Aka dinga ziga mutumin nan akan yaƙara Aure tunda bata haihuwa amma yaƙi, gashi babban ɗan Sanda yana matuƙar son matar nan tasa, yana da rufin Asirinsa dai dai gwargwado, matar nan tasa tana matuƙar kyautata masa shida 'yan uwansa dukda yadda suka tsaneta suka sata gaba, suna ganin komai ya samu akanta yake ƙarewa, gata da yawan larura Kasancewar tana da Athma, kuma genotype ɗinta AS ne, dan haka kusan kullum cikin rashin lafiya take da zaryar Asibiti, shi kuma yana jin tausayinta saboda mahaifiyarta bata raye, ga mahaifinta bashi da cikakkiyar lafiya shima.
Idan ciwonta ya tashi, shine yake ayyukan gidan, ko kuma yayi zaman jinyarta a gida ko a Asibiti, duk wata kulawa daya dace ya bata yana bata, katsam Allah ya bata ciki ba zato ba tsammani, ya dinga murna shida ita, sedai cikin beje ko ina ba ya zube saboda yawan rashin lafiya.
Bashir mutum ne me tawakkali dan haka be taɓa gazawa ba, baya nuna mata ya ƙosa da rashin lafiyar da take yawan yi, ya kance a tausayi irin na mata da son da matarsa Jidda ke masa, idan shine yake a halin yawan larurar nan bazata guje shi ba, to shi meze sa ya gujeta, bayan ba ita tayi wa kanta ba, Allah ne ya jarabceta.
Bashir Ya zama abun kwatance a dangi, mijin tace nusari da ire iren wannan miyagun sunayen haka suke kiransa, wai ya ƙare a gindin mace seta talautashi tukuna ta tsiyata shi, kullum cikin ciwo gashi bata da wata mamora tunda ba haihuwa take yi ba, ya zamana saboda irin wannan cin mutunci da ake mata ko shiga tarurrukan biki ko suna ko makamancin haka ya hanata, saboda muddin zasu haɗu da 'yan uwansa gorin nan ne se anyi shi.
Idan suka fuskanci baya gari, haka zasuje har gida su zazzaga mata rashin mutunci iri iri, su ɗauki abunda suka ga dama, suce ai kayan ɗan uwansune, banda tayi Asiri ta mallake shi, ta yaya ze dinga bata abubuwa bayan juyace ba haihuwa take ba, se aikin larura dasa ɗanuwansu zaryar Asibiti, duk ta tsiya tashi saboda yawan rashin lafiyar da take yi, yayi da lafiyarsa yayi da aljihunsa, dan hatta jini idan ta buƙata shike bata.
Ita kuma ba sawa ba fitarwa, haka zasuyi abunda suka ga dama idan sun tafi ta sha kukanta, kamar yadda suka saba baya gari sukaje suka mata cin kashi yadda suke so, ya dawo ya tarar da ita tasha kuka, ya tambaye ta meyasa meta? Tace masa ai bakomai, seda taga ze ɗau zafi sannan ta gaya masa, shi yayi mamaki, be taɓa sanin har gida suke biyota suyi mata ba, aikuwa yaje yayi musu tatas, kuma yace musu mutu ka raba shi da matarsa, tana da matsayi me girman gaske a zuciyar sa, dan haka komai tayi bata laifi a gurinsa, yace larura da lafiya duk na Allah ne, me lafiya na ina komawa mara ita, mara ita ya samu, babu wanda yake sa kuɗinsa dan ya sai cuta, sedai Allah yana jarrabar komai, dan haka ya yadda rashin haihuwar Jidda, da rashin lafiyar ta jarabtace Allah ya jarrabesu dan ya gwada imaninsu.
Nan ma dangi suka kuma kwaroroto, suna yamaɗiɗi dashi, waiya fifita matarsa akan danginsa, abun takaicin hadda maza ake wannan sakarcin, ba abunda yake ƙona masa rai irin hadda ƙannensa da suke uwa ɗaya uba ɗaya suke ƙin abunda yake so, ya tabattar a zuciyar tausayi da imani na mahaifiyarsu, da tana da rai duk bazata bari ayi masa haka ba, shikam Bashir ya musu banza dasu da surutun da suke yi, yayi kamar besan sunayi ba.
Daga baya ma ya koma, indai zeyi tafiya ta 'yan kwanaki wani garin harkar aiki, da ita yake tafiya suje su dawo, dan karma wani daga danginsa su bita gida su ɗaga mata hankali Wataran tafiya ta kama shi, yace ta shirya su tafi Tare, haka kuwa akayi suka tafi tare, seda sukayi wata guda sannan suka shirya dawowa Kano, sedai dare yafa yi musu a hanya, Bashir yace 'Jidda, dole idan muka shiga gari mu samu Hotel mu kwana, kin san ƙasar nan ba security "
Jidda tace " dama abunda nake son in gaya maka kenan, dan a tsorace nake "
" to sarkin tsoro, karki damu muna samun guri zamu tsagaita da tafiyar "
Da yake daga kudu suke, wani dajin idan sukabi, sesu shafe tafiyar awa guda basu ga ko giftawar me keke ba, balle abun hawa.
Daga nesa suka dinga hango hayaƙi, gaba ɗaya Jidda ta tsurw tace "Anya bazamu juya ba? Nifa tsoro nakeji hayaƙin meye wancan?" '
"idan mun juya mu koma ina? Aiba inda zamu se naga meke faruwa a gurin"
Jidda ta cigaba da salati, dan tunda yasa kansa seya ƙarasa, saboda Bashir Jarumi ne sosai, bashi da tsoro.
Suna suka ga wata motace tayi hatsari a gurin, sun daki bishiya motar ta kama da wuta, ma'aurata ne a ciki sun kasa buɗe murfin motar su fita, se matar ta daki glass ɗin motar da yayi saura be ƙarasa rugurgujewa ba, ya fashe, tana ta ihu Wuta na cin jikinta tana Yusuf ɗana, ɗana Yusuf ta jefo jariri daga Widow, hannun ta duk ya ƙone se salati take, da alama shi mijin nata dama tuni ya mutu.
Ta wurgo jaririm ta wannan tagar, sedai jikinsa lafiya ƙalau beji ciwo ba, amma gefen wuyansa ya yanke, saboda glass ɗin motar daya fashe, yaron yasha hayaƙin gobara, baya numfashi sosai ga jini na zuba a wuyansa, Jidda tai Wuf ta ɗauki kyakkyawan jaririn a towel, se ƙamshim turare da ƙaurin hayaƙi yake yi, suna ji suna gani haka Wuta ta ƙone motar da iyayen wannan jariri yake.
Jidda tai kuka tai kuka, tunda take bata taɓa ganin bala'i da tashin hankali irin wannan ba, Bashir ya rarrasheta, suka shiga mota ya dinga tsala gudu, har suka fita gari suka sami Asibiti suka shiga, kasancewarsa ɗan sanda id card kawai ya nuna akayi admiting ɗin jaririn.
Bashir ya ɗakko waya daga aljihunsa, Jidda tace "wa zaka kira?"
Bashir yace "zanyi wayane, in gayawa abokan aikina incident ɗin ɗaya faru, azo a san yadda za'ayi muyi mus handing ove jaririn mutafi gida"
Girgiza kai ta shigayi tace "dan Allah Yaya Bashir ina son yarom nan ka barmin shi, karma ka gayawa 'yan sanda mun samu yaro, kabarmin ina so tunda ban taɓa haihuwa ba"
"to yanzu ai danginsu zasuji daɗi idan suka ga yaron ya kuɓuta"
"Yaya Bashir, komai nasu fa ya ƙone, ta ina za' a fara neman dangin nasa, dan Allah ka barmin inajin ƙauna da tausayin Yaron nan a raina, dan Allah ka bsr maganar nan, zan raini yaron nan in dai kamin izinin hakan, dan Allah"
Bashir yayi shiru, ganin yadda take kuka, bilhaƙƙi son ɗan nan take dagaske, yasa yace "shikenan is ok, Allah ya tayaki riƙo maman Yusuf, Allah ya raya mana Yusuf bisa tafarki madaidaici, ya bashi haƙuri da juriya irin na me sunan"
Nan ta dinga murna, ta rungume Bashir tana zuba masa godiya da Addu'a, ita da Bashir sukaje yayo siyayyar kayan jarirai kala kala, da duk abunda zasu buƙata, seda suka kwana uku a Asibitin daba'a garinsu ba, dan jaririn ya samu sauƙi.
Bashir kuma yayi waya, akaje aka kwashe gawarwakin nan a inda aka yi hatsarin.
A kwana ukun nan madara take haɗawa ta bashi, Jaririn sam bashi da rigima, harta ɗan fara damuwa ko jikin nasa ne be gama warwarewa ba, daga baya kuma ta fuskanci haka halinsa yake, bashi da rigima sam, bayan an sallamosu suka kamo hanyar gida, amma tun a hanya ta fara tunanin me zata cewa dangin mijinta idan suka ganta da ɗa? Bashir ya lura da yadda tayi shiru, yace "Maman Yusuf, ya kuma naga damuwa a fuskarki?"
Ta ɗan yi ajiyar zuciya tace "Yaya Bashir, ina fargabar amsar da zamu bawa mutane, idan suka ganni da jariri, mussman su Yaya Asma'u"
Bashir yace "ba dai kina son ɗanki ba?" ta jinjina masa kai alamar eh.
"to karka damu da abunda mutane zasu faɗa, kisa a ranki ba rainon kariri kawai zakiyi ba, harda na ƙalubale ki manta da wani ƙalubake da abunda mutane zasu faɗa, mu rungumi jaririnmu, Allah ne ya bamu"
Ta kallesh tace "dagasake kaima kana son jaririn nan?"
Yace "meze hana, muda muke nema Allah ya bamu, ai ina son duk abunda kike so, ina son Yusuf nima bari kiga mu koma gida, hakika zan kuma yanka masa, muyi shagalin suna dan Jaririn naki befi watanni biyu ba, gashi me kyau masha Allah kamar ke"
Jidda tayi murmushi tace 'mijina ɗan Aljanna, Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira "
" Ameen tare da ke matata"
Se fargabar da take ta ɗan ragu, suka nufi gida.
Bayan la' asar suka isa gida, bayan sun yi salla sun huta, ta dafa ruwa ta yiwa jaririnta wanka, ta canza masa kaya, ta goya abunta tana jin ƙaunarsa a ranta.
Bashir da kansa ya sai cingam, ya dinga aikawa mutane cewar za suyi taron sunan jariri, mutane suka dinga mamaki dan su dai basu san tana da ciki ba.
Nan 'yan uwansa sukazo domin ganin ba' asi, aikuwa suka tarar da ita da Jariri.
Wani Yayansa ya sashi a gaba da tambayoyi, akan sun san matarsa ba haihuwa take ba, ina suka samo ɗa Bashir yaƙi gayamusu, suka haɗashi da wani ƙanin babarsu, ya kira shi ya tambayeshi,
Bashir yace "gidan marayu sukaje suka ɗakko yaro, jaririn iyayensa ne suka yi hatsari suka mutu, kuma ba'a san daga inda suke ba, shine sukaje gidan suka karɓo shi.
Nan ma 'yan uwa suka samu nayi, wai ya biyewa matarsa sunje gidan marayu sun ɗakko shege, babu wani iyayen yaron sun mutu, duk yaran dake gidan shegune.
Jidda ta dinga kuka tana ɗanta ba shege bane, Bashir yaita rarrashinta, ya gayyaci mutane akayi sunan Yusuf, akayi shagali sosai aka watse.
Jidda ta rungumi jaririmta da mijinta, sedai wani abun mamaki da iko na ubangiji, tunda Allah yasa suka fara rainon ɗan nan, Jidda ta dena wannan rashin lafiyar da take yawan yi, ta warke sarai ta dena kwanciyar Asibiti, idan ba an faɗa maka ba bazaka ce tayi fama da jinya ba a baya, sosai suke rainon Yusuf, bazaka taɓa cewa ba ɗansu bane, idan har kana son farincikin Jidda da Bashir to kaso ɗansu Yusuf.
Sedai fa dangin mijinta suka kuma sata a gaba, suka tsani yaron nan ƙarara suke nuna masa ƙyama, suke ce masa shege, Sedai Jidda tayi kuka, ita dai tasan Yusuf ba shege bane da iyayensa, amma haka take sharesu ta cigaba da kulawa da shi ita da mijinta Bashir.
Jidda ta kauda kai daga duk wani ƙalubale da take fuskanta, akan rainon Yusuf ta kowane ɓangare, Bashir yana iya ƙoƙrinsa akan Yusuf, daya isa shiga makaranta ya sashi a makarantar kuɗi, wanda a wannan lokacin se 'ya' yan wane da wani ake kaiwa private school, amma yasa shi a private school, yasa shi a makarantar islamiyya, ga tahfeez sannan aka ɗaukar masa malamin lesson, idan Bashir na gari shike kai Yusuf makaranta ya ɗakko shi, idan baya nan kuma Jidda ke kaishi, Yusuf ya taso cikin gata da kulawa, yayin da gefe guda dangin babansa suka sake ɗora masa karan tsana shida iyayensa, mussman Jidda waita asirce musu ɗan uwa tasa sun ɗakko shege yana masa bauta, ya taɓe a gindinta dana wannan shegen yaron.
Babban abun mamakin be wuce yadda suma yana wahalta musu dai dai gwargwado yadda ze iya amma basa gani.
Yusuf ya tashi da tarbiyya da ilimin addini dana zamani, gashi da matuƙar haƙuri, da wuya kaga yayi fushi, be fiye shiga faɗace faɗacen yara ba, karatunsa ya fiye masa komai.
A tsakanin maƙwabta ma ana samun hassada da ƙyashi, ganin kaf tsukinsu babu me gatan Yusuf, komai ana masa sam bashi da wata damuwa, hakan yasa maƙwabta suma suka fara jin haushinsa, abun wasa duk tsadarsa zakaga Yusuf dashi, shi kaɗai amma keken hawa uku ne dashi na hawa, shekararsa takwas a duniya, amma har system yake da ita saboda karatun Al'qur'ani da sauran litattafan addini dana zamani, dan haka Ƙwaƙwalwar Yusuf na kawo wuta sosai.
Nanma maƙota suka fara jin haushinsa, saboda wannan gata da tarairaya a cewarsu dama gashi shege kuma ana ƙara sangarta shi, Yusuf tunda ƙuruciyarsa yake jin kalmar shegen nandm daga bakin mutane, besan ma'anar kalmar ba, amma yasan kalmace me muni, da wasu lokutan maƙotan ko yaransu kan gaya masa, ko kuma dangin Abbansa, Yusuf yana da matuƙar haƙuri da kawaici, ko wasa ya fito cikin yara idan yaga za'ayi faɗa ko rigima, seya bar gurin ya koma gida, wasu lokutan har haushin haƙurinsa Bashir ya kanji, yaita masa faɗa ya dena yadda yara suna masa rashin mutunci yana ƙyalesu, se yace ai malaminsu yace "Allah yace yana son bayinsa masu haƙuri"
Katsam ranar suka yi faɗa da wani yaron maƙwabcinsu, akan kayan wasan Yusuf ɗin, yaron ya dinga zaginsa, uwar ɗan ta fito ta shigarwa Ɗanta, Yusuf ya juya ze koma gida, yaron ya biyo shi ya dake shi, Jidda ta fito jin Hayaniya, Jidda tace "Maman Salim bekamata ki dinga shiga faɗan yara ba, ɗa na kowane kamata yayi ki haɗasu ki musu nasiha, in da kara ɗana da ɗanki ai duk naki ne, idan zaman tsakani da Allah akeyi, Yusuf da Salim duk namune'
" Ke saurara karki ƙara haɗa ɗan sunna da shege, tsintacciyar mage wadda bata mage, akan me? Kedai da kika ɗakkoshi kikaga zaki iya se kije kiyi, kekaɗai ne ɗanki amma ni wannan yaron ba ɗana bane"
Nan da nan ran Jidda ya ɓaci, kawai ta durƙusa a gurin fashe da kuka, da yake ita bata da baki sosai, Yusuf yazo ya rungumeta yai shiru yana sake juya kalmar shege a ransa.
