_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣
Da alama ranta a b'ace yake ga k'aguwa a zahirinta ya bayyana, sake kallon agogo tayi na karo ba adadi sannan ta kalli k'ofar douche d'in taja dogon tsaki tana magana k'asa k'asa "wannan wulak'anci dame yayi kama, sama da awa d'aya kina wanka, ki bani wani banzan serviette (towel) na rik'e kamar ke wata musaka ce."
Sake kallon agogon tayi sai dai kafin ta maido kallonta taji an bud'e k'ofar douche ana fitowa, da sauri ta kalleta amma saboda ganin santaleliyar budurwar ta fito daga ita sai d'an k'aramin silip (pant) d'inta ko soutien ( bras) babu yasa tayi k"asa da kanta, ita kam ko a jikinta takowa tayi ta zo gabanta ta karb'i serviette d'in ta d'aura a k'irji sannan ta karb'i dayan ta d'aura a kanta, gaban coiffeuse taja kujera ta zauna tana kallon madubi ita kuma mai aikin ta matso ta d'auki mai ta fara shafa mata, bayan ta gama ta shafa mata powder da pink d'in jan baki, ta fito mata da wani silp d'in da soutien ta bata ta saka sannan ta fito mata da riga da siket na atamfa, d'inki ne na yan zamani yayi kyau sosai gashi ya zauna a jikinta daram , mai aikince ta zuge mata zip d'in dake bayan siket d'in wanda ya kamata sosai komai nata ya fito masha Allah, d'an kwali ta kashe d'aurinshi sannan ta fito mata da sarka da yan kunnai da gani kasan sunji kud'i, sannan ta fito mata da jaka da takalmin da suka dace ta aje mata gabanta, sakawa tayi sannan ta d'auki turare ta fesheta dashi ita kam tana tsaye kamar gunki, tana kamalawa ko jiranta bata tsaya ba kawai tayi k'ofar fita abinta.
Binta tayi da harara tana fad'in "wannan zanso naga gidan aurenki , mijinki ne zai miki wannan hidimar ko kuma mai aiki zai samar maki."
Gyara d'akin tayi kamar yanda maishi zata buk'aci ganinshi sannan ta fito ta rufe mata d'akin.
Ba tare data kalli kowa dake kan table a manger (dinning) d'in ba taja kujera ta zauna, wata mai aikince dake tsaye kusansu ta matso ta fara zuba mata abincin, ta zuba mata fritte zata bud'a wani kwanon kawai ta d'aga mata hannu tare da kallonta cike da wulak'anci tace,
"Ya isa haka, ni ba jaka bace kamarku da zan zauna ina had'iyar abinci haka."
Ja baya tayi kanta k'asa bata kalleta ba ita kuma ta fara cin fritte d'in, mahaifiyarta ce tace "mu kike so mu fara gaidaki kenan?"
Cike da nuna an takura mata tace "ina kwana."
Mamar ce tace "nice kad'ai a wajen?"
Kallon saurayin da suke fuskantar juna tayi, amma ganin wani kallo da yake mata tare da murmushi yasa ta zabga masa harara, maida kallonta tayi ga mahaifinta, d'auke kai tayi ta kalli mahaifiyar tata tace "ki tabbatar min jiya bai shigo cikin maye ba, ni kuma saina gaisheshi."
A tsawace uwar tace "ke, ashe baki da mutunci, wannan ba mahaifinki bane da zaki fad'a masa haka?"
A wulak'ance ta kalli uwar tace "shi kenan mutunci ne yake sashi shigowa cikin gida a buge? kinga nifa karki b'ata min rai da safiyar nan."
Duk da k'ok'arin rik'e hawayen da tayi saida suka zubo, cikin muryar kuka tace "ba laifinki bane, kiyi yanda kike so."
Tana fad'a ta juya ta nufi d'akinta tana zubar da hawayen takaici, ita kuma ko kulata ba tayi ba bare taji ba dad'i, saima mahaifinta data kalla tace "zaifi maki kyau ki daina saka damuwa a ranki akan wannan da baisan kina yi ba."
Tashi tayi ta bar abincin zata fita ,mahaifinta ne kalleta a marairaice yace "kiyi hak'uri mana gimbiyata, nayi alk'awari ba zan sake ba."
Kallonshi tayi ta kalli saurayin dake zaune kusanshi tace "ka fad'awa wannan wawan watak'ila shi zai yarda da abinda ka fad'a, amma bani ba *Khairat*."
Fita tayi ta nufi wajen motarta, d'aya daga cikin jami'an dake kula da mahaifinta ne ya taho shima a gadarance ya karb'i jakar hannunta da makullin mota ya nufi motarta dasu, dan in baiyi ba to masifa zaisha amma ba k'aramin d"aci ba abin ke mishi, har zata shiga mota taji saurayin nan yace "nine wawan?"
A wulak'ance ta juyo ta kalleshi tace "to da wa in ba kai ba? da wani ne wanda ya fika zama wawa a duniyar nan? ai kai kad'ai ne namijin dake zuwa gidan wacce yake ikirarin yana so kuma ya zauna zaman dirshan har da mik'e qafafu."
Nunashi tayi da yatsa tace "wallahi harka gama wa'adin daka dibarwa kanka ba zan tab'a kallonka a matsayin mutum ma bare harna fara tunanin soyayya da kai, désolé."
Tana fad'a ta shiga motarta ta bar gidan cikin matsanancin gudu, shi kuma taushe b'acin ranshi yayi da har yanzu yana ji a jikinshi zata iya zama tashi, a ranar da kuma hakan ta faru zata gane wanene shi.
********************
Kafin ta fara gudanar da komai saida tasa masinger ya siyo mata fritte mai had'e da soyayyen nik'akk'en nama da jus d'in albasa da moutarde, tasa *Habiba* ta had'a mata kakkauran tea da zuma sannan ta fara wani sabon petis de jeûner d'in, tana fara ci Habiba ta sake shigowa cikin ladabi tace "madame, manager ne ke son ganinki."
Kallonta tayi a wahalce tace "uhum, kice ya shigo."
Juyawa tayi dan cika umarninta, takai wata lomar bakinta taji shigowarsu, amma jiji da kai yasa ta kasa koda kallonsu da ido, tsaye sukayi a kanta hakan yasa ta musu nuni da hannu akan su zauna, saida suka zauna sannan ta kallesu gaba d'aya ta kuma kalli manager tace "kai kad'ai aka ce kana son ganina, yana ganku ku biyu?"
"Eh madame, wannan shine wanda za muyi magana akan ci gaban daya kawo mana."
Sake kallon saurayin tayi wanda idonshi ke kan kallon yatsun hannayenta da take cin abinci dasu, jan lallen da suka sha da dogayen akaihu na kanti wanda suma ta lullub'esu da pink couleur d'in vernie, sosai suka birgeshi duk da dai ya tsani mai su d'in, maida kallonta tayi ga plate d'in abincinta taci gaba da ci har saida ta gama sannan ta d'auki bidon (gora) d'in ruwa ta zura hannunta ta tagar dake bayanta ta wanke hannu ta juyo da nufin aje bidon d'in ta d'auki lotus dan goge hannu, karaf idonta suka sauka akan gayen nan daya kasa d'auke idonshi akan kyakyawar hallitarta, da sauri ya d'auke idonshi tare da had'e fuska tamkar hadarin gabas, dan tunda ta fara aiki anan take tak'ama wajen mahaifinta ne ya lura tana da raini shi kuma ba zai d'auka ba, saida ta goge hannun ta tsaya ba yare data zauna ba ta kallesu tace "ina jinku."
Hannu manager yasa a jaka ya fito da takalma ya mik'a mata yana fad'in "wannan shine sabon sanfarin da wannan ma'aikacin namu ya fito mana dashi, shine nace kafin muci gaba da bugawa sai mun samu izininki."
Karb'a tayi bayan ya gama mata bayanin ta kallesu da kyau, tabbas sanfurin ya birgeta dan kuwa basu da maraba dana maza harda gidan babban yatsa, ga kuma tudunsu shima kamar dai na maza, ajesu tayi qasa ta cire na qafarta tasa wad'annan, su kam kallo suka bi qafar da ita yayin da saurayin ke ma qafar kallon qurilla wacce tasha jan lalle sai dogayen akaihu itama data saka masu kamar dai na hannuwa, ganin yanda suka zauna a qafarta suka mata kyau yasa ta cire ta zauna a kujerarta tace" kuje kawai ku ci gaba da bugawa, ku bar min wannan zanyi publié a Internet nasan zamu samu masu so."
Cikin farin ciki bayan sunyi godiya suka tashi zasu fita, muryarta ta tsayar dasu tace "fasahar waye?"
Juyowa sukayi manager kuma yace "wannan ne madame." ya fad'a tare da nuna na kusa dashi.
Saida ta fito da wayarta a jakarta sannan tace "meye sunanka?"
" *Umar Faruk*." ya fad'a a daqile.
"Zo nan." ta fad'a kamar ta kira yaronta.
Kamar ba zai zo ba saida manager ya sake cewa "madame na kiranka."
Takowa yayi tare da k'ara d'aure fuskarshi, saida ya tsaya gaban tebur d'inta yana kallon idonta, jujjuya kujerar ta fara yi tana juyawa da ita ta fara magana "karka bari mu sake had'a ido da kai da sunan had'arin kallo, karka sake bari na maka magana so d'aya har sai an maimaita maka, karka bari na sake jin raina ya b'ace a kanka, sannan karka sake kallon min bayana idan na juya."
Tsaye ta mik'e tare da d'aukar lotus d'in data goge hannu ta saka masa shi a aljihun gaban riga tace "ka aje min shi, gobe zan tambayeka."
Zaune tayi tace "zaka iya tafiya."
Saida ya gama mata kallon raini kafin ya gyara tsyuwarsa yace "idan baki son ana kallonki, to ki zama kamilar mace ta yanda ba zaki rinjayi shed'anun dake cikin zuk'atanmu ba bare har mu kalleki , ni kaina nasan nayi zunubi kuma dole na nemi gafarar ubangijina akan hakan, sannan ki sani ni ba d'anki bane da zaki takani yanda kike so, haka kuma talaucina bai k'ask'antar dani izuwa matakin dake kike k'ok'arin d'orani a kai ba, ina fata kin fahimta."
Yana fad'a ya juya bar bureaux d'in, ita kuma ta bishi da kallo tare da tunanin koya masa hankali.
Kasancewar bata jima da fara aiki a wajen ba yasa har yanzu akwai rashin sabo, yanzu haka tattara kayanta tayi Habiba ta biyota dasu ta nufi gida saboda bacci kawai take so tayi.
********************
Tunda ta shiga gidan taga guardcord (bodyguard) d'in mahaifinta kuma taji shiru dan haka ta shiga babban falon da zai sadata da nata d'akin, duk da ba bak'on abu bane a wajenta amma dai ta tsorata, tunda taji sautin tasan mahaifinta ne ke dukan mahaifiyarta, da gudu ta nufi d'akinshi ta jefar da jakarta, bata tsaya komai ba ta kutsa kai cikin d'akin ai kuwa bata tsaya ba wajen kaiwa mahaifiyarta d'oki , saman gadon ta fad'a ta rumgumo mahaifiyarta tana k'ok'arin kare jikinta, tunda ya ganta ya jefar da wayar hannunshi ya fara zare ido, yana kakkare jikinshi saboda daga shi sai gajeran wando, kama mamanta tayi suka sauko daga gadon ta d'auki rigarta a k'asa daya ketata da qarfi ta rufe mata jiki, tana rik'e da mahaifiyarta ta kalleshi sai k'yabta ido yake tace "wallahi idan ka sake dakar min uwa, to ka sani justice (kotu) ce zata rabani da kai, dan ba zai yiyuba ka dinga shak'o giyarka kana zuwa kana narkar min uwa ba."
Tana fad'a suka fita daga d'akin saida ta kaita har d'akinta ta d'auko mata riga doguwa ta sauya ta d'auko mata maganinta ta bata tasha sannan ta kwantar da ita tana rufeta tana fad'in "banga abinda kike tsinta a gidan nan ba da ba zaki barshi ba, amma da nayi magana sai kice saboda ni kike zaune, ni zan kula da kaina ki koma wajensu Mammie ki zauna."
Tana fad'a ta juya itama ta koma nata d'akin ta cire kayan jikinta ta watsa ruwa sannan ta d'auki kayan data fi jin dad'in zama dasu a cikin gida ta saka, wando ne na jeans fari tas sai dai iya cinyoyinta ya tsaya sai kuma riga ta dan sauko har cibiya amma k'ananan hannuwa gareta, kwance tayi ba jimawa bacci ya d'auketa.
