"Mommy tun ɗazu nake yi miki filis kwal mi (Please call me) amma na ji ki shiru, ni kuma wayata babu kuɗi." Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Wallahi ban lura ba ina kuka shiga ne." Nan take Nabila ta sanar mata da abin da ya faru, Mommy ban da surfa bala'i babu abin da take yi. Suna gama wayar ta nufi sashen Baba Abubakar fuuuu tana tafe tana surfa faɗa kamar za ta ari baki. Ko sallama bata yi ba ta doka ƙofar ɗakin tana faɗin, "Daddyn yara wai yaushe ka zama haka ban sani ba? Waye ya haifamin su Nabila da za ka kwashe mini su ka kaisu gidan su Fauziyya, na lura zaman lafiya ne baka so amma wallahi a wannan karon zan nuna maka ɓacin raina." Sai da ta kammala ya juya ya kalle ta ya ce: "Na ji kin ce ba za ki koma Ɗangwauro ba shi ya sa na kwashe yarana na kaisu gidan ɗan'uwana, domin da kai da kaya duk mallakar wuya ne." Taku biyu ya yi ya buɗe durowar kayansa ya zaro wata doguwar takarda ya ɗora mata akan gado yana faɗin, "Don haka na yanke wannan hukunci ina ganin zai fi zama masalaha, ki tattare kayanki wuri ɗaya saboda gobe zan turo a ƙarasa kwashe kayan gidan nan." Yana gama maganar ya fara ɗaura agogon hannunsa, ya ci gaba da harkar gabansa kamar ma bai san da mutum a wurin ba.
Tuni jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi idanunta suka ciko da ƙwalla ta kasa ɗaga ido ta kalle shi ta ce, "Daddyn yara sakina ka yi saboda abin da bai taka kara ya karya ba?" Turare ya fesa a jiki sannan ya ɗauki wayoyinsa zai fita ta sha gabansa ta ci gaba da cewa, "Wallahi indai akan maganar auren Aseem ne bana ɗar ko dana-sanin hukuncin da ka yanke, tabbas na yadda Namiji ƙudan zuma ne (Littafin Maman Islam ne, ku neme shi don jin yanda labarinta yake mai tafe da ɗaukan darasi.) Na yarda duk yadda mace ta kai da shekaru a gidan aure, dole akwai shafin da namiji zai iya buɗe mata ba tare da inkiya ba. Na gode sosai da wannan son zuciya da kuka nuna min." Hawaye ne ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarasa maganar bakinta.
Murmushi ya yi da jin kalamanta saboda ya san dama muddin ta yi tozali da takardar da ya ajiye mata abin da za ta kawo kenan, shi kuwa gani yake wane laifi za ta aikata masa wanda zai saka mata da hukuncin saki? Matar da ta aure shi tun yana malamin makarantar firamare har Allah ya ɗaga dajarasa ya zama babban malami a makaran jami'a. Yana tsaka da tunani ya ji ta ci gaba da cewa:
"Kai namiji ne ba lallai ka fahimci ɗacin abin da nake ji na mahaifiya ba, ace ina matsayin mahaifiyar Aseem a yi masa mata ba tare da sanina ba har sai bikin ya rage ƴan kwanaki. An ce za mu koma ƙauye rayuwar ƴaƴana za ta nakasta, duk wannan bai isa ba har sai da ka raba ni da ƴaƴana me ya sa ahalinku suka fiye san kansu ne?" Maganganunta sun taɓa shi sosai kuma tabbas kowacce mahaifiya ba za ta so abin da aka yi mata ba, amma hakan shi ne mafita tun da shima yana yi ne domin biyayya ga mahaifiyarsa. Tana shirin sake magana ya ɗaga mata hannu tare da cewa, "Maganar auren Aseem fatan alheri za ki yi masa, domin bakinki kamar yankan wuƙa yake idan kika aibanta auren ba Dubu kawai kika yi wa ba, bakinki zai iya faɗawa har kan zuri'ar da za su haifa." Yana gama maganar ya fice daga ɗakin. Sai da ta zauna ta ci kuka ta godewa Allah sannan ta ɗauki takarda ta wuce ɗakinta, ta fara haɗa kaya sannan ta wuce unguwar Ɗorayi gidan mahaifiyarta.
Duk abin da ka ga bai zo ba sai dai idan ba a ƙayyade masa lokaci ba, ranar juma'a iyalan Yaya babba suka tarkato gabaɗaya suka koma sabon muhallinsu da ke cikin gidan Marigayi mai carbi. Hajiya Fauziyya ban da cika da batse babu abin da take yi, duk yanda ta kai ga biye-biyen malamanta akan komensu gidan abin ya faskara, sai dai ta ci alwashin sai ta gasawa Yaya babba aya a hannu cikin kisan mummuƙe ta yanda babu wanda zai gano ta. Hajiya Rahama dama macece mai sauƙin kai, tuni suka shirya da mijinta ta fauwalawa Allah lamuranta tare da neman alkairin komawar tasu. Sauran surukan cikin gidan murna a wurin abin baya musaltuwa saɓanin ƴaƴan Baba Abubakar da Baba Adamu da suke jin su kamar waɗanda suka koma rayuwar ƙunci. Yaya babba bakinta har kunne har wani annushuwa take ji da farinciki ganin kan zuri'ar Mai carbi ta haɗu wuri ɗaya.
Wannan kenan!
Aseem ya shiga cikin matsananciyar damuwa, har wata ƴar rama ya yi sai dogon wuya, fuskarsa ta yi fayau. Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci rashin kwanciyar hankali ya samu matsuguni a jikinsa. Ko sati ba a rufa ba aka yi masa canjin aiki shi da Nasir, Nasir aka kai shi Kaduna shi kuma Aseem a ka kai shi garin Kano. Abin da ya daɗe yana so ne ya samu amma kuma wannan canjin aiki ya zo masa lokacin da baya buƙatar zamansa a kusa da gida. Amma babu yanda ya iya haka suka haɗa kayansa kowa ya koma wurin da aka yi posting ɗinsa.
Hajiya Nafisa tun da ta koma gida ta sanarwa da Mahaifiyarta abin da yake faruwa, da farko mahaifiyarta ta ji zafin Baba Abubakar amma daga baya ta riƙa nunawa ƴarta kuskurenta amma da yake idonta ya rufe, sai dai ta bi da Mahaifiyarta ta yanda take yi mata faɗa. Ƙanin mahaifiyarta Malam Mudam ne ya je gidan ake sanar masa da abin da ya faru, shi kansa ya ji haushin abin da ya faru don haka ya dubi Hajiya Nafisa ya ce, "Ke Nafisa saki nawa ya yi miki? Idan da kome zan nemi Abubakar ɗin mu yi magana. Ita rayuwa ai ƴar haƙuri ce, tun da ƙuruciya ba a yi wannan shashancin ba sai yanzu da girma ya zo." Hajiya Nafisa ta ɓata fuska ta ce, "Kawu ka barshi kawai ai sai ya ga kamar gajiya na yi da zaman nan ɗin." Daƙuwa ya yi mata da hannu ya ce, "Wannan sakarcin banza ne ai, duk abinki ke da Abubakar kun zama ɗaya." Hajiya Nafisa ta ce, "Ai ni tun da na sa takardar da ya bani a jaka ban ƙara bi ta kanta ba, tun da haka ya ga ya fi ai shi kenan." Ba don ta so ba haka ƙanin mahaifiyar tata ya tilas mata ɗauko takardar, tana buɗewa kunyar duniya ta isheta. Babbar takarda ce sai kuma ƙanana guda biyu da basu kai ta farkon girma ba, sai kuma cheque ɗin kuɗi a tsakiya. Takardar farko rubutu ya yi mata kamar haka:
"A kodayaushe ina gaya miki girma ya riga da ya kama mu, tsayawa kace-nace bai da amfani. A lokuta da dama abin da muke ƙi shi ne mafi alheri a gare mu, don haka Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Kada a tsananta soyayya kuma kada a tsananta ƙiyayya." Bakin uwa na da matuƙar tasiri akan ƴaƴanta don haka ki yi wa Aseem fatan alheri, shi ne abin da ya fi alheri. Ni Abubakar ina ƙaunarki fiye da tunanin mai tunani, don haka idan na sake jin kalmar rabuwa a bakinki sai na hukuntaki da hukunci mai tsanani." Takarda ta biyu kuma gabaɗaya kalaman soyayya ne dattijon mijin nata ya cika mata da su, sai cheque ɗin kuɗi masu yawa da ya bata ya ce ta riƙe saboda sha'anin biki.
Lokacin da ta karanta wata irin soyayyar mijinta ta ji na ratsata, nan take ta sanarwa da Kawunta abin da yake faruwa. A take a wurin ya ɗaga waya ya kira Baba Abubakar ya sanar masa da abin da Hajiya Nafisa ta yi tare da sheda masa ya zo ya ɗauki matarsa a ranar nan take.
