"Wace ce ke?" Intisar ta saki malalacin murmushi ta fara zagaye ɗakin tana ƙarewa Mama Uwani da ke ɗauke da mummunar siffa ta ce, "Menene damuwarka har kake son sanin ni wacece? Dama ka yi abin da yake gabanka don sanin wacece ni ba zai amfane ka da komai ba." A haukace Mama Uwani ta buga uban tsalle da waɗansu manyan fuka-fukai da suka fito daga ƙasan hammarta, ta dira a gaban Intisar haɗe da karta mata faratanta bisa tsautsayi farcen ɗan yatsanta ɗaya ya karci gefen fuskarta. A zafafe ta matsa baya cikin huci, nan take fatar jikinta ta fara darewa tsokar namanta ta fara bayyana a fili, kanta ya fara rabewa gida biyu wani dogon ƙaho ta fara tsorowa daga tsakiyar kanta. Tana shirin mayar da martani daga can bakin ƙofa suka ji maganar Mommy na ƙwalawa Mama Uwani kira, kamar ƙiftawar ido tuni suka koma hallitarsu ta ainihi. Mama Uwani ta zubawa Intisar wani mugun kallo cike da takaici ta furta, "Idan kere na yawo zabo na yawo watarana za a haɗu."
Intisar ta ɗaga kafaɗa cikin rashin nuna damuwa ta ce, "Kamar yadda Ungozoma ke jiran mai naƙuda haka koyaushe nake dakon haɗuwarmu domin nasan ba a dauwama da kashi a ciki." Dire zancen Intisar ya yi daidai da shigowar Mommy cikin ɗakin wasu baƙin mata na biye da ita, kallon Mama Uwani ta yi a ɗan faɗace ta fara faɗin, "Mama Uwani kina ji ina ta magana lafiyarki kuwa?" Kamar yadda ta saba ladabi a gaban su Mommy haka Mama Uwani ta dausashe murya ta ce, "Hajiya a yi haƙuri yanzu na zo wuce wa na hangi wannan baƙuwar ta shigo ɗakin nan shi ne na shigo don na sanar mata cikin gida ake zaman makokin, wallahi na sha'afa ban ji ki ba." Mommy ta faɗaɗa murmushi tana kallon Intisar ta ce, "Ƴanmata sannu da zuwa." A kunyace Intisar ta sunne kai haɗe da tsugunnawa har ƙasa tana faɗin, "Mommy ina kwana?" Mommy ta dafa kafaɗarta tana ɗago ta, ta c: "Lafita ƙalau 'yata tashi tsaye." Intisar ta amsa da, "Mommy ina Raihan?" A firgice Mama Uwani ta ɗago cikin suɓutar baki ta furta, "Me Raihan za ta yi miki?"
Da sauri Mommy ta kalli Mama Uwani fuska babu walwala ta ce, "Mama Uwani ya haka ne?" Mama Uwani ranta ya sake ɓaci, ta russunar da kai tana faɗin, "Ayi haƙuri Hajiya." Mommy bata tanka mata ba, ta juya wurin baƙin da take tafe da su ta ce, "Ga baƙi nan ki wuce da su sashenku." Ta juya wurin Intisar ta ce, "Ni kamar Intisar nake gani." Intisar ta sosa kai a kunyace ta ce, "Ni ce Mommy, dama na ji abin da ya faru ne na zo in yi mata gaisuwa." Mommy ta sake goge hawayen fuskarta da yake zuba, don mutuwar Mama Hasiya ba ƙaramin dukanta ta yi ba, ta riƙo hannun Intisar don dama tun da ta ganta take yi mata kallon sani, abin da ya hanata gane ta sau ɗaya ta taɓa ganin wani zuwa da suka yi da Raihan. Intisar ta sake lafewa a jikin Mommy suka nufi hanyar fita, Mommy tana faɗin, "Allah sarki Intisar, ya su mommynku." Intisar ta ce, "Duk lafiya ƙalau ta ce a yi muku gaisuwa kafin ta shigo." Mama Uwani jiki a saluɓe ta ja baƙin suka nufi sashensu, Intisar tana tafe tana sakin wani shu'umin murmushi haɗe da bankawa Mommy harara a fakaice.
Wuce mutane suka rinƙa yi duk in da ta keta sai gaisuwa ake yi mata, mommy har lokacin hawaye ne ɗauke a fuskarta. Suna zuwa ta wuce da ita sashen Raihan, Raihan na zaune da su Batula ƴaƴan ƙanne da yayyan mommy, suma ƴan mata ne kuma ta su ta zo ɗaya da Raihan.
Intisar na shiga Raihan ta faɗaɗa fara'arta tana miƙa mata hannu daga zaune, da sauri Intisar ta rungumeta tana faɗin; "Besti ya ƙarin haƙuri." Idanun Raihan ya ciko da ƙwallah, sai da ta sa hannu ta goge hawaye cikin shassheƙar kuka ta ce, "Besti wai Mama Hasiya ce ta mutu, idan kin tuna hirarmu da ke last ba nace miki ni na ɗauki alƙawarin Baby shower ba idan ta samu Ciki?" Intisar ta matso hawaye cikin sigar tausayi ta furta, "Kayya Besti ya za a yi na manta da hirar Mama Hasiya." Raihan ta ci gaba da kuka tana faɗin, "Intisar Mama Hasiya na sona kamar ita ta haife ni, wai ita ce ta mutu shi kenan mun rasata." Kamar haɗin baki lokaci ɗaya suka fashe da kuka mai ban tausayi, sai da ƙyar aka lallashe su musamman Raihan.
Bayan wani lokaci suna zaune tuni an sallaci Mama Hasiya an kaita makancinta, Mama Uwani ce ta turo ƙofar ta shiga saboda gabaɗaya zuciyarta ba ta aminta da Intisar ba, don tun ranar da ta fara ɗora ido a kanta ta fahimci ita ba alheri bace a rayuwar Raihan. Sai dai duk yadda ta so bin diddigin gano wacece ita abin ya faskara, don haka ko da ta shiga ɗakin sai ta hau goge-goge don ganin abin da yake faruwa. Intisar na ganin haka ta saki murmushi a fakaice don ta san tsiyar da za ta shukawa Mama Uwani, yamutsa fuska Intisar ta yi ta ce, "Besti pls ki ce Mama Uwani ba ni ruwa and takalmana suna waje ta kwasominsu." A hargitse Mama Uwani ta wurgawa Intisar mugun kallo saboda ɓacin rai har sai da ta so bayyana fushinta a fili, kai tsaye Raihan ta dubi Mama Uwani ta ce, "Mama Uwani ki ɗaukowa Intisar ruwa a falo na firij ɗina ya ƙare." Ganin rainin hankalin Intisar ya yi wa Mama Uwani yawa ya sa bata tanka wa Raihan ba ta kalli Intisar, ta fara wani huci idanunta suka fara sauya lauyi ba tare da Raihan da sauran mutanen ɗakin sun lura ba.
Kofar toilet ɗin Raihan ta kalla lokaci ɗaya kofar ta buɗe da ƙarfi, wani tafkeken maciji ne ya fara silalowa bakinsa na fidda baƙin hayaƙi. Wata uwar ƙara suka ƙwalla a firgice kowa ya fara neman hanyar fita, kafin wani lokaci tuni duk sun fice daga ɗakin har Intisar don ko kaɗan bata yinƙurin yin wani abu a gaban Raihan da zai bayyana ita ainihin wacece.
Mama Uwani nan take ta ɓace a wurin, macijin ra rabu gida biyu ɗaya ya rikiɗa zuwa siffar Raihan ɗaya kuma yana nan a siffarsa ta farko, ita kuma Mama Uwani ta ɓace tare da Raihan ɗin ainihi. Kamar ƙiftawar ido haka Mama Uwani ta ɗira a wani tsibiri mai ɗauke da dogayen bishiyu masu duhun gaske, sai wasu korayen tsuntsaye masu yawan da wasu hallitu masu siffar ƙadangaru sai dai jelunar su gashi gare ta kamar jelar tunkiya. Raihan da take sume ta shimfiɗar, Mama Uwani ta zauna ta zura mata ido, nan take ta rikiɗa zuwa surarta ta ainihi wato HUZAIFA. Miƙewa ya yi da surar wata ƙatuwar hallita mai matuƙar tsawo, fatar jikinsa kamar bayan kada ga wata zabgegiyar jela a bayansa mai ɗauke da kawunan macizai masu fidda aman wuta. Hannuwansa ɗauke suke da manyan farata sai harshensa da suke dalalar da wani baƙin ruwa mai yauƙi.
Kamar wancen karan da ya kaita daularsa ta ƙarƙashin ƙasa, a yanzu ma zuwa ya yi daidai wurin da take kwance ya zuba mata ido wata matsananciyar sha'awar Raihan na sake fisgarsa. A hankali Raihan ta sauke ajiyar zuciya sanyin shukokin wurin ya fara dukan gangar jikinta, motsi ta fara yi alamar za ta farfaɗo. Ruwan bakinsa ya ɗiga mata a saitin goshinta, a cen gefe ya je ya ɗauko wannan ƙaramar hallitar mai siffar kunkuru ya ɗagata da hannuwa biyu yana kallo yana jin daɗi, domin babu abin da ya fi saurin faranta ransa sama da ya ga ya haɗa Raihan da abin da ta haifa masa. Mayar da jaririn hallitar ya yi sannan ya dawo kan Raihan da ke kwance, a hankali ya fara mu'amala da ita yana sarrafa sassan jikinta ga wata irin kewarta da ya yi don ya jima bai kusance ta ba, tun ranar da ta haifi wannan mumummunar hallitar tun da ba ya iya ɗaukan kwana biyu cir ba tare da ya kusance ta har ya yi mu'amala da sassan jikinta ba.