*******************
Tana tashi bayan la'asar brush tayi kawai ta fito bata damu dayin sallolin dake kanta ba, a falo ta zauna saman lunstumemiyar kujerar dake kai tana kallon tv, mai aiki ce ta kawo mata abinci tana ci mamarta ta fito rik'eda carbi , zaune tayi tace "kinyi sallah?"
"Nayi." ta fad'a dan karta sake damunta.
_Wannan yarinya ba dai k'arya ba_
Haka suka kasance wunin ranar ba wani dad'i, sai dai takalmin data d'ora a internet sun samu masoya, anan wasu manyan 'yan kasuwa suka ce suna son dayawa akan sari, anan suka tsayar akan gobe zasu zo ma'aikatar tasu sai suyi magana, kasancewar manyan mutane ne yasa tace wa mahaifiyarta ta tasheta k'arfe takwas na safe danta shirya da wuri, cikin dare sosai tana kwance tana chat taji motsi a falo, lek'owa tayi abin mamaki *Mujahhid* ne yake shiga d'akinshi cikin tsananin maye tare da wata budurwa, tsaki taja tace "dubunka ta cika, wallahi saika bar gidan nan tunda bana ubanka bane."
Komawa tayi d'aki ta ci gaba da abinda take har bacci ya d'auketa da ecouteur a kunne tana sauraren wak'ok'i iri iri.
*********************
*Da safe* zaune take a tsakiyar wani faffad'an gado na alfarma cike da magagin bacci da har yanzu bai saketa tace "nifa wallahi kun takura min, wai dole saina tashi ne?"
Sake komawa tayi ta kwanta taja wata kakkabrar zanin rufa ta rufe, matar dake tsaye gefenta ta sake yaye zanin tana fad'in "dole ki tashi, ke da kanki kika ce na tasheki takwas daidai saboda bak'in da zasu zo."
Tana jin haka ta tashi firgigit tana zare ido tare da kallon mahaifiyar tata tace "k'arfe nawa yanzun?"
Tab'e baki tayi tace "08:20."
Ai kuwa kamar zata bige uwar haka ta diro daga kan gadon ta nufi k'ofar fita, ta bud'e k'ofar matar tace "ina kuma zaki je da wannan kayan?"
Ko saurarenta ba tayi ba kawai ta fice abinta, da gudu ta sauko daga matakalar benen, tsinkayar mahaifinta tayi a farfajiyar gidan d'aya daga cikin masu tsaron lafiyarsa ya bud'e masa mota yana daf da shiga, da gudu ta k'arasa tana kiran "papa, papa."
Tsayawa yayi ya juyo yana kallonta, sai dai bashi kad'ai ba harda masu tsaron lafiyarsa dake cikin tenue d'insu na sojoji su hud'u, kayan baccine wando iya cinyoyinta sai kuma k'arama kuma siririyar riga mai kamar puscier, abinka ga fara kuma doguwa kyakyawa, ba tare data kulasu ba kawai tace wa mahaifinta "papa, ku jirani na shirya saiku ajeni a service d'in."
"Motarki fa?" cewar papan
Juyawa kawai tayi ta nufi cikin gidan tana fad'in "bana jin tuk'i yau."
Ajiyar zuciya ya sauke dan babu yanda zaiyi dole ya jirata, yayin da jami'an suka bita da kallo iri iri suna kallon mazaunanta dake juyawa gwanin ban sha'awa.
Kasancewar tana sauri yau shi yasa bata jima douche ba ta fito cikin k'ank'anin lokaci ta shirya, doguwar rigar tattausan tissue (matériel), wacce ta kama jikinta sosai k'asa kuma ta bud'e, kallabin rigar kawai ta d'aura ta d'auki jakarta tasa takalmi ta fito bayan fessa tsadaddun turarukanta masu d'aukar hankali dayawa, duk da jan jan-baki ne ta shafa kad'ai amma hakan bai hana kyawunta fitowa ba sai k'ananun kitsonta da suka kwanta a gadon bayanta.
Tana fitowa matar na zaune a d'aya daga cikin kujerun falon ta kalleta, cike da nuna rashin jin dad'i tace "me yasa kullum kike burin mu dinga nanata kalma d'aya, yanzu ko nauyi ba kiji ki fita haka babu gyale bare hijabi."
Wata babbar fridge ta bud'a tana fad'in "kece kike sha'awar bawa kanki wahala da kike maimaita abu guda kullum."
Tana fad'a ta d'auki wani gateau da holandia yagourt ta fice abinta, tana zuwa jami'in ya bud'e mata gidan baya kusa da mahaifinta, shagalta da yayi da kallonta yasa bai bud'e k'ofar da kyau ba, cikin jin haushi ta daka masa tsawar da saida kowa ya zabura dake wajen tana fad'in,
"Imbecile, q'est ce que tu regarde?"
Da sauri ya bud'e mata ta shiga tana jan tsaki tana fad'in "sakarkarin banza kawai, ni banga abinda suke tsinana maka ba da har yanzu kake tare dasu, in banda k'yauyenci da shirme babu abinda suka sani."
Haka suka ja motocin, mota d'aya ce a gabansu sai kuma wata d'ayar a baya tasu a tsakiya, saboda tsaro.
Gâteau ta fara ci tana korawa da tana ci gaba da mita, shi dai mahaifinta saurarenta kawai yake,amma hankalinshi baya wajenta, har saida suka isa suna tsayawa a babban masana'antar ta sake kallensu tace "kenan babarku ce zata bud'e min k'ofar ko me?"
Wanda baya tuk'in ne ya fito ya bud'e mata, tana fita ta kalli mahaifin nata tace "idan kaje mashayar ka shawu son ranka, kaga saika shigo mana gida a buge."
Kallonta kawai yayi baice da ita k'ala ba, ita kuma ta wuce ta tunkari ma'aikatar, tana shiga ma'aikatan suka fara shan jinin jikinsu yayin da kowa ke gaisheta, sai dai babu mai sa'ar da zata amsa mashi gaisuwar , secretaire d'inta mai sunan *Habiba* ce ta karb'i jakar hannunta ta fara take mata baya tare da fad'a mata programme d'insu na yau bayan sun sallami bak'in, juyowa tayi a hassale ta kalleta tace,
"Ki soke duk wani programme na yau dan babu abinda zan iya, bak'in nan kawai zan gani na koma gida."
Shiru tayi suka haura sama a cikin acessaire in da zai sadasu da d'akin da bakin suke, tana shiga kallon mutanen ya dawo kanta in da kowa ke yaba kyawun fuskarta dana hallita da Allah yayi mata, bakin turawa ne duka ta mikawa hannu cikin sakin fuska suka gaisa kafin ta zaune kujerar dake tsakiyar sauran kuberun , saida kowa ya zauna mazauninshi harda secretaire d'inta ta zaune daga bayanta danta d'auki rahoton abinda zasu tattauna, sai lokacin kuma kallonta ya kai ga wata kujera da babu mazauninta, kallon habiba tayi tace,
"Wane sakarai ne anan da bai shigo ba?"
Cikin ladabi Habiba tace " *Umar Faruk* ne."
Za tayo magana suka ji an bud'e k'ofar wajen, ganin saurayin cikin hanzari yake yasa ta tashi tsaye cike da raini tace "sannu da zuwa yallab'ai."
Kallonta yayo ya kalli mutanen dake wajen, take ya fahimci abinda take nufi dan haka yace "je demande vos esxuze, je..."
Tsawar data masa yasa yayi shiru "yi mana shiru, kenan muna zaune nan dan ka zo ka bamu hak'uri, kai mahaukacin ina ne da baka san mahimmancin lokaci ba? kawai mutane jahilai daku babu abinda kuka iya sai tumasanci da banlag...."
"Ke, ya isheki haka."
Wannan maganar ita tasa tayi shiru bata shirya ba.....
Cikin b'acin rai ya ci gaba da cewa "me kika d'auki kanki? su waye jahilan? fad'a min matakin karatunki da har kike fad'a min haka, to bari kiji wallahi kika sake kirana jahilai saina fasa miki baki a wurin nan, ke in ba jahilce ke damunki ba me yasa zaki kira wasu da jahilai, kuma bari kiji aikine da nake a service d'inku zaisa kimin kallon banza ko? to na daina daga yau, saiki zauna ki cinye wurin idan zaki iya."
Yana fad'a ya juya ya barta nan tsaye sake da baki, a fusace ya bar wurin kayanshi ya had'a dake kan teburd'inshi yana shirin fita, ta baya yaji an dafa kafad'arshi, juyowa yayi ya sauke idonshi akan babban abokinshi....
*Luv you guy's*😍
06/08/2019 à 00:06 - Meerahgee❤: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
_Bismmilahir-rahman-rahim_
_Manzo (S.A.W) yace "Imanin d'ayanku ba zai cika ba har saiya soma dan uwansa abinda yake so ma kansa."_ *Imamul Bukhari da muslim suka ruwaitoshi*
2⃣
"Faruk lafiya na ganka rai a b'ace?"
Cikin masifa yace "ina fa lafiya, wannan 'yar rainin hankalin tana nema ta b'ata min rai kawai dan tana ganin nan mallakin mahaifinta ne, ni dama tunda naga yarinyar nan nasan ba za ayi abun k'warai a wurin nan ba."
Wani murmushi yayi yace "Faruk, to yanzu meya faru kenan?"
"Me kuwa ya faru, na baro mata wurin,kuma daga nan gidanmu nayi dan ba zan iya aiki a k'arkashin yarinyar nan ba."
Da sauri ya rik'e hannunshi daga shirin rataya jakar da yake shirin yi yana fad'in "me kace? Faruk kana da hankali kuwa? kasan me kake shirin aikatawa?"
"To bari kaji in fad'a maka kuskuren da kake shirin aikatawa, wannan aiki shekara hud'u mukayi muna neman abinyi amma bamu samu ba, ka sani kafin mu sameshi munsha wahala sosai, bama wannan ba Faruk me yasa ba kayi tunanin mutanen da suka ci suke sha ta dalilinka ba, ko ka manta da irin nauyin dake kanka ne, sannan ka sani wannan aikin da kake neman watsarwa a yanzun, to ka sani akwai dubbun nan mutanen dake qaunarshi kuma d'aruruwan mutane ne zasu so da burin samun kujerar daka tashi, dan haka kayi tunani kafin ka yanke hukunci."
Barinshi yayi tsaye yana tunanin abinda ya fad'a, ganin baida wata mafita data wuce ya zauna yasa ya ajiye jakar cikin sanyin jiki ya koma sale d'in bak'in, a hankali ya bud'e kofar yayi daidai da har sun gama tattauna abinda ya tarasu, kallonshi take sosai da mamakin abinda ya maidoshi, saida ta bawa bakin nata hannu sukayi musabaha sannan suka wuce, saida ta gama kallonshi shi kuma ya kasa cewa komai, wayarta ta dauka Habiba ta biyota da jakarta suka fita daga wajen, acessaire (lift) suka shiga Habiba na shirin rufewa ya kutsa kai ciki, tana ganin haka ta fito cikin zafin rai ta nufi matattakalar bene da sauri ta fara sauka, da sauri shima ya fito harda gudu gudu ya tari gabanta ya soma sauka ta baya yana kallonta yana fad'in "magana zamuyi dan Allah ki saurareni."
Bata saurareshi harta sauka suna kaiwa tsakiyar ma'aikatar ya sake tare gabanta yana fad'in "dan Allah ki saurareni, hak'uri zan baki...."
Marin daya sauka a kunci ne yasa yayi d'uf, dafe yake da kunci yana kallonta, itama shi d'in take kallo haka kuma duk mutanen wajen ita su suke kallo, kafin wani abu ya sake faruwa sai kuwa Faruk ya zabgeta da marin da yafi wanda ta mishi.
Dafe kuncinta tayi baki bud'e tana kallonshi saboda mamaki, kasa motsawa tayi daga wajen yayin da shi kuma ya d'ora mata da wani sabon bayani "wallahi ke baki isa ba kisa hannu ki mareni, akan me? saboda kawai muna k'asanki."
D'aukar kayanshi yayi ya bar ma'aikatar gaba d'aya, cikin fushi da ba zata iya misaltashi ba ta bar wajen, gudu take sosai a mota ba tare da tunanin wani abu ya sameta ba.
Tana shiga ko rufe motar ba tayi ba ta wuce cikin gidan da gudu, daf da k'ofar shiga ta fad'a saman mutum, kallon kallon suka tsaya yi tana gama gane waye ya rik'eta ta fizge jikinta tana tureshi baya, shi kuma murmushi kawai yake mata, cikin masifa da son sauke bala'inta a kanshi ta fara magana,
"Meye haka, kai mahaukacin ina ne? baka ganine da zaka bigeni harda wani tab'a jikina? to bari kaji wallahi yau duk uban daya tsaya maka a garin nan saika bar gidan nan, tunda bana ubanka bane."