Bayan tariyarsu da kwana biyu Yaya Babba ta nemi ganin iyalan gidan gabaɗaya a sashenta ita da Inna Furai, kusan gabaɗaya iyalan gidan sun hallara, sai ƴan tsirarun da suke aiki a nesa da gida irinsu Aseem, da waɗanda suke fita fatauci garuruwa. A ƙalla iyalan da suke zaune a tsakar gudan sun haurewa mutum tamanin, kowanne yana zaune da matansa da ƴaƴansa sai Yaya babba da Inna furai da suke zaune akan wani dogon benci. Sanye suke da tamfarsu iri ɗaya tare da hijabinsu ruwan toka iri ɗaya kamar yanda suka suba tun farkon rayuwarsu a gidan marigayi.
Bayan buɗe taro da addu'a Inna furai ta fara da cewa, "Da farko za mu ce Allah ya jiƙan malam ya haskaka kabarinsa." Yaya babba ta saci kallonta a ɗan ƙufule don bata so ta yi mata katsalandam ba, gabaɗaya mutanen wurin suka amsa da, "Amin ya rabbi." Inna Furai da bata lura da irin kallon da Yaya babba take yi mata ba ta ci gaba da cewa, "Mun tara ku ne domin mu ƙara jan kunnenku domin gabaɗayanku babu yara a ciki, don haka babu wanda zai kawo mana zazzagar rashin ɗa'a a wurin nan."
Dubu da ke gefe ta yi karaf ta ce, "Inna yanzu Ma'azu da ake yi wa shayi shi ma ba yaro bane? Kin ga su Iro fa." Ta ƙarasa maganar tana nuna Iro da yake kan cinyar mahaifiyarsa yana shan mama. Ai kuwa kamar mai jira Hajiya Nafisa ta ce, "To zaƙin zaƙafere... Ke kaɗai ce mai bakin magana manya na magana za ki sa baki saboda rashin ɗa'a." Baba Abubakar ya ɗago ya kalli Hajiya Nafisa amma sai ta kalli wani wurin daban don ta san haka za ta iya faruwa. Dubu ta watsawa Hajiya Nafisa harara tana mata fari haɗe da murguɗa baki, Hajiya Nafisa ta cije baki cike da takaici. Dama a ƙule take saboda kiran da Yaya babba ta yi mata ba don san ranta ta je shi ba saboda ko kaɗan ba ta san haɗa inuwa da sauran facalolinta don gani take ba ƙaramin zubewar mutumci ba ne a wurinta. Matan Baba Abubakar ma don ta san babu abin da nata mijin ya fi na su shi ya sa bata cika kawo musu wargi ba.
Baba Abubakar ne ya yi magana hayaniyar da ke tashi ƙasa-ƙasa a wurin ta lafa, amma kallon yanda Hajiya Nafisa take duban Dubu za ka tabbatar da babu ɗigon ƙaunar sirukar tata a zuciyarta.
Inna Furai cike da ƙwarin gwiwa ta ci gaba da cewa, "Fatan mu dai ku zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Allah ya sani bama son tashin hankali da gutsiri-tsoma, gabaɗaya tushe ɗaya kuke sai a ɗorar da zazzagar zaman lafiya. Amma duk wacce ta kawo mana wargi alƙur'an mai hana mu zazzage albarkar da ke kanta sai Allah ko ba haka ba Yaya." Yaya babba murya can cikin ƙasan maƙoshi ta ce, "Wacce falsafa za ki tambaye ni Furaira? Meye nawa a ciki kuma bayan tun farko baki bani girma da darajata ba. Ƙwarakwatsa dubu ba don kar na baki kunya a gaban su Auwalu da Ado ba, babu abin da zai hana watsa miki falsafar rashin ɗa'a." Yaya babba muryarta ta fara rawa alamar za ta yi kuka, ta dubi Inna Furai ta ci gaba da cewa, "Alƙur'an ban taɓa sanin za ki yi ɗiban karen mahaukaciya da wasiyyar Malam ba. kaico! Rayuwar duniya." Inna Furai ta fara zuwa wuya don haka a ɗan hassale ta ce:
"Yanzu me ye ma ba ki yi mini ba, wacce irin albarka ce baki zazzage mini a tsakar ka ba." Sai kuma ta juya musu baya tana faɗin, "Allah ya sani Yaya kin zazzage mini kwandon ɗiban albarka." Yaya babba ta taɓe baki ta ce, "Ai kinsan dai ni ce babba a gidan, tun zuwanki gidan nan ni nake fara komai, amma ƙasa ta rufe idon Malam har kina neman kwara mini falsafar rashin mutumci." Inna Furai ta kusa kaiwa bango, a fusace ta miƙe za ta bar wurin tuni su Baba Munkaila suka fara sa baki ta zauna.
Inna Furai ta harari gefen Yaya babba ta ce, "Dama duk daɗinka da kishiya sai ta yi maka zazzagar rashin mutumci. To ni dai nan gani nan bari, kujera ce dola a zauna a kaina."
Wannan maganar ba ƙaramin ɓata ran Yaya babba ya yi, ai kuwa nan take ta fashe da kuka. Wurin shiru ya ɗauka ban da sautin kukan Yaya babba babu abin da yake tashi, Inna fura ta ɗauke kai gefe alamun ita ko a jikinta. Sai da Yaya babba ta yi mai isarta sannan ta fara leƙe-leƙe, daga can gefe ta hango Salisu, da ɗan yatsa ta nuna shi tana faɗin, "Salisu zo nan don girman Allah." Salisu na jin haka ya fara noƙewa don fatansa bai wuce, Yaya babba karta kunyata shi a gaban iyaye da sirikansa ba. Jin ya yi shiru ya sa Baba Sule ya yi masa magana jiki ba ƙwari ya fita ya je gefen Yaya babba ya russuna ya ce,
"Gani Inno."
Yaya babba ta ruƙo hannuna Salisu tana goge hawaye idonta, ta ce, "Allah shaida kaine shaidata Salisu, daga yau babu ni babu Furaira ko a lahira idan ta nuna ta sanni ban yafe ba." Tana rufe baki mutane wurin kamar haɗin baki suka ɗauki salati lokaci ɗaya. Yaya babba ta hango Sha'aban Jikan Inna Furai na huɗu shi ma ta ƙwala masa kira, yana zuwa ta riƙe hannunsa ta ci gaba da cewa, "Sha'aban na fasa wakilta Salisu saboda sam bai da ɗa'a bashi da kunya, Kaine shaida ko a gaban Ubangiji ka za ka shede ni." Salisu zuciyarsa fes har zai bar wurin Yaya babba ta fisgo ƙugunsa ta tana faɗin, "Dawo munafuki babu in da za ka dama da biyu na shirya zaman nan, saboda kai da yarinyar nan Zulfa. Amma dai Allah ya yi wa Soja albarka, yaron nan shi kaɗai yake da kawaici." Yaya babba ta mayar da kallonta wurin mutanen da ke zaune kowa ya zuba idanu suna jiran abin da za ta faɗa.
"Munkaila!" Ta ambaci sunan Baba Munkaila a hankali ya amsa don yana gudun kar a kwatanta ta kwanaki. Yaya babba ta ci gaba da cewa, "Kwarankwatsa dubu ka shawarta da ƴan uwa wallahi auren nan janyo shi za a yi; ku rufa mini asiri ku aurar da yaran nan na daina jin miyagun maganganun da kunnena suke ji, wai ma saura kwana nawa?" Baba Munkaila ya haɗiyi yawo cike da fargaba don har zuwa lokacin bai gama haɗa kuɗin kayan gadon Zulfa ba, shi kuma baya jin zai iya taɓa kiwonsa ko kaza ce ya sayar. A hankali ya ce, "Yau saura kwana goma sha takwas."
"To a rage kwanakin nan gaskiya, don na gaji da jin falsafar rashin ɗa'a a kunnena. Ina dalili ina zaune ƙalau a janyo mana fushin mala'iku har cikin gida. A'a don Allah ka rabani da faɗawa halaka, me ye haɗina da Jahannama ana zaune ƙalau? A'a wallahi ina daga sahun farkon masoyiya Manzon Allah (S.A.W)" Kowa dai ya yi shiru cikin zuƙutansu da irin wasiƙar da suke karantawa.
Yaya Babba bata damu ba ta ci gaba da cewa, "Ku gane mini shi don Allah wa zai ce Salisu halin yahudu gare shi? Maganganun da ya faɗa rannan a ɗakina alƙur'an da ƙyar bacci ya ɗauke ni." Baƙin cikin duniya ya cika Salisu, ban da harare-harare babu abin da yake yi.
"Wai har da I musu yu, don Allah ku ji kalmar arnanci kamar me kiran muzuru, ni Soja nake yi wa kallon ɓatacce mai halin Yahudawa ashe ina tare da shi a kusa ban sani ba" Hajiya Nafisa ta cika fam wannan kalmar na ƙona ranta idan ta ji Yaya babba na danganta jininta da yahudawa.
Cike da takaici Inna Furai ta juyo ta ce, "Yaya raba kanki da aibanta mini jika idan ba haka ba alƙur'an babu mai hanani zazzage miki albarka a ka." Yaya baba ta sakar mata harar mai ɗauke da manufar, ai ba ke kika haifar mini mahaifinsa ba. Sannan ta ɗora da cewa, "Furai wa ya haifar mini Uban Salisu a gidan nan?"
