Jabun Raihan na shiga ɗaki ta ji Huzaifa na ƙwala mata kira, ta kusurwar bango ta wuce cike da ɗoki don zamanta a cikin gidan jin ta take kamar a kabari take.
Huzaifa da ke tsaye a gaban Raihan ya dubi Jabun Raihan ya ce, "Mugaza ta yi mata rauni zan mayar da ita ga mahaifanta amma zan ci gaba da bata kulawa kamar yadda na kwashe dubban shekaru ina tsaye a kanta. Ki je na sallame ki idan da yuwar wani lokacin na buƙace ki za ki ji ni." Cike da farinciki jabun Raihan ta rikiɗe zuwa siffar wani ƙaton tsuntsu mai ɗauke da manyan fuka-fukai ta ɓace daga wurin, daga wurin da yake ya ɗauki Raihan ya ɗora ta akan gadonta sannan ya ɓace daga wurin.
Bayan shigar jabun Raihan ɗaki ta fara kiran Mama Uwani, cike da girmamawa ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Ga ni hajiya."
Mommy ta kalli kulolin kan dianning ta ce, "Mama Uwani yau mun wayi gari da wani abin almara, dubi kulolin nan wai Raihan ta cinye." Da mamaki Mama Uwani ta zaro idanu ta ce, "Hajiya duka ita Uwarɗakin nawa ce ta cinye?" Mommy ta taɓe baki ta ce, "Dama ke ba ta laifi a wurinki ai, yanzu a sake dafa wani abincin bari na haɗa cornflakes." Mama Uwani ta fara tattara kwanukan tana faɗin, "Hajiy ai kowanne laifi kika ɗauko cewa kike ita ce, ni kuma uwarɗakina bata laifi." Tana gama maganar ta kwashe kwanukan ta wuce kitchen da su.
Raihan ba ita ta farka sai bayan azahar, a hankali ta buɗe idonta da suka yi mata nauyi dum! Tana ƙarewa ɗakin nata kallo. Lumshe idonta ta yi saboda yadda ta ji kanta yana sara mata kamar zai tarwatse, yunƙurawa ta yi zata tashi zaune ta ji jikinta ya yi mata wani irin tsami, ƙafarta ta hagu ta ji ta yi mata sanyi kamar ba a jikinta take ba. Da ƙyar ta samu ta fara dafa bango tana jan ƙafar tata da take jin ta yi mata nauyi kamar gungumen icce, tana zuwa falo ta fara yamutsa fuska tana bin ko'ina da kallo, a gefe ɗaya kuma ta fara wani shinshine-shinshine a haukace kamar mahaukaciya sabon kamu, da rarrafe ta fara watsi da kayan fallon cikin wani irin yanayi tana wani irin ƙaraji da gurnani kamar zakanyar da take tsaka da farauta. Ƙarar fashewar kayan ne ya fito da Mommy daga ɗaki a tsorace tana bin wurin da kallo, tana shirin yin magana su Goggo suma suka turo ƙofa suka fito don ganin abin da yake faruwa. Gilas ɗin center table da ta fasa ta fara ɗauka tana wurga musu tana faɗin, "Waye ya ɗauke min ɗana, ɗana ne wallahi duk wanda ya taɓa min shi sai na kashe shi." Inno da Goggo na ganin haka da rarrafe suka juya cikin ɗaki a tsorace, suna shiga suka bankawa ƙofarsu sakata jiki na rawa.
Mommy jiki na karkarwa ta ce, "Raihan lafiyarki kuwa?" Raihan ta sake wurgawa Mommy wata kwalba da sauri ta sa hannu ta kare, kwalbar ta yanketa a hannu jini ya fara zuba, jin ƙarnin jinin mommy ya sa ta fara wurga mata wani mugun kallo tana lasar baki. Ta ci gaba da surutai ba fasali, Mama uwani ta shigo a tsorace tana kallon abin da yake faruwa.
Hanyar kitchen ta nufa tana zuwa a haukace ta fisgo wata ƙatuwar roba wacce take ciki da ɗanyan kifi, tana zuwa falo ta rungumeta da hannuwa biyu tana sauke ajiyar zuciya.
Mommy na shiga ɗaki hankali a tashe ta ɗau waya ta fara kiran Daddy, ba a jima ba ya ɗauka ko jiran cewarsa bata yi ba ta fara faɗin, "Alhaji muna cikin tashin hankali, da alama ciwon Raihan na shekarun baya ne ya dawo sabo don Allah ka yi maza ka zo." Amsa mata ya yi sannan suka yi sallama ya katse wayar a gaggauce, Mommy na daga wurin da take a ɗaki tana jiyo ƙarara fashe-fashen kayan da Raihan take yi. Bayan wani lokaci shiru ne ya biyo baya, jin shirin ya sa Mommy ta miƙe a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin. A falo ta hango Raihan zaune rungume da ɗanyun kifi, gabaɗaya ta ɓata jikinta da falon da ruwan kifi ban da ƙarninsa babu abin da yake tashi. Daddy ne ya turo ƙofa ya shigo yana gaba Dr Hamza na biye da shi, sai dai ganin yanayin falon ya sa ya fahimci wannan ciwon nata har ya ninka na baya. Jin sallamar Daddy ya sa ta ɗago da jajayen idanunta tana yi masa wani irin kallo, a haukace ta zaburo kansu tana faɗin, "Kar wanda ya taɓa mini ɗana jinina ne ba zan laminta a raba ni da shi ba." Tana rufe baki ta wurgowa Daddy wata kwalba saura kaɗan ta same shi a fuska ya kauce, Daddy ne ya fara kiran Yunusa mai gadi yana zuwa suka shiga kiciniyar riƙe Raihan sai da ƙyar suka samu nasarar riƙeta Likita ya yi mata allurar bacci, a take bacci ya ɗauketa ta faɗi gefe.
Kan kujera suka ɗorata Likitan ya fita yana yi wa Daddy bayani.
"Wato Alhaji da alama ciwon yarinyar nan ya dawo sabo, domin idan har abin da mahaifiyarta ta faɗa ne za mu iya cewa ya ninku a kan na da, saboda a da tana surutai kawai idan abin ya tashi, amma a wannan karon tana nuna kifi a matsayin ɗan cikinta. Akwai issue mai girma a game da lamarin ciwonta, za mu yi bincike mai zurfi a kai, sannan kar a riƙa wasa da magungunanta ta riƙa sha akai-akai." Jikin Daddy a sanyaye ya miƙawa Dr Hamza hannu yana faɗin, "Na gode sosai Dr don Allah a yi wani abu kai, ka san ina matuƙar son Raihan ba zan iya jure rashinta." Dr Hamza ya jinjina kai ya ce, "Insha Allah Alhaji kuma a ci gaba da addu'a everything will be successfully." Daga haka suka yi sallama da Likita. Yana komawa ciki tuni ma'aikatan gidan suka shiga hada-hadar gyaran falon, kusa da ita ya je ya zauna ya zura mata ido, hannu ya ɗora a kan goshinta zuciyarsa babu daɗi ya ce, "Wish you quick recovery dear, me ya sa al'amuranki basa zuwa da sauƙi why? Allah ya baki lafiya my baby." Mommy na ƙarasowa wurin ta dubi Alhaji cikin damuwa ta ce, "Habibi ni kam wata shawara gare ni." Bai furta mata komai ba ya ɗago yana kallonta ya yi mata alamar yana sauraronta. Jingina ta yi da bango ta ce, "Gani nake yi mai zai hana ciwon yarinyar nan a haɗa shi da na islamic chemist ko akwai shafar aljanu a ciki..." Tun bata dire zancenta ya buga mata tsawa da cewar, "Ba na son na ƙara jin kin danganta min Raihan da wani jinsin bayan bil'adam, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci. Me ye wani islamic chemist malaman da kaje wurinsu sai dai su fara yi maka turare da hayaƙi, da sun samu wuri za su fara yi maka maula. Idan ba za ki taya ni mu nema mata magani ba don Allah ki cire hannunki daga cikin maganar, ni kaɗai na isa na nema mata lafiya." Ran mommy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, amma babu yadda ta iya haka ta ja bakinta ta tsuke don ta san akan wannan maganar sai su haura sama su faɗo. Daddy ne ya cicciɓi Raihan zai kaita ɗaki da sauri Mommy ta nuna masa ɗakinta tana faɗin, "Ka kaita Toilet ɗina zan gyara mata jikinta a can sai ta kwanta." Bai tanka mata ba ya wuce ya kaita ɗakin Mommy don har lokacin fushi yake yi.
Mommy da kanta ta gyara Raihan ta kwantar da ita a kan gadonta, zama ta yi a gefe tana kallon ƴartata cike da tausayawa. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla, ta sharce ƙwallah ta furta, "Wannan ita ce kalar tamu ƙaddarar, Allah ya baki lafiya Raihan."
Raihan ta jima tana bacci sai bayan wani lokaci sannan ta tashi, ɗingisawa ta ci gaba da yi har ta fito zuwa falo. A lokacin an gyara falon sai ƙamshin turare yake. A zaune ta hango Mommy Mama Uwani na zaune a ƙasa tana matsawa Mommy ƙafa, cike da farinciki Mama Uwani ta ce, "Uwar ɗakina kin tashi?" Kafin Raihan ta yi magana Mommy ta furta, "Barka da tashi My Princess." A ɗingishe ta ƙaraso wurin cikin damuwa mommy ta ce, "Me ya samu ƙafar taki?" Raihan ta yamutsa fuska ta ce, "Wallahi haka kawai na ta yi min nauyi. Mommy kamar mun je wani wurin ko? Ko dai mafarki na yi ne?" Mommy a tunaninta lokacin da ciwon Raihan ya tashi take nufi, ita kuma Raihan tana son tuna zuwanta Duniyar su Huzaifa amma kanta ya yi nauyi ta manta. Mama Uwani ta kafeta da ido sannan ta ce, "Uwar ɗakina sannu kin ji, ai ke kin zama ƙadagaren bakin tulu a karki a kar tulu a barki ki ɓata ruwa." Raihan ta ce, "Yauwa Mama Uwani, don Allah haɗo min ruwan tea." Ta yi maganar cikin jin daɗin kanbabawar da Mama Uwani ta yi mata, Nan take Mama Uwani ta tashi ta nufi hanyar kitchen. A hankali Goggo ta turo ƙofa ta fito falo, don tun lokacin da ciwon Raihan ya tashi da suka shige ɗaki babu wacce ta fito a cikinsu, kallo ɗaya za ka yi wa Goggo ka tabbatar da tsoro ya mamaye zuciyarta amma sai ta dake ta fara yashe baki tana faɗin, "Rehanu hutawa ake yi." Raihan ta taɓe baki ta ce, "Ni kam ko karatu ne wallahi Goggo ya ci ki haddace sunana, kullin sai na ce miki ba sunana Rehanu ba amma ina miyar kuka ta toshe ko'ina." Mommy ta ɓata fuska ta ce, "Gidanku Raihan." Goggo da ta lura Raihan ta dawo cikin hayyacinta, ta yi mata daƙuwa ta ce, "Gata a zaune ita kika gayawa haka." Goggo ta nemi wuri ta zauna tana faɗin, "Abu kunna mini wannan shirin da suke na ƙasashen labarawa ko idanuna sa ƙara ƙarfi." Inno ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Allah ya sani ba za mu kalli masu jajayen kunne ba, ni dai ki kai mini shirinsu wannan yaron Adamu zango da Ali Nuhu, ki saka mana sangaya mu kallah." Mama Uwani ce ta ƙaraso da kofin shayi ta taimakawa Raihan suka wuce ɗaki, don ƙafarta sosai ta yi mata nauyi ɗingisawa take yi.