Duk da maganganunta sun masa zafi amma daurewa yayi yace "bake kika kawoni ba, ba kuma zaki fitar dani ba idan banyi niyya ba."
Cike da gatsali tace "saboda uban kane ya gida gidan?"
Cike da hassala ya fizgo hannunta kamar zai had'ata da jikinshi yace "wai ke me yasa baki da wayo ne, me yasa duk abinda ya zo bakinki fad'inshi kike? ke dai kinsan ubana ba matsiyaci bane bare kice zaki min gorin da kike wa wasu."
Sake fizge hannunta tayi ta tureshi iya k'arfinta tace "banza kawai, wani arzik'i mahaifin naka yake da da har zaka fad'a min, to bari kaji yau dole ka bar gidan nan, dan ba zai yiyuba ka zauna kana kawo mana mata a gida ba bayan kasha giyarka."
Muryar Mamie ce suka ji tace "Khairat dama rashin mutuncin naki har ya kai haka? waike wace irin yarinya ce marar ganin girman na gaba da ita? me yasa kika zab'arwa kanki wannan kakkaussar rayuwar da ba zata kaiki ko ina ba a matsayinki na mace?"
K'arasa shigowa tayi cikin falo tana kallon uwar tace "nice ai ya kamata na miki wannan tambayar, me yasa kika auri mutumin da kinsan baya da hallaye masu kyau? sannan karki sake cemin bana da mutunci, dan inma hakane to gadone nayi"
Kafin tayi wata magana ta d'ora da "kinga, wallahi yaron nan ya bar gidan nan yau, idan kuma ba haka ba zansa Papa yayi rashin mutunci a gidan nan, idan kuma shiya kasa saboda yana tsoronki, toni da kaina zanyi kuma zaku sha mamaki."
A fusace ta rab'a uwar tayi d'akinta ta barsu nan, hawayen da suka fara taho mata ne tayi saurin saka hannu ta share tana kallon Mujahhid, murmushin yak'e ta masa tace "kana ji ko yarona, kayi hak'uri dan Allah k....."
Katseta yayi ya matso kusanta da sauri yana fad'in "karki damu Mamie, ba komai wallahi, zan tafi, amma ni ke nake tunani yanda zaki ci gaba da rayuwa a gidan nan cikin kad'aici."
Kallonshi tayi tace "a'a, karka damu dani, aini na saba, zan ci gaba da zama a haka, har lokacin da Khairat zata fitar da mijin aure, dan aurenta ne ya tsayar dani gidan nan."
"Shikenan Mamie, zan tafi, bara naje na had'a kayana."
Tana shiga d'aki ta jefar da jakarta ta k'arasa gaban coiffeuse tasa hannu tayi watsi da kayan dake wajen, matuk'a ranta a b'ace yake kuma tana so tayi abinda yafi wanda aka mata ciwo, a hankali ta fara zamewa a jikin bango tana sulalewa har takai qasa, fashewa tayi da kuka sosai, ta jima a gurin tana kuka har saida mai aiki ta bud'a d'akin zata shigo, cikin daka tsawa tace "ki fita ki bani wuri, bana son ganin kowa."
Abinda ba'a so ne ya faru, saboda tsananin damuwa da kuka yasa qirjinta ya fara matsanancin ciwo haka kuma kanta ya fara mata bala'en'en ciwon da tafi fatan mutuwarta a kanshi, jin haka yasa ta rarrafa ta bud'a coffre ta d'auki maganinta, duk da dishidishi take gani hakan ta duba amma bata ga ruwa ba ba a d'akin , k'arfin hali tayi ta tashi ta nufi k'ofa danta samu ruwan, tana kusa ga kaiwa kawai ta fad'i a guri numfashinta kad'an yake fita, hannayenta ne duk bisa kanta saboda yanda yake fizgarta, daga haka kuma bata sake sanin meya k'ara faruwa ba a gaba.
*Da misalin* 16:30 Papa ya shigo gidan, Mamie na zaune akan kujera cikin damuwa da tunanin halin da Khairat take ciki, ba tare da sallama ba kawai ya zauna kusa da ita yana fad'in "sannu da gida."
Cikin sanyin jiki da tabe baki tace "yawwa, sannu da shigowa?"
"Ba dai Khairat bata dawo ba?" ya fad'a yana cire hular kanshi.
Saida ta sauke ajiyar zuciya tace "bata wuce awa d'aya ba da fita ta dawo, tana d'akinta."
"Bacci take?"
A sanyaye tace "gaskiya ban sani ba, ta shigo kamar ranta a bace yake, harma suka samu matsala da Mujahhid wanda yayi sanadiyar komawarsa gida, amma tunda ta shiga d'aki bata fito ba, kuma mai aiki taje ta dubo halin da take ciki ta korota."
Jin tayi shiru yasa ya kalleta yace "ina jinki, sai akayi yaya?"
"Ba komai, har yanzu tana ciki."
Tsaye ya mik'e yana girgiza kai yace "ban san me yasa kike nuna mata rashin kulawarki ba kamar ba 'yar da kika haifa ba, da bake kika haifeta ba sai nace ba kya sonta, kinfi kowa sanin duk baccin da Khairat za tayi ba zata kai wannan lokacin tana bacci ba, amma ki kasa duba halin da take ciki."
Yana bud'e k'ofar ya k'arasa a guje yana fad'in "oh mon Dieu, Khairat, Khairat!!!."
Maida kallonshi yayi ga Mamie wacce ta shigo yanzu, cikin b'acin rai yace "kin gani ko, kin gani abinda kika jawo mana, wai me yasa kike nunawa yarinyar nan rashin kulawa ne? ki dubi sakacinki abinda yake nema yaja mana."
Mamie da bata san meya faru ba itama cikin fad'a tace "to miye anfanin kulawar da zan dinga nuna mata, naga kaima da kake nuna mata kulawar ba wani girmanka take gani ba, bare kuma ni à banza...."
Duk da ta kai k'arshen aya amma saida ta dire kalmar ba daidai ba saboda tsawar daya mata, cikin d'aga murya yace "dallah ki min shiru, zaki kama min ita ne ko kuma burinki ta mutu?"
Qafafunta ta kama shi kuma ya d'auki duka rabin jikinta suka nufo da ita waje, ma'aikatan gidan na ganin haka suka fara tambayar lafiya meya sameta, biyarsu suke a baya har chauffeur ya bud'e musu k'ofar mota suka kwantar da ita a baya sannan suka shiga suka bar gidan, ma'aikatan kowa jini kan akaifa , ba zasu ce suna jin dad'i ba saboda rashin lafiyarta , amma dai sun san sun d'an samu hutu na wani d'an lokaci.
********************
*Faruk* ne zaune akan taburma shi da abokinshi *Ishaq*, yayin da wata dattijuwar mata mai kamala ke gefensu akan kujera yar tsugunno, sai kuma babban malamin dake tsaye ya tisasu a gaba yana fad'a akan aikinshi daya baro, cikin fad'a ya sake cewa,
"Kai yanzu badan baka da hankali ba, daga k'aramin abu sai kawai kayi hushi, kai gaka uban zuciya ko? to bari kaji wallahi wannan aikin idan har ka bari ya kubuce maka, to wallahi za kayi nadama da daka sani, kai kafi kowa sanin kaine kusan rabin k'arfin gidan nan, to idan kace ka daina aikin kenan duk yayanka ne zai had'a ya d'auki har nauyinka.?"
D'ago kanshi yayi yace "Baba bafa k'aramin abu bane, marina fa tayi a fuska, wallahi ko k....."
Tsawar da Baba ya masa yana fad'in "ta mareka d'in, nace ta mareka saime? idan baka rama ba mutuwa za kayi, kuma tun farko ai kai kaja komai."
"Dan haka ka jini da kyau, ka tashi yanzun nan ga Ishaq nan ya rankaka kuje ka sameta ka bata hak'uri, karka yarda ka rasa wannan aikin, in kuma kayi sake to ka sani, wallahi abincin gidan nan ma ka daina ci tunda kai sarkin zuciya ne, waika gaka *Umar Faruk* ko?"
Sake d'ago kai yayi yace "Baba, cewa fa kake naje na...."
"K'warai haka nake nufi, dole sai kaje ka bata hak'uri, in kuma ba haka ba to duk matakin dana d'auka kanka, kai ka siyo da kud'inka."
Sai lokacin mahaifiyarshi tace "in banda abin Umar faruk ma, kaida maganar aure ka keyi amma kake k'ok'arin aje aikin da shine gatanka."
"To, fad'a masa dai, tunda naga shi baya da hankali zuciya ce kawai yasa a gaba."
Ishaq ne yace "kaga, ba wani abin damuwa bane, yanzu ya tashi mu tafi mu koma service d'in mu samu manager, nasan insha Allah zai taimaka mana kamar yanda ya taimaka mana muka samu aikin nan da farko."
Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya kalli Baba yace " kuyi hak'uri Baba, insha Allah zanje na bata hak'uri kamar yanda kuka ce."
Addu'a Mama ta bishi da ita da fatan samun dacewa, Baba kuma na sake jaddada masa ya tabbatar ya bata hak'uri sosai harta hak'ura, haka suka fito da niyyar tafiya ma'aikatar wajen manager.
Sun samu manager kuma Ishaq ya fad'a masa komai daya faru, yayi mamaki sosai dan baisan wainar da aka toya ba, yayi jimami sosai tare da k'ara tsorata Faruk akan karma ya fara tunkararta ya jira hukuncin da mahaifinta zai d'auka a kanshi ko kuma ita da kanta, baiji shakka ko d'ard'ar ba akan matakin da zasu d'auka, matsalarshi d'aya shine yanda mahaifinshi ya d'auka da zafi sosai, ganin baice komai ba yasa manager cewa,
"A gaskiya *Umar Faruk* ba zan yarda a dalilinka na rasa nawa aikin ba, kayi hak'uri, amma taimakon da zan iya maka na riga da nayi maka shi, shawara d'aya da zan baka kawai shine, idan har ta dawo d'aukar fansa to ka qasqantar da kanka, ka nuna mata kayi nadama kuma a bisa kuskuren rashin sanin ko wacece ita ka mareta, idan kayi sa'a ta iya yafe maka, amma gaskiya bana tunanin zata hak'ura, dan wallahi yarinyar nan rashin mutuncinta ya kai mak'ura, bata kallon kowa da idon daraja babu tausayi ko imani a zuciyarta, kuma tun ranar da mahaifinta ya mallaka mata masana'antar nan na fad'a muku dukanmu sai munyi hak'uri da ita, saboda kaushinta yayi yawa."
A sanyaye Umar faruk yace "zan jaraba na gani, bara naje bureau d'in nata."
Murmushi manager yayi yace "ta yaya kake tunanin zata zauna a wajen nan, ina jin a lokacin da naga tafiyarta to a lokacin ne abun ya faru."
"Kenan yanzu tana gida?" cewar Faruk d'in.
"Ina tunanin haka."
"Shikenan, zamu je har gidan, watak'ila ma tafi saurarenmu." cewar Ishaq
Faruk ne yace "a'a fa Ishaq, gaskiya bana so naje gidansu, idan taga haka zata san nadamu sosai, zata d'auka gaba d'aya na bada rayuwata wa aikin nan, hakan kuma zaisa ta qara wani rashin mutuncin."
"Muji ta d'auka a hakan in har ba zata koreka ba, meye a ciki?"
Kai Faruk ya girgiza yace "waiku me yasa ne kuke shakkarta har haka? mutum ce fa kamarku kuma mace mai rauni a kanku, me yasa zaku dinga tsoronta har haka, nifa wallahi bana son irin haka gaskiya, dan wannan ai bayar da maza kuke, yarinyar da da zaku bud'e mata ido sau d'aya dole zata fara shakkarku itama, amma duk kubi kuna wani tsoronta kamar ita ta halliceku."
Fuskar manager d'auke da murmushi yace "bawai muna jin tsoronta bane, sai dai ka sani kowane d'an adam a rayuwa yana buqatar ci da sha kafin ya rayu, to tamu k'addarar ta damka cin mu da shanmu ta sanadiyarta ne, ita kuma bata da kirki duk da bata jima a garin nan ba, amma na samu labarinta sosai kamar wanda yayi rayuwa a gidansu, dan ba tun yau muke tare da mahaifinta ba, kaga dole mubi a sannu."
Faruk ne ya tashi tsaye yace "zamu je gidan, ina fatan ta amince kodan saboda Baba."
Cikin tsokana Ishaq daya mik'e shima yace "da kana so amma kake wani nuna baka damu ba."