Yana tsaka da mu'amala da ita ya ji wata iska ta fara, kaɗawa mai tafe da sarewa. A hankali ya ɗago kansa yana kallon abin da yake faruwa don ko ba a faɗa ba, ya san Mugaza ce za ta dira a wurinsu. Tun bai gama tunaninta ba ya ji kecewar dariyarta a tsakar kansa, miƙewa ya yi daga kan Raihan a lokacin ya bayan ya samu nutsuwa da ita, ya taka wurin Mugaza fuska a haɗe cikin wata irin murya ya furta, "Me ya kawo ki Turakata bayan kinsan hutawa nake yi?" Haushi ne ya sake rufe Mugaza da ke ɗauke da surar wani ƙaton tsuntsu mai kan angulu. Sai da ta yi tsalle-tsallenta sannan ta dira a gabansa rai a ɓace ta mayar masa da martani, "Akwai wani hutu da ya dace ka yi bayan bana kusa da kai?" Huzaifa ya ƙare mata kallo yana shirin magana ta ci gaba da cewa, "Sau nawa zan gaya maka ka fita daga rayuwar yarinyar nan, idan ba haka ba wallahi sai na halakata ta hanyar kisa mai muni." Wani uban tsalle ya buga haɗe da girgiza sannan ya rikiɗa zuwa surar matashin saurayin bil'adam, ya kalli matarsa Mugaza tare da sakin wani shu'umin murmushi ya ce, "Wannan yarinyar da kike gani na fansar da raina a gareta idan kin ga ban tsayawa rayuwarta ba sai dai bana numfashi, ita ɗin ta zama jinin jikina ko iyayen da suka haifeta idan suka nemi raba ni da ita sai na tarwatsa rayuwarsu." Jinjina kai Mugaza ta yi haɗe da sakin wata irin shu'umar dariya sannan ta ce, "Wannan shi ne gargaɗi na ƙarshe da na yi maka a kanta, tun da baka ji ba za ka ga ni a gaba kuma idan kwaɓarka ta yi ruwa karka yi kuka da ni. Sai dai zan ci gaba da baka kulawa a matsayina na matarka mai ƙaunarka, amma a kan wannan yarinyar babu wata kalma da za ta sake shiga tsakaninmu. Sai na ladaftar da ruhinta ta yadda za ta yi danasani, sai na azabtar da gangar jikinta domin sai na shayar da ita azaba mai raɗadi" Tana gama maganar ta tashi daga cikin tsibirin ta fice, ko a jikin Huzaifa ya ƙarasa wurin da Raihan take kwance ya sake rikiɗa zuwa siffar marigayya Mama Hasiya haɗe da sauya fasalin wurin, a hankali ya sa hannu ya fara tashinta tare da faɗin sunanta. Ahankali ta buɗe idonta tana kallon wurin da take da Mama Hasiya da take kanta a tsaye.
Bayan fitowar su Intisar a kan idonta Mama Uwani ta sauya Raihan da wata Raihan ɗin, murmushi ta yi don ta fahimci manufarta na yin haka kuma ita ma ta shiga nazartar yadda za ta ɓullo mata. Nan take gida ya ruɗe da maganar macijin da aka gani a ɗakin Raihan, hankulan mutane ba ƙaramin tashi ya yi ba. Lokacin da Mommy ta samu wannan labarin da sauri ta aika aka kira Kabiru (Matashin bafulatani Maigadin gidansu Raihan.) Saboda Kabir bai da tsoro sam, bai fi sati biyu da fara aiki a gidansu Raihan ba. Tsayayyen namiji ne mara tsoro don akwai ranar da aka samun kulɓa a kitchen ɗin Mommy, Kabiru na zuwa ya fitar da shi. Kafin Kabiru ya zo Sulaiman ɗan ƙawar Mommy ya miƙe yana faɗin, "Daga wurin ina yake yanzu na fice da shi, ba wani shege kura ma mun kara da ita mun kaita ƙasa." Babu wanda ya hana shi don jikinsa na rawa ya nufi cikin gidan, saboda yana mutuwar ƙaunar Raihan don haka yake son ya yi wani abin bajinta ko ya samu ya ƙara samun masauki a zuciyar Raihan.
Yana zuwa duk matan da ke zagaye da ɗakin suka dare, ya tura ɗakin da ƙarfinsa. Yana shiga ya samu macijin a tsakiyar ɗakin ya naɗe wuri ɗaya kamar gammo ya fasa kai, bakinsa yana fitar da feshin wuta, a hankali ya waiga yana faɗin: "Wani ya miƙo min katako." Har rige-rigen tafiya mutane suke yi babu jimawa aka ɗauko masa wani ƙaton katako, kansa tsaye ya tunkari macijin cikin dakiya ya ɗaga ya buga masa a tsakiyar ka. Tsalle macijin ya yi, Sulaiman ya gantsare duniyar na juya masa. Sannu a hankali macijin ya rarrafo ya fara nannaɗe shi har sai da ya naɗe masa jiki, nan take Sulaiman ya hau kakari ƙwayar idonsa duka biyun ta faɗo ƙasa, jini ya fara zuba ta hancinsa da bakinsa. Tun Sulaiman yana iya kakari har ƙarfinsa ya ƙare, tsokar jikinsa ta fara burtsowa daga jikin fatarsa nan take hallitar Sulaiman ta sauya tamkar ba bil'adam ba. Mutane na ganin haka suka fita da gudu cikin kururuwar neman taimako.
************
Raihan ta shi ta yi zaune jikinta ba ƙaramin tsami ya yi mata ba, ta dubi Huzaifa da ke cikin siffar Mama Hasiya ta ce, "Mama Hasiya kece? Dama baki mutu ba?" Huzaifa ya gyaɗa wa Raihan kai yana furta, "Ban mutu ba amma na dawo nan wurin da zama za ki zauna da ni?" Raihan ta yi shiru tana nazartar maganarsa jiki a sanyaye ta ɗago tana cewa, "Gaskiya ban yarda ba ina su Mommy?" Huzaifa ya riƙo hannunta lokaci ɗaya ta ji wani yaarrr a cikin jikinta, tana kiciniyar ƙwacewa sai gani ta yi ta fisgo da ƴan yatsu biyu na jikin hannun Huzaifa, a tsorace ta wurgar da su ta fara ja da baya jikinta na karkarwa. Cikin rawar murya ta ce, "Don Allah ki yi haƙuri karki cutar da ni." Ganin haka ya sa Huzaifa ya fara ƙyaƙyacewa da wata irin dariya har sai da ta sa hannuwa biyu ta toshe kunnuwanta, kakin yawu ya yi ya tofar nan take ƙasar wurin ta fara rozayewa ya sa ɗan yatsa ya nuna mata wurin yana faɗin, "Ki bar wahalar da kanki domin ba za ki taɓa guje min ba, ki zo ki shiga wurin nan idan ba haka ba za ki dauwama a wurin nan."
*********
Al'ummar da ke zaman makoki kusan rabi da kwata kowa ya cika wandonsa da isa, don ceton rayuwarsa. Hatta Inno da Goggo cikin ayarin ƴan ceton rai suke ba tare da su mommy sun farga ba. Hankalin Daddy ba ƙaramin tashi ya yi ba da ganin abin da ya faru, a hankali Kabiru ya fara takawa cikin gidan dukda yana ta cin karo da mutane masu guduwa hakan bai hana shi sake kutsawa cikin falon gidan da zai sadaka da ɗakin Raihan ba, a bakin wata ƙofa ya ci karo da Intisar da ke tsaye ƙyam babu alamar tsoro a tattare da ita. Suna haɗa ido ya ji kansa ya sara juwa ta fara ɗibansa, sama-sama ya fara jin wata irin hayaniya har sai da ya dafa kansa da hannuwansa, a hankali ya fara karanto addu'o'in tsari yana karantawa duk wacce ta zo bakinsa. Lokaci ɗaya ya ji komai ya ɗauke masa, ya dawo cikin hankalinsa sai dai tuni jikinsa ya jiƙe da gumi sharkaf. Idanu ya kafe Intisar da su har ya gagara sarrafa kansa, ya fara takawa zuwa gabanta cikin hausar da bata gama zama a bakinsa ba ya ce, "Washeshe kai?" Intisar ta saki murmushi ta ƙarasa gaban Kabiru ta ce, "Kai bafulatanin ƙauye, karka shiga abin da babu ruwanka." Yana shirin sake magana Daddy ya ƙaraso wurin hankali a tashe yana faɗin, "Kabiru mu je ka ga abin da yake faruwa meye abin yi?" Kabiru ya yi gaba yana waiwayen Intisar haɗe da ɗora mata zarge-zarge a kanta.
Da ƙarfin gaske Kabiru ya tura ƙofar ɗakin cikin zuciyarsa yana ci gaba da karanta ayoyin tsari dana kariya, Jabun Raihan ce ta ƙaraso ƙofar ɗakin. Abin da ya ji da farko a lokacin da yake tare da Intisar haka ya ƙara ji a wannan karon a haukace ya juya, ya shaƙi wuyan Raihan cikin wani irin ƙaraji ya furta.
"Washeshe kai? Me kake yi a wurin nan?"
DA ALAMA KABIRU YA YANKI TIKITIN BARIN AIKIN GADIN DA YAKE YI A GIDANSU RAIHAN😂 TO WAI SHI MA KO YANA DA ALAƘA DA SU NE😂 SHIN DADDY ZAI ZURA IDO YA GA AN MAƘURE GUDAN JININSA? SHIN SU DADDY ZA SU FARGA DA MAMA UWANI BA MUTUM BACE SHI NE AINIHIN ALJANIN DA KE RAYUWA DA ƳAR'SU? KO KUMA HUZAIFA ZAI ƘYALE KABIRU HAR YA TONA MUSU ASIRI🤭🤭🤭
TAFIYAR FA HAR YANZU BA A FARA BA DOMIN LABARIN TAFE YAKE DA SARƘAƘIYA🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️ KARKU MANTA HAR YANZU RAIHAN BATA SAN MAMA UWANI CE TA KAWO WANNAN TSIBIRIN BA, ITA DAI TA BUƊI IDO DA MARIGAYYA MAMA HASIYA. WAI INA LABARIN INNO DA GOGGO NE INA SUKA BAZAMA WAYE ZAI TARO SU? 😂😂
Share Fisabillah🌚
[7/12, 10:15 PM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*
© *AMEERA ADAM*
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
FREE PAGE 6
Raihan kallon ramin ta yi da yake ci gaba da rozayewa ƙasar wurin na ruftawa, ya yin da ramin yake ci gaba da ƙara girma yana tunkaro wurin da take. A hankali ta riƙa ja da baya cikin rawar jiki, firgici da tashin hankali. Tuni hawaye ya wanke fuskarta ta ci gaba da yin baya ba tare da ta fahimci wurin da take jefa ƙafarta ba, bata yi aune ba ta ji wani dutse ya tokareta ƙasar da ke zaftarewa ta ƙaraso har wurinta har sai da ya rage bai fi taku ɗaya ba ta dakata bisa bin umarnin Huzaifa da ke cikin surar Mama Hasiya. Cikin kuka Raihan ta dubi shi tana faɗin, "Don Allah ki yi haƙuri karki cutar da ni, ban san abin da na yi miki ba kika kawo ni wurin nan alhalin mommy ta ce mini kin mutu." Huzaifa ya ƙyaƙyace da wata mahaukaciyar dariya ya fara takowa wurinta yana tafe yana zare sauran ƴan yatsun hannunsa yana zubarwa, kafin ya ƙarasa wurinta tuni ya tsinke yatsun hannunsa sai iya dungulmin kaɗai ya rage, daga guraben ƴan yatsun wasu baƙaƙen farata ne suka fara tsirowa a hankali har sai da suka fito zaƙwa-zaƙwa da su, ta cikin ramin ya shiga kamar ƙiftawar ido ya dira a gabanta cikin wata irin murya mai amsa kuwwa ya sake ce mata. "Ki biyo ni cikin ramin nan idan ba haka ba za ki dauwama a nan." Raihan ta sake girgiza masa kai tana cewa, "Don Allah ki mayar da ni wurin su Mommy." Baki ya buɗe zai fara dariya wasu dogayen fiƙoƙi suka fara fitowa, da sauri Raihan ta runtse ido tana ƙwallah wata razananniyar ƙara. Wata iska ta ji mai sanyi na ratsa jikinta a hankali ta buɗe idonta, ga mamakinta sai na yi ta yi wurin ya sauya mata ta ganta wani kogon dutse mai ɗauke da ƙananan bishiyu, a hankali ta fara takawa har zuwa bakin kogon dutsen don ta hango hasken rana daga bakin dutsen. Tana fita daga cikin dutsen ta fara gudu da iya ƙarfinta don ganin ta ceci rayuwarta.
