawa, kalaman yaudara da kake yaudara ta dasu na fara amince maka zaka butulcemin mana"
"Yi haƙuri dan Allah karki ɗaga murya mana, zomu je ɗaki muyi magana"
Widad tace "bazani ba, nace bazanje ba, ka ƙyaleni"
Yusuf ya sake marairaicewa yace "nasan haushina kikeji, a ƙule kike dani amma please and please am very sorry, kiyi haƙuri mu koma ɗaki"
Ƙarshe ma juya masa baya tayi, alamar idan ya gama ze iya tashi yayi gaba.
Abun duniya ya ishi Yusuf, haka ya tashi ya tafi ɗaki, jiki a sanyaye, ya dinga tunanin dama tun farko data fara zancen cikin, ba haka ya ɓullo mata ba, gashi ta birkice gaba ɗaya, tama ƙi saurararsa.
SE kusan sha ɗaya da rabi, dabar hirara nan ta watse, kowa ya tashi ya tafi makwancinsa, Widad ma ɗakinsu ta nufa, sedai tana zuwa ta tarar da Yusuf a zaune be kwanta ba.
Tazo ta tsallake shi ta shige abunta, tana ƙoƙarin canza kaya, Yusuf yace "Widad, akwai buƙatar ko sau ɗaya ki bani dama, in kare kaina yana da kyau kiji ta bakina kafin yanke hukunci"
"baka da ta cewa fa, ai labarin zuciya a tambayi fuska babu wani abu da zaka gayamin, fuskarka ta bayyana abunda ke cikin zuciyar ka, dan haka ka ƙyaleni kawai, bana san sake jin komai kawai ka rabu dani, kuma ɗane idan Allah ya bani kace ba naka bans, ni ima so kuma bana buƙatar taimakonka a rainon ɗana, da can baka san cikin ze shiga ba kake mu'amala dani, ko in an tashi bani ciki shawara za'ayi da kai? "
" Nace dai kiyi haƙuri please, zan gayamiki dalilina dan Allah, amma kiyi haƙuri ki dena wannan fushin"
"Se kuma kayi, kanka ake ji"
"Widad, Widad magana fa nake miki"
"kaga idan ka takurani wallahi zan fita ina kwana a waje, ka ƙyaleni"
Ya dinga binta da kallo harta kwanta abunta taja bargo ta rufe kanta.
Amal ce zaune tayi tagumi jugum, kamar an musu mutuwa tace "Mummy, yanzu idan kinje gurinsu Alhaji Haruna me zaki ce musu? Kuma ta ina za'a fara binciken inda ya tafi?"
Hajiya Halima tace " sanin gaibu se Allah Amal, zanje dai inga yadda zamuyi dasu ne kawai"
Ramlah tace "to yanzu idan aka ganshi Meza kiyi masa?"
Hajiya Halima tace "ubansa zanci da farko, sannan ince masa duk abunda aka gayamasa ƙaryane"
"Mummy, Yaya Anwar fa isa almost 30 years, he is not kid, tayaya zaki gayamasa haka ya yadda, idan kuma ba gaya masa akayi ba wani abu ya gani fa?"
"Waike Amal bakinki baya faɗar alheri se sharrine, to rufen baki tunda bazaki faɗi abun alkhairi ba"
Ramlah tace "bahaka bane Mummy, yanzu idan kika je neman mafita gurinsu Alhaji Haruna, kina ganin suna ganin Asirinsu ze tonu idan suka ganshi zasu ƙyaleshi hakane? Karfa ki manta har yanzu babu wanda yake sa tabbas na Bala yana raye a kurkuku, saboda sun tsoron Asirinsu ya tonu ana cewa sunsa an kashe shi, kuma sun cigaba da aiki da Saleb, ba tare da yasan sun kashe ɗan uwansa ba, those people are evil, they are very dangerous fa"
"Na shiga uku ni Halima, yanzu ya zanyi wallahi duk cikinku ina sonku, babu wanda zan iya zuba ido inga ya cutu in haƙura, duk ni na haifeku ina ƙaunar ku"
Amal tace "mun sani Mummy, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki a nemo mafita mana"
Isa megadi na zaune a bakin gate, riƙe da 'yar radionsa, yana ta fama ya kama stationsa amma se wani ɓurari take saboda rashin batur, ya dire radion yana zage zage da Tsinewa Hajiya Halima, ganin kuɗin batirin radio ma ya ga gareshi.