Shigar su ɗaki keda wuya, Mama Hasiya ƙanwar Daddy ta yi sallama cikin falon. Fara'a ɗauke a fuskarta ta shiga cikin falon. Mommy da murmushi ta tarbi Mama Hasiya tana faɗin, "Mai gidan da ba awo ba cefane, ba waya ba labari." Mama Hasiya ta zame mayafin jikinta tana faɗin, "Mutum da gidansa wacce waya zai yi." Mommy ta saki murmushi tana faɗin, "Barka da zuwa wai da yamman nan kike tafe." Mama Hasiya ta ajiye jakar hannunta tana faɗin, "Wallahi dole ce ta kawo ni, kin san Hubbi ya yi tafiya ƙafar Dubai to sun yi waya da DR John wai yau zai shigo gari so kin san matsalar hospital ɗin Dr John idan kana son ganinsa sai dare." Mommy ta sauya fuska cikin yanayin damuwa ta ce, "Allah ya sa a dace wai wancen karon ba ya ce ƙasa da six months komai zai iya faruwa ba? Ya ce za ki iya samu ciki a kowanne lokaci." Mama Hasiya ta jinjina kai ta ce, "To kin ga dai shiru, lamarin rashin haihuwar nan ba ƙaramin damuna yake yi ba. Tun hubbi bai fara damuwa ba yanzu na fuskanci abin ya fara damunsa, shekara sama da goma sha biyar ba haihuwa an ya ina da rabon ganin ƙwaina a duniya kuwa?" Mama Hasiya ta yi maganar idanunta na cikowa da ƙwallah. Cikin sigar lallashi Mommy ta dubi Mama Hasiya tana faɗin, "Komai kika ga ya faru da bawa da sanin Allah, ba a nan take ba. Komai fa lokaci ne mutane da dama akwai waɗanda suka fiki daɗewa kuma Allah ya kawo musu mafita, mu ci gaba da addu'a komai ya yi farko zai yi ƙarshe." Mama Uwani ta ƙaraso cikin falon fuskarta ɗauke da fara'a tana faɗin, "Hajiya barka da zuwa." Bayan sun gaisa ta fara kawo mata kayan ciye-ciye da shaye-shaye bata jima da barin wurin ba su Inno suka fito falo, nan take suka ci gaba da hira.
Mama Hasiya ƙanwar Daddy ce uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, tana auren wani hamshaƙin ɗan kasuwa a unguwar Hotoro. Sun shafe shekara goma sha biyar da auren saurayi da budurwa, sai dai Allah bai basu haihuwa ba duk wannan tsahon shekarun, sun yi yawon ƙasashe amma duk ba a dace ba har sai da suka fara ganin wani likita Dr John, ta taɓa samun ciki ta yi ɓari har sau biyu daga haka ko ɓatan wata bata sake yi ba, don haka ta nace wa Dr John lokaci-lokaci take zuwa ganin likita.
DR JOHN SPECIAL HOSPITAL shi ne sunan asibitin da Mama Hasiya take zuwa ganin likita, asibitin a bayan gidan su Mommyn Raihan yake. Duk ranar da Mama Hasiya za ta zo ganin likita a gidan Daddy take kwana saboda asibitin sai goman dare Dr John yake fara ganin patient, wannan dalilin ya sa idan ta ga likita take dawowa gidan ɗan'uwanta ya kwana, yawaici tare suke zuwa da Mommy saboda mai gidanta yana tafiye-tafiye, kuma yawo babu inda ba su je ba don neman haihuwa.
Cikin Dare.
Wata irin guguwa mai ɗauke da amsa kuwwa marar daɗin sauraro ta fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dodon kunnuwanta, a hankali iskar ta fara kaɗa labulayen ɗakinta. A hankali ta fara ratso bangawayen da gidan tana raɓewa ta jikin ƙananan shukokin da ke harabar gidan, ta jikin bangon ɗakinta ta ratso jikinta ɗauke da jajayen kaya masu ratsin baƙi haɗe da ɗishi-ɗishin busasshen jini a jikinta. Tana shiga ɗakin Raihan ta tsaya cak a bangon gudu, ta fara huro mata iska nan take Raihan ta miƙe zaune hannuwanta toshe a kunnuwanta ta dubi Intisar. Cikin wata irin girgiza ta ƙaraso wurin Raihan ta kama hannuwanta tana shirin yin magana Raihan ta ce, "Intisar me kika zo yi yanzu gidanmu?" Intisar bata bi ta kanta ba ta hura mata iska a fuska nan take ta fara layi tana shirin faɗuwa, da sauri Intisar ta tarota tana dafe kafaɗarta ta ce, "Za ki bi ni?" Babu musu Raihan ta gyaɗa mata kai, Intisar bata bi ta kanta ba ta riƙe hannunta nan take suka ɓace daga ɗakin.
Gudu suke zabgawa cikin sararin samaniya a can wani ƙasurgumin dajin wani makeken gida suka sauka, Raihan ban da ido babu abin da take bin ƙawarta Intisar da shi. A wani katafarn kogon dutse suka dira mai ɗauke da wasu irin mutane masu mummunar hallita, ɗauke suke da jajayan sitiru sai zanen jini a jikkunansu. Wata mummunar hallita ce a tsugunne mai ɗauke da kan barewa da manyan ƙahunhuna ga wani irin jini da yake ɗiga daga bakinta a cikin wani ƙaton faifai. Zuwansu ke da wuya wani tiƙeƙe da ya kasance babbansu ya dubi Intisar ya ce, "Hatsabibiya Bungulu na maraba da baƙuwa mai daraja." Intisar da dubi Raihan ta ce, "Ki yi gaisuwa ga Habibiya Bungulu ta saka miki albarka." Kamar bawa da uban gidansa haka Raihan ta dubi wannan hallitar ta duƙa kamar yadda ta ga suna yi ta miƙa gaisuwa. Da wani ƙaton sirinji wani ɗan tsamurmuri ya zuƙi jinin da wannan hallitar take ɗigarwa daga bakinta, a shammace ya samu damtsen hannun Raihan ya kafa mata har sai da ya juye jinin jikin sirinjin a jikinta, sannan ya zuƙo nata ya fesa a jikin hallitar. Lokaci ɗaya ta fara rawar ɗari kamar mai jin sanyi, tun tana daga tsaye har ta duƙushe a wurin tana karkarwa. Tana jima tana abu ɗaya sannan ta tsagaita da rawar ɗarin, a zabure ta miƙe tsaye cikin wani irin ƙarfi ta zurawa mummunar hallitar tana jiran umarninta.
Buɗe bakinsa ya yi nan take wasu baƙaƙen macizai suka fara fitowa daga bakinsa, suna faɗowa suke fasa kai suna zagaye Raihan. Cikin wani irin yanayi hallitar ta miƙe tsaye tana girgiza sannan ta fara magana da wani irin yare har sai da ta yi yare ya fi kala goma, sannan ta yi magana da harshen hausa.
"Tabbas mun yi babban kamun da muka jima muna jiran wannan rana. Domin ƙara tabbatar da abin da muke zargi goɗiya za ta kawo mana jini mafi muhimmanci wanda zan shayar da mai gidana domin samun lafiyarsa." Tun bai rufe baki ba Raihan ta russuna tana faɗin, "An gama Hatsabibiya Bungulu." Mummunar hallitar ta nunawa Raihan wata ƙatuwar ƙwarya mai cike da tafasasshen jini ta ce, "Babu buƙatar haka domin da alama ke shugaba ce, muna buƙatar jinin wannan matar yanzun nan..." Raihan ta amsa mata tun bata ƙarasa maganar ba da cewar, "Jininta ya halarta a gare ki, duk duniya babu jinin da za ki buƙata ya gagara a wurina." Tana rufe baki Hatsabibuya Bungulu ta miƙa mata wani busasshen ƙashi da alama ƙashin jikin bil'adam ne. Raihan na karɓa ta wuce cikin sararin samaniyar iskar sihiri bata tsaya ko'ina ba sai a katafaran cikin gidan Mahaifinta, sai da ta zaga ɗakunan gidan sannan ta dira a ƙofar ɗakin mahaifiyarta.
🤭🤭🤭 WASAN YANZU YA FARA, MAZA HANZARTA KI BIYA NA KI DON JIN WACECE AINIHIN ZAUJATU JINNUL-ASHIQ ƊIN, SHIN A CIKIN SU WACECE ƳAR GABAN GOSHIN ALJANIN SOYAYYAR? SHIN WACECE WANNAN INTISAR ƊIN KUMA WACECE HATSABIBIYA BUNGULU? 😁 AMSOSHIN NA GABA DON JIN ƘULALLEN ƊAURIN DA KE CIKIN LABARIN.
Share Fisabillah🌚
[7/10, 10:33 AM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*
© *AMEERA ADAM*
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
FREE PAGE 4
Raihan na fita Intisar ta ƙarasa gaban Hatsabibiya Bungulu rai a matuƙar ɓace ta ce, "Hatsabibiya uwar hatsabibai, sai kai mai siffar dabba a bayan fage ki koma bil'adama. Babu hallitar da ta gagare ki rikiɗa duk girmanta duk ƙanƙantarta, yaya ina tunanin lokacin share mini hawayena ya zo amma na ga wankin hula yana shirin kaini dare. Na kawo Raihan domin a salwantar mini da rayuwarta amma da alama tana shirin samun fada a wurin nan, yake Hatsabibiya tun farko kin san ba haka muka yi da ke ba."