Daga nesa-nesa ta fara jiyo kukan jarirai haɗe da haniniyar doki, a hankali ta fara rage gudunta don yadda ta lura hanyar da take tunkara a nan take jin sautin kukan jaririn na sake karaɗe kunnuwanta. Tana tafe tana waiwaye ta bata yi aune ba ta ji ta yi karo da wata murgujejejiyar hallita, hallitar riƙe take da wasu ƙananan jarirai masu surarta, tsayin hallitarta ya ninka ta sau biyu, tana da ƙiba sosai don kaurin cinyar hallitar ya yi kaurin Raihan sau huɗu. Tana ɗauke ƙafa da hannuwa irin na birrai sai ƙaton kai irin na dorinar ruwa. Bakinta tsayi gare shi idanunta kwala-kwala masu ɗauke da launin ja, Raihan na shirin ja da baya Hallitar ta ƙurawa Raihan Ido tana miƙa mata hannu alamar ta zo gare ta. Da gudu Raihan ta juya don ta koma cikin kogon dutsen, karaf ta ji ta yi karo da Hazaifa da ke ɗauke da surar Mama Hasiya sai dai kammanina sun sake munana.
Ajiyar zuciya ta sauke don ko ba komai ta ji daɗin ganinsa, hankalinta ya fi kawanciya da shi a kan na wannan mummunar hallitar. Hallitar na ganin Huzaifa ya ɗauke Raihan sun koma zuwa kogon dutsen ta juya ta koma daga wurin da ta fita, Huzaifa ya saki malalacin murmushi bayan sun koma ciki ya zaunar da Raihan akan wani faffaɗan dutse, ya zauna a gabanta yana kallonta. Tana shirin yin magana ya katseta da cewar, "Kina son komawa gida?" Da sauri Raihan ta gyaɗa masa kai. Jinjina kai ya yi sannan ya ce, "Zan mayar da ke gida amma da sharaɗin..." Da sauri ta katse shi da cewar, "Na amince da kowanne sharaɗinki indai za ki mayar da ni gida."
Wannan jaririn hallitar ya ɗauko mata mai shige da siffar kunkuru ya ce, "Ya zama wajibi ki shayar da wannan domin shi ɗin jininki ne." Idanunta ne suka firfito waje ta ƙarewa hallitar kallo tana yamutsa fuska, bai saurari abin da za ta faɗa ba ya ci gaba da cewa. "Ya zama wajibi ki yanke alaƙarki da wannan yarinyar Intisar." A hargitse Raihan ta sake ɗagowa ta yi tana kallonsa don a duniya bata da aminiya sama da Intisar, bata da wacce tasu ta zo ɗaya sama da ita amma lokaci ɗaya ya ce dole ta rabu da ita.
*********
A haukace Daddy ya yi kan Kabiru ya rufe shi da wani mahaukacin duka, sai da ya gaji don kansa sannan ya janye Jabun Raihan ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya. A cen gafe Kabiru ya faɗi yana sauke ajiyar zuciya yana sauke numfashi cikin wahala, ɗagowa ya yi suka haɗa ido da Jabun Raihan a fakaice ta sakar masa wani malalacin murmushi ta fara motsa baki tana magana ba tare da ta wani ya ji abin da take faɗa ba. Duk maganganun da Jabun Raihan take yi a kannen Kabiru, ransa ne ya sake ɓaci ya dubi Daddy da yake jifansa da mugun kallo, cikin bagwariyar hausarsa ya ce, "Alhagi shi wannan yaron ba mutumin kirki ba ne, azzalumi ne so yake ya shushe ki." Daddy ya sake dunƙule hannu ya kaiwa Kabiru naushi a baki ya ce, "Don uwarka a gabana kake ce min ƴata ba mutuniyar kirki ba ce, ina maka kallon mai hankalin ashe kaima ɗan iska ne, wallahi a yau ba sai gobe ba sai an rufe min kai na ga gatanka mahaukacin banza mahaukacin wofi." Raihan da ke maƙale da Daddy ta sake langwaɓewa tana ɗangale ƙafa. Alhaji Mustafa Indabawa ne ya dubi Daddy yana faɗin, "Abokina don Allah ka yi haƙuri, yanzu mu ƙarasa wurin da gawar yaron nan take." Kabiru ya yunƙura da kyar bakinsa na ɗigar da jini. Daddy na leƙa cikin ɗakin ya yi tozali da gawar Sulaiman, da sauri Daddy ya ja da baya jikinsa na tsuma don ba ƙaramin tsorata ya yi ba. Alhaji Mustafa shi ma yana leƙawa a zabure ya ja da baya har suna gware da Daddy. Lokaci ɗaya Daddy ya yi zuru-zuru hankali a tashe ya furta, "Wannan tashin hankalin ne ya faru a ɗakin Raihan?" Intisar da ƙarasowarta kenan ta amshe maganar da cewar, "Daddy tun da nake ban taɓa ganin maciji mai muni irin wannan ba." Daddy da jikinsa ya gama sanyaya ya fara jinjina kai, suna nan tsaye macijin nan ya fara warware kansa daga jikin Sulaima. Ganin haka ya sa mutanen wurin suka fara darewa, Kabiru ne ya dafa ƙofar a hankali ya zura ƙafarsa ɗaya cikin ɗakin.
Kallon-kallo aka fara yi tsakanin kumurcin macijin nan da Kabiru, a hankali Kabiru ya fara karanta duk wata addu'ar tsari da ta zo bakinsa. A zabure macijin ya fara ja da baya Kabiru na sake tunkararsa, wani kofi Kabiru ya hango da ruwa a jarka da sauri ya ɗauka ya zuba ruwa a kofi ya fara karanta ayoyin tsari yana tofawa. Daddy ban da leƙe babu abin da yake yi. Kasancewar Jabun Raihan ta san irin soyayyar da Mahaifin Raihan yake yi mata ya sa ta kwaɓe baki a lokacin da ta ga Kabiru ya tasamman halaka Macijin da ubangidanta ya turo, ta ƙwalla wata ƙara tana faɗin, "Daddy wuyana." Kabiru ya waiwayo yana kallonta, Daddy ya kai hannu kan wuyanta yana faɗin, "Mu je asibiti a duba ki, wallahi duk abin da ya samu ƴata ka kuka da kanka." Daddy ya ƙarasa maganar yana watsawa Kabiru mugun kallo. Raihan ta sake langwaɓewa ta ce, "Daddy don Allah a bar korar macijin nan kar wani ya ƙara mutuwa kawai ka kira fire service." Daddy ya kalli wurin da Kabiru yake ya ce, "Kai maza fito daga ɗakin nan kar kaima ka yi mana mushe." Intisar ta kalli jabun Raihan ta watsa mata harara, sannan ta mayar da kallonta wurin Daddy ta ce, "Daddy amma naga kamar macijin ya fara ja da baya mai zai hana a bari a ga ƙoƙarinsa..." Alhaji Mustafa ya katse ta da cewar, "Tabbas ni ma haka na gama ayyanawa don yaron nan kamar akwai wani taimako da zai yi mana." Kabiru bai bi ta kansu ba ya sake tunkarar wurin macijin, lokaci ɗaya ya watsa masa ruwan tofin hannunsa bakinsa na ci gaba da ambaton Allah. Nan take macijin ya faɗi gefe yana wani iri gurnani, zaburowa ya sake yi da niyyar kai wa Kabiru sara da sauri Kabiru ya watsa masa sauran ruwan da ke hannunsa. Wata dariyar farinciki Intisar ta saki don ko ba komai ta san an yi wa Mama Uwani illa, jikinsu Daddy ba ƙaramin sanyi ya yi ba da ganin gwagwarmayar da suka yi tsakanin Kabiru da macijin.
Jabun Raihan ta sake kallon Intisar ta saki ƙwafa a takaice, ta so ace Huzaifa ya bata umarni da tuni ta nunawa Intisar iyakarta. A wahalce Kabiru ya sa hannu ya hanyo macijin, ya fito daga ɗakin fuskarsa ɗauke da gumi lokaci ɗaya Daddy ya ji Kabiru ya birge shi saboda jarumtar da ya nuna, wannan ne karo na farko da ya ji ba zai iya ɗaukan mataki a kan wanda ya taɓa gudan jininsa ba, saboda yana matuƙar son mutum mai dakakkiyar zuciya. Sai dai har lokacin yana jin haushin Kabiru saboda abin da ya yi wa Raihan a idonsa.
Kusan tare suka tarkata suka fito daga sashen, kowa da abin da yake faɗa. Kabiru fita ya yi da macijin can bayan gidan Daddy ya kai ya wurgar da shi, Daddy da kansa ya sa aka rufe sashen Raihan tare da cewar sai ya kira ma'aikata sun yi wa ɗakin feshin magani, a ɓangare ɗaya yana tunanin barinsu daga gidan gabaɗaya.
