*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
FREE PAGE 5
Da sauri Baba Munkaila ya juyo yana muzurai don har lokacin banda huci babu abin da yake yi. Tun kafin ya ƙaraso Dubu ta riƙe hannun Yaya babba tana bata haƙuri, don duk cikin gidan babu wanda Dubu take tsoro kamarsa. Zuciyar Hajiya Nafisa fes don ko ba komai ta san zai gyarawa Dubu zama, yana ƙarasowa ya ce, "Inno ga ni." Yaya babba ta kalli Dubu da ta yi wuri-wuri sai zare ido take yi saboda gari banza ma Baba Munkaila ba ya raga mata ina ga yau da yake cike da haushin kashe masa zabbinsa.
Yaya babba ta ɗauke kanta daga wurin Dubu tana cewa, "Munkaila don Allah ka raba ni da yarinyar nan Dubu, ni take son yi wa ɗiban albarka. Wai don Allah meye dalilin da ya sa ba za ka tafi da ita sashenka ba..." Tun bata gama magana ba Baba Munkaila ya zuba mata ranƙwashi a ka. Ai kuwa ta daka uban tsalle ta faɗa uwar ɗaki. Ganin haka ya sa Yaya babba ta sallame shi amma sam ba haka Hajiya Nafisa ta so ba.
Cikin Dare.
Tun dare bai gama tsalawa ba ƴan bijilanti suka yi wa gidan Marigayi mai carbi dirar mikiya, hannuwansu ɗauke da gorori sai fitilun da suke haskawa masu ɗan karen haske. Ban da haske-haske babu abin da suke yi, da sun ji motso ko na dabbobin gidan ne za ka ga sun haske sun nufi wurin da gudu. A wannan ranar ma Dubu da wuri ta yi kwanciyarta don ta samu damar gabatar da aikinta idan ta farka ciki dare. Sai dai wannan karon tsoro ne mamaye a zuciyarta saboda irin gororin da ta gani a hannuwa su Duna da Kuraye. Tana son suma ta nuna musu iyakarsu amma tana shakkar ta inda za ta ɓullowa lamarin saboda sun zagaye ko'ina ga fitilun da suke haske-haseke da su.
Dabara ce ta faɗo mata don har sai da ta murmusa a fili saboda mugunta. Ta shi ta yi a hankali cikin sanɗa ta ɗauko butar Yaya babba sai da ta zo daidai kan Barira wacce take kwance da Ƴarta ta tsiyayawa yarinyar a jikinta , idan ka ga yanda ta yi sharkaf sai ka rantse da Allah fitsari ta yi. Ɗaga rigarta ta yi ta zaro guntun likkafanin da ta ɓoye sai ta ɗaura a ƙafar Baraka ƴar wurin barira. A hankali ta fara jan ƙafar yarinyar har sai da ta kaita ƙofar ɗaki, ta koma ta riƙa jan ƴaƴan mutane tana kaisu bakin ƙofa sai da ta gama sai kawai ta haɗa ƙafafuwa su ɗai-ɗai ta riƙa ɗaurewa da likkafani. Sai da ta kai kusan yara biyar bakin ƙofa sannan ta janyo tsintsiyar kwakwa ta tsinka ta riƙa bi tana kartawa iyayen da yaran, da sauri ta bi gefe ta wurin da yaran suke kwance a bakin ƙofa ita ma ta yi luff ta tura ƙafarta ciki tasu. A hargitse mutanen ɗakin suka tashi carko-carko suka fara wawurar fitila, Barira na haska fitilarta a ka hango yaran suna firƙai-firƙai suna koke-koke. Kowacce da sauri ta je ta rarumi Ɗanta ai suna ganin Likkafani a ƙafar ƴaƴan kowa ya fara shan jinin jikinsa.
Maraƙisiyya ta dubi Barira ta ce, "Don Allah Barira me idona yake gane mini kamar likkafani." Barira dama bakinta ƙunshe yake da magana don dai tana tsoron furtawa a samu matsala, ai kuwa tana jin haka ta yi farat ta ce, "Lashakka fihi wallahi likkafani ne don Allah ku taimaka mana fatalwar nan za ta ja mana yara." Jin wannan maganar ta Barira da sauran hayaniyar mutanen ɗakin ya sa Ƴan bijilantin suka tattaru a ƙofar ɗakin Yaya babba suna tambayar ba'asi. Dubu na ganin haka ta zari buta tana matse-matsen ƙarya wai fitsari take ji, da sauri Yaya Babba ta yi farat ta ce, "Dubu ki raba ni da wannan ƙaddararran fitsarin da za ki yi yanzu, so kike ki fita fatalwar nan ta yi gaba da ke?" Dubu ya sake zabura tana buga ƙafa ta ce, "Wallahi fitsarin ya matse ni."
Barira ta wurga mata fo ɗin Sa'ima ɗayar ƴar tata ta ce, "Maza hau fo ki yi amma babu in da za ki." Wata uwar harara Dubu ta watsa mata ta ce, "Allah ya sawaƙe a gabanku da su Duna zan yi fitsarin ni dai wani daga cikinku ya raka ni." Haushi ya ƙule Yaya babba ta zabga mata carbinta da bacci ya kwashe ta yana hannunta ta ce, "Wallahi idan kin ga fita ta ko ƙofar ɗakine ba Mai jama'a ya haife ni ba." Dubu ta dubi Kuraye ta ga yanda yake ta Muzurai yana hange-hange shi a dole ga wanda yake fagen fama. A zuciyarta ta ce, "Wallahi kuma sai kun kwashi rabonku dan ubanku." Ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka ta ce, "Inna don Allah ki ce Duna ya sa ɗaya daga cikin yaransa ya raka ni." Duna na jin haka kansa ya ƙara fasuwa don a duniya babu abin da Duna yake so yake ƙauna sama da a fasa masa kai yana fagen aiki. Don idan ya saka uniform ɗin su na Ƴan bijilanti har ji yake ya fi wani Major general ɗin na Sojoji. Don haka cike da izza ya fara buɗa kafaɗa ya ce, "Babu damuwa muje zan raka ki. Ba fatalwa ba ko Aljan ne idona idonsa sai na ɗaye masa fata daga ƙafa har ƙeya."
Dubu na gaba ya yi yana haske mata fitila suka fita daga cikin ɗakin, sauran yaransa kuma suna tsaye a bakin ƙofar sai dai gabaɗaya yanzu sun kasa taɓa likkafanin da suka gani yashe a gefe wanda ake ce musu fatalwar ce ta ɗaure ƙafafuwan yaran da shi.
Sai da suka yi ta fi me ɗan nisa da yake banɗakin na da nisa da wurin ɗakuna kamar yanda al'adar ginin ƙauye yake. Suna ratsewa ta bayan ɗakin Marigayi Dubu ta zabga ihu tana yin gefe da sauri haɗe da faɗin, "Wayyo Allah hannuna." Durƙushewa ta yi a ƙasa tana murza hannu haɗe da yamutsa fuska. Duna ba ƙaramin tsorata ya yi ba don idan idonsa ba gizo yake yi masa ba gani ya yi kamar wurgar da Dubu aka yi gefe. Gyaran murya ya yi yana kallon hagu da damansa a ɗan tsorace, amma sai ya basar don kar Dubu ta fahimci tsoron da yake ciki ya ce, "Ke Dubu lafiya, me ya samu hannun naki?" Dubu da ke satar kallonsa ta gefe ta sake shafa hannu ta ce, "Wani abu ne mai kaifi kamar farata na ji yana niyyar fisgata daga baya sai ji na yi an hakaɗa ni."
Wata irin karta cikin Duna ya yi nan take gumi ya fara neman game jikinsa amma sai ya ɗaga gorarsa yana ƴan haske-haske ya ce, "Yana daga wurin ina." Kusurwar ɗakin Marigayi mai carbi ta nuna ta ce, "Daga can ne." Duna ya coge daga wurin da yake ya ce, "Wuce mu je ki nuna min to."