Salim ya ɗau dutse da nufin ya jefi Yusuf, amma ya samu Jidda a gadon baya, karo na farko da Yusuf ya harziƙa, beyi wata wata ba yai sama da Salim ya sake shi a kwata.
Nan babar Yusuf ta gigice ta biyo Yusuf zata daka, dai dai lokacin motar Bashir ta shigo layin, take yayi parking ya fito yace "ke lafiya zaki dakarmin ɗa? Ke kuma Umman Yusuf meya sameki haka kike kuka?"
Aikuwa ba tayi nauyin baki ba ta gaya masa komai, nan ya fara sirfa bala'i, yace "na lura mutanen nan bakwasan zaman lafiya, wallahi duk wanda ya kuma kiran ɗana da shege sena ɗaure mutum, kai kuma Yusuf duk yaran da ya kuma gayamaka haka, ko ya dakeka baka zanemin shi ba, ni zan zaneka da kaina, ba babarka zaka dinga shigarwa faɗa ba, duk wanda yayi maka ka masa duka ka lallasan mon yaro, in yaso akawomin ƙararaka zan bada haƙuri "
Tun daga nan Yara suka ɗan saurarawa Yusuf, saboda babansa mutum ne me raha da barkwanci amma be iya fushi ba da tashin hankali, Yusuf ya cigaba da tasowa, tun be gane kalmar da ake gaya masa ba harya gane ma'anarta, baze manta ranar wata Juma'a ba, wadda itace ranar da ya gane mariƙansa basu suja haife shi ba, ya ɗauka ana gayamasa shegene kawai dan a zageshi, amma ya gane basu suka haife shiba.
Ƙanwar Bashir, me suna Balaraba ta haihu, saboda gudun magana yasa Jidda ta shirya, ta shirya ɗanta tsaf dasu, kai kace wata matar hamshaƙin attajirice, saboda Bashir baya wasa gurin kula da gidansa, daga ci har sha da sutura, baya wasa gurin basu, shiyasa kullum iyalinsa suke tsaf dasu.
Suka shirya tun safe Bashir ya tafi kaisu gidan suna, a ƙofar gidan yayi parking ya kalli Jidda yace "kin san Allah, ba dan kin matsa ba da bazakuzo sunan nan ba, ke kin damu Yusuf yasan 'yan uwana, saboda halin Rayuwa ni kuma nasan babu wani amfani da hakan zeyi, dan haka idan kimga ba hali ki samu abun hawa kukoma gida, idan kinga zasuyi muku cin mutunci ki kirani a waya ko ku koma gida kinji ko? "
Jidda ta jinjina kai, Bashir yace "ki kularmin da kanki da Yarona, ya kalli Yusuf yace " My boy, zaka shiga cikin yara, bance ka saurarawa duk wanda ya taɓamin kai ba kaji ko? "
Yusuf yayi murmushi ya sunkuyar da kai, Bashir ya sumbaci goshinsa, sannan suka shiga gidan, suna shiga basu samu wata karɓar arziki ba, sema bimta da aka dingayi da kallo a nayiwa zanin jikinta kuɗi, da kayan jikin Yusuf.
Suka dinga zage zagen su, suna faɗar baƙaƙen maganganu, Jidda ta tashi da nufin ta taya su aiki, suka dinga caccakarta kamar zasu cinye ta ɗanya, suna mata gori suna zaginta.
Ta tashi ta koma gefe, ta ɗau Yusuf ta ɗora akan cinyarta, tana share hawaye, Yusuf ya kwanta a jikinta yayi lamo yana jin yadda take kuka, har kusan ƙarfe ɗaya ana ta rabon Abinci, amma aka hanata ita da Yusuf, ga lokacin da shabiyu na rana tayi, take bawa Yusuf abinci, se can wata mata daga maƙotan Balaraba ce ta kawo musu Abinci, dambun shinkafa aka kawo musu, sedai Yusuf baya cin dambu, se Jidda ta aiki wani yaro tace
"Dan Allah jeka gurin da ake rabon Abinci, kace a baka waina zan bawa yarone, in basu baka ba kazo ka karɓi kuɗi ka siyomin wani abun in bashi"
Yaron yana zuwa yace a bashi waina, wata ta kalle shi tace "waye yace a baka"?
Ya nuno Umman Yusuf yace "gata can, ita ce tace a bata zata bawa yaronta, wai baya cin dambu"
Asma'u tace "iyeee ina abun yake inji Mayya, saboda samun guri har wani zaɓen Abinci yaron yake yi, lallai abunda mamaki samun guri, dama ɗan uwanmu ne ya haife shi da sauƙi, amma kin sashi a gaba anje gidan marayu an ɗakko shege se wahala yake akanku, ke gaki juya shi gashi shege ba dangin iya babu na baba an samu guri se iskanci ake, kina ci kina ƙiba kina narka kashi, gefe shegen daba'a san asalinsa ba ma yana cin nasa rabon, kin kanainaye mana ɗan uwa kin hanashi yayi mana komai "
Balaraba tace " wai lafiya kike wannan kwarmaton haka? "
" inafa lafiya, za'amin iyayi da feleƙe wai wannan shegen yaron sun samun an basu Abinci, hadda turowa wai a canza masa bayacin dambu, saboda samun guri wai Abincin ma seya zaɓa, dan ubanka da a gidan Marayun ka taso, naga uban da zakawa sanaben baka cin kaza, kai kaza kake ci"
Jidda ta toshe baki ta fashe da kuka, a nan Yusuf ya fara fuskantar ashe ba Babansa ne ya haifeshi ba, idan be manta ba a makarantar su sun taɓa zuwa gidan marayu, akace musu wanda iyayensu suka yadda sune, kokuma wanda iyayen suka rasu, wato kenan shima yadda shi akayi, ko iyayensa na asali sun mutu.
Jidda ta tashi, ta kama hannun Yusuf ta baro gidan nan, kafin ta fito ma shaddarta milk ta sha aiki, suka watsa mata dagwalon kayan miya, haka suka tafi tana tafe a hanya tana kuka,
Yusuf yace "Umman Yusuf kiyi haƙuri, kidena kuka Allah yana son masu haƙuri, haka ya sayyadina yake gayamin"
Amma ta kasa dena kukan nan, ta rasa wani abu tayiwa dangin Bashir suka tsaneta haka, banda hauka ina laifin Yusuf a wannan al'amarin? Me yayi musu? Shida yake yaro ƙarami, take tayi wani tunani ita yanzu daba cikakkiyar lafiya ba, idan ta mutu waye ze kular mata dashi, ita dai Allah ya jarrabeta da son Yaron nan, tasan babu matar da zata kulamata da ɗanta tsakani da Allah haka.
Gaba ɗaya wunin ranar haka suka yi shi babu daɗi.
Bashir na dawowa ta dake ta maze, ta ɓoye duk wata damuwa da take ciki, ta saki fuskarta, suka ci Abinci ya rungume Yusuf yana faɗin
"ɗan Babansa, meyafaru ne? You look somehow disturbed, meyafaru ne gayamin"
Yusuf yace "am ko Abba, ba abunda yake damuna, munje gurin suna amma ba'ani Babyn na ɗauka ba"
Bashir yace "Subhanallah, to shikenan rabu dasu, da kaina zan kaika a baka ka ɗauka tunda kana so"
Yusuf yace "to Abba nagode, nima Allah yasa Ummana ta haifi Baby, in dinga kular mata da ita ina goya ta"
Bashir yace "Ameen ya Allah yarona, waini idan ka girma me kake son ka zama ne?"
"Daddy doctor nake son zama, surgeon doctor"
"Wow that's good my Boy, Allah ya bani rai da lafiya inga burinka ya cika Yusufana, kenan baza'abi sahun Abba ba a kare dukiya da rayukan al'umma ba?"
"Ina so Daddy, amma bana son in dinga cin hanci, ustaz ya cemin ba kyau"
Bashir yayi murmushi yace "babu aikin daba'a cin hanci Mu Son, nima na gashi police bane, kaga ina irin wannan?"
Yusuf yace "A'a".
"To ko duk 'yan sanda zasu lalace, amma kai ka tsaya kai da fata akan gaskiya idan wasu basu yi nasara ba, wasu zasu samu sassauci a sanadin ka, dan haka' yan sanda ba 'yan rashawa bane kaji Masoyina"
Jidda tace "Abba, ko kunya ba kaji kake cewa ɗan fari masoyinka ko? Allah yasa tsofaffi su jika, kasha zazzaga"
Bashir yace "sedai suyi su gaji, amma ina son masoyin nan nawa, inajinsa a zuciyata, idan na kalle shi ina samun farinciki da nutsuwa, nasan ko bayan raina akwai amfanin da zewa al'umma, ɗan waliyin Allah me halin sufaye"
Jidda tace "ina ganin ikon Allah, kabari a faɗa mana kawai kasa shi a gaba kana ta koɗashi, Taso muje in maka addu'a in kwantar da kai"
Bashir yace "ke yanzu me kike inba shagwaɓashi ba, baccin ma sekin kaishi, ƙyalemin yarona ya gama jin ɗumina tukuna"
"Ka maida shi ciki mana ƙarewar soyayya"
Sukayi dariya gaba ɗaya.
Yusuf yace "Abbana ɗan aljanna, ina sonka da kai da Umman Yusuf, Allah yasa ku a Aljanna"
"Ameen ya Allah, ɗa ɗaya tamkar da goma"
Suka cigaba da hirarsu cikin so da ƙaunar juna, can Yusuf yayi shiru yana tunani, Bashir yace "ɗan waliyin Allah, me kake tunani ne? Kowani abun akayi maka da kuka fita, gayamin ko waye inci ƙaniyarsa"
"Abba meyasa ka ɗakkoni daga gidan marayu? .......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
100_101
Tsit sukayi gaba ɗaya suka shiga kallon kallo ita da Bashir, Bashir yace
"Yusuf, waye yace maka a gidan marayu kake? Wani mara hankalin me ya faɗi haka?"
Yusuf yace "Yaya Asma'au naji tana faɗa, Mamansu Amira, kuma rannan dana tambaya ance mana a makaranta wanda suke gidan marayu basu da iyaye, tsintarsu akayi an jefar dasu"
Bashir a fusace yace "ƙarya take yi kaji ko, ba wani gidan marayu da aka ɗakkoka, ƙarya take nina haifeka"
Jidda tace "Abba ya zakace masa ƙarya take, babba ce fa ba haka yakamata ka faɗa ba, tunda yarone bekamata kace masa babba kamar wannan tana ƙaryaba, ka gaya masa wani abun dai"
Bashir yace "idan bance ƙarya take ba me zance? Ko so kike a sawa ɗana wani tunani na daban a zuciyarsa, nina haifi ɗana duk wadda ta kuma gayamaka haka kace Nine nan babanka, in ba haka su gayamaka gidan marayun dana ɗakko ka, kuma duk wanda ya kuma gayamaka haka kazo ka sameni ka gayamin, kaga yadda zan da mutum"
Ran Bashir ya ɓaci sosai ya dinga faɗa yana mita, dan ba ƙaramin jin haushi yayi ba, abun yana damunsa yadda ake aibata masa yaro, yaron da yake jin sonsa a cikin jikinsa
Bashir yace "Ke yanzu a gabanki ake gayawa ɗana haka, amma ba kice komai ba, kuma ni baki gayamin ba balle in ɗau mataki, ɗana me haƙuri da hazaƙa amma a fara cusa masa tunani da ƙuruciyarsa, bazan lamunta ba Wallahi tabbas duk wanda ya kuma wannan gangancin zanyi maganinsa"
Ya tashi Fuuu ya ɗau Yusuf, ya kai shi ɗakinsa ya kwantar da shi, ya zauna yaita masa addu'a yana shafa kansa me ɗauke da tarin suma me kyau, har bacci ya kwashi Yusuf, dukda zuciyarsa na cike da zullumi da tunani iri a kan maganganun da mutane ke gayamasa.
Haka Rayuwa ta cigaba da gudana, Yusuf yana cikin gata da jin daɗi dai dai ɗan talaka me rufin Asiri, Yusuf akwai tsanani biyayya da haƙuri, gashi tun yana yaro yana da ilimi sosai, gashi mahaddacin Al'qur'ani ne.
Bashir ɗan Sanda ne nagari, mutane sukance masa cinnaka ba ka san na gida ba, ko suce masa murmushin talaka, saboda gaskiya da riƙon Amanarsa, komarli kuɗinka da Arzikinka baze saurara maka ba idan baka da gaskiya, sannan umarni in dai na san zuciya ne, ba daga sama ba koda gurin uban waye baze karɓi umarnin san zuciya ba, aikinsa kawai yake bilhaƙƙi, ba son zuciya da cin Amanar ƙasa,shiyasa talakawa ke masa addu'a suke ƙaunarsa.
Shekarar Yusuf tara a duniya, Babansa Bashir akayi masa kiran gaggawa yayi tafiya Lagos a hanya 'yan fashi suka kashe shi, shi da uban gidansa.
Umman Yusuf da Yusuf sunji mutuwar nan, sun kaɗu dajin mutuwar nan, sunyi kuka, sunyi kuka dan sunsan sunyi rashin babban bangon jingina, Bashir mutum ne nagari, dukda ɗan takun saƙar dake tsakaninsa da maƙotansa akan Yusuf, amma sunji mutuwarsa, mutum ne me barkwanci da raha, ga kyauta da girmama mutane, mafi akasari in kaga anyi faɗa dashi to haƙƙin wani za'a take, shi be fiye daɗa akan kansa dan an masa wani abuba, sedai in an taɓa Yusuf ko Jidda, ko an danne haƙƙin wani, dan haka da talakawa masoyansa, da iyalansa da jama'ar unguwa sunji mutuwarsa sosai, hatta su kansu rundunar tsaron sun san sunyi rashin ma'aikaci.
Bayan an gama zaman makoki maƙota suka farayi da Jidda, wai saga yadda zata yi, ta miƙe ƙafa komai sedai miji yayi mata, hatta slifas na tsakar gida Bashir be yadda ta siya ba shiyake siyan komai, yanzu tunda ya mutu a ga yadda zata yi, gata ga yaron da ba'a san wace tayi cikin shege ta yar ba, sukaje suka ɗakko, yanzu ai taje ta maida ɗan da suka ɗakko ai.
Jidda bata da matemaki se Allah, rayuwa ta fara musu zafi, saboda bata da hanyar samun kuɗi, ta fara tunanin sana'ar da zata yi danta samu suci Abinci, kar ɗanta yasha wahalar rayuwa.
Manyan 'yan sanda suka shiga yi mata romon baka, akan cewar zasu shiga su fita a samu haƙƙinsa ya fita, duk da jajircewar Bashir da wahalar da yayiwa Ƙasa, babu wanda ya kuma bi ta kan iyalansa, haka Umman Yusuf ta shiga faɗi tashin yadda zata yi domin ganin basu tagayyara ba, amma abun mamakin, komai ta kasa na siyarwa se maƙotanta suƙi siya, ko kuma su karɓe bashi su barta, sunaji suna gani haka ta cire Yusuf daga makarantar kuɗi ta maida shi ta gwamnati, dama ya gama primary secondary ze shiga, wasu lokutan har Abinci ma se tayi fama sannan suke iyaci, mutanen da Bashir ya dinga tallafawa babu wanda ya kuma bi takansu, dama ba'a batun danginsa tunda ba ƙaunarsu suke ba, haka Umman Yusuf ta samu Nanny a wata makaranta da ƙyar, ta kaɗa ta raya su ɗauketa aiki, tana da diploma amma suka ƙi, waisu masu degree suke ɗauka, sedai su bata Nanny, haka ta karɓi aikin Nanny take yi, tana zama ta zubda hawaye idan ta tuna Bashir, wata wahalar duk bata santa ba se daga baya, dama 'yan uwanta duk kusan matane, kuma uba ɗaya suke ba uwa ɗaya ba, kuma mahaifim nasu ya rasu, gashi dama suma duk fama suke da kansu, talakawa suke Aure, dama ita suke raɓa su samu wani abun, shima suna yi suna mata hassadar tana auren me rufin Asiri, tunda aka gama zaman makoki babu wanda ya sake ya waiwayarta.