Inna Furai ta taɓe baki ta ce, "Yoo don kin haifi ubansa ni da Malam ya yi mini kyautar ubansa tun yana tsammafa." Yaya babba ta saki dariyar ta ce, "Yoo wa yake bin wasiyyar matacce, Malam dai ya mutu Allah ya jiƙansa amma ba wanda ya isa ya yi mini iko da jinina."
Inna Furai ta ɓata fuska har da huccinta, ta kalli Auwalu ta ce, "Auwalu Allah idan baka rakani ofishin human rai (Human right) ba kwarankwatsa mai hanani zazzagewa gidan nan albarka sai Allah. Allah ko ka rakani a bi mini haƙƙina ko ku neme ni ku rasa daga nan nida Indo shari'a har ƙashen duniya." A tsorace Yaya babba ta dafe ƙirji ta ce, "Furai yau ni kike ambata da Indo gatsal? Wallahi magana dai na yi kai Sha'aban ga ƙarin wata shaidar, kwarankwatsa dubu ko a lahira ka shaida abin da Furai ta yu mini, yoo ƙarya na yi masa ba da kunnena na ji watsewar kalaman yahudawa ba wai I musu yu (I miss you), abin da ko a mafarki ban taɓa ji Soja na faɗa ba dukda shi ma ina kokwanto akan tauhidinsa, yo me ake da aikin Soja na aikin kafirai masu busasshiyar zuciya. Allah ya sani Garba ka cuceni da ka sa mini Jika a harkar ɓata don..."
Sallamar Aseem ce ta katse Yaya babba daga jawabin da take yi.
Zuwansa kenan daga garin Lagos, ya shiga cikin gidan ya ga duk babu kowa don haka ya yanke shawara zuwa sashen su Yaya babba. Yaya babbb na ganinsa ta fashe da dariya tana faɗin, "Kun ga Ɗan'halak. Soja zo nan." Da mamaki ya fara bin mutanen wurin, yana mamakin abin da ya kawo su suka tattaru wuri ɗaya. Bai ankara ba ya ji muryar Yaya babba raɗau a kunnensa tana ci gaba da cewa.
"Soja ka dubi Allah da Annabi, ka san dai Sule bashi da wuta da aljanna bare idan ya ji ka faɗi gaskiya a kan Ɗansa Salisu ya babbakeka. Ka gaya mini meye I musu yu? Don wallahi ba zan juri zama cikin fushin Ubangiji ba?"
Shafi na biyun ƙarshe🤸🏻♀️💃🏼 daga shafin gobe an gama free pages ku yi hanzari ku fara biya kar a yi babu ku💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
*DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV
LAST FREE PAGES 13
Guntun tsaki Aseem ya ja ba tare da kowa ya fahimce shi ba, yana daga wurin da yake ya ce, "Inno lafiya kuwa na ga mutanen gidan sun taru?" Ya yi maganar fuska a tamke don ba ya son ta sake jefa masa wata maganar, saboda gabaɗaya ransa a dagule yake. Bai rufe baki ba idanun mutanen wurin suka sauka a kansa, yadda ka san sun ga sabuwar hallita haka suka zura masa idanu. Dubu kuwa sai kallonsa take tana yashe baki, musamman da ta tuna irin huɗubar da Yaya babba ta yi mata akan kissa da kisisina, wai murmushi ma yana daga cikin abin da yake sace zuciyar namiji. Don haka Dubu ta zage ta riƙa yashe haƙora tana kallon saitin wurin da Aseem yake, har sake miƙa wuya gaba take don ya fi hangota a kan sauran mutanen wurin.
Yaya Babba na jin kalaman Aseem ta ɗan ɓata fuska ta ce, "Tsiya ta da kai kenan Soja. Don Allah ka ƙaraso ka taya ni jin wannan lamarin ko so kake na ji ni kaɗai?" A hankali ya fara takawa yana saƙale da jakar goyonsa wacce kayan aikinsa suke ciki, sai kuma trollybag wacce ke ɗauke da sauran kayansa suke ciki. Ƙirjin Hafsa ban da lugude babu abin da yake yi, tana jin zuciyarta na wani iri kamar za ta faso ƙirjinta. Soyayyar Aseem na ci gaba da mamaye zuciyarta, a fakaice ta sunkuyar da kai ƙasa ta sharce hawaye ba tare da ta bari wani ya lura ba.
Aseem na ƙarasawa shi ma Yaya babba riƙo hannunsa tana faɗin, "Soja wai saura kwana nawa aurenku don Allah?" Nan take fuskar Aseem ta sake haɗewa ya ɗauke kai gefe ya ce, "Na manta." Ta yashe baki tana kallon mutanen wurin ta ce, "Kun ji abin da nake faɗa, alƙur'an Soja da ba kallon da bana yi maka don Allah ka gafarceni. Allah ya sani ko Garba ba zai nuna maka kunya ba, don shi ma da kake ganinsa a lokacin samartaka ƴanmatan da ya yi Allah ne kaɗai masani. Allah mai sarauta irin soyayya da Garba ya yi da Kandala da gidan nan na magana da ya shede ni, bana buƙatar shedar Furaira don ko a lahira na yanke zumunci da ita."
Aseem bakinsa sai motsi yake yana san ya yi magana amma yana gudun ta fito mara daɗi, yana shirin cire hannunsa daga jikin nata ya ji Inna Furai ta ce,
"Me ye naki na ambatar sunana kuma? Wallahi ko a aljannah sai na zazzage miki albarka a tsakar ka." Yaya babba bata bi ta kan Inna Furai ba ta ci gaba da cewa, "Amma dai har Garba ya auri uwarka wallahi ban taɓa jin kalmar Allah wadai a bakinsa ba, gaskiya ba da ni ba wannan falsafar dole a dakatar da ita, maganar gaskiya Shehu auren nan ranar juma'a mai zuwa za a ɗaura shi. A kai yaran nan ko ma huta; ina dalili laifinsu ya shafe mu, mu riƙa sallah ba a karɓa Mala'iku su yi fushi da mu." Ta ƙarasa maganar tana kallon wurin Baba Shehu.
Baba Shehu ya kwantar da murya ya fara cewa, "Inno da za a taimaka a bari lokacin nan ya zo, mun riga da mun buga katin gayyata duk mun aikawa mutane idan wani abin yaran nan suka yi bayan taro ya watse sai mu zauna a tattauna." Yaya Babba ta ƙura masa ido har ya gama sannan ta ce, "Dole ka nuna mini iyakata Shehu, ba sai ka faɗa ba dama ai ba ni na haifa muku su ba." Yaya babba ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.
Wurin shiru ya ɗauka aka rasa mai bakin magana, Baba Aminu ya ɗago ya dubi mutanen wurin ya sallame su. Ɗaya bayan ɗaya haka suka fara wucewa suna barin wurin, dama Aseem da Salisu kamar a kan ƙaya suke tun Baba Aminu bai rufe baki ba suka wuce gaba.
Shiru wurin ya yi daga Yaya babba sai Inna Furai da sauran iyaye maza kowa yanayinsa ba daɗi. Baba Abubakar ya ƙarasa wurin Yaya babba ya ciro hankicif ɗinsa ya miƙa mata ya ce,
"Inno share hawayenki."
Yaya babba bata ɗago ta kalle shi ba ta ce, "Ka barni ya yi ta zuba idan ya ƙare na mutu kun huta ai." Murmushi suka yi don ta so basu dariya, ya juya wurin Inna Furai ya ce, "Inna don Allah ki sa baki ta tsaya mu yi magana." Inna Furai ta ɗauke gefe tana wurga masa harara ta ce,
"Wacce zazzagar kuke so na yi? Maganar gaskiya abin da Yaya ta faɗa yana hanya, wai me ye a ciki lamarin nan fa na gida ne kuma auren nan ko yau aka ɗaura shi akwai wanda zai ce don me?" Baba Abubakar ya yi shiru don ya lura gabaɗaya a rikice suke, Inna Furai ta ci gaba da cewa, "Ba zan hana Yaya ba saboda Allah ina dalili ana nuna muku Annabi kuna runtse ido." Yaya babba na jin haka ta sake rushewa da kuka. Sai da ta yi mai isarta ta miƙe za ta bar wurin, da sauri suka dakatar da ita sai da ƙyar suka shawo kan Yaya babba ta zauna. Amma duk yadda suka so a bar biki a lokacin da yake fir ita da Inna Furai suka ƙi amincewa. Babu yadda suka iya haka suka amince akan ɗaurin auren ranar juma'a mai zuwa wanda a lokacin gabaɗaya saura kwanan huɗu.
Tun a ranar su Baba Abubakar suka riƙa kiran mutane suna sanar da su janyo lokacin bikin, haka a cikin garin Ɗangwauro kafin wani lokaci tuni labarin ya karɗe ko'ina. Baƙin ciki a wurin Hajiya Nafisa har ya ƙi musaltuwa don ranar kwana suka yi suna yin babu daɗi ita da Maigidanta. Haka daga wurin Aseem ranar kusan kwana ya yi cikin takaici, amma Dubu ko a jikinta baccinta ta yi hankali kwance. Hafsa ma kusan kwana ta yi tana kuka don gani take lokaci ne ya yi da za ta rasa masoyinta ba tare da cikon muradinta ba.