Dubu tsabar mugunta ji ta yi dariya na neman suɓuce mata don haka ta miƙe sai kuma ta fara tafiya a dudduƙe tana riƙe ciki alamar fitsari ya matseta. Ganin haka ya sa Duna ya ce,
"Fitsari ko? Wuce muje idan mun dawo ma duba koma meye." Shima da biyu ya faɗi haka saboda a lokacin da za a kuma yin wani ƙwaƙƙwaran motsi mai ƙarfi yana iya fita da gudu. Suna zuwa ta shiga banɗaki ta yi fitsari ta fito don kafin ta fito tuni Duna ya ƙagu saboda gani yake kamar wani abu zai kama shi. Suna tafe har suka bar wurin banɗakin suna yin gaba Dubu ta buga tsalle tana cewa, "Duna kanka ga shi nan zai warci kanka." A guje Duna ya zuba yana ƙwalla ƙara haɗe da dafe kansa, don fitilar hannunsa sai da ta yi tsalle uku sannan ta tarwatse a ƙasa, batiran ciki suka yi gabas, kan fitalar ya yi yamma. Gangar jikin fitilar ta yi arewa gorar hanunsa ta yi Kudu. Dubu na ganin haka ta rufa masa baya sai dai tun a tsakar gida suka raba hanya don tuni Duna ya dafe katanga ya dire yayin da Dubu ta yi cikin ɗakin Yaya Babba a guje, Yaran Duna na ganin haka suma suka zuba a guje kowa ya kama gabansa. Su Barira da sauran mutane ɗakin Yaya babba suka hau gwara kan ƙananan yara aka rinƙa ƙwallo da su kamar yanda ake gara ƙwallo a filin wasa. Cikin ɗakin ban da kukan yara da ihun manya babu abin da yake ta shi a ciki.
Daga ɗakinsu Inna Furai suma tashi suka yi don tun lokacin da suka ji ihunsu Barira, gabaɗaya suka watssake. Lantan ce ta fara miƙewa a zabure mai bin bayanta Inna Furai sai kuma ragowar mutanen ɗakin kowa ya yi tsuru-tsuru. Jin maganar ƴan bijilanti ne ya sauƙaƙa musu damuwar da suke ciki. Sai dai ihu da gudun Duna ya yi ya fi komai kaɗa musu ciki don, a wannan lokacin sun gama sadaƙƙarwa da indai Fatalwar ta fafake su babu mai tsira daga hukuncinta. Lantan hawaye ne ke zuba a kan dakalin fuskarta ga wani irin kaɗawar ciki da take fama da shi. Cikin kuka ta dubi Inna Furai ta ce, "Furaira sai da na gaya muku ku bar ni na tafi amma aka hanani tafiya ni da zuri'ata, yanzu don Allah idan tsautsayi ya ritsa da ni fa? Maganar gaskiya idan na mutu ta wannan hanyar ranar gobe ƙiyama sai an yi mana hisabi da Garba don shi ne sila." Ta ƙarasa maganar tana son jin ta bakin Inna Furai amma sai gani ta yi ta zura mata ido tana kallo, Lantan dafa mata hannu ta ce, "Furaira ko bakya ji na ne?" A wannan karon ma gani ta yi Inna Furai ta sake zura mata ido tana kallo ko ƙiftawa bata yi ba. Lantan na jijjiga Inna Furai sai gani ta yi baya luuu!
Lantan ta zuba kabbara haɗe da cewa, "Innalillahi yau me nake gani haka jama'a ku taimaka mana wallahi sun fara ta kan Furaira." Nan fa suka ƙara ruɗewa sai Mardiyya ce ta yi ƙarfin halin yayyafa mata ruwa don ta fi zargin Inna Furai suma ta yi. Inna Furai na farfaɗowa suka fara jero mata sannu sai ji suka yi tana amsawa da,
"Ashhadu'anlla'ilaha'illallahu, wa'anna Muhammadarrasulillahi."
Lantan ta yi sauri ta ce, "Furaira me kike faɗa ne?"
Inna Furai da bata cikin hayyacinta ta ce, "Wa saumu ramadana. Amma Hajji kam sau ɗaya na taɓa ziyarta." Lantan rasa abin yi ta yi sai kawai ta fashe da matsanancin kuka tana yi tana fatar majina ta ce, "Tun da Uwata Mai carbin Malam ta haife ni ban taɓa ganin ƙadaddararrun ranaku kamar waɗannan ba kai jama'a yanzu Furaira daga suma sai hauka." Inna Furai bata san me ake yi ba don haka suka ƙarasa ganin daren har zuwa asuba Inna Furai na yi musu sumbatu.
Washegari.
Tun asuba da mazan gidan suka fito aka sanar da su abin da yake faruwa, don tun da suka wayi gari da ganin gororin ƴan bijilanti da fitilar Duna sai kuma takalmin ɗaya daga cikinsu, suka tabbatar da babu lafiya. Da aka sanar da su abin da yake faruwa wasu daga cikin mazan zuciyarsu ta fara aminta fa zancen fatalwar, saboda dama da Auwalu da Baba Sule tuni suka aminta da abin da aka sanar da su. Ba shiri aka ɗauki Inna Furai aka wuce da ita asibiti, saboda jikinta wani irin zafi da ya yi ga sumbatu ta take yi ba kai ba fasali.
Kaso casa'in da tara na mutanen da suka halarci gidan mutuwar a wayewar garin duk suka ɗaɗe kowa ya kama gabansa. Lantan dama ko sallama ba ta yi musu ba tana idar da sallar asuba ta fice ko jakar kayanta bata ɗauka. Ta so ta yi wa Autalliyarta magana ta ɗauko Salihu su tafi amma gani take ko ya ta ƙara ƴan sakanni komai zai iya faruwa. Wannan lamarin ba ƙaramin daɗi ya yi wa Dubu, don gabaɗaya gidan abin da ya rage daga ƴaƴa sai jikokin gidan. Wasu daga cikinsu har sun yi niyyar tafiya aka ce su bari a ga yanda jikin Inna Furai zai yi. Yaya Babba ta sake jaddadawa ƴaƴanta tana son zama da su idan komai ya daidaita akwai maganar da za su tattauna mai muhimmanci.
Wannan zaman da aka ce za su yi ba ƙaramim ɓata ran Hajiya Nafisa da Hajiya Fauziya ya yi ba. Ita kuwa Hajiya Rahama ko a jikinta damuwarta ɗaya fargabar da suke ciki ta rashin kwanciyar hankali.
Asalin Zuri'ar Mai Carbi.
Asalinsu mutanen garin Kano ne cikin ƙaramin ƙauyen Ɗangwaro dake jihar Kano. Mai carbi Su biyar ne a wurin Mahaifi da Mahaifiyarsu. Maza uku mata biyu amma acikinsu saura Mutum Uku rayayyun. Yaya Idi, Malam Munzali sai Lantan wacce dama ita ce ƴar autarsu. Sunan Yaya Babba Aisha wacce aka fi yi wa laƙabi da Indo. Ƴar uwar Marigayi Mai carbi ce ta fannin Mahaifinsa ƴar maza zar suke, an yi musu auren zumunci suka zauna anan cikin garin Ɗangwauro.
Inna Furaira ita ce matarsa ta biyu ita ma ƴar uwarsa ce ta ɓangaren Mahaifiya, ita ma auren zumunci aka yi musu sakamakon Mahaifiyar Mai carbi ta nuna itama dole ya auri ƴar ƙaninta tun da ya auro ƴar ƙanwar Mahaifinsa. Wannan dalilin ya sa aka sake yi masa aure bayan yin aurensa da shekara biyu a lokacin Yaya Babba tana goyon Baba Abubakar.