*************
Raihan bata da zaɓi don haka ta gyaɗa masa kai tare da faɗin, "Duk abin da kika faɗa na amince don Allah ki mayar da ni." Huzaifa ya yi murmushi jindaɗi don shi kansa ya lura da yadda Raihan ta gama tsorata da shi. Lokaci ɗaya ya ji ta bashi tausayi, ya sa hannu ya zaro fiƙoƙin bakinsa waɗanda suka tsiro ya wara hannuwansa da niyyar Raihan ta rungume shi amma fir ta ƙi. Ya kalli fuskarta ya ce, "Kina ƙaunata." Raihan bata da zaɓi duk abin da ya faɗa sai dai ta amsa masa da amincewarsa. Tana tsaka da tunani ta ji ya ce, "Rufe idonki." Kallon hagu da dama ta fara yi a hankali ta furta, "Don Allah kar ki yi min komai." Huzaifa ya yi murmushi ya ce, "Kina rufe ido za ki ganki a gida." Tun bai rufe baki ba Raihan ta rufe idonta da ƙarfi, bata jima da rufewa ba ta ji tashin hayaniya na tashi sama-sama. Tana buɗe ido ta ganta zaune a falon Daddynsu, a hankali ta fara bin wurin da kallo, ta hango Intisar da sauran ƴanmatan da suke tare da su a ɗakinta. Suna haɗa ido da Intisar ta ji gabanta ya faɗi rass musamman da ta tuna irin gargaɗin da Mai siffar Mama Hasiya ta yi mata, a hankali ta miƙe ba tare da furta komai ba. Tana fita ta nufi sashen Mommy a kan step ɗin bene ta ci karo da Mama Uwani, tana ganinta ta washe baki ta ce, "Barka da hutawa uwar ɗakina." Sama-sama Raihan ta amsa, "Yauwa Mama Uwani ina Mommy take?" Mama Uwani ta nuna ɗakin mommy ta ce, "Tana ciki yanzu na kaiwa baƙi abinci ko na yi miki jagora." Raihan ta dakatar da ita da cewar, "A'a Mama Uwani ki je kawai." Mama Uwani ta yi murmushi tana faɗin, "Hutawarki lafiya uwar ɗakina." Raihan bata amsa ba ta wuce cikin ɗakin. Kafin Mama Uwani ta sauka daga kan bene Intisar ta doshi wurin, kallon-kallo suka fara yi wa junansu don ma mutane na zaune a falon, Mama Uwani ta saki wani malalacin murmushi ta wuce ba tare da ta tanka wa Intisar ba.
Intisar na shiga ta yiwa Mommy sallama don a cewarta za ta tafi gida, amma koda ta yi wa Raihan magana ko ƙurarta bata kalla ba balle ta tanka mata. Tun da ta ga haka ta sha jinin jikinta, don haka tana fita daga gidan ta ɓace daga ƙofar bata tsaya a ko'ina ba sai a tsibirin ƙungiyar asirinsu.
Raihan na zuwa jiki a sanyaye ta zauna, tana son sanarwa da mahaifiyarta cewar Mama Hasiya bata mutu ba amma tana tsoron abin da zai sake faruwa da ita. Tana nan zaune Daddy ya kira wayar Mommy ta waya yake sanar da ita, ɓacewar su Inno da Goggo sannan ta ce ta haɗa duk wani kayan sakawarsu don ya sa a ɗauke su daga gidan da suke zuwa gidansa da ke Unguwar sharaɗa. A cewarsa gidan cike yake da miyagun dabbobi, ba za su ci gaba da zama a ciki ba.
(Abin da bai sani ba duk in da zai je indai yana tare da Raihan tana tare da ZAUJATU JINNUL-ASHIQ😂 Idan kuma yana tare da Mama Uwani yana tare da JINNUL-ASHIQ😂 Mu je zuwa.😎)
Duk yadda Daddy ya so hukunta Kabiru ya ji zuciyarsa ta gagara ɗaukan mataki akansa, sai dai abu ɗaya ya riƙe duk abin da ya samu Raihan sai ya ɗauki mummunan mataki a kansa. A wunin ranar suka tare a sabon gidan Daddy da ke sharaɗa, da sauran ƴan gaisuwa suka tare. Ɗakin da ke jikin gate aka bawa Kabiru, yana shiga ɗakin ya ga akwai komai na buƙata sai dai lokaci guda ɗakin ya rikiɗe masa zuwa tafka-tafkan maciji masu fasalin irin wanda ya kashe a ɗakin Raihan. Yana shirin ja da baya ya ji wani ya faɗ masa a gadon baya lafin ya yi wani yunƙuri, ya fara nannaɗe masa jikinsa.
Intisar na zuwa ta kwashi gaisuwa wurin Hatsabibiya bungulu, bayan ta yi gaisuwa Hatsabibiya ta dubi Intisar ta ce, "Me yake tafe da ke da tsakar rana?"
Fuska ba walwala ta ce, "Hatsabibiya akwai tarin matsaloli domin Huzaifa ya saka ni a gaba, bayan Huzaifa akwai wani bafulatanin maigadinsu da alama zai kawo mana matsala. Amma wanda ya fi kawo mana matsala Huzaifa ne, don haka na ce ba zan yi ƙasa a gwiwa ba sai mun san abin yi don yanzu haka..."
Tun Intisar bata rufe baki ba Hatsabibiya Bungulu ta katseta da cewar, "Duk na ga abin da ya faru har ɗaukan Raihan da ya yi zuwa tsibirinsa." Intisar ta jinjina kai cikin huci tana cewa, "Da alama ya tsoratar da ita kuma a kowanne lokaci tana gabda bijirewa umarninmu."
"Sai mu kashe Huzaifa idan zai kawo mana matsala." Hatsabibiya ta faɗa kanta tsaye ba tare da ji shakku ko shayi ba." A firgice Intisar ta ɗago cikin tashin hankali ta zubawa Hatsabibiya ido, bakinta na rawa ta furta. "Kin manta wanene Huzaifa a wurina? Mijina ne fa." Hatsabibiya ta wara hannuwa cikin halin ko'inkula ta ce, "Ci gabanki ya fi zamantakewarki da shi don haka bana ganin zai amfane ki da komai." Intisar ta turɓune fuska ta ci gaba da cewa, "Ba zan lamince a kashe mijina kuma uban ƴaƴana ba, amma tabbas dole a nemi wata hanyar da za a samu mafita."
🤭 NA SAN DA YAWA ZA KU YI MAMAKIN JIN INTISAR MATAR HUZAIFA CE, KO KUN TUNO MUGAZA😂 ITA CE INTISAR. AMMA MAI YA SA HUZAIFA BAI GANE TA BA HAR SUKE TAKUN-SAƘA, SHIN WACCE RIBA MUGAZA ZA TA CI DA TA JEFA RAIHAN A ƘUNGIYAR ASIRI? IDAN SU MOMMY SUKA KOMA SHARAƊA SUN TSIRA KO DA SAURAN TAFIYA?
Share pls🌚
[7/14, 5:09 PM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*
© *AMEERA ADAM*
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
FREE PAGE 7
Daddy yana tafe Raihan na riƙe a hannunsa har suka shiga cikin gidan ayyane-ayyane yake yi, yana mamakin wane irin macijine da nan take zai naɗe mutum ya kashe shi, kuma a ce ya fito daga ɗakin Raihan ɗin sa. Kwafa ya yi yana tunanin irin matakan tsaron da zai ƙara akan na da, har suka shiga ciki. Mommy jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba don tun lokacin da abin ya faru ta fahimci macijin ɗakin Raihan ba ainihin dabba ba ne. Sai dai a wannan karon ta ci alwashin faɗawa Daddy gaskiya duk irin ɓacin ran da zai yi, don haka suna zuwa ta nemi ganawa da shi a sabon ɗakinsa dama gidan ya gina shi ne da sunan bayan wasu watanni su tare, amma kasancewar ba a gama masa ƙaƙale-ƙaƙale ba ya sa suka dakata da komawar, amma dole ta sa suka tashi a rana tsaka suka koma. A gaggauce Daddy ya dubi mommy ya ce, "Faɗi ina jin ki, kin san yanzu aka yi mini waya wai ankai su Inno da Goggo Hisba dole sai na zo, wani tashin hankali wai an tsinci su Inno a cikin masallacin Malam Isa na ƙarshen layi." Sai a lokacin Mommy ta zaro ido don bata san abin da yake faruwa ba, ganin ta shiga tashin hankali ya sa ya dube ta fuska ba walwala ya ce, "Ba fa wani abu ne na ɗaga hankali ba, komai ya zo da sauƙi yanzu dai ina zuwa." Yana gama maganar ko jiran cewarta bai yi ba ya fice daga ɗakin, jigum Mommy ta yi abu goma da ashirin ya haɗe mata.