Hatsabibiya Bungulu ta yi girgiza lokaci ɗaya ta rikiɗa zuwa wata kyakkyawar budurwar, zaune take tsirara sai wasu sassan gaɓɓoɓin jikinta da ke rufe. Wani malalacin murmushi ta saki sannan ta dubi Intisar ta ce, "Da mun san kina da wannan yarinyar da tuni mun jima da umartarki ki kawo mana ita, sai dai kash! Silar saninta na daga gare domin biyan buƙatarki. Kin kawota domin mu kashe ta sai dai ba za ta mutu ba." Da hannuwa biyu Intisar ta sa ta toshe dodon kunnenta saboda yadda ta ji kalmar a kunnenta, a duniya idan da wacce ta tsana to Raihan ce. Lokaci ɗaya ta murtuke fuska tana shirin yin magana Hatsabibiya ta ci gaba da magana.
"Na tabbata baki san wacece Raihan ba, da kin san amfanin da za ta yi mana a cikin ƙungiya da bakinki bai furta kalmar kisa a tattare da ita ba. Shin ko kinsan Muraza?" Da sauri Intisar ta ɗago da kai tana kallon Hatsabibiya tana girgiza kai bakinta na rawa ta ce, "Ina zan santa ya ke Hatsabibiya mu da muke nemanta ido rufe." Matashiyar budurwar da ake kira da Hatsabibiya ta yi girgiza nan take ta rikiɗe zuwa surar wani ƙaton tsuntsu, sai da ya yi tsalle-tsallensa sannan ya koma kan kujerarsa ya zauna ya ci gaba da magana cikin siffar tsuntsu.
"Tabbas Raihan ita ce Muraza, tun shigowarta kogon dutsen nan alaminta da babban matsafi ya sanar da mu suka bayyana. Ƙofar nasarorinmu ta buɗe ƙarfin iko, tsafi da sihiri da ƙarfin ƙungiyar asirinmu za ta sake dawowa da ƙarfin ikonta, domin haske ya bayyana inuwarta ɗauke take tartsakin wuta mai halakar da magautanmu, za mu riƙe hannu bibbiyu domin saminta tamkar samun lu'ulu ne a ƙarƙashin teku, idan muka yi sake ta kubce mana tabbas mun tafka babbar asara." Intisar ta faɗaɗa murmushinta sai da ta yi taku biyu sannan ta waiwayo ta ce, "Haƙiƙa zan jinkirta buƙatata har tsawon wani lokaci bayan mun cimma matsayarmu, amma tabbas ko ba yanzu ba akwai ranar da Ya za ta ɗakin ƙanwa, lokaci na tafe zan aiwatar da abin da yake ci mini tuwo a ƙwarya. Ni ma lokaci ya dawo mini da zan karɓo sihirtacciyar sandar mahaifiyata Bokanya Shirzan, a lokacin ne duk wani cikar ikona zai dawo." Tana rufe baki suka fara ƙyaƙyata wata irin dariya mara daɗin sauraron mai ɗauke da amsa kuwwar kukan jakuna, suna tsaka da kuka sai ga wani matashin saurayi ya diro cikin ɗakin hannunsa ɗauke wani jariri sabuwar haihuwa. Jaririn sai mutsu-mutsu yake ko jikinsa ba a gyara ba balle a yanke cibiyarsa, a kan tafin hannun wani gunkin tsoho da ke tsaye ya wara hannuwansa. Yana ɗora jaririn a kai nan take wannan Hatsabibiya da ke ɗauke da siffar tsuntsu ta taso ta dira a kan cikin jaririn. Wata ƙara ya ƙwalla saboda wata irin azaba da ke ratsa sassan jikinsa, da ƙafafuwansa tsuntsun ya huda ƙirjin jaririn ya kafa kai yana tsotsar jinin jaririn. Kafin wani lokaci tuni idanun jaririn sun ƙafe jikinsa ya saki numfashinsa ya ɗauke, tana ganin haka ta tashi daga kanta sai Intisar ta ƙarasa ta banƙare ƙirjinsa ta ciro zuciyarsa ta wurga bakinta ta cinye.
Ɗaukan gawar jaririn ta yi ta miƙawa sauran mutanen wurin, da sauri suka caɓe shi suka buɗe wani ƙaramin ɗaki mai ja da baƙin labule suka wurga ciki.
Raihan na zuwa gida a hankali ta fara zaga bangon da ke cikin ɗakunansu, ga mamakinta tana bi ta cikin ɗakinta ta hangi mai siffarta kwance a kan makwancinta a gefe ɗaya ga Mama Uwani tana zaune tana gadinta. Amma ga mamakinta sai gani ta yi ta gifta ta gabanta ba tare da ta lura da ita ba. Hasalima ratsawa take yi ta ko'ina ba tare da gini ko ƙofa sun yi mata shamaki ba, a hankali ta ci gaba da tafiya kamar mai tafiya a sararin samaniya har ta dira a ɗakin Mahaifiyarta sai da ta ƙare mata kallo sannan ta wuce ɗakin da Mama Hasiya take kwance tana bacci. Kamar yadda Hatsabibiya ta umarceta haka ta tsaya a saitin kanta, ƙashin hannunta ta kai saitin fuskar Mama Hasiya lokaci ɗaya ta buɗe idonta firgigit ta sauke su a kan Raihan, sai dai a cikin idanunta gani ta yi Raihan ta siffanta da wata mummunar hallita, cikin rashin tausayi Raihan ta ƙarasa gabanta ta damƙo maƙogaronta, nan take Mama Hasiya ta fara kakari idanunta suka firfito waje.
Da murya mai wahalarwa Mama Hasiya ta fara karanta kalmar shahada, tana yi tana ambaton sunan Maigidanta da duk sunan wanda ya zo bakinta.
Ana cikin haka wasu tafka-tafkan kunamu suka fara ratsowa ta jikin bango girman kowacce ɗaya ya fi girman kan jariri, da gudu suka fara rarrafowa suka haye gadon sun kai kusan goma suka maƙale a jikin Mama Hatsiya kowacce ta kafa bakinta suka fara zuƙar jini.
Cikin tsananin azaba Mama Hasiya ta fara wani irin ƙaraji da gurnani, tun tana cikin hayyacinta har ta fara fita daga haka idanunta suka kafe rai ya yi halinsa. Raihan na ganin haka ta saki wuyan gawar Mama Hasiya ta faɗa kan gado yaraf ta ja mayafi ta rufeta sannan ta miƙawa kunamin nan hannu lokaci ɗaya suka maƙaleta, ta ɗago da su saitin fuskarta. Haƙoranta ne suka fara girma ga wata fiƙa irin ta karnuka da ta fito mata, bakinta ya fara zubda wani baƙin jini mai yauƙi. Ƙwayar idanunta zazzago suna wani irin juyi, a hankali ta fara takawa ta fice daga ɗakin ta koma ta sashen ɗakin Mahaifiyarta, ta jima a bakin window sai da ta yi ƙwafa sannan ta ratsa ta jikin bango ta fice daga gidan.
Bayan sun wurga Jaririn cikin wannan ɗakin wata irin tsawa aka yi mai haɗe da walƙiya, a hankali hatsabibiya ta shiga ɗakin tuni wata mummunar hallita mai ɗauke da kawuna har guda goma a jikinta, a kowanne baki akwai aikin da yake aiwatarwa. A ɗaya daga cikin kan mummunar hallitar ta cafke jaririn tana laƙumewa, wani kan kuma ya fara amayo da kuɗaɗe kala-kala har da na ƙasashen waje, ya yin da wani kan ya fara tatsar da wani ruwa mai yauƙi yana zuba watsu ƙananan ƙwari suna zuwa suna tsotsa.
Suna nan tsaya Raihan ta diro cikin gidan, hannuwanta biyu saƙale da kunamu tana tafe cikin takun ƙasaita dauke mummunar hallita. Tana zuwa Hatsabibiya ta fito fuskarta ɗauke da murmushi, shigar Raihan wurin ya sa jikin wannan dattijon ya fara ɓamɓarowa daskararran jikinsa ya fara rozayewa a hankali har ya rozaye gabaɗaya. Wata irin girgiza ya yi nan take ya fara kallon mutanen wurin ɗaya bayan ɗaya, Hatsabibiya ta tako a hankali fuskarta ɗauke da annuri ta ce, "Barka da dawowa cikin rayuwarka ta ainihini Ya masoyina." Hannuwanta ya riƙo yana bin ta da kallo lokaci ɗaya ya rungume ta yana shafa bayanta sannan ya ce, "Ina godiya da sadaukarwarki, amma ya aka yi kika samu tsarkakken jini alhalin an ce sai ta silar Muraza shin kun samota ne?" Hannunsa ta ja bakin wata tsohuwar rijiya da ke cikin ɗakin tana faɗin, "Mu je turaka zan baka labari." Tana rufe baki suka faɗa cikin rijiyar shigewarsu keda wuya wurin ya shafe tamkar ba a taɓa hallitar wani abu a wurin ba.
Wani tutturnan mutum da suke kira da Mataimaki shi ya ƙarasa wurin Raihan ya karɓi kunamin hannunta, ya zuba su a cikin wani ƙoƙon kai sannan ya dubi Raihan ya ce, "An gaishe ki Jaruma, Shugaba mai cikakken iko sai ke gagabadau. Za ki iya tafiya sai ranar taro na gaba amma a ranar muna buƙatar tukwicin sabuwar gawar mace mai ƙarancin shekaru kar su yi ƙasa da talati kar kuma ta haura shekara arba'in." Raihan ban da jinjina kai babu abin da take yi, tana gama sauraronsa ta dubi Intisar alamar su tafi. Intisar ta nuna mata wata ƙoriyar ƙwarya mai cike da wani ruwa mai ɗauke da launin jini kamar anwanke nama, sannan ta ce: "Ki kuskure bakinki da ruwan tsarki domin samun albarka." Ba musu Raihan ta ƙarasa ta ɗauki ƙwaryar ta kafa kanta, tana kafa kai ta ji kanta ya sake yin nauyi dumm! A hankali ta iya kai ƙwaryar bakinta ta kuskure wata irin kasala ta mamaye jikinta, ga wani irin addababban bacci da ya lulluɓe idanunta. Tana ajiye ƙwaryar ta tafi luuuu za ta faɗi da sauri Intisar ta taro ta jikinta, sannan ta saɓa ta a kafaɗa ta fice daga cikin kogon dutsen kai tsaye ta wuce gidan su Raihan.