A hakan ana wannan faman, amma Umman Yusuf bata yadda Yusuf ya fita da mummunar kama ba, ko yayi mummunar cima ba, ta yadda ta zauna da yunwa, Yusuf yaci.
Ga aikin Nanny ɗin nan babu wata riba, se zunzurutun wahala, ga wulaƙanci daga malamai, yaran da iyayen su dukda wannan ƙoƙarin da take yi ba'a gani.
Yusuf idan yaga tayi shiru se yace "Ummana kiyi haƙuri kinji, nima bana son wannan aikin da kikeyi, nima zan duba sana'ar da zan iya in dinga temaka miki, ki bar wannan aikin"
Umman Yusuf tace "A'a ban yadda ba, yarone kai ƙarami kamata yayi ka maida hankali akan karatunka, idan kasan daɗin kuɗi bazaka maida hankali ba"
Fafur ta hana shi neman kuɗi, idan bashi da littafi yana son ya siya baze tambayeta ba, sedai ɗan ashirin ɗin motar da take bashi, da kuɗin break ɗinsa haka ze tafiyar ƙafa, dan ya rage ya siya, karya tambayeta yasan bata dashi, dubu goman da'ake bata na aikin bata zuwa ko ina.
Watarana Ummansa ta tashi babu lafiya, kusan sati biyu ba taje makaranta ba, gashi babu kuɗin magani, ko zuwa Asibiti tana ta fama da Asma, dan haka bata sani ba Yusuf yaje gidan Yayan Bashir, Ɗanlami yaje ya gaya masa amma yayi masa kaca kaca ya kore shi, yace baze taimaka musu ba, bayan zagi da cin mutunci da yayiwa Yusuf da gorin aishi ba ɗan ɗanuwansu bane, tun daga nan Yusuf ya ƙuduri aniyar kome ze samesu, baze ƙara neman taimako a gurin wani ba.
Haka Yusuf ya samu guri a hanya ya zauna yayi kuka, yayi kuka yai me isarsa sannan ya koma gida haka ya zuba ido, Jidda tasha jiki ta rame tayi wani iri, tana ɗanji sauƙi ta koma makaranta suka bata dubu huɗu, suka ce sun koreta, dukda sun san bata da lafiya, haka suka koma gida suka tsuguna, Umman Yusuf ta rasa inda zata saka ranta, ga larura ga babu ta musu katutu, kuɗin da aka bata dubu huɗun nan baze sai musu ishashsen Abinci ba, balle ta sai magani, maƙota babu me taimakonta dako ƙwayar hatsi, sedai in ta fito aita mata habaici ana yada mata magana.
Abunda bata taɓayi ba, ta shiga ɗibar zannunwanta tana siyarwa, dan a lokacin Yusuf kansa bashi da lafiya, dauriya kawai yake yi, tun yana daurewa harta koma ta kwanta babu lafiya, shima ya kwanta ba lafiya, dan komai se tayi masa saboda zafin ciwo.
Haka ta kwashi flasanta da Bashir ne mafi akasari yake sauya mata, ta kai kasuwa akayi musu sayen wulaƙanci, ta karɓo kuɗin ta ɗau Yusuf zuwa Asibiti, suna zuwa aka basu gado, Ulcer ta masa mummunan kamu, ga typhoid da malaria, ita bata ta kanta ta lafiyar Yusuf take, Bill ɗinsu kusan dubu goma sha huɗu dukda Asibitin gwamnati ne, haka ta zare ta biya, taje pharmacy ta karɓo magani zata koma ward, 'yan sanda suka kawo wasu sunyi accident.
Wani ya kalleta yace "wannan kamar matar Bashir"
Ta kalle shi tace "eh nice"
Yace "Ai na sanki, ai tare mukayi aiki da Bashir, baki ganeni ba? Isyaku ne fa, amma yana ganki haka, baki da lafiya ne?"
Tace "A' a Ɗanmu ne ba lafiya, na kawo shi nan aka bamu gado, an kaantar dashi"
Mutumin yace "A'a, naga da kamar private Hospital kuke zuwa? Ya zaki kawo yaranku nan gurin? Ke kanki kamar baki da lafiya fa"
Haɗe rai tayi, dan mutumin nan ya fara isarta tace "lafiyata ƙalau ni"
Yace "yi haƙuri, naga kamar kin fara hasala, amma ai naga kuɗinsa ya fito wata biyu baya, amma ya zan ganku haka, kuma kuɗin nasa dayawa"
Ta kalle shi da sauri tace "Yaushe kuɗin nasa suka fito?"
"Kina nufin baki sani ba? To 'yan uwansa da wasu' yan sanda sun haɗa kai sun karɓi kuɗinsu, ai na zata an baku naku?"
Da gudu ta wuce ɗakin da Yusuf yake kwance, tana kuka yanzu kuɗin mijinta sun fito amma sun karɓa sun cinye, tasan babu yadda za'ayi ko ficika su bata, ga tarin wahala da suke ciki, amma ba imani suka hanata kowani kasone a ciki, haka taje ta zaunatayi kuka kamar ba gobe.
Kwanansu takwas a Asibiti aka sallami Yusuf suka koma gida, ta ƙarasa jinyarsa a gida ya koma makaranta, tayi tayi makarantar nan da take Nanny su maida ta bakin aikinta amma suka ƙi, haka ta haƙura duk yadda ta kai ga danne zuciyarta, seda tayiwa dangin mijinta Allah ya isa, akan haƙƙin mijinta da suka danne suka cinye sukaɗai.
A ɓoye wani maƙocin su yaga yadda taketa wahala, yai mata hanya gurin wani ɗan siyasa a temaka mata, amma mutumin nan ya nuna mata halin bunsurai, dan haka bata kuma zuwa ba, itace wankau, itace aikatau na biki kona taro, Yusuf yana Sss1 aka tafi da shi Quiz Abuja na akan harkar lissafi, aikuwa Yusuf yazo na ɗaya aka bashi kyautar dubu ɗari biyar, malamansu suma suka cicciri nasu dana babu gaira ba dalili, ƙarshe dubu ɗari biyu aka bashi.
Umma tayi murna da samun kuɗin nan, Yusuf yace "Umma duk an kwashe fiye da rabin kuɗin, kinga da mun samu da yawa, dubu ɗari biyar fa aka bani"
Umma tace "Yusuf ina lefi, da ina muka samu wannan ɗinma? Ai Alhamdilillah mai dai Allah yayi maka albarka, ya ƙara hasken makaranta ya jiƙan Abbanka'
Yusuf yace " Ameen Umma, ga kuɗin nan, wace sana'a kike ganin zamu fara ne? "
Umma tace " Yusuf ka maida hankali a karatunka, sannan kuɗin nan ka ɗau abunda zaka ɗauka, semu yi tunanin abunyi"
"haba Umma, na girma fa ki bari in fara sana'a mana, kuma ni ba abunda zan ɗauka a kuɗin nan, muyi tunanin abunyi"
"A'a Yusuf, dole ka sai sutura, zan shiga kasuwa in samo maka yaduka, da takalama, dako ɗan agogone, ka fara zama saurayi, ina kallo kayanka duk sun mutu, ba yadda zanyi ne kawai"
Yusuf yace "Umma karkice zaki kashemin kuɗi dayawa, ina sa ran zamu kuma zuwa wani competition ɗin, kema ki sai wani abu a ciki, nace ko injin markaɗe zamu siya, se a ajiye shi a ƙofar gida idan na dawo in dinga zama"
Aikuwa Umma ta yadda da shawarar Yusuf, suka ajiye kuɗi basu taɓa ba tukuna, suna shirin siyan injin markaɗe.
Yusuf ya dawo daga makaranta sukaje kasuwa suja siyo inji, akazo aka saita komai suka sai kayan Abinci da sauran buƙatu.
Da safe idan Yusuf ya tafi makaranta, Ummace take markaɗen a cikin gida, idan ya dawo ya fito dashi waje yayi zuwa magariba, se maƙota suka fara surtu wai ana cika musu kunne, bayan a ƙarshen kayanma akwai babbn gurin niƙa, da suke wuni guda niƙa, amma suka zo sukace wai suna takura musu da ƙarar inji.
Duk shiru na Yusuf ya dinga faɗa, yace "wallahi babu wanda ya isa ya hanamu sana'a, me kuke so muyi ƙasa zamu ci kome, yanzu da wani fitinannen na zama sekunfi kowa tsinemin, ba irin wahalar da bamu shaba, kuma mun kafa sana'a kuce semun ɗauke baze yuwuwa ba"
Maƙwabcinsu Na jikin gidansu yace "kai dalla har kana da bakin magana, banza tsintacce wanda ba'asan asalinsa ba, karuwa tayi ciki ta haife ta yar, an tsintoka an rufa maka Asiri, amma kazo kanawa mutane Iskanci a gari"
Maganar nan tayiwa Yusuf ciwo, yaji haushin maganar nan, yaji kamar ya soka masa mashi a zuciyarsa, amma ya dake yace "idanma hakan akayi, inma ba hakan bane, ba a kaina aka fara ba, kuma ba kaina za'a ƙare ba"
Umma dake cikin gida, tazo ta janye hannun Yusuf tana kuka suka koma cikin gida tace "Yusuf mi haƙura da markaɗen nan kawai, bazan iya jure ana cimim zarafinka ba, bazan iya ba"
Ya goge mata hawaye yace "Umma idan mun dena Meza muci, kidena damuwa ni baya damuna, saboda nasan bani da wasu iyaye inba Ummana ba, da Abbana Allah ya jiƙansa, ki rabu dasu kawai, komai lokacine wataran in ance suyi min ba zasuyi ba"
Haka yaita rarrashinta yana bata haƙuri, washegari ya tafi makaranta, bayan ya dawo tun daga soro ya fara jiyo kukan ummansa tana "da ikon Allah se Allah yasakamin abunda kukayi min, yadda kukayi nufin tozartani Allah yasakamin, wallahi ɗanlami da kai da Ballo da 'yan uwanka bazan yafe muku zaluncin da kukamin ba, wallahi Allah ya isa"
Yusuf ya shigavda sauri, yaje ya sameta a dirƙushe tana kuka, ga su Yaya ɗanlami da wasu mutane.
Yusuf yace "Umman Yusuf, lafiya kuwa me suke mana a gida? Me kuma mukayi musu?"
Yaya Bello yace "kai dalla tafi can banza, meye naka a ciki wani wai me muke muku a gida, inane gidan naku meye haɗakinka da Bashir,? Ɗan tsintuwane fa kawai amma ko taku baka dashi a abunda ya bari, seka bazama neman karuwar da ta haifeka ta yasarka ta nuna maka ubanka"
Cikin kuka Umma tace "Wallahi karka ƙara shegantamin ɗa, Yusuf ba karuwa ce ta haife shi ba, ɗana ne, kuma ɗan sunnane duk Wanda ya kuma shegantashi ban yafe ba"
Yusuf bece komai ba, yaje ya durƙusa ya ɗago Umman dake kuka yace "Umma meyafaru ne wai?"
"Yusuf kaga, bayan sunje sun karɓe haƙƙin Babanka sun cinye, babu wanda ya waiwaye mu, sun saida gidan da muke ciki, an bamu notice, wai bazasu bamu gadon komai na Bashir ba, Yusuf an mana adalci kenan? Yanzu sun kyauta kenan? Yusuf ynzu kana ganin da Bashir ne a raye ze musu haka? "
Yusuf ya rumgumeta ganin yadda jikinta har rawa yake tana kuka, gata ba cikakkiyar lafiya ba yace "Ummana kiyi haƙuri, ai Allah baya bacci ni idan bani da gadonsa aike matarsa ce yakamata su baki"
"Yusuf gidan nanfa nawane nida kai, har rubutu Bashir yayi ya bari kafin ya rasu, kuma Bello ya sani amma shine suka saida gidan, idan na tashi daga nan mu koma ina? Me nake dashi idan na bar nan?"
Ɗanlami yace "koma gidan ubanwa zaki ki tafi, ai dama ba gidan ubanki baane, seki koma gidan ƙasar da ubanki ya mutu ya bari, shi kuma ya koma gidan ajiye shegu da kuka ɗakko shi"
"Wallahi se nayi shari'a daku, se an ƙwatar mana haƙƙinmu"
"Haba Umman Yusuf, aishi Allah baya bacci, kuma Allah na kowane baya barin zalunci, menene gida idan sunyi haka dansu wulaƙantamu Allah baze basu dama ba, ki kwantar da hankalinki mun rasa Abba ma, kuma dangana mukayi mukai haƙuri, dan haka gida ɗazune, in da rai da lafiya insha Allah sena gina miki gida na ban mamaki, gidan a wanke hannu kafin a taɓa "
Yai maganar yana goge mata hawayen fuskarta, yana murmushi dukda Shima fuskarsa sharkaf take da hawaye.
Murmushi tayi na ƙarfin hali tace " na dena Yusuf, na barwa Allah nasam baze wulaƙantamu ba"
Saboda keta haddi da cin mutunci, tana zaune wai za'a wuce da masu siuen gida har ɗakin baccinta a duba, Yusuf ya miƙe ya tare ƙofar yace "dul abunda zakumin zan iya jurewa, amma wallahi duk garin nan babu mecin mutuncin uwata in ƙyaleshi, ɗakin baccinta gurin sirrinta ne, dan haka babu me shiga, jibi in Allah ya kaimu zamu tashi mu bar muku gidan, ba zamuyi shari'a daku ba, amma Allah ya biwa Ummana haƙƙinta"
Bello yace "kaikuma kai a wa? Gayyar tsiya arna a idi? Kama je kayi shari'ar damu mana, dalla gafara nan a duba ɗaki sirrin banza sirrin wofi"
"Wallahi taku ɗaya ka ƙara daga inda kake, kai yunƙurin shiga ɗakin nan idan na ɗaga ka se nayi jifa da kai ta katangar nan wallahi"
Tabbas yadda ƙirar jikin Yusuf take, dukda ba wani girma yayi ba tsaf ze iya aikatawa, haka suka haƙura suka tafi suka ƙyalesu.
Umman Yusuf ta cigaba tana cewa "Yusuf Allah yasaka mana, kana gani ana cewa an kashe Abbanka, aka dawo da motarsa suka ɗauka suka siyar, banyi magana ba, kuɗinsa suka fito suka wuce gaba suka karɓe suka cinye, se a bakin jama'a naji labarin kuɗin sun fito, duk 'yan kadarorin daya bari sun siyar, kuma suna kallon wahalar da nake yi, babu tausayi babu imani a tare da su, ya suke so muyi da ranmu Yusuf, sun cutar damu"
Tai maganar cikin kuka da sheshsheƙa, Yusuf yace "Umma kidena kukan nan, zanje a samo me siyan injin markaɗen nan, da ɗan cinikin da mukayi mu samu gida ko ƙaramine mu kama"
Jinjina masa kai kawai tayi, tana share Hawaye, Yusuf yace "Umma wao ya akayi kika san haƙƙin Abba ya fito sun cinye?"
Ta share hawayenta, ta gayamasa yadda suka yi da ɗan sandan nan, Yusuf yace "Umma tunda ya gayamiki haka, kuma beyi ƙoƙarin taimakonmu ba to tabbas dashi aka ci kuɗin nan, dan babu yadda za'ayi ba'aci kuɗi dashi ba yasan anyi, abunda nakeso dake shine kiyi haƙuri, Allah baya bacci, ki bar batun kaisu ƙara, mu barwa Allah, Insha Allah Ummana wataran zaki yi dariya zamuji daɗi, kidena kuka Umman Yusuf "
Yana maganar yana goge mata hawaye.
Yusuf kai inji kasuwa ya siyar, sedai babu wata daraja, saboda anga a Matse suke, suka har haɗa suka bada rabin kuɗin gida, suka wani ƙaramin gida haya, suka koma ciki suka zauna.