Gari na wayewa Aseem ya fice daga gidan yana fita ya kira wayar Nasir ya sanar da shi, nan dai Nasir ya jajanta masa daga baya kuma ya tambaye shi ko akwai wani party da za su yi. Aseem na jin haka ya katse wayar, Nasir ya yi ta kiransa amma fir ya ƙi ɗauka.
Shirye-shirye gabaɗaya sun gama nisa a cikin gidan, daga ɓangaren Mazan har matan. Da yake duk lamarin na cikin gida ne rana ɗaya aka kai lefen su Dubu wanda a lokacin bikin saura kwana biyu. Inna Furai da Yaya babba bilhaƙƙi suka dage da gyaran amare su ne jiƙa wannan, dafa wannan duk a basu. Sai kuma gyaran jiki da Hadiza take zuwa tana yi musu, Dubu ta yi kyau sosai hasken fatarta ya sake fitowa. Sai dai gashi shi ne ya yi mata cikas. Donma tana da kufan gashi kan ya yi dubu sumar ta fara fitowa, sai dai daga baya idan ka hangota sai ka rantse da Allah namiji ne. Duk wani abin buƙata da mace take yi na Party da wasu harkokin Baba Abubakar ne ya bawa Dubu, wannan dalilin ne ya sa ko kaɗan Dubu bata wani damu da rashin ganin Aseem ba. Ita kuwa Yaya babba da yake mutane sun fara cika gidan sabga ta sha kanta ya sa bata bi ta kansu ba.
Mutane sai mamaki suke da akan auren Dubu kasancewar duk sai daga baya aka ji zancen haɗin nata auren da Aseem, nan dai aka ci gaba da shagali. Aseem kuwa daga Nasir babu wanda ya sanarwa a cikin abokansu, don gani yake ci baya ne ace an yi masa aure da yarinya kamar Dubu.
RANA BA TA ƘARYA...
Kimanin ƙarfe biyu na ranar Juma'a aka ɗaura auren jikokin marigayi Mai carbi, ciki kuwa har Dubu da Aseem a babban masallacin gidan Sarki da ke cikin garin jihar Kanon Dabo. Mutane masu tarin yarawa ne suka shaida wannan ɗaurin auren, fuskar su Salisu abin ba a magana saboda farinciki. Shi kuwa Aseem ban da cin ɗaci babu abin da yake yi, daga Nasir sai abokansu da basu kai goma ba. Suma duk Nasir ne ya sanar musu lokacin da Aseem ya ji labari kiran Nasir ya yi, yai masa fata-fata har sai da suka yi faɗa a wurin. Daga wurin ɗaurin aure suka ɗungumo zuwa gida.
Daga can gida mata ne suke ta shagali, an kira masu kiɗan ƙwarya sai cashewa ake. Idan ka ga yadda Dubu take cashewa sai ka ɗauka ita ma ƴar taron biki ce ba amarya ba, su Yaya babba da Inna Furai an sha atamfa mai kyau sun yi anko sai fama ake da jama'a. Bayan angwaye sun dawo gida nan fa aka shiga hotuna angwayen da iyayensu fuskarsu fal farinciki. Abin da ya hana Aseem tafiya sashensu don kar ya kunyata Mahaifinsa, saboda ya san matuƙar ba a gan shi ba an riƙa tambayarsa kenan, don haka ya daure aka yi ta ɗaukan hotuna sai daga baya ya zame jikinsa ya wuce can sashensa shi da su Nasir.
Da daddare.
Gabaɗaya angwaye da amaren aka haɗa a babban falon Yaya Babba, haɗe da iyayensu maza da mata, Sai Yaya babba da Inna Furai. Tun da magriba da doso Yaya babba take sharar ƙwalla, lokacin da aka tattaru a ɗakin duka amaren kansu na cikin mayafi a lulluɓe da alama kuka suke wanda bai kai har zuci ba. Wasu daga cikinsu ma babu ko ɗugon hawaye, Angwayen kuwa sai sunne kai ƙasa suke yi saboda wani irin nauyin Iyayen nasu da suke ji. Dubu da ke cikin mayafi a lulluɓe ban da satar kallon mutanen ɗakin babbu abin take yi, da ta gaji da kallonsu ta cikin mayafi sai ta riƙa ɗaga mayafin tana fakar idonsu tana leƙe, da sun haɗa ido da ɗaya daga cikin kawunnan nata sai ta maza ta sauke mayafinta.
Baba Mumkaila ne ya yi gyara murya haɗe da addu'a sannan ya ɗora da nasiha, daga ƙarshe ya buƙaci su Yaya babba da su yi wa amare d angwaye nasihar zaman aure.
Yaya babba har lokacin ban da kuka babu abin da take yi, ganin haka ya sa Baba Abubakar ya ce Inna Furai ta wakilci Yaya babba. Inna Furai ta rangwaɗa kai gefe sannan ta ce, "Garba ban ƙi ta taka ba amma ka san dai bin na gaba bin Allah? Tun da kuka taso a cikin gidan nan kun taɓa ganin na shige gaba a abu ba tare da Yaya ta fara yi ba." Yaya babba ta sharce hawaye ta ce, "Bar shi Furaira so yake ki kaucewa tarbiyyar Malam. To gaskiya ba haka mu ke ba, kar dai ka yi wani mugun halin a gaban yaran nan su ɗauka suma su idar a gidajen aurensu. Shi ya sa mu ke aikata alheri ni da ƴar uwata, don mu samu rabo da gidan Aljannah." Yaya babba ta ƙarasa maganar tana kallon Inna Furai. Baba Sule ya gyaɗa kai sannan ya ce, "To Inno bismillah!" Yaya babba ta gyara zama tana cewa:
"Ku ba ni hankulanku wuri ɗaya domin zaman aure ba wasa ba, ku dubi iyayenku kamar yau aka kawo mana su ɗakin nan ga shi yau sun aurar da ku. Zan fara da ku matan alƙur'an ku ji tsoron Allah ku yi wa mazajenku biyayya, idan ba haka ba har abada babu ni babu ku. Ga Furaira ita ce sheda ko a lahira kar wanda ya nuna ya sanni, tun da duk wacce bata bi aure ba kwarankwatsa dubu makomarta wuta. A'a ku raba ni da zan cen jahannama a na zaune ƙalau, meye haɗina da ita bayan ina sahun masoya Annabi (S.A.W). Ku yi biyayyar aure ku samu Aljannah mu haɗu da ku a zangon barka-barka a cikin Aljannah. Idan na hango Zulfa na ɗaga mata hannu sai na hango Dubu musha alkausara, mu ci abin da muke so mu sha abin da muke so. Yoo zaman duniyar nawa yake a kan idonku dai Munkaila yake gadinmu ni da Furaira, don masifa naman ma suna hanamu ci ina dalili. A'a rabani da wannan mugun halin ku yi biyayyar aure mu ci nama mu ci ƴan shiloli tare ba wanda zai mana iyaka, idan kun ƙi kum a kaiku Jahannama a haɗa ku da Mala'iku su yi muku walmukalifatu." Mutanan ɗakin ne suka sa dariya don yadda Yaya babba take haƙiƙancewa a zancen aljannah sai ka rantse da Allah tuni an yi mata bushara da tata aljannar tun a duniya. Ta juya wurin angwayen suma ta ƙare musu kallo ta saki murmushi tana faɗin:
"Allah mai iko ku dubi su Soja fuska sai walƙiya take, don Allah ban da aure wa zai yi maka haka? To ku saurareni da kyau don har ga Allah ba zan lamunci baku jikokina ku riƙa gasa musu aya a hannu ba, a'a raba ni da wannan falsafar. Yara dai amana muka basu ku kyautata musu da ma zaman aure sai haƙuri, iyayenku ma duk da haka suka kawo nan. Ga dai Ado nan ga sauran iyayenku tun da nake da su ban taɓa jin wata falsafar tashin hankalin ta ɓullo daga wurinsu da matansu ba. A cikinsu duk wacce ta ɓata muku rai ku zo ku same ni ku gaya min ranar mai cetonta a hannuna sai Allah, ku riƙa kula da su ɗan tsiren nan da ƴan kajin nan kun san suma suna ƙara danƙon ƙauna. Allah dai ya ƙara yalwata kaji a faɗin duniya ba don su ba da tuni ba a haife ka ba Salisu, ga Uwarka nan ba zan mata ƙarya ba, lokacin da aka aurota alƙur'an bata ƙaunar Ubanka. Amma da yake Ubanka ma'abocin siyan kaji ne sai wayar gari na yi na ga uwarka da ciki, don Allah ka gaya min idan kaji suka yi ƙaranci ya ya gidan aure zai yi." Ɗakin dai kowa ya yi shiru ba su tanka ba. Yaya babba ta yi ƙasa da murya ta ci gaba da cewa:
"Kun san dai sha'anin tsoho sai haƙuri, ni dai tun da nake baku taɓa yi mini komai ba amma ni dai ku gafarce ni idan na ɓata muku rai, yanzu Furaira ta ci gaba da nasihar."