Intisar bata tsaya a ko'ina ba sai a tsakiyar ɗakin Raihan, tana kallon Mama Uwani ta saki wani malalacin murmushi. Kwantar da Raihan ta yi sannan ta fara zagaye ɗakin ba tare da idanun Mama Uwani sun gane mata Intisar ba, lokaci ɗaya ta saki wata mahaukaciyar dariya. Tun tana dariya a tsaye har ta durƙushe a wurin sannan ta ratse ta ƙarƙashin ƙasa ta fice daga ɗakin.
WASHEGARI
Da Asuba bayan su Inno sun gabatar da sallah suna zaune kowacce a sallayarta suna jan carbi, Goggo ta dubi Inno ta ce: "Wai ni kuwa yarinyar ta tashi sallah kuwa don ko motsinta ban ji ba, saboda Allah neman haihuwa ya fi bautar Ubaniji. Jiya na ga saboda neman haihuwa raba dare suka yi a wurin wancen Kafiriin, gaskiya a tambayi Malamai an ya; ya hallata neman haihuwa wurin kafiri." Inno takaici ya fara rufeta, ta dubi Goggo ta ce, "Zinaru ki yi ta kanki idan kika kafirta min yarinya a yau ba sai gobe wallahi sai Audullahi ya mayar da ke Albasu. Kafira ce da har yanzu za ta zauna babu sallah babu salati?" Goggo cikin nuna rashin damuwa ta wara hannuwa tana faɗin, "Allah shi ne masanin daidai, ba zan amsa ba ki sa na yi wa ƴar mutane ƙazafi akan abin da ban ji ba ban gani ba, ni dai na san da Hasiya ta tashi za ta leƙo wurinmu. Bari ki ga na je na tashe ta ko na samu lada mai tsoka, bar zancen Albasu tun da ko jini baki taɓa zubarwa a cen balle a binne mabiyyarki." Goggo na ƙarasa maganar ta fice daga ɗakin, tana tafe tana mita har ta ƙarasa bakin ƙofa tana ƙoƙarin buɗe ƙofar sai ga Inno ta rufo mata baya ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Saboda Allah Zinaru in haifi abartawa a ciki amma ki nemi ki yi mana farraƙu da ita, Allah ya sani idan Hasiya ta ga ban tashe ba na ɓalɓalce don ɗauka za ta yi baƙin cikin shiga aljanna nake yi mata." Goggo bata bi ta kan Inno ba ta tura ƙofar tana rangaɗa sallama, kamar haɗin baki suka shiga ambatar sunan Hasiya amma shiru suka ji kamar an shuka dusa. Inno ce ta yaye zanin rufar jikinta nan take suka yi tozali da gawarta, kusan suman tsaye suka yi aka rasa mai furta koda kalma ɗaya ne. Nan take Inno ta yanke jiki ta faɗi, Goggo jiki na tsuma ta juye hanyar waje tana ƙwalawa Mommy kira. Can sashenta ta wuce saboda fargaba tini ta zubar da carbi don lokaci ɗaya ya tsinke ya tarwatse, da kusan rarrafe Goggo ta hau sama tun bata ƙarasa ba suka ci karo da Mommy shi kansa Daddy kiran Goggo ne ya sa shi fitowa daga ɗakinsa a lokacin yana zaune yana cike-ciken takardu.Hankali a tashe suka shiga jera mata tambayoyi ban da nuna musu ƙofa babu abin da take yi, sai da ƙyar suka samu ta iya furta, "Hasiya babu ta riga mu gidan gaskiya." Cikin rashin fahimta suka ce, "Wace Hasiya?" Saboda ko a kaɗan basu kawo Hasiya a ransu ba. Goggo cike da jin haushi ta ce, "Hasiya dai ƙanwarka Audullahi ko kana da wata Hasiyan ne." Kusan tare suka nufi hanyar sauka don zuwa su ganowa idanunsu.
Kamar masu rige-rige haka suka shiga ɗakin da Hasiya ke yashe a kan gado, Daddy ne ya fara zuwa kan Inno Mommy ta ƙarasa wurin gawar Hasiya ta fara tattaɓata tana ambatar sunanta amma shiru tafiya ta miƙa. Da hanzari Mommy ta wuce firji ta ɗebo ruwa ta fara yayyafawa Inno sannan ta yayyafawa Hasiya, nan take Inno ta fara motsawa saidai da alama bata cikin hayyacinta amma Hasiya ko alamar motsi bata yi. Daddy ne ya rungumo Inno ya fita a guje yana ƙalawa maigadi waya, kusan gware suka yi a hanya Daddy ya nufi wurin motoci yana faɗin, "Maza-maza buɗe min gate." Tun bai rufe baki ba Driver ya fara kiciniyar buɗe ƙofa nan take bawa motarsa wuta ya fice daga gidan, Mommy jiki a sanyaye ta bi bayan motar da kallo fuska ɗauke da hawaye. Ɗakin ta koma ta janyo hannun Goggo ta rufe ɗakin, kan kujera ta zauna ta rafka tagumi ban da hawaye babu abin da take yi, saboda ba ƙaramin shaƙuwa suka yi da Hasiya ba. Goggo ban da sintiri babu abin da take yi tana nan tsaye suka ga Mama Uwani ta fita, cikin rashin sani ta fara tambaya, Goggo da sai a lokacin kuka ya kubce mata cikin shassheka ta ce, "Bari Uwani yau mun wayi gari da tashin hankali Hasiya babu, yarinyar nan jiya-jiya muka gama hira da ita amma yau sai labari." A tsorace Mama Uwani ta nufi ɗakin don ganewa idonta, tana shiga ta samu gawar a kan gado cikin hanzari ta buɗe ta tana ƙarewa gawar kallo.
Ido ta zurawa gawar tana jinjina kai a hankali ya furta, "Tabbas akwai lauje ciki naɗi amma akwai ɓoyayyan al'amari a dangane da gawar nan." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin zuwa falo, ba a ɗauki lokaci ba sai ga Daddy ya dawo. Dawowarsa babu wuya mommy ta tashi Raihan ta sanar da ita halin da ake ciki, murtsuke ido ta yi tana yamutsa fuska ta ce, "Mommy waye ya mutu?" Mommy ta sake maimaita mata, "Mamanki Hasiya yanzu haka gawarta na ɗaki mutane sun fara taruwa." Lokaci ɗaya ta ji kanta ya yi mata nauyi dum! Har sai da ta runtse idonta ta buɗe ta dafa kanta da hannu biyu ta ce, "Mommy me ya sameta ta mutu?" Da sauri Mommy ta rufe mata baki tana faɗin, "Raihan wa yace miki sai an yi ciwo ake yin mutuwa?" Jikin Raihan ba ƙaramin mutuwa ya yi ba, a hanakali ta tashi tana haɗa hanya jikinta sanye da rigar bacci shara-shara babu abin da ta ɓoye na surarta. Ɗakin da Mama Hasiya take ta tunkara Mama Uwani na hangota da sauri ta nufi wurinta ta rungomata tsam a jikinta tana faɗin, "Uwar ɗakina sai haƙuri." Wani iri Raihan ta ji a jikinta yarr a lokaci ɗaya kanta ya yi mata yaaaam! Tsigar jikinta ce ta ci gaba da tashi, a hankali ta saki hannunta tana bin Raihan da wani mayatattacen kallo.
Kafin wani lokaci tuni gidan ya cika da mutane ban da koke-koke babu abin da ake yi, Raihan can gefe ta raɓe ta fashe da wani irin matsanancin kuka. Mai gidanta da aka gaya masa da farko ƙaryatawa ya yi sai da ya zo ya ganta, zama ya yi kamar mace ya yi ta kuka sai da ƙyar ya yi shiru. Kimanin ƙarfe goma aka gama wanke gawarta aka shiryata, ana gabda za a fita da ita sai ga Intisar ta turo ƙofa ta shiga gidan tana kallon mutanen gidan ɗaiɗai tana shigowa ana ɗaukan gawar, tana kalle-kalle Mama Uwani ta fisgi hannun Intisar ta ja ta ɗakin baya wanda baƙi suke sauka a ciki. Rai a matuƙar ɓace ta dubi Intisar ta ce, "Me ya kawo ki gidan nan?" Intisar dariya ta yi ta fara takawa a hankali sai da ta yi taku uku sannan ta juya ta kalli Mama Uwani ta ce, "Abin da ka ke yi cikin suffar tsofaffi shi ne ya kawo ni a wannan suffar."
[7/1, 6:00 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV
FREE PAGE 1
Babban gida ne mai ɗauke da ɓangare daban-daban har kusan sashen mutum goma sha biyu. A taƙaice za mu iya cewa gidan gandu ne da ya haɗa Kakanni, 'ya'yaye da jikoki. Garin Ɗangwauro yana ɗaya daga cikin ƙanana ƙauyukan da ke cikin ƙwaryar Kano, Allah ya azurta su da noma, kiwo da kasuwansu. Gidan Malam Muhammadu mai dogon Carbi sanannan gida ne a kaf cikin garin Ɗangwauro. Tun daga titi idan ka tambaya za a kai ka har cikin gidan, sakamakon gida ne gidan yawa don wani lokaci mutane na yi masa laƙabi da gidan 'Ya'ya da yawa.
Gidan Mai dogon Carbi cike yake da mutane sakamakom wayar gari da suka yi da rasuwar rashin wannan Dattijo mai yawan shekaru, ba iya gidan ba hatta garin Ɗangwauro ya girgiza da rashin wannan Dattijon mai dogon zamani. Yaya Babba da Inna Furai sune matan wannan Dattijo da ya rasu mutuwar ba ƙarmin taɓa su ta yi ba.
Bisa ga al'adar Malam bahaushe a ranar da aka yi mutuwa mutane sun fi nuna damuwarsu ta hanyar koke-koke, kukan ma yana taƙaita yawancin bayan ankai mammaci. Hakan ce ta faru a gidan Mai dogon carbi domin an fita da gawarsa a yi mata sallah yara da Manya sai kuka suke yi.
A gefe ɗaya Hali dubu na hango rakuɓe sai muzurai take lokaci-lokaci tana share hawaye, sai dai cikin zuciyarta haushin mutanen gidan take ji saboda ta lura babu wanda yake bi ta kanta don ya rarrasheta, duk kuwa da irin gursheƙen kukan da take yi. Kallonsu ta fara yi tana ayyana irin abin da za ta yi domin ta janyo hankulansu kanta. Tun da ai ita gani take kamar ta fi su jin mutuwar koda suna yawan faɗa da Mai dogon carbi amma kafin ya rasu, ai ita ma Kakanta ne.