Wani irin zafi Kabiru ya fara ji a jikinsa kamar wanda yake gaban wuta, hajijiya ya ji ta fara ɗaukansa ga wata irin matsa da macijin yake yi masa, tun yana daga tsaye har ya durƙushe a wurin yana son furta ayar Allah, amma macijin ya matse masa maƙogaronsa. Kakari ya fara yi kamar wanda ransa zai fita, a zuciyarsa yana son biya ko da ayatulkursiyyu ce amma wani abu mai nauyi ya ji ya tokare masa ƙirji kamar dutse. Yana cikin wannan halin ya ga ɗaya daga cikin macizan ya miƙe tsaye cak ya fasa kai, a hankali fatar jikin macijin ta fara saɓewa tana fita daga jikinsa sai kuma ya fara rikiɗa daga siffar maciji zuwa siffar bil'adam. A hankali wata matashiyar mace ta bayyana ilahirin jikinta gashi ne tun daga kanta har zuwa ƙugunta, ya yin da ƙugunta yake a nannaɗe cikin surar maciji. Harshe ta fara zaro masa nan take wani jaririn maciji ya faɗo, ta damƙe shi a hannunta ta kalli Kabiru da yake cikin mummunan hali ta fara magana, "Kai matashin bafulatani, wa yace maka takun saƙa da ni sauƙi gare shi? Ka san wa ka illata kuwa? Ka san wa ka kashe min kuwa? Ko kana tsammanin ka ci bulus ne?" Kabiru ya ɗago yana sauke numfashi da ƙyar idanunsa jawur ga gumi na ci gaba da tsiyaya daga jikinsa. Baki yake son buɗewa amma ya kasa, ganin haka ya sa ta sake bushewa da wata mahaukaciyar dariya sai da ta yi mai isarta sannan ta fashe da matsanancin kuka, ta jima tana yi sai ta tsagaita da kuka ta sake kallonsa ta ce, "Ba kai kana taƙama da addu'a ba ka yi ta mu gani, har za ka kashe min miji kana tunanin za ka zauna lafiya?" Macijiyar na gama maganar ta fara rarrafowa zuwa gaban Kabiru, ganin ta nufoshi gadan-gadan ya sa Kabiru ya ƙara yunƙura yana ja da baya, ya fara bude baki yana ƙoƙarin karanta addu'a haɗe da motsa baki sai dai ko kaɗan muryarsa bata fitowa, tana tunkararsa hushin numfashinsa ya doki gangar jikinta ba shiri ta ja da baya saboda wani irin zafi da ta ji yana fita daga bakinsa. Kallon-kallon suka fara yi a tsakaninsu, bata daddara ba ta sake yunƙurowa a kashi na biyu da niyyar hallakashi. Duk yadda Kabiru ya kai ga buɗe muryarsa ya yi addu'a abin ya gagara. Dabara ce ta faɗo masa ya fara biya ayatulkursiyyu a zuciyarsa, tana tunkaro shi ya fara tofa masa. Ganin tana niyyar hallaka ya sa ta sake yin baya, nan take macizan da ke gewaye da shi suka ɓace. Ƙaton da ya naɗe shi tuni jikinsa ya saki da ƙyar ya rarrafa ya bi ta jikin bangon ɗakin ya ɓace. Ɗakin Kabiru ya rage daga Macijiyar sai Kabiru, ya yin da ta sake kafe shi da ido tana ƙare masa kallo don ta fahimci makasar da za ta samu a jikinsa ta yi masa illa. A wahalce Kabiru ya faɗi can gefe yana mayar da numfashi, jikinsa gabaɗaya ya yi ja saboda irin tsananin matsar da macijin ya yi masa. A hankali jikinsa ya fara raɗaɗi, yana kai idanunsa kan fatarsa ya lura da yadda ta fara sauya launi zuwa fatar maciji. Macijiyar kallon Kabiru ta yi ta fara ƙyaƙyacewa da wata irin shu'umar dariyar ƙeta, hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya yi da ganin abin da yake faruwa da fatar jikinsa ba. Yana tsaka da tunani ya riski muryar macijiyar tana faɗin, "Ka kashe min mijina ba tare da wani dalili ba, Huzaifa ya nemi tallafin mijina akan ya zo taimakonsa ka kashe shi, zafin mutuwarsa ta sa na ji tamkar na kashe ka amma ba zan kashe ka yanzu ba sai na gama wahalar da ruhina da gangar jikinka sannan na hallaka da hannuna. Ka je ko da wannan hallitar fatar macijin na barka ƙuncin rayuwar duniya ya ishe ka." Tana gama maganar ta sake naɗewa ta koma murtukekiyar macijiya, juyi ta fara yi daga wurin da take nan take ta baje a ƙasa ta fara nutsawa cikin ƙasa har ta ɓace ɓat. Ilahirin jikin Kabiru ban da rawa babu abin da yake yi, babban tashin hankalinsa yadda ya ga fatar jikinsa ta koma ta maciji illa iya fuskarsa, hannu da ƙafarsa ne kaɗai basu rikiɗa ba da yake macijin bai taɓa masa nan ba.
A fusace Hatsabibiya ta ɗago da ta sake kallon Intisar ta ce, "Idan ba mu kashe shi ba kina da hanyar da za mu ɓullo masa? Ko kuma kina da shawara akan yadda za mu kawar da tunaninsa akan Raihan?" Intisar ta yi shiru tana nazari don ita kanta ta san wanene Huzaifa da tsananin bincike irin nasa, ta san tun da ya kafa mata ƙahon zuƙa dole zai bi diddigin wacece ita da asalinta. Ta san muddin ya gano ta ba ƙaramar ƙura ce za ta tashi a tsakaninsu ba, a baƙar zuciya irin tashi yana iya hallakata. Don ma tana amfani da sirrin tsafi da sihiri ko a yanzu yadda ya ɗora ransa akan Raihan da tuni ya gama da ita. Tana cikin tunani ta sake riskar muryar Hataabibiya ta ci gaba da cewa, "Idan har baki da wata dabarar ga tawa shawarar." Intisar ta dubi Hatsabibiya tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ina jin ki Uwargidana maganin kukana, da ke da Abar bauta ku kaɗai na dogara da ku duniya da lahira (Wa'iyazubillah) ke kika saba ɗauke min duk wata damuwata a yanzu ma ina biye da ke don jin mafitar da za ki kawo mana kafin abar bauta ta bayyana."
Hatsabibiya kanta ya sake girma, ta miƙe daga wurin da take ta ɗauki wani dogon ƙaho mai faɗi da tsawo ta kafa shi a bakinta sannan ta durƙushe a gurin. Ta kafa tsinin ƙahon a doron ƙasa sannan ta busa shi da ƙarfinta, lokaci ɗaya tsibirin ya ɗauka tsananin ƙararsa kamar zai tsaga dajin gida biyu. Tun bata rufe baki ba aljanu masu ɗauke da munanan hallitu suka fara fitowa wasu daga ƙarƙashin ƙasa wasu daga cikin duwatsu ya yin da wasu suka fara fitowa daga ɗakin tsafi. Kafin wani lokaci tuni sun taru suna masu sujjada a gabanta, tare da yi mata kirari kamar yadda suka saba sannan suka ƙame wuri ɗaya suna jiran umarninta.
Wani irin kuka haɗe da dariya ne ya fara tashi, lokaci ɗaya tsibirin ya fara girgiza suna nan tsaye wannan mummunar hallitar mai ɗauke da kawuna (Abar bauta.) Ta ziro kawunanta zuwa harabar wurin da take. Suna yin tozali da ita suka kwanta a wurin har hatsabibiya suna masu yi mata sujjada, haɗe da kirari. Kafin ƙiftawar ido Wani baƙin aljani ya dira a gabanta cikin girmamawa yana tambayarta.
"Ya ke uwargijiyata shin jariri kike buƙata, uwar jariri tsoho ko tsohuwa kike buƙata." Ɗago da kawunanta ta yi, sai ta saki kuka kamar na bujimin sa. Jin kukan San ya sa aljanin sake rissunawa yana faɗin, "Kin samu kin gama." Yana gama maganar ya ɓace daga wurin.
Kallonsu ta yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta fara magana da murya mara daɗin sauraro, "Duk abin da kuka tattauna mun saurara don haka babu amfanin maimaitawa sai zartar da hukunci." Jikin Intisar tuni ya fara tsuma nan take gumi ya rufe ta, don bata san irin hukuncin da Abar bauta za ta yanke a kan Huzaifa ba. Tana tsaka da nazari ta riski muryarta tana ci gaba da cewa, "Ba za mu kashe Huzaifa ba sai dai dole a sauyawa taku salo, sanin kanku ne a da ɗanyan kifi yana haukatata. Sakamakon ɗan da ta haifawa Huzaifa yana da haɗin jinsi da hallitar kifi. A yanzu za mu sake haukatata fiye da lokacin baya, a cikinku waye zai iya aiwatar da abin da muke buƙata?" Wata aljana da ta miƙe tsaye tana faɗin, "Abar bauta zan riƙa haukatata da surar mahaifiyarta..." Tun bata rife baki ba Abar bauta ta katse ta cikin tsawa tana cewa, "Kina tunanin wannan mafita ce? Idan kika yi haka dole za su nema mata lafiya, mu kuma duk wanda zai nuna hanyar lafiyarta sai mun tsotse jininsa." Haka aljanun da ke wurin kowa ya riƙa ɗaga hannu yana faɗin abin da zai aiwatarwa Raihan. Duk acikinsu shawarar guda biyu aka ɗauka, ɗaya daga ciki ya ce zai riƙa shiga jikin maguna yana haukatata, sai wacce ta ce za ta riƙa shiga jikin ƙadangaru sai dai kowanne da abin da zai aiwatar.
Abar bautarsu ta ji daɗin abin da suka yi, don haka ta yi na'am da wannan shawarar. Suna nan zaune aljanin da ya tafi ɗauko mata jinin da za ta sha ya dawo hannunsa ɗauke da wani Dattijon tsoho, suna shigowa tun ba su ƙarasa gaban abar bauta ba, ta miƙa hannunta guda ɗaya ya warto Dattijan haɗe da ƙwaƙule masa ido tun bai ƙarasa gabanta ba ya yi fata-fata da shi, sauran kawunan da ke jikinta suka kafa kawunansu nan take suka gama da Tsohon. Aljanin ya sake russunawa yana faɗin, "Abar bauta ya isa ko a ƙaro wani." Gyatsa ta yi, tana lashe jinin bakinta, sai da ta tsotse ƙashin ƙoƙon kan tsohon sannan ta ɗago ta ce, "A ina ka samu wannan hallitar mai daɗi?" Aljanin ya washe bakinsa yana murmushi bakinsa ya yi girman rijiya saboda wannan ne karona na farko da abar bauta ta yabi naman ɗan'adam. Ya russuna yana faɗin, "Fansar iyayena na mallaka miki abar bauta, ki fanshi wanda kike so. Ke kika hallakawa kike tseratarwa kike kashewa kike rayawa, na samu hallitar bil'adam a cen bakin wata ƙatuwar bola fitowarsa kenan daga wurin Boka Harisu, yana shirin saka laƙanin asirin da aka bashi a ƙarƙashin shara na ɗauko maka shi." Hatsabibiya ta sake kallon wurin da ƙoƙon kan Dattijon yake tana hura masa iska nan take ƙoƙon kan ya fara mirginawa, har sai da ya yi sau uku sannan hallitar tsohon ta sake dawowa kamar yadda take har da kayan jikinsa. Abar bauta ta kalli Aljanin da ya kawo Dattijon ta ce, "A ɗauke shi a mayar da shi wurin da yake rana ita yau a sake dawo min da shi jinin jikinsa bai ishe ni ba." A firgice tsohon ya kalle su nan take jikinsa ya hau tsuma, ya tsugunna yana roƙo da magiyarsu, yana cikin haka ya ga anɓace da shi daga wurin.
Abar bauta ta dube su ɗaya bayan ta ce, "Na wakilta guda ɗaya daga cikinku da ƙadangare da mage, kuma ya zama wajibi a yau ba sai gobe Raihan ta kawo mana ziyara, shi kuma Huzaifa ku bar min lamarinsa a hannuna amma ba zan cutar da shi ba ko halaka shi alfarmar Mugaza da take kawowa ƙungiya ci gaba." Wata gwauruwar ajiyar zuciya Intisar/Mugaza ta saki tana lumshe ido, ɗaya bayan ɗaya suka fara darewa daga wurin, Hatsabibiya ta yi wa abar bauta rakiya zuwa turakarta sannan ita ma ta ɓace daga wurin.