Amsa mata suka yi sannan Inno ta ci gaba da jawabi. "Ni dai ƴar taƙaitacciyar nasiha gare ni. Gabaɗaya zan ce su ji tsoron Allah idan ba haka babu abin da zai hana mu zazzage musu albarka a tsakiyar ka. Ku matan yi na yi bari na bari sai kwalliya kissa da kisisina kamar yadda muka koya muku, Allah ya sani idan kuka saɓawa Allah babu sa hannunmu a ciki. Ku kuma mazan ku ne jagorori idan laifi suka yi banda duka ko zagi, don Allah ya sani ba za mu juri haka ba duk wanda ya taɓa mana jika alƙur'an mai hana mu maka shi wurin human rai (Human right) sai dai idan bama numfashi. Da haka nake yi musu fatan alheri."
Daga haka iyayensu maza suka yi musu nasiha sannan Baba Adamu ya sa aka shigowa da kowanne ango ledar kajinsa da ledar drinks haka ya basu gabaɗaya. Daga nan suka fice sannan aka ɗauki amare aka kai su ɗakin mazajensu. Dubu sai da aka zo tafiya da ita ta sa kuka wai dole su tafi da Yaya babba, wannan kalamai na Dubu ya sake karya zuciyar Yaya babba da ƙyar aka lallaɓa Yaya babba ta yi shiru aka wuce da Dubu ɗakin mijinta Aseem.
Ɗakin Dubu ya yi kyau sosai Baba Abubakar shi ya yi mata kayan ɗaki irin na ƴan birni, kayanta ba a yi ƙarya ba daidai rayuwar rufin asiri. Ɗan gidan gwanin birgewa komai sabo sai ƙamshi yake, Dubu aka kai aka ƙara yi mata nasiha sannan suka fito aka bar daga Dubu sai ƙawayenta biyu A'ilo da Raliya. Su Nasir sune kan gaba wurin rako ango, Aseem na gaba Nasir da abokansu biyu na rufa masu baya. Suna shiga Dubu ta ɗago kai ta mayafi tana satar kallonsu, tana ganin sun haɗa ido da Aseem ta mayar da kai cikin mayafi tana ƙyalƙyalewa da dariya. Nasir na zuwa ya ce, "Amaryarmu ga ango mun kawo miki da fatan za ki riƙe mana shi amana, don so muke nan da rana iya yau mu ga wannan ramin wuyan nasa ya shige." Aseem ya watsa masa kallo ya ce, "Nasir ranka zai ɓaci." Bai rufe baki ba ya ji Dubu ta ce, "Ai wallahi ko sati ba za a rufa ba sai kun yi mamakinsa, don baka san Laminu mijin ƙawata Zuwai ba yadda ka ga Me lob (My love) haka yake amma yanzu ko tunbinsa aka ɗora ma ka ji..."
Tsawar da Aseem ya buga mata ne ya sa sauran maganarta maƙalewa, ya dubi Nasir fuska ba walwala ya ce, "Bar min gida dama ban gayyace ku ba." Nasir na dariyar ƙeta ya ce.
"Ɗan iska ba sai ka nuna min ba matsayinmu ɗaya ba, ni ma kwanannan zan yi wuff da wata ka ga mun yi one-one." Ya ƙrasa maganar yana dire ledar da suka yi wa Aseem siyayya na shiga ɗakin Amarya, suna fita ya kalli su A'ilo da suka yi zuru-zuru ya buga musu tsawa, tun bai rufe baki ba suka miƙe suka fita, sai da suka yi gware ya kai sau biyu sannan suka samu ƙofa suka fice da gudu.
Suna fita Dubu ta fige mayafinta haɗe da ɓata rai ta ce, "Wallahi ka kunyata ni akan me za ka korar mun ƙawaye ko ladan siyan baki ba a ba su ba..." Ba ta ƙarasa magana ba ya bige mata baki ba shiri ta ja baki ta yi shiru.
Drower ya buɗe ya ciro sabuwar doguwar rigarsa ya fita falo sannan ya faɗa toilet ɗin tsakar gida. Yana fita Dubu ta yi maza ta buɗe akwati ta sauya kaya cikin doguwar rigar bacci, kannan nata ranƙwal babu gashi a kai kuma babu abin da ta sa a kan. Ledar kazar ta fizgo ta buɗe ta fara ci tana shan youghort ban da lumshe ido babu abin da take yi. Tana nan zaune Aseem ya shigo ya same ta, ba ƙaramin mamaki ta bashi ba binta yake da kallo yana ƙarewa kayan jikinta kallo, mamakinsa ɗaya yadda Dubu take da wayewar ido wai har ta san ta sa wasu kayan bacci, zama ya yi a bakin gado yana watsa mata kallo cike da takaici.
Bai tsinke da lamarin Dubu ba sai gani ya yi ta turo masa cinyar kaza saitin bakinsa ta ce, "Me lob kazar masoya." Ta ƙarasa maganar tana wani irin farfari da ido. Rasa abin yi ya yi yana juyawa ya fisgo wayar cazarsa da ya ajiye akan gado, Dubu na ganin haka ta yi tsalle ta fice daga ɗakin tana ihu, Aseem ya rufa mata baya ba su tsaya a ko'ina ba sai ɗakin Yaya babba.
Da gudu Dubu ta kwakume Yaya babba hannunta ɗaya ɗauke da kaza bakinta shane-shane da mai.
Yaya Babba ta rungume Dubu ta dubi Aseem tana faɗin, "Kayya Soja kai a komai sai ka nuna halin yahudawa da rashin imani. Dubu fa ƙaramar yarinya ce, a'a rabani da wannan falsafar yarinya ko kaza bata gama cinyewa ba kake niyyar afka mata."
ME KUKE TUNANI ZAI KASANCE? YAYA ZA A BUGA RAYUWA TSAKANIN SOJA DA DUBU?😂 WAI SHIN TA DAINA SHAƘIYANCINTA BAYAN AUREN KO KUWA SABON SHAFI ZA TA BUƊE😂😂😂😂 DON ALLAH KU HANGO MIN RAYUWAR AUREN SOJA DA DUBU MU JI YA ZATA KWASHE.
MAZA HANZARTA💃🏼 KI SIYA ƊARI BIYU BA YAWA🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️ NA TABBATA BA ZA KI JI KAICO BA, KI SIYA KI SHA NISHAƊI DA BAN DARIYA🤸🏻♀️💃🏼💃🏼
[7/9, 9:22 AM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*
© *AMEERA ADAM*
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
https://chat.whatsapp.com/J0qrgC0rXNQ57u50VzeewR
FREE PAGE 1
Girma da nauyin cikin da ke jikinta kamar an kifa ƙwarya, bai hanata gudun da take yi na ceton rai ba. Gudu take zabgawa saboda miyagun hallitun da ta yi tozali da su, masu kawo mata farmaki da zimmar cafkar tsohon cikin da ya yi tsini tamkar zai fashe.
Zuwanta bakin wata bishiyar kuka mai duhun gaske ya bata damar tsugunnawa cikin haki, saboda ji take kamar bayanta zai ɓalle gida biyu saboda azaba, ajiyar zuciya take saukewa akai-akai kamar wacce ta shekara tana matsanancin gudu a tsakiyar rani. Dafe bayanta ta yi wani irin azabar ciwon baya da mara ya sarƙeta kamar ana tsaga marar tata da kaifaffiyar aska. Sannu a hankali ta waiga bayanta don ganin mummunar halittar da ke bibiyarta kamar yanda inuwar mutum take bibiyarsa. Kukan jarirai ne ya fara yi mata amsa kuwwa kamar saukar aradu a tsakiyar ka! Ta ko ina take jin sautin kukan na su kamar kunnuwanta za su tawatse.
Kuka haɗe da dariya ne suke ta shi a cikin dajin, zuwa can ta hango inuwar wata hallita na tunkaro ta, matsananciyar guguwa ce ke tashi bishiyoyi na kaɗawa da ƙarfa yanda kasan za su jijjigo daga jikin jijiyoyinsu.
Cikin wani irin gwamamman yare ta riski muryar inuwar tana cewa, "Sai kin halaka ke da abin da yake cikinki, kin zama halakakkiya keda tsiron da ke cikinki." Ba ta yi aune ba ta fara jin abu na bin ƙafarta zuu! A daidai lokacin da ta ji wani irin nishi ya taso mata.
Durƙushewa ta yi a wurin tana murƙususu, nan take wani irin kukan Jarirai mai haɗe da kukan Jaki ya fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dajin tamkar zai tsage gida biyu. Sannu a hankali Jarirai suka fara rarrafowa suna zageta kamar ana zagaye wainar gero. Duk da halin da take ciki bai hanata yunƙurin tashi domin tseratar da rayuwarta ba, amma ina! Haihuwa ta tunkarota gadan-gadan nan take jaririn ya faɗo.
Sannu a hankali ya rinƙa bin duk wurin da jini ya zuba yana lasa shi da sauran 'yan uwansa Jarirai, tamkar waɗanɗa suke da'irar ƙungiyar asiri. Raihan da ke durƙushe da sauri ta zabura kamar wacce aka ɗanawa ruwan dalma, tana yunƙurin tashi nan take mabiyiya ta faɗo. Kamar yanda Kura take ƙishirwar nama haka suka afkawa Mabiyyar kafin wani lokaci tuni suka gama da ita.