Sumi sumi sumi ta tashi da yaƙunannan hijabinta ta bi hanyar soron gidan tana waiwaye, sai da ta je soron ƙarshe daga shi sai fita Hali dubu ta ɗora hannuwa biyu akanta ta dawo cikin gidan da gudu tana cewa, "Wayyo Allah! Wayyo ni na shiga uku na lalace." Lokaci ɗaya hankulan mutanen gidan ya dawo kanta, da sauri aka yi carko-carko a kanta masu jero tambaya na yi. Zuciyarta ƙal don ko ba komai ita ma za a rarrasheta kamar yanda aka saka su Yaya Babba ana basu haƙuri. A fakaice take satar kallonsu tana sake sharce hawaye amma ta yi biris babu wanda ta tankawa duk irin tambayoyin da mutane suke yi mata. Baba Munkaila ne ya shigo ya hango cincirindon mutane a tsaitsaye da sauri ya ƙarasa wurin, ganin Hali dubu a zaune ya sa ya ja guntun tsaki sannan ya buga mata tsawa, "Ke lafiya kike yi wa mutane ihu?" Kamar sabuwar Marainiya haka ta ɗago shanyayyin idanuwanta ta kalle shi sai kuma ta waiga ta saci kallon ƙofa ta kuma duƙunƙune kanta cikin alamun tsoro da firgici. Kamar haɗin baki dukansu suka kalli bakin ƙofar suna neman ƙarin bayani, babu abin da ta furta musu sai ma kuka da take yi tana nuna musu ƙofar da ɗan yatsanta. Baba Munkaila tsawa ya sake buga mata ya ce, "Me ye a cen ɗin?" Hali dubu ta kuma kallon ƙofar ta rushe da kuka tana cewa, "Baffa ne!" Cikin haɗin baki duka suka ce, "Baffa kuma? Wane Baffan?"
Bata bi ta kansu ba sai kawai ta baje a wurin ta fara wata irin birgima tana cewa, "Wayyo Baffa ne ya tafi ya barni!" Takaici ne ya rufe Baba Munkaila domin ya san za a rina don ya tabbata ganin Dubulliya tana wannan kukan ba banza ba. Cikin faɗa-faɗa ya fara yi mata magana amma ko gezau ba ta motsa ba. Can gefe ya hango wata igiyar dabbobi ai kuwa bai yi wata-wata ba ya fara tafka mata, tana jin shigar bulala ta tashi ta yi cikin gida ta gudu.
Can ɗakin Yaya Babba ta shiga ta haye ƙarshen gado tana kuka, ga haushin Baba Munkaila ya tsinkata a cikin mutane. Tambayar duniya Yaya Babba ta yi amma Dubuliyya kanzil! Bata ce da ita ba. Sai ma ta yi zamanta a nan domin duk duniya babu abin da tafi tsana kamar taron jama'a a gidansu. Domin ba ƙaramin takura take yi ba, dalilinta na haka kuwa ta yanda za ta ji mutane na bata ji ko kuma ta cika rashin ji kamar ƴar aljanu. Tana daga kwance dabara ta faɗo mata ta yanda za ta kore jama'ar gidan ta ruwan sanyi domin ta san yanda danginsu suke sai a kusa arba'in da mutuwar da sauran baƙi tsiraru. Saboda haka Baffa mai dogon Carbi ya saba musu tun yana raye, idan suka zo taro baya barin ƴan uwansa su koma a kwana kusa. Wannan dabara tata ba ƙaramin daɗinta ta ji ba don har sai da ta murmusa saboda farin ciki. Kamar wacce aka tsirawa allura haka ta zabura da sauri ta fice daga ɗakin Yaya Babba, ita kanta Yaya Babba ba ƙaramin daɗi ta ji ba kasancewar duk duniya babu Jikarta da take so kamar ita sakamakon Marainiya ce gaba da baya.
Dubu tana fita ta yi garau da ita kamar ba ita ta sharɓi kuka ba, nan fa mutane suka fara yi mata tsiya, har da masu cewa dama ita zuma ce sai da wuta. Wasu kuma su ce gara da ya yi mata haka ga shi ta ware ta fara harkokinta. Shiru ta yi babu wacce ta tankawa sai dai duk wacce ta yi magana tana auna maganar tata a mizani domin ta san irin hukuncin da za ta yi mata.
Tun da Magriba ta doso Dubulliya ta fara haɗa kayan aikinta a fakaice cikin hikima da basira, ba tare da wani ya fahimci halin da take ciki ba. Sakamakon babban gida ne kowa da wurin da yake nema ya kwanta saboda ko ina a wadace yake hakan ne ya sa Yaya Babba bata damu ba da Hali dubu ta ce za ta sashen Baba Munkaila ta kwana a cen.
DA DADDARE
Da daddare gidan ya yi tsit ban da kukan tsintsaye da ƙananan dabbobi babu abin da yake tashi, sai munsharin bacci da yake tashi daga ɗakunan daban-daban. Dubuliyya tana daga sashen Baba Rufa'i cikin ɗaya daga cikin ɗakunan ƴaƴan gidan. Sai da ta ci baccinta ta more sannan ta farka cikin talatainin dare ta ji gidan tsit kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki ta zaro kayan marigayi Baffa ta saka rigarsa da babbar riga har da hula ta naɗa rawaninsa ta ɗauki zabgegen carbinsa ta maƙala ta fito, hasken farin wata ne ya haska mata hanyar da za ta rinƙa bi har fice daga sashen gabaɗaya. Can wurin da ya zamewa Marigayi Baffa mai carbi wurin alwala can ta je ta tsugunna, daga nesa idan ka hango Dubu a tsugunne sai ka rantse da Allah Baffa ne, sai da ta waiga hagu da dama sannan ta taƙarƙare ta fara zabgo kaki irin yanda Baffa yake yi, Baba Sule da ke kwance cikin baccinsa ya fara jin alamar kaki tamkar yanda mahaifinsu yake yi duk asuba. Fakare ya yi yana zare idanu, yana cikin wannan yanayin ya sake jin an yi kaki har da irin tarin tsofaffin nan da Baffa yake yi. Janyo wayarsa ya yi yana dubawa ya ga ƙarfe biyun dare, nan take ya hau murza idanu yana sake kasa kunne. Dubu kamar ta san ana sauraronta ta kausashe murya sai ka rantse da Allah Baffa ne yake magana ta fara cewa, "Tabbas rayuwar barzahu daɗi gare ta." Baba Sule ya waro idanu wace cikinsa na karta masa, don ya tabbata hatta dabbobin gidan da suna magana za su ce sun shaida maganar Baffa ce cikin daren nan.
Dubu na tsugunne ta ji alamun tahowa wata zuciyar ta ce mata ta tashi ta ɓuya, wata kuma ta ce ta zauna ta ci gaba da abin da take yi. Tarin Inna Furai ta ji ta saci kallonta ta hangota da ƴar buta a riƙe za ta je banɗaki. Dubu wani kakin ta sake yi tana daga tsugunne, hasken farin wata ne ya hasko mata mutum durƙushe da fararen kaya da rawani tamkar marigayin mijinsu. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa ta fara motsa baki cikin addu'a don a zatonta mugun gamo ta yi.
Ɗauke kai ta yi don ma kar ta ci gaba da kallon wurin da Dubu take ta ci gaba da tsoratata, sai da ta kusa da wurin da Dubu take ta ji muryar marigayin mijinsu raɗau a kunnenta yana cewa, "Wato ita dai rayuwar barzahu daɗi gare ta. Babban daɗin idan ka kawo ziyara tsohuwar rayuwarka sai kuma ka tafi da matarka." Inna Furai na jin haka ta dafe ƙirji tana ja da baya jikinta har tsuma yake ta ce, "Yau na haɗu da zazzagar rayuwa ni Furaira. Allah na roƙeka karka jarrabe ni ta wannan fannin." Dubu na jin haka ta miƙe tsaye tana gyara zaman babbar rigar jikinta ta sake kausashe murya ta ce, "Wuni ɗaya har na yi abokai miliyan ɗaya da ɗari biyar a cikin Fatalen har da masu tashi sama. Ƴan sama jannati ku zo ga wani naman mun samu, kuma daga yau mun fara ɗauka kenan a gidan nan. Duk wanda ya wayi gari ya ga likkafani a jikin kayansa shi za mu yi wa ɗaukan amarya." Inna Furai tuni fitsarin da take riƙewa ya samu sukunin tsiyayowa, sakin butar hannunta ta yi jikinta na tsuma donma bongon da ke bayanta ya tokareta.
Dariya ce ta so ƙwacewa Dubu amma ta maze ta ce, "Ƴan uwana ƴan sama Jannati! Ku zo na fara samo muku ƴar uwa." Inna Furai ta saki salati tana cewa, "Yau na haɗu da zazzagar rayuwa shi kenan tawa ta zo ƙarshe." Dubu sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta fara takowa gaban Inna Fuarai ta ce, "Idan kina son fansar kanki sai kin sake shayar da ƴaƴanki tamkar yanda kika shayar da su suna jarirai, tun daga kan Larai (Ita ce babbar Ƴar Inna Furai) har zuwa kan Sabi'u (Shi ne autanta) idan kika kuskurewa haka tabbaci haƙiƙa sai mun zo ido biyu mun tafi da ke babu wanda ya isa ya hana."
Baba Sule tuni cikinsa ya ɗuri ruwa yana son fita domin ceton Matar Mahaifinsa tsoro ya cika masa ciki, bai gama tsinkewa da lamarin ba da ya ji an fara kiran yan sama jannati. Dubu don ta ƙara razana Inna Furai ta sake dakushe murya ta ce, "Ki isarwa da mutanen gidan nan saƙona muddin suka ci gaba da kwanaki sai na yi musu ɗauki ɗaiɗai. Shi kuma na ɗaki da yake laɓe yana sauraronmu, shi kuma ɗauke shi za mu yi gabaɗaya." Dubu na cikin magana sai gani ta yi Inna Furai ta zube ƙasa. Gabanta ne ya faɗi ta ji fargabar kar tsohuwar mutane ta mutu a hannunta. Da sauri dubu ta waiga sai kuma ta kurma ihu tana maƙe murya ta zunduma ihu, sannan ta zuba a guje ta yi cikin gida. Ta nufi ma'ajiyar kayan Baffa ta lallaɓa ta shige ta kwanta.