"Amma ai kaji me nace, ina fata ta amince saboda Baba." ya fad'a ba tare daya kalleshi ba.
Suna fita akan mashin d'in Faruk suka kama hanyar zuwa gidansu Khairat......
_Shin kuna ganin za suyi nasara kuwa? to wai zama su samu ganin Khairat d'in ko kuwa dai...???_
*********************
Suna zuwa k'ofar gidan suka tsaya suka sauka akan mashin d'in suka nufi k'ofar gidan, mai gadin gidan ne mai sanye da kaki irin na sojawa ya taresu yana fad'in "yadai malamai, daga ina, wa kuke nema?"
Ishaq ne yace "sannun ko, dan Allah munzo ganin Hajia Khairat ne."
Kallon tuhuma ya musu yace " Hajia Khairat? to tasan da zuwanku ne?"
Kallon juna sukayi tare da yin shiru na 'yan dak'ik'u kafin Ishaq ya sake cewa "gaskiya bata san da zuwanmu, mu daga service d'inta muke, manager ne ya turo mu saboda wani aiki daya d'an taso."
Kallonshi Faruk yayi saboda jin abinda ya fad'a , mai gadin ne yace "kuyi hak'uri mazaje, duk wanda ku kaga ya shiga gidan nan to an san da zuwanshi koda kuwa d'an uwane, kunsan gidan manyan mutane."
"Yanzu kenan babu wata dama da zata saka mu ganinta?" cewar Faruk.
"Gaskiya babu, dan Hajia Khairat ko tasan da zuwan mutun ma zata iya tsayar dashi a k'ofar gidan nan na tsawon awa uku, idan na barku kuka shiga zan iya rasa aikina."
Faruk ne yace "yanzu dan Allah to ya zamuyi muganta?"
Mai gadin ne yace "in dai abu mai mahimmaci ne, to zan iya fad'a muku wurin da zaku sameta, yanzu dai kunga ta shiga gida, kuma da alama ranta a b'ace ta shigo."
"To kenan ina zamu sameta?"
"Duk kwana uku takan je wajen casu, amma takamaimai wajen da take zuwa kuma wannan kuma ban sani ba, dan tana zuwa club da dama daga manya har qanana, yau kuma nasan zata fita saiku had'u acan."
Da mamaki Faruk ya kalleshi yace "malam, mufa a ma'aikatarta muke aiki, ba wani abu bane a tsakaninmu da ita ba, amma ta yaya zamu sameta a wannan wajen kuma fa sai cikin dare."
D'aure fuska mutumin yayi yace "kunga dan Allah kubar nan, taimako kuka ce kuma shi nayi muku."
Yana fad'a ya koma mazauninshi ya barsu tsaye, mashin d'insu suka hau akan hanya suna tunanin wata shawarar, amma Faruk yace shi bai tab'a zuwa gidan rawa ba ba kuma zai fara zuwa yau ba.
Suna zuwa gida suka fad'awa Baba yanda ake ciki, fafur Baba ya rufe ido yace bai yarda su tashi su koma, ganin basu son tafiya yasa Baba ya tisa k'eyar Umar faruk gaba yace su tafi, haka kuwa akayi akan mashin d'inshi suka tafi, amma wannan karan suna zuwa mai gadin yace musu an tafi da ita likita babu lafiya, da alama ma kamar babu rai a tare da ita, tabbas Umar faruk yaji ba dad'i kuma yana tsoron ace abinda ya faru tsakaninsu ne ya janyo faruwar hakan, likitar aka fad'a musu suka nufi can shi da Baba.
_Faruk ni dai a ganina da kun hak'ura da son ganinta kawai._😉
Cikin sa'a kuwa suna zuwa sukaga masu tsaron mahaifinta a kusa da d'akin da aka shigar da ita cikin gaggawa, kusa da d'akin suka tsaya amma ba suyi magana ba saboda ganin mahaifin nata nata kai komo a wajen ya gagara nutsuwa, duk da baisan mahaifiyarta ba amma da gani yasan ita ta haifeta saboda tsananin kamar da suke, kuma dama tun daga fatar jiki zaka san uwace tayi ba mahaifinta ba dake tillik'ik'e kuma bak'i wulik dashi,🤣 had'in gambiza ba, duk da akwai damuwa sosai a fuskarta amma dai babu alamun hawaye a tare da ita.
D'auke kai sukayi kamar ba wajensu suka zo ba, amma abin mamaki shine muryar Baba da sukaji yace "kina zaune hankali kwance, da alama so kike ta mutu ki huta ko? to ta Allah ba taki ba wallahi."
Tsaye ta mik'e cikin jin zafi tace "eh, so nake ta mutu na huta, kai a ganinka idan ta mutu ba zan samu salama ba? idan da abinda ya janyo mata wannan halin bai wuce kai ba, wallahi duk kai kaja mana halin da muke ciki saboda bak'in halinka, yarinyar nan tun tana k'arama ta fara fahimtar halayenka, amma hakan baisa ka daina ba, me kake so ta zama? wallahi ka sani alhakin lalacewar rayuwarta yana wuyanka ne, addu'a d'aya nake mata yanzu shine, kar Allah yasa ta fara shaye shaye da bin maza kamar yanda kake lalata 'ya'yan wasu."
Fizgota yayi daf dashi cikin hassala yace "ke ya isa haka, ke me yasa baki da kunya ne? a cikin mutane zaki nime tozarta ni, kuma ni ai nasan 'yata, wallahi ba zata tab'a bin maza ba."
Fizge hannunta tayi tasa gyalenta ta share hawayen idonta tayi murmushin takaici tace "kenan baka so ta fara bin maza ko, ka manta da fad'ar Manzo (S.A.W) ne, _cewar duk abinda kayi sai an maka_? kayi gaggawar aurar da ita, idan kuma ba haka ba to wallahi ni zan barka na koma wajen iyayena, dan ba zan iya supporter naji kona ga wani abu ya sameta ba."
"Ke marar mutunci, wallahi zai karyaki a warin nan, shashashar banza kawai."
Duk maganar nan yayita ne da d'aga hannu kamar zai mareta, zaburowa tayi tace "ka dakeni mana, ina jin tsorone ? dukanka wane irine ban gani ba ai sai dai kuma na gaba."
Hannu ya d'aga kam da nufin kai mata mari sai kawai ya tsaya cak saboda ganin Khairat d'in da aka shiga da ita ranga ranga amma ta fito da k'afafunta, kamar dai yanda suka taho da ita haka ta fito babu takalmi ba kallabi, kallon iyayen nata kawai take sai huci take saukewa, takowa ta farayi gabansu docteur kuma ya biyo bayanta yana neman ta tsaya dan farfad'owarta kenan taji hayaniyar iyayenta, saida ta tsaya gabansu ta kallesu da kyau sannan ta kalli drivensu tace "muje ka mayar dani gida."
Wucewa tayi mahaifin nata ya rik'e hannunta yana fad'in "gimbiyata, ina kuma zaki je ya jikin naki?"
Da iya k'arfinta ta fizgo hannunta tana mashi jan kallo tace "lache moi ma main." ta k'arashe da d'aga murya.
Wucewa tayi suka bi bayanta Papa na kiran sunanta harta shiga mota ta rufe, haka suka shiga motar ba tare da kowa yayi magana ba har suka kai gidan.
Faruk kam da Babanshi mutuwar tsaye sukayi, mamaki ya gama kashesu a wurin, tabbas akwai wasu abubuwa a cikin rayuwar gidan, da alama arzik'i ne Allah ya musu amma babu kwanciyar hankali.
_Wallahi da auren wani mai kud'in gwara auren talaka in dai da kwanciyar hankali, Allah ka k'ara mana kwanciyar hankali da ni'ima a qasarmu dama sauren qasashe baki d'aya._
*********************
Gida suka koma dan sunga babu alamun nasara, amma duk da haka Baba bai hak'ura ba yace koma da safe ya shirya ya tafi gurin aikinshi kamar yanda ya saba, watak'ila idan da rabo ma ba zata masa magana.
*Luv you guy's*😍
06/08/2019 à 00:06 - Meerahgee❤: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_My BK, kiyi sauri ki dawo fa._
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
_Bismmilahir-rahman-rahim_
*Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yace* " _Kaji tsoron Allah a duk inda kake_"
*Rawahu muslim*
3⃣
Tunda ta shiga d'aki wanka tayi ta saka kayan data saba sakawa wato k'aramin wando iya cinya da k'aramar riga, zaune tayi akan gado tana tunanin abinyi, har akayi sallah magrib da isha amma bata tashi daga in da take ba, wani tunani da tayi yasa ta tashi ta fito daga d'akin, duk da duka iyayen nata na zaune a falon amma babu wanda ta kula bare ta masa magana, farfajiyar gidan ta fita, masu tsaron mahaifinta ne zaune a kusa da mai gadi suna hira, tsaye tayi nesa dasu cike da raini tace "kuzo nan."
Kallon juna sukayi cike da raini suka tashi a kasalance suka nufi wajenta, tsaye sukayi kowa ya d'auke kai babu mai kallonta, cikin jin haushi ta daka musu tsawa "kai, ni kuke wa wannan kallon? to ku saurareni da kyau kuji aiki zan saku."
Shirun da sukayi yasa ranta ya sake b'aci , a harrzuk'e ta shak'o uwan rigar d'aya daga cikinsu tana fad'in "kai matsiyacin banza, ku har kun isa ina magana daku kuna wani d'auke kai, ko kun manta k'ark'ashin mahaifina kuke, kufa ba komai bane face maqasqanta wanda suke wuni dare da rana a bayan iyayenmu domin tsare lafiyarsu, yaushe kuka fara tunanin kuna da matsayi da har zaku rainani?"
Mai sauk'in cikin sune yace "kiyi hak'uri Hajia, ki fad'i aikin da zamu miki."
Tureshi tayi yayi baya baya kamar zai fad'i sannan ta kalli wanda yayi maganar tace "ku nutsu ku jini da kyau, akwai wani saurayi da nake so ku d'auko min shi gobe, ina so ku kaishi d'aya daga cikin gidajen Papa, idan kun d'aukoshi saiku kirani zan sameku acan, amma kafin nazo ku tabbatar kun canzamin kammaninshi ta yanda ba zai iya gane kanshi ba bare kuma wani."
Da hannu ta nunasu tace "kun fahimta?"
D'aya daga cikine yace "amma ta yaya zamu iya ganeshi kenan?"
Sai lokacin ta tuna da hakan, a wulak'ance ta kallesu tace "ku jirani anan, yanzun nan zan samo photonshi."
Binsu tayi da harara tare da fad'in "banzaye kawai marasa anfani."
Tana wucewa wanda ta shak'e ma wuyan riga yayi wani huci tare da rik'e gudu yana kallonta, a hassale yace "wallahi saina ma yarinyar nan rashin mutunci ta yanda gobe ba zata sake sha'awar wulak'anta wani ba, dan muna aiki qasan mahaifinta bashi ke nuna maqasqanta bane kamar yanda take d'auka, wallahi na gaji dan abinda take mana ko wannan banzan mashayin uban nata bai isa ya mana ba bare kuma ita banza."
D'aya daga cikine yayi dariya yace "toya zamuyi tunda Allah ya d'orasu akanmu, kuma da kake cewa zaka mata rashin mutunci, ita fa 'yar akuya kai kasan haka, kenan me kake tunanin yi mata?"
Da sauri ya bashi amsa da "dukan tsiya zan mata wallahi har saina sab'a mata kammaninta."
Shak'iyin cikin ne ya lashe baki tare da d'an cije leb'e yace "ku naku duk wasa ne, irin yaran nan ai duka baya gyarasu, karfa ku manta gatane ta gani shi yasa take abinda take so, ni wallahi ban tab'a jin wai na daketa ba, dan duka ba shine mafita ba."
"Miye mafita to? danni dai na gaji da rainin hankalin yarinyar nan."
Saida ya kalleshu yana murmushi kafin yace "kona fad'a ma ba zaku iya ba, dan haka ku barni kawai ni zanji da komai."
"Kamar ya ba zamu iya ba? ka fad'a in dai har za muyi maganinta wallahi za muyi."
Sake kafesu yayi da ido yace "kun tabbata?"
"Eh, ka fad'a kawai."
Ajiyar zuciya yayi yace "kullum tana cikin qananan kaya, hakan kuma na tayar min da sha'awata, abinda za muyi kawai mu takurata ta hanyar samun biyan buk'atarmu, ta hakane kad'ai zamu iya huce abinda ta mana."
Tuni d'aya daga ciki har shaid'an ya k'awata masa abin, cewa yayi "kuma fa hakane wallahi, dan shi fyad'e idan kayiwa mace ba zata tab'a mantawa ba har abada, kaga zamu tashi 1-1 mu da ita ,ita ba zata manta ba muma ba zamu manta irin wannan cin kashin data mana ba."