Daddy shi da abokinsa Alhaji Mustafa suka ƙarasa ofishin Hisbar da su Inno suke, yana zuwa ya samu su Inno a zaune duk sun yi zuru-zuru kamar waɗanda suka wuni suka kwana basu ci ba, musamman Inno da take tsaka da jin mutuwar Hasiya. Suna ganinsa Inno ta fashe da kuka ta kalli ɗan hisbar da ke gefe tana faɗin, "Amma dai kai ƙaramin ɗan sanda Allah ya watsa maka albarka, wallahi ku bar ni a ofishinku amma ni da gidan Audullah sai a lahira ma sadu da juna." Daddy yana shirin yin magana Goggo ta tsugunna a gaban ɗan hisban ta ce, "Yaro ka dubi Allah ka dubi Ma'aiki ko tasha ne ka kaini na wuce albasu." Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Inno me yake faruwa zuwa na yi mu tafi fa." Inno sunne kai ƙasa ta yi kamar ba ta ji me yake faɗa ba, ta kalli Goggo ta ce, "Don Allah ki duba min hallitar jikin Audullahi ta cika ko akwai nasaka, ada na ƙaryata ki amma Allah ya sani gidan Audullahi Makarai ne suke cin karensu babu babbaka a ciki." Daddy zai yi magana ɗan hisbar ya dakatar da shi, don labarin abin da ya faru tuni ya karaɗe ko'ina musamman da ƴan jarida suka samu zancen yaɗawa, Likitoci suka shiga binciken gawar Sulaiman a ya yin da suke neman Kabiru babu inda ba a duba ba amma basu ganshi ba.
Ɗan hisban da kanshi ya yi wa su Inno nasiha, ya sake faɗarkar da su da cewar duk wani abu yana faruwa ne da izinin Ubangiji kuma addu'a takobin mumini ce. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu su Inno suka bi Daddy gidan har sai da ya tabbatar musu da cewar ya sauya musu wurin zama.
Lokacin da su Inno suka koma gida tuni gidan ya yi shara-shara babu mutane sosai, don tun a tsohon gidansu ganin abin da ya faru ya sa mutane da dama kowa ya yi ta kansa. Su Goggo a ɗaɗɗare suka shiga sabon gidan, suna tafe bakinsu na motsi da alama addu'a suke yi don ba ƙaramin tsorata suka yi ba. Mommy da kanta ta kaisu ɗakinsu, kowacce ta zauna shiru don ƙawayensu da suka zo gaisuwa tuni kowacce ta cika wandonta da iska.
BAYAN MAGRIBA.
Raihan na kwance a ɗakin mommy lamo kamar mara lafiya, don gabaɗaya wani sukuku take jin ta kamar ba ita ba tun da ta dawo daga duniyar aljanu. Tana daga zaune ta ga wurgawar abu, da sauri ta tashi zaune tsigar jikinta na tashi. Wani ƙadangare ta gani yana buɗe mata baki alamar dariya, sai kuma ya fara ƙada mata jela yana yi yana tunkarota. Ƙura masa ido ta yi lokaci ɗaya ta miƙe tsaye, ta fisge ɗankwalin kanta nan take gashin kanta ya hargitse, ƙananan kifaye ne suka fara fita daga bakin ƙadangare. Lokaci ɗaya ta yi kukan kura ta fisgoshi haɗe da ƙwalla uwar ƙara, tana ɗaukansa ta tura kansa cikin bakinta nan take ta fisge masa kai ta wurgar a wurin gangar jikin ƙadangaren yana hannunta. Mommy da wata ƙanwarta har rige-rigen shiga ɗakin suke saboda duk wanda yake gidan babu wanda bai ji ihunta ba. Suna tura ƙofar suka ganta a tsaye tana riƙe da gawar jangwalagwada jini yana ɗiga, ga kansa can gefe sai zare ido take tana faɗin, "Duk wanda ya ce zai hallaka mini Ɗana wallahi sai na fidda masa kai.
🤭🤭🤭🤭 WUYAR AIKI BA'A FARA BA, HAR YANZU FA ASHAFI NA BAKWAI AKE😎😎 KUN GA KUWA AKWAI SAURAN TAFIYA, AKWAI ƘURA A GABA.🤸🏻♀️💃🏼
Share Hilis🌚
[7/16, 12:01 PM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*
© *AMEERA ADAM*
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
FREE PAGE 8
Ilahirin jikin mommy rawa ya ɗauka Aunty lubna ta zaro ido hankali a tashe don ko a mafarki bata taɓa cin karo da wannan mummunan abin da Raihan ta aikata ba. Mommy tana son tunkarar Raihan amma tana gudun hukuncin da za ta zartar a kanta, murya na rawa ta dubi Raihan ta ce, "Raihan lafiya me kike yi haka? Ƙadangare ne fa a hannunki." Raihan da har lokacin idonta jawur suke ta sake kai kallonta kan ƙadangaren hannunta, ta sake saka wurin jelarsa a baki ta cisgeta da ƙarfin tsiya ta kalli saitin da su Mommy suke ta tofar a wurin. Wani irin huci ta fara yi idanunta na sake firfitowa ta ce, "Ɗana yake shirin cinye min don haka dole na hallaka shi." Mommy ta tunkari wurin tana son Raihan ta wurgar da ƙadagaren hannunta amma tsoron abin da kaje ya zo ya hanata. Don a lokacin da take da shekara goma ntana da makamancin ciwon ta ya tashi ta taɓa cirewa wani almajiri ɗan yatsa, a lokacin shi ma zuwa ya yi zai ƙwaci agwagwar malaminsu da ta fito kiwo Raihan da Mommy sun fito daga mota, a lokacin da suka kai ziyara Albasu. Tuno da haka ya sa mommy take son tunkararta amma tana jin tsoro. Daga nesa da ita Mommy ta leƙa fuskarta tana faɗin, "Raihan ki yarda abin hannunki." Cikin wani irin ƙaraji ta nufo wurinsu gadan-gadan da ihu tini ba shiri su Mommy suka fice a guje kowa yana gudun ceton ransa.
Hankali a tashe mommy ta nufi sashen Daddy tana ƙwala masa kira. A bakin ƙofa ta ci karo da shi tana ganinsa ta fara nuna masa hanya tana faɗin, "Alhaji Raihan ce..." Maganarta ta maƙale saboda yadda take sauke ajiyar zuciya. A zabure Daddy ya kama kafaɗarta yana jijjigawa yana faɗin, "Me ya samu Raihan ɗin ki faɗa min tana ina?" Hanya ta riƙa nuna masa tana faɗin, "Tana can ta tsintsinka ƙadangare da haƙoranta." Da gudu ya nufi hanyar ɗakin Raihan hankali a tashe. Nan take ragowar mutanen da ke cikin gidan suka yi tsilli-tsilli, kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci tana cikin matsanancin tashin hankali.
Daddy kai tsaye ɗakin da Raihan take ciki ya tunkara yana shiga ya same ta a cen gefe ta faɗi da alama bata numfashi. Kallon ɗakin ya fara yi saboda yadda jinin ƙadangaren ya ɓata saman carpet ɗin ɗakin, daga gefen hannunta ya hangi gangar jikin ƙadangaren hannunta ya jiƙe sharkaf da jini. A hankali ya ƙarasa wurin ya mirgino da ita yana ambatar sunanta muryarsa a raunace, shiru ne ya ratso a ɗakin babu abin da yake tashi sai karar AC da saukar numfashin Daddy. Tsugunnawa ya yi a gabanta ya tallafo da kanta zuwa kan cinyarsa, murya na rawa ya furta: "Me yake samunki ne Raiha? Me ya sa waɗannan abubuwan suke faruwa da ke?" Kuka ne ya ci ƙarfinsa ya kafa kansa a jikinta yana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Daga bakin ƙofa Mommy ce ta shiga jiki a sanyaye, ita kanta lamarin Raihan ya fara bata tsoro. Kusan shekara goma sha biyar kenan suna fama da abu ɗaya, babban tashin hankalin da ciwon kullin gaba yake yi baya raguwa. A sanyaye ta zauna a gefen Daddy ta ce, "Daddyn Raihan." Ɗagowa ya yi ya dube ta idonsa na ci gaba da zubda ƙwallah, ita ma hawaye ne ya fara zuba a fuskarta ta sa hannu ta share sannan ta ci gaba da cewa, "Ka daina kuka don yanzu babu buƙatarsa a gurbin halin da muke ciki..." Tun bata rufe baki ba Daddy ya katseta da cewar, "Ido yana zubda hawaye ne ba don gangar jiki da ruhi suna buƙata ba, sai don samun sauƙi ga raɗaɗin ƙunan zuciya. A da na ɗauka rashin haihuwa babban masifa ne a gare ni sai ga shi a yau na wayi gari Allah ya bani gudan jinina ga kuma masifar da tafi min rashin haihuwar..." Da sauri Mommy ta rufe masa baki tana girgiza kai ta ce, "Bai kamata ka riƙa furta irin kalmomin nan ba, domin duk abin da ya samu bawa yana daga Ubangiji shi ya fi mu sanin dalilinsa na yin haka." Mommy ta numfasa sannan ta ci gaba da cewa, "Ya zama wajibi ciwon yarinyar nan a koma yin da Islamic don wannan yana da alaƙa da shafar aljanu..." A razane ya katse ta yana faɗin, "Kina hauka ne? Na gargaɗe ki da ki daina danganta jinina da jinsin aljanu." Wanna karon mommy ita ma hassala ta yi ta ci gaba da cewa, "Kar ka sake furta kalma ta ƙasƙanci a kaina, don duk taƙamar da kake yi ba kai kaɗai ka haifeta. Raihan ƴata ce idan kai ba za ka nema mata maganin Islamic ba dole ni zan nema mata." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin, Daddy ko a jikinsa tana fita ya ɗauki waya ya kira likitan da ke duba Raihan, zayyana masa komai ya yi sannan suka yi sallama ya ci gaba da zubawa Raihan ido yana tunane-tunane a zuciyarsa.