Ƴaƴan Yaya babba Shida Maza biyar Mace ɗaya. Akwai: Baba Abubakar, Baba Munkaila, Baba Sule, Baba Shehu, Baba Aminu, Baba Adamu sai Hadiza. Inna Furai tana da ƴaƴa biyar akwai: Larai, Baba Sabi'u, Baba Musa, Baba Sha'aibu sai Baba Auwalu.
Gabaɗaya waɗannan ƴaƴayen kowanne yana da tashi zuri'ar, daga cikin waɗanda ba sa cikin gidan gandun, akwai Baba Abubakar Mazaunin unguwar Na'ibawa, kuma lakcara (Lectural) ne kwalejin Sa'adatu rimi. Sai Baba Adamu.
Baba Abubakar yana da mace ɗaya Hajiya Nafisa da yara Huɗu: Aseem, Nabila, Husna da Humaira. Aseem da Humaira sunan Mai carbi da Yaya babba suka ci amma ana kiran Humaira da Ummi. Baba Adamu yana zaune a unguwar Gyaɗi-gyaɗi likitane yana aiki a asibitin Aminu Kano. Yana da mata biyu Hajiya Rahama ita ce Uwar gida tana da ƴaƴa biyu Fahad da Fatima sai Hajiya Fauziyya mai ƴaƴa uku Halifa mai sunan Marigayi Mai carbi, Zainab sai Hafsa. Sai Hadiza da Larai da suke aure a wasu gidajen.
Tsayawa zayyano wannan ahalin Marugayi mai carbi ba ƙaramin ɓata lokacin mai karatu bane.
Dawowa Labari.
Kimanin sha biyun rana da ƴan mintuna, zaune yake a cikin motarsa yana ƴan danne-dannensa. Ya kai kimanin mintuna ashirin da faka motar amma yana ciki bai fito ba. Ɗaiɗaikun yara ne suka fara zagaye motar suna kallo wasu daga cikinsu har da masu shafawa. Tsirarin ƴan mata sa'annin Dubu har da masu kallon fuskarsu a jikin mudubin motar, ganin suna niyyar yi masa ɓarna ya sa ya zuge galashin motar. Wani sihirtaccen ƙamshi ne ya fito daga cikin motar nai sanyin ƙamshi. Ƙamshinsa ne ya ankarar da su akwai mutumin da ke cikin motar. Kallon su ya fara yi kowa ya shiga taitayinsa sakamakon ganin fuskarsa ko ɗigon murmushi babu. Mugun kallon da ya wurga musu ne ya sa kowacce daga cikinsu ta kama kanta, sum sum sum suka wuce. Gajiya ya fara yi da zaman motar sannu a hankali ya zuro ƙafarsa waje tare da fitowa ya jingina da jikin motar yana ƴan danne-danne a wayarsa. Kakin sojan ba ƙaramin ƙarɓarsa ya yi ba, ya yi kyau matuƙa ga wani kwarjini da yake da shi.
Kasancear mutanen ƙofar gidan sun watse sakamakon ruɗanin da yake faruwa wasu daga ciki kuma sun tafi asibiti wurin Inna Furai.
Lambar mahaifiyarsa ya kira sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗauka. Kamar zai yi kuka ya fara yi mata magana: "Momma don Allah ki zo ki shigo da ni banga su Daddy ba kuma na san gidan cike yake da mutane..." Bai ƙarasa magana ba Baba Munkaila ya ƙarasa wurinsa yana washe baki ya ce, "Wa nake gani kamar Soja? Soja mazan fama saukar yaushe." Zame wayar ya yi yana sosa kai ya ce, "Yanzu na ƙaraso Baba."
"Bismillah mu je ciki mana" Baba Munkaila ya nuna masa hanya. Sai da ya kulle motar sannan suka ƙarasa cikin gida.
Dubu tun a hanya su Kaltume suka tare ta da zancen baƙon da suka yi. Hura hanci ta yi kanta na ƙara girma sannan ta ce, "Wani dogo mai mota baƙa? Yau ma da kayan sojoji yazo ko?" Har rige-rigen bata amsa suke sannan ta tallaɓi ƙwaryar tsakin da ta karɓo ta fara buɗa kafaɗa tana cewa, "Ai shi ya sa nake gaya muku duk shegen da ya kawo raini wallahi haɗa shi da Yaya Aseem zan yi ya ci ubansa. " Tana gama maganar ta yi gaba. Su kuwa kowa ya yi zuru-zuru don basa manta ranar da suka taɓa ganinsa da bindiga.
Dubu cike da ɗoki ta shiga gidan don ko ba komai so take ta riƙa ƙare masa kallo tana ayyana wai shi ma ɗan uwanta ne a matsayinsa na soja. Ita ba shi yake birgeta ba illa kakinsa na soja da sautari idan zai zo garin da su yake zuwa.
Kamar wacce aka wurga tana shiga gidan ta yi ciki da Nabila ai kuwa suka fara faɗa, juyawar da Dubu za ta yi a zafafe ta sheƙawa Aseem garin tsakin da ta karɓo daga injin niƙa. Sai ga Aseem da ke cikin unifom ɗin sojoji har da hankicin ɗin goge-goge ya fito furu-furu kamar wanda ya yi wanka da toka. Gashin kansa har wani tsinin farin garin masara ya yi.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[7/1, 5:59 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
FREE PAGE 6
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels
Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.
Duk wannan abin da ya faru sam Dubu bata lura ba, masifa na cin ta bata san da ta sheƙa wa Aseem garin masara a jiki ba, sai ma uban tsalle da ta buga ta cukumi wuyan Nabila tana kai duka tana cewa: "Wallahi ba za ki daki banza, kwarankwasa dubu sai na koya miki hankali, hegiya tsigi-tsila da ƙafa kamar ta tsinken tsintsiya" Ganin ɗankwalin da ke kanta na niyyar kawo mata cikas ya sa ta fisge shi wurga shi ta baya sai kuwa ya sauka a kan fuskar Aseem, ban da tsami da bashi babu abin da yake tashi a cikinsa. Sai ga kitson kanta ya fito duk ya tuje hatta da tsagar kitson ta haɗe sai furu-furun amosani a saman kan.
Warin ɗankwalin ne ya doki fuskar Aseem har ya shaƙa da ƙofofin hancinsa ya sa shi farkowa daga suman tsayen da ya yi na wucin gadi. Aseem tun da ya zo duniya ba a taɓa yi masa abin da ya fusata shi lokaci ɗaya kamar abin da Dubu ta yi masa, dom shi abin daga haushi ma sai ya koma ba shi mamaki. Bakinciki da ganin yadda mutane suka zura masa ido ne ya ɓata masa rai har ya gagara sanin abin da zai aiwatar don ya wanke masa zuciya. Amma tabbas sai ya koya mata hankali don ya lura har lokacin Yaya babba ba ta ɗora ta a hanyar arziƙi ba.
Duk yanda Dubu ta so nunawa Nabila ƙarshen iyawarta abin ya ci tura don a girme Nabila ta girme ta da kusan shekara huɗu. Gudun kar a kunyatata cikin jama'a ya sa Dubu ta tattara ƙarfinta ta fara wani fisge-fisge kamar mai aljanu tana kai duka ta ko'ina, ai kuwa ta ɗaga ƙafa bisa taautsayi ta harbawa Aseem da ke saƙa da warwara akan irin abin da ya dace ya yi mata. A hassale ya ƙarasa wurinta cikin zafin nama ya fisgi hannunta. Cikin tsiwa da rashin sanin wa ya riƙe ta Dubu ta ce, "Wallahi duk wanda ya riƙe ni sai na yi masa jini da majina dalla ku sake ni wallahi ba za ta daki banza ba." Ai kuwa ya sauke mata mari a fuska, kafin wancen marin ya gama ratsa fuskarta ya sake kifa mata wani marin har sa da ta ga wasu irin taurari na gilma mata. A gigice Dubu ta buga tsalle cikin fitar hayyaci ta ce, "Innalillahi wayyo Baba Munkaila zai kashe ni wayyo! Inno fuskata."