Kamar haɗin baki haka suka waiwayi wurin da take tsaye, tamkar 'ya'yan Birrai haka suka fara tsalle suna ɗane jikinta har Allah ya basu nasarar hawa jikinta. Lokaci ɗaya suka fara lasar jikinta, ihu take kurmawa kamar zautacciya amma babu ɗaya daga cikinsu da ya yi alamun dakatawa. Daga can ƙafarta ta hango Jaririn da ya fito daga jikinta yana bin jinin ƙafarta yana lasa. A haukace ta ƙwalla ƙara tana ambatar sunan Mahaifiyarta kamar wacce ake zare wa rai.
Firgigit ta farka daga bacci tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta ci gasar tseren gudu, jikinta rawa yake kamar mazari, ta haɗa gumi sharkaf kamar wacce take gaban maƙera.
"Barka da tashi ranki shi daɗe." Ba ta yi aune ba ta ji kalaman Mama Uwani a tsakiyar kanta. Da sauri ta ɗago ta kalle ta har lokacin jikinta rawa yake, sai da ta jingina da bangon gadon ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Yauwa Mama Uwani."
"Kina buƙatar wani abu?"
Girgiza mata kai ta yi tana murza idanu, hamma ta yi haɗe da miƙa sannan ta dubi Mama Uwani tana faɗin, "Mama Uwani ki haɗa min Tea kafin na fito." Cike da girmamawa Mama Uwani ya russuna tana faɗin, "An gama shalelen Uwani, gabanki gata bayanki gata. Duk abin da kika faɗa haka za a yi uwar ɗakina." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin, Raihan miƙewa ta yi tana ɗan waƙe-waƙenta sannan ta faɗa toilet don ɗaura alwalar sallar asuba. Sai dai rana ta buɗe sosai wacce take nuni da gari ya waye tangararan don ƙarfe tara har da kwata a lokacin.
Sai dai har lokacin mafarkin da ta yi bai gama sakin jikinta, wani abin da ya bata mamaki bai wuce zuwan period ɗin ta ba alhalin ba lokacin zuwansa ba ne.
Mama Uwani tana fita bayan Raihan ta shiga toilet wata baƙar mage ce ta ratso daga bangon kusurwar ɗakin, idanunta jawur suke kamar gauta ga ƙarshen jelarta wani tafkeken kan maciji ne ban da sheƙi babu abin da yake yi. Kalle-kalle ta fara yi tana shine-shine sannan ta fara girgiza cikin wani irin yanayi, lokaci ɗaya ta fara rikiɗa zuwa kaloli daban-daban. Sai da ta rikiɗa zuwa kaloli sama da goma sannan ta dawo kalarta ta farko, ta buga tsalle zuwa kan gadon da Raihan ta tashi wanda har ya ɗan fara ɓaci da jini. Tana hawa kai ta fara lasa sai da ta siɗe shi tas sannan ta sauko cikin takun ƙasaita tana kalle-kalle, a hankali ta taka zuwa kan mudubin Raihan da ke cike da kayan shafe-shafe da turarruka kala-kala.
Girgiza ta yi lokaci ɗaya ta rike zuwa wata mummunar hallita mai siffar dorinar ruwa da ranƙwalelen ƙaho a goshinta, a hankali ta fara zuƙe mayuka da tururrukan da ke cikin kwalabe da robobinsu, nan take komai ya zama wayam babu komai a ciki. Wani irin ruwa ta shiga ɗurawa mai yauƙi sai da ta gama cika su sannan ta hura iska suka dawo tamkar mayuka da turarrrukan da ke ciki da farko. Mama Uwani ce ta tunkaro ƙofar da sauri wannan hallitar ta sake rikiɗewa zuwa mage wannan karon jelar rabuwa ta yi gida biyu dukkansu ɗauke da kan maciji. Tana jin alamun buɗe ƙofa da sauri ta ratse ta jikin bango ta ɓace daga ɗakin, sai dai takaicinta ɗaya da bata samu ta ƙarasa cimma abin da yake tafe da ita ba.
Mama Uwani jere kayan abincin Raihan ta fara yi, a daidai lokacin Raihan ta fito ɗaure da towel. Da murmushi Mama Uwani ta riƙo hannunta tana faɗin, "Ƴar gatan Uwani me kike buƙata bayan wannan?" Ɗan yamutsa fuska ta yi ta ce, "Babu." Mama Uwani cikin wani yanayi ta fara bin ɗakin da kallo, Raihan ta ɗan ja guntun tsaki tana faɗin, "Mama Uwani ki bani wuri bana buƙatar hayaniya."
Mama Uwani ba don ta so ba ta juya jiki a sanyaye ta fice daga ɗakin tana waige, fitarta ke da wuya Mommy na kawo kai tana ganin Mama Uwani ta ce, "Uwani yarinyar ta tashi kuwa?" Mama Uwani cikin ladabi ta ce, "Ta tashi hajiya yanzu na kai mata abin kari." Mommy bata tanka mata ba ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, Raihan na gaban mudubi za ta fara shafa mai. Mummy ta kira sunanta tana ci gaba da cewa, "Raihan ba dai yanzu kika ta shi kika yi sallaha ba?" Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Haba Mommy wai me kika mayar da ni, ni ba sallah ma zan yi ba period ɗina ya dawo." Fuska ɗauke da damuwa Mommy ta ce, "Period kuma, ina ce yau ko sati biyu ba ki da gamawa ba." Cikin rashin damuwa ta gyaɗa kai tana ci gaba da shafa mai, juyawa Mommy ta yi ta fi ce tana faɗin, "Gaskiya idan ya ci gaba da yi miki wasa dole mu je mu ga likita." Raihan ta tura baki gaba ƙasa-ƙasa da murya tana faɗin, "Kawai don period ɗina ya dawo sai ace sai na je wani Hospital ana zaune ƙalau." Turo ƙofar da aka yi ne ya sa Raihan waigawa a lokacin ta fesa turare tana saka wata doguwar rigar bacci, Mama Uwani ce ta sake shiga hannu ɗauke da kunun gyaɗa ta ajiye, Raihan na ganin haka ta saki murmushi mai sauti ta ce, "Mama Uwani dama kin yi kunu shi ne baki kawo min ba, ai kuwa da na cika cikina sai kin kwashe min tass kin ɗura min kunun nan." Ta ƙarasa magana tana zame towel ɗin jikinta don ita Raihan bata kunyar ko a gaban waye ta cire kayanta ko ta sauya wasu.
Mama Uwani na ganin haka ta fice daga ɗakin, Raihan na cikin saka kaya ta ji kanta na sara mara lokaci ɗaya jini ya fara bin ƙafarta ga wani irin raɗaɗi da jikinta yake yi ta ko'ina, nan take ta yanke jiki ta faɗi a wurin. Wani irin hayaƙi ne ya fara zirarowa ta jikin ƙofa har sai da ya zo gaban Raihan da ke kwance jini ya fara malala daga jikinta, lokaci ɗaya hayaƙin ya rikiɗa zuwa siffar mutum. Kallon kan mudubin Raihan ya yi yana girgiza kai cike da baƙin ciki, ɗaya bayan ɗaya ya fara zuƙewa mayuwan ciki da yake ganinsu da kalar ruwan nan mai yauƙi, kusurwa bangon ɗakin ya kalla ya ce, "Tabbas ba aikin kowa ba ne sai naki Mugaza, na lura kin fara wuce makaɗi da rawa amma ranki sai ya yi mummunan ɓaci." Tun bai rufe baki ba magen nan ta sake ɓullowa ta bango, har sai da ta zo gabansa ta yi girgiza cikin surar wata matashiyar budurwa ta ce, "Ka ga laifina don na nakasta mai shirin tarwatsa farincikina? Ko kana tsammanin zan zura ido ka ɗauko mini kishiya alhalin ka san wannan haramtacciyar al'ada ce a zuri'armu. Wani abin takaici ma ka rasa wacce za ka aura sai bil'adam salon ka ja mini abin kunya cikin ahalina, wallahi ba zan lamunci haka ba kuma wannan somin taɓu ne ka zuba ido ka gani." Tana gama maganar ta sake rikiɗa zuwa mage ta ɓace daga ɗakin, cike da takaici ya kalli gadon Raihan sai kawai ya fara kiran sunan Hidaya. Sai da ya kira sau uku sannan wata matashiyar budurwa ta ratso ta ƙarƙashin ƙasa mai zubin siffar Raihan babu abin da ya bambamta su har kayan jikinta. Wurin abincin Raihan ya nuna mata ya ce, "Ki maye gurbinta kuma bana buƙatar a samu matsala idan ba haka ba har abada ke da biyan buƙatar ƙudurinki."
Idanunta ne suka ciko da ƙwallah ta ce, "Wuskarbat min kalsusbima wakfit karmu linkasbu muzrabatu fisgatmuha warmi Jalkisu Mu'az." (Don Allah karka yi mini haka, ka san duk duniya babu wanda nake ƙauna kamar Yarima Mu'az.)