Lokacin da Macijiyar ta ɓace daga ɗakin Kabiru, daga gefen hagunsa ya fara jin wani irin gurnani irin na riƙaƙƙun kumurcin maciji, a hargitse ya sake miƙewa yana kalle-kalle bakinsa na furta Amanarrasulu don a tunaninsa macijin ne zai sake bayyanar masa. Ya jima yana jin wannan gurnanin daga baya ya ji shiru komai ya ɗauke daga dodon kunnensa, daga jikin hannun rigarsa wata fata ya ga ta kwakkwaɓo irin saɓar fatar maciji wacce yake yi. Da sauri ya ɗago ta cikin tashin hankali don lamari ya fi ƙarfin tunaninsa, ido ya zurawa gwiwar hannunsa ta wurin da fatar ta faɗo ya ga wurin ya sake yin sheƙi tamkar bayan maciji. Kwalla ce ya ji ta zubo masa saboda duk wanda ya lura da halin da yake ciki ba zai taɓa zama a kusa da shi ba, kallo ɗaya za ka yi wa jikinsa ya firgita ka don bambamcinsa da maciji kai, hannu da ƙafafuwa. A hankali ya ƙarasa wurin buhun kayansa, nan take ya fara zazzagewa yana birkito kayan da zai saka don ya rufe jikinsa. Sanin kansa ne ko masu aikin gidan suka fahimci halin da yake ciki zamansa a cikin gidan ya ƙare balle kuma a ce Alhaji ya lura da yadda surar jikinsa ta koma. Sai da ya tura ƙofarsa ya rufeta ruf don kar wani ya turo, sannan ya tuɓe rigar jikinsa da yake mai gajeren hannu ce. A jikin mudubin ya tsaya yana ƙarewa jikinsa kallo fatar jikinsa ta koma sak irin ta maciji, wani hawayen ne ya sake gangaro masa ya sa hannu ya share sannan ya ɗauko wata tsohuwar rigar shadda mai dogon hannu, ya ɗauko wani tsohon mayafinsa da wanda ya gada a wurin mahaifiyarsa ya naɗe wuyansa da shi. A jikin bango ya jingina a fili ya fara magana cikin karyewar zuciya, "Allah sarki Baffajo ba don rashin lafiyarka ba, da babu abin da zai hanani barin wannan gidan, don da alama wannan ba wurin zama ba ne." Kabiru ya ɗaga hannu sama ya ci gaba da cewa, "Allah ka bawa Baffajo lafiya, da yardar Allah sai na bar gidan nan don na nemawa kaina lafiya." Daga gefensa ya ji an bushe da dariya, yana juyawa ya hangi matashiyar budurwa tana tsaye tsirara babu kaya a jikinta. Hannuwa biyu ta wara masa tana faɗin, "Ina da hanyar da zan kawo maka mafita matuƙar za ka bani dama." Kabiru ya kauda kansa gefe yana faɗin, "Wa'iyazubillah." Ɓangaren da ya juya fuskarsa ta sake komawa tana faɗin, "Indai akan matsalar abin da ya faru da jikinka ne zan warkar maka da shi matsawar za ka bani haɗin kai." Kabiru ya ɗago da kansa yana shirin yi mata magana, karaf idonsu suka haɗu wuri ɗaya nan take ya ji tsigar jikinsa na tashi. Da ƙyar ya iya saita kansa sannan ya furta, "Ki taimaka min ki raba ni da wannan fatar macijin, ki gaya min me kike buƙata daga wurina yanzu na aiwatar miki?"
Duk wani shige da fice da su Mommy suke yi akan idon Mama Uwani, lokacin da ta ji labarin abin da ya faru ta shiga tashin hankali don ta san wannan abin da Raihan ta aikata baya daga cikin abubuwan da take saka Raihan tana aikatawa. Fitowa ta yi ta fara kaiwa da kawowa nan take wata dabara ta faɗo mata, sai da ta shige ɗakinta da yake babu kowa a ciki sannan ta ɓace daga ɗakin. A lokacin da ta ɓace Dr Hamza yana gidansa ya gama shiri don zuwa gidansu Raihan, Huzaifa na zuwa da ya ga haka don kar ya kawi masa matsala ya bige shi a kan gado nan take bacci ya yi gaba da Dr Hamza. Cikin siffar Dr Hamza ya kira lambar Daddy bugu ɗaya kawai ya yi ya ɗauka, a gaggauce Daddy ya furta, "Dr ka ƙaraso ne?" Huzaifa da ke ɗauke da surar Dr Hamza ya amsa masa, nan take Daddy ya bashi umarni da ya shiga. Daddy da Huzaifa a harabar gidan suka haɗu, Huzaifa sai murmushi yake ƙasa-ƙasa don ko ba komai ya samu damar da zai aiwatar da abin da yake ransa. Suna shiga Raihan tana nan kwance kamar gawa bata numfashi ko hannunta baya motsawa, ido ya zura mata yana son sanin musababbin abin da ya sa ta tsinka ƙadangare gida biyu don ko kaɗan babu sa hannunsa a ciki. Yana tsaka da nazari ya riski muryar Daddy yana faɗin, "Dr don Allah ayi wani abu ciwon nan sai ƙara gaba yake yi." Huzaifa ya miƙe tsaye yana zare gilashin idonsa, ya yi jim kamar wanda yake damuwa sannan ya fara magana, "Gaskiya yanayin ciwonta ya fara bani tsoro Alhaji, amma abin da ya fi akwai wani abokina a India ina tunanin sai an fita da ita, amma a yanzu zan yi bakin ƙoƙarina na ga ta dawo daidai kafin wani lokaci. Amma idan ba shawo kan matsalar aka yi ba lamarin zai rinƙa yin gaba, tun da sannin kanmu ne a da ciwonta bai yi tsanani haka ba." Daddy kamar jira yake ya ce, "Hakan ma ya yi min daidai, abin da ya sa ma ban sake tunanin fita ba saboda ka san ba irin yawon da ba mu yi ba tun Raihan tana ƙarama."
Hamza yana shirin yin magana Inno ta turo ƙofa tana tafe Goggo na biye da ita, Inno cike da faɗa tana faɗi:
"Saboda Allah haka kawai ace duk wani tashin hankali bai faru ba sai a ranar da Ƴata Hasiya ta kwanta dama, ina dalili yarinya sai rikiɗa take kamar wahainiya. To Allah ya sani idan ban watsa mata albarka ba Mamman mai ƙawa'idi bai haife ni ba, ku bar ni yau ko ni ko Rihanu a gidan nan." Daddy ya waiga wurin Inno da niyyar zai yi magana, suna gano halin da Raihan take ciki da sauri su goggo suka yi baya cike da tashin hankali. Goggo ta dafe ƙirji jikinta sai tsuma yake yi kaɗan ya rage fitsari bai zubo mata ba, ta nuna wurin da Raihan take ta fara faɗin, "Laƙadi ja'akum yau na shiga uku. Allah ya sani duk garin Albasu babu mayya ko guda ya aka yi aka samu maita a zuri'ata, a'a wannan lamarin dole akwai ayar tambaya wallahi idan Raihanu bata shiga ƙungiyar asiri ba Na koma Albasu a ƙafa." Huzaifa ya waigo wurinsu yana faɗin, "Iya don Allah ku yi shiru ina kan Patient bana buƙatar hayaniya." Inno ta riƙe haɓa saboda takaici don gani take abin nasa kamar har da cin fuska, ƴarta ta mutu ba a yi zaman makoki yadda ya kamata ba kuma a kawo mata maganar Patient. A zuciye ta ƙarasa gaban Huzaifa sai da saita daidai fuskarsa ta wara hannunta a kai tana faɗin, "Ƙaniyarka ka ji, fitsararre kana fama da fuska kamar teba." Huzaifa ya kalli Inno a zuciyarsa yana ayyana idan da ya ga dama wurgi ɗaya zai yi da ita ta baje a ƙasa. Bai dawo daga tunani ba ya ji ta sake nuna shi da yatsa tana ci gaba da cewa, "Kai baƙin munafuki ka gaya min idan da ƴarka ce ta musu waɗannan masifun suke faruwa me za ka yi?" Daddy ya zagayo ta wurinta yana cewa, "Inno don Allah ki yi haƙuri shi fa wannan babu ruwansa a ciki." Goggo ta leƙa fuskar Huzaifa tana kwaɓe baki ta ce, "Akan wannan baƙin munafukin kake shiga gaban mahaifiyarka?" Ta waiga wurin Huzaifa ta ci gaba da cewa, "Wallahi ka fito ka gaya masa gaskiya ko na watsa maka albarka, ka san dai ciwon Yarinyar nan bana mai jan kunne ba ne." Huzaifa ya dubi Daddy kamar abin bai dame shi ba ya ce, "Alhaji a kawo min ruwa." Daddy na jin haka da sauri ya fita daga ɗakin, yana fita Huzaifa ya warto su Inno a hannu ya matse su wuri ɗaya. Kamar waɗanda aka naɗe su da igiya aka ɗaura haka su Goggo suka ji, suna shirin yin ihu bakinsu ya yi musu nauyi. Sai da ya yi hajijiya da su sannan ya watsa su can gefe kamar kayan wanki, zannuwa da ɗankwalen su Inno tuni suka maƙale a saman fanka.
Lokacin da Raihan ta faɗi a lokacin ne Abar bauta ta bada umarnin ga Raihan da ta kawo mata ziyara, nan take ruhinta ya fita daga jikinta zuwa tsibirin da ƙungiyar asirinsu take. Tana zuwa ta russuna ta yi gaisuwa ga Hatsabibiya, a take ta turɓune fuska ta dubi Raihan tana faɗin, "Mun aika kiran gaggawa ne don Abar bauta na buƙatar ku sha jinin mai naƙuda tare da ke, kuma yau ita ce ranar da za a yi miki wankan tsarki dole ke ce za ki kawo mana jinin da za mu sha daga jikinki, Muna buƙatar jinin mahaifiyarki daga yau zuwa gobe idan ba haka ba Abar bauta za ta iya yi wa danginki ɓarna." Ruhin Raihan wata irin zabura ya yi da jin wacce aka ce ya kawo daga cikin danginta, sai dai hakan bai hanata amincewa da buƙatarsu ba. Cikin girmamawa Raihan ta russuna tana faɗin, "Fansar Mahaifana yana gare ku na baku wuƙa da nama, mai naƙuda a ko'ina take zan kawo mana ita yanzun nan." Tana gama maganar ta bi ta iska ta fice daga tsibirin.
Ruhin Raihan na fita bai tsaya a ko'ina ba sai cikin wani babban asibiti, kai tsaye daƙunan majinyata ta fara shiga har za ta fice ta hango wata tsohuwa da alama tana jin jiki, a kan ruwan cikinta ta dira har ta kafa bakinta za ta tsotsi jini majinyaciyarta ta ƙaraso gabanta tana karanta mata ayatulkursiyyu tana tofa mata saboda tuni sun samu bacci ya ɗauketa, ta karanta mata addu'a saboda ita ma bacci take son yi. Da sauri Raihan ta tashi daga kanta ta matsa gefe tana sauke numfashi, daga can gadon ƙarshe ta hango wata mara lafiya bata jinkirta ba ta hau kanta tuni ta kafa bakinta a kanta ta fara zuƙar jini. Nan take jikin matar ya rikice ganin haka ya sa majinyaciyarta kiran nurses, sun kai mutum huɗu a kanta duk yadda suka kai ga bakin ƙoƙarinsu abin ya ci tura, nan take rai ya yi halinsa. Raihan na ganin haka miƙe ta fice daga ɗakin kai tsaye ta wuce can ɗakin haihuwa. Raihan na shiga ta hangi mata kusan uku masu naƙuda, a kan idonta ɗaya ta haihu ta cikin mutum biyun ta dira a gadon ta tsakiya. Tana niyyar kafa kanta a ƙirjinta daga bayanta ta ji an ce, "Jinin Matata ya fi ƙarfinki." A zabure ruhin Raihan ya waiga don ganin wanda ya dakatar da ita ga abin da take shirin aiwatarwa.