Hannu ya bashi suka bige suna dariya yace "da kyau mutumina ka fahimceni daidai, kuma ma wannan yarinyar ai da gani kasan ba mune zamu fara ba, da alama wasu sun rigamu kai da gani kasan ba budurwa bace, a idone kawai muke ganin haka."
"Gaskiya ne kuma."
"To amma ni gaskiya ina d'an jin tsoro, gaskiya ban tab'a yi ba tunda nake, kuma kaga za ayi binciki akan lamarin nan idan aka ganemu, kunga fa shikenan munyi asarar rayuwarmu mun b'ata k'uruciyarmu a banza."
"Bama za'a ganemu ba, ai za muyi anfani ne da kasancewarmu sojiji miyi aiki da ilimi, insha Allah komai zai wuce babu abinda zai faru, kuma muma ai bamu tab'a yi ba."
"To ya zamuyi kenan?"
"Abu mai sauk'i, kawai za muyi anfani da gidan rawar da take zuwa duk kwana uku sai muyi komai acan, kunga ta haka zamu fita daga zargi kuma babu wani bincike, domin kuwa cikin biyu dole suyi tunanin d'aya."
"Kamar me dame kenan?"
"Na farko za suyi tunanin kodai ita da samarinta ne da suka saba shek'e ayarsu, ko kuma dai tunda wajen rawa na b'ata garine , kaga za'a ce ta had'u da marasa jine kawai suka mata fyad'e wannan shine."
Cikin dariya d'aya ya bashi hannu yana fad'in "gaskiya Musa kanka naja sosai, wannan tsarin fa yayi."
Cikin dariyar mugunta yace "ko baiyi ba dole zan fito da wani, dan burina kawai buk'atata ta biya a kanta."
Musa ne yace " ku zama cikin shiri , dan ko yau bata fita saboda abinda ya faru, watak'ila kwana uku mai zuwa ta fita."
Da wannan shawara suka tsaya akai.
_Allah ya kiyaye_👏
Tana shiga d'aki wayarta ta d'auka a saman gado k'irar IPhone XMax, kira ta aikawa manager yana d'auka cike da salon bada umarni tace "ina so cikin 5 minute ka aiko min da adreshin gidansu yaron nan tare da photonshi."
Tana gama fad'a ta kashe wayar, zaune tayi tsakiyar gadon tana jiran shigowar sak'on manager, 2 minute saiga sak'on ya shigo adreshi da kuma photonshi, a hankali ta furta sunan unguwar tasu " *Bassora*"
Take ta tuna marin daya mata, bata san lokacin data goge photon ba daga wayar saboda b'acin rai, ajiye wayar tayi a gefenta ta fara sauke nunfarfashi ita kad'ai, jin qirjinta ya fara nauyi yasa ta tashi ta bud'a coffre ta d'auki maganinta tasha sannan ta koma gado ta kwanta, bacci harya fara d'aukarta wayarta ta fara k'ara, tana dubawa taga sunan *Macho* ya fito, d'auka tayi ta d'ora a kunne tare da jan zanin rufarta ta rufe tace "hello macho."
Daga d'aya b'angaren tace "yane macho? naganki shiru, yau kin fito ne?"
"A'a macho ba zan fito ba, kawai ki tafi kuji dad'inku."
"Haba macho, me yasa to ba zaki je ba? kin ganni fa harna shirya."
"Ba zanje ba macho, kije kawai, sai gobe naje."
"To in dai hakane, nima saina bari har goben sai muje kawai."
A daqile tace "wannan kuma matsalarki ce."
Tana gam fad'a ta kashe wayarta gaba d'aya ta koma baccinta, a cikin bacci taji kamar ana tab'ata, bud'a ido tayi taga mahaifiyarta ce ke shafar kanta sai kuma mahifinta daga gefenta a tsaye, cike da masifa ta tashi zaune tace....
"Meya kawoku nan kuma a wannan dar....."
Da sauri Mama ta rufe mata baki tace "kiyi hak'uri Khairat, na yarda nayi kuskure, amma ki sani mufa iyayenki ne dole mu damu da halin da kike ciki, mun kasa bacci saboda tunanin damuwar dake damunki."
A raunane ta kalleta tana shirin fashewa da kuka tace "Mamie, ya kike so nayi? kince na daina shiga harkarki kuma na daina, yanzu me kike so nayi to?"
Shiru sukayi kafin ta sake cewa "Mamie, ki fad'a min tunda muke dake kin tab'a nuna min soyayyarki, kullum hantara kike da yimin fad'a tare da kokarin aibatani, ban tab'a yin daidai ba a wajenki idan nayi ma bakya yabawa, babu abinda kuka koya min babu abinda kuke koya min wanda zai anfane ni, da fadanku na bud'e idona kune kullum cikin fad'a da aibata junanku, duk da kunsan matsalar da hakan ya janyo min amma baku daina ba, shin so kuke sai ranar da kuka bud'e ido baku ganni a duniya sannan zaku daina?"
Kuka Mamie ta fashe dashi tace "a'a Khairat, wallahi ina sonki, kinsan babu yanda uwa za tak'i yar data haifa, ni ina so ki zama yarinyar kirki amma mahaifinki bai damu da rayuwarki ba, ina damuwa da halin da kike ciki, kawai dai akwai dalilin da suka sakani nuna miki rashin kulawa, amma ki yafe min kinji yata ba zan sake nesantarki ba."
Ta fad'a tana rumgumeta, itama rumgumeta tayi cikin kuka tace "Mamie na riga dana b'ata rayuwata."
"A'a Khairat, kar kice haka, wallahi......"
Kafin ta k'arasa uban dake tsaye yace "wato kullum laifina ne ko, kullum burinki shine ki d'ora min laifi ni kad'ai ko? to wallahi baki isa ki rabani da yata ba muguwa kawai."
Kallonshi Mamie tayi tace "eh naji, in ni muguwa ce kai kuma fa? ai kaine babban mugu tunda duk kaine ka jefamu halin da muke ciki, kuma wallahi in har baka tuba zuwa ga Allah ba sai kayi *nadama*."
Matsowa yayi kusanta a hassale yace "wallahi kika sake magana a wajen nan saina tattakaki, saboda kin rainani ina fad'a kina fad'a ko?"
"Allah yana gani bai rainaka ba kaine dai ka raina kanka, kuma nasan Allah ma ba zai kamani da laifi ba."
"Ke..." wata k'ara da Khairat tayi yasa suka maida hankalinsu kanta, saukowa tayi daga kan gadon ta kama hannayen iyayen nata ta tisa k'eyarsu suka fita daga d'akin, saida ta kallesu kafin ta rufe k'ofar tace "ba zaku tab'a gyaruwa ba, wannan shine babbar damuwata, baku damu daku tozartani ba ko a dinga yayatani ba, a duk in da kuka samu kanku fad'a ku keyi da junanku."
Tana fad'a ta rufe k'ofarta ta koma gado ta dinga kuka da takaicin rayuwar iyayenta.
_Novel hausa akace, dan haka kuyi hak'uri 'yan uwa, ba zan sake saka muku wani harshe ba insha Allah domin kowa ya fahimta._
*Shin su musa za suyi nasara akan Khairat kuw*?
*Wai me yasa iyayen Khairat suke haka*?
*Meye matsalar da Khairat ke ciki?*
_Kafin sanin amsoshin bara mu koma baya mu fara sanin tushen labarin._
_Ku biyoni😍_
06/08/2019 à 00:06 - Meerahgee❤: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣
*TUSHEN LABARIN*
*Alhaji Mani Bukar* babban mutum kuma mai babban dangi, asalinshi haifaffan garin *Maradi* ne kasuwancine ya kaishi *niamey* daga nan kuma harya tsunduma siyasa, mahaifinsu mutum ne daya sha boko sosai ya k'oshi, hakan yasa yake da kula da takatsantsan da yaranshi, matan mahaifinshi biyu amma gaba d'aya yaranshi guda biyar saboda tazara da ake sawa, mahaifinsu irin tsofaffin masu kud'in nan ne, hakan yasa bayan rasuwarsa yaransa suka kwashi rabonsu bayan rabon gado.
Bayan rasuwar mahaifin sai kowa ya fara abinda yaga dama, haka ma Alhaji Ousmane wanda sukafi kiranshi da *Mani*, bana ce muku mutumin kirki ne ba amma dai yana da wasu manyan halaye wanda muke da tabbacin duk mai aikatasu, to tabbas babu abinda zai iya gagararsa kuma zai iya yin komai, wannan halaye kuwa sune *zina* da shan *giya*, duk da wannan halayen amma ubangiji ya masa talala ta hanyar k'ara sakawa dukiyarsa albarka, yana cikin holewarsa tare da abokai kuma sai Allah ya had'ashi da *Na'ima*.
*Na'ima Bilal Abdallah*, yarinya mai hankali nutsuwa da kuma tarbiya, ta samu duk wannan ne a wajen iyayenta saboda yanda suke tsaye a kanta, asalinsu mutanen *Arlit* ne amma aiki ya kai mahaifinta qasashe da dama tun kafin aurenshi da kuma lokacin da yayi auren harda cikinta ma, wanda daga qarshe dai a *India* aka haifeta, bayan wasu shekaru sai mahaifin nata ya rasu, kasancewar a ma'aikatar ana kula da ma'aikatan da kuma iyalensu yasa basu bari mahaifiyar da yarinyar sunsha wahala ba, sunci gaba da zama a gidan compagnie tare da d'aukar d'awainiyarsu, a lokacin tana da shekara ashirin suka zo Arlit ganin danginsu, wanda kuma suka tarar da auren cousine d'inta wacce za'a kawota Maradi, dole tasa suka zo anan kuma qaddararta ta fad'a dan anan suka had'u da Mani.
Tunda ya d'ora ido a kanta sai Allah ya jarabceshi da sonta har cikin zuciyarshi kuma karo na farko da yaji yayi sha'awar aure, Na'ima kam tunda ta ganshi ita kuma sai taji bai mata ba, bugu da qari da taji k'awayen amarya na fad'in halinshi na son mata saiya dinga lasar baki yana maka kallon iskanci, gashi kuma Allah ya masa muni dan babu wani abun birgewa a tare dashi, bak'i k'irin yake ga kuma k'iba da yayi saboda hutu, haka ya fara nuna mata abinda ke ranshi amma bata bashi dama ba, bayan shagalin ya kammala haka ya nemi sanin komai a kanta, rana kwatsam saiga Mani Arlit kamar daga sama.
In dai tak'aice muku, abinka ga mai kud'i wanda dama zamanin nan masu kud'i suke auren kyawawan mata, haka ya shiga ya fita tare da kutsawa duk cikin wani danginta mai ruwa da tsaki a kanta har saida ya samu Na'ima, babu irin kuka da bala'in da ba tayi ba ta kuma fad'a musu ba mutumin kirki bane, amma su basu ga haka ba dan yanda ya nuna musu, a qarshe dai amarya ta tare gidanta a Maradi, bayan qalubalen data fiskanta tun daga darenta na farko har zuwa sauran darare, bayan wani lokaci kuma sai suka koma niamey da zama to tun daga shi sai dai suzo gaishe da dangi Maradi da Arlit, bayan lokacin kad'an kuma sai mahaifiyarshi ta rasu itama.
Komawarsu niamey yasa ya k'ara tandarewa babu uwa babu uba babu mafad'i sai abinda yaga dama yake yi, kuka a wajen Na'ima harya zama jiki dan a wannan lokacin baya neman mata idan ba cikin gidanshi ba bayan ya shigo a bige, abun na matuk'ar damunta sosai ga rashin sonshi ga kuma bak'in cikin da yake d'ura mata, wani abin takaici shine lokacin data gama gane halinsa saita fara masa qiyo a shinfid'a in har ya nemeta, abinka ga mashayi kuma haka zai zage qarfinshi ya daketa son ranshi idan ta jikkata sannan ya turmusheta da qarfinshi ya biya buqatarsa, yarinya mai kama da indien sai gashi ta fara fita hayyacinta ta fara lalacewa, wata uku ta d'auka a wannan rayuwa, a lokacin data rame sosai saiya fara zargin ko cikine da ita shi kuma bai shirya hakan ba yanzu, daya tambayeta sai tace bata da komai dan itama bata sani ba, domin d'aukar mataki saiya fara bata qwayoyin hana d'aukar ciki, kwana uku da fara shan maganin saita fara ciwon mara kafin kace me sai jini ya fara mata zuba, bayan zuwa asibiti aka tabbatar ta cikin jikinta ya zube sakamakon shan magani ba abisa qa'ida ba , duk da taji tayi asarar beby amma kuma taji dad'i ko ba komai bata fatan haihuwa dashi.