Yusuf ya kusa shiga aji shida ma sakandire, dan haka yasan dole za'a buƙaci kuɗi a hannun su, kuma yasan Umman bata dashi, ga kuɗin hannunsu babu, ɗan Abincin da suka koma gida dashi babu, ga babu jarin sana'a, kuma kuɗin haya rabi suka bayar .
Yazamana Yusuf ya fara tunanin mafita, ana idar da sallar Asuba, yake zuwa ya karɓi hayar kura yayi ga ruwa, ya tattara abunda ya samu, ya dawo gida ya saimusu abun karyawa, Umma ta matsa se taji inda ya samo kuɗi, yayi mata bayani aiko se kuka tace "Allah ya jiƙan Bashir, da yana raye nasan babu yadda za'ayi ya bar abun ƙaunarsa yayi wannan wahalar, Kayi haƙuri Yusuf nakasa baka kulawar data dace"
"Haba Ummana, aini na wuce lokacin da zaki nemo ki bani, sedai in nema in baki, dan Allah kidena kukan nan, kidena wannan tunanin please"
Haka rayuwa ta cigaba da ja, Yusuf sana'a iri iri, yayi wannan yayi waccan komai ƙasƙancinta kuwa, harya ɗan tarawa Ummansa jarin saida man ƙuli da manja a cikin gida, a haka suka tara cikon kuɗin haya, suka biya suka ɗan samu sassauci gurin samun Abincin da zasu ci.
Dayake da suka tashi ba nisa sukayi da unguwar tasu ba, dan haka wani lokacin idan ya turo kurar ruwa, yakan haɗu da maƙotansu na da, se yaji suna "Ohh rayuwa juyi juyi, wai yau ɗangata ke tura kurar ruwa, dama shiya dace dashi tunda dai ba'a gatan aka haife shi ba"
Yusuf baya tankawa, shi dai babban burinsa asirinsu ya rufu shi da Ummansa.
Allah ya temake shi yaci qualifying, dan haka kuɗin Neco kawai ya biya, da na Jamb dayake Asusu sukayi shida Umman, suke jefa abunda ya samu saboda hidimar karatunsa.
Yusuf ya zana jarrabawa gaba ɗaya, Waec, Neco, da kuma Jamb, dayake Allah maji roƙon bawane, kuma kullum cikin yi masa addu'a Umma take, Se Allah yasa ya tsallake gaba ɗaya jarabbawarsa, ya samj maki me kayu da ake nema, dan haka har admission ya samu a jami'a, sedai fannin daya ɗauka na medicine, kuɗinsa ya kai kusan naira dubu sittin ta wannan lokacin, wadda kuma kuɗi ce masu yawa a wannan zamanin, Nanfa murnar Umma ta koma ciki, ina zata samu wannan kuɗin? Me take dashi wanda zata yi ta cika burin ɗanta? Burin da dashi Abbansa ya rasu, Yusuf yayi karatu ya amfani al'umma......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
102_103
Abu ya zamana ga ƙoshi ga kwanan Yunwa, ga bikin zuwa babu zanin ɗaurawa, course me wahalar samu gashi Allah yabawa Yusuf amma babu hanyar yinsa.
Yusuf kam ya fidda rao, dukda ƙaunar karatun da yake a ransa, amma babu yadda iya, tunda yasan basu dashi.
Allah sarki, Jidda ta damu kanta, tasan ba lallai ya kuma samun wannan damar ba, yana son karatun sosai, idan be samu ba tasan abun ze dameshi, amma baze nuna mata ba, ta duƙufa addu'a, ta nayi tana rarrashin Yusuf akan idan karatun nan be samuba, su barwa Allah, Allah ya kawo masu mafita.
Sam Yusuf baya nuna mata da ya damu lallai se yayi karatun, 'yan unguwa suma ganin yadda suke fama da rayuwarsu, amma babu me tallafarsu se Allah.
katsam aka kira shi a waya akace gwamnati ta bashi scholarship, an fidda gwarazan shekara na makarantun kimiyya da fasaha, kuma Sunan Yusuf ya fito ya samu.
Shi Yusuf jin abun ya dingayi kamar almara, banda iko na ubangiji wa zeyi wannan hukuncin haka? Umma kamar ta zuba ruwa a ƙaaa ta sha dan farinciki, tayi murna ta godewa Allah, babu zato babu tsammani dama tazo musu ba tare da wata wahala ba.
Akayi shirye shiryen komai ya fara karatu, sedai wannan karatun karatune me wahalar gaske, ba karatun ne matsalar Yusuf ba sedai kuɗin transport, na handout excursions, practicals, field trips, kullum cikikn kawo kawo ake, gashi baya samun damar yin 'yan sana' oinsa saboda zaman makaranta.
Dama a unguwa babu ruwansa da kowa, ko abokai bashi da su saboda gudun gori da wulaƙancin mutane, Amma dukda haka be tsira ba, aita surutu waiya fiue girman kai, daba'a san wayeshi bane shine ze dinga jawa mutane aji, yana wani hura hanci, shi dai shirune nasa, baya tofa komai baaa gaban sa.
Karatu abu fa ya fara gagara, da ƙyar Yusuf ke iya karatun nan, saboda babu, Yusuf gashi ƙwaro na gaske saboda haddar Al'qur'ani babu karatun dake bashi wahala.
Shekararsa biyu yana karatun, akayi zaɓe aka canza gwamnati, ba tausayi ba ragayya ga yaran talakawa gwamnati tace babu kuɗi, bazata iya cigaba da biyawa yaran da aka bawa scholarship kuɗin makaranta ba, wanda yake da hali ya ɗau nauyin kansa.
Yusuf yanaji yana gani ya ajiye karatun medicine ya dawo gida ya zauna, Umma seda tayi kuka, shiko Yusuf akwai dakiya yaita bata haƙuri yace "Umma da bamu san zan fara karatun bama, Allah ya bani dama, yanzu kuma ya ƙwace damarsa, mu ɗauka a ranmu Allah yayi mana wani tanadine wanda yafi wannan karki damu Ummana"
Ita babbr damuwarta kar karatun ya fita daga ransa, yazo ko an samu damar ya ƙiyi takasa cika masa burinsa.
Nanma 'yan unguwa suka ɗau surutu, dan Ya dena zuwa makaranta, baƙaƙen maganganu habaici da zunɗe haka yake ganinsu kala kala, Yusuf ya kan rufe kansa a ɗaki da daddare yayi kuka, yayi kuka har ya gaji ya bawa kansa haƙuri, tun tasowarsa yake fuskantar ƙubalen cin zarafin wai shi bashi da iyaye, a gidan marasa iyaye aka tsinto shi,har yanzu yi ake ba'a fasa ba.
Yusuf ya dawo zaman gida, ya shiga neman yadda zasuyi su rufawa kansu asiri shida Ummansa, a haka wani mutum anan maƙotansu, dan sun ɗanfi wanda suka baro mutunci, ya samowa Yusuf Form na polytechnic, Yusuf yaji daɗi Sosai dan shi yanzu duk abunda yazo masa a rayuwa karɓarsa yake, bashi da wani zaɓi wanda ya wuce hakan, ya sake jamb ya cike Civil engineering a nan polytechnic, aikuwa ya samu ya fara zuwa, cikin ikon Allah sana'ar Ummansa ta mai ta kafu ta karɓu, ana siya sosai, ta nemawa Yusuf gurin koyon sana'a a gurin masu furniture, shima seda ta biya kusan dubu hamsin sannan aka karɓeshi.
Kullum idan ya dawo daga makaranta, se yaje gurin koyon aiki, idan ya tashi ya shiga kasuwa yaga meze samu yayi, saboda baya san ɗorawa Ummansa wahala, sam Yusuf bashi da hutu, a haka ya kammala poly, Umma tace baze tsaya ba, ya nemi Form na D. E ya tafi, shi gaba ɗaya jikinsa ya fara sanyi da harkar karatun nan, ta bashi kuɗi yaje ya karɓo form yayi applying, aikuwa by luck ya samu suka bashi level 2 a university, haka nan yau akwai gobe babu haka rayuwa ta dinga tafiya, a wahalce da ƙyar Yusuf ya kammala karatun nan, aka zo maganar tafiya service, Umma taji bazata iya jure Yusuf ya bar gari ya batta ba.
Haka akayi cuku cuku, Yusuf yayi service ɗinsa a kano, bayan an kammala yazo babu aikin yi, sedai kame kame, ga inda yake koyar aikin kafintan Wasu yarabawa ne, masu muguntar tsiya, ganin yana da saurin ganewa yasa suke masa mugunta, gurin koyarwar.
Zaman haka ba aiki ba sana'a ya ishi Yusuf, sedai 'yan bige bige, amma a hakan idan Ummansa taji tana da kuɗi a jikinta, haka take siya masa kaya masu tsada na sawa, shiyasa bazaka ce suna fama da rayuwa ba.
Rannan yana zaune yana duba wayarsa, yaga wani posting, mutane nata tofa albarkacin bakinsu akan harkar tsaro, sedai babban abunda ya bashi mamaki, be wuce yadda mafi yawa sharhin da akayi, ƙorafine akan jami'an tsaro, seya tuna hirar da suka taɓa yi da Abbansa kafin ya rasu, ya tuna yadda akayi aka haɗa kai aka cinye haƙƙin ummansa, tabbas kamar yadda Abbansa ya faɗa, koda mutum ɗayane yake nagari a cikin 'yan sanda, ko yaya wani ze amfanu dashi, dan haka se yaji yana sh' awar yayi applying shima.
Sun gama cin Abinci shida Ummansa da daddare yace "Umma"
Tace "Na'am yaron kirki"
"Umma wata magana ce dama nazo da ita, so nake in gaji Abbana"
"Kamar yaya kenan?"
"Ɗan sanda nake son zama"
"Kamar yaya Yusuf? Bana son rasaka kamar yadda na rasa Abbanka, dan Allah kabar maganar nan"
"Umma, idan baki amince ba shikenan, amma Umma bakya tunanin da akwai wani tsayayyen ɗan sanda me gaskiya a gurin da an tsaya mana gurin karɓo haƙƙinki, Umma kin san mutane nawane ke shiga garari sakamakon rashin aiki yadda yakamata da wasu maciya amana sukeyi a ƙasar nan? Umma in dai zamu dinga ƙyamar aikin mu dingawa 'yan sanda kuɗin goro to tabbas za' aita cutar mutane, duk abu ba'a rasa na Allah, sedai idan suka yi ƙaranci zalunci ne yake yawaita, Umma idan kika bibiya akwai mata irin irinki wanda aka zalunta, kuma za'a cigaba da yi idan har ba'a ɗau mataki me kyau ba, ina son yin aikin ɗan sanda ne saboda in temaki al'umma, ima son zama ɗan sanda dan in ɗora daga inda mahaifina ya tsaya, dan Allah Umma ki amince, amma in bakya so na haƙura "
Jikinta ne yayi sanyi, ta ɗanyi shiru taga tabbas maganganun Yusuf haka suke, kuma tana da yaƙinin cewa Yusuf mutum ne nagari, abune mawuyaci a haɗa kai dashi a cuci wani.
Ta numfasa sannan tace " Shikenan Yusuf, na amince ubangiji Allah yayi maka jagora, ya goyi bayanka ya kareka a duk inda kake, Allah ya wuce maka gaba a al'amuranka, ina fatan zaka zama mutum nagari me gaskiya da riƙon Amana, Allah yasa a sanadiyar ƙudirinka ya zamana an share hawayen wanda aka zalunta, kayi gaskiya da adalci Yusuf "
Yusuf yayi murmushin jin daɗi da farinciki, yace " Insha Allah Ummana, in Allah ya yadda ba zanyi wani abu wanda ya saɓawa Alƙawarin da mukayi dake ba, Addu'ar ki nake buƙata, Allah ya kauda zuciyata daga aikata duk wani abu da ze saɓawa Allah "
Umma tace "Addu'a ai kullum cikinta nake Yusuf, ina fatan Allah ya tsare, amma bana son ka sha wahala, training ɗin nan nasufa da wuya, karka je su baka wanda bazaka iya ba, Abbanka yana bani labarin wahalar abun nan"
"Haba Umma, sekace wani ragon maza, kin ganina santalelen ƙato dani, se in goya maza goma in gudu dasu a bayan nan nawa"
Umma tai dariya tace "eh lallai, ba shakka naga alama kam"
Nanma Allah ya temake shi ya samu makarantar horar da 'yan sanda, Yusuf yasha wahala ya fuskanci ƙalubale daban daban, a haka harya kammala makarantar nan, sukayi passing out, Allah ya temake shi ya fita da babban rank, sakamakon yayi karatu yana da degree.
Yusuf ya kama aiki, sedai Umma kullum cikin nasiha take, na akan yaji tsoron Allah akan wannan aiki daya fara, cikin ikon Allah yana fara samun salary yazo ya zubewa Umma kuɗin yace "Umman Yusuf, Insha Allah inaji a jikina lokacin da zamu samu sassauci yazo, ga wahalarmu ta wannan watan, na karɓo salary"
Umma tace "Alhamdilillah, dama komai yayi farko zeyi ƙarshe ai, Allah yayi albarka amma ka ɗau kuɗinka, ni duk abunda ka sanmun karɓa zanyi ince Allah yayi albarka"
"Haba Umman Yusuf, wannan nakine halak malak, na bar miki, ba abunda zanyi dasu ni duk abunda kika sanmun a ciki shikenan nagode, ki fara more wahalar da muka sha Umma"
Kawai seta fashe da kuka, Yusuf ya rikice gaba ɗaya yace "subhanallah, Umma laifi nayi mikine? Yi haƙuri dan Allah, ban san zan ɓata miki rai ba"
Ta girgiza kai cikin kuka tace "Tun kana ƙarami Yusuf, naso inyi duk me yuwuwa dan ganin baka gane bamu muka haifeka ba, amma hakan ya gagara, duk yadda muka kai ga ɓoyewa nida Abbanka abu ya gagara, bakin mutane yakasa yin shiru, suka dinga wulaƙantamin kai da maganganu marasa daɗin gaske masu muni, har seda suka saka kasan bani na haifeka ba, amma haka kake min biyayya kamarni na haifeka, A baya nayi kukan Gorin rashin haihuwa, an goran tamin nayi kuka nayi kuka, amma tunda Allah ya bani kai, na dena wannan kukan, nasan ba lallai ɗan dana haifa yayi min biyayyar da kake mun ba Yusuf " ta ƙarasa maganar cikin kuka, Yusuf yaji ta fama masa ciwon dake raɗaɗi a cikin zuciyar sa, yaji kamar ya fashe da kuka, sedai be taɓa gangancin zubda hawayen rashin sanin suwaye iyayensa a gaban Jidda ba, dan idan yayi haka ya zama butulu abun Allah wadai, ya tattara nutsuwarsa ya dake, ya riƙe hannunta yace "wayema yace ba Yusuf ba ɗan Ummansa bane, samun uwa kamar Umman Yusuf me sadaukarwa da juriya a wannan lokacin se anyi tonawar gaske, Wa Yusuf zeso in be so Ummansa ba, waze wa Biyayya idan bebi Ummansa ba, Ummana ina neman Aljannata, duk me neman Aljannarsa Annabi salallahu alaihi wassalam yace yabi Allah da ma'aiki sannan yabi uwa, shiyasa nake bin tawa mahaifiyar domin neman albarka da samun wannan Aljannah, shiyasa nake bin Ummana nasan babi da abun biyanta ladan shayarwarta da ɗawainiyarta, Allah ya haɗamu a Aljanna gaba ɗaya, amma wannan kuɗin na Umman Yusuf ne halak malak, da Yusuf da abunda Yusuf ya mallaka duk na Ummane"
Ta rungume Yusuf ta fashe da kuka, a hankali Yusuf ya lumshe ido yana zubar da nasa hawayen ƙasa ƙasa, dan karta ji yana kuka, ta goge hawayenta tace "Yusuf indai nice, nagode sosai Allah yayi Albarka, amma ka ɗauki kuɗinka, kaje kayi buƙatunka gabanka, sedai ka ɗan sai mana Abinci"
Yusuf yace "Umma, nifa kuɗin nan bazan ciba, ki sanmun na mota zuwa gurin aiki kawai"
"A'a Yusuf, bana son jayayya fa"
Yusuf yace "ni na isa inyi Jayayya dake, tunda kin rasa abunyi dasu bari in baki shawarar yadda za'a kashe, ki rabasu biyu, rabi ki ban abunda zakimin, ki riƙe sauran, rabin idan mun samu kuɗi mudinga ƙarawa a kai, mu nemi fili a wata unguwar, mu fara gini, gara mu koma gidan kanmu "
Umma tace " na daɗe ina wannan tunanin Yusuf, yana da kyau ko fili mu siya, sedai bazan karɓe maka kuɗi duka ba, nasan kana da buƙatu kaima "
Yusuf ya haɗe rai, tace " ya dai naga ɓata rai"
"Umma ni zan baki abu kiƙi karɓa ko? Allah ya jiƙan masoyina, nasan da shine baze min haka ba"
Umma tace "shikenan, naji Allah yayi albarka, Allah ya kareka daga sharrin maƙiya"
Shigar Yusuf aikin ɗan sanda na farin kaya, nan da nan sunansa aka fara saninsa, musamman jin laƙabin sunan mahaifinsa, Yusuf Bashir Maitama, Yusuf akwai ƙwazo akan harkar aiki, baya wasa ba ruwansa da cin hanci ko rashawa shidai aikinsa kawai.