Ɗaukan Raihan ya yi da ke kwance ya saɓa a kafaɗa sannan ya kalli jabun Raihan da ke tsaye ya ce, "Dole ki ɗauki ɗabi'a irin ta Raihan hatta yare dole ki ci gaba da irin yarenta ba namu da muka saba yi ba. Na gaya miki idan aka samu matsala ke da Yarima Mu'az har abada." Yana gama maganar ya daki tsakar ɗakin nan take ƙasar wurin ta dare ya faɗa ciki hannunsa ɗauke da Raihan suna shigewa ƙasar wurin ta haɗe ta shafe kamar wani abu bai taɓa faruwa a wurin ba.
SHARE HILIS🌚
Daga yau za ki iya turo kuɗinki don karki bari ayi babu ke🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[7/9, 9:22 AM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*
© *AMEERA ADAM*
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
FREE PAGE 2
https://chat.whatsapp.com/J0qrgC0rXNQ57u50VzeewR
A hankali Jabun Raihan ta fara bin ɗakin da kallon, miƙewa ta yi ta fara buɗe drowers ɗin kayan Raihan sai kuma ta bi hotunan ɗakin Raihan da ke maƙale a jikin bango tana kallo ɗaya bayan ɗaya, tana jin motsi ta koma wurin kayan abincin ta zauna. Kallon abincin take don sam bai burgeta ba cikin zuciyarta take mamakin irin abincin bil'adam don ita bata ga abin daɗi a ciki ba. Goggo ce ta turo ƙofar tana faɗin, "Rehanu! Ke Rehanu wai ina kika shiga ne tun jiya ban ji wulgawarki ba, yarinya sai iya shege don kin ga na damu da ke." Turus ta yi tana kallon Jabun Raihan da ke cin abinci tana yamutsa fuska, daƙuwa ta yi mata da hannu tana faɗin, "Kin ci ƙaniyarki Rehanu dama kina jina kika yi shiru to kin wulaƙanta uwarki Abu. Meye wannan ɗin kike ci kina yamutsa fuska kamar abinci?" Jabun Raihan a daƙile ta ce, "Gashi kuwa kin gani."
Goggo ta shiga ɗakin ta yi tsaye a kan Raihan tana faɗin, "Oho dai kowa ya raina uwar wani tashi ya raina, wallahi duk maganar da kika gaya min uwarki da Ubanki kika gayawa." A fusace ta ɗago tana duban Goggo da ke tsaye tana zazzaga ruwan masifa, farantan gabanta ta kalla tana motsa baki lokaci ɗaya ta cinye abincin ciki sai kwanukan, tana kallon Goggo kamar wacce ta basu umarni sai farantan suka yi tsalle zuwa gaban Goggo, wuƙar da Mama Uwani ta haɗowa Raihan don ta riƙa yankar farfesun ƙafar sa ce ta yi tsaye a daidai fuskar Goggo saitin idonta tana wani juyi, kamar za ta tsokane mata ido. Jabun Raihan ta kalli Goggo fuska ba walwala tana cewa, "Kika sake zagar mini iyaye sai na tsokane idonki, ke da sake gani har abada. Wannan kwanukan kuwa sai na basu umarni su yi ta ranƙwale miki kai har sai sun illataki." Goggo daskarewa ta yi a wurin, tuni fitsari ya jiƙe mata zani gumi sai yanko mata yake ta ko'ina. Tun Jabun Raihan bata gama magana ba, Goggo ta juya da gudu tana ƙawalawa Mahaifiyar Raihan kira, sai dai yadda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi ya sa ta fice da rarrafe zanin jikinta kuwa tuni ya samu mutsuguni a bakin ƙofa.
Tana fita Jabun Raihan ta miƙe tana kaiwa da kawowa don gabaɗaya zaman wurin ya gundureta, abin da ya sa ta bi umarnin Huzaifa don biyan tata buƙatar amma ba don haka ba babu yadda za a yi ta amince da rayuwa cikin siffar bil'adam.
Huzaifa bai tsaya ko'ina ba sai cikin wani ƙasurgumin daji mai ɗauke da jajayen furanni, da jajayen ƙoramu. Komai na wurin ja ne hatta ciyayin da suke wurin, sai waɗansu korayen kifaye da su kaɗai ne suka bambamta da jajayen abubuwan da ke wurin. Kan wani jan dutse ya kaita ya kwantar da ita nan take ya fara gyara mata jikinta, kafin wani lokaci tuni ya gyara mata jikinta ya ɗauko wani ƙaramin jariri da ke kwance cikin wata ƙorama mai ɗauke da siffar kunkuru, sai dai kansa ɗauke yake da kawuna huɗu kowanne da surarsa. Akwai kai mai siffar jaki, agwagwa, mage da mai siffar kifi, a kowanne kai akwai manya kahunhuna guda biyu, daga jelar hallitar ɗauke take da tafkeken kan maciji. Yana zuwa ya ɗora shi a gefenta sannan ya ɗaga hannunta ya tura shi ƙarƙashin jikinta kamar yadda uwa take rungume jaririnta. Nesa da su ya koma yana sakin murmushin farinciki a fili ya fara faɗin, "Na jima ina burin haka ban samu dama ba domin gudin abin da zai ɓata miki rai, sai dai a wannan karon dole na ɗau wannan matakin domin haka ne kaɗai sai tseratar da ke daga kaidin Mugaza, idan ba haka ba duk yadda za ta yi sai ta halaka min ku. Ni kuma ba zan juri rabuwa da ke ba wanda ya nemi raba ni da ku zan iya hallaka shi ko wanene, ko da kuwa Mahaifina ne Jingas." Yana gama magana ya ɗaga dutsen da Raihan take kwance da jaririnta, naɗe su ya yi cikin wani kogon dutse sannan ya hura wani kogi da korayen kifayen nan suke ciki, nan take ruwan ya dare Huzaifa ya jefa su ciki ya sake hura ruwan ya haɗe gabaɗaya.
Mommy na daga falo ta fara jiyo muryar Goggo na ƙwala mata kira, da sauri ta nufi wurin da ta ji muryar Goggo tana zuwa ta yi turus ganin Goggo na rarrafe daga ita sai ɗan fatari. Da sauri ta sunkuya tana faɗin, "Goggo lafiya kuwa ko ƙafar ce ta motsa?" Tun bata rufe baki ba Goggo ta ci gaba da faɗin, "Abu ki dubi Allah da ma'aiki ka mayar da ni Albasu wallahi na yafe zaman gidanki, ki maida ni Albasu na mutu cikin aminci tun bata tsaface ni a gidan nan ba." Goggo na maganar hawaye da majina na zuba, a gefe ɗaya fitsari ne ke zuba don Goggo ta yi fitsari daga ɗakin Raihan zuwa babban falo ya kai sau uku.
A ɗan tsorace Mommy ta waiga tana faɗin, "Goggo lafiya kuwa wace ce ta zama matsafiya?" Goggo ta fyace majina da gefen zaninta ta ce, "Wa kuwa kika sani idan ba Rehanu ba. Wallahi yadda na ga tana tsafi ido biyu na ga Annabi haka..." Tun bata ƙarasa maganar ba Mommy ta fara waige tana katseta da sauri cikin ƙasa-ƙasa da murya.
"Goggo don Allah ki daina faɗin haka wallahi Alhaji yana gida kar ya ji abin da kike faɗa, kin san fa baya kawaici a kan yarinyar nan Raihan." Tana rufe baki Inno ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Allah ya tonu asirinku, ashe gulmar Ɗana kuke da jikalleta to ahir ɗinku wallahi ke Zinaru ki yi ta kanki arziƙi kika zo ci ba zan miki baƙin ciki ba, gida dai gidan Ɗana ne ba a isa a sawa jikata ido." Goggo takaici ya sake cikata tana ganin kamar gori Inno take yi mata, don haka a zafafe ta ce, "Allah ya sa ni na haifi Abulle har ɗan naki ya aura, magana ce na gama ta yau za a mayar da ni Albasu don wannan sheɗaniyar jikar taki ba za ta sayar da kaina ina ji ina gani ba." Inno na jin haka ta yi zaman ƴan bori daɓar sai kawai ta fashe da kuka, da sauri Mommy ta koma wurinta tana rarrashinta amma fir taƙi yin shiru. Suna nan zaune Alhaji Abdallah ya sauko cikin dakakkiyar shadda ruwan toka da hula baƙa, kayan ba ƙaramin kyau suka yi masa ba. Tun kafin ya ƙaraso Mommy ta fisge ɗankwalinta ta rufawa Goggo, yana ƙarasowa ya ce, "Lafiya dai Inno mai yake faruwa?" Inno na jin haka ta rushe da kuka tana faɗin, "Audullahi ka dubi irin sitirar da ka yi wa Zinaru ita da ƴarta amma da yake sun samu wuri wai cin naman ka suke da ƴarka ɗaya tilo a gidan duniya. Don Allah ko don darajar haihuwa Abulle ai da ɗagawa yarinyar nan ƙafa ina dalili tana uwarta tana cin namanta?" Goggo ta ƙanƙance ido cikin masifa ta ce:
"Audullahi wallahi tun wuri ka san halin da kake ciki, kwarankwatsa dubi Rehanu ta shiga ƙungiyar asiri."