Wata babbar dama ce ya bata dan tun daga lokacin saita fara shan maganin ba qaqqautawa, tun bai fara saka abin a kanshi ba harya fara damuwa saboda ganin an d'auki lokaci mai tsayi, wasa wasa sai gashi ta d'auki shekara biyar ba tare da nadama ko data sanin abinda take yi ba, a lokacin ne kuma Mani ya dakatar da ita tare da cewa ya shirya haihuwa, hakan baisa ta daina ba dan ranar ya shigo a bazata ya samu za tasha maganin, a ranar dukan tsiya ya mata bana wasa ba sannan ya karb'e duka maganin, cikin ikon Allah wata biyar saita samu ciki, amma kuma mai matuk'ar had'ari da wahala.
Saboda shan maganin data dinga yi yasa mahaifarta a had'ari hakan yasa cikinta ke buk'atar kulawa dan komai zai iya faruwa da bebynta, a lokacin da cikin ya fara girma aka mata scanning aka tabbatar da macace a cikinta, take sai Mani yaji qaunar yarinyar tun ba'a haifeta ba, visa ya samar musu suka koma India tare wajen mahaifiyarta wacce tafi jin dad'in zamanta acan.
A lokacin data haihu aka tabbatar da mahaifarta ta lalace ba zata sake samun wata haihuwar ba, babu yanda ta iya dole aka cire mata mahaifar domin rage mata nauyi, Allah kuma ya jarabcesu da son *Khairat*, da k'yar Na'ima ta dawo gida niger amma zamanta gaban mahaifiyarta ya mata dad'i sosai, dan tunda suka tai bai nemeta ba, sai dai daga yanda yake fita ya jima yasa take jin ya samu wasu masu d'ebe masa kewa.
*Rayuwa bayan haihuwar Khairat* tafi mata k'unci akan kafin haihuwarta, dan a wannan lokacin ya fara harkar siyasa, baya zama gida harkoki sunsha gabanshi, harkar mata ta k'aru sai dai shan giya ya d'an ragu sai daddare kawai, duk wannan bai damunta kamar yanda idan yayi shigowar dare yake ritsata a gaban Khairat ya nemeta, duk k'ok'arin da zatayi na samun dama baya barinta, haka zai kwanta da ita a gaban Khairat duk da tana bacci, ta d'auka kodan tana qarama ne yake haka duk da ba a hayyacinshi yake ba, amma sai gashi Khairat tayi wayo da girmanta da komai zai fara k'ok'arin nemanta, yarinyar ce kawai ke barin wurin saboda tsoro.
Duk da haka Khairat na ganin soyayya a wajen mahaifinta da k'auna , babu wanda ya isa ya harareta baiga wulak'anci ba gata take samu a wajenshi sosai, sai dai duk da haka takan ji tsoronshi kuma bata zuwan wajenshi sai inshi ya zo wajenta, ta fara karatu a ecole (school) d'in da tafi kowace a garin, sai dai duk k'ok'arin Na'ima na ya barta taci gaba da zuwa makaranta amma ya k'iya saboda ta fara zuwa ranar ta dawo tace malam ya daketa, bai bari ta sake zuwa ba kuma Na'ima data fara koya mata a gida, ranar ya samu tana kuka bayan ya tambayeta tace mama ta daketa dan bata iya karatun data koya mata ba, bayan fad'a da Na'ima tasha y kuma ce karta sake shiga harkar 'yarshi, saboda b'acin rai sai yasa Na'ima yin alk'awarinba zata sake kulashi da yarshi ba, idan Allah ya nufeta da shirya ta shiryu, idan kuma akasin hakane to matsalarsu ce.
_Kash, wannan ba mafita bace, duk inda aka je aka dawo ke uwace kin fishi asara , dan ko gidan aure taje za'a ce laifin uwane._
*Ranar talata* rana ce da Khairat ta kasa mantawa da iya duk da k'arancin shekarunta, mahaifiyarta na saka mata kayan bacci ya shigo, kamar dai yanda aka saba daga yanayin bud'e k'ofar ta gane waye da kuma halin da yake ciki, ganin yana yowa kanta yasa ta fahimci komai, tsaye ta mik'e ta tura Khairat gefe tace "kije d'akinki ina zuwa."
Kallonta Khairat tayi a matuk'ar tsoro ta kalli mahaifin nata, bayan mahaifiyarta ta koma ta b'oye, lokacin kuma ya kawowa uwar cabka ya fara k'ok'arin keta rigarta, sake turata tayi ta nufi k'ofa tace "kije nace ko."
Duk da tsawar data mata baisa ta tafi ba, wani mari ya kifa mata a cikin muryar 'yan shaye shaye yace "d'iyar tawa zaki ma wannan tsawar, ita sa'arki ce, nace sa'arki ce ita, tsararki ce da zaki mata wannan tsawar?"
Duk ya k'are tambayoyin ne da marinta, belt (ceinture) d'inshi ya fiddo zai fara dukanta Khairat ta fita a guje tana kuka, bakin k'ofar d'akin ta tsaya tana sauraren kukan mhaifiyarta da kuma sambatu da kukan mahaifinta keyi, kamar abu yayi sauk'i sai taji k'arar belt d'in nan da kuma kukan mamarta, ta tabbatar itace yake duka, kasa jura tayi kawai saita shigo d'akin a hankali, ganin mahaifinta babu komai a jikinsa haka ma mahaifiyarta kawai sai tayi k'ara mai tsanani ta fad'i qasa somammiya, shine ya fara kai mata d'auki kafin uwar tasa kayanta ta nufi wajenta itama, a daren ba suyi bacci ba ko kad'an bayan sun samu Khairat ta farfad'o, daga lokacin sai abubuwa suka fara canzawa amma fa na d'an wani lokaci.
Khairat ta daina walwala a gidan mahaifinta, tafi so ta zauna shiru ko kuma tasa écouteur (hearpeas) a kunne tana sauraro, Na'ima kuma ta fita harkarta daidai da gaisuwa bata had'ata da ita, ko abinci bata ce mata fito kici ta dinga nuna mata rashin kulawa, mahaifin kad'ai ke kulata ke kuma bata farin ciki.
Khairat nada *shekara sha shida* ta fahimci abinda iyayenta keyi a kowane dare wanda kesa mahaifiyarta kuka, kowane dare da abin sauraro take saboda kar taji abinda ke faruwa a wajen iyayen nata, a hankali sai damuwa da kad'aici da kuma tsoro yayi tasiri sosai a rayuwar Khairat, hakan kuma ya janyo mata matsanancin ciwon qirki da kuma ciwon kai dake damunta duk lokacin da ta shiga b'acin rai ko damuwa, bayan Mani ya fahimci hakan saiya kaita asibiti anan aka d'orata akan magunguna, amma matsalar ba daga ita bace daga garesu ne, ganin abin ba sauk'i yasa Mani ya mayar da ita india wajen mahaifiyar Na'ima, komawarta can kuma yafi mata kwanciyar hankali da jin dad'i, gata da lele ta sake samu acan saboda ita d'in ta zama 'yar gudaliya a wajen kakar tata, sannu sannu sai Khairat ta fara zama mai tsauri da rashin kunya kuma marar qaunar talakawa mai wulak'anci gana k'asa da ita, taci gaba da karatunta acan kuma ta shiga gidan koyan rawa wanda hakan baima Na'ima dad'i ba ,amma tunda tace ta daina shiga harkarta yasa bata mata magana ba, a kwana a tashi saiga Khairat har akan je da ita wajen concert ko wani competition na rawa kuma ta zama zak'ak'urar 'yar rawa da shugabansu ke ji da ita, soyayyar data fara da wani yaro abokin rawarta mai sunan *Rajveer* yasa hankalin Na'ima ya tashi lokacin da ta zo ganin mahaifiyarta, ganin basu da shamaki sukan tab'a juna ba tare da jin wani abu ba yasa bata tafi ba sai tare da ita, duk da ita bata so ba amma haka suka tafi, yayin da Raj yaji mahaifiyar bata gyara masa ba danshi yana sonta sosai.
*Shekara d'aya* da dawowarta kuma Mani ya mallaka mata wannan compagnie nashi a matsayin kyautar anniversaire d'inta na cika shekara ashirin da biyar, a lokacin ne kuma ta fara aiki a ma'aikatar, duka duka sati uku kenan da fara aikinta, amma gashi *Umar Faruk ya b'ata mata rai.*
*Luv you guy's*😍
06/08/2019 à 00:06 - Meerahgee❤: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
_Bismmilahir-rahman-rahim_
*BILQEES*
WANNAN PAGE TAKI CE, KE KIKA FARA COMMENT.
5⃣
*CI GABAN LABARI*
A hankali ta farka daga baccinta, saida ta tashi zaune tayi hamma sannan ta d'auki wayarta ta duba agogo, 10:40 tashi tayi ta fito sai dai bata sauko ba daga sama ta dinga hangen falon harta hango d'aya daga cikin mai aikinsu, daga saman ta kwallo mata kira "Biba."
"Na'am Hajia." ta fad'a cikin ladabi tare da zubewa qasa.
Juyawa tayi kawai ta koma d'akinta ta zauna saman gado tana wasa da kitson kanta, Biba ce ta shigo ta durk'usa tace "gani Hajia."
Kanta qasa tace "ki had'a min ruwan wanka."
"To." tace ta nufi bayin.
Saida ta gama had'a mata da duk wasu turaruka da take aiki dasu sannan ta fito ita kuma ta shiga, saida ta d'auki awa d'aya sannan ta fito daga bayin, d'aya mai aikin ta samu wacce take tayata shiryawa, kamar yanda suka saba yanzu ma hakane ya faru, da taimakonta ta shirya cikin riga da siket na shadda wanda suka kama jikinta sosai suka fito da k'irarta, d'an k'aramin gyale ta d'auka sai dai a d'aya kafad'a kawai ta d'orashi tare da rik'e jaka a hannu da wayarta sannan ta fita, a falo ta samu duka iyayen nata a tsaye da alama magana suke, wucewa tayi ba tare data kallesuba tace "da alama kun tashi lafiya."
Bata jira amsarsu ba tayi gaba, Mamie ce tace "Khairat abincinki fa?"
Bata ji ba bare ta amsa saboda ta rigayi da tayi nisa, motarta ta shiga k'irar RENGE ROVER ta nufi ma'aikatarsu da tunanin had'uwarta da Umar faruk.
Ai kuwa kamar yanda ta saba da shan k'amshinta ta shigo wajen, a gadarance take kallon kowa har saida idonta ya sauka akan Faruk, murmushi ta farayi tana takowa wajenshi har saida ta tsaya gabanshi, jin tattausan k'amshin turare a bayanshi yasa ya juyo a hankali, da sauri ya mik'e tsaye gabanshi na fad'uwa dan baisan me zai biyo baya ba, dama ya zone saboda umarnin mahaifinshi, cikin rainin wayo tasa yatsarta ta shafi sajen fuskarshi tana fad'in "Umar Faruk ko?"
"Sannu jarumi, sai dai kuma nayi mamakin ganinka anan, na d'auka ai ka daina aiki, amma kuma saina ganka nan, meya faru?"
Bata bari yayi magana ta kama mab'ullin rigarshi ta fara b'alle masa tana fad'in "karka d'auka ka mareni ka ci bulus kenan, ka kula da kanka dan babu abinda zai hanani *d'aukar fansata* a kanka ba, kayi abinda ko iyayena ba suyi ba, da wannan nayi alk'awarin cin mutuncinka ko ta wace irin hanya, ina fata ka fahimta?"
Wasa wasa ashe ta cire duka mab'allan rigarshi, saida ta wuce bureau d'inta sannan ya fahimci hakan, maida mab'allanshi ya farayi yana kallon mutanen dake kallonshi, saida kowa ya fara aikinshi ya sulale ya nufi bureau d'in nata, Habiba ce ta shigo tace yana son ganinta amma tace ta fad'a masa bata son ganin kowa, rok'on alfarma yayi akan ta barshi ya shiga, a gadarance tace ta barshi ya shigo, shigowa yayi yana kallon fuskarta har ya tsaya gabanta, saida ta kallesa rai b'ace tace "kayi kuskure, kafin ka bar nan wajen zan saka wani aiki."
Kud'i ta fito dashi 'yan goma goma guda uku ta bashi tace "karb'i wannan, kaje ka samu masinger ka tambayeshi komai akan abinda yake siyo min, saika siyo min dan banyi kari ba."
Wani kallo ya mata yana lumshe ido d'aya kamar zai sake bigeta amma saiya dake ya juya ya fita, haka yaje ya samu masinger ya tambayeshi, tsaf ya fad'a masa komai sannan ya hau mashin d'inshi ya tafi.