A MIN SHARE FISABILILLAH🌚
[7/18, 4:07 PM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*
© *AMEERA ADAM*
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
FREE PAGE 9
Rangaji ta fara yi tamkar bishiyar dalbejiyar da take kaɗawa da iskar damuna, a hankali Kabiru ya ɗan fara ja baya don ko kaɗan hankalinsa bai kwanta da ita ba. Cikin wata irin murya mai jan hankali ta fara magana, "Ka amince min da buƙatata ƙwaya ɗaya ce tal na yi maka alƙawarin yaye maka wannan matsalar da take jikinka." Kabiru da yake jin wani abu yana yawo a zuciyarsa game da ita ya runtse idonsa sannan ya fara magana cikin wata irin kasalalliyar murya, "Ba na buƙatar ganinki cikin wannan yanayin." Tun bai rufe baki ba ta ƙarasa wurinsa ta sa hannu tana ƙoƙarin taɓa shi ta furta, "Laƙani aka bani domin cikar burina a kan Daularmu ta Daulatul jinnul-Turabiy. Idan har ka amince min za ka kusance ni kuma zan warkar da kai, idan ka yi min haka zan mallaki Daularmu da abin da yake cikinta, na zo a sirrance ne ta sanadi ƴar uwata wacce ta yi maka haka..." Tana tsaka da magana ya katse ta da furta, "A'uzubillahi minnasshaiɗanirrajim." Da sauri ta ja da baya tana hakki saboda yadda ta ji wani irin hucin zafi daga jikinsa. A hankali ya tattaro jarumta ya ci gaba da karanta ayoyin kariya da duk wata addu'a da ya san ya taba biyata. Nan take ta ɓace daga gabansa don yadda take ji tamkar zai halakar da rayuwarta, ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa saboda yadda hankalinsa ya sake tashi fiye dana da. A wannan lokacin ya yanke ƙauna don ji ya yi zama a gidan ya fice masa daga rai, gani yake zai iya haƙura da zaman gidan idan ya so duk wata sana'a da ya sani zai fita ya nema don ganin ya ci gaba da nemawa mahaifinsa lafiya. Yana gama nazarin ya miƙe ya ɗauki buhun kayansa, sai da ya leƙa ta window ganin hankulan mutane baya wurinsa ya sa ya yi zaraf ya fice daga ɗakin sannan ya zare sakatar gate ɗin ya fice daga gidan. Gudu-gudu sauri-sauri haka Kabiru ya fara tafiya, kasancewar unguwar shiru babu mutane ya sa bai haɗu da kowa a hanya ba, ta bayan wata doguwar katanga ya raɓa yana tafiya ba tare da ya san inda yake saka ƙafarsa. Yana tsaka da tafiya ya ji ya ci karo da mutum a gabansa, a hankali ya fara ja baya yana ƙoƙarin sake hanya ya ji mutumin da suka yi karo da juna yana faɗin, "Assalamu alaikum." Kabiru da ya fara tsorata a ɗan ja da baya sannan ya amsa masa sallamar, don gabaɗaya a rikice yake. Mutumin da har lokacin Kabiru bai tantance ko shi waye ba ya ci gaba da cewa, "Bawan Allah da wa ka dogara?" Kabiru ya fara sakin jikinsa don ya fahimci ɓoyayyan baƙonsa ne, murya can ƙasa ya ce, "Da Allah na dogara." Mutumin ya ƙara taku biyu zuwa gaban Kabiru ya ce, "Ka dogara da shi a ko'ina kake shi zai isar maka." Kabiru ya jinjina kai yana shirin yin magana, mutumin ya ci gaba da cewa: "Ina ƙaunarka fisabillahi don haka zan baka shawara karka ji tsoron kowa idan ba Allah ba." Kabiru na jin haka ya zaburo da sauri da niyyar kama hannun mutumin yana faɗin, "Don Allah wanene kai da kake yawan zuwa kana gaya min maganganu masu daɗi, da shawara akan al'amuran rayuwata?" Tun bai ƙarasa wurinsa ba mutumin ya ɓace, da sauri Kabiru ya hau waiwaye don neman wurin da zai ƙara ganin ɓullowarsa. Daga can bayansa ya ƙara jin muryarsa yana faɗin, "Karka damu da sanin wanene ni domin mai ƙaunarka na tare da kai a koyaushe, ni masoyinka ne ina mai ƙara tunasar da kai muhimmanci dogaro ga Allah." Yana gama maganar ya sake ɓace wa daga wurin. Jiki a sanyaye Kabiru ya jingina a jikin katangar, ban da kukan kwaɗi da ƙananan ƙwari babu abin da yake tashi a wurin. Lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa ta aminta da nasihar da bawan Allahn nan ya yi masa, nasihar da Mahaifinsa yake yi masa ta sake dawo masa, a fili ya fara furta Astagfirullah sannan ya koma ya nufi hanyar gidansu Raihan.
Inno kusan suma suka yi ban da juwa babu abin da suke ji, Huzaifa ya ƙarasa gabansu ya ya zaro musu ido. Suna haɗa ido suka ga ƙwayar idonsa na ci da wuta, kakin yawu ya yi ya tofar a kan tafin hannunsa nan take wuta ta tashi. Goggo tuni ta saki fitsarin da take matsewa ta sunne kai ƙasa cikin tashin hankali, Huzaifa ya buga musu tsawa yana faɗin, "Duk wacce ta sake gangancin shiga lamarin Raihan sai na banka mata wuta ta ƙone ƙurmus, kuma duk wacce ta sake ta furta wata magana a kaina da abin da ya faru sai na hallata shi cikin dare." Huzaifa ya ɗago ya damƙi wuyansu sannan ya ci gaba da cewa, "Kuma duk wacce ta ce za ta bar gidan nan tana fita zan ɗaye fatar jikinta." Inno da idonta yake runtse ta ce, "Babana mun gode, ko a ɗakin nan ka ce mu dauwama har ranar mutuwarmu mun bar sauka ƙasa." Huzaifa bai bi ta kansu ba ya ɗebe su ya watsa a saman fanka, sai ga su Inno a maƙale jikin fanka sai ciccila ƙafafuwa suke yi. Sai da suka jigata sannan ya miƙa hannunsa ya ɗauko su yana nuna musu zannuwansu dake can gefe ya ce, "Maza ku ɗaura zaninku ku fice daga ɗakin nan." Tun bai rufe baki ba Su Inno suka fara wawurar zannuwansu suna yi suna layi kamar waɗanda suka maku saboda juwar da take ɗibansu. Suna zuwa bakin ƙofa Daddy ya turo ya shigo mommy tana biye da shi Inno ta kusa tafiya luuuu za ta faɗi da sauri Daddy ya ruƙota yana faɗin, "Inno lafiya?" Inno ta fisge jikinta tana faɗin, "Sake ni ka ji Audullahi, jeka kan Raihanu Allah dai ya watsawa Likitanan albarka." Daddy ya yi murmushin jin daɗi don ya ga sauyi a wurin Tsofaffin saɓanin kafin fitarsa da ya tafi suna kwashe wa Likita albarka. Su Inno na fita suka zube a bakin ƙofa suna mayar da numfashi, Goggo ce ta fara rarrafawa tana sauka daga ƙafar bene, Inno ta leƙa tana faɗin: "Kai jama'a yanzu a daren nan za ki rarrafa Zinaru sai makarai sun makeki a hanya." Goggo da ta gama zuwa wuya a zuciye ta juyo ta ce, "Yooo shi wanda kika kuɓuto daga hannunsa Mutum ne? Ki yi ta kanki daga nan ni kam Albasu zan wuce don na tabbata ko ba aljani bane yana cikin ƙungiyar asiri, don wallahi mutum ba zai aikata abin da ya yi ba idan ba haka ba Malam mai allo bai haife ni ba." Nan take cikin Inno ya sake kaɗawa da sauri ta fara rarrafawa ta bi bayan Goggo suka sauka, suka wuce ɗakinsu.
Su Inno na fita Huzaifa ya koma kan Raihan tare da gayyato Jabin Raihan don ta maye masa gurbin Raihan ko ya samu ya sake dulmiyar da su Daddy ga zuwa ƙasar Indiya, saboda matuƙar suka je Indiya hakan zai taimaka masa wurin gano takamaimai abin da yake faruwa da ita. Kafin ƙiftawa ido sai ga Jabin Raihan ta fara motsawa tana sauke ajiyar zuciya, Sai dai babban abin da ya fi ɗaga masa hanakali da ya so ɗaukar gangar jikin Raihan zuwa Tsauninsa abin ya gagara, wannan ya sake tabbatar masa da akwai ɓoyayyan al'amari a dangane da ciwon Raihan, tashin farko Mugaza ce ta faɗo masa don ya san akan baƙin kishinta tana iya aikata komai don biyan buƙatarta. Daddy ne ya tsinke masa tunanin da yake yi yana faɗin, "My Raihan barka farkowa." Mommy da ke gefe ta ce, "Sannu Raihan." Da ido take bin su da kallo tana gyaɗa musu kai tamkar ƙadangaruwa. Mommy ce ta koma daga ɓangaren Raihan ta tsugunna ta fara karanta ayatulkursiyyu tana tofa mata, da sauri Huzaifa ya zabura ya matsa gefe cikin huci a gaggauce yana faɗin, "Shi kenan yanzu zan wuce Alhaji duk abin da ake ciki za ku ji ni saboda akwai wani patient da yake jirana." Daddy ya miƙa masa hannu suka gaisa cikin jin daɗi ya ce, "Ba damuwa na gode sosai Dr." Da sauri Huzaifa ya yi gaba har ya je bakin ƙofa Daddy ya ce, "Dr babu wani magani da za a ƙara mata akan na da ka san fa wancen ya ƙare." Huzaifa ya fara sosa kai sannan ya ce, "Babu damuwa zan turo maka text ta waya." Tun bai jira cewar Daddy ba ya fice daga ɗakin.
0 comments:
Post a Comment