Ihun da Dubu ta yi ba ƙaramin razana Baba Sule ya yi ba da jim kalaman da da aka ce za a ɗauke shi matuƙar ya saki hannun matarsa. Yana daga gefen gado da sauri ya matsa ya kama hannuwan matarsa ya riƙe ƙam, don kar a neme shi a rasa. Cikin bacci Sahura ta fara masifa da yake Allah ya yi ta masifaffiyar macece. Tana jin ya riƙo mata hannu ta ce, "Don Allah sakarni Uban ƴan naniƙa." Da yake bacci ya hau kanta bata kuma tanka masa komai ba.
Daga ɗaki mai kallon gabas Baba Auwalu ne ya ɗaga labule yana haskowa da fitila zaraf matarsa Yahanasu ta miƙe tana tambayarsa da yake su sabbabun amare ne. Daga can nesa suka hango Inna a yashe tana ko numfashi bata yi. Gabansa ne ya faɗi yace, "Wa nake gani kamar Inna a ƙasa." Sahura ta dafa kafaɗarsa ta ce, "Auwaluna ni ban yarda ita bace kawai magauta ne suka yi maka ture."
Duk duniya babu abin da Auwalu ya tsana sama da a ɓata ran Yahanasu amma tabbas wannan karon ba zai iya haƙura ya bar Mahaifiyarsa a wannan yanayin ba. Kasancewar dare ne amma bai hana sakar mata murmushi ba ya ce, "Allah shi zai kare ni amma bana tunanin wani zai yi mini ture cikin dare." Kafin ta yi magana tuni Auwalu ya yi gaba, ganin haka ya sa ta ja tinga ta tsaya don har ga Allah a tsorace take musamman da ya kasance ranar ne aka yi rasuwa.
Hankali a tashe ya fara yayyafawa Inna ruwa ganin ta fara motsi ya sa ya kamata yana bubbuga ƙofar Baba Sule, Baba Sule na ji ya yi fakare kamar mai bacci don gabaɗaya ya gama rikicewa. Sama-sama Sahura ta fara jin bugun ƙofa firgigit ta miƙe sai ji ta yi Sule ya riƙe hannunta gam, tana shirin yin magana Baba Sule ya janyota cikin raɗa ya fara cewa, "Kada ki yi magana za su yi sama da ke" Waigawa Sahura ta yi tana kallon ƙofa don ita a tunaninta masu buga ƙofar ne za su yi sama da ita. Suka ƙarajin bugun ƙofa Auwalu yana cewa, "Yaya Sule fito ka taimaka mini jikin Inna ya yi tsanani ina jin makewayi za ta ta faɗi." Sahura ta ja guntun tsaki ta ce,
"To! Sai ka tashi tun da ta ka ji muryar Auwalu." Baba sule ya sake ƙasa da murya yanda daga shi sai Sahura ne za su ji abin da yake faɗa ya ce, "Ki koma ki kwanta kawai ina ji a jikina waɗannan ƴan sama jannati ne suka rikiɗa. Takaici ya kama Sahura yanda ta ga Maigidanta yana rawar ɗari ga shi ba lokacin zafi ba, ta miƙe tana fusgar hannu ta ce, "Sakarni ko ƴan ƙasa jannati ne babu abin da zai hanani fita."Tana jan hannu Baba sule yana ja don a tunaninsa muddin ta saki hannunsa shi kenan za su yi sama da shi.
Sororo Sahura ta yi tana kallon ikon Allah, don ita a iya saninta da Sule ba su taɓa irin wannan wasan da shi, don haka ta sake ɓata fusaka ta ce, "Sule wai wani abu ne yake damunka ko gamo ka yi cikin dare n sani ba?" Baba Sule ya yi wura-wura yana kallon hagu da dama ya sake ƙanƙance murya ya ce, "Sahura a kowanne lokaci za a iya yin sama da ni." Wani takaicin ne ya sake rufe ta, ta miƙe tana ƙoƙarin fisge hanunta amma abin ya ci tura don ƙarfin mace dana namiji ba ɗaya.
Auwalu da ke jin ƙusur-ƙusur a ɗaki sai ya sungumi Inna don a ganinsa bai kamata ya sake buga ƙofar ɗakin ma'aurata cikin dare ba. Can sashen su Inna Furai ya nufa Yahanasu ta ƙwalla masa kira tana cewa, "Auwaluna ina za ka ni dai tsoro nake ji." Auwalu ya waigo ya ce, "Shiga ɗaki Inna zan kai na dawo."
Dubu na daga ɗaki tana jin duk abin da yake faruwa, tana jin Baba Auwalu ya tafi ta yi zaraf ta fito cikin sanɗa sai da ta zo daga bakin ƙofar Yahanasu ta yi gyaran murya ta sake kausashe murya irin ta Marigayi mai carbi ta ce, "Wato ita rayuwar barzahu daɗi gare ta ni Mamman. Yanzu tun da na zagayo rayuwata ta baya dole na ɗauki mai ɗakin nan." Cikin Yahanasu ne ya kaɗa nan take jikinta ya hau karkarawa kamar mazari. Dubu ta yi irin tarin tsofaffin ta sake cewa, "Amma ita Yahanasu za mu ɗaga mata ƙafa sai dole ta bi sharaɗinmu ko ba haka ba ƴan sama jannati?" Dubu ta sake sauya murya ta ce, "Ai dole ma ta bi umarninmu ko yanzu mu faɗa ɗakin." Yahanasu bata san lokacin da ta yi farat ta ce, "Wallahi ku faɗa ko meye zan bi."
Dubu ta maƙale murya ta ce, "Dole ki zama makauniyar ƙarfi da ya ji muddin kika buɗe idonki sai dai ki wayi gari a ƙiyama." Tun Dubu bata rufe baki ba Yahanasu ta runtse ido biyu ta ce, "Wallahi na rufe har abada ba zan sake buɗe su ba amma don Allah karku cutar da ni."
Dubu har da ƴar tsawarta ta ce, "Kin tabbata kin rufe ko na aiko da Ƴan sama jannati su shigo?" Yahanasu ta sake runtse idonta tana cewa, "Na rufe wallahi na rufe." Dubu ta saki murmushin mugunta a ƙasan zuciyarta tana cewa, "Yau zan ga ƙaryar soyayya kullin a ishe mu da Auwaluna." A fili Dubu ta ce mata, "Maza tashi tsaye ki rungume bango." Da sauri Yahanasu ta fara lalaube-lalube har ta taɓo bango.
A hankali Dubu ta zura kai ta leƙa ta hango Yahanasu na rungumar bango, zuruf ta faɗa ɗakin cikin sanɗa. Sai da ta je daidai wurin Yahanasu sannan ta ɗaga zabgegen Carbin Marigayi ta zabgawa Yahanasu a ƙeya, sai ta fara wani gunji tana cewa, "Gargaɗin yan sama jannati kenan." Tana faɗar haka har ta fice daga cikin ɗakin.
Yahanasu tun da ta gantsare take hawaye a tsaye sai dai ta kasa buɗe idonta saboda tsoron abin da kaje ya zo.
Duk abin da yake faruwa a kunnen Sahura da Baba Sule, cikin Baba sule ne ya sake ɗurar ruwa. Sahura ita kanta jikinta ya fara sanyi musamman da ta jiyo Ihun Yahanasu, shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta duk masifar da take yi ta daina. Domin da alama zancen Sule ya tabbata.
Lokacin da Auwalu ya ƙarasa ɗakin Inna Furai, har lokacin bata dawo hayyacinta ba. Yana shiga ya kwantar da ita akan ƙaramin gado, sannan ya fara tashin ƙanwar Mahaifinsu Lantan da ta zo daga garin Zariya. Ganin halin da Inna Furai take ciki ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen ɗakin ya yi ba. Auwalu ya juya zai fita Inna Furai ta riƙo hannunsa ta ce, "Auwalu! Yau na haɗu da zazzagar rayuwa. Don haka ka haɗo mini kawunan ƴan uwanka mazan su da matan su a yanzun nan. Idan ba haka ba wallahi sai na zazzagar da albarkasu kowa ya lalace."
Auwalu da sauran mutanen ɗakin sun yi tsammanin zafin ciwo ne ya sa Inna Furai take sumbatu. Lantan ta ƙara matsawa kusa da Inna Furai ta ce, "Furaira sanu kin ji Allah sa dai ba akan makarai kika faɗi ba." Wannan magana ba ƙaramin fusata Inna Furai ta yi ba, a zafafe ta ɗago ta ce, "A kan bulikiya na faɗi! Lantan bana son zazzagar wulaƙanci. Kai Auwalu ka tara mini ƴan uwanka a daren wallahi tun ban zazzage albarkar da ke kanka ba." Kamar sabon munafiki haka Auwalu ya fice sum sum sum daga ɗakin. Haka ya rinƙa bi ɗaya bayan ɗaya yana taso su. Wannan tashin da Auwalu yake yi wa ƴan uwansa ne ya sa kusan rabin mutanen gidan suka tashi daɗin daɗawa idan kowa ya ji ance Inna Furai ta faɗi a hanyar banɗaki sai ya wartsake masu tafiya ɗakinta na yi masu jaje suma suna yi.
Kafin wani lokaci tuni ɗakin Inna Furai ya cika da ƴaƴanta su rai takwas maza biyar mata uku. Sai da ta kalle su ɗaya bayan ɗaya sai kawai suka ga ta ɗaga riga ta ce, "Larai bisimillah" Larai zuciyar ta ɗaya ta ɗauka Inna Furai so take a ƙarasa cire mata riga, nan take ta fara cikiniyar tuɓe mata riga. Cikin ƙaraji Inna Furai ta fisge tana cewa, "Larai yanzu bijirewa umarnina za ki yi? Ni za ki zazzagewa albarka a ka" Sai ji suka yi Inna Furai ta fashe da matsanancin kuka. Lokaci ɗaya suka kalli juna domin ba su ga abin da zai sa Inna Furai kuka ba. Auwalu ya sunkuyo ya ce, "Inna ki yi hakuri me kike so?"
Inna Furai ta ɗago mamanta ɗaya ta ce, "Mahaifinku ya zazzage mini albarka ɗazu nan domin daga zuwansa lahira har ya haɗa kai da ƴan sama jannati. Ba zan zazzage maka bayani gabaɗaya ba amma Auwalu ungo sha ka ji."