Bayan ya fara aikine ya gano irin cakwakiya da maguɗin dake cikin aikin, da irin tuggu da maƙrƙashiya dake aikin, ga me laifi ƙiri ƙiri kana gani amma saboda yana da wane ko yasan wane, se ace a ƙyaleshi, amma idan aka kamo ɗan malam wane ƙarshe 'yan sanda suna iya ajalinsa, ko ka samu case ka fara aiki a kai, daga sama se a turaka wani gurin a karɓe aikin, ko a ƙirƙiri laifi a ɗorawa wani dan a samu wani abu a hannun sa, da ire iren wannan ha' incin, A haka Yusuf yai tunanin yadda rasuwar mahaifinsa ta kasance, a nan ya gane tabbas set up ne mutuwar mahaifinsa da ubangidansa, sedai bashi da evidence dan in be manta ba, suna kan wani case ne, aka kira shi shida ubangidansa can Lagos, daga tafiyarsu se gawarsu, Yusuf baya son ɗagawa ummansa hankali dan haka be gayamata bata ba, ya bar zancen.
Yusuf ya dage da aikin ginin gidansu, dukda muguntar da'ake masa a gurin koyon aiki, a haka ya iya aikin kafinta, ya kama shago ya zuba yara suke masa aikin yana biyansu.
Duk yadda aka so asa Yusuf a harkar cin hanci amma yaƙi, aka dinga cewa shima tsinannen kafiya da taurin kaine dashi kamar ubansa marigayi, ko talauci ze kasheshi baya karɓar kuɗin rashawa.
Yusuf ya kammal ginin gidansu, da kansa yayi furnitures ya zuba a gidan, kamar gidan wata amarya, gidan yayi kyau hatta kayan sawa seda ya canzawa ummansa kafin su koma gida, ya zuba kayan Abinci rana ɗaya yaje ya ɗakkota ya kawo ta gidan nan, umma sarkin kuka seda tayi kukan nata data saba, yaita rarrashinta, suka kwaso sauran kayan buƙatunsu suka dawo sabon gida, Yusuf ya sai Babur lifan me kyau.
Alhamdilillah rayuwa ta fara yi musu sauƙi, Daidai gwargwado suna hutawa, ga salary ɗinsa ga gurin furnitures, ya hana Umma sana'ar komai, data motsa se yace "Umman Yusuf me kike so, Ummana me za'ayi miki?"
Sam bata da damuwar komai, dama gata ba wani girma tayi ba dan lokacin da Suka tsinci Yusuf ba tafi sha bakwai ba, dan da ƙuruciyarta sosai akayi mata Aure, bayan mutuwar Bashir wasu sun nuna suna sha'awar Auren ta, amma taƙi Aure saboda rayuwar Yusuf, tasan ba lallai a riƙe mata ba.
Babban abunda yake damun Umma da Yusuf shine ko abokan kirki bashi dasu, gashi kamar mace wani lokacin kullum yana naniƙe da ita, da girmansa da komai amma idan zata unguwa, seya bita, ya jirata a waje itakuma ta shiga, ko zata wuni yana gurin a zaune, idan kasuwa ce haka zasu tafi tare, haka idan Asibiti ne, idan ya dawo daga makaranta, idan ba masallaci ba baze je waje ya ɗanyi hira da abokai ba, tayi faɗan harta gaji amma yaƙi denawa, abun da Ummansa bata gane ba shine, shi hana gudun magana ne, ko ace anyi rigima yana gurin ko kuma wani abu ya haɗashi da wani ayi masa gori.
Yanzu gashi ya kammala karatu, ga aikin yi gashi ya zama cikakken namiji amma ko budurwa bata taɓa jin Yusuf yayi ba, to mutumin da bashi da abokai mazama balle wata budurwa, ko a gurin aiki abokinsa ɗaya da yake biyo shi gida shine Abbas, banda wannan Yusuf bashi da wasu Abokai.
Rannan yayi musu Abincin dare, ya zubi suna ci Umma tace "Wai nikam Yusuf, kai ko budurwa baka da ita ne, sa'aninka sun fara Aure, amma kai ko zancen budurwa baka yi, ko dai nice ake ɓoyewa"
Ya ɗan tura baki yace "Umma ni me zanyi da wata budurwa kuma, ni bani da wata budurwa"
"Saboda me baka da budurwa? Se kace ba namiji ba, haka zancigaba da zama da kai gunsumeme ba Aure, sedai duk inda zani kana biye dani? Ai lokaci yayi da zaka nemi iyali kaima"
"Nidai umma bana so, ki ƙyaleni a hakana kawai"
"Iyeee, kai kodai baka da lafiya ne? Idan bahaka ba, amma kace baka so in ƙyaleka, idan baka da lafiya ne ka gayamin in san abunyi, amma ta yaya za ka ce baka son Aure?"
Ya gane inda Umman ta dosa amma yace "Umma wane irin rashin lafiya, niba zazzaɓi ba ba wani ciwo ba, kina ganina rasam danu, kawai ni matan ne se a hankali, bana son wadda zata zo ta damemu"
"Ai ina maka addu'a, kuma nasan Allah ya amsa, Insha Allah mace tagari zaka samo mana, amma dai gaskiya anemomin sirika, ko kuma ni in nemo"
Yusuf ya miƙe tsam yace "Hajiya Umma kenan, me abun mamaki Allah ya ƙaro mana Arziki in biyamiki Makka, ni nayi nan seda safe"
"Au zancen ne baka so shine ka gudu ko? Zakazo ka sameni kuwa dan ƙaniyar ka, jikoki nake son gani, na ƙagu ka ƙara gaba yara nake son gani "
Yusuf yayi waje yana dariya yace "Hajiya Umma, tawa ta kaina.
Yusuf ya cigaba da aikin sa, da neman kuɗinsa.
Wataran ya dawo a babur ɗinsa, ze wuce gida yaji ance " Sannu da zuwa "
Ya waiga yaga wata matashiyar budurwa ce, shi dai yasan yana ganinta a nan unguwarsu, amma besan daga inda take ba, kuma ba abunda yake haɗashi da ita, dan haka be kawo dashi take ba yai gaba abunsa.
Aikuwa yaji haushin ƙin kulatan da yayi, haka ta wuce ta tafi nata Aiken.
Da safe ya fito ze sai bredi, suka kuma haɗuwa da ita, tace masa ina kwana, ya waiga ya kuma kallonta tace "nace ina kwana"
Yusuf yace "lafiya ƙalau" daga nan yai gaba.
Ya zamana kusan kullum in dai ze fita kokuma ya dawo seya ganta, kuma seta kula shi, shi harta fara bashi haushi ma.
Wataran Asmar Umma ta tashi ga zazzafan zazzabi, Yusuf ya kaita Asibiti aka rubuto mata ruwa da allurai, aka sama ta wasu a can ya taho da sauran gida.
Da daddare za'ayi mata allura, yaje chemist ɗin bakin titi, yaje ya gayawa me chemist ɗin ko zezo yayi mata allurar a gida seya biya shi
Me chemist yace "karka damu, kaje zan turo ƙanwata tayi mata"
Yusuf yace "tasan gidan ne?"
Yace "eh ta sani, zata zo insha Allah"
Yusuf ya koma gida yana jira, yai girki ya tattara kwanukan yana wankewa, tayi sallama, ya miƙe kalleta aikuwa ya haɗe rai yace "ke lafiya?"
Taya fari da ido tace "ba gurinka nazo ba kake wani haɗemin rai, ina mara lafiyar tamu?"
Yusuf ya harareta yace "wace mara lafiyar? Malama ƙara gaba ba nan bane"
"Kamar yaya, Yaya Sani ya cemin inzo zan mata allura fa"
"Wai dama kece?"
"Eh nice, ina Umman tawa take?"
Yusuf a ransa yace "ji wani iyayi, wai Ummanta ummana dai ni kaɗai"
Yai mata jagora gurin Ummansa, Yadda ta dinga lallaɓa Umman ne, yaji daɗi Sosai, bayan ta gama yace 'nawa ne? "
Ta Harare shi tace "in mutum yayiwa mamansa abu seya biya? Ummana Allah ya ƙara sauƙi"
Umma tayi murmushi tace "nagode sosai' yata, Allah yasaka da alkhairi"
Yusuf ya tsaya sororo yana kallonta tace "kaje ka cigaba da wanke wankenka mana, Umma seda Safe Allah ya ƙara sauƙi, likita ya rubuta a samiki ruwa, safe da yamma na kwana biyu, zanzo in samiki insha Allah"
Umma tace "to shikenan nagode Allah yayi albarka, amma baki gayamasa nawane kuɗin ba ya biya"
Yarinyar tace "Abunda ze biya shine, yaje ya ƙarasa wanke wankensa, yai miki shara ya siyo miki duk abunda kike so kici, kiji ƙwarin jikin ki"
Umma tace "to shikenan kana dai ji ko?"
Yusuf kawai ya sosa kai, Yarinyar tace "dan Allah ka fitar dani bakin hanyar nan taku, lungunku da duhu ina jin tsoro"
Umma tace "Yusuf raka ta mana"
Ya kalli Umma ya kalli yarinyar, ta kashe masa ido ɗaya tayi gaba.....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
104_105
Yusuf ya bita da kallo yana hararta, Umma tace "eh yakamata, Yusuf rakata hanya kaga dare ya fara yi, ni baki gayamin sunanki bama gashi zaki tafi"
Tai murmushi tace "Sunana Salma"
Umma tace "to Salma nagode, ki gaida mutan gidan"
Salma tace "zasuji insha Allah"
Badan Yusuf yaso ba ya biyota suka fito, Salma tace "wai kai baka amsa gaisuwa ne?"
"Eh bana amsawa"
Salma tace "A'a kace dai nice baka amsa gaisuwa ta, da safe idan na ganka koda yamma idan na gaisheka seka wani basar kamar baka ji ba, kuma fa kana jina"
Banza yai mata suka cigaba da tafiya, "au kana ji ina maka magana shine kamin shiru, ga mara hankali ko?"
Ko kallonta beba ya cigaba da takunsa majestically.
"Shikenan kar Allah yasa ka kulani ɗin, kuma ma bana son rakiyar"
Yusuf yace "to ki gaida gida"
Ya juya ya koma gidansu, Salma tace "lallai ka cika ɗan rainin hankali, dani kake zancen"
Washegari da Safe yakasance weekends ne ba aiki, dan haka bayan ya dawo daga salla, ya duba Umma yaga jikin nata da sauƙi, yakoma ɗaki ya baje ya dinga bacci, saboda baya samun hutu sosai, yana tara gajiya matuƙa.
Se kusan ƙarfe goma na safe ya tashi da sauri, dan ya manta shaf zeyi girki, ya tafi ɗakin Umma da sauri ya shiga da sallama ya tarar da Umma a zaune da ruwa a hannuta, Yusuf yace "Ummana dan Allah kiyi haƙuri, bacci ne ya ɗaukeni me nauyi, ashe har an samiki ruwan ban sani ba ne, bari inje in ɗora ko tea ne inje in siyo bredi"
Umma tace "A'a baseka ɗora ba, ni a ƙoshe nake"
"me kika ci haka, har kika ƙoshi?"
Salma ce tayi sallama ɗakin, hannunta ɗauke da plate da kofi, Yusuf yana zaune a falon Umma, daga shi se gajeren wando da vest, dan haka kyakkyawar surar jikinsa ta bayyana, namijin gaske me tsabar kwarjini da kamala.
Yana ganin Salama ya miƙe yace " ke meye haka zaki shigowa mutane babu sallama, baki tsaya an baki iziniba kika shigo?"
Umma tace "A'a ai tun ɗazu tana gidan nan, ita taimin shara da aikace aikace ma"
Ya kalli Salma da ta tsatstsareshi da ido yace "to waye ya sata, Da kin bari Umma idan na tashi ai zanyi, ke Malama ajiye kwanukan nan ki tafi angode, zan kaiwa yayanki kuɗinki ya ajiye miki"
Hararrasa Salma tayi harda murguɗa baki, Umma tace "jimin yaro da faɗan ba gaira ba dalili, daga taimako ita meta yi maka?"
"To Umma data gama aida seta tafi, amma kalli yadda ta ganni a haka ba kaya, kuma ta wani tsareni da ido"
Umma tace "to ubanwaye yace ka fito a hakan, ƙyaleshi kinji yau ban san dame ya tashi ba, naga yau rigima yake ji"
Yusuf ya fice daga ɗakin yana mita.
Haka aka ƙarashe kwanakin nan a haka, kullum tazo se sunyi faɗa da Yusuf, in dai tazo seta yiwa Umma 'yan aikace aikace kafin ta tafi, ko su zauna su sha hira ita da Umma, Salma tana da kyau dai dai gwargwado, gata' yar kwalliya da iya ƙwalisa, tana da hasken fata da matskaicin tsawo, sannan tana da ƙirar jiki me kyau, ta yadda ko tafiya take tana ɗaukar hankali.
Mazan unguwar nan dana wajen umguwar da yawa suna rushing a kanta, amma bata da lokacin su, ba matasan samari ba har manyan masu kuɗi suna nuna tayinsu amma basu isheta kallo ba, Saboda mace ce me class, a mazan ma ba kowa ke iya tunkarar ta ba, saboda duk girmanka idan kamata abunda beyi mata ba, zata keta kane yadda take so kuma ko a gaban waye, Tayi school of Nursing, tayi midwife tana ji da kanta sosai.
A bakin yayyyanta taji suna hirar Yusuf wataran da daddare, ɗayan yace "Habu gaskiya gayen nan da yaja salla da Asuba dama ya zasu bashi limanci, jar uba kaji ƙira'a kamar a Misra"
Habu yace "bari Usman, ni kaina da yaja sallar nan kamar kar ya dena karatun nan, ai rashin zuwan liman da wuri yau munga 'yan Islamiyya, anya wannan a ƙasar nan yai ilimin Addini?"