Sauke hannun Aseem ya yi daidai da fitowar Yaya Babba za ta zagaya banɗaki. Da sauri ta saki butar hannunta ta fashe da kuka ta ƙarasa wurinsu, tana shirin riƙe hannun Dubu; Aseem ya sake fisgar Dubu ya nufi hanyar fita da ita. Duk irin kiran da Yaya Babba take yi masa ko waiwayenta bai yi ba bare ta saka ran zai tanka mata.
Duk yanda zuciyar Dubu take a bushe wannan karon sai da hanjin cikin ya kaɗa, tsoro ya mamaye ta musamman ta lura da irin ɓarin makauniyar da ta yi masa da garin masara. Suna zuwa soron ƙarshe ta yi ta maza ta fara ƙoƙarin fisge hannunta tana faɗin:
"Wai ina za ka kaini? Ka sakar mini hannu malam." Idanunsa sun kaɗa jawur saboda ɓacin rai don haka tambayar Dubu ba ƙaramin baƙanta masa rai ta ƙara yi ba. Bai tanka mata ba ya sake fusgarta da ƙarfin tsiya ya buɗe mota ya wurga ta sannan ya buɗe mazaunin direba ya zauna.
Ganin ya tuƙa mota da ya fice da gudun tsiya ya ƙara hargitsa hanjin ciki Dubu, don wannan karon har ta fara bubbuga gilashin motar tana ihu. Can gefen titi ya gangar ya faka motar sai dai uffan bai ce ba. Sai da ya share minti biyar a haka yana jin kukan da Dubu take yi da ɗan ƙarfinta, ya zaro ƴar ƙaramar bindiga ya juya yana ce mata.
"Idan baki rufe mini baki ba zan harbe ki na wurgar da banza a wurin nan." Wata ajiyar zuciya da Dubu ta sauke idan ka ji za ka yi tsammanin numfashinta na ƙarshe ne zai fita. Bata san lokacin da ta haɗiye kukanta ba, ban da raba idanu babu abin da take yi, haɗe da jin wata irin da-na-sanin zuwanta duniya. Saboda ta san da ba'a haifo ta ba babu wata ƙaddara da za ta haɗo ta shi har ya nemi kashe ta da bindiga murus ya wurgar a gefen hanya. Don tun da take bata taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai dai ko idan tana daga moto ta hangota a hannun Sojoji ko ƴan sanda. Amma yau har ita ake yi wa iƙirarin harbewa da ita da rana tsaka. Tana son tambayarsa inda zai kaita amma tsoro ya hanata, tana cikin tunani ta ji ya sake fisgar motar da wani irin matsanancin gudu, ai kuwa ta ƙwalla uwar ƙara tare ta ƙanƙame jikin kujera.
A wannan yanayin suka ƙarasa gidan Mahaifinsa da ke unguwar Na'ibawa. Yana zuwa ya ciro mukulli ya buɗe gate ɗin gidan ya shiga da motar sannan ya buɗe murfin motar ya fisgi hannun Dubu, ai kuwa tana ganin zai shiga gidan da ita ta riƙe ƙofar gate ɗin gidan da sauri tana cewa.
"Wallahi ni ba ƴar iska ba ce da za ka kawo ni gidan nan." Maganarta ba ƙaramin dariya ta so bashi amma ya sake tamke fuska ya ce, "Ni ko ɗan iska ne an gaya miki zan yi iskanci da kucaka irinki?" Yana gama maganar ya sake fisgar hannunta aikuwa ta rungume wani ƙarfe tana cewa, "Kwarankwatsa dubu ba zan shiga ba, dama Inna ta ce ƴan iska ne suke bin maza." Tsugunnawa ya yi cikin ɓacin rai zai yi mata magana, ita kuwa Dubu tuni ta shagala da ƙarewa fuskarsa kallo don tun bayan fitowarsu ta lura da abin da yake jikinsa. Ai sai tsoro ya sake kamata saboda bata taɓa zaton haka garin masarar ya yi masara furfurar da bai shirya ba. Ta maza ya yi ya tsugunna a gabanta don wani tsami ne yake bugar hancinsa, saboda tun da aka yi rasuwa Dubu bata ƙara saka ruwa a jikinta ba. Dama wankanma sai Yaya babba ta yi da gaske take yi to rurumar jama'a ya sa ta basar ta ci gaba da harkokinta. Zaro bindigar aljihunsa ya yi ya ɗora mata akan goshinta nan take kuwa ƙirjin Dubu ya fara bugawa da ƙarfi, da hannu ya nuna mata ƙofa alamar ta shiga Dubu ta soma hawaye tana cewa, "Don Allah ka yi haƙuri idan saboda na zuba maka garin masara ne. Wallahi ban kana kusa ba."
Idan ka ji yanda Dubu take magana a ladabce za ka rantse da Allah mutuniyar kirki ce. Iya nadama Dubu ta shige ta don ta gama tsorata gabaɗaya, amma duk da haka bata jin za ta bi Aseem cikin gidan saboda ba za ta taɓa manta Baraka da ta yi ciki ba aka riƙa tsangwamarta ƙarshe sai sayar da gidansu Mahaifinta ya yi suka bar garin. Ita kuwa idan ta yi ciki ai ta san ko sama da ƙasa za ta haɗe babu wanda zai yarda a sayar da gidan Mai carbi.
"Idan kika bari na ƙirga uku ba ki tashi ba zan baki mamaki." Maganar Aseem ta farkar da ita daga dogon tunanin da ta tafi. Cikin hawaye Dubu ta ce, "Don Allah me za ka yi mini a ciki."
Banza ya yi mata yana buga bakin bindigar a ƙasa a hankali cikin sigar, idan baki tashi ba kin san sauran. Dubu bata yi ƙasa a gwiwa ba ta sake tambayarsa. Bai ɗago ya kalle ta ba ya ce, "Idan kin shiga kya gani."
"Wallahi ko me ka ce zan yi amma ni ba ƴar iska bace." Dubu ta faɗa lokacin da gumi da hawaye ya gama mamaye ilahirin fuskarta zuwa wuyanta.
"Ni ɗan iska ne." Ya bata amsa yana miƙewa a fusace ya fisgi hannun Dubu tana ihu tana fisge-fisge ya wuce da ita ciki. Yana shiga ya datse ƙofar ya wurgar da ita gefe sannan ya faɗa wani ɗaki da ke ɓarin hagu. Dukda gidan ba baƙon Dubu ba ne amma a wannan ranar gabaɗaya bata da nutsuwa. Bai jima da shiga ba ta ga ya fito da wani abu a hannunsa na dama, ɗayan hannun hagun kuma wata ƴar ƙaramar wuƙa ce, ai kuwa ta zabura kamar wacce aka ɗanawa wuta za ta gudu. Fuska a murtuke ya fisgi hannunta ya wuce da ita cikin banɗaki. A wannan karon Dubu duka ta fara kai masa tana cewa.
"Jama'a ku taimaka min zai yanka ni. Kuma ka rabu da ni na ce maka ni ba ƴar iska bace. Wallah idan ka kashe ni na rataya a wuyanka duk zunuban su Inna Furai dana ɗauka kai za a ɗorawa." Suna shiga ya sa hannu ya bige bakinta har sai da ya fashe ai kuwa Dubu ta fashe da wani marayan kuka bai bi ta kanta ba ya sa kilifar aski ya ɗora mata akan gaban goshinta. A zabure ta matsa baya ta ce, "Aski za ka yi..." Idanun da ya zuba mata ne ya sa ta haɗiye maganar ba tare da ta ƙarasa faɗa ba. Ta ci gaba da hawayen baƙinciki da nadama.
"Idan kika sake yi mini magana sai na yanke harshenki da wuƙar nan." Dubu na ji na gani haka Aseem ya sauke mata sumar kanta ban da hawaye babu abin da take yi. Kafin wani lokaci sai ga kan Dubu ya fito ral da shi babu gashi. yana gamawa ya nuna ta wuƙa hannunsa ya ce:
"Wannan da kika gani somin taɓi ne amma matuƙar kika sake shiga hannuna sai na yi miki zanen gobirawa da wuƙar nan a fuskarki." Ganin wuƙar na sheƙi ba ƙaramin razana Dubu ta yi ba, kuma a yanda ta ga babu ɗigon tausayi a fuskarsa ta san zai iya aikatawa don haka ta hau gyaɗa kai hawaye na zuba. Hannunta ya fisga zuwa falo ya sata tuƙin mashin. Dubu tun tana ganin kamar da wasa yake har ta tabbatar da yau sai ya kusa halakata a cikin gidan. Tana ganin ya ciro belt ta shiga taitayinta. Kuka take wiwi saboda yanda ƙafafuwanta suka ƙage, gashi ko nan da cen Aseem ya ƙi matsawa bare ta samu ta zauna ta huta. Tana zama kuma yake lafta mata belt ba shiri za ta sake miƙewa ta tashi tana soshe-soshe.
Sai da ya ga Dubu ta yi lugub sannan ya miƙe ya faɗa banɗaki ya yi wanka.
A wurin Dubu ta zube tana sauke numfashi da ƙyar, ta jera masa Allah ya isa ya fi a ƙirga. Kamshin da ya game hancinta ne ya ankarar da ita dawowar da Aseem ya yi. Ya yi kyau sosai cikin ƙananan kaya, haushinsa ne ya sake mamaye zuciyar Dubu don bata taɓa yadda da faɗar da ake yi akan sojoji mugaye ba ne sai a wannan lokacin. Kan kujera ya zauna sannan ya kirata, da sauri ta ƙarasa wurin ƙafarsa ta zauna. Danne-danne ya fara yi har sai da Dubu ta gaji da zaman sanna ya kalle ta ya ce, "Har yanzu kina nan da rashin kunyarki ko? Inno ta ɓata ki kina shuka tsiyar da kika ga dama. Wallahi daga yau na sake ji ko ganin kin aikata wani abin na rashin ɗa'a gaba hannu da ƙafafuwanki zan yanyanke miki, wannan bakin naki sai na datse shi na ga ta ƙaryar iskanci." Kamar ƙosashen ƙadangare haka Dubu ta riƙa gyaɗa kai tana hawaye. Yana gama maganar ya fisgi hannunta suka fice daga cikin gidan.
Yaya babba na ganin irin marin da Aseem ya yi wa Duba ta zuba salati haɗe da dafa ƙirji, don har jin saukar marin sai da ta ji wani iri a jikinta. Tana ganin fitarsa ai kuwa ta zauna daɓar a wurin ta fashe da wani irin kuka. Hajiya Nafisa ci kanki ba ta ce mata ba, sai ma jin zuciyarta da ta yi ta mata fes saboda ta san tun da ta tabo Aseem ba za ta ji da daɗi ba. Saboda ko su Nabila baya musu ta daɗi bare Dubu da kowa ya shaida fitinarta. Yaya Babba wayarta ta zaro ta miƙawa Hadiza tana faɗin.
"Maza kira mini Garba idan shi ya ɗaure wa wannan fitsararren yaron yake shuka rashin matumci, har ina kiransa yana ji na sai ya mini bayani. Wallahi ba Soja ba yau ko Barek ɗin ce da kansa sai an yi mini iyaka da shi." Hadiza jiki a sanyaye kamar kazar da aka tsamo daga ruwa ta karɓi wayar ta fara lalubo lambar, amma a ƙasan zuciyarta tana ayyanawa irin rikicikin da za a kwasa a cikin gidan.
Baba Abubakar suna hanyar dawowa gida daga asibitin da Inna Furai take kwance har an bata sallama, da yake dama likitocin sun ce damuwa da fargaba ne ya jefa ta a halin da take ciki. Bai yi aune ba ya ji kiran waya. Hadiza na jin an ɗauki wayar ta miƙawa Yaya babba, shi kansa Baba Abubakar tun da ya ga kiran mahaifiyarsu ya ayyana dole akwai abin da yake faruwa. Ɗaukan wayar ya yi da sallama jiki babu ƙwari, Yaya babba ko amsa sallamar sa ba tayi ba ta ce, "Garba! Garba!! Garba!!!" Gabansa na faɗuwa ya amsa sannan Yaya Babba ta ci gaba da cewa, "Sau nawa na kira ka?" Ya amsa mata.
"Sau uku Inno"
"Wallahi tun ban kwashe wa ɗanka falsafar albarka ba ka zo gidan nan yanzu-yanzu" Kansa ɗaurewa ya yi don shi ya manta ma da sun yi magana da Aseem akan zai zo gaisuwa saboda haka ya cewa Yaya babba.
"Inno wa kenan?"
Yaya Babba ta fashe da kuka tana cewa, "Karka zo ka bari idan ya kashe mini jika shi kenan."tana gama maganar ta katse kiran. Da sauri Baba Abubakar ya danna wayar Aseem sai dai ya ji ta akashe don lokacin tuni ya kashe ta saboda ya san dama tabbas za a neme shi.
Wayar Hajiya Nafisa ya kira tana ɗauka ya shiga jero mata tambayoyi, tana jin haka ta saci kallon Yaya babba da ta cika fam sannan ta bashi amsa da, "Ka san dai yarinyar nan Dubu ba kunya gare ta ba, daga zuwan Aseem ta sheƙa masa garin masara. Dama kuma ta cikumi Nabila tun da ta rainata kamar takalmin ƙafarta. Sauran maganar dai sai ka zo." Yana tafe a mota amma gani yake kamar tafiyar bata sauri don ya san lamari ya gama kwaɓewa gabaɗaya amma gyarawa sai Allah.
Yana zuwa ya samu Yaya babba a zaune ban da hawaye babu abin da take yi, a gefenta ya tsugunna ya ce, "Ga ni Inno."
"Garba ka raba ni da wancen mai busasshiyar zuciyar. Wallahi ni an cuce ni da aka tura mini jika aikin soja, dama tun tuni na ce bana son wannan aikin saboda cire musu imani ake yi amma aka ƙi yanzu ga irinta nan. Yaro ya koma kamar basamude haka ya riƙa kifawa yarinyar mari babu tausayi barr imani. Wallahi idan ya kashe mini jika ba zan yarda ba shari'a sai ta kaimu har kotun ƙoli." Sai ta kuma rushe wa da kuka tana ci gaba da cewa, "Saboda Allah me Dubu ta tsare masa da zai riƙa zabga mata mari kamar Allah ya aiko shi. Kana ganin wannan shirgegiyar matar ta min tsaye a ka, ko ta tsawatar masa wa ya sani ba ko ita ta saka shi don na lura ba ƙaunar Dubulliyata take ba. Kaico yanzu yarinyar ko a wane hali take oho." Yaya Babba ta sake rushewa da kukan da ya fi na farko taɓa zuciya.Nan take aka yi wa Baba Abubakar bayanin abin da ya faru, ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Da ƙyar ya samu ya lallaɓi Yaya babba ta rage faɗan sai dai bakinta ya kasa yin shiru.
Bayan wani lokaci suna nan zaune Aseem da Dubu suka shiga cikin gidan, fuskar Dubu duk ta yi zurur-zuru tana tafe tana gwale ƙafafuwa. Gabaɗaya mutanen wurin binta suka yi da kallo, Baba Abubakar rai a matuƙar ɓace ya tari Aseem da kyakkywan mari. Dubu kuwa na ganin haka ta sake ɗangalewa ta rushe da kuka ta faɗa kan Yaya Babba.
Da sauri Yaya babba ta matsa baya tana zaro ido ta ce, "Dubu me nake gani kamar aski akanki." Dubu ta rushe da kuka ta ce, "Inno wallahi aski ya mini kuma wallahi ɗan iska ne." Cak Yaya Babba ta tana ƙarewa Dubu kallo sannan ta ce, "Dubu je ki can mu gani." Dubu ta tashi tana ƙobare ƙafafuwa saboda irin gwale-gwalen da ta sha.
Ba su yi aune ba sai ga ni suka yi Yaya babba ta faɗa ɗaki ta rushe da kuka. Da sauri suka bi bayanta saboda kusan kowa bai ji daɗin abin da Aseem ya yi ba musamman Mahaifinsa, faɗa yake yi masa sosai sannan suka shiga ɗakin. Yaya babba kallonsu ta yi fuska a murtuke ta ce, "Garba ka tara mini ƴan uwanka saboda wannan ba maganar tsaye ba ce. Kuma idan har Aseem ya farke mini Dubu na rantse da Allah ba ita kaɗai ya yi wa illa ba, ya fi kowa shiga uku domin babu makarin maganin ƴan shafi mu lerar da za a bashi. Kai ni wallahi ban lamince ba ke Nafisa ke ce uwarsa wuce ki je ji bincike shi tas, don wallahi Idi ɗan wanzan ya mutu babu wani magani da zai karya laƙanin aikin, saboda aikin har da haɗin ƴan shafi mu lera." Tana gama maganar ta fisgo Dubu tana shafa mata suɗaɗɗen kanta ta ci gaba da cewa, "Ka ga yanda Kan Dubu ya sulle kamar bayan sulba. To kwarankatsa dubu idan har ka farketa kaima haka wurin zai shafe kamar bayan silba."
Kallon-kallon aka fara yi da juna, jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi dukda ta san a tarbiyyar da suka bawa Aseem ba zai taɓa yi wa Dubu fyaɗe ba. Amma shaidar ɗan yau bata da tabbas, domin ɗa ne ka haifshe baka haifi halinsa ba. Babban abin da ya fi ɗaga hankalinta da ta ji an ce Aseem ɗin ta ya koma kamar bayan silba. Ita da take yi masa tanadin Yusra ƴar aminiyarta ya aura.
Baba Abubkar ya kalli Aseem da kallon tuhuma rai a ɓace, Aseem ya sunkuyar da kai ƙasa saboda ba ƙaramin takaici kakar tashi ta bashi ba. Da wata irin murya Baba Abubakar ya ce, "Abin da Inno ta faɗa haka ne?"
Aseem ya furzar da iska mai huci ya ce, "Daddy don Allah ka bar biyewa maganar tsohuwar nan ka san dai wasu maganganun nata ba su..." Bai ƙarasa ba Baba Munkaila ya buga masa tsawa ya ce, "Ka iya bakinka Aseem duk yanda Mahaifiyarmu take furta lafazi Mahaifiyarmu ce."
Yaya Babba ta wara hannuwa ta ce, "Kuma na fi wannan gajeriyar uwar tashi mai kama da gajeren turmi, na gama maka komai tun da na haifo uban da ya haifeka. Atoh gara ka yi bayani wallahi babu inda zani in wahalar da kaina wurin neman maganin gargajiya. Alƙur'an dama sai da Idi wanzan ya gaya mini ɓat haka za a nemi komai a rasa. Wa ya sani ma ko aljanunsa ne za su ɗauke su cinye su barka a shafe.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[7/1, 5:59 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
FREE PAGE 7
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels
Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.
Waɗannan kalamai na Yaya Babba ba ƙaramin sake ɗaga hankalin Hajiya Nafisa suka yi ba, ciki a kaɗe hankali a tashe ta dubi Yaya babba da babu abin da take yi ban da huci ta ce, "Inno ba mu fahimce ki ba. Shi Aseem ɗin za a mayar kamar bayan silba?"
"Ke Nafisa ki fita daga idona, dama ban faɗa don ku fahimce ni ba ehe. Hadiza meye laifina don na nemawa marainiyar jikata maganin tsari?" Hadiza ta girgiza tana faɗin, "Babu laifi Inno!" Yaya babba ta ci gaba da cewa:
"Allah ya jiƙan Idi ɗan wanzam ya gafarta masa shi ya bani laƙani na yi wa yarinyar nan Dubu, akan duk wanda ya farketa to shi da sake zama namiji har abada kenan." Hajiya Nafisa ji ta yi ƙafafuwanta sun yi sanyi har tsayuwar na neman gagararta. Don haka ta jingina ta bango tana bin Aseem da wani irin marayan kallo.
Kafin wani lokaci gabaɗaya iyalan gidan sun hallara a ɗakin Yaya babba dama kuma gidan babu kowa sai iya su ƴan gidan, don haka suka hallara kowa zuciyarsa babu daɗi. Yaya babba ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya sannan ta fara cewa, "Na san dai kun san dalilin tattara ku da na yi a wurin nan. A zahirin gaskiya Soja ya keta mini rigar mutumci, saboda Allah wane mugun abin yarinyar nan ta yi wa yaron nan da zai aikata mata wannan mugun halin..." Kuka ya ci ƙarfin Yaya babba saboda zuciyarta ɗaya ta ɗauka Aseem wani abu ya yi wa Dubu da ta tafiyarta ta sauya.
Baba Adamu ya yi sallama sannan ya fara fa cewa, "Inno don Allah ki yi haƙuri. Amma kafin a yanke wani hukunci ya kamata a ji ta bakin yaron nan bana jin Aseem zai aikata abin da ake magana akai..." Yaya Babba ta yi farat ta katse Baba Adamu da cewar, "Ado ƙarya na yi kenan? Ku tashi ku fice daga gabana idan ba so kuke na yaye falsafar albarkar da ke kanku ba." Baba Adamu ya yi ƙasa da murya ya ce, "Inno don Allah ki yi haƙuri ba haka nake nufi amma duk yanda kika ce haka za a yi."
"Ke Dubu me soja ya yi miki bayan ya tafi da ke." Dubu da har lokacin da sauran tsoron Aseem a zuciyarta ta saci kallonsa aikuwa suna haɗa ido ya watsa mata mugun kallon. Sai a kan idon Yaya babba ta ga irin kallon da Aseem ya yi wa Dubu, ai kuwa wani irin gumi ne ya fara yayyafowa Dubu ta fara inda-inda. Yaya babba ta fara salati tana tafa hannuwa ta kalli Aseem ta ce, "Ittaƙillah Soja ka ji tsoron rabbissamawati, idan ka zare mata ido a nan duniya a cikin kabari za ka zare wa Mala'iku ido ne. An ya Soja haka ka koma ban sani ba?" Ta mayar da kallonta wurin Dubu ta ce, "Za ki yi wa mutane bayani ko sai na sa Munkaila ya zane miki jiki ciki da bai." Dubu ta muskuta gefe ta fara cewa, "Da ya kaini mota bindiga ya ciro wai zai harbe ni ya wurgar da gawata a gefen hanya." Da sauri Yaya Babba ta dafe ƙirji ta ce, "Kun ji ko? Na gaya muku tuni ya riga da gama da ita." Hajiya Nafisa saboda ɓacin rai ji ta yi kamar ta shaƙo Dubu da Yaya Babba ta shaƙe su. Dubu ta ci gaba da cewa, "Muna zuwa gidan ya yi mini aski kuma wai da har billen gobirawa zai yi mini. Daga nan ya sani tuƙin babur shi ne muka taho gida." Yaya babba jikinta ne ya fara sanyi ta ce, "Daga haka bai yi miki komai ba?" Dubu ta ce, "Eh"
A ɗan ƙufule Yaya babba ta ce, "To da kika ce ɗan iska ne?"
Dubu ta ɓata fuska ta ce, "Eh mana ba ke kika ce mini duk mace mai bin namiji, ita da shi duka ƴan iska bane?" Wata gwauruwar ajiyar zuciya Hajiya Nafisa ta sauke, Yaya babba cikin jin haushi ta ce, "Amma Allah wadaran halinki Dubu da za ki iskanta mini jika, ina ji ina gani a gaban iyayensa. Kedai an yi makira yanzu ba sai ki sa Garba ya ce ba na son Ɗansa ba. Ni dai kin cuceni za ki haddasa gaba a tsakanina da ƴaƴana. Tashi ki bani wuri makira in Allah ya yarda ba zan ga ɗan iska a kan jikana ba. Don Allah ku gaya mini abin da Soja ya tsare wa Dubu da za ta yi masa mugun fata haka?" Kowa ya yi shiru a ɗakin bai tanka mata ba. Yaya babba ta dubi Aseem da fuskarsa ta yi murtuk saboda ɓacin ra ta ce, "Soja ka gafarce ni wallahi wannan makirar ce ta ingiza ni, ni dama sai da zuciyata ta raya mini babu abin da za ka yi wa Dubu." Ci kanki Aseem bai ce mata ba, sai kuma ta fara matsar ƙwalla ta ce,
"Garba kana gani Soja ya ƙullace ni har ya ɗau fushi da ni. A gidan duniya idan ban yi wa jikana magana ba wa zan yi wa? Kana gani hakkin Soja zai bar ni kwanciyar kabari?" Baba Abubakar ya ce, "Inno bai ƙullace ki ba ina jin bai jiki ba ne." Ya faɗi haka ne don kar wutar rikicin Yaya babba ta ƙara tashi. Yaya babba ta saki murmushi tana goge hawaye ta ce, "Soja!" Ya ɗago ya dube ta har lokacin fuska babu walwala ya ce, "Na'am" ta ci gaba da cewa, " Allah dai ya yi maka albarka. Wallahi ka biyani da ka askewa yarinyar nan kai." Da sauri duk suka ɗago suna kallonta don ba su taɓa zaton haka daga bakinta ba.
Ta janyo Dubu tana sulle hijabin da ta ɗaura ta rufe kan da shi ta ce, "Wari dai akanta yanda ka san an buɗe shadda, idan Dubu ta buɗe kai a kusa da kai alƙur'an ko yawu ba za ka iya haɗiya ba. Kwanaki haka na saka mata fiya-fiya saboda kwarkwata amma yarinyar nan duk ta watsar a banza. Don Allah ka gaya mini wane saurayi ne zai ɗauki Dubu tana fama da tsamin kai dana hammata?" Hajiya Rahama ta yi murmushi ta ce, "Inno ai har yanzu Dubu yarinya ce tana ƙara zama budurwa duk za a nemi wannan ƙazantar a rasa." Yaya babba ta taɓe baki ta ce, "Ke Rahama rabani da cewa Dubu yarinya. Yarinyar da tun bara ta fara jini, ki gaya mini ta zama budurwa ko bata zama ba? Ga Ma'awiyya ƙawarta nan tun kwanaki aka yi mata aure wai sai ga ciki, nace kai waɗannan ƴaƴa an yi jarababbu yanda kika san a bakin ƙofa suke cin karo da shi. Yarinyar nan haka ta riƙa kuka da zan kaita ɗakin miji da yake ƙud-da-ƙud muke da kakarta, ina ta zuba ido na ji an ce yarinya tana gudun miji tana dawowa gida, kamar yanda muka riƙa yi muna amare ba sai muka ji shiru ba. Hali ne dai a ƙoƙon rai Dubu ba za ta daina wannan halin ba, ban ƙi ba idan ta haɗu da miji ɗan gayu kamar Soja." Ai kuwa Aseem na jin haka ya ɓata fuska bai gama tsinkewa da lamarin Yaya Babba ba sai ji ya yi ta ce, "Ai shi ma wannan shirun da yake yi ba banza ba wallahi, aure yake so don dai bai gaya muku bane. Ya yi gadon Kakansa Malam, don haka ya bani labari shi ma yana matashi Allah ya jiƙan Malam babba shi ya fahimci aure yake so, ba a ɗau lokaci ba aka ɗaura mana aure. Shi ma Soja ana haɗa shi da ƴar budurwa kamar Dubu shiru za ku ji sai dai ku ji ciki." Aseem a daƙile ya miƙe zai fita saboda takaici. Yaya babba ta bushe da dariya ta ce, "Kun ga abin da na gaya muku wai ya ji kunya na tona asirin zuciyarsa." Baba Adamu ya yi murmushi ya ce, "Yanzu Inno magana ta wuce kenan kowa zai iya tafiya?"
Take ta murtuke fuska ta ce, "Sam ban sallame ku ba wallahi akwai muhimmiyar maganar da nake son yi da ku ko Dubu?" Ta faɗa tana kallon Dubu da ke cika tana batsewa.
Dubu ta gyaɗa kai don fushi take da Yaya babba saboda irin bankaɗar da Yaya babba ta yi mata a gaban mutane, Yaya babba ta gyara zama sannan ta fara cewa.
"Garba wata shawara na yanke don Allah ya sani an daɗe ana shiga haƙƙina." Gabaɗaya suka kalleta suna mamakin jin kalamanta sai dai ba wanda ya tanka suna jiran jin ci gaban sauran maganar.
"Tun Malam yana raye nake son ganin kan iyalaina a haɗe ba wannan ya yi gabas, waccen kudu wani arewa ba."
Hadiza ta jinjina kai sannan ta ce, "Maganarki hake ne Inno amma ai kanmu a haɗe yake don gabaɗayanmu babu mai bijirewa maganar na gaba da shi." Yaya Babba ta washe baki ta ce, "Ai shi ya sa nake son na ƙara haɗa kanku idan na waiga na ga wannan inna juya na ga wannan ko ba haka ba Dubu?" Dubu ta yi murmushi don ta san muddin Yaya babba ta zartar da hukunci to ba fa ba shakka suma sun zama ƴan gayu irin yanda ƴaƴan Baba Adamu da Baba Abubakar suke rayuwa.
"To na zauna mun yi shawara ni da Dubu kuma ta bani shawara mai kyau akan haka." Wannan kalamai na Yaya babba ya yi daidai da shigowar Aseem zai ɗauki mukullin motarsa. Yaya babba ta yi farat ta dakatar da shi da cewar, "Kai Soja tsaya ayi da kai ka ji alherin da zai same ku don wallahi ba ƙaramin gata zan yi muku ba. To ina dalili in kwanta inmutu zuri'a a tarwatse, a'a sam haka ba za ta faru ba dama abin da na riƙa nusar da kakanka kenan ya ƙi gane wa." Aseem bai so zama ba don ya san ban da rikici babu abin da za ta yi musu a wurin. Amma gudun tashin hargitsinta ya sa ya koma ya zauna ba tare da ya tofa uffan ba.
"Yauwa magana muka yi ni da Dubu kuma wannan shawara da ta bani na yi na'am da ita. Na yanke hukunci kai Garba da ɗan uwanka Ado za ku dawo gidan nan da zaman. Kowa ya kwaso iyalansa ya kawo su ɓangarensa. Yo ina dalili ace da mahallinku a gidan gado kowa da ɓangarensa sai dai ace wai idan an kawo mana ziyara a sauka a ciki. A'a sam ba da ni za a yi haka ba Dubu ta ce sai mum fi cin daɗi kuma waye baya san daɗi a rayuwarsa Garba." Ta ƙarasa maganar tana tambayar Baba Abubakar da ya yi suman zaune. Kasancewar ya tafi wani tunani can bai ma san irin tambayar da Mahaifiyar ta shi take yi masa ba.
Hajiya Nafisa da ta cika fam har wani ɗaci take ji a zuciyarta ta ce, "Inno yanzu shawarar Dubu za a ɗauka? Dubu har wata mutum ce da za a saurari shawara daga bakinta. Maganar gaskiya wannan ci baya ne ace shekara sama da ashirin da bakwai muna zaune a cikin birni rana tsaka a ce mu dawo ƙau..." A hanzarce Baba Abubakar ya ce: "Nafisa! Bana son jin bakinki!"
"A'a ka barta Garba idan bata tsefe ni ba ai ba za ta nuna mini ta isa ba. Don Allah ka gaya mini lokacin da ka auro Nafisa a ina ka aurota da ya wuce ƙauye. Ka tuna lokacin da kuka je ƙauyensu ɗaurin aure Labaran ƙanina cewa ya yi ruwan garinsu kamar turɓaya haka yake. Nan dai gidan gado ne ko ana so ko ba'a so dole mutum ya dawo." Rai a matuƙar ɓace Aseem ya ɗago yana kallon Yaya babba, da Dubu da ke gefe. Furzar da iska ya yi ya sunkuyar da kai yana danne-danne da waya, sai dai ba zai ce ga takamaimai abin da yake latsawa ba. Baba Adamu ya russuna ya ce, "Inno a duba lamarin dai saboda yanayin aikinmu ga makarantar yara. Idan sha'awar zama kike kusa da mu ni ko Yaya Abubakar wani sai ya ɗauke ki, koma can da zama."
"Haram giya a gidan liman! Ba da ni ba. Ba zan taɓa bijirewa umarnin Mahaifinku ba, na gama magana idan za ku dawo nan kowa ya gyara wurinsa ya dawo, idan ba za ku dawo ba shi kenan" Tana gama maganar ta rushe da matsanancin kuka.
Zuciyar Baba Munkaila fes don ya san ko ba komai ya san idan suka dawo cikin gidan za su iya ɗauke masa cefanen gidansa. Baba Abubakar yanayinsa sam babu walwala ya dubi Mahaifiyarsa ya ce:
"Inno wannan kawai kike buƙata?" Da sauri Hajiya Nafisa ta hangame baki. Hajiya Fauziya ma ta cika fam tana watsawa Yaya babba harara ƙasa-ƙasa.
Yaya babba ta share hawaye ta ce, "Garba idan kuka yi mini wannan duniya da lahira kun biya ni haƙƙin mahaifiya. Ni dai Allah ne gatana kuma da shi na dogara, ko na dogara da ɗaya daga cikinku?" Baba Munkaila ya ce, "Inno mu kuma fa?"
"Munkaila a gidan duniya ka gaya mini wane abu ka taɓa yi mini." Baba Munkaila zai yi magana, Baba Abubakar ya katse shi da cewar, "Shi kenan zamu dawo Inno amma ki ɗan bamu lokaci tun da kin ga tashin namu babu shiri dole akwai abubuwan da za mu gudanar."
"Allah dai ya yi muku albarka Garba, ku yi komai a nutse wallahi. Me ake da gaggawa aikin shaiɗan. Me ye haɗinmu da shaiɗan muna masoya Mazon Allah (S.A.W). Allah ya yi mana tsari da shaiɗan, ku bi komai a sannu ko nan da sati biyu ne." Cikin haɗin baki suka ce, "Sati biyu Inno?"
"Ko ya yi yawa?"
Baba Adamu ya ce, "Inno Sati biyu ai ya yi kaɗan ina laifin nan da wata guda kinsan ko a gun aiki sai mun ɗauki uzuri." Ya gaya mata haka ne don ya san yanda take bawa aikinsu muhimmanci. Sai da ta yi jim sannan ta ce.
"Eh ka fi ni gaskiya Ado maza ku je ku yi komai a nutse kar wurin aikin su ji haushi su sallame ku ko?" Hajiya Nafisa kamar za ta yi kuka ta ce, "Yanzu Alhaji shi kenan ka amince nan ɗin za mu dawo?" Aseem ya sa hannunsa ya damƙi hannun mahaifiyarsa don ba ya son ace ita ta fara ɓullo da wata maganar. Fisgewa ta yi ta ci gaba da cewa, "Maganar gaskiya ba a yi mana adalci ba, sai da aka ga ƴaƴanmu sun zama ƴanmata za a ce mu dawo ƙauye wallahi da sake..." Cikin tsawa Baba Abubakar ya ce:
"Nafisa ya isa haka! Tashi ku fice an sallame ku." Rai a ɓace gabaɗaya matan nasu suka fice daga ɗakin. Baba Abubakar ya russuna ya ce, "Na barki lafiya Inno." Yana fita Baba Adamu da tsirarun ƴan uwansu suka bi bayansa. Ɗakin ya rage daga Baba Munkaila, Aseem, Dubu, Yaya babba sai Hadiza.
Jiki a sanyaye Yaya babba ta kalli Baba Munkaila ta ce, "Munkaila an ya yaran nan ba haushina suka ji ba kuwa? Na ga kamar a fusace suka fita. Don Allah meye laifina don na nemi haɗa kan zuri'ata?" Baba Munkaila ya washe baki ya ce, "Babu Inno kawai dai haka kika gani amma babu abin da suka ji, ya za a yi su ji haushinki." Yaya babba ta yi murmushi cikin jin daɗi.
Hadiza da ke gefe ta ce, "Gaskiya Inna bai kamata ace kowacce shawara Dubu ta gaya miki ki ɗauka ki yi amfani da ita ba. Mu fa mune ƴaƴanki mu ya kamata ki kira mu ji shirinki amma nawa Dubu take da za ta baki shawara." Yaya babba ta yi shiru kamar mai nazari sannan ta ce, "Kuma maganarki fa haka take don kin manta shawarar da Dubu ta bani akan sayar da ƙaton ragona ta ce na siyo ƴan tsaki, me ake yi da kiwon kaji idan ba asara ba? A rana ɗaya sai a fitar mini da mushen biyar suka lalace a banza bai fi ƙwara goma muka mora ba cikin Sittin. Kai amma Dubu an yi shakiyyiyar yarinyar, da ta ga kaza ta fara rufa sai dai na ji ta wasa wuƙa ta yanka, ni an ya ba da biyu ma Dubu ta riƙa yanka kajin nan ana soyawa ba?" Hadiza ta taɓe baki ta ce, "Ai koma meye Inno kun fi kusa. Amma kiwon kaji ana samu da shi wacce kika ɗora akai ce dai sai a hankali. Yanzu mu koma maganar su Yaya Adamu maganar gaskiya Inno ba za su ji daɗin zaman gidan nan ba, tun da sun saba da zaman cikin gari kina gani tun a gabanki me Nafisa take faɗa. Kina ganin zamansu a kusa da ke babu wata matsala?" Yaya Babba ta saci kallon Aseem sannan ta ce, "Ni fa Nafisa ta birgeni, sabo fa aka ce miki Hadiza. Sabo turken wawa, kuma ko ke ce haka za ki faɗa. Gaskiya ki daina cin naman mutane a ɗakina karki haramta mini mala'ikun rahama shigowa ɗakina ina zaune ƙalau. Yanzu ga Soja a zaune idan ya ji kina aibata mahaifiyarsa ba sai ya ɗauki gaba da ke."
Aseem bai tanka musu ba Hadiza ta ce, "Inno gaskiya fa na faɗa ko a gaban Nafisa zan faɗa ba wai Aseem ba. Ina guje miki abin da za a zo ana yin babu daɗi Amma tun da haka kike so shi kenan Allah ya dawo da su lafiya." Hadiza na gamaƙ maganar ta tashi ta fice, Baba Munkaila ya rufa mata baya.
Aka bar Yaya babba da riƙe haɓa, Aseem na shirin ta shi ta ce masa, "Soja don Allah ka bar ni na kwashewa yaran nan albarka, kana ganin abin da duk suka yi mini wai haɗe mini kai za su yi su ware ni daga cikinsu. Cikin halin ko'inkula Aseem ya ɗaga kafaɗa ya ce: "Ki kwashe musu mana, idan kin ga dama ki tsine musu ƴaƴana ko naki. Wallahi akwai abubawan da dama da idan muka dawo zan saita muku zama ke da sheɗaniyar jikar taki mutum ya kawo mini wargi na sa bakin bindiga na harbe shi." Yana gama maganar ya fice a fusace. Da sauri Yaya babba ta dafe ƙirji a firgice da jin maganar da Aseem ya faɗa.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
*DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
0 comments:
Post a Comment