[7/1, 6:02 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV
FREE PAGE 2
Auwalu sam bai fahimci inda maganar Inna Furai ta dosa ba, don tun da ya ji ta ambaci Mahaifinsu ya tabbatar da zafin ciwo ne yake damunta da kiɗimewar rashin da aka yi musu. Saboda gudun faɗanta ya sa ya wayance da cewa, "Inna ban fahimci abin da kike faɗa ba. Amma kuma duk wanda ya mutu kin san sai dai mu bishi da addu'a ita ce mafita." Inna ta yi ƙuri tana kallonsa sai zuwan can kawai ta fashe da kuka. Lantan da ke gefe takaici da baƙin ciki gabaɗaya suka turniƙe ta, don gani take kamar har da biyu Inna Furai take lanjarewa. Kasa haƙuri ta yi ta ce: "Furaira don Allah ki shafa mana lafiya ki bar mu, mu ji da abin da yake damunmu. Haka kawai ki tayar mana da balli a tsakiyar dare akanki aka fara mutuwar miji? Ko kuma ke kaɗai kika san zafin miji muna zaune ki ishe mu da zancen fatalwa. Ki barni na kwanta na yi baccin da ban samu na yi shi jiya ba."
Inna Furai ta fyace majina da gefen zaninta ta waiga ta ce, "Wallahi babu ƙatuwar Matar da za ta zo mini ɗaki ta nemi kawo mini zazzagar albarka ido biyu. Idan ba za ki iya ba ki tashi ki fice dama ni bana gayyar tsintsinya da bulugari, bare kuma mafici abin banza." Lantan jin maganar Inna Furai ta yi kamar ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta zaburo a hasaale ta ce, "Ban da ƙaddara da rashin ɗan'uwana da na yi, me zai kawo ni ɗakinki kaico Allah ya jiƙanka Yaya Mamman. Wai yau jininka ake wulaƙantawa saboda ƙasa ta rufe mata ido, kai jama'a ɗan'adam butulu. Wanne irin karamci ne Ɗan'uwana bai yi miki ba?"
Inna Furai ta jingina da ƙarfen gado sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, tana yi tana fatar majina. Abin duniya goma da ashirin ne damu su Auwalu, don haka kowa ya yi jim! Babu wanda ya iya tofa magana ɗaya sai gani suka yi Inna Furai ta fara haɗa ƴan kayayyakinta na sawa da ke kan gado. Sabi'u ya ce: "Inna lafiya kuwa wai me yake faruwa ne kike haɗa kaya?"
Inna Furai ta juyo a fusace ta ce, "Zaman ku a nan bai amfane ni da komai ba. Kuna gani ta gama zazzage mini rashin mutumci a ka babu wanda ya tanka mata. Wallahi ko ku bi mini haƙƙin zazzagar albarkar da ta yi mini a ka ko kuma yanzu na fice na baku wuri ku yi yanda kuke so. Gara ni tawagar Malam da ƴan sama jannati ta zo ta ɗauke ni ko kowa ya huta, dama na kiraku ne domin mu kashe mu binne amma da alama ku dai ba ƴan goyo ba ne, don na lura za ku iya zazzage mini sauran albarka da ta rage mini a kaina.
Gabaɗaya shiru suka yi suna nazarin abin da yake damun Mahaifiyarsu, don rikici sun san Mahaifiyarsu mace ce mai matuƙar rikici amma wannan karon gani suke har da mutuwar mahaifinsu da ta taɓa ta.
Lantan na gama sauraron Inna Furai ta miƙe tsaye tana shartar ƙwalla, ɗan ƙullin kayanta da ke ƙarƙarashin gado ta janyo ta fara kiciniyar ɗorawa a ka tana matsalar hawaye. Da sauri Auwalu ya miƙe ya riƙe kayan yana cewa, "Inna Lantana don Allah ina za ki a tsohon daren nan?" Lantan ta kunto mayafinta ta yafa a kanta ta ce, "Auwalu don Allah karka kawo mini maganar da za ta tunzurani har ta kai ga na nemi shaƙe wannan tsohuwar har lahira. Duk irin cin mutumcin da ta yi mini a gabanku baku gani ba za ka taso tsalo-tsalo kana tambayata ka bar ni yau ko ƙasa da sama za ta haɗe ba zan kwana a gidan nan ba."
Nan fa hayaniya ta fara ta shi a cikin gidan, Inna Furai na gama saurarar maganar Lantan ta sa hannu bibbiyu ta dafe ƙirji a razane tana zare idanu kamar wacce ta yi tozali da kumurcin maciji. Bata tanka musu komai ba sai gani suka yi ta sauko ƙasa daidai wurin da Lantan take tsaye ta fashe da kuka haɗe ta rungumo ƙafafuwan Lantan tsam a jikinta. Tana cikin kuka ta ɗaga kai ta dubi Lantan tana cewa, "Wallahi ba za ki bar ɗaƙin nan ba sai kin zazzage ragowar numfashin da nake shaƙa, Lantan yau ni kike muradin kashewa a gaban ƴaƴana. Ai kuwa ko ba yanzu na mutu ba na rataya a wuyanki Kai Auwalu ku shaida haka."
Inna Furai ta juya ga su Auwalu tana musu mugun kallo ta ce, "Allah na tuba wacce uwar na haɗa da su bayan alaƙar haihuwa? Da su Auwalu da Sabi'u kuma ni kam gara ma a ce ban da kowa tun da babu mai tare mini faɗa a gidan nan. Har ana niyyar halakani da sauran rayuwa kai jama'a Lantan an ya kina tsoron Allah kuwa? Duk wanda ya kashe wani dai wuta za shi."
Lantan ta yi tsalle can gefe abin ka da da marar jiki, can gefen babban gado ta matsa tana cewa, "Laƙadi ja'akum... Tuf! Aniyarki ta faɗa kanki karki ja mini masifa ki maƙala mini sharrin kisan kai ina zaune ƙalau." A wannan karon Inna Furai bata tanka mata ba sai gani suka yi zaraf ta fice daga ɗakin, da sauri iyalanta suka bi bayanta suna roƙon ta dawo ɗaki saboda dare.
Tana fita ita ma Lantan ta sa ƙafa ta fito ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin su Auwalu ya yi ba, musamman shi da yana tsaye a nan ne amma zuciyarsa na wurin Yahanasu yana tunanin halin da take ciki. Inna Furai na ganin Lantan ta fito ta bita jiki a sanyaye kamar kazar da ake jefa da gishiri ta ruƙo hannunta sannan ta fashe da kuka. Ita ma Lantan zuciyarta ce ta karye sai kawai ta fashe da kuka, sai da suka yi mai isarsu sannan Inna Furai ta ce, "Yanzu Lantan da na barki tafiya za ki yi a daren nan?" Lantan ta fyace majina a haɓar zaninta ta ce, "Ina zan iya tafiya na barki Furai kina cikin jimamin rashin miji, Furaira rashin miji tashin hankali ne har kin tuno mini da rasuwar Mahaifinsu Ɗan'iya kai rayuwa babu tabbas Allah ya jiƙanka Malam Mudassiru." Lantan ta rushe da matsanancin kuka. Rabe ya matso da niyyar rarrashinsu Inna Furai ta doke hannunsa tana cewa, "Allah wadaran naka ya lalace. Wallahi kaf gidan nan banga wanda zai hanani zazzage muku albarka ba. Wai kamar yanda Lantan take a wurina ta tashi za ta tafi cikin dare amma babu mutum ɗaya da zai hanata tafiya kaico! Wallahi kun ji jiki ƴan bakinciki bantaɓa sanin bakwa ƙaunar aminiyata ba kuma ƙanwar Mahaifinku ba sai yau."Inna Furai na gama maganar ta ja hannun Lantan suka bar su Auwalu a tsaye sake da baki.
Ba su da zaɓi haka suma suka bi su Inna Furai ciki, cikin ƙaguwa Auwalu ya ce, "Inna za mu iya tafiya yanzu?"
Inna Furai ta saki salati ta na kallon Auwalu da wani yanayi har sai da ya tsargu ya ɗan fara sosa ƙeya sannan Inna Furai ta ce, "Wallahi kai dai Auwalu na riga da na san matsayina a wurinka. Tun mahaifinka na raye har ya mutu ban taɓa musa wa maganarsa ba, sai yau don ƙasa ta rufe masa ido?" Ta fashe da kuka tana ci-gaba da cewa, "Ban shirya mutuwa da shiga jahanna ba. Sharaɗi fatalwar mahaifinku ta bani sai na shayar da ku mama kamar yanda na shayar da ku kuna yara, kuma ban ga wanda zai hanani bin umarninsa ba."
Lokaci ɗaya suka ɗauki salati gabaɗaya saboda ta'ajibin jin maganar Mahaifiyarsu, Larai cikin matsananciyar damuwa ta ce, "Inna kin san me kike faɗa kuwa? Yanzu kina nufin Baba ne ya yi miki fatalwa? Inna don Allah kar wani abu ya ruɗe ki ko ya tsorata ki saboda wanda ya mutu ya mutu kenan ba zai ƙara dawowa ba. Sai dai idan shaiɗan ne yake son razanar..."
A hassale Inna Furai ta katse Larai da cewar, "A'uzubillahi minasshaɗanirrajim. Ba zan ga shaiɗan da idona ba Larai kafirta ni kike son yi da za ki haɗa ni da Shaiɗan la'anannan Allah?" Larai rasa hanyar da za ta ɓullowa Mahaifiyarta ta yi don gabaɗaya sun rasa gane kanta. Lantan da ke gefe ta kalli Larai ta ce, "Wallahi ki tubar wa Allah idan ba haka ba, azabar Allah tuni za ta yi fata-fata da ke. Kuma ni gani nake maganar Furaira tana kan hanya don ni kaina lokacin da Malam Mudassiru ya rasu har gizo ya riƙa yi mini a tsakar ɗaki. Don haka ku yi biyayya idan ba haka ba duk cikinku babu mai kaucewa azabar Ubangiji, musamman kai Rabe da ka fi tsoka wallahi tuni wuta za ta tsotse namanka ka lalace a jahannama."
Ganin wannan lamarin yana ƙoƙarin zama babba ya sa Auwalu ya zame jikinsa ya je Shagon Soro ya taso Yayan mahaifinsu ya sanar da shi halin da ake ciki. Har ɗakin Inna Furai ya shiga yana shiga ya same ta, ta yashe riga a sama tana kumfar bakin Larai ta tsugunna ta fara karɓa tun da sauran mazan taurin kai za su nuna mata. Da sauri ya ɗauke kansa gefe don bai yi tsammanin abin da suka faɗa da gaske ba ne. Nan take ya shiga yi mata nasiha amma duk da haka Inna Furai ta shafawa idonta toka ganin haka ya sa ya fara lallashin ta bari zuwa safiya sai a san abin yi. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu shawo kan Inna Furai ta haƙura zuwa safiya sannan kowa ya kama gabansa. Bayan tafiyarsu Lantan ta zabga uban tagumi sannan ta ce, "Yanzu Furaira da idanunki biyu kika yi tozali da Yaya Mamman ni fa ɗazu ƙarya na kirfo da na ce ina ganin Fatalwar Mudassiru, saboda yaran nan sai su raina mu ni kuma a duniya babu abin da na ƙi jini irin raini."