Usman yace "waya san masa, gaskiya ya iya karatu inaga zanje muyi bonding kona samu hasken makaranta"
"A gidan uwarwa zaka samu hasken makarantar? Bayan ko sauka Al'qur'ani ba muyi da kaiba ka fece neman kuɗi"
Habu yace "eh naji, aiba sharaɗine se mutum yayi sauka za'ayi abota dashi ba"
"To bari in gayamaka, kaga duk wannan ilimin nasa shegen girman kaine dashi, baha kula kowa, iyakaci in ze wuce yai muku sallama, ban da haka ko aboki bashi da shi a unguwar nan, inda gayen ya ban haushi kenan, dan kana da ilimi ubanwa zakayiwa girman kai, kai ba wani shahararraen attajiri ba, ba basarake ba amma kace bazaka kula mutane ba"
Habu yace "Aikuwa ilimin baze masa amfani ba, dan girman kai rawanin tsiyane, ni harnaji ya bani haushi wallahi '
Salma tace " Kukam Allah ya shirye ku, kawai kun zauna kuna tayi da bawan Allah kamar kun rasa abunyi "
Usman yace " ke abun da haushi fa, mutum be fika da uban komai ba amma ya dinga hura maka hanci, baze dingawa mutane magana ba, ai dole ayi dashi"
Salma tace "to ka sani ko haka nature ɗinsa take, maybe jan ajinsa yake yi".
Habu yace "Nature ɗin banza da wofi, kuma jan ajin me sekace mace, jan aji ai se mata, kana namiji ubanwa zaka jawa wani aji, yana gaddi ina gaddi za'a jamin aji, wallahi mutum be isa ba"
"Nikam nafison irin haka, inga mutum gentle, yafi ma wata macen jan aji amma ace duk inda mutum ya zauna dan yana namiji ya dinga sakin baki haba, ai abun ba tsari"
Habu yace "wannan yarinyar kinci kai tabbas baki da hankali, namiji in ba ɗan daudu ba meye na wani jan aji"
Haka suka cigaba da wannan jayayya a tsakaninsu, ya zamana kusan kullum se anyi zancen Yusuf, saboda ko minti biyar liman ya ƙara bezo ba, se kaji ana Malam Yusuf a jamu salla, saboda kawai suji ƙira'arsa me daɗin sauraro.
Zuciyar Salma ta kwaɗaitu da san ganin Yusuf, saboda yadda take jin ana maganar sa, wataran da yamma taje karɓar kuɗi a chemist ɗin Usman, Yusuf yaje siyawa Umma Inhaler, tunda ya shiga daga tafiyarsa ma taga yadda yake taku cikin nutsuwa, yayi sallama suka amsa sannan ya gaishesu, ƙamshin turarensa ya gauraye shagon, Salma ta shagala da kallonsa, wanda shi sam be san ta nayi ba, ya karɓi abunda ze siya yai waje.
Yana fita Salma tace "Masha Allah, Yaya wannan ma a unguwar nan yakene? Kaga mutum nutsatse, ga ƙamshin turare, wanda seka gifta maza goma ba kaji ba, se warin hamnata mussman irinsu Yaya Habu"
Usman yace "Allah yasa yaji abunda kikace ya casaki san ransa, shegiya uwar leƙe leƙe, duk tarin samarinki amma kuma kina yaba wani"
Tace "kai Yayana, wallahi ko kai da kake namiji kasan gayen nan ya haɗu, kaga da yai murmushi, wasu dimples suka lotsa wayyo Allah na, gaskiya me kyau ne, kuma me ajine"
Usman yace "dalla wuce can, haka zaki ƙare ƙarshe mummuna zaki aura"
Tace "Allah ya kiyaye, aini naga miji"
"A ina?"
"wannan wanda ya fita ɗin mana, in dai a unguwar nan yake, ina ciki"
. Usman yace "aikuwa zakiyo waje daga cikin da kika shiga, dan girman kaine dashi kamar ƙaruna"
Salma tace "kamar yaya kenan?"
"Shine fa Yusuf ɗin da muke magana, wanda Habu yake zagi"
Salma tace "haba dai? Wayyo Allah na gaskiya ya haɗu, bashi da makusa, ga kyau ga ilimi ga nutsuwa ga tsafta, gaskiya yamin"
"to 'yar wahala, wata wahalar ta ganki kenan, dan wannan banga ta inda ze kulaki ba, dukda wannan koɗaɗiyar fatar taki"
"to fatar tawa ma hassada ake mata, to Allah ya shiryeka, ni na tafi ka tayani addu'a kawai"
Ta juya ta fita da sauri, tun daga ranar ta gano gidansu Yusuf, take daidaitar lokacin fitarsa da dawowarsa, idan ta ganshi se tayi masa magana, farko da yake ƙin amsa gaisuwarta tayi zaton zancensu Habu haka yaje yana da girman kai, seda taje gidansu sawa Ummansa Ruwa taga yadda yake aikin gida, ga shagwaɓa kamar mace, ga tsananin biyayya ga mahaifiyarsa, anan ta gane mutane da yawa basu fahimce shi ba, bashi da son shiga mutane ne, amma mutum ne simple.
Tun daga nan Salma ta liƙe masa, idan ta ganshi seta masa magana kota tsikane shi, wataran sedai ya harareta yai tafiyarsa, ta maida gidansu Yusuf gidan zuwanta, ko tayo girki ta kawowa Umma, ko tazo nan gidan ta tayata aiki.
Sabo ne ƙarfi ya shiga tsakanin Umma da Salma, tana jin daɗin yadda take girmamata take tayata wasu ayyukan, dukda Yusuf haushin Salma yake ji amma a hankali, saboda soyayyar da take nunawa Ummansa da mutuntawa yasa, yake ɗan saurara mata kuma har cikin ransa yake jin daɗin kulawar da take nunawa mahaifiyarsa.
Wataran Salma taje gidansu Yusuf wajen ƙarfe sha ɗaya na Safe, ta tarar da babur ɗinsa be fita ba, ta shiga cikin gidan ta tarar da Umma a tsakar gida hannunta da mayafi, Salma tace "Umma ina zuwa haka? Kuma Yaya Yusuf be fita bane? naga babur ɗinsa"
Umma tace "dama chemist ɗin yayanki zanje, kwanan sa kusan biyar yana zazzaɓi sama sama, nayi nayi yaje Asibiti yaƙi yau jikin nasa rau da zazzaɓi ko gurin aiki ya kasa fita, shine nace bari in kira yayanki, ya duba shi idan akwai abunda ze iyayi masa to, in kuma babu mutafi Asibiti, yana jin jiki, kin san shi da dauriya da taurin kai, yauma dan yaji uwar barine ya kasa fita gurin aiki"
Salma tace "Ina Yaya Yusuf ɗin yake? Nima zan iya duba shi ai"
Umma tace "muje yana ɗakinsa"
Umma na maganar aka kirata a waya, ta tsaya ɗagawa Salma ta shiga ɗakin nasa da Sallama, ɗakin tas dashi kama r na mace, komai fes fes se ƙamshin turaren wuta da drumer ke tashi, gwanin ban sha'awa.
Ta hango Yusuf kwance akan gado, ya lulluɓa da bargo, a hankali ta ƙarasa gaban gadon nasa, tasa hannu ta janye bargon tace "to shagwaɓaɓɓe, kazo ka kwanta kaƙi zuwa Asibiti, ka tayarwa da Umma hankali"
A hankali ya buɗe idonsa ya kalli Salma, cikin ƙarfin hali yace "malama fitarmin daga ɗaki"
"bazan fita ba ɗin, meke damunka ummance tace inzo in duba inga me ya kamata ayi maka"
Lumshe ido yayi yaƙi magana, Umma tazo tace "Salma yaya? Za'a iya duba shi a gida"
Salma tace "eh, za'a iya, zanje in karɓo ruwa da allurai in masa, amma ya rage kayan jikinsa, ki shashshafa masa ruwa ina zuwa"
Haka akayi Salma ta sassaka masa ruwa, da allurai sannan Yusuf ya samu kansa.
Washegari da safe da ta dawo, ta tarar da abokan aikinsa sunzo duba shi, babu wanda yasan Yusuf ɗan sanda ne a unguwar dan haka Salma tayi zaton 'yan uwansa ne suka zo duba shi, ta taho masa da Abinci daga gida.
Abbas yace "Yusuf ka samu kaci Abincin mana"
Yusuf yace "bani da appetite ne, amma zanci"
Sakina tace "ko in zuba naka, ka ɗanci ko kaɗanne?"
Salma tace "No karki damu, zeci in kun tafi da kaina zan bashi ko Yayana"
Sunkuyar da kai yayi yai mata shiru, yayin da Abbas suka shiga tsokanarsa, Sakina kuwa ta dinga harar Salma, ta dinga cika tana batsewa, saboda gaba ɗaya Haushi Salma ta bata.
Bayan ya warke ya koma gurin aiki, sedai Sakina ma ta fito da manufarta na soyayyar ta ga Yusuf, sedai Yusuf ya nuna mata sam shi babu wannan, babu maganar soyayya a tsakaninsa da ita.
Salma kuma ya maida ita kamar Ƙanwarsa, dan wataran shike ɗakkota ma daga inda take attachment, kusan duk ta kori samarinta saboda Yusuf, se sukai sha ɗayan dare suna waya, amma sam shi Yusuf ba wai dan yana sonta ba, dan ya ɗauketa ƙanwa ne kuma takan bashi shawarwari masu kyau.
Ita kanta Umma ita duk a zatonta soyayya ce tsakanin su, tana ta jin daɗi tana murna Yusuf zeyi dacen mata, dan Salma akwai kirki sosai.
Wataran Umma ta sai wata doguwar riga me kyau, ta saiwa Salma ta bawa Yusuf tace shi ze kai mata rigar.
Haka Yusuf ya karɓi riga ya kai a matsayin shine ya siya, Salma ta dinga murna tana masa godiya, har ze tafi tace "Yayana nawa nikaɗai"
Yusuf yace "meye kuma? Dare fa yayi ki bari in tafi gida"
Salma tace "Yusuf yaushe zamuyi Aure ne?"
Yusuf yace "what? Aure kuma Salma? Ai babu batun aure a tsakanin mu, ni ƙanwa na ɗaukeki fa"
"Yusuf, ƙanwa kuma? Yanzu duk abunda ke tsakaninmu ba soyayya bace? Yusuf na kori kowa a samarina, babanmu ya tambayeni, nace ni kai na tsayar yace in sallami masoyana, amma ka cemin babu soyayya a tsakanin mu?"
Yusuf yace "Salma, banyi hakan da cutar dake ba, amma dan Allah kiyi haƙuri, ni gaskiya ban shirya yin aure ba"
Ai bata jira me zece ba ta shige gida da gudu tana kuka, Yusuf ya dinga mamakin son da take masa.
Kwana biyu Umma taga kwana biyu ba taga Salma ba, tacewa Yusuf "kaga kwana biyu banga 'yata ba, ko zaka je anjima ka jimin ko lafiya?"
Nan Yusuf ya warwarewa Umma komai, aikuwa ta sameshi ta inda ta shiga bata nan take fita ba, "haba Yusuf, dan wulaƙanci yanzu duk sintiri da ɗawainiyar da yarinyar nan take damu, kace kai bakama san sonka take ba? Ni ina nan na saki baki zan samu Kayi Aure amma ka cemin kai bakama son sonka take ba? Idan ba sonka take ba ubanka take yi? Wani irin mutum ne kai Yusuf? Haba Yusuf haka rayuwa zata yi? Ba zakayi Aure ba haka zamuyi ta zama a cikin gidan nan, kamalar mutum ai aure, amma kai in anyi gabas seka yi yamma, duk abunda mutane ke gani daidai kai Ba haka yake a gurinka ba? Haka rayuwa zata tafi a haka? Wallahi in baka yi wasa ba haƙƙinta ze kama ka "
Ganin ran Ummansa ya ɓaci, yasa ya shiga damuwa ya dinga bata haƙuri, tace idan yana son ta haƙura yaje ya rarrashi Salma sannan ya amince zw Aure ta, tunanin Farko daya fara zuwa zuciyarsa shine waye ze tsaya masa yayi Auren? Amma gudun ɓacin ranta yai shiru.
Yaje gidansu Salma ya tarar bata da lafiya duk tayi wani iri saboda damuwa, Yusuf ya dinga rarrashinta, ya tabattar mata da ya amince da batun Auren, Salma ta dinga murna, take taji tama warke daga ciwon.
Suka shiga soyayya shida Salma, shi dai tausayinta da yake ji yafi yawa, dan baze ce ga takamaimai feelings ɗin da yake dashi akan Salma ba, Sone da tausayi, ko kuma tausayin ne kawai.
Nan aka shiga gulma a unguwa, wai Yusuf daga zuwansa yasa Salma ta kori kowa yana juyata yadda yaga dama, ya maida ita 'yar aikin babarsa, kullum cikin sintiri take a gidansu, saboda Salma yasa ya fara kula yayyenta a hankali sukuma suke jansa cikin jama' ar unguwa dan seka zauna dashi zaka gane bashi da wani girman kai.
Wataran suna sitting room ɗinsu Salma suna hira ita da Yusuf, ta sha ado se zabga ƙamshi take, suna ta taɗi ya miƙe ze tafi aka ɗauke wuta, aikuwa ta rungume shi tana kukan Shagwaɓa wai ita tsoron duhu take.
Yusuf yace "Salma ki cikani, kar wani yazo ya ganmu, amana mummunar fassara"
"Ni tsoro nakeji, tai maganar cikin Shagwaɓa tana sake kwanciya a jikinsa, ga wani ƙamshin turare da take yi, take jikin Yusuf ya fara tsuma, karo na farko daya rungumi mace a jikinsa, ya dinga jin wani irin yanayi yana bijiro masa, sheɗan na ƙoƙarin yi musu lalata, nan da nan yasa hannu ya raba Salma da jikinsa yai waje da saurin gaske.
Ko daya koma gida, ya sauya kaya ya kwanta ya kasa manta abunda ya faru, gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idonsa, tunani iri iri, a nan ya ƙara yadda da tabbas ya kai munzalin da lallai yana buƙatar mace a tare da shi, sedai waye ze tsaya masa, tunda harkar Aure dole seda uba, ko wakilansa.
Azumi ya gabato Yusuf yayi wa Salma siyayyar kayan Azumi, dana salla, Umma ba ruwanta da duk abunda ze siya ya kaiwa Salma, sema dai ta dinga yakamata ka ƙara kaza.
Ya haɗa sha tara ta arziki ya kaiwa Salma, Salma ta dinga murna tana godiya, Yusuf yana kashe mata kuɗi sosai.
Bayan kwana biyu mahaifinta yasa aka kira masa Yusuf, yace ya turo magabatansa ayi maganar Aure, tunda dai sun fuskanci juna, wahalar da yake ta isa haka.
Sedai Yusuf ya koma gida cike da zullumi a zuciyarsa, waze turo? Wa yake dashi banda Allah da Ummansa?
Bayan ya koma gida daya gayamata tayi murna, sedai itama kanta seda jikinta yayi sanyi, amma ta dake tace masa shikenan bakomai, Insha Allah za'a tura a tambayar masa, Yusuf be cikata da tambaya ba ya ƙyaleta.
Umma ta shirya ta tafi gurin Yaya ɗan lami, ta gayamasa cewar dan Allah Yusuf ya samu yarinyar daze Aura ne, tana so ba dan ita ba su wuce masa gaba su tambayar masa Aure, Yaya ɗanlami yace mata ai ba matsala, bakomai dan dai wannan, zasuyi zasuje su tambayar masa Aure.
Umma ta dawo gida tana ta murna tana farinciki, Yusuf ze Aure ze zama cikakken mutum shima kamar kowa.