Cikin awa d'aya ya dawo, har bureau ya kawo mata ya aje, kallonshi tayi cike da mugunta tace "kaga plateau ( plate)can d'auko ka saka min."
Kallonta yayi amma babu yanda ya isa sai d'aukowa ya zo ya zuba mata, tura mata plate d'in tayi tasa hannu ta fara ci ya fito da kud'i ya aje gabanta tare da cewa "canjinki."
Fuska a had'e tace "aini bana karb'ar canji, ka rik'e wanjenka nasan zasu maka anfani."
Ganin kamar ba zai d'auka ba yasa ta kalleshi tace "ba kaji mena ce ba?"
Dauka yayi ya rik'e a hannunshi sannan yace "dan Allah kiyi hak'uri akan abinda ya faru, wallahi kuskure ne insha Allah ba zan sake maimaita kamarsa ba."
Saida ya gama ta kalleshi tace "ka d'auko min ruwa masu sanyi a fridge."
Yanda yayi tsaye baida niyyar yin abinda tace yasa ta jingina da kujerarta ta lumshe ido, idonta ya kalla wanda sukasha mascara sai sukayi kamar fossile, fridge d'in ya nufa yana fad'i a ransa "kyawunta hallinta babu kyan hali, ina ma zaki gyara d'abi'unki da kin more kyawunki duniya da lahira."
Daukowa yayi ya aje mata, cikin marairaicewa ya sake cewa "dan Allah kiyi hak'uri, wallahi idan na rasa aikin nan mahaifina zai iya yin hushi dani, ki taimaka min dan Allah kar....."
Katseshi tayi da fad'in "ka kira min manager."
Kallonta yayi ya kalli telephone d'in dake kusanta wanda anfaninshi kenan kiran wanda take so, juyawa yayi rai b'ace ya fita ya kira mata manager, tare suka shigo sukayi tsaye suna kallonta, ji yake kamar ya gaggabjeta da wasu marikan yanzu haka, kallon manager tayi tace "ka turo min takardar sallamarsa zansa hannu a kai da kaina."
Manager kallonta yayi ya kalli Faruk babu damar da zai bada hak'uri, cewa yayi "to Hajia."
Zai juya Faruk ya rik'e rigarsa yana kallonta yace "dan Allah kiyi hak'uri wallahi ba zan sake ba, da aikin nan na dogara, dan Allah karki koreni wallahi zanyi duk abinda kike so."
Wani murmushi ta saki ta kalleshi tace "ka tabbata za kayi komai?"
"Wallahi zanyi in dai ba zaki koreni ba."
Lotus ta d'auka ta goge hannunta ta jingina bayanta a kujera tana juyata tace "to ka durk'usa ka ban hak'uri, ni kuma saina yafe maka."
Shiru yayi yana tunanin abinda zaiyi, amma tuna hukuncin da Baba ke shirin d'auka a kanshi yasa yayi kasa da kanshi, a hankali ya sulale gwiwoyinshi ya zube qasa kamar yanda take so, kasa had'a ido yayi da ita saboda tafasar da zuciyarshi keyi, abune da bai tab'a faruwa dashi ba sai yau, haka kawai yaji hawaye na fitowa a idonshi dan Baba ko Mama ce kad'ai idan suka masa fad'a bada hakk'inshi ba yake sashi zubar da hawaye, ganin ya kasa furta komai yasa ta mik'e tsaye da wayarta a hannu tace "tunda ka zama kurma ni zan fita waje."
K'ofa ta nufa tana shirin bud'ewa yace "kiyi hak'uri."
Tsayawa tayi ta dawo ta zauna tana kallonshi tana murmushi, cike da raini tace "tashi, kaje gida ka kwanta ka huta, ba zan hak'ura cikin sauk'i haka ba."
Tsaye ya mik'e ba tare daya bari sun had'a ido ba ya juya ya fita,manager ma zai fita tace "zan turo maka da adreshin club d'in da zanje an jima, ka fad'a masa ya sameni acan."
"To Hajia."
Yana fita tayi dariya tace "zaka gane kuranka, zan had'aka da macho tamin maganinka."
Misalin *14:00* tayi parking a wata restaurant mai sunan *Amandine* dan taci abinci kafin ta wuce gida, saida taci ta k'oshi kafin ta mik'e zata fita, juyowar da za tayi sukayi karo da juna ita da wani had'add'en matashi, ware manyan idonta tayi ta kalleshi kafin ta fara k'ok'arin wuceshi, saurayin kam da yayi mutuwar tsaye saboda ganinta saurin rik'e hannunta yayi, a fusace ta fizge hannunta ta kalleshi tace "akan me zaka tab'ani?"
Saida ya kalli tsayayyan qirjinta ya lashe leb'e sannan yace "yi hak'uri, ban tambayi izini ba kafin na tab'a."
"Mtsssss." taja dogon tsaki ta wuceshi, biyo bayanta yayi yana kallon k'ugunta ya kasa magana, bud'a motarta tayi ta aje jakarta da wayarta sannan ta shiga ta tayar, zata fara tafiya ya tari gabanta yace "ko zamu iya yin magana?"
"Babu lokaci." ta fad'a tana sake taka motarta, rik'e k'ugu yayi yace "in baki bani dama ba, to sai dai mu kwana anan."
Murmushin gefen labb'a ta masa tace "sai dai ka kwana asibiti."
Tana fad'a ta tako motar ta nufo kanshi gadan gadan, ganin da gaske take yasa yayi saurin kaucewa sai dai ina saida motar ta bugi gwiwarshi, rik'e gwiwar yayi yace "kuttt, wannan fa yar akuya ce ta gaske." yaji zafi sosai dan da qyar ya taka qafar ya koma cikin restaurant d'in yana tunanin sanin ko wacece ita da kuma k'arasa abinda yayi niyyar yi a kanta.
Yana zaunawa akan kujera abokinshi wanda shigowarshi kenan a wajen kamar yanda sukayi akan su had'u anan, ko zaune baiyi ba yace "kai wa naganka da ita yanzu?"
Wata uwar harara ya wurga masa yace "wace tambayar iskanci ce kuma, daga zuwa ko zama ba kayi ba sai tambaya akan wata cika, wallahi tafi mu shed'anci wannan daka gani."
Zaune yayi yana kallonshi da mamaki yace "ba saika fad'a ba nasan da haka, ina so nasan meya had'aka da Khairat?"
Shima da mamaki ya kalleshi yace "ka santa ne, dan Allah fad'a min gidansu, wallahi saina tarfa yarinyar nan, kasan meta min kuwa?"
Tab'e baki yayi yace "koma meta maka in dai Khairat ce ta wuce haka, danta wuce duk in da kake tunaninta, ka ganni nan ko gaisuwa bata tab'a had'ani da ita ba, kuma unguwarmu d'aya da ita."
"Kai dan Allah, kenan itama a *Présidentielle* take? kenan kace babbar yarinya ce?"
"Sosai ma kam, kaga muyi abinda ya kawo mu."
"Kai, nifa wallahi yarinyar nan ta shiga raina kuma ni gaskiya."
"Gaskiya me? kai hin wallahi fita idona in rufe, karka ja mana abinda yafi k'arfinmu , karka d'auka mu yayan manyan mutane ne, to ubanta wallahi ya take ubanninmu ya jikesu ya shanye, domin kuwa d'iyar *Mani Bukar* ce."
Ido ya fiddo yace "ashe abun babba ne, ah dole tayi rashin mutunci saboda sune gwamnati."
D'ora mashi yayi da "kuma ga kud'i an tara mata."
Da haka suka rufe shafin maganar suka fad'a abinda ya kawosu , ita kuma tana kaiwa k'ofar gida ta tsaya saboda wani dattijo daya taho kanta da dugu gudu yana mata sannu da zuwa, kashe motar tayi ta fito a kasalance tana wani yak'una fuska, duk gaisuwar da tsohon keyi babu wacce ta amsa saida yayi shiru tace "lafiya ko?"
Cikin muryar kuka ya fara magana "Hajia dama 'yata ce ke asibiti babu lafiya, mun kaita an rubuta mana magani, sai dai bamu da halin siyan maganin, shi yasa na zo ki taimaka mana kamar yanda Allah ya taimakeki."
Takardar dake hannunshi tasa hannu ta amsa ta bud'a, saida ta d'auki kusan 2 minute sannan ta kalleshi tace "Baba, me yasa kuka yiwa yarinya aure da qananan shekaru? yanzu gashi kun jefa rayuwarta a matsala, ina mijinta yanzu?"
Cikin kuka dattijon yace "ai tunda ta kamu da ciwon yoyon fitsari mijin ya saketa."
Ajiyar zuciya ta sauke ta mika masa takardar ta bud'a motarta ta d'auko jakarta ta fito da kudi, mika masa tayi tace "na duba kudin maganin, jikka talatin da shida da rabi ne, nan kuma jikka hamsin ne, kaje ka siyi maganin sauran kuyi wani abun dasu, idan kuma wani abun ya taso kayi gaggawar zuwa ka sanar dani."
Tana gama fad'a ta shige motar mai gadi ya bud'e mata ta shige ciki, godiya sosai dattijon keyi mata yana hawaye tare da saka mata albarka, wani abu daya k'ara birgeshi shine, wannan shine karo na biyu daya zo neman taimako kuma ta taimaka masa.
_Duk da Khairat bata da halin qwarai, amma akwai wani babban arzik'i da Allah yayi mata, shine *taimako*, duk wanda Allah ya bawa zuciyar taimako to hak'ik'a yayi dace, dan ko baya da abun bayarwa zaiyi iya qoqarin da zaiyi yaga ya kyautatama wani, wani kuma idan Allah bai bashi zuciyar taimako, sai kaga Allah ya wadatashi da abin duniya amma sai yaji baya iya cire ko sile ya taimaki wanda baya da, Allah ka wadata zuciyarmu._
Babu kowa a falon sai masu aiki a farfajiyar gida suka mata sannu da zuwa, kai tsaye d'akinta ta nufa ta cire kayan jikinta ta watsa ruwa ta saka kayan da tafi so, wayarta ta d'auka da abin sauraro ta laka a kunne sannan ta fito da silipas a qafarta, Mamie ta samu zaune a kujera tana kallo, zaune tayi kusanta tare da fad'in "sannu Mamie."
"Yawwa sannu, yaushe kika shigo?" cewar Mamie cikin sakin fuska.
Ita kam mamakin ganin sakin fuskar yasa ba tace komai ba, sake cewa tayi "kinci abinci kuwa?"
"Naci abinci kafin na shigo."
Janyo kanta Mamie tayi ta d'ora saman cinyarta ta fara shafar kanta, mamaki duk ya ishi Khairat dan rabon da haka ta faru harta manta, sun jima a haka kafin Mamie tace "ni kam Khairat wai sai yaushe zaki kawo mana sirikina ne?"
Gyara kwanciyarta tayi ta fuskanci Mamie tace "Mamie, nifa har yanzu ban shirya aure ba saboda ban samu wanda ya dace dani ba."
Cikin zolaya Mamie tace "haba gimbiyar Papa, yanzu duk samarin nan naki ace babu wanda ya dace dake? amma ai naga duk kyawawane masu aji da ilimi, ki duba kiga d'an uwanki fa Mujahhid, ga kuma *Muzaffar* ga *Ahmadi*, ace duk cikinsu babu wanda ya miki."
Tashi tayi zaune tace "Mamie, Mujahhid bai dace dani ba, eh shi kyakyawane ajin farko amma idan na auresa zanyi irin rayuwar da ki keyi ce yanzu, Muzaffar kuma yana da wani hali da ban sonshi, yana da son mata da kuma qyamar talakawa, Ahmadi kuma gaskiya shi yana da babban familly ne masu yawa, ni kuma ba zan iya d'aukar kwaramniyar danginshi ba."
Komawa tayi ta kwanta qafarta tana fad'in "kawai kici gaba da min addu'a na samu wanda ya dace, ni ban damu sai mai kyawu ba, ina son samun namijin da kallo d'aya zaka samu tabbacin lalle cikakken namiji ne shi."
Mamie dai bata sake magana ba tana saurarenta tana biyar wak'ok'in da take saurare har bacci ya d'auketa, ci gaba tayi da shafar kanta bata gushe a wajen ba har saida la'asar tayi ta tashi sannan tace taje tayi sallah itama ta nufi nata d'akin dan yin sallah.
Misalin *22: 30* ta fito cikin shirin tafiya club, kallonta Mamie tayi sosai tace "Khairat dan Allah ki zauna gida karki fita wurin nan bai dace ba."
Cikin sakin fuska tace "karki damu Mamie, akwai wanda zamu had'u dashi ne, ba jimawa zanyi ba."