Inna Furai ta miƙawa Lantan hannu ta ce, "Lantan taɓa ni na ji." Da sauri Lantan ta kai hannu tana shafa hannunta. Inna Furai ta mirtsika ido ta ce, "Billahilazi idan har wannan taɓawar da kika yi mini mafarki ce to a mafarki na ga Malam. Wallahi da idanuna na ganshi a wurin zaman alwalarsa amma tun da baku yadda ba nan gaba na kuma ganinsa nasa ya fitowa kowa a zahiri." Kamar wacce aka tsamo daga ruwan sanyi haka jikin Lantan ya yi sanyi ta rasa abin faɗa don hantar cikinta ta fara kaɗawa musamman da ta san Inna Furai ba ta yin rantsuwa sai da ƙwaƙƙwaran dalili. Kwanciya suka yi sai dai kowa da abin da yake wassafawa a cikin zuciyarsa.
Duk cikin ƴaƴan Inna Furai babu wanda ya fi farinciki da tafiyarsu irin Auwalu saboda zuciyarsa gabaɗaya hankalinsa yana wurin Yahanasu don ya san a wannan lokacin tuni ta yi fushi sai ya yi aikin rarrashi. Yana tafe yana haska fitila har ya ƙarasa ɗakin, sai dai turus ya yi a ɗan tsorace yana karewa ɗakin da Yahanasu kallo. Fitsarin da ya ƙarasa gangarawa ƙafarsa ne ya dawo da shi daga duniyar tunani, matsawa ya yi gefe yana leƙa fuskar Yahanasu da ke manne da bango ya ce,
"Yahanasu lafiya kuwa?" Yahanasu na jin muryar Auwalu ta rushe da kuka tana cewa, "Auwalu fatalwar Baba na gani wallahi shi ne har cewa ya yi za su tafi da ni." Cikinsa ne ya bada wani sautin ƙulululu! Da sauri ya ja baya yana dafe ƙirji ya ce, "Kina nufin da gaske kema kin ga fatalwar Baba?" Yahanasu ta nuna masa gadon bayanta ta ce, "Duba ka ga shatin carbinsa a bayana har dukana ya yi da shi kuma ya ce daga yau kar sake buɗe idona." Tsoro ne ya mamaye zuciyar Auwalu musamman da idanunsa suka yi tozali da shatin carbin Mahaifinsu ruɗu-ruɗu a jikinta. Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da ya hango wani guntun likkani a gefen ƙafar Yahanasu. Da sauri ya fisgota suka faɗa gado jikinsa na rawa ya ce, "Yahanasu wallahi maganarki haka take kin ga Likkafani can a ƙasa." Yahansu na jin haka ta ƙara rintse ido tana kuka kamar hawayenta za su ƙare. Auwalu ne ya yi ta maza ta miƙe cikin sanɗa ya banko musu ƙofa da ƙarfi ya sa sakata.
Duk abin da yake faruwa a kunnen Baba Sule da Sahura har zancen Likkafani, wannan maganar ba ƙaramin ɗaga musu hankali ta sake yi ba. Don da har bacci ya fara yunƙurin awon gaba da su kukan da Yahanasu ta rushe da shi ne ya wartsakar da su tare da sa su yin carko-carko kamar masu shirin ko ta kwana.
Dubu tun da ta koma ta yi luf sakamakon motsinta ya so tashin Hasiya Matar Rabe, don haka ta yi kasaƙe daga haka ba a jima ba bacci ya yi gaba da ita don hatta sallar Asuba sai da aka yi da gaske sannan Dubulliya ta samu gabatar da ita.
Washegari.
Jama'ar gidan gabaɗaya kowa ya tashi an ci gaba da harkoki kamar ba taron mutuwa ba. Sai dai gabaɗaya labari ya watsu a ko'ina Inna Furai ta yi ido huɗu da fatalwar Maigaidansu, labarin da wasu suka riƙa ganin kamar tsufa da rikici ne yayin da wasu suke ganin tsabar dukan da mutuwar ta yi mata ne. Sai dai babban abin da ya ja hankulan mutane ganin ɗakin Baba Sule da Auwalu ya rufe. Ko motsinsu babu wanda ya ji bare a sa ran za a ga fitowarsu.
Ɗakin Baba Sule aka fara zuwa ana bugawa, Sahura ta zabura za ta miƙe saboda ta ji muryar mutane don ta yanda ta ayyanawa zuciyarta muddin ta samu ta fice daga ɗakin to ba za ta ƙara kwana a gidan ba sai gidan Mahaifinta. Sai dai tana miƙewa caraf Baba Sule ya damƙi hanunta yana cewa, "Ina za ki tafi ki bar ni?" Sahura ta ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce, "Ai mutanen gida sun tashi ka ga muma sai mu fita zaman ɗaki ba zai kai mu ba." Baba Sule ya yi fakare yana nazari sannan ya ce mata, "Sahura yau ko bayan gida za ki shiga wallahi sai dai mu tafi tare, don ba zan bari matattu su tafi da ni da kwana na a gaba ba." Bugun ƙofar ne ya tsananta don haka suka taso riƙe da hannun juna suka zare sakata, sai dai suna buɗe ƙofa kyallen likafanin da Dubu ta soka musu ya faɗo. Daga waɗanda suke tsaye a ƙofar ɗakin har su na cikin ɗakin bazama suka yi a guje, suka yi cikin gida. A cen ɗakin Yaya Babba suka yada zango sai dai har lokacin Baba Sule yana riƙe da hannun Sahura. Yaya babba sakin baki ta yi tana kallon Baba Sule da ya yi tsamo-tsamo a cikin mata ta ce, "Sule me kake yi a kan cinyar Uwani?" (Uwani ƙanwar Mahaifiyar Sahura ce.) Baba Sule gabaɗaya zuciyarsa a dagule take saboda gani yake rayuwarsa ta zo ƙarshe.
Ba baka sai kunne. Baba sule ban da hawaye babu abin da yake yi. Wannan shirun da Baba Sule ya yi ba ƙaramin ɓata ran Yaya Babba ya yi ba, don haka ta dube shi ta ce, "Bana son iya shege kai Sule idan ba za ka yi magana ba, ka fice mini daga ɗaki ko na kwashe maka albarkar da ta yi saura a kanka." Baba Sule ya sake matsar ƙwalla ya ce, "Inna wallahi Fatalwar Baba ce za ta tafi da ni matukar na saki hannun Sahuwa ƴan sama jannati ne za su tafi da ni." Ku san mutuwar zaune Yaya Babba ta yi saboda labari ya risketa daga wurin kishiyarta ga shi Ɗan cikinta ma ya sanar da ita.
Nan fa gida ya hautsine hantar cikin kowa ta kaɗa saboda fargaba, Sai da Yaya babba ta yi da gaske sannan Baba Sule ya saki hannun sahura. Ai kuwa yana sakin hannunta ta ranta ana kare. Baba Sule na ganin haka ya rufa mata baya. Sai da ƙyar aka samu aka tsayar da su a soron gidan tare da tura Baba sule cikin ɗaki don Yayan Mahaifinsu gani yake kamar gamo ne suka yi. Dubu ban da dariyar mugunta ƙasa-ƙasa babu abin da take yi.
Sai daga baya aka farga da su Auwalu da suke ɗaki don haka da sauri Yayan Mahaifinsu ya je ya sa suka buɗe ƙofar da ƙyar, Auwalu yana maƙale da Yahanasu don gani yake idan ya sake ta kamar Fatalwar Mahaifinsa za ta yi awon gaba da ita.
Malam Idi shi ne yayan Mai Carbi, tara mutane gidan ya yi gabaɗaya yana yi musu nasiha da nusar da su illar yarda da amincewa abin da suka yi tozali da shi. Sai da ya gama wa'azin sannan ya bawa Inna Furai damar ta yi magana.
Inna Fuarai ta karkace ta ce, "Yaya Idi yadda na ga Fatalwar Malam na ga Annabi. Ganin idona na ganshi kuma har umarnin shayar da su Auwalu ya yi." Sai da suka gama jin jawabinta tsaf sannan aka ce Yahanasu ta yi faɗi abin da ta sani, Yahanasu da ta buɗe ido da kyar tana sunne kai ƙasa don duk yanda hankalinta ya ɗan kwanta har Yaya Idi ya sa ta buɗe ido bata gama sakewa ba. Ta fara yi musu bayani dalla-dalla sanna ta ɗora da cewa, "Kuma da bakinsa ya sanar da ni duk wanda ya wayi gari da likkafani a ɗakinsa to gaba shi za su ɗauka. Shi ya sa na ce tawa ta ƙare." Auwalu ya rumgumota yana cewa, "Ba za ki mutu ba Yahanasuna" Yaya Idi ya yi jim sannan ya ce, "Idan na fahimta wani ne kawai yake son razanar da mutanen gidan amma babu damuwa ku bar mini komai a hannuna zan san yanda zan ɓullowa lamarin.
Dubu tana gefe tana jin duk wainar da ake toyawa don haka ta saci jiki babu wanda ya lura da ita, kuma babu wanda ya taɓa kawo ita za ta aikata wannan abin. Dubu na tafiya ta wuce ɗakin Marigayi ta zaro wasu kayansa da yake zuwa sallar juma'a da su. A wanke suke a goge fari ƙal da su, sai da ta bubbuɗa su ta je bakin katangar banɗaki wacce mutum zai iya haurawa ta wurin ta ajiye, hularsa ta saƙale a jikin wata itaciyar tunfafiya sai kuwa ta kwaso a guje ta shiga wurin taron da suke gabda kammalawa. Ihu take kwarawa kamar wacce ake ɗanawa wuta tana cewa, "Wayyo Allah na ga Fatalwar Baffa na gani zai tafi da ni. Kafin ka ce wani abu tuni wurin ya watse sai takalma da ɗankwalaye da aka barsu suna cin karen su babu babbaka. Yaya Idi sai da ya yi kusan adungure biyu sannan ya samu ya shige ɗakin Inna Furaira. Hularsa kuwa ta yi tsalle ya fi sau biyar kafin ta samu sukuni faɗuwa can bakin ƙofa.
[7/11, 7:44 PM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
0 comments:
Post a Comment