Kamar wanda aka zagi iyayensa haka Alhaji ya ɓata fuska sai da ya haɗiyi yawu mai ɗaci ya ce, "Goggo kin san wa kike faɗa kuwa? Raihan ɗina ce ta shiga ƙungiyar asiri?"
"Ƙarya na yi maka kenan Audullahi?" Goggo ta tambaye shi tana ɗage kai gefe. Shiru ya yi don ya san idan ya buɗe baki a kan Raihan za a iya samun matsala shi kuma yana ganin girman Mahaifiyar matarsa, ba zai so wani abu ya haɗa su ta sanadiyyar Raihan ba. Ganin haka ya sa Mommy ta riƙo hannun Goggo tana cewa, "Goggo ta so mu je ɗaki don Allah." Inno na ganin haka ta fashe da kuka tana faɗin:
"Allah ya fini sanin dalilin da ya sa bai bani ƴa mace ba, amma ya yi mini komai da ya bani Audullahi da ban haihu ba sai na rasa mai kaini ɗaki nima." Tana gama maganar ta kalli Alhaji ta ci gaba da cewa, "Audullahi nima ka kaini ɗaki ba sai an goranta min ba, kuma wallahi aure za ka ƙara don ba za ka zauna da macen da bata ganin mutumcina ba."
Daddy na shirin yin magana suka ji Raihan ta turo ƙofa ta fito fuskarta murtuk babu fara'a, da sauri Goggo ta fara ja baya tana leƙenta. Daddy na ganinta ya saki murmushi ya rungumota yana faɗin, "Barka da fitowa habibtyn daddy." ƙarasowa wurin ta yi ta ce, "Daddy ba dai fita za ka yi ba?" riƙo hannunta ya yi ya ce, "Yanzu ma kuwa don na gama komai."
Fisge hannunta ta yi ta koma kan kujera tana faɗin, "Na faɗa maka gaskiya za ka yarda?" Murmushi ya yi ya ƙarasa wurinta ya ce, "Faɗi babyna."
"Ka haƙura da fita da baƙar mota idan ba haka ba za a samu matsala."
Mommy ta kalle ta tana faɗin, "Raihan me ya sa bakinki baya furta alheri ne? Ke kin san gaibu ne da za ki yanke masa wannan hukuncin." Goggo da ke gefe tana son yin magana tsoro ya hanata. Daddy ya gyara zaman agogonsa yana faɗin, "Baby sai abin da kika ce da wacce kike son da ita." Daga wurin da take ta ce, "Kowacce ka yi niyyar fita da ita amma ban da baƙar." Daga haka sallama ya yi musu Mommy ta wuce raka shi, Raihan na ganin haka ta ƙarasa gaban Goggo ta tsugunna a wurinta tana faɗin, "Wallahi na kuma jin kin danganta ni da ƙungiyar asiri Allah za ki yi mamakina, sai na kaiki Daulatul Jinnul nariy na azabtar da ke." Inno da ke gefe ta karɓe zancen da faɗin, "Wallahi kema kya gaya mata ai ni wallahi ban yafe wannan ƙazafin da ta yi miki ba. Ni dai wannan larabcin da kika yi ne ban san me kika faɗa ba, amma idan za ki tafi da ita don Allah ki kaini na ga yadda Zinaru za ta yabawa aya zaƙinta." Raihan bata bi ta kansu ba ta wuce kan dianning table, saboda yadda yunwa take sasaƙar cikinta don abincin da ta ci babu in da yaje mata. Tana zama ta fara buɗe kulolin da ke wurin nan take ta fara tasa kulolin a gaba, ɗaya bayan ɗaya tana cinyewa, kuloli huɗu ne a wurin amma da zaman ta ko minti biyar bata yi ba ta cinye abincin ciki gabaɗaya, tare da shanye shayin da ke cikin fulas ɗin ta kora da ruwa sannan ta dawo falo ta zauna. Lokacin da ta dawo tuni su Inno sun wuce sashensu don haka basu lura da abin da Jabun Raihan ta aiwatar ba.
Sanyin da yake busawa a wurin ne ya doki gangar jikinta wanda ya sa ta buɗe idanunta a hankali tana ƙarewa wurin kallo, cikin rashin ƙwarin jiki ta miƙe zaune har lokacin kallon wurin take yi da tsananin mamaki. A hankali wannan jaririyar hallitar ta fara matsowa har sai da ta hau cinyar Raihan, zamanta a cinyarta ya sa ta lura da wurin a zabure ta miƙe tana ƙwalla ƙara haɗe da ja da baya zafin buguwar ya sa hallitar yin can gefe wanda yake nuni da jin zafin da ta yi. Waige-waige ta fara yi tana ambatar sunan mahaifiyarta, kamar daga sama ta riski muryar Mommynta tana faɗin, "Ga ni nan zuwa Raihan."
Tafiya ta fara yi daga wurin da ta fara jin sautin muryar, ta wani lungu ta hango Mommynta ta fito cikin doguwar rigar shadda tana sakar mata murmushi, kallo ɗaya ta yi mata ta ji gabanta ya yu mummunan faɗuwa. Dafa Raihan ta yi tana faɗin, "Kin tashi Raihan?"
Kuka Raihan ta fashe da shi tana faɗin, "Mommy ina ne nan menene wancan abin?" Ta ƙarasa maganar tana nuna wurin da wannan hallitar take rarrafowa a hankali, Mommy ta kalli wurin tana murmushi ta ce, "Taho mu je ki rabu da wancen abin." Har sun fara tafiya Mommy ta kalli Raihan ta ce, "Amma duk wanda zai ce miki ki bishi kar kije wurinsa cutar da ke zai yi ni ce mahaifiyarki babu abin da zan yi miki." Har lokacin Raihan a tsorace take don haka ta kalli yanayin wurin ta ce, "Amma mommy ya aka yi muka zo nan?" A ɗan tsawace ta ce mata:
"Za ki taho ko tambaya ta za ki tsaya yi." Ba musu Raihan ta bi bayan wacce take gani da siffar Mommynta, har sun kusa fita sai gani ta yi Daddynta ya diro da ƙarfin gaske yana faɗin, "Raihan." Da sauri ta waiga wurinsa tana shirin yin magana mai ɗauke da siffar Mommynta ta fara fisgar hannunta tana faɗin, "Karki saurare shi wuce mu je." Da sauri ya ƙaraso wurin rai a ɓace ya fisgi hannun Raihan sannan ya dubi Mai ɗauke da siffar Mommy yana faɗin, "Mugaza ki shiga taitayinki fa, na gaya miki ki fita harkar yarinyar nan ba na son na hukuntaki a kanta amma wallahi idan kika illatata sai na baki mamaki." Lokaci ɗaya ta rikiɗa zuwa wata mummunar hallita mai ɗauke da siffar ƙadangare sai dai kawunanta goma kowanne ɗauke yake da wasu irin manyan harsuna masu kama da kaifin takobi. Da gudu Raihan ta rungume mai ɗauke da siffar mahaifinta tana wani irin kuka tare da faɗin, "Daddy tsoro nake ji." Ilahirin jikinta ban da rawa babu abin da yake yi, rumgume ta ya yi tsam a jikinsa yana shafa bayanta cikin wata irin soyayyarta da take fisgarsa, don karta fahimci wani abu ya sa ya iya riƙe kansa ba tare da kusanceta ba. Wannan abin ba ƙaramin ɓata ran Mugaza ya yi ba, a shammace ta kaiwa Raihan cafka da ɗaya daga cikin harshenta a ƙafa, da sauri Huzaifa ya janyeta amma sai da harshen nata ya samu ƙafarta. Wata uwar ƙara ta ƙwalla sannan ta faɗa jikin Huzaifa wanda yake nuna suma ta yi.
Wata irin mahaukaciyar dariya Mugaza ta fara ƙyaƙyatawa lokaci ɗaya ta murtuke fuska tana faɗin, "Ki je ki da wannan damuwar zan baki rata kafin na sake waiwayo ki." Tana gama maganar ta ɓace daga wurin.
Cike da tausayi Huzaifa da ke ɗauke siffar Daddy ya shimfiɗar da Raihan, a daidai wannan lokacin jaririn hallitar nan ya ƙaraso wurin ya kwantar da kansa a jikinta. Hannu biyu Huzaifa ya sa ya ɗago jaririn idanunsa ɗauke da ƙwallah ya ce, "Mahaifiyarka na fuskantar ƙalubalen rayuwa, amma daga yanzu zan tsaya mata tsayin daka don kare martaba da ƙimarta." Yana gama maganar ya sake ɗora mata shi a kanta yana motsa baki, lokaci ɗaya jaririn hallitar ya ɓace.
Yana ganin ɓacewarsa ya kalli Raihan da ke kwance ya ce, "Daga yau za ka kasance tare da Mahaifiyarka ko baby komai za ka riƙa ankarar da ni kamar yadda ka ankarar da ni kafin Mugaza ta cimma ƙuduri a kanta."
Share hilis🌚
0 comments:
Post a Comment