Wataran ya dawo da yamma, daga gurin harkar furnitures ɗinsa, yazo ya tarar da cincirindon mutane a ƙofar gidansu, se gabansa ya faɗi ya zaci wani abune ya samu Ummansa, dan haka a guje ya ƙarasa cikin gidan yana ture mutane, yaje ya tarar da ita a zaune tana kuka, ga kayan daya saiwa Salma na Azumi dana salla, a baje a gabanta wasu mata suna cewa
"gayyar tsiya ashe bashi da uba, ya lallaɓo ze aurar mana 'ya, to Allah ya rufamana Asiri, seku koma gidan marasa iyaye inda aka ɗakkoshi, a ɗakko masa mata a can ba dai' yarmu ba, banda mutanen nan na kirki ne sunje sun gayamana, da haka zamu bawa mara uba 'ya, ai kema kin san bakiyiwa kanki adalci ba"
Yusuf ransa ya ɓaci, dan yau an masa tozarci mafi muni, dama abunda yake ta gudu kenan Umma takasa ganewa, maimakon a dawo masa da kayansa salin alin, shine seda aka tara wannan gayyar mutane sannan za' aci zarafinsa haka, kuma ma dan baƙin ciki akazo akasa mahaifiyarsa a gaba da cin mutunci kuma aka cika gidan kamar wanda sukai sata ko maita, cikin tsananin ɓacin rai da juriya, Yusuf ya kalli Matan yace "mun muku laifi, Allah ya baku haƙuri, tunda kun gama abunda zakuyi, zaku iya fita"
"Ai dole kace haka mana, tunda ka lallaɓo zakayi cuta, yarinya da samarinta na arziki amma zaka cuceta, yarinya 'yar dangi kyakkyawar gaske"
"Wallahi idan kika kuma gayamin maganar banza sena wanka miki mari, get out from here"
Yadda yayi maganar a fusace ne yasa jikinsu na rawa, sukayi waje dasu da gayyar mutanen da suka cika gidan, anata ƙananan maganganu, wai ashe duk girman kan nasa ma bashi da uba, yana taƙama da wannan kyan nasa yana hura hanci, ashe ma shegene.
Yusuf be cewa Umma komai ba, ya tattare kayan yaje ya ajiye, ya wuce ɗakinsa ya kwanta, zuciyarsa na masa wani irin raɗaɗi mara misaltuwa.
Umma tasan ba kowa ne yaje ya gaya musu wannan maganar ba face su ɗanlami, tayi danasanin zuwa ta samesu akan su wucewa Yusuf gaba akan harkar Aure, yanzu shikenan baza'a auri ɗanta ba saboda wannan dalilin? Dukda tarin nagarta dayake da ita.
Tun daga ranar ko hanyar gidansu Salma ,Yusuf be ƙara biba, ba damar ya fita ko yazo wucewa se yaji ana yada masa da maganganu marasa daɗi, ya goge lambar Salma, da duk wani abu daya shafeta.
Sedai hakan ya zame masa tamkar wani ciwo a ransa, Yana kewarta saboda sun shaƙu sosai.
Wataran ya fito ze fita aiki ya ganta a ƙofar gidansu, ya ɗauke kai ze wuce amma ta sha gabansa tace "Gurinka nazo"
Yusuf ya kalleta yace "meyafaru sauri nake"
"Yusuf, ni kaina banji daɗin abunda akayi maka saboda ni ba, ban san haka abun yake ba, amma abun yafi ƙarfina ba yadda na iya, dan Allah kayi haƙuri, kuma ka bawa Umma haƙuri, ga katin ɗaurin Aurena nan, ina buƙatar addu'arka, kuma ina fatan ubangiji Allah ya baka wadda ta fini, komai da komai nagode da lokacin ka Yusuf "
Ta zira masa katin ɗaurin Auren a gaban babur ɗinsa, ta juya tana share hawaye, shiba katin Aurenta nema ya dameshi ba, kukan da take ne ya bashi tausayi.
Gaba ɗaya ya rufe babin Salma a rayuwarsa, ya koma rayuwarsa sedai mikin nan baze taɓa barin zuciyarsa ba.
Yusuf yayi ajiyar zuciya sannan yace "ko wata biyu ba'ayi ba da abunda ya faru, aka bani aikin nan akanki, da farko nace ba zanyi ba, amma Abbas ya takurani, saboda wai ina da haƙuri, sedai ranar farko dana fara tozali dake, dukda isarki da izzarki, duk da jan aji da wulaƙancinki, se da naji zuciyata tayi bugun da bata taɓayin irinsa ba, ga kwarjininki yasa na kasa haɗa ido dake, ban shirya ba banyi tsammani ba na shiga kokawa da zuciyata akan Sonki da take, na nemi 'yar talakawa ma ban samu ba, saboda rashin asalina, ina ga ' ya kamarki, me Asali me dukiya gashi uwa uba naje a matsayin direba, se akanki na tabattar da Biyayya ce da shaƙuwa tasa na karɓi Salma a wancan lokacin, Amma wannan karon zuciyata ce da kanta ta zaɓi abunda take so, Widad bani da tabbas idan Dagaske Umma take na cewar, hatsari iyayena sukayi aka jefoni ta taga, nasan zata iya gayamin hakan dan hankalina ya kwanta, amma zance mafi yawa shine a gidan marayu aka ɗakkoni, Yanzu zaki yadda ki haɗa zuriya da mutum irina? Ki haihu dani alhalin bani da dangi se Allah se Ummana? Ni ba ina gudun haihuwa bane, nima ina fatan ganin jinina a duniya, amma kinji dalilina Auren nan kansa da mukayi a cikin zullumi nake Widad, ni dai nasan ina sonki amma bani da asalin da za'a nuna, nasan Ko Daddynki baze amince ba Widad, tuntuni nake zullumin gayamiki wannan labarin nawa, zaki zauna dani a haka?, ina sonki Widad, akanki na fara jin shauƙin soyayya, naji zan iya duk wata sadaukarwa saboda ke, dan Allah kar rashin iyayena yasa ki gujeni, ina sonki Widad ni kaina ina mamakin son da nake miki"
Ya ƙarasa maganar yana kuka, shaɓe shaɓe da hawaye kamar mace, Widad ta ƙanƙameshi itama tana kukan, ta rungumeshi kamar jariri a ƙirjinta, ta dinga shafa sumar kansa tana
"Am sorry Yoseef, am sorry kayi haƙuri please"
Kamar ta ƙara tunzura Yusuf, kuka yake sosai harda sheshsheƙa, da alama abun yana cin zuciyarsa.
Tana kuka take cewa "Yoseef dan Allah kayi haƙuri, ka dena kukan nan haka please"
Ya girgiza mata kai yace "ki ƙyaleni inyi inji sassauci a zuciyata Widad, ban taɓa yiwa wani kukan rayuwar da nayi ko na tashi a ciki ba seke, i need a shoulder to cry on, ƙyaleni inyi matata"
Widad ta rungumeshi tana kuka, tana tausayawa irin rayuwar da suka yi, dan daga ita har Yusuf kowa yaga rayuwa, kowa da irin ƙaddarar daya fuskanta a raguwarsa, amma na Yusuf ya ratsata sosai, ya bata tausayi matuƙa, ya wahala a rayuwarsa.
"zan rayu da kai a duk ya kake, zan karɓi kowane ƙalubale daze taso saboda kai, ina son Aurena Yoseef, ina son zama da kai, ba ruwana da waye kai, nagartar ka da gaskiyar ka sun wadatar dani, stop crying my Husband, nima ai kana gani ba dangin ne dani ba, daga Allah se Babana, duk dangin babu, dan haka ina so mu zama ɗaya mu samar da family nida kai, ka dena kuka mijina "
TAMMAT BI HAMDILLAH, NA KAMMALA KASHI NA BIYU ZAN SHIGA NA UKU, WANDA SHINE NA ƘARSHE DA YARDAR ALLAH
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
106_107
Yusuf ya sake ƙanƙame Widad yana cigaba da zubda hawaye.
"Yoseef dan Allah Kadena kukan nan, zaka ɗagamin hankali, ya isa haka please kar kanka yayi ciwo kaji"
"Hmm, my wife tsawon shekaru talatin da biyu, abu yana damuna a zuciya, ban samu nayi kuka yadda nake so ba, dan haka dan Allah ki barni inyi, kin ƙyaleni nika ɗai nasan what i go through, na shiga damuwa da baƙin ciki daban daban a rayuwata, i suppose to cry ko zan rage "
"No Yoseef, kace Alhamdilillah daya barka da ranka da lafiyarka, kuma insha Allah daɗi yana tafe, dan bayan duk wata wuya se daɗi da yardar Allah, ka dena kuka kaji Ɗan uwana, we are now family ai ko?"
Ajiyar zuciya ya dinga saukewa, yace "Widad dagaske zaki cigaba da zama dani, koda mun koma gida?"
Widad tace "dagaske nake, Insha Allah mutu ka raba nida kai, kaine dai dai da rayuwata Yoseef, a yanzu kasanni fiye da yadda kowa ya sanni, ciki harda mahaifina, kasan abunda nake so kasan wanda bana so, you are such an amazing guy, kuma ni labarinka da naji, bazan iya rabuwa da kai ba, ƙaddarorinmu suna kamanceceniya da juna, dan haka zamanmu zeyi dai dai da yanayin rayuwar mu, zan zauna da kai Yoseef, ba ruwana da a inda aka samo ka ko makamancin haka, kuma insha Allah bazaka sake zubda hawaye saboda haka ba, ka dena kuka kaji Mijina "
Tai maganar tana share masa hawaye, itakuma tana zubda hawayen, Yusuf ya ɗago kansa yana share mata hawayen fuskarta itama yace " Am sorry Baby, na saki kuka ko? Yi haƙuri yau nayi ragwanci a gaban matata, zata rainani"
Ya ƙarasa maganar yana murmushin yaƙe, "kwanta muyi bacci, dare yayi kar gobe in Allah ya kaimu a barni da yunwa"
Yai murmushi tare da kwanciya a jikin ta, tasa hannayenta ta zagaye bayansa dashi, tana shafa sumar kansa da hannunta ɗaya, Yusuf yana ta jan ajiyar zuciya, ta shiga ɗan duddukan bayansa alamar rarrashi.
Wani irin kallo Hajiya Halima ta shiga yiwa mutumin, Mutumin yace "kina mamakin ganinane? Ai bekamata kiyi mamaki ba, butulu mara Alƙawari"
Ramlah ce ta fito ita da Amal, Ramlah tace "Mummy ya har yanzun baki tafi ba? What are you still doing their?"
Suka ƙaraso inda take tsaye ita da mutumin nan, Amal ta buɗe baki tare da dafe ƙirji, Ramlah tace "Mummy wannan kuma wanene? Barar ce baza'a bari kifi ta ayimiki ba, se an biyoki har nan, mutane sun fiye zalama kamar zasuyi ƙwace dan azabar son kuɗi"
Amal tace "kai Ramlah, babanmu ne fa, baki gane shi bane?"
Ramlah tace "What? Wannan ɗin kalle shi wani buguzun buguzun dashi kamar korarre"
Hajiya Halima tace "rufemin baki dan ubanki, Babanku ne"
Ramlah tace "Taɓɗijan, God forbid in nuna wannan ince shine ubana, alhalin ina bearing da Sunan Nasir Daula, sannan wannan yazo yace wai shi ne babanmu, Allah ya kiyaye wallahi wannan ko riƙon jakata bazan ɗauke shi ba, ni ubana ya mutu da daɗewa, sedai babansu Anwar"
Ta juya ta shige gidan tana ci gaba da maganganu, mutumin ya kalleta yace "Halima haka mukayi dake? Saboda son zuciya irin naki haka kika mayar min da 'ya' ya, yarinyata ta kalleni tana gayamin wannan maganganun, dama haka mukayi dake?"
Hajiya Halima tace "kaga, dan Allah karka ɗagamin murya a gaban ma'aikatana, kazo mu shiga daga ciki ayi duk wacce za'ayi mana"
Ya bita suka shiga cikin falo, Amal ta tafi gurin Ramlah ta buɗe ƙofar ɗakin nata ta shiga, ta sameta tana zaune tana danna waya, Amal tace
"Ramlah bekamata kiyiwa mahaifinmu haka ba, ai duk lalacewarsa shine ya haifemu"
Ramlah tace "wait, wai dan Allah dagaske wannan bagidajen shine mahaifinmu?"
"Ramlah ki gyara maganarki fa, wallahi babanmu ne ya zaki manta fuskarsa, wallahi babanmu ne"
"gaskiya sedai Babanku, kalli mutum a koɗe kamar baya cin Abinci, kalli suturar jikinsa yazo yace shi babanmu ne, gaskiya niba ubana bane, ai abun kunyane mu nuna wannan muce ubanmu ne, bayan duniya tasan da sunan Daula muke amfani, ai kawai babanmu ya mutu, amma wannan ai be kai mutum ba balle ace masa uba"
Amal tace "ikon Allah, wallahi Ramlah kina sane, babu yadda za'ayi kice kin manta kamanin mahaifinmu, dukda tunda muka bar gurinsa bamu kuma zuwa ba"
Ramlah tace "ke ina sane wallahi, na gane shi sarai, amma ni karan kaina kunya nakeji in kalle shi ince mahaifina ne, haba mutum a tsiyace kamar matafiyin da guzuri ya ƙare masa, kuma ya tsaya ze fara kora bayani a gaban wannan gidadawan, salon su raina mutane"
Amal tace "lallai Ramlah, ke abun naki babbane ma"
"Haba shu'aibu, ya zakazo a wannan lokacin da ake tsakiyar tarzoma da tashin hankali? Kazo babu aike bau Sanarwa haka akeyi, kuma ka tsaya kana neman ka tona min Asiri a gaban mutane, kai har yanzu bazaka waye ba?"
Shu'aibu ya kalleta yace "dama ina zan waye, mara mutunci dama haka mukayi dake? Nace haka mukayi dake? Akan yarjejeniya mukayi komai, amma da yake ke butulu ce, kinzo kin samu jin daɗi kin watsar dani, kinyi watsi da Yarjejeniyar da mukayi, shine nazo in miki tuni, ki cika Alƙawari sannan ki bani 'ya' yana"
"wane 'ya' yan naka, malam karma ka ɗakko wannan maganar, dan ba zata yuwu ba, me ka sani na 'ya' yan naka, seda na gama wahalar? Lokacin mora yayi sannan kace in baka no, baze yuwu ba"
Shu'aibu yace "kin san Allah Halima, sekin bani 'ya' yana gaba ɗayansu bazan bar ko guda ba, kuma sekin cika Alƙawarin da mukayi daku"
Tsaki tayi tace "bani account number ɗinka, zan baka dubu ɗari biyar, ka tafi ka bani guri dan Allah"
"Ni zaki kalla ki bawa dubu ɗari biyar, ki riƙe kayarki amma ki saurari abunda ze biyo baya"
"Kaga dan Allah karmuje ga haka, ka zauna muyi magana, Alƙawari da mukayi fa har yanzu wannan kuɗi basu samu ba, ya kake so inyi ne"
Shu'aibu yace "ƙarya kike, shakrar ki nawa a gidan nan, kima nufin duk zamanki a gidan nan baki samu komai ba, aiko duk jikina kunne ne bazan yadda ba Wallahi"
"Wai kai baka san 'yarsa itace ta hana ruwa gudu ba,? dan Allah karka ɗagamin hankali ka bani account number, zan samaka million ɗaya"
Shu' aibu yace "ashema bani da hankali, kusan shekara goma sha, ko ficika bata shiga hannuna ba kice zaki ban million ɗaya, baki nemi sulhu ba tabbas, kuma abunda ze biyo baya baze miki daɗi ba na gaya miki"
Hajiya Halima tace "kaga shua'aibu bazaka zo ka ɗagamin hankali ba Wallahi, yanzu ma daka zo a wani zullumin bala'in nake, ko dai ka haƙura da abunda zan baka kokuma ka haƙura, dan ban san ya kake so inyi ba, yarinyar daza'a karɓi dukiyar a hannuta ba'a san inda take ba, shi kansa me gidan ba'asan a inda yake ba, komai yana nema ya jagwalgwale min, kuma kazo kana gayamin maganar banza, dan Allah ka sauraramin"
"Naji zan saurara miki, amma nima ki saurari abunda ze biyo baya, kin sanni kin sam abunda zan iya aikatawa, wallahi nima zan baki mamaki, zan ƙara miki matsala akan wadda kike ciki, sannan ki gayawa 'ya' yana ina nan zuwa in ɗauke abuna"
"ka ɗauki wa? Can kaje ka nemi 'ya' yanka, karka ƙara ce mana 'ya' yanka, can ka nemi 'ya' yanka malam" Ramlah da ta fito daga part ɗinta take faɗa.