Jiya yi ana bugun gate ɗin da ƙarfi kamar za' a karya ƙofar, shi dai beji horn ɗin mota ba, dan baka ya miƙe a fusace yana bala'i yana masife yana cewa "wani jakin me wannan yake mana wannan bugun se kace gidan ubansa, kokuma wani ɗan fashi, mutum se kace gidan uabansa, ko yaya kuka buga anaji, muma za'a buɗe amma komai se mutane sun yi hauka, aikin banza iyayen maula kawai"
Haka ya ci gaba da surfa masifa, sannan ya buɗe gate ɗin, wani mutum ya gani a tsaye, da wani koɗaɗɗen yadinsa shara shara, hularsa ma tayi baƙi ƙirin saboda dauɗa wani zaburarre dashi kamar korarre, Isa ya ƙare masa kallo yace "mutane ba dai Jaraba ba, baka san an sace me gidan ba, dama shine yake baku, wannan mastiyaciyar me hannun jarirar ba'a ɓanɓararta jeka Allah ya baka haƙuri, an dema sadaka a gidan nan"
Mutumin yace "ba Sadaka nazo nema ba, gurin Halima nazo"
"au gatsal kake faɗar sunantaa? Allah yasa ta jika, tukuna ma a danginta ban taɓa ganin mutum kamarka yazo ba, daga ina ko kwatance akayi maka?"
"ba kwatance akayimin ba, kaje kace mata tayi baƙo, ita tasan waye"
Isa yace "shikenan, shigo daga ciki seka zauna akan benci, amma in turoka akayi a baka aikima, babu guri dan muma ba biyanmu take ba, mace ce hannu kamar kuturwa, tasan a bata amma bata san ta bayar ba"
Haka Isa ya cigaba da soki burutsunsa, yaje ya sanar da Hajiya Halima zuwan baƙon nan, amma ƙarshe seda ya fito da baƙin ciki da dana sanin zuwa sanar da saƙon nan.
Har kusan awa guda bata fito ba, Muratalah ne yaji tausayinsa ya bashi ruwa, dan da gani muyumin ya jigata kafin yazo, ita shaf tama manta da wani baƙo da akace tayi, ta shiryo tsaf abunta zata fita, har an ɗakko mata mota, Nura yace "Hajiya baƙonki fa"
A fusace ta juya zata yi masifa "wai wane jarababbem ne haka aka dameni dashi"
Muyumin yace "nine nan"
Tana waiwayawa ta zare ido ta dafe ƙirji tace "Na shiga uku, Shu'aibu!!!"
Abun duniya ya dami Yusuf, baccinma ya gagar ɗaukarsa, jin shiri yasa ya zata ko Widad tayi bacci, kwana biyu kenan basu kwanta manne da juna ba, duk yaji babu daɗi, a hankali ya lalaɓa yaje bayanta ya kwanta ya shiga bargon nata, ya rungumeta a jikinsa.
"Malam meye hakane? Ka lallaɓone kazo ka samu abunda kake so in anjima nace Allah ya bani ciki ka haɗe rai"?
Yusuf ya girgiza mata kai yace "Aa', ɗumin jikinki nake son ji, dan Allah kimin afuwa Widad, ki saurareni please"
"Dan Allah nima ka ƙyaleni, wallahi bana son jin komai daga bakinka, lallaɓani zakayi in yarda da kai, in anjima kuma ka juyan baga"
"babu juya baya tsakanina dakw Widad, ina son ki fahimceni ne kawai, bari in baki labarin wani yaro"
Miƙewa take ƙoƙarin yi, tace "bana son ji, ka riƙe abunka"
"Dan Allah ki tsaya kiji, yana da mahimmanci sannan akwai darasin rayuwa a ciki"
Ganin bata da niyyar saurararsa yasa ya janyota jikinsa, ya rungumeta gam sosai yana ajiyar zuciya, a hankali taji ɓacin ran nata na raguwa, dan haka ta kwanta tayi shiru tana sauraren bugun zuciyarsa.
Yusuf ya nisa sannan yace "Labarin yaron nan zaki ji daɗinsa sosai, bari in gayamiki abunda ya samu yaron.....
Mun kusa ƙarƙare part 2, idan part 2 kawai kika siya karki sake ayi 3 babu ke.
0 comments:
Post a Comment