Tana fad'a ta fita ta shiga motarta, tana d'aukar hanya su Musa suka bi bayanta cikin bak'ak'en kaya da rufaffiyar fuska ta yanda ba zata iya shaidasu ba, a hanya kuma ta turawa manager adresse d'in in da Umar zai sameta, sannan ta kira macho amma sai tace tuni tana wajen.
_Allah ya kareki Khairat._
06/08/2019 à 00:06 - Meerahgee❤: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
_Bismmilahir-rahman-rahim_
*Alhamdulillahi lazi ahyana ba'ada ma amatana wa illaihi-noushour.* _Addu'a tashi daga bacci._
6⃣
Umar Faruk na k'ofar gida saman dakali yana chat yaga sak'on manager, zaune yayi daga kishingid'ar da yayi yana kallon sak'on, bud'ar bakinshi yayi yace "kodai akwai abinda yarinyar nan ke nufi danine, me yasa ba zamu had'u a wani wajen ba?
Ganin babu wata mafita yasa ya shiga gida yayi wanka ya shirya cikin kayan da yafi ta'ammali dasu qanana, turarenshi ya d'auka *Gold* ya fesa bayan yayi anfani da *nivea men* sannan ya d'auki makullin mashin d'inshi ya fita, yayi doguwar tafiya kafin ya isa club d'in, yana sauka daga mashin d'in ya hangi motarta, tsaki yayi sannan ya nufi k'ofar masu tsaron k'ofar ne suka tareshi, ganin kallon da suke masa yasa kafin suyi magana yace "Khairat na ciki?"
D'aya ne yace "kaine Umar Faruk?"
"Eh nine." ya fad'a yana hararensu.
Bud'a mashi hanya sukayi ya wuce, yana shiga yaji ranshi ya sake b'acewa, hayak'i da wari ne kala kala na kayan shaye shaye, ga masifaffen kid'in dake tashi duk da a wurinsu mai tab'a zuciya ne, yanda mata da maza ke cakud'e ya sake harzuk'ashi wasu tsirarane kawai baka kirasu amma da kayan dake jikinsu basu da maraba da tsirara, ga hasken wurin mai jane sai sauran fitilun dake bayar da haske mai kala kala, haka yake kutsawa yana shiga har ya tsaya cak saboda hango Khairat da yayi, tsakiyar fili take tana tik'ar rawa abinta tare da wani dogo kuma had'add'en guy, tabbas ta iya rawa sosai dan daga yanda take sarrafa jikinta zaka gane haka, shima matashin da alama ya iya rawar sosai, abun haushi shine yanda suka rik'e da juna suna tab'a jikinsu duk yanda suka so har wani cirata yake sama, ran Faruk kam k'ara b'acewa yayi daya kalli kayan jikinta, rigace a jikinta bak'a mai kyau da walk'iya amma mai siraren hannaye iya cinyoyinta, duk wutsilniyar da take har pant d'inta na ciki ake gani fari shima bai wuce cinyarta ba, balerine ne a k'afarta sai dogayen kitsonta data sakeshi yake kad'awa yanda yake so shima, kid'in da suke takawa ne ya zo qarshe dan haka suka k'arar da kid'in tare da rungume juna suna sauke numfashi, tapi aka musu da shewa sannan suka raba jikinsu dana juna, sakinshi tayi zata koma mazauninta ya fizgota ta sake komawa qirjinshi, kallon juna suke kamar daga sama ya kalli kwayar idonta yace " *ina sonki* Khairat."
Yana fad'a ya kai bakinshi a nata ya sumbata, da sauri ta raba bakinsu tana kallonshi, amma saita kasa cewa komai ta nufi mazauninta, babbar kujerace a wajen ita kad'ai zaune, haushine ya nemi kashe Faruk dan haka kawai yaji ranshi ya matuk'ar b'acewa, jiki a sanyaye ya fara d'aga qafarsa zai nufi wajenta, cak ya sake tsayawa saboda wani sabon saurayin daya zauna kusa da Khairat suka rumgume juna, da alama babban yaro ne dan harda masu tsaronsa a bayanshi.
K'ura masu ido yayi yana kallo cikin takaici yana ji kamar zuciyarshi zata fashe, a hankali ta raba jikinta da nashi, kallonta yayi yace "Khairat, me yasa baki so ina kusantoki?"
Saida ta harareshi tace "to me yasa kai kuma saika kusanceni, mu zauna a haka mana."
Cikin wata irin murya yace "Khairat ba kowa bane zai iya, in dai namiji lafiyayyene ya ganki dole yaso kasancewa dake, wallahi Khairat kasa bacci nake, kece ke zuwa min a cikin tunani na."
Hannu ta d'aga masa tace "kaga Muzaffar, nifa saboda kaine yasa har yanzu na kasa tsayawa waje d'aya, kullum da club d'in da nake zuwa amma na rasa ta yaya kake sanin in da nake, me yasa kake takurawa rayuwata ne, dan Allah ka rabu dani bana sonka."
Kasancewarshi mutum ne mai saurin fushi kawai saiya mik'e tsaye yace "ke baki isa ki wulak'antani ba wallahi, ina sonki Khairat kuma ko zaki mutu wallahi saina mallakeki koda kuwa bayan darenmu na farko zamu rabu dake."
Tsaye tayi itama tace "oho, kenan burinka kawai daren farko, kaga ka nuna min kai jikina ne kawai a gabanka, to kaji wallahi yafi k'arfinka har abada ba zaka sameni ba."
Baiyi magana ba sai wucewa da yayi da k'arfi har saida ya bangaje Umar tsabar hushi, binshi da tayi da kallo yasa ta sauke idonta akan Umar Faruk dake kallonta, da d'an yatsa ta masa alamar ya taho, takowa ya farayi sai dai d'uffff, wutar wajen ta d'auke, wayoyi wasu suka fara k'ok'arin kunna fitila kafin haka ta faru kuma, Musa ya toshe bakin Khairat ya d'auketa daga wajen.
Kasancewar sun shirya abun hakan yasa babu wanda ko yaji faruwar wani abu, bayan 'yan mintuna wutar ta dawo amma babu Khairat a in da take, rik'e kugu Faruk yayi yace "dama danta raina min hankaline yasa tace na zo nan."
K'wafa yayi tare da juyawa ya fita daga wajen, k'awarta kam tana can tana soyewarta bata san wainar da ake toyawa ba, tafiya yake akan mashin d'inshi yana tsaki yana sake hangota a jikin mazan da ba maharramanta ba, k'ok'ari yake ya share kawai amma ya kasa sai dawo masa take a kwakwalwa.
Kallon motar dake gabanshi yayi ganin yanda take gudu, yana kallo har motar ta shiga wata kwana ta ratsi wata hanyar kamar zata bar gari, wucewa yayi shima amma abun mamaki saida ya sake juyawa ya kalli motar sai yaji gabanshi ya fad'i, tsayawa yayi yana kallon da motar tabi kawai kuma saiya tayar da mashin d'inshi yayi gaba abinshi.
Tunda yaje gida ya shiga d'akinshi kasa samun nutsuwa yayi, haka kawai yake jin gabanshi yata fad'uwa ba kuma shine abinda yafi damunshi ba, shine yanda Khairat ta kasa barin tunaninshi, ganinta kawai yake a idonshi , kasa samun nutsuwa yayi sai gashi ya raya darenshi da tunani da k'ara jin tsanar Khairat da haushinta, ba kamar yanda ya saba rayashi da anbaton ubangijinshi ba.
Wani gida suka kaita suka jefata saman k'aramin gadon dake ciki, tun a cikin mota suka d'aure mata baki da qafafu lokacin da zasu d'aure mata hannuwa saita fara kokawa dasu, hakan yasa ba tare da tausayi ba suka bank'are mata hannu har saida taji k'arar hannu kuma ta tabbatar ya karye, tana ganin sun jefata ta fara kallonsu cikin tsoro sai dai ba zata iya fahimtar kosu waye ba, so take tayi magana amma ina babu baki sai gunguni kawai kake ji, baya baya ta fara ja daga kwance saboda ganin d'ayan yana nufota yana zare zip d'in wandonshi, kuka ta fashe dashi mai tsanani tana ci gaba da ja baya kamar tafiyar tsutsa, kusan fad'uwa tayi hakan yasa Auwal dake bayanta ya turota da k'arfi ta dawo tsakiyar gadon, Musa na ganin haka ya k'arasa janyota ya haye sannan ya kallesu yace "ku bamu wuri ko, zan kiraku."
Wucewa sukayi Bello na fad'in "saura kuma ka kwashe komai ka barmu."
Suna fita ya kwance mata d'aurin qafafun ya bud'e qafarta da k'arfi yana shirin zare pant d'inta, k'ok'arin tashi tayi saiko ya kama gashinta ya fizgota , fashewa tayi da k'ara sai dai bata fito ba ma bare aji, cikin jin zafi tasa qafafunta ta fara harbinshi, shima cikin b'acin rai ya wanketa da mari ya kuma janyo kanta ya had'ashi da kan gado, tuni kanta ya fashe sai jini duk da haka bata sasuda ba tayi nasarar yakushinshi ta bayan hannu, saboda dogayen akaihu da tasa yasa har saida jini ya fito masa, ai kuwa sai yasa hannu da iya karfi da tsabar mugunta ya fizgo akaihun, wani ihu ta saki saboda azabar da taji, akaihunta uku ne suka fita tare da asalin akaihunta, shak'e mata wuya yayi ya sunkuya cikin kunne ya rad'a mata "zaki mutu a banza kuma ba zamu fasa abinda mukayi niyya ba."
Yana fad'a ya janye pant d'inta daga jikinta, ware qafafunta yayi ya fara k'ok'arin shigarta, bille bille take tana kuka amma ina ko saurarenta baya yi, hanya yake nema amma abun ya gagara, ya d'auki lokaci yana so ya shiga amma shiru, ganin abun bana lafiya bane yasa ya sake buda qafafunta sosai har saida magangamar cinyarta tayi qara, da gaba d'aya karfinshi ya tusa kanshi ciki, duk da bakinta d'aure yake amma data fasa ihu saida sauran dake waje suka ji, ganin ya samu hanya saiya fara aiki tuburan.
Saida ya nutsu sannan ya barta, yana fita d'aya ma ya shigo a haka suka dinga shigowa d'aya bayan d'aya har suka kammala, kuma duk wanda ya shigo cikinsu saiya nemi k'ofarshi da kanshi saboda matsewar da take, wannan itace hallitar Khairat, tun tana motsi harta daina gaba d'aya bata san meke faruwa ba, tsaye sukayi akanta suna kallonta Bello yace "wallahi ban d'auka budurwa bace da ban fara ba."
Musa ne yace "kai dallah fita harkarta, ba dai mun gama ba, to ku tsaya ku gani."
A hankali ya cire belt d'in k'ugunshi kafin suyi magana harya fara labta mata shi, tambayarshi suke me yasa amma bai iya ce musu komai ba, saida yaga ya mata ligaliga harta sauya kammani sannan ya maida belt d'inshi ya kallesu yace "ubanta da yake lalata 'ya'yan wasu aishi baya musu haka, kuma duk lokacin da za'a rama mugunta to ka rama fiye da wacce aka maka."
_Wannan ba gaskiya bane, ba kuma koyarwar shari'a kenan ba, Allah ka shiryemu shirin addininmusulunci_
K'aramar rigarta data yagalgale cire rigar sukayi suka kwasheta a haka suka fita da ita, a mota suka sata bayan sunyi tafiya mai nisa suka tsaye, Musa da Auwal ne suka fito suka kamota, a gefen hanya suka jefar da a ita suka tafiyarsu.
😭😭😭😭😭😭😭
Kwance take kamar gawa babu alamun rai, a haka ta zauna bakin titin na tsawon lokaci, sallah asuba tasa mutanen dake wajen suka fita sukayi sallah, wani dattijo ne da gidanshi ke bakin kwalbati yazo tsallakawa da fitila a hannu yaga mutum kwance tsirara, tsorata yayi da farko amma saiya daure ya sake haskawa , gaba d'aya yaga mutum duk da kalarta harta fara sauyawa , nan ya fara kwaroroto yana d'aga murya har mutane cikin gida da waje suka hallara.
Nan fa suka fara shawarar yanda za ayi, wani matashi ne mai zafin nama ya k'arasa wajenta, rigarshi ya cire ya rufe mata k'asanta zuwa k'irji, kallon mutanen yayi yace "dan Allah ku samo abin hawa mu kaita asibiti."
Basu b'ata lokaci ba suka suka samu mota aka saita suka nufi asibiti da ita koda ta mutu ma sai a nemi danginta.
0 comments:
Post a Comment