Shu'aibu yai murmushi yace "Allah sarki yaro yarone, Halima na fuskanci wannan yarinyar halina ta ɗakko, Rawar kanta da zafin kanta kamarni, amma ki gargaɗeta in ba haka ba, abunda ze biyo baya ke dasu baze muku daɗi ba Wallahi"
Mummy tace "ke Ramalh, wannan fa mahaifinku ne, kidena gayamasa maganar da kika ga dama kinji ko?"
"wallahi karki ƙara haɗani dashi, can ya nemi yaransa ba dai niba, uwar meya maganta mana a rayuwar daze zo yana wani mu 'ya' yansa ne, dan Allah mu yayi ya wuce ya bamu guri, kidena ssaurarensa ki fita a samo mafita akan ɓatan Anwar, idan ba hakaba kika biyewa wannan koɗaɗɗen mutumin, komai ze iya faruwa, Anwar ze iya tona miki asiri idan wannan be tona miki ba"
Zaro ido shu'aibu yayi yace "Anwar ɗin ne ya ɓata? Halima dagaske ne abunda nakeji?"
A fhaace tace "Eh gaske ne shu'aibu, duk akan a samu kuɗin nan, Anwar ya gudu ya bar gidan nan, se me ina nikaɗai naita ɗawainiya dasu ina ruwanka dasu, dan Allah ka barni inji da kaina"
"zan barki kiji da kanki, zan tafi a yanzu bazan kuma dawowa ba se a lokacin daya dace, ko kuma in cigaba dayi miki aike, zan baki account number na, ina buƙata kuɗi naira million hamsin, nan da kwana bakwai idan baki turamin wallahi, wallahi abunda ze biyo baya baze miki daɗi ba"
Ramlah tace "ai se kazo ka ƙwata ai, tunda kai ka tara mata"
Aikuwa ya shammaci Ramlah ya wanketa da mari, jikinsa na rawa kamar wanda aka kaɗawa gangi yace "da uwarki nake magana, ba dake ba ko ita lokacin da tana hannuna idan ina magana tana magana, tasan me yake biyo baya, idan kin manta dan lokacin kina ƙarama gara in tuna miki, Halima ki gargaɗeta ki gaya mata abunda zan iya, idan na kuma zuwa gidan nan, taimin tsinin baki sena yagalgalata a gurin nan, kuma nan ba gidana bane, zanzo in ɗauke ku, lokaci yayi da zan mori abunda na haifa nima"
Ramlah ta zabura zata yi magana, amma Hajiya Halima ta dakatar da ita, ta hanata, shi kuma ya juya ya fice yana huci yana sauke numfashi.
Tunda garin Allah ya waye, Widad take nan nan da Yusuf, se wani lallaɓashi take tana tarairayarsa, daya tashi da safe, idanunsa sunyi ja sosai sun ɗan kumbura, saboda kukan da yayi jiya, da ta kalli Yusuf se taji kamar ta fashe da kuka, idan ta tuna labarin daya bata, da irin wahalar da ya sha shida mariƙiyarsa, sun sha wahalar rayuwa sosai.
Ta ɗakko kunu, ta dinga ɗebowa tana bashi a baki, Yusuf yace "yau kuma nina koma jaririn? Se wani lallaɓani kike?"
"ba dole in lallaɓaka ba, nima kana lallaɓani ai, ko baka sone?"
Yace "ina so mana, ai gara kiyita lallaɓanin"
Ta dinga bashi Abinci a baki, yana ci yana lumshe ido, dan dauriya kawai yake, har yanzu zuciyarsa babu daɗi, gaba ɗaya a cunkushe ransa yake, amma ya daure yana murmushi dan kar ya ɗaga mata hankali.
Ta ɗago ido taga ya ƙura mata ido yana kallonta, ta miƙa masa kofin kunun bakinsa, kawai taga idonsa ya cika da ƙwalla, tasan dauriya yake kawai, amma ransa babu daɗi.
Ta ajiye kofin tace "Yoseef menene kuma?"
Girgiza mata kai yayi, alamar bakomai, "da komai Yusuf menene ke kuma?"
Kawai ya lumshe idonsa ya bawa hawayen daya taru a idonsa damar gangarowa, ɗaya bayan ɗaya suna zarya a fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya tallefe fuskarsa, hawaye na cigaba da bin fuskartasa.
Itama hawayen ne ya shiga zubo mata, tasa hannu ta janye masa hannayen daya rufe fuskarsa, ta janyo kansa jikinta, tana son rarrashinsa amma tama rasa me zata ce masa, aikuwa ya kwanta sosai a jikinsa, yana kuka hadda sheshsheƙa, kai kace wani ɗan yaye ne.
"Haba Yoseef, habe Yoseef is ok please, kana son wani ciwon ya kama min kaine? Idan ciwo ya shige ka ya zanyi, baka son kaga Lokacin da zamuyi building namu family ɗin, Allah yayi maka gata daya baka rai da lafiya Yusuf, Insha Allah zan share maka hawayen ka a rayuwa, bazan ƙara bari a maka gori ba, komai ya wuce ai, ya zama tarihi tunda ba shiri duk da kowanne mu ya fidda ran samun abokin rayuwa amma Allah ya haɗamu ya ƙaddara aurenmu, ba tare da mun shirya ba, tabbas ƙaddararmu tana kamanceceniya da juna, ni wallahi jinake dama ni na samu uwar riƙo kamar ummanka, Yoseef kana kallo ni ga gatan ga komai, amma inaji ina gani aka maidani mahaukaciyar ƙarfi da yaji, aka haɗani da larurar Ƙwaƙwalwa da zuciya, ga rashin kwanciyar hankali, ina so kamanta da wannan abun kamar be faru ba, kodai tunanin Salman kake ne? "
Duk da kuka yake, seda ya ɗan murmusa sannan ya girgiza kai yace " inda ke babu macen da Yusuf ze tuna"
"to ina son ya zamana in dani, babu damuwar da yuzaraef ze tuna"
Yace "to Allah yasa hakan"
"Ameen ya Allah, Amma ai yanzu zaka yadda mu koma gidanmu ko?"
Yusuf ya girgiza kai, alamar a'a, Widad tace "saboda me?"
"Saboda ke nake so ba dukiyarki ba, ko abunda kika mallaka, dukiyarki ta kice mallakinki ce, dan haka zan sai mana gida daidai ƙarfina, in cigaba da aikina da sana'ata in riƙemu, ai zaki zauna dani da talaucina ko, duk abunda zan baki zaki karɓa ki zauna dani? "
Yai maganar yana kallonta, tai murmushi tace " na zauna da kai a ɗakin ƙasa, duk abunda ka banj na karɓa naci, kuma muke rayuwar mu a haka, ina ne zaka kaini bazan bika ba, amma gaskiya ni bana son aikin nan naka"
"Saboda me?" ya tambaye ta
Ta ɗanyi shiru sannan tace "Yoseef, DSP Bashir shine Abbanka da aka kashe saboda case ɗin Ammina fa"
Yusuf yace "na sani"
Kallonsa tayi tace "ya akayi ka sani"?
Yusuf yace "tun lokacin ina miki aiki, na nake bincike akan statement ɗin kashe mahaifina da akace 'yan fashi sunyi, inata tunanin abun, kina bani labarin ki Nagano musababbin kisan Abba, kuma na gane dalilin da yasa da najewa Umma da batun aiki a gidanku, take cemin bata so, dukda bamu taɓa hirar da ita ba"
Widad tace "Amma ya akayi baka gayamin ba?"
Yai murmushi yace "a gurinki na koya ai"
"Yoseef Kayi haƙuri kaji, ka dena koke koken nan hak, kana karyamin zuciyata sosai, ka dena kuka kaji ɗan gidan Umma"
Ya ɗan ja kumatunta yace "tom insha Allah zan dena"
"ka dena ko zaka dena"?
"Nima ban sani ba, amma ina fatan Allah ha haɗani da wani, wanda yake yana da alaƙa da iyayena, ko 'yan uwana komai talaucinsa ina son in samu in ga wani daga dangina, koa yake is not possible, tunda babu wanda ya sanni a dangin nawa, kuma nima ba wanda na sani "
Widad tace " bazaka dena kukan ba kenan? Ba gani ba, ba nace maka zamu haɗa namu family ɗin ba, mu haifi yara ga Daddy, ga Umma gamu da 'ya' yan da zamu haifa, ba Family ya haɗu ba kenan?"
Yusuf yace " bazaki gane ba Baby, anyway nagode sosai da kulawarki, banjin wani bayan Ummana ya taɓa min rarrashin daya shigeni kamar wanda kikamin, ban taɓa zama nayi makamancin hirar nan da wani ba, duk alaƙata dashi kuwa, ko Umma bama wannan hirara da ita, balle wani saboda kar in ɗaga mata hankali, taga hawayena dan kar taga kamar ta gaza da kula dani ne, dan nasan tabbas idan na saɓamata Allah baze barni ba, ta shayar dani ta bani duk wata kulawa ta uwa da ɗa, kece kawai nayi wannan hirar dake, shiyasa I express all how I feel in my heart, kuma naji daɗin gayamikin da nayi, naji na rage kaso mafi yawa na damuwata thank you sweet heart"
"Allah sarki mijina, kayi haƙuri kaji, tamu jarabatar kenan, amma ko abokinka Abbas baka taɓa yiwa zancen ba?"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a ban taɓa yi masa ba, amma me yasa kika tambaya?"
Widad tace "saboda na tsane shi, gaba ɗaya siffar munafukai ce dashi haushi yake bani, shiyasa nasa aka rabaka dashi, aka maida shi nesa da gurin aikinka"
"Amma Widad meyasa? Abokinane fa ya bani gudunmuwa sosai fa a harkar aiki da sauran mu'amalar rayuwa"
Widad tace "Oho nidai na tsane shi, kuma wallahi idan ya kuma raɓarka sena ɗaureshi"
Cikin mamaki ya kalleta yace "but Baby why"
"Z" ta bashi amsa tare da ƙura masa ido, alamar bata son zancen.
"Yanzu za kamin Addu'ar in samu Babyn, kokuwa har yanzu baka son in haihu da kai"
Ya girgiza kai yace "Ai magana ta ƙare, tunda har kika amince dani dukda kinji labarina, Allah yabamu masu albarka Babyn Yoseef"
Washe baki tayi tana murmushi, ta rasa mema zata yi dan murna, kawai ta rungume Yusuf ta haɗe bakinsa da nata tana kissing ɗinsa, Yusuf ya rungumeta shima yana kissing ɗinta suna murmushi, daga nan kuma aka shiga wani bigire daban ..... (Nikuma na fece 🚶 🚶 🚶)
Bayan fitar shu'aibu Halima a fusace ta hau Ramlah da faɗa
"Ramlah kinyi haukane? Koba komai mutumin nan mahaifin kune? Kin san hatsarin dayake dashi kuwa? Ko dan kuna ƙanana na bar gidansa baku san irin halayensa ba, shu'aibu da kike ganinsa bashi da imani, bashi da tausayi tsohon ɗan dabane gawurtacce makuwa kuma matsafi, idan kika zaƙe wallahi ze iya kauda ke, dan akan rigimar gonar gado har ɗanuwansa uwa ɗaya uba ɗaya ya kashe, dan haka ki kiyayi wannan tsinannen bakin naki, wanda besan yakamata ba kina zaƙewa dayawa, tynda kika ga ina binsa sannu sannu, nasan hatsarin dayake da shine, idan kinƙi ji bakyaƙi gani ba, idan kin gadama ki gyara idan bahaka ba, matakin daze ɗauka baze mana daɗi ba dagani harku"
Ramlah tace "wallahi, wallahi ba ruwana da hatsabibincinsa, tunda ya haifeni ze gane ya haifi uwarsa a hatsabibanci, harni ze ɗaga ƙazamin hannunsa duk faso ya mara? Zan nuna masa ya haifi 'yar da zata kawo ƙarshen hatsabibancin da yayi a rayuwarsa, besan wacece niba ze gani"
"Ke rufemin baki, bana son cika baki kin san shi rashin jin da yayi"
Ramlah tace "shi ta shafa bani ba, but he must pay for what he did"
Tai gaba fuuu tana ci gaba da masifa.
Hajiya Halima ta girgiza kai tace "Amal ɗakko mayafinki, kizo ki rakani gurin Alhaji Haruna, zan kira shi a waya yanzu, idan yana nan muje mu sameshi ayi maganin wannan matsalolin"
Amal tace to, ta tafi ɗakko mayafi a ɗakin ta.
Gidan Alhaji Haruna sukaje, aka musu iso part ɗinsa, yana zaune yana kallon labarai a tashar Al Jazeera.
Suka samu guri suka zauna, tunda suka shigo yake bin Amal da kallo, kamar tsohon maye.
Hajiya Halima tace "gurinka nazo"
Yace "yaukuma da wacce kikazo? Danke kullum cikin rigima kike"
Hajiya Halima tace "nikam duk a bar wannan maganar, yaron wajena daya ɓata ba sace shi akayi ba, guduwa yayi daga gida, kuma baun takaicin shine, ya gano abubuwan da nake aikatawa, dan hara takadda ya bari"
Alhaji Haruna yace "Halima kina me haka ta faru? Garin yaya yasani, wannan yaron naki me kama da ustazai kin san ze iya tona mana asiri fa"
Halima tace "hmm wallahi ban san yadda akayi ya sani ba, shekara Goma ina ƙumbiya ƙumbiya muna wannan harƙallar tare, amma be sani ba, ban san wane munafikin ne ya gaya masa ba, kuma ma ba wannan ba ɗazu fa uban 'ya' yana yazo"
Yace "Wake nan?"
"Shu'aibu mana, koka manta bisa yarjejeniya da aka yi dashi ya sakeni, kuma tunda muka rabu, ba'a cika masa Alƙawarin ba, dan haka yazo yana barazanar karɓe yaransa, kuma wai sena tura masa wasu maƙudan kuɗaɗe koya tona mana Asiri"
Alhaji Haruna yace "toki tura masa kuɗin mana, ko kin fi son asirin naki ya tonu?"
Hajiya Halima tace "wace irin maganace wannan, kafa san hatsarin da mutumin nan yake dashi fa"
Alhaji Haruna yace "lallai akwai matsala gagaruma makuwa, amma yanzu abunda za'ayi ki saurareni, zamuyi magana dasu, yadda aka yanke zan miki magana"
Hajiya Halima tace "to shikenan, amma dan Allah kuyi maganar da wuri"
Yace "shikenan, karki damu wannan ma yarinyar kice ne? Naga harta fi yayarta kyau"
Hajiya Halima tace "eh itace 'yar auta ta ai, daga Ramlah se ita"
"Masha Allah, yaran naki masu kyau, sunfi kama da yayarta, Anwar ne ban san kamannin wa yayi ba"
Hajiya Halima tace "kamanin Ubansa yayi, wasu lokutan kuma dani yake kama"
Alhaji Haruna yace "A' a baya kama da shu'aibu sam, kamarsa daban shima"
Hajiya Halima tace "Amal jeki falo ki jirani kinji"
Amal ta miƙe tana haɗe rai, saboda kallon da Alhaji Haruna yake mata.
Tana fita Hajiya Halima tace "Anwar fa ubansa daban shima, dana rabu da mijina na fari akwai cikinsa ko wata ɗaya beba na auri shu'aibu, na haifeshi a gidansa amma ba shine ubansa ba"
Alhaji Haruna yace "ikon Allah, to waye nasa uban?"
"kaga a bar maganar nan kawai, ba wanda na taɓa gayawa se kai duk yadda kukayi se muyi waya"
Ta miƙe ta fito, ya biyo bayanta yana sake bin Amal da kallo, kamar wani maye.
Saleh yayi 'yar siyayyar daya saba yi, ya shirya domin kaiwa su Widad ziyara, ya tafi tasha da nufin ya hau mota, da yake tafiyar dare yake yi in dai zeje garin dasu Widad suke, ya zuba kayansa a motar haya, ya zaga banɗakin tasha domin ya kama ruwa, yana fitowa yaji an shaƙa masa wani abu anyi sama dashi, daga nan be sake sanin inda kansa yake ba se......
0 comments:
Post a Comment