"A'a! Amma ki ji tsoron Allah Dubu kar ki sa na tuhumi Garba ya sake ɗaukan gaba da ni." Dubu ta ɓata fuska ta ce, "Ai dama ke ba a magana da ke sai kin kwashe kin gaya musu, haka kika gama ci mini mutumci a gabansu kina kirana da ƙazama." Yaya babba ta janyo Dubu cinyarta ta ce, "Ina sane na gaya musu haka idan ba haka ba wallahi Soja gaba zai ɗauka da ni amma ki bar ni da su idan suka dawo gidan nan duk za mu saita musu zama." Dubu na jin haka ta bushe da dariya don har ta gama tamawa yanda za ta yi wasan kura da Nabila don da alama ta lura ita ce hoton Hajiya Nafisa da duk wasu halayenta.
Inna Furai tun da suka dawo daga asibiti take ta bacci ba ita ta farka ba sai bayan magriba, tana farkawa ta hangi Larai a gefenta. Da murnarta ta tarbe ta da sannu sai dai ta lura da yanda Mahaifiyar tata take ƙarewa ɗakin kallo, matsawa kusa da ita ta yi ta ce, "Sannu Inna ya jikin?" Inna Furai ta yunƙura za ta tashi, Larai ta taimaika mata tashi sannan ta ce, "Larai ina su Lantan suke?" Larai ta yi murmushi ta ce, "Inna su Lantan ai sun wuce tun safe yanzu dai bari ki yi alwala ki yi sallah sai ki ciki abinci, ko sai kin fara cin abincin?" Inna Furai ta girgiza kai tana faɗin, "Wane mutum sallah ai ita ce gaba da komai, bare yanzu da Fatale suke kawo mana farmaki. Amma ya maganar tawagar fatwar da ƴan sama jannati?" Larai ta ce, "Inna don Allah ki bar maganar nan wannan fa duk ya wuce komai ya daidaita yanzu bari na kawo miki ruwa ki yi alwala." Tun daga lokacin Inna furai ta ɗan saki jikinta ta fara harkokinta.
Kafin wani lokaci tuni maganar dawowar su Baba Abubakar ta karaɗe cikin gidan, wasu daga cikin facalolin ban da murna babu abin da suke yi don dama ba ƙaramin haushi suke ji ba, a duk lokacin da suka ga su Hajiya Rahama sun zo garin fes kowacce ta ƴaƴanta cikin gayu. Wasu daga ciki kuma suna jin haushi don gani suke matuƙar matansu Baba Abubakar suka dawo gidan sun koma bola a wurin Yaya babba, don a haka ma ya suka iya da tsiyar da Dubu take shuka musu amma basu da abin faɗa? Wasu kuma murna ɗaya suke ta dawowar tasu don suma su dangwali abin arziƙi saboda ko banza za su ci gaba da cin mai kyau saɓanin da, da sai dai su ga an direwa Yaya babba kayan alatu na more rayuwa sai dai idan ƴaƴansu sun je ta zaunar da su ta ba su, su ci su yi ƙat su suna daga gefe suna lasar baki.
Kamar haɗin baka duka matan Baba Abubakar da Baba Adamu suka haɗa kai kowacce ta kwashi ƴaƴanta suka yi tafiyarsu. Shi kansa Aseem yana fita ya shiga motarsa ya yi gaba, Hajiya Nafisa ta tasa ƴaƴanta suka wuce bakin titi suka tari abin hawa suka tafi don saboda ɓacin rai ko ta kan Maigidanta bata bi ba. Hajiya Rahama da Hajiya Fauziyya ma tafiya suka yi, a hanya babu mai tankawa kowa saboda takaici har suka ƙarasa gida.
Suna zuwa gida kowacce ta yi sashenta da iyalanta saboda ko da cen ma dama ba wani cikakken zaman lafiya suke yi ba. A ranar ma abin da ya sa wani abu bai haɗo su ba saboda ba daɗi ya sa su tafiyar ba kowacce zuciyarta cunkushe take da baƙin ciki.
Gidan Baba Abubakar.
Hajiya Nafisa na zuwa gida ta ɗau waya ta kira ƙawarta Hajiya Ikilima, bata jima da shiga ba aka ɗauka da sallam. Ko ƙwaƙƙwarar gaisuwa ba su yi ba Hajiya Nafisa ta fara da cewa, "Ƙawata don Allah kina ina? Ina son ganinki cikin gaggawa!" Daga can ɓangaren ta bata amsa, "Lafiya kuwa Ƙawas ko tsohuwar ita ma ta sheƙa ne?"
Hajiya Nafisa ta yi murmushin takaici ta ce, "Wallahi da za ta sheƙa da na fi kowa murna a rayuwar duniyar nan. Kai ni tun da nake na taɓa ganin ƙaddararriyar tsohuwa kamarta kuwa, yanzu kina ina kizo na dawo gida don Allah maganar gaggawa ce ina son ganinki." Hajiya Ikilima ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Gani nan zuwa yanzu kuwa amma ince dai mijinki baya nan ko? Don kinsan gani yake kamar ni nake zuga ki shi ya sa ma bana son zuwa idan yana nan." A ƙagauce Hajiya Nafisa ta ce, "Ba fa ya nan ya can ƙauyensu ni dai sai kin ƙaraso." Daga haka suka yi sallama, Hajiya Nafisa ta fara sintiri a cikin ɗaki.
Tana nan tsaye ta ji sallamar Aseem, tun bai tufe baki ba ta fita falon idanu a ƙanƙance ta fara magana: "Aseem yanzu saboda Allah wannan tsohuwar ta yi mana adalci kenan? Saboda Allah a ce duk abin da waccen ƴar iskar yarinyar, mai zubin sheɗanun ta gaya mata da shi za ta yi amfani. Wacce rayuwar za mu tsinta a zaman ƙauye? Tun da ba ta ce mu koma ba sai da ta ga yaranmu sun zama ƴanmata wato yanda waccen za ta zauna a ƙauye tana baƙincikin su Nabila su sami miji a birni. Da sake wallahi, Allah sai dai Mahaifinka ya zama ko zaman ƙauyen ko kuma mu raba gari."
Dama ya san za a rina don haka ya shiga sashen mahaifiyar tashi don ya samu ya taushe ta. Amma maganarta ta ƙarshe ta fi firgita hanjin cikinsa, saboda tun da yake bai taɓa jin makamanciyar wannan maganar daga bakin Mahaifiyarsa ba. Shi kansa sheda ne duk irin ɗabi'un Mahaifiyarsa na rashin haƙuri amma mace ce mai kyawawan ɗabi'u. Matsalarta ɗaya rashin haƙuri da kawar da kai sai kuma son kanta da saurin ɗaukar zuga, amma bayan wanna baya jin tana da wasu halaye marasa kyau.
Cikin sigar lallashi ya kalli mahaifiyarsa ya ce, "Don Allah mommy zauna mu yi magana." Bata musa ba ta zauna a kan kujera tana kallonsa. Aseem ya ci gaba da cewa, "Mommy don Allah ki kwantar da hankalinki wannan fa ba abin tashin hankali bane. Kamata ya yi a ajiye maganar nan agefe har zuwan bayan sadakar bakwai, amma Mommy kun taho gida ke da su Nabila da Aunty kina ganin Daddy zai ji daɗi?"
"Dama ban aikata haka don jin daɗinsa ba, Aseem idan kana da wata maganar bayan wannan ka yi amma magana ɗaya za a gaya mini na saurara cewar mun fasa komawa ƙauye. Ina nan wallahi mahaifinku zai dawo ya same ni." Tashin hankali wanda ba a sa masa rana. Miƙewa Aseem ya yi ya ce, "Allah ya huci zuciyarki Mommy amma hakan sam bai dace ba yanzu idan Iya ce (Mahaifiyar Hajiya Nafisa) ta ɓata miki rai na san ba za ki yi haka ba, kin ga Daddy shi ma gani zai yi don ba mahaifiyarki ba..."
"Fita ka bani wuri" Hajiya Nafisa ta faɗa tana nunawa Aseem ƙofa azafafe. Sum sum sum ya miƙe zai fita ta ci gaba da faɗa, "Ai wallahi dama na sani wannan zaman daɓaron da tsohuwar nan take zuwa duk lokacin dana haihu ba banza ba, ta gama asirce mini ƴaƴa fa magane-maganen da take basu tun jarirantaka. Ban da lalacewa kai ba me shigar mana ba ne sai inda ƙarfinka ya ƙare, a'a kai gudun ɓacin ran mahaifinka kake yi." Aseem ya fice daga falon ya bar Mhaifiyarsa tana da sababi.
Gidan Baba Adamu.
Hajiya Rahama ita kaɗai ta ƙule a ɗaki tana nazari, lokaci ɗaya ta ji kamar ba su kyauta da abin da suka yi ba domin suma idan mahaifansu ne dole su yi musu biyayya. Tashi ta yi jiki a sanyaye ta nufi sashen Kishiyarta Hajiya Fauziya, a falo ta same ta tana waya, tana ganin Hajiya Rahama ta ce, "Ok, ba damuwa za mu yi waya an jima." Hajiya Rahama ta kalli Hajiya Fauziya ta ce, "Mamin yara na zo mu yi magan." Kujera ta nuna mata fuska ba walwala ta ce, "Zauna ina jin ki."
"Gani nake kamar ba mu kyatawa Alhaji ba, saboda Mahaifiyarsa tamkar mahaifiyarmu ce idan ta mu mahaifiyar ce muma babu yanda muka iya dole mu yi mata biyayya. Kina gani ko sadakar uku ba a yi mun taho gani nake gaskiya akwai..." Tun bata ƙarasa ba Hajiya Fauziyya ta katse ta da cewar,
"Don Allah idan wannan ne ya kawo ki kwashi tsummokaran ƙafafuwanki ki ƙara gaba, bana son kutungwila da shegen iyayi kamar ta macen kyankyaso. Kin san da haka kika ɗebo ƙafa kika taho ai sai ki tashi ki koma ba sai kin zo min ba." Hajiya Rahama ta miƙe tana cewa, "Ni na kawo kaina duk abin da kika faɗa, nina ja wa kaina."
"Oho fice ki bani wuri tun da ban gayyatoki ba, kinibabbiya kawai." Hajiya Fauziyya ta faɗa tana huci kamar wacce ta yi tseren gudu."
Hajiya Rahama na komawa sashenta ta samu ana kiran wayarta, tana dubawa ta ga lambar maigidansu har sai da hanjin cikinta ya kaɗa, da ƙyar ta yi ta maza ta ɗauki wayar da sallam. Bai amsa mata ya fara da cewa, "Rahama ina yi miki kallon mai hankali ashe ba haka ba ne. Kun nuna mini Mahaifiyata bata isa da ku ba, kun kama hanya kun taho ba tare da izinina ba. Na gode kun nuna min ni kaina ba wata tsiya bace a wurinku." Jiki a sanyaye Hajiya Rahama ta ce, "Don Allah ka yi haƙuri Alhaji wallahi nima na yi nadama amma yanzu zan taho insha..."
"Duk wacce ta sake ta fito daga gidan nan wallahi-wallahi a bakin aurenta. Tun da kun riga da kun yanke hukunci shi kenan, rasuwa dai Mahaifina ne ya rasu bana buƙatarku kuma komawa Ɗangwauro kamar mun koma mun gama, duk wacce ta ga za ta koma bismilla wacce ta ga ba za ta iya ba za ta iya komawa gidansu. Ita ma waccen zan kira na shaida mata." Yana gama maganar ya katse bai jira cewarta ba. Lokaci ɗaya ta ji duniya ta yi mata zafi don ita kanta ta san abin da suka yi ba su kyauta ba.
Gidan Baba Abubakar.
Hajiya Ikilima ce zaune cikin mamaki ta dubi Hajiya Nafisa ta ce, "Wai wannan maganar da kike gaya mini da gaske ne ko kuma zolayata kike yi?" Haushi ya fara kamata da jin kalaman aminiyar tata ta ce, "Ƙawas kin san bama irin wannan wasan da ke. Serious ki bani shawara Allah dana koma Ɗangwauro gara aure ɗna ya mutu da bawan Allahn nan." Cikin zuciyar Hajiya Ikilima ƙyal saboda farinciki don ta jima tana hangen kanta a gidan wannan baƙin bafulantin mai cike da kwarjini, amma ina ƙawarta ta yi mata shamaki. Ta dube ta da fuskar tausayi ta ce, "Gaskiya dole ki ɗau mataki kika koma ƙauye wallahi kin faɗo, yanzu abin yi ki shirya na raka ki Ƙauyen tudun-wada akwai wani Malami yana taimako wallahi, zai taimaka miki sosai ke ko kashe tsohuwar nan kike son yi murus za a gama da ita." Hajiya Nafisa ta zaro ido waje tana faɗin, "Kin san fa ni bana haɗa hanya da ƴan tsibbu shawarwarin da kika saba bani dai su za ki bani. A kashe ta, ta rataya a wuyana. Ba za a yi haka ba kedai..." Bata ƙarasa maganar ba Aseem ya shiga falon don sarai ya ji abin da suke tattaunawa, sai ya wuce kan daininga da kofin shayi a hannu yana danne-dannen waya. Hajiya Ikilima ta saci kallonsa cikin ƙasa da murya ta ce, "Ko dai ya ji mu?" Hajiya Nafisa ita ma kallonsa ta yi sai ta ƙanƙance murya ta ce, "An ya kuwa amma bari ki ga." Hajiya Nafisa ta kalli Aseem ta ce, "Aseem jeka ɗakina ka ɗauko kuɗi akan mudubi ka tsallaka titi ka siyowa mamanka fura." Babu yanda ya iya haka ya tashi ya tafi kamar zai yi kuka don ya so jin ƙarashen hirar tasu. Dama ya jima yana zargin wannan matar da zuga mahaifiyarsu ashe kuwa ita ɗin ce take zuga ta.
Yana fita Hajiya Ikilima ta ci gaba da ɗora Hajiya Nafisa akan shawarar banza. Sai dai abin da kullin yake ɓata mata rai duk yanda take son ɗora Aminiyar tata akan biye-biyen malamai taƙi bada kai bori ya hau, kuma da haka take son cimma ƙudurinta akanta amma bahaushe ya ce a juri zuwa rafi watan tulu zai fashe.
Bayan Sadakar Bakwai.
Dubu ce tafe za ta tafi makarantar Islamiyyar Malam Jafaru, tana tafe da ƴar maƙalaliyar jakarta ta buhu tana rera waƙar Bureka (Breaker) ta Jaruma, idan ka ji yanda take rairawa sai ka rantse ita ta biyawa mawaƙin waƙar. Ɗan'iya da ke tafe da Mahaifiyarsa ya ƙwala mata kira. "Dubu!"
Dubu ta juya hagu da dama sai a can daga nesa ta hango Ɗan'iya ai kuwa ta yashe baki, tana ɗaga masa hannu. Ɗan'iya sai da ya ga sun ɗan yi nisa da Dubu sannan ya ce, "Dubu mai kan Silba mun san komai ashe ƙwaryar molo aka yi miki." Lawandi da taron abokansa da ke bakin bishiyar dalbejiya me za su yi idan ba dariya ba. Ma'azu har da tuntsirawa kamar zai faɗi ƙasa. Wannan abu ba ƙaramin ɓata ran Dubu ya yi ba, ta tattakura ta ɗaga murya da cewa, "Eh na ji ɗin Ɗan gidan Balaraɓe kwarton dare" Da sauri su Lawandi suka riƙe baki kasancewar dama ana ta raɗe-raɗin wannan zargin da ake wa Balarabe ashe har kunnen yara ya fara bazuwa.
Hansatu mahaifiyar Ɗan'iya ta nufo wurin Dubu a fusace tana zuwa ta ce, "Iskancin na ki yau akan mijina ya sauka? Dan uwarki za ki ƙara cewa mijina kwarto?" Bata rufe baki ba sai da ta zabgawa Dubu mari sannan ta ɗora da cewa, "Wallahi ba Balarabe ba ko Bala na sake ji a bakinki sai na yi ƙasa-ƙasa da ke. Na lura iskancinki ƙara yawa yake saboda baki da mafaɗi..." Dubu ta fisge hijabinta tana cewa, "Allah ya isa kuma wallahi bashi kika ɗauka. Na faɗa waye bai san Balaraɓe kwarto bane har ɗakin Baba Auwalu sai da ya taɓa leƙawa lokacin da Yahanasu tana amarya. Banza kina gida kina tare da ɗan iska..." Kukan kura Hansatu ta yi ta fisgo Dubu ta fara jibga kamar Allah ya aikota. Jin Hansatu na niyyar hallakata ya sa ta fara kiciniyar ramawa, ai kuwa Hansatu ta cukwikwiye Dubu a cikin hijabi ta riƙa dukanta ta ko'ina sai da ƙyar su Lawandi suka ƙwaci Dubu. Suna fisgarta sai ga hijabinta a hannun Hansatu nan fa kan Dubu ya fito ral da shi yana ƙyalli don ranar Yaya Babba ta sharɓane mata shi da man kaɗanya. Nan Ɗan'iya ya fara tafi yana cewa, "Yeeh Dubu mai kan Silba (Silver)" Ai kuwa kafin wani lokaci tuni yara suka taru ana kallo, dukda tsoron da suke yi wa Dubu amma ruruma ta ɗauke hankalinsu suka fara sowa da tafi suna cewa, "Yeeh Dubu mai kan silba."
Idanun Dubu ne suka kaɗa jawur saboda baƙin ciki, sai dai har lokacin idanun Dubu a bushe suke babu ko ɗison hawaye don gudun kar a ga hawayenta yara su rainata. Cikin takaici ta kalli Hansatu ta ce, "Kwarankwatsa dubu bashi kika ɗauka kuma da ni kike zan cen." Ta juya ta kalli sauran yaran da suke tsokanarta ta ce, "Ku kuma za mu gauraya da ku kowanne shege sai na sa an harbe Uwarsa." Tana gama maganar ta suri jakarta da ke cen gefe ta fisgi hijabinta ta ɗora aka ta yi tafiyarta. Sai dai kusan rabin yaran jikinsu ya yi sanyi don suna tuno Yayan Dubu soja ne hantar cikinsu ta kaɗa har da masu bin ta suna bata haƙura amma babu wanda ta waiga, bare ya sa ran za ta amsa masa.
Dubu tun daga soron gidansu ta fara barke baki tana ihun kuka, amma ci kanki babu wanda ya tanka mata saboda sanin hali irin nata. Matan kawunan nata suna gani ta wuce cikin gida. Tana zuwa sashen su Yaya babba Inna Furai ta tare ta da tambaya, "To ƴar nema wa kika tsokano wanda ya fi ƙarfinki?" Dubu ta goge majina da hijabin hannunta sannan ta kuma yage baki tana ihu har sai da Yaya babba ta fito tana tambayarta.
"Inno wallahi daga yau ba zan ƙara fita waje ba. Ki dubi irin cin mutumcin da Hansatu ta yi mini ita da Ɗan'iya yau kashe ni ne kawai ba ta yi ba. Yara suka taru suna ce mini mai kan silba. Ni dai wallahi Allah ya isa da askin nan da azzalumin nan ya yi mini." Dubu ta faɗa tana sake fashewa da kukan baƙinciki, don abin ba ƙaramin ciwo ya yi mata ba. Yaya Babba ta karɓe zan cen da cewar:
"Wallahi faɗi ki ƙara Dubu Allah ya iskan ki, don Allah me kika tsarewa Soja da zai sauke miki gashi ana zaune ƙalau? Hassada dai ka rasa wa za ka yi wa sai jininka. Na rantse da Allah ko uwarsa Nafisa ba za ta gwada miki gashi ba. Kanta da har gobe kamar hamtar ɗan isa ga uban sanƙo da almajiran ƙeya. Wallahi ni bansan abin da Garba ya gani a jikin gajeriyar matar nan ba ya aura, mace sai faɗin ran tsiya tana baje hanci kamar tattasai ya ji sanyi wuri." Dubu ban da tuntsira dariya babu abin da take yi har da hawaye saboda ƙeta don tuni ta goge hawayen idonta saboda ko ba komai Yaya babba ta biya ta, da ba'ar da ta yi wa mahaifiyar Aseem.
Inna Furai da ke gefe ta sa dariya ta ce, "Yaya ai ba za ki ga baje hanci ba sai ta shiga gaban mota yanda kika san funkaso." Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya. Yaya Babba ta ce, "Furaira wai dama ranar da muka fita da Garba tana gaba kina ankare da ita?" Inna Furai ta ce, "Ina gani mana wai har ca take ka saya mana wani abin mana a danja wai ita mai miji." Ai kuwa dubu me za ta yi idan ba dariya.
Yaya babba ta saki dariya ta ce, "Furaira alƙur'an ni kuma fuskar Nafisa ta ƙi ɓace mini lokacin da muka karɓi haihuwarta ta wannan yaron soja kin tuna lokacin har cewa take wai Inno zo na goyaki. Na ce mata ke Nafisa rabani da zancen goyon nan, rabona da goyo tun shekaru tsububu sai yau da kike nakuɗa za ki goya ni, na turmushe ki Garba ya ɗau gaba da ni." Inna Furai dariya har da hawaye sannan ta ce, "Yoo kafin ki zo har cewa take Inna karɓi cikin, na ce Nafisa lamari ya lalace ina Uwar Garba na karɓi cikin Garba ai ba kanta sai cewa ta yi har Garban na bar miki gabaɗaya." Dubu ta kife a wurin ban da dariya babu abin da take yi.
*DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
FREE PAGE 9
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels
Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.
Sallamar Baba Munkaila ne ya dawo da Dubu cikin hayyacinta, ba shiri ta shiga nutsuwarta ta fara kumbure-kumbure don ta san babu makawa zai samu labarin abin da ya faru tsakaninta da Hansatu. A daidai kan Dubu ya tsaya fuska babu walwala ya ce, "Ke!" Kamar bata ji shi ba ta yi biris, sai da ya sake buga mata tsawa sannan ta amsa. Cikin faɗa ya ci gaba da cewa, "Dubu ki kiyaye ni fa, kullin iskancinki da iya shegenki ƙara gaba yake ko? Ƴar ƙanƙanuwarki da ke har kin isa tarar matar aure ki ce za ki yi dambe da ita. Wallahi a hir ɗinki idan kika shiga hannuna na lahira sai ya fiki jin daɗi." Dubu dama kamar me jira yana dire zancensa ta fashe da kuka tana faɗin, "Dama na san komai ni za a ɗorawa alhalin ita ce bata da gaskiya." Rankwashi ya sakar mata a tsakiyar ka aikuwa ba ƙaramin shigarta ya yi ba, a zabure ta yi gefe ai kuwa Yaya babba dama ta fara cika ta dubi Baba Munkaila cikin faɗa ta ce, "Munkaila nakasa marainiyar Allah za ka yi? Ka duba irin ƙusar da ka sakar mata a tsakiyar ka sai ka huda mata kai, ka cuceni ka cuci Ado. Ko da ya kasance likita ba sai an sayi magunguna da alluran da za a yi mata aiki ba. Gaskiya bana so ka fita rayuwar yarinyar nan shi ya sa ga tana kamar ruwan aski kullin bata kumari." Baba Munkaila bai tankawa Yaya Babba ya dubi Dubu ya ce, "Tashi ki ɗau hijabinki ki wuce makaranta. " Tun bai rufe baki ba Dubu ta suri kayanta ta fita waje tana kurma uban ihu.
Inna Furai ta ja tsaki ta dubi Baba Munkaila ta ce, "Munkaila wai me ya sa ko yaushe burinka ka zazzagewa yarinyar nan albarkar da ke kanta? Yanzu da ka kaɗa ta waje idan ta shiga gari wa ya shiga uku idan ba mu ba." Yaya babba ta cafe zancen da cewa, "Wallahi idan na rasa Dubu hukuma ce za ta raba ni da Munkaila dama na daɗe ina zargin ba ƙaunarta kake ba." Baba Munkaila ya yi murmushi sannan ya ce, "Inno yanzu so kuke a zurawa Dubu ido ta taso babu nutsuwa da rashin ilimi? Kuna ganin Fatima yarinyar nan kowa sha'awarta yake, saboda ilimin addininta. Mu kuwa wa yake sha'awar Dubu? Ku shaida ne a rana sai a kawo muku ƙara ta yi sau goma. Amma Inna furai ai bai kamata mu zura mata ido haka har girmanta ba."
Yaya babba ta yi shiru tana nazari sannan ta ce, "Munkaila ka yi tunani, kuma wallahi ina jin hannu aka sawa Dubu dole na sake nema mata maganin baki don wallahi baki ba ɗan'uwa ba ne." Baba Munkaila na ganin ya yi wa Tsofaffin iyayen nasa dabara ya tashi ya fice daga gidan.
Dubu na fita ta goge hawayenta ta maƙale jakarta ta ɗauki hanyar islamiyya, sai dai tana saƙa da warwarar abin da za ta yi wa Hansatu don ta fanshewa abin da ta yi mata. Kamar daga sama tana shan kwanar hanyar da za ta sadata da makarantarsu sai ga Ɗan'iya ya fito da tallar wake da shinkafa a kansa, hannunsa na riƙe da bokitin ragadada. Yana ganinta ya yi baya da sauri a tsorace don ya san mai ƙwatarsa a hannun Dubu sai Allah, don haka bai yi wata-wata ba tun Dubu bata tanka masa ba ya fara cewa, "Dubu don Allah ki yi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba." Kamar wani abu bai haɗasu ba, haka Dubu ta basar da Ɗan'iya ta ce, "Da aka yi me?"
Ɗan'iya ya washe baki ya ce, "Faɗanki da Innarmu mana." Dubu ta zurawa bokitin ragadadar hannunsa ido, take ta ji yawunta ya tsinke, ta kai hannu za ta taɓa ya janye da sauri. Dubu ta riƙe ƙugu tana jinjina kai sannan ta ce, "Ɗan'iya wallahi ko ka bani bokitin nan ko kuma in haɗa gabaɗaya da Shinkafa da waken da shi bokitin ragadadar in kifar da su don wallahi wannan rigimar mun fara ta kenan ni da ku."
Tun ba ta rufe baki ba Ɗan'iya ya soma hawaye ya ce, "Don Allah ki mun rai wallahi Innarmu duka za ta yi min." Dubu ta yi dariyar mugunta ta ce, "Idan ka koma gida in ta tambayeka ka ce ta zo gudanmu ta karɓi kuɗinta." Ɗan'iya ya fara ja da baya Dubu na tsaye ta ce, "Tsaya-tsaya Ɗan'iya gaya mini duka kayan naka na nawa-nawa ne?" Ɗan'iya a tunaninsa rangwame Dubu za ta yi masa idan ta ji tsadar abinci ya taƙarƙare da ƙarfinsa ya ce, "Shinkafa da wake na Dubu biyu ne Ragadadar dubu ɗaya ce." Dubu ta yamutsa fuska ta ce, "To Allah ya yi belinka saboda wallahi da babu kayan nan sai na jiƙa maka jikinka, amma yanzu dole za ka bani bokitin ragadadar nan wallahi, ko in haɗa da kai da su duka na damalmale ku a cikin ƙasa." Ɗan'iya ya yi shiru yana nazari don ya san ciniki ko hamsin ne babu a ciki, Innarsu cin ubansa take bare bokitin Ragadada gabaɗaya. Ragadadar da sai sun yi da gaske suke samu Mahaifiyarsu ta ke basu yanka ɗaiɗai yau ita ce zai ɗauka ɗungurungun ya bada bokitinta.
Dubu na ganin haka ta buga tsalle tana ƙoƙarin janyo robar shinkafar, Ɗan'iya na ganin haka ya miƙa mata da sauri don kar ya yi biyu babu. Wani wawan kuka ya saki lokaci ɗaya ya juya zai koma gida Dubu ta sha gabansa ta ce, "Maza wuce wallahi ba za ka koma gida yanzu ba sai ka sayar da abincin nan salan ka min mugunta tun ban gama cinyewa ba ka sa azo gidanmu. Munafiki yana zare idanu kamar shege a rabon gado." Ta ƙarasa maganar tana ɗake masa ƙeya. Babu yanda ya iya haka ya nufi titi yana share hawayen fargaba da tashin hankali.
Dubu sai da ta saita Ɗan'iya ya bi titi sannan ta bi wani layi bata tsaya ko'ina ba sai cikin wani sabon gini da ba a ƙarasa ba. Zama ta yi dirshan ta kwashi ragadada tana ci tana siɗar romo, kafin wani lokaci tuni ta cinye shi tas, saboda ba ƙaramin daɗi ya yi ba, ya ji farin magi zaƙwai ga ɗan yaji-yaji. Tana gama ci ta sa gefen hijabinta ta goge baki. Ta ɗauki bokitin ta cika shi da yaji ta ɓoye a cikin hijabi ta fice daga cikin kangon.
Dubu bata tsaya ko'ina ba sai ƙofar gidan Hansatu, Hansatu na tsaye a kan ƴarta Mairo da take ta zuba ragadada a ƙananan robobi, ta hango Dubu tsaye a ƙofar gida. Suna haɗa ido Dubu ta ƙarasa ciki kamar mutuniyar kirki ta ce, "A bani ragadada." Tana maganar tana sakin wani irin murmushi. Hansatu ta hangame baki tana yi wa Dubu kallon mamakin wato rashin kunyar Dubu ta bunƙasa haka. Balabare da ke bakin bishiya yana sharɓar ragadada ya yi zaraf ya ce, "Dubulliya ta nawa za a baki?" A fusace Hansatu ta ce, "Ta nawa za ki siya?" Ba musu Dubu ta miƙa naira ashirin nan fa Balarabe ya fara leƙenta yana kashe mata ido ɗaya. Dubu ta ɗauke kai kamar bata gan shi ba. A fakaice Dubu ta sunkuya tana gyara takalminta ta cikin hijabi ta dire mata bokitin ragadada, ta bayan ƙatuwar tukunyar ragadadar. Ta matsa can gefen bishiyar da Balarabe yake zaune. Hansatu mace ce mai matuƙar son kuɗi don duk abin da zai haɗa ku da ita muddin ka zo siyan abu wurinta bata zuciya. Tana da tsumulmula saboda ko ita bata iya zagewa ta ci ragadada idan ba mijinta Balabare da Allah ya jarrabeta da mutuwar sansa ba. Duk abin da Balarabe ya tambaya ba ta iya hana shi. Don haka a ƙa'ida kullin ta sauke tukunyar ragadada kwanonsa daban yake, kuma ko kara ya ajiye ba za ta iya tsallakawa ba.
Hansatu na ɗauko leda ta shiga wurgawa Dubu harara sanna ta fara zuba mata, za ta ƙulle ledar Balarabe ya ce, "Ke Hansatu ƙara mata ta hamsin." Ai kuwa kamar ya watsa mata ruwan zafi ta ɗago a zafafe ta ce, "A kan wane dalili za ka siya mata bayan ɗazun nan yarinyar nan ta gama ci mini mutumci..." Nan fa Hansatu ta zayyanewa Balarabe yanda suka yi, kamar ta rufe bakinsa shiru kake ji sai dai sam ba haka ya so ba, Dubu na karɓar ragadadarta ta nufi hanya za ta fita sai ga Ɗan'iya ya shiga gidan yana kwala ihu.
Da kallon mamaki ya bi Dubu har ta fice, Hansatu don sauri zaninta har faɗuwa yake. Ta fara jefo masa tambaya a hargitse, "Ɗan'iya ina bokitin ragadadar?" Tun bata rufe baki ba ya hau nuna ƙofa ya ce, "Dubu ce ta karɓe mini." Ai kuwa kamar wanda ya ɗanawa wuta haka Hansatu ta zabura tana cewa, "Buhun uban can, kai buɗe baki ka yi mini magana yanda zan fahimta." Dubu na jin haka ta fara zuba sauri bata tsaya ko'ina ba sai islamiyya.
Ɗan'iya ya zayyanewa Mahaifiyarsa abin da ya faru. Hansatu na jin ƙarashen labarin ta shuri takalma garin ɗaukan takalmi ƙafarta, ta shuri bokitin Ɗan'iya da ke cike da yashi. Hansatu ta nuna Bokitin tana faɗin, "Ɗan'iya ba wannan ba ne bakitin da ka fita da shi?" Nan take mamaki ya cika su. Hansatu ta suri bokitin ragadadar da ke cike da yashi, ko ta kan Balarabe bata bi ba ta wuce gidansu Dubu tana kumafar baki.
Lokacin da Yaya babba ta gama jin jawabinta, kallon sheƙeƙe ta yi wa Hansatu sannan ta ce, "Hansatu kura ko mayya kika mayar mini da Dubu da za ta iya cinye bokitin ragadada guda? Allah na tuba me ye ragadada abin da duk yaɗi da jijiya ne, me ye Dubu bata ci a gidan nan?" Takaici ya kama Hansatu ta yi ƙwafa sannan ta ce, "Dama ai sake ta samu shi ya sa take shuka tsiyar da take so, to wallahi daga kaina ba za ta sake yi wa wani haka ba." Tana gama masifar ta fice, Inna furai ta bita har soro tana mayar mata da martani.
"Aniyarki ta faɗa kanki, azzulama mai baƙin baki. Bayan zazzagar iya shegen da kika yi mata shi ne bai ishe ki ba za ki biyota har gida kenan." Sai da ta ga ficewar Hansatu ta juya ta samu Yaya tana faɗin, "Yaya an ya maganar yarinyar nan bata kan hanya, na san halin Dubu sarai za ta iya tare yaron nan ta karɓe bokitin ragadadar fa." Yaya babba ta yi ƙwafa cike da takaici ta ce, "Ai kuwa wallahi da na ɗebe mata falsafar albarka alƙur'an da babu ni babu ita."
Hansatu kai tsaye wurin mai unguwa ta wuce bayan ta kwashi gaisuwa ta zayyane masa abin da yake faruwa, ba shiri ya aika da kiran gaggawa gidan Marigayi mai carbi. Zuwan dogarawan ya yi daidai da zuwan Baba Abubakar shi da Aseem, wannan sammaci ba ƙaramin ɓata ran Baba Abubakar ya yi ba. Ya ci alwashin idan kuwa haka ta tabbata Dubu ce ta cinye ragadadar, tabbas ba ƙaramin hukunci zai ɗauka akanta ba don duk abin da Yaya babba za ta faɗa sai dai ya toshe kunnuwansa. Shi da Aseem suka wuce wurin mai unguwa ba tare da sun shiga cikin gidan ba. Suna zuwa aka aika kiran Dubu, tare da Dogarawan suka taho tana zuwa ta yi turus! Jiki a sanyaye ta zauna ta hangi Aseem na wurga mata harara sai Ɗan'iya da idanunsa suka yi wuri-wuri, saboda kukan da ya sha. Hansatu lokaci-lokaci take kallon Dubu tana ƙwafa cike da jin haushi.
Shiru wurin ya ɗauka Mai gari ya ƙurawa Dubu ido yana son gano gaskiyar lamari, don ya san sarai Dubu za ta yi abin da ya fi haka, bayan an gabatar da abin da ya tara su a wurin, Mai unguwa ya kalli Ɗan'iya ya ce, "Ɗan'iya ko za ka gaya mana yanda abin da ya kasance." Ɗan'iya ya fyace majina sannan ya zayyane duk abin da ya faru tsakaninsa da Dubu. Tun bai rufe baki ba Dubu ta yi caraf ta fara magana, "Alƙur'an ƙarya yake yi mini haka kawai zai yi mini sharri saboda ba ƙaunata ake..." Da sauri Baba Abubakar ya katse ta yana yi mata daƙuwa Hansatu ta tura ɗankwali gaba tana faɗin, "Allah ya taimakeka ka yi mini tsakani da Dubu wallahi muddin ta sake shiga gonata sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Ƙwaranƙwatsa kuma sai an biya ni kuɗin ragadadata." Mai unguwa zai yi magana Aseem ya zaro dubu biyar ya miƙawa Hansatu yana faɗin, "Shi kenan magana ta wuce." Dubu na gefe da ta ga maƙudan kuɗin da aka bawa Hansatu ta yi zaraf ta ce, "Wallahi ragadadarta bata kai da kuɗin nan bayan kafin na karɓi bokitin Ɗan'iya ya ce mini ta dubu ɗaya ce." Ta ƙarasa maganar za ta warci kuɗin da sauri Hansatu ta maƙe su tana cewa, "Ai irin wannan asara kullin ma Allah ya kawo ta." Baba Garba saboda ɓacin rai sallama ya yi wa Mai gari ya tafi ya tafi, shi kuwa Aseem hannun Dubu ya fisga suna tafe yana haɗa hannunsa da nashi yana murzawa. Ban da wash! Babu abin da take yi saboda yanda hannunta yake yi mata raɗaɗi.
Suna shiga cikin gidan suka wuce sashen su Yaya babba har lokacin hannun Aseem na riƙe da Dubu. Tun da Yaya babba ta hango su take sakin murmushi, don shi kansa Aseem har sai da ya saki murmushi saboda yanda ya ga kakar ta shi cikin farinciki. Tun kafin su zauna ta sake washe baki tana faɗin, "Allah ƙadiran alamanyasha'u. Ikon Allah! Allah mai sanin abin da yake cikin zuciya." Gabaɗaya ba su kawo komai a ransu ba sai ɗan murmushi da suka yi. Bayan sun gaisa cikin ɓacin rai Baba Abubakar ya fara yi wa Dubu faɗa, kasancewar mutum ne ba mai zafi ba ya sa bai cika faɗa ba, amma Dubu ba ƙaramin tsora ta yi ba. Saboda dama mai haƙuri bai iya faɗa ba. Yana gamawa Yaya babba ta dasa nata faɗan.
"Maganar gaskiya Dubu kin wulaƙanta ni ki rasa me za ki karɓarwa yaro sai ragadada?" Inna Furai ce ta shiga ɗakin tana girgiza kai ta ce, "Don Allah Garba ka ji wata muguwar ɗabi'a, ka gaya mana meye Dubu bata ci a gidan nan?" Yaya babba ta yi ƙwafa ta ce, "Gane mini hanya Furaira neman maganar fa. Garba ka rabani da Dubu tun takaicinta bai kashe ni ba, ba zan iya ba gaskiya ba za ta ƙara kwanar mini a ɗaki ba. Ina dalili ta kashe ni ta cuci iyalaina, ko da dai kun girama shi fa Maraici ba daɗi gare shi. Don Allah Garba idan babu ni ba kun zama marayu gaba da baya ba? Na gaji gaskiya, ka sa Dubu a gaba ka tafi da ita na bar maka ita halak malak."
Baba Abubakar ba ƙaramin daɗi ya ji ba, don dama ya jima yana san ɗaukan Dubu Yaya babba ce take hanawa. Ya gyara zama ya ce, "Dama Inno na daɗe ina yi miki maganar amma yanzu tun da kin amince zan tafi da ita." Madadin Yaya babba ta yi magana sai ta yi jim sannan ta ce, "Ni fa Garba ba raba ni da Dubu ne bana so ka yi ba, gaskiya a riƙa zalintar marainiyar Allah ne bana so. Wannan matar taka ba ƙaunar Dubu take ba, sai ta zo ta yi ta gallazawa marainiyar Allah, ina nan ban san halin da ake ciki ba. Kai kuma mutuwar sonta kake ballantana ka tsawatar mata. Gidan Ado kuma Fauziyya sai jaraba mace sai masifa ko ƴaƴan cikinta ba ƙaunarsu take ba bare kuma Dubu, raba ni da bawa Ado Dubu ana zaune ƙalau. Ita kuma waccan mai tausayin ƙasar komai nata ba kuzari ina dalili inkai Dubu ta riƙa barinta da yunwa? Ni inbawa Rahama Dubu ta kashe ta da yunwa Allah ya tsare ni. Don Allah Garba wacce riba suke ci wai Rahama basa karyawa sai goman safe, mu da anan ƙarfe goma an fara haramar na rana. A'a gara Dubu ta yi zamanta a nan ina ganinta ina jin daɗi." Baba Abubakar ya girgiza kai don dama sai da ya ayyana haka amma ya ci alwashin ko da dabara sai ya karɓi Dubu muddin ya dawo gidan da zama, don barinta a haka har girmanta akwai gagarumar matsala.
Yaya Babba ta kalli Inna Furai ta ce, "Furaira ki gaya masa mana ai kyayi mini kara dai ko?" Inna Furai ta washe baki ta ce, "Garba wani abin alkhairi muka hango kuma mun san da kai da kaya duk mallakar wuya ne. Mun yanke shawara ni da Yaya ya kamata a ci gaba da yaɗa zumunci." Gaban Baba Abubakar sai da ya faɗi don ya san wataƙila wani abin za su ɓallo masa.
Inna Furai ta karɓe zan cen da cewa, "Ka san dai bikin su Salisu da su Zulfa bayan babbar sallar nan ne kuma dududu bikin saura wata guda ina jin." Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, "Ai ina jin lokacinma mun dawo nan." Inna Furai ta yi dariya ta ce, "Ai za ku sha hidima tun da auren ƴaƴa shida ba wasa ba." Baba Abubakar ya yi murmushi don shi kansa idan ya tuna bikin har daɗi yake ji ace cikin gidansu za su aurar da ƴaƴa shida maza da mata kuma duk auren gida abin akwai farinciki.
Yaya babba ta katse masa tunani da cewar, "Ka ga da Zulfa da Bintu duka Dubu fa ta girme musu." Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, "Ai suma Yaya don kun matsa ne amma duka nawa yaran suke?"
Nan take Yaya babba ta ɓata fuska ta ce, "Yara dai Allah ya kawo musu mijin aure kar ka yi musu buƙulu, kai da ɗan'uwanka ba kun ɗorawa kanku bokon jaraba ba. To gaskiya bana son hassada Garba kuma na yanke shawarar haɗa Dubu da Soja don gaskiya ba za a zo ana yi mata gori ba tun da ƙawayenta kusan duka sun yi aure wasu ma sun haihu."
*DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
FREE PAGE 10
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels
Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.
Baba Abubakar da Aseem lokaci guda suka ɗago suna kallon Yaya babba, da ta ci gaba da zayyano zance ko a jikinta. Dubu na maƙure a gefe sai raba idanu take don ita kanta ba ta san da wannan shawarar da Yaya babba ita da Inna Furai suka yanke ba. A madadin fushi sai ma wani murmushi da Aseem ya ke yi, wanda kana gani za ka tabbatar da murmushin mamaki ne da tsantsar baƙin ciki. Yaya babba da bata kawo komai a ranta ba ta ci gaba da cewa, "Allah ya sani dama wannan ne dalilin da ya sa na aika kiranka kai da Soja, don kune maganar ta shafa ba su Munkaila ba. Waye ya haifa maka Soja bayan kai da uwarsa Nafisa?" Yaya babba ta tambayi Baba Abubakar. Shiru ya yi yana murmushinsu na manya, sannan ya ɗago da kai ya ce,
"Inno na ji daɗin wannan maganar ta ki, kuma ni zan fi kowa farinciki da wannan haɗin domin abin da ya yi Dubu shi ya yi Aseem. Amma wani hanzari ba gudu ba..." Da sauri Yaya babba ta katse zancensa da cewar:
"Don Allah Garba ka faɗi alheri ko ka yi shiru. Wannan fa abin farinciki ne, kuma me ye aibun Dubu yarinya san kowa ƙin wanda ya rasa. Ƙwaranƙwatsa dubu babu abin da Soja zai nunawa Dubu, kyau ya fita ko tsafta? Yarinyar da sai ta yi wanka sau uku a rana ko ba haka ba Furaira?" Inna Furai ta taɓe baki ta ce, "Ina dalili tun ba a ji ta bakin yara ba Garba za ka kawo mana hanzari, wannan kamar zazzage albarkar da ke cikin auren za ka yi. Gaskiya karka ɓata auren yara tun ba a je ko'ina ba, yoo Allah na tuba wane hanzari gare ka da ya wuce ka sa albarka?"
Baba Abubakar ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Inna ni fa baku fahimce ni ba. Ina nufin su yaran a fara ji ta bakinsu don kar ayi abu ba da son ransu ba. Amma idan kuna faɗin haka sai in ga kamar kuna nuna Dubu da Aseem ba ɗaya ba ne a wurina." Yaya babba ta washe baki ta ce, "Shi dai Soja na san ai ba zai ƙi ƴar uwarsa ba, ita kuwa Dubu kar ku ji ta, na san ta yanda zan shawo kanta." Aseem saboda takaici miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin, Yaya babba na ganin haka ta saki dariyar farinciki tana faɗin,
"Ai na gaya muku wannan shiru-shirun da yake yi wallahi aure yake so, ja'iri ga shi nan kunya ta kama shi ya fita yana sunne kai, yoo waye zai samu Dubu bai yi farinciki na? Alƙur'an ana auren ku basu wata tara sai dai ku ji haihuwa, Soja wai mu zai yi wa hikima bai san na daɗe da gano lagwansa ba." Baba Abubakar ya yi shiru yana nazari domin ya san ba ƙaramin ruwa Yaya babba ta kunto masa ba, saboda ko makaho ya shafa fuskar Aseem ya san yana cikin yanayi marar daɗi. Saɓanin Dubu da ba za ka tantance ainihin halin da take ciki ba, na farinciki ne ko baƙinciki ba.
Yaya babba cikin murmushi ta kalli Baba Abubakar ta ce, "Yanzu dai Garba ka je ka shaidawa Nafisa halin da ake ciki don a fita haƙƙinta na mahaifiya, kar ta ji magana daga sama don ma bata da fushi ba kamar Fauziya Matar Ado ba, kai gaskiya Garba duk cikin ƴan uwanka akwai wanda ya yi dacen mace irinka kuwa? Allah ya sani Nafisa macen arziƙi ce idan na zageta sai dai na yi mata ƙazafi. Suma ƴan uwanka zan shaida musu abin da yake faruwa don kar su ji maganar aure bagatatan, na san Sule da baƙar zuciya sai ya ɗau fushi da ni ba gaira babu dalili. Yo ko auren na yi musu ban sanar musu ka ga laifina Garba? Kai ne dai uban soja halak malak, wani ne ya haifa mini kai? Ni ina na iya gaba halin ƴan wuta, ina masoyiyar Annabi (S.A.W) me zai haɗa ni da wuta ana zaune ƙalau? A'a rabani da wannan falsafar zan sanar da su da kaina, kar shaiɗan ya ɗebe ni idan suka ɗau gaba da ni na biye musu, ana zaune ƙalau na tsine musu su ɓalɓace." Baba Abubakar ya zaro kuɗi a aljihu ya dire musu a gabansu ya yunƙura jiki ba ƙwari ya ce, "To shi kenan Inno Ni bari na wuce." Cikin haɗin baki Yaya babba da Inna Furai suka fara faɗin, "Ka gaida gida Allah ya yi albarka."
Yana fita Dubu ta ɓata fuska ta ce, "Wai ke Inno ce miki na yi ina son shi bayan mugu ne, baki ga irin wuyar da ya bani ba rannan." Yaya Babba ta rungumo Dubu cikin lallashi ta ce, "Ke yi shirunki, kin san me ya sa na yi wannan haɗin?" Dubu zuciyarta ɗaya ta girgiza, Yaya babba ta ci gaba da cewa: "Allah ya sani Dubu idan ba mutuwa ba zan iya rabuwa da ke ba. Idan kika auri Soja a cikin gidan nan za ku zauna, ga wuri nan a gyara masa ku yi zamanku. Amma idan bare kika aura kin san dole ki fice daga gidan nan. Na san irin rayuwar da za ki yi a can gidan? Sam! Ba zan laminta ba a rabani da Marainiyar Allah ina ji ina gani." Daɗi ne ya kama Dubu lokaci ɗaya ta washe baki cikin farinciki. Lokaci ɗaya kuma sai ta ɓata fuska ta ce,
"Inno idan ya harbe ni da bindiga fa? Wallahi ba shi da tausayi tsaf kashe ni zai yi." Inna Furai ta hau jinjina kai sannan ta ce, "Wallahi har kotun ƙoli sai mun je a kan shari'ar nan. Ke bar zancen bindiga tsaf za ki saye zuciyar shi, tun da da me na birnin za su fiki?" Dubu ta ci gaba da washe baki tana jin nishaɗi ita a dole za ta auri Soja kuma ɗan gayu.
A ranar Yaya babba da Inna furai suka gama isar wa da Mutanen gidan, hukuncin da suka yanke har suke ɗorawa da cewar, yara tuni sun haɗa kawunansu don Aseem tsabar kunya tun da ya fito bai dawo ba. Ita kuma Dubu ban da murmushi babu abin da take yi, nan fa ƙananan maganganu suka fara tashi a cikin gidan kowa da abin da yake tsakura yana isarwa.
Lokacin da Baba Abubakar ya fita a cikin mota ya samu Aseem, yana zaune ya haɗa kai da sitiyari. Har Mahaifinsa ya shiga bai sani ba ya zurfafa cikin tunani. Da kallon tausayi ya dubi ɗan nasa ya ce,
"Aseem!" Jiki a sanyaye idanu jawuri ya ɗago ya kalli Mahaifinsa, murya a shaƙe ya ce, "Na'am Daddy."
"Dukda ban shiga zuciyarka ba amma san wannan hukuncin ba lallai ya yi maka daɗi ba." Kamar mai jira ya shagwaɓe murya yana faɗin, "Yanzu shi kenan Daddy duk abin da su Inno suka faɗa, komai ta ce sai dai ku hau ku zauna? Gaskiya ni kam babu yanda za a yi na auri waccen yarinyar. Yarinyar da kowa ya san bata da nutsuwa, don Allah Daddy ya za a yi ma na auri wata Dubu? Never wallahi." Ya ƙarasa maganar a shagwaɓe kamar zai yi kuka. Baba Abubakar ya yi murmushinsu na manya ya ce, "Rashin nutsuwarta ba komai ba ne idan har kana sonta, kai namiji ne za ka iya nusar da ita akan abin da ya dace." Cikin hanzari ya furta, "Ni ba na ma sonta, Allah ya sani ta nemi wani ta haɗa ta shi amma ba ni ba."
A karo na biyu Baba Abubakar ya sake kiran sunansa, "Aseem." A marairaice ya ɗago ya amsa sannan Mahaifinsa ya ci gaba da cewa, "Inno fa mahaifiyata ce kana ganin zan iya kaucewa umarninta, idan har ina neman albarka duniya da lahira? Su fa iyaye biyayya ake musu akan duk abin da suka buƙata matsawar bai saɓawa mahallici ba, ko da kuwa baka ƙaunar abin sai ka ga wata rana abin ya zame maka alkairi." Murya a raunane Aseem ya ce, "Daddy nima ban taɓa saɓa umarninka ba, amma maganar gaskiya idan aka tilasta ni na auri Dubu sai dai na barta a gidan nan, na yi tafiya ta."
"Da ka wulaƙanta ƴar ɗan'uwa bayan ka aureta; ai gara ka ce mini ban isa na saka ko na hanaka ba. Zan yi ƙoƙarin ganin na shawo kan Inno idan ta amince shi kenan, idan bata amince ba, ka yi haƙuri ka amshi ƙadaddararka hannu bibbiyu, ka san kowanne bawa baya kaucewa ƙaddararsa, ta yiwu alkairin na gaba kai da kanka za ka ji daɗin haka. Saboda sautari muna ƙin abin da shi ne alkairi a tattare da mu sai daga baya mu fahimci haka." Shiru ne ya ratsa Aseem ya kasa furta komai, zuciyarsa ban da zafi babu abin da take yi masa. Jiki a sanyaye ya tuƙa mota suka wuce gida, kowa na saka da warwara a cikin zuciyarsa.
Tun shigar su cikin gidan Hajiya Nafisa ta fahimci gabaɗaya babu mai cikakkiyar walwala a tattare da su, har ta fi damuwa da damuwar Aseem saboda Baba Abubakar ba wani zaman daɗi suke yi ba, duk akan maganar komawarsu Ɗangwauro. Aseem na shiga ɗaki ta bi bayansa, a ɗaki ta same shi yana kaiwa da kawowa haɗe da kaiwa bango naushi. A ɗan tsorace ta fara watsa masa tambayoyi:
"Lafiya Asem? Wani abin ne ya faru da ku daga kai har Daddynku na ga baku da walwala?" Murya a can ƙasa ya ce, "Mommy babu komai, kawai wurin aiki ne suka kira ni akan wani issue ɗin." Kallon tsaf ta yi masa tana son gano gaskiyar abin da ya faɗa sannan ta ce, "An ya ba wani abin ne yake faruwa a Ɗangwaro ba?"
Da sauri ya kalle ta sai kuma ya ɗauke kai gefe saboda ambatar sunan garin, ba ƙaramin dawo masa da ɓacin rai ya yi ba, ya zauna a gefen katifarsa ya dafe kansa da hannu bibbiyu ya ce, "A'a Mommy." Taɓe baki ta yi ta ce, "Idan ma wani abin kuke ɓoyewa indai Hajiya babba ta kafe kai da fata na san ko ba daɗe ko ba jima zai fito fili." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin.
Aseem ya ƙi sanar da Mahaifiyarsa ne saboda ya san Daddynsu ba zai taɓa sanar mata a wannan ranar ba, duba da yanayin zaman da suke a wannan lokacin. Uwa-uba kuma ya san idan ya gaya mata kamar ya ƙara hura wutar tashin hankali a tsakanin iyayen nasu ne. Lokaci ɗaya tsanar Dubu ta mamaye zuciyarsa don duk ita ce silar komai, dukda hali irin na mahaifiyarsa tun da ya taso bai taɓa jin suna sa'insa ita da Mahaifinsa ba. Amma lokaci ɗaya ta tarwatsa farincikinsu ga auren iyayensu, da yake tangal-tangal tun da har lokacin Hajiya Nafisa na kan bakarta da ta koma ƙauyen nan, gara ya sallameta ta kwashi ƴaƴanta, ta riƙe a wurinta ko sa samu irin mijin da take buri da fatan su samu. Kamar yanda ta gama yi wa Aseem tanadin ƴar ƙawarta, saboda komai ta fi so su yi cikin bajinta da harkar girma.
A daren ranar ya haɗa kayansa tsaf a cikin jaka, washegari da sassafe ya wuce Lagos da yake acen yake aikinsa. Wannan ya ƙara tabbatarwa da Hajiya Nafisa tabbas akwai wata a ƙasa, amma zafin zuciya irin nata ya sa ba za ta iya tambayar mahaifinsa don jin abin da yake faruwa ba. Kuma ta lura shi kansa har lokacin baya cikin walwala, ga yawan waya da ta ga yana yi da ƴan'uwansa. Ga shi ba wata kyakkyawar alaƙa gare ta da facalolinta ba, bare ta kira ɗaya daga ciki don ta ji halin da ake ciki ba.
BAYAN SATI BIYU
Duk wani daɗin baki da dabara irin ta tsofaffi Yaya babba ta yi wa Dubu, kuma tuni ta ji ta aminta da Aseem a matsayin mijin aure. Don ba ƙaramin ƙawatawa Yaya babba ta riƙa yi mata ba, tana nuna mata irin rayuwar jin daɗin da za ta yi matuƙar da auri Aseem, hatta wanki ta daina sai dai ya ɗauko mai yi mata. Kan Dubu ba ƙaramin girma ya ƙara ba don ji ta yi duk faɗin garinsu babu wacce ta yi dacen mijin aure sama da ita.
Tuni maganar auren Aseem da Dubu ta karaɗe cikin ƙauyen Ɗangwauro, mutane da yawa mamakin wannan haɗin suke yi ganin Aseem cikakken ɗan gayu amma ya ƙare a auren Dubu. Cikin dangi sai tsegungumi ake da wannan maganar, lokacin da labarin auren Aseem da Dubu ya isa kunnen Hafsa ƴar wurin Hajiya Fauziyya, zama ta yi dirshen tana kuka don duk duniya babu wanda take so da ƙauna sama da Aseem, amma rana tsaka a ce wai Dubu ita ce za ta aure shi. Tun daga ranar ta bar walwala bata da aiki sai zaman ɗaki, ga shi an yi tambayar duniya ta ƙi faɗa, sai dai ta ce bata jin daɗi.
A wannan lokacin saura kwana uku tariyarsu a Ɗangwaro, sun gyara sashensu da sauran ɓangarorin gidan, gidan ya fito kamar a birni. Har fasalin ƙofar gida suka sauya suka rushe gaban gidan, suka saka ƙaton gate wanda mota za ta iya shiga har harabar wurin da suka zagaye da ya zama wurin parking space. Haka bikin su Dubu a lokacin saura sati biyu cif, su Yaya babba har an fara gyaran Amare. Aseem da Dubu a gefen sashen su Yaya babba aka gyara musu, gini ne mai ɗaki uku sai kitchen da banɗaki. Sai Salisu da Zulfa suna maƙota da su Dubu, Bilalu da Murja suna maƙotaka da Baba Auwalu sai kuma Bashari da Maryama a suke maƙotaka da su Baba Adamu. Duk gyaran da ake wa amaren Yaya babba da Inna Furai sune jigo da ragamar komai.
Sai dai duk wannan budurin da ake yi mai gayya mai aiki, Mahaifiyar Aseem bata san wainar da ake toyawa ba har sai ana gobe tariyarsu, a lokacin da suke tsaka da hatsaniya ita da mijinta. Suma ganin Manyan akwatuna ta yi a ɗakinsa kishi ya rufe mata ido don a tsammaninta idan sun koma Ɗangwaro aure zai ƙara. Bayan ya gama sauraronta ya saki murmushin ƙeta don ya san muddin ya sanar da ita abin da yake faruwa ba lallai ta samu damar runtsawa a ranar ba. Saboda yana da tabbacin Aseem bai sanar mata da abin da yake faruwa ba, saboda har lokacin shi ma ɗaukan maganar yake kamar almara. Kafin lokacin akwai lokacin da Baba Abubakar ya kira a kan maganar kayan lefe, amma babu wata tsayayyiyar amsa da Aseem ya bashi. Hakan ne ya sa ya bugi ƙirji ya yi masa komai, saboda idan ya biye ta tashi ya san babu abin da Aseem zai yi.
Shi kuwa Aseem har kullin sai ya yi yunƙurun sanar wa mahaifiyarsa halin da ake ciki, amma fargabar tashin hankalin da za a shiga sai ta hana shi, don haka ya danne a bari Mahaifinsa ya sanar mata da kansa. Kuma dama sun riga da sun yi maganar shi da Mahaifinsa ya ce masa kada ya gaya mata har sai shi ya tunkareta ya gaya mata.
Bakinsa ɗauke da murmushi ya ce, 'Kanyan ɗanki Aseem ne za a kai masa na aure, yanzu haka saura sati biyu bikin dama ko baki tambaya ba yau na yi niyyar sanar da ke." Ku san suman tsaye ta yi jikinta har rawa yake ta ce, "Idan ma wasa kake min don Allah ka fito ka gaya mini gaskiya, idan aure za ka ƙara ba sai ka ɓillo min ta wannan sigar ba." Bai tanka mata ba ya buɗe durowar kayansa ya zaro katin ɗaurin aure ya miƙa mata. Hannu na rawa ya karɓa ta fara karantawa da yake ɗaurin auren mutane da yawa ne, sai ba za ido take don ta ga sunan Aseem da sunan Amaryar da za a aura mata ba tare da ta santa ba.
Ƙauyen Ɗangwauro.
"Inno kullin haka kike faɗa amma fa har yau ko kirana a wayarki bai taɓa yi ba, kina ganin su Zulfa kullin cikin waya suke." Dubu ta faɗa tana kwaɓe fuska. Yaya babba ta washe baki ta ce, "Kin san Soja da kunya, tun yana yaro duk cikinku babu mai kunyarsa. Allah na tuba wacce kunya gare ku rannan ina jin Zulfa tana waya akan gadona, munafukar yarinyar ta ɗauka bacci nake har cewa take ko Lobin-lobin ko I Lobiyu. Wai har da cewa tana kewarsa. Don Allah Dubu ki ji mini falsafar rashin kunya ta dubi gardi kamar Salisu ta ce, tana kewarsa wannan bata cancanci istigifari ba?" Dubu ta bushe da dariya ta ce, "Yasin Inno kaɗan ma kika ji." Inno ta dafe ƙirji a tsorace sannan ta ce:
"Au tana faɗin abin da ya fi haka? Amma dai Zulfa an yi ƴar banzar yarinya, ta yi ta sunne kai ƙasa kamar mumina ashe shakiyya ce." Dubu ta ɗauko wayar Yaya babba ta ce don Allah Inno ki kira min shi."
Yaya babba ta ƙanƙance ido tana kallon wayar ta ce, "Kin san dai ba iya nemo lambarsa na yi ba, duba ki kira shi." Cike da ɗoki Dubu ta fara dubo lambar Aseem sai da, A ɗin kawai ta riƙe amma takamaimai sunan Aseem ba ta san shi ba. Sai da ta kira mutane biyu waɗanda sunansu ya fara daga A, na farko ta kira Baba Adamu da aka sawa Yaya babba sunansa da Ado sai lambar Auwalu. Sai a na uku ta samu ta yi nasarar kiran Aseem.
Cikin wata irin sanyayyiyar murya ta ji ya ɗauka da cewa, "Salamu alaikum." Lumshe ido ta yi ƙirjinta na bugawa ta yi ta maza ta ce, "Wa'alaikas salam."
Jin ba muryar Yaya babba bace ya sa ya furta, "Wace?"
"Me lob ni ce na kira ka, Dubu ce i lobiyu." Dubu ta faɗa cike da ɗoki don ta saba jin waɗannan kalaman a bakin su Zulfa idan suna waya da samarinsu, suna cewa My love da i love you.
[7/1, 10:17 PM] Ameera Adam🌚: *DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV
FREE PAGE 11
Aseem kusan sandarewa ya yi da jin kalaman Dubu, don ya fahimci inda maganar tata ta dosa dukda bata faɗa yanda ake furtawa ba. Babban abin da ya fi ba shi mamaki yana yi mata kallon ƙaramar yarinya sakarai marar wayo, ashe shi take yi wa kallon haka? Tun da har ta san ta kira saurayi ta ce masa My Love, ba tare da kunya ko jin nauyi ba. Jin ya yi shiru ya sa Dubu ta saci kallon Yaya babba ta sake cewa:
"Me lob wallahi ina ta kewarka kuma na yi musun ɗinka." Yaya babba na jin haka ta saki murmushin farinciki, don bata ɗauka Dubu za ta iya nutsuwa lokaci ɗaya ta yi waya da saurayi a haka ba.
Aseem bai gama tunani ba Dubu ta sake jefa shi cikin kogin mamaki, da jin kalaman da idan za a sa mata wuƙa bata san takamaimai abin da suke nufi ba. Dubu ba ta damu da jin shirun da ya yi ba ta ci gaba da jawabi.
"Me lob dama kiran da na yi maka don mu gaisa ne, na san kaima ka yi kewata; kuma ban ji ka ce komai ba..." Tun bata ƙarasa ba ya buga mata tsawar da ta katse ragowar kalamanta da cewar: "Ke! Kina hauka ne?" A tsora ce Dubu ta zame wayar daga kunne, ganin haka ya sa Yaya babba ta kalleta tana faɗin, "Dubu lafiyarki kike razana kamar wacce aka ɗanawa wuta?" Wayar Dubu ta miƙa mata tana faɗin, "Riƙe ki ji abin da yake faɗa Inno." Da sauri Yaya babba ta karɓi wayar ta sa a kunne tana faɗin, "Sojaaa." Aseem na jin haka ƙit ya kashe wayar yana huci. Maganganun Dubu sun jima suna yi masa yawo a rai, yana mamakin har yaushe ta ga makwancinsa da za ta kira shi a waya tana ce masa My love.
Yaya babba ta yi zuru tana nazari sannan ta ce, "Dubu me kika yi wa Soja da zafi haka da zai hau yi miki barazana?" Dubu ta kwaɓe fuska ta ce, "Inno kina ji dai a gabanki na yi wayar." Wayar ta sake miƙawa Dubu ta ce, "Maza lalubo mini lambar Garba, alƙur'an idan shi yake zuge shi a kanki zan ji dalili. Saboda Allah me ya sa Garba ya cika hassada? Dama tun rannan na lura da hassadar da yake yi wa Soja akan aurenki. A'a ba halina ya gada ba bare kuma mahaifinsa, Allah ya sani wannan ɗabi'ar ƴan wuta ce idan kuma Garba ya ɗore a haka na shiga falsafar tashin hankali a ce jinina na da ɗabi'ar ƴan wuta ina na kama." Dubu ta gama dube-dubenta ta miƙawa Yaya Babba wayar ta ce, "Kin san dai ba iya nemo lambarsa na yi ba Inno kawai ki kira Baba Munkaila, ki sa ya kira shi" Suna cikin haka Salisu ya shiga shi da abokinsa Musbahu, da sauri Yaya babba ta miƙa masa waya ta ce, "Maza kira mini Garba." Da ido ya tsare Dubu da kallon tuhuma, don ya san ita take juya Yaya babba kamar waina, ya ce, "Me za ki ce masa Inno."
"Me ye ma ba zan ce masa ba Ɗan nan? Ka kira mini shi idan ba za ka kira ba, wuce ka kira mini ubanka ko Munkaila in sa su kira shi." Gudun magana irin na Yaya babba ya sa ya karɓa ya kira mata Baba Abubakar, sai dai an yi rashin sa'a wayar a kashe take.
Musbahu abokin Salisu cikin ladabi ya gaishe da Yaya babba ta washe baki ta ce, "Lafiya ƙalau Musbahu ya Uwale?" Ya amsa mata cikin girmamawa, Yaya babba ta ɗora da cewa:
"Ina ma Soja ya samu abokan ƙwarai irin ka Musbahu, don Allah da bai more ba? Don Allah waye ba ya san farantawa, ka duba yarinyar nan Dubu daga kiran Soja zai fara sauke mata falsafar rashin mutumci, ana zaune ƙalau don Allah wannan halin mutumci ne?" Musbahu ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya bai kyauta ba Inno, amma ki yi haƙuri."
"Don Allah rabani da haƙurin nan Musbahu! Kai Salisu ba ina ji rannan Zulfa na ce masa tana kewarka ba. Musbahau don Allah ka ji wata lalata irin ta ƴaƴan zamani. Lokacin da aka ɗaura auren uwar Zulfa, ni kaina da nake uwar miji sai da ta kwana a ɗakina, kwananta biyu tana gudun miji za ta yi na uku na ce, a'a ta rabani da wannan falsafar kar Munkaila ya ɗau gaba da ni ana zaune ƙalau. Munkaila kunya Kulu kunya yooo gadon wa tayo a cikinsu na rashin kunya? Don Allah gane mini hanya Musbahu." Salisu ya karɓe zancen da cewa, "To ke tsohuwa ina ruwanki da sa ido ne?"
Kafin Yaya babba ta yi magana Baba Munkaila ya shiga ɗakin da sallama, Yaya babba na ganinsa ta saki dariya ta ce: "Ɗan halaka kaƙi ambato!" Baba Munkaila ya yi murmushin jin daɗi don ya ɗauka labarin wata bajintar ta shi Yaya babba take bayarwa, da ta ganshi ta faɗi haka.
Yaya babba sai da ta ga Baba Munkaila ya zaune a gefe kusa da ita, ta ɗaga faifai ta miƙa masa kwaɗon rama ta ci gaba da cewa, "Kun ganshi nan a daren angwancinsa ma kasa shiga ɗakin amarya ya yi, kunya dai a cikin Munkaila har da ta siyarwa. Ashe biyu ce ta haɗu shi kunya Kulu kunya, yoo bayan kwana biyu ba sai amarya ta hau guje-guje ba."
Kunyar duniya ta kama Baba Munkaila da ke zaune a ɗaki ɗaya, da Ɗansa Salisu kuma saurin babbar ƴar sa Zulfa da ake shirin ɗaura musu aure. Hakan ce ta faru a ɓangaren Salisu ba ƙaramin kunya ya ji ba, daga shi har Musbahu aka rasa mai bakin magana. Dubu na gefe sai sunne kai take tana dariya ƙasa-ƙasa, musamman da ta lura da yadda Baba Munkaila ya yi fiƙi-fiƙi da idanu, ba abin ya tashi ba yaran ɗakin su fahimci abin da ya tashe shi daga ɗakin. Yaya babba kuwa ko a jikinta ta ci gaba da cewa:
"Kai Allah dai ya sawaƙe kuma bayan kwana biyu fa sai ganin ciki muka yi, na yi dariya na ce Allah mai iko ashe dai rabon a kusa yake. Yoo ashe kunyar duk ta banza ce ban sani ba sai ranar da Kulu take naƙuda." Salisu ya yi karaf ya ce, "To mu dai ba tambayarki muka yi ba." Saboda kunya Baba Munkaila kasa ɗaukan lomar hannunsa ya kai baki ya yi.
Yaya babba ta taɓe baki ta ce, "Salisu ka fita a idona tun da ba kai nake gayawa ba, Musbahu ko ka ji na ambaci sunansa?" Musbahu ya ce, "A'a Inno." Dubu da ke gefe ta ce, "Inno idan baya son jin labarin ai mu muna so." Baba Munkaila ya zuba mata uwar harara, Ita kuwa Yaya babba kamar wacce aka ƙarawa ƙaimi ta ce, "Allah dai ya yi miki albarka Dubu. Kin ga Munkaila ban taɓa sanin ya iya waƙar salawatu ba alƙur'an sai ranar da Kulu take naƙudu. Ranar mun ga abu iri-iri ni da Furaira, daga fara biya mata suratul Khaifi sai ya zarce da salawaitu. Ni kuwa na hau istigifari don ina gudun fushin Ubangiji an haɗa ayarsa da waƙa. Ban tsinke da lamarin Munkaila ba sai da na ga yana kuka wai ta mayar masa cikin jikinsa. Ni kuwa na ce raba kanka da haihuwa Munkaila idan cikin ya dawo jikinka, daga nan har ƙofar dawanau sai an ji ihunka. Yo wa ya gaya masa haihuwa ta maza ce wannan jarumtar sai mata..." Baba Munkaila a hanzarce ya miƙe zai fita daga ɗakin, saboda tun da yake bai taɓa jin kunya irin ta ranar ba, bisa tsautsayi ya yi tuntube jallabiyyar jikinsa ta taɗe shi ji kake kiriiiiif ya zube a ƙasa.
Dubu kuwa ta kwashe da wata irin dariyar ƙeta, don dama ta jima tana dannewa bata samu ta yi dariyar ba sai ta wannan dalilin. Salisu na ganin sirikinsa ya faɗi ya fara faɗin, "Subhanallah Sannu Baffa." Duk suka yi carko-carko Salisu na son zuwa ya taimakawa Baba Munkaila yana fargabar faɗansa, Musbahu da yake gimtse dariyarsa ya kalli Salisu yana yi masa inkiya da ya je ya taimaka masa. Yaya babba ta riƙe haɓa tana faɗin,
"Ikon Allah wai na kwance ya faɗi. An ya Munkaila baka taɓa yi wa mutanen wurin nan fitsari a tsakiyar kai ba kuwa? Idan ban manta ba wannan ce faɗuwarka ta biyar tun daga haihuwarka. Ta ƙarshen da ka yi kafin wannan idan na tuna tun baka fi shekara goma ba lokacin an yi muku shayi kai da su Ado, ka warto cinyar kaza a hannunsa ya biyo ka ya murɗe ya karɓe; to gashi yanzu ma an kwatanta." Dubu dariya take har da hawaye dukda ta san wannan dariya da take yi tamkar bashin duka ta ɗauka da hannunta. Salisu ya ƙarasa wurin yana dafa Baba Munkaila ya ce, "Sannu Baffa ko na taimaka maka." Da sauri Baba Munkaila ya fisge hannunsa ya ce, "Sake ni bana so." Da hanzari ya miƙe yana ɗingisa ƙafa ya fita daga ɗakin.
Yaya babba ta jinjina kai ta ce, "Allah ya fissheka alheri Salisu don wallahi Munkaila ya ɗau fushi da kai, yo meye za ka ce za ka taimaka masa gazawa ya yi?" Salisu a ɗan fusace ya ce, "Don Allah Inno ki yi mana shiru, ta ya za a yi na fusata shi bayan ke kika ɓata komai kin zauna kina zancen angwancinsa a gabana; wai har da waƙar salawaitu, ba dole ki sashi ya tashi ya fice ba." Yaya babba ta hamgame baki ta ce, "Don Allah Musbahu me ye laifina a nan don na baku labarin angwancin Munkaila, ba Uba yake a wurinku ba?" Musbahu ya yi murmushi ya ce, "Inno Salisu fa sirinkinsa ne auren Zulfa zai yi kin ga ai hakan da kika faɗa bai kamata ba a gabansa." A sanyaye Yaya babba ta kalli Salisu ta ce, "Salisu kana ganih Munkaila bai yi fushi ba?"
"Ai idan da abin da ya fi fushi ya ɗauka da ke duk ɗaya makafi sun yi dare." Salisu ya yi maganar a ƙule. Yaya babba ta russunar da kai ta ce, "Allah ya sani ban iya gaba ba halin ƴan wuta ne, ni kuwa me zai haɗa ni da wuta a na zaune ƙalau? A'a raba ni da Munkaila ya je ya yi ta gabarsa ko a lahira karma ya nuna ya sanni, bare mu ƙulla alaƙa. Musbahu ku shaida ko a lahira za ku tsaya mini shaidu a gaban Allah."
Da sauri Salisu ya ce, "Ai ko a gidan duniya ba zan tsaya miki shaida ba Inno bare a lahira, kema ki yi ta kanki a wannan ranar da har kike neman wani ya yi miki shaida tsakanin ki da Baffa." Yaya babba ta yi ƙwafa a fusace ta ce, "An ya kana ƙaunata Salisu kuwa?" Salisu ya wara mata hannu ya ce, "Ba tabbas!" A tsorace Yaya babba ta ce, "Alƙur'an bari su Sule su zo sai sun yi mini iyaka da kai, ko a lahira karka nuna ka taɓa sanina." Salisu ya miƙe shi da Musbahu sannan ya ce, "Inno a ina ma zan ganki muna can sahun ƴan aljanna." Yana gama maganar suka fita, ai kuwa Yaya babba ta fashe da kuka tana ƙwalawa Baba Sule kira da sauran ƴaƴanta kira.
Gidan Baba Abubakar.
Hajiya Nafisa ba ta san lokacin da ta lailayo wani ashar ta maka ba, a tsananin fusace ta ce, "Ƴar gidan uban waye da za ka bata ɗana ba tare da shawara ba? Nawa Mahaifinta ya baka da za ka yi abu cikin ƙanƙanin lokaci? Wacece wannan Haliman? Wane muƙami ubanta yake da shi a ƙasarnan?" Ta jero masa tambayoyi wannan na bin wannan kamar tsohuwar ƴar jarida, saboda yanda idonta ya rufe ko sunan Mahaifin Dubu da inkiyarsu ta ƊANGWAURO ba ta yi ba. Murmushin tura haushi ya yi ya ce, "Hala baki lura da bayanan da ke jikin katin ba? Me kike ci na baka na zuba Nafisa? Ai duk gaggawar Unguwar zoma ta bari a haihu. Ki wara ido da kyau ki sake karanta bayanin da ke cikin katin.
Kamar sabuwar makauniya haka ta fara ware idanu tana bi daki-daki, kamar wacce kunama ta ɗanawa harbi lokaci ɗaya ta zabura jikinta har rawa yake. Idonta ya sake ƙanƙancewa, fuskarta murtuk saboda ɓacin rai. Ja da baya ta fara yi tana nuna shi bakinta na rawa ta ce, "Wai kana nufin Dubu za a ɗaura masa? Wallahi ba zai yuwu ba. Na rantse da Allah idan nina haifi Aseem ba zai auri wannan jakar yarinyar mahaukaciya ba." Murmushin takaici ya yi a karo na biyu fuskarsa ba walwala saboda ɗacin maganganunta, tabbas shi kansa ya san Dubu na da wasu ɗabi'u, da dole tana buƙatar gyara amma kalaman sun yi zafi akanta, duba da irin riƙon da Yaya babba ta yi mata. Kuma duk lalacewarta ƴan ɗan'uwansa ce, ta ya za bari a ci zarafinta a gabansa? Tana shirin sake yin magana ya katse ta da cewa, "Hawainiyarki ta kiyayi ramata Nafisa, karki ƙara furta kalma mara daɗi akan yarinyar nan idan ba haka ba kuma ranki zai yi mummunan ɓaci. Aseem ɗana ne kuma ina da ikon aura masa duk yarinyar da na yi niyya, Alhamdullah biyyyyar da nake wa Mahaifiyata ba ta tashi a banza ba, domin Aseem bai watsa mini ƙasa a ido ba. Tabbas wannan abin ɗaga hannu ne na godewa Ubangiji, saboda ba kowanne matashi mai ji da ƙuruciya za a yi wa wannan auren ba, kuma ya amince." Sakin baki ta yi tana kallonsa, dukda gwiwoyinta sun fara sanyin da jin kalamansa, hakan bata sa ta bada ƙofar da Baba Abuabakar zai ga lagwanta ba, murya a daƙile ta ce, "Shi da kansa Aseem ya amince da wannan maganar? Tabbas biri ya yi kama da mutum! Amma za mu gauraya da shi wallahi sai dai ya zaɓa ko ni ko auren waccen ballagazar." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin fuuuu kamar guguwar da take tsaka da tashi a tsakiyar sahara. Yana ganin fitarta ta ɗau waya ya kira Aseem tare da sanar masa da ya zauna cikin shiri, don a kowanne lokaci mahaifiyarsa za ta iya kiransa a waya akan wannan maganar.
Lokacin da Aseem ya katse kiran da ya yi wa Dubu, dogon tsaki ya yi yana furzar da iska mai zafi. Nasir da ke gefe ya zura masa ido bayan wani lokaci ya ce, "Aseem!" Bai ɗago ya kalle shi ba sai ma girgiza ƙafarsa da yake yi, don ayyanawa yake yau da yana kusa da Dubu mai hana shi shaƙeta a gidan sai Allah. Nasir bai damu ba ya ci gaba da cewa, "Tun bayan dawowarka na lura kana cikin damuwa, na yi tsammanin ni da kai mun zama ɗaya ashe ba haka ba ne. Ko makaho ya shafa ka ya san kana cikin damuwa, wai mene ne yake damunka?" Aseem ya ɗago da jajayan idanunsa ya ce, "Nasir ba ni kara ɗaya na busa."
Da sauri Nasir ya yi baya haɗe da zaro ido waje, kamar wanda ya yi arangama da kumurcin maciji. Ya fara gyaɗa kai kamar kosasshen ƙadanfare sannan ya ce, "Lallai gumi ta yi gumi arniya da ambaton Allah. Aseem kai da kake hanani busawa yau kai ne kake neman kara ɗaya? Abokina bana fatan ka fara wannan harkar muma da muke busa sigarin Allah ya ye mana, meye labari."
"Aure za a yi mini."
Aseem ya faɗa murya na rawa kamar zai yi kuka. Nasir ya riƙe baki tare da bushewa da dariya ya ce, "Shegen kaya ka ce kakarka ta yanke saƙa, ɗan iska sanyin bana sai dai ka ji a bakinmu."
Aseem ya sake tamke fuska ya ce, "Nasir don Allah fita ka bani wuri." Nasir ya yi murmushi ya ce, "Tuba na ke abokina ya ake ciki?" Nan take Aseem ya zayyana masa duk abin da yake faruwa, kasancewar Nasir abokin Aseem ne tun kafin su shiga aikin Soja, kusan kowa ya san cikin ɗan'uwansa game da harkokin yau da kullin. Lokaci ɗaya Nasir ya buga tsalle ya ce, "Shi ne kake wani marairaicewa kamar mace, kai fa ba wayis ba ne. Wallahi irin ƴan shilolin nan sun fi saurin ɗaukan darasi sai ma ka yi..." Aseem ya katse shi da cewar, "Kai dama duk in da iskanci ya zo ya sameka shi kenan zai shafawa ransa salama." Suna tsaka da magana Daddy ya kira shi ya sanar da shi maganar Mommy, ba a ɗauki lokaci ba Mommy ta kira shi, tashi ya yi tsam daga ɗakin zai fita, ai kuwa Nasir ya bushe da dariya ya yi ƙasa da murya ya ce, "Ka ga Ango ya kusa shan mai, a miƙa min gaisuwa idan an gama yayyafawa fure ruwa mai sanyi." Aseem bai bi ta kansa ba ya fice daga ɗakin.
Kamar kazar da aka tsamo daga kogi haka Aseem ya dawo cikin ɗakin a sanyaye, kan katifa ya haye ya kwanta yana jin maganganun mahaifiyarsa na sake dawowa masa sababbi fil a cikin kunnuwansa. Ganin haka ya sa abokinsa Nasir ya fita ya bar shi domin ya fahimci abokin nasa na cikin wani yanayi.
Bahaushe ya ce, "Sanin hali ya fi sanin kama." Tun bayan da kace-nace ya faru tsakanin Baba Abubakar da Hajiya Nafisa, washegari ya kwashi su Nabila a mota ko su bai sanar da su inda zai kaisu ba, sai da suka je ƙofar gidan Baba Adamu sannan ya kalle su fuska a tamke ya ce, "Ku shiga gidan Baffanku za su wuce da ku Ɗangwauro, duk wacce ta saɓa umarnina zan gauraya da ita." Duk abin da yake faruwa Mommy ta sanar da su, don haka sun san duk halin da ake ciki. Sun san waye mahaifinsu domin mutum ne mai matuƙar haƙuri, amma idan ransa ya ɓaci kallon fuskarsa kaɗai zai sa ka shiga taitayinka. Ko kaɗan ba sa son komawa Ɗangwauro, amma babu fuskar da za su yi wa mahaifinsu musun maganar. Sai da ya ga shigar su da jimawa sannan ya tada mota ya bar ƙofar gidan, saboda tuni sun gama magana da ɗan'uwansa akan zuwan na su Nabila. Baba Abubakar da biyu ya yi wa Hajiya Nafisa haka, saboda ya san yanda take da matsanancin son yara ba za ta taɓa jurar ya rabata da su ba. Shi kansa yana son matarsa saboda wani hargitsi bai cika haɗa shi da ita ba, hasalima tun da suka yi aure ba su taɓa wani gagarumin tashin hankali kamar wannan ba. Ya santa sarai idan ya ce zai biyota ta lallami ba za ta taɓa komawa ba, amma idan ya biyo mata ta wannan sigar za ta fi ɗaukan abin da muhimmanci kuma za ta aminci cikin ruwan sanyi.
Tun a ranar ta kira Aminiyarta Hajiya Ikilima ta sanar da ita duk abin da yake faruwa, sam abin bai ɗaga mata hankali ba sai ma mamaki da tayi lokacin da ta ji Aseem ya amince da maganar auren. Abin da ya sa bata damu don bata da ƴa mace, saboda a koyaushe ta kalli Aseem rayawa take da tana da ƴa mace, da ko sama za ta faɗo sai ta yi duk yanda za ta yi Aseem ya aure ta. Rufaida ƴar yayarta ta so haɗata da shi, amma da ta ga Rufaida ta samu wanda ya fi Aseem kuɗi shi kenan ta watsar da maganar Aseem.
[7/2, 3:24 PM] Ameera Adam🌚: *DUBU JIKAR MAI CARBI*
0 comments:
